A Dalilin So 1 To End-1

Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 175

[5:07PM, 7/13/2017] +234 706 196 7803: 1)

A DAREN FArko
kotun ta yi tsit, kowa ya yi jigum, ana sauraran abinda xai fito
daga bakin alkalin wanda yasunkuyar da kansa yana rubuce-
rubuce.
Lauyoyi dasauran ma,'aikata wadanda suke da alhakin zama a
kotun sbda sauraron shari'ah, kowanne yana xaune a
mazauninsa daya dace dashi,haka yan kallo da iyayen yarinyar
da ake gudanar da shari'ar a kanta al'amarin yan ba kowa
tausayi shiyasa indai mutum yakalli fuskokin kaso tara cikin
goma na mahalarta kotun sai kaga kowa cikin matsananciyar
damuwa musamman wadanda abin yashafa, iyayenta da yan
uwanta knan.
Mai shari'ah usman muhammad yadaga kansa a hankali
yadubi wacce ake ka ra tana tsaye inda ake tsaida wadanda
ake tuhuma hannayenta biyu sanye da ankwa.
Bakar rigace a jikinta da bakin hijjabi sanye akanta, ba
dankwali idanuwanta sunyi wani irin ja saboda tsabar kuka, ba
ta son dago kai tadubi kowa saboda tsanar kanta datayi don
haka ma da alkalin yakira sunanta bata dago kanta ba ta dai
amsa cikin dashashiyar murya wadda da kyar ake iya jin
abinda ake fada.
Alkalin yakuma cewa "Fatima Musa"
Ta amsa "Na'am"
"Ke kika kashe doctr Abubakar saddik wanda akafi sani da
doctr khalifa???
Fatima tayi shiru alkali yana maimaita tambayar har sau uku
batayi magan ba, yadda kasan kotun ba kowa saboda tsabar
shiru, koda fatima da mai shari'a yake kallo ana sauraron
abinda fatin xa tace amma taja bakinta tayi shiru kamar dam
chan yadda Llah yahalicce ta ba ta da bakin magana.
Mai shari,'a Muhammad Bamaina yana magana cikin yanayi na
tausasa harshe yace "Fatima kotu tana tuhumarki da laifin
kashe mijinki Dr. Khalifa kamar yadda ka kamaki da gawarsa
shiyasa muke son ki bayyanawa kotu gasjiyar al'amari da
bakinki tunda ke ba bebiya bace kuma ba kurma bace kina jin
abinda muka fada kuma kina iya magana.
idan ke kika kashe shi kifadawa kotun sannan kifadi dalilin
dayasa kika kashe shi, idan ba ke bce ba to kidanyi magana
kiyi bayani.
Fatima tadago kanta a karo nafarko tadubi duk jama'ar kotun
suka hada ido da mahaifiyarta wadda tazuba tagumi dukda
nisan dake tsakaninsu da Fati, Fati ta san kuka take wiwi tana
girgiza kai, Fati tadubi mai shari'a sai kawai taj kanta yana
juyawa kafafunta suka shiga rawa, hakan yasa suka gaza
cigaba da daukar gangar jikinta tazube a gun, nan take mai
shari'a Usman M Baina yadaga shari'a zuwa uku ga watan
gobe idan Allah ya kaimu.
Kotu tarude da hayaniya, koke koken iyayan fati da yan uwanta
ya cika kotun ga uar uwarsu a matsananciyar hali amma ba
yadda xa ayi su taimaketa, sunaji suna gani wasu yan sanda
mata suka daga fati aka fice da ita da gaggawa sbda
numfashinta ne yake sama saa kamar zai dauke.
*******×*×***********×***×******×**
Yammaci ne akalla za mu iya kiran lokacin karfe biyar na
yamma dawasu mintuna, ummi na zaune gefen tabarma ta
hada kai da guiwa tana kuka kamar ranta xai fita, goggo Abu
ne gefenta itama tana goge hawaye cikin yanayi na tsananin
damuwa kobaka sansu ba kaga halin dasuke ciki sai ka tayasu
wnnan kuka dasuke, ko ba a maka bayani ba ka san damuwar
daxata sa a yi irin wannan kuka ya isa a tayashi kuka.
Malam musa yashigo da carbi a hannunsa yayi sallama
yatsaya chan daga bakin kofa yana kallonsu tsawon mituna
biyar sanan ykaraso inda suke ,Allah sarki bawan Allah mai
saukin kai wanda bai dauki duniya a bakin komi ba, fuskarsa
cike da tausayi da karaya yake kallonsu ya ka sa magana, xuwa
chan goggo Abu tagoge hawayenta cikin karfin hali tace
"Malam ka dawo?? sannu daxuwa.
Ya daga mata hannu yace ba na son gaisuwar ta kui tunda
idanuwanku baxasu daina xubda hawaye ba akan abinda ba xai
yi mana amfani ba. kokuwa wannan kukan xaiyi mana magani
akan damuwar damuka samu kanmu aciki??
Goggo Abu tace "Mala to yaya xanyi tunda abinnan yfaru ummi
bata daina kuka ba. na yi lallashin duniyar nan yarinyar nan ta
ki daina kuka har na rasa wacce kalma xan gaya mata wanda
xa yasa tayi hakuri.
Malam yace "Ummi kiyi hakuri ko mu damuka haifi fatima babu
abinda xa mu iya akan wannan lamarin sai dai addu'a.
Cikin matsananciyar damuwa Ummi tace "Shin baba shikenan
daga hakuri babu abinda xa ku iya gaya min wanda xan samu
sassauci a xuciyata game da halin da fatima take ciki???
Wyyo Allah kaicon rayuwata ni ummi in har xan xauna ina
rayuwa a cikin tunannin fatima na kulle a kurkuku ana
tuhumarta da laifin dani daku daduk duniya sun san baxata
taba iya aikata shi ba.
Ya ya xa ayi ace fatima xa takashe rai, kisan ma ace tarasa
wanda xa takashe si mijinta? kadubi wannnan al'amari ayi wani
abu akai har yaushe muna zaune fatima na cikin mummunan
zargi irin wannan".
Malam. musa yai xaman dirshan a wurin yace "Ummi toh yaya
xamuyi? Saboda girman Allah me kike ganin xa mu iya yi
kinsan indai ace muna da bakin yi din da yanxu ba wannan
xancen akeyi ba.
kinsan mudai ba kudi garemu ba, kuma ko idan mutum na da
kudi idan akace case din me xafi ne da tsanani irin wannan ba
ka da tacewa, kudinka ba xa suyi amfani ba dan ba xa su sayi
ran da aka kashe ba balletana kasiya domin ko da ke biyan
diyya idan wani yakshe wani ba a irin wnnan yanayin ake biyan
diyya ba kinsan ita shari'a sabanin hankali ce, duk yadda kaje
tunaninta ta wuce nan.
Kuma idan ma muna da abin yin a yanxu ba xa mu iya ba idan
Fatima ba ita takashe docta Khalifa ba tai magana man a kotu,
kinaji kina gani daxu a kotu ka sa magana tayi ,tayi shiru
tabude bakinta tace ba ita takashe shi ba tafdi yadda abu
yafaru akalla idan ma akwai abinda za a yi ai a yi tunda tayi
shiru me za ace??
Yagirgiza kai cikin dan zuciya yace "Allah kadai yasan yadda
wannan abu yakasance sai kuma fatima.
Ummi taciji yatsa har yanxu kuka take mai ciwo a rai tace "Shi
kenan baba shikenan goggo tunda kuma kun yarda fatee ita
takashe doctor sai kusa ido itama a kasheta ba tare da
hakkinta ba, amma dai inaso kusani ko ku kuka haifi mutum to
ba kune kuka halicceshi ba yadda kake da hakkin yayi ma
biyayya haka shima yanada hakinsa akanka idan kadanne Alah
subhanahu wata'ala xai tuhumeka baba.
Nikam ba xan bar maganar fatee tawuce haka ba ,ba xan bari
acigaba da xalintarta akan abinda bata aikata ba, zan shiga
infita ko xan rasa zanin daurawa sai na taimaki Fati Insha
Allahu.
Malam yace ummi ba na shakku akan abinda kika fada mun
tabbatar xa ki aikata fiye da abinda kik fada akan fatima
kaunar dake tsakananin ku ya wuce a fadadeta da baki, Allah
kadai yasan iyakacinta, sai dai inason kisani ba wai mun yarda
cewa fati itace ta aikata kisan ba, kifahimci wani abu day
ummi ba mu da kudin daxamu iya daukan lauya daxai kare fati,
ba ki da bukatar mugaya miki halin damuke ciki na kaka ni ka
yin rayuwa a gidannan kinsan kome da ina mukaga halin
daukar lauya sannan idan ma mun dauka dawacce hujja xa
mufidda fati daga wannan zargi tunda ta ki magana? wannan
shi ne a dalilin dayasa muka mikawa Allah lamuranmu, idan
fati ba ita takashe likita ba insha Allahu Llah xai bayyanar da
gaskiyar alamari Allah xi kawo mana mafita.
Ummi duk wanda na sa yashiga matsanancin hali irin wannan
ya gama kwanciyar hankali kada kidauka bamu dmu da ita ba
illa iyaka shi lamari irin wannan idan kaga kanka acikinsa ba ka
tsananta damuwa wadda ita dama rayuwa jarravawa ce
acikinta, idan Allah yajareba ka dawani alamari kagode masa
kawai karokeshi yabaka juriyar cin wannan jarbawa dayayi
maka domin ba wanda ya isa yakaucewa jarabawar Ubangiji .
kiyi hakuri ummi.
Ta jinjina kai yace "Na hakura baba, na hakura dakuka na
hawaye, tunda ba ka son ganin hawayen saidai ba xan iya
hakuri da fati ba ko da nima xan shiga halin datake ciki, ko
nima xan rasa raina, idan ba halin daukar lauya ai muna da
halin daukar akwai guraren da ake taimako a samu agaji su
taimako ne a gabansu kawai a gabansu ba kudi ba, su ake kira
gatan mara gata"
Goggo tace"Allah shi ne gatan mara gata shi xai xama
gatanmu, Ummi kiyi hakuri"
Tayi murmushin karfin hali tace goggo nakanyi mamakin masu
cewa inyi hakuri akan maganar fati, wa yace banyi hakuri ba?
Tabbas na yi hakuri domin na hakura daduk wani farin ciki
Insha Allahu akan nemawa fatee hKkinta sai inda karfina
yakare ko da hakan shi xai kasance abinda xan aikata
nakarshe a rayuwata".
***********************************
Suna a wani dan daki mara girma Ummi da Barrister Nuruddin
,aka bude kofar dakin wani kakkauran dan sanda ne a gaba
fuskarsa ba fara'a, fati na biye dashi a baya kamar kamar
koyaushe bakar rigar nan ce ajikinta da bakar hijabi kai ba
dankwali ta rame sossai ta yi duhu idanuwan nan kamar gauta
saboda jan dasukayi, hannayenta biyu cikin ankwa, wani dan
sanda a bayanta saidai shi fuskarsa akwai sassaucin ra'ayi.
Fati tadubi ummi tayi murmushi cikin dasasshiyar muryarta
tace "Ummi ku ne?
Dan sandan yace "mintunanku ba su dayawa ku gaggauta yin
abinda yakawoku dan kar kuyi asarar lokacinku".
Ummi tagirgiza kai hawaye wasu na bin wasu ta ta so tadafa
kafadar fatima tace "sannu Fati da izinin Allah zai kawo mana
mafita a cikin alamarin nan, mun shiga tashin hankli da dmuwa
akan halin dkike cki fati inajin ciwon damuwarki kamar
xuciyata xa ta buga sbda tashin hnkali.
WNnan shine barrister Nuraddin Mustapha,na daukeshi ne dan
yazamo lauyan dazai kare ki a kotu. Fati inaso kibamu hadin
kai duk tambayoyin daxai miki ki bashi amsa sannan idan anje
kotu a zama nagaba kibude baki kiyi magana.
Fatima tayi murmushi hade da hawaye tace "Ummi bansan
dawani kalamai zanyi amfani gun gode miki ba ,komi nafada
ba zai wdatar dxuciyata ba hai inji cewa na nuna miki godiyata
kan soyayyar da kikemin dakuma kokarinda kike don ganin kin
ceci ryuwata daga wahala.
Saidai inaso kifahimci wani abu duk yadda kaso yankewa
mutum wahala idan Allai bai kaddara lokacin yankewar
wannan wahala ta sa ta yi ba ba za ka iya yanke masa ba. na
godewa Allah daya kaddara min shiga wannan hali ina fatan
wannan jarabawar da Allah yayimin tazamo kaffara agareni,
ummi inaso kisani ban tsananta bakin ciki akan halin danake
ciki ba ni a karan kaina wannan kukan dako dayaushe za aga
idanuwana na yi inayinsu ne sbda tausayin iyayena daku yan
uwana a Bisa halin dxaku shiga ba bakin cikin halin dana tsinci
kaina a cikinsa, dkuma uwa uba rashin mijina wanda xuciyata
ba ta da juriya akan wadannan abubuwa biyu, wannan
damuwar ba zanyi kuka ba inhar akan halin danake cikibne.
Zaman danake ummi ina jiran ranar da za ayanke min
hukuncin kisa ne inbi mijina. idan har akwai taimakon danake
da bukata daga gareku ayanxu shi ne ku taimaka ayanke min
hukunci inhuta wannan damuwar kuma kuhuta domin idan an
kasheni kun daina ganina dole watarana kuhaura idan ko ina
raye haka xa kuyi taxama cikin damuwa.
Wannan shi ne dalilin dayasa naki magana a kotu kuma ina
nan akan bakana na ba xance komai a kotu ba don ba ni da
abin cewa duk abinda xan furta bai wuce ince ba ni nakashe
doctor ba, idan nace ba ni nakashe shi ba in neman kariya
knan wadda e nufin inci gaba da rayuwa alhali ni kaina banga
amfanin rayuwata a duniya ba.
Umi kiyi hakuri kiba iyayena daduk yan uwana hakan kirokar
min su gafara kowa yayi hkuri yamanta dani ba na bukatar
taimakon kowa agareku sai addu'a, na gode kwarai dagaske
kada kisake wahalär dakanki gun dauko min lauya.......
Ummi takatseta cikin huci tace "Fatima kin amince kidauki
laifin daba na ki ba, kin amince kikashe kanki,? wayake kin
taimako kin amince kijawa dukkan zuri'arki abin fadi?
kina zaton wannan ba zai zama mugun aibi ga zuriarki ba?
wanda xaija adinga aibata muku zuri'a mata surasa mazajen
aure?
Kina zaton idan ankashe ki wani zai sake zama lafiya acikin
iyayenki da yan uwanki?
To kisauya tunani lauya tunda kince ba kya so na janye shi,
amma ko shakka babu kuskure ne babba wanda xa kitafka idan
har kikayi ikirarin kece kika kashe docto khalifa alhalin ba ke
kika kashe shi ba.
Fatima tace toh idn ni nakashe shi fa ummi?
Ummi tayi murmushin takaici tace ba ke ce kika kashe docta
ba, dankuwa ba ki da dalilin kasheshi, kina fadin hakanne
kawai dan kin gaji da duniya ba kyason rayuwa a halin da
kinason ki gaggauta barinta, shiyasa kike furta abinda xai raba
ranki da gangar jikinki".
Dan sanda yace "Lokaci ya yi"
Ummi tace kayi hkuri ina fada mata abinda xai amfaneta ne.
Yace ba shi da amfani gareta da saita karba kidaina wahalar
da kanki.
Ya tisa keyar fatee, kallon data waiwayo tayiwa ummin tawuce
shiya sa tsigar jikin ummi tashiga tashi tazube a kasa tarika
kanta da hannu bibbiyu.
Shi kansa barrister nura jikinsa ya yi sanyi, ya jima xaune agun
yana kallon ummi daga can yadan ja numfashi yace "Tashi
mutafi ummi tun anan na tabbatar yarinyar nan fati ba ita
takashe docta ba dukda Cewa ta ki amincewa daduk wani
taimako daxa abata ta rufe duk wata kofa takariya daxa a ba
ta, bawani abune kuma yasatayi hakan ba ta yi ne kawai sbda
bakin ckin dake damun xuciyarta wanda yake tafarfasa
xuciyarta yasa rayuwa tafita a zuciyarta.
Hakan yasa taki mgana a kotu sannan taki yarda da taimakon
da za a ba ta, ba komi Llah yana tare damasu gaskiya, sannan
ba ya goyon bayan zalinchi, indai ba ta da hakki dasannu xa
kiga hukuncin da Allah xaiyi. "
Ummi bata kuma cewa komi ba har suka fice daga gun.
[5:07PM, 7/13/2017] +234 706 196 7803: A DAREN FARKO
2
dasauri yagoge hawayen dake zuba a idonsa jin sallamar
matarsa, goggo Abuwa tazauna sharaf a gabansa jikinta na
rawa ta ajiye flask d'in abincin datazo kawo masa, yadda
jikinta ke rawa haka muryarta take rawa, tace "Innalillahi wa
inna ilaihir raji'un malam kuka kake?
Yayi d'an murmushi yace "haba dai kuka ba kuka nake ba
Zainabu. "
Tace "Dom Allah karkace haka malam bayan na gani da idona
kana kukan kuma na ji shasshe'kar kuka, malam idan kayi kuka
akan wannan al'amari mu kuma yaya za muyi da ranmu?
Kai kake nuna mana muyi ha'kuri bisa fushi dayin Allah me zai
sa kai kayi. "
Malam musa yace "Zainabu al'amarin nan yana matu'kar bani
mamaki da d'aure min kai, ya ya za ayi fati ta iya kashe
mutum? idan munce ba ita takashe shi ba wa ne yakashe shi?
alhalin da Ita sai shi a gidan d'akin a rufe da sakata taciki.
Meyasa fati takashe Dr. khalifa me yayi mata?
Meye iyayen khalifa basu yimana ba? shi kansa khalifan meye
bai yi mana ba? Ace fati tarasa tukuicin dazata saawa wad'an
nan bayin Allah saida wannan mummunan aikin? "
Goggo Abu tace "malam ka yarda fati ita takashe Dr. khalifa?
Yace "to zainabu idn a ita bace waye? daga ita sai shi a d'aki
yashiga yarufe 'kofa shi zai kashe kansa ne zainabu? "
Tayi shiru na lokaci mai tsawo, daga bisani tajinjina kai tace
"ko shakka bbu acikin wannan al'amari akwai rikitar da
'kwa'kwalwa sannan duk wanda yayi wannan aikin wanda
yasan sirrin gidan ne, tabbas fati ba ita takashe dr. khalifa ba
don ba ta da dalilin kashe shi ko tanada dalilin kashe shi ba ta
da 'karfin halin dazata aikata wannan mummunan aikin, saboda
zuciyarta tanada sau'ki akan al'amura, Allah kad'ai yasan
yadda al'amarin nan yakasance. "
Cikin sanyin murya malam yace "Zainabu nima abinda yake
damuna knan kowa ma haka yake fad'a su kansu iyayan khalifa
haka suke cewa basu yarda fati takashe shi ba, to amma
meyasa ba za tayi magana akotu ba idan akaci gaba da tafiya
a wannan hali za asamu mafita ? Tunda ba ita bace tayi
magana mana "
Goggo tace "wannan shi ne abinda yadamu kowa ma ba kai
kad'ai ba malam. "
************************************
Kasancewar mahaifin marigayi Dr. khalifa babban mutum,d'aya
daga cikin masu fad'a aji a cikin gwamnatin garin yabasu
damar ganin fatima cikin isashen lokaci batare da tsayawar
'yan sanda ba, ko kuma ankwa. Alhaji Muhammadu Nazif
mahaifin marigayi Dr. khalifa da hajiya maijidda mahaifiyarsa
suna zaune a wani babban d'aki da aka 'kawata da kujeru,
Malam musa da goggi suna zaune gefensu sai babban wansu
fatima dakuma ummi da Barrister Nuraddeen, fatima na
tsakiyarsu kanta a 'kasa ba kuka takeba su d'in ne baki
d'ayansu ke sharar 'kwalla sakamakon matsanancin tausayi da
bayanin datake furtawa yabasu Alhaji muhammad yace
"Fatima abinda nakeso kigane shi ne dukkanmu nan mun san
ba ke kika kashe Dr. khalifa ba sbda kamar wanda zaiyi kisan
kai ya fita daban, ko da auren dole akai maki dashi ba za ki iya
kashe shi ba balletana anyi auran nan ne da amincewarki, ke
yarinya ce mai biyayya ga iyayenki, wadda kike zaune dakowa
lfya kowa na yabon kyawawan halayenki tayaya za ayi Muyarda
kin kashe Dr. khalifa.
Ki bud'e bakinki fatima nan ba kotu bane mu ba lauyoyi bane
mu iyayenki né duk duniya ba wanda kike dashi wadanda suka
fimu idan rufin asiri ne ba rufin asirin dayafi na Allah, ba wanda
zai rufa miki asiri bayan mu, kigaya mana saurin lamari waya
kashe Dr khalifa ??
Falon yayi tsit kamar ba kowa sai 'karar A. C ko motsi fati
batayi ba ballantana tabasu amsa, malam yace "fati dame
muke magana kigaya mana yadda akayi idanma ke kika kashe
khalifa ya ya za muyi dake ? khalifa dai ya mutu kuma ba zai
dawo ba, fad'a mana gaskiya shi yafi dacewa, kullum
hankalinmu a tashe yake fati ba mu da sukuni idan mun
kwanta don muyi bacci bacci ba ya yiwuwa, abinci ba ya
ciyuwa, muna cikin matsananciyar damuwa ,bansan dawani
ido zan kalli iyayan khalifa ba, bansan da wanne ido zan
cigaba da kallon 'yan uwansa ba damutanan unguwa, ba wani
abu ne ma ba fatima shirun dakikayi har yau baka fad'i Wata
magana wadda za a kama ba akan maganar nan kin mana
adalci, dukkan 'yan uwansa da masoyanki kowa yana cikin
damuwa. "
"Ni na kashe shi baba. "
Akayi tsit kowa yazuba mata ido, maijidda kallonta kawai take
ta yi tagumi d'ansu da suke mutuwar so khalifa ta sake
rushewa da kuka,
Goggo Abu tace "shikenan tunda kince ke kika kashe shi to
lallai ne kidaina wahalar da mutane idan anje kotu kifad'i dalilin
dayasa kika kashe shi, kin san ba wai kice ke kika kashe shi
kiyi shiru ba dole ne kifad'i abinda yasa kika kashe shi.
Ummi tari'ke hannun goggo tazaunar da ita tace "goggo me
mye amfaninki yi hushi da fati alhalin kowa anan ya san takura
matan da akayi da maganar nan yasa tace Ita takashe shin to
haka idan ma akaje kotun aka takura Mata abin da za tace
knan 'karshe idan tace ita takashe shin dole tayi shiru tunda ba
ta da dalilin dazata fad'a wanda yasa takashe shi. "
Goggo tace "shikenan ummi haka za muyi tazama cikin
damuwa tunda ba ita takashe shi ba idan anje kotu ta fad'i Iya
abinda tasani mana. "
Fatima tana kuka tace "kiyi ha'kuri goggi ba'kin cikin damuwar
danasa ku ya fi damuna fiye dakowa sai dai ba yadda zanyi,
goggo ba zan iya cewa ba ni nakashe Dr. khalifa ba sbda gaba
d'aya bayanan sun tabbatar dacewa ni nakashe shi."
Kuyi ha'kuri shirun danayi a kotu wannan shi ne abin da yafi
damuwa na, idan nace zanyi magana bansan abinda zan fad'a
ba 'karshe dai na san duk abinda shirun na wa zai haifar bai
wuce a yanke min hukuncin wanda yayi kisan kai bane a kashe
ni.
To dama abinda nake jira knan, ni kam rayuwa ta 'kare a guna
sai dai sai dai jiran lokaci ko ba'a kasheni ba ba'kin cikin
halinda iyayena kuka shiga a sanadiya ta da ba'kin cikin rashin
mijina shi zaisa zuciyata tabuga in mutu ba zan iya cigaba da
rayuwa ba shi yasa ba na bu'katar taimako tako wani fuskar
lauya don ku'butarwa idan akwai abinda nafi bu'kata bai wuce
addu'a ba, wannan ba sai na ro'keku ba na san kuna yi min.
Dan Allah kuyi ha'kuri kuyafe min babu abinda zan iya cewa a
kotu.
Aliyu yayan fati yayi mgana a karon farko tun zamansu a
d"akin yace "fatima bamu amince kici gaba dayin shiru a kotu
ba dole kiyi magana. "
Tace "shi knan yaya zanyi magana.
Alhaji muhammadu dakowa yafi sani da, abba yace "kar kice ke
kika kashe shi fati".
Tace "Abba idan nace ba ni nakashe shi ba waye? idan kuma
akayi bincike aka gane ni d'in ce abinda ake gudu shi zai faru,
kuna fad'in hakane don fa kusamar min mafita wadda za ta ba
ni damar ci gaba da rayuwa a duniya, yayin da ni kuma ba na
son rayuwar ta fita daga raina so nake na mutu na bar duniya
yadda mijina yabarta. "
Aliyu yace "Anya fati baki samu ta'bin hankali ba? "
Tace "lafiya 'kalau nake yaya ".kowa yarasa abin fad'i a kayi
shiru.
*********************************************
*********
Da sassafiyar ranar daxa a koma kotu hajiya maijiddah da
akafi sani da mama tana kwance kan faffad'an gadonta na
alfarma tunani da ba'kin cikin duniya ya isheta tarasa abin dake
mata dad'i, tana mutuwar son D'anta an kashe mata shi wata
'kanwarta dake tayata zama wato anty sadiya tashigo d'auke
da abincin karin kumallo tazauna kusa da ita suka gaisa tace
"kidaure ki sha ko da ruwan sanyi ne zama da yunwa ya fi
komi illa duk abinda yafaru rubuttaccen alamari ne babu
wanda ya isa yago ge shi. "
Tami'ke zaune tazubawa anty sadiya ido tace "anty sadiya kina
ganin haka yadace mu zubawa lamarn nan ido kullum Alhaji
yana cewa fatima ba za ta kashe khalifa ba toh ni so nake
agaya min wa yakashe min d'ana?
Anty sadkya tace "tabbas kam fatima ba za ta iya aikata
wannan mugun aiki ba abinda yake da sar'ka'kiya shi ne daga
shi sai ita a d'akin to waye yashiga yakashe shi?
Mama tace "ke sadiya idan ma ba ita takashe shi da hannunta
ba to da had'in bakinta aka kashe shi sbda ana ganin ubansa
yana da dukiya d'ansa d'aya ne ko don a mallake dukiyar
ubansa za ta iya yimasa haka.
Anti sadiya tace "kigafarce ni amma ban tari numfashinki ba to
amma idan haka ne da had'in bakin fatima ya ya za ayi ita data
kasheshi ko ta had'a baki aka kasheshi bata gudu ba har akazo
aka kamata? Allah (SWT) dasu kuma mahukuntan tunda Allah
yabasu basiran gano gaskiyar wannan alamari cikin hikima da
izinin Allah za su gano mana wanda yakashe mana d'a jininsa
ba zai tafi a banza ba.
A bisa hanyarsu tazuwa kotunne cikin mota mitar da mama ke
tayi wa abba kenan yayi tsit yana jinta ko tari vaiyi ba ya yi
tagumi yana jan charbi.
Suna shiga su malam da goggo suka shigo suka gaisa, Abba
yace"malam bana jin dad'i Yadda kake kaucewa had'uwa dani
tunda wannan abu yafaru. "
malam yarufe fuskarsa da babbar riga dan kar abba yaga
fuskarsa yace "haba alhaji me, zan ce dakai? menake dashi
wanda zan gaya maka dahar zaisa intsaya in kalleka, kaico.
Ina ba'kin ckin faruwar wannan alamari har ina cewa ina ma
ace banzo duniya ba da dai ace 'yar cikina ta kashe d'an
mutumin kirki kamar kai d'in nan Alhaji muhammadu.
Abba yaja hannunsa suka wuce cikin kotu ba tare dayace komi
ba, wuri d'aya suka zauna mutane suna mamaki sosai yadda
suke ganin iyayan wanda aka kashe da iyayan wacce ake
zargin ta yi kisan. wannan abu yana matu'kar baiwa mutane
mamaki haka zakaga jama'a na kallonsu, yai d'in ne ma dai
hajiya maijidda tasauya fuska sama sama suka gaisa ba wani
magana dasukayi fuska tamau ko da aka shigo da fatima ma
ko kallon inda take batayi ba.
ummi kamar ta fi su kansu fati shiga tashin hankali ta rame ta
lalace
.
Fati na shigowa kotu da ummi suka fara ido sannan tadubi
iyayanta dasauri tad'auke idonta xuwa 'kasa tashin hnkali
datake ganin iyayanta a ciki ko wannan ma ya ishi mutum
tashin hnkli da ba'kin ciki ina amfanin rayuwarta.
Yau kam duk abinda zai faru sai dai yafaru lallai sai ta kawo
'karshen wannan zaman kotu.
Bayan da akayi abubuwan daya dace ayi aka zauna mai
karanta 'kara yakaranto, tuhumar da akewa fati na ta kashe
mijinta a ranar da aka d'aura musu aure a daren farko.
Mai shari'a Usman Muhammad Bamaina yace "fatima musa
kinji tuhumar da ake miki a karo na biyu? "
Ta gyad'a kai tace na ji ya mai shari'a, yau kowa na jin
muryarta sosai, kuma kowa ya ji dad'in yadda tayi mgana har
alamun natsuwa a fuskar iyayanta da 'yan uwanta musamman
ummi wadda har tsima jikinta yake a ranta tana fad'in yawea
fati gara ki yiwa kanki adalci da iyayanki damu masoyanki.Mai
shari'a yace "fatima musa me za ki iya Fad'awa kotu akan
haka? ma'ana kin amince ke kika kashe mijinki Dr. khalifa.?
Kai tsaye fati taware muryarta tace "Eh ni na kashe shi ya mai
shari'a.
[5:07PM, 7/13/2017] +234 706 196 7803: A DAREN FARKO
3
Gabad'aya kotu tarud'e da sallalami kowa na fad'in albarkacin
bakinsa ,iyayan fati dasu kansu surukan suka rud'e, ummi kuwa
hannu tad'ora aka tana fad'in "wayyo Allah na wayyo fati
meyasa kikace ke kika kashe Dr. khalifa bayan ba ke kika kashe
shi ba.
Mai shari'a yayi tsawa akayi tsit sai dai kukan 'yan uwan fati da
ba ya 'karewa, ita kuwa fatin yau tana tsaye 'kyam ko gezau
gadukkan alamu zuciyarta ta fara soyewa, idanuwan amma ba
kuka take ba zafin zuciya ne, ba ta son takalli iyayanta taga
mummunan tashin hnkalin dasu ke ciki, dama chan ita mutum
ce mai tsananin tausayin mutane balletana iyayenta.
Mai shari'a yace "fatima kotu tanason kiyi mata bayanin dalilin
dayasa kika kashe mijinki a daren tarewarku.
Fati tace "ban san dalilindayasa kika kashe mijinki a daran
tarewarku".
Fati tace "bansa n dalilin dayasa nakashe shi ba, ba abinda
nao na zai iya furtawa a kan haka ya mai shari'a ina ro'kon
wannan kotu mai alfarma Data taimaka min tayanke min
hukuncin kisa a yau in bar duniyar nan inhuta, ba na son
bugawar da zuciyata keyi yazamo sanadin mutuwata na fi son
a yanke min hukunci dai dai da laifi na.
Tanumfasa tana kallon al'kalin daga bisani tad'auke idanunta
daga kansa zuwa kan jama'ar dake kotun, gaba d'ayansu su
ma ita suke kallo kowanne da abinda zuciyarsa ke sa'kamasa
game da ita.
Tayi shashe'kar ajiyar zuciya tace "iyayena da 'yan uwana da
dukkan masoya na ina ro'konku don girman Allah kuyafe min
wannan yanayi dana sa ku nadamuwa sannan kuyi min addu'a
rayuwa ta fita daga raina minti d'aya ba na son in 'ka ra yi a
duniya na fi son inbi mijina. "
Tayi shiru kamar yadda kotun ma tayi tsit kai ka ce ba kowa a
kotun, al'kali yana 'yan rubuce rubucensa, haka a 'bangaran
lauyoyi wasu suna rubutu wasu shiru kawai sukayi suna kallon
fatima.
Taci gaba da fad'in "ya mai shari'a a karo na biyu ina ro'on a
taimaka a yanke min hukunci daidai da laifina na amsa laifina
ni ce nakashe mijina".
Wani daga cikin lauyoyi yami'ke yanemi izinin magana daga
gun mai shari'a yace kanada daman magana.
Yayi godiya yadubi fatima yace "sunana barrister Abbas
Mukhtar inason kare wadda ake 'kara sbda na fahimci ba ita tai
kisan ba ina nufin fatima musa ba ita takashe mijinta Dr.
khalifa ba ina ro'on wannan kotu
mai adalci data ba ni damar yin cikakken bincike a kan
wannan al'amari, kuma inason a ba ni damar dazan yiwa
fatima tambayoyi akan abinda ake tuhumarta dashi. "
Mai shari'a yace "kanada damar yin haka.
Yayi dariya yana d'an murmushi ya'kara maida fuskarsa ga
fatima wadda itama shi take kallo fuskarta a tsuke, yace
"malama fatima musa 'karfe nawa aka kaiki gidan mijin kuma
a wace rana ce. "
Fatima tayi shiru kamar ba da ita ake magana ba, Barrister
Abbas ya'kara maimaita tambayar tare da ro'kon kotu data
tursasa fati tayi magana".
Mai shari'a yayi hakan amma Fatima cewa tayi "nagode da
kake burin taimakona a bisa halin danake ciki, sai dai inason
kayi ha'kuri gaskiyar magana ba zan iya ba ka amsa ko d'aya
ba a bisa tambayar dakake min sbda ba so nake in ku'buta
daga halin danake ciki ba, wanda yake bu'katar lauya shi
yakeson yatsira nagaya muku ba na bu'katar rayuwa dan Allah
kuyafe ni.
Mai shari'a Usman muhammad Bamaina yadubi wani dogon
d'an sanda dake tsaye gefe yace "Za a gwada 'kwa'kwalwar
fatima don mu tabbatar da mai hankali muke shari'a, idan
munyi zama na gaba za mu ji sakamakon sannan mud'ora a
inda muka tsaya.
Daganan aka d'aga 'karar zuwa mako biyu idan Allah yanuna
mana,amma kotun ta ba wa 'bangaran lauyoyi guda biyu damar
suyi duk binciken su akan yadda al'amarin yakasance don ba
da kariya dawadda ake zargi.
Yau ma kamar wancan karon kotun ta tashi da hayaniya kowa
na fad'in albarkacin bakinsa akan kafiyar da fati tayi a shari'ar
mamakin da take bawa yawancin mutane shi ne tayaya za ayi
mutum yace shi ya fidda rai kwata kwata da rayuwa mutuwa
yake muradi, wasu suna ganin wannan ya isa kowa ma ya
amince ba ita tayi kisan ba, yayin dawasu ke ganin dan ace ba
ita bace shi yasa tasallama tami'ka wuya, idan ba ita bace
waye? Gida su biyu kachal ba kowa d'aki a kulle su biyu in har
ance ba fati takashe Dr. khalifa ba to sai dai ace shi yakashe
kansa, hatta hajiya Maijidda mahaifiyar marigayin dayawa
daga 'yan uwansu abinda suke gani knan wannan kukan da
take abinda suka d'auke shi kukan munafinci ne kawai.
A harabar kotun kafin sutafi gaida malam musa ya tsaida
barrister Abbas yana masa godiya a bisa 'ko'karinsa nakare
'yarsa, barrister yayi murmushi yace, "Ba komai kada kadamu
baba na yi wannan ne domin Allah da tsananin tausayin da
fatima ke ba ni tun randa aka fara tsaida ita a gaban shari'a na
tabbatar ba Ita tayi wannan kisan ba, duk wanda yakashe Dr.
khalifa na gida ne wanda yasan sirrin gidan insha Allahu da
izinin Allah zamu gano ko waye,sai dai inason kataimaka min
fatima tadinga ba da amsa a kotu sannan xanje inganta
kutaima ka min tayimin cikakken bayani duka tambayoyin da
zan mata dan insan yadda zan 'bullowa al'amarin.
Malam yace "To ni na rasa me yasa fati take tsuke bakinta
komi sai tace ba za ta iya fad'a ba sbda rayuwar ta fita Daga
ranta.
Barrister yayi murmushi yace "bako mi tsananin damuwa ne
yasa take fad'in haka, matsayinku na iyayenta ku yadace
kulalla'bata tafad'i yadda akayi.
Malam yayi masa godiya mai yawa bayan tafiyarsu malam d'in
barrister na xaune a motarsa shi kad'ai yana nazarin alamuran
fatima tausayin ta har ya yi masa yawa a zuci.,daurewa kawai
yau yayi ya zo kotun tun a wancan zaman da akayi hankalinsa
yatashi sosai gameda al'amarin yarinyar, tun lkcn abinda yake
d'aga masa hnkali matsalar d'aya matsalar kowama ita ce
shirun da fati tayi tana neman mutuwa ido rufe ta 'ki ba da
had'in kai ballantana a samu mafita.
*********************************************
A hankali ummi tafito daga motar tabi bayan mama zuwa cikin
gida, kowanne zuciya ba dad'i , a falo suka zauna gaba d'aya
yayin da ita ta dawo dabaya zuwa ainihin d'akin Dr. khalifa na
gidan har yanzu mukullan d'akin yana hannunta ita kad'ai take
bud'ewa tashiga tunda ga lokacin daya mutu zuwa yanzu,
komi na nan yadda yake wani irin 'kamshi mai dad'in gaske
yana tashi a d'akin, gaba d'aya kayansa nasawa suna jere a
cikin wardrobe gwanin ban sha'awa manyan hotunansa da
akayi enlargement d'insu guda biyu na gefe da gefe na gadon
ya yi kyau ba na wasa ba.
Tazauna a gefen gadon tanasa hannu tad'auki hoton
tarungume kam kam idanunta a rufe hawaye wasu na bin wasu
zuwa chan ta ajiye tashiga bud'e durowowin jikin madubin
hotunan bikinsa da fatima ne birjik musamman ma gun
lunching da dinner dayawa yarungume fatin ne 'kam 'kam a
'kirjinsa wasu kuma tare da abokanansa maza da mata.
Kan cinyar ummi yaji'ke dahawaye kamar ruwa aka zuba mta a
cinya tun ranar da aka kashe Dr. khalifa take kuka amma bata
ta'ba kuka irin na wannan rana ba, har sai dataji numfashinta
kamar zai d'auke.
Ba za ta ta'ba mantawa da abinda yagya mata ba a yammacin
lahadin daza akai fatima gdansa wanda kuma a wannan rana
ce aka kashe shi bai sake kwana a gidan duniya ba.
Yana tsaye a harabar gdansu tare da manyan abokansa biyu
wad'ana baida aminai kamar su.
Manyan likitoci Dr. Hafiz Bala Muhammad da Dr. Mustapha
Abubakar kura, yana tsakiyarsu suna hira, sai ita ummi tafito
daga cikin gida tana ganinsu tahau yimusu hoto a wayarta, Dr
khalifa yaharareta yace "wai meyasa kike daraina mutane ne
ummi ni kikewa hoto?
Sai Dr. Mustapha yace "kaima kanada saurin hushi khalifa ko
wacce rana idan an maka abu za ka 'bata rai banda wannan
rana wadda tazamo ta auranka da matar dataza mo allura
cikin ruwa kaine kaxamo mai rabon daka zu'kota. "
Dr. khalifa yarausayar dakai yana murmushi tare da lumshe ido
yace "ka fad'i gskiya Dr. Mustapha tabbas ni ne na cafko
wannan allurar data zamo tamai rabo ce, a daidai lokacin dana
fidda rai da ita sai najita kawai a hannuna ,tabbas wannan rana
ta dace tazamo ta farin cikina, ranar dazan sadaukar da komi
na wa sbda Fatima. "
Ummi tay murmushi tace "shiyasa nima nake maka hoto
domin ka yi min kyawun daban ta'ba ganin ka yi shi ba a
duniya dukda cewa kai d'in me kyau ne kullum kyau kake da
ado. "
Dr. Hafiz Bala yace "har bayan hoto yanada kyau ma yayi miki
kyauta ta musamman ummi."
Dr. khalifa yayi murmushi yace "ko shakka babu a wannan rana
ina cikin farin cikin daban ta'ba samun kaina a cikin shi ba, sai
dai kasan tun safiya gabana ke fad'uwa bansan dalili ba
wannan yayi sanadin dayasa tun ruwan shayi danasha rabin
cup d'azun bayan d'aurin aure ban iyacin komi a bakina ba.
Ummi tayi wal da ido tace "fad'uwar gaba kuma Dr. a irin
wannan rana? ni dai na san ko kusa bakayi kama da wanda
mace za ta ba wa tsoro ba ballantana ince firgita kayi sbda
fatima.
Dr. Mustapha ya bugi kafad'arsa yace "wa wannan? ni tunda
ake ma gwargwadon bud'ewar idanuna ban ta'ba ganin
namijinda yayiwaa mata farin sani irinsa ba, farin ciki ne yayi
masa yawa sbda soyayyarshi yasa ma gabansa yake
fad'uwa....... "
Tunanin ummi yakatse a nan lokacin da mama taturo 'kofar
d'akin tatsaya tana kallon ummi kukan datake yabata tsoro
ta'karaso dasauri ta kamata takwashe hotunan dasuka ji'ke da
hawaye ta mayar, takamo hannunta tafito da ita tarufo d'akin
takar'be makullin tace "daga yau ko 'kofar d'akin nan ba na so
kisake zuwa, haka kada ki 'kara zuwa kotu ba xa muyi biyu
babu ba, mun rasa Dr.khalifa muna cikin ba'kin ciki mai tsanani
kema damuwa na neman xama ajalinki to B xai yiwu ba.
Cikin kuka ummi tace "Don Allah mama kada kiharamta mini
shiga d'akin likita, yin hakan ne kad'ai zaisa zuciyata ta
sassauta daga damuwar danake ciki, na rasa d'an uwana ga
aminiyata na cikin matsancin zargi na bi duk hanyoyin daya
kamata inbi don ganin fatima ta ba lauyoyi had'in kai ta 'ki
burinta akasheta meyasa ba zanyi kuka ba mama?
mama tayi tsaki tace "ina mamakin yadda ke Da Alhaji kuka
d'auki damuwar duniya kuka d'orawa kanku akan fatima shin
dakuke cewa batace komi ba me za tace, fatima ba ta da abin
cewal shiyasa tai shiru, ko a hankalce kun san 'karyane ace
akwai. mutumin da ake tuhuma irin hka ya'ki amsar taimako
daga lauyoyi don kawai yana burin mutuwa.
kinta'ba ganin wanda yazauna yana jiran mutuwarsa kuma yana
maraba da ita, saidai fa in ta zo a kar'beta don ba yadda za ayi
da ita.
Ummi tasaki hannun mama tazubla mlatla ido muryarta a
dashe tace "mama shin kina nufin kin amince fati za ta iya
kashe likita?
Mama tayi murmushi tace "ummi ummi kiji tsoron duk wanda
kika taimakawa.
Akoda yaushe idan za ki taimakawa mutum to kitaimake shi
kai tsaye don Allah ba wai don zai saka maki da alherin dakika
yimasa ba, shi dama mutum bbu abinda yake cika cikinsa sai
'kasa shi. mai butulcewa mahaliccinsa ne ma ballantana ace
wani gama garin mutumin don hka ba abin mamaki bane ga
mutumin daka d'auko shi daga rana kadawo dashi inuwa shi
kuma yaturaka ranar,a cikin mutane mutumin dayake salihi ko
mai shiru shiru irin fatima mutane ba sa zarginsa da mugun
abu sbda yanayinsa amma Allha (SWT)daya halicci zuciya shi
yasan abinda ke cikinsa.
Ummi tayi shiru na lokaci mai tsawo daga bisani tace "Mama
kina nufin kin amince akashe fatima akan kisan likita? "
Tace "ummi ba ni da masaniyar abinda shari'ar za tahaifar,
sbda ita shari'a macece da ciki ba wanda yasan abinda za
tahaifa sai Allah mudai mun mi'ka kukanmu ga Allah
yabayyanar da gaskiya. "
Tayi gaba tabar ummi tana binta da ido jikinta yayi sanyi
'kalau, da'kyar tad'aga 'kafa tabita cikin gida.
.
.
[5:08PM, 7/13/2017] +234 706 196 7803: A DAREN FARKO
4
maganganu sunyi yawa a kan abubuwan dasuke faruwa a kotu,
wasu sun fara yarda tunda tace takashe Dr. khalifa yayin
dawasu har yanzu suna ganin ba'kin cikine yahanata magana
dukda cewa su d'inma suana gnin fati ba ta da hujjar da za
tasa taja bakinta tayi shiru ta 'ki cewa komi.
Kwana biyu a zauna kotu malam musa da mahaifiyarsu fatima
da da ummi da Barrister Abbas suka isketa a inda take tsare
abisa alfarmar dom mahaifin marigayi Alhaji muhammad
amma fa akwai sa idon 'yan sanda guda biyu.
Fatima tarusuna tagaida mahaifinta ciwon rai ya'kara damunta
sakamakon ramewar dataga ya dad'a yi ya fita hayyacinsa
kaida gani ka san yana cikin matsananciyar damuwa da takaici,
sannan tagaisa dasu ummi da barrister.
Malam yace "fatima.
Ta amsa 'na'am baba.
Yace "fatima wannan shi ne zuwa na 'karshe dazanyi gunki
akan in ro'ki kiyi bayani a kotu idan kinga dama kiyi magana
fati idan baki ga dama ba kicigaba dayin shiru tunda kinfi
'bukatar mucigaba dazama cikin tashin hnkali darashin sanin
abin yi.
A yau na zo ne ba dan in ro'ke ki kiba lauyoyi da al'kali amsar
duk tmbayar dsuka bu'kata agunki ba zuwa nayi in ba ki umurni
a matsayina na mahaifinki idan ya cancanta kiyi min biyayya
kiyi fatima idan kuma ban isa ba kici gabadayin shiru kamar
yadda kika saba.
Fatima tace "baba idan nayi bayanin zai sauya 'kaddara ne? ko
kuwa bayanin na wa zai dawo da rayuwar Dr. khalifa izuwa
gidan duniya, baba idan ni ce nakshe Dr. khalifa idan ma ba ni
bace Allah SWT ya san haka tunda shi yake ganinmu a lokacin
damuke kulle mu biyu acikin d'aki ni da Dr. khalifa, ni dai
abinda nakeso ayi amfani dashi shi ne tunda naji na gani na
amince ni ce nakashe shi na yi i'kirari da bakina a yi min
hukunci dai dai da laifina shiknan shari'a sai a gaban Allah
(SWT) wannan itace rana daza a tsage gskia ranar dakowa
zaiyi bayanin abinda ya aikata da ga'bo'binsa bama da bakinsa
ba kuma itace dawwamammiyar rayuwa wadda va za ta'kare
ba har abada.
Don Allah baba kayi ha'kuri kada kayi fushi dani akan hka bbu
abinda bakina zai iya furtawa a lamarin kisan nan.
Ummi tace "fati mahaifanki sun kasance suna masu alfahari
dake a bisa biyayya da kike musu, baki ta'ba yin musu dasu ba,
ba'a ta'ba samun wata rana da suka baki umurni kika sa'ba ba,
meyasa a wannan karon za kisa'ba musu?
Ba ki da hujjar dazakice rayuwarki ta zo 'karshe fati, ko kuma
dan kina jiran mutuwa shiyasa kike ganin biyayya ga
iyayankinya va ta da amfani?
To bari in tunatar dake wani abu guda d'aya ance akwai
mutumin dazai ta aikin alheri wanda yake share masa hanyar
tafiya aljannan sai 'karshen rayuwarsa tazo sai kawai ya aikata
wani abu wanda zai kaishi wuta sai ya shiga wuta.
Yayin dawani zaita aikata aikin dazai kai shi wuta gab da
mutuwarsa siya aikata abinda zai kaishi aljannan saiya shiga
janna.
Fatima ina ro'kon ki kiyi abinda iyayanki suka bu'kata ba ki da
hujjar dazaki sa'bawa umarninsu, ba ki da tabbacin kwann ki ya
'kare mutuwa zakiyi fatima.
Barrister kallon fatima kawai yake yarasa yadda xaiyi da
tausainta a zuciyarsa, yamatso daf da ita muryarsa 'kasa 'kasa
yace "fatima 'karfe nawa aka kaiki gidan Dr. khalifa?
Ta amsa 'karfe biyar da rabi Zuwa shida a wannan d'an
tsakanin ba'a wuce haka ba.
Gaba d'aya sai da fuskokinsu suka nuna jin dad'in had'in kan
data fara badawa, barrister yace a wace rana knan fatima?
Ta amsa "A ranar lahadi biyar ga watan uku"
Ya gyad'a kai yana murmushi yace "fatima suwa dawaye suke
cikin motar da aka kaiki?
Tayi d'an jim daga bisani tayi murmushi tana kallonsu tace
"ummi za ta fini snin suwaye a motar da ka kaini sbda ni
fuskata a rufe take ba wanda zan iya shaidawa a lokacin sai
dai tabbas na san ina tare da manyan aminai na guda biyu
kamar ita ummin da d'ayar aminiyar ta wa Jiddah.
Barrister yace "yawwa ko za ki iya tuna 'karfe nawa kowa
yawatse acikin gidan aka barki ke d'aya lkacin dakike jiran
ango kamar yadda al'adar amare take a ranar da aka kaisu
d'akunan mijinsu,?
Tace 'lallai kam ba zan manta ba bayan an yi sallar isha'i
wuraren 'karfe takwas nadare su ummi da maijidda dawasu
'kannan mahaifiyata biyu kad'ai suka rage a gidan inda mukai
sallar isha tare dasu sannan sukayi shirin tafiya suka tafi gaba
d'ayansu.
Barristr yace "bayan haka waye yashigo gidan kafin zuwan
ango dr. khalifa? "
Tajima tsit tana nazari tace "gaskiya ba wanda yashigo kuma
banji motsin kowa ba ni kad'ai nazauna.
Barrister yace "zaman minti nawa kikayi 'kiyasi kafin dai zuwan
ango ?
Tace "tace ba'ayi minti sha biyar ba naji tsayuwar motarsu
shida manyan abokansa guda biyu wad'anda sukayi masa
rakiya.
Barrister yace "kafin dai zuwan angon ba wanda yakiraki ko da
awaya ne?
Tagirgiza kai ba wanda yakirani in barda shi angon Dr. khalifa.
Me yace miki?
"Cewa yayi inyi ha'kuri suna hanya "
Ke kuma me kika ce masa?
Cewa nayi to Allah yakawosu lfya.
Yace "dukda haka bakiji ko da alamar motsi a gidan ba har
lokacin da dr. khalifa da abokanansa suka iso.
Tagirgiza kai gaskiya babu wani alamun motsin danaji saifa
lokacin dasuka shigo.
"Su nawa suka shigo. "
Barrister yaci gaba da tambayar har yanzu idanuwansa na
kanta.
Tace su uku wato shi da abokan na sa guda biyu.
Yace "yaya sunayensu.Ta amsa "daya sunansa Dr. Mustapha
kura d'aya Kuma Dr. Hafiz. B. Muhammad. "
Yace kafin auranku yaya ala'karku dasu abokan na sa? ina
nufin sun amshe ki a matsayin matar abokin su ko kuwa ba sa
yi dake?
Fatima tace "Nikam alhmdlh Dr. khalifa da iyayansa da
abokansa da yan uwansa ko sau d'aya babu wanda yata'ba
nuna min wata 'kyama ko wani abu wanda zai sa ince lallai
wane ba ya 'kaunata, daidai gwargwado ina samun had'in kai
daga garesu to sai shi kuma abinda yake na nasani mutum
yakeda masaniya akai abinda yazamo na bad'ini Allah kad'ai ke
da masaniya akansa sa sai dai mubarwa Allah ikonsa".
Barristr yace "to fatima za ki iya gaya mana maganar dasuka yi
lokacin da za suyi sallama daku a wannan dare?
Tace "eh gaba d'aya tunda sukazo nasihohin zaman lfya suke
mana bayan hka sun mana addu'o i na neman zaman lfya
bayan haka sukayi mana sallama suna mana barkwanci irin na
abokan ango ranar siyan baki irin wannan.
To daga nan sai me yafaru?
Tace "saiya rakasu"
Ke kuma kina ina?
Ina zaune akan gado ko motsi banyi ba kamar yadda suka
sameni, bayan ya rakasu saiya dawo yazauna kusa dani yana
d'an zolayata.
Barrister yace "dukda haka a lokacin ba wani motsi a gidan
sannan shi d'inma bai nuna miki ya ji motsin wani abu ba ko
kuma ke kin fahimci wata razana a fuskarsa? "
Tace "gaskiya banga komi ba yana cikin nishad'i sosai yadda
yakamata ango yakasance a irin wannan dare. "
Daga nan fa?
Sai yace dani kinga hayaniya tayi yawa a kaina ko sallar isha'i
banyi ba nayi 'ko'karin inyi kafin mutaho su mustapha suka
daman akan inyi sauri su garin za subari a daran.
"Garin za subari? inji barrister yafad'a yanayinsa yasauya.
Tace "haka dai yace daganan kuma bai 'kara fad'ar wata
magana wadda tashafi wad'annan abokai na S ba yatashi
yafita bansan ina yaje ba saiya dawo.
Ya yi kamar minti nawa dafita kan yadawo?
Tace zaiyi kamar minti goma saiya dawo yacire babbar rigar
jikinsa ya Ajiye kan gado yace ya kamata inyi sallar nan dashi
kuma inajin yunwa tun d'azu anti take ce min ga abinci na ka
sa zama inci sda jama'a gaba d'aya na ji abincin ya fita daga
raina ba na sha'awarsa sai yanzu nakejin yunwa,amman bari
inyiwa mama waya tasa akawo mana abincin hatta kazar
amarcinki ma tana gun mama ita tace za tagasa dakanta
akwai tanadin datayi miki a ciki.
Duk yayi wad'annan maganganun ne a tsaye yana murmushi
tare da daddana wayarsa tahannu yakira maman bayan sun
gama wayar sai ya ajiye wayar akan madubi danufin yashiga
toilet sai aka kirashi yayi magana mai tsawo dawanda
yakirashi d'in sannan yakashe yadubeni yace "idan mutum yana
harka da jama'a sai ha'kuri, tashi kema kiyi alwala idan nayi
sallar isha'i sai muyi Nafila ko bari inyi tawa a d'akina sai
intaho da littafina daganan saiya fice waje Nikuma nashiga
toilet na idar da alwala na fito ne na iske gawarsa akan gado.
Barrister yagirgiza kai cike da tausayi yace "fatima. "
Yanayin fuskarta ba d'ad'in gani sbda tamkar lamarin datake
bayarwa yana fama mata wani gyambo nazuciyarta wanda
yake mata tsananin zugi a zuci yake rabata da duk wani zaman
lfya da walwala a zuciyarta, hatta kallon datayiwa shi barristan
lokacin daya kira sunanta ya firgita shi zuciyarsa tabuga yayi
mata tsai da ido don yana son taci gaba da bashi amsar
tambayoyin dayake mata.
Yace "fatima kin kai minti nawa a toilet d'in lokacin da kika
shiga danufin yin alwala.
Tace "minti kamar goma don na d'anyi wasu abubuwan kafin in
gabatar da alwala.
To sai kika fito inda kika ga gawar mijinki Dr. khalifa shimfid'e
akan gado, haka ne?
Tace "eh ina daga band'aki naji motsin bud'e 'kofa sau biyu
dakuma motsin bud'e kwaba ko me zan kawo a rainadon na ji
wannan motsin, d'auka zanyi shi ne tunda ba kowa a gdan a
iya sanina dagani sai shi.
Yace "kuma ba motsin gudu?
Tace "Gaskiya banji wani motsi wanda yake tabbatar da rashin
gaskiya ba ko kusa.
Yace "to bakiji 'karar mijin na ki ba ko wani abu da yayi kama
da haka a lokacin da za a kashe shi?
Tace "nidai banji komi ba yadda nagaya maka naga gawarsa
haka nagan shi ba wani abu da na sani bayan wannan.
Yace "dame aka kashe shi?
Ta amsa "wu'ka ce 'karama.
kin ta'ba wu'kar?
Tace "eh lokacin danafito daga band'akin hankalina yayi
mugun tashi natafi dagudu nad'aga wu'kar daga cikinsa domin
wu'kar tana kan cikinsa ne bayan an luma masa sai aka zareta
aka d'orata akan cikin na sa nikuma danazo saina d'aga wu'kar
shi ne dai dai lokacin da 'kaninsa isma'il ya 'kwan'kwasa 'kofa
jin ina ihu innalillahi wa inna ilaihir raji'un saiya danno 'kofar
yashigo da food flask d'in abinci a hannunsa wanda mama
tabashi yakawo mana.
Barristr Abbas yace "fatima lokacin dakika iso kan mijinki dr.
khalifa yanada sauran rai ko ya mutu?
Tace "dasauran ransa don kuwa har yana d'an juya kansa yana
cewa ta kasheni ta kashe ni har lokacin dashima isma'il
yashigo d'akin yana magana ganin yanayin da ya iskemu aciki
yasa isma'il d'in yawatsar da abincin hannunsa ya isa kan d'an
uwansa a gefe ana fad'in, ya ya wa yakashe ka, yakasa
hannuwansa daidai bakin dr. khalifan yana cewa don Allag
gaya min wadda takashe ka nima yanzu inkasheta.
Ban san yaya akayi ba ko shi Dr. khalifan a lkcn bansan waye a
kansa yake masa magana ba ne ban sani ba naji Da kunnena
dai lokacin Da dr. khalifa ke cewa Fatima ta kasheni, fatima ta
kasheni.
Fatima tayi shiru zuciyarta na bugawa kamar lokacin abin
yafaru, daga barrister har malam da ummi dashi kansa d'an
sandan dake tsaye a kansu sun ji'ke sharkab da gumi sbda
tsananin tausayi da tashin hnkali.
Idanuwan fatima sun 'kafe ba zancan hawaye sai tsananin zugi
da rad'ad'i dasuke mata 'kirjinta kuwa kamar zai 'balle dan
azabar zafin da yake mata numfashi na fita da'kyar.
Tunda al'amarin yafaru yau ne ta iya bud'e baki tabada labarin
yadda abubuwan suka wakana.
Sun jima zaune shiru tuni lokacin daya dace sufita yawuce shi
kansa d'an sandan ya kasa cewa sufita hnkalinsa shima a
tashe yake..
Barrister abbas tagumi kawai yayi da tambayoyi a bakinsa,
bakin ya yi masa nauyi la'b'bansa sun bushe da'kyar yake iya
numfashi tare dacewa, shi cikakken lauya ne Kum 'kwararre
mai cin gashin kansa don tuni ya jima da 'kasaita akan aikinsa
sbda matakin daya ta ka nakaratu, irin wadannan abubuwan ba
bakin al'amura bane gareshi, aikinsu nako yaushe jin abubuwan
tashin hnkali amma bai ta'ba fuskantar alamarin dayake
tsananin d'aga hankalinsa da ba shi tausayi irin wannan ba, ya
damu da mGanar 'kwarai dagaske.
Kafin ma yayi mata tmbaya taci gaba da fad'in "Abinda
bakinsa ke furtawa knan har yabar duniya, wato ta kasheni
fatima, takasheni Fatima.
Isma'il yana ihu akansa yana cewa "yaya fatima ce takashe ka?
fatima ce takashe ka? bai 'kara motsi ba yaci gaba da jijjigashi
ko shurawa baiyi ba, tuni jini yayi faca faca akan gadon.
Wu'kar tana hannuna ina tsaye har izuwa lokacin da isma'il
yasake shi yafita baice min komi ba, ban ajiye wukar ba sai
lkcin da yan sanda suka shigo d'akin wani acikinsu yalulku'be
hannunsa da safa yakar'bu wu'kar daga hannuna.
Tayi ajiyar zuciya tace "ba wani abu dana sani bayan wannan
,bbu kowa a gidanmu lokacin da aka kashe Dr. khalifa sai mu
biyu a gidan ni da shi ni kaina na shaida banji motsin kowa ba,
idan ba ni nakashe shi ba wa zance ykashe shi?
Idan nace ba ni nakashe shi ba dole inyi bayanin wanda
yakashe shi to waye?
sannan ni akazo aka iske da wuka a hannu haka nan bakinsa
gana furta takasheni ,idan akace wa sai yace fatima..
Fati tarushe dakuka mai tayar da hankalin mai imani tace
"kaicon rayuwata na yi nadamar zuwa wannan duniya ace an
wayi gari a rasa wanda zai kashe Dr. khalifa sai ni ni fatima me
xanyi da rayuwa..
me zan tsinta a cikinta,
wane farin ciki zanyi a gaba?
Don Allah kudaina yun'urin kareni kuyarda ni nakashe Dr.
khalifa a kashe ni in huta da wannan ba'kin cikin rayuwata ba
ta da amfani.
Wannan bayanin da nayi iyakarsa zan iya fd'a ba zan ta'ba
bud'ar bakina a kotu ince wani abu ba game da ranar da dr.
khalifa ya bar duniya, hukunci kawai nake jira kuyi ha'kuri
kuyafe min.
Barristr Abbas yace "to shikenan munji ke kika kashe Dr.
khalifa gaya mana meyasa kika kashe shi?
Ta amsa "ni ma bansan dalilin dayasa na kashe shi ba.
Ba wani laifi dayayi miki?
Bai min komi ba sai alheri, ba komi tsakanina dashi sai alheri,
ban sani ba ko alkairin ne yasa nayi masa sakayya da kisan kai.
[5:08PM, 7/13/2017] +234 706 196 7803: DAREN FARKO
5
TSAKIYAR dare ne za mu iya kiran lokacin 'karfe biyu da rabi
nadare, fatima na zaune kan dandayyar siminti ana muku
mukun sanyi ne a lokacin amma ita ta ji'ke sharkab da gumi
sakamakon matsanancin halin tashin hnkalin da gararin
darayuwarta ke fuskanta.
Ita kanta yadda alamuran suka faru suna matu'kar ba ta
mamaki, koyause tambayar datake wa kanta itace waye
yakashe Dr. khalifa?
Me yayiwa wanda yakashe shi? Meyasa ba'a kashe shi ba sai a
daren su nfarko A DARAN FARKO na amarcinsu aka biyo shi
har cikin gida akan gadonsu aka kashe shi, tabbas duk wanda
yakashe Dr. khalifa ya isa azzalumi, ita da Dr.khalifan ne baya
so shi yasa aka kashe shi a sigar da duk wanda yagani zaice
itace takashe shi.
Ita da Dr. khalifa mesuka yiwa wani daya daidaici irin wannan
dare a gunsu yakashe mata miji?
Wannan itace tambayar datake wa kanta tun lokacin da aka
kulleta a wannan guri, itace tmbayar da ciwon dayake mata a
zuci ke barazanar sa zuciyarta tabuga ta tadda mata ajalin
sbda tsananin damuwa, Allahu akbar ashe ko kwana d'aya ba
za tayi a gidan miji ba, bala'i zai fad'a musu A DARANSU NA
FARKO.
Sai kace ana tariyo mata rayuwarta da abinda yagudana a
tarihin rayuwarta gaba d'aya haka yarin'ka wanzuwa a zuciyarta
da 'kwa'kwalwarta kamar shirin fim.
*******************************,******
Malam haruna shi ne mahaifin malam musa wanda yakasance
shi ne mahaifi ga su fatima.
Asali malam Haruna bafullatanin gombe ne yawon neman
karatu yakawo shi kano kasancewarsu fulani ne na jame inda
yazauna a hannun wani shahararran malami mai babbar
tsangaya anan kano, Allah ya yi malam haruna mutum ne mai
tsananin ha'kuri da biyayya malamin nan da iyalinsa suna
matu'kar jin dad'in zama dashi inda a sanadin haka ne suka
d'au d'iyarsu Maryama suka ba shi auranta ita kuma tahaifa
masa 'ya'ya maza har bakwai, malam musa ne autansu.
Bayan rasuwan malamin, malam haruna shi yazamo magajinsa
don duk acikin almajiransa na wannan lkcin ba wanda yakaishi
sha'kuwa dashi, ga kaifin basira yaci gaba da jagorantar
tsangayar kuma shi yari'ke iyalan malam har zuwa shima
lokacin da Allah (SWT) ya kar'bi ransa sai d'ansa malam musa
yagajeshi a lokacin ma bai dade da auran fari ba inda matarsa
zainab tafito itama daga zuri'ar tsohon malamin marigYi
malam Yakubu, an ce na ji dad'i shi ne gari ba na saba ba.
Malam musa yayi kyakyawan gadon hali na hakuri datsananin
juriya irin na mahaifinsa, mutum ne mai matukar saukin kaida
sanin yakamata, hka itama matarsa zainabu bbu abinda
yadameta da zafafawa kanta game da rayuwar duniya.
Suna zaman su lfya a dan karamin gidan da yake haya kusa da
makarantarsu basu dogara da kowa ba sai Allah mutane ne
dako kadan va su da kwadayi, mutanan unguwar sunajin dadin
zama dasu sosai ana zaune lfya.
Aliyu shi ne d'a na farko da goggo Abu tafara haifawa malam
sai mai sunan malam Yakub suna cewa dashi malam, sai
rukayya sai fati sai mai sunan malam Haruna suna cemasa
baban gida sai muhammadu nazifi sai nuraddeen ba su da
wadata da dukiya rayuwa ce tarufin asiri amma akwai wadatar
zuci da son juna, rayuwarsu tana yawan ba wa mutane sha'awa
yadda suke kamun kak da tarbiyya da girmama jama'a da
'ya'yan gidan masha Allahu hka suke amma ba kamar fatima,
itace tafi fad'a kowa d'auko halayyar mahaifinsu kamar yadda
tafi kowa kama sak da mahaifinsu don hkane tafi kowa kyau a
gidan.
kaf zuri'ar marigayi malam haruna kyawawan gaske ne har
kwatance ake dashi a garin sbda kyaunsu ga uwa uba farin jini
dukda cewa ba masu kud'i bane ba su da komi sai rufin asirin
Allah.
Tun fati tana 'yar mitsitsiyarta ake mata shaidar hkuri dasau'kin
kai duk inda fatima tashiga sai an yaba halayyarta, balletana
biyayya ga iyaye wad'anda takeji kamar tayi musu numfashi
don tsananin so da 'kauna ko kuma takwanta sudinga bi ta kan
ruwan cikinta don biyayya.
Hka a makaranta malamanta ke ji da ita bayan maida hankali
akan karatu da gudun fitina ga biyayya da tsafta.
Fatima kyakyawar gaske ce daga ganinta ka ga bafulatana sak
zai wahala mutum yagaji da kallonta sbda Allah ya yi mata
baiwar kyau mai tsayawa a zuci.
Bayan auran yayarta rukayya da shekara biyu wata rana da
daddare malam musa yana zaune kan tabarmarsa goggo Abu
tana gefe itama kan tata tabarmar yayin da fatima ke zaune
kusa da su tana yi masa firfita.
Yace "zainabu yaya batun d'an gidan rukayya ya warware ko?
Ta ce "Alhamdulillah jiki kam dasau'ki yau danaje na iske shi
yanata wasa da yara.
Yace "Masha Allah, sannan yagyara zama yadubi fatima yace
"fati yaya batun haddarki ta jiya kin haddace"
Tace "na haddace har d'azun na ba da a gaban malam
musbahu ya dad'a min wani.
Yayi murmushi yace "Alhamdulillah yana daga cikin ni'imar da
Allah yake yiwa mutane shi ne yabasu 'ya'ya na gari salihai
wad'anda zasu zamo farin ciki a gareka, fatima ina matu'kar
alfahari dake sbda kinada hankali da biyayya ban ta'ba shakku
akan biyayyar da kike mana ba wannan shi ne dalilin dayasa
kai tsaye ko shawara banyi dake ba na daukeki nabawa malam
musbahu auranki sbda na fahimci halayyarku ta zo d'aya.
Shi ma mutum ne da Allah yahore masa ha'kuri dasanin
yakamata tunda nake dashi bai taba aikata min wani abu na
assha ba, sai dai ajizanci irin na d'an adam wanda yake kai
mutum ga kuskure.
Amma dukda hka ina neman yardarki, idan kin yarda ba wani
abune mai girma agareni ba don ina da ya'kini da kwanciyar
hnkali akan hakan, idan kuma kin ce baki yarda ba ma'ana ba
kya son shi ina mai yimiki rantsuwa da girman Allah ba zan
damu ba na san Allah ne bai 'kaddara musbahu mijinki bane
shi yasa kika'ki amincewa dashi.
Fatima kanta na 'kasa ta shiga shararar 'kwalla batace komi
ba, malam yace "fatima kada wannan magana tad'aga miki
hnkali balletana tajefa zuciyarki cikin damuwa.
Cikin shashe'kar kuka fati tace "dole indamu baba ban ta'ba
tunanin akwai watarana dazakayi tunanin zan bijirewa
umarninka ba, har inada abinda zanyi wanda zaisa inyi gaban
kaina ba tare da umarninka ba.
Wlh idan har akwai watarana wadda za tazo in bijirewa
umarninku ba na fata tarismeni ina numfashi a duniyar nan
gara in mutu da in ganta sbda haka baba ba na bukatar ka kara
neman yardata a bisa wani bu wanda kake nufin zartarwa a
kaina.
Na amsa malam musbahu hannu biyu biyu kuma zan yi masa
biyayya bakin iyawa ta.
