Alqawarin Allah Huguma

Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 201

🪐 *ALK'AWARIN ALLAH* 🪐

_HUGUMA_

0️⃣ 1️⃣
0️⃣1️⃣

"Allah ya taimakeki" lafazin da ya shiga kunnenta kenan,lafazin da a bakin


mutum daya take jinsa,furucin da ko mutuwa tayi ta dawo bata jin zata kasa tantance
daga bakin wanda yake fitowa dare da rana,a hankali ta waiwaya fuskarta qunshe da
murmushi,yana tsaye daga bayanta kamar koda yaushe,wannan annurin data saba gani
kan fuskarshi kowanne lokaci na nan shimfide saman fuskarsa,kwarjini cikar zati da
haiba cakude saman kyakkyawar fuskarsa,batasan me ya shigeta ba,sai taji bacin rai
ya sauko mata a take,b'acin ran daya sanyata ta dinga ja da baya,ja da bayan daya
zama silar data soma ganinshi dishi dishi,yana tsaye hannayenshi goye a
k'irjinsa,dubanta yake ba tare daya tsaidata ko yace mata komai ba,saidai annurin
fuskarshi ya ragu cikin kaso d'ari zuwa kaso ashirin cikin d'ari.

A firgice ta farka,sa'annan tayi zumbur ta miqe tayi zaman dirshan saman


gadon nata,dukka hannayenta ta sanya ta dafe kanta dasu bayan ta dora gwiwar
hannunta saman cinyoyinta,gashinta mai tsaho da sulbi ya sako ya rufe fuska da
hannayen nata gaba daya,inda zaka ga fuskarta a sannan zazzafan hawaye ne ke layi
saman kuncinta,inda ace tana da iko data hana kanta mafarkinsa,da ta isa data
hanashi bayyana a duniyar mafarkinta,sam ko kusa ko alama bata da buqatarsa a
duniyar mafarkinta kamar yadda bata da buqatarsa a zahiri
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" idan ka kasa kunnenka da kyau zakaji tana
fada cikin muryar kuka.

Ta jima cikin wannan yanayin kafin ta iya lallashin zuciyarta,kanta ta dago


sannan ta sanya hannayenta guda biyu ta tattare gashinta baya ta daureshi,kyakkyawa
kuma sassanyar fuskarta datayi jajur ta kuma tasa saboda kukan data yi ta fito fes
duk da qarancin haske da d'akin keda shi,a hankali ta zuro qafafunta qasa sannan ta
yunqura ta miqe,kai tsaye ta nufi wata qofa dake kallon gadonta ta murda ta shige.

Mintuna biyar kyawawa tayi ta fito daure da alwala,ta bude ma'ajiyar kayanta
ta fidda after dress da hijabi ta sanya,sannan ta nufi wani kebantaccen waje dake
daura da gadonta tahau saman abun sallar dake shimfide a wajen ta kabbara sallah.

Ita kanta batasan adadin lokutan data kashe zaune saman abun sallar ba,don
sam bata marmarin sake komawa barcin da tayi mafarkinsa a ciki,saidai shi bacci ba
wanda yafi qarfinsa,saboda haka sanda yazo yayi awan gaba da ita bata shiryawa
hakan ba,sai jingina da tayi da jikin gadon,carbin hannunta kuma ya silale ya fadi
nan saman dardumar.

******* **** ********

Qarfe takwas na safiya ta kammala shirinta tsaf,tsaye tayi kawai tayi gaban
mudubin tana qarewa kanta kallo,tayi kyau iya kyau,irin kyan nan mai sanyi,saidai
wasu abubuwa da suka soma mata yawo akai take suka d'auke duk wata sauran walwala
da taketa yunqurin d'orawa fuskarta,qarar kira daya shigo wayarta yaso janye
hankalinta,saita zubawa wayar dake gefan mudubin ido tana kallonta ba tare data
tabata ba gudun zuciyarta na qaruwa,bata kuma da niyyar hakan ma gaba daya,har ta
qaraci b'urarinta ta katse,tamkar mai jira kiran ya katse din kuwa tayi gaggawar
surar wayar ta kasheta gaba daya sannan ta jawo locker din madubin ta jefata ta
maidata ta rufe.

Cikin kasala kamar wadda tayi wani babban aiki ta koma da baya ta zauna
gefan gadonta tana ci gaba da kallon fuskarta cikin mudubi,ko kad'an bata qaunar ta
raba wani abu ajikinta da zai sata tayi kyau,don dai kawai bata k'aunar bata ran
anty zubaida ne,amma da bata ga dalili ko alfanun kasancewarta a haka ba.

"Auntyyyyy...." Muryar huda ce ta ratsa kunnenta,firgigit tayi tana dubanta


kafin ta samu qaqaro murmushi wa fuskarta
"Anty ina kwana"
"Lafiya huda ta,kin shirya kenan?" Ta furta tana janyo yarinyar kusa da ita tana
gyara mata daurin jelar rigar makarantar dake jikinta
"Ummi tace ki fito karmu makara"
"Muje na gama ai,fitowa kawai xanyi" ta fada tana miqewa,ta qarasa ma'ajiyar
jakankunanta ta ciro daya daga ciki da zata dace da shigarta,sannan ta dauko wata
daban ta zuge,ta fiddo da tarkacen ciki ta maida wadda zata fitan da ita sannan ta
kama hannun huda suka fice.

A kitchen suka tadda anty zubaida tsaye tana shirya lunch box din
huda,sanye take da rigar bacci da qaramin hijabi,kallo daya anty zubaidan tayi mata
ta karanci yanayin data shiga,don haka bayan sun gama gaisawa ta shigar da
qorafinta
"Yauma kinyi halin ne?" Murmushi kawai tayi wanda ya fito da ciwo tun daga
zuciyarta zuwa labbanta,maimakon ta amsata saita shigo da wata maganar
"Yanzu anty dan Allah ta yaya zanci gaba da kwanciya kina tashi kina girki bayan
kula da uncle aby da kike?"
"In kinason komawa kitchen sai kiyo qoqarin maida mode dinki yadda yake....." Cikin
seriouse ness ta waiwayo tana dubanta
"Cikin shekaru biyu mun soma yin nasara shahida....saidai bansan meke neman
tarwatsa nasarar da muka samu muka yi ta tsahon shekara biyun ba" ta fada cikin
nuna damuwa,shuru shahida tayi tana k'okarin kokawa da damuwar data taso mata,tun
lokacin data san cewa suna rayuwa ne ashe cikin gari d'aya da anwar bata sake samun
peace of mind ba,murmushin yaqe kawai ta jefi anty zubaida dashi,don bata son
dukkan abinda zai sake jagula nutsuwar da take ta yunqurin samarwa kanta,shuru ne
ya ratsa tsakani,ganin bata da niyyar magana anty zubaidan ta saki hannayenta tana
dauko lunch boxs din huda ta miqa mata gami da cewa
"Shikenan,ku wuce ku karya karku makara,amma dai.....kota halin qaqa karki bari
abinda ya riga ya gabata a rayuwarki ya bata future dinki,koda anwar ko babu ki
baiwa kanki qwarin gwiwar xaki rayu,rayuwa mai inganci...."
"Zan rayu babu shi ne anty rayuwa mai inganci,babu batunshi ma cikin babin
rayuwata" ta fada wani radadi na tasowa tun daga cikin zuciyarta har saman
fuskarta,murmushin da ita kadai tasan ma'anarsa anty zubaida ta sako,shahida mutum
ce me confidence,tana da qwarin gwiwa saidai har zuwa yau kaman hakan yaqi tasiri
ga wannan lamarin,duk da koda yaushe tana yunquri da fadi tashin baiwa kanta wannan
qwarin gwiwar,da idanu ta bisu har suka fice daga kitchen din ita da huda sannan ta
saki ajiyar zuciya tana yiwa deejan addu'a a fili da zuciyarta.

Suna gama karyawar abby ya fito,sanye yake da jallabiyya,mutum d'an kimanin


shekara arba'in da takwas,mai cikar kamala da fara'a,cikin girmamawa shahida ta
gaidashi,ya amsa fuskarsa qunshe da fara'a yana fadin
"Teacher uban karatu....baku wuce ba kenan?,hala yau keda dalibar taki tare zakusha
bulalar latti" murmushi ta fidda,tana mamakin abbyn sau da dama,wuta ne shi a wasu
lokutan,amma wani lokacin yafi xuma dad'i
"Yanzun nan zamu wuce abby" ta fadi tana sab'a jakarta
"Gwara kam,don qila hadi(mai adaidaitan dake kaisu makaranta)yana waje yana jiranku
na sanshi da himma" dai dai sanda anty zubaida ta fito daga kitchen din sukayi mata
sallama suka wuce.

A bakin k'aton gate din *NOOR INTERNATIONAL ACADEMY* ya saukesu


"Daganan zan kai adaidaitan wajen gyara....amma zanyi qoqari in sha Allahu na dawo
na d'aukeku"
"Karka damu,yauma muna shirye shiryen wasu abubuwa da za'a gudanar a makarantar,ina
zaton ma zamu d'ara lokacin tashi,zamu bi ta haya mu koma"
"To na gode,amma du da haka idan na gama akan lokaci zanzo" bata sake ce masa komai
ba ta kama hannun huda suka ratsa gate din makarantar zuwa ciki.

Dukansu ita da hudan sashen 'yan nursery da primary suka nufa,saboda a nan
ne deejan ta zabama kanta ta koyar,duk da tarin ilimi da Allah ya bata,wanda tana
da cikakkiyar damar da zatayi lacturing amma bisa wani dalili nata ta zabi koyarwa
a qaramin mataki na 'yan nursery da primary,tun daga bakin section din yara ke
gaidata cikin nuna qauna da soyayya,yayin da ita kuma take amsa musu cikin fara'a
da jansu a jiki,sai da zata shiga staffroom sannan suka rabu da yaran,suka wuce
azuzuwansu ita kuma ta shiga ofishin malamai.

Office ne madaidaici mai girma da tsari,duk da girman office din su uku ne


kacal a ciki,makaranta ce da kallon farko.idan kayi mata zakayi tsammanin private
ce irin mai tsadar nan,saidai sam ba haka abun yake ba,makaranta ce da wani
shahararren d'an kasuwa ya ginata saidai akwai sa'ido da kulawar gwamanti
akanta,duk da cewa shike dauke da duk wani nauyi na makarantar,kama daga school
unifoarm,littafan karatu,abincin da yaran zasuci na break da dai sauran dukkan wasu
lalurori,aqidarshi ce haka,yakan gina makarantar a duk inda yaga hakan ya dace,ya
kuma hada hannu da gwamnatin garin donta tayashi lura da makarantar,bawai lura na
su bada wani abu ba,a'ah,tsarin gudanarwa tsaro da sauran abubuwan da ya
kamata,kusan kowacce qasa dake africa ya gina makarantu d'aya,saidai a inda
makarantun suka fi yawa a nigeria ne yankin arewa,duk dalibin dake karatu cikinta
yana farinciki haka iyayensa farinciki da kasancewar dansu a cikinta,saboda ta
tsaru da tsari mai kyau,hakanan tana da dukkan wani qualities da akeson makaranta
dashi.