Malam musa yagirgiza kai yace "Allah yayi miki albarka fatima,
Ubangiji Allah yasa kigama da duniya lfya, biyayyar dakikayi
mana Allah yasa 'ya'yan dazaki haifa suyi miki wadda tafita,
dukda haka ina mai tabbatar miki dacewa hakkinki ne in nemi
amincewarki akan auranki da malam musbahu kamar yadda
nayi miki bayani a baya ba wai dan ina shakkun amincewarki a
gareni ba sai dan in ba ki hakknki a matsayina na mahaifinki.
Yadda nake miki wannan magana haka na zaunar da musbahu
nace dashi musbahu yau fiye da shekarar ka goma a hannuna
tun lkcin dakazo da sassafe kana kuka kana ce min in
taimakeka inje in ba wa kawunka hakuri matarsa ta yi maka
sharri zai dake ka natambayeka abinda kayi mata kace min
cewa tyi dashi na yi mata sata, malam musa yace "fatima a
lokacin ne nasa musbahu a gaba har gidan kawunsa wanda
yake bayan wannan layin na mu, kasancewarsa maraya,
mahaifiyarsa ta rasu tun yana yayayye, yayin da mahaifinsa
yarasu bayan shekara d'aya tsakani wannan shi ne dalilin
dayasa kanin mahaifinsa yadaukeshi yabawa matarsa wadda
ita kuma tadauki tsanar duniya ta dora masa, take wahalar da
rayuwarsa.
Abunda yasa musbahu yazo guna shi ne "lokaci lokaci kawun
na sa yana zuwa dashi nan don daukar karatu da magriba
kuma ya san akwai fahimtar juna tsakani na da kawunsa.
Lokacin damukaje gdan nayi sallama da kawun yafito yana
ganina tare da musbahu ya hau fada ko gaisawa bai bari munyi
ba inda yake shiga ba nan yake fita ba, dakyar nasa yayi shiru
nace "Alhaji Habibu ba haka ake lamarin duniya ba, idan mace
tagaya maka magana saika bincika kafin ka dauki mataki,
sha'anin mata idan akace ba su suka haifi d'a ba sai a hnkali
ballantana d'an dayake maraya.
Albaji habibu yace "duk abinda yagaya maka karya ne don ya ji
Kawai ana cewa maraya ne duk abinda aka ajiye a gidan nan
saiya sace yasiyar sannan idan nayi masa magana sai ytafi
yana hadani da muatane ana cewa muna cutar dashi alhali shi
maraya ne don ba mu muka haife shi ba.
Ina dalilin wannan, haka kawai an ba ni ajiyar kudade masu
yawa yabi dare ya bi rana har dakina ya sace, to ba zan iya ba
yan sanda zansa sukama shi su kulle in huta ko kuma in kai shi
gidan kangararrun yara ka ga na huta.
Na dubeshi tsam sai da yagama fadace fadacensa nace"to ni
kam ba zan bari kakai musbahu gidan kangararrun yara ba
tunda shi ba kangararre bane, idan kai ba za ka iya rikon shi ba
dan kawai ba kai kahaife shi ba ni zan iya, sai dai ina son
kadinga Tunawa wannan yaron maraya ne kuma maraya ne a
gareka, idan kaci amanarshi Allah ya tambayeka kamar yadda
yazo acikin hadisin ma'aiki(SAW) ,sai ya tambayi kowa akan
abinda yaba shi kiwo, maigida mai kiwo ne Allah sai ya
tambaye shi akan iyalansa ya yatafiyar dasu..........
Ya katseni cikin hushi yace "Ni bance kayi min wa'azi ba tunda
nan ba makaranta bace, ka ce za ka iya rike musbahu, ka ga
gashinan kuje kukarata idan yagwada maka mugun halin sa za
ka koreshi ne, da kai ka kama da sannu zan ganku a rana. "
Nace "Insha Allahu ba za kaganmu a rana ba, kai ne dai za kayi
nadamar abinda kayi masa, da sannu za kaga sakayyar da
Allah zaiyi masa kuma da sannu za kagani watarana zai zama
abin taimako gareka da iyalin na ka ma wadanda kuka hada
kai dasu kuka walakantashi.
A lokacin kawun musbahu yashiga dakin da musbahu yake
kwana a zaure yadinga watso masa kayansa yana masifa a
haka nataya shi mu*a kwaso kayan, wannan shi ne dalilin
zaman muśbahu a gidan nan lokaci lokaci dangin iyayansa na
uwa dana uba sukanzo guna suna yi mini godiya shi ma yana
ziyartarsu.
malam musa yaci gaba dacewa fatima lkcn dana gama
tunasar da musbahu wannan lbri kansa na kasa nakara da
fadin "musbahu lkci ya yi dazakayi aure shekararka ashirin da
bakwai a duniya, kana bukatar ajiye iyali tunda kke baka taba
cemin ga wata mace dakakeso ba sbda kunya dakake da ita
da kawaici.
Musbahu ka rayu kana hidima gareni vakin iyawarka, allah
kadai yasan kaunar danake maka, wannan shiyasa nadauki
diyata mafi soyuwa a zuciyata nabaka ita dan tazamo matarka
uwar yayanka.
Yayi saurin fadin fTima yana me dafe kirji da fiddo idb
stories
A DAREN FARKO
7
A babban falon alhaji aka sauki iyalan malam,
falon da ba kamarsa a gdan duk wani
kasaitaccan bakon da zai gana dashi a gidan nan
yake sauke shi, aka kawo musu abubuwan ci
dana sha na alfarma.
Alhaji da hajiya maijidda suka fito aka gaisa,
malam yagabatar dasu ga iyalansa aka shiga yi
musu godiya mai yawa, alhaji hace "malam
kwarai dagaske na ji dadi matuka da zuwanku
gidan nan, sbda dama wannan gda ne na mutane
ba mu da 'ya'ya in banda d'a guda d'aya da
Allah yabamu amma idan kashigo koyaushe za ka
iske mutane da yawa a gdan ko da yaushe muna
godewa Allah kalar jama'a kam ba wadda ba ma
gani a wannan gida sai dai a gefe guda banji
dadin wannan zuwa na ku ba da sunan godiya
don banga abinda nayi ba, wlh da ace malam za
ka baiwa 'dana khalifa auran 'yarka da na yi
murna duk dan kusan d'aya muke da kuwannan
dukiyar da Allah yabani ba ta gabana ballantana
har in ga wai na fi wani.
Malam yayi shiru yana tunanin maganganun
Alhaji muhammadu, shi kam vai taba burin kai
diyarsa irin gida na aljahi muhammadu ba hakan
yasa hnkalinsa yatashi sosai jikinsa yayi sanyi.
Bayan sun dawo gida suna zaune a tsakar gida
da da daddare zainabu tace "malam ai kuwa a
dazu rukayya take ce min tunda alhaji yanemi
aure a gdan nan mai zai hana abashi fatima.
Sai ya bata rai yace "shi yasa hnkali na yatashi
lokacin da alhaji yafurta wannan magana a
gabanku, sbda ku mata ne karamin tunani gareku,
tunanin ku ba ya wuce karan hancinku, ko da
yaushe kyale kyale na duniya kan dauki
hankalinku ku aikata abinda zuciyoyin ku suka
raya muku sai daga baya azo ana nadama sbda
haka ba na son wannan magana daga yau, shi
yasa ko amsa ban ba wa alhaji ba lokacin da ya
fada, ba na ra'ayin diyata tayi auran dukiya, idan
alhaji ya kasance mutumin kirki mai taimakon
talakawa sai akace muku shi dan na sa da
sauran danginsu haka suke? da zaran mun dauki
fatima mun ba su shikenan kowa ma cewa zaiyi
kwadayi yakaimu ba za ace su suka nemi auran
ba cewa za ayi ni ne nanemi khalifa ya auri
fatima duk gorin da akanmu da duk walakancin
da akayi mata mu muka jawo.
Goggo Abu tace "kuma hakane fa malam bbu
wanda yayi wannan tunanin acikinmu kowa kirkin
Alhajin yake kallo.
************
Tun daga wannan lokacin aminci mai karfi da
zumunci yashiga tsakanin mutanan da iyalansa
da alhaji da hajiya maijidda a lokacin nan shi
khalifa yana kasar germany inda yake karatunsa
na likita.
Alhaji bai da abokin shawara sai malam haka
hajiya maijidda ta dauki goggo Abu kamar yar
uwarta tajini, dukda cewa alhaji muhammadu bai
ka ra nuna wa malam yana son yabawa dansa
khalifa auran 'yarsa fatima ba tun daga wannan
lomacin hankalin malam bai kwanta ba ba wai
don yana kin alhajin ba, malam yana matukar
kaunar alhaji har cikin zuciyarsa kamar yadda shi
ma alhajin yake nuna masa kauna ta tsakani da
Allah, auran fati ne kawai ba ya son yabawa
khalifa sbda abinda zai je yazo.
Bayan shi kansa alhajin akwai mutane wadanda
suke da kima a idon malam suna nuna
sha'awarsu akan malam yaba 'ya'yansu auran
fatima sbda kamun kai na yarinyar da uwa uba
kyawun halittarta bai taba furtawa wani ya ba shi
ba, sai dai yayi dariya kawai yace aure nufi ne na
Ubangiji.
A ranar da alhaji yazo wurin malam da daddare
bayan sun gama karatu da addu"o i yace dashi
"malam idan Allah ya nuna mana rana itayau
khalifa zai dawo daga kasar germany.
Gaban malam yafadi amma bai bari alhaji ya
fahimci fargabar da zuciyarsa ke ciki ba, ya
fadada fara'arsa yace "masha Allah ya kammala
karatun knan.
Alhaji yace "kwarai kuwa karatu ya kammala lfya
don ya samu cikakkiyar takardarsa ta shaida ya
kammala karatun sa a matsayin cikakken likitan
mata.
Malam yace "mun godewa Allah, Allah yasa anyi
a sa'a kuma Allah yadawo dashi lfya. "
*****************
Shi kansa malam baisan dalilin dayasa
hankalinsa yatashi sosai da maganar dawowar
Dr. khalifa ba, tun da alhaji yashaida masa
zancen dawowar yashiga damuwa sosai ko
goggo Abu bai gayawa ba, shi kadai yake tunani
a ransa karshen tunaninsa shi ne ba abinda
yadace yayi wanda yawuce yaba auran fatima
kafin dawowar Dr. khalifa ko da alhaji ya tada
maganar idan yagaya mai ya bada ita shikenan
an huta.
Wannan ahi ne dalilin dayasa yadauki fati yaba
amintaccan almajirinsa kuma d'ansa wanda
yayarda dashi fiye dakowa,a 'ko'karinsa na ganin
iyalansa sun zauna lfya a gidajan mazajansu, tun
ranar daya shiga gdan alhaji yatabbatar wannan
rayuwar ta fi 'karfin fatima ba za ta iya ba me
zaisa yada'u d'iyarsa yakaita inda za tashiga
wani hali rayuwar da mutum ya sabayi ita yake
iyawa,idan yaje inda aka fi 'karfinsa wahala zai
sha.
***************'Karfe bakwai daidai na yammacin
litinin jirgin IRS yasauka dasu Dr. Abubakar
Assadiq wanda aka fi sani da Dr. khalifa a filin
jirgin saman Malam Aminu kano dake nan kano
wanda yad'aukesu daga filin jirgin saman murtala
muhammadu dake birnin ikko jihar lagos, bayan
da jirgin da jirgin daya d'akkosu daga jamus ya
ajiye su da asubahin wannan rana.
Dr. khalifa dogon matashi ne kyakyawan gaske
irin mazan nan da ko wace mace ke burin
mallaka ba wai don shi da mahaifan sa sun
mallaki abun duniya ba sai dan haduwarsa na
gwarzon namiji wanda ya isa a kalleshi a san
cewa shi d'a namiji ne abin kwatance acikin
mazaje.
Yana da madaidaiciyar 'kiba wacce tadace da
tsawonsa ma'ana 'kibar da tsawon basuyi masa
yawan dazasu sa shi muni ba.
Babu inda yabar mahaifinsa alhaji muhammadu a
kyau kamanninsu d'aya har tafiyarshi dai
bambamcin halayyar abbansa mutum ne mai
matukar kirki da sau'ki kai da son mutane yayin
da Dr. khalifa yakasance miskili tun yana yaro bai
da son magana sai dai 'kar'karfar mutum ne
kuma gwarzo wanda ba shi da tsoro ko kad'an.
Dr. khalifa ya taso cikin gata da kulawar iyaye bai
san wani abu wai shi babu ba duk abinda yakeso
shi akeyi masa, hakan ne yasa yagirma cikin izza
da isa da raina mutane, sai dai yana raina wanda
yashiga harkarsa ne, idan baka kalli inda yake ba
ba ruwansa dakai, kuma bai ta'ba damuwa da
yawan alherin dayake yi wa mutane ba idan ma
Allah yayi mutum yana da rabo idan kazo neman
abu gun abbansa sai yabaka abinda yafi wanda
abban zai ba ka ma'ana dai shi kyautar sa
taganin dama ce kuma sa'a ce.
Bayan ya kammala karatun sa na secondary
yafara karatu anan jami'ar bayero dake kano.
Inda Allah yataimake shi shine dukda gatan da
yakeda shi na iyayansa bai wasa da karatu kamar
yadda sauran 'ya'yan gatan ke shagwaba suyin
karatu sbda iyayansu suna da dukiya. Dr. khalifa
tun yana nursery yake da kaifin basira wannan
yasa yake da farin jini a gun malamansa har
izuwa jami'a inda anan ne yazamo kamar jinjiri
wata sha kallo sbda farin jinin dayake dashi,
bayan dai tsabar kyau da iya dressing da Allah
yahore masa.
Kaifin basirarsa yana burge kowa sannan ga
'barnar dukiya dayake wa abokai maza da
mata,shi yasa duk inda Dr. khalifa yake sai ka ga
mutane ana wata irin shafta mai dad'i.
A cikin Bayero 'yan matan dasuka shiga
mawuyacin hali akan son Dr. khalifa Allah kadai
yasan yawansu yayin dashi bai san suna yi ba,
wasu suna ganin sbda dukiyar ubansa ne suke
sinsa, kasancewarsa dan gata ahi kad'ai suka
mallaka duk wannan tarin dukiyar da Allah yaba
mahaifinsa shi ne mai mallakarta to kuma shi
akwai 'ya'yan manyan masu kudi suna matkar
sonsa, su ba abinda suke nema dashi sai shi
kansa, shi mutum ne mai saurin d'aukar hankalin
d'iya mace sbda Allah ya ba shi surar da mata
keso wadda take burge su.
Sai dai kash babu soyayya acikin ra'ayin Dr.
khalifa, babi wata d'iya mace daya taba kallo
yace yana ao da bakinsa wadanda suke nuna
masa soyayyarsu ma share su yake kamar bai
gane ba, a lokuta da dama har tambayar kansa
yakanyi wai meye so?
Ta yaya kake ganewa ka kamu da son wance?
Shekarar sa hudu da kammala digiri dinsa
nafarko a Bayero mahaifinsa alhaji muhammadu
yace "yayi shirin tafiya germany inda yakeson
yayi karatun zama cikakken likitan mata.
Lokacin dayake gaya masa wannan magana suna
zaune ne a falon abban na cikin gida dasafe suna
breakfast tare da mamansu hajiya Maijidda.
Dr. khalifa ya ajiye cup din shayi yana kallon
abbansa yace "abba na ji koda yaushe fa kana
gaya min bbu abinda kafi bukata wanda yawuce
inzauna kusa dakai in kula maka da harkokin
kasuwancinka.
Abba yayi murmushi yace "ina sane da wannan
khalifa sai dai hakan ba zai hana in yi abinda
ydace ba, ina burin kazamo likita don in gina
maka babban asibiti anan kano wanda zan
sadaukar dashi sbda Allah a dinga taimakawa
bayin Allah wadanda ba su dashi.
Yace "abba toh kasuwancin na ka fa? ba ka son
in taimaka maka akansa?
Yace "kada kadamu da wannan saddik ina
bukatarka a kusa dani a ko da yaushe sbda
abubuwa suna mini yawa sannan yaran danake
dasu ba kowane yakeda amana ba, sannan ina
samun matsalar rashin masu sa ido a kan
abubuwa dukda kokarin danake da ganin na basu
hakkokinsu gudun samun matsala irin wannan
toh amma matsalata ba za tasa in ki taimakon
al'umar musulmi ba, na hakura da amfanuwar da
kasuwancina zaiyi dakai kaje kayi wannan karatu
don ka taimakawa al'ummar musulmi 'yan
'uwanmu.
Mama tace "to amma abba kafin yatafi yanada
kyau yayi aure yatafi da matar ko?
Dr. khalifa tadafe 'kirji tare da fiddo ido yace
"aure mama? sghekaruna duka duka ashirin da
biyu ina ni ina maganar aure? don Allah karki
'kara wannan maganar mama ni tun da nake ma
ban ta'ba ganin wata mace da zuciyata ta ta'ba
so ba, wadda har nakejin zan iya aure.
Mama ta ta'be baki tana harararsa tace "kai da
Allah rufe mana baki ni za kacewa ba wata mace
daka taba so, duk 'yammatan dake biyoka har
gidan nan ba 'yan matanka bane? kokuwa kana
zaton ba ni da masaniya kan abinda kake?
Yalangabar dakai yace 'Alah mama ba budurwata
ko daya aciki? su duk wacce kikaga ta zo gdan
nan nemana kawata ce ina nufin abokan karatu.
Abba yayi murmushi yace "to ko ma dai meye za
katafi germany a haka ba tare da aure ba amma
idan Allah ya dawo dakai lafiya za ka yi aure
insha Allahu ka fahimta ko?
Kansa na kasa bai ce komi ba shi kan baya so ko
zancan aure a yi masa don ba batun soyayya a
gabansa ama batun kawaye wadanda ake debe
kewar rayuwa dasu ai babu wadda babu.
Bayan fitar khalifa abba yabata rai yana kallon
mama yace "ba na son kina matsawa yaron nan
kan batun aure tunda ba shi da ra'ayi har 'kwara
nawa khalifan yake da za ace dole sai ya yi aure.
Mama tace "Alhaji ai kaine dai bakasan abinda ke
faruwa ba, dukiyar daka sakarwa yaron nan tasa
yanayin abinda duk yaga damar yi masa auren
shi ne abinda yafi dacewa.
Ya kara tsuke fuska yace "ni fa ba na son zargi
irin wannan muci gaba da dagewa da addu'ar
damuke masa insha Allahu Allah zai tsare mana
shi.
Tace "shikenan alhaji kuma bayan haka kana
sane da maganar yarinyar nan zainab tana
matukar son khalifa amma 'ki'ri'kiri yake nunawa
ba ya son ta ka ki yin wani abu a kan wannan
maganar dakayi inason kabani goyon baya ne don
ayi auransu da zainab har kunyar mahaifiyarta
nakeji yadda fa yake d'angata itama 'yar gata ce
mahaifiyarta na sonta kaga......
Abban yace "Don Allah kihutar da bakinki da
fad'in abinda ke kanki kinsan ba zai yiwu ba.
Daman na ce miki mahaifiyar zainab ba ta son ta
ne, kokuwa kin ta'ba ganin wanda yahaifi d'ansa
yace ba ya so? kawai dai kud'i ake nunawa da
so? kinfi kowa sanin cewa ba zan ta'ba
tursasawa d'ana auran matar da ba ya ra'ayi ba
don muna da dangantaka da iyayanta, kamar
yadda nima ba zanso a tursasawa wata d'iya ta
auri khalifa ba alhali ita ba ta so.
Inaso idan khalifa yatashi aure ya auri matar
dayake matukar so itama tana matukar sonsa,
insha Allahu zanyiwa khalifa bikinda za a jima a
garin nan ba a ga biki na d'an gata irin sa ba.
Farin cikina da kwanciyar hnkalina bai wuce
auran soyayya bane don hka idan khalifa yanason
zainab zai aureta a lokacin daya nuna yana son
aure, idan kuma ba ya sonta zai auri wadda yake
so ne bbu dlilin dazaisa don tana son shi ace
dole sai ya aureta, hkan na nufin ita an mata
adalci shi kuma an tauye masa hakki nsa knan?
Tace "shknan ya wuce.
A DAREN FARKO
8
Ummi d'iya ce ga Hajiya Hauwa yayar Abba
wadda take bin babbar yayarsu Hajiya jummai
duk da cewa kafin tasowar ummi hajiya Hauwa
ba sa shiri da mama don tana cikin masu zakewa
'yan gaba gaba a kan sai abba ya yi aure tunda
ita maman ba haihuwa take ba, in banda hajiya
jummai datafi karfinsu ita kuma tana matukar son
mama sbda kirkinta yayin dasu hajiya hauwa gani
suke duk kirkin dasu jummai ke cewa tana dashi
na kissa ne da munafunci don ta mallakesu su da
d'an uwan tare dacewa babu abinda alhaji
muhammadu ba ya musu hatta saudiya shi yakai
hauwan ita da mijinta kasancewar duk cikin 'yan
uwan nata ma itace ta auri mai karamin 'karfi sai
dai tsananin soyayya, kayan abinci da kudi akai
akai yake musu aike dukda haka hajiya hauwa ba
ta gani kawai sbda ba ta son matarsa hajiya
maijidda, yan biyu hajiya hauwa tafara haifa
sannan tahaifi wani namijin mai suna
Abdulrasheed tahaifi wasu 'yan biyun su kuma
mata ummi ce d'iyarta ta biyun 'karshe inda taci
sunan mahaifiyar abbansu ake cemata ummi
daga ita sai dan autansu umar.
Hajiya hauwa na matukar son ummi
kasancewarta mai halayya irin ta ta, tun tana yar
karama take abokiyar shawara gareta ,ba laifi
itama tanada kyau da d'an gwargwadon abinda
yasa ake dad'a ganin kyaun ummi bai wuce
yanayinta ba da kuma bkin tsiwarta tsiwar kanta
tan yi mata kyau, tana burge mutane da dama.
Bata fiye zuwa gdan abba ba sai ana wani
sha'anin sbda ba shiri take da mama ba, tanada
d'abi'ar duk wanda hajiyarsu bata shiri dashi
itama baza tayi shiri dashi ba, tana biyewa ra'ayi
da son zuciyar hajiyarta shi yasa ra'ayinsu ya zo
d'aya.
Ummi na aji hud'u na secondary Allah yayiwa
mahaifinsu rasuwa kuma a gun zaman makokin
ne wata irin soyayya tashiga zuciyar ummi da Dr.
khalifa farat d'aya a lokacin ummin shekarunta
goma sha shida kacal a cikin 'yan maan ma bata
ri'ka ba shi ne lokacin dasuke tasawa.
Ranar da aka kwana bakwai da rasuwar suna
zaune a d'akin hajiya hauwa ita da babbar
aminiyarta kuma makotansu wato jidda khalifa
yashigo tare da sallama fuskarsa a tsuke yake
amsa musu gaisuwa yace "ina hajiya? "
Jiddah tace "tana gaisawa da ba'ki a sit room
d‹in baba.
Yace "to idan ta fito kice mama ta ce maganar
sa'kon nan zatayi mata waya yanzu dai bai samu
ba ni sauri nake ba zan iya jira tafito ba.
Bai saurari abinda za suce ba ya fice su ma
basuyimagana ba ya ga toh dasuka hada baki
suka fada lokaci guda.
Bayan Fitarsa jiddah tadubi umi tana murmushi
tace "Oh ni tunda nake ban taba ganin mutum
mai jin kai da isa irin yaya khalifa ba ko dan yana
ganin ya had'u ne.
Ummi tayi ajiyar zuciya tace "lallai kam ba abinda
yake sashi ta'kama wanda yawuce haduwarsa sai
kuma dukiyar mahaifinsa wadda yake takama da
ita kina ganin duk tsadar mota khalifa zai hauta
da zarar an shigo da mota sabuwar yayi 'kasar
nan komi tsadarta abbabnsa zai siya masa ya
hau, kuma dan wani karin jin kai da alfahari ma
ba zai yawo a mota d'aya ba sai ya jera motoci
goma yana tsakiya tare da abokansa yana homa
daga bisani ne surutu yayi yawa a dangi da
abokan abbansa ya tsawatar masa a kan yadaina
fita da motoci da yawa haka shi ne yanzu yake
fita da motoci biyu ko uku.
Jiddah tace "duk abinda yayi ya yi daidai don ya
isa yayin, ni kam yaya khalifa yana matukar
burgeni ina mai ba ki shawara ummi in har za ki
iya shiga zuciyarsa kada kibari ya subuce miki.
Ummi tayi ajiyar zuciya tace "jiddah kin san dai
yaya khalifa kuma kinsan yadda rayuwarsa take,
nima kinsan gwargwadon wayewata da fahimtarki
da rayuwa kina ganin zan iya shiga xuciyarsa ina
nufin kina ganin ina da nagartr da zai so ni?
Jiddah tace ummi kina da kyau kuma kina da
wayewa, meye zai gagareki idan kika bar wannan
damar tawuce miki za kiyi nadama.
Ummi ta jima tana nazari kanta na 'kasa tace
kada kijefa min damuwa a zuciyata kan abinda
samuwarsa gareni zaiyi wahala.
Jiddah tace "idan kika sa wa zuciyarki damuwa
akan samuwar khalifa gareki to lallai wahala zai
zame miki, yayin da idan kika sa wa zuciyarki
abu ne mai sauki mai sauki ne kada kidamu da
jin kan yaya khalifa ko haduwarsa da takamarsa
kina da hanyar da za ki iya mallakar zuciyarsa
cikin sauki mata irinmu da ba mu da alaka ta jini
tsakaninmu shi ne zai mana wahalar samuwa ke
kuwa uwa daya uba daya iyayanku suke gdanku
gdansu ne haka gdansu gdanku ne, kitashi tsaye
ki mallaki miji na fita kunya mijin da za a iya
shiga dashi ko ina a kalleku bayan kyau ga dukiya
ga uwa uba ilimi ba jiya kikace min zai tafi
germany karatun likita ba?
Cikin sanyin murya ummi tace "jiddah na yi
mamakin wannan magana ta ki sai jace kin shiga
zuciyata, wlh jiddah tun kafin in mallaki hankalin
kaina insan waye namiji insan menene so nake
matukar so da sha'awar yaya khalifa duk sanda
na ganshi nadinga kwatantashi a matsayin mijina
abinda yas nakasa kusantar kaina gareshi sbda
miskilancinsa kina gani ko gaisawa akayi sama
sama yake amsawa, ban taba gaida khalifa ya yi
min murmushi ba al'amarin har tsoro yake ba ni,
amma khalifa shi ne nakema son dana tabbTar
babu wani d'a namiji da zanwa ko da rabin son
danake masa, tabbas a wannan rana kin fama
min inda ke min 'kai'kayi a da na kwantarwa da
zuciyata soyayyarsa dake raina amma yau kin
tayar min da ita insha Allahu sai inda karfina
yakare xan nemi soyayyar yaya khalifa bakin raina
zanyi duk abinda zan iya don ganin na mallake
shi ba zanyi sakaci wata d'iya mace tarabani
dashi ba ko ta halin 'ka'ka.
Tami'ke a hankalin ta tsaya gaban madubin dake
bango tana kallon kanta tun daga sama har kasa,
doguwar rigace a jikinta wadda tafito da zahirin
suffar jikinta, gashin kanta ya sauka har gadon
bayanta, kamar yadda take doguwa mai kyau siffa
tana daga cikin abinda yake dauker hankalin
maza tare da ummi shi ne gogewar fatarta, ba
fara bace 'kal 'kal amma tana da haske sosai,
fuskarta tanada daukar hankalin mai kallonta,
sannan tana da daukar dressing in dai za tasa
kaya sai sun amsheta sbda ba zai yiwu tasa
kayan dabasu dace da kalar jikinta ba, haka duk
d'inkin dazatayi sai ta tabbatar zaiyi mata kyau
sbda ita Allah ya yi ta da iya zabar kaya dan shi
kanshi telanta daban ne shi yake mata tsala
tsalan dinkuna nagani, duk kayan daza tasa sai
an tabbatar an yi matching dan a birge ai kuwa
tana birgewar, ko a salon iya tsara magana aka
tsaya musamman ummi za tatafi da imanin
mutum yatsaya yasaki baki yana kallonta yadda
za kaga tana tsara xance daya bayan daya mai
shiga cikin wannan ne yasa takeda mutane a gida
da makaranta, hatta malamansu sun santa kan
tsananin iyayinta da son gayu duk kudin da
hajiyarta tasamu akan sayawa ummi sutura mai
tsada da kayan kwalliya suke tafiya kowanne kya
sai an hada mai mayafi, takalmi da fashion don
ace dai an yi kyau.
Ummi tana matukar jin kanta ba kowani d'a
namiji take kulawa ba duk da dumbin masoyan
dake nuna mata zahirin kauna ba wani d'a namiji
daya taba burgeta sai yaya khalifa.
**************
Jidda ce kawai ta 'kud da 'kud kuma aminiya ga
ummi tun suna yara ba ajin kansu kasancewar
katanga ce kadai taraba gdansu kafin rasuwar
mahaifin ummi baida abokin shawara kamar
aminin daya wuce babansu jiddah shi ne dalilin
dayasa zumuncin na su yakara kwari, duka
makarantun dasuke zuwa guda uku a kowacce
rana duka ajinsu daya kullum tare suke wuni babu
abinda yake rabasu sai bacci, kullum shawararsu
daya banbancinsu shi ne jiddah ta fi ummi tanada
tsiwa da jin kai da raina mutane, yayin da jiddah
ke da girmama mutane da gudun zuciya.
Iyayan jiddah hamshakan masu kudi ne su biyu
suka haifa daga ita sai yayanta Habibullah wanda
yake kasar england karatu, itama jira suke
takammala secondary su fidda ita kasar waje tayi
karatun ta na jami'a dukda cewa ta ce babu inda
za taje sai fa in za a hadasu da aminiyarta ummi,
lokacin data fadi haka mominta ta yi murmushi
ne tace "jiddah manya, jiddah aminiyar ummi,
idan har ummi da iyayanta sun amince za ta
outside karatu mai zai hana dady dinta yabiya
mata insha Allahu indai kinga ummi baku tafi tare
da ita ba ,ita ko iyayanta suka ce ba za ta ba.
Cikin tsananin farin ciki jiddah tashigo gdansu
ummi dagudu ta isketa cikin dakin hajiya tana
kwance bisa gado tana karatun littafin hausa
tafisge littafin ta watsar tace "Albishirinki.
Ummi ta lumshe ido tace "kina burgeni jiddah
sbda koyaushe ina ganin ki cikin nishadi da
wahala mutum ya fahimci wata damuwa a
zuciyarki.
Tace 'hakane ummi ban cika sa wani abu a
azuciyata ba ballantana yadameni ina daukar
raywa da sauki dan kada in dami zuciyata zuwa
nayi in gaya miki insha Allahu idan mun gama
secondary tae za mu tafi outside karatu.
Ummi tayi shiru batace komi ba fuskarta ko
walwala babu ballantana tanunawa jiddah ta ji
dadin maganarta, itama jiddar gimtse far'arta ayi
tace "ummi yaya ni dana taho da batu mai dadi
gareki ina mai gaggawar yi miki albishir sai inga
fuskarki ta ahiga damuwa kamar wadda tazo miki
da labarin tashin hankali ?
Ummi tayi doguwar ajiyar zuciya tace "jiddah ba
wai farin cikine banyi ba ba yadda za ayi ayiwa
mutum albishir irin wannan yakasa farin ciki sai
dai inason kiyi hakuri jiddah na gode kwarai da
gaske da kaunar dakike min wadda tasa har kike
jin ba za ki iya tafiya wani gari kiyi rayuwa babu
ni ba, iyayanki suka amince miki akwai haka tare
Dacewa kudi za su kashe ba na wasa ba, babu
inda za ayi haka sai in akwai kauna mai yawa
kuma kauna wadda take ta gaskiya sbda Allah to
sai dai inda gizo ke sakar shi ne jiddah kiyi
hakuri, zuciyata ta yi nisan kiwo a cikin soyayyar
yaya khalifa, ba zai yiwu bayan kammala
secondaru din mu in bar kasar nan zuwa wata
kasa ba ba tare da na san matsayina a zuciyarsa
ba.
Ba tare dani ba duka hanyar da ta dace nabi don
in nemi soyayyarsa ba don in nemawa kaina
masauki na din din din a zuciyarsa.
Tagyara zama har yanzu idanuwanta na kallon
jiddah taci gaba da fadin "jiddah zuciyata tana
yiwa yaya khalifa wani irin so wanda ban taba
tunanin akwai irin son a duniya ba, ba zan iya
bayyana miki irin yadda nake jin ciwon sonsa a
zuciyata ba.
Kullum dashi nake kwana in tashi kullum
soyyayarsa karuwa take a zuciyata ban kuma
samu mafita ba akan yadda zan bullowa lamarin
har gashi tafiyarsa germany ta matso.
Tun a yanxu ban samu mafita ba inaga in yatafi
tafiyar dazata dauke shi shekaru hudu.
Ina matukar tausayawa rayuwata jiddah ban san
halin da zuciyata za takasnce ba yayin dana rasa
yaya khalifa.... .
Jiddah takamo hannunta cikin tausaya wa tace
"ki kwantar da hankalinki ummi in dai yaya
khalifa mijinki ne da izinin Allah za ki aure shi, in
har baki auri khalifa ba to Allah ne bai kaddara
aure ba ba za ayi ba, shi ne amfanin daukar
rayuwa dasauki.
Ummi hakika na san yaya khalifa miji ne abin so
gakowacce irin d'iya mace kowa cece ita kuwa,
ko ni kaina din nan abinda yasa nake nesanta
kaina daga burgewar da yake min na san ya yi
min nisa ne ba zan same shi ba, ke din ma
bansan za ki tsanantawa zuciyarki matsananciyar
soyayyarsa har tashafi duk rayuwarki ba, da tun
farko ban zungure ki da maganarsa ba, ko
dacewa kina sonsa daman chan a baya tun kafin
in tuntubeki da maganar amma tuntubar danyi
miki ita tajefa ki a wannan damuwar.
Ummi ina mai ba ki shawara ta gaskiya akan ki
dauki rayuwa dasauki duk abinda kika zafafa shi
zafi zaiyi gareki Kuma ba wanda zai dagawa hnkli
sai ke din.
Ki cigaba da fafutuka akan neman soyayyar yaya
khalifa har kiga kin aure shi amma dan Allah
kada kibari damuwa ta lalata miki tunani ki
dogara ga Allah sai komi yazo miki dasauki.
Ummi bata kara cewa da jiddah komi ba har aka
fara kiraye kirayen sallan magriba tayi mata
sallama takoma gdansu, dakyar tatashi tayi
sallah taci gaba da zama a daki kan daddumar
datayi sallah tana jan carbi tayi tagumi idanunta
sunyi jawur.
Hajiya hauwa taahigo dakin ta sha adon ta kamar
yadda tasaba kai bakace ita ta ajiye manyan
samari irin su hassan ba, mace ce mai son gayu
shi yasa ummi ke samun daurin gindin gayu da
kece raini a gunta.
Tayi sororo tana kallon diyar tata tace "ummi wai
lafiya kike kuwa kwana biyun nan kin sauya ko ba
ki da lfya ne?
Ummi tadago ido zuciyarta ba dadi tace "hajiya
zauna kiji wata magana.
Dasauri tazauna ummi tace "hajiya barin kashi a
ciki ba ya maganin yunwa, yau zan fayyace miki
damuwata dan kisamo min mafita a cikinta,
hajiya zuciyata ta kamu da tsananin son yaya
khalifa inaso kigaya min hanyar dazanbi yasoni.
Hajiya tadafe kirji tare da fiddo ido tace "ummi
kinsan maganar dakike fada kuwa? a duniya kirsa
wanda za ki so sai khalifa?
Kara gaya mini ko dai ba khalifan dana sani ba
kika ce kina so?
Ummi tamatso kusa dai tadora kanta akan
cinyarta tace "hajiya babu wani khalifa dazan yi
magana akansa wanda yawuce na mu ba zan iya
raba zuciyata da son sa ba kuma ba na bakin ciki
da son da zuciyata ke masa insha Allahu ba xanyi
nadama ba mafita ce ban sani ba ita nakeso
kisanar dani hajiyta.
************
Maganarta tadamu hajiya hauwa yau dai ba ta
son mahaifiyar khalifa haka shi kansa khalifan ba
kaunarsa take ba, a daran takira kanwarta hajiya
sauda wadda ita ke binta ko gaisawa bata bari
sunyi ba tace "saude tashin hankali ne ya saman
a daran nan.
Hajiya saude tace "har gabana ya fad'i "meya
faru yaya hauwa?
Tace "wai ummi tarasa wanda takeso sai wannan
yaron mai shegen girman kan tsiya wanda ko
kallo mutane basi ishe shi ba.
Hajiya sauda tace "wai waye ne ?duk kin rikitani.
Hajiya hauwa taja dogon numfashi cikin takaici
tace "waye in banda khalifa.
Hajiya sauda tace "to sai me dan ummi ta ce duk
duniya babu wanda takeso sai khalifa, kada kibani
kunya mana yaya hauwa kamar ba ke ba ko in ce
kamar ba mu ba?
Hajiya hauwa tace "uhm saude dole hankalina
yatashi kina kallo fa yadda rayuwar yaron nan
yake, ko kallo mutane basu ishe shi ba, gaisuwa
da yake mana ma dan ya zama dole ne a gareshi,
in banda haka khalifa bamu isa yagaidamu ba ni
kam ba khalifa da uwarsa na tsanesu ba zan taba
kaunarsu ba shiyasa da ummi tabudi baki tace
min ba ta da gwani wanda yawuce khalifa hankali
na yayi mugun tashi nayi gaggawar kiranki a
waya dan musan abin yi.
Hajiya sauda tayi murmushi tace "Allah sarki yaya
hauwa ni ko da kika gaya min maganar nan sai
naji zuciyata ta yi 'kal 'kal, na jima banji maganar
data faranta min rai irin wannan ba.
Hajiya hauwa tayi tsaki tace "ke da Allah ana ga
yaki ke kina ga kura me za muyi khalifa, yarinyarn
nan ummi duk dan abinda na samu a gun kayan
kwalliya suke tafiya don dai musamu gallelen
alhajin birni mu darje amma ta lalace kan khalifa,
wannan sangartaccen yaron da bai san yafita
neman na sa ba sai dai dukiyar ubansa dasuks
jiku a ciki shi da uwarsa.
Hajiya hauwa tace, "to sai me idan khalifa bai
nnemi na sa ba sai na ubansa? dama me muke
nema ne? burin mu dama aibai wuce musamu
wani ba ko d'an wani, to bamu samu wanda yake
wanin ba ai a karan kansa sai dan wani to
dawani da d'an wani in dai za mu shaki dukiya ai
mu burinmu ya cika.
Hajiya saude tayi ajiyar zuciya tace "to in banda
abinki saude taya za mu iya mallakar wannan
yaron mai masifar girman kan tsiya, zancan
danake miki fa a satin dazai kama idan Allah ya
kaimu zai tafi germany karatu sai ya yi shekaru
hudu zai dawo, na ji uban abban hajiya yana
gayawa jummai wai so yake yazama cikakken
likitan mata, don haka karatu yakeso yayi a
germany mai zurfi. wlh saude idan kinji kudin da
muhammadu yakashe akan wannan tafiyar na
khalifa sai kin rike baki sai hankalina ya kasa
karba inda zai zauna ma tsawon wannan
shekarun hudun da aka zuba akan su ya ishe irin
mu mumore mun gama arziki a duniya dai.
Wai amma jummai maimakon tai mashi fada
yarage kashe kudi haka akan khalifa sai fadi take
ya yi daidsi.
Hajiya saude tayi murmushi tace "to ko anan za
kisan lallai auran ummi da khalifa shi zaisa mu
mallake dukiyar alhaji muhammadu cikin sauki
kinsan ana cewa daka haifa gwamna gwara
kahaifi matar gwamna saita kawo maka gwamna
har gida sai ka shekara kana yawan neman ganin
gwamna ma baka ganshi ba amma idan kabi
takan matarsa lokaci guda sai kaganshi ba tare
da ka samu matsala ba sbda ita mace mace ce
daban take, yanzu idan muka bi duk hanyar data
dace gun cusa ummi a zuciyar khalifa shikenan
mun mallaki khalifa, idan muka mallaki khalifa sai
yadda mukayi dashi ko uwarsa bata isa tayi
yadda takeso ba sai mu din dai.
Da ba a so muci arzikin slhaji muhammadu kinga
munci dan bakin ciki sai dai yamutu.
Kuma anan ne za mu fanshe haushin da mukeji
na hajiya maijidda uwar khalifa, tana ji tana gani
za mu aurawa khalifa ummi za mu mallake shi
'kaf shi da dukiyar uban na sa tunda dama alhaji
muhammad ba shi da tunani sai khalifa, idan
ummi ta auri khalifa shi kuma zai kasance ba shi
da tunani sai na ummi sai yadda mukayi dashi da
dukiyar ta shi, hajiya maijidda tazama yar kallo
yadda tamaida mu yan kallo mu da dukiyar dan
uwanmu ba mu da iko akanta muna gefe sai
abinda aka sammana me zai hana muyi farin ciki
akan soyaygar da ummi ke wa khalifa, wannan
itace hanya daya tilo da burinmu zai cika kuma
za mu nunawa maijidda ita ba komi bace hancin
gauta ce bata isa komi a miya ba.
Hajiya hauwa tace "tabdijam amma fa kinyi tunani
saude shi yasa ake cewa mai shawara ba ya
aikin banza, tabbas gaskiya kika fada sai dai
abinda nake jinjinawa shi ne tayaya za mu
mallaki khalifa kidinga tuna masifar jin kansa fa.
Hajiya saude tace "kash yaya hauwa ni kunya
nakeji kamarki wannan maganar kalaman nuna
karaya da gazawa suna fitowa daga bakinki,
khalifan banza khalifan wofi har meye shi, wa
yayi ma ballantana yafi wani ko za murasa zanin
daurawa sai mun mallaki khalifa, sai mun shiga
ko ina zamu shiga dan mu tura ummi gdan
khalifa, matakin farko dazamu fara dauka shi ne
ummi za takoma gdansu khalifa dazama, hikimar
yin hakan shi ne a matsayinta tamace wadda
takai mace muka dade muna koyar da ita kissa
da kisisinar jan hankalin namiji tabi hanyar duk
data dace tafara kafa gwamnatin ta a zuciyar
khalifa kafin tafiyarsa germany a wadannan
gajerun kwanakin 'kididdigaggu, ko yaya ne mu
tabbatr khalifa ya bar kasar nan ne da tunanin
ummi ba wai soyayyarta ba.
Kafa soyayya a zuciyar wanda kwata kwata
hankalinka ba ya kansa abu ne mai wahala sai a
hankali, lamari ne da ba ayi masa gaggawa a
cikin lamari irin wannan to ko shakka babu ba zai
ci nasara ba, ana kaddara cewa mutanen dasuke
cin nasarar abubuwan dasuka sa gaba na rayuwa
su ne masu hakuri a dukkan lamarinsu.
Sbda ita nasara kafad'a da kafad'a suke tafiya da
hakuri, ballantana lamari irin wannan ba abu bane
mai wahala amma fa ga mace datasan abinda
take wadda takaranci halayyar d'a namiji, kada ki
jinjinawa ummi jin kan khalifa har jikinta yayi
sanyi, ki kashe mata guiwar taji cewa ba za ta
iya ba ,ko da tanajin cewa ita d'iya mace ce da
za ta iya jan hankalin d'a namiji ko waye shi,
idan kika jinjina al'amarin itama girmama zaiyi a
zuciyarta daga nan sai ta kasa yin komi sai
asarar tashafe mu baki d'aya.
Amma idan kika nuna mata ba kowane khalifa
face namiji kamar kowa shikenan saita ka ra
samun kwarin guiwar kokarin janyo hankalinsa
har muyi nasara.
Yadda za ayi takoma gdansu khalifa da zama
kuwa wannan sai idan Allah ya kaimu wayewar
gari gobe lfya idan nazo sai musan abin yi.
***************
Ba kowa a gidan sai fatima ita kadai, sauran
kannanta suna makaranta yayin da goggonsu Abu
tatafi barkan haihuwa da akyi musu, ta karasa
tankadan garin tuwon datake takai kitchen
tashare gidan tadora ruwan tuwon sannan
takoma kan tabarma tadauki wani littafi na
addu'a tana dubawa maisuna Du'a'ul mustajaba.
Zuwa can ta ajiye ta kwantar danta kan pillow
tana tunanin auran da za ayi mata da malam
musbahu nan da lokaci kadan har yanzu dai
malam bai yanke lokacin da za ayi bikin ba haka
zalika musbahu bai taba kiranta da sunan zancan
ba, kunyarta yakeji kamar yadda ita matake
bala'in jin kunyarsa, kafin malam yafurta cewa
zai hada su aure, malam musbahu ba wanda yafi
shiri da shi a yaran gdan sai ita, tun tana karama
musbahu ya fi kaunarta fiye da kowani d'a a
gidan nan duk abinda yasamu kafin yaba kowa
sai ya ba ta har sai da mutane suka shiga zargin
ko dai son ta yakeyi, ganin bai furta ba yasa aka
watsar haka itama take bala'in kaunarsa tun
lokacin da bata sani ma musbahu ba dan gdansu
baneballantana data mallaki hankalin kanta
tagane musbahu maraya ne yahadu da zaluncin
matar kawunsa har malam ya amshi ragamar
rigimar rikonsa, sai tausayinsa yasa take ka ra
kaunarsa suka rike shi tamkar dan gdansu, in
banda wannan lokaci da malam yake gayan mata,
da ya gayawa mutanensa cewa zai ba wa malam
musbahu auran diyarsa fatima sannan dayawa
wasu suka san ba malam bane yahaifi musbahu
ba sbda yadda malam din da ita goggo Abu din
da yayansu ke matukar ji da musbahu shi ma
haka yazamo dan halak agaresu ya sadaukar da
rayuwarsa gaba daya gun soyayya a garesu,
kyautata musu tamkar su suka haife shi, koda
yake ako da yaushe yana gayawa malam cewa
bai taba kaunarsa a matsayin iyayan riko ba
kullum a matsayin mahifa yake daukarsu wanda
ba shi da kamarsu a duk fadin duniyar nan kamr
yadda yake da tabbacin suma haka suka dauke
shi, rayuwa suke a gdan mai dadin gaske ga shi
dai ba su da abin duniya sai rufin asirin Allah,
abinda yakesa suke jin dadin rayuwa shi ne
girmama junansu da kaunar juna da ake sbda
Allah da tarbiyyar data ratsa duk d'an dayake na
gidan ne, nisan da fatima tayi cikin tunani yasa
har ruwan data d'ora bisa wuta ydinga tafsa
tamanta dashi sannan mutum na tsaye a kanta
bataji takunsa a lokacin daya shigo ba ballantana
sallamar da yayi mata saida yatsuguna gabanta
yace "fatima wani irin tunani kike haka kina
yarinya karama mai kankantar shkaru haka ina ke
ina wannan tunani?
Kafin yagama rufe baki fatima tatashi dagudu
jikinta na rawa za ta shige daki, musbahu ya
mike shima yana murmushi yatare kofar dazata
shiga yana murmushi yace "fati haka za mu
zauna koda yaushe kina guduna kamar dodo
tunda malam yace ya ba ni ke ban kara magana
dake ba ko gaida ni ba kya zuwa kiyi ina dalili.
kan fatima na kasa kamar za ta nutse a gun sbda
kunya, tarufe fuskarta da tafukan hannayenta
yace "je ki kigama tuwon kuma kada ki kona
mana tuwo amma fa lallai yau ke za ki kawo
mana tuwo ni da abokina mansur, idan har bazaki
kawo mana da kanki ba ba na cin tuwon, idan
kinyi kada ki aiko dashi zan kwana da yunwa, bai
saurari abinda za tace ba yafice yabarta tsaye
kamar an zare mata jijiyoyin jikinta tana kallon
yadda ruwa ke tafarfasa akan wuta amma ta
kasa tashi tayi talge, hankalin fati ya tashi kwarai
da gaske idanunta suka cika da kwalla har ji tayi
kirjinta ya yi mata nauyi numfashinta yana sama
sama kamar zai dauke .
Tun tasowar fatima babu wani d'a namiji daya
taba cewa yana sonta ta amsa mai ballantana
maganar soyayya ta had'a ta dashi shekarunta
goma sha shida da haihuwa ajinta hudu a
secondary, tun tana shekara sha biyar ake cewa
ana sonta kasancewar ita yarinya ce da Allah
yahorewa kyau ba na misali ba abin sai wanda
yagani sannan tana da shiga rai yadda kasan
wadda aka tsuma ta da maganin farin jini, in dai
namiji zai ga fatima sai ya yi shaawar ace
matarsa ce.
sbda bayan kyaun ga natsuwa ko magana fati
take ka san ta samu tarbiyya irin wanda duk d'a
namijin arziki yake burin mallka a matsayin matar
aure.
Shigowar goggon ta Abu yasa tatashi dagudu
tawuce 'yar rumfar kwanon dake gaba kitchen
dinsu inda suke hura wuta, goggo tarike baki
fatima yau me ya sameki sai yanzu ake talgen
tuwo? kina sane dacewa ba na son ayi tuwon
dare a gidan nan, fati bata saba karya ba don
haka tai saurin kallon idanunta kadai, goggo dai
ta san akwai abinda ke damunta yau abinka ga
babba ballantana wanda yahaifeka, ta jima tana
nazarin fuskar fatima sannan ta gyada kai tawuce
daki.
Har fati tagama tuwo a sanyaye jikinta yake ko
magana akai mata dakyar take amsawa hatta shi
kansa bakinta ya yi mata nauyi, bayan sun idar
da sallar isha tana zaune kusa da goggo sanye
da hijjabinta da charbi a hannun ta tana ja
hawaye sai neman xubo mata sukeyi tana maida
su dan kar goggon ta gane tayi mata tambayar
da za ta gagara amsawa amma ina dole tatashi
daga gun tashiga dakin dasuke kwana da
kannanta tazauna tana sharar kwalla, har goggo
tashigo tazauna kusa da ita cikin saryin murya da
tausayawa irin na d'a da mahaifi tace "fatima na
san duk abinda zai dameki bai wuce maganar
auranki da musbahu ba, fati kada kicutar da
kanki idan ba kya son musbahu kina sane malam
bazai matsamiki ba, shi ma tunda farko abinda
yasa yace ya ba shi ke kai tsaye dan ya san
dakake har musbahu babu wanda ba zai yi masa
biyayya ba.
Sannan ya yi la'akari dacewa ke da musvahu
akwai kaunar juna mai karfi a tsakaninku tun
kafinn ku mallaki hankalin kanku kusan ku waye
ku a rayuwa.
Fatima tace 'goggo inason yaya musbahu sbda
ba shi da makusa da mace za ta ki shi hasalima
banga abinda baba na zai bakata in ki yi masa
ba, inji ina kinsa a matsayinku na iyaye na,
biyayyarku a gareni wajibi ce, wannan damuwar
tawa ba ta da nasaba na kin yaya musbahu sai
dai ni kaina bansa abinda yashiga xuciyata ya
tsunduma ni a bakuntar rayuwa a yau din nan .
Goggo tayi murmushi tace "ai baki shiga bakuwar
rayuwa ba fatima sai randa kika shiga gdan aure
kika zamo matar aure lokacin ne za kishiga cikin
bakuwar rayuwa wadda baki santa ba amma da
sannu saiki zama 'yar gari har wata rana kigaya
wa wasu yadda aka gaya miki, kowacce mace sai
da tashiga irin wannan bakuwar rayuwar.
Tashi maza ki kaiwa musbahu abinci daga yau
haka za kidinga yi.
Bayan goggon ma cigaba tayi da zama ta kasa
tashi har sai da goggon taleko takara yimata
magana sannan tafita tadauki abincin tanufi dakin
musbahu dake zaure, ta yi sa'a ba kowa a dakin
ta ajiye dasauri za tafita sai ga shi yafito daga
toilet yace "to dawo kidana murna dodon na ki
yananan, har wani rawar jiki kike za kigudu ko?
Tayi murmushi tatsuguna daf da gado tarufe
fuskarta da hijabi, yazauna akan kujera yace
"fatima ki rufe fuskarki yadda kikeso sbda kina da
abin rufewar, mace kyakyawa irinki ta isa tayi irin
kowacci yanga ga kowane d'a namiji ko waye shi
ballantana almajiri kamar ni.
Fatima tun lokacin da baba yabudi baki yakira
sunana har sau uku hankalina a tashe nadinga
amsa masa sbda bansan wace magana zai
gayamin ba wadda har tasa yayi min irin wannan
kiran.
Tun kafin yagaya min na san duk abinda zai gaya
min din magana ce da muhimmancinsa ta isa.
Fatima malam yabude baki yace dani "musbahu
na ba ka auran fatima, wlh fati ban taba kwana a
zaune ba, yadda naga rana haka naga dare
hnkalina ya tashi kwarai dagaske ba dan komi ba
sai dan tunanin dame zan rike mace kamar ke
fatima.
Ina sane dacewa mutane da dama suna tunanin
inasonki ne sbda yanayin shakuwar mu tun kina
karama nima ina karami to Allah yasani fatima
ina matukar kaunar ki sbda haduwar jini da Allah
kan hada tsakanin mutum da mutum amma Allah
ya sani tun da nake ko da wasa ban taba kallonki
da wata siffa ko da wata manufa ba, bayan
kanwata ina kallonki ne a matsayin kanwata
wadda muke ciki daya.
Yana magana ne cikin yanayin tausayin kai
muryarsa kasa kasa yana mata wani irin kallo,
lamarin yajefata ckin sabon tashin hnkali da
rudani idanunta suka kama zubar da hawaye,
fatima ban taba tunanin akwai lokacin da xan iya
zama in miki maganganu makamantar wannan ba
sbda kallon ki nake kamar kanwar damuka fito
ciki daya.
Shi yasa nayi ta jinjinawa yadda zaman aure zai
kasance tsakanina dake.
To amma a safiyar yau abokina mansur yasauya
min tunani akanki ya ce dani 'tunda aure bai
haramta tsakanin ka da fatima ba ba yadda za ai
kunya tahana muku nishadantar da zuciyarku ta
hanyar soyayya, shi aure dakuke gani ba bu
abinda yake rike shi yazauna lfya sai soyayya.
Ya jawo abinci yakama ci yana cewa "fatima har
na rasa dawata kalma zanyi amfani a bakina kan
yiwa Allah godiya daya azurtani da mace kamarki,
fatima in sonki wlh don Allah ni ma ki ce kina so
na inji dad'i.
Bai aune sai kawai yaga ta tashi ta faki idonsa ta
fice daga dakin a guje ya kyslkyale da darya har
da tafa hannu yace Allahu akbar, fati manya shi
abinda yake ba shi mamaki shi ne wai an wayi
gari shi da fatima sun zamo masoya soyayya
kuma irin ta aure.
Tabbas Allah ya amshi ran mahaifinsa ya zamo
maraya sai dai shi maraya ne wanda yai rashin
mahaifa amma ba wanda yarasa iyaye ba, a
rayuwa iyaye suna da daya wa mahaifa ne kwara
d'aya kachal, shi kam Allah yai masa baiwa da
iyaye nagari yagirgiza kai yana murmushi.
****************wannan page goron jumma'a ne
gareku ba ki d'aya,,,, daga jiddan nan dai 'yar
mutan
A DAREN FARKO
9
karfe goma da minti hamsin hajiya saudat ta faka
motarta a kofar gdansu ummi, ta sha ado da
wata galleliyar shadda maroon colour, ta yi kyau
kasancewar su kam Allah ya hore musu kyau da
son gayu.
ita mijinta ba wani mai wadatar zuciya bane
sosai kusan itace mai kudin don yar kasuwa ce,
daga kasar dubai ake kawo mata kayan sa wa na
mata, koyaushe gdan ta cike yake da mata
business takeyi ko ta ina.
Ita kam Alhaji muhammad ne asalin ba ta jari
amma duk da haka ba sa gani.
Taahigo uwar dakin hajiya hauwa tana kwance
kan gado ummi na kwance gefenta zancen
khalifan dai suke, saude tace "kitashi mana tun
yanzu kifara shirya kayanki don da kaina yau zan
kaiki gdan alhaji muhammadu chan za ki zauna ni
zan xan gaya masa cewa tunda Allah yayiwa
mahaifinku rasuwa ya zama dole a tallafa yaya
hauwa a gun rikonku, na san dai idonsa da kunya
ba zaice ba za ki zauna mai a gda ba sannan ita
hajiya maijidda na san za tai farin cikin xaman ki
a gdanta, don za ta ga cewa haka zaisa tasamu
fada a gunmu ke Kuma idan kinje ba cewa akayi
kisaki jiki kina bacci ba, yakin neman zuciyar
khalifa za kiyi ko ta halin kaka sannan ki dage
dun kyautatawa uwarsa, yin haka ne zai sa in
yadawo daga germany ko bai sonki da kansa ita
za takalli kyautatawar da kike mata ta tursasa
shi ya aureki, kin san son uwa shi ne son d'a,
Hajiya hauwa tace "wannan shi ne hanya mafi
dacewa.
Zuciyar ummi fari kal san da tagama sanya
kayanta suka nufi gdansu khalifa, .
A bisa hanya hajiya sauda atana ta wassafa
mata yadda za tai amfani da damarta duk san da
take dashi don jan hnkalinsa.
Ummi jin ta kawai tana dura mata a zuciyarta,
daga alhajin har hajiya maijidda sun nuna jin
dadin zaman ummi a gdan daman fada ne ba na
so nayi a samu matsala in ba haka ba in ba haka
ba idan hauwa da duk yaranta sukace za su
zauna a gdan nn, rikesu xan iya insha Allahu.
Daki guda aka warewa ummi a gdansu khalifa
kusa da na mama, akwai gado da dressing mirror
da toilet acikin dakin, tun a ranar da taje gdan
aka gama wannan mama maijidda tace da ita
'"gdan nan gdanku ne kin sani ki dauki kanki fiye
da yadda kike rayuwa a gdan iyayanki, duk abinda
kkeso akwai su idan ma babu kada kigawa kowa
kigaya min in har da kudi za a siye shi zan saya
miki ummi.
Batazo gdan nan dan cutar da khalifa ko iyayansa
ba dan haka za ta nemi soyayyar khalifa a bisa
hanya ta gaskiya da tsakani ga Allah.
Ta tashi tabude kofar sakamakon kwankwasawar
dataji ana yi, daya daaga ckin yan matan dake
aiki ne tace da ita,
"Mama ta ce in zo in ce miki an gama sanya
abinci a tebur kifito kici.
Ummi tace "ki ce ina zuwa. Har yar aikin ta tafi
ta kirata tace "meye aikinki agdan nan?
Tace wanke wanke wani lokaci ina yin girki.
Ta jinjina kai tace "wa ye yakedafa abincin da
yaya khalifa yake ci?
Tace"yana da kyankyami bai yarda da abincin mu
ba shi da abbansa mama ke dafa musu abinci sai
dai mu tayasu shirya tebur kawai
Tace "yanzu ya dawo?
Tace "eh yana falon dasuke cin abinci shi da
iyayansa.
Cikin zumudi ummi takoma daki gaban katon
madubi ta tsaya tana kallon surar jikinta, daga
sama har kasa tana tmbayar kanta shin tana da
tagomashin da zata iya jan hnkalin namiji kamar
khalifa?
Tafito falo cikin yauki khslifa yana zaune kusa da
abansa kan kujerar zaman mutum uku sanye yake
da bakar kot, da wandonsu.
Zahiri da badini khalifa ya yi kyau ba na wasa ba
kamar yadda yake kyau a idon kowacce mace
ballantana ummi data mutu acikin soyayyarsa.
Ta gaidasu gaba daya, kallo daya shi ma khalifan
yayi mata yamaida kansa ga jaridar da yake
dubawa kafarsa daya tana kan daya, mama ce
tace dashi khalifa ga kanwar ka nan ummi ta
dawo gdan nan da zama.
A nan ne yadan ajiye jaridar akan cinyarsa yakalli
ummi suka hada ido yayi mata murmushi
takaitacce yamaida ganinsa ga mama yace "ya yi
dai dai hakan kinga kin samu mai tayaki zama.
Tsigar jikin ummi yadinga tashi sakamakon
murmushin khalifa da ta gani kuma ita yayiwa
murmushin.
Karfe taran dare khalifa yatashi yawuce dakinsa
ya kara yin wanka yasauya zuwa blue din jeans
da farar t shirt yazuba wani mai tsadar takalmi
ga farin gilash dan siriri ya manna ya fesa turare
yadawo falon da iyayansa ke zaune yarusuna daf
da abbansa yace"abba ba ni aron makullin
motarka za ni unguwa in dawo.
Ba musu yazaro key din ya damka masa yakalli
mama yace "mom sai na dawo.
Ta sha kunu sosai tace ina za ka a wannan
daren?
Yadubi agogo yace "mom wani abokina zan duba
a asibiti da asubahi za a tafi dashi egypt.
Tarasa abinda za tace sai kallo tabisa dashi har
yafice kamar yadda itama ummi ta lalace kan
kallon sa.
Tabdijam ashe jan aiki ne a gabanta
**********
Khalifa bai dawo ba sai biyu da rabi na dare,
yana shiga dakinsa yafada bisa gado bacci yai
awon gaba dashi .
Da sassafe ummi tariga kowa tashi agdan tayi
wanka tatsala ado za tashiga kitchen sa'ar da
tayi ita gwanar iya girki ce da kwalliya ta yi cos
din wadannan abubuwa guda biyu a gun
hajiyarta.
Mama tafito wurin karfe bakwai d rabi tana shirin
hadawa abban kayan tea sbda fitar da zaiyi
dawuri, sai taji kamshin girki ya game dakin.
tashiga kitchen suka hada ido da ummi tarike
baki tana murmushi tace 'oh sannu da himma
ummi irin wannan kamshi hka?
Ummi tatsuguna tana murmushi tagaida tace
"ummi ke za kidinga girki a gdan nan, girki ba zai
hanaki bacci ba a lkcn da kowa ke hutawa ko yan
aikin nan a yanxu haka suna chan suna bacci
idan ba abban ne zai fita da wuri ba sai karfe
gomaake gama abinci sannan aci.
Ummi tace "mama ai daga wannan rana dana
dawo gdan nan da zama insha Allahu ruwan
shayi ba za ki sake dafawa da kanki ba sai fa in
ba na nan, kuma yau ma na tashi da wuri ne jin
abban ya ce zai fita dawuri.
Mama tagyada kai tace "ya yi kyau lallai na san
za ku shirya da yayanki khalifa don yana son
abinci mai dadi.
Gabanta yadan fadi tayi murmushi kawai.
A kwanaki shida da ummi tayi a gdan kafin
tafiyarsa germany sai da tayi kokarin da khalifa
yake kulata a kalla yana amsa mata gaisuwa
cikin fara'a har yakan ja ta da magana a wasu
lokutan.
Ranar laraba da asuba ta kama tafiyar khalifa
germany a daran talata bai shigo ba sai sha biyun
dare yan can wurin abokansa da yamatansa da
sunan sallama.
Mama tana zaune a dakinta ita kadai bayan ta
idar da sallar shafa'i da wutiri da casbi a
hannunta, ummi tashigo da food flask a hannunta
tatsuguna gaban mama tace "mama yaya khalifa
ya ce amala yau yakeso da miyar kubewa ya ce a
gama da wuri, na yi masa tun magriba ga shi har
yanzu bai dawo ba.
Mama tace "na yi zaton ma kinyi bacci dama tun
dazu kina falo jiran khalifa? lallai baki san gararin
khalifa ba, idan yaga dama in yazo yaci idan
baiga dama ba cikinsa.
Tace "mama ko dai injira in ya ce bazai iya ci va
ya yi sanyi in dafa mai wani abun.
Mama tace "habadae sai kace kin zamo baiwarsa,
tashi ki mayar da abincin falo kitafi ki kwanta.
Ummi tadawo da flask falo maimakon taje
takwanta sai ta zauna tayi tagumi a daidai
wannan lokaci shi khalifa na daki tare da ramcy a
yau ta kare mai gida taviyo shi har gdan ubansa,
kamar yadda tasha gaya masa ta ce "duk abinda
zai faru in dai a kaina ne ta dauka ba gudu ba ja
da baya.
Khalifa ya rasa yadda zaiyi da ramcy yau ta rikice
msa yini guda yayi a gidanta tun safe har dare
bata barshi ya motsa ba amma da dare yayi bai
san yaya akayi ba har ta biyo shi a motarta ba,
sbda shi kansa a yau ckin natsuwa yake sbda
alhinin rabuwa da gda ba wasa bane tun safe
jikinsa yake a sanyaye dan hka yinin dayayi a
gdanta ma ba abinda ya iya aikatawa sai
kwanciya tana kallonsa kawai.
Sa'ar da yayi shi ne lokacin da zata biyo shi ta yi
shigar mutumci ta sa dogon hijjabi mai hannu
har kasa yana shiga da motarsa itama tasa tata
motar mai gadi zai mata hayaniya kasancewar
dare yayi kuma bai taba ganin motar a gdan ba
khalifa yace yakyaleta bakuwarsa ce.
Suna shiga daki yarufe ta da bala'i yace "ni za ki
walakanta haka? baki san uwata da ubana suna
gdannan ba? me kike son a daukeni dakika
biyoni, toh abinda xan gaya miki shi ne na barki
kin shigo nan dakinnan ne don kar inyi hayaniya
dake a waje wanda bai san abinda ake ciki ma ba
yasani, ki tashi kikoma inda kika fito...
Sai tayi wuf takamoshi tarungumeshi kam kam
tana masa kiss, wannan ne dalilin dayasa khalifa
ba ya hada ramcy da wata dan wata hanya ta
kan shawo kan namiji ta sani komi fushin da yayi
kuwa, tace "khalifa me na rasa ne? meye
mahaifina bazai iya mallaka min ba a rayuwa? sai
kai kai ne kadai mahaifina bai da ikon yamallaka
min sbda kudi bazai siye ka ba to yaya zanyi da
raina khalifa?
Jikin khalifa yayi sanyi kwarai da gaske bai taba
tausayin wata diya mace irin yau ba, musamman
yadda take me kuka da hawaye.
Dai dai wannan lokaci ummi ta gaji da zama a
falo tana takaicin ace khalifa bai ci wannan
abincin ba yadda tzauna ta tsara shi hakan yasa
ta kasa juriyar tafiya ta kwanta ta zuba abincin
ta jera a plate tanufi dakinsa tunaninta shi ne
tabar masa a dakin nasa tunda tana da makullin
dakin shi da kansa yabata sbda yanajin dadin
yadda take gyara masa komi a dakin a tsaftace.
Tana isa kofar dakin tasa makulli ta bude, abinda
tagani yasa gabanta mugun fadi, yaya khalifa
rungumeda mce tana sanye da hijjabinta, bayan
Runguma ba wani mummunan abu da ummi
tagani amma duk da haka sai da abincin
hannunta yasubuce ya tarwatse a gun takoma
ckin gida da gudu tana haki, wani abin takaicin
tahadu da mama a falo za ta sashen abba.
Gaban mama yafadi tatsare ummi da tambaya,
hnklin ummi yatashi tarasa abinda za tace wani
karya za tawa mama, mama tawuce tabarta jiki
na tsuma.
Khalifa ture ramcy yayi yace shkan hnklinki ya
kwanta kin tona min asiria gdan mu ko?
Za tayi magana yadaka mata tsawa yace, "kawai
kifita idan kikaci gaba da tsayuwa anan komi zai
iya faruwa dake tunda asirina ya tonu ba na
fargabar komi dn haka kama gabanki.
********
Karfwme dayan dare tayi khalifa ya kasa
runtsawa, ganin da umi tai masa rungume da
mace ya tayar mai da hnkli matuka bai san wani
irin kallo yarinyar za ta ci Gaba da yi masa ba a
yadda take ba shi girma shknan ta daina ganinsa
da kima bayan wannan za ta iya gayawa mama
daga nan maman za ta iyasa wa ai masa aure da
diyar da maman ke son ya aura itace 'yar
aminiyarta mai suna ummi.
Yamike cikin tsananin mutuwar jiki cikin sanda ya
kwankwasa dakin ummi a hnkli ya san dai da
wahala su abba su ji.
ummi tamike ckin tsoro tace waye?
A hankali yace ni ne khalifa, dasauri tamike ko
kayan bacci yau bata sa ba, kayan jikinta ne
hijjabin datayi sallah, ta tsaya jikin bango tana
kallonsa, cikin kakkausar murya ta jaruman maza
yatsare ta da idanunsa.
A wannn lokaci hnkalin ummi yai matukar tashi
yace "ummi
Murya na rawa ta amsa yace me ya kaiki dakina
dazun?
Tace abinci kawai naje kai maka na ga ka jima
baka dawo ba ni kuma ba na so yakasance baka
ci abinci ba sbda tun azahar na shiga kitchen
nahda maka shi.
Ya danna mata harra kamar zai shaketa yace
'damaa a dakina nasaba cin abincin?
Sai dai na zo ne dan in gargadeki dan kisani kada
wani yaji kinga wata mace a dakina.
Idan kuma naji ko da wasa wani ya furta ta ko
shakka babu na san ke kika fada, saiki saurari
matakin dazan dauka wanda ba zai taba yimiki
dadi ba.
Sannan maganar soyayya tsakani na dake bbu, ni
ba sa'anki bane, idan naji kince da mama ko
abba ko wani cewa kina sona xa kisha mamakin
matakin dazan dauka akanki, idan wannan ce
gulmar da kika dakko kikazo gdan nan da ita
sbda ni to kikoma don ba xa kiyi nasara ba, yaja
tsaki cikin hushi yafice daga dakin.
*******
Tabdijam su duka biyun bbu wanda yayi bacci a
wannan dare, abinda yadaga hnkalin kowa daban
kowa tunaninsa daban.
Bayan fitar khalifa ummi tatashi ckin tashin
hnkali tayi kuka kamar ranta zai fita tadubi agogo
karfe biyu da minti ashirin bata ga nisan dare ba
takitra mahaifiyr ta a wannan dare tana kuka
wayar a kashe, hajiya sauda itama a kashe, takira
babbar aminiyarta jiddh bata kashe waya ba,
jiddah tadauka a figice tana fadin "inalillahi wa
inna ilaihir raji'un. tadaga wayar abinda tace shi
ne "ummi waye yamutu?
Musanman kukan dataji ummin na rusawa kamar
ranta zai fita, tace ni ce na mutu jiddah mesa
kuka ban kwarin guiwar in so wanda ba zai so ni
ba?
Jiddah tayi ajiyar zuciya tace "ummi yau
kwananki nawa a gdansu khalifa?
Tace "shidda.
Ta j tsaki tace "gaya min abinda yasa kika kira
kanki matacciya gashi kina raye.
Cikin sanyin murya ummi tabayyanawa jidda
abubuwan dasuka fru a wannan daren, jiddah tace
"kin ban kunya da hushi ummi kuma kin kashe
kanki a wurin khalifa.
jiddah tace "ummi ita nasara tare suj tafiya da
hakuri, tunda khalifa tafiya zaiyi abu daya yarage
miki shi ne kiyi kokarin yin abinda zai matukar ba
shi tausayi tyadda idan yaje jamus abin zai tsaya
masa a rai, .
Khalifa na sanye da bakar kot ya tsuke sosai
fuskar nan ba fara'a ya sha kunu, mama tana
dakinta ko fita batayi ba, ummi ta bishi dasauri
ta tsaya daga baya a langabar da kanta a jikin
bango tana kallon khalifa yana taku dai dai.
Lokacin dazai shiga motar ne ya waiwayo sai
karaf kuwa suka hada ido da ummi, sai yayi cak
yana kallonta bai shiga motar bazuciyarsa
tashiga harba wa, ganin haka sai ummi tadaga
hannu sama da nufin tana masa addu'a kuma
tashiga yi masa bai bai da hannu tashiga ckin
gda da gudu.
Khalifa yafada mota abbansa na kusa dashi
direbansu yahaya yaja motar zuciyar khalifa ba
dadi abubuwa da dama suka cunkushe masa a
zuciya.
Tausayin ummi suka kamashi har suka isa filin
jirgin saman malam Aminu kano hannunsa biyu
tallafe a kumatunsa, abubuwa da dama suka
tsaya mai a rai, abokansa da yammatansa ba
wanda bai nunawa tsananin damuwa ba ama ba
wanda yatsaya mai a rai irin ummi.
Ya kwana yanajin zafinta a ransa a tunaninsa ma
yarinya karama dako secondary bata gama ba
tatsaya gaban namiji tace tana sonsa.
Lokacin dazai shiga jirgi yarike hannun
mahaifinsa yace "abba kayi min addu'a zan bar
kasar nan cike da kewarku zuciyata ba dadi.
Abban yarufe me baki yace "a duk lkcin da mutum
zaiyi tfya abinda yake tsirga mishi shi ne abinda
yafaru lkcn rabuwarku.
Kamar yau danazo maka rakiya insha Allah kamar
yau xanzo taryarka in dai muna raye.
Kazauna da kowa lfya kaji tsoron Allah gun
muamularka da mutane sannan kariki gskiya da
amana ba za ka tabe ba kuma ba za kayi asara
ba insha Allahu
Duk dauriyar xuciya irin na namiji khalifa sai da
yashiga jirgi yana goge hawaye abbansa yabishi
da kallo yana murmushi

A DAREN FARKO
10
Ummi tagyara zama tare da jan dogon numfashi
tace "jiddah khalifa ya tafi ba tare da na amfana
da zaman da nayi a cikin gdansu ba, face bacin
rai da mugun gani da idanuwa na suka gani.
Jiddah tabata rai tana yimata wani irin kallo tace
"wai me yasa kika fiye gaggawa ne ummi, anya
za ki rinka cimma nasara a kan abubuwa, idan
kika dubi tsarin khalifa gaba daya da yadda kike
ba abu ne mai sauki ba mallakar zuciyarsa sai
anyi da gasken gaske.
Ummi tace "to in banda abinki jiddah tawace
hanya zan samu nasara idan nayi hakuri, kada
kimanta fa shekaru hudu khalifa zaiyi a germany
kafin yadawo kasar nan, yana chan Ina nan zan
iya jan hankalinsa jiddah, dole xuciyata takaraya,
ke bari in gaya miki wani abu daya da ban yi
zaton zan gayawa wani ba, ina cikin gdan nan fa
ina kokarin jan hankalinsa na ganshi da mace
rungume a jikinsa a dakinsa, idan zan iya jan
ra'ayinsa zai kawo mace gdan nan ina cikinsa?
Jidda ta ja dogon tsaki tace "daman kina
tsammanin ko khalifa a karan kansa yake sonki
za ki rabashi da yammata ne, namiji irin khalifa
ko baice yana son 'yanmata, za su yi tabinshi tun
bai kula ba watarana sai ya kula, don hakama
shawarar da zan ba ki itace idan kinyi nasarar
mallakar khalifa to ki sanya hakuri mai yawa a
zuciyarki akan 'yanmatan da za suyi ta bibiyar
khalifa don ba namijin mace daya bane.
Ummi tajinjina kai tace "tabdijam hakika zan
girgiza kowa a kan khalifa ba zan hada miji da
wata ba, ba zan yi tarayya da wata macen a
dakin khalifa ba.
Jiddah takyalkyale da dariya tace "ummi manya
har khalifan ya zo hannu da za ki wannan cika
bakin.
Ta lumshe ido tace "kuma fa hakane maganar
dakika fada ne naji kamar har na mallake shi na
ji tsananin takaicin hadashi da wata da zanyi a
sunan kishiya .
*************
Malam musbahu yana cigaba da karfafa
zuciyarsa ga kaunar fatima tare da tattalin farin
cikinta sai dai ba ya samun hadin kanta sbda
tsananin kunyarta, ba ta iya sakewa dashi hakan
yasa tadaina sakewa a gidan duk abinda take
idan yashigo sai taji kamar za ta nutse a kasa
don kunya hakan na takura shi shima don ya fi
son tasaki ranta auyi soyayyar da za su fahinci
juna kafin lokacin auransu.
Ranar laraba da safe inna ta tursasawa fatima
kaiwa musbahu abincinsa a kokarin innar na
ganin sun shaku ta fuskar soyayya kamar yadda
tafahimci basu sake da junansu ba, fatima ba ta
son shiga dakin musbahu sbda maganar soyayya
da yake mata na daga mata hankali alhali bata
saba ba.
**********
Lafiya kalau khalifa yasauka a kasar germany
inda zai zaman karatun likita ,har yanzu damuwar
daya taho da ita daga nigeria yana makale a
ransa ga kewar iyayansa tamkar bai taba tafiya
ba sai a wannan lokacin, yana shirin shiga motar
dazata kaishi masaukinsa kamar daga sama yaji
an rike mai hannu, yajuyo dasauri yazu bawa
yarinyar ido, Anisa? Yafada cikin shakku dan ba
shi da tabbacin ko daidai yafada sunan.
Tayi murmushi tace "amma na ji dadi daka iya
kiyaye sunana.
Yace "nikam mamaki nayi dana ganki a kasar nan
yaushe kikazo?
Tace "sai mun zauna zan ba ka labari yanzu muje
naga masukinka ko za ka fara zuwa ganin na wa
masaukin?
Yace "ah ba komi inga waya ba sai mun tafi ba.
ta langabe kai tace "kada ka sanyaya min jiki
bayan na yi farin cikin ganinka kayi murnar
ganina.
Yace "hakika na yi farin cikin ganinki domin ina
bukatar abokin debe kewa a wannan kasa da
nazo.
Tace"to kayi hakuri mutafi mana.
Yace "to muje.
Sashensa daban a gdan da zai zauna, falo guda
daya da bedroom ba dai wani girma bane amma
akwai kayatarwa, kitchen kamar na mace sbda
tsaruwar da yayi shi kansa saida yayi sha'awar
ace yanada matar aure wadda za tarika dafa
masa abinci irin na mamansa, wadda yayi mugun
sabo dashi, a zaman da yayi da mamansa bai da
matsalar komi ta fuskar abinci duk abinda yakeso
shi ake masa, duk yawonsa da gararinsa bai iya
cin kowani abinci sai a gdansu sbda shi mutum
ne mai kyama da kuma son cin abinci mai dadi
duk dadin abinci bai iya ci sai a gdansu ko a
halin yanzu yunwa sosai a cikinsa bai san yadda
zai yi ba tunda bai iya girki ba ko ruwan tea bai
iya dafawa ba, hakan yasa tunda ya zube akan
gado bai kara motsawa ba dan ko takalmansa
anisa ce tazare masa.
Tana zaune daf dashi tace "khalifa bayan gajiya
kana tre da damuwa kataimaka kagaya min.
Ya lumshe ido yace "Anisa ba za ki iya magance
min matsalata ba shi yasa nace kar ki biyoni, ba
za ki ga walwala ta ba a wannan lokacin.
Ta marairaice kamar za tai kuka tace "dan Allah
kafada min Abbakar.
Yace "Anisa yunwa nakeji kuma ba za ki iya dafa
min irin abincin dazai gamsar dani ba.
Ta bushe da dariya tace "Abbakar idan yau ban
dafa maka abincin daya gamsar dakai ba to mata
na rako duniya, kuma har yanzu bakasan wacece
ni anisa ba, ko ka san cewa sbda na ji labarin
kana matukar son abinci mai dadi na shiga
fafutukan koyon girki ko ta ina?
Ya fiddo ido yna kallonta, tamike tace banga
tazama ba kafin kagama nazarin maganata bara
in dafa ma abincin.
Ido yabita dashi har ta fice yamaida idonsa kan
rufin dakin.
A wani party suka fara haduwa wanda wasu
dalibai suka shiga sbda nishadi, a lkcn bata dade
dafara xuwa mkarantar ba, tana zaune tare da
kawarta nafisa, suna hira wasu samari suka
tskoanesu har nafisa za tayi magana anisa
tahanata tace "kyalesu dan mu kulasu ne zo mu
bar gun.
Za suci gaba da binsu shi kuma khalifa yana
kallonsu ya aika a gaya wa wadannan samarin su
shiga hankalinsu su kyale su anisa ko yasa a
musu tsirara a gun, samarin wanda sakon yafito
daga gareshi yasa sukayi nasu gurin, ya aika
akira mai anisa.
Mamaki yakamata jin ance wai wani ne yake
kiransu kamar wasu 'ya'yansa taduvi dan aiken
tace "kaje kace a za mu zo ba. ..
Nafisa tayi saurin rufe mata baki tace kinsan
waye Abbakar muhammad? zo muje kawai.
Anisa tace "to me zai mana da har zai ce muzo?
Idan wani abu yakeso garemu mai zai hana shi
yazo da kansa? kai je kace bazamu zo ba.
Dan aiken khalifa yace "idan kika kara furta kalma
mara dadi akan maigidana zanje in gaya mai idan
kuwa nagaya mai daga wannan rana kin daina
farin ciki a wannan makarantar.
Ga dukkan alamu ita kawarki ta san shi ke kuwa
bakuwa ce shiyasa nayi miki uzuri.
Anisa takara fusata sosai za tayi magana nafisa
tarufe mata baki ta ja hannunta tace zo muje.
Har anisa ta dage akan ba ta zuwa sai kuma taga
bara taje taga abinda wannan mai gadarar yake
takama dashi tabashi mamaki.
Khalifa na zaune kan kujera tare da abokansa,
Anisa da Nafisa sukazo gabansu, Nafisan ce tayi
musu sallama ita kuwa anisan bakinta ne yayi
nauyi duk abinda nayi niyyan fada masa ya
gagara sai ido data bishi da shi.
Yayi murmushi yanuna musu gun zama yace
"kuzauna 'yammata.
Bata san sanda tazauna ba, gayen ya gaji da
haduwa ya yi mata ya burgeta anya kuwa ta taba
ganin matashi mai kyaun wannan a rayuwarta?
Tun daga wannan rana suke gaisuwar mutunci da
shi da abokansa, zuciyar Anisa ko yaushe a cike
yake da kuncin son khalifa batasan yadda za ayi
tasamu soyayyar ta sa ba, hatta nafisa duk yadda
suke ba sa boyewa juna sirrinsu amma ta kasa
gaya mata .
Lokacin dataji cieon so na neman hallakata ne ta
sanar da nafisa halin datake ciki, tayi dariya tace
"haba sister na san halin dakike ciki boye min din
da kikayi ne yasa na nuna miki ban sani ba.
Tace ni dai na ji ina mafita? Anisa kai tsaye
zance ba za kisamu khalifa ba, ba za ki iya
mallakarsa ba sai dai in Allah ya sa ravonki ne
amma sai kinyi hkuri mai nisa kafin kicin ma
nasara, kada kifito kigaya mai kina sonsa saidai
kici gaba da hakurin bin wasu hanyoyi dan kija
ra'ayinsa.
Anisa taci gaba da binciken rayuwar khalifa daki
daki me yakeso da wanda bai so, har a gdansu,
abinda yatsorata ta shi ne mata dayake
mu'amula da su sannan ba shi da niyyar aure.
Lokacin daya kammala karatunsa na Bayero duka
shekararta biyu a nata karatun, anan ne
hankalinta yatashi sosai ganin bbu hanyar da
zata kara ganinshi kuma tashiga binciken ina
yasa gaba a rayuwarsa, aiki zai fara ko ci gabada
karatu, bata samu cikakken byani ba sai da aka
dade tana fama da azaban ciwon sonsa a
zuciyarta, tadagawa mominta hankali akan sai an
maidta kasar germany ta karsa karatunta acan,
momin tadube ta cike da mamaki tace "ke kuwa
sbda me?
Kasancewar nisa ce diya tafari a gun mahaifiyarta
kamar kawa da kawa haka suke bata iya boye
mata duk wani sirrin daya shafeta ko meye shi,
taciro wayarta tanuna mata hoton khalifa tare da
bayyana mata halin datake ciki a kansa, tace
"momi tsawon shekaru biyu zuciyata ta rayu ckin
azabtacciyar soyayyar har wani lokaci inaji a
raina kamar mutiwa zanyi idan ban mallakeshi
ba, mom ba zan iya rayuwa bbu khalifa ba ke
kadai ce za ki iya min wannan taimakon.
Hnklin mmin yatashi sosai ta tausaya wa Anisa,
ta jima tana kallonta sannan tayi ajiyar zuciya
tace, "Anisa ba zan ga laifinki ba dan kin kamu da
soyayyar wanda kikeso tunda ba mutum ne yake
dorawa kansa so ba kuma zan yi iya kokarin inga
burinki ya cika.
Zan sa abanku yashirya maki zuwa germany
kiriga khalifa zuwa, zanyi ta binciken tafiyar shi
da saukar shi a kasan, inaso ki kasance a filin
jirgin lkcn dazai sauka domin kibashi mamaki,
dan zai sauka ckin kewar iyaye da abokansa Na
gida tabbas sai ya yi farin ckin ganinki.
Abu guda daya zan rokeki Anisa shi ne kitsare
mutuncinki, kada kiyarda soyayyarsa tasa kibiye
mishi ya lalata miki rayuwa.
Ta gyara zama tace "mom ban taba kallon khalifa
da wata manufa ba mara kyau burina shi ne
muzama miji da mata, ba zan iya bata rawana da
tsalle ba akan khalifa.
Mom tayi murmushi tace "anisa duniya fadi
gareta abinda kika sani shi kika sani wanda baki
sani ba baki sani ba, na san mutumcin soyayya
kuma ina darajata, ni ce mace ta uku da mahaifin
ki ya aura kinsan da wannan ko?
To ina mai tabbatar miki da cewa ni ce mace
tafarko daya fara so a rayuwarsa".

ries
: A DAREN FARKO
11
anisa tafiddo ido tace "to momi me ya hana
yafara auranki har sai da ya auri su hajiya da
mama?
Momi tayi murmushi tare da girgiza kai tace
"Anisa tun ina 'yar shekara goma sha daya
mahaifinki yake so na, so ba na wasa ba tun
muna ganin d wasa yake har kowa ya amince so
yake min na gas*iya,yadinga hidima dani, duk
abinda yasami niyake ba mawa, hr na kammala
secondary dina lokacin aurena ya zo knan ba na
kula kowa.
Lokacin daya tuntubi babana da mganar aurenmu
lokacin na yi candy sai yace ydaka ta masa sai
ya yi shawara da 'yan uwansa, hnklin abbanku
yatshi yanuna min damuwarsa akan haka nace
yayi hakuri na san babana bazai ba mu matsala
ba.
Ahe kuwa matsala na tare damu domin babana
biris yayi har takai ga ya kira abbanki yace
yadaina zuwa guna dan kuwa ya yi min
miji,munga tashin hankali abban ki Ibrahim a
wannan rana domin kuka da hawaye yadi? ga yi
yana rokin abbana yayi hakuri yarufa mai asiri
kada yacuce shi da chan ba a hana shi ba sai
yanzun, ba afi sati ba babana yadaura min aure
dawani d'an d'an uwansa wanda yace shi yzaba
min a matsayin miji.
Wannan abu yajefa abban*u cikin matsanancin
tashin hnkli domin kuwa ba karamin so yake min
ba kowa ya san da wannan.
Hakan yasa yan unguwa akayi ta zagin babana
ana cewa bai kyauta ba anci amanar ibrahim,
wannan ne dalilin dayasa mahaifiyar ibrahim tayi
fushi tazo har gida tana gayawa babana bakaken
maganganu yace da ita ai ba maryam ce kadai
diya mace a duniya ba, bai ba wa ibrahim diyarsa
ba ai ba wani yahaifa masa ita ba, idan anyi
hushi ta aurawa ibrahim mata biyu koma hudu a
rana daya shi ne zai tabbatar ita mai zuciya ce.
Ai kuwa abinda yafaru knan, hajiyar ibrahim ta
nemo mai 'ya'yan aminanta biyu itace hajiya
hauwa uwar gidan abbanku ta yanzu da hajiya
hafsa dakike ce ma mama.
Ibrahim yayi namijin kokarin ba wa mahaifiyarsa
hadin kai dan kada yakunya ta ta a idon duniya
ganin walakancin da akayi mai a kaina,ya amince
da auran hauwa da hafsa wadanda aka daura
auransu rana daya aka fara kai hauwagdan da
hajiyar ta sa tagina mai daga bisani bayan sati
daya aka kai hafsa ,yayin da ni kuma bayan wata
daya da daurin aurena da Aminu aka kaini gdan
iyaynsa dake bayan layinmu.
Na yi kuka na yi bakin ciki mara misaltuwa sbda
ko ido ba na sn in buda in ga Aminu.
Sai daga baya zance yabayyana cewa mahaifin
Aminu ne yake bin babana wasu kudade masu
yawan gaske yabukaci yabashi abinsa ba shi
dashi, mahaifin aminu yace "tunda lokacin
damuka yi za kabiya ya yi kuma babu to sai dai
kabaiwa Aliyu auran maryam in ba haka ba kuwa
zaiyi kararshi ne kuma nan take dole yabiya sa
kudinsa, yace wadannan kudi in dai yabada
maryama to sune a matsayin kudin aure da
kayan lefe, sadaki kawai zai biya a daura aure,
hnklin babana yatashi sosai sbda ya san dai da
kunya yahana ibrahim auran maryam lokaci daya
yabawa Aminu bayan lokaci mai tsawo ibrahim
yadeba yana hidima da maryam tabbas ya san
sai duniya ta zageshi, yayi duk tunanin dazaiyi
dan yasamu mafita bai samu ba, kudi kuma bai
da hanyarsu, hakan yasa yarufe idonsa yana
takaici yaba Aminu aurena, lokacin daya ga
damuwar goggona ya yawaita ne yasa yagaya
mata yadda akayi shi ne nikuma tagaya min.
Hakan danaji yasa zuciyata tadan sosu tadamu
na tausayawa babana domin ko yaushe tunanina
shi ne yadda babana ke son ibrahim meyasa
yahana shi aurena rana tsaka ,bayan babana
mutumun kirki ne ba mutum ne mai kwadayin
abun duniya ba.
: Shekarata biyu a gdan Aminu kowatan bata ban
taba yi ba, shi da mahaifiyarsa suka shiga min
walakanci suna cewa ba na son Aminu shiyasa
naki yarda in haihu, ni kam ina iya kokari na duk
da ba son Aminu nake ba ina mai biyayyaya
shikuma yana wahalar dani kasancewar ba wani
mutumin kirki ne sosai ba halayyarsa ba masu
kyau bane.
Watarana ina kwance a dakina yace dani "in fita
inje gdanmu ya sakeni ba zai iya cigaba da zama
dani ba, ba ni da wani amfani sai inci inyi kashi,
natafi gda na fadawa babana daya tuntubi
mahaifin Aminu kan maganar sai yakama fada
yana cewa kar a gaya mai zancen banza mana
maryama ce tahura wa Aminu wuta sai ya saketa
gar da yi masa gori cewa ita ba shi takeso ba
kuma tunda an yi masa haka kudinsa dinnan dai
sai an biyashi tunda baiga amfanin auran
maryama ga aminu ba, babana yace bai isa ba
tunda dai yakafa sharadi kuma anyi auran a bisa
sharadin daya kafa zancen kudi kuwa babu shi
sai dai in kara zaiyi.
Momi tadan yi shiru tana kallon fuskar anisa
wadda tazuba mata ido tana mamakin labarin da
take ba ta tace,"to momi yaya akayi har kika auri
babana?
Momi tace "Anisa hakika abbanku ya san darajar
soyayya kuma ya mutunta kaunar dake tsakanina
dashi; ahaifin Aminu yayi karar babana yace sai
ya biyashi kudinsa tunda dai diyarsa maryam ta
ki zama da Aminu, kiri kiri alkalin nan yagoyi
bayan mahaifin Aminu bayan ni da baba na mun
bayyana a kotu yadda abubuwa suka kasance wai
sai alkalin nan yace sai na kawo shaidar mutum
daya kwakkwara wanda zai min shaidar cewa
Aminu ne yasake ni da kansa ba ni nace yasakeni
ba, nace banda shaida sai Allah dan shi ne
masanin dukkan abubuwan dasuka faru,, alkali
yace dole sai babana ya nemo kudin Aminu ya
biyashi lamarin daya tayar da hnklin kowa a
gdanmu har kuka sai da babana yayi, kwasam
Allah mai iko bayan kwana biyu dayin hakan sai
ga abbanku ibrahim ya zo gun babana yakawo
mai kudin da sukafi wanda baban Aminu yake
binsa, mamaki yakamashi da kunya yarasa
abinda zai ce, Ibrahim yace karka damu baba ni
fa kaunar dana kewa maryam Allah kadai yasan
iyakarta, duk abinda yashafe ni ya shafeku, Allah
ne bai kaddara itace matata tafarko ba shiyasa
abubuwan dasuka faru suka faru.
Babana yabiya baban Aminu kudinsa kuma yace
bai yafe masa ba, ina kammala idda aka daura
aurena da Ibrahim, ban cika shekara daya ba na
haifeki a cikin shekarata ta uku a gidan nan na
haifi kaninki mahmud, kuma a wannan shekarar
ne Allah yadaukaka arzikin mahaifinku wanda
izuwa yanzu shi da kansa bai san abinda ya
mallaka ba.
Har yanzu iyayena ba su da abin Kauna kamar
ibrahim kamar yadda nima ban iya hada shi da
kowa, abinda nakeso inkaiki gareshi guda daya ne
Anisa mahaifinki dani kaina mun san martabar
soyayya muna mutunta ta.
Mahaifinki ya nuna min kaunar da ban taba jin
wani da namiji dayai wa mace halacci irin wadda
ya min ba ko da kuwa a labari, shi yasa ban
wasa da duk abinda yasha fe shi.
Duk da kasancewarsa adali a tsakanin matansa
amma kowa ya san soyayyar dayake nunamin ba
karama bace shiyasa hajiya da mama suka
tsaneni to amma ba su da ikon komi akaina sbda
sanin halayyarsa.
Wlh Anisa ni kadai ce matar da zan tunkareshi da
kowace irin bukata yayi min ko baida ra'ayi don
hka zan umarce shi da ya shirya miki tfya xuwa
kasar germany don ki karasa karatun ki a chan.
Anisa ina rokon ki kiji tsoron Allah a wannan
tafiya da zakiyi kada kija min bacin rai,duk rintsi
duk wuya kada ki lalata rayuwarki idan ban gani
ba Allah ya gani ki min alkawarin tsare mutuncin
kanki.
Anisa tace "mom na maki wannan alkawari insha
Allahu.
Kowa yayi mamakin batun tafiyar anisa har kasar
germany da sunan karatu tun da babanta dai ba
shi da wannan ra'ayin ko babban dansa da hajiya
hauwa tafara haifa anan kasar yake karatunsa na
jami'a hakan yasa aka dauki hassada aka daura
akan anisa amma dan ita abin bai dameta ba
cikar burinta ne kawai damuwarta har a ranar da
za tabar gida nigeria zuwa jamus batun mominta
guda daya ne.
"Anisa kiji tsoron Allah kada ki zubar da mutuncin
ki baki da takamar data wuce budurcinki a gun
mijin da za ki aura duk abinda zai rudeki kiji
tsoron Allah kada ki biye masa bbu inda zai kaiki
face ga nadama wadda zai sa kiyi ta kunkan da
ba ki da ranar dazaki daina, duk abinda d'a namiji
zai aikata a rayuwarsa ado ne mace ce a cikin
hadari da bakin ciki idan batayi taka tsan tsan da
rayuwarta ba.
A cikin jirgin anisa ta hada kanta da guiwa ne
tana tunanin wadannan maganganun na
mahaifiyarta wadanda suka tsaya mata a rai,
hawaye suka dinga zuba a idonta wani na bin
wani, taji tausayin kanta da iyayan ta jikinta yayi
sanyi sosai batasan yadda rayuwarta za
takasance a wannan kasa ba.
***********
Jiddah zaria
Babban magana wai namiji dasuna Hajara, anya
kuwa Anisa za ta iya cika wannan alkawari na
mahaifiyarta???? ni ma dai jiki na ya yi sanyi
amma dai ga mai fili ga mai doki........ karku gaji
dai kukasance kuna biye dani a baya ganin yadda
za takaya.... Ni ce dai 'yar mutan zazzau.
Hawwa umar. a.k.a jiddah zaria.
A DAREN FARKO
12
Kamshin da khalifa yaji ya halarci hancinsa yasa
yamike xaune yana kallon Anisa, tace "ga abincin
nan tashi kaci kayi wanka kayi sallah.
Ya fubi abincin cike da gamsuwa yace "amma fa
nagode Anisa kin fara ragemin damuwata zauna
kigaya min dalilin zuwanki garin nan.
Tayi murmushi tace "karatu nazo yi nima, rakiya
nayo wa wata kawata za tayi tafiya kamar daga
sama na ganka.
Yajinjina kai yace "na godewa Allah daya kawoki
daidai lokacin da zama ya kamani a nan.
Farin ciki ya mamaye zuciyarta ta fara jiyo
kamshin nasara a cikin muradinta duk da cewa ta
san akwai aiki ja a gabanta.
********
Ruwan sama akayi kamar da bakin kwarya tun
safe har gab da za ayi sallar azahar sannan
yadauke, garin kano yadauki sanyi mai dadi
kasancewarba sanyin takurawa jikin bil'adama
ba. fatima tagama shiryawa cikin atamfarta
maroon mai adon ja da fari, ta yi mata kyau
sosai tadauki littafanta za tafara karantawa inna
tadubeta ta ce "Ajiye littafin nan za ki yi ki kaiwa
hajiya maijidda wamcan man shanun na soyashi
tun daren jiya naso akai mata.
Ta dan bata rai tace "nikam inna ba na son shiga
wannan godan.
Inna tarike baki tace "me mutanan gdan suka yi
miki mutane masu kirki da mutunci wai ke
meyasa ba kya son mutane ne fatima?
Tace "ba haka bane inna kin sani duk abinda
mutum yakeyi ana kallonsa idan ina yawan zuwa
gdan karshe ace kwadayi ne yake kaini.
To a fada din mana "inna tafada a fusace sannan
tadora da fadin "idan har za kibiyewa surutun
mutane ba abinda za ki aikata a rayuwarki dan
duk abinda ka aikata din mutane ba fasa magana
za suyi ba.
Fatima ta dakko hijjabinta tasa ta dauki bokitin
man shanun tanufo gdan abba.
Hannu bibbiyu mama ta amshe ta suna zaune ita
da ummi a falo suna hira, ta tsuguna ta gayar
dasu tamika mata bokiti tace "Gashi inji inna.
Tace "Oh Allah sarki inna da hidima take na gode
Allah saka da alheri zauna sai anjima kya tafi ke
in kin shigo gidan nan sai kace ana korarki na
rasa sanda za kisaba da mutane fatima.
A haka ta dan zauna a darare sai kace akan kaya
tazauna, ummi tadubi ta da fara'a tace "fatima
kin iya kitso ko rannan naga na kan kanwarki
Aysha tace ke kikayi mata yaushe zanzo ki min
irinsa?
Tace 'idan kin shirya yanzu ma sai in miki.
Tace "yawwa kamar kin san kan yadameni da
yawa ina kuiyar saloon, tadkko kibiya da mai da
komi tace "xo mu shiga daki kimin ma yi hira ma.
Mama tayi murmushi tace "Ayi hira ko gulma idan
ba gulma ba me zai hana a yi kitson a nan falon
sai an shiga daki.
Ummi tace "mama wannan hiran ai ta sirri ce.
Tace 'gulma dai knan.
Fatima na mamakin jin dadin da ake a wannan
gida ita kanta ummi ace an shirya mata
kasaitaccen daki irin wannan, tfara mata kitso
suna hira tana ba ta labarin makarantar ta wadda
saura shekara daya ta kammala, ummi tace
"fatima amma idan kin gama za kici gaba da
karatunki ko?
Tace "a'a aure za ayi min in barda ma inna ta so
inyi candy ai da yanzu anyi bikina da malam
musbahu.
Ummi tace "ba dai malamin ajinmu na islammiyr
yamma ba.
Tace "shifa ai dan gidan mu ne.
Ummi tasake kallon fatima tana rayawa a
zuciyarta yaya za ayi yarinya tanada kyau na
garari irin wannan takare gun wani malamin
islamiyya.,kwata kwata fati ba ajin malam
musbahu bace, domin kyaunta yasa wasu har ce
mata suke beauty, dukda cewa ba ta da sakin jiki
da mutane ba ta ayyanar da tsabar kyaunta ta fi
zama da nikab a fuskarta amma dukda haka
kallonta ake ana zuzuta kyaunta, sbda zahiri
Allah yayi mata kyakyawar sura tadaukar hankali
da ace fati irin wayayyun 'yan matan nan ne
masu budaddan ido ba karamin kudin maza zataci
ba sbda in dai batun kyau ake fati ta fi gaban
kwatance abin sai wanda yagani, ita kanta ummi
aduk sanda tadubi fatima ji take kamar takwace
kyaunta, tabbas ace tanada kyaun fati khalifa bai
isa yace ba ya sonta ba, hankalinta bai kara tashi
da fati ba sai watarana dataje gdansu fatima ta
isketa ba dan kwali ta fito daga wanka tana taje
gashin kanta, ummi taga yadda bakin gashin nan
ya kwanta lanban a bayan fatima yana daukar ido
kamar irin yammatan indiyawan nan, ga kirar
jikinta abin sha'awa irin wadda ake cewa coca
cola shape, ita kanta ummi datake mace saida
taji tanason fatima sbda kyaunta kyaunta yayi
mata ga tadai yar talakawa ba wani kayan ado
dazai fiddo da itatake samu ba hakanan ta ki
tawayar da kanta ,duk da haka fati ta isa abar
kallo, kyaunta gdan wani hamshakin maikudi inda
za ta jiku da jin dadi lallai za ayi kallon mace
anan.
Bayan ta gama mata kitson ummi taja hannunta
zuwa kan dressing mirror tarike kugu tana
kallonta tace "fatima kinga acikin kayan
kwalliyarmu mata babu nau'in kalar da babu anan
na baki dama ki zabi duk abinda kikeso wanda za
ki dinga kayatar da kanki dashi gun ado, don
Allah fati ki sani jikinki domin inason kizamo
wayayyar mace mai ado za ki zama abar kallo
fati, Allah ya yi miki baiwar kyaun sura wadda
duk wata diya mace za taso ta mallaki sura irin
wannan, dan banga abinda kika rasa ba fatima.
Fatima tace "Nagode ummi da kaunar da kike
nuna min, sai dai ina son kiyi hakuri ba zan dauki
komi ba anan dan idan nadauka narabaki da
abinki ba zan yi amfani dasu ba.
Ummi tagyada kai tace "fati na fahimci kyamar
dukiyar nan gdan kike yi.
Fatima tace "haba ummi kada kiyi min muguwar
fahimta mana.
Ta tareta dasauri tace "me zai hana in fadi haka
ba muguwar fahimta bane gskiya nafada miki.
Ta girgiza kai tace "kiyi hakuri ba haka bane.
Tace "to in dai ba haka bane zan hada miki kayan
kwallia dakaina dan Allah kidaure kidinga amfani
dasu.
Tayi dariya tace " to na ji ummi amma dai zan
tunasar dake abu daya wanda kwalliya ana yinsu
ne dan afita kinga dai ni babu inda nake zuwa in
banda makaranta,kuma ba wasu maza ke zuwa
guna ba kinga dai ba su da amfani a gareni.
Ummi tace "to in banda abinki fatima shi malam
musbahun ba ya da bukatar yaga kwalliyarki,
gskiya kanki a duhu yake dayawa kibani hadin kai
in wayar miki dashi kada kiyi aure a cikin wannan
yanayin dukda kasancewar malam musbahu
malami ne amma xa ku iya samun matsala acikin
zaman auranku idan kika cigaba da tafiya a
wannan tsarin na ki, namiji dakika ganshi ko wani
iri ne yana bukatar matarsa tayi masa ado yana
bukatar matarsa takasance wayayya mai iya lura
da abubuwa na jan hankali, idan akace mazan
suke waje kadai za ayiwa ado banda na mazajen
aure hakika kwalliya bata biya kudin sabulu ba
knan, mace in har ta amsa sunan mace to tattalin
rayuwar mijin auranta take domin shi ne na ta,
wata kila kina ganin misbahu malami ne kuma
dan gdanku ne ba ya bukatar sai kin masa wata
kwalliya ta jan ra'ayi, wannan kuskure ne idan
ma ra'ayinki ne haka to kisauya domin misbahu
namiji ne kamar kowa rayuwar da zakuyi ta aure
tanada banbanci mai yawa da wadda kukayi a
gida, dole sai kin ajiye wannan kunyar da kke
fama da ita domin tuni na fahimci kunya itace
tahana ki sakin ranki ki zama wayayyiya mace,
idan nace wayewa ba ina nufin kizamo mara
kunya ba a'a kizamo mai wayewa ta fuskar
rayuwa, matukar baki bin wannan hanyar dana ke
son doraki a kanta ba, za kisamu matsala ba za
kiji dadin zaman auran ba.
Fatima tayi shiru tana tunanin abinda ummi
tafada mata, ummi taci gaba da fadin "kiyi nazari
sosai za kiganoinda nasa gaba, kinada kyau
fatima kyaunki kadai ya isa yamallaka miki da
namiji to amma fa masu iya magana kan ce in
kanada kyau ka kaara da wanka,, dan Allah kisaki
ranki da misbahu kidinga tsala ado sosai kina
tsayawa kuna hirar soyayya za kiga yana dada
rudewa akanki, a tunanina babu wani abun
Burgewa ga mace wanda yawuce mijinta na aure
yayi ta sonta ya kasance kullum hankalinsa na
kanta, matukar kuwa bata bi hanyoyin dazata rike
shin ba ba zata samu yadda takeso ba daganan
sai kiga anata samun matsalar rayuwar aure a
dalilin a dalilin hakan za kiga aure ba ya danko
kiyi taganin kananan zawarawa a gari, wadannan
abubuwan da matan mu na hausa ba sa kulawa
dasu suna taka muhimmiyar rawa gun lalacewar
zamantakewar aure.
******
A DAREN FARKO
13
Har fatima tadawo gida tana tunanin
maganganun ummi wadanda suka jefata a wasi
wasi amma tana karfafa kanta dacewa gaskiya ne
mamakinta shi ne yadda ummi tasan wadannan
abubuwan ba tare da ta yi rayuwar auren ba
ballantana tasan matsalolinsa da abubuwan da
ke haifar da matsalolin, koda yake kallo daya
inkayiwa ummi za kasan kanta a waye yake sosai
ta fuskar rayuwa haka karance karancen datake
na littafin hausa suna taimaka mata sosai nagano
abubuwa da dama da suke ckin rayuwar auren.
Fatima na zaune a dakin da suke kwana ne a
wannanlokaci da bai wuce karfe takwas na dare
ba sallar isha'i ta idar tadauko kayan da ummi
tahada mata na kwalliya tana dada kallonsu har
da kayan sawa materail ne kala biyu da
mayafinsu da fashions da agogi ga turarruka har
kala uku, kuma taroke ta idan gari yawaye
tadawo daga makaranta tazo zata rakata saloon
u gyara mata gashin ta, a dazun da wayo da
wayo sai da ummi taja hankalin fatima takai
la'asar a gdansu tana cusa mata maganganu na
jan ra'ayi don dai ta samu ta aminta da
maganganunta har sai da taci nasarar da fatin
tasaki jikinta take ba ta labarin yadda shi kansa
malam musbahu yake nacin son tadinga sakin
jikinta suna hirar soyayya tadaina gudunsa, tace
wani lokacin har tausayi yake bata idan yafaye
mata magiyar tayi mai hirar soyayya ko kaka ne
dan yaji sanyi a zuciyarsa, amma ina tsabar
kunya yasa ba ta iyawa, ko hada ido ba ta yi
dashi, ummi tace "kinji ko ? "
Tace "wannan idan baki bar wannan halin ba idan
anyi auran yagaji zai dinga kula wasu yammatan
ko yadaina baki kulawar dakike bukata kema.
Lokacin data dawo gida innarta rike baki tayi tace
"Tabdijam kece kika yini yau a gdan hajiyar ?
Tace "uhm ummi ce tatsareni da magana kinga
kayan ma data ba ni.
Inna taduba tayi godiya.
Fatima ta san cewa ummi na kaunarta kawai don
Allah, don haka tasaki jikinta da ita sosai tana
kokarin kwatanta abinda take gaya mata, tadaina
dari dari da ummin zama take suyi hira sosai
tazamo tazamo kamar irin aminan nan dasuka
jima da shakuwa da juna, ita kanta fatin ko
dayaushe idan takalli irin alherin da ummi take
mata da yadda tadamu da ita tana nuna mata
tsantsar kauna sai ta dinga mamakin kaunar da
take mata, yakasance ko yaushe ummi na gdansu
fatima ko ita tana gdansu suna hira, malam
musbahu yana matukar jin dadin kawancen
fatima da ummi sbda ta samu cigaba mai yawan
gaske a cikin rayuwar fatima, hakan yasa yake
mutunta ummi tazamo abokiyar shawararsa kan
abin da shafi fatima, duk abinda yataso ita yake
fadawa. ,kuma ckin ikon Allah sai ta nusar da
fatima hanyar data dace nan da nan abubuwa
suka dawo daidai kunyar nan ta fati duktazama
tarihi har tana iya caba ado tatsaya suyi hira
sosai da malam musbahu.
********
Yadda Anisa tashiryawa khalifa abincin safe hka
ta tsara mai na dare wanda yafi na safen dadi
yana can yana baccinsa ya iske an shirya tebur
sai kamshi mai dadi ke tashi tana zaune kan
kujera tana kallon wani fim da ake haskawa ya
dubeta yana mur. mushi yace "godiya nake ranki
yadade.
Tace "na fika farin ciki da yabawarka Abbakar dan
haka ni yafi dacewa in yi godiya gareka bisa
karbar bakunci na dakayi a gdan ka, idan ka
kammala zan koma masauki na abokaina na
karatu suna jirana yanzu muka gama waya dasu.
Ya rausayar da kai har yanzu da murmushi a
fuskarsa yace "bakiyi laifi ba idan kin tafi dole in
barki ki tafi domin bansan zan sameki ba na hadu
dake amma dai va zan ji dadin tafiyarki yau ba
me zai hana ki daure ki tayani kwana.
Ta lumshe ido tare da ajiyar zuciya takwantar da
kanta tana kare mai kallo lokacin daya zauna
yabude abincin yana fadin "A bisa ra'ayinki za ki
kwana a hidan nan idan gari yawaye sai muje
nima inga na ki masaukin, amma idan kinga da
takura sai muje yanzu ba na son inyi abinda xan
matsawa mutum.
Bai jira abinda za tace ba yafara cin abincinsa,
idanunta a lumshe taje tunanin abi ? da kwananta
a gidan zai haifar, har yau idan sunyi waya da
mominta rokon da take mata shi ne tarike
mutuncin kanta kada tayarda wani ya yaudareta
ya lalata mata kuka yaja mata abinda za tayi
kukan da ba ranar karewa., ance idan mace da
namiji suka kebenta a wuri daya su biyu na ukun
su shaidan ne, soyayyat da takewa khalifa ita
kanta har tsoro yake ba tazuciyar ta ta tsananta
da ciwon so mai zafi da tsanani shin akwai
abinda zai nema a gareta ta hanashi.
Bayan ya kammala cin abincin ya wuce dakinsa
ya zuba wasu kananan kaya da suka kama
jikinsa kam kam sun mai kyau abin har ba a
magana, kamshin turarensa ne yafara baibaye
Anisa kafin yabayyana gareta, hawaye suka taru a
ido? ta Allah ya taimaketa suka koma ba tare da
sun zubo ba amma duk da haka idanuwan ta
sunyi jawur zuciyarta ta kuntata tunda take
rayuwa da ciwon sonsa dake hana zuciyarta
sakat bata taba jin abinda taji yau yana mata
yawo a zuciyarta ba, hakan ne yasa tamike
dasauri tace "bari in dakko jakata muje in wa
sisters di na bayani sai mudawo.
Yanayin muryarta yakarantar dashi wasu
abubuwan game da ita, ko da yake yana sane
dacewa tana son shi duk wasu alamu ta nuna
masa ya dai ki nuna mata ya fahimci inda tadosa
ne sbda tausayin ta yakeji.
Ganin bata fito ba yasa yazauna kan kujera
kafarsa daya kan daya yana tuna watarana a b.
u. k aboki? sa bukhari ke ce masa "khalifa kafito
kanunawa yarinyar nan anisa ce ba ka ra'ayin ta
don tadaina wahalar dakanta son da take maka
ba kadan bane.
Ya ja tsaki yace "wai ku mesa ba kwa rabuwa da
gutsiri tsoma, ita anisan ce tace ma tana so na?
Buhari yace "kai da Allah kar ka raina min wayo
ka fi kowa sanin son da take maka idan kuma za
ka iya ba ta soyayyarka to kabata fuskar da za
ta bayyanar ma da abinda ke ranta.
Yayi murmushi yace "Buhari tausayin anisa nakeji
sosai a zuciyata, ban shirya batun aure ba ba ni
da ra'ayinsa idan nayi soyayya da ita naravu da
ita wahala za tasha gara tayi hakuri dani a yanxu
akan ta shaku da soyayya ta a gaba ta rasa ni,
shiyasa nake nuna mata kamar bansan abin da
takeyi ba.
Anisa ce takatse mai tunani lokacin data murda
kofar dakin tafito rataye da yar madaidaiciyar
jakarta tace "inaga ba sai mun fita ba na yi masu
waya sun taho nan din yanzu.
Yace "ba laifi.
Suka zauna shir7 kowa tunanin dayake kara kaina
a zuciyarsa, lokaci zuwa lokaci takan kalleshi
tashare kwallan dake taruwa a idonta, ta kagu
sisters dinta su zo tahuta anya za ta iya kwana a
gda daya da khalifa?
Namijin data kwallafa rai akansa take masa son
da batayi tsammanin anawa wani d'a namiji ba,
suka kirata a waya sukace ga su a kofar gdan
tamike dasauri taje tashigo dasu.
Fadilat da Ramat su ne abokan anisa wanda take
ji dasu komi na su tare suke aiwatarwa gida daya
suke zaune wanda yake kusa da makarantarsu,
amincewar da iyayanta suke nuna mata yake
tsoratata yasa take matukar kiyaye rayuwarta,
Fadilat da ramat suna rayuwar dasuke so da
samari? su yayin da ita ba ta da sakewa da
mazan.
Ita kanta anisan bata ji dadin irin tarbar da
khalifan ya yi wa su Ramat ba, ta dai daure
tagabatar dasu a gareshi sannam taya musu
cewa za ta taya shi kwana ne, basu jima sosai
ba sukace xa sukoma tabiyo su don yi musu
rakiya, suna fitowa fadila datake ta fi ramat zafin
kai ta hau ta da fada tace "dama haka Abbakar
din yake kika gayyato mu gdansa? kina sane da
cewa a rayuwata babu ab8nda natsana kamar
walakanci, meye dalilin na nuna mana isgilanci
haka?
Tace "kuyi hakuri nima banji dadin abinda yyi
mukun ba haka halinsa yake bai da son magana.
Ramat tace "halinsa yake bai da som magana
kuma to haka kike tsammanin za ki iya
mallakarsa, gskia anisa jikina ya yi sanyi da
yanayin khalifa dole ki sassautawa zuciyarki burin
da kika ci akansa.
Jikin anisa yayi sanyi tace "ina bukatar ku tayani
da addu"a xuciyata ba wanda za taso bayan shi,
fadila tayi tsaki tace "aikin banza wai dole sai kin
rayu da khalifa?
Suka tafi suka barta tsaye, ta jima a gun daga
bisani takoma ckin gdan, a nan falom data bars&i
ta tadda shi yana magana da iyayensa a waya
har sai da barci ya dauketa, bayan ya gama da
iyayansa yai tunanin ckin yammatansa wa zai
kira tadebe masa kewa, yanajin wani iri ne a
ransa zaman anisa a gdan ya taimaka masa
amma hakanan yake jin tausayinta ba zai iya
maidata abokiyar debe masa kewa ba yayin da
kudirin datake dashi a kansa ba zai yiwu ba.
Yakoma cikin daki yafidda kayan jikinsa yabar
gajeran wando kawai yahaye gado sai kuma
ummi tafado masa yayi murmushi yakira laila
daya daga cikin yammatan na sa, wayarta a
kashe, yaja tsaki yakashe wayar ya kama barci.
*********
Posting a yan kwanakin nan sai hakuri a dalilin
muna ta hidimar biki, duk yadda aka gani a
hakura da hakan.
A DAREN FARKO
14
GIDAN ainihin iyayan ummi yau hajiya saude tayi
ma tsinke ta iske hajiya hauwan tana shirin fita
tace "yanzu kuwa nake shirin kiranki a waya inji
ko kina gida in biyo ki min rakiya.
Saude tace "ai zuwa nyi inji labarin inda aka
kwana da batun ummi da khalifa, wai shin har
yanzu babu wani labari?
Hauwa tace "uhm wani labari ne ban da na
takaici saude? wannan yaron zai wahala mu
cimma nasara kansa yana da jin kan tsiya.
Saude tace "shi din banza, ke fa yadda uwarsa
taraba mu da dan uwanmu haka za mu rabata da
danta, ba za mu samu wannan damar ba har sai
khalifa ya auri ummi.
Hauwa tace "to tana can dai tana faman bautar
girki a gdan idan yadawo ma san abin yi, yanzu
kam sai hakuri tunda ba ya nan.
Saude tace '"duk da haka bai dace muyi kasa a
guiwa ba da safe ake kama fara idan mukayi
sakaci wankin hula yakaimu dare bazamu samu
yadda muke so ba.
Hauwa tazauna gefen gado tace "to me za muyi
yanzu?
Tace "gun boka za muyi duk abinda yadace a yi a
ja ra'ayin khalifa ga ummi idan ma ta kama
muhana shi zaman jamus din gaba daya yadawo
ya aureta ba matsala.
Zuciyar hajiya hauwa ta karfafa sosai tace,
"wannan shawara ce mai kyau tashi mune.
A daidai wannan lokacin babbar aminiyar ummi
wato jiddah tana wurin ummi ta je yimata
sallama don lokacin tafiyarta london karatu ya yi.
Suna zaune dakin ummi su biyu fatima tashigo
sanye da doguwar rika baka after dress ta yi
mata kyau sosai, malam musbahu ne yasayo
mata da sukaje kaduna da malam, suka gaisa da
jiddah. Ummi tace "kinyi kyau mutuniyar bari in yi
miki hoto ,Allah yasa dai angon ya ganki na san
zai yaba wannan kwalliyar.
Tayi wal da ido tace "shi ne ma ya aiko ni da
kwan zabi yace in kawowa hajiya sunje kauye da
malam sukayo tsaraba, bari ma inje yana jira na
anjima zan dawo insha Allahu.
Ummi tace "muje kitchen in ba ki wani lemo dana
hada hirar taku za tafi armashi idan kunayi kuna
sha..
Fati tace "kai antina kina shagwaba mu dayawa.
Tace "haka yadace.
Bayan tafiyar fati tadawo daki gun jiddah tace
"Allah ya sani ina matukar son yarinyar nan
fatima sbda kyaunta da halayenta masu kyau.
jiddah tace "ai na ga alama za a iya dawo da ita
gidan nan idan tafiya tayi tafiya.
Tace "ai da za ta dawo din ai da na ji dadi mama
da abba ba su da matsalar komi gdansu gdan
jama'a ne suna son suga mutane suna ta zuwa
gdan nan.
Ta ce "ai hakan yana da kyau shin kuna waya da
khalifa?
Tarike baki tace "wane ni?
Tunda yatafi suke waya da iyayansa bai taba
tambayata ba, gaskiyar magana jiddah ina ci
gaba da zama a gdan nan ne dan inajin dadin
zaman gdan a dalilin kirkin mama da abba amma
ba na jin zan samu khalifa ya fi karfina.
Jiddah tace "ni abinda yake hada ni dake saurin
karaya har yanzu dasauran batu, idan da rai da
rabo idan kikayi hakuri watarana za ki cimma
nasara akan khalifa, kidaure kici gaba da zama a
gdan nan a matsayin mai yakin neman zuciyar
masoyinki idan kika ci gaba da kyautata masa zai
iya auranki musamman dayake kin shiga zuciyar
iyayansa duka biyun.
Tace "toh Allah yasa inafa cigaba da addu'a na
san bbu abinda yafi karfin Allah.
Jiddah ta mike da niyyar tafiya ta ce "ina takaici
da zanyi wannan tafiyar ni kadai ba tare da ke ba
soyayyar khalifa ta nisanta ki da kowa.
Suka fito suna ci gaba da tattauna maganar
shawarar da bata wuce abinda yashafi khalifa ba
daga karshe ummi tace "jiddah soyayyar khalifa
tayi min yawa a zuciyata abin har tsoro yake ba
ni ,ina ta kokarin ganin na fidda shi a zuciyata
don in huta amma abin ya ki yiwuwa, ina jiyewa
kaina abinda zan iya aikatawa akan kowa idan
narasa shi, idan na rasa khalifa bai auri wata
macen ba nasan zan iya hakura abu daya ne ba
zan taba iya hakura akaiba shi ne khalifa ya auri
wata macen, ina nufin idan zai zauna haka ba na
ganin mace a tare dashi shike nan.
Jiddah taja tsaki tace "ni wannan shirmen na ki
ne ba na so, wadannan maganganu? ba za
subaki khalif ko su hanaki shi ba.
Tace "ni fa ki sani haka jidda ina gaya miki ne
dan ki san abunda ke ckin zuciyata wannan shi
ne abin tsoron.
Bayan tafiyar jiddah gdansu fatima tanufa ta
iskesu ita da musbahu a zaure suna hira, wani
yaro yashigo da sallamarsa yace "wai wani a
waje ya ce don Allah wadda tashigo yanzu tazo.
Ta tsuke fuska tace "kai tafi kace ba za tazo ba.
Malam musbahu yace "haba ummi bai dace kiyi
haka ba mu maza ba ma son muga anawa yan
uwanmu haka.
Fatima tace "malam ko kaje mana kaji me ke tafe
dashi.
Kafin malam yadawo suka shige cikin gida
innarsu fati ta je unguwa a tsakar ida suka zauna
kan tabarma, fati ta bata rai tace "ummi duk
abinda nayi kina bata rai akan banyi daidai ba
meyasa ke nake ganin ba kya iya sauraron duk
masu kaunarki? shin ke abunda kikeyi daidai ne?
ko kuma dan komi ke ce kika iya;?
Malam musbahu yashigo cike da fara'arsa yana
fadin "don Allah ummi kizo kugaisa da mutumin
nan na san shi mutumin kirki ne sosai.
Tace "don Allah malam kasallame shi yatafi kace
an yi min miji kun taba ganin na saurari wani?
Yayi dan jim sannan yace "to ba zan matsa miki
ba amma zan shawarce shi akan yanemi shawra
a gun abbanku.
Bayan fitarsa fatima ta ci gaba dayi mata kallon
tuhuma ranta a bace take fadin "baki ba ni amsar
tambaya ta ba.
Ummi tayi murmushi tace "fati knan kin more
mijinki ma ya mori mace duk abinda kikayi kyau
yake maki batan ran ma da kikayi yanzu bakiga
yadda kika kara kyau da haduwa ba.
Fatima takara fusata tace "ni ba wannan na
tambayeki ba dole sai kin ba ni amsa ta gaskiya
bisa tambayar dana yi miki idan kuma ba haka
ba nima na daina yin abinda ki ke umarta ta.
Ummi tana dariya tace "idan kin kwantar da
hankalinki ko baki bata rai ba zan fada miki
komai.
Ta mike zaune suna fuskantar juna tace "fatima a
cikin rayuwa bbu abinda ba ya samun mutum
wani yasamu yadda yakeso wani akasin haka,
wanifarkonsa yana ckin jin dadi karshensa
wahala, yayin da wani zai taso ne cikin wahala
karshensa yasamu jin dadi, fatima ni kam bbu
wanda zanso a rayuwata bayan mutum daya da
zuciyata ke muradi.
Waye wannan?
Na san ko baki san khalifa a ido ba hotunan da
kike gani a gdansu zai sa ki shaida shi idan kin
gan shi a fili, khalifa shi ne mutumin da zuciyata
ta rataya da soyayyarsa, wannan shi ne dalilin
dayasa ba na kula kowa dalilina shi ne duk
wanda na kula bata mai lkaci zanyi domin
zuciyata ba za ta so shi ba, me ye amfanin in
yaudari mutum in nuna amincewa na gare shi
alhali zuciyata tana tare da son wani, in dai ba
yaudarar mutum zanyi ba to gwara in kyaleshi
bbu wanda zan mallakawa zuciyata bayan shi,
bbu wani da namiji da zai samu farin ciki a tare
dani sai shi domin shi ne nake da kwarin guiwa
dazan farantawa zuciya ko ina so ko ba na so
sbda karfin kaunar danake masa ba mai
misaltuwa bace, son danake masa ba zai bari in
yi abinda zan bata masa rai ba, wannan shi ne
dalilin dayasa nake ta burin ace shi na aura don
in samarwa kaina farin ciki da kwanciyar hnkali a
auran, kuma insamu tsira a gaban Allah idan nayi
mai biyayya, fatima ina zaton wannan shi ne
dalilin dayasa ake ba ma'aurata daman zabar
wadanda suke so yayin neman aure, wanda
zuciyar mutum ta aminta tana so shi take iya bi.
Fatima tace "toh ummi an yi maganar auranku ne
da khalifan kan tafiyarsa ?
Tayi murmushi "fatima in banda khalifan iyayansa
ma basu san ina masa wannan son ba, ya
gargade ni akan kar in sanar da iyayansa
ballantana a matsa masa kan ya aureni, khalifa
ba ya so na ni ce dai zuciyata ba ta iya hakuri
dashi.
Fatima ta girgiza kai"anya kuwa za ki ce kai
tsaye bai son ki ummi ? shin meye abin ki a tare
dake, ko halayyarki ta arziki ta sa mutum yaso
ki.
Tace "Allah sarki fatima ke ce kime ganin haka, ai
ita soyayya ba ruwanta da kirki ko rashinta, idan
kana son mutum to kana sonsa idan ba ka so
kuma ba za ka so shin ba koda ya fi kowa kirki.
Fatima tace "to yanzu meye abinyi ummi ni bar
na ji na tsani khalifan sbda rashin tausayin daya
nuna miki, bai dace ka watsawa wanda yake
sonka kasa a ido ba ya dace yatausaya miki, ni
kam ina bakin cikin wannan damuwa ta ki inama
inada halin taimakonki wlh da sai inda karfina
yakare.
Ummi tace "fatima idan kika biyewa damuwata za
kiyi tazama cikin damuwa ne domin kuwa
damuwa ba ta kare mini don lokacin dana fara
son khalifa nake kuka nake zama a cikin
damuwar da har sai da nasaba da ita, inata
kokarin raba kaina da soyayyarsa don in huta
amma ko yaushe soyayyarsa karuwa take a
zuciyata abin ko sauki ba ya yi, tunda har aka kai
wannan lokacin khalifa bai waiwayeni ba ba zai
tausaya min ta fuskar soyayya ba kuma dagaske
yake bai sona, ban isa in tursasawa khalifa ya
aureni ba dole knan in hakura da auransa, amma
ba zan iya hakuri dashi ba, ba zan auri ko wanne
namijj ba ba zan hakura da khalifa ba.
********
Khalifa ya fara karatu mai zafi a kasar germany
cike da zuciya mai karfi da cikawa mahaifinsa
burinsa na ganin ya zamo cikakken likita dan
yataimaki al"umman musulmai, Anisa tana tre
dashi a gdansa ta zamo tamkar kukunsa itace
abincinsa na safe da yamma a bisa ka'idarsa na
cin abinci guda biyu kamar yadda ya tsarawa
kansa, ko kusa Anisa batayi niyyan zaman gdan
khalifa ba illa soyayya data rinjayi zuciyarta
wadda ba ta barinta tayi tasiri a tare dashi, duk
abinda yace mata dashi take amfani, yana
matukar gamsuwa da nau'ikan abincin da take
shirya masa kuma yana yaba mata tare da nuna
mata jin dadinsa, lamarin dayayi mata dabaibayi
knan take jin cewa data sabawa dr. khalifa gara
ita ta matsawa kanta, babbar abin mamakin shi
ne duk irin yadda ake neman soyayar mace ga da
namiji zuciyar anisa ta gama nisan kiwo a ckin
son khalifa amma a takure take da zaman gdan
na sa sbda bbu abunda yake hadata dashi sai
hirar duniya ba batun soyayya, idan gari yawaye
tagama masa abin karyawa zai fita zuwa
makaranta itama za taje ta ta, idan tadawo sai
tayi abincin yamma, in dare yayi zai shirya ya
dau ado yafice yawon zaga gari yayin dazai barta
a gida kamar wata yar jiran gdansa, sai ya gama
gararin ta zai dawo yabarta a falo yashige
dakinsa, anan take kwana, wani lokacin tanaji
zaiyi ta hira da yammatansa taci kukanta tagaji
tahakura, idan tayi yunkurin barin gdan sai taga
wata dai sabuwar damuwa ce za ta hada kanta
da ita idan ba ta ganinsa.
Yau ta tashi da kasala zuciyarta bbu dadi tahada
abincin safen kamar yadda tasaba tashiga falon
fuskarta bbu walwala, dr. khalifa na zaune teburin
cin abinci bai fara cin abincin ba magana yake a
waya tazauna tana mai kallo, a kullum shi me
kyau ne amma kyaun dayayi yau na daban ne,
wani irin abu taji ya kara turnike mata zuciya,
idanuwanta suka kada jajur tazauna kan kujera
taci gaba da kallonsa yanata hirarsa a waya cike
da nishadi abubuwan dayake fada suka cigaba
dasa zuciyarta a wani yanayi tadinga jin cewa
meye amfani zamanta a gdan khalifa kullum ranta
na baci, bata san inda tadosa ba, ya kamata
tayiwa kanta fada.
Bayan ya kashe wayar ya kawo ganinsa gareta
yace "ya akai sister an tashi lfya ko,?
Wani irin kallo tayi masa wanda bai taba gani ba
tare da ita yataso zuwa gabanta yatsaya
hannayensa zube ckin aljihun wandonsa yana
kayataccen murmushin nan na sa mai kayatar da
zuciyarta amma yau takaici ne yakara rufeta,
hawaye suka taru a idonta tai sauri tashige daki.
Khalifa yatsaya shiru yana kallon kofar dakin nata
cike da mamakinta, ko dayake bai kamata hakan
yazamo abun mamaki ba gareshi don yanada
tabbacin son da Anisa ke masa ne yasa tayi
shahadar zama a gdansa tare da sadaukar da
kanta gun hidimar dafa abinci da gyara mai gida,
hatta gadonsa ita ke gyarawa za tawanke mai
toilet tagyara mai kayan sawar sa da komi na sa,
in banda ya dage akan bai so tai masa wanki da
gugar kayansa da tuni ita ke wankewa don har ta
fara ya yi mata jan ido yace ba zai yiwu ba
ayyuka za suyi mata yawa, ita ba lada zai biyata
ba ballantana yadinga biyanta kudi ,damuwarsa
itace bai san dawani ido zai dubeta ba ranar data
gaji ta bayyana mai batun soyayya da bakinta
tare da bukatar aure, alherinta yanada yawa a
gareshi.
Bai jima da fara zuwa makaranta ba yasamu
aboki guda daya mai suna Faisal wanda yafito
daga gda Nigeria jihar kaduna, Faisal tantirin
matashi ne mai budaddan ido yadda khalifa ke da
farin jinin yammata haka faisal yayi fice a wannan
fannin, sa'ar da akayi shine faisal na da kokarin
karatu, wannan shi ne dalilin dayasa khalifa yaji
dadin abota dashi bayan haka faisal ba bako bane
a kasar germany ya saba zuwa kuma yanada
yammata da yawa, tun da suka fara abota khali:a
yasaki ransa sosai ko yaushe suna tare sai
lokacin barci suke rabuwa anan fa 'yammata
suka fara kawo kansu ga khalifa, son karatu
dayake yasa bai son su shiga jikinsa sosai don
kada su shagaltar dashi.
A yammacin jiya bayan sun kammala da
makaranta wata budurwar khalifa mai suna
shukura dasuke cewa 'shu baby'ta nace akan sai
ta biyoshi gdansa yau dai ta tayashi kwana tace
in kuma bai sonta yafito yagaya mata, yace
"nikam ba na bukatar kwananki a gidana kiyi
hakuri.
Tace "ni na rasa dalilin dayasa kake min haka ko
dai matar aure gareka a gdan.
Faisal ya ja tsaki yace "ke ce kika kwallafa ranki
kan wannan wahallaln ina mamakin dabi'unka
khalifa har yaushe kanada matsayi irin wannan a
rayuwa za ka takura kanka.
Khalifa yace "faisal na fi shu baby bukatar ta a
gidana ina kaucewa hakan ne sbda Anisa.
"Anisa ?
Faisal yafadi ckin mamaki.
Ya amsa mai da fadin "Anisa mana, anisa ta
cancanta in kaucewa abinda zai bata mata rai
tana hidima dani sosai.
Faisal yace "ka ga tunda ba ka iya debe kewar
rayuwa da ita kasallameta daga gdan mana
kadauki yaron gda wanda za ya dinga maka duk
hidimar da Anisa ke maka tunda ba kudin dazaka
biya karasa ba, yaya za ayi kazauna kana
shakkar sakewa a gdan ka sbda Anisa, gskiya
kasauya tunani.
Tausayin anisa yakeji sosai a ransa shi kansa
yana bukatar mai debe me kewa a gidan ba zai
yiwu yadinga kwana shi kadai a gado ba bayan
yanada ikon yin hakan.
Yayi ajiyar zuciya yamike da niyyar yaci abincinsa
yabar gdan, sai yakasa yanufi dakin data shiga
yabude tana kwance rub da ciki bisa gado tana
kuka, yahaye gadon yakwanta kusa da ita yana
shafa bayanta da fuskar ta cikin muryar nan tasa
mai taushi da kayatar da zuciya yace da ita
"bansan dalilin wannan kukan naki ba Anisa in
dai ina da matsayi a gunki na hadaki da Allah ki
bayyana min damuwarki.
Tabude idonta zuciyarta a karaye tace "Abbakar
ba za ka iya min maganin damuwata ba da za ka
iya da bamu kawo wannan lokacin cikin wannan
yanayi ba.
Yace 'haba anisa Allah musuru gareni da zan san
damuwarki har in magance miki ita alhali baki
sanar dani damuwar ta ki ba.
Tamike zaune tana goge hawayen dasuka cigaba
da zubo mata tace "Abbakar meye dalilin zamana
a gdan nan?
Ya amsa "kauna.
Me yasa kace kauna?
Ya amsa "Na san babu abinda zaisa ka zauna da
mutumin da ba ka kauna, dan haka kaunar da
kike min ce tasa kika zauna tare dani.
Bayan wannan za ka iya rantse min da Allah akan
cewa bakasan wani abu a zuciyata ba game da
kai.
Yace "to in banda abinki anisa akwai wanda
yasan abinda ke cikin zuciya bayan Allah?
Ya matso jikinta sosai yakamata yarungume yayi
mata kiss yace "kidaina sawa zuciyarki komi
game dani kidaina bari ranki yana baci duk
abinda kike bukata zan miki.
Ya yi hakan ne dan yahanata fadin abinda yasan
tana daf da fadinsa, yashga shashafa mata
bayanta da cinyoyinta nan da nan jikinta yayi
sanyi tadinga jin wani irin abu na yi mata yawo a
jiki, so ya yiso a zuciyarta kallon kyakyawar
fuskar khalifa ya hanata ta hanashi aiwatar da
abinda yake mata alhali nasihohin mominta na ta
kai kawo a zuciyarta, zuwa can khalifa yadinga
fidda numfashi dasauri dasauri yana cakudata
yadda yaso, abin yafara ba ta tsoro tayi kokarin
janye jikinta daga na sa yayi wuf yakamota yana
fadin "kar ki gujeni a wannan lokacin ke ce kika ja
ra'ayina ba zan iya hakura dake ba ki daure
kibani hadin kai zan maki maki duk abinda kikeso.
Ya kwantar da ita bisa gado yadanneta da
faffadan kirjinsa yarufe ta ruf yana mata kiss,
gabadaya hankalinta ya tashi sosai sai jikinta
yake rawa, a haka dai khalifa yasan ta diya mace
yayi mamakin yadda yasanta a matsayin sabuwar
budurwa wadda bata taba sanin da namiji ba,
dama "yammata suna kaiwa wannan lokacin da
budurcin su?
A DAREN FARKO
15
yamike yayi wanka yafito falo cike da nishadi yaci
abincinsa bai koma dakin ba yafita abin da
yasawa ransa shi ne ashe yanada abar hutawa a
gda tun farko yaki ba ta kai .
Anisa tayi kuka tayi kuka har taba uku lada,
zazabi da ciwon kai suka rufeta takasa tashi,
takira number ramat tace "ke ni fa ba zanzo gdan
wannan abin jin kan tsiyar ba ke dai da kike
mayen sonsa kikaga za ki iya zaman gidansa sai
kiyi tayi, ni dai ina ba ki shawarar kidauke ranki
akan khalifa ba za ki iya mallakarsa ba ke ko kin
mallake shi wahala za kisha dan namiji ne me
garari da tsada.
Anisa ta jefar da wayar taci gaba da kuka sam
dawani ido zata dubi mominta ko da ta san cewa
ba za tasan abinda yafaru ba abin takaici ne ace
ta karya alkawarin datayi wa momin ta ta na
cewa za ta rike mutuncin kanta, shin ina
makomarta a gun khalifa, shin meye amfanin
zuwanta germany ne?
****
Bayan tafiyar jiddah london karatu abunda su
hajiya sude suka maida kai shi ne yawon gdajen
malamai da bokaye wai su burinsu khalifa yaso
ummi ko ta halin kaka, mafi yawan malamai na
bayyana musu cewa khalifa fitinannen yaro ne
mai jarabar kwadayin mace amma bbu batun aure
ko kadan a zuciyarsa, haka shi mutum ne da ba
ya son raini da ace yanada sausaucin ra'ayi zai
iya kula ummi da sunan soyayya tunda da
sha'awa mai zafi amma a bisa la'akari da yadda
yanayinsa yake bazai iya baiwa ummi fuskar
soyyaya ba dan gudun kada tarai na shi tunda
yana ganin ta ne a karamar kanwarsa, malamin
daya fara shaida musu wannan batu ya tabbatar
musu da cewa wannan shi ne hakikanin ra'ayin
dr. khalifa wanda yake tafiya akai, hajiya hauwa
tace,"to malam ba za a iya tankwasa zuciyarsa
yasota ba ko ya ki ko ya so, malam mahaifin
yaron nan dan uwanmu ne matarsa ta asirce shi
bai jin maganar kowa sai tata duk wannan uwar
dukiyar daya tara idan bbu shi ita da khalifa za
su mallaketa.
Malam yayi murmushi yace "akwai hanyar hakan
amma ba zai yiwu ba har sai ya dawo kasar nan
dazama sbda za muyi amfani da kasar daya taka
ne muyi masa aikin da mukewa lakani da bita zai
zai, zaita bin ummi sai yadda tayi dashi, anan ne
suka dan yi murmushi hnkalinsu yafara kwanciya.
"Yace suyi hakuri nasara sai a hankali da hakuri
ake samunta ba da gaggawa ba,.