Hidaya kawai ta samu cikin office din tana hada littafan dalibai da tayi
marking,da alama tana da ajine qarfe takwas,murmushi suka yiwa junansu
"Kinso makara yau malama shahida"
"Yau da gobe hidaya...." Ta fada tana zaman kan kujerar teburinta.
"Sai Allah..." Hidayan ta qarasa mata kana ta gyara yafen mayafinta
"Mun tashi lpy...."cewar hidaya
"alhmdlh....mun godewa Allah"
"Ma sha Allah....zan wuce aji don Allah idan kausar ta iso kice mata ga kayan nan
ta duba"
"Babu damuwa" cewar shahida,tana kallon hidaya ta bude office din ta fice sannan ta
maida qofar ta rufe musu,saita maida kanta a hankali ta kwantar saman teburin dake
gabanta,idanunta a lumshe,batason tuna komai,batason tunanin komai,tanason ta saita
kanta kafin lokacin shigarta aji yayi,don nan da minti goma sha biyar periode dinta
zai shiga.

***********************

"Dukkanin takardun na cikin wannan file din,sauran takardun da za'ayi amfani


dasu a d'akin taron ma gab suke da kammala,na shiga dakin buga takardun na musu
magana sunce nan da mintina goma da izinin Allah....engine ne yaso basu matsala"
mutumin d'an kimanin shekara arba'in dake zaune saman d'aya daga cikin qawatattun
kujerun dake shirye a qayataccen office din ya fada,yana bayanin ne ga dogo kuma
tsayayyen matashin dake tsaye tsakiyar office din yana kai kawo a hankali,hannunshi
riqe da dan madaidaicin glass cup,yayin da d'aya hannun nasa yake riqe da wata
zungureriyar takarda yana dubawa,sanye yake da suit masu azabar kyau da d'aukar
idanu,wankan tarwada ne shi,dogo wanda ke tafe da tsaho da kuma 'yar qiba
kadan,wadda kai tsaye ba zaka kirata da qiba ta zahiri ba saidai ace murjewar
jiki,doguwar fuska gareshi wadda take cikakka,lumsassun idanu mai kama da wanda
kejin bacci,saidai da girmansu idan ya budesu sosai aduk sanda yaso hakan,bashi da
cikar gashin gira can,saidai gashin idanunshi a cike suke,siraran labba masu
taushi,da qawataccen qasumba da aka gyarata aka rage mata yawa da fadi,ta zagaya ta
hade da habarsa da kuma qasan hancinsa,kanshi saisaye ne wanda ya qawata fuskarshi
saboda gyaran fuska da aka yi masa,kana kallonshi kasan tsafta hutu da iya dressing
sun kama gida a wajensa,kana kallonshi kasan ba ma'abocin fara'a bane,sosai ya bada
hankalinsa kacokam kan takardar hannunsa da gani kasan abune mai muhimmanci yake
dubawa,yayin da ta wani b'angaren daban ya bada hankalinsa ga wanda ke masa bayanin
"Ina imran?"
"Yana sashen aje tsaffi da sabbin qarafa" kai ya gyada yana ci gaba da takawa sannu
a hankali,har yanzu hankalinsa na kan takardar hannunsa
"Amma ba tuni na bada umarnin a cire wancan a sanya sabon da mukayo order ba?"
"Sorry sir.....engineer din ake dako,yaudai yayi alqawarin zuwa ya hada" ya fada
cikin nuna tsantsar ladabi,bai sake cewa komai ba har na tsahon wasu mintina,sannan
ya isa gaban teburinshi ya aje kofin hannunsa,ya taka zuwa gaban matashin dake
zaune ya bude files din dake gabansa ya sanya takardar ciki ya rufe,sai a sannan ya
dubeshi
"Karku wuce qarfe biyu ba'a gama kammala komai ba,bana son delay...."kafin ya gama
fada qofar office din nashi dake aiki da lantarki ta bude da kanta,wanda hakan ke
nuna muhimmin mutum ne zai shigo ciki,don ba kasafai take budewar da kanta ba sai
bayan sakatariyarshi ta sanar masa ya bada umarni sannan ta bude din.

Dukkansu maida idonsu sukayi kan qofar,tun kafin ta qarasa shigowa ya fahimci
wacece,hakan ya sanya ya maida idanunsa kan yaqub,don bashi da tabbacin yanayin da
zata shigo dashi,don haka ya sallameshi
"shikenan....zaka iya tafiya" a bakin qofar sukayi clashing da ita tana
shigowa,cike da girmamawa ya rusuna yana miqa mata gaisuwa,kaman yadda aka saba
haka ta amsa a daqile,cike da izza,shan qamshi taqama da isa,yaqub ya wuce ita kuma
taci gaba da takowa cikin office din.

Fuskarta qunshe da murmushi,hakanan idanunta na kan fuskarshi,taku take d'ai


d'ai harta kusa cimmasa,yayin da shi kuma yake kallonta yana nazarin shigarta,babu
laifi shigar tata tayau,doguwar riga ce mai wrapper,saidai kuma gajeran hannu
ce,tayi rolling mayafi qarami a kanta,high hill ta saka a qafafunta,hannunta ba
komai daga waya sai key din motarta
"It seems kamar bakayi farinciki da ganina ba M.A" ta fada a shagwabe tana
kallonshi
"Uhummm....who told you?"
"Ba kowa....kawai yau nayi missing ganin cute face dinka,ka fita tun da sassafe ban
samu ganinka ba,me yasa baka yi break fast ba yau a gida?" Takawa yayi zuwa d'aya
daga cikin kujerun wajen yayiwa kanshi mazauni,itama yayi mata nuni da yatsa yana
nufin ta zauna,sai data zauna sannan yace
"Me yasa zaki fito a irin wannan lokacin?" Farrr tayi da ido,tana jin wani dad'i na
ratsata,a duk sanda ya nuna kulawa a gareta takanji babu ya ita a fadin duniya,sai
data saki murmushi sannan tace
"Kai kadai na fito don na gani,kasan bazan iya wuni ban ganka ba" shuru yayi yana
dubanta,can qasan ranshi yana jinjina wanne irin so nafisa ke masa?,kalamanta sunyi
shigen kama da na wata,wadda ya soma qoqari da kokawar badda ta daga ranshi a
yanzun da takeson taso mishi,don ko kusa bashi da sha'awar hakan,itama kallonshi
take,tasan cewa wannan plan din nata ya d'anu,tanason dukkan wasu kalamai nata da
yanayin kulawa yayi kama dana waccar da tasan ta taba wanzuwa cikin rayuwarshi,duk
da tana baqinciki da cewa kwaikwayonta shine zai sama mata wani gurbi data dauki
tsahon lokaci tana neman samu a zuciyarsa,duk da irin baqin fenti da qin jini da
yayyabe tarihinta a zuciyarsa,amma duk da haka kishinta take fiye da komai a
rayuwarta
"Naso na iso tun dazun sai aka samu akasi" ta katse kallon kallon da sukema
juna,dan muskutawa yayi kadan,cikin muryarshi dake nuna halayyarshi yace
"Akasi?,name fa?" Sai data d'an jaa fasali sannan ta sake cewa
"Wallahi wasu 'yammata ne suka so yiwa motata b'arna..."
"Me ya gamoki dasu?" Ya tambayeta kai tsaye yana ci gaba da dubanta,kafad'a ta daga
sannan tace
"No,karka damu,na musu uzuri saboda a make suke,kana ganinsu kasan sunsan sirrin
shan syrup,har zan hadasu da police sai kuma na wuce don bai kamata na b'ata
lokacina akansu ba" sexy eyes dinshi ya lumshe gaba dayansu,yana jin wani abu mai
ciwo na sauka saman zuciyarshi kamar ana d'iga masa wuta,wani boyayyen murmushi ta
saki sannan cikin shagwaba tace
"Karka damu nawan....ba abinda ya faru dani,am safe..." Bude idanun nasa yayi kaman
zai kalleta saiya kalli wani sashe na daban,yana sauke ajiyar zuciya a boye,a duk
sanda yaji ko yaga labari irin wannan babu wadda yake tunawa sai ita,hakanan haushi
tsana da qyamarta yakan sake ninkuwa a ransa.

"Yaya" ta kirashi tana son kauda damuwar data ziyarceshi,tunda haqarta ta


cimma ruwa
"Yaune fa zamuje yaya?,don Allah karki sake cewa kana da wani uzurin"
"Saura minti goma sha biyar mu shiga meeting....saidai bayan mun kammala kuma" ya
fada yana miqewa a hankali kai tsaye ya wuce bandakin dake cikin office din nashi
ta bishi da idanu tana tantamarsa.

A hankali ya tura qofar bandakin sannan ya maidata ya kulle,gaban dan fanfon


dake maqale a bango mai hade da madubi dake manne a samanshi ya isa,yasa dukka
hannayenshi ya dafe sink din tangaran dake qasan famfon,qirjinsa na zafi haka
zuciyarshi,ya jima a haka kanshi a duqe yana kokawar maida yanayinsa yadda yake
sannan ya dago yana duban kanshi a madubin kamar baisan halittar kansa ba
saiyau,maganganu yake da zuciyarshi,magana yake gayawa kansa wanda shi kadai yasan
meke kai kawo a ranshi harna tsahon wasu lokutta sannan ya zare 'yar samam suit
dinshi ya daura alwala bayan ya tattare dogon hannun ta ciki,sai daya saka dan
qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa sannan ya maida rigar ya fito.

Da sauri ta jiyo a firgice suka hada idanu dashi,tana tsaye gaban wani
dan qaramin akwatinsa da ake budeshi da lambobin sirri,wanda ta budeshi ta kuma
soma fiddo wasu kayayyaki dake ciki,dauke idonsa yayi daga kallonta ya maida kan
d'an akwatin dake zaune dirshan daga can wani saqo na office din,baya taja cikin
rawar murya muryarta can qasa tace
"Am sorry" baice mata uffan ya taka a hankali zuwa wajen,inda ta janye jikinta ta
rabe a bango,ya durqusa ya dinga daukan kayan d'aya bayan d'aya yana maidasu
muhallinsu,duk abu guda idan ya dauka yana jin kaman yana qarawa zuciyarsa nauyi
ne.

Har ya saka wani abu ya sake cirosu ya kalla,suna nan kamar yadda ta bashi
su,hatta da ledarsu itace dai wadda ta qullesu a ciki,d last thing data bashi a
tarayyarsu,da hanzari ya maidasu ya rufe sannan ya sauya lambobin sirrin ya miqe
zuwa gaban teburinsa ya amsa wayar daketa burari,sai daya kammala a nutse sannan ya
aje,ya kalli nafisa data tsarki kanta tare da ala wadai da shegen qwaqwqwafinta da
yakeson ya bata mata dukka plan dinta
"Ki wuce gida,saina qaraso" daga haka ya soma diban wasu files,dai dai sanda P.A
dinshi ya shigo suka soma yunqurin barin ofishin,hakan ya sanya dole tabi bayansu
jiki a sanyaye,a wajen elevator suka rabu,su suka hau wadda zata kaisu third floor
ita kuma tayi qasa don barin companyn.

*GA MAI BUQATAR WANNAN LITTAFI ZAI BIYA NAIRA KACAL 200 YA SAMESHI,WANDA KE
BUQATAR DUKKA ZAFAFA BIYAR DUN KUWA ZAI SAMESU NE AKAN FARASHIN NAIRA 500*

👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA
SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_🪐 *ALK'AWARIN ALLAH* 🪐

_HUGUMA_

0️⃣ 1️⃣
0️⃣1️⃣

"Allah ya taimakeki" lafazin da ya shiga kunnenta kenan,lafazin da a bakin


mutum daya take jinsa,furucin da ko mutuwa tayi ta dawo bata jin zata kasa tantance
daga bakin wanda yake fitowa dare da rana,a hankali ta waiwaya fuskarta qunshe da
murmushi,yana tsaye daga bayanta kamar koda yaushe,wannan annurin data saba gani
kan fuskarshi kowanne lokaci na nan shimfide saman fuskarsa,kwarjini cikar zati da
haiba cakude saman kyakkyawar fuskarsa,batasan me ya shigeta ba,sai taji bacin rai
ya sauko mata a take,b'acin ran daya sanyata ta dinga ja da baya,ja da bayan daya
zama silar data soma ganinshi dishi dishi,yana tsaye hannayenshi goye a
k'irjinsa,dubanta yake ba tare daya tsaidata ko yace mata komai ba,saidai annurin
fuskarshi ya ragu cikin kaso d'ari zuwa kaso ashirin cikin d'ari.

A firgice ta farka,sa'annan tayi zumbur ta miqe tayi zaman dirshan saman


gadon nata,dukka hannayenta ta sanya ta dafe kanta dasu bayan ta dora gwiwar
hannunta saman cinyoyinta,gashinta mai tsaho da sulbi ya sako ya rufe fuska da
hannayen nata gaba daya,inda zaka ga fuskarta a sannan zazzafan hawaye ne ke layi
saman kuncinta,inda ace tana da iko data hana kanta mafarkinsa,da ta isa data
hanashi bayyana a duniyar mafarkinta,sam ko kusa ko alama bata da buqatarsa a
duniyar mafarkinta kamar yadda bata da buqatarsa a zahiri
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" idan ka kasa kunnenka da kyau zakaji tana
fada cikin muryar kuka.

Ta jima cikin wannan yanayin kafin ta iya lallashin zuciyarta,kanta ta dago


sannan ta sanya hannayenta guda biyu ta tattare gashinta baya ta daureshi,kyakkyawa
kuma sassanyar fuskarta datayi jajur ta kuma tasa saboda kukan data yi ta fito fes
duk da qarancin haske da d'akin keda shi,a hankali ta zuro qafafunta qasa sannan ta
yunqura ta miqe,kai tsaye ta nufi wata qofa dake kallon gadonta ta murda ta shige.

Mintuna biyar kyawawa tayi ta fito daure da alwala,ta bude ma'ajiyar kayanta
ta fidda after dress da hijabi ta sanya,sannan ta nufi wani kebantaccen waje dake
daura da gadonta tahau saman abun sallar dake shimfide a wajen ta kabbara sallah.

Ita kanta batasan adadin lokutan data kashe zaune saman abun sallar ba,don
sam bata marmarin sake komawa barcin da tayi mafarkinsa a ciki,saidai shi bacci ba
wanda yafi qarfinsa,saboda haka sanda yazo yayi awan gaba da ita bata shiryawa
hakan ba,sai jingina da tayi da jikin gadon,carbin hannunta kuma ya silale ya fadi
nan saman dardumar.

******* **** ********

Qarfe takwas na safiya ta kammala shirinta tsaf,tsaye tayi kawai tayi gaban
mudubin tana qarewa kanta kallo,tayi kyau iya kyau,irin kyan nan mai sanyi,saidai
wasu abubuwa da suka soma mata yawo akai take suka d'auke duk wata sauran walwala
da taketa yunqurin d'orawa fuskarta,qarar kira daya shigo wayarta yaso janye
hankalinta,saita zubawa wayar dake gefan mudubin ido tana kallonta ba tare data
tabata ba gudun zuciyarta na qaruwa,bata kuma da niyyar hakan ma gaba daya,har ta
qaraci b'urarinta ta katse,tamkar mai jira kiran ya katse din kuwa tayi gaggawar
surar wayar ta kasheta gaba daya sannan ta jawo locker din madubin ta jefata ta
maidata ta rufe.

Cikin kasala kamar wadda tayi wani babban aiki ta koma da baya ta zauna
gefan gadonta tana ci gaba da kallon fuskarta cikin mudubi,ko kad'an bata qaunar ta
raba wani abu ajikinta da zai sata tayi kyau,don dai kawai bata k'aunar bata ran
anty zubaida ne,amma da bata ga dalili ko alfanun kasancewarta a haka ba.

"Auntyyyyy...." Muryar huda ce ta ratsa kunnenta,firgigit tayi tana dubanta


kafin ta samu qaqaro murmushi wa fuskarta
"Anty ina kwana"
"Lafiya huda ta,kin shirya kenan?" Ta furta tana janyo yarinyar kusa da ita tana
gyara mata daurin jelar rigar makarantar dake jikinta
"Ummi tace ki fito karmu makara"
"Muje na gama ai,fitowa kawai xanyi" ta fada tana miqewa,ta qarasa ma'ajiyar
jakankunanta ta ciro daya daga ciki da zata dace da shigarta,sannan ta dauko wata
daban ta zuge,ta fiddo da tarkacen ciki ta maida wadda zata fitan da ita sannan ta
kama hannun huda suka fice.

A kitchen suka tadda anty zubaida tsaye tana shirya lunch box din
huda,sanye take da rigar bacci da qaramin hijabi,kallo daya anty zubaidan tayi mata
ta karanci yanayin data shiga,don haka bayan sun gama gaisawa ta shigar da
qorafinta
"Yauma kinyi halin ne?" Murmushi kawai tayi wanda ya fito da ciwo tun daga
zuciyarta zuwa labbanta,maimakon ta amsata saita shigo da wata maganar
"Yanzu anty dan Allah ta yaya zanci gaba da kwanciya kina tashi kina girki bayan
kula da uncle aby da kike?"
"In kinason komawa kitchen sai kiyo qoqarin maida mode dinki yadda yake....." Cikin
seriouse ness ta waiwayo tana dubanta
"Cikin shekaru biyu mun soma yin nasara shahida....saidai bansan meke neman
tarwatsa nasarar da muka samu muka yi ta tsahon shekara biyun ba" ta fada cikin
nuna damuwa,shuru shahida tayi tana k'okarin kokawa da damuwar data taso mata,tun
lokacin data san cewa suna rayuwa ne ashe cikin gari d'aya da anwar bata sake samun
peace of mind ba,murmushin yaqe kawai ta jefi anty zubaida dashi,don bata son
dukkan abinda zai sake jagula nutsuwar da take ta yunqurin samarwa kanta,shuru ne
ya ratsa tsakani,ganin bata da niyyar magana anty zubaidan ta saki hannayenta tana
dauko lunch boxs din huda ta miqa mata gami da cewa
"Shikenan,ku wuce ku karya karku makara,amma dai.....kota halin qaqa karki bari
abinda ya riga ya gabata a rayuwarki ya bata future dinki,koda anwar ko babu ki
baiwa kanki qwarin gwiwar xaki rayu,rayuwa mai inganci...."
"Zan rayu babu shi ne anty rayuwa mai inganci,babu batunshi ma cikin babin
rayuwata" ta fada wani radadi na tasowa tun daga cikin zuciyarta har saman
fuskarta,murmushin da ita kadai tasan ma'anarsa anty zubaida ta sako,shahida mutum
ce me confidence,tana da qwarin gwiwa saidai har zuwa yau kaman hakan yaqi tasiri
ga wannan lamarin,duk da koda yaushe tana yunquri da fadi tashin baiwa kanta wannan
qwarin gwiwar,da idanu ta bisu har suka fice daga kitchen din ita da huda sannan ta
saki ajiyar zuciya tana yiwa deejan addu'a a fili da zuciyarta.

Suna gama karyawar abby ya fito,sanye yake da jallabiyya,mutum d'an kimanin


shekara arba'in da takwas,mai cikar kamala da fara'a,cikin girmamawa shahida ta
gaidashi,ya amsa fuskarsa qunshe da fara'a yana fadin
"Teacher uban karatu....baku wuce ba kenan?,hala yau keda dalibar taki tare zakusha
bulalar latti" murmushi ta fidda,tana mamakin abbyn sau da dama,wuta ne shi a wasu
lokutan,amma wani lokacin yafi xuma dad'i
"Yanzun nan zamu wuce abby" ta fadi tana sab'a jakarta
"Gwara kam,don qila hadi(mai adaidaitan dake kaisu makaranta)yana waje yana jiranku
na sanshi da himma" dai dai sanda anty zubaida ta fito daga kitchen din sukayi mata
sallama suka wuce.

A bakin k'aton gate din *NOOR INTERNATIONAL ACADEMY* ya saukesu


"Daganan zan kai adaidaitan wajen gyara....amma zanyi qoqari in sha Allahu na dawo
na d'aukeku"
"Karka damu,yauma muna shirye shiryen wasu abubuwa da za'a gudanar a makarantar,ina
zaton ma zamu d'ara lokacin tashi,zamu bi ta haya mu koma"
"To na gode,amma du da haka idan na gama akan lokaci zanzo" bata sake ce masa komai
ba ta kama hannun huda suka ratsa gate din makarantar zuwa ciki.

Dukansu ita da hudan sashen 'yan nursery da primary suka nufa,saboda a nan
ne deejan ta zabama kanta ta koyar,duk da tarin ilimi da Allah ya bata,wanda tana
da cikakkiyar damar da zatayi lacturing amma bisa wani dalili nata ta zabi koyarwa
a qaramin mataki na 'yan nursery da primary,tun daga bakin section din yara ke
gaidata cikin nuna qauna da soyayya,yayin da ita kuma take amsa musu cikin fara'a
da jansu a jiki,sai da zata shiga staffroom sannan suka rabu da yaran,suka wuce
azuzuwansu ita kuma ta shiga ofishin malamai.

Office ne madaidaici mai girma da tsari,duk da girman office din su uku ne


kacal a ciki,makaranta ce da kallon farko.idan kayi mata zakayi tsammanin private
ce irin mai tsadar nan,saidai sam ba haka abun yake ba,makaranta ce da wani
shahararren d'an kasuwa ya ginata saidai akwai sa'ido da kulawar gwamanti
akanta,duk da cewa shike dauke da duk wani nauyi na makarantar,kama daga school
unifoarm,littafan karatu,abincin da yaran zasuci na break da dai sauran dukkan wasu
lalurori,aqidarshi ce haka,yakan gina makarantar a duk inda yaga hakan ya dace,ya
kuma hada hannu da gwamnatin garin donta tayashi lura da makarantar,bawai lura na
su bada wani abu ba,a'ah,tsarin gudanarwa tsaro da sauran abubuwan da ya
kamata,kusan kowacce qasa dake africa ya gina makarantu d'aya,saidai a inda
makarantun suka fi yawa a nigeria ne yankin arewa,duk dalibin dake karatu cikinta
yana farinciki haka iyayensa farinciki da kasancewar dansu a cikinta,saboda ta
tsaru da tsari mai kyau,hakanan tana da dukkan wani qualities da akeson makaranta
dashi.