****
Fatima da jiddah daga can london din ke damun
ummi akan tadinga neman khalifa a waya da
sunan za ta gaida shi bai dace tabar damuwa a
cikin ranta haka ba, suna ba ta wannan shawarar
ne saboda ganin yadda hnkalinta ke tashi
musanman fatima da ke kusa da ita tana ganin
yadda ummi ke kuka akan rashin khalifa tun tana
boye wa har kukanta ya bayyana ita kanta mama
ta fara gane damuwar da ummi take ciki, dukda
cewa ba a san abinda ke damunta ba idan ta
tambayeta sai tace bakomi, mama ba ta son
takurawa ummi sbda tanajin dadin zama da ita.
Rannan dai da fatima ta matsa mata akan sai ta
kira khalifa a waya tayi murmushi tace "fati idan
yabamu amsar da za ta daga mana hankali fa?
da muguwar rawa ai gwamma kin tashi, fatima
tagirgiza kai tace "wannan hujjar ta ki ba za tasa
mi ta zama ckin damuwa ba, idan kin ce da
muguwar rawa gwamma kin tashi ai kuma kar ki
manta ance a rashin kira karen bebe ya bata
kuma a rashin tayi akan bar arha, ummi tajawo
wayarta ba tare da ta ce komi ba ganemo
nomban khalifa takira ckin sa'a tashiga.
Bata jima ba tana ringing yadaga cikin
kasaitacciyar muryarsa yai sallama gaban ummi
na faduwa tasa hands free dan fatima taji da
kunnanta.
Ta gayar dashi ya amsa tace "ka gane me
magana yayana?
Yace "na gane mana ba ummi bace.
Tace "ni ce kira nayi dan mu gaisa na ga tun
tfyarka kana tmbayar kowa a gdan nan amma
ban da ni, bansan laifin da nai maka ba, .
Yayi dan jim kamar ba zai amsa ba, daga bisani
yace "ina cewa kowa lafiya? idan nace kowa
lafiya kina ciki.
Ta ce "shi knan nagode yaya karatu.?
Ya amsa "karatu Alhamdulillahi.
Za takara magana taji dif ya kashe wayar tayi
murmushin takaici tace "kin ji ko?
Wadannan abubuwan ne suka sa ba na son
bugawa khalifa waya, ba wai dan ba na jmson jin
muryarsa ba kullum farin cikina ko da a waya ne
in dinga hira da khalifa ina jin muryarsa amma ba
zan samu wannan hadin kan daga gareshi ba,
sbda ba ya bukatar soyayya dani.
Hawayen dasuka zubo mata yahana. ta cigaba da
magana, hankalin fatima ya kartashi taji tsanar
khalifa ya kara kamata, wai wani irin mara imani
ne wannan tasa dankwalin ta tana sharewa ummi
hawaye, tace "ki yi hakuri insha Allahu khalifa zai
zamo mallakinki.
Ta ina?
Akwai wanda zai yiwa khalifa auren dole? idan
har kuwa ba auren dole za a yi masa ba to ba
zan same shi ba don baya sona, rokon dazan miki
daya neduk yadda mama za tayi miki akan ki
gaya mata abinda yake damuna kada kisake
tasan cewa khalifa nake so.
Fatima tayi mata wani irin kallo tace "matsalarki
knan ummi banga ta inda za a samu mafita ba
ana wannan boye boyen.
A DAREN FARKO
16
.Sai da dare yayi sosai khalifa khalifa yadawo
gdan tare da shu baby yau ta yi masa nacin da
dole ya amincewa kwananta. agdansa, ahi kansa
bai san dalilin dayake gudun kawo mace gdansa
ba sbda anisa, tun daga nau'in kayan jkin shu
baby za kasan lalacewar ya yi yawa, a ranta tace
"tabbas yau sai na ga abunda khalifa yake tsoro,
tabi bayansa zuwa ciki, anisa na kwance a bisa
kujera a fali tana kallon wani film a wayarta, duk
zamanta a gdan bata taba ganin khalifa ya zo da
mace ba duk da ta san yana tare dasu sai fa yau,
suka dubi kowa ita da shu baby kowacce tashaki
wani masifaffan kishi a zuciyarta, anisa ta maida
kanta tana kallonsu suka wuce dakinsa, bby tace
"sbda wannan figigiyar yarinyar dama kake kin
kawo ni gdanka?
Yamata wani irin kallo yace "kiyi abinda ke
gabanki shuu wannan kanwata ce ba na son....
Bai cigaba da maganar ba yashige toilet yayi
wanka yayi alwala, bayan ya idar da sallar dake
kansa yaleka falon yace "anisa wannan da kika
gani abokiyar karatuna ce ki kawo mana abinci
daki kuma ina so ki gaisheta.
Yawan kukanta yana ba shi haushi ganin ta fara
share kwalla yasa ya koma cikin daki, tunanin da
anisan tayi shi ne wai ita wacece ne a gun dr.
khalifa da har zai gujewa bacin ranta, tunda
takawo kanta zama a gdansa dole tahakura da
duk abinda za taji ko tagani, a sanyaye tamike
tashirya abinci a tray tashiga dakin da sallama
tatsuguna ta gaisar da baby tafita, kallon daya
bita dashi yakara baiwa baby haushi taja tsaki
tabude abincin taxuba a plate tafara ci, dandanon
abincin ya burgeta ga takaici da kishin wadda
tadafa, shima yazuba na sa yana ci yana fadin
"kai aniaa ta iya girki mijin ta ya mori mace.
Sun kwana suna morar junansu ta hanyoyi daban
daban wadanda suka kware a kansu ko
wannenau ba baya bane a wannan harkar, sun
gamsu iya gamsuwa hakan yasa kowanne
zuciyarsa wasai ba damuwa, khalifa na son yayi
bacci sosai amma yunwa ta hana shi baccin dole
yafito falo sai dai tebur wayam yaleka kicin ba
abinci bbu anisa yadawo dakinta ya iske doguwar
takarda mike bisa gado tun kafin yakaranta ya
san abinda ta kunsa yace"shikenan shukura ta ja
min asarar mai dafa min abinci da kula da gdana.
Salam.
Abbakar ina maka ban kwana tare da fatan allah
yasa kagama karatunka lafiya ka koma gda lfya,
xamana a gdanka ya kare ba tare da na gaji da
ganinka ba sai dai yin haka shi yafi mana ni da
kai, na gode kwarai dagaske da masuakin daka
ba ni a gdanka duk da cewa hakkana bai cimma
ruwa ba na samun masauki a zuciyarka wanda
shi ne makasudin zuwa na wannan kasar, amma
dai na godewa Allah daya ba ni ikon aikata
abinda natabbatar zai wahala ka manta dani har
ka koma ga mahallincinka, ina rokaonka a duk
sanda katuna dani kai min addu'ar alheri. khalifa
na zo wannan kasa ne dan neman soyayyarka da
take ta cin zuciyata tun daga ranar da idanuna
suka fara ganinka na yi suk kokarin da zan iya na
ganin na ja raayinka banyi nasara ba, tun daga
gda nigeria har izuwa yanzu dana tabbatar ba
zan same ka ba, daga karshe ina maka fatan
dukkan alherin duniya dana lahira.
Ni na san bbu namijin dazanso bayan kai,
Anisa....
Iya abinda takardar takunsa knan, har gumi yaji
yana keto masa sbda tsabar tausayin anisa,
yadinga jin wani iri a ransa yana tunanin rayuwar
dasukeyi wadda ba ta da wani amfani a garesu,
idan suna gaban iyayansu sai su dinga nunawa
su na kirki ne amma a bayan idon iyayan na su
suna aikata abinda suka ga dama.
Shin tsakanin iyaye da Allah wa ya fi dacewa aji
tsoro, in har suna boyewa iyayansu halin dasuke
cki ne don suna tsoronsu, Allah daya halicci
mutum shi yafi dacewa a ji tsoro, kuma Allah
yana kallon mutum a ko wani hali yake.
Wannan nasiha da khalifa yaiwa kansa yasa yaji
nan take komi ya fice mai daga rai ya tsani yan
matan dayake tare dasu na holewa, yana bukatar
yazamo natsatsen mutum wanda yake biyayya ga
Allah da manzonsa, takaicin abubuwa da dama
suka kamashi har yaji kyamar kansa da kansa
yakeji, yamike jikinsa ba kwari yafito daga dakin
yadawo dakinsa, ya isje shu bby har yanzu
baccinta take cike da nishadi da kwanciyar
hankali, yasa hannu yagirgizata dakarfi tabude
ido tana fadin "bacci ke damuna,yace " ba na iya
juriyar yunwa.
Tace "ina yar aikin gdan nan?
Yace "ba ta nan.
Ba abinda shukra tatsana irin girki amma da yake
khalifa ne haka tadaure tadafa ruwan tea da
dankali da plantain, ba wani kwarewa tayi da
girkin ba yunwa ce tasa kawai yaci.
*****
A DAREN FARKO
17
Tun daga wannan lokaci rayuwar khalifa ta sauya
gaba daya yadaina sauraror kowacce mace har
da ita kanta shuu babyn, hatta fAisal ya watsar
dashi sbda ya yi ya yi yaja hankalinsa don shima
yadawo hanya tagari faisal ya yi masa wani irin
kallo shekeke yace "kai kiwa meya sameka da za
kace mudaina rayuwarmu, tajin dadi mu takura
kanmu, ko mafarki kayi ka mutu an sa ka a
wuta?
Khalifa yace "ko kusa banyi wani mafarki ba na
dai yi wa kaina fada ne dan na fuskanci gaskiya,
na ga yakamata inja hankalinka kaima damu
daina wannan rayuwar kafin ranar nadama tazo
mana.
ko wata amsar kirkifaisal bai ka ra bashi ba
yamike yavarshi a gurin,hakan yasa khalifa ya
janye jikinsa yakoma rayuwarsa shi kadai, yanemi
masu dafa masa abinci da gyaran gida bai zuwa
ko ina sai makaranta inya dawo yakan kulle
kansa a dakinsa yayi ta nazarin abinda yake
karantawa ko karatun alkur'ani mai girma wanda
a baya ko bude shi ba ya yi sbda shagalta da
rayuwa da ya ya mata dayayi, sai yake jin dadin
rayuwarsa a haka hatta hotunan sa da
nambobinsa ya goge, yayi ta karfafar zuciyarsa
tare da neman gafarar Allah yana rokon Allah
yataimake shi yaraba shi da wannan rayuwa.
A haka a haka har Allah yataimake shi
yakammala karatunsa yakawo shi inda ya fito da
kyakyawan sakamako zuwa babban likitan mata a
lkacin ya dada kasaita irin mazan nan ne da dole
idan aka kallesu a kara sbda cikar zatinsu,
kwarjini da ilimi, 'yammata sun yi sunyi suja
ra'ayinsa kowacce tana fatan yasota amma ya ki
bada kai, matar aurance har yanzu baiga wadda
yagamsu yaji ta yi masa zai zauna da ita a
matsayin matar aure ba, amma dai mace ta
holewa ya yi alkawarin insha Allahu ya daina.
Kafin ranar dawowarsa gida nigeria ya yi ta
neman yadda za ayi yaga anisa ya rasata haka a
kano bai san a ina zai ganta ba, yana yawan jin
tausayin ta tare da yimata addu'a duk sanda
yatuna ta.
Tunda ya daura damarar tahowa gida damuwarsa
itace yarinyar nan ummi ya san ta yi girma yanzu
sosai ta kara wayo a baya ma ta iya budar baki
tace tana son shi ballantana yanzu, bayan shi ba
wani sakar mata fuska yakeyi ba ballantana ace
shi kwata kwata ba ya da ra'ayin auran zumunci
kuma ko yana dashi ma ummi bata cikin
lissafinsa, cikin hikima yatambayi mamansa a
waya ko an yiwa ummi aure, tace ai bata fidda da
mijin ba ma ba ta sauraron kowa tun da tayi
candy abban k7ma ya ce ya dace ta fidda mijin
aure tunda mutane dayawa suna nunawa suna
sonta in ya so taci gabada karatun a gdanta sai
tace wai wanda takeso din ya yi doguwar tafiya
idan yadawo za ta gabatar dashi.
Wannan yafadarwa dr. khalifa gaba ya tabbatar
yarinyar nan in baiyi da gaske ba zata zame
masa matsala, har ranar dawowar tasa tunanin
da yake fama dashi a xuciyarsa knan, yarinyar
tashiga ran mamansa za a iya cewa sai ya
aureta ko da yake bai da matsala da abbansa,
maganar mamansa kuma da karfi a kansa baya
son bata mata rai.
*****
Karfe sha biyun rana fatima tagama shiryawa
cikin wata blue din batik mai haske riga da zani
ne amma kai kace siket ne sbda yadda kayan
suka zauna a jikinta suka yi mata kyau abin har
ba a magana, ita da kanta ta yi sha'awar kanta
sbda kayan sun mata kyau, telan dayayi dinkin ya
gwanance a fagen tsarawa mata dinki, ta jima
tana gyara gashinta ya dau kyalli ta tsara daurin
dankwalin sosai yadda yadace da adonta tazuba
fashion da mayafin da suka dace da kayan, ummi
ce ta bukaci taraka ta gdansu yau wato gdan
iyayanta, fati bata fiye son xuwa gdansu ummi ba
sbda jininsu bai haduwa da hajiyarsu ummin ba
tare da ta san abinda tayiwa hajiyar ba, tana cin
darajar diyarta ummi ne kawai sbda a halin yanzu
ummi tanad\ matsayi lamba daya a zuciyar
fatima ba ta da na biyu kowacce irin alfarma
fatima za ta iya yi akan ummi.
Innar tana zaune a kofar dakinta tace "inna sai
mun dawo.
Tace "adawo lafiya a gaida su.
Tayi sallama a kofar dakin malam musbahu
yadago yadubeta sai yayi saurin bude idonsa
gaba daya yace "kai fatima wacce irin kwalliya ce
wannan? kin ga yadda kikayi kyau kuwa?
Ta lumshe kyawawan idanuwanta tana murmushi
tace "ka manta na gaya maka za muje gdansu
ummi.
Yace "fatima gskiya in banda ummi na da
matsayi mai girma a gareni ba zan iya barinki fita
cikin wannan kwalliyar ba ban taba ganin ranar
dakikayi kyau a ido irin wannan rana ba, fatima
ina fatan Allah ya mallaka min ke.
Tace "malam ai ya mallaka ma saura kadan
yarage komi lokaci ne.
Ganin zai tsaida ita da maganganu na santin
kyaun datayi yasa tawayance tafice tabarshi yana
hadiyar yawu kamar yabi ta yayi ta kallonta yau
kyaun datayi masa daban ne.
Bayan sun gaisa da mama tawuce dakin ummi ta
iske ta tana shiryawa tace "mutuniyar kin hadu
kayan nan sun yi miki kyau bana wasa ba.
Fatima tace "kai wai ke ba kya gajiya da yaba
kyau na ne? kullum sai kin cena yi kyau.
Tayi dariya tace "to ai yabon gwani ya zama dole
kinyi kyaun ne ba na gajiya da kallonki fatima,
don Allah idan kinyi aure kada kidaina kwalliya
kina matukar yin kyau da kwalliya dukda cewa
idan ma bakiyi kwalliyar ba kyau kike yi ke kam
Allah ya yi miki baiwa da yawa fatima.
Tace "don Allah kiyi sauri mutafi kadda yamma
tayi ba kya gajiya da surutu.
A cikin mota suna tafiya ummi tana tuki fatima
tana gefenta suna hira, tace "duk inda muka wuce
fa sai an kalleki fatima ina kallon wani dazun da
danja ta tsayar damu sajra kadan yabuga wa
wani sbda kallonki, kidinga sa nikab kidaina
daukar hankalin mutane.
Ta dubeta tace "su sukaga za su iya ni bance
wani yakalleni ba duk wanda wani abu yasame
shi a dalilin kallona to shi yadauki alhakin kansa,
muyi wata hirar.
Tace "yawwa ai kuwa yau zan miki gagurumin
albishir.
Fatima tace "Allah sarki ai kuwa ni bani da wani
labari da nake son ji mai faranta rai daya wuce in
ga khalifa ya dawo ya amince da batun auranki
da shi, wlh a wannan rana bansan farin ckin
dazanyi ba, bansan yadda zan fassara wannan
rana ba, gskiya anty ummi ina kaunar khalifa ne
sbda son da kike mishi., duk da cewa na tsane shi
tawani fannin sbda ba ya da tausayi.
Ummi tayi dariya tace"ummi misali idan ke ce
wani namijin yazo yana miki irin son danake wa
khalifa za ki tausaya mai kiyarda da auran ko da
ba kya sonsa ?
Fatima tace "ummi ni mutum ce da ba na son
ganin musulmi dan uwana a cikin damuwa in dai
har na san yana zubda hawaye akan ciwon so na
irin yadda kike zubda hawaye akan son khalifa
zan tausaya mishi.
Ummi ta girgiza kai "to albishirinki soyayya ba
haka take ba.
Tayi saurin katseta da fadin "ko ma yaya take
ummi, khalifa ba shi da kirki, ba shi da tausayi,
ya kamata mutum yaso mai sonsa, ya kamata
mutum yakasance mai tausayi, nikam ba zan taba
yiwa khalifa uzuri ba, duk da haka don Allah ina
rokon idan khalifa yadawo kasar nan...... "
Ummi tayi fakin a kofar gdansu tace "ki kwantar
da hankalinki idan Allah ya kaimu gobe khalifa zai
dawo kasar nan.
Tadafe kirji tare da fiddo ido tace "don Allah
dagaske kike ?
Tace "kada kiyi shakkar hakan kizuba ido gobe za
kiga dr. khalifa.
Ita kantaa ummi bataji dadin samun hajiya saude
a gdan ba sbda a fili suke nuna ba sa son fatima,
yayin da ita kuwa ta tsani mutum ya nuna mata
ba ya son fatima, tana matukar kaunar fatima a
ranta.
Fatima tatsuguna har kasa tagayar dasu su ka
amsa kowacce fuska ba fara'a suka ja baki suka
tsuke, wayar fatima tafara ringing tamike tayi
sauri tafita ganin sunan malam musbahu, nan da
nan hajiya saude tazubawa ummi harara tace
"wai me kike nufi da yawo da wannan kodaddiyar
yarinyar, duk inda za ki sai da ita za ki, sai da ita
za kizo gdan nan ma kin dauko ta kina nufin duk
abinda xa mu tattauna akai sai dai muyi a
gabanta knan ba mu da wani sirri sai ta ji ?
Hajiya hauwa tayi tsaki tace "ba ma wannan ne
abin haushin ba saude sai yadda ummi take bata
rai idan munce muna son magana da ita wai lallai
sai duk abinda za a fada a fada a gaban fatima.
Bayan ita fatimar idan sun tashi na su sirrin da ta
ta uwar tafiya take gdansu suyi maganarsu ba a
gaban ummin ba.
Hajiya saude tace "ai ummi ba ta da wayo na
rasa wacce irin soyayya takewa fatima kamar
wadda ta asirceta, ga ta dai a haka kamar wata
mai wayo nan kuwa ba komi a ranta sai wauta,
mu da mukeso mu mallaki khalifa ta jawo
wannan mai kama da aljanu ta jawota gdan
kullum a gdan take yini idan yadawo ba kya jin
ba zai ce fatima yake so ba ?
Ummi tace "hajiya ya ya za ayi khalifa yace yana
son fatima bayan an kusa bikinta, kwanaki kadan
suka rage akaita gdan mijinta.
Hajiya tace "wohoho ummi sai yaushe za ki
fahimci halayyar mutane ne kidinga taka tsan
tsan dasu, ki guji sharrin wanda kika taimaka wa,
lokacin daka tausaya wa mutum kadakko shi
daga rana kayi masa gata kadawo dashi inuwa
bbu wanda zai tura cikin rana sai kai.
Kin ga dai ke ce kika wayar da fatima da iya
kwalliya da komi hatta magana ke kika koya mata
amma babu wanda fatima za ta fara yiwa illah
sai ke, tabbas idan bakiyi taka tsan tsan ba sai
kin ce na gaya miki.
A DAREN FARKO
18
Ummi takwana tana jujjuya maganganun su
mahaifiyarta tana musanta duk abunda suka fada,
ita kam ta yarda da fatima dari bisa dari bazata
cutar da ita ba ta tattara duk maganganun na su
ta watsar, ta fuskanci ranar dazata fuskanto ta
wato ranar dawowar mutumin da ba tasan abinda
sakamakon dawowar ta sa za tahaifar mata ba,
farin ciki ko bakin ciki dole a daya biyu ne don
haka a wannan daren bacci ta ragagge ne duk
sanda tafarka sai ta ji gabanta ya fadi.
Da sassafe takira fatima a waya tace don Allah
tazo, tace lafiya, tace "banjin dadin jikina ne da
zuciyata inason ki zo miyi hira.
Fatima tace "don Allah ki kwantar da hankalinki
khalifa fa ba wani bane illa mutum kamar kowa,
meye na(aga hankalin ki akansa ?
Tare da fatin suka shiga kitchen lokacin dataxo
gdan wuraren karfe tara na safiya, ko da yaushe
mama na yabawa yadda suke tsara girki da tebur
a halin yanzu fatima dai da iyayanta sun zamo
yan gda sosai a gdansu mama, suna yawan yi
musu alheri na kayan abinci da sutura, wani
lokacin mama dakanta take zuwa gun innar su
fatima suyi hira sosai tanajin dadin shawarwarin
datake ba ta akan rayuwa, sun shaku dayawa
haka malam da abban khalifa sun zamo aminan
juna ,idan kashiga gdan za kace fatima 'yar gdan
ce sbda sakewar da takeyi, ci mai kyau da sha
mai kyau ga kayan ado hakan yasa fatima tayi
kyau ba na wasa ba kamar a taba jikinta jini
yafito ta zamo kamar irin taurarin matan nan da
suke zamowa ababan kallo a duk inda suka shiga,
mafi yawan mazan dasuke shige da fice a gdansu
mama idan sunga fatima sukan nace suna sonta,
ba ta sauraron kowa duk kudin mutum da
kasaitarsa, fatima ba ta bari yashiga ranta sbda
alkawarin datayiwa babanta na auran malam
musbahu yana tsaye a zuciyarta, bata taba wasa
da maganar iyayanta ba koyaushe farin ciki ? su
shi ne ranta.
Gargadin karshe dasu hajia hauwa suka yiwa
ummi shi ne "ta sallami fatima daga gdansu
mama kafin khalifa yadawo kasar nan in ba haka
ba tai kuka dakanta, ta jiye ma kanta abinda
zaisa ta tayi kuka ba iyaka, bbu maganar data
kama ummi aciki face ma dariya dasuka bata,
magana daya tayi musu inda tace "su kwantar da
hankalinsu da ace fatima za tayi soyayya da wani
da tuni ta yi kafin ma khalifa yadawo sbda
mazaje dayawa masu matsayi da takama da
dukkan abinda da namiji yake takama dashi sunce
suna sonta bata taba sauraron wani ba, ta rike
maganar iyayanta dagaske ,tunda dai fatima bata
yi soyayya da wani da namiji ba ba za tayi da
khalifa ba.
Hajiya saude tace "haka kike gani, ke mesa kikace
ba kya son kowa sai khalifa ?
Tace "wannan kuma daban soyayya gamon jini ce
bai zamo dole don ina son wani yakasance wance
itama shi tame so, masu iya magana ma kance
abincin wani gubar wani.
Gaba daya ummi ta san basu gamsu da hujjojinta
ba, hankalinsu a tashe yake a bayan azahar in
yau sai da hajiya takirata tana tmbayarta "in ce
ko fatima ba ta gdan nan, na ji ance khalifa ya
iso gda nigeria yana Lagos yana shirin isowa
kano.
Ummi tace "hajiya itace take tayani hada mai
abinci, kin san yana son abinci mai dadi.
Taja tsaki takashe wayar har tarasa yada za tayi
da ummi.
Karfe hudu na yamma dun abubuwan ci da na
sha da sukaiwa khalifa sun hada a tebur, gida ya
dau kamshi an gayare mai dakinsa fes yanata
kamshi, bayan fati Ta idar da sallar la'asar tazura
dogon hijjabin ta da nufin tafiya gda.
Ummi ta fito daga wanka tace "zan tafi idan
bakon ya isa ki ce muna masa sannu da zuwa.
Ummi tace "ai kuwa baki isa ba dole ki tsaya
kiga khalifa ya dace kigan shi.
Tace "To ai na sanshi a hoto duk wanda ke
shigowa gdan nan ko bai taba ganinsa a fili ba ya
san shi a hoto ko ina a gdan nan fa hotonsa ne.
Tace "ai na san da hakan nace kitsaya kigan shi
duk yadda yake a hoto ya fi nan.
Fatima tayi dariya tace "na san zaifi haka ummi
idan za ki lura ai ban taba cewa kinyi laifi don kin
wa dr. khalifa son da kike masa ba, ya cancanci a
so shi dan ya hadu kowa yana son abu mai kyau,
ba laifi bane don mace ta so mijinta yakasance
mai kyau irin dr. khalifa sai dai bbu ,gskiya yi
hakuri ba zan boye miki ba ba na farin ciki da
gani ? khalifa, ina tayaki murnar dawowarsa ne
kawai don shi ne farin ckin rayuwar ki ina son
abinda zai faranta ranki ummi fiye da farin cikina,
da ace dr. khalifa ya amince ya karbi soyayyarki
da zan kasance cikin dumbin farin ciki mai yawan
gaske amma duk da haka....
Ta katseta "fatima in dai dagaske kina son farin
cikina tsaya dr. khalifa yazo don Allah.
Fati bata sake magana ba tafidda hijjabinta
tahaye gado takwanta, doguwar rigar shadda ce a
jikinta ruwan powder, daga sama ta matseta
yayin da tayi fadi daga kasa, babu kwalliya
fuskarta gashin kanta ne dai ya sha gyara
yakwanta a kafadarta ,a cikinsu babu wanda
tasan khalifa ya shigo gdan.
Ummi tace "don Allah fatima dako min ragowar
furar dana rage a fridge.
Fatima tafito a yadda take ko dankwali babu
tashiga kitchen din falo tadakko furar kwatsam
suka hada ido da dr. khalifa daya fito daga dakin
mamansa, abbansa na biye dashi da manyan
abokansa biyu dr. hafizu da dr. bashir, gaba daya
taji kunya ya kamata cikin karfin halin gaske
tarusuna tace "barka da isowa.
Kallon da yayi mata yasa jikinta ya hau rawa ta
wuce dasauri cikin dakin ummi tace "ke ai
mutumin na ki sun shigo.
Ummi tadafe kirji tace "don Allah ? furar da bata
sha ba knan tazuba wata doguwar riga amma ita
ta atamfa ce tayafa dankwalin a kanta ta fesa
turare ta fito falon, tuni har sun haye tebur sun
fara cin abinci.
Fatima tabude dakin taleko don taga kallon da dr.
khalifa zai yiwa ummi, ai kuwa fuskarsa baa
fara'a yake amsa mata gaisuwa, su dr. hafiz ne
masu zolayarta, shi kam gogar na ka ya yi dif
abinci kawai yake durawa cikinsa.
Wani irin takaici yakama fatima kamar taje
tashake dr. khalifa tahuta an masa abinci ko
yabawa ba zai yi ba yana walakanta wadda tayin.
Wai wane irin mutum ne haka, nan da nan tayi
takara tsanar sa, taja tsaki takoma kan kujera
taharde .
Ummi tashigo dakin harara tafara samu a idon
fati tace "mi yiwa Allah ki daina son dr. khalifa ba
shi da kirki.
Ummi jikinta a sanyaye tazauna tayi tagumi tace
"kiyi hakuri haka halayyarsa yake har in mutu ba
zan daina sonsa ba, shi kadai nafara so a rayuwa
rata, ba na iya hadashi da kowa ko bai aureni ba
ba zan hakura dashi ba kitayani addu'a kawai.
Fatima tafigi hijjabinta tace "to gaskiya ni ba zan
iya ci gaba da zama a gdan nan ina ganin wanna
abin haushin ba.
Bata ji kiran da ummi ke mata ba tafice, sai dai
abi ? takaicin dole tawuce ta falo gashi ba ta son
kara ganin dr. khalifa yayin da shikuma dr. din
kamar an ce yadago idonsa sai yadago karaf
akan fatima za tafita, shi kansa bai fahimci
muryarsa ba lokacin daya ke ce wa, "ke zo nan"
Tayi dan jim, ba wata a falon lallai ta san da ita
yakeyi, ya dace ta walakanta abin da ummi ke so,
ranta a bace ta nufo inda suke ta tsuguna a gefe
kanta na kasa tace "Ga ni .
To bai san dalilin dayasa yakirata ba, ballantana
yasan abinda zai gaya mata, ya samu kan shi da
zuba mata ido shi dai bai san ta a gdan ba, Dr.
hafiz ne yace "yammat don Allah ya sunanki ?
Fatima kawai tace.
Kafin wani cikin su yakara magana tamike
dasauri tabar gdan.
Dr. khalifa ya ajiye spoon din hannunsa yayi
ajiyar zuciya yace "fatima.
Kai wannan yarinya Allah ya hore mata kyau.
Dr. bashir ya kyalkyale da dariya yace "likita knan
bokan turai nan kuma kagano ance inda baki
yakarkata nan yawu ke zuba.
Fitowar mama takatse maganar tazauna suna
hira, dr. khalifa yace "mama ina kuka samo
fatima ?
Tace "yarinyar nan makwabtan mu ne wanda
kuka gaisa da babanta a waje dazun wanen
malam musa.
Ya basar da maganar kamar bai damu ba sukaci
gaba da wata hirar.
*****
Tun a daren masu zuwa yiwa dr. khalifa sannu
dazuwa suka fara cika gdan yawanci tsoffin
abokansa ne musamman na B. U. K da 'yan'uwa
da abokan ckin dangi, wayoyin sa ma kashe wa
yayi don yahuta, bai samu kansa ba sai sha biyun
dare yahada ruwa mai zafi yai wanka yafesa
turare yahaye gado, tunanin bai samu masauki a
zuciyarsa ba yahau bacci sallar asuba ma sai da
abbansa yatayar dashi suka nufi masallacin tare,
ita kanta sallar idanunsa a rurrufe yayi ta suna
dawowa yakoma wani sabon barcin.
Yayin da ummi takwana ckin fargaba da kai komo
a zuciyarta da tunanin tayaya za ayi dr. khalifa
ya aureta ? zancen haduwa yanzu ba a magana,
a tsaya bayyana tsarin kyau da Allah ya hore wa
dr. khalifa bata baki ne, zuciyarta takara rudewa,
sabuwar soyayyar data ninka ta bata ta karu
akan ta da, ummi ta ji kanta tamkar tsawa tsawa
yake mata.
Da sassafe kamar yadda tasaba tashiga kitchen
tafara hada abincin dr. khalifa na musamman,
mama ta fita tace mata takira fatima a waya tazo
tataya ta domin akwai wasu abokan dr. khalifa
daza suyi breakfast tare nan da karfe takwas.
An yi sa'a fati ba ta kashe waya, lokacin da
ummi tabayyana mata bukatarta amsawa kawai
tayi ba dan ranta ya so ba, hakanan take jin wani
irin abu a zuciyarta jininta bai hadu da dr. khalifa
ba, kallon da yayi mata ya firgita ta kwarai
dagaske, ba ta da matsala da inna da babanta
akan zuwa gdan mama, hijjabinta dogo har kasa
tasaka tafito zuciyarta cike da sake saken abinda
zai je ya xo.
Aikin suke kowacce da abinda zuciyarta ke
sakawa, karfe takwas komi yakammala a tebur
suka debi na su sukayi dakin ummi.
Kinga dr. khalifa ko fati ?
Ummi tayi tmbayar tana kallon idon fatima wadda
tagyada kai fuskarta a tsuke tace "eh na ganshi
meye. "
Ummi tasa gefen mayafinta tana sharar kwalla
takasa cigaba da magana, zuciyar fati ta kuntata
sosai yadda abincin yaki ciyuwa a gun ummi
itama kasa ci tayi, tace "ummi ko zuwa zanyi in
rokeshi yasoki.
Tace "karki yi haka ya gargade ni akan kada in
fadama cewa ina son shi, dole in kiyaye dokarsa
in dai inason in zauna lfya.
Fatima tace "to yanzu haka zamuyi ta zaman
damuwa ?
Ummi tace "damuwa ta kam ba zata gushe ba
amma na ci alwashin ba zan bar dr. khalifa ba ba
zan yarda in rasa shi wata tasame shi ba.
Tunda ummi take irin wadannan kalaman jinta
kawai fati take ta san me za ta iya ? hakuri ne
yazame mata dole in batayi ba tayi tashan
wahala idan so cuta ne hakuri kuma magani ne.
*****
A wannan rana malam musa mahaifin su fatima
yafidda bayanin cewa sati biyu rak za ayi bikin
fatin da musbahu akai tagdansa, har inna tace
"malam bai yi wuri ba har yaushe aka gama shiri.
Yace "shi kam wannan lokaci yasanya kuma ba
zai daga ba, fatima na dawowa gda malam
musbahu yatare ta da zancen yana cikin farin ciki
mai yawa, itama ta nuna gamsuwarta tare da
fatan alheri garesu baki daya, yatambayeta
abinda za tayi da kawayenta na shagalin biki tace
ta fi sha'awar walima a ranar jumma'a da
yamma amma dai za tayi shawara da antinta
ummi.
Data shiga ckin gda takira ta a waya tashaida
mata, ummi tarangada guda tace "amarsu ta
ango knan wannan sai mun zauna an tsara yadda
za ayi, zanso ganinki ranar wannan biki za kiyi
kyau na jan magana.
Fati tace "fatana aure dai Allah yasanya mai
alheri da albarka ba na na so inga anyi aure anyi
shagali aure na soyayya amma auren bai je ko
ina ba sai kiga ya lalace ko ayi ta samin matsala
a rasa laifin waye mazan ko matan ?
Ummi tace "kowa na da laifi fati a tsakanin
mazan da matan ko wanne akwai rawar dayake
takawa gun haifar da matsaloli ckin auran da
rabuwarsa, amma dake insha Allahu za kuzauna
lafiya da malam musbahu domin aure ne da aka
gina shi a bisa kyakyawar turba, kuma za ayi shi
ne don Allah,.
Bayan ummi ta kashe waya tafito falo, ganin dr.
khalifa ya hakimce bisa kujera wata lafiyayyar
shadda a jikinsa maroon colour dinkin da
matasan zamani ke yi yayi, ya yi kyau har ya
wuce misali, farin gilashin idone a fuskarsa bai
damu da zaman ummi a gun ba yaci gaba da
fadin "mama kinsan maganar aure tana bukatar
nazari da bincike, wlh a rayuwata bbu auran dana
tsana irin je ka kadawo, ayi aure ana farin ciki da
zarar an je an zauna a kasa fahimtar jin dadin
dake ckin zaman auren, kullum kana ckin
damuwa matarka na ckim damuwa meye amfanin
hakan, amma idan aka natsu za asamu kwalliya
tabiya kudin sabulu sbda na sani bbu wanda ya
isa yakaucewa abinda Allah ya hukunta masa.
Yayi shiru anan yana nazarin fuskar mama don
ya fahimci yadda tadauki maganar, batace komi
ba tajuyo tadubi ummi tace "'yammata yaya
akayi ne yau fatin batazo tayin hira ba ?
A sanyaye tace "batazo ba waya tamin yanzu
tace malam ya ce idan Allah ya kaimu nan da
sati biyu za ayi bikinta.
Mama tatsuke fuska tace "wani irin sati biyu
kuma ?
Tace "haka dai tace.
Tace "to je ki kiramin fatin har yaushe akayi mata
shiryen shiryen amaren.
Dasauri ummi tabar gun tafada daki don tasamu
damar yin kukan data ke ta hadiyewa.
A falo kuwa dr. khalifa ne yaji wani irin abu ya
tsirga masa a cikinsa zuciyarsa takama bugawa.
Fatima Za ayiwa aure nan da sati biyu ko kuwa
wata fatin ce daban, nan da nan yanayinsa
yasauya gaba daya yawaiwayo tare da zare space
din sa yadubi mama yace "mama wace fatin za
ayiwa aure ne ?
Tayi murmushi "fatima yarinyar nan dai ta
makotanmu daka gani jiya.
Yace "doyar malam musa ?
Tace "yawwa ita kuwa.
Abinda yafito daga bakinsa shi kansa ya ba shi
mamaki don bai san sanda yace "Lallai da sake".
******
A DAREN FARKO
19
Mama tayi masa wani irin kallo tace "me kake
nufi ?
Anan ne yadan shiga natsuwarsa yace "mama
wannan yarinyar nakeso na aura don gskiyar
magana ita neke ganin ta dace da rayuwata da
tsarina haka nan zuciyata ta aminta da soyayyar
ta dari bisa dari don...
Ckin zafin rai mma tadaga mai hannu tace "kai
ya isa haka, saita bakinka kasan abinda kake
fada, fatima an yi mata miji tsawon lokaci mai
yawa kuma ba za a fasa ba shi a ba ka ba.
kada kasoma sanyawa zuciyarka soyayyarta
wahalar da kanka za kayi don baza kasame ta
ba.
Bai ce komi ba yamike yabar faol zuwa daki ? sa
yakira dr. hafiz yace "kana ina ? "
Yace"ina asibiti yanzu muka fito daga meeting..
Yace "to ina ka dosa ?
Yace "gida za ni akwai magana ne ?
Yace "kwarai kuwa magana ma babba ba karama
ba.
Yace "kasameni a gida mana.
Mota yadauka yanufi gdan dr. hafiz da ke hotoro
ya iske ya rigashi isa, yace "matar gdan fa da
yaran ?
Dr. hafiz yatabe baki yace "ai mata ba su da
matsalar data wuce biki, sunan wai kanwa ta ce
data haihu tun karfe bakwai tabar gdan nan ko
abinci ba a tanadar min ba kuma yunwa nakeji
sosai, yanzu sbda Allah a irin wannan tsarin idan
munce, za muyi aure munyi laifi ? ko yanzu da
zance zanyi aure sai ka ji bala'i na tashi nakan
rasa su mata wane iri ne.
Dr. khalifa yabushe da dariya yace "na san duk
yunwa ce tasaka wannan surutun ai kai da sauki
ma tunda ka iya shiga kitchen ka sarrafa
abincinka kaci ni ko tea ba na iya dafawa.
Dr.hafiz yace "to ai kuwa ka koya mata ba su da
tabbas surutu da soyayya a waje suka iya idan
an shigo gdan sai a hankali musamman idan an
fara ajiye yara, bara in dafa indomie kaina har
ciwo yake sbda yunwa.
Bayan ya gama dafa indomie din suka mike a
kasa suna ci yace "mutumina wai wace babbar
magana ce ?
Yace "ina fatan ka gane fatima"
Dr. hafiz yace "ba zan kasa fahimtarta da wai ba
domin na fahimci zuciyarka ta amsheta da
gaggawa.
Yace "kwarai ba ka yi fahimtar kuskure ba, kallo
daya nayiwa yarinyar naji zuciyata ta aminta
tazamo mata ta.
Dr. hafiz yace "to ai bbu matsala yarinyar datake
rayuwa a cikin gdan ku na yi farin cikin han.
Dr. khalifa yace "kai dakata saura sati biyu
bikinta.
Dr. hafiz yace "to ba sai a lalubo wata ba abinda
ga matan nan dayawa dakansu suke cewa ma
suna so.
Dr. khalifa yace "kai likita mata suna suka tara,
duk yawan dasukayi irin su fatima daban suke, a
iya budewai idona da yawace yawace na ban taba
ganin mace mai kyaun fati ; a ba, tare da kyaun
fuska ,dubi yadda tsarin halittar jikinta
yake,habawa wannan ai itace mace mutumi na.
Dr. hafiz yayi dariya sosai yace "kai wani irin
kayatarwa fatima tayi maka, ne karude haka ?
Haba likita kada kabari fatima taji za ta rainaka
ka ga yarinya ce karama ko ka mance kana cewa
ba ka son karanar yarinya ?
Dr. khalifa yace "kai tafi chan wannan lokacin ya
wuce ba zan iya hakura da yarinyar nan ba.
Dr. hafiz yabata rai yace "kai Abbakar muyi
magana ta gaskiya yarinyar daya rage saura sati
biyu bikinta yya za ayi kace kana sonta ? ko a
shari'ance ba kyau nema cikin nema ,kayi hakuri
kawai mace in dai mace kake bukata za kasamu
wadda tafi fatima kyau sai dai in fa fatima kake
nema.
Dr khalifa yadan marairaice yace "haba dr. hafizu
yaya za ayi ka sanyayar min da jiki ? bayan ka
san ban taba nuna maka wata diya mace dana
damu da ita ba ballantana har in nuna damuwata
akan sonauranta, tunda nagaya maka ai ka san
dagaske nake ya kamata kataimake ni da
shawarar dazan samu mafita ba kasace min
guiwa ba.
Dr. hafiz yace "to ai ni banga hanyar mafitar bane
Abbakar, sati biyu fa yarage biki sai kuma muce
muna so ? wannan ai son kai ne da zuciya, kuma
kasani son kai da zuciya ba dabi'a ce ta mutan
arxiki ba.
Dr. khalifa yace "knan so kake kace min sai dai
inyi hakuri da fatima ?
Yace "Don Allah kayi wannan hakurin sai Allah
yabaka wacce tafita....
Dr. khalifa yace "kai hafiz daina min wannan
maganar da wuya in za tayiwu bakasan menake ji
bane game da wannan yarinyar, ban taba sanin
haka so yake ba.
******
Tun a wannan rana mama tafara shirya amarya
fatima da kayan gyaran jiki na mata suka tunkari
lamarin dagaske, batasan rikicin da dr. khalifa ke
ciki game da matsananciyar soyayyar fatima da
ta damki zuciyarsa ba, a wannan daren yakasa
sukuni yakwana yana tunanin tawace hanya zai
samarwa kansa mafita.
Abin da dai yasawa kansa shi ne ko ta wani
hanya zai mallaki fatima babu yadda za ayi yayi
sakacin dazai rasa ta, bai san haka ciwon so
yake ba sai yau.
A gdan fatima takwana suna tattauna yadda biki
zai kasance, abinda fati take jaddadawa ummi shi
ne "ta sani khalifa sbda ba ya da tausayi, tace "ni
kam ummi na rasa yadda zanyi da takaicin dana
ke ji a raina game da yaya khalifa, ko ganinsa ba
na son yi sbda kawai ya nuna ba ya sonki.
Ummi tayi murmushi tace 'to yaya zanyi na
zubawa sarautar Allah ido na zubawa dr. khalifa
ido, na tabbaatarwa raina ko ban samu dr. khalifa
ba to zan tabbatar wata diya mace bata same shi
ba, idan narasa shi sai dai kowa ma yarasa .
Fatima tace "kina nufin za ki hanashi aurene ?
yaya mutumin da ka kaasa jawo ra'ayinsa
yasoka za kasawa ranka cewa za ka iya hana shi
aure ?
Ummi ta girgiza kai "ba aure xan hana shi ba ban
isa in hanashi aure ba ni dai na ce sai dai kowa
yarasa .
Riga da zani na atamfar egyptian ce a jikin fatima
tana tsaye ita kadai a kitchen tana suyar kosai,
kawai ganin mutum tayi a kusa da ita yana fadin
"fatima aiki ake yi ne ?
A firgice tawaiwayo tadubi dr. khalifa yana sanye
da doguwar riga fara kal kamshi mai dadin gaske
yana tashi a jikinsa, ta matsa gefe ganin yadda
yatsaya daf da ita kamar zai taba ta, yayi
murmushi yace "ya kike matsawa haka kamar
kinga wani dodo ? zo ki kwashe kada yakone.
Ta katsa motsawa sai gabanta ke faduwa a
lkacin ummi tashigo tana fadin "fatima kin
gama ?
Ganin wanda ke tsaye a kitchen din yasata
tsayuwa turus tana kallonsa shi da fatima, ganin
ummi yasa yatsuke fuska yafice daga kitchen din
ummi takwashe kosai tana fadin "yau kuma meya
kawo doctor kitchen din nan ko wani abu yake
nema ?
Kokarin da fatima tayi shine na daidita muryarta
don kada ummi tazargi wani abu a ranta tace "ni
ma gani nayi ya shigo.
Kallon da ummin tayi mata shi ne yasa tafahimci
kuskuren ta a bisa abinda tafada, to sai dai kuma
batasan abinda za tafada din ba in ba hakan
tafada ba, jikinta yakara sanyi sosai ganin ummi
bata sake magana ba, takwashe kosan tace
tadakko kunun gyadan dasuka dama zuwa falo.
Bayan sun gama shirya tebur din ne tadubeta
tace "ki je kigayawa doctor an gama shirya tebur
kada yai sanyi yakasa ci.
Cikin dacin rai fati tace "ni ce ma zan fadi mai ?
kin taba ganin na nufi hanyar dakinsa.
Ummi ta tabe baki tace "ai ba abin zafi bane gani
nayi ya fi son yi miki magana fiye dani amma kar
ki damu bari ni inje in gaya mai.
Fatima taja tsaki tawuce daki, yayin da ummi
tanufi dakin dr. khalifa ta kwankwasa yace
"waye ?
Tace "ni ce ummi.
Ga mamakinta sai yace "shigo"
Ta bude jikinta ba karfi yana kwance bisa gado
yanuna wata kujera yace "zauna in miki tambaya.
Ummi na son kallon fuskar dr. khalifa yana yawan
burgeta nan da nan taji hawaye ya taru i donta
tayi kasa da kanta, yana sane da halin datake
shiga idan tana kusa dashi yashare domin shi ma
din a halin yanzu abin tausayi ne duk yadda take
son sbi ya fita son fatima kuma ya fita shiga
hadari domin kuwa gab yake da yayi babbar
asarar rasa fatima.
Ke ummmi gaya min dangantakar ki da fatima".
Abin da yace da ita knan lamarin dayasa tadago
cikin sauri zuciyarta na bugawa sosai tace "ban
gane ba yaya khalifa.
yamike zaune bai ce komi ba, tunanin da yake kai
komo a zuciyarsa shi ne shawarar da dr. bashir
yaba shi duk a daren jiya lokacin daya same shi a
waya yabashi labarin halin daya ke ciki yace
"Bash don Allah kada ka kashe min guiwa ba zan
iya hakuri da fatima ba ni kadai nasan halin da
zuciyata ke ciki.
Dr. bashir yayi shiru kamar ba zaiyi magana ba.
Khalifa yce "ya ya naji ka yi shiru.
Bashir yayi ajiyar zuciya yace "Abbakar ta yaya
xa a maido wannan aure a kanka bayan sati biyu
yarage kace ayi mata aure.
Yayi tsaki yace "amma dai ni ne nafada maka
saura sati biyu ayi bikin ko ? ka ga ba na bukatar
kasanar dani shawara dai nanemeka bashir.
Yace "to shi me rai ba ya rasa motsi, hanya daya
ce wata kila idan munbi za mu iya dacewa.
"Fadi inji"
Bashir yace "ta hanyar ummi da mama ne kawai
za mu iya yin nasarar jan hankalin fatima idan da
rabo sai ayi nasara.
Ummi tace Bashir ?
Ya amsa "ita nace dalilin dayasa nace ita kuwa
inada labarin cewa fatima ba ta da kawa aminiya
abokiyar shakuwar data wuce ummi, ummi na iya
sauya ra'ayi da tunanin fatima sbda yarda da
amincin dake tsakaninsu, yayin da mma ke da
girma a idon ummi ba ta iya musa maganar
mama.
Dr. khalifa yajinjina labarin a ransa yace "hakane
Bashir to amma fa kada ka manta ba wanda
ummi ke so sai ni, ban amince da auranta ba ta
yaya za ayi ta amince da wannan batu ?
Ba ka ganin za tayi amfani da wannan damar gun
lalata min al'amarina da fatin ?
Bashir yace "to ai daman ba kai tsaye za kagaya
matan ba sai ka bi tawasu hanyoyin na hikima
wanda zaisa ta fahimci kana sassauta zuciyarka
akanta,ma'ana kadinga sakar mata fuska kuna
hira kuma karara kanuna mata cewa kana
bukatar ta taimaka maka akan fatima za kayi
mata duk abinda take so, idan kayi mata za ta
amince tunda tana sonka ba ta son damuwarka,
sannan ita kuma mama ka marairaice mata sosai
kanuna mata ba za ka iya rayuwa ba fati ba, so
so ne amma son kai ya fi da sannu za ta tausaya
maka tagoya ma baya.
Dr. khalifa yakashe wayar kansa a daure tamau
yana jinjina yadda zai iya jan hankalin ummi har
ta taimaka masa, bayan magana ma ba yi mata
yake ba, ya kwana yana tunanin abin ga dumbin
ciwon so na karuwa a zuciyarsa har yana jin ina
ma zai iya fidda son fati daga ransa ya huta,
amma ina duk yanayin dazai shiga in dai zai
mallaki fatin dole yajure tunda mallakar ta shi ne
kadai kwanciyar hankalinsa da farin cikin
rayuwarsa, amma fa yana takaicin hakan bai
damu da lallaba mama ba ya san tana sonsa da
tausayinsa, ummin ce dai matsalarsa kuma ya
amince ta hanyar ummi zai iya cimma nasara..
Wannan shi ne dalilin dayasa da gari yawaye
yanufi kitchen ya san ummin ce ke dafa abincin
safe a gdan ga mamakinsa sai yaga gimbiyar ce
a kicin din...
Yakatse tunaninsa anan yadawo da ganinsa ga
ummi wadda tayi tagumi tana goge hawayenta
wadanda tayi kokarin tsaida su suka ki tsayuwa
takyalesu suyi ta zubar lokacin su ne.
Ummi"
Muryar dr. khalifa ya ratso kunnanta da sassan
jikinta tadago kai suka kalli juna tace "Na'am".
Ina son ki yi min wani taimako daya za ki iya ?
Idan bai fi karfina ba insha Allahu zanyi maka,
fada min inji"
Ummi "inason kawarki fatima.
Inason in aureta za ki iya taimaka min ki ja min
ra'ayinta a fasa ba musbahu auranta a bani ?
Wai shin mafarki ne wannan ko gaske ?
Dr. khalifa datake tsananin so ne yake gaya mata
da bakinsa cewar fatima aminiyarta yake so ya
aura har yana neman ta taimakeshi. wane irin
raini khalifa yake mata, wani irin cin fuska ne
wannan ?
Hawayen idanuwan ummin suka kara ballewa
tashiga kuka kamar ranta zai fita, Dr. khalifa yace
"ummi idan ba za ki iya taimako n ba kitashi ki
ban guri.
Tace "ya ya khalifa ba ka da tausayi kuma baka
san darajar soyayya ba, baka san ciwon so ba, da
ka san zafi da dacin rai dake cikin ciwon so da
baka nufeni da wannan maganar ba, ka san
yadda nake ji a zuciyata kuwa ? tamike tsaye
idanunta tazuba kansa wadanda suka kada jawur
tana huci tace "khalifa na sani ba ka so na, ba
zan yi maka dole kaso ni ba, kuma ba zan taba
bin wata hanya don kaso ni ba,, ni kam ina sonka
son da ba zan taba dainawa ba, abu daya nake
son tabbatar maka wanda shi ne ba zan taba
barwa wata kai ba sai dai kowa yarasa ni kam na
ami ? ce na rasaka....
Amma ba zan hakura ba.
A fusace tabude kofar tafita, yabiyota dasauri
yasha gabanta ya sausauta murya yace "haba
ummi kitsaya ki fuskance ni da kyau mana na yi
miki alkawarin zan miki duk abinda kikeso
matukar na mallaki fatima.
Murmushi tayi masa tace "ka yi kuskure babba
doctor daka fuskance ni da wannan maganar.
Ta zagaye shi tashige cikin gida.
Abba da mama ne kawai a falo suna breakfast,
tashige dakin dasauri dan ba ta son sukalli
idonta.
Ba karamin faduwar gaba fatima tayi ba ganin
ummi ta shigo tana kuka, tamike tariko ta tana
tambayarta lafiya ? me khalifan yayi miki ?
Ta ja hannunta suka zauna tana goge mata
hawaye, ummi tace "ummi babu abinda dr.
khalifa yayi min fyace ya shaida min cewa yana
sonki yana son in taimake shi yasamu auranki.
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. fatima
kefadi muryarta na rawa tace "bai san an kusan
bikina bane, ke ko ba a kusan biki na ba ina ni
ina shi.
Wani irin abu ummi taji ya tokare mata zuciya,
kirjinta yamata nauyi, kanta ma yashiga sarawa
nan da nan taji jiri ya fara dibarta, tadaure tatashi
tadauki hijjavinta tayi sa'a abba da mama sun
shige daki tafice daga gdan taja mota sai gdan
mahaifiyarta.
Hajiya Hauwa na barci ummi tafada jikinta tana
kuka mai tsanani, a rude hajiyar tatashi tana
tambayar lafiya lafia ?
Wa ye yamutu ?
Tace "hajiya na ga takaina na shiga uku, wai
khalifa ne yau din nan yakirani yana shaida min
cewa ba macen da yake son aura sai fatima.
Yana son in taimake shi yasamu hadin kan
fatima.
Hajiya tace "yawwa abinda nake gayan miki ya
auku ko ? ai lokacin da muke gaya miki gani kike
ba zai taba yiwuwa ba, bayan mu munsan
faruwarsa abu ne mai sauki, idan kika kalli fatima
da tsarinta mace ce da maza ke burin mallakar
irinta, ta yaya khalifa yana ganinta a gdan zai
hadiye maitarsa.
Ummi kuka take tana karawa fargaba da takaici
sun sa ta kasa samun abinda za tace yayin da
hajiya ke ta fadace fadacenta inda take shiga ba
nan take fita ba, takira hajiya saude a waya tace
"kinga abinda muke gudu saida ya auku, taurin
kan yarinyar nan zai ja mana asara.
Bayan saude ta saurari abinda ke faruwa daga
bakin hajiya hauwa tace "kujirani za mu yi
maganinsu dukkansu wannan karon sai mun bude
musu wuta duk tsawon lokacin da muka dauka ya
tashi a banza knan ? wannan abu ne da ba zai
taba yiwuwa ba.
Ba afi minti daya ba hajiya saude tayi dirar
mikiya a gdan tadubi ummi tace "kukan banza da
wofi idan mutum bai aiki da shawarar na gaba
dashi yana tare da nadama, gun malam za mutafi
yanzun ba za mu rangantawa khalifa ba.
Hajiya hauwa ta tabe baki "ba sai in za tayi
abubuwan da aka ce mata ba.
Tace "to kada ma tayin batayi ba ta isa tazo tana
mana kuka anan ?
Har suka isa gdan malam din kuka sosai ummi
takeyi ita takaicin ta ace dr. khalifa yarasa wa
zai so sai aminiyarta fatima, tunda su hajiya suke
gaya mata abin da zai iya fruwa ganin take bazai
taba yiwuwa ba ashe kuskure tayi babba, hajiya
hauwa da hajiya saude ke ta tattaunawarsu kan
matsalar ita kam ta sunkuyar da kanta tana
tunanin yadda za takasance in har fati ta amshi
soyayyar dr. khalifa koda yake abu ne da take
ganin kamar zaiyi wahala sbda koyaushe fatima
na tabbatar mata da cewa bbu abinda zai hana yi
ma iyaynta biyayya, tanayin wannan magana ne
idan wasu daga kawayensu suna cewa"kyaun
halittarta ya fi karfin ta auri malami almajiri irin
malam musbahu wanda ba wayewa a tare dashi,
to anan ne take tabbatar musudacewa "malam
musbahu ya fi kowanni namiji a gunta tunda shi
iyaynta suka zabar mata dole tayi iyayya gasu
sbda yardar Allah take nema a cikin al'amuranta
ba wai kyale kyalen duniya da abinda ke cikinta
ba.
Ummi tana cigaba da gasgata abubuwan da fatin
ke fada ne ganin yadda bata kila kowani irin da
namiji duk matsayinsa, hakan ne yasa ummi ta
tabbatarwa kanta cewa ko dr. Khalifa yadawo ya
ce yana son fati bazata amince da batunsa ba,
sbda akidar biyayyar iyayanta data sawa
zuciyarta to in dai haka ne ma me zaisa in daga
hankali na ? Ta tambayi kanta in dai fatima
bazata amince da dr. Khalifa ba me zaisa ta
tayarwa kanta hankali, to a daidai lokacin da
wannan tunanin ke tasiri a zuciyar ummi har
tafara jin saukin zafin da zuciyarta tadauka sai
kuma dai wani gdfen na zuciyarta yafara tunasar
da ita cewa fa dr. Khalifa kyakyawan namiji ne ga
ilimi ga naira, mata kuwa ba abinda suke so a
gun da namiji wadanda suka wuce kyau da naira
ballantana abin yahadu da ilimi da wayewa,
kadan ne suke la'akari da addini da kyawawan
dabi'u, fatima kam tanada banbanci da sauran
matan zamani, iya zaman ta da ummi ta tabbatar
za ta mata wadannan kyawawan shaidar a ko ina
fatima ba ta da kwadayin abin duniya don da
tanayi da dr. khalifa bai dawo yasa meta, wannan
tunanin duk yake kara kuna a zuciyar ummi
sunada tasiri mai karfi don ta tabbatar da hakan.
Ummi na wannan dogon tunani ne kafin malam
yabasu damar shigowa, hajiya suka shaida masa
abinda ke tafe dasu, yajawo wani rairayi dake
bayansa yafara zane zane yana tambayarsu wasu
abubuwan dasuka shafi dr. khalifa da fatima da
iyayanta.
Malam yajinjina kai yace "hakika khalifa ba
karamin so yakewa fatima ba, kai hasalima bai
taba jin son wata diya mace a ransa
kwatankwacin yadda yake son fatima ba, kuma
ya yi dammarar auranta ko tawani hali.
Wannan bayanin na malam yasa ummi tunani
kamar kirjinta zai tarwatse sbda faduwar gaba,
hajiya hauwa tace "to malam yanxu knan khalifa
ba zai auri ummi ba, kuma kana ganin auransu
da fatima mai yiwuwa ne dukda cewa an kusan
bikinta ?
Malam yace "to ni dai na gaya muku abinda
nagano tar da khalifan ne, batun yiwuwar auransa
da ummi idan kun bi abubuwan dazan tsara muku
anyi an gama, fatima kuwa zan fatattaki
soyayyarta ne daga zuciyarsa, amma gskiyar
magana ba aiki ne mai sauki ba.
Hajiya saude tace "malam indai za asamu nasara
wahala mai sauki ne kuma me wucewa ne me ake
bukata ?
Malam ya gyara zama yace "dafarko kamar
yadda nagaya maku a baya za ku kawo min
kasar da khalifa ya taka, za ku kwao gashin
kansa da hankicinsa da hularsa da hotonsa, za
ku biya kudin fararan raguna guda uku, jajayan
akuya guda uku, jajayan zakaru bakwai, sauran
abubuwan kuma mu za mu samo su, kudin aiki
dubu dari, ku zuba ido za kuga aiki da cikawa.
Suka tsaya akan cewa bayan kwana biyu za
akawo duk abinda aka bukata har kudin, suka
dawo gda da shawarar yadda za asamu kudin
dasuka kama har kusan dubu dari biyu, a karshe
dai Alhaji muhammad mahaifin dr. khlifa aka
buga wa waya suka mai karyar cewa asibiti za su
yace zai aaiko musu da kudin dama sun saba
dahaka duk abinda suka bukata zai musu iya
ikonsa amma ba sa gani, su dai matarsa da
dansa ne ba sa so dashi kansa sai dai dukiyarsa
A DAREN FARKO
20
Fitar ummi yakara dagawa fatima hankali sosai
takifa kanta a cinyarta tana sharar kwalla,
meyasa dr.khalifa zai mata haka, ya ya za ayi
yarasa wadda zai fadawa cewa ma yana sonta
sai ummi wannan ba karamin cin fuska bane da
walakanci, duk abinda zai sa ummi tayi hushi da
ita abin ya yi yawa ko da yake ta san dole ne
ummi tayi fushi da ita akan dr. khalifa, ba wanda
ummi ba za ta iya juyawa ba sbda son datake
masa ba kadan bane, ta gaji da kukan bakin ciki
da takaici tatashi a sanyaye. zata tafi gda taci
karo da mama a harabar gida tana magana da
ado me musu wanki da guga, yanayin ta da
mama tagani yasa tayi saurin matsowa daf da ita
tace " 'yammata lafiya ? kukan me kikayi haka ?
Ba kuka nayi ba wani abu ne yafada min ido.
Tace "ina ummi ?
Tace "ta fita ban san ina taje ba.
Tace "ke ina za ki yanzun ?
Tace "gida za ni yanzun xan dawo.
Kamar zata hanata tafiya sai tayi tunanin bai
dace ba batasan abin da za tayi ba don haka ta
kyaleta tatafi tadawo falo tazauna.
Dr. khalifa yashigo cikin shirin fita yazauna suka
gaisa tace "ba za kaci abincin bane naga ka yi
shirin fita ?
Ya girgiza kai"ba zan iya cin komi ba xuciyata
tana ckin damuwa bansan mafita ba a cikin halin
danake ciki.
Mama tayi murmushi tace "khalifa Allah (SWT)
daya halicce mu cewa yayi "ban halicci mutum da
aljan ba sai don su bauta min, to ni dai a ganina
ba wani abinda zai dagawa mutum hankali akai
in dai ba bautar Allahn nan ba, to ita kanta
bautar Allah ba zafafa mana akai ba, Allah ba ya
daurawa wata rai sai abinda za ta iya, in kuwa
haka ne bbu abinda zai zamo mai tsanani a cikin
wannan rayuwa ko meye shi kuwa, musanman
ida mutum yana la'akari da rayuwar duniya,
wadda fararriya ce kuma kararriya, duk wani abu
dakasani dayake a cikin duniyar nan a dayan biyu
yake, ko dai ka kare kabar shi ko shi yakare
yabarka, to meye dalilin damuwa.
Khalifa yayi ajiyar zuciya yace "mama na san za
ki yi min shaidar hakuri da kau da kai a cikin
al'amarin rayuwa idan yataso min, mama a
wannan karon na samu kaina a yanayin dana
kasa mallakar kaina, don na sa hakurar da
zuciyata tayi hakuri da abinda take nema.
Wallahi ji nake k ; ar zan mutu sbda ciwo fmda
radadin da nakeji a zuciya ta.
Mama tayk mai zumu da ido tana kallon fuskarsa,
tabbas yanayin fuskarsa ta nuna tabbatar da
abinda yake fada haka ne, tausayin sa yakamata
amma tjure don kada ta dada karayar mai da
zuciya tace "khalifa daman akwai abinda ba za a
iya hakura dashi ba a duniyar nan ? a matsayin
mu na musulmi munyi imani da cewa dukkan
abinda yasa me mu haka Allah ya kaddara mana
kuma ba mu da ikon kaucewa abinda Allah
yakaddara mana ,kadaure kayi hakan mana.
Yace "mama ba zan iya hakuri da fatima ba, don
Allah ki taimake ni duk yadda za kiso alheri a
gdan wanda za a ba auran fatima ba kamar a
gdan nan ba.
Mama ta jima kanta a kasa tarasa abinda za
tace, Dr. khalifa yaci gaba da fadin "wlh mama
babu abinda zan iya aiwatar wa a rayuwa ta in
dai ina cikin wannan yanayin ni dai kisha min kan
yarinyar nan da iyayanta ina matukar kaunarta.
Tace "khalifa wace irin son zuciya kake son mu
aiwatar ne ? don Allah kayi hakuri.
Ya tareta dasauri yace "don Allah kada ki ba ni
umurnin yin hakuri ina son fatima dayawa zan iya
kowani irin hali idan ban mallaketa ba, ke za kiyi
hakuri ki taimakeni ba wai ni zanyi hakuri ba
waye zai iya hakuri da abinda yake so mama"
Tace "ahi ke nan kabani kwana biyu zanyi tunani.
Nan take mama tgano dalilin kukan da fatima ke
yi knan, to kuma meye dalilin fitar ummi da safen
nan ba tare da ta sanar dakowa inda za ta ba, ta
kira wayar ummin a kashe takira hajiya hauwa ita
kuma tana ringing ba a daga ba, ta aje wayar a
gefe tayi tagumi tunani ya sha mata kai, shin
yaya za ta yi da wannan al'amari, tana bukatar
shawara, ko dayake duk wata shawara ba ta
wuce ta lallashi khalifa yayi hakuri ba domin
wannan son zuciyar ba yiwuwa zaiyi ba.
Takira sadiya kanwarta dake tayata zama a gdan
a dalilin mutuwar auranta tashaida mata abinda
ke faruwa.
Sadiya tace "tabdijam wannan ai babbar magana
ce.
Tace "to sadiya nima haka nagani, na rasa ta ina
zan gano mafita.
Sadiya tayi murmushi tace "to amm fa mama so
so ne sonkai ya fi, tun kafin khalifa ydawo kasar
nan idan nakalli fatima nakanji sha'awar ina ma
itace khalifan zai aura, hakan yasa ba na so ma
in ji ana hirar auranta me zai hana tunda dai
khalifa ya nuna wannan damuwa ta sa mu san
yadda za muyi ya aureta dama ance matar
mutum kabarinsa wani bai auran matar wani.
mama tagirgiza kai tace "kai anty sadiya anya
wannan maganar ta yi daidai kuwa ?
Sadiya tace "ta yi dai dai mana mama abinda
yasa nace dake haka, idan khalifa bai samu auran
fatima ba ba zai maida kansa kan aure ba
sannan tunda ita yakeso in ya aureta hankalinsa
zai kwanta sosai, yarinya ce mai hankali da
natsuwa, gskiya mama kada muyi wannan
sakacin daga karshe mu zo muna nadama.
Mama takwantar da kanta bisa kujera idonta na
kallon silin, sadiya ma ta zo da maganar daya
cancanta a duba, abin ne da nauyi dole kam tsan
abin yi in banda wannan matsalar ta fi kowa son
khalifa ya auri fatima sbda fatima mace ce tagari
to ya ya za tayi tadubi fati tace tafasa auren
musbahu ta auri khalifa ???
******
Tunda fatima tashiga gdansu bayan gaisuwa
datayi da iyayanta bata kara cewa kowa kmi ba
tashiga dakin innarta takwanta tana ci gaba da
hawaye.
Inna ta tambayeta damuwarta tagaya mata komi
tace "tabdijam abin da malam ke gudu ne yafaru
kin san shi Alhaji baban khalifan ya taba cewa
yana son malam yaba dansa auranki yace ya riga
ya ba da ke.
Fatima tace "to ai inna ko da ba a bayar dani ba
bazan taba amincewa khalifa ba, sbda aduniya
dai banga da namijin da ummi ke so irin sa ba,
ummi ba ta da burin daya wuce mallakarsa, ta
kwallafa rai a kansa tana matukar so da
kaunarsa.
Matsayin ummi gareni ya wuce in yi mata haka,
don Allah inna kada ki saurari maganar khalifa ba
shi da tausayi bai da adalci.
Tace "to ina ma za ayi haka ? dole yahakura.
Fatima tadinga nacin kiran ummi a waya wayar a
kashe take, dole taje ta lallashi ummi, ummi ta fi
komi a gareta.
Bayan sallar azahar tashaidawa inna za ta
gdansu ummi tace sai ta dawo, ko ganin gdansu
dr. khalifa ba ta son yi ,sbda takaicin ya cuceta
ya hadata da babbar aminiyarta abokiyar
shawararta.
Tana tsaye bakin titin kan layinsu tana neman
adaidaita sahu kawai sai ganin mota tayi ta yi
fakin a gabanta, bakaken gilashin da aka zuge
yabata damar ganin wanda ke ckin motar. dr.
khalifa ne gabanta yafadi tsmatsa dasauri tana
masa wani irin kallo, yace "ina za ki ne fatima. "
Tayi shiru kamar ba da ita yake ba, yace "don
Allah kigaya min inda za ki in kaiki.
Anan ne ta hasala tace "ina ruwanka da inda za
ni, ni ba neman taimakon mota nake ba.
Yakashe motar yafito yana kare mata kallo daga
sama har kasa, yana murmushi a wannan lokacin
ne yadada tabbatarwa kansa yana son fatima
kuma ba zai iya sakacin dazai rsata ba insha
Allahu wannan yarinyar matarsa ce ta sunnah.
Kwatsam adaidaita sahu ta tsaya a gabansu,
ummi ce tafito idanunta fes akansu bata ce komi
ba tabiya dan adaidaita kudinsa tawuce za ta
tafi, fatima tabita tana fadin "ummi ai gdanku za
ni Allah ne yataimaka bamuyi sabani ba.
Ummi tajuyo suka hada ido ,kallon datake mata
yana dagawa fatima hankali, tawuce dasauri
tabar gun, ta tsaya sororo tabi ummin da kallo.
Dr. khalifa ya iso gabanta yace "fatima don Allah
ki tsaya ki saurareni, zuciyata tana matukar so da
kaunar ki don Allah ki tausaya min.
A fusace tace "ai kai ba abin tausayi bane, babu
wani dalilin dazaisa a tausaya maka, tunda kaima
ba ka tausayin mai sonka, tun yaushe ummi take
fama da ciwon sonka a zuciyarta amma ka ki
kadubeta kake walakanta ta sbda kawai tana
sonka ?
Yazuba mata ido yana murmushi wai shi yarinya
kamar fatima ke wa tsiwa haka, son da yake
mata ya yi tasiri da isarsa ta namiji ba zai yi
komi a kanta ba, a iya rayuwarsa bai taba samun
kansa a yanayi irin wannan ba.
Tayi tafiyarta tabarshi a gun yana binta da kallo,
gumi yana yanko masa har ta bace sannan
yashiga motarsa yaja zuwa gdansu.
Baiyi tunanin nan gdan na su fati za tazo ba sai
yaganta za tashiga yayi murmushi kawai ,tafizge
kanta tashiga ckin gda tayi sa'a mama ta fita
anguwa sai 'yan aikin gdan suna hidimomin su,
ta iske ummi a daki tana hada kayanta .