Hidaya kawai ta samu cikin office din tana hada littafan dalibai da tayi
marking,da alama tana da ajine qarfe takwas,murmushi suka yiwa junansu
"Kinso makara yau malama shahida"
"Yau da gobe hidaya...." Ta fada tana zaman kan kujerar teburinta.
"Sai Allah..." Hidayan ta qarasa mata kana ta gyara yafen mayafinta
"Mun tashi lpy...."cewar hidaya
"alhmdlh....mun godewa Allah"
"Ma sha Allah....zan wuce aji don Allah idan kausar ta iso kice mata ga kayan nan
ta duba"
"Babu damuwa" cewar shahida,tana kallon hidaya ta bude office din ta fice sannan ta
maida qofar ta rufe musu,saita maida kanta a hankali ta kwantar saman teburin dake
gabanta,idanunta a lumshe,batason tuna komai,batason tunanin komai,tanason ta saita
kanta kafin lokacin shigarta aji yayi,don nan da minti goma sha biyar periode dinta
zai shiga.

***********************

"Dukkanin takardun na cikin wannan file din,sauran takardun da za'ayi amfani


dasu a d'akin taron ma gab suke da kammala,na shiga dakin buga takardun na musu
magana sunce nan da mintina goma da izinin Allah....engine ne yaso basu matsala"
mutumin d'an kimanin shekara arba'in dake zaune saman d'aya daga cikin qawatattun
kujerun dake shirye a qayataccen office din ya fada,yana bayanin ne ga dogo kuma
tsayayyen matashin dake tsaye tsakiyar office din yana kai kawo a hankali,hannunshi
riqe da dan madaidaicin glass cup,yayin da d'aya hannun nasa yake riqe da wata
zungureriyar takarda yana dubawa,sanye yake da suit masu azabar kyau da d'aukar
idanu,wankan tarwada ne shi,dogo wanda ke tafe da tsaho da kuma 'yar qiba
kadan,wadda kai tsaye ba zaka kirata da qiba ta zahiri ba saidai ace murjewar
jiki,doguwar fuska gareshi wadda take cikakka,lumsassun idanu mai kama da wanda
kejin bacci,saidai da girmansu idan ya budesu sosai aduk sanda yaso hakan,bashi da
cikar gashin gira can,saidai gashin idanunshi a cike suke,siraran labba masu
taushi,da qawataccen qasumba da aka gyarata aka rage mata yawa da fadi,ta zagaya ta
hade da habarsa da kuma qasan hancinsa,kanshi saisaye ne wanda ya qawata fuskarshi
saboda gyaran fuska da aka yi masa,kana kallonshi kasan tsafta hutu da iya dressing
sun kama gida a wajensa,kana kallonshi kasan ba ma'abocin fara'a bane,sosai ya bada
hankalinsa kacokam kan takardar hannunsa da gani kasan abune mai muhimmanci yake
dubawa,yayin da ta wani b'angaren daban ya bada hankalinsa ga wanda ke masa bayanin
"Ina imran?"
"Yana sashen aje tsaffi da sabbin qarafa" kai ya gyada yana ci gaba da takawa sannu
a hankali,har yanzu hankalinsa na kan takardar hannunsa
"Amma ba tuni na bada umarnin a cire wancan a sanya sabon da mukayo order ba?"
"Sorry sir.....engineer din ake dako,yaudai yayi alqawarin zuwa ya hada" ya fada
cikin nuna tsantsar ladabi,bai sake cewa komai ba har na tsahon wasu mintina,sannan
ya isa gaban teburinshi ya aje kofin hannunsa,ya taka zuwa gaban matashin dake
zaune ya bude files din dake gabansa ya sanya takardar ciki ya rufe,sai a sannan ya
dubeshi
"Karku wuce qarfe biyu ba'a gama kammala komai ba,bana son delay...."kafin ya gama
fada qofar office din nashi dake aiki da lantarki ta bude da kanta,wanda hakan ke
nuna muhimmin mutum ne zai shigo ciki,don ba kasafai take budewar da kanta ba sai
bayan sakatariyarshi ta sanar masa ya bada umarni sannan ta bude din.

Dukkansu maida idonsu sukayi kan qofar,tun kafin ta qarasa shigowa ya fahimci
wacece,hakan ya sanya ya maida idanunsa kan yaqub,don bashi da tabbacin yanayin da
zata shigo dashi,don haka ya sallameshi
"shikenan....zaka iya tafiya" a bakin qofar sukayi clashing da ita tana
shigowa,cike da girmamawa ya rusuna yana miqa mata gaisuwa,kaman yadda aka saba
haka ta amsa a daqile,cike da izza,shan qamshi taqama da isa,yaqub ya wuce ita kuma
taci gaba da takowa cikin office din.

Fuskarta qunshe da murmushi,hakanan idanunta na kan fuskarshi,taku take d'ai


d'ai harta kusa cimmasa,yayin da shi kuma yake kallonta yana nazarin shigarta,babu
laifi shigar tata tayau,doguwar riga ce mai wrapper,saidai kuma gajeran hannu
ce,tayi rolling mayafi qarami a kanta,high hill ta saka a qafafunta,hannunta ba
komai daga waya sai key din motarta
"It seems kamar bakayi farinciki da ganina ba M.A" ta fada a shagwabe tana
kallonshi
"Uhummm....who told you?"
"Ba kowa....kawai yau nayi missing ganin cute face dinka,ka fita tun da sassafe ban
samu ganinka ba,me yasa baka yi break fast ba yau a gida?" Takawa yayi zuwa d'aya
daga cikin kujerun wajen yayiwa kanshi mazauni,itama yayi mata nuni da yatsa yana
nufin ta zauna,sai data zauna sannan yace
"Me yasa zaki fito a irin wannan lokacin?" Farrr tayi da ido,tana jin wani dad'i na
ratsata,a duk sanda ya nuna kulawa a gareta takanji babu ya ita a fadin duniya,sai
data saki murmushi sannan tace
"Kai kadai na fito don na gani,kasan bazan iya wuni ban ganka ba" shuru yayi yana
dubanta,can qasan ranshi yana jinjina wanne irin so nafisa ke masa?,kalamanta sunyi
shigen kama da na wata,wadda ya soma qoqari da kokawar badda ta daga ranshi a
yanzun da takeson taso mishi,don ko kusa bashi da sha'awar hakan,itama kallonshi
take,tasan cewa wannan plan din nata ya d'anu,tanason dukkan wasu kalamai nata da
yanayin kulawa yayi kama dana waccar da tasan ta taba wanzuwa cikin rayuwarshi,duk
da tana baqinciki da cewa kwaikwayonta shine zai sama mata wani gurbi data dauki
tsahon lokaci tana neman samu a zuciyarsa,duk da irin baqin fenti da qin jini da
yayyabe tarihinta a zuciyarsa,amma duk da haka kishinta take fiye da komai a
rayuwarta
"Naso na iso tun dazun sai aka samu akasi" ta katse kallon kallon da sukema
juna,dan muskutawa yayi kadan,cikin muryarshi dake nuna halayyarshi yace
"Akasi?,name fa?" Sai data d'an jaa fasali sannan ta sake cewa
"Wallahi wasu 'yammata ne suka so yiwa motata b'arna..."
"Me ya gamoki dasu?" Ya tambayeta kai tsaye yana ci gaba da dubanta,kafad'a ta daga
sannan tace
"No,karka damu,na musu uzuri saboda a make suke,kana ganinsu kasan sunsan sirrin
shan syrup,har zan hadasu da police sai kuma na wuce don bai kamata na b'ata
lokacina akansu ba" sexy eyes dinshi ya lumshe gaba dayansu,yana jin wani abu mai
ciwo na sauka saman zuciyarshi kamar ana d'iga masa wuta,wani boyayyen murmushi ta
saki sannan cikin shagwaba tace
"Karka damu nawan....ba abinda ya faru dani,am safe..." Bude idanun nasa yayi kaman
zai kalleta saiya kalli wani sashe na daban,yana sauke ajiyar zuciya a boye,a duk
sanda yaji ko yaga labari irin wannan babu wadda yake tunawa sai ita,hakanan haushi
tsana da qyamarta yakan sake ninkuwa a ransa.

"Yaya" ta kirashi tana son kauda damuwar data ziyarceshi,tunda haqarta ta


cimma ruwa
"Yaune fa zamuje yaya?,don Allah karki sake cewa kana da wani uzurin"
"Saura minti goma sha biyar mu shiga meeting....saidai bayan mun kammala kuma" ya
fada yana miqewa a hankali kai tsaye ya wuce bandakin dake cikin office din nashi
ta bishi da idanu tana tantamarsa.

A hankali ya tura qofar bandakin sannan ya maidata ya kulle,gaban dan fanfon


dake maqale a bango mai hade da madubi dake manne a samanshi ya isa,yasa dukka
hannayenshi ya dafe sink din tangaran dake qasan famfon,qirjinsa na zafi haka
zuciyarshi,ya jima a haka kanshi a duqe yana kokawar maida yanayinsa yadda yake
sannan ya dago yana duban kanshi a madubin kamar baisan halittar kansa ba
saiyau,maganganu yake da zuciyarshi,magana yake gayawa kansa wanda shi kadai yasan
meke kai kawo a ranshi harna tsahon wasu lokutta sannan ya zare 'yar samam suit
dinshi ya daura alwala bayan ya tattare dogon hannun ta ciki,sai daya saka dan
qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa sannan ya maida rigar ya fito.

Da sauri ta jiyo a firgice suka hada idanu dashi,tana tsaye gaban wani
dan qaramin akwatinsa da ake budeshi da lambobin sirri,wanda ta budeshi ta kuma
soma fiddo wasu kayayyaki dake ciki,dauke idonsa yayi daga kallonta ya maida kan
d'an akwatin dake zaune dirshan daga can wani saqo na office din,baya taja cikin
rawar murya muryarta can qasa tace
"Am sorry" baice mata uffan ya taka a hankali zuwa wajen,inda ta janye jikinta ta
rabe a bango,ya durqusa ya dinga daukan kayan d'aya bayan d'aya yana maidasu
muhallinsu,duk abu guda idan ya dauka yana jin kaman yana qarawa zuciyarsa nauyi
ne.

Har ya saka wani abu ya sake cirosu ya kalla,suna nan kamar yadda ta bashi
su,hatta da ledarsu itace dai wadda ta qullesu a ciki,d last thing data bashi a
tarayyarsu,da hanzari ya maidasu ya rufe sannan ya sauya lambobin sirrin ya miqe
zuwa gaban teburinsa ya amsa wayar daketa burari,sai daya kammala a nutse sannan ya
aje,ya kalli nafisa data tsarki kanta tare da ala wadai da shegen qwaqwqwafinta da
yakeson ya bata mata dukka plan dinta
"Ki wuce gida,saina qaraso" daga haka ya soma diban wasu files,dai dai sanda P.A
dinshi ya shigo suka soma yunqurin barin ofishin,hakan ya sanya dole tabi bayansu
jiki a sanyaye,a wajen elevator suka rabu,su suka hau wadda zata kaisu third floor
ita kuma tayi qasa don barin companyn.

*GA MAI BUQATAR WANNAN LITTAFI ZAI BIYA NAIRA KACAL 200 YA SAMESHI,WANDA KE
BUQATAR DUKKA ZAFAFA BIYAR DUN KUWA ZAI SAMESU NE AKAN FARASHIN NAIRA 500*

👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇


*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA
SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_*ZAFAFA BIYAR NA


KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI
TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi
SHARING*🙏🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

0️⃣ 2️⃣
***
0️⃣2️⃣

Qarfe biyu na rana suka shigo gidan ita da huda,a falo suka tadda anty zubaida
gabanta plate ne dauke da alala guda uku tana ci
"Wash" kadija ta fada tana zama saman kujerar dake falon,sannan ta zame dankwalin
kanta don tasha iska,dogon gashinta da bashi da cika saboda santsi da tsahonsa ya
bayyana
"Ina kuka jima haka yau?" Muskutawa shahida tayi,muryarta dauke da alamun gajiya
tace
"Kin manta na gaya miki muna shirye shiryen ziyarar da mai makarantarmu zai kawo
mana next week?"
"Af,na manta haka ne fa....amma da alama ba qaramin shiri kukewa zuwan nasa ba,ga
dalibarku nan ta kasa zaune ta kasa tsaye" inji anty zubaida tana duban huda dake
zare safarta tana dariya,yatsina fuska shahida tayi cike da qosawa
"Nima abun duk ya soma ginsata anty,duk sun d'aga hankalinsu duka malaman
makarantar.....amma hakan qila baya rasa nasaba da halayyarsa,don a yadda kausar ke
gayamin bashi da sauqi sam,kuskure kadan zai gani da bai masa ya dauki mataki,don
bai qaunar abinda zai taba students din,last year yazo lokacin ban soma koyarwa a
makarantar ba"
"To Allah ya taimaka yayi jagora...kece ma,da kin amshi aikin kamfaninsu abban huda
da duk wannan jigilar kin huta da ita,har mota zasu baki kyauta saboda matakin da
aka baki aiki akai yakai a bakin" murmushin gefan baki kawai tayi,sannan tayunqura
ta miqe tana tattara mayafinta zuwa dankwalinta da jakar makarantarta
"Au....kinga naso na manta...nuraddin ya bada saqo,yayita kiran wayarki wai bai
samu ba" cak shahida ta dakata da abinda take ba kuma tare data juyo ba,fitar
furucin daga bakin anty zubaida zuwa kunnuwanta jinsu take kamar harbin bindiga
"Waima....ina kika aje wayarki?,nayita kira ni dinma ban sameki ba......anya
shahida anya?,sai yaushe zaki saki ki koma dai dai?,saboda nuradden ne kika kashe
wayarki?,nuradden kuwa deeja ya cancanci haka kuwa?" Batasan idanunta sun soma
fidda hawayen da suka cikasu ba sai data ji saukarsu kan hannunta dake cukuikuye da
mayafinta,kasa jure tsaiwa tayi saitayi gaba cikin sassarfa.

Da kallo anty zubaida tabita harta bacewa ganinta sannan ta girgiza kai tana
furta
"Allah ya kyauta" bata sake tankawa ba saita maida hankalinta kan alalanta da take
ci.

Ganin har huda ta gama komai shahidan bata sake ko leqowa ba,sai anty zubaida
ta bawa hudan saqon tace ta shiga ta kai mata,sannan ta gaya mata ta fito taci
abinci.

Qarfe hudu na yammaci ta fito a shirye tsaf cikin doguwar riga abaya wadda ta
wadatu da adon duwatsu,tayi rolling da wadataccen mayafinta,tayi kyau duk da babu
ko digon hoda fuskarta bare akai ga kwalliya,hakanan idanunta tarwai suke babu
kwalli ko d'aya a cikinsu.

Ci gaba da kallonta anty zubaida tayi harta kammala tsakurar alalen sannan tace
"Zanje na dubo umma"
"Saikin dawo,Allah ya tsare,bari na baki saqo" ta fada tana miqewa zuwa cikin
dakinta,mintina qalilan ta fito da leda ta miqa mata
"Gashi kikai mata" hannu biyu ta saka ta amsa sannan tayi mata sallama ta fice daga
gidan,don 'yar rakiyar tata huda yau akwai islamiyya ta riga data wuce kuma,tilas
ta wuce ita d'aya.

A hankali take takawa zuwa bakin titi,jikinta a mace yake kamar yadda take jin
zuciyarta sam babu wani qwarin gwiwa ko karsashi tattare da ita,tun daga can nesa
ta hango shigowar motar,kallo d'aya tayi mata ta gane motar kota wace,hakan yasa ta
sake tsananta d'aure girarta gami da kau da fuskarta tamkar bata ga motar ba.

Ilai kuwa yana zuwa dab da ita ya rage saurin motar,saidai yadda ta dauke kai
tare da qara saurin tafiyarshi ya hanashi damar ce mata komai,tana jinsa ya qara
yin gaba,hakan ya nuna mata reverse zaije yayi ya dawo,don haka ta qara sauri,cikin
sa'a ta cimma titi kafin ya juyo ta samu abun hawa ta shige ko waiwayenshi ma
batayi ba bare ta san ya iso ko bai iso ba.

Tsam tayi da ranta cikin abun hawan lokacin da yake sake kusantata da
ainihin unguwarsu,wadda anan komai na rayuwarta ya samo asali,a nan duk wani babu
na quncinta ya bude,anan komai ya wanzu ya kuma wakana cikin shafukan rayuwarta.

Tafiyar mintina talatin suka iso,ya gangara da ita cikin layinsu kamar yadda
ta saba aduk lokacin da tazo unguwar tasu bata sauka a titi saita dangana da qofar
gidansu,kanta ta dauke gefe guda lokacin da sukazo gifta wani katafaren gida,bata
maida kanta ga kallon gabanta ba har sai da suka isa qofar gidansu,sauka tayi ta
sallami mai motar tana cusa kai cikin gidan gami da yin sallama.

Fakadeden tsakar gidan nasu wanda ada can zamanin quruciya takejin babu
wajen daya kaishi dadin xama da dadin yin wasa,kafin wasu murd'addun al'amura su
zama silar da zaman tsakar gidan ya zame mata tamkar zama kusa da ramin maciji,babu
kowa a tsakar gidan saidai a share yake sarai fes cikin tsafta da kulawa,batayi
mamakin ganin babu kowa din ba don tasan a irin wannan lokacin saura qannenta na
islamiyya.

Daga falonta ta amsa mata sallama,shahida taci gaba da takawa har zuwa qofar
falon ta sabule takalmanta ta shiga tana sake maimaita sallamarta.

Cikin sanyi ta amsa mata kamar kowanne lokutta,wanda hakan kusan ya zame
musu jiki ita da umman tata
"Yanzu kike tafe?" Umman tata ta fada cikin jin nauyin d'iyartata wanda har yau ya
kasa barinta
"Wallahi umma,na manta yaune ranar da nake zuwa sai wajen uku na rana na tuna"
"Da kin bari sai gobe ai,tunda yamma tayi.....mubina ma ta riga da tayi wankin
harsun bushe ta shanya,tunda taga rana ta soma baki zoba tace wataqila yau yaya ba
zata samu zuwa ba"
"Me yasa?,da ta jirani ai ina kan hanya" gaida ummantata tayi ta amsa tana
tambayarta anty zubaida huda da mai gidan,ta miqa mata saqon da anty zubaidan ta
bata wanda itama batasan meye a ciki ba,bayan umma ta gama godiyarta ne kuma shuru
ya biyo baya,shahida ce ta dinga qoqarin sako hira jefi jefi,ko kusa a yanzu
batason yadda umman take qin sakewa da ita,kaman ba ummanta ba?,komai ya canza
tsakaninsu tun shekarun baya da suka shude.

Qarfe biyar ta shiga kitchen ta soma dorawa ummantata abincin dare da taga
tana niyyar daurawa,ita kuma tana daga tsakar gida zaune kan tabarmar da suka
shimfida,duk wani motsin rahama na kan idanunta,itama rahaman ta ankara da hakan
saidai ta nuna bata kula ba,irin wannan kallon umman tata ta saba binta dashi da
dadewa,kallon tausayi,kallon nadama,kallon kaicon biyewa son rai da son zuciya da
sukayi ita da mahaifin rahama shekarun baya da suka shude,har hakan yaso jefa diyar
tasu cikin hallaka,da tuni yanzu bayan shudewar mai gidan ita daya zata ci gaba da
kurbar baqinciki da bacin ran abinda suka aikatawa rayuwar rahaman.

Qarfe shida qannenta nata suka shigo,ta bisu da kallo sanda suke shigowar
cikin jin dadi tare da musu addu'a cikin ranta,koda yaushe tana jin dadi har cikin
ranta na yadda rayuwarsu ta banbanta da tata rayuwar a sanda take da shekaru kamar
nasu,kallo daya zakayi musu kasan suna samun kulawa da tarbiyyar data dace,mubina
ke bin rahama(shahida),sai khadija,faruq,sajid sai qaraminsu nasir.

Dukkansu fuskarsu qunshe da walwala suka iskota,ta jima cikinsu yayin da


mubina ta amshi aikin girkin,tana yi suna hira da yayarta da sauran qannunta.

A nan kan qatuwar tabarmar suka ci gaba da zama,suka gabatar da sallar


magariba,sannan mubina ta zuba abinci cikin babban tray.

Gaba dayansu kowanne ya sanya hannunshi suka soma ci,suna hira lokaci
lokaci,har cikin ranta tana jin dadin kasancewa cikin 'yan uwanta,saidai wannan
kallo da duba da umma ke mata tana qaunar ya gushe daga idanunta,ta manta da
faruwar komai,ya zama tarihi kamar ma bai taba faruwa ba.

Sallamar usman d'an maqotansu shi ya katse hirar tasu,ya gaida ummansu sannan
yace
"Ana sallama da anty shahida" hada idanu sukayi da umman,yayin da kowa abinda ke
yawo a zuciyarsa ya tashi daban da na d'an uwanshi,qas da kanta shahida tayi tana
kokawar hadiye lomar tuwon data riga ta saka abakinta,batakai ga hadiyewa ba saqon
usman ya shiga kunnenta,sai taji gaba daya abincin bai mata dadi a bakinta,ya kuma
gagara wucewar,hakan ya sanya ta miqe tsam ta isa bakin rariyarsu ta zubda tuwon
sannan ta wuce dakin umman ba tare data bi takan aiken da akayo mata ba.

Suya kawai qirjinta yake,waye wannan yakeson mata kutse ne cikin rayuwarta a
sanda bata shiryawa hakan ba?,waye shi da zai tunkari rayuwarta a sanda bata da
dukkan wani tsari akan kowanne d'a namiji?.
Shigowar umma dakin shiya katse mata tunaninta,ta yunqura ta miqe ta zauna
sosai daga kasalalliyar kwanciyar da tayi,wani mummunan tashin hankali ya ziyarceta
sanda ta dubi idanun umman taga hawaye na biyo kuncinta,cikin matuqar rudewa da
gigita tace
"Um....umma...hawaye fa kike umma meya sameki?,don Allah kibar kukan,kiyi shuru
kice wani abu"
"Dole nayi kuka shahida....bazan daina kuka ba harsai sanda abinda yake damuna ya
gushe,tashin hankalin da kika shiga kadai sanda aka aiko kiranki ya tabbatarmin
akwai sauran rina akaba,kuma hakan ke nunamin cewa dafin da muka zuba a zuciyarki
har yau bai gama wankewa ba" zamowa tayi daga saman kujerar tayi gurfane a gaban
umman tata itama hawaye na sakko mata cikin tashin hankali
"Ko kad'an umma,kufa iyayena ne,kune kukayi silar zuwana duniya,umma....ba tun
yauba na gayamiki ki goge duk wani abu daya faru daga ranki,ki daina alaqanta duk
wani yanayi da zaki gani tattare dani da cewa laifinku ne"
"Indai kinason hakan ta faru shahida ki koma yadda kike....ki amshi wani cikin masu
sonki kiyi aure,anwar bashi kadai bane namiji da don ya miki wani abu zai zama
silar da zaki maida kanki wata aba daban ba,indai ina ci gaba da ganinki a haka
baki sauraren kowa bare akai ga batun aure bazan daina zargar kaina ba har na koma
ga mahaliccina,kamar yadda mahaifinki bai daina zargin kanshi ba har ya koma ga
mahaliccin......" Maganar tata saita riqe,kuka sosai ya qwace mata,tana tuna
abubuwa marasa dadi da suka faru a rayuwarsu,tana tuna komai tar cikin
kwanyarta,qaruwar kukanta ya qara dasa tashin hankali a zuciyar shahida,wadda ta
miqe ta figi mayafinta cikin rawar murya tace
"Zanje,zan fita umma indai hakan shi zai sanya farinciki da walwala a cikin
zuciyarki" bata qara second guda ba tayi waje,kai tsaye kuma ba tare da saurarar
komai ba ta wuce zuwa qofar gidansu.*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON
GIRMAN ALLAH)KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don samun shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi*

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

0️⃣ 4️⃣
*AA*
0️⃣4️⃣

Kasa cewa komai tayi,maganar hudan ta cillata tunanin wata duniya can baya,wanda
duk yadda takai ga hana kanta batasan sanda ta fada ba.