Ta amsa sallamar fatin ba tare da ta kalleta ba,
fatima tazauna a bakin gado muryarta a kasa
kasa takira sunan ta, ta waiwayo tace,"na'am
fati.
Tace "ummi meye laifina akan wannan al'amarin
lokaci daya za kijuya min baya ki tsane ni ? shin
ni na budi baki nace ina son khalifa ? ko zuwa
nayi sashensa naja ra'ayinsa don yasoni ?
Ummi tayi mata wani lalataccen kallo tace "ke ki
kama kanki, kin san dai ban tare ki dawata
magana ba akan khalifa, don haka ba na bukatar
kiyi ta nemana dawasu maganganu.
Fatima tadaga murya tace "wlh ummi ko kusa
bakiyi min adalci ba, na yi zaton a gun ki zan fara
samu shaidar wani da namiji va zai taba samun
masauki a zuciyata ba, ko ina son khalifa ko babu
maganar musbahu a kaina ba zan taba ba, dr.
khalifa fuska ba sbda na san waye shi a gunki,
ballantana kwanaki suka rage a daura min aure,
hakanan ba na son shi ba na ra'ayin shi to meye
na damuwa, don Allah ummi kada kidauki alhaki
na kada ki watsa mana zumunci ki kwantar da
hankalinki insha Allahu ta hanya ta za ki iya
mallakar dr. khalifa in dai Allah ya kaddara mijinki
ne zan yi amfani da damar dana samu a kansa in
ja ra'ayinsa gareki amma fa sai in na samu hadin
kanki.
Ummi tayi dif tan juya maganganun fatima
wadanda sukan saurin fisgar hankalinta tadawo
natsuwarta, idanunta da zafin kishi yasa suka
rufe suka bude domin ta fara jiyo kamshin nasara
a maganganun fatima.
Ta taso tadawo kusa da fatin tazauna muryarta a
hankali tace "kiyi hakuri fatima a cikin gaba daya
al'amura na ba na wasa da dr. khalifa sbda
soyayyar danake mishi, ban taba jin za a wayi
gari watarana inji ba na san na budi ido in ganki
ba sai ranar da dr. khalifa yabudi baki yace min
"ke ce mace daya dayake so ya aura a duk fadin
duniyar nan, a wannan lokacin ji nayi na tsaneki
fatima duk da na san ba laifinki bane ba ke kika
sa yasoki ba amma wannan baiyi tasirin daya
Hana inga laifinki ba.
Fatima tayi murmushi tace "ke ma ba ki da laifi
ummi domin ba laifi bane don mutum ya yi kishin
abinda yake so, ballantana soyayya irin ta ki ga
dr. khalifa, hnkalina ya tashi don sabon danayi
dake ta ina zuciyata xa tasake kin juya min baya,
ummi inason ganin kin mallaki dr. khalifa don
haka zn daure shi da jijiyoyin jikinsa tunda ya ce
yana sona to ya kawo kansa garemu, kiyi hakuri
da duk abinda za kiga yana nuna mini na so,
kafin mu cimma burimmu, kuma kibashi hadin kai
a duk maganar dazai miki a kaina ki nuna mai kin
goyi bayansa, xai kasance yana son magana dake
sbda hirata da kuke.
Nan take ummi taji zuciyarta ta yi mata wasai,
kaunar fatima takaru a zuciyarta, tafasa hada
kayanta tabar gdan kamar yadda tayi nufin yi,
bayan tafiyar fatima gda takira wayar hajiyarta
tashaida mata yadda sukayi da fatima, hajiya
tace "anya kuwa dagaske take ummi ? kada fa
tayaudare ki, sai wahala ake awai wata manufa a
zuciyarta.
Hajiya tace "to ki dai yi taka tsan tsan kuma
kisan yadda kikayi kika kawo mana abubuwan da
malam yace a kawo wadanda suka shafi khalifan.
******
Cikin dacin rai fatima tadawo gida tana takaicin
son zuciyar dr. khalifa duk da ta san ba zaiyi
nasara a kanta ba amma abin yana ba ta haushi
sosai, ga mamakinta sai ta iske mama da anty
sadiya a gdan na su suna hira da inna ga zogala
a gabansu suna ci.
Ta fadada fara'arta tace "lah mama dama nan
kika shigo.
Tace "eh amma mun biya kasuwa kafin mushigo
nan din.
Inna tatashi tace "bari in tuka tuwon nan in hada
miya in dawo.
Mama ta ji dadin fitar inna tace " 'yammata na
zo ki zauna anan kiji wata magana.
Daf da ita fati tazauna tace "wannan zuwan na ki
ne don gunki muka zo.
Tace "ni mama.
Tace "kwarai kuwa fatima ko baki kai matsayin
daza muzo gunki ba.
Tayi kasa da kanta tana girgiza kai, mama tace
"fatima munzo da kanmu ne nan dan kidauki
abinda mukazo miki dashi da mahimmanci, a
wani lokacin idan za kagawa mutum abu mai
muhimmanci to kadubi yanayin dazaka fada masa
dan yafi kama batun da daraja. fatima na san
matsayin uwa nake a gunki ckin gdan nan na san
bbu abunda xan nema in rasa shi sai fa in ba ku
dashi.
ko da yake maganar danazo miki da ita mai nauyi
ne amma duk da haka nauyinta ba zai hana in
gaya miki ba, sbda na san wacece ni a gunki, ba
kuma ina nufin yin amfani da wannan damar bane
in tursasa ki ba a'a alfarma ce nake fatan kiyi
min.
Fatima dan uwanki khalifa ne ke neman alfarmar
ki amince mai ya aureki sbda ke kadai ce
zuciyarsa ke so, kuma ta aminta ya aura.
Tunda mama tafara magana fatima tasan inda
tadosa, dataji ta yi shiru tace "mama duk abinda
kika fda haka yake, kuma alfarma kowace iri zan
yiwa kowa a gdanku amma a wannan karon sai
dai in ba ki hakuri mama abu guda daya ne zai
hana in amsa wa yaya khalifa soyayyarsa itace
ummi.
Ummi kuma fatima ?
Me ya kawo ummi ckin wannan maganar ?
Fatima tagyara zama tace "mama ummi itace za
tayiwa yaya khalifa shamaki dani domin kuwa ta
fi karfin in auri wanda maitar so da farautar
nema, ummi tana tsananin so da burin auran dr.
khalifa ,da wani ido xan dubeta in na aureshi,in
banda haka da a yau dinnan xan tabbatar miki da
matsayinku a gareni mama ta hanyar amsar
bukatar dr. khalifa, kiyi hakuri mama ki taimaki
rayuwar ummi ki ceto zuciyarta daga halin datake
ciki ta hanyar sa khalifa ya aureta, mama kin zo
gdan nan ne nasan sbda ttausayn sa di kikeji da
gudun fadawarsa wani hali idan bai samu yadda
yake so ba, mama to kisani ummi ta fidr. khalifa
kuncin zuciya don shi a cikin kwanaki kalilan yake
fama da ta shi damuwar yayin da ita tadade tana
fama da damuwa, akwai daran datake kwana
kuka akwai ranakun da ko abinci ba ta iya ci,
,kullum ciwon rai ke damunta akan dr. khalifa, in
dai akwai abin tausayi ta fannin soyayya to ummi
ce, kiyi hakuri mama kituno hadisin manzon
rahama (SAW) da yace imanin dayanku ba ya
cika har sai ya kasance yana sowa dan uwansa
abinda yake sowa kansa.
A DAREN FARKO
21
A cikin uwar dakin mama ita da anty sadiya ne ke
zaune suna fama da magana daya dai dataki
karewa, khalifa yashigo fuskarsa ba walwala
yazauna kan stool yana fuskantar mama yace
"gani"
Tace "khalifa don Allah kayi hakuri da batun
fatima ba za ta amince da batun auranka batunda
dai har nataka kafata har ckin gdansu na roki
alfarmarta bata amince ba, karshe ma tashiga
kawo min wa'azi wai yadda naji tausayinka a
matsayinka na da na har nake fafutukar ganin ka
samu abun da kake bukata to itama ummi in
tausaya mata in taimaketa ta aureka.
Khalifa yaja dogon numfashi yace "wlh mama ni
ma bansan abunda ke damuna ba, na kasa hakuri
da yarinyar nan wani irin abu nake ji a cikin
zuciyata kamar idan ban samu auranta ba
mutuwa zanyi, ina jinjina wannan yanayi danake
cki mama, a ni kaina ba na ra'ayin auran zumunci
ba zan auri ummi ba, fatima kuma yanzu nafara
sonta ki ci gaba da kokarin taimakona da addu'a
da duk abinda za ki iya mama.
Wayarsatafara ringing yatashi yafita, mama taja
tsaki tadubi sadiya tace "to yanzu me za muyi,
nikam ban san abinda za a zarge ni da son
zuciya, ba na son in ja wa kaina zagi.
Sadiya tace "kidaina damuwa mama in fa fati
matar khalifa ce sai ya aureta, dole muci gaba da
jan ra'ayin fatima tunda ita yakeso itace farin
ckinsa.
Bayan dr. khalifa yagama wayar da aka kira shi
dakin ummi yanufa tana zaune tana duba wani
littafi, ta amsa mai sallama cikin fara'a, yazauna
gefen kujerar dake gaban madubi ya amsa
gaisuwar tayi masa yace "ina fatima?
Tana gdansu.
Ya gyada kai "ummi"
Ta amsa "na'am yaya khalifa.
"Ba ki da wata hanya daza ki iya ja min ra'ayin
fatima, ina sonta dayawa fa.
Ba karamin namijin kokari ummi tayi ba gun
shanye damuwarta da tsananin kishi? ta tace
"yaya khalifa tunda dai kana son fatima zan
taim*e ka kasameta, ko ba komi dai na godewa
Allah dayasa kakejin irin abinda masoya keji a
zuciyarsu yayin dasuka rasa masoyansu.
Bata jira abinda zaice ba tamike tace "bari ma
inje in zo maka da fatin.
Ya bita da ido har tafita, ya ji ciwon maganar
data fada masa na karshe amma babu yadda
zaiyi soyayyar fatima ce taja masa, in bar da
haka har ummi ce ta isa tagaya mai magana,
yaja tsaki yayi tagumi.
dr. bashir ne ke dada karfaf masa lallai yanemi
taimakon ummi maganarta na da tasiri sosai a
gu? fatima kada yadamu da abinda zaiji yagani
domin duk abinda kake neman nasara a kansa
sai ka yi hakuri, ba abi? da yatsana irin raini,
Allah yasa ba alhakin 'yammatan daya wahalar
ke bibiyarsa ba.
Yana ckin wannan tunanin fatima da unmi suka
shigo dakin idanunsa akan fatima yaji wani irin
sanyi a ransa kamar yatashi yarungumeta nan
take yakara sallamawa al'amari ummi a gun
fatima, bai dada tabatar da haka ba sai da fatin
tarusuna ta gayar dashi tace "ga ni yaya khalifa.
Ummi tace "yawwa nikam na gama aikina, ke
fatima kinsan dai yaya khalifa yayanmu ne.
Ta gyada kai tace "na gane anty ummi.
Bayan fitar ummi, dr. khalifa yakamo hannun
fatima ya mikar da ita tsaye ya kura mata
kyawawan idanuwansa masu laushi da daukar
hankali, nan take yafara jefa mata wani bakon
al'amari a zuciyarta, nan da nan tayi kasa
dakanta tana jan numfashi dakyar, lamarin
dayasa takasa cigaba da tsayawa ta janye
hannunta ta zauna, yazauna daf da ita yace
"haba fatima dago idonki kidube ni mana, wai
meye aibuna da ba kya son kallona?
Ta maraice murya tace "don Allah yaya khalifa
kaji tausayin ummi ka amsa soyayyarta tana
sonka dayawa, kayi hakurin fiddani daga
zuciyarka, an riga an ba da ni kwanaki kadan
suke rage nazamo matar wani....
Yasa hannu yatoshe mata baki yace "in kina son
in a; hi batunki dago ki kalli kwayan idanuna.
Ba ta son kallon idonsa sbda idon na sa daban
yake dana sauran maza, amma bukatarta datake
son tabiya yasa dole tawatsar da abinda takeji
tawarware idonta ta dubeshi, ya lumshe ido yana
mata kyakyawan murmushi, tamaida kanta kasa
yace "fatima idan fa kina son in yi miki yadda
kike so sai dai kiyi ta kallona har sai na ce
kidaina.
Tun fatima na zamewa kallon na sa har tafara
rikicewa domin wani irin yanayi tafara ji a jikinta
wanda bata taba jinsa ba, yakara matsowa daf da
ita yasa hannayensa biyu yadafa kafadarta, "wlh
ina sonki fatima inajin kihar ckin jijiyoyin jikina
don Allah fati kada kibari kirasa ni kada kibari in
rasaki, fati duk wanda yayi ceton rai...
Yakasa cigaba da maganar sakamakon wasu
siraran hawaye dasuka shiga zubo masa, lamarin
dayasa fati tarude tana fadin "meye abin kuka
khalifa ?
Yace "ke ce bakiga abin kuka ba.
Yasaketa yamike, tamike itama tatsaya a
gabansa takasa magana, sun jima a haka daga
bisani yafice daga dakin yana cigaba da sharar
hawayensa, yawuce mama a falo yafita, gabanta
na faduwa sbda ta ga yanayin daya fito nan take
tsoro ya mamaye zuciyarta.
A cikin dakin fatima sororo a tsaye tana tunanin
khalifa, karo nafarko dataji tausayinsa ya kamata,
ta yaya za tayi da wannan al'amarin, abinda
yatsaya mata a rai shi ne hawayen khalifa da
kyakyawan murmushinsa,dr.khalifa ya zamo
namijin farko dataji lallai tanason taji ta a jikinsa
sbda burgetan da yyi.
Ta kwanta bisa gado tayi luf, a lokacin ne ummi
tashigo dakin da zumudin jin yadda sukai ganin
kwanciyar da fatima tayi da yanayin jikinta yasa
gabanta yafadi sosai.
Ko dai khalifa ya fara wa fati tasiri a zuciya, a
sanyaye tzauna daf da ita muryarta cikin wani
irin yanayi tace "fati yaya akayi naga kin zama
wani iri.
Fati tayi firgigit tamike zaune idnuwanta a waje
tana kallon ummi tace "an samu nasara domin
kuwa ya fara amsa min zai min duk abinda nake
bukata.
Ummi tayi ajiyar zuciya "fatima lallai idan kika
ceci zuciyata daga halin da take ciki kin yi
taimako.
Tadafa kafadarta tace "ba komai kidaina yawan
damuwa.
******
Tsakiyar dare ummi takira jidda dake londn ta
fayyace mata abubuwan dake faruwa, jiddah tace
"Dr. khalifa na son fatim
Tace "kwarai kuwa jiddah soyayya kuma ba gama
garin soyayya ba original one, domin kuwa tunda
yadora idonsa a kanta gaba daya ya rikice ya
rasa sukuni, kin san dai yadda khalifa ba ya sakar
min fuska ko ?
To a halin yanzu sbda in masa kamfen a gun
fatima za kiyi mamakin yadda yake ja na a jiki ko
kunyata ba ya ji.
Jidda tayi ajiyar zuciya tace "anya kuwa umi ko
dai dr. khalifa tsammani yake son wasa kike
masa.
Tace "haba jiddah wani irin wasa kuma, da dai
ace mun saba wasa ni dashi to zaiyi tunanin
haka, mutumin da bai min ko kallon arziki za kiyi
mamakin yadda yasauya akan son fatima abin
har tsoro yake ba ni jiddh.
Ta jinjina kai tace "to yanzu wani mataki kika
dauka akansu ? ko kin hakura dashi ?
In hakura jiddah ?
Tabdijam ai idan kika ga na hakura da khalifa to
numfashin karshe nayi a duniya, ma'ana
rayuwata ta kare amma idan ba haka ba matukar
ina numfashi ba zan hakura da doctor ba.
Jiddah tace "to ummi ta wce hanyar za ki
mallakeshi bayan kin san ko da akewa maza
auran dole a wani lokaci ba za ayiwa dr. khalifa
ba.
Tunda kinfi kowa sanin cewa mahaifinsa yana
fifita shi akan komi yana kara akan komi banda
khalifa.
Ummi tace "eh nima bance za ayi mai auran dole
ba kawai dai ba zan bar ma wata shi ba.
Jiddah tace "ko da fatiman ta ki ta aura ?
Tace "wannan ne abinda yafi daga min hankali
ban so yakasance dr. khalifa fatima yake so ba
sbda kaunar da nakewa fatima ba na son wani
abu na bacin rai ya sameta, in da nake dan
samun natsuwar zucia shi ne fatima ba son dr.
khalifa rtake va, bayan kasancewar saura
kwanaki kadan a daura auranta, fatima tanada
burin biyayya ga iyayanta shi yasa bata kula
kowanne da namiji, wannan yanuna kwanciyar
hankali.
A DAREN FARKO
22
Gaban abban yafadi ras yayi wa dr. khalifa wani
irin kallo yace "ai an kusan bikinta da musbahu.
Yace "na sani abba ai aaure nufi ne na Allah idan
matata ce sai kaga....
Ya katse shi yace "kai khalifa wannan abu ne da
ba xai yiwu ba nima na so auranka da fatima
domin yarinya ce mai hankali da sanin ya
kamata,to amma ta ina xanje in ce a fasa ba
musbahu aure a ba ka, gskiya sai dai kayi hakuri
Allah yabaka wata.
To shima khalifan ya san abun da nauyi soyayyar
dayake mata ne yasa yarufe idonsa yakeso ya
mallaketa kota wani hali, bai ka ra cewa ko ; i ba,
abba ya bishi da ido jikinsa gaba daya yai sanyi
ba ya son dan na sa yanemi wani abu yarasa a
rayuwarsa.
Nan da nan yanayin abba ya sauya ganin
damuwar da ke tare da khalifa, yamike yashiga
dakin mama, tamike dasauri daga kwanciyar da
tayi tace "daman ka fito Alhaji ?
Fuskarsa ba walwala yace "na fito, khalifa ne
yazo min da maganar data dagan hankali.
Mama tace "uhm Allah yasa ba maganar fatima
yakawo maka ba",.
Ya dada bata rai yace "af daman kinsan da
zancen baki fada min ba ?
Mama tace "to Alhaji idan na fada maka me za
kayi !? abinda zai yiwu ahi ake, ta yaya khalifa
zai samu auran fatima idan kuwa ba zai samu ba
meye amfanin tattauna maganar.
Alhaji yazauna gefen gado yana fadin "to haka za
mubarshi a ckin damuwa hajiya ? gaskiya ba zai
yiwu ba.
Mamaki yakama mama ganin yadda abba ke
neman rufe ido kiri kiri yayi son kai, tace "alhaji
gskiya sai dai hakuri domin ni da kaina naroki
yarinyar tanuna min gskiya ba zai yiwu ba,ni
abinda ke hadani da Khalifa shi ne idan yakallafa
ransa kan son abu ba zai iya hakura yabi abin a
hankali ba, sai dai ydga hankalinsa yadaga wa
wani hankali.
Abba yace "ba dole yadaga hankali ba, in bai
gaya mana damuwarsa ba wa zai gayawa, kin
san zafin soyayya kuwa ?
Tace "hakane ban sani basai ka nema mai auran
nasan dai sai da amincewar yarinyar da iyayanta
za ayi ko ?
Abba yace "Gaskiya ba zan bar yaron ckin
damuwa ba, dole in bi duk hanyar dazan bi don
ganin na samar mai dafarin ciki a rayuwarsa.
Yajuya yafita yayin da mama tabishi da kallo cike
da takaicin yadda abba ba ya son nunwa Khalifa
yadda rayuwa take.
****
Fatima ce zaune a runfar innarta ta yi tagumi ta
kasa cin abincin dake gabanta, innar tana dakin
malam, sauran kannanta duk sun tafi makaranta,
musbahu yashigo da sallamarsa, tadaga ido ckin
ladabi ta amsa muryarta a sanyaye tace "ina
kwana.
Idanuwan daya kafa mata yasa tayi kasada kanta
yazauna kusa da ita yace, "fatima a kwana biyun
nan kin sauya kamar ba ki da lfya sai ramewa
kike ko dai fargabar auran ne ?
Ya fada yana dan murmushi a kokarinsa na
kwantar mata da hankali, itama murmushin tayi
tace "lafiya kalau.
Yajawo abincin gabanta yafara ci yana fadin "kai
abincin nan yayi dadi da yawa na san ke kikayi.
Bata ce komi ba, yaci gaba "gaskiya fatima Allah
ya yi miki baiwa da yawa shi yasa zuciyata ke
kara sonki don Allah nima ki soni kuma kidinga
tausaya min wahala zan sha idan nasamu sauyi
daga gareki.
Anan ma shiru tayi masa don bata san abinda za
tace dashi ba, wani iri takeji a jikinta ko kallonsa
ba ta iya yi, yace "ftima don Allah kiyi min
magana ko zanji dadi mana kin san ina sonki.
Fatima bansan abinda zai same ni ba hakanan
nake jin zuciyata tana cik e da fargaba idan
nakwanta bacci kuma sai in ta mafarkai barkatai
marasa dadi wanda yafi daga min hankali shi ne
wanda nayi yau da asuba wai wani ya kwace min
ke ta karfin tsiya, shi ne jikina duk yakara sanyi.
Ga mamakin ta sai taji hawaye ya taru a idonta,
tatashi dasauri tashige daki tace dashi "ina zuwa
.
Misbahu yabita da kallo har yagaji dazama
yatashi bata dawo ba bai san meke faruw aba
baiyi tunanin binta ckin dakin ba yafice daga
gdan.
Itama inna data shigo dakin kallon mamaki tabita
dashi ganin yadda take saharar kwalla tace "lfya
fatima?
Tace "ba komi inna
Ba komi kike kuka?
Takasa magana domin itama batasan dalilin
kukan na ta ba ballantana ta bayyanawa inna,
inna ta jima a tsaye tana kallonta daga bisani
tadaga kai tafita .
Wayar fatima tafara ringing tadauko ta bakuwar
lamba ce, tadaga tare da sallama, daga can
bangaran aka amsa mata "Khalifa ne.
Gabanta yafadi "ko baki fahimci khalifan bane?
"Na fahimta.
"To ai na ji kinyi shiru.
Tace!"bansan abinda zan ce bane.
Yayi dariya "za kisani yanzu kuwa, so nake kizo
mugaisa tun da natashi idanuwa na ke son
ganinki zuciyata na azalzala min da yawa don
Allah kidaure ki zo.
Tace "haba khalifa meye ma'anar zuwana
gareka? me ganin zai haifar maka, me yasa kke
mantawa na kusa zama matar wani ne....
Ya katse ta.
Don Allah kidaina gayamin wannan maganar ki
daure ki zo muyi wa kanmu maslaha.
Shi knan a ina zan sameka?
'Yawwa tawan ina kofar gdanmu ckin mota ta.
Hijabi tasa wanda yazo har kafafunta ydda
idanunta ke kode sunyi ja haka tafita bayan ta
shaidawa innarta cewa za ta gun ummi..
Ta wuce musbahu a kofar gda tare da wani
abokinsa mai suna Aminu, khalifa yana hangota
ya bude mata kofar motar tarike kofar tana kallon
sa tace "idan na shiga mota ina zamu? ko a cikin
motr za muyi magana?
Yace "inaso kiyi min rakiya wani wuri. ne ba nisa.
Ta waiwaya tadubi musbahu ita yakafawa ido, ta
dawo da idon ta kan khalifa tace "kn ganin hakan
y dce?
"Eh ya dace mana kowa ya sanba na satar
mutane, Fatima maslaha muke nemawa kanmu
ina bukata kema haka in haka ne ki shigo mutafi.
Bbu abinda ummi ke kallo sai rayuwar ummi
wannan ce damar da zatayi amfani dan tallafawa
ummi, sai ta zuke fargabarta tshga motar tarufo.
.
Ta gabansu musbahu, kbalifa yawuce idon ta ckin
na musbahu taji gabanta ya fadi an ya ta yi dai
dai kuwa.
Gdan dr. bashir yanufa da fatima, matar dr. bashi
ta asheta hannu biyu zuwa falonta takawo musu
abinci da shayi, dr. khalifa yahada tea yafara sha,
dr bashir ya harare shi "wato haka Za kadinga
son kai ko ita amaryar fa.
Don Allah ku rufa min asiri ina tare da matsaloli
ko yanzun ma na biyo shi ne domin in fahimtar
dashi.
Farida tahada mata shayin taja hannunta zuwa
ckin daki tace "fatima don Allah dagaske ba kya
son Khalifa?
Fatima tawaro ido tace "me son na shi xai
amfana min, a rayuwata bbu abin da na tsana irin
in yi abu in dawo ina nadama.
Farida tace 'dr khalifa yadaga hnkli akan tsananin
sonki, da za ki amsa soyayyarsa xa ki mori
rayuwar aure, irin su tsada garesu.
Fatima tace kin san kyaun mijin daxan aura da
halayansa? an masa adalci in nabarshi na auri
Khalifa? aminiyata na tsananin son khalifa ya
kamata in watsar da batunta in aure shi? abinda
khalifa ke nunawa fa son kai ne kuma ba dabi'ar
musulmin kwarai bane, ya kamata kidnga fadwa
Khalifa wadannan, don ydinga sa hkuri a
zuciyarsa a rayuwa ba komi mutum ke so yake
samu ba.
Farida tarasa abin da xa tace sbda hujjojin fati
sun daure mata jijiyo tamike tadawo falo tace da
Khalifa da wuya fati ta amince yahakura kawai.
Khalifa yace kai ba zai yiwu ba turo min ita, ban
taba neman abu na rasa ba ba xan fara akan
fatima ba, fatima ba ta ckin matan da za a iya
hakuri dasu.
****
Tun daga ganin yanayin fuskarsa ta san ba lfya,
bayan sun gaisa ta tambayeshi "yace "ummi don
Allah ko kin san wani abu tsakanin ummi da
khalifa?
Tace "wani abu kagani?
Yace "kwana biyun nan na fahimci wani abu na
damunta ta ce min ba komi, daxun kuma naga ya
dauketa sun fita a motarsa, na kira wayarta bata
daga ba.
Ummi ta fiddo ido "fatiman? yace itafa abin ne
nima yabani mamaki da yawa shiyasa nakasa
aurewa sai sun dawo nazo inji ta bakinki na san
kin san komi.
Ummi tayi shiru kanta na kasa ".
Lamarin daya dada firgita musbahu gabansa
yashiga faduwa yashiga rokonta da Annabinsa in
ta san wani abun kada taboye masa.....
A DAREN FARKO.
23
Dr. khalifa yaci gaba da cusawa fatima
maganganu a cikin kunnuwanta, suka dinga ratsa
mata zuciya ga hgangar jikinta, lamarin daya sa
ta kuma jin tsigar jiki? ta tana tashi tarabu da
marsh war zuciyarta ,lokacin da dr. Khalifa ya
fahimci ya yi ntasirin jan hankalinta sai ya saketa
ya zaunar da ita gefen gadon yazauna a kasa.
yace "fatima kiyarda in zama mijinki zan shayar
dake zumar soyayya, zan dandana miki wata
rayuwa wadda mafarkin ki bata taba ba ki ba, duk
wani jin dadi da kwanciyar hankali da diya mace
take fatan samu a gdan mijinta zan ba ki shi ba
dan komi ba sai don ina sonki, ni kaina na san
zuciyata tana sonki ba zanyi wasa da duka
abinda yshafe ki ba.
Abinda ke tafiyar da fatima shi ne son kallon
fuskar Khalifa da idanuwanta ke nacin yi, idan
kuma takalle shin sai taji wani irin abu nai mata
yawo a cikin zuciya d jiki, ckin kasalalliyar murya
tace "wai don Allah ya kakeson in yi da
matsallina ? yaya xanyi da musbahu da ummi.
Yaja tsaki yace '"don Alah ki ce kin amince dani
kina sona za ki aureni, musbahu na san yadda
zanyi dashi, unmi kuwakadaki kara min
maganarta tunda nace ba na sonta ban sonta ba
zan auri matar da ba na so ba.
Tace" amma docter ya dace katausaya mata
yadda kake son kaima. a tausaya maka yadda
kake kokawa a bisa soyayyar dakake min tana
wahal ma da zuciya, kowa fa yataimake wani
Allah zai taimaka masa.
Ya dan harare ta yana murmushi.
"To na ji sarkin iya wa'azi.
Takara langabe kai "to baka ce komi ba.
Yace "to wai so kike in hakura dake in auri ummi
,ko kuwa in aure ku tare.
Yana tsaye ne kyam a gabanta, kai wannn bawan
Allah dakyau yake Allah ya yi halitta anan, ta
hadiyi yawu tace"ni dai ina so ka aureta.
Yace "to baki amsa ba in hakura dake ko in
aureku tare ?ki je kiyi tunani ki zo min da amsa
nan da gobe tashi mutafi gida.
A hanyarsu ta komawa gda yatsaya a wani
makeken super market yadinga zabar mata kayan
kwalliya masu tsadar tsiya da burgewa sannan
yajuya kan ciye ciye da na masarufi sai daya
jibgesu a kujerar baya tana kallonsa.
Wannan karon ma musbahu yana zaune shi kadai
a kofar gidansu fatima kan benci, khalifa yayi
parking, sakinbaki yayi yana kallonsu har suka
fito tashige cikin gida dasauri yayin da khalifa
yashiga kwasar kayan da zai iya, yakira wasu
yara suka dinga deban buhunhunan shinkafa da
kwalaye suna shiga dasu, duk wani abu na
kurewar jin dadi a fannin ci da sha khalifa ya siye
shi ba kadan ba.
Inna tana tsaye a tsakar gida tana kallon ikon
Allh ana ta jibge kayn tatmbayi yaran sukace
khalifa ne yace a kawo.
Fatima kam daki tashige, xuwa chan dr. khalifan
yashigo inna takarbe shi da fara'a zuwa rumfarta
"duk dawainiyar da ke damu bata isa ba si anyi
wata.
Yace "don Allah kar ku damu inna ni dai fatana a
yi mana addu'a.
Tace "addu'a kam dare da rana bata yankewa
daga bakinmu, Allah yai muku albarka, Allah yara
ba ku da duniya lafiya,Allah yaraba ku da sharrin
makiya da mahassada.
Khalifa yadinga fadin "amin amin inna ngd.
Yana son magana ya kasa bayyana wa inna abi?
dake tafe dashi ya dan jima zaune shiru daga
bisani yayi mata ama yafice daga gdan.
Malam misbahu yavishi da kallo zuciyarsa ckin
matsanancin kishi da kunci, me khalifa da fatima
ke nufi dashi ? saura kwana takwas kachal
yarage a daura musu aure amma yana jan fatima
a mota yana fita da ita a mota, ba Khalifa ne abin
mamaki ba fatin ce, kowa ya san ta da kyawawan
dabi "u ya za ayi akan khalifa tasauya lokaci
daya haka ?
Yatuna yadda sukayi da ummin dazu a gdansu
Khalifa lkcn da yayi ta rokon ta da Allah tafdi
masa abinda tasani game da mu'amalar fati da
Khalifa ,ya hadata da girman Allah akan kada
taboye masa gskiar abinda tsani.
Ummi dakyar ta iya rike kanta a lokacin itama ta
kanta take ji ta fi musbahu shiga tashin hankali,
jin cewa wai dr. khalifa da fati sun fita a mota ina
za su ? meye dalilin fitar ta su ? da wace manufa
fati tabishi ? shin ta bi shi ne dan taci gaba da
jan ra'ayinsa akan yaso ita ummin ko Khalifa ya
ja ra'ayin fatin ne ta fara son shi ? abubuwa da
dama suka dawo mata game da yanayin jikin
Fatima dake sanyi a duk lkcn da suka kebeda
Khalifa idanuwan ta sukan yi jawur me yakawo.
haka, itama lallai tana bukatar wadannan
tambayoyin da gaggawa.
Wannan tunanin ne yahana ummi magana ga
musbhu ya tsareta da ido hnkalinsa a tashe yana
ckin fargaba, da. kyar ta iya bude baki tace mishi
"kayi hakuri fatin tadawo zanji ta bakinta.
Kina nufin baki san komj ba ?
Kadafa ki manta na hadaki ne da girman Allah.
Tace "ban ce maka ban sani ba kayi hakuri akwai
wasu bayanai danake son tattarawa xan gaya ma
gskiyar dana sani amma ba yanzu ba.
Dakuar ummi ta lallabashi yahakura yatafi, tunda
yadawo gida yakasa zaune yakasa tsaye,
tunaninsa me fati da khalifa suka fita yi a mota?
kuma fatin tana ganin shi a tsaye ko kunyarsa
bataji ba suka wuce meye hadin ta da khalifa?
har zaiyi wa inna maganar yaga bai dace ba, shi
ne fa tun da yafito waje yazauna bai iya tashi ba
har su fati suka dawo, ganin dukiyar da ake shiga
da ita gdan yakara rudewa, ga fati ta wuce ko
sannu batayi masa ba yadinga fadin "Lahaula
wala kuwwata illa billahil azim.
Babu tunanin da bai yi ba a wannan lokacin
hnkalin sa ya tashi sosai.
A DAREN FARKO
24
A rikice ummi tashiga gdansu tazube a gaban
hajiyarta hauwa tana shaida mata cewa ga
dukkan alamu fatima za ta ba wa khalifa hadin
kai, ra'ayinta ya fara karkata gare shi.
Hajiya tace "to ai dama ke ce kika yarda da ita,
fatima karya take tace za taki khalifa akan
wannan musbahun, wa yaki dadi? ballantana
daula irin ta gdansu khalifa ga shi dan gata, ke ce
baki da wayo yaudararki kawai take tana gaya
miki cewa za ta taimake ki yasoki, soyayyarsu
suke yi, dan kada kijuya mata baya ne take miki
haka, kinga dai ke ce kika wayar wa da fati kai
amma tafi ki wayon, iya zaman duniya da
mutanan ckinta.
Ummi ta jinjina kai tare da cije lebe tace "Amma
lallai fatima ta tafka babban kuskure idan har ya
tabbata yaudara ta tayi bata yaudareni ba kanta
ta yaudara, do min kuwa sai na nuna mata cewa
duk wanda yariga ka bacci sai ya rigaka tashi ba
zan barta ta mallaki khalifa ba, domin ban cancan
ci yaudara a gun fatima ba.
Hajiya tace "to ki dai san abin yi bai dace wannan
wahalar damuke sha yatashi a banza ba.
Tace "karku damu in dai ban samu khalifa ba to
na hakura dashi to bbu wacce za tasame shi ko
zan rasa raina na amince akan khalifa.
Ta fiddowa hajiya guzurin kayan data yi musu
itama tace abban khalifa ya aiko mata da kudin
don haka suka yiwa gdan malam tsinke da
tsakiyar rana.
Hajiya ta jadadda masa cewa ayi wa khalifa aikin
da uwarsa ma bata isa dashi ba sai ummi, tace
"malam muna so mu mallake shi shi da dukiyar
tasa gaba daya data uban.
Malam yayi dariya yace "ai kar ku damu tunda
kuka kawo wadannan abubuwan ai an gama. ku
sa ido za kuga yadda khalifa zai zamo a
hannunku.
****
Kwance take laga laga tana cike da tsananin
shaukin jikin dr. khalifa da son jin muryarsa,komi
na ta ya suaya fatima ta tsinci kanta a wani irin
sabon yanayi na bukatar rayuwa,tunda take
rayuwa a duniya bata taba jin abinda taji yau ba
game da Khalifa,, kamshin sa har yanzu yana tare
da jikinta, kyakyawar surarsa tadinga gani a
idonta, ta hasko mijin da za ta aura rana ita yau
musbahu, nan take taji ta tsane shi, daman bata
taba jin tana son shi ba biyayya biyayya ce
kawai.
Lallai a yau ta fuskanci meye so, don kuwa ta
samu kanta cikin irin yanayin da ummi ke
bayyana mata tana shiga a kan soyayyar khalifa.
khalifa kam ya isa miji abin so da burgewa .
Tamike zaune tazuba tagumi shin yaya za tayi da
musbahu da ummi, ko shakka ba ta yi a halin
yanzu tana son Khalifa kuma shi za ta aura,
musbahu da ummi fa? mutane ne masu kima da
daraja a idonta me za tace dasu?
Duk bata san inna ta dade tsaye a kanta ba sai
data yi mata tsawa tadago da sauri ta dubeta, a
fusace inna ta tsare ta da ido tace "tunanin uban
wa kike tun dazu nake tsaye akan ki ina magana?
Fati tayi shiru takasa magana, inna ta jinjina kai
tace "tabdijam amma kina da jan aiki fatima, da
can wani namiji bai ja ra'ayinki ba sai yanzu, yau
din nan fa za a fara rabon goron bikinki, to
karkace kunnuwanki da kyau kiji idan ma son
khalifa kike to kishiga taitayinki, kisan abinda
kike, kinsan dai mu ba kwadayayyu bane duk
abinda iyayan khalifa suka mana mun gode ba za
muce bamu gode ba amma dai ba rokonsu
mukayi ba ba za mu kai kammu inda Allah bai kai
mu ba, dan mu tsira da mutumcin mu, ni kaina na
gamsu duk abubuwan da iyayan Khalifa ke mana
sunyi ne don Allah to amma mutanan dake
gefenmu kallon kwadayi suke mana, kin ga dai su
suka ja mu a jiki amma yanzu da zarar an ji wata
magana ta fito fassarar kwadayin nan za a yi
mana, sbda haka kisan abinda kike kada ki soma
daukar dabi'ar da ba ta ki ba ki sa wa ranki
wahala, kitsaya a matsayin da Allah ya ajiye ki
sai ki zauna lafiya.
Bayan fitar inna, fati tayi shiru tana tunanin
maganganun inna, wadanda akan hanya da
gaskiya suke, sai dai kash zuciyarta ta kamu da
soyayya farat daya hankalin ta da tunanin ta sun
dawo kan Khalifa, tana jin sa a ko ina a jikinta.
****
Ummi da hajiyarta da hajiya saude sun dawo gida
zuciyarsu cike da tabbacin abinda malam yagaya
musu zai auku har tadinga jin kamar ma ta
mallaki khalifan ne, sai fatima ce dai a ranta ita
ke daga mata hankali.
Takira jiddah a waya ta gaya mata abinda ke
cigaba da faruwa.
Jiddah tace "ummi in tambayeki mana"
Tace "Allah yasa na sani.
Tace "wai shin dama a baya khalifa bai taba wata
budurwa ba sai fatima? mesa za ki daga hankalin
ki haka akan fatima? bayan kina sane da cewa
duk inda yake "yammata natare dashi.
Ummi tace "ke jiddah tsaya kiji duk wata 'ya
mace dake tare dashi ita ke nace masa bai damu
dasu ba fatima kuwa shi yake sonta, tarihin
rayuwarsa ba macen daya ke nunawa zai shiga
kowani irin hali a k anta sai fatima, wannan
al'amari yana matukar daga min hankali da ba ni
tsoro jiddah.
Jiddah tace "kai wani irin soyayya ce wannan? ko
da yake fatin da khalifa duka ababen so ne,
hakika ba abin mamaki bane dan namiji ya shiga
kowani irin hali akan fatima, wannan yarinyar
Allah ya hore mata kyau me shiga zuci, sannan
khalifa Allah ya hore masa kyau na daukar
hankali, fatima za ta iya kamuwa da son khalifa
haka Khalifa zai iya kamuwa da son fatima fiye
da duk yadda kike kwatantawa, amma shawar da
zan ba ki itace kiyi hakuri kiyi hakuri idan
Allahyakaddara fatima matar khalifa ce kiyi hakuri
kiyi hakuri Allah yabaki wanda za kifi so fiye da
son da kikewa dr. Khalifa.
Tace "jiddah idan nahakura ya ya zanyi da son
danake wa dr. khalifa?
Tace "ummi tun a fari ni ce na sa ki a hanyar ki
so khalifa, amma hakan bai hana a yanzu in ba ki
shawarar kiyi hakuri da Khalifa ba sbda maslahar
zuciyarki, ummi yanada kyau kisani duk abinda
Allah bai kaddara makasamunshi ba ba za kataba
samun na sa ba har abada sbda Allah ya kaddara
ba rabonka bane, kitsaya akan wannan don ki
zauna lfya.
Ko kusa shawarar jiddah bata samu karbuwa a
zuciyar ummi ba, domin abu ne da ba zai taba
yiwuwa ba, ji take har gwamma ta sallamawa
wata khalifa in da za ta iya yin hakan akan ta
sallamawa fati.
Su hajiya ma sun tsaya tsayin daka akan sai
ummi ta mallaki dr. Khalifa ko da yake su
dukiyarsa kadai suke kwadayi.
Dab da sallar magriba ummi ta iso gdansu
khalifa, ta iske shi suna alwala tare da dr.bashir
,ta tsaya suka gaisa abin mamaki fara'a ce
karara a fuskar khalifa yana fadin "yawwa
kanwata daman ina son ganinki, bari in dawo
daga masallaci.
Ta shige gida cike da zargi iri iri a zuciyafmrta,
musamman ganin yadda fatima tadaina neman ta
ko da a waya ne, tabdijam ckin dakin mama
tafara shiga ta iske ta ta tayar da sallah ita
dayake ba sallar za tayi bata watsar da jakarta
da mayafinta tazauna gefen gado tayi tagumi.
Mama ta idar da sallah tazuba mata ido tace "sai
yanzu ?
Ta sauko kasa suka gaisa tace "mama yaushe
rabon fatima da gdan nan ?
Tayi murmushi tace "ai fatima ta dauke kafarta
daga gdan nan ne sbda mun zamo surukanta.
Tace "kamar yaya mama ?
Tace "uhm kina nufin baki san meke faruwa ba ?
Tace "mama idan ma na sani ina bukatar karin
bayani daga gareki.
Mama tace "ummin hankalina a tashe yake domin
abbanku ya goyi bayan son zuciyar da khalifa
yazo dashi karara bayan ya san hakan bai
cancanta ba.
Bakin ummi na rawa tace "mama kina nufin abba
ya goya ma khalifa baya ya auri fatima.
Tace "wannan shi ne damuwata. ina tsoron kallon
da mutane za suyi mana musamman kasancewar
musbahu talaka khalifa me kudi abin da kowa zai
ce shi ne anyi amfani da dukiya gun dannewa
musbahu hakki don ba shi da dukiya, ya kamata
abba ya takawa Khalifa burki yanunamasa jan ido
tunda ba shi za ya daurawa kansa auran ba, dole
yahakura amma ya ce ba xai hana shi yin abinda
ba ya so ba ina jiyewa khalifa rayuwar da abba
yasa shi bai san bbu ba bai san yanemi abu
yarasa ba sai dai duk abinda yanema sai ya
samu, wace irin rayuwa ce wannan ? idan khalifa
bi san rayuwa ba yanzu sai yaushe zai sani ?
Cikin nauyin baki da takaici ummi tace "mama to
ke kin amince ?
Ta amsa "to yaya zanyi ummi ? ina da ikon yiwa
abba musu akan wani abu daya tsara akan
khalifa ?
Ummi tajinjina kai a zuciyarta tace "gaba
dayanku kunyi kuskure wato cikinku babu wanda
yadamu da damuwata sai damuwar danku ?
Hakika son zuciyarku da kanku ya zame muku
damuwa daman ance son zuciya bacin ta.
Tabude baki za tayi magana wayarta tafara
ringing, khalifa ne tadaga yace da ita "taho mana
da abinci mana dakina.
Ta tambayi mama abincin na su tace yana kan
tebur.
Wani iri ummi take jin zuciyarta kamar ba ita ba,
tadauki abincin tanufi dakin na sa, bayan ta
zauna Khalifa yace "ina kawar ta ki ?
Tace "fatima.
Yace "eh.
Tace "ai ina zaton a halin yanzu ka fini sanin inda
take tunda ka fi ni kusa da ita.
Yace "um um ummi ba haka bane kina da
matsayi babba a gun fatima koyaushe tana
maganarki da kokarin ganin ta nema miki mafitar
da za ta haifar maki da kwanciyar hankali,kada
wani abu yarufe miki zuciya ki zargeta da abinda
bai dace ki zarge ta dashi ba.
Gaba daya taji takaici da bakin ciki sun kara
rufeta maganganun sa kara mata damuwa suke,
meye amfanin abunda yake fada mata kan ftima,
tamike da niyyar tafita yakira sunanta yace
"zauna.
Takoma ta zauna tana kallon sa yace "ummi ya
zamo dole in miki godiya domin kin taimaka min
akan fatima, zuciyarta ta karkata a gareni ta
amince ta amshi soyayya ta duk da cewa wasu
abubuwan suna firgitata wadanda sune suka
hanata sakin ranta sosai tabani hadin kan daya
dace, ina miki godiya ne ummi sbda kin taka
muhimmiyar rawa akan hakan. Tayi masa wani
irin kallo cike da mamakin abinda yake gaya
mata, ba ta son tayi kuka sbda lokacin kuka ya
wuce gareta, ta dade tana kuka akan khalifa
lokaci ya yi da za ta daina kuka, don da ace
kukan zai mata maganin damuwarta da ya yi
abinda yadace da ita shi ne tanema wa kanta
mafita kawai ko ta wani hali, tadubi khalifa tace
"a takaice daikwalliya ta biya kudin sabulu fatima
ta amince da soyayyar ka ko ?
Ya amsa "eh hakane abu guda daya zuwa biyu ne
damuwarta ke da musbahu tana jinjina yadda za
ku kalleta, shiyasa nakiraki yanzu dan in roke ki
kinunawa fatima ba komi kuma kisaki ranki sosai
da ita kamar yadda kuke rayuwa a baya, yin
hakan ne kawai zaisa ta kwantar da hankalinta
tabani hadin kan danake bukata.
Kai khalifa da wauta yake.
Abinda ummi ke fadi a ranta knan ko da yake
gani yake ya fi karfin komi tabbas khalifa ya
rainata, shi yasa ko wani irin danyar magana sai
ya tareta da ita to kuwa za ta shayar dashi
mamaki daga shi har fatima da iyayansa masu
son zuciya.
A fili kuma dubansa tayi tace "karka damu zanyi
yadda kace.
Yayi murmushi yace "nagode ummi zan miki
kyauta mai ban mamaki".
A DAREN FARKO
25
Tsakiyar dare ummi ta kasa barci tana tuna
abubuwa iri iri ta saka wancan ta kwance, tun
tana ganin auran fati da khalifa ba mi yiwuwa
bane har nesa tafara matsowa kusa, abinda ya
faru da karfe goman daren yau ne yatabbatar
mata da haka.
Wato ta zo za ta shiga dakin mama ta tsinkayi
muryar mama da anty sadiya suna hira da daga
murya soai, anty sadiyance take fadin "to wai
mama idan Allah ne yakaddara fatima matar
khalifa ce fa ? kin san dai babu wanda ya isa ya
shirya wannan al'amarin sai Allah ko ? tunda ita
kanta yarinyar ta amince to meye na damuwa ?
kin san babu yadda za a yi abba ya sauya
ra'ayinsa, kada ki jawo abin da zai zamo na
rigima.
Mama tace "haba sadiya yanzu ko a hankalce
wannan ya yi dai dai, da kunyar son da ummi ke
masa zanji ko da malam musbhu.
Anty sadiya tace "duk ki kwantar da hankalinki ki
kaddara cewa Allah ne yakaddara faruwar hakan
ki toshe kunnuwanki daga duk wani surutun
mutane idan kika biyewa mutane babu wani abun
alherin dazaki kulla a rayuwarki, ki kyaleshi ya
aureta Allah yasa haka shi yafi alheri itama kuma
ummi Allah yabata wani haka shima musbahun.
Abin da ummi taji mama tafada ne takara
tsinkewa da al'amarin cewa tayi "sadiya ni ma na
fi son Khalifa ya auri fatima fiye da kowacce
mace, sbda tarbiyyarta da nagartarta, na san
inaha Allahu za yi alfahari da auranta, Allah yasa
haka shi yafi alheri.
Anty sadiya tace "to Alhajin ya yiwa mahaifin
fatiman magana ? ni na fi son ayi komi a gama
hankalin kowa yakwanta.
Mama tace "eh da magribar dazu ya ce idan
yafita masallaci zaiyi wa malam maganar zan
tambaye shi in ji yadda sukayi, na san dai da
wahala in za su ki.
A hankali ummi taja jikinta tadawo dakinta
zuciyarta na azalzala mata tamkar za tafashe,
tabude wayarta ta binciko wani kyakyawan hoton
khalifa data faki idonsa ta dauke shi bai sani ba
tadauke shi a falo, yana sanye da kananan kaya
dasuka matukar karbar jikinsa, murmushin da
yayi ya dada kayatar da kyaun hoton. wata rana
tazauna tazubawa hoto ido, fatima ta iso kanta
bata sani ba, ta jima tsaye tana kallonta ganin
bata motsa ba fatima tazare wayar tana fadin
"wa ki ke kallo haka ?
Ummi tamike takwanta bisa gado tana dariya
tace "wa kika san zan kalla in banda sahibi na.
Fatima tadubi hoton tace "yayi kyau kam amma
zan ba ki shawara.
Tace "tame fa yar kawata ?
Tace "ummi ina matukar jin tausayinki game da
al'amarin khalifa, kina sonsa da yawa kada ki ja
wa kanki wahala yayin da so ya tsananta a
zuciyarki don Allah ki dinga bi a hankali yadda za
ki iya daukar duk abun da zai faru me dadi ko
akasin haka.
Murmushi ummi tayi tace "hakane fatima amma
za ki iya fada min dalilin dayasa kika min wannan
nasihar ?
Tace "ba wani abu ne yasa nace haka ba illa
la'akari da yanayin khalifa anya wannan zai tsaya
kan mace guda daya ? idan ma bai ce yana so ba
sai ance ana son shi, wata rana idan bai amince
ba watarana zai amince amfanin shawarar dana
ba ki itace idan kin bi komi a hankali sai komi
yazo miki da sauki.
Ummi tace "fatima wai don Allah kina ganin zan
samu dr khalifa.
Tace "ummi wannan lamari ne na Allah babu w ?
da ya isa ya yanke hukunci sai shi, za ki iya
samun sa za ki iya rasa shi, ba komi mutum yake
nema yasamu ba
Ummi ta rausayar da kai tana dan murmushi tace
"fatima don Allah idan ke ce xa kiyi hakuri da
khalifa akan soyayyar danake masa ?
Fatima tayi dariya sosai tace "ummi kin ganni
nan wallahi har yanzu ban san meye so ba.
Ummi tafiddo ido "fati wace irin magana ce kike
haka ? meye matsayin musbahu a gunki knan
idan dai baki san meye so ba. ?
Fati ta tabe baki tace "musbahu zabin iyayena
na, ba na fatan ganin ranar da zan sabawa
umurnin su, shi yasa na tallafe shi hannu bibbiyu
kuma na yi damarar rike shi da kyau in dai batun
so za ayi to ban san me akeyi idan ana son
mutum ba.
Ummi tace 'Don Allah dr. khalifa ya taba birgeki ?
Tayi mata wani irin kallo tace "ni dai na yarda
har zuciyata khalifa ya isa namijin da za a so shi,
ko da nace bn san so ba, na san cikakken namijin
kuma na san namijin dazan kalla in ce ya hadu,
shi yasa ba ni ganin laifinki don kina damuwa da
khalifa face ina jan hankalinki don ki dauki komi
dasauki...
Ummi ta buga kwafa, lallai ba abin mamaki bane
don fatima ta amince ta amshi soyayyar khalifa,
sai dai ita tana tausaya mata don ba karamin
kuskure tayi ba.
A DAREN FARKO
26
Ba karamin tashin hankali inna tayi ba lokacin da
fatima da kanta ta zauna tana yi mata wani
mamaki wanda yabata mamaki, kallon fatin take
kamar ba ita ba, tun tana fada har ta dawo yi
mata nasiha amma fati ta murje idanunta kukan
da take ma yau batayi ba don tsakaninta da Allah
so take inna ta amince da abinda take fada mata.
Inna tayi tagumi tana kallonta tace "maimaita
min abinda kika fada.
Fatima tace "inna kiyi hakuri ni na san wannan
magana ba za tayi muku dadi ba amma kuyi
hakuri ku karbeta a matsayin abinda Allah ya
kaddara mana ni daku, inna don Allah kiyi hakuri
kada kuyi fushi dani nima ban taba tunanin zan
bijire wa auran malam musbahu ba sai a wannan
lokacin dana samu kaina a cikin yanayin da ban
taba tsammaninsa a gareni ba, tayi shiru ta kasa
ci gaba da magana ganin yadda inna ta tsareta
da ido kamar za ta shaketa.
Fuskarta a tsuke alamun fushi da zuciyarta ke
ciki, jin shirun ya yi yawa inna tace "kici gaba
mana tunda bakiji kunyar fara fadar wannan
maganar ba ba wani dalilin dazai sa kiji kunyar
karasawa.
Kan fati na kasa bakinta ya mata nauyi ga
maganganu na cinta ta kasa karasawa bayan ta
zauna a gaban innar ne cike da azamar fada din
sbda ance barin kashi a ciki bai maganin yunwa.
A daran jiya ne da barci ya gagari idanuwanta ta
kwana tana juyi kamar zuciyarta xa ta tsage, ta
yanke shawarar idan gari ya waye za ta tari inna
da maganar duk abinda zai faru yafaru, itama a
halin yanzu tasan meye so ta san abinda ake nufi
da ciwon so.
Bayan tayi duk sallar asuba tazauna shiru tana
tunanin ta yadda za tadubi tsabar idon inarta ta
shaida mata cewa su yi hakuri su bata khalifa shi
take so, ba wata manufa data wuce hakan amma
akwai tashin hankali mai yawa a cikin al'amarin
da ban tsoro, iyayanta suna matukar kaunar
musbahu kamar su suka haife shi, ba sa wasa da
abinda ya shafe shi, kamar yadda shima yake
matukar sonsu da kula da al'amarinsu, ko da su
suka haifeshi ba zai yi musu biyayyar da tafi
haka ba ko da yaushe malam yashiga yafita
maganarsa musbahu, duk abinda za ayi a gdan
musbahu ne zai ce yayi, shi kuma ba ya kasa a
guiwa gun aiwatar musu da abin da suke so ko
meye shi kuwa, in dai ba wanda yasani ba ba mai
cewa musbahu ba dan gdan bane, ta ina iyayanta
za su amince da damuwar musbahu, damuwa
kuma irin wannan.
Idan fatima takalli girman son da takewa Khalifa
sai ta tuna matsayin musbahu a gun iyayanta ba
karamin tashin hankali bane a yanzu tace zata
juyar da ra'ayin iyayanta daga auran musbahu
zuwa khalifa.
Tana cike da wannan rashin kwarin jiki da karayar
zuciya taci gaba dakulla shawarwarin yadda za ta
tunkari inna da maganar kafin ma malam yaji
wanda yafi kowa son musbahu.
Da gari yagama wayewa tafito tsakar gida duk
sanda suka hada ido da inna sai gbanta ya fadi,
lokaci lokaci takan faki idon inna tagoge kwallar
dake taruwa a gefen idonta, innar ce tagaji takira
ta daki tazaunar da ita tace yau sai ta gaya mata
abin dake cin zuciyarta wanda yasa tadaina
walwala.
Ta mayar da kanta kamar bakuwa a gdan, da
farko shiru fatin tayi tana sharar kwalla, inna tace
"uhum ta yaro kyau take ba ta karko, babu abi ?
da zai sa ki tashi a gun nan sai kin min bayanin
abinda ke rufe min zuciyarki....
A kofar gdan malam musa, Alhaji muhammadu
mahaifin khalifa ne zaune kan tabarma, shima
malam din suna hira, musbahu yafito musu da
kunun ayar da inna tahada musu yayi sanyi sosai
yana ta kamshin kayan yaji, suna sha suna ci
gabada hira.
Abba yana son gayawa malam abin da ke tafe
dashi kunya ta kamashi yarasa ta ina zai faro
maganar, bai yi tunanin zaiji nauyin maganar da
take ta damun zuciyarsa ba, bai san me xe ce da
Khalifa ba idan yakoma gda a haka har suka
gama hirar yabar gurin zuwan gdansu, ai kuwa
khalifa ya iske shi a falo tare da mama ta tare shi
da tambayar "Abba ya kuka yi da malam din!?
Ya fidda babbar rigarsa da hula ya ajiye yazauna.
Khalifa naje na kasa gaya masa, ban san dalili ba
naji bakina ya rasa yadda zai furta maganar
khalifa me xai hana ka daure kayi hakuri komi na
Allah ne.
Mama tayi farat tace "yawwa abba don Allah
kadinga nuna masa hakan irin wannan son kan ba
shi da dadi.
Khalifa ya kwantar da kan shi a jikin kujera yace
"abba ni zanje dakaina in sami mala.m din in
gaya masa, ni bakina ba zai ji kunyar fada ba,
wannan yarinyar ba zan taba iya hakura da ita ba
a rayuwata don Allah kuyi hakuri ku ci gaba da
tayani addu'ar Allah yasa auran fatima alheri ne
a tare dani.
Yamike zai fita abba yace "kayi hakuri kar kaje
zan kara yin tunanin akan al'amarin.
Murmushi yayi yafice.
Yana fitowa harabar gdan yakira fatima a waya
yanayin dayaji muryarta ya tabbatar itama tana
fama da damuwa.
Bayan sun gaisayace "a ina zan ganki?
"kazo gdammu kawai ina son kowa yatabbatar
ina snka kuma na amince dakai.
An gama gimbiyar mata.
Inna da malam, zaune a tsakar gida suna hira
,khalifa yayi musu sallama, cikin fara'a sosai suka
amshe shi ya tsuguna suka gaisa nan da nan
kamshin turaransa ya game gdan, farar shadda
ce a jikinsa sai walwali yake, yace "inna yaya
naganku a duhu?
Tace "khalifa ai ka san ba kullum suke kawo
wutar ba?
Yace "ba injin a gdan nan?
Sukayi shiru, yace "idan Allah ya kaimu gobe za a
kawo muku injin.
Malam yace "Don Allah khalifa kudaina mana
hidima haka abin ya yi yawa.
Yace "haba abba meye amfanin arzikin da ba za a
taimaki al'umar musulmi dashi ba, mu dai a dinga
sanya mu cki? addu'a yanzu ma bukata nazo da
ita gareku.
Malam yace "in dai bata fi karfinmu ba insha
Allahu za muyi maka kai da mahaifinka kunfi
karfin komi a gdan nan.
Kansa na kasa yace "baba dazun abba ya zo
gdan nan da nufin isar da sakon dana turo shi
dashi gunka amma ya koma yace min ya kasa
gaya ma, shi ne ni nazo in fada maka kuma in
roko alfarmarku.
Malam musa yayi murmushi, "amma alhaji ya ba
ni. mamaki yanzu har akwai abinda zai ce yaji
nauyin gaya mana, ni dashi ai mun zama daya
fada min khalifa ko meye in dai mallaki na ne zan
maka shi.
Khalifa yaji sanyi a ransa guiwarsa takara karfi
yace "baba auran fatima nake son kabani.
Gumi yashiga karyowa malam kansa na kasa yayi
shiru yakasa magana, itama innar shirun tayi
yayin da fatima ke cikin daki a zaune tana jiyosu
sai gabanta ke faduwa.
Zuwa can malam yadago kansa yace "ikon Allah,
khalifa ban taba zaton bukatar da za kazo min da
ita ba knan, ko dayake ba abin mamaki bane don
ka so fatima Allah ne mai hada zukatan bayi su
so juna kuma na ji dadi sosai na gode da son da
kakewa fatima, amma ina ba ka hakuri na riga na
ba da fatima, a inda ba zan iya karbota in ba ka
ba, in banda haka wallahi zan ba ka fatima
khalifa kayi hakuri insha Allahu za miyi ta maka
addu'ar Allah yabaka matar datafi fatima.
khalifa yayi shiru kansa na kasa lokaci lokaci
yana sharar gumin da yake tsatsafo masa, gdan
ma ya yi tsit kamar ba kowa a gdan, daga bisani
yamike dakyar ko ina a jikinsa ya yi mai nauyi
yace "to na gode baba Allah yasanya alheri.
Malam yamike yabiyo khalifa kofar gda suka
tsaya, malam yace "Abbakar ina matukar bakin
cikin hanaka auran fatima amma kayi hakuri Allah
ne bai sa matar ka bace, akwai abubuwa da
dama da Allah kan jarrabi bawansa don yagwada
imaninsa, idan yajure yayi hakuri sai Allah
yamusanya mai da abinda yafi wannan alheri
sakamakon hakurin da yayi da abinda Allah
yajarrabe shi dashi.
Duk kokarin da dr. khalifa yayi na mayar da
hawayen da suka taru a idonsa don kada malam
ya gani abin yaci tura, domin sai da yadinga
sharar kwalla yana jan numfashi da kyar, daga
karshe kasa ci gaba da tsayuwa yayi sai
durkusawa yayi, hankalin malam yatashi sosai
tun yana iya magana har yayi shiru ya zurawa
khalifa ido, yaji tausayinsa a wannan lokaci
,tausayi mai tsanani, zuwa can khalifa yatashi
yatafi gida ba tareda yakara cewa da malam komi
ba.
Malam ya jima yna kallonsa sannan yashige ckin
gida ya iske inna itama na ta jikin a sanyaye,
yazauna yace "kai yaron nan dagaske yana son
fatima.
"Itama tana sonsa malam ".
Inna tafadi tana kallonsa.
Yace "wane irin tana sonsa kuma da maganar
musbahun a kanta take son wani.
Tace "wallahi kuwa fatima ta yi abinda ban taba
zato ba a yanayin rayuwarta, tadubi idona tace a
yanzu ita khalifa take so tana son mu fasa ba
musbahu auranta mu bata shi in bar da tana son
sa za tayi haka? tunda tagaya min wannan
maganar jikina ke rawa hankali na yatashi sosai,
ni dai yin wannan rana na yi shi ne kawai amma
zuciyata tana cike da sarkakiya da damuwa, sbda
fatima ta ban mamaki ta ba ni tsoro, duk abinda
fatima za ta budi baki tayi magana akansa ba
karami bane, tana da kunya sosai da zurfin ciki,
tunda harta iya magana to da gaske tana son
khalifa, yawan kukan datakeyi shi yake dada
dagan hankali har na rasa yadda zan bullowa
lamarin.
Malam yace "amma wannan zancen banza ne, ni
za ta mayar karamin mutum, sa rai da ci shi ke
kawo jin yunwa in barda ta sa soyayyar ta sa ai
ba za ta daga hankalinta akan shi ba, tun yaushe
aka sa wa musbahu rai da batun auran ta, ya
saki jiki itace matarsa kawai sai ta dawo tace ga
wanda take so, a gun nan nafada mata idan ba ta
son musbahu ba zan mata dole ba tace ta ami?
ce, yanzu ya kike zaton mutane za su daukeni
idan nafasa ba musbahu naba khalifa, kwadayi?
Babu ta inda zan fidda kaina a gun musbahu da
yan'uwansa dasauran jama'an gari na sayowa
kaina zagi.
Inna tace "wallahi malam ni ma ban goya mata
baya ba don na san son zuciya ne karara tazo
dashi.
Haushi yakara kama malam ya kwalawa fatima
kira, tafito tana rabe rabe ta tsuguna ybuga mata
harara yace "na fahimci cewa ke ce kika ba
khalifa fuskar yazo gdan nan yazo min da batun
auranki alhalin kina sane da musbahu, kin ba ni
mamaki fatima ban taba shakku akan lamarinki
ba sbda biyayyar ki garemu kada ki bamu kunya
kada kija abinda zai ja mana damuwa alhali
muna zamanmu lafiya.
Fatima tayi doguwar ajiyar zuciya tace "kuyi
hakuri baba ni ma banyi tsammanin zan wayi gari
ckin wannanyanayi ba, ni kam ina son khalifa don
Allah ku ba musbahu hakuri....
"Salamu Alaikum
Muryar musbahu knan, suka daga kai a razane
suka zuba mai ido fuskarsa a cunku she yazauna
jagwab kusa da malam muryarsa na rawa yace
"Baba hakika na ji duk tattaunawar ku da fatima
kuma na ji matsayina a gunku, ba ni da abi? da
zan ce muku sai godiya, kyautatawar dakuka mini
Allah ne zai biyaku domin don shi kukayi.
Baba na san ina son fatima soyayyar da tasa
nake jin cewa idan na rasata zai wahala in yi
aure domin bansan ta yadda za ai in so wata
mace ba bayan ita, ko da yike komi na Allah ne
amma wannan soyayyar danake mata ba za tasa
in aureta alhali na san ba ta so na ba, kayi hakuri
baba kaba fatima khalifa...
Cikin zafin rai malam musa yace "yi min shiru
musbahu, wannan yarinyar bata isa tasauya min
ra'ayi ba, tunda tun farko da amincewarta aka sa
bikin auran nan kadarra cewa ma ka auri fatima
ka gama.
Ranar da aka sanya za a daura wannan auran ba
fashi, insha Allahu za a daura in dai ka ga ba a
daura ba sai dai in ranar ce tariskeni ba na
numfashi, za a daura auranku kuma za a kaita
gdanka, a ranar tahadiya zuciya tamutu a kawo
min gawarta.
Musbahu yabude baki zaiyi magana malam yayi
mai tsawa yace "in dai kaima ba so kake kabata
min rai ba kayi min shiru, idan Allah yakaimu
gobe kaje ka amso katunan daurin auran a kaiwa
kowa.
Yatashi yafice ,musbahu ma yabi bayansa, itama
innar tashige daki tabar fatima tana kuka.
Tunda take bata taba batawa iyayanta rai ba
ballantana suyi fushi da ita sai yau, shin me ya
shiga zuciyarta ne tasauya haka, a duk lokacin da
ake magana, soyayyar khalifa ce take karuwa a
zuciyarta, kamar ana hura mata wuta, idanuwanta
suka kada jawur tarasa yadda za tayi da ranta.
Soyayyar dr. khalifa ta gama rufe mata zuciya ji
take kamar ba xa ta iya rayuwa ba in ba shi,
gabaki daya ta watsar da batun ummi ta kanta
kawai take, tana ji a ranta in dai ta auri khalifa
duk abinda zai biyo baya me suki ne, iyaka dai
ummi tadaina kulata ita in dai tana tare da khalifa
bukatar zuciyarta ta biya, matsalarta yanzu
iyayanta wadanda sun dau zafi dayawa.
Ta daga kai ta amsa sallamar musbahu, haushi
yakara kamata tabishi da ido har yatsuguna
gabanta yace "fatima.
Bata amsa ba sai kallo yace "kiyi hakuri.
Ta mike tashige ckin daki a zuciyarta tana fadin
ai kai hakuri yakama ba ni ba.
Musbahu yayi zaman dirshan a gun yazuba
tagumi da hannu bibbiyu shin wani irin iftila'i ne
yasa me shi haka?da can bai rasa fatima ba sai
da yagama sakin jiki bai da mata sai ita, yakasa
juriya yabita dakin na su, ya isketa a kwance tana
kuka.
Yace "fatima baki min adalci ba don Allah ki
kwatanta idan ni nayi miki haka za ki so? a ce a
irin wannan lokaci in ce na fasa auranki wata zan
aura?
Ya tsuguna a gabanta kamar mai neman gafara
yace "don Allah fatima ki taimake ni wlh ba
karamin so nake miki ba, ni ban isa in ce
kwadayin duniya ne yasa kike son khalifa ba idan
akwai kwadayi ba za ki tsaya akaina ba, masu
kudi dayawa sunce suna sonki baki ba su hadin
kai ba.
Fatima batayi niyyar yi ma musbahu magana ba
dan ita kanta ta san ba ta da abinda za tace
musa, amma a bisa wannan maganar tasa da taji
ya dace tace wani abu a kokarinta na samin
mafita.
Tace "Nagodewa Allah dayasa da kanka kayi min
shaidar ba kwadayi yasa nace ina son khalifa ba,
ka san cewa soyayya ce don Allah, ina son kayi
hakuri kayi min adalici, soyayya Allah ne me
sanyata a zuciya ba mutum ba.
Ya katseta zuciyarsa cike da daci yace "fatima ki
fito a gaban ido na kawai ki ce ba kya so na,
khalifa kikeso, na gode fatima nagode.
Yamike dasauri yafice yana goge hawaye.
Fati tace "innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
A DAREN FARKO
27
izuwa wannan lokaci ummi ta tabbatar fatima ta
daina yi mata aikin komai ita takewa kanta, ta
fahimci soyayya suke shimfidawa da dr. khalifa ta
gaske duk da cewa rigima ake tafkawa a gdansu,
ga katunan daurin auren yau an fito dasu har an
kawo na Abba gdan, a kalla kwana uku kachal a
daura auran musbahu da fatima, har takaici da
kishi ya yiwa ummi yawa, yaudara ita take
fassara fatima ta yi mata tunda gashi ta fita
hanyarta tunda gashi ta fita hanyarta gaba daya
ko neman ta ba ta yi lallai mutum abin tsoro ne.
Ta iso gdansu da katin daurin auran ta nunawa
hajiyarta tace "to ai zance ma ya kare in dai aka
mata aure aka kaita dakin mijinta ai dole khalifa
ya hakura da ita duk maitarsa .
Unmi tace "kayya dai hajiya khalifa yana son
fatima in kinga abin da yake nunawa za kiyi
mamaki.
Tace "duk ihu yakeyi bayan hari shi zai bawa
kansa auran na ta? ki kwantar da hankalinki
malam yana nan yana buga mana aiki da kafarsa
khalifa zai zo gdan nan.
Ita dai ummi hnkalin ta ya ki kwanciya son da
khalifa ke nunawa dmfatima kadai ya isheta
takaici, ita ko kallon ta ba ya yi tamkar ba aiki
ake yi a kansa ba.
*****
Ummi ce take sha'aninta khalifa bai san an fara
rabon katin auran fatima ba sai da yamma daya
dawo daga asibitin su dr. hafiz ya iske katin a
hannun abbansa, yana gama karantawa yazube a
gun.