Sai data sallami huda sannan taci gaba da sabgar girkinta,batasan me yasa ba
sam batajin yunwa,ko zancan da huda tayi ne ya cushe mata cikinta gaba daya ya
sanya har walwalarta ta ragu.

Tana tsaka da kwashe abincin cikin coolers huda ta shigo da sauri hannunta
dauke da wayar shahida tana fadin
"Anty ana kiranki,zata katse" ta fada tana miqa mata,bata amsa ba ta kalli screen
din wayar dake hannun huda,nuraddeen ne,saita dauke kai taci gaba da juye abincin
tana cewa
"Ajiyeta kawai huda,aiki nake" juyawa yarinyar tayi ta fice da wayar zuwa falo da
gudu don kada cartoon din da take kallo ya wuceta.
Tana cikin kintsa wajen sallamar anty zubaida ta karade falon sannan ta
taddata cikin kitchen din
"Sannu da dawowa maman huda"
"Yauwa sannunki shahida,kin ganni sai yanzu ko?,wallahi layi yau na samu....me aka
dafa mana ne yau da yunwa na dawo" nuni shahida tayi mata da food flask din dake
jere a wajen,ta qarasa tana budawa
"Hmmmmm,kice yau na musamman ne abincin,bari wannan sai nayi wanka zan zauna sosai
tukunna na kwashi dabge" qaramin murmushi shahida tayi mai fitar da d'an sauti tana
duban anty zubaidan,har takai bakin qofa ta dawo
"Au....ni kuwa kinsan nuradden na qofar gida zaune cikin mota yana jiranki?"
Asanyaye ta daga kai ta dubi anty zubaidan,sai ta sadda kanta tana goge plates din
data wanke zata jerasu a muhallinsu,hakan da tayi shi ya tabbatarwa anty zubaida ya
kira bata daga ba kenan
"Shahida.....wannan wacce irin rayuwa ce kika daukarma ranki?,mai sonka fa ya wuce
ka wulqantashi,laifin wani dama yana shafar wani?" Shuru ta sake zabar tayi,saboda
tana ganin sun gaza fahimtarta ne gaba daya,ta yiwa soyayya hidima,ta yiwa soyayya
halacci,ta yiwa soyayya dukkan wata kara da alkunya,qarshe data tashi ita mai ta
bata?,data tashi da wanne sakamako tazo mata?,sunfi kowa sani saboda haka sunfi
kowa amsar dukka tambayoyinta,ko daya bata tsinci komai cikin soyayya ba face
tsantsar butulci mummunan sakamako da kuma mummunar makoma,shin ta yiwa kanta a
dalci kenan idan ta sake cusa kanta a wannan bigiren?
"Nidai ya roqeni alfarma,saboda haka idan na isa dake ki leqa ko gaisawa ne kuyi"
zancan anty zubaida ya katse tunaninta,daga haka bata sake cewa komai ba ta ida
ficewa daga kitchen din,tana jinta sanda ta kira huda suka haye sama tare,tasan
kuma tayi hakanne don sanin halinta,ba qaramin aikinta bane ta fita ta baro masa
huda ta cikashi da surutu wanda idan ya gaji da zama yake sallamar huda shima ya
wuce nashi guri.

Anty zubaidan tafi qarfin komai a wajenta,don haka ta dauraye hannayenta ta


wuce dakinta,ta zari hijabi ta saka ta sanya slipper dinta ta wuce qofar gidan.

Kamar kowanne lokaci yana zaune cikin motar,bayanshi jingine da seat din
kujerar dayake kai,da alama ya jima zaune a wajen,duk da haka ganin fitowarta bai
hanashi miqewa ba yana sakar mata murmushi harta qaraso
"Barka na tunda na samu kin fito" ya fada tamkar wanda baiyi zaman jiranta ba
"Inda kayi aiki da shawarata tun a karon farko da duk bamu kawo wannan matsayin da
muke kai yanzu ba" ta fada kanta tsaye tana dubanshi,kafin daga bisani ta janye
idanunta,har ga Allah wulaqanta dan adam ba dabi'arta bace,zatafi kowa farinciki
idan har noraddeen ya janye daga qudurinsa daga kanta,ga sabanin tunaninta sai taga
ya saki murmushi
"Bani da damuwa shahida,nasan cewa mahaqurci mawadaci,zan iya jure koma meye indai
a kanki ne shahida" idanunta ta lumshe tana jin kamar jiri zaya kada ta,a rayuwa
yanzu babu abinda ke damunta sama da matsalar nuradden,ya soma shiga jiki da
zuciyar makusantanta,bata da buqatar a yanzu dukkan abinda zai kuma d'aga ma
rayuwarta hankali.
"Koma meye tabbas mai wucewa ne watan wata rana" furucin nuradden ya sake ratsa
dodon kunnenta,a sanda take kiciniyar dai daita kanta
"Don Allah.....shahida inason ki bani dama,ki saurareni koda wayata ce kadai ki
dinga dagawa,bazan takuraki kan koda yaushe saikin fito na ganki ba,amma ki daga
wayata,hakan kadai ya isarmin....don Allah" ya fada yana hade hannayensa waje d'aya
alamar roqo
"Naji ya isa,ka sameni ta wayar" ta fada tana juyawa don ta shige gida kamar wadda
take kan qaya ko wuta
"Tsaya mana shahida....." Yayi hanzarin fada,tsayawa tayi cak kamar yadda ya
umarta,saidai bata waiwayo ba a haka ya cimmata,gabanta yasha,yana murmushi ya miqa
mata wata leda
"Ga wannan,ki karba don Allah....." Batason doguwar magana saboda haka ta saka
hannu ta amsa kawai ta shigeshi,kallo ya bita dashi yana jin dad'i cikin ranshi,yau
an samu wani ci gaba da har shahida karo na farko ta amshi abun hannunsa,tabbas
watarana yana saka ran komai zai wuce,bai taba tsammatar tsintar kanshi cikin
soyayya makamanciyar wannan ba,saidai shahida ta cancanci komai,tana da nutsuwa
tana da hankali uwa uba kyau,shahidan tayi masa,tako ina ta amsa sunan irin macen
da yakeso,yake da burin mallaka,macen da cikin dubu sai an duba.

Tana shiga a nan falo ta ajewa huda ledar,tace ta dauka ta bata,tana jin huda
na tsallen murna da kacaniyar bude ledar tawuce dakinta ta hau sabgar gabanta,duk
don ta yakice komai,wanka ta soma yi,sannan ta jawo plate din abincin data shigo
dashi daxu sanda zata fita wajen nuraddeen din ta soma tsakurar abincin ciki,ci
take kawai,amma ko za'a rutsata da bindiga batasan wanne taste ke ga abincin
ba,tana cusa wa ne kawai maganin yunwa,duk sanda taji irin wannan yanayin tattare
da ita tasan cewa can cikin zuciyarta ba lafiya qalau take ba,ta hanata kanta
dukkan wani tunani,ta bude jakar makarantarta ta dauko exams din dalibanta ta shiga
marking tana shigarwa cikin paper din dake dauke da sunayensu.

Tana tsaka da haka wayarta dake aje can gefe ta soma haske,don dama abadan
wayarta a silent take,batason wani qwaqwwaran motsi da xai dameta,daga kai ta
dubeta,kamar ba zata daga ba saita miqe tsam tace ta duba,anty amina sunan dake
yawo saman screen din kenan,dan qaramin murmushi ta saki wanda bai bayyana ba koda
saman fuskarta ba bare mutum ya gane,saida ta bari wayar ta katse da kanta sannan
tabi kiran
"Ranki ya dade yallabiya,don naga alama kin xama hukuma saida lallashi,kinbar
rayuwar kowa bare ki nemeshi ko?" Wani murmushin ta kuma saki wanda yafi ja daxu
armashi fa bayyana,sai data koma ta zauna inda ta tashi sannan tace
"Ni na isa,ta yaya zan manta da anty amina ta?" Ta fada tana tura hular kanta zuwa
baya,hakan saiya qara fidda kyanta,sakamakon gashinta mai santsi daya bayyana
"Gashi kuwa?,kin d'aura aniyar mantawa dani din?,anya duniya da amana kuwa
shahida?" Duk sai komai ya tsaye mata cak,duk da cewa gaskiya anty aminan ta
fada,abinda bata sani ba tana gujewa kiranta ko haduwa da itane,saboda tana daga
cikin abubuwan dake tuna mata baya,wanda take ra yaqi shafe komai shekara da
shekaru
"Yanzu dai ayimin afuww,inayini anty amina mun yini lpy?"ta fadi tana kada biron
dake hannunta hagu da dama
"Lpy alhmdlh....ya gida?"
"Lpy qalau muke,ina yarana?"
"Yaranki duka sunyi fushi" murmushi ta sake saki
"Suyimin afuwa,ina nan zuwa,zuwan ba zata"
"Haka dai,kullum maganar kenan,fafur kin qimu kin gujemu,na rasa ma LAIFIN NA
WAYE?" jin anty aminar nason fadawa wani bigiren na daban ya sanyata soko wata
hirar don kauda waccar maganar
"Zan baku mamaki anty amina,kedai ki sharen hanya"
"Yo sharar hanya kuma ta nawa,na share na share har na gaji,kedai sai an ganki
kawai" sai ta miqawa yaran nata wayar suka shiga gaisawa d'ai d'ai da d'ai,su dinma
bikonta sukeyi duk tace musu tana nan zuwa susha kuruminsu,daga bisani suka miqawa
mamarsu wayar suka dan sake tattaunawa sannan sukayi sallama da juna.

Tana shirin aje wayar wani kiran ya sake shigowa,anty zubaida ce take kiranta
"Ki sameni a falo" ta fada kawai ta yanke kiran,saita sauke wayar daga kunnenta
tana miqewa tsaye ta gyara daurin zaninta,tana zura hijabinta wayar ta sake
haske,nuradden ne ke kira saita dauke kai ta qarasa saita hijabin nata ta fice a
falon.

Abbi anty zubaida da huda ne zaune gaban kwanukan abincin,kamar yadda


al'adar abbi take bai hawa dining saidai a sauke masa abinci a qasa a shimfida masa
table mat,yanzun ma abincin suke ci,ta qarasa cikin nutsuwa ta zauna gefan huda
tana gida abbun,ya amsa mata fuska a sake kamar kullum yana tambayarta
dalibai,murmushi tayi ta sani sarai baison koyarwar da take ko kad'an,amma ya
haqura ya bata damarta don baison ya tauyeta ko ya hanata abinda ta zabawa
kanta,duk da cewa tana koyarwa ne bisa wani sharadi da bata tunanin ma akwai randa
sharadin zai gindaya yayi sababin afkuwar barinta makarantar
"Wannan kayan da kika baiwa huda fa?" Cewar anty zubaida tana nuna ledar da
baki,waiwaya tayi yana duban ledar don sam ta mance ma tayi kyautarta,kunya ce ta
dan kamata ganin kayan da suke ciki,katuna ne masu dauke da kalaman soyayya sai
sauran tarkacen kaya da suka shafi masoya,idan ma akwai abinda ya shafi huda a ciki
bai wuce choculet masu tsada dake ciki ba,dan satar kallon uncle abbu tayi taga shi
sam hankalinshi ma ba'a kansu yake ba,saita maida wajen antyn
"Ki cire mata choculets din saiki ajemin sauran kayan"
"Eh da yake ni aka bawa ko?,to tattara kayanki ki bar wajen dasu tun ban gayawa
abbu abinda kike yi ba" da hanzari ta miqe tana miqawa anty zubaidan ban haquri da
ido,haka ta tattare kayan tana jin kamar ta watsar dasu a wajen
"Yaushe zakuyi hutu ne khadija?,inason wannan karon kuje kankia kuyiwa su dada
hutu,tanata qorafin kin yada su gaba daya bakya ta tasu"
"Kwana uku ya rage,donma sun tsaya jiran zuwan mai makarantar ne"
"Na qagu abbu ranar tazo wallahi...." Cewar huda cikin zumudi,waiwaya shahida tayi
tana duban hudan,batasan me yasa take yawan zumudi da zuwan mutumin da kowa yake
masa shaidar baida sauqi ko rangwame ba,kamar anty zubaida tasan tadin me take a
ranta tace
"Oh hudaaaa...irin wannan zumudi kullum zancanki kenan?"
"Ummi....yana da kirki wallahi,yanasonmu,idan yazo kowa sai an bashi chaculets masu
dadi da biscuits manya manya"
"Sarkin kwadayi...." Abbu ya fada yana lakuce mata baki,dariya sukayi gaba daya
"Ina tunanin randa zakuyi hutu ranar su faruq zasu dawo suma" abbu ya fadi yana
zuba lemo a cup,shahida dake niyyar barin falon ta dakata,fuskarta qunshe da
murmushin data kan jima bata yi ba,tayi kewarsu sosai,duk sanda suka koma makaranta
gidan baya mata dadi,tace
"Abbu amma baka gaya mana ba sai yau?" Dubanta yayi,yana mamakin shaquwarsu
"Eh,saiku hanamu sakat da shirin zuwansu,kaman su kadai ne mutane a gidan" ya
qarashe zancan nasa yana duban anty zubaida,tasan sarai su yake tsokana ita da
shahida,don haka ta dauke kai kaman bata jishi ba,murmushi mai sanyi shahida ta
saki ta juya tana ci gaba da tafiya
"Allah ya dawo dasu lafiya"
"Amin" ya amsa,huda kam ta kasa zaune ta kasa tsaye,yayun nata kamar qawaye suke a
wajenta,ita daya ce mace banda zuwan shahida gidan itama idan suka koma makarantar
ita kadai ke watangaririya a gidan,saidai idan ta gaji ta gudu gidan kakanninta na
wajen uwa.

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

A nutse yake kai abincin bakinsa,yayin da rabin hankalinsa ke kan wayarsa dake
aje gefan plate dim abincin,zaune take kan kujerar dake fuskantar tasa,tasha
kwalliya iyaka,kai kace zata je wajen wata dinner dinne,cikin dinkin lace riga da
skert take,hannayenta gaba daya biyun ta tallafe kumatunta dasu,yayin data zuba
masa idanunta,duk wani wani motsinsa yana yinsa ne kan idanunta,batasan wanne
kalarso take masa ba arayuwa,saidai koma meye tasan cewa son da take masa wani
bangarene mai girma a rayuwarta.

Kanshi ya daga daga wayar yana sake kai wani spoon din abincin bakinsa,sai a
sannan ya lura da irin kallon da take masa
"Hey!" Ya fada yana murza yatsunsa,hannayen ta sauke tana dan qaramin murmushi
bayan ta sauke ajiyar zuciya
"Kallon fa?" Ya tambayeta a taqaice,muryarta cikin rauni da nuna fargaba wanda ya
wanzu har saman fuskarta tace
"Ina tsoron kar na rasaka anwar,ina jin kamar watan watarana zan rasaka" ta fada
can qasan ranta tana jin kishinta na cin zuciyarta,tana jin kamar zata dawo
rayuwarshi ta rabasu,ta san cewa a yanzu sun yiwa rayuwar juna nisa saidai ta kasa
samun nutsuwa da kwanciyar hankali duk da haqarta ta cimma ruwa,aje cup din da yayi
niyyar kaiwa bakinsa yayi,ya hade hannayenshi waje guda gami da saka yatsunsa cikin
na juna
"Meye abun jin tsoro a ciki?" Kai ta kada tana gyara zamanta bayan ta goya
hannayanta a qirji
"Kai din kalar namijin da kowacce mace keso da buri ne,don me bazanji tsoron kar a
rabani dakai ba?" Bai bata amsa ba sai kofin daya aje dazun yanzu ya sake
dauka,yana mamakin yadda take daukar abubuwan da suka shafe shi da girma
haka,saidai har yanzun baya jin wani feeling na daban ko na musamman tattare da
ita,yana dorata ne kawai bisa mizanin wasu abubuwa da martabarta ke alaqantuwa
dasu
"Shine dalilin kenan da kikai qorafi wajen anty hasana?" Ya jefo mata tambayar yana
kafeta da ido,gefe guda kuma yana karantarta a fakaice
"Aure kikeso?" Kai tsaye ta gyada masa kai a sanyaye tana mai fata da addu'ar cikar
burinta,shuru ya ratsa na tsahon minti daya ba tare da wani daga cikinsu yace komai
ko yayi wani qwaqwaqwaran motsi ba,ture kujerar da yake kai yayi baya sannan ya
miqe tsaye yana kwashe wayarshi da muqullin motarsa
"Zamuyi magana later" ya fada yana sauka daga step din da dining din yake kai,da
hanzari ta biyoshi a baya tana son tace wani abu,kacibus sukayi da hajiya bilkisu
mahaifa ga nafisa,dan dakatawa yayi kadan cikin girmamawa
"Au harka kammala kenan?"
"Eh zan wuce office ne ana jirana"
"To ko saika dawo din?,da akwai maganar da da nakeso muyi"
"To ba damuwa" ya fada yana ja da baya,ta wuce yabi bayanta zuwa cikin falon.

"Alhaji ne yace na tuntubeka,me zai hana ka dawo cikin gidan nan kaci gaba da
zama damu kamar yadda ake a baya?" Nafisa dake lafe kusa da hajiya bilkisu ta daga
kai a hankali tana satar kallonshi,addu'a take a ranta Allah yasa ya amince da
hakan,da tafi kowa jin dadi a duniya,koda yaushe bata da burin daya wuce ta ganta
kusa dashi
"Ayima alhj godiya na gode sosai,saidai yanayin aikina bazai bani damar hakan
ba,hakan ma alhmdlh babu wata a matsala" dan shuru tayi sannan ta jijijjiga kai
"Toh shikenan...babu damuwa Allah ya dafa...."
"Don Allah ya an....." Nafisa tayi hanzarin fada don ba hukuncin dataso anwar din
ya yanke kenan ba,harara hajiya bilkisu ta jefa mata wanda shine silar yankewar
sauran maganar tata,miqewa yayi yayi mata sallama kana ya fice daga falon gaba daya
zuwa inda ya aje motarshi.

"Ke wace iriyar yarinya ce ne nafisa?,bakiji gargadin da nake miki koda


yaushe akan ki dinga kama kanki gaban anwar?,a haka kike tunanin zaki samu qima da
daraja wajenshi?" Langabe kai tayi cikin sigar tausayi tace
"Afwa mom...." Bata sake ce mata komai ba ta gyara zamantabta dauki wayarta ta
shiga danne danne,hakan ya sanya nafisan itama miqewa ta haura sama inda dakinta
yake.

Kai tsaye gaban mudubi ta isa ta tsaya sosai tana qarewa kanta kallo,har yau
cikin zuciyarta bata jin ta mallaki anwar yadda takeso,tanaji a jikinta har yau
zuciyar anwar ba tata bace,meta rasa?,meye bata shi?,ta fita komai,ta kere mata a
komai,tun daga kyau,kudi zuwa matakin karatu,amma tana jin har yau kamar ta kashe
maciji ne bata sare kanshi ba.

Da hanzari ta koma da baya ta lalubi wayarta dake aje gefan pillow dinta,sai
data fara tura mishi saqo dake qunshe da kalaman soyayya sannan ta lalubi number
mema ta kira,bugu hudu ta d'aga
"Yayinki ake" mema ta fada cikin daga murya mai cakude da dariya dariya,murmushi
nafisa ta saki tana shaf fuskarta zuwa wuyanta,yayin da take sake qarewa kanta
kallo a madubi,wannan kalma na mata dadi,amma gaba daya kaman bata aiki akan
anwar,duk da cewa bata da wata qwaqwqwarar hujja da zata nuna cewa babu sonta cikin
zuciyarshi,saidai ita din bata gamsu da yadda mu'amalarsu ke gudana ba har zuwa yau
"Wannan kalma mema taqi amfani akan anwar har yau"
"Kai haba?,wane mutum?,shi ya isa?,me ya fiki dashi da zai...."
"Dakata mema....kice komai a kaina amma banda akan anwar....mema,ina tunanin mun
kashe maciji ne amma bamu sare kanshi ba,zuciyata da ruhina har yau basu gamsu
ba,ta yaya zan sake binneta da ranta?,ta yaya zan sake b'atar da ita daga
duniyarshi?,inason haskena shi kadai ya wanzu a cikin ruhi da rayuwarshi"
"Yanzu me kike tunani?,me kike gani?"
"Ke zanwa wannan tambayar" shuru mema tayi na wasu 'yan sakanni sannan tace
"Alright ina da wadansu 'yan dabaru da shawarwari,amma yanzu bana qasar,ina benin
republic...."
"Ubanme kike jeyi can?,ke mema???" Nafisa ta katse meman cikin zabura,tun kafin ta
gama bayanin nata,dariya mema ta saki sannan tace
"Share kawai"
"Ohk....ya zama dole ki dawo to"
"Saboda me?" Ta fada a dan tsiwace
"Saboda matsalata,kin sani sarai bana son jira?"
"Haba hajiyata....kinsan me ya kawoni nan din?,asara kikeson janyomin kenan"
"Har ta nawa?" Ta tambayeta kai tsaye
"Dubu dari ce ba yawa"
"Zan biya....ki tabbatar gobe kin dawo,wajen yammaci mu hadu a indomie joint"
"Allah ya barmin hajiyata,karkiji komai,bari na fara hada kayana" ta katse wayar
yana fadawa saman katifar dakinta,ba wani benin da taje,ba nisa tayi ba,don a yanzu
haka ma tana cikin katsina.