Abba yatashi a firgice yana jijjiga shi tare da kiran
sunan sa da karfi ina khalifa ko motsi baiyi ba
numfashinsa yatsaya cak, abba yafita dagudu
yakira mai gadi yace yazo sudauki khalifa ba lfya,
mama da anty sdiya ma suka fito daga daki
ganin yanayin khalifa yatashi hankalin kowa sun
shiga dimauta, suka nufi wani asibiti mai zaman
kansa har suka isa khalifa ko motsi abba salati
yake yana fadin "shike nan Khalifa ya mutu akan
son ftima na ga takaina.
Likitoci suka amshe shi ckin gaggawa suka kaishi
wani daki suka fara ba shi taimakon gaggawa,
dakyar suka lallashi abba y tsaya a waje dan
cewa yayi sai ya shiga dakin, gani yake kamar
khalifa ya mutu, mama datake mace ma ta fi
abba karfin hali, itatadinga ba shi baki tana nuna
masa cewa ba mutuwa khalifa yayi ba, yadinga
kai komo a kofar dakin ba likitan daya fito, yagaji
yashiga buga kofar yana fadin "ku fito min da
gawar khalifa na san ya mutu.
Wani bakin likita dogo siriri yafito yaja hannunsa
suka shiga dakin yaba shi kujera yazauna daf d
gadon da aka kwantar da dr. khalifa yace "Alhaji
duba kagani yana numfashi ko?
Anan ne abba yayi doguwar ajiyar zuciya, ashafi
fuskar khalifa zuwa wuyansa yaji sanyi kalau,
numfashinsa yadawo normal amma lokaci daya
yarame fuskarsa takara haske.
Likitannan mesuna dr. mansur yadan rusuna kusa
da abba yace"ka gamsu bai mutu ba ko?
Yace "hakane amma nikam likita jikina na ba ni
mutuwa zaiyi, khalifa ba zai yi dogon kwana ba a
duniya...
Dr. mansur yarufe me baki yace "haba alhaji ya
za kadinga wadannan maganganun a matsayinka
na musulmi? mutuwa daban ciwo daban, kayi
hakuri mun sha kan matsalar khalifa dimuwa ce
kawai takai shi ga shiga wannan halin in dai ku?
yi kokarin magance masa damuwarsa shi knan
komi zai tafi yadda yakamata.
Su mama ma an ba su damar shigowa ita da anti
sadia, gaba daya suka zubawa khalifa ido cike da
damuwa jikinsu ya gama sanyi da al'amarin .
Abba yagirgiza kai yace "hajiya wani irin tsari ne
haka, shi knan akan mace mutum yadaga
hankalinsa kamar zai bar duniya,ni wallahi har na
rasa yadda zan bullowa al'amarin na khalifa
tunda ga wanda iyayanta suka yiwa kawari na yi
na yi yayi hakuri ya ki fahimta,ban taba ganin
abinda khalifa ydga hankalinsa akan sa ba sai
akan fatima, wacce irin soyayya ce wannan, daga
ganin katin daurin aure.
Mama tagirgiza kai tace "wallahi abba nima
tunda khalifa yafara maganar yana son fatima
hankalina a tashe yake, sbda yanayin daya ke
nunawa abin fargaba ne, in an yi magana yace
wai a kyale shi b a san abinda yake ji bane, to
rayuwa za tatafi a haka, wani abun idan mutum
yana so yana samu wani abun kuwa duk
maitarsa da kaunarsa da abin ba zai same shi ba
sai hakuri.
To shi khalifa ji yake kamar ba zai ci gaba da
rayuwa ba idan bai mallaki yarinyar nan ba,.
Suka yi shiru kowanne idonsa kan khalifa, daga
bisani abba yaja numfashi yace "wai yaya za mu
bullwa lamarin nan ne?
Mama tace "to yaya za muyi kuwa abba in barda
muyi hakuri dole fa khalifa yahakura da fatima.
Abba yace "kai hajiya a irin wannan yanayin, dubi
fa yadda yake.
Tace "to idan bamuyi hakurin ba ta karfin tsiya
za mu ba shi fatima?
*****
Ga dai lokacin biki ya zo gadan gadan amma
gdansu fatima yanayin babu dadi domin kuwa
ango da amaryar suna cikin damuwar dataja jikin
kowa ya yisanyi babu mai walwala,Fatima ce
zaune kan kujerar zaman tsakar gida da wayarta
ta hannu ta kurawa sakon daya shigo wayarta ido
zuciyarta na azalzala sako ne daga khalifa yace.
Fatima soyayyarki xa ta hallakani bbu wani
taimako daza kimin don Allah kiji tausayi na kada
ki bari iyayanki su bawa musbahu ke wallahi na fi
son ki fatima.
Tagoge hawayen dasuka gangaro mata tayi ta
maimaita sakon tana girgiza kai, ta tashi tashiga
dakinsu tacimma katunan gayyata na biki da
musbahu yakawo mata da la'asar din dazu, ganin
idon katunan sun tsaru sun yi kyau amma ita
bakin ciki ne yakara turnuke mata zuciya data
gansu, ganin katunan yakara kusanto mata
lokacin bikinta knan kuma lokacin rabuwarta da
masoyinta dr. khalifa, kuma idan tayi wasa
wankin hula na daf da kai mata dare.
Shi kansa musbahun lokacin daya kawo mata
katin sai da yabata tausayi, tana sallah yashigo
yatsuguna bakin kofa kamar me neman gafara,
data idar bata kalleshi ba tajawo pillow ta
kwanta, a sanyaye yace "fatima ga katinan
gayyatar.
Tadube shi wani iri tace "to ajiye anan.
Ya matso daf da ita ya ajiye, uace "ko kina
bukatar wani abu daya danganci bikin?
Ta ki magana sai da yayi ta mata naci sannan
tace "Ni fa ba abinda nake bukata.
Yace "shi knan sai anjima.
Yamike yafita yayin da tabi bayansa da ido cike
da takaici.
Gabadaya dr. khalifa ya sauya mata yanayin
rayuwarta, kafin dawowarsa tana zaune lafiya ba
ta damuwa da komi babu abinda yake tayar mata
da hankali sai daya dawo.
Tun randa dr. khalifa yafara cewa yana snta bata
kara samun kwanciyar hankali ba, gabadaya ya
jefata a ckin damuwa da rudani kullum tunani, ta
zamo abar tausayi akan kanta domin yanayin da
zuciyarta ke ciki ba dadi, ba ta jin dain halin data
sanya musbahu sbda babu abinda yayi mata, ya
rayu yana tattalin abin da take so tun tana yar
karama yake tattalin rayuwarta har maganar aure
ta bullo a tsakaninsu, ya dauki son duniya ya
daura mata kullum kamar zai lashe ta, ba ya son
abinda zai daga mata hankali, kowa ya shaidi
musbahu da kyawawan dabi'u ababan so ga
kowacce mce, dari bisa dari ta amince da batun
auransa, shi yasa bata tava kallon wani da namiji
da sunan so ba, sbda ita dai yardar Allah kawai
take nema a rayuwarta, bata taba damuwa da
kyale kyalen duniya ba, bbu kwadayi ko son
zuciya tsarinta, shi yasa tafiyarsu da musbahu
yaxo daya svda shima akan wannan tsarin na ta
yake tafiya. kowa yana kyautata zaton za su
zauna lfya a dalilin kowannen su ya dauki rayuwa
dasauki, iyayanta suna cike da murnar auran ba
su da fargabar komi, sai da abin yazo daf dr.
khalifa ya bayyana cikin rayuwarta shi knan
zuciyarta tasauya.
*****
A DAREN FARKO
28
Tana cike da jin nauyin musbahu, soyayyar dr.
Khalifa ce take da karfi a zuciyarta shi yasa
takasa tuna komi.
A bangare guda da ummi, ummi ta taka
muhimmiyar rawa a kanta ta hanyar nuna mata
kauna da aminci na gaskiya takuma haifar da
cigaba a rayuwarta, a daidai lokacin datake
kokarin taimakon ummi don ta cimma kufurinta a
kan dr. khalifa soyayyar khalifan yakama
zuciyarta, wanda a wannan lokacin ne ta fahimci
meye so tasan zakinsa da dacinsa kusan wahalar
da zuciya ke sha akan ciwon so, tausayin ummi
ya yawaita a zuciyarta domin ta dade tana fama
da ciwon son khalifa, alhali ba ta da tabbas din
komi a kansa, ga misali itama dayake son ta
tanayin ciwo me zafi a rayuwarta na son sa ina
ga ummi da ta tabbatar ba ya sonta ,kowannansu
kam abin tausayi ne, ama dai ita ta fi zama abun
tausayi tunda ita tana sa ran samun khalifa wani
abu ne yake neman yi mata shamaki dashi, ummi
kuwa dama tana sa rai ne tana cire ranta, tunda
ta san bai karbi soyayyarta ba.
Wannan shi ne tunanin fatima.
*****
A bisa wani dan benci dake kofar gdansu
fatima,musbahu ne zaune ya yi tagumi lokaci
lokaci yana fidda nannauyar ajiyar zuciya wadda
ke cike da damuwa da dacin rai,idanuwansa sun
kada jawur ,yau so yake yi ma yayi kuka ya kasa,
wai shin me ke faruwa dashi ne, da can bai
fuskanci matsala da fatima ba sai yanzu, an ya
ba mafarki yake ba, fatima ce tadawo ko ganinsa
ba ta son yi, a baya ko yaushe in suna magana
idan ya kutso mata maganar rayuwa takan bata
rai tace ita kuwa me za tayi da wani namijin
bayan ga zabin da iyayanta suka yi mata, ta
kance k kwantar da hankalinka ba ni da abin da
yafi iyayena in dai zuciyarsu za tayi haske to ni
burina ya cika ba ni da damuwa .
Ire iren wadannan maganganun suke ba shi
cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali,
musamman a bisa la'akari da rayuwar fatima ba
mai tsada bace in ban da haka kallonta kadai ya
isa hnkalinsa yayi ta tashi sbda kyawun halittar
da Allah yayi mata zai dinga jan hankalin mazan
zamani kanta, to kuma si gashi abubuwa sun
sauya a lokaci guda fatima tajuya masa baya
khalifa take so, yadinga jin wani azababban kishi
da takaici yana tafarfasa zuciyarsa kamar zaiyi
hauka, iyakar tunanin sa bai san yadda zai
bullowa al'amarin fatima ba haka zai aureta
hankalinta na kan khalifa ya girgiza kai, inama
sai da akayi auransu khalifa yadawo, da ba zai
ganta bama ballantana yace yana sonta har
yadaga mata hankali yadagawa kowa.
Yashiga harar kwalla, sai yanzu yaji zuciyarsa ta
yi masa dama dama daya samu hawayensa suka
zubo, tabbas yana son fatima amma yanzu fati
tsoro take ba shi "kukan me kake musbahu?
A firgice yadaga kansa yadubi malam wanda yake
tsaye a kansa yana kallonsa, yaci gaba da sharar
hawayensa ba tre da y ce komi ba, malam yace
"Biyoni ckin gida.
Ckin sassarfa musbahu yake tafiya suka shiga
dakin malam din suka zauna, yakara maimaita
mai tambayar "kukan me kake?
Muryarsa a dashe yace "baba ban san yadda za
ayi in shawo kan fatima hankalinta yadawo kaina
ba, ina jiyewa kaina tsoron abubuwa da dama
game da fatima.
Malam yace "musvahu ni ne fa na haifi fatima ni
ne na yarje ma auranta, har a halin yanzu ina
dada tabbatar maka da cewa in dai ranar daurin
auran nan tazo ina raye ba zan daurawa fati
kowa ba sai kai, to meye na tayar da hankalinka
kan fatima in dai in dai tana ckin gdan nan tana
karkashin ikn mu za a kaita gdanka kuma dole ne
tayi biyayya gareka in har tana son zaman lafiya
damu, ita kanta ta san ba na kwadayin abun
duniya bana son zuciya a kanta kuma ba zan fa
ra ba.
*****
A son ran ummi tayi zamanta a gdansu kada
takoma gdansu khalifa wai a tunanin ta hakan zai
sa hankalinta yakwanta, ta huta da bakin ckin dr.
khalifa da fatima ke haifar mata amma ina lokacin
da dare yayi dare sai taji hankalinta ya tashi
sosai khalifa kawai take bukatar gani.
Tabdijan ashe dai tana da jan aiki a gabanta ace
duk sanda ba ta gdansu hnkalinta ne zai ding
tashi haka, knan va za ta iya rayuwa ba sai tana
ganin khalifa? ta mike zaune zaman ya gagara
tamike tsaye anan ma tashiga sunturi ta dauki
wayarta tayi kiran nomban khalifa bai daga ba
bata san abinda za tace masa ba amma dai in
taji muryarsa watakila tasamu tayi bacci ta huta,
in dai a haka xuciyarta za ta tafi tana da babbar
matsala.
Takira nomban fatima bugu daya fatima tadaga
tayi mata sallama da siririyar muryarta, tace
"fatima bakiyi barci ba?
"Eh banyi ba.
"Meya sa?
Tayi shiru.
Tayi murmushi tace "na san tunanin dr. khalifa ne
yahanaki bcci, don Allah haka ne.
Fatima tayi ta maza tace "Na san kin san haka
ne unmi shiyasa kika fada.
Tayi ajiyar zuciya tace "fatima da ma na san ba
za ki iya kaucwa soyayyar dr. khalifa ba duk da
cewa a baya na mi? ce har ckin zuciyata za ki
taimake ni a kan dr. khalifa to sai ga shi kema....
Haushi yakama fatima ta tabbata soki burutsun
na rashin abin yi ne yasa ummi ke mata wannan
shiriritar dan haka takashe wayarta.
Mamaki yakama ummi ta jima tana kallon
wayarta wai yau ita fatima ke ma haka, bata ma
da lokacin saurararta, hakika ya zamo dole ta
dauki mataki mai kwari akan fatima.
Da gari ya waye da sassafe ta tashi tayi wanka
ko tunanin cin abinci batayi ba tashirya tace da
mahaifiyarta "na tafi gdansu khalifa.
Hajiya na zaune a kicin tana suyar wainar fulawa
tayi mata wani irin kallo tace "wai me ke daminki
ne ummi, abin ci ma ba za kidinga tsayawa kina
cinsa ba sbda khalifa? wannan wainar ma sbda
ke nake yinta na san kina sonta amma ki ce
tafiya za kiyi?
Tace "don Allah hajiya barni in tafi hankali na a
tashe yake ko barci banyi ba jiya.
Tana tuka mota tana wasi wasi a haka har ta iso
gdan masu aiki suka tarbeta da mummunar labari
a asibiti dr. khalifa yakwana ba shi da lfya, tayi
saurin kiran nomban mama tayi mata kwatancen
asibitin dasuke tafigi mota ta nufi can.
Hankalin ummi yakara tashi ganin yadda taga dr.
khalifa mike isa gado, yana wani irin bacci wanda
ga duk alamun bai san a inda kansa yake ba,
mamane zaune bisa dadduma a kasa sadiya a
gfenta abban na zaune kan wata kujera dake
gefen gadon khalifa yazuba masa ido kawai.
Ta tsyguna ta gayar dashi tare da jajanta masa
ciwon khalifa ta zauna kusa da mama tana
tambayarta "me ye musababbin ciwon ne?
Mama ta tabe baki tace "katin daurin auren
fatima yagani.
Ummi tafiddo ido gabanta na faduwa tace "don
ya ga katin daurin auran fatima yashiga wannan
halin?
Mama tace "kwarai kuwa tunda muka kawo shi
asibitin nan bai farka ba har yanzu, nasarar da
akaci dai nu; fashinsa ya dawo dai dai sabanin
lokacin da muka kawo shi dan ko numfashi bbu,
ni zatona ma ya mutu.
Jikin ummi yakara mutuwa murus takoma jikin
bango itama tayi shiru har tarasa abin da za
tace.
Wato wannan soyayyar har ta kai zafin haka, ina
aikin da malamin su yace zai musu mai zafi
wanda yaci musu alwashin zai raba soyayyar
fatima da khalifa da ta duk wata diya mace sai
ita ummin,. Amma abin mamaki kamar karawa
dr. khalifa soyayyar fatima ake, me malamin nan
ke nufi knan, aikain yake musu ko yaudararsu
yake"
Ta jinjina kai a baya kam ta san dr. khalifa yana
son fatima haka yanayinsa yanuna, to amma yau
ne yadada tabbatar da soyayyar nan ba ta wasa
bace duk inda ake tunanin abin ya wuce nan,fidda
soyayyar fati daga zuciyar khalifa abu ne mai
wahalar gaske.
Tadubi mama tace "to yanzu me likitocin suka
ce?
Mama tace "cewa sukayi a samar masa da
abinda yasaka a ransa yana so din idan ana son
rayuwarsa.
Tace "to wani mataki aka dauka?
Mama tace "har yanzu bamu san abinda za muyi
ba. fatima dai tunda ba mu da ikon ba shi ita ai
sai hakuri .
Ta jinjina kai tace "To Allah ya sawwaka bari inje
gda in kawo muku abinci ko zai farka ya bukaci
wani abu.
Mama tace "ga abin cin nan na asibiti an kawo.
Tace "ai khalifa ba zai iya cin abincin asibiti ba
bari dai in dafo wani abun.
Lallai dr. khalifa ya yi nisa ba yadda za ayi yaji
kira, gdansu fatima tafara shiga sai ita kadai a
rmfar inna tana fama da waya, inna tana dakin
malam suna hiran bikin fatima.
Ta amsa sallamar ummi ckin fara'a tamkar ba
wani abun, tukukin bakin ciki yakara turnukewa
ummi zuciya, tayiwa fati kallon sama da kasa
lokacin datake ce mata zauna mana anty ummi.
Tace "ba zama nazo yi ba zuwa nayi in tamvayeki
ina amsar taimakon dakika dauka za kimin a gun
dr. khalifa.?
Nan fatima tarasa abinda za tace tayi shiru,
ummi tace "dama na san bbu abinda za ki iya
cewa, tunda ba ki da abin fada din kinyi amfani
da damar dakika samu kinja ra'ayin dr. khalifa
har soyayyar dayake maki ta kaishi ga kwanciyar
ciwo, to yana asibiti bai san inda kansa yake ba a
dalilin ya ga katin daurin auranki da musbahu, sai
kije ki duba shi kafin yakarasa mutuwa.
Tajuya za ta tafi fati tajawo hannunta tace "Don
allah ummi kar ki tai zauna ki taimake ni nasamu
kaina a wani irin hali.
Wani taimako zan maki fatima? ni van taimaki
kaina ba wa zan iya taimakawa? in kura na
maganin zawo me yasa batayi wa kanta ba?.
Fati na kuka tace "ai rai ba ta rasa motsi ummi
tasaya kiji.
Ta jingina da bango tare da rungume hannayenta
a kirjinta tana kallon fatima, fati tace "a wane
asibitin khalifa yake?
Tace "idan za ki wuce muje.
Gaba dayansu sun rasa abinda za su cewa
junansu kowacce tana neman taimakon 'yar
'uwarta ne ,unmi tace "tunda baki da abin fadi
nima na rasa abinda zan ce miki kisameni a gda
zan hadawa khalifan abinci sai muje asibitin,
dasauri tfice daga gdan.
Yayin da fatima tanufi dakin babansu ta durkusa
tashaida musu cewa za su je karbar dinkin tada
mama tayi musu na biki da ummi, sukace a dawo
lfya.
Ta sauya kaya ko wanka batayi ba tafice daga
gdan, musbahu na kallonta tashige gdansu khalifa
ba shi da ikon yi mata magana sai kallo, fatima
ta fi karfin sa yanzu.
Ummi na kicin tana ta hada abincin cikin
gaggawa, fatima ta yi zaune a falo tana ta kallon
hoton khalifa gabanta sai faduwa yake, wani
babban hotonsa ne yakewa mutum maraba da
zarar ka shigo falon, murmushi yayi a hoton
murmushin dayayi matukar kayatar da fuskarsa,
takagu ummi tagama su tafi taga halin da
masoyin ta ke ciki.
Bayan ummi ta kammala komi a mota tashiga
dakinta da niyyar yin wanka ganin ta jima bata
fito ba a fusace fatima ta bita ckin dakinta
tashiga buga kofar toilet din tana fadin 'haba
ummi wane irin jan rai ne haka? kinsan fa jiranki
nake.
Ummi tace "to don kina jira na ba zanyi wanka
ba, karki dameni malama asibitin ma ganin damar
kaina nayi ko kin sani ne ba sai da na gaya miki
ba.
Fatima tarasa me za tace da ummi don haushi,
kuma karin haushi ne yasa bata kara ce mata
komi ba sai da tagama abinda take a
toilet,sannan tafito tafara shiryawa,fatima takara
fusata a karo na biyu tace "ummi idan ba za ki
rakani asibitin nan ba ki gaya min in yi tafiyata.
Ummi tarausayar dakai tana murmushi tace "yi
hakuri taso mutafi.
A cikin mota tafiya suke kamar wasu kurame,
kowacce da abinda take fama dashi a zuciyarta,
da suka shiga harabar asibitin tasamu wuri tayi
parking fatima ta tayata diban kayan abincin
suka shiga dakin.
Abba ne yakama fara'a yana fadin "fatima ke ce
da kanki?
Kunya da tausayi suka kamata lallai abba na
cikin damuwa ta tsuguna tagayar dasu tare da
tambayarsu mai jiki, Abba yace "to fatima mai jiki
dai ga shi nan sai yadda Allah yayi, soyayya ce
mai wahalarwa ya hdu da ita, sai dai hakuri.
Mama dai shiru tayi tazuba tagumi tana ganin
ikon Allah, magana in dai ta khalifa ce abba ba ya
kawaici akanta, yaci gaba da fadin "fatima dubi
halin da khalifan yake ciki har yanzu bai san
wanda yake kansa ba, ni wlhi ban taba ganin inda
akewa mutum irin son da khalifa yake miki ba, ga
shi ba mu da ikon bayar dake gareshi, shin yaya
za muyi da wannan tashin hankalim.
Kukan fatima yafito karara tana juya kanta mama
tace "Alhaji bai kamata kadinga fitowa da fatima
irin wadannan maganganun ba sbda aikin gama
ya gama alkalami ya bushe, hakuri dai khalifa
zaiyi Allah yatashi kafadunsa.
Cikin sanyin murya abba yace "ai nima ba wani
abu nace ba.
Fatima tace "Abba don Allah karoki babna ya
janye mganar aurena da musbahu yana jin
maganarka tare da girmama bukatarka, wlh nima
khalifa nake so.
Mama tarike hannunta tace "fatima mun san kina
son khalifa Allah ne bai kaddara Khalifa mijin ki
bane shiyasa duk abinda yafaru yafaru, wannan
son zuciya ne karara idan har muka nacewa
iyayanki da rokon su bawa khalifa ke,sbda shima
musbahun yana sonki ba ya son yarasaki, idan
mukayi amfani da wata dama da muke da ita
muka rinjayi iyayanki suka ba khalifa auranki
bamuyi amfani da hadisin manzon Allah dayake
cewa imanin dayanmu ba ya cika har sai ya
kasnce mun so wa yan uwammu abinda muke so
wa kanmu, sannan na biyu mutane za su zagemu
don a zahiri munyi rashin adalci mu mun san
iyayanki basu hana mu auranki dan kiyayya ba
sai dan girman alkawarin dasuka wa musbahu.
Fatima takara rikicewa da kuka tana kallon dr.
khalifa take cewa wallahi mama ba na son
musbahu, khalifa nake so, ba ina fadin hakan
bane don a gabanku ne ina son shi ne kawai don
shi ne ra'ayina na amsa wa iyayena auran
musbahu a lokacin da ban san meye so ba, yanu
na fahimci inda rayuwa ta dosa don Allah mama
kutaimaka ku fahimtar da iyayena kada su dauran
auran da ba na so xan iya shiga ko wani hali idan
ban auri khalifa ba.
Aka yi tsit dakin kukan fatima kadai ke tahi,
ummi kallon iyayan khalifa da fati kawai take
tana girgiza kai ta ji dadi da hawayenta basu
zuba ba domin ta gaji da kuka lokacin kuka ya
wuce a gunta illa neman mafita, son kai ba
musbahu kadai ake naman yi mawa ba har ita
gara ma musbahun da yake so ake kwace masa
matr ana ta nanata yadda za ayi dashi ita kuwa
ba wanda yadamu da damuwar ta idan ma
mutuwa za tayi tayi ta mutu, wai fati ce ke kuka
a gaban iyayan khalifa tana rokonsu ita dai tana
son khalifa, takallesu gaba daya tagirgiza kai tare
da cije lebe.
Anty sadiya tace "mama kinga abinda nake gaya
miki wai meye amfanin yin shirun da akayi alhalin
an san halin da zuciyoyin yaran nan ke ciki. ya
kamata ayi musu adalci, shi musbahu bai san
aure nufi ne na Allah ba, a zaunar dashi a yi mas
bayanin kudubi halin da khalifa ke ciki daga ganin
fa katin daurin auranta yashiga wannan halin ina
ga idan an wayi gari yasan an kaita gdan
musbahu?
Tagirgiza kai.
Gaskiya mama a san abin yi kada fa azo ana
nadamar da ba ta da amfani gara tun kafin lokaci
yagama kurewa a yi wani abin.
Abba yace "maganarki haka take sadiya tabbas a
yau din nan zan bi hanyar data rage tarage don
ganin ankawo karshen wannan matsalar wannan
lamarin na khalifa ya fi karfin a sa ido dole a
yiwani abin a kai.
Kofar dakin tabude dr. mansoor yashigo tare da
wata nurse a bayansa ya isa gaban gadon dr.
khalifa yace "har yanzu bai farka ba.
Abba yace "ai ko motsin kirki ba ya yi nifa in
banda ina ganin numfashinsa da yanzu na ce
khalifa ya mutu.
Dr. mansoor yadaga hannun khalifa ya mayar ya
ajiye, yadakko wata karamar na'ura yadaura mai
akan kirji yana latsawa tare dasa wani abu a
kunnansa, zuwa can yacire yajuyo yadube su
gaba daya yakira sunan nurse din da ke tare
dashi mai suna jamila yace "ki lura dashi sosai.
Tace "ba damuwa sir.
Yamaido ido ga abba yace"kuyi hakuri Alhaji
insha Allahu khalifa zai samu lafiya ni yanzu xan
tafi gida.
Abba yace "haba dr.yaya za kace za ka tafi
bayan har yanzu ko farkawa khalifa baiyi ba.
Dr. mansoor yace "Alhaji kada kadarra cewa
samun lfyar khalifa yana hannuna wannan
hukunci ne na Allah,Allah yahore mana taimakon
al'umma ta hanyar ilimi daya azurta mu dashi a
bisa yardarsa muke yin komi ,nan da dan lokaci
kadan likitan daya karbi aiki zai shigo yaci gaba
da kula dashi, Allah shi ne me ba da lafiya, kafin
dai in tafi inaso idan da hali ayi duk kokarin da za
ayi a nemo abinda zai sanya khalifa farin ciki
yayin daya farka ma'ana da zarar ya bude idonsa
yakasance ya ga wani abu dazai faranta masa
rai, wannan zai taimaka gun sanya natsuwa a
zuciyarsa.
Abba ya waiwayo yadubi fatima sannan yamaida
kallonsa ga likitan yace dashi "ka ga wannan
yarinyar?
Dr. mansoor yadubi fatima dake tsugune gefe
tana sharar kwallah abba yace "to itace yarinyar
da khalifa ke so kuma iace silar fadawarsa cikin
wannan halin.
Dr. mansoor yace "Alhaji kana nufin itace fatima.
Dasauri Abba yace "itace kuwa likita ina kasan
sunanta?
Yace "a jiya da kuka kawo khalifa lokacin da
numfashinsa yafara dawowa bayan salatin Annabi
da yayi sunanta muka ji yana ambata tun daga
nan muka kaddara cewa a dalilin mace yafada
ckin wannan damuwar, to tunda ga ta meye abin
tashin hankali ba sai a bashi auran na ta ba kowa
yahuta.
Abba yayi murmushin takaici yana girgiza kai
yace "Likita wannan yarinyar tafi karfin khalifa,
kudi ba sa sayan mutum da ace kudi na sayan
mutum ko nawa fatima takai sai na siyawa
khalifa dan in rabashi da wannan damuwar
dayake fama da ita, saura kwanaki biyu kachal
awa 48 fatima tazama matar wani ban san halin
da khalifa zai shiga ba, Inalillahi wa inna ilaihir
raji'un.
Dr. mansoor ya jinjina kai yace "gaskiyar magana
abba tunda halin da khalifa yashiga ya kai haka
to kanemi iyayan yarinyar nan ku daidaita
magana su zo suga halin da danka yake ciki su
taimaka kowa yataimaki wani Allah zai taimake
shi, kada kabari wani ya auri fatima alhali khalifa
na ckin wannan halin.
Akayi shiru gaba daya har Dr. mansoor yafita bbu
wanda yasake magana.
A DAREN FARKO
29
Karfe daya daidai Abba yace zaije gida yayi
wanka yayi sallah yadawo.
Mama ta biyo shi har mota tana rokon yadaure
yaci abinci.
Ya dubeta da jajayen idon sa yace "cikin nawa ne
bbu dadi tun dazun nake jin zuciyata na tashi
kamar zan yi amai ga kaina na juyawa.
Tace "kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka
komai na Allah ne, duk wadannan abubuwan dake
fruwa idan Allah ya yi fatima matar khalifa ce zai
aureta, za kaga yadda Allah zai juya al"'amarinsa
daga damuwa izuwa farin ciki, babu abinda ya
gagari Allah shi ne me yadda yaso a lokacin daya
so, yayin da duk damuwar da za ayi da duk halin
da za a shiga idan Allah bai kaddara matarsa
bace sai dai mutari muyi hakuri muyi fatan
alkhairi.
Abban yadora kansa a kujerar da yake kai idonsa
na kallon sama ,sun samu shiru daga bisani yace
"Hakane sai na dawo. yaja motar ita kuma
tadawo ciki.
Tace "Fatima ku ci abinci kutafi gida ku huta don
Allah ki daina yawaita wannan kukan ba zai yi
mana maganin komi ba sai addu'a da hakuri.
Cikin shashekar kukan tace "ni kam mama a
idanuwa na ba za su taba daina zubar da hawaye
ba sbda tashin hankalin da take ciki.
Mama tace "kiyi hakuri fatima kada ki ja abin da
za ki bata da iyayanki bayan a baya kuna zaune
lfya kullum inna tana yabon halayyarki, iyaye suna
da kima sosai a gun dansu in dai da yana son a
gama da duniya lfya to yabi iyayansa, na
tabbatar ba za su so ace ba ayi auranki da
musbahu ba sbda shi ne xabinsu, hakan ba yana
nufin suna kin khalifa ba, idan muka ce iyayanki
ba sa son khalifa ba muyi musu adalci ba
tundamuna sane da yadda al'amuran suke.
Fatima duk da cewa ni na haifi khalifa na fi kowa
jin ciwon da tashin hankali halin nan dayake ciki,
idan a son raina ne izuwa yanzu yakasance kina
dakin khalifa a matsayin matarsa sbda son da
yake miki kowa ya san bashi dawani farin ciki
wanda yawuce ya mallae ki, yanayi ne wanda
kowa yasan khalifa bai taba samun kansa a ciki
ba, ai wannan dalilin ne yasa kowa yake tabbatar
da son da yake miki na gskiya tun yana fada da
baki har gashi yau a gadon asibiti bai san waye a
kansa ba, to amma duk da haka ba zan rufe ido a
kan abinda ba ma gskiya da adalci ba na hakura
na zubawa sarautar Allah ido idan Allah ya yi
khalifa zai rayi zai tashi, ni dai na san rayuwa
cike take da jarabbawa iri iri, komi lokaci gare shi
duk yadda tsanani ya tsananta insha Allahu
akwai sauki da zai biyo bayansa, a ckin alkur'ani
mai girma ma Allah (SWT) yana fadin, dukkan
tsanani suna tare da sauki.
A wannan lokacin fatima dora kanta tayi bisa
cinyar mama tana kuka har sai da hawayenta
suka jikawa mama zaninta, lamarin dayasa itama
mama takama sharar da kwallah duk kokarin data
dinga yi gun hadiye hawayenta tun safe abin ya
ci tura, wannan karon kuka take sosai, sai anty
sadiya da ummi ke basu hakuri.
Mutmryar khalifa tasa suka mike gaba daya a
rude suna kallonsa, idonsa yabude yana fadin
"Lahaula wala kuwwata illa billahil azim.
Gaba daya suka iso kanaa suna masa sannu.
Bai fahimci a inda yake b kansa a rude yake don
haka yamaida idonsa yarufe, rudewa tasa Fatima
ta manta tana tare da mahaifiyar khalifa takamo
hannun khalifa tana fadin "Don Allah katashi daga
barcin nan ya isa haka.
Kamar a mafarki yake jin muryar fatima, sai yayi
saurin bude idonsa, ai kuwa fatin ce a kansa ya
zuba mata ido har yanzu dai a tunanin sa
rayuwar mafarki yake, yace "Fatima.
Ta amsa "Na'am khalifa.
Ya matse hannunta yace don Allah fatima kada ki
auri wani ba ni ba mutuwa zanyi idan na rasaki,
mafarki nayi wai na ga katin daurin auranki
fatima bai dace ki yi min haka ba ko so ki ke in
mutu? Ni kadai iyayena suka haifa, ko su ya dace
ki tausaya wa.
Fatima tarufe me baki tace "ka kwantar da
hankalin ka insha Allahu za ka mallakeni kasan
nima ina sonka.
Bayan khalifa ya yi sallolin dake kansa yana
zaune kan darduma fatima thada mai ruwan
shayi shi kadai yace zai iya sha gaba daya jikinsa
yayi sanyi kallon kowa yake kadan kadan yake
iya bude idonsa, kowa yazamo dan kallo, fatima
ce ke da bakin magana a gun, shayin ma ita ta
matsa masa tace sai ya sha gudun kada tayi
masa hushi yasa ya hakura zai sha, amma bbu
abunda yake sha'awa.
Kofar dakin tabude, abba da malam musa mahain
fatima da musbahu da inna suka shigo.
Fati tatashi zumbur daga gaban khalifa domin
zaune take sosai a gaban na sa tana rokon ya
daure ya dan ci abinci ko kadan ne, kunya ce
takamata sosai musamman ganin kallon da
iyayanta ke mata duka fuskokin su ba walwala,
ballantana musbahu wanda yake jin kamar ita
kanta fatin ya shaketa kowa yahuta.
Bayan sun gama gaisawa da tambayar jikin
khalifa, musbahu yadubi malam da Abba yace
"Don Allah ku yi hakan baba a kawo karshen
wannan damuwar a yau, har abada hankalina ba
zai taba kwanciya ba idan ya kasance dan uwana
musulmi yana ckin damuwa a dalili na kuma zan
iya taimakawa gun magance masa damuwar.
Musbahu yayi shiru yakasa ci gaba da fadin abin
da yayi niyyar fadin sbda wani irin abu da yaji ya
tokare masa kirjinsa da makwagaronsa haka
bakinsa yayi masa nauyi idanuwa sun yi jawur,
dakin yayi tsit kowa kallon tausayi yakewa
musbahu sbda matsananciyar damuwar data
bayyana a fuskar sa.
Da kyar yaja dogon numfashi yaci gaba da fadin
"Baba na san ina son fatima har ga Allah ina jin
daci da ciwon rabuwa da ita amma ba yadda
zanyi kukan ya zame mini dole sbda in da baki
yakarkata nan yawu ke zuba, in ji masu iya
magana, tun kafin mukawo ga wannan halin na
tabbatar wa zuciyata fatima khalifa take so, na
auna abubuwa dayawa na ga dai hankalinta ya
karkata akai wannan ne yasa na tilasta kaina
nabar masa ita, na barwa khalifa fatima don Allah
baba ku ma kuyi hakuri ku ba shi ita, ku dubi
yanayin dasuke ciki ku kauda tunanin komi mu
kaddara haka Allah yanufa, wannan rana da aka
sa za a daura mana aure da fatima a daura da
khalifa ina fatan Allah yasa haka shi yafi alheri
gare mu gaba daya.
Mama tadaga mai hannu tace "gaskiyar magana
ba za ayi haka ba musbahu, tun yaushe kake son
fatima, tun yaushe aka ma alkawarin an ba ka
ita, amma lokaci daya a rufe ido a yi maka kwace,
wane irin kallo mutane za suyi mana knan?
fassarar da kowa zai mana ita ce ta rashin
adalci, khalifa ne zai yi hakuri da fatima.
Musbahu yayi murmushi tare da girgiza kai yace
"mu wuce wannan gun mama tunda har fatima ta
amince khalifa take so shi yadace a aura mata,
ita diya mace in har ana son a zauna lfya da ita a
bata wanda take so.
Ya kasa ci gaba da maganar sbda wani abu
dayake jin yana tokare masa makoshi, kirjinsa
yana mai nauyi gudun kada suga hawayansa
yatashi yafice daga dakin yanufi hanyar fita daga
asibitin cikin sauri yasamu wata hanya a bayan
asibitin yashiga yazauna a kasa yajingina dawata
katanga yahada kai da guiwa yana ajiyar zuciya,
a lokacin ne yasaki hawayen da yake ta boyewa
yakama kuka mai ciwo da karfi, hannunsa daya
dafe da kansa, kai da ganinsa ka san yana ckin
tashin hnkali mai yawa da damuwa, tabbas yau
ya san ya rasa fatima ya rasa yarinyar daya ke
matukar so so mai yawan gaske, yarinyar da bai
taba hadata da wata diya mace ba ballantana
yakalli wata da sunan so bayan ita ba, hakika ba
ka sanin kana son abu sai sanda karasa shi,
wannan ciwon dayake ji a ransa ya san har ya
mutu ba zai barshi ba, amma wajibi yayi hakuri
fatima ba ta son shi abinda yayi shi yafi masa.
A DAREN FARKO
30
A wannan rana aka sallami dr. khalifa daga asibiti
duk da ba jin sauki yayi ba ko a ganin ido idan ka
dubeshi ka san yana fama da ciwo irin na zuci
wanda fuska ke bayynar da shi, bbu wanda ya
samu bakin tattauna wata magana sai da suka
dawo gida gaba daya.
Jikin fati a sanyaye ta bi iyayanta zuwa gdansu
gaba daya a razane take domin fuskokin iyayanta
sun nuna mata akwai babbar magana wadda ba
za ta taba yi mata dadi ba, ta zauna lakwas a
rumfar inna tana jiran abinda za ace mata
musamman ganin yadda malam musa yazauna
ya lankwashe kafafu yace "fatima ai kamata yayi
tunda kin zabi khalifa sai ki koma gdansu da
zama a yi bikin na ku a can ko?
Inna tace "Ni ma haka na gani malam.
fatim tace "Don Allah baba kuyi hakuri kada kuyi
fushi dani, ba ni nace musbahu yafurta ya hakura
dani ya barwa khalifa ba shi yayi niyyar kansa.
Inna tace "ke da Allah rufewa mutane baki waye
sa'anki a nan da za ki zo mana da wannan
maganar ta bnza da wofi, da ace ba ki nuna
ra'ayin khalifa kike ba musbahun zai fadi haka,
misbahu ya san ciwon kansa kuma yana kishin
kansa dole yace ya hakura domin ba zai zauna a
walakanta shi a banza ba.
Malam yabude baki zai yi magana wani kanin
fatima me suna ibrahim yashigo yashaidawa
malam cewa ga abba can a waje yace yana son
ganinsa.
Tsaki yayi yamike yafito, ya umurçi Abba daya
shigo zaure, ibrahim yadebo kujerun zama na roba
suka zauna suka ka ra gaisawa.
Alhaju mahammadu yace "malam na yi wa khalifa
iyakar nasihar dazan masa Alhamdulillahi kuma
ya fahimceni ya amince da nasihata ya hakura da
fatima, na yi hakane sbda dogon nazarin da nayi
a kan al'amarin don Allah malam kuyi hakuri kada
kuyi fushi da fatima, fushin iyaye ba ya taba
gyara sai illa, a bata goma daya bata gyaru ba,
idan kukayi fushi da fatima al'amarin ne gaba
daya zai lalace ba za asamu mafita ba, idan dai
za muyi hakuri mu klli rayuwar yadda take tafiya
cikin yaran bbu wanda yake da lifi face haka Allah
yakaddara, kowane mutum da Allah ya halicce shi
yarubuta abinda zai faru dashi a rayuwarsa kuma
babu wanda zai kaucewa wannan kaddarar tasa.
Kan malam na kasa nauyin maganar Abba sun
masa nauyi aka har sai da yaji kunya ta kama shi
sosai wato Abba ya fahimci ba sa son ba wa
khalifa auran fatima shi yasa yadanne damuwarsa
duk yadda yake son khalifa ya auri fatima ya
hakura, ko kusa bai cancanta suyi wa Alhaji
muhammadu haka ba duk yadda mutumin kirki
yake mai son mutane da kula da hakkin makotaka
yakai Alhaji sai son barka yana samun yabo a
bakunan mutanan unguwar, su kam alhaji babu
abunda bai yi musu ba ko kusa bai cancanta suki
dansa ba.
Ya daga ki yace "Don Allah alhaji kar kayi
tsammanim hana khalifa fatima nake son yi.
Abba ya katse shi da sauri yace "wallahi ba haka
nake nufi ba, ko a baya damuwar da khalifa ke
ciki tasa idona yarufe na shagala daga baya nayi
nazari na sawa zuciyata hakuri.
Malam yace "Alhaji na gamsu da bayananka na yi
fatan Allah yasa haka shi yafi alheri garesu gaba
daya, na bawa khalifa fatima.
Abba yace "don Allah abba kada kayi hushi da ita
albarkar auran nan ake nema in dai kuna fushi da
fatima wannan albarkar ba samuwa za tayi ba.
Sai a lokacin xuciyar malam ta dan sassauta
daga damuwar da yake fama da ita, bayan tafiyar
Alhaji ya dawowa inna da bayanin abinda abin da
abba yazo mai dashi, inna tace "kai ni dai kam ba
zan fasa fadar cewa wannan abu bai yi min dadi
ba, to idan ma naboye ban bayyana a bakina ba
Allah na gani xuciya b dadi .
Malam yace "ba komi. mu barshi a haka Allah
yakaddara din mu yi fatan alheri ,fushi ba namu
bane. fushin mu ba zai yi maganin matsalar ba
face yakara jagula al'amarin, duk yadda zamuyi
ba za mu ba musbahu fatima ba tunda Allah bai
kaddara matarsa bace.
Tace "to malam yanzu ina musbahun?
Yace "Ni tunda yafita daga asivitin nan ban kara
ganinsa ba, ban san ina yayi ba wayarsa ma
gashi a kashe take tun da muka dawo banganshi
ba nake ta kiranta bata shiga ba.
Inna tayi tsaki tace "Duk fatima ce taja tun farko
in da bata ba khalifa fuskar yaso ta ba zai so ta?
mutumin da ya san an yi masa baiko ina shi ina
kula wani namiji. Fatima ta ban mamaki Allah
malam wannan halayyar arota kawai tayi ba ta ta
bace, ina matukar jin kunyar yaron nan yagama
sawa ransa ba shi da mata sai ita lokaci guda
ace yarasa? haba ai abin da ciwo.
Fatima dai na daga dakinsu tana ji bata ji dadin
abubuwan a ranta amma soyayyar da takewa
khalifa tasa tashare komi in dai za ta samu cikar
burinta akan dr. khalifa xancen ya kare.
Yawan kuka datayi ya haifar mata da zazzabi da
ciwon kai, tasamu babban zani ta kudundune
kanta a ciki tana wasi wasi wayarta tafara ringing
ganin nomban khalifa yasa tadaga dasauri.
Muryarsa a sanyaye yace "Fatima me ki ke yi
yanzu?
Tace "A kwance nake zazzabi ne yarufeni.
Yace "Subhanallahi *in sha magani?
Tace "yanzu dai zan sha.
Yace "zan iya zuwa in ganki?
Tayi shiru, yace "ko akwai matsala?
Tace "Gani nayi ba ka da lfya.
Yace "na ji sauki tunda na sameki dama rasaki da
naga da gaske zanyi ne yaja min ciwo, lokacin
danaga wannan katin na tabbatar na rasaki sai
naji gaba daya duniya ta min kunci, abin cikinta
ma ya min kunci, hankalina ya tashi gaba daya
na kasa mallakar kaina, ,na yi kokarin in daure
damuwa ta ta kai matakin data kai amma da
yake ba ni ne nasa kaina a damuwar ba hakan bai
yiwu ba gareni dole sai da kowa ya fahimci
matsalata da farko na yi zaton mfarki nake ashe
gskia ne don Allah fatima ki nemar mini iso gun
inna da malam su amince in ganki zuciyata ba ta
da juriya a kanki ba zan iya jurewa rashin ganin
ki ba.
Fati ta runtse ido tabude tace "Ba komi kazo
gdan kuma zan fito zaure kaganni.
*****
A gdansu Dr. khalifa xanceb da ake ta nanatawa
knan za a daura auran khalifa da fatima nan da
kwana biyu masu zuwa, reshe ya juye da mujiya
,nan da nan Abba yashiga kiran abokansa da yan
uwa a waya yana shaida musu batun daurin
auran dan lelen dansa biki daisai bayan sati daya
domin ba abu ne na wasa a tare dasu ba, auran
khalifa abin alfahari ne a tare dasu sai kowa
yasan ana yi, mama ce dai bata nuna farin cikinta
sosai sbda ta tsani abinda za ace ta yi son kai
ko son zuciya wanda tabbas ta san sai an
fada,anty sadiya tai ta tsaki a ranta.
Ko yushe tananuna mata cewa aure nufi ne na
Allah babu wanda za ya auri matar wani, Allah
yayi fatima matar dr. khalifa ce dole shi zai auri
matarsa, surutun mutane ba karewa yake ba duk
yadda kaso da taka tsantsan dinka sai an yi
surutun, idan b a yi maka akan wani abin ba sai
an yi a wani abin shiyasa idan mutum yagane to
yasa*i ransa yayi komi kansa tsaye kawai
yahuta, mutum ya fuskanci Allah a cikin
al'amarinsa to karya damu da surutun mutane.
Mama tace "kai sadiya duk fa yadda za ki kare
abin nan ba zan fasa cewa Khalifa yayi son kai
ba.
Tace "to mama shi yace sai an ba shi ta karfin
tiya? muna zaune fa aka ce an bashi to sai ya ki
karba don kada mutane su ce ya yi son kai?
A bisa dole mama tahakura don bata samu goyon
baya ba ta kowanne fannin, dayake harka ce ta
masu kudi duk da kasancewar baa gayawa yan
uwa ba tun auran da wuri ba amma daga lokacin
da aka fara bada sanarwar daurin auran gdan
yafara cika da mutane maza da mata yan taya
murna.
Ummi tana gdansu tun lokacin da dr. khalifa
yafito daga asibiti ta tabbatar za a yi auransa da
fatima ta karasa rikicewa hankalinta a tashe
tajewa hjiyarta da labarin, ta bayyana mata duk
yadda abubuwan suka faru tace "Hajiya mama da
abba babu abunda suke sosai farin cikin dansu,
Abba da kansa yaje ya sanar da mahaifin fatima
halin da dansa ke ciki a kan yarsu, suka taho
asibitin da niyyar dubashi lamarin dayasa musbhu
yace ya barwa khalifa fatima sun manta ina son
khalifa tun kafin yaso fatima, bbu wnda yadamu
da hlin danake ciki ana nan an fara shirye shiryen
auran gadan gadan.
Hajiya tashare mata hawaye tace "Daina kuka
ummi in dai ina raye a gdan duniya nan zanyi
miki maganin damuwarki, ba zan taba cewa
kidaina son khalifa ba don ita zuciya ba a rabata
da abinda take so a zauna lfya, idan har muka
hakura da khalifa to mata muka rako duniya,
wannan dogon lokacin damuka dauka muna
nemansa ba zai tashi a banza ba, tashi mu koma
gun malam.
Ummi tadanyi jim sannan tace "hajiya bai dace
mucigaba da wahalar da kammu a gun zuwa
gdan mlami ba da wahala idan hakan zai amfanar
damu tun da a baya bai mana amfanin kmi ba.
Hajiya tafiddo ido tace "ke saurara nsara a hankli
samunta idan lokacin samuwarta ya zo za kiyi
mamakin aikin malam, ke de muje muji ta
bakinsa, motsi ai yafi labewa, bari in karasa
miyar can yunwa nake ji.A DAREN FARKO
30
A wannan rana aka sallami dr. khalifa daga asibiti
duk da ba jin sauki yayi ba ko a ganin ido idan ka
dubeshi ka san yana fama da ciwo irin na zuci
wanda fuska ke bayynar da shi, bbu wanda ya
samu bakin tattauna wata magana sai da suka
dawo gida gaba daya.
Jikin fati a sanyaye ta bi iyayanta zuwa gdansu
gaba daya a razane take domin fuskokin iyayanta
sun nuna mata akwai babbar magana wadda ba
za ta taba yi mata dadi ba, ta zauna lakwas a
rumfar inna tana jiran abinda za ace mata
musamman ganin yadda malam musa yazauna
ya lankwashe kafafu yace "fatima ai kamata yayi
tunda kin zabi khalifa sai ki koma gdansu da
zama a yi bikin na ku a can ko?
Inna tace "Ni ma haka na gani malam.
fatim tace "Don Allah baba kuyi hakuri kada kuyi
fushi dani, ba ni nace musbahu yafurta ya hakura
dani ya barwa khalifa ba shi yayi niyyar kansa.
Inna tace "ke da Allah rufewa mutane baki waye
sa'anki a nan da za ki zo mana da wannan
maganar ta bnza da wofi, da ace ba ki nuna
ra'ayin khalifa kike ba musbahun zai fadi haka,
misbahu ya san ciwon kansa kuma yana kishin
kansa dole yace ya hakura domin ba zai zauna a
walakanta shi a banza ba.
Malam yabude baki zai yi magana wani kanin
fatima me suna ibrahim yashigo yashaidawa
malam cewa ga abba can a waje yace yana son
ganinsa.
Tsaki yayi yamike yafito, ya umurçi Abba daya
shigo zaure, ibrahim yadebo kujerun zama na roba
suka zauna suka ka ra gaisawa.
Alhaju mahammadu yace "malam na yi wa khalifa
iyakar nasihar dazan masa Alhamdulillahi kuma
ya fahimceni ya amince da nasihata ya hakura da
fatima, na yi hakane sbda dogon nazarin da nayi
a kan al'amarin don Allah malam kuyi hakuri kada
kuyi fushi da fatima, fushin iyaye ba ya taba
gyara sai illa, a bata goma daya bata gyaru ba,
idan kukayi fushi da fatima al'amarin ne gaba
daya zai lalace ba za asamu mafita ba, idan dai
za muyi hakuri mu klli rayuwar yadda take tafiya
cikin yaran bbu wanda yake da lifi face haka Allah
yakaddara, kowane mutum da Allah ya halicce shi
yarubuta abinda zai faru dashi a rayuwarsa kuma
babu wanda zai kaucewa wannan kaddarar tasa.
Kan malam na kasa nauyin maganar Abba sun
masa nauyi aka har sai da yaji kunya ta kama shi
sosai wato Abba ya fahimci ba sa son ba wa
khalifa auran fatima shi yasa yadanne damuwarsa
duk yadda yake son khalifa ya auri fatima ya
hakura, ko kusa bai cancanta suyi wa Alhaji
muhammadu haka ba duk yadda mutumin kirki
yake mai son mutane da kula da hakkin makotaka
yakai Alhaji sai son barka yana samun yabo a
bakunan mutanan unguwar, su kam alhaji babu
abunda bai yi musu ba ko kusa bai cancanta suki
dansa ba.
Ya daga ki yace "Don Allah alhaji kar kayi
tsammanim hana khalifa fatima nake son yi.
Abba ya katse shi da sauri yace "wallahi ba haka
nake nufi ba, ko a baya damuwar da khalifa ke
ciki tasa idona yarufe na shagala daga baya nayi
nazari na sawa zuciyata hakuri.
Malam yace "Alhaji na gamsu da bayananka na yi
fatan Allah yasa haka shi yafi alheri garesu gaba
daya, na bawa khalifa fatima.
Abba yace "don Allah abba kada kayi hushi da ita
albarkar auran nan ake nema in dai kuna fushi da
fatima wannan albarkar ba samuwa za tayi ba.
Sai a lokacin xuciyar malam ta dan sassauta
daga damuwar da yake fama da ita, bayan tafiyar
Alhaji ya dawowa inna da bayanin abinda abin da
abba yazo mai dashi, inna tace "kai ni dai kam ba
zan fasa fadar cewa wannan abu bai yi min dadi
ba, to idan ma naboye ban bayyana a bakina ba
Allah na gani xuciya b dadi .
Malam yace "ba komi. mu barshi a haka Allah
yakaddara din mu yi fatan alheri ,fushi ba namu
bane. fushin mu ba zai yi maganin matsalar ba
face yakara jagula al'amarin, duk yadda zamuyi
ba za mu ba musbahu fatima ba tunda Allah bai
kaddara matarsa bace.
Tace "to malam yanzu ina musbahun?
Yace "Ni tunda yafita daga asivitin nan ban kara
ganinsa ba, ban san ina yayi ba wayarsa ma
gashi a kashe take tun da muka dawo banganshi
ba nake ta kiranta bata shiga ba.
Inna tayi tsaki tace "Duk fatima ce taja tun farko
in da bata ba khalifa fuskar yaso ta ba zai so ta?
mutumin da ya san an yi masa baiko ina shi ina
kula wani namiji. Fatima ta ban mamaki Allah
malam wannan halayyar arota kawai tayi ba ta ta
bace, ina matukar jin kunyar yaron nan yagama
sawa ransa ba shi da mata sai ita lokaci guda
ace yarasa? haba ai abin da ciwo.
Fatima dai na daga dakinsu tana ji bata ji dadin
abubuwan a ranta amma soyayyar da takewa
khalifa tasa tashare komi in dai za ta samu cikar
burinta akan dr. khalifa xancen ya kare.
Yawan kuka datayi ya haifar mata da zazzabi da
ciwon kai, tasamu babban zani ta kudundune
kanta a ciki tana wasi wasi wayarta tafara ringing
ganin nomban khalifa yasa tadaga dasauri.
Muryarsa a sanyaye yace "Fatima me ki ke yi
yanzu?
Tace "A kwance nake zazzabi ne yarufeni.
Yace "Subhanallahi *in sha magani?
Tace "yanzu dai zan sha.
Yace "zan iya zuwa in ganki?
Tayi shiru, yace "ko akwai matsala?
Tace "Gani nayi ba ka da lfya.
Yace "na ji sauki tunda na sameki dama rasaki da
naga da gaske zanyi ne yaja min ciwo, lokacin
danaga wannan katin na tabbatar na rasaki sai
naji gaba daya duniya ta min kunci, abin cikinta
ma ya min kunci, hankalina ya tashi gaba daya
na kasa mallakar kaina, ,na yi kokarin in daure
damuwa ta ta kai matakin data kai amma da
yake ba ni ne nasa kaina a damuwar ba hakan bai
yiwu ba gareni dole sai da kowa ya fahimci
matsalata da farko na yi zaton mfarki nake ashe
gskia ne don Allah fatima ki nemar mini iso gun
inna da malam su amince in ganki zuciyata ba ta
da juriya a kanki ba zan iya jurewa rashin ganin
ki ba.
Fati ta runtse ido tabude tace "Ba komi kazo
gdan kuma zan fito zaure kaganni.
*****
A gdansu Dr. khalifa xanceb da ake ta nanatawa
knan za a daura auran khalifa da fatima nan da
kwana biyu masu zuwa, reshe ya juye da mujiya
,nan da nan Abba yashiga kiran abokansa da yan
uwa a waya yana shaida musu batun daurin
auran dan lelen dansa biki daisai bayan sati daya
domin ba abu ne na wasa a tare dasu ba, auran
khalifa abin alfahari ne a tare dasu sai kowa
yasan ana yi, mama ce dai bata nuna farin cikinta
sosai sbda ta tsani abinda za ace ta yi son kai
ko son zuciya wanda tabbas ta san sai an
fada,anty sadiya tai ta tsaki a ranta.
Ko yushe tananuna mata cewa aure nufi ne na
Allah babu wanda za ya auri matar wani, Allah
yayi fatima matar dr. khalifa ce dole shi zai auri
matarsa, surutun mutane ba karewa yake ba duk
yadda kaso da taka tsantsan dinka sai an yi
surutun, idan b a yi maka akan wani abin ba sai
an yi a wani abin shiyasa idan mutum yagane to
yasa*i ransa yayi komi kansa tsaye kawai
yahuta, mutum ya fuskanci Allah a cikin
al'amarinsa to karya damu da surutun mutane.
Mama tace "kai sadiya duk fa yadda za ki kare
abin nan ba zan fasa cewa Khalifa yayi son kai
ba.
Tace "to mama shi yace sai an ba shi ta karfin
tiya? muna zaune fa aka ce an bashi to sai ya ki
karba don kada mutane su ce ya yi son kai?
A bisa dole mama tahakura don bata samu goyon
baya ba ta kowanne fannin, dayake harka ce ta
masu kudi duk da kasancewar baa gayawa yan
uwa ba tun auran da wuri ba amma daga lokacin
da aka fara bada sanarwar daurin auran gdan
yafara cika da mutane maza da mata yan taya
murna.
Ummi tana gdansu tun lokacin da dr. khalifa
yafito daga asibiti ta tabbatar za a yi auransa da
fatima ta karasa rikicewa hankalinta a tashe
tajewa hjiyarta da labarin, ta bayyana mata duk
yadda abubuwan suka faru tace "Hajiya mama da
abba babu abunda suke sosai farin cikin dansu,
Abba da kansa yaje ya sanar da mahaifin fatima
halin da dansa ke ciki a kan yarsu, suka taho
asibitin da niyyar dubashi lamarin dayasa musbhu
yace ya barwa khalifa fatima sun manta ina son
khalifa tun kafin yaso fatima, bbu wnda yadamu
da hlin danake ciki ana nan an fara shirye shiryen
auran gadan gadan.
Hajiya tashare mata hawaye tace "Daina kuka
ummi in dai ina raye a gdan duniya nan zanyi
miki maganin damuwarki, ba zan taba cewa
kidaina son khalifa ba don ita zuciya ba a rabata
da abinda take so a zauna lfya, idan har muka
hakura da khalifa to mata muka rako duniya,
wannan dogon lokacin damuka dauka muna
nemansa ba zai tashi a banza ba, tashi mu koma
gun malam.
Ummi tadanyi jim sannan tace "hajiya bai dace
mucigaba da wahalar da kammu a gun zuwa
gdan mlami ba da wahala idan hakan zai amfanar
damu tun da a baya bai mana amfanin kmi ba.
Hajiya tafiddo ido tace "ke saurara nsara a hankli
samunta idan lokacin samuwarta ya zo za kiyi
mamakin aikin malam, ke de muje muji ta
bakinsa, motsi ai yafi labewa, bari in karasa
miyar can yunwa nake ji.
Ummi tace "ni don haushi ma ko yunwa ba ta
damuna. ina mamakin son kan da ake nunawa
kowa akan khalifa amma ta watsar da komi ta
kanta kawai take ko kunyar idona ba ta ji.
Hajiya tace "duk ki kyalesu son zuciya bacinta da
sannu dukka za sugane kurensu.
Ummi ta tashi tashige dakin hajiya ta tsaya a
gaban madubi tana karewa kanta kallo tare da
tuno siffofin fatima a idanuwanta tajinjina kai tare
da ajiyar zuciya tace "ba komi.
Sai bayan sallar isha'i suka isa gdan malam
shima yana mamakin ganinsu a wannan lokacin
ya san ba lfya. suka baje masa bayanin komi.
Unmi ta marairaice tace "Don Allah malam
kataimakeni xan rayu ckin bakin ciki mai tsanani
idan narasa dr. khalifa dole in yi kishin fatima
domin ta san sirrina ta san abinda ke ckin
zuciyata, ko zan hakura dr. khalifa yarayu da
wata diya mace ba dai fatima ba, na amince in
rasa shi amma kada wata ta mallake shi.
Malam yabushe da dariya yaja ra'ayinsu ya fara
zane zane yana bajewa lokaci mai tsawo suna
kallonsa sannan yadago kai ya dubesu yace
"haba ko da naji ai uwar Khalifa ce tashiga
malamai aka tsare mata jikin khalifa don kada
wata macen tasamu damar asirce shi ta rabata
da shi, tunda tasan yammata za su so shi da
yawa ita kanta fatiman don soyayyar da yake
mata ta ra'ayin kansa ce shi yasa duk ayyukan
da muke jifansa dasu ba su tasiri akansa, to
amma ba komi akwai aljanin da zamu hada shi
da shi sai yayi tasiri a kansu shi da fatiman kuna
zaune za kuga ya tsaneta hankalinsa ya dawo
kan ummin, amma sai an sayi sa babba wanda
za a yanka shi a yi aikin a kan sa aiki irin
wannan karfi gareshi sai an yi yanka.
Ganin sun yi jim yasa yaci gaba dayi musu dadin
baki tare da kwadaitar dasu amfanin aikin idan an
yi, yace "wa kukaga ya ji dadi ba tare da ya sha
wahala ba, duk wadannan abubuwan tarihi za su
zama idan Khalifa yazo hannu sai ya baku
tausayi ku dai ku daure.
Suka dawo gida suna tattauna yadda za su nemo
kudin sa, sun yi ammana aikin malam zaici, ummi
tace "Hajiya dole ne in saki jiki wurin gudanar da
al'amarin bikin nan xan nuna kamar bbu wani avu
a zuciyata xa ayi komi dani, amfanin hakan shi ne
dan in samu kudin da za muyi amfani dasu.
Hajiya tace "Lallai kin zo da dabara, idan har kika
nunawa khalifa cewa kina son auran sa da fatima
komi za musamu a jikinsa da abbansa, kin ga
knan mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya.
A DAREN FARKO
31
Ana ya gove daurin auren fatima da khalifa
wasikar musbahu ta iske mallam inda yake
shaida masa cewa kada su daga hankalinsu a
dalilin rashin ganinsa ya kauracewa gdan ne don
ya samar da zaman lfya da walwala yayin bikin
fatima, a cikin wasikar yace.
"Malam idan naci gaba da zama kana ganin
damuwata za ku dinga jin zafin fatima yayin da ni
kuma zuciyata ba za ta taba yi min dadi ba in dai
yakasance kuna jin ahushin fatima a sbda ni da
ace da ace zan iya shanye damuwata da zan
dawo amma hakan hakan ba zai yiwu gareni ba,
zuciyata ba ta da wannan karfin. Baba da inna
ina rokon ku yi hakuri don Allah ku dauki wannan
al'amarin a matsayin kaddara kada kuyi fushi da
fatima, fushinku matsala ce babba ga rayuwarta
ina nan ina ta mata fatan alheri, insha Allahu da
zarar an gama bikin an kaita gdanta zan dawo.
Sun ji tausayin al'amarin kwarai da gaske sai dai
ba yadda za suyi al'amarin kaddarar nan dai da
kowa ke fada itace dole ayi hakuri a karbeta,
surutun da ake gudu shi ake tayi a cikin unguwa
da dangi, kwadayi kwadayin abin duniya shi ake
tafada musamman lokacin da sanarwar daurin
auran ta cika gari ta hanyar kafafan yada labarai
dake arewacin kasar nan ba ma nan kano kadai
ba tare da sanarwar za ayi gagarumar wlima
bayan daurin auren da yamma amma na maza
zalla,tuni aka cikawa malam gdansa da nau'ikan
kayan abinci na alfarma wanda za ayi amfani
dasu a gun bikin, hatta nama kala kala aka kawo,
kayan da amarya za tasa lokacin biki mama da
anty sadiya suka tsara mata su gun kwararrun
telolinsu dake tsara musu dinki, kaya ne msu
tsadar gaske haka dinkunan sun sha kudi amma
fa sunyi kyau sun dace da amaryar, kayan lefene
suka ce sai an gama hidimar daurin aure ango da
amaryar za su tafi da kanta za ta xabi irin kayan
da take so da kanta.
Anty sadiya ta hurawa mama wuta akan lallai su
za su gyara amarya tun daga kan fatarta da
abubuwan da ake sha masu kawo ni'ima ga
amarya, mama tarike baki tace "sadiya wannan ai
na su ne na iyayanta da yan uwanta ina dangin
miji ina gyaran amarya.
Sadiya tace "Tabdijam ai kuwa mama anan ne
ma yadace ki yi gyaran da hujja, me yasa kikayi
mata a baya lokacin da za ta auri musbahu, kika
gyara don dan wani ma ballantana na mu, ai ajiye
kunya za muyi mi tattalin farin cikin danmu
zamanin duhun kai ya wuce ina innarta za ta iya
irin wannan abub tana fama da kunya.
Mama tayi dogon tunani taga gaskiyar fa sadiya
barin kashi a ciki bai maganin yunwa, musamman
yadda taga khalifa yana cike da tsananin farin
cikin auran daya samu ko kawaici bai iya yi.
Lokacin da ummi ta iso gdan da safe tashaida
mata cewr tana son tadan yi dabarar da dan ja
hankalin fatima tadawo gdan nan tazauna a yau,
duk abinda aka fada akan fati sai ummi ta ji
tsigar jikinta ya tashi, sai dai bata bari a fahimci
damuwarta ta saki ranta sosai, a wannan lokacin
ma fadada fara'arta tayi tace "Ba damuwa mama
ai ke ce uwar amarya uwar ango mu kuma mune
kirjin biki.
Bayan sun gama cin abinci tanifi gdansu fatiman
ta iske su ita da ango dr. khalifa a soron gdan
suna hira, tarike baki tana murmushi tace "to ai
dai aski ya zo gaban goshi yaya khalifa meye na
mannewa anan?
Ni na dauka ma ka fita.
Ya bata rai yana harararta yace "ke wai ni abokin
wasanki ne xan dauki mataki akanki idan baki
shiga taitayinki ba.
Tace "a'a yi hakuri kamaida wukar ni dai
katayamu murna Allah yasa rakiya tayi nisa.
Suka bushe da dariya gaba daya ita da fatiman
tawuce cikin gida tana fadin "Bari mugaisa da
inna kafin kugama.
Khalifa ya matso kusa da fatima yana dan
rausayar da kai fuskarsa dauke da murmushi
yace "Wallahi fatima har na rasa wacce hanya
zan nuna miki soyayya duk abin da nayi miki don
in tabbatar maki da soyayya sai in ga ya yi kadan
matsayinki ya wuce nan.
Ta kwantar da kanta a jikin bango tana kallonsa,
shadda ce a jikinsa ruwan kwai, iya guiwa rigar
ta tsaya masa ta dan matse me jiki, fuskar nan
fes fes tamkar kullum kyau ake kara masa, bbu
wani da namiji da fatima take tsayawa tamasa
kallon kurilla sai jan gwarzanta Abbubakar saddik,
sbda ahi take kallo taji sanyi a ranta, duk
damuwar datake ciki in dai za taga khalifa sai taji
sanyi a ranta kuma sai taji lallai ta gamsu ta ga
da namiji cikakke wanda in dai ka kalleshi ka san
ka ga da namiji.
Khalifa yaci gaba da fadin "Fatima Allah ne yayi
ke rabona ce shi yasa nadawo gida a dai dai
wanna lkacin, godiya nakewa Allah daya ba ni ke,
domin da na rasaki ban san halin dazan samu
kaina ba fatima.
Wani irin kallo take masa tana dan lumshe ido
tana budewa tare da marairaice fuskarta domin
za tayi kuka, lamarin daya dagawa dr. khalifa
hankali sosai yakasa rike kansa yakara matsowa
daf da jikinta yakai bakinsa kunanta yace "Don
Allah fatima zo mu shiga dakin nan in dan ji
dumin jikinki zuciyata za ta fashe yanzu.
Tayi wal da ido ta waiwaya gaba da baya ba
kowa.
Ko me yasa bata iya musu da dr. Khalifa tana
sane dacewa bukatarsa gareta bata dace ba
amma ba za ta iya kaucewa abin da yake so ba,
sai kawai tabishi suka shiga dakin musbahu
wanda yake zauran gdan, dasauri ya rungumota
sannan yayi ajiyar zuciya mai karfi yayi mata
kiss, ya saketa yace "to zo ki shiga gida.
Mamaki yasa ta tsaya galala tana kallonsa,
yakama dariya yace "ai dama ba wani abu mai
yawa zan miki ba soyayya ce ta yi mini yawa, shi
yasa idan idan ina gabanki bana iya jurewa, ki yi
hakuri daga gobe idan Allah yakaimu na zamo
mijinki za ki ga abubuwa da dama a tare dani,
kada kidamu soyayya ce wadda za takasance
abar alfahari gareki, sai kinyi tsammanin kin fi
kowace mace sa'a a duniya, zan tabbatar miki ina
sonki, zan baki kaina kiyi yadda kika ga dama
dani fatana dai kiji tsoron Allah, kiyi min adalci
kada kiyi amfani da wannan damar ki wahal dani,
kiyi hakuri mu zauna lfya shi ne kadai abinda zai
sa in samu farin ckin rayuwata.
Babu abinda fati ke iya ce masa sai kallo da ido,
abubuwan datake ji game dashi a zuciyarta ya fi
karfin ta iya fda masa da baki sai dai tabarwa
zuciyarta, ita dai ta san tana son dr. khalifa kuma
in dai haka soyayya take hakika masoya suna
fama da wahala, meye wahala? wahalar ciwon so
daban ba kamar kowacce wahala bace, in da
wahalar take shi ne in dai mutum bai ga wannan
masoyin na sa ba to zuciyarsa na cikin fitina da
garari.
Yarike hannunta kam kam yayi mata kiss, sannan
ya saketa ya fice, ita kuma tashiga gida ta iske
ummi da inna suna hira.
A cikin daki ummi tadubi fatima tarike kugu tana
murmushi tace "amarsu ta ango in ji ko dai dr.
khalifa ya fara latsa jikin ki ne.?
Tafiddo ido tace "Ban son sharri ummi.
Itama ta tsareta da na ta idon tace "ke fatima
kada ki mayar dani yarinya karama mana daga
lokacin da soyayya ta tsumu a zuciyar mace
budurwa mai tashen kuruciya irinki har takai
namiji ya fata tabata sai ta sauya.
Duk da kyau da ki ke dashi a baya amma yanzu
kina da bambamci, idan ke baki san yanayin
jikinki ya sauya ba ni na san ya sauya.
Fatima taja doguwar ajiyar zuciya ta zauna gefe
tana kallon immi, takasa magana.
Ummi ta kyalkyale da dariya tana tafa hannuwa
tace "Daman akwai lokacin da za ki iya
soyayya ?
Tadan yi murmushi tace "Anty ummi ai dr.
khalifan ne ya isa a so shi ya hadu.
Ummi taji wani dam a jikinta da zuciyarta kamar
za ta shaki wuyar fatima tace "tashi ki shirya fita
zanyi a yi miki gyaran jiki mun dai makara jibi a
cigaba.
A kofar gdansu dr. khalifa, fatima ta kafe akan ba
za tashiga ba ita kunya take ji, ummi tace "ki
rufa wa kanki asiri idan mama taji kin ki shiga
fushi za tayi dake, idan ma kin sa wa zuciyarki
surukuta da kunyar mama to wahala za ki ba
kanki tunda kin san ita wayayyar mace ce bbu
ruwanta da irin wadannan abubuwan.
A harabar gdan suka ci karo da mama ta yowa
baki rakiya, bata amsa gaisuwar fatima ba sai
harararta datayi tace ke kin dauke kafarki daga
gdan nan wai ke suruka ko ?
Fatima ta sunkuyar da kai tana murmushi, ta
gayar da baki, tawuce ckin gda da sauri jin mama
tana fadama bakinta cewa wannan ce amaryar
khalifa.
Ai kuwa suka fara fadin "kai msha Allahu wannan
yarinya da kyau take ya more mace ga kyau ga
kuruciya.
Daya daga ckin bakin tace "to ai ta fishi morewa
a wannan zamanin samun namiji irin da na
khalifa sai an tona kinga kuwa mu za muyi yanga
va mu za a yiwa yanga ba, tunda duk inda danmu
yake rububinsa ake.
Bayan sun tafi mama tadawo ckin gida ta
samesu a falo tare da anty sadiya ,tace "yawwa
"yammata a zo a dafa ma abba abinci saura yan
mintuna kadan bakinsa su iso.
A ? ty sadia tace "mama munada abubuwa da
yawa da za muyi fa lokaci zai kure mana.
Tace "ai komi za ayi dole a tsaya a yiwa mai
gidana abinci in kuma ba haka ba a fasa fitar.
Ummi tace "tabdijam ai kuwa mama a yadda
muke ji da amaryar nan tamu yau ko tsakar dare
za mukai a gdan mai gyaran jikin nan xa mu kai,
mai kunshin ma daukarta za muyi mutafi da ita.
Mama tace "Lallai abin naku nayi ne sai ku kira
angon a waya yazo yabada kudin kunshin don
kuwa bbu wanda zai biya masa kudin kunshin
matarsa tunda don shi za a yin.
Anty sadiya tace "Eh ko zai bayar kema sai kin
bayar da wani abu mama kudin fa da yawa.
Tace 'Au tausayin khalifa kukeyi ni baku tausayi
na ? duk fa abubuwan nan da ake yi ko sisinsa
bai kashe ba hatta walimar nan da za ayi idan
allah yakaimu goben su dr. hafiz ne suka dauki
nauyi da wani abokinsa da sukayi karatu a jamus,
to ko nawa yabayar gun kunshi ai ba wani abu
ko ?
Ummi takirashi a wya tace "yaya kana ina ne ?
Yace "mun fita dasu dr. bashir.
Tace "To muna bukatar kudin kunshin amarya da
gyaran gashinta.
Yayi wani mur. ushi yace "Da kyau ummi idan har
aka yiwa amaryar nan tawa adon daya birgeni ni
nasan kyautar da zan miki ko nawa ne zan biya a
yi mata in dai zai yi kyau.
A DAREN FARKO
32
Ummi tayi dariya tace "yaya knan in dai batn
kyau ne yau za mukai amaryarka in da za ka
kasa gane ta sbda kyaun da za tayi.
Khalifa ya kyalkyale da dariyan da bata taba jin
ya yi ba yace "kia ina ja fa ummi amaryata fa me
kyau ce shi yasa na zabeta a cikin dubban mata
nace ita kadai zan aura sbda dogon nazari nayi a
kanta tun daga lokacin da idanuwa na suka fara
gani? ta.
Ummi ta cije lebe tare da runtse ido har wani
gumi taji yana tsiyayo mata sbda daci da ciwon
maganganun da khalifa yake yaba mata, ji take
kamar ruwan zafi ake watsa mata a jiki, shi yasa
nan take tajike da gumi, a hankali tace "yaya
khalifa wai don Allah me yasa kazabi fatima ka
fifita ta akan duk wata diya mace, har kabata
matsayi me girma a zuciyarka?
Yace "Ummi na ji dadin wannan tambayar da kika
yimin domin ina son in ji ina fadawa wanda
yashafi fatima matsayin fatiman a zuciyata don
yarinka karfafa mata xuciya tana sanin cewa
dagaske nake.
Ummi tace "to in banda abinka daman yaya
khalifa ai fatima ta san kana sonta ,yanayin
soyayyar dakake nuna mata ne ma yake karfafa
mata zuciya take kara sonka tare da sakin
zuciyarta ta yarda da son da kake mata, in ban
da haka fati za ta iya sanya shakku a zuciyarta
game da kai sbda yanayinka.
Khalifa ya dan tsuke fuska yace "sbda me kika ce
hka ummi? wannan magana ta ki ta ban mamaki
don Allah yi min karin bayani.
Tace "yaya khalifa a yanayin rayuwa irin na
fatima dole taji tsoron sakin jiki dakai idan tana
kallon yadda rayuwarka ke tafiya, kayi mata nisa
nesa ba kusa ba, amma dayake kana nuna mata
soyayya mai karfi ta yarda dakai ta amince akan
kana mata so na gskiya, ina ganin idan haka ne
ba ka da bukatar wanda zai ci gaba da nusar da
fati soyyarka gareta.
Khalifa yace "kuma hakane amma duk da haka
ina bukatar taimakon ku fatima yarinya ce.
Bayan sun yi sallama ummi ta ajiye wayar a gefe
tayi tagumi, wannan soyayyar da dr. khalifa kewa
fatima tana da yawa, fidda fati daga zuciyarsa
abu ne mai wahalar gaske, wace hanya za tabi
knan, ta ina za tasamu khalifa?
Duk kudin da suke kashewa a gun malamai abin
ya ci tura tamkar suna asirin karawa dr. khalifa
soyayyar fatima ne, aiki ne ja a gabanta tun da ta
tabbatar wa ranta ba za ta hakura tasa ido wata
diya macen ta mallaki khalifa ba in dai tana raye.
Tayi kwafa tamike tabi fatima da anty sadiya
inda suke girkin abincin Abba.
Suna ckin shirya tebur khalifa yashigo gdan cikin
sauri tare da dr. Bashir, kai tsaye suka wuce
tebur din wai dama yunwa sukeji, mama ta harare
su tace "ai duk yunwar ku ba za kuci wannan
abincin ba.
Khalifa yaduvi fatima zai yi magana mama tace
"oh za kace mini matarka ce tayi ko?
Yarufe baki yana dariya, fatima dai tabar dakin
dasauri tanufi dakin ummi suka yi sallar azahar
ummi tashigo musu da abinci suka ci a tsatsaye.
Kudin da dr. khalifa yaba ummi na gyaran jikin
amarya sai da suka firgita su sbda yawansu, ta yi
murna sosai domin abin nema ya samu a ranta
tace "ka ba da kudin da za a yaki soyayyar fati a
zuciyarka da sannu za kagane kuskurenka.
Mama ma tadada musu kudin tace su sayo duk
abu! uwan dasuke bukata har na su ma kansu ita
da anty sadiya.
Da yake lamari idan nakudi ne bbu matsala suna
zuwa gdan gyaran jikin aka watsar da kowa a ka
dukufa akan fatima babban guri ne kamar wata
ma'aikata, ayyuka sukeyi kala kala, cikin awa
biyu xuwa na uku fatima ta sauya gaba daya ta
dauki walwali abin ba acewa komi, anayi ana
turara mata jiki da turaren wuta masu kamshi mai
sanyi da shiga rai ga humra ana mulkawa.
Bayan an gama da nan aka zuba mata kamshi
kafa da hannu masu gyaran gashi na tsaye
sunayi fatima tazamo tamkar tauraruwa a cikin
taurari hatta su ummi da sadiya lalacewa sukayi
gun kallon fatima sbda kyau datayi ya wuce
misali, ga wani kamshi mai dadin gaske na tashi
a jikinta, basu dawo gda ba sai karfe sha dayan
dare, tuni angonta yadamu da son ganinta yanata
kiransu a waya suna mishi dariya.
Yana tsaye yana waya dawasu abokansu yan
kaduna yaga shigowar motarsu, yayi saurin katse
wayar yace zai kira yafito.
Kafin ya iso garesu anty sadiya taja hannun
fatima suka shige gida, suka turata toilet wai tayi
wanka ba ta son dr. khalifa ya ganta lokaci guda
yarikice.
Jikin fatima kawai yake bukata, yashiga dakin
mama tana zaune tana hada wata zuma da tsimi
da za taba fatima. Tayi mai wani irin kallo ganin
yanayin daya shigo dashi tace "kai kuwa lfya?
Yace "Mama ina fatima?
Tayi tsaki tace "wai kanka daya kuwa? da tsakar
daren nan kake nemanta me za tayi maka?
Ya dan langabar dakai yashiga in ina yarasa
abinda zai cewa mama, karshe yace "wai da
indomie za tadafa min.
"To da basu dawo da ita nan gdan ba fa?
Wa zai dafa maka? ta watso mai tambayar tana
harararsa tace "to bace min da gani kaje kace
ummi tadafa maka.
Zaiyi magana tace "Allah idan kana matsa mata
xan hanaka ganinta.
Yafice zuwa falo abinda yasawa ransa shi ne ba
zai iya barci ba sai ya rungumi fatima a jikinsa
ko ta halin kaka.
Anty sadiya tafito daga dakin dasu fatin suke za
tashiga dakin mama ganin shi a tsaya yasa tace
"yaya akayi boy?
Ya tsareta da ido fuskarsa ba walwala yace "ina
fatima?
Tace "wanka take.
Bai ce komai ba yasa kai dakin ummin, ta bishi
da kallo tana jinjina kai tashige dakin maman
tazauna kusa da ita tace "in kin gama ki ban in
ba ta tasha ba za tasaki jiki tasha a gabanki ba.
Mama tamika mata a sanyayae tace "kazar "yar
sokoto ta kawo ma yana kitchen idan za ta iya ci
ki hada ki bata wannan fitinannan yaron za a sha
matsala dashi dole sai an gyara fatima, sai dai ni
kam jikina ya yi sanyi wannan soyayyar da khalifa
ke nunawa fatima ta yi yawa, kada fa idan sun je
aun zauna tayi amfani da wannan damar tadinga
juya shi kamar waina.
Anty sadiya tace "don Allah mama kada ki sawa
ranki irin wannan damuwar kowa da lokacinsa
kuma a yanayin fatima ba za tayi haka ba
yarinyar ta samu tarbiyya me kyau.
Mama tace "uhm sadiya mutum ba a shaidarsa
mace tana da wani irin hali yayin da da namiji
yadaga hankali a kanta yana sonta dayawa shike
nan tasamu damar yi mai yadda taga dama
maimakon tayi amfani da wannan damar gun
rikeshi da kyau sai tadinga murza kambunta
yadda taso.
Sadiya tace "mama ki yarda da Allah ki yarda shi
ne me komi, addu'ar da kikewa khalifa ke da
abbansa ba zai taba faduwa a kasa ba, insha
Allahu bbu abunda zai faru da aurensu sai alheri,
kidauki fatima kamar "yar dakika haifa sai Allah
yakalli kyakyawan niyyarki yatsare khalifa daga
dukkan wanda zai masa abin da zai gusar da
hankalinsa, idan kaji tsrom Allah ka kyautatawa
'ya'yan wasu Alkah zai dubi na ka zuri'ar ko ba
ka da rai.
mama tace "Hakane anty sadiya ina kaunar
fatima dayawa nima yanayin soyayyar da khalifa
ke nuna mata ne yayi yawa ni na rasa me yakeji
a zuciyarsa game Da ita, in dai akan fatima ne to
fa zuciyarsa ba ta da sukuni, zai iya hakuri akn
komi banda ita.
Duk su mama na wannan tattaunawar ne dai dai
lokacin da fatima tagama wanka tafito daga toilet
daga ita sai dauri kirji sai ko dan tawul din data
yafa a kafadarta bata san khalifa na dakin ba,
ganin shi kawai tayi tsaye jikin madubi ya kuma
zuba mata wadannan fitinannun idon na sa masu
tsananin kyau da laushi, tatsaya sororo tana
kallonsa kamshin dayaji yana tashi a jikinta yaji
kamar ana fizgarsa zuwa jiki? ta, lamarin dayayi
sanadiyar daya kasa rike kansa sai da ya isa
gabanta yaja hannayenta biyu yahadata gam da
jikinsa yasa harshensa yana lasar lebbenta, gaba
daya jikin su yadauki rawa ita tsoro takeyi kada
wani yashigo ya iskesu a haka yayin da shikuma
jikinsa na rawa ne sbda wata fitinanniyar shawa
data jefa shi a cikin yanayin da bai taba shiga ba
a rayuwarsa, yakama kunnuwanta yana gaya
mata kalaman dashi kansa bai san yana fada ba,
har sai da fati taji tsigar jikinta na tashi tasa
hannu tarufe mai baki.
Kwatsam ummi taturo kofar dakin tashigo, khalifa
yasaki fati yajuyo yayi wa ummin wani irin kallo
yafice, ta ajiye abin cin data zubo musu kamar ba
abinda tagani tashiga jan fatin da hira nan kuwa
zuciyarta kamar za ta tarwatse sbda wani
azababben kishi da taji ya tokare mata kirji, sama
sama fatima ke iya magana, hira ta ki yiwuwa
domin hankalin fatiman ba ya tare da ummin, Dr.
Khalifa angonta ne kawai a gabanta shi take
muradin kasancewa tarea dashi.
*****
Tunda sassafe wasu yayyan innarsu fatima suka
iso gdan duk da ba yau ne za a kai amaryar ba
sai sati ya zagayo amma za su dafa abinci sbda
'yan'uwa maza daza su zo domin auran.
Yaya kubura tace "Ina amaryar ne?
Inna tace "Tana gdansu angon amma yanzu za
tazo.
Gaba daya suka rike baki sukece "wani irin tsarin
banza da wofi ne haka?
Yaya kubura ce tafi sauran fusata tace "Ni na
taba jin irin wannan? yaya za ayi ace amarya na
gdansu ango?
Ke ba kya tsoron ace kwadayi ne yasa ta tattare
a gdansu angon?
Yaya rabi tace "ke kike wannan xancan kubra tun
yaushe ake cewa kwadayi ne yasa ciki sati daya
aka fasa bawa musbahu aure aka bawa khalifa
don kawai babanaa yanada farcan susa, to
ballantana yanzu ace tan gdan wai acan ma
takwana, in barda zuvarwa kai daraja meye
wannan?
Inna tace "Ai ba wani abu yasa taje ba sbda
kunshi ne da gyaran gashi.
Yaya kubra tace "duk wani gyara ita batasan inda
za taje ayi mata ba sai ta tafi yawon tallan kanta
a gdan surukan, To Allah dai ya sawwake amma
gskiya kidinga lura kuna jan mutuncin ku irin
wannan abu ne ke sawa a dinga wa mutum gori
daganan mutumci yazuve. "
Inna dai tana jinsu bata sake cewa komi ba,
itama kanta ba a son ranta fati takwana gdan su
Khalifa ba mutumcin mama ne yasa ba ta iya
musu da ita, sun nuna suna son fati daywa,
hakanan fatima tasauya ra'ayin ta gaba daya
akan Khalifa.
Wuraren karfe takwas da rabi su fati suka shigo
tare da ummi, tun kafin matar da aka dauka
musamman dan tayi mata kwalliya tazo fati har
ta fara daukar ido abin gwanin ban sha'awa,
kowa yakalleta sai ya kara, fuskarta dai ce ta dan
kumbura sakamakon rashin barcin da bata samu
ta yi sosai ba a daren jiya, tsabar tunanin khalifa
da kaunarsa da asuba ne bayan sun idar da salla
tazauna jugum tayi tagumi.
Ummi tajanye hannun na ta tace "haba matar
yayana tunanin yayan ke damunki?
Tayi mata wani irin kallo tadauke kai bata ce
komi ba, ummi tayi murmushi tace "Ba kiyi laifi
ba dan kin kasa sukuni akan dr. khalifa, ni na san
tabaki yake yana dandana miki zuma a baki,
shiyasa hnklinki ke tashi dayawa, fatima ba ki da
laifi don kin damu da yaya Khalifa, bai dandana
wa mace irin wannan zumar ba ta rikice akansa
ballantana ke da yake nuna miki so irin haka har
yana hada jikinsa da naki'.
*****
Karfe goma sha dayan safiyar lahadi daruruwar
alummar musulmi suka shaidi daurin auran Dr.
Abubakar Saddiki Muhammad da Fatima Musa,
daurin auran daya samu halartar manya manyan
mutane tun daga kan manyan yan kasuwa da
sunan su yayi fice a fadin kasar nan zuwa
manyan yan siyasa da kusoshin gwamnati da jiga
jigan malaman da ake ji dasu a jihar mu ta kano,
hatta bangaran sarauta sun halarci daurin auran
ballantana likitoci da abin yazama nasu maganin
a kwabe su, maroka suka rinka yayata sunan
ango da amarya da iyayansu yayin da gdajan
rediyoyi ke ta bayyana yadda abubuwan ke
gudana, sai shiga ake ana fita da nau'ikan
abubuwan ci da na sha na alfarma daga gidansu
dr. khalifa da gdansu inna.
Angon ya sha ado ya yi kyau daya wuce misali,
abin sai wanda yagani shadda ce mai tsadar
gaske fara kal riga da wando da babbar riga sai
akayi aikin babbar riga da blue din zare, hula
kansa ma ya kasance fara da blue takalminsa
blue, a ckin gda amarya fatima irin shigar ango
aka mata fari da blue, ba a iya tantance wa yafi
kyau tsakanin angon da amaryar kowanne ba
baya bane ko ina masu hoto ne da bidiyo ke
daukar ango da abokanansa sannan suka shigo
gda tare don gaida iyayan amarya..
Gdansu fatima ma cike yake da mata anata
rangada guda d sanya albarka, fatima ta zamo
matar dr. khalifa rana ba ta karya sai dai uwar
diya taji kunya, farar tukunya mai fidda farin
tuwo, kirari iri iri maroka suke tayi musamman a
gdansu khalifa inda anan ne ake facaka da kudi
kamar ba nemansu ake ba.
Abba yadinga kyautar muhimman abubuwa yana
fadin "ai wannan rana ce ta farin ciki garesu ranar
auran dansu daya.
To fa.
Ina su hajiya hauwa da hajiya saude kannan
abba iyayan ummi? wadanda duk wani burinsu a
wannan rana bai wuce ace da diyarsu ummi aka
daura auran ba, amma hakan bai yiwu ba, khalifa
da iyayansa basu damu da damuwar kowa ba sai
ta su.
Da farko basuyi niyyar zuwa gdan ba a yau daga
bisani saude tace gara suje karshe a zo anayi
damu ai idan baka iya kama barawo ba kai sai ya
kamaka.
Ba za ka iya shaida bacin ran dake tare dasu ba
amma zuciyarsu fal bakin cki da takaici, da
isowarsu a safiyar abba yaraba musu sabbin kudi
rafa rafa yace suyi liki, duk da haka ransu ba dadi
tunanin su shi ne da da ummi aka daura auran
nan ai sun more irin wannan dukiya haka.
Bayan gama daurin auren suka kebe a ckin wani
daki, saude tadubi hauwa tace "ke wadannan
mutanen ba na wasa bane sun fi mu shiri.
Hauwa tace "Yo ba kiji abin da malam yace jiya
ba? yace ai uban fatima ne yahada wani
gagarumin asiri ya dabaibaye zuciyar khalifa
yadda b ya son kowacce mce si yarsa fatima
shiyasa muke tayin aiki aikin ya ki kama khalifa,
yace. a wani lokacin yana so ya so ummi sai
asirin yayi tasiri a zuciyarsa yakasa katabus yaji
kamar ba ya da iko a kansa sai son fatima.
Hajiya saude tace "Haba ko da naji ni nasan arina
wai an saci zanin mahaukaciya, wannan aikin da
malam keyi ba zai tashi a banza ba da mugun
abinda da sukayi, duk mu mun manta uban fati
malami ne sai da yayiwa khalifa asiri duk iyayan
ya gama dasu anma ba komi jiya da dare na je
na kaiwa malam kudin bajimin sa dayace a kawo
za a zubar da jini yace musa ido za muyi kallo
dakansu sai sun gane kurensu kowa yaci tuwo
damu miya yasha.
A DAREN FARKO
33
Mama tana iya kokarin ta akan bawa su hajiya
hauwa 'yanci a gdan dan dai kada ayi korafin
amma bata tsira ba duk inda tayi binta suke da
harara suna kwafa.
Karfe hudun yamma angwaye da wasu daga ckin
mutane aka fara daukan mutane zuwa inda akayi
gagarumar walima maza zalla, ana kiran slar
magriba aka tashi kowa yana farin ciki da sanya
alheri.
Karfe tara da rabi na daren dr. khalifa ya fito
daga wanka a dakinsa abokansa biyun nan Dr.
Bashir da Dr. Hafiz su biyu suka rage bayan kowa
ya watse,yafada bisa gado yana mai da numfashi
da kyar.
Dr. Bashir yadubeahi yana dariya yace "Ango na
amarya, amaryar ka ta yi kyau yau abin har ba a
magana sai dai kwalelen ango, ko ganinta yanzu
ba damar yi.
Dr.khalifa yace "Ba komi ai komi lokaci gareshi
rana ita yau iyanzu babu wanda zai mini shamaki
tsakanina da ita zamu kwana a daki daya sai
yadda naga dama da ita.
Kafiz yace "Oho dai ba haka aka so ba wai kanin
miji ya fi miji kyau, ko in je in dauko maka ita?
Dr. khalifa yace 'Rufa mini asiri dazun nan mama
takirani dakinta tana gaya mini idan taji na je
gdansu fatima sai ta batan rai don Allah kaji wani
danyan hukunci mutum da matarsa.
Dr. Baahir yace "Ai ta yi ma haka ne don ta san
halinka, a gdan iyayan na ta ma sai kabita ka
matseta kai ba kunyar mutane kake ji ba.
Yace "kai ba a irin gdansu fati ake wannan ba ka
san akwai inda ake barin halak don kunya.
Dr. Hafiz yace "To kai ka san kunya ne Abbakar?
ko dayake yanzu ka sauya kamar ba kai ba, son
fatima ya sauya ka dayawa kamar bakaji tashan
'yN mata ba, tunda kadaura idonka akan fatima
kadaina tunanin 'yammatan ka, tun wasunsu na
damuwa suna damun mu har sun hakura.
Yace "Kai ni ai babu sauran wata diya mace a
zuciyata tunda na mallaki gimbiyar mata fatima
ta rufe kofa gaba daya.
****
Da gari ya waye mama tazo da kanta taroki inna
da malam akan a bata fatima akwai shirin da za
ayi mata, a zuciyoyinsu basu ji dadin haka ba har
ita kanta fatiman sbda ta san dr. khalifa
matsamata zai yi a gidan amma mama tafi karfin
komi garesu, iyayan khalifa suna da kimar da za
su iya yi musu komi surutun mutane ne yake
damun su fassarar nan ta kwadayi ita take damin
inna komi akayi idanuwan mutane na kai kuma
sai sun yi magana.
Bayan tafiyar mama abinda inna da malam ke
tattaunawa knan, Fatima na dakinsu na yara a
kwance tana fama da barcin gajiya ita kanta ta
san a yanzu ta canja, ta baza kunnuwa tana
addu'ar Allah yasa kada malam ya amince da
komawarta sai dai kash sai ji tayi malam din na
cewa ta tafin kawai.
Amma dai kija mata kunne tasan abinda takeyi,
kuma tasan kanta. Ya sa kai yafita.
Inna ta kwala mata kira ta fito ckin rashin kuzari
kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki tazauna
daf da ita, tace "To malam dai ya amince da zan
ki a gdansu khalifa, jan kunne da zanyi miki shi
ne ke diya macece ki san darajar kanki idan har
kina son ki samawa kanki kima a gun khalifa na
san yadda kike biyewa al'amarin khalifa sbda son
da kike masa, to kisani namiji sai ana taka tsan
tsan da al'amuransa dole mace Tayiwa mijinta
biyayya domin aljannarta. na karkashin kafarsa
amma kada ki zake karki ja wa kanki abin fadi.
Jin tayi shiru yasa fatima a sanyaye tace "Inna
don Allah kibarni anan nima ba na son zama a
gdan nasu.
Tace "to yaya za muyi kin san ko a yanzu khalifa
ya fimu iko dake in dai aure ke sa ayi iko da
mace tunda an daura kasancewar ba a kaiki
gdansa ba ba zai hana dokar Allah aiki a kanki ba
a cikin hakkokinsa da Allah ya jarabta akanki, kai
mace daki ba shi ne sharafin biyayyar aure ba
shaidu da sadaki sune aure in dai an yi su ya
zama dole mace tayiwa mijinta biyayya ko a ina
take kuwa kinga in dai haka ne dole mu amince
da zuwanki gdansu khalifa.
Fatima taji zuciyarta ta karaya bata ankara ba
kawai sai jin hawaye na xubo mata, ,ita kanta
bata san kukan metake ba batasan ma'anar
kukan na ta ba.
Inna tayi murmushi tace "To meye na kuka,
khalifa zabinki ne fatima kin manta yadda kika
dinga kuka kina rokon a bashi ke?
Duk abinda khalifa yazo dashi dole kiyi biyayya
domin aure kikayi na soyyaya na zabin ranki da
zuciyarki,ban taba zaton xan ga hawayenki ba
bayan kin zamo matar khalifa fatima, ki share
hawayenki ki mike kafafuwanki kiyi walwala kin
auri wanda kike so.
Fatima tayi jugum ta san magana ce irin ta gugaz
zana inna take gaya mata akan abinda tayi akan
musbahu ,taci gaba da kuka sosai ,taci gaba da
kuka sosai inna ta tashi tashiga hidimomin
gabanta tana fadin "Ai sai kiyi.
Fatima ta koma ckin daki ta kwanta bata san
abi? da ya daga mata hankali ba hawayanta suka
ki tsayawa, ummi ce ta yaya lavulan dakin da
sallama tayi turus tan kallonta tace "Kukan
amarci kike tun yanzu fati ko wani abu aka miki?
Babu Babu amsar da za ta iya ba ummi don ita
kanta bata san kukan da take ba.
Ummi tace "to koma dai meye kisaki kukan tashi
kiyi hakuri kiyi wanka ki shirya tafiya za muyi
ango yana jiranki za mu fara fita hada kayan
sayan baki kafin na lefe shi khalifan ma ya so
ace Dubai za aje a hado har kayan dakinki mama
ta ce babu inda zai tafi dake ba tare da an kaiki
gdanki ba.
Fatima dai ba ta son magana ta tashi tayi
wankan, ummi tagama shirya mata kayan ta,
suka yi sallama da inna suka nufi gdan mama,
dogon hijabi da nikab tasa suna shiga harabar
gdan fati tayi sauri tashige ciki don kar su hadu
da khalifa ta zauna a falo a kunyace tagaishe da
abba da mama ko kanta ba ta iya dagawa.
Sai mama ke mata dariya tace "in har wannan
kunyar za ki sawa ranki za kiyi ta wahalar da
kanki ke kawai ni dai ba suruka na dauke ki ba a
matsayin diyata kike har yanzu, tashi ki wuce
daki idan kin huta akwai girke girke na abokan
mijinki.
Da zarar an kra dr. khalifa mijinta sai taji wani iri
a jikinta, tana jinjina alamarin kamar a mafarki
,duk yadda ta so shi a ranta take tsananin son
tadinga ganinsa a ko yaushe sbda burgetan da
yake yau tsoron ganinsa take, fatanta kada
yashiga gdan suhadu, tayi sa'a kuwa har magriba
tayi bai shiga ba tuni suka gama hada abinci mai
rai da lfya suka shirya kan tebur tashige daki tayi
wanka tasa doguwar rigar shadda koriya takara
gyara gashinta tayi sallar isha'i tana shirin hawa
gado takwanta aka turo kofar cikin tattausar
muryar nan tasa yayi mata sallama.
Khalifa ne.. A figice tadago idonta taxuba masa
yana ckin wata lafiyayyar shadda brown me
haske an mata aiki da dark brown din zare irin
dinkin tazarcen nan, kamshin turaransa yadinga
ratsa mata zuciya, ya fidda gilashinsa ya
baibayeta da fitinannun idonsa ba walwala sosai
a tare dashi yace "Fatima.
Duk kokarin da tayi na tsayuwa ta kasa svda
rawar da kafafunta suka shiga yi, ta durkusa a
gun tadafa gado.
Ya kara kirn sunanta a karo na biyu a nan ne ta
amsa, yace "Tun karfe nawa kikazo gdan nan?
Muryarta na rawa tace "sha biyu.
Yace "Amma ba ki san hanyar dakina ba
ballantana ki zo ki gaisheni.
Gabanta yafadi tadago ido a tsorace tana
dubanshi abinda ta gani a cikin kwayar idonsa
yasa tayi saurin maida kanta ksa, yace "kin yi
daidai knan?
A hankali tace "kayi hakuri.
Yayi saurin katseta yace "Ba zan yi hakurin ba.
Tabude baki cike da mamaki tana kallonsa abin
ya ba shi dariya ya iso gabanta ya kamo
hannunta yamikar da ita tsaye, kai tsaye
yahadata da jikinsa ya matseta yadda ba za ta
iya motsi ba, ya cusa bakinsa ckin nata yadinga
tsotson lebbanta ckin wani irin salo na
gwanancewa a harkar sarrafa mace har jikinsa
yafara rawa yafara manta a ina yake.
Kwatsam yaji mama na kwalawa fatin kira daga
falo dasauri yasake ta yafito falon, mama tayi
mai wani irin kallo fuskarta a tsuke tace "Daman
kana ciki?
Yayai dan murmushi yana sosa keya yace "Yanzu
na shiga.
Ta harare shi tace "To me ka shiga yi?
Yace "A'a gani nai dai ban ga fatin a falo ba shi
ne na bita ciki.
Mama taja tsaki tace "ka ji dashi dai ina fatiman.
Yace "Kayanta take swa, ya wuce tebur yana
bude buden kayan abincin yace "mama asa su
fatima su kawo mana dakina muna da yawa.
Tace "kai kafita daga idona khalifa babu abunda
zai kawo fatima dakinka kuma idan baka saurara
dashiga dakinsu ba zanyi maganin ka.
a zuciyarsa yace "a baya ma na taba fatima
ballantana yanzu, ai zancan ace kada in taba ta
ma bai taso ba, mutum da halak malak. Unmi ce
ta taya shi kai abinci tana zolayarsa yana dariya,
ummi tana mamakin yadda khalifa yazamo mai
mata walwala akan fatima ya dawo kamar ba shi
ba, mutumin da murmushi ma a baya tsada yake
masa, shi ne yanzu ake hira dashi yana dariya, in
dai kana son ganin walwalar khalifa yi masa
zancan fatima, wannan lamari yana taima zuciyar
ummi tare da gigita ta, abinda ta tabbatarwa
ranta shi ne na raba zuciyar Dr. khalifa da son
fatima sai dai mutuwa idan ransa yabar jikinsa
amma ba dai wani boka ko malam ba.
A DAREN FARKO
34
Abokansa suka tsare su dtambayar ina amarya
tunda an ce tana gdan dole suna son ganinta,
khalifa ya marairaice fuska yace "to ya zanyi !?
Mama ta yi ruwa ta yi tsaki ta ce fatima ba za
tazo dakin nan ba, ni ban taba ganin irin wannan
tsarin ba mutum da matarsa a dauki ido a dora
mai ko kallon fatima nayi mama sai ta hau fada
na rasa dalili bata san jin zuciyata nake kamar za
tafashe ba idan tana hanani ganin mata ta. "
Wani a cikinsu mai suna Nura yace "Ai mama tayi
min daidai sanin halinka ne yasa tayi ma
haka,idan aka kyaleka za ka iya kwana da fatima
a dakin nan da safe kuma kayi mirsisi kana kallon
idon mutane.
Khalifa yakara fusata yace "Kai da Allah kar ka
dada batan rai haramun ne dan na kwana da
matata.
Dr. Bashir yabushe da dariya yace "Wannan ihu
ne dai bayan hari in ka isa katafi dakin mama
kayi mata wadannan fadace fadacen karshe tace
sai bayan wata uku za a kaima amaryar in ga
kuma yadda za kayi.
Khalifa yayi dariya yace "Tabdijam ai kuwa da na
basu mamaki nima in ga yadda za ayi dani.
Nura yace "Uhum ka bisu dai a sannu idan kai
baka ba su mamaki ba su subaka mamaki.
*****
Mama tayi tsayuwar daka gun gyara amarya da
abubuwan da za sukawo mata ni'ima a jikinta, ita
dai burinta hankalin danta yakwanta,. Fatima ta
cika ta batse ta kara wani irin kyau kyaun ma
mai ban sha'awa, tayi fresh babu abinda ke
damunta.
Mama ta hanata fita ko ina don kar ta shiga
dakin khalifa sai dai shi in ya shigo su gaisa iya
fali.
Ya yi fushin ya yi mitar har ya gaji ya zuba ido
shi kadai yasan damuwar da yake fama ita a
zuciyarsa, a ranar da fatima tayi kwana biyu a
gdan ana ya jibi za a kaita gdan Dr. Khalifa aka
kai kayan lefenta gdansu, lefen da aka dinga
surutun karya tayi yawa, wannan ai
almubazzaranci ne da dukiya kamar ba masu
neman taimako da za a kashe dukiya irin wannan
a lefe,? Abinda 'yan'uwan abba sukayi ta fada
knan, daga bisani wannan yazamo ba abin surutu
ba lokacin da aka kaisu ganin gdan dr. khalifa da
fatima za su zauna wanda yake court road, da
irin kayan alatun da aka dankara a gdan abin sai
ya wuce ayi magana da baki sai gani da ido, duk
wani abinda za a kawata gda dashi a kalla asan
ya yi kyau sai da akasa a cikin wannan gda, komi
ya kammala amarya kawai ake jira.
Washegari ranar asabar wanda yakasance saura
kwana daya akai fatima gdanta tatashi da ciwon
kai abisa dole mama tace khalifa yashiga dakinsu
ya dubata, shi bai ma san ba ta da lfya ba svda
hushi yayi yadaina shiga harkar mama da ita
kanta fatin, idan ma yashigo falon ta gayar dashi
fuska a tsuke yake amsawa sbda ya gaji da jan
ran da ake masa kawai don an ga ya damu.
Lokacin daya shiga falon suka gaisa da mama
yawuce kan tebur zai ci abinci ta dubeshi tace
"Yau baka tambayi matar ta ka ba.
Ya dan tabe baki kamar bai damu ba yace "Oh
tana ina ne ?
Tace "Tna daki ba ta da lfya.
Yaji wani irin abu ya dakar masa zuciya duk da
haka yashare bai bari mama ta fahi ; ci halin da
zuciyarsa tashiga ba, yayi zamansa yafara
tsiyaya tea a kofi yana fadin "Me ya sameta ?
Ta amsa "Tashi tayi da ciwon kai da amai idan
kagama kashiga kaduba ta.
To kawai yace yaci gaba da cin abincinsa, da ya
gama din ma maimakon yashiga dakin au fatima
sai yadauki hanyar fita.
Mama tace "Ba za kaduba fatiman bane ?
Yace "Af har na manta.
Yamurda kofar dakin tana kwance bisa gado
nannade da bargo, idanuwanta a rufe, yazauna
kusa da ita yayaye bargon data rufe, ya taba
wuyanta zafi sosai, yace "Subhanallahi.
Nan da nan yaji tsigar jikinsa ta kama tashi,
yakira dr. hafiz a waya ya gaya masa irin
magungunan dazai aiko masa dasu, yafita dan
yadan hada mata abinda za taci sbda allurar da
zai mata.
Mama tace "za su fita da anty sadiya yanzu za
su amso dinkunan fatima tunda ba kowa a gdan
yazauna yalura da ita.
Zuciyarsa tayi mai fari kal 6au ya sami dama
amma sai yadan kanne yaduba agogo yace "Da
fita zanyi kuwa.
Tace "Kadan jira mudawo bai dace a barta gda
ita daya ba sai 'yan aiki alhali ba ta da lfya.
Bayan fitar su mama yahada mata shayi ba
madara yazuba mata dankali shi kadai yanufi
dakin, yazauna gefen gadon yajawota jikinsa yana
lallabata kamar kwai yarungumeta yana bata
shayi tana dan sha a hankali tace ita dai ta koshi.
Wata daga cikin ma'aikatan asibitinsu dr. hafiz
takawo magungunan yabata tasha yayi mata
allura guda daya tana zuba shagwabarta yadda
taga dama, hankalin khalifa yakara tshi zuciyarsa
ta tsimu komi na jikin fatima ya bayyana a
gareshi, domin wasu riga da siket ne a jikinta
marasa nauyi takara zama fara kal, ko idanunsa
bai iya daukewa a kanta ba, itama tana son
tadinga kallonsa duk da tanajin nauyinsa, ganin
ya fara shafa mata cinya da ciki yasa tadan janye
jikinta ta matsa, yayi narai narai da idanuwan
nan na sa yana mata wani irin kallo mai daga
hankali.
Yace "Haba fatima kin san matsayinki a guna bai
dace ki biyewa mama kina wahalar dani ba, wai
ace fatima tsakanina da ke sai gani da ido daga
nesa,. Ni fa mijinki ne ina da hakki akanki ko kin
manta ne ?
Doguwar ajiyar zuciya tai tace "mama ce ba ta
son in zo gunka nikuma ba zanyi abu ? da zai
bata mata rai ba.
Yace "ai dama ba cewa nayi ki bata mata rai ba,
amma ya dace ace ko da daddare ne kina dan
fakar idonta kizo dakina kitayani hira ki debe min
kewa tunda kin san dole ina fama da damuwa a
zuciyata ko ? tunda kika dawo gdan nan dazama
kullum dare ba na iya barci sbda kewarki fatima,
ina son ko kakane in dinga jin dumin jikinki, ko
rungumarki nayi na miki kiss ai zan ji dadi a
zuciyata ko ? Amma ke ba ruwanki sai ki biyewa
mama ki shareni sai dai in shigo in ganki kyaunki
na karuwa zuciyata tayi ta fama da kewarki ya
kamata ki tausaya min Fatima.
Ya kamo hannunta yakara janta jiki ? sa
yarungumeta sosai yaci gaba da cewa "Wallahi
fatima ina sonki son da ban taba zaton zan ma
wata diya mace a duniya ba, sbda kafin ke ba zan
iya tantance miki meye soyayya ba, nidai nasan
ina mu'amula da mata amma ban taba damuwa
dawata diya mace ba saida nafara ganinki nadin
ga jin tamkar zan mutu idan ba na tare dake, duk
wata natsuwa takan gushe mini idan ban ganki
ba, shi yasa na rikice na gigice lokacin danaga
katin daurin auranki da musbahu, Fatima idan
ciwon sonki ya tsananta a zuciyata sai in dinga
jin kamar ba zan yi doguwar rayuwa dake ba,
fargaba takan kama mini zuciya in rasa yadda
zanyi da raina, fatina dan Allah,. Yayi shiru
yakasa cigaba da magana.
Tausayin sa yakamata sosai taji ciwonta ya
sauka gaba daya babu abinda ke gabanta sai
khalifan tadinga jin wani so da shauki yana ratsa
mata zuciya kamar yau ne tafara sanin khalifa, a
wannan lokacin da kanta tasa hannayenta biyu
tarungumi dr. khalifa kam kam a jikinta tana
hawaye.
Yasa harshensa yadinga lashe hawayen na ta
yana fadin "fatima, fatima kukan me kikeyi.
Ta tura bakinta cikin kunnuwansa tace," kukan
farin ciki ne kada yadameka.
Yadda tayi mai shima haka yayi mata yace "Farin
ciki kala kala ne fatima don Allah fassara min
yanayin farin cikin daya sa ki kuka.
Tace "Babu wani farin ciki ga masoyi wanda
yawuce mai sonsa ya soshi, hausawa kan ce son
maso wani koshin wahala ne, idan mutum yana
son wanda ba ya sonsa ya gamu da wahala idan
kuwa mutum yana son wanda yake son sa yana
ckin farin ciki da kwanciyar hankali, a yau ban san
wanda yafini farin ciki ba shiyasa nake kuka.
Khalifa yayi murmushi yace "Allah sarki ashe in
dai hakane za kiyi ta kuka tunda ni yanzu nafara
nuna miki so da tattali har zuwa ranar da Allah
(SWT) zai karbi rayuwata.
Fatima ina fatan Allah yasa in mutu in barki sbda
nasan insha Allahu za kiyi tamin addu'ar neman
gafarar Allah. Bayan haka ina jimantawa kaina
halin da zan shiga idan na rigaki mutuwa,
mutuwata sutura ce a gareni idan yakasance kin
mutu fatima don Allah ki dinga yi min addu'a.
Ta katse shi ckin damuwa tace "Don Allah
kadaina batun mutuwar nan haka.
Yace "kyaleni in yi fatima duk mai rai mamaci ne
duk yadda muka kai ga son rayuwar duniya sai
mun mutu, tuna mutuwa shi kesa mutum yayi wa
kansa hisabin ayyukansa yadinga sanin cewa zai
hadu da Allah kuma zai ga abinda ya aikata me
kyau ko kishiyarsa.
Tace "To nidai na ji don Allah mubar wannan
maganar.
Yayi murmushi yace "Shikenan na barta, yaci
gaba da dan latlatsa mata jiki har sai da yayi
nasarar kashe mata jikin gaba daya ya kasance
ba ta da wani kuzari, sai yadda yayi da ita, duk
zazzabin da take fama dashi sai da taneme shi
tarasa sai tsabar tsananin son khalifa da shaukin
sa.
Ya zare jikinsa yamike yasawa kofar key yakara
rufe lavulayen dakin yayi dan duhu duhu, tsoro
yacika zuciyar fatima ta tsahi zaune tana rokon
don Alla ya taimaketa kada yayi mata wani abin,
yace "kiyi hakuri kawai fatima nima ba na son
yimiki wannan abin anan gdan sai a gdanmu
amma a halin yanzu zuciyata ba xa ta taba iya
hakuri ba, kada kijefa nin ckin fushin Ubangiji kisa
in je in aikata sabon Allah, kada kijefa kanki kema
ckin fushin Allah kuma kinsan matsayin matar
datake gujewa mijinta.
Jikin fatima yadinga rawa ganin yadda yanufo ta
gadan gadan sai kawai ta sallama zuciyarsa ta
gama karaya ta tabbatar idan bata bashi hadin
kai ba zaiyi ta karfin tsiya, tunda idanuwan sa
sun rufe hankalinsa a tashe yake sosai.
Kokarin da khalifa yayi shi ne ya saita kansa
sanin cewa fatima budurwa ce wadda taba taba
sanin da namiji ba, sannan yarinya ce karama in
barda haka da yau fati ta yabawa aya zaki ? ta,
duk ilahirin jikinta saida khalifa yabi yalashe,
yajuya ta nan yajuya ta chan tading jan numfashi
dakyar don kafin a kai ga bbabban al'amarin
fatima ta galabaita, lokacin datafiya tai nisa
yasamu nasarar rabata da budurcin ta bata san
lokacin data saki wani kara mai karfi ba sbda zafi
da taji ya ratsa mata har kwakwalwar kanta,
tafita hayyacinta hatta numfshin ta sai da yayi
daukewar yan mintuna sannan yadawo, khalifa
yana sane da halin da take ciki sai daya gamsu
son ransa sannan ya kyaleta.
*****
A DAREN FARKO
35
Tuni zazzabin fatima yadawo jikinta yadauki zafi
sosai, yayi saurin dagota yakaita bandaki yasa
tawul da ruwa yadinga shafa mata a jikin sannan
yace tadaure tayi wanka.
fatima kuka take sosai da kyar tayi wankan, gaba
daya jikinta ciwo yake mata ba karamar wahala
tasha ba. Idanuwanta suka yi ja, bayan ta gama
wankan tadaura zaninta tazauna jugum tayi
tagumi tana tunanin wannan azabar ake sha idan
an yi auran ? shin haka khalifa zai yi ta gwada
mata karfi yana gana mata azaba, kai gskiya da
sake.
Yaturo kofar bandakin ya shigo, a tsorace tamike
har abin ya bashi dariya daya fahimci tsoronsa
take ji, shi kansa ya san ya ba ta wahala, ya
matsa dab da ita yace "kiyi hakuri fatima kowace
mace da kike gani tana rayuwa da mijinta sai da
tasha wannan wahalar, ki kwantar da hankalin na
lokaci daya ne daga yau ba za ki kara jin zafi
haka ba.
Tadinga sharar kwalla yace "Don Allah kidaina
kuka in dai ba so kike nima in miki kukan ba.
Wannan abin na yi miki ne don ina sonki, bai
dace yazamo abun damuwa a zuciyarki ba kinga
gdan nan ba mu kadai bane idan su mama suka
dawo suka ga kina kuka kinsan za tadamu don
Allah kiyi hakuri kidaina tunda ba kyaso ba zan ka
ra yimiki ba.
Ya lallabata yakara rungumeta a jikinsa yana
gaya mata kalamai masu sanyi har zuciyarta ta
dan lafa, tafito daga toilet din ta taras ya sauya
shimfidan gadon da kansa, mutumin da ba abinda
yasani a rayuwarsa sai yahuta komi yimasa ake
yi.
Bayan ya gama yafito lokacin ta gama sa
kayanta ta haye gado har yanzu idanuwanta
jawur suke, ta ki yarda su hada ido da khalifa a
bisa dole ya kyaleta yakoma gefe yazuba mata
ido yana murmushi, shi kadai yasan abinda yake
ji a zuciyarsa game da ita, shi dai kam yau ya
san ya kwanta da mace ya gamsu yafara sanin
meye sirrin dake tare da matar aure ta sunna
wadda ke da banbanci data bariki, wadda a baya
suka dauka itace rayuwa ta cinyewa da burgewa,
ashe duk wani sirrin kwanciyar hankali na tare da
matar aure, hakika zai rike fatima dakyau domin
yau kam ya san ya yi aure na birgewa da
morewa, yadaga hannunsa yna ma Allah godiya
daya bashi fatima.
Yamike yadan shafi fuskarta ba ya son fita daga
dakin amma haka yadaure yafita, hankalinsa a
kwance ganin hr yanzu su mama basu dawo ba,
sai dai yana fitowa yaci karo da motarsu ta
shigo, a tsatsaye yayi musu sannu dazuwa ta
tambaye shi jikin fatin yace da sauki yadau
motarsa yabar gdan.
Dakinsu fatima yafra shiga, jin zafin da jikinta
yayi fiye da dazun yasata kira dr. khalifa a waya
ta hau shi da fada tace "Ya naji jikin Fati da zafi
haka ? Baka ba ta magani bane ?
Gabansa yafadi yayi zaton ko wani abu tafahimta,
ya san halin mamansa da wayo, Har allura nai
mata mama zai sauka ne.
Tace "wane irin xaxxabi ne wannan an auna
jininta ?
Yace "Ina zuwa za mu zo da Br. Bashir yanzu mu
auna.
Ya iske Dr. Bashir a office dinsa a asibiti ba aiki
yake ba kulle kansa kawai yayi yana hutawarsa,
Dr khalifa yace "Ka taso muje ka auna min jinin
matata zazzabi yake damunta.
Idanun Bashir a lumshe yace "Kai me kakeyi da
baza ka debo jinin kataho dashi nan a auna ba,
don Allah ka kyaleni barci nakeji jiya kwana nayi
ba barci shi yasa naki tafiya gda don ba za
subarni in yi barci ba idan naje.
Dr. khalifa yace "Don Allah taso muje mama sai
fada take min.
Dr. bashir yatashi yana mita yadauki wasu kayai
aiki suka shiga motar dr. khalifa suka danno
gdan.
Fatima bacci take sosai sai mama ce a kanta ko
da jin yanayin fitar numfashinta ka san tanajin
jiki, mama tafice tabarsu.
Dr. khalifa yazauna kusa da ita yadakko hannunta
yadora kan cinyarsa ya amshi sirin jin yasoka
mata akan jijiya zai debi jininta tasaki kara mai
karfi, yavuga kafa da karfi yace "Oh my God ka ga
abinda nake gudu ko.
Dr. Bashir ya amsa jinin yana harararsa, yasaka a
cikin waya 'yar na'ura daya riko a hannunsa,
Fatima ta tashi takama kuka.
Dr. khalifa ya kara rudewa yarungumeta yana
lallashinta, Dr. Bashir yace "Ka ga idan ba za ka
saketa muyi aikin da zamuyi ba zan yi tafiyata,
haba mutun sai nacin soyayya tamkar akanka aka
fara aure.
Ya maida idonsa ga fati yace "Ke fatima karfafa
jikinki ba na son shagwaba tashi kiyi tafiya in
gani.
Fatima takara narkewa a jikin mijinta cike da
shagwaba tace "Ni kafata ciwo take ba zan iya
tashi ba.
Dr. bashir yafiddo ido yace "Ai ko dole kitashi
idan baki mike ba ya ya zan fahimci ciwonki.
Khalifa yace "Ni fa ba na son iskanci duk ciwon
da za kagani za kagani a jikinta ba za ka wahalar
min da mata ba ko don ciwon ba a jikinka yake
ba..
Dr. Bashir yace "Allah ta tashi kaine kake kara
shagwaba yarinyar nan.
Khalifa ya lallaba fatima ta tashi tafara tafiya da
kyar takai bango tadawo za ta zauna, Dr. Bashir
yace "a'a bai isa ba cigaba da tfya.
Khalifa yafusata yace "Kada Allah yasa kadubata
in dai sai ta cigaba da wahalar tfya kana gani fa
dakyar take tafiya.
Bashir yayi murmushi yace "Abbakar kaine ka
haifarwa da fatima wannan ciwon.
Yaja tsaki "To ina ruwanka kai dai kayi aikin ka
mana ni ban son sa ido.
*****
An yanke shawarar sai an kai fatima gdan wanda
yahada da yini da party guda biyu amma a ranar
da za akaita da yamma za ayi kamu hade da
walima, ta dai ji sauki sai abinda ba a rasa ba,
tun a safiyar yau lahadi tadawo gdansu, a gdan
dan hausa aka shirya za ayi kamun, ango da
abokanansa ma za su halarci gun domin za ayi
kamun ango daga karfe hudu zuwa biyar xa ayi
komi a gama, dan haka karfe uku da rabi na
yamma aka fara daukar mutane zuwa gdan dan
hausan, mawakan zamani na ta cashewa ana
wasa ango da amarya da iyayansu mama da
abba da inna ma sun halarci gun malam ne yace
va zai je ba.
Yau shigar ango da amarya ta kasnce dark da
light brown, shi shadda ita less, abin ba a
magana kyau an yi shi sai wanda yagani duk
wanda yake gun ya yabawa haduwar ango da
amarya sbda sunyi kyau na daukar ma'ana ayau
an ga abinda ake kira matching, kalandar da aka
raba a gun ta ja hankulan mutane da yawa domin
anyi hoton ne a wani irin yana yi me ban sha'awa
wanda yake tabbatar wa da jama'a tsananin so
da kaunar dake tsakanin ango da amaryarsa.
Lokacin da mawaki yanemi fitowar ango da
amarya filin rawa don su taka rudewa gun yayi
domin cewa yayi zai ga wanda zai riga wani
mikewa tsakanin ango da amarya.
Fatima tayi wuf tariga dr. khalifa mikewa, gaba
daya aka shiga tafa mata, mawaki yace "kyautar
fatima tafarko ce sannan ta dr. khalifa tunda ta
rigashi mikewa.
Lokacin dasuka iso filin rawan, iyayansu da
abokai da dangi aka dinga yi musu ruwan kudi
har ya kasance babu abunda kake gani a gun sai
sabbin kudi suna tashi sama da kasa.
Karfe biyar da rabi akayi kamun amarya karfe
shida kuma akayi kamun sngo, shida da rabi aka
rufe taro da addu"oi na musanmman daga
manyan kuma shaharrarun malamai, bakwai
saura kwata aka tashi.
Karfe takwas aka shiga wata liyafar inda malamai
mata suka yiwa ango da amarya fadakarwa ta
awa daya kachal yadda za su zauna da junan su,
karfe taran dare aka dauki amarya zuwa dakin ta
bayan iyaye da yan uwa da abokan arziki sun yi
mata nasihar zaman lfya tare da addu'ar Allah
yasanya wa aurensu alheri tare da albarka.
Duk inda amarya tagifta sai kamahi mai dadi da
sanyaya zuciya ke tashi.
*****
Wannan shi ne asalin labarin masu karatu sai
kuyi jimirin biyoni kuji yadda aka kaya, an dai
kashe Dr. khalifa a DARANSU NA FARKO da aka
kai fatima, shin waye ya kashe Dr. khalifa ? shin
ina labarin musbahu ku biyoni.
*****
Karfe shida daidai na yammacin Alhamis jirgin da
ya taso daga Lagos yadire Jidda a airport din
Malam Aminu Kano dake birnin kano, tana rataye
da jakarta ta hannu, tashiga motar gdansu da
aka zo daukar ta, tana shiga gdansu aka rude da
murnar ga jiddah ga jiddah, ta zauna a falom
mahaifiyarta suka gisa tare da tambaye tambayen
'yan'uwa da abokan arziki.
Ummansu tace "ke dai jiddah idan kika sawa
ranki abu sai kinyi shi har yaushe kikaje london
din da za kice sai kin zo hutu ?
Tace "wallahi umma nima banyi niyyar zuwan ba
haka kawai a wannan satin naji gaba daya
hankalina ya tashi da zaman london din ga
mafarkai ina tayi marasa dadi nayi nayi in jure na
kasa kwana biyun da suka wuce ko barci bana yi
sosai.
Umma tace "To Allah yasa alheri, Allah yarabamu
da muagun ji da mugun gani.
Tace "Amin, ina Abba ? "
Tace "Ya fita amma tunda yamma tayi yana
hanyar dawowa.
Tace "Bari in yi sallah in je gdan su Ummi wai
tana shigowa kuwa na san rashin kirkita.
Umma tagirgiza kai tace "Wayyo Allah ai ummi
gaba daya ba ta ckin natsuwarta hankalin kowa a
tashe yake sakamakon wani abin tausayi daya
faru.
A firgice jiddah tace "Mr ye umma ? ko shiyasa
idan namata waya ba ta shiga a kwana biyun
nan ?
Tace "ai idan kikaga ummi sai kin tausaya mata
sbda firgicin data shiga ai na yi zaton ta gaya
miki a waya ma ?
Jiddah tace "wai me yafaru ne umma ?
Umma taja dogon numfashi tace "Uhum ai jidda a
ranar aka kashe Dr. khalifa da Fatima ,yanzu
haaka zancen danake miki fatima na kulle ana
tuhumarta da laifin kashe Dr. khalifa.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Jiddah ke
maimaitawa jikinta na rawa tabugi kirji tace
"Mama an kashe khalifa ?
Ta amsa cikin tausayi.
'"An kashe Khalifa jiddah kuma fatima tana cikin
mummunan zargi don ita da kanta ta amsawa
kotu cewa ita ta kashe shi.
Jiddah ta girgiza kai ta mike tsaye tace "Fatima
ba za ta kase Dr. khalifa ba, ko da ace ba ta son
shi ba ta da dalilin kashe shi akwai wadda na
sani wadda ke da dalilin kashe shi kuma shi ta
kashe shin ni ce zan fasa kwan, nasan waye
yakashe Dr. khalifa.
Alhamdulillahi.
Masu karatu a yi hakuri ayi jimirin biyoni a littafi
na hudu kuma na karshe don jin ya zata kasance,
waye yakashe Dr. Khalifa ?
A DAREN FARKO
36
NI na san wanda yakashe Dr. khalifa da dalilin
dayasa aka kashe dr. khalifa.Jiddah taci gaba da
tayar da maganar wanda yasa mahaifiyar ta ta
cikin tashin hankali, ta zaro idanuwanta gaba
daya cikin kaduwa take kallon jiddah tace "Ke
'yar nan kin san abinda ki ke fada kuwa ?
Na sani Ummah, "kin sani jiddah ?
"Eh na sani mana umma, idan babu rami babu
abunda ke kawo batun rami, wannn maganar da
idan mutum yadauketa ya san abinda yataka,
haka kawai baxai fada ba sai yana da hujjah
hujjar ma mai karfi.
Umma ta jinjina kai har yanzu fuskarta a razane
tace "Jiddah ki yiwa Allah da Annabinsa kada ki
kara furta wannan maganar ballantana wani
yajita kija bakinki ki shiru.
Jiddah tai murmushi tace "Ummah na yi zaton za
kitambayeni inda nasan wannan maganar me cike
da gagarumin sirri ba wai ki dinga rokar kada in
fada ba, yaya lallai in boye wannan maganar ko
kuma kiyi shakkar inda naji ta.
Umma ta girgiza kai tace "Jiddah tsoron hadarin
dake cikin maganar ne ya firgitani yasa narude ni
din ma dakike fadawa tsoro nakeji ballantana idan
magana tafasu kowa yaji, kin san irin wannan
maganar gagurama ce kuma ni banyi shakka don
na ce kina da masaniya akan kisan khalifa ba
sbda bazai yiwu kifadi hakan ba face lallai kin
sani, mamaki na shi ne a ina kika sani ke da ba
ki a kasar, to amma tsoron danaji yasa maganar
mamaki ta kau a zuciyata nake roko ki rufawa
kanki asiri ki rufa mana.
Da zarar kin furta wannan maganar za a shiga
tuhumar mu.
Jiddah tace "Umma yaya za ayi ina ganin gskiya
kiri kiri a rufeta, yanzu sai kisa ido a kashe
Fatima ? Alhali ba ita takashe khalifa ba dole in
bayyana wanda yakashe khalifa yau din nan,
tamike tsaye.
"Umma ki kwantar da hankalinki babu abinda zai
same mu sai alheri insha Allahu, itama umman
mikewa tsaye tayi tace "ta ina zan kwantar da
hankalina jiddah ? ai hankali ya bar kwanciya in
dai kika fasa wannan maganar ni dama na sani
ban fadi miki ba.
Tace "Ummah ko baki gaya min ba zanji ke dai ki
tamin addu'ar neman kariyar Allah ahine me
kowa da komi, tarike hannunta lokacin data yi
hanyar fita tace "jiddah kar dai kijefa kanki ckin
hadari, takatse ta umma bazaki tambaye ni
wanda yakashe dr. khalifa da dalilin kashe shi ba
sai rayuwa ta kike neman karewa to bari kiji,
"Kariya tana gun Allah ban taba tunanin zan dawo
nigeria a wannan lokaci ba haka kawai ina zaune
hankali na naji ya tashi, Allah ya dawo dani ne
don yatoni asirin wadanda sukayi wannan kisan .
Allah ya dawo dani ne don ya kubutar da Fatima
kinga kuwa ba ni da dalilin dazai sa in rufe bakina
don in kare rayuwata, jin an yi kiran sallar
magriba yasa jiddah tafita tana fadin "ina zuwa
ummah.
Hankalin ummah yatashi sosai zuciyarta tashiga
harbawa, kar fa yarinyar nan tajawo mana fitina
ya kamata in sanar da babanta halin da ake ciki,
wannan maganar me hadari wa zai sa kansa a
ciki don wauta ?
Tana cikin wannan tunanin babansu jiddah
yashigo tare da babban yayansu Alhaji Nazifi,
tace "Yawwa Alhaji gara da Allah yaka wo ka
jiddah dai ta dawo mana da fitina tana neman
jefamu ckin zargi.
Yace "me ya faru daga dawowarta ?
Ta bayyana masa duk abubuwan dasuka tattauna
da jiddah, hankalinsa shima yatashi, Nazifi har ya
fi abban na su fusata yace "kin ga yarinya mara
hankali ? wa yagaya mata ana irin wannan ?
Alhaji yce "Dakata, tanada dalilin fadin hakan, ta
gaya miki ?
Umma tace "Yo Alhaji ni da hankali na yatashi ina
na tsaya tmbayarta wanda take nufi ya yi kisan.
Yace "yanzu tana ina ?
Tace "ta fita nasan dai ba za tawuce gdansu dr.
khalifan ba ko gdansu fatima.
Yadubi Nazifi yace "maza nemo mini ita a waya,
zo muje masallaci mudawo, Alhaji Nazifi yayi
kwafa xuciyarsa cike da haushi nomban jiddah
tana dagawa yace "Ke fitinanniya munji maganar
dakika zo da ita sai ki zo kiyi mana bayani. Bai
jira jin abinda za tace ba yakashe wayar.
Suka yi alwala suka nufi masallaci. itama umma
alwalar tayi tai sallah zuciyarta cike da fargaba
sai a yanzu take son jin hujjar da jiddah ta taka
take furta cewa ta san wanda yakashe dr. khalifa.
****
A harabar gdansu ummi, jiddah ke tsaya tana
neman wata waya kiran yayanta yashigo, don
haka tafasa shiga gdan tadawo da baya zuwa
gdansu kafin baban na ta sudawo daga masallaci
itama tayi ta ta sallar.
Kannanta duka suna falon da abokiyar zaman
umanta hajiya zainab da suke cewa Anti, Abba da
Nazifi suka shigo har gara fuskar Abban tana
nunawa zai karbi maganar da fahi ; ta.
Nazifi kuwa gallawa jiddah harara yake kamar ya
shaketa yahuta, ya tsani ana zaune lafiya a tado
da ftina.
Jiddah na zaune gaban abbansu ta lankwashe
kafafu kanta na kasa tana mai bayanin daya
daurewa kowa kai, babu wanda yakatse ta sai da
tayi shiru.
Nazifi yaja tsaki yace "kai jiddah ni duk da haka
inain wannan abubuwan dakika fada bai isa ya
zamo hujja akan wannan gagarumin magana ba,.
Shari'a fa sabanin hankali ce kuma ita an yi mata
lakani da mace mai ciki ba a san abinda za ta
haifa ba, sannan hausawa sunce idan baka iya
kama barawo ba barawo sai ya kamaka, eh
abubuwan da kika fada mana ya isa a dubesu a
yi nazari amma ba zai isa gamsashiyar hujjar da
za a tunkari kotu da ita ba kai tsaye sai an yi
dogon bincike da taka tsan tsan sbda kotu ba
gun wasa bane. wannan maganar saita jefamu a
wahala.
Umma tayi farat tace "yawwa alhaji abinda nake
son ka kalla knan mutum yana ckin zaman sa
lfya bai dace yadauko ma kansa abinda zai zama
fitina gunsa ba, wannan magana ce me sarkakiya.
Jiddah tace "ki kwantar da hankalinki insha
Allahu Allah zai fitar damu ni dai addu'arku nake
nema, ina ji a jikina wani nauyi ne ya hau kaina
wanda ya zamo dole in yi magana a cikin wannan
lamarin idan nazauna inajin tsoro za ayi kwaba.
Gaba daya suka yi shiru kowanne zuciyarsa bata
gamsu da abunda jiddah ke niyyar yi ba a son
ransu abba ya hana amma ga mamakin su sai ga
abban na cewa "Allah ya taimake ki jiddah, Allah
ya tsareki.
Dama kowa ya san fatima ba ita tayi kisan nan
ba fatima ba za takashe khalifa ba.
*****
Daga wanna rana rayuwar Jiddah ta kasance a
boye babu wanda yasan tana kano sai 'yan
gdansu har zuwa ranar da kotu za tazauna don
yanke huku ? cin karshe tunda dai wadda ake
zargi ta amsawa kotu karara cewa ita tayi kisan.
A ranar fatima fuskarta ba tashin hankali sosai
idanuwan ta ba hawaye sai dai jawur dasuka yi.
Yau kotun ta cika makil, 'uyan'uwan fatiman har
wadanda basu taba halartar kotun ba yau sai da
suka zo. Ummi na zaune kusa dasu inna kamar
yadda tasaba kanta na kasa.
Fatima na tsaye kan minbarin amsa kara bayan
mai karanto kara ya karanto.
Kafin kowa yace komi sai akaji barrister abbas ya
tashi ya nemi izinin magana.
Alkalin yace "yana da damar yin hakan, yayi
godiya sannan yashaidawa kotu cewa yau ya zo
da babbar hujjar da zata gamsar da kowa cewa
ba fatima ce tayi wannan kisan ba, aka bashi
izinin yagabatar da hujjarsa.
Wata kofa ce tabude jidda ce tafito, lamarin
dayasa kallo yakoma kanta ana shirin ganin
abinda zai faru, itama fatiman kallon jidda kawai
takeyi cike da mamakin lamarin kamar yadda
fuskar kowa a kotun yanuna ckin wadanda suka
san jidda, kowa ma knan ballantana babbar
aminiyarta ummi.
Barrister abbas ya gabatar wa da kotu jidda da
kuma rokon kotu tabawa jidda daman gabatar da
bayanin datake dauke dashi, ake ce duk za a iya
yin hakan.
Bayan jiddah ta yi sallama tafara da fadin "Ina
gdan da nake zaune birnin london wani yamaci
naji wayata na ringi ? g ina dakkowa naga
nomban babbar aminiya ta ummi, hakan yasa
nadaga dasauri muka gaisa na tambayeta labarin
gida da rayuwa.
Tace "komi lfya jiddah, sai dai ni ina cikin
matsanancin tashin hankli wanda yasa rayuwat
ma gaba daya ta fita daga raina.
Nace "Subhanallahi me ke damunki kike fadin
haka ummi.
Tace "eh to jidda a iya saninki dai kin san tun
tasowa ta ma'ana lkacin da na mallaki hankalin
kaina babu abinda yake barazana da duk wani
farin ciki na rayuwata wanda yawuce dr. khalifa
ko ?
Na amsa mata "eh na sani ummi.
Tace "To dr. khalifa shi ne matsala ta ko kin san
cewa zancen auransa da fatima ya tabbata.
Nace "to kiyi hakuri mana ummi, ni dai na san
duk abinda ke faruwa Allah ne yahukunta hakan
zai faru sai dai kiyi hakuri domin kuwa lamari na
Ubangiji yadda yakaddara haka zai faru, cikar
imanin musulmi yadda da kaddara cikin abinda
yayiwa mutum dadi ko akasin haka.
Ummi taja dogon numfashi tace "Jidda kina nufin
in hakura da dr. khalifa ? duk lokacin dana bata
ina jiran dawowarsa daga grmany ya tashi a
bansa knan.
Nace "Bai tashi a banza ba idan har za kiyi aiki
da shawarar dazan ba ki, abinda nake so kigane
shi ne idan zuciyar mutum tadamu da son wani
abu kuma bai samu ba yadan gana ga Allah yayi
hakuri, yakaddara cewa Allah ne bai kaddara abin
nan da rabonsa bane to Allah zai dubi niyyarsa ya
musanya masa abin nan da wanda yafishi, don a
lokuta da dama mukan so abunda ba alheri bane
garemu, abinda nakeso inkaiki gareshi ummi shi
ne ki kaddara dr. khalifa ba rabonki bane a bisa
abinda Allah ne yakaddara ba wani ba, domin
wani ko wata bai isa ya kwace maka abinda Allah
yakaddara rabonka bane, in dai kin yarda da haka
to saikiyi hakuri na san abinda ciwo amma in kin
daure kin yi hakuri don Allah, zai miki maganin
damuwar ki, ance idan so cuta ne hakuri magani
ne.
Ummi taja dogon numfashi tace "jidda hakika
shawararki itace akan hanya anma wannan
hanyar binta ba zai yiwu ba idan nabita mutuwa
zanyi.
Nace 'Haba ummi ya ya za ace wanda yabi
hanyar gskiya yamutu.
Tace "jiddah ba zan taba iya hakuri da dr. khalifa
ba idan kuwa nace zan hakura dashi to mutuwa
zanyi.
Nace "To ni dai kuma ban san abinda zan ce miki
ba ummi ba ni da abinda zance sai dai kiyi
&akuri.
Tace "Ba zan yi hakur ba jiddah na yarda na rasa
dr. khalifa amma yadda na rasa shi sai dai
kowacce mace tarasa shi, babu macen da za ta
moreshi.
Na ce "ummi me kike nufi da fadin haka ?
Kai tsaye tace "Kashe shi zanyi.
A nan ne jidda tayi shiru.
Yayinda jama'ar kotu suka rude da hayaniya ana
fadin "Lahaula" wasu na salati, sai da aka
tsawatar sannan kowa yai shiru.
Mai shari'a ya dubi jiddah yace "kotu ta ji abinda
kikace, akwai karin bayani ko shi knan hujjar ta
ki ? sannan kuma akwai shaidar da za ki
tabbatarwa da kotu cewa kunyi wannan magana
da wadda kika kira ummi.
Ta gyda kai tace "Ina da kwakwarar hujjah ya
mai shari'a.
Cikin rudani na tambayi ummi "kashe shi za kiyi ?
Tace "Abinda kunnanki yagaya miki shi nake nufi
tare da kara tabbatar miki da hakan kar ki dauka
da wasa nake......
Na katseta nace "ummi an taba irin wannan
maganar da wasa ?
Tace "Yawwa gara da baki wahal da kanki gun
shakkar abinda nafada ba.
Nayi ajiyar zuciya nace "ummi meye dalilin da
yasa za ki furta wannan maganar mai tada
hankali ?
Tayi dariya tace "na gaya miki idan har na rasa
khalifa to sai dai kowa yarasa shi har iyayensa
da kowa nas.
Nace "amma lallai yau ummi na tabbatar ba ki da
hankali kuma ba ki da tunani.
Tace "in dai akan son dr. khalifa ne ba damuwa
duk abinda za ki kirani kinyi dai dai.
Idanuwana a makance suke babu abunda zan
hango illa abunda nasa gaba zan aiwatar wanda
shi nake ganin zai bani mafita, haka kunnuwana a
toshe suke ba zan iya sauraron kowani nasiha ko
gaskiya ba da ace zan vi hanyar gskiya wannan
hanyr da kika nuna mini ba zan kauce mata ba
tunda hanya ce ta hakikanin gskiya.
Na marairaice murya "ummi bakin ki ne ke furta
wannan kalma na ta'addanci ki ji tsoron Allah
kidaina fada ni har kin sa tsoro ya kamani.
Tabushe da dariya tace "kidaina damuwa jiddah
babu wanda nataba fadawa wannan maganar sai
ke, kuma na gaya miki ne sbda ke din sirrina ce
babu maganar da ba zan iya gaya miki ba duk
nauyinta kuwa.
Nace "meye amfanin gaya min din tunda na ba k8
shawara kin ki dauka, har da bakinki kince abinda
nafada gaskiya ne kiyi wa Allah ummi kiyi hakuri
da dr. khalifa kada soyayyarsa tasa ki haukace,
don ni na fara zargin kin samu tabin kwakwalwa
ne, lfya kalau kike ba za kidinga furta wannan
mummunan lafazin ba.
Tace "Lafiya ce ta sani furta wa kuwa jidda zan
kuma aikata.
Na ce "to meye laifin khalifa don bai so ki ba, ana
soyayya dole ? ke yanzu za a tursasa ki son
wanda ba kya ra'ayinsa ?
Tace "Nima bance miki dr. khalifa ya aikata min
wani laifi ba, zan kashe shi ne don kowa yarasa
shi sbda sun nuna min rashin tausayi shi da
iyayansa sun san ina son khalifa amma lokacin
daya dawo daga germany ya rikice akan cewa
fatima yake so sai suka watsar da komi ba sa
kallon kowa sai dansu suka fifita bukatar sa akan
ta kowa aka bashi fatima sbda gata ana bukatar
farin ckinsa, idan har khalifa zai kasance ckin fari
ciki to basu damu da kowa ba da komi ba
wannan ne dalilin dayasa zan kashe shi kowa
yarasa.
Nace "kai lallai ummi kin cika mara hankali, to na
ji za ki kashe shi ba kya tsoron kema kar a kashe
kin ? kinsan fa hukuncin wanda yai kisa kashe shi
akeyi ko bakisan da haka ba.
Dariya sosai tayi tace "na sani mana jidda ai ni
mutuwa hutu ce gareni da akan rashin khalifa, ke
bari in gaya miki wani abu matukar ina cikin
duniyar nan ba zan bar khalifa yarayu da wata
diya mace ba ne ko zan yi hakuri da auran khalifa
ba dai fatima ba don fatima ta ci amanata ta
yaudareni na gama gaya mata sirrin zuciyata da
niyyar ta taimake ni tasama mini fada a zuciyar
khalifa amma ina maimakon tayi min hakan ganin
son da khalifa yake mata sai tayi amfani da
wannan dama tabi hanyar data mallake zuciyarsa
har yadinga nunawa tamkar zai mutu ne idan
yarasat., duk fa fatima da khalifa sun san halin
danake ciki basu tausaya min ba, jidda ko ke din
nan bakisan sirrin zuciyata cikin abinda yashafi
khalifa ba yadda fatima tasani, ta san ydda nake
kwana ba na barci, ta san yadda nake kwana
idona na zubar da hawaye, ta san yadda nake
yini ba ci ba sha, duk sbda na rasa khalifa, amma
fatima tashare tashiga fafutuka akanta, har sai
data mallakeshi, ita kadai yake kallo, itace a
gabansa, wannan shine dalilin dayasa nace yadda
narasa shi itama tarasa shi.
Nace "Don Allah ummi me zan gaya miki ki
fuskanci cewa wannan kuskure ne babba za ki
tafka ? duk wannan abubuwan da kike fada ba
hujja bane wanda za tasa ki raba fati da khalifa
ta wata hanyar m bllantana ta wannan
mummunar hanyar, don Allah ummi kiyi hakuri.
Tace "Jiddah karki bta bakinki da ace, zan iya yin
hakuri da tuni na ba wa kaina hakuri.
Nace 'na ji ki bi duk hanyar da za ki bi don ganin
kin rabasu amma ba wannan ba.
Tace "jidda kudimmu dayawa sun salwanta akan
in raba fati da khalifa in ja hankalinsa sai
yakasance ma kamar soyayyarta ake kara masa,
babu wata hanya da za tayi tasirin rabasu sai
wannan hanyar da zan bi, dole in bita kiyi hakuri
kawai
Nace "To naji tawace hanya xa kibi ki kashe
shin ? ashe ke yar ta'addace ban bansani ba ?
Tabushe da dariya tace "duk lokacin dakika samu
labarin an kashe dr. khalifa, ni ummi ni na kashe
shi, idan kin dawo kya ji bayanin hanyar da zan
bi....
To nan ne takashe wayarta.
Tun daga wannan rana ban sake samunta a waya
ba, hankalina ya tashi sosai idan nayi yunkurin
kiran wani sai in ji a jikina kamar ba da gaske
ummi take ba ko kusa ban yarda za ta iya aikata
kisan kai ba, to kada yakasance nafada ita kuma
ba gaske take ba dana rasa yadda zanyi sai nayi
shiru naci gaba da addu'a. Ba a dade dayin haka
ba wata rana da safe wani matashi yazo gdan
danake zaune a london yace sako ke tafe dashi
yana son magana dani, nace "daga ina ?
Yace "Daga kano, na zo miki da wani muhimmin
abu amma na roki yazamo sirri a gareki.
. ****
Jiddah zaria,,, to ko wani sirri ne kuma
wannan ???
A DAREN FARKO
37
Duk da cewa zuciyata bata kwanta da mutumin
ba amma na daure nace ba kmai shigo muka
zauna a falo yana duba na yamiko min wani
memory card, nace "Na meye.
Yace "karbi xan miki bayani.
Na jima ina kallonsa sannan nace "kana tunanin
zan karbi abinda ba ni da masaniya akan sa.
Yayi murmushi yace "don Allah kar ki damu
wannan abin ba zai taba zama abin cutarwa
gareki ba face yazamo abin amfani na tabbatar
ba za ki taba mantawa da zuwana ba yayin da
kika fahimci muhimmancin wannan abin a gunki
idan bukatar sa ta taso.
Nace "to ai ni bansan daga ina kake ba, ban san
meye a cikin sa ba ballantana in san dalilin daya
sa ka ban shi, ka fada min mana idan kana son
in karba.
Yace "jidda kiyi hakuri dai ki karba wannan
memorin ba wani ya shafa ba illa aminiyarki
ummi.
Yajefo min kan cinyata yamike tsaye yana cigaba
da kallona yace "na daina lallabaki akan ki karba
idan kin ga dama ki jefar dashi nidai ai na kawo
miki, ina son kisani lokacin da ummi tayi miki
wayatace za ta kashe dr. khalifa ina zaune duk
wani bu da kuka fada yana ckin wannan memory
daga bisani za kiga wasu muhimman abubuwa
da xai miki amfani a ciki, in kuma har yanzu baki
gamsu ba za ki iya jefar dashi.
Yana gama fadar haka ya kama hanya zai fice,
na dauki memodin jikina na rawa nabishi ina
rokon yadawo yagaya min sunansa kuma yayi
min karin bayani don ba karamin rikitani yayi ba.
Yace "Babu wani bayani dazan kara miki, jin
sunana kuma ba ya da amfani gareki a yanxu
tunda dai kikaji nafadi haka kin san wannan
memorin yanada amfani gareki, kiyi hattara ki
kiyaye kada ki bude shi sai bukatar hakan ta
taso.
Iya abinda yafada min knan yafice yabarni tsaye
da memory card a hannuna jikina na rawa.
Jidda tayi shiru.
Kowa ma a kotun shiru yayi ana kallonta, masu
rubutu na yi masu nazari na yi. fatima na tsaye
kyam inda aka tsaida ta ko motsi ba ta yi ba,
kallon dakowa yake wa jidda itama shi take
mata.
Ummi kuwa da kai tsaye ita abin yake shafa tana
zaune tadaura kanta bisa cinyarta itama dai bata
motsa ba, mutanan da basu sn ita abin yashafa
ba basu kalleta ba iyayan marigayi dr. khalifa da
iyayan fatima fatima da wadanda suka san itace
umin da ake nufi sun dawo da kallonsu kanta, ina
zaton shi ne dalilin daya sa ta sunkuyar da kanta
bata dago ba, to ama dayake hankalin mutane na
kan jidda da mahukunta suna son jin yadda
al'amarin ya kaya sai basu motsa da wani abu ba
suka fuskanci jiddah don jin yadda za ta kasance
cikin wannan al'amari mai ban mamaki, aka ba
ma jidda umarnin taci gaba bayyana labarin
datake bayyanawa, tadora da fadin.
Bayan tfiyar wannan mutumin nazauna shiru ina
tunanin al'amarin nayi shawarar in bude wnnan
memory a wautata in ga meye a cikinsa, haka
kawai sai naji tsoro ya kamani, kamar wadda
akayi wa dabaibayi nakasa budewa kuma nakasa
bayyanawa kowa al'amarin, nayi masa ajiya mai
kyau har zuwa lokacin danaji gabaki daya na
kasa samun natsuwa idan nakwanta bacci sai
bacci ya gagareni, in kuwa nasamu barcin zan yi
ta fama ne da mafarkai masu ban tsoro, dole
tasa nabaro london ina ckin karatu na nadawo, a
ranar dana dawo din nasamu lbrin an kashe dr.
khalifa lamarin daya tayar mini da hankali sosai,
nana da nan natuno hirar da mukayi da ummi a
waya wanda tun daga wannan rana ban sake
samun ummi a waya ba sannan itama bata sake
kirana ba, a wannan lokacin ne nadakko wannan
menoryn nabude naga abinda ya kunsa.
Jidda takara tausasa lafuzanta cike da ladabi
tace "ya mai shari'a wannan memorin shi ne
shaidata dukka abinda nafada yana ciki.
Mai shari'a yabada umarnin akawo na'urorin
dazasu haskawa dukkan jama'ar da ke gun abin
da ke cikin memorin, nan da nan aka kawo
jama'a suka baza idanuwa cike da mamaki, har
lokacin ummi bata daga kanta ba kuma babu
wanda yayi mata magana.
Abinda allon talabijn din yafara nunawa shine
ummi ce tsaye a wani guri ita kadai, ta sha ado
tayi kyau dayawa ,wani matashi yabullo ta
bayanta yace "ummi gani na zo.
Ta waiwayo tadubeshi tana murmushi tace
"sannu dazuwa yaya.
Yayi murmushin shima yace "yauwa ummi ya
akai naga fuskar ki ckin damuwa ?
Daga gani wani abu yana damun zuciyarki, gaya
mim ko meye zan taimake ki in dai zan iya.
Tayi murmushi tace "na san za ka taimakeni yaya
shi yasa na fiddo maka damuwata, duk da cewa
magana ce nazo maka da ita mai tsananin nauyi.
Yabushe da dariya yace "kada nauyinta yadameki
maganar dakika iya dauka nikuma sai ta
gagreni ? Dubeni da kyau fa ummi.
Ta jinjina kai.
Yaci gaba da fadin "ummi tun lokacin dana ganki
zuciyata take bala'in son ki, kina ta shareni kin ki
ba ni hadin kai, kin sha walakantani a gaban
yarana ina kyaleki, kowa na mamakin yadda naki
tsayawa in dauki kwakwaran mataki akan ki, na
san ke da kankikin san kina yaudarar kanki ne
kina ganin kamar kinfi karfi na ne shiyasa ban
dauki mataki akan ki ba, ba haka bane ummi da
ace na yi niyyar rabaki da rayuwarki gaba daya
da yanzu na gama dake, da ace na yi niyyar
dauke ki in boye da yanzu na yi, amma dayake
duk ba wannan manufar ce a zuciyata ba na sa
miki ido duk dacewa kullum kwanar duniya
azabtuwa nake da soyayyarki, Allah ne yasa min
sonki a zuciyata ba tare da manufar komi ba face
in aure ki, ban taba sha'awar auran diya mace ba
sai ke, tun daga ran da na ganki sai naji kawai
ina sha'awar ace na gina gda na ajiye matar aure
nima ta haifa mini 'ya'ya yadda maza keyi sai
gashi ban samu hadin kanki ba.
Aka hasko fuskar ummi tayi murmushi tace "ba
komi ka kwantar da hankalin ka yaya lokaci ya yi
da za kasamu hadin kaina yadda kake bukata.
Yace "Za ki aureni ummi ?
Ta amsa "zan aureka in dai kai min wani aiki shi
ne sharadin aurena da kai.
Yace "wani irin aiki ne wanann ummi gaya min
shi komi wahalar shi zanyi in dai zai sa ki aureni,
aurenki shi ne cikar burin rayuwata a duniya, ba
ni da bukatar komi domin na mallaki dukiya, mace
sai wadda na zaba in yi amfani da ita, ke kadai ki
ka tsaya mina zuciyata ba na son bata miki rai
na fi son in aureki in zauna dake a matsayin mata
ta, yanayi ne daban taba fuskanta ba a rayuwa
ta.
Unmi tace "wannan damuwa ta ka ta zo karshe in
dai kayi min abinda nakeso zan mallaka ma kaina
a matsayin matar aure.
Yace "To fada min meye wannan aikin ko zan
rasa raina zan miki.
Tayi murmushi tace "Akwai wani mutum mai
suna Abakar ana cemasa dr. khalifa.
Shi nake so kawai ka kashe mini in dai khalifa
yabar duniya kazo a daura mana aure.
Yavushe da dariya mai karfi yace "shi knan ko da
wanda za akashe bayan shi ?
Ta Girgiza kai "shi kadai ne ba na son gani a
duniya.
Yace "an gama yaushe kike son a kashe shi ?
Tace "A DARANSU NA FARKO da amaryarsa kuma
ina so a kashe shi ne ta sigar da za ayi zaton ita
amaryar ta sa ce takashe shi, in dai kayi min
haka ka biya dukiyar auran ummi.
Yasake bushewa da dariya yace "in dai kisan
kaine ko ta wacce hanya mun iya ta sai dai in
bamu sa kammu ba.
To daga wannan shafin sai aka hasko dakin da
aka kai fatima, fuskar ummi ce ta bayyana yaya
na binta a baya tabude mai murfin kwaba
yashiga.
Sai kuma aka hasko ummi t shiga daya murfin
kwabar ta rufe.
A wani shafin kuma an hasko fuskar dr. khalifa
ne ya bude kofar kwaban da yaya ke ciki, sai ga
yayan ya fito tsulum ya tsaya gaban dr. khalifa
cikin zafin nama yadamke masa baki ya hantsila
shi kan gado yasa filo yadanne bakinsa.
Sai aka hasko fuskar ummi ta fito ta maida
murfin kwaba ta rufe ta hau kan gadon da
karamar wuka a hannunta ta nunawa dr. khalifa
daf da kunnansa takai bakinta tace "Ni ce ajalin
ka.
An hasko fuskar khalifa yanata wutsil wutsil
bashi da damar magana.
Sai kuma aka hasko yaya ya amshi wukar
hannun ummi ya chakawa dr. khalifa sau biyu,
sai suka fice daga dakin suka rufe kofar shi da
ummi.
Bayan wannan,
Sai akaga fuskar yaya a zaune kan kujera unmi
na gefensa yace "Aiki dai ya kammala kuma ya yi
kyau ummi ya batun aurammu ?
Ummi ta harareshi tace "wai kai meyasa ba ka da
hankali.
Yaya yazaro ido "Ni ne ba ni da hankali ummi ?
Tace "To ina kaga hankali.
Yayi murmushi yace "Ni kuwa nake da hankali.
Ta girgiza kai tace "babu rashin hankalin daya
wuce kace kai dinnan kanada hankali kai daman
ka yarda zan aureka ?
Ya kura mata ido yace "ummi ni kikawa haka ?
kin san waye ni kuwa ? ki guje shiga cikin hadari.
Tamike tsaye tace "shi yasa nace ba ka da
hankali kamar ni in rasa wa zan aura sai dan
ta'adda, ko ka manta kai dan ta'adda ne, ka
gaggauta fiddani daga zuciyarka domin bazaka
taba samuna ba.
Yayan yamike tsaye yanuna ta da yatsa yace "kin
yi babban kuskure ummi sai kinyi da na sani da
kika mini domin baki yaudareni ba illa kanki.
Ta kyalkyale da dariya tace "yaya ba zan yi da na
sani ba har abada domin ka mini aikina dr.
khalifa dai ya mutu kuma ba zai dawo ba buri na
knan yadda na rasa shi kowa ma yarasa ka ga
zancan nadama ma gareni bai taso ba, in kuma
za ka kashe shi ne to bismilla.
Yace "Ba zan kashe ki ba sbda na yi alkawarin ba
zan kashe ki ba ummi amma xan ba ki mamaki
daman jikina ya ba ni za ki yi min wannan
butulcin shi yasa na shiryawa hakan, kin z hannu
ummi.
Daga wannan ranar ba za ki kara yaudarar wani
a duniya ba, idan ma kin ci gaba da rayuwa ni
daman nawa ta kare.
Iya abinda memorin ya kunsa knan TV tayi dif
kamar yadda kotun tayi shiru kamar ba kowa duk
da yadda tacika makil da mutane, abin mamaki
har yanzu kan ummi na kasa bata dago ba.
Bayan wani dan lokaci mai shari'a yadago kansa
bayan ya ajiye biron da yake rubutu yace.
"Kotu ta gamsu da bayanan da jidda tazo dashi
tare da hujjojin dakowa yagani a zahiri, don haka
ba tareda bata lokaci ba nan take wannan kotu ta
sallami fatima kuma ta bada umarnin a kawo
ummi da wanda yakashe khalifa, shari'a ta dawo
kansu wannan yakawo karshen zargin da akewa
fatima na kisan mjinta Dr. Abubakar Saddiku a
bisa kwararan hujjoji na shari'a.
A DAREN FARKO
38
Karfe takwas na dare agogo ya nuna, malam
musa mahaifin su fatima na zaune kan tabarma
da rediyo gefensa yana jin shirin iya ruwa fidda
kai da akeyi gdan rediyon kano.
Inna tafito daga dakinta tazauna dab da shi tce
"malam ni fa lamarin nan na fatima ya dameni.
Yarage sautin rediyon idanunsa na kanta yana
mata kallon rashin fahimta yace "me kuma
yafru ?
Tace "ka ga yau satin ta biyu da fitowa daga
kurkukun nan amma har yanzu ta ki daina kuka
idan an tmbayeta sai tace wai babu komi, ni abin
nata har ya fara ba ni tsoro.
Malam yace "kira min ita.
Ta kwalawa fatima kira tafito a sanyaye ta
tsuguna a gefe yace "Haba fatima wannan kukan
da kike yana nuna cewa tamkar ba ki ki yarda da
kaddara bane shi duk abinda Allah ya hukuntawa
bawansa va makawa sai ya faru, godiya ya
kamata muyi wa Allah daya takaita mana
al'amarin ya tsaya a haka, addu'ar da muke yi ce
tayi tasiri da karshen al'amarin yazo, ko meye na
tsananta damuwa, tunda kika fito daga kurkuku
kike kuka kin ki cin abinci isashe, kin ki magana
kin daina barci isashe to yaya kike son mi miki ?
Fatima tayi ta yi tahadiyi kukan dake makale a
idanunta ta kasa ta dora kanta a guiwarta
hawaye suka dinga ambaliya a fuskarta, tace
"kuyi hakuri baba wallahi ina jin ciwon
damuwarku sakamakon damuwar da nake ciki
wadda tayi sanadin damuwarku ban san yadda
zanyi indaina kuka ba tabbas da na daina amma
ba yadda zanyi nima ban san lokacin da nake
kukan ba, zuciyata ce ba za ta iya jurewa
abubuwan dasuka faru ba, ina cikin bakin ciki da
damuwar abinda ummi tayi min nakasa sabawa
da damuwar rashin khalifa, ummi bata yi min
adalci ba da tasa aka kashe khalifa na san tana
sonsa amma ita tanuna min ta hakura dashi ta
gaya min cewa idan bai aureta ba kashe zhi za
tayi da.....
Malam ya katseta yace "Fatima khalifa ya rsu
kuma ba zai taba dawowa ba har abada, tunda
aka halicci duniya bbu wanda yataba dawowa
bayan ya mutu haka khalifa ma ba zai dawoba,
kin g kuwa idan hakane babu amfanin aci gaba
da tattaunawa da maganar, zai fi kyau miyi
hakuri, wannan al'amarin daya faru mu barshi a
matsayin kaddara, Dr. khalifa babu abunda za
muyi masa illa addu'a, Allah yaji kansa yakai
rahama kabarin sa, kuka da zaman damuwa ba
zai sa yadawo ba kuma ba zai goge abin da
ummi tayi ba, da ace zai goge ko yadawo mana
da khalifa da sai ai tayi, kiyi hakuri Allah yabaki
wani mijin.
*****
Tun a lokacin da kotu tagama yanke hukunci
ummi tafadi bata kara sanin inda kanta yake ba,
a bisa dole aka kaita asibiti tun tana numfashi
har ya kaance ba ta iya numfashi da kanta sai da
taimakon oxygen.
Kowa sai Allah wadai abinda ta aikata akeyi tare
da mamai mai tsanani, abinda yafi zama abin
mamaki shi ne yadda ummi ta tayar da hankalin
ta bayan mutuwar khalifa, ta fi kowa nuna
damuwarta akan mutuwar ta sa, tunda aka binne
dr. khalifa ummi take kuka ta rasa sukuni, kullum
ckin zirga zirgar masu taimakon ta don fidda
fatima daga zargi tare da binciko wanda yayi wa
khalifa kisan gilla, abin mamaki wai itace ummul
haba isin kisan, wannan shi ne a na zatom wuta
a makera sai ga ta a msaka.
Hakika fatima ta ba ma kowa mamaki ta bar ma
mutane abin tattaunawa kowa na fadin albarkacin
bakinsa ciki dai har da iyayan ita kanta ummin
ballantana wadanda suka haifi khalifa, mama ita
ke tare da ummi kullum tun kashe dr. khalifa har
yau ita tafi kowa sanin damuwar da ummi ke ciki
da irin kukan da takeyi a lokuta da dama ita
maman ce ke lallashin ummi amma ckin wani irin
yanayi ya bayyana cewa ummi ce ta kashe
wanda take kokawa mutuwarsa kukan da batayi
ba a lokacin da mahaifin ta yarasu, abin
tambayar anan shi ne shin me yasa ummi take
kukan mutuwar khalifa ? bayan ita takashe shi,
sbda bata son rayuwarsa a doron kasa a bisa
gurguwar hujja wai don ta rasa shi kowa ma sai
dai yarasa idan akace don ta yaudari mutane take
wannan kuka tana zargin daman asirin ta zai
tonu ne, kokuma ta yi abin ne don ya dameta,
shiyasa take kokawa kanta don ta san ta yi
babban kuskure da ganganci a rayuwarta. To
koma dai meye Allah kadai yasan dalilin kukan
ummi bayan kisan datasa aka yiwa dr. khalifa da
kanta.
Ga ta nan dai a bisa gadon asibiti batasan inda
kanta yake ba, karkashin kulawan jami'an tsaro,
likitoci sun bada sakamakon binciken dasukayi
akan ummi cewa damuwa tasa tashiga wannan
halin, akwai yiwuwar tadawo normal akwai
yiwuwar tarasa ranta, sbda tsananin damuwar
datake ciki yayi yawa.
Mahaifiyarta hajiya hauwa ce me jinyarta,
hankalinta a tashe sosai yake sbda yadda ake
yayata labarin a kafafen yada labarai na jihar har
da makota, tayi kuka ta yi kuka har ta ba uku
lada, ba a barin kowa ganin ummi sai dai tasa
ummin a gaba tana kuka, tunda aka kawo ummi
bata taba farkawa ba, numfashinta yahau ya
sauka sai dai wani lokacin tana motsawa kamar
za ta farka sai kuma tacigaba da barcin da in
barda ana ganin numfashinta sai kace ta mutu
,kunyar mutane yasa hajiya hauwa ba ta iya fita
ko ina batasan yadda za ayi ta iya hada ido da
iyayan khalifa ba, dansu kwaya daya ummi ta yi
sanadiyar barinsa duniya sbda wani hujjarta mara
tushe ballantana makama.
Tuni dai yan sanda sun sami nasarar chafke
matashin nan me suna yaya wanda ya tabbatar
shi yakashe dr. khalifa da hannunsa a bisa
umarnin ummi, bai wahalar da shari'a ba ya
amsa laifin sa har yayi magana da yan jaridu
cewa ai dama kawo kansa hukuma ne kawai bai
yi ba amma zaman jiran kamu yake tunda shi da
kansa ya bayyanawa duniya ta yadda al'amarin
yakasance kuma yabari aka ga fuskarsa to ai ya
yi talla da laifinsa knan.
A gdansu khalifa abin ya zamo tamkar na
jajantawa yadda jama'a suka dinga ta zuwa
bayan 'yan jaridu dake zuwa neman labari, Abba
na iya magana da 'yan jarida ita kam mama
wannan al'amari ya dawo mata da mutuwar
khalifa sabo fil a zuciyarta, tayi kuka ta yi kuka
kukan da bata taba irinsa ba a rayuwarta, jama'a
na bata hakuri tana fadin, "ku kyaleni in yi kuka
abin kukan ne ya sa mun, ummi ta cuci kanta me
yasa ta hau dokin zuciya.
Wasa wasa lamarin mama tadaina barci tsabar
takaici ne fal a zuciyarta, dan na su kwara daya
shi ne don masifa sai da aka salwantar.
Wannan daran ma zama tayi daram a dakin abba
tazuba tagumi tana kallonsa yana barci ita kuwa
ta kasa tayi juyi ta yi juyin shiru, ta gaji ta tashi
tazauna hawaye wani na bin wani, tadunga tuno
yadda al'amrin yakasance bayanmutuwar khalifa.
A DAREN FARKO
39
UMMI takan zauna tana kuka kamar ranta zai
fita, watarana mama ta isketa a zau? e a harabar
gdan tana sana'ar ta ta, mama tace "ummi ya ya
kika fito nan kina kuka? kowa yana kallonki duk
kukan na ki ya wuce ckin gida sai kinzo waje.
Ummi tace "mama wai ba ni da dalilin kuka ne?
duk wanda yashigo gdan nan abin mamaki ne
don ya ganni ina kuka? Wallahi mama tun daga
ranar da aka sa khalifa a kabari har yau har nima
in mutu ba zan daina kuka ba.
Mama tace "haba ummi a matsayimmu na
musulmi dole mu dogara ga Allah a bisa kaddarar
da Allah yadora mana, ni ce fa na haifi khalifa wa
ya fini sanin ciwon sa? a cikina ya rayu nayi
nakudarsa na raine shi, bbu wanda zai nuna min
son khalifa tunda na hakura na karbi kaddara ya
dace kema kiyi hakuri.
Ummi tadago jajayen idanunta tadubi mama tace
"na san da haka mama amma kin san wani abu
daya, kuna kukan rashin khalifa ne don ku kuka
haife shi nikuwa kukan danake daban ne da zan
iya bayyana miki wani gagarumin sirrin dake
zuciyata da daga yau na san ba za ki kara cewa
indaina kuka ba mama.
A wan? lokacin da ummi ta fadwa mama wannan
magana babu abunda tasa a ranta face sirrin da
ummi ke nufi bai wuce na soyayyar da take wa
khalifa ba.
Abba dake ta barci yamike zaune kamar an tashe
shi ya zubawa mama ido yace "maijidda wanan
tunanin zai ci gaba da hanaki barci a kowane
dare idan har ba za kiyi hakuri ba.
Mama tafashe da kuka tace "Alhaji ta yaya tunani
da damuwa za su fita daga xuciyata, wane irin
bakin ciki ne wannan?
Yace "kiyi hakuri Allah ne yakaddara kwanan
khalifa ya kare shiyasa suka samu nasarar kashe
shi, kuma da sukayi hakan meye meye ribar da
suka samu banda faduwa, tunda aka kai khalifa
kabari ummi bata sake samun natsuwa ba babu
abunda yaja mata hakan face hakki, haka shima
wanda tasa yayi kisan hakki ne yasa ya tonawa
kansa asiri da kansa.
To kinga lah za muyi wa godiya muyiwa khalifa
addu'a .
*****
Jiddah ce tadaga labulen dakin inna tare da
sallama, inna ta fadada fara'arta tace "maijidda
ke ce tafe da yamman nan, daga ina? zauna ga
kujera nan.
Bayan sun gaisa tace ina fati;a?
Inna tace "Tana daki shiga.
Ganin fati a kwance yasa tabata rai tace "wai don
Allah fatima sai yaushe za ki kwantar da hankalin
ki ki dinga walwala? dubi yadda kika rame kika yi
duhu kullum idanuwan ki ckin zubar hawaye har
sun zama jajaye fati me yai zafi haka?
Fatima tamike zaune tace "jiddah duk wadannan
abubuwan dakuke ganin laifina da rashin dauriya
na kune baku san ina dauriya akan su ba, jiddah
tun da nake rayuwa a duniya ban taba kwatanta
so ba sai akan khalifa, ko da cewa a baya na yi
niyyar auran musbahu na ami? ce ne sbda da
darajar iyayena amma ko sau daya ban taba jin
digon soyayyarsa a zuciyata ba, ni kadai nasan
asarar dana tafka wadda ba za ta taba mayar da
ko da kwatankwacin mijina ba ballantana fa
daidai dashi .
Jidda tadafa mata kafada tace "kiyi hakuri yadda
Allah yabaki khalifa ya amsa abinsa haka zai
musanya miki da wanda zuciyarki za taso,
lamarin na ubangiji ne babu abunda zai fi karfinsa
in dai bawa zai dogara dashi to ya isar masa.
Fati tace "jidda har ban san kalaman da zan yi
amfani dasu gun gode miki ba, kin yi namijin
kokari a gareni Allah yayi miki sakayya da
mafificin alherin sa na duniya da lahira.
Jidda tace "fatima godiyar nan ta isa na gamsu
Allah shi ne abin godiya daya nufeni da in yi
hakan da bai ba ni iko ba ban isa in yi ba, yanzu
wata alfarma nake son ki yi min.
Fati tace "ki fada jidda ko mene zan miki in dai
xan iya, kin fi karfin komi a gareni.
Jidda tace "sanin hakan danayi shiyasa nazo, a
safiyar yau din nan ne mahaifiyar ummi taxo tana
rokona in taimaka in zo in roke ki ki je asibitin da
ummi ke kwance ki dubata domin ta farfado
amma tana ta kuka tana rokon a kawo mata ke
da iyayan dr. khalifa za ta fada maku wata
maganar, dafarko nace da hajiya babu ruwana sai
nagata kama kuka tana rokon in taimaketa tace
wllhi jidda nima ba laifina bane ba ni da masaniya
ko ta kusa ko nesa game da abinda ummi ta
aikata,.
Fatima ta jinjina lamarin sosai a ranta, yanzu
kam a duniya ba ta da makiyin daya wuce unmi,
ji tayi kamar za ta hadiyi zuciya ta mutu sbda
bakin ciki me za tayi da wadda tarabata da
masoyinta, kai hakika ummi ta gama cutar ta har
me za ta gaya mata.
Babu yadda ta iya da jidda tana ganin kimarta da
yawa don haka ya amsa mata cewa za ta, ta
sanar dainna da malam suka mata izinin zuwa,
dogon hijjabinta me hannu da nikab tasa ravon ta
da fitowa waje tun ranar da aka sallamo ta daga
kurkuku, hawaye suka dinga zuba daga idonta har
suka iso asibitin., a lokacin taga mama suma
suka iso su biyu jidda takira hajiyar ummi a waya
tace dasu sun zo tafito tashiga dasu dakin da
ummin take.
Duk yadda zuciyarsu ke cike da tsanar ummi da
bakin ciki sai da jikinsu yai sanyi, sakamakon
yadda suka ga ummi ta yi wata muguwar rama
kamar an sauya ta, ta yi baki ta fita daga
hayyacinta, babu wanda yazauna sun kame ne
suna kallonta.
Ummi ckin rawar murya hawaye wasu na bin
wasu tace "Abba, mama, fatima na gode kwarai
da kuka danni zuciyarku kuka zo nan, na bukaci
zuwanku ne don kuga halin danake ciki kafin Allah
yakarbi rayuwata, domin ni tawa ta kare ba zan
kai labari ba ba kuma so nake ku tausaya min ba
don ni ba abin tausayi bace,
kuyi hakuri masu karatu a littafin babu page
47-51
Kwanan ummi goma sha shida a gadon asibiti
karkashin kulawar lokitoci da jami'an tsaro
tarasu, bayan aman jini ta hanci da baki data yini
tanayi saita dinga sai tadinga zabura tana gwara
kanta da bango tana ihu, "Na cuci kaina, shi ne
kadai abi? da bakinta yake furtawa har tadaina
numfashi, lokacin da labarin mutuwarta yazo
kunnan fatima ta yi kuka har sai da zazzabi da
ciwon kai suka rufeta..
*****
Wai shin masu karatu kutambayeni ina musbahu
yashiga mana? ku biyoni kuji.
Lokacin da musbahu ya tabbatar ya rasa fatima
sai ya kaddara a ransa cewa dama ba matarsa
bace, .
Musbahu gdan kawun sa malam habibu yafara
zuwa ya sanar dashi abinda yafaru, kawun ya ji b
dadi a ransa amma ba yadda za ayi in dai mutum
mai hankali ne da adalci babu yadda za ayi yayi
wani zargi akan malam da inna don sun rike
musbahu tsakani da Allah, Allah ne bai kaddara
fati rabonsa bace.
Musbahu ya shaidawa malam cewa zai tafi garin
bauchi gun yayar mahaifiyarsa ne sbda yana so
yayi nisa da kano a dalilin ba ya so yaga daurin
auren fatima.
Karfe biyar da rabi na yamma yashiga gdan
goggo mairo dake ckin garin bauchi tayi mamakin
ganinsa tace "ango na amarya kaine tafe?
Yace "Gwoggo ina wuni mun sameku lfya.
Tace "lfya kalau yashi kaje dakin au sagiru yana
nan yana barci kayi wanka kayi sallan xan aiko
ma da abinci idan kaci sai kazo mu gaisa sosai.
Sagiru kusan sa'an musbahu ne shi ne dan
goggo na biyar ya biyo mata biyu maza biyu,.
Tun a ranar yafara devewa musbahu kewar
damuwar dayake fama da ita, sbda mutum ne me
ban dariya, da alheri ga son mutane.
Musbahu ya bayyana masa abin da yarabo shi da
kano, sun tausaya mai sosai ganin damuwar
dayake cki yasa nan take goggo tace ga diyarta
nan hafsa in dai yana son ta ta ba shi, musbahu
yayi dan jim bai ce komi ba, goggo tace "ko bata
yi maka bane in dai ba ka son ta babu dole.
Yace "ba haka bane goggo ina tunanin yadda
malam yace ya bani fatima tace ta amince sai da
na saki jiki da ita nabata amanar soyayya ta
sannan tace ba ta so na, dr khalifa take so shi ne
ra'ayinta nikuma ra'ayin iyayanta, nayi mata
uzuri cewa ba ita ta zabeni ba niyyar biyayya ga
iyaye tayi .
Gwoggo mairo tayi murmushi irin nasu na manya
tace "musbahu duk wannan abinda yafaru
kaddara ne Allah ya hukunta cewa ba matarka
bace, idan xa ka lura duka kwana nawa yarafe a
daura maku aure khalifan ya bayyana, da ace
matarka ce ba zai bayyana ba ko ya bayyana
kuma ba zaiyi tasiri a zuciyarta takalle shi da
sunan so ba.
Ba wai ina gaya ma hakan ne don kaso hafsa ba,
in kana raayin hafsa ga ta nan in ba ka ra'ayi
kayi zamanka har Allah ya baka wadda kake so.
Musbahu yakara dukar da kai yace "wallahi
goggo hafsa tafi karfin namiji yaki ta, in ta
amince dani ma ta yi min alfarma domin ta girmi
ajina.
Goggo tace "karka sake fadar haka kaje gareta ku
daidaita kanku, Allah yatabbatar mana da alheri.
A cikin sati biyu musbahu da hafsa suka fahimci
juna, yasameta yarinya mai sauki da son mutane
kamar mahaifiyarta, ga ladabi da biyayya, kowa
ya yi farin ckin wannan al'amari a dangin su, nan
da nan aka tsaida magana babansu hafsa yace
zai ba musbahu aron gda su zauna kafin su koma
kano, ba wani kudi musbahu yakashe ba illa iya
abinda yayo sai da goggo tai masa fada cewa
daya suke dashi da hafsa a gdan nan.
Bayan wata guda aka daura aure sukayi biki
sosai suka kashe kudi, musbahu har mamakin
gatan da suka nuna masa yake, aka gama biki
lfya aka kai amarya dakinta, a ranar da zai shiga
dakin ne yadinga tunanin abubuwan daya tanada
zaiwa fatima a ranar da aka kai masa ita, ashe
ba matarsa bace yanzu haka tana chan da
angonta ta ma manta dashi shikuwa yana fama
da ita a zuciyarsa.
Sai da yadinga addu"a Allah yataimake shi
yarabashi da tunanin fatima kada ya cutar da
hafsa sbda ya lura hafsat ta yi dammarar zaman
aure dagaske tare da biyayya, ckin ikon Allah
yataimake shi yasamu natsuwa a zuciyarsa
yamaida hankali sosai gun kyautatawa matarsa
sukayi zamansu lfya kowa yana sha'awar auran
na su.
A DAREN FARKO
40
Kusan watanni shida knan da rasuwan dr. khalifa
an dan samu cgaba a rayuwar fatima sbda ta fara
rage damuwa har ta shiga wataislamiyya nakusa
dasu da akeyi alhamis da juma'a, ta kuma fara
tunanin komawa makaranta a halin yanzu ba ta
da aminiyar da ta wuce jidda koda yaushe suna
tare itama jiddan bata koma london din ba ta
dawo da karatu? ta BUK tana karanta mass
comm. kasancewarsu tare da jidda ya taumaka
kwarai gun debewa fatima kewa sai dai har yanzu
idan tatuno dr. khalifa takan yi kuka mai tsanani
sbda soyayyar da take masa tayi mata yawa a
zuci, shi yasa yau da jidda tazo mata da wata
magana sai da taji kanta yana mata tsawa.
Ta zubawa jidda iso kawai tana nazarin fuskarta
bata katseta ba sai da taji tayi shiru sannan
tamike zaune tace "jidda maimaita abinda kika
gaya min yanzu.
Jidda tabata rai tace "kina nufin baki ji abinda na
gaya miki ba?
"Na ji ina so in kara ji ne.
Jidda tace "cewa nayi yayana usman ya aikoni in
mika mai kokon bararsa gareki da fatan za ki
amsa mai bukatarsa.
Fatima tayi ajiyar zuciya tace "ni kam jidda na yi
mamaki danaji wannan maganar a bakin ki, na yi
zaton ko yaushe ke nake gaya wa cewa babu
wani namijin da zan iya sawa a zuciyata in haka
ne kuwa bai dace ki zo min da batun wani namiji
ba.
Jiddah tace "Fatima kin san dai ba zai yiwu ki
zauna babu aure ba don dr. khalifa ya rasu dole
sai dai kiyi hakuri ki amshi kaddarar da Allah ya
hukunta miki yarda da kaddara shi ne cikar
imanin musulmi mumini.
Ko kusa fatima ba ta jin dadin hirar don haka
tace "To na ji ba ni lokaci zanyi tunani.
Ganin yadda fuskar jidda ta nuna rashin jin dadin
maganar tasa tace "kiyi hakuri jidda ba cewa nayi
ba na son dan'uwanki ba wlh zuciyata ce ke cikin
matsanancin hali har yanzu karfin hali nake ni
nasan abinda nake ji game da ciwon kisan da
akayi wa khllifa, ,na kasa sabawa da wannan
damuwar, duk namijin danace xan aura a yanxu
na cutar dashi domin ba zan ba shi kulawar data
dace in bashi ba, wannan shi ne dalilin dayasa na
fidda batun aure a zuciya ta, zan yi zamana haka
har lokacin da Allah zai karvi rayuwata nima.
****
To a bisa wannan ra'ayin fatima take tafiya da
gaske ba ta son wani namijin yasake shiga
rayuwarta, ba ta son sake soyayya dakowa sbda
wahalar datake sha, amma ina yadda kasan kofa
aka bude ma maza nasu sota, wasu su kan biyo
tagun malam ganin bbu fuska ta fuskar fatima,
wasu ma ta gun tsohon surukinta Alhaji
muhammadu mahaifin dr. khalifa kasancewar
zumuncin su ya dada karfi, Abban yana da
tacewa a cikin rayuwar fatima, ya maida ita
kamar diyar sa dan ma dai ba t son zuwa gdan
ne a dalilin yawan kukan da take,.
Bayan dawowar ta daga islamiyya yau ta idar da
sallar azahar inna ta shaida mata cewa mama ta
aiko nemanta, nan da nan rant yabci, to kawai
tace tamike tayi wanka tasa wata doguwar riga
ta shadda tasa dogon hijjabi fuskarta ba fara'a
tashiga gdan su mama ta tsaya a harabar gdan
tana kallon dakin dr. khalifa, har yanzu bbu
abunda aka taba a ciki? sa har motocin sa suna
nan cikin tamfal ta jima tsaye a vun daga bisani
tagoge hawayen daya gangaro mata tawuce cki
tasamu mama a cikin dakinta tana kwance bisa
gado da carbi a hannunta tana ja.
Ganin fatima yasa tamike cke da fara'a tace
"sannu da zuwa diyata.
A sanyaye tazaun a kasa ta gayar da ita, mama
ta zuba mat ido tace "fatima kullum kara ramewa
kke kina duhu kullum b ki da kuzari da walwala
wai shin haka raywa zata tfi, tunda fa ba mu
muka halicci kammu ba ba mu da iko kuwa da
kammu dole ne muyi hakuri da abinda Allah ya
jarrabe mu.
Tadinga sharar kwalla tana fadin "wallahi mama
ban san yadda zanyi in daina damuwa b, damuwa
ta min yawa ji nake kamar nim mutuwa zanyi.
Mama tace "mutuwa lokaci gareta fatima idan
kwana yakare kowa zai mutu, kidaure kidin ga
sakin ranki kina walwala kuma ya zama wajibi a
cikin masu sonki ki fidda guda daya ki aura,
samun abokin rayuwa zai rae miki damuwa.
Tadago tdubi mama tace "aure fa kikace mama,
har da ke a masu cewa in yi aure kema ba ky
kishin khalifa?
Mama tayi murmushin karfin hali tace "Allah sarki
fatima to idan nayi kishin khalifa ya zanyi, zan
iya dawo dashi duniya?
Ta girgiza kai.
Mama taci gaba da fadin "A daran jiya Barrister
Nuraddeen ya zo gdan nan gun alhaji yana son ya
tambayar masa malamko zai ashi auranki, abba
yace in tambayar masa ke in kin amince ba ya da
matsala da barriater nura sbda ya san iyayansa,
da rayuwarsa gaba daya ba bukatr sai anyi wani
vincike a kansa.
Kanta yakara mata nauyi zuciyarta takara kuntata
tarasa abinda za tacewa mama da abba sunfi
karfin komi a gareta, ga jidda na naci akan
yayanta usman itama jiddah ta fi karfin ta
wofantar da maganarta sbda sadaukar daranta
da tayi don ganin ta ceci rayuwarta.
Mama tace "kina da damar da zkije kiyi tunani,
idan har mce takasance mai hankali to kada tabi
ta kyale kyalen duniya gun zabar miji tazabi
nagari kawai, ko dayake zabi yana gun Allah idan
mutum ya dogara da Allah sai ya zaba masa miji
na gari wanda zai rike shi tsakani da Allah.
*****
Fatima tadawo gda cke da tunani a ranta abi? da
ta lura dashi shi ne zabar mijin aure ya zamo
dole in ba haka ba ba za a kyaleta ba, kuma abin
takaici suna bullowa ne ta hanyar dasuke da
kima a gunta.
Ta bayyanawa innarta yadda sukayi da mama
dakuma maganar usman yayan jidda.
Inna tace "fatima matukar kina son kwanciyar
hankalin mu to ya zama wajibi ki fidda miji ki
aure mu ma mun gaji da surutun da akeyimana a
dangi da mutanan unguwa.
Fatima tamike tashige daki takira jidda a waya
bayan sun gaisa tace "ki turo min Usman in gan
shi.
Jidda tace "sai yau kikaga damar bshi izini yazo.
Haushi yasa fati kshe wayarta tana tsaki.
Bayan sallar isha'i jiddah takirata tace Usman
yna bisa hanya,.
wanka tayi ta murza mai tashiga atamfa super ta
tsaya tana kallon kanta wai yau itace za tayi
zance.
wayarta ta kama ringn tadaga a sanyaye tayi mai
sallama, Allah yasa da fatima nake magana,
Abinda yce mata knan. Ta amsa "Ni ce.
Yace "to nima ni ne usman ina jiranki a kofar gda
tunda yau an min izinin zuwa..Tsaye ta iske shi
jikin motarsa yana danna handst, gabanta yafadi
hasken fitila ya haske mata shi tun daga sama
har kasa, kananan kaya ne a jikinsa, za suyi
tsawo daya da dr. khalifa, sajensa ya kayatar da
fuskarsa in barda haka ba za a kirashi maikyaun
fuska ba.
Ya amsa sullamar da tayi masa ckin fara'a yace
"Gimbiya fatima kn wahalar dani da yawa, da kin
san yadda nake fama da tunaninki a zuciyata da
kin tausaya min baki min wannan jan ran ba.
Itadai batsan abinda za tace masa ba tayi shiru
kanta a kasa, yaci gaba "fatima ina fama da
matsananciyar soyayyarki a zuciyata don Allah ki
ba ni hadin kai ina bukatar ki ckin rayuwata, ina
da damuwa mai yawa.
Tayi wal da ido a lokacin ne suka hada iso tace
"ban fahimci abinda kake nufi ba.
Ya gyara tsayuwarsa yace "fatima na san kinsan
uwa daya uba daya mu*e da jidda,na yi aurena
shekaru biyu da suka wuce a nan kano matsalar
da na samu itace matata farida batasan me ake
kira aure ba, ina nufin duk wasu hakkokin miji da
suka rataya wuyan mace farida bata san su ba ko
kuma ta sansu ba za ta sauke bane sbda dalilin
da ita tasani...
AYYAH KUYI HAKURI RUBUTUN SUNYI DAMEJI
BA NA IYA GANI...
Abinda ke faruwa a gdan usman ba ya yiwa kowa
dadi a danginsu sbda fitinar matarsa tayi yawa,
ko dayake tun kfin auran an sha gaya msa gdan
dayake neman aure ba gdan tarbiyya bane,
mahaifiyar su farida sai abin da tace da babansu
yake yi, kuma a haka ta trbiyyantar da diyanta
mata, usman yawatsar sbda soyayya dayasa
ransa .
Hjiyr su farida tan da tsananin son abun duniya,
son da farida ke ma usman ne yasa ta amince za
ta ba shi , yayin da dabi'un gdan ke damun
iyayan usman, babansa ya ce ba zaiyi aure ba sai
ya samu aiki ,bayan ya samu aikin akayi bikin
inda babansu yabashi gdan dasuke cki a zoo
road.
Da farkon auran an mori soyayya, a cikin wata na
uku kachal da auran usman yafara fuskantr
matsala da farida dayawa tatatara mai
kawayenbanza a gda, ko da yaushe gdansa cike
da "yammata wani lokacin har da zawarawa da
matn aure irinta wadanda suka fi karfin mazajen
su, sai yawon gdajen kawaye, abin takaici wasu
yammatan har da samarinsu ke zuwa daukarsu a
taya su hira a shiga har falonsa, girke girken
abinci, abin takaici ba zai zo yasamu gdan sa ba
baki ba sai dai yashige daki yazauna.
Yayi kokarin yim hakuri ya kasa yashiga nunawa
farida rashin dacewar abinda take, ranar da ya
fara mata maganar fiddo da ido tayi tace "ina
ruwanka dasu man? kadubi fa yadda suke
girmama ka amma kace su daina zuwa, ni kadai
zan dinga zama a gdannan ga unguwa shiru,ni
ban saba zaman kadaici ba a gdan mu sai dai
kayi hakuri.
Daga nan tashiga yin allurar hana daukar ciki ba
da sanin sa ba, tadaina zama a gdan tadaina
mishi abinci sai randa taga daama, ya yi ya yi ya
saita ta ta ki, shi dalilin daysa yafara tunanin
aure don yasamu sauki tawani bangran, lokacin
daya furt a gdansu kowa yai murna sbda tausaya
masa da halin dayke cki, sai dai abin fargabr
wace mace zai aura su zauna lfya da farida a
yadda ba ta da kunyar nan ta raina kowa.
Shima din bai san wa zai aura ba ya maida
hankalinsa ga addu'a, kwatsam ydor idonsa akan
fatima lokaci guda yaji wani salon soyayar da bai
taba jin ta ba., a gdansu ya ganta wataran t zo
gun jidda, byan tfyarta ykira jidda yasha kunu
yana tmbyrt shin fatima ta tsaida mijin aure ne,
tayi dan jim tace "yaya sonta kake?
Yace "son ta nake ko ba za ta amince min ba.
Tace"ko ban sani ba amma dai ina fargabar
hakan zan sanar da ita.
Fatima tashiga zuciyar usman kwarai dagaske
yashiga addu'ar Allah ya mallaka mai zuciyarta
don yna hangen maslaha a tare da aurenta, Allah
yataimakeshi aikin dayake fafutukar nema Abuja
yasamu a wannan satin, fatan sa idan fati ta
amince yatafi da ita su zauna. chan yabar farida
takarata a kano.
Yabar fatima a gdansu zuciyarta ba wani
kwantawa yayi da auran usman ba, ta kwanta
tana tunanin yaya za tayi knan.
washegari da yamma barrister nuraddin kuma
yazo da tasa bukatar datafi na usman zafi,
lamarin dayasa taji kamar tayi ta kuka sbda
damuwa.
Yace "fatima ina fatan sakona ya zo gareki, Allah
ya jarrabi zuciata da tsananin soyayyarki da
bukata mai zafi a kan auranki ina fatan zan samu
hadin kanki.
Kwarjinin barrister yahanata hada ido dashi
hasalima batasan abinda za tace masa.
Tadai cije tadaure tace Allah ya tabbatar mana
da alheri.
Ya dan ji sanyi a ransa yayi murmushi yace "knan
kin ami? ce da soyayyata fatima?
Taji dam a zuciyarta ita dai ba za ta iya cewa a'a
ba idah kuma tace eh ta yi karya.
Bata sake cewa komi ba yawuce gaba tayi mai
rakiya yace "fatima ban san abinda kika fi so ba
ballantana in kawo miki ga wadannan kudin kisayi
duk abinda ranki ke so.
Tadubi sabbin kudin a razane tace "ina zan kai
wannan kudin barrister, don Allah kabarsu ni ban
bukatar komi.
Yace"nima ban ce kina bukata ba na ba ki ne a
matsayin kyauta kuma ba a mayar da hannun
kyauta baya, na hadaki da girman Allah ba dan ni
ba ki karba.
Hannu biyu tsa tare da risinawa takarba tace "na
gode Ubangiji Allah yasaka da alheri.
Ya lumshe ido yace na ji dadin wannan addu'ar
ta ki.
Zai shiga motarsa knan malam yadawo daga
anguwa, fatima tashige gda dasauri yayin da
barrister yazube a gun yana gaida shi, da fara'a
malam musa ya amsa tare da kara masa godiya
akan namijin kokarin daya musu a kotu, yace ba
komi sai dai ya zo ne yana son fatima kuma ya ji
ta bakinta ta amince taimakon dayake son a
masa shi ne a bashi ita dawuri don tfya ce a
gabansa.
Malam yace "ba komi yabashi kwana biyu zai
neme shi.
Bayan tfyar barristr malam yashiga gda da kudin
daya basu masu yawa ga wanda fatima tashigo
dasu, inna tace "wallahi malam nikam na kagu a
aurar da fatima a huta da wadannan fitinannun.
Wannan zuwan da ake wannan yazo da katuwar
mota, gove ma wani yazo an dau ido an sanya
mana a unguwa, ni dai tafidda wanda tafi so
tsakanin lauya da usman a daura auran a kaita
kowa ya huta.
Malam musa yace "nima abinda nake bukata
knan a yau din nan za ta gaya min wanda
takeso..
Fatima na kuka tace "don Allah baba kuyi hakuri
zuwa da safe zanyi istihara duk wanda Allah ya
zaban min shi ne zabina nikam ba ni da zabi.
Duk inda aka ce Allah angama magana gaba daya
takashe musu jiki dole suka kyaleta.
A DAREN FARKO
41
A wannan daren fatima *wana tayi tana kai
kukanta ga Allh tana rokon yazaba mata mijin da
zai fi alheri a tare da ita, da mutum biyun nan
takwana a zuciyarta amma da usman ta tashi ba
brriater b.
Shi taji ya fi kwanciya mata a rai duk da cewa shi
yana da mata amma hakan taji shi taji tafiao, don
haka kai tsaye ta sanar da babanta cewa yab
barrister hakuri ta tsaglyar da Usman a matsayin
mijinta,suka sanya mata albarka tare da fatan
Allah yasa hakan shi ne mafi alheri a tare dasu.
Duk yan gdansu usman fatansu ftima ta ami? ce
ta auri usman sbda ba karamar damuwa bace
dashi a gdansa, ba kamar jidda wadda duk tafi
kowa tsanar farida ko gaisuwa ba ta hadasu har
faridan ta daina zuwa komi na danginsu itama ba
mai zuwa inda take dama ba haihuwa ba ta mike
kafa ne tana abinda taga dama.
Lokacin daya samu tabbas daga mahaifin fatima
cewa an bashi ita yaturo manyanaa, hannu
yadaga yana wa Allah godiya, nan da nan aka kai
kudin aure aka sa ranar aure nan da sati hudu
daurin aure da biki gaba daya.
Ya shiryawa fatima gda da lefe mai ban mamaki,
har aka kusan biki farida bata sani ba domin
yanzu yawonta ya kara kaimi tunda juma'a kawai
usman ke zuwa kano yakoma abuja ran lahadi,
sai da yarage saura kwana uku kachal daurin
aure wata kawarta nafisa tazo gdan da yamma
tace da ita.
'Farida anya kuwa kin san me ke faruwa dake
naga kiba ma kikeyi ba kisan tashin hankalin
daya tunkaro ki ba ko?
Farida tayi mata wani irin kallo na rashin fahimta
tace "me kike nufi.
Nafisa tabude jaka tafidda katin daurin auren
usman da fatima ta dora mata a cinya ya ta ce.
"Karanta anan za ki fahimci me nake nufi.
Farida ta tashi zaune hannu na rawa ta dauki kati
ganin sunan mijinta yasa ta gwalalo idanu tace
"nafisa a ina kika samu wannan katin?
Tace "a gari mana ana nan ana ta rabawa jama'a
na gayyata ni nasan tunda baki mana zancan ba
jiya a gdan hajiya ladidi na san baki sani ba.
Gumi yadinga ketowa farida ta kasa motsi sai
numfashi take fitarwa da kyar dga bisani tatashi
tace "nsfisa bar masa gdansa zanyi.
Nafisa tace "wannan shi ne aikin banza harara a
duhu, kina zaton yanzu kina gaban usman ne,
idan ma kin tafi cewa zaiyi ya huta, tashi zakiyi
yanzu muje gdansu amaryar mu ci mutumcin su
muyi musu kaca kaca mu firgitasu ta ydda ba xa
tayi sha'awar shigo miki gida ba, shi kuwa bakin
munafikin idan yadawo ki nuna ki nuna mai
hauka ki ganar dashi kuransa ta yadda zai shiga
taitayin sa dole a fasa auran.
Farida tazauna daram a kan wannan shawarar
don jin zuciyarta take kamar za ta fashe.
****
A ckin motar da usman ya siyawa farida suka fito
tare da nafisa, farida ce ke tukawa fuskarta a
tamke kamar za ta fashe tana ci gaba da daukar
shawarar nafisa har suka isa kofar gdansu fatima
kasancewar nafisan ta binciko komai.
Cike da isa suka shiga, sukayi sa'a fatima ce
kadai a tsakar gda tana wanke wanke.
Mamaki ya kamata ganin mutane sun shigo musu
gda ba sallama.
Farida ta nunata da yatsa tace "ke ce fatima?
Tace "eh ni ce lfya.
Kawai fatin bata ankara ba taji farida ta cafko
mata wuyar riga da karfi ta jijjiga ta tace "ni ce
farida matar usman idan ma baki sanni ba yau ki
sanni ganina ya fi ji na.
Inna tafito dagudu daga bandaki tana salati tace
"ke yar nan lfya za ki zo har gda kiyi mana
tijara?
Farida tasaki fatima tanuna inna da yatsa tace
"ke yi min ahiru munafuka idan kina neman kai
da wannan figigiyar 'yar taki ne ki kawota gdana
kusha mamaki kwadayayyu kawai.
Fatima tayi tsalle itama za tadamki farida, inna
tariketa tace "kyaleta fatima duniya ce suk abinda
kayi za ayi maka, kishiya dai duk bala'in ta za
amata gda dai sai kin shiga takashe ki jahilar
banza da wofi.
Nafisa tace "ai ba cewa mukayi karta shigo ba,
mun fi so ma tashigo mu nuna mununa muku su
waye mu shi yasa yanzu muka fara zuwa har gda
mu sanar daku.
Farida tace "ga ku ga gdan usman nan daidai
kushigo kugani idan idan kuna tsammanin
barazana muke muku.
Suka fice a fusace suka shiga mota, farida ta
fizga da karfi suka fita daga layin suna kyakyata
dariya.
Karfe ukun yamma uaman yashigo gdan a gajiye
yake sosai sbda yau shi yatuko kansa, tun daga
hanya yake tunanin yadda zai fuskanci farida da
maganar auransa, duk abinda ake ciki, ya sha
alwashin yau zai sanar da farida, tun da aka fara
batun auran tunanin dayake knan bai san tashin
hankali gashi ita kuma anan takware.
A falo ya sameta baiyi mamakin kin amsa mai
sallamar datayi ba, dan haka shima bai kalleta ba
yawuce da jakarsa zuwa dakinsa yashiga wanka.
Farida tashigo a zafafe zu-iyarta kamar wuta don
tsabar bala'i hatta idanuwanta sunyi jawur,
idanuwanta suka fara dira kan wayarsa ta dauka
hoton fatima ne yafara yi mata maraba ta sha
ado ta yi kysu abinta har ba a magana.
Wato ma har akan screen usman yake dora hoton
fatima, batayi tunanin komi ba tadaga wayar ta
dokata akan tayal ta tarwatse gaba daya, daidai
lokacin usman yafito wanka hankalinsa yatashi
dayaga barnar da farida tai masa, ya zubawa
wayarsa ido mai tsaadar gaske yarasa abinda zai
ce mata sai ya tsuguna zai kwashe sim din sa, ta
daddage ta hankada shi tace "wa to ma ka
maidani mahaukaciya ba ka a lokacin kulani ko?
Ya tattara ta ya watsar gefe guda yace "Ba ki da
hankali wa zai saurari marar hankali, abinda zan
gaya miki ki gaggawar shiga hankalinki tun kafin
ki jawa kanki abinda za ki zo kina nadama.
Cikin daga murya tace "awai nadamar data wuce
na aurankada nayi, ka cuceni ka ci amanata ban
taba zaton kana ckin munafukan maza ba sai
yau...
Saukar mari mai karfi tajia. kuncinta wnda ya gigi
ta tafita dagudu tadauko wuka, ,ganin haka yasa
ya muedeta zai amse wukar, taja wukar da karfi
tazuge mai hannu, jini yafara zuba duk da haka
sai da ya karve yace "ba ki da hankali farida, ba
ki da hankali.
****
Tafiyar su farida da nafisa gdansu fatima akayi
jugum ana tunanin wannan bakon bala'i ,fatima
kuka take tana fadin "inna ba zan iya da wannan
masifaffiyar matar ba na fasa auran usman don
Allah ki kirashi a waya yanzu ki gaya masa na
fasa auran sa yazo ya amshi komi na sa yazauna
da matarsa, kina ji har cewa take sai ta zamo
ajalina.
Inna tace "ke ba komi irin barazana ce yau kika
fara jin inda akai irin wadannan abubuwan, to ki
dogara ga Allah matar usman ba kowa bace akan
wasu matan don duk abinda kayi wani ya ninka
naka kuma anga karshensa, haka duniya tagada,
duk wannan abinda tayi ta yi ne don a tsorata
ace an fasa idan an fasa din taci galaba daga nan
ta samu damar takawa yadda take so, ki kwantar
da hankalinki addu'ar da muku da wadda kikeyi
insha Allah za tabaki kariya ba abinda zai sameki
sai alheri, ba na son ki gayawa kowa ma.
*****
Jikin fatima yayi sanyi sosai har dare ba ta da
kuzari, lokacin da usman yazo ma haka tafito
masa fuskarta ba walwala sai yaji duk abin
duniya ya yi masa zafi.
Yace "fatima meke faruwa ne akwai damuwa a
tare dake don Allah ki gaya min,.
Tadago tayi mai wani irin kallo tace "dama haka
matr ka take?
Gabansa yafadi yace "me yafaru?
Ta labarta masa duk tijarar da farida da kawarta
sukayi musu, ransa yabaci yace "na ji dadi
datazo har gda ta nuna muku mugun halinta, ai
da farko na fara gaya mikikikace ba kya son ji,
don Allah kiyi hakuri zan dauki mataki a kanta,
barazaana ce kawai don ta tsorataki babu
abunda ta isa tayi miki ke ba a garin ma za ki
zauna ba a ina za taganki ballantana tayi miki
wani abu.
Ganin fatima ta ki sakin ranta hankalinsa ya dada
tashi, sai kawai gani tayi ya durkusa a gurin yana
bta hakuri, tace "haaba haba usman ba girmanka
bane.
Yaki mikewa tsaye yace ba zai tashi ba sai ta ce
ta hakura, dasauri tace "na hakura na hakura.
KARSHE
karfe sha daya aka tabbatar musu da cewa an
daura auran usman da fatima, farida tayi kasa
tana birgima tare da fadin "ahikenan na shiga uku
na gama yawo.
Isha ta daga ta tace tashi baki shiga uku ba,
fatima abin da za ayi shi ne idan usman yadawo
gdan nan kinuna masa kuranki da nadamarki, ckin
ruwan sanyi sai mu gasata mu korera da kissa.
Gaba daya sukayi na'am da wannn shawara.
Karfe goma sha biyun dare usman ya iso gdan,
har zai wuce dakinsa sai dai yafasa ya murda
kofar dakin farida,. Ga mamakinsa sai yaga ta
saki fuskarta ta amsa mai sallama tare da mai
sannu daxuwa.
Usman ya saki baki galala yana kallonta cike da
mamaki da farin cki a zuciyarsa.
Da gari ya waye ne take tmbayarsa ina za akai
amaryar bataga anyi shirin komi a gdan ba.
Yace "ai abuja za mutafi da ita anjima tunda kin
ga gdan nan ya yi muku kadan. tace ai ma hakan
yayi daidai kaima za kafi jin dadin zaman abujan
amma dai zanyi rakiya ko tunda dama ban taba
zuwa ba.
Yayi dan jim bai so hakan ba amma ya daure
yace "shknan sai ki shirya mutafi.
****
Karfe go;a sha biyun ranar talata an gama shirya
amarya fatima za a tafi abuja, shi kuwa ango da
uwargda suka taho a sabuwar motarsa.
Babbar hudubar hajiya itace "kin san dai baki
taba budar ido kin ganni dakishiya a gdan nan ba,
haka yan uwanki idan kim saki baki kin zamo
wadda tarako mata duniya, xa kizo kina nadamar
da za tasaki kuka da idonki.
Farida tasaki ranta sosai kamar ba ita ba ta
gayar da dangin mijinta tare da tmbayar ina
amaryar take za taje su gaisa,jidda da tafi kowa
tsanar farida tayi tsagal tace "kin ga malama ba
ruwanki da amarya kiyi harkarki tayi ta ta.
Farida tayi murmushi tace "haba jidda meye don
na ce zanje mugaisa.
Daya daga cikin yayyan usman hajiya hadiza tace
"kin ga dakin nan shiga ni ban son hayaniya.
Tamike tashiga dakin da aka nuna mata tayi
sallama, suka amsa tace "na san baku sanni ba ni
ce farida matar usman na rakoshi taryar amarya
ne.
Daya a cikinsu tace "ai kin kyauta mun gode
sosai.
***
Farida ta kwana ne a dakin usman sbda ta
marairaice masa yan uwanta dana fatima
tsangwamarta sukeyi, har ckin ransa ya amince
da ita har yaji a ransa ba dadi, yace to tadawo
dakinsa tazauna kawai.
Tayi ta amfani da damar data samu gun jan
ra'ayinsa yana bata kulawa, da safe ma bata
barshi ya fito daga dakin da wuri ba duk da ya
san da yan baka a gdan amma sai yadinga ji da
farida bai son damuwarta, har su jidda suka
gama hidiman cin abincin su da wanka.
Farida dashi usman din suka shigo, farida tai
saurin zama kusa da ita takamo hannunta tace
"haba amarya wani irin kuka ne haka kamar
zamanin da, sbda fa in deve miki kewa nazo in
dan tayaki zama kafi? ki saba don Allah ki hakuri
ki saki ranki.
Farida ta kalallame usman tahana shi sakewa da
fatima da zarar zai shiga dakin sai tabi shi tana
fadin, "man muje muga halin da amaryarmu ke
ciki. Shi duk bai san kishi bane ya dauka dai
kyautatawa ne shiyasa yake biye mata.
Farida tabar usman a falo tashiga daki ta fada
toilet takira wayar isha take tambayarta yaya za
tayi tahana uaman kwana da fatima.
Isha tace "shiga za kiyi dakin ke kadai ki nuna
mata wuka ki cemata wallahi idan tayarda usman
yashigo lallai sai kin kasheta, idan usman
yashigo lallai tai ta ihu har sai ya fita, to da
zarar ya fito ke kuma sai ki janye ra'ayinsa kuyi
daki, gobe kuma sai mu shirya mata wani tuggun
a haka har yagaji da ita yakoreta kiyi zamanki a
abuja.
Farida ta kyalkyale da dariya tace 'kai Allah yabar
mana ke isha kin iya tsara tuggu shiyasa nake
sonki.
Tace "sai kinji ni aminiyar...
Ba karamin frgita farida tayi ba, jikinta yadauki
rawa sakamakon ganin usman tsaye a kanta yana
mata wani irin kallo.
Ya zabga mata wata muguwar harara yace
"kaiconki Farida,zuciyarki tana miki saka da
mugun zare, dama biyoni kikayi don ki rabani da
matata ko?
Allah bai baki sa'a kin kori fatima ba kanki kika
kora, don ina son ki tattara ki bar min gdana na
sake ki.
Faida takwala kara zata fara yi mai hauka yafice
yashige dakin fatima ya sama kofar key,.
Fati tatashi a tsorace tana kallonsa, nan da nan
idonta yaciko, yayi murmuahi yace "haba fatima
sai kace kinga dodo.
Tashiga mai magiya, ko kula ta baiyi ba yakashe
fitila, tun tana kokarin kwatar kanta har tagaji
tahakura.
****
Da kyar fatima tatashi tayi sallan asuba taci gaba
da barci, bata farka ba sai sha dayan safe.
Ta tsuguna tagaishe shi cke da fara'a ya amsa,
tace "ina anty farida mu gaisa?
Yayi tsaki yace "ba ta gdan.
Ina tatafi?
Bansan inda tatafi ba.
Tayi mai wani iein kallo wace irin magana ce
wannan?
Yajawota jkinsa dakarfi yahadeta da kirjinsa
takama kuka tana kici kicin kwacewa.
Yace "dama kin hakura kin hadu da cingam.
Hankalin fatima yakara tashi ganin yadda yake
neman cire mata riga, Allah yabata sa'a tafisge
kanta ta gudu ckin dakinta.
Kafin tarufe kofar ya danna kai yatsaya yana
mata dariya, yace "kin fiye tsoro fatima.
Ta durkus tana fadin "Don Allah kayi hakuri na
tuba.
Yarungumeta tsam yana shafa mata jiki, yace
"wai don Allah fatima so dadi gareshi ko wahala?
Me yasa ciwon so yakeda daci a zuciya?
Me yasa soyayya ba ta barin zuciya tazauna
lafiya.
Ba ni wannan amsar".
Alhamdulillah.
Daga taku
RABI'ATU NASIDI ABUBAKAR.

You might also like