Aje wayar nafisa tayi,sannan ta juya ta shige bandaki.

Jujjuya wayar yake a hannunshi bayan ya kammala karanta saqon nafisan,sau


tari bai fiya maida mata amsa ba,har hakan ya zame mata jiki bata fiya damuwa
ba,har zuciyarshi yake hakan bawai da gayya bane,bayajin wani abu dangane da duk
wata kalma da zata fito daga bakinta ko ta saqon waya,maida wayar yayi aljihunsa
sannan ya fito daga motar tashi ya kashe ya tunkari ginin kamfanin.*ZAFAFA BIYAR NA
KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI
TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

0️⃣ 5️⃣
*AA*
0️⃣5️⃣

Qarfe sha biyu na rana ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta,siririn
tsaki taha qasa qasa,tun daxun ake maimaita magana d'aya taqi ta qare,da d'ai da
d'ai d'ai take qarewa malaman dake zaune a office din shugaban makarantar ana
tattauna taron da gobe ne za'a gabatar a kuma rufe makarantar don tafiya hutun
azumi,don tsarin makarantar ne basa karatu cikin azumi,suna rufe makaranta ne azumi
saura sati daya ,su dawo karatu bayan sallah da sati biyu,caraf idanunsu suka
hadu,saita janye tata qwayar idanun taja tsakin a sanda yake jifanta da
murmushi,malam musbahu kenan,mutum daya tak daya takura rayuwarta cikin makarantar
fiye da kowacce halitta,itakam shi da nuraddeen batasan wanda yafi wani naci
ba,harma gwara nuran yakan d'aga mata qafa lokaci zuwa lokaci,tun dazun take jinta
not comportable ashe shike kallonta.

Sake duban agogon nata tayi sannan ta miqe lokaci guda,ta kuma nemi izinin
tafiya kan tana da wani uzuri,babu musu shugabannin sashen secondry dana primary
suka bata izini
"Bamuso tafiyarki ba ayanzu miss shahida,saboda yanayin gudunmawar da kike badawa
ta bambanta data kowa" malam musbahu ya fada yana dubanta qasa qasa,bata amsashi ba
har sai data kammala hada takardunta sannan tace
"Ba wanda nafi a nan,kuma duk wata gudunmawa data dace na riga dana bada ita" a
nutse ta juya ta fice bayan tana yunqurin ciro wayarta daga jaka.

Sai data kira anty zubaida ta shaida mata ta wuce gidan anty amina sannan ta
tsaida abun hawa,don idan azumi ya kama bata fita ko ina sai an kammala,in bata
jewa anty aminan ba batasan lokacin zuwanta ba,hakan yasa ta daure zuciyarta ta
yanke shawarar gwara taje din kawai.

Tafiyar minti arba'in kacal daga makarantar zuwa gidan anty aminan,da
sallama ta shiga gidan,saidai hayaniyar yara bai bari anji ba saidata sake wata
sallamar,hamida ita ta soma ji,ta nufi shahida da gudu tana mata oyoyo,kafin kace
meye wannan sun lullubeta,qarin tashin hayaniyarsu shiya ankatar da anty amina dake
kitchen tana shirya musu abincin rana saboda lokacin tafiya islamiyya ya gabato,ta
leqo cikin mamaki tana duban shahidan,bata taba tsammatar ganinta ba,yadda ta saki
baki ya bawa shahida dariya,saita murmusa sanda take ciro alewa daga jakarta tana
barewa qaramin yaron anty aminan faisal
"Ku qarasa ciki ina zuwa" ta fada tana komawa kitchen din,da haka suka qarasa falon
anty aminan suka zube kowa na murnan ganinta,sun kasa qarasa shiryawa ma zuwa
islamiyyar.

Duk sai data raba musu abinda ta ruqo sannan sukaci gaba da hirar kowa tana
biye dashi,ta jima rabonta da walwala irin haka,tunda can maison yara ce dama
ita,hakan yasa taji wani sukuni na musamman na shiga cikin ranta.

"Yayaa,ina uncle kuwa?,yayimin alqawarin sweet har yau bai dawo ya kawomin ba"
sadiq yaron anty amina ya fada yana saka rigar islamiyyarshi,dai dai sanda anty
aminan ta shigo da plates din abinci,cak shahida taji komai ya tsaya mata,ta kasa
hadiye biscuit din data farke cikin wanda ta kawo musu ta d'an soma ci saboda
hamida data takura mata cewa da dad'i,yadda ta tsaya cak haka anty aminan ta tsaya
tana dubanta,don tasan saddiq ya b'arota,yayin da sauran yaran duk suka zuba mata
idanu suna sauraren amsarta,don gaba dayansu suna da buqatar sanin dalilin daina
ganinsa dare d'aya lokaci daya kuma gaba d'aya
"Ya mutu" furucin ya fito daga bakinta kamar mai ciwon baki,idanunta kan saddiq
wanda ya kasa qarasa saka rigar tashi jin abinda shahidan ta fada,harga Allah tana
daukarshi tamkar matacce ne a ruhi da zuciyarta,duk da dama ya dade da mutuwa a
cikin tata zuciyar
"Ya mutu yayaa?"saddiqa ta fada tana zaro idanu,alhini da mamaki ya bayyana qarara
kan fuskar yaran gaba daya
"Kai banason dogon surutu,ke hamida dauki abincinku ki kai muku dakinku kuci a can
ku shirya maza ku fice ku bani waje" cewar anty amina tana musu wuta wuta,don tasan
tabbas ba qaramin furuci bane wannan a wajensu,duba da yanayin sabo dake tsakaninsu
dashi,c gaba fa maganar kuma dai dai yake da hargitsa lissafin shahida da dukkan
walwalar data samu cikin gidan,hakanan yaran suka dinga fita daga dakin jikinsu a
matuqar sanyaye.

Sai da suka gama fita gaba daya sannan anty amina ta qarasa kusa da shahida
ta aje kwanon abincin idanunta na kan shahida data sauke kanta qasa
"Har sai yaushe shahida zakici gaba da rayuwarki kamar kowa?,sai yaushe zaki maida
abinda ya faru kaman bai faru ba?,yaushe zaki rufe wannan tarihin daga babin
rayuwarki?,me yasa wannan lamarin yaqi fita daga ranki kamar sauran abubuwa?" Kasa
bata amsa tayi sai tafukan hannayenta data saka guda biyun ta rufe fuskarta
dasu,ita kanta tana son ta koma normal,tana son ta zama kamar kowa,tanason ta manta
da komai amma ta gagara yin hakan?,me yasa abun yafi tsaya mata fiye da komai?.

A jigace ta dawo gida bawai don tayi wata gajiya ta azo a gani ba,illa dai
zuciyarta data dahu lugub ta kuma saare tun sanda yaran suka jefa mata tambaya a
kanshi,batayi dogon zama a falon ba ta yiwa anty zubaida sallama kan cewa gobe da
wuri zata tashi tana son isa makaranta da wuri don gobene ranar hutunsu.

*1:26 pm*

Tsaye yake cikin wani makeken fili wanda ya qawatu da fareren furanni tas da
jefi jefin koraye,waje ne daya ni'imtu,ya kuma qawatu da wata irin iska mai dadi da
taush take kai kawo iya fadi da girman filin,cakude iskar take da qamshi mai sanyi
wanda ke ratsa zuciya,fararen kayane qal a jikinsa,yana tsaye gaban wata qaramar
qorama mai garai garai,kana iya hangen kifayen dake linqaya da kai kawo daga can
qasanta.

Ingarman bayanshi take iya hangowa,ta zuba mishi idanu tana jin wani bugu da
zuciyarta keyi,tana jin tsoro da zumudin tunkararsa lokaci guda na mamayarta,a
hankali ta dinga takawa gareshi,iska na diban gashinta tana watsashi gaban fuskarta
hagu da damanta,lokaci lokaci tana sanya hannu tana d'aukewa.

Dab da bayanshi ta tsaya taci gaba da kallonshi gabanta na faduwa,tanajin


kamar zata kira sunanshi sai bakinta ya kasa furta komai,ta dan jima a haka sannan
ta miqa hannu da niyyar kama kafadarsa sai ya waiwayo,fuskarshi cike fal da annuri
kamar yadda ta saba ganinsa,yayi kyau ya canza kamar bashi ba,cikin sakan kad'an
dukkan wani annurin fuskarsa ya gushe,ya hade girar sama da qasa,bacin rai ya
bayyana qarara a fuskarsa
"Me kike yi a nan?!" Ya fada cikin tsawa da fusata
"Ban sani ba!" Itama ta maida masa cikin tsawa da fushi,sai kuma ta juya cikin
gaggawa ta bashi baya ba tare data bar wajen ba,ta d'an jima ahaka sannan ta
waiwaya,saidai wayam baya wajen,babu shi babu alamarsa,wani tashin hankali da
batasan na meye ba ya rufto mata,musamman sanda taga duhu ya soma mamaye
wajen,kiran sunanshi ta soma yi a jere babu qaqqautawa,saidai babu alamun yana
jinta bare ta saka ran zai amsa.

A firgice ta miqe daga kwanciyar da take bakinta d'auke da sunanshi kamar


yadda take kiranshi cikin mafarkin,a hankali hankalinta ya dawo jikinta ta fuskanci
mafarki ne,saita sauya sunan nashi da ambaton sunan Allah,yayin da hawaye ya soma
sauka daga idanunta masu zafin gaske,wanne wacce irin jarrabawa ce?,har a mafarkin
ma bazai haqura ya barta ba,tayi shiri hakanan ta tattara dukkan qarfinta tana yaqi
dashi haiqan,saidai ta fuskanci kaman fad'an gwaggo a kofa take.

Sai data gama kukanta son ranta sannan ta sauka a hankali don karta tashi
huda da yau take tayata kwana,ta shiga bandaki ta daura alwala,saidai yau ta kasa
sallar kamar tadda ta saba,saboda wata irin kasala da mutuwar jiki data sakar
mata,abinda ya gudana a mafarkin ya soma dawo mata tar a kwanyarta,duhun da taga ya
soma mamayarta shine abu na farko daya daga mata hankali,me hakan yake nufi
kenan?,saita tuna ranar da suka ga fuskokin juna na qarshe,komai ya soma dawo mata
d'aya bayan d'aya cikin rayuwarta kamar wadda aka kunnawa magijin film.

*_ZAN RAYU DAKE_*

Ranta a matuqar bace take kallon botikanta guda biyu dake shaqe da shinkafa
da waken sadaka wanda tuni suka hadu da qasa suka saje,botikam kuma sukayi fata
fata dasu,sannan ta sake d'aga kai ta dubi ahmadi dake tsaye gabanta shida
abokanshi biyu yana kallonta cikin gadara
"Anzubar kiyi duk abinda zaki,yarinya ba kowan kowa ba sai shegen isa da izza,don
kina raba mana sadaka saikin gindaya mana sharadi,bamu da hannun diba mu zuba da
kanmu?"
"Ni kuka yiwa haka?" Ta fada tana hadiye wani qullutun bacin rai da baqinciki
"Ke aka yiwan,ki dauki duk matakin da zaki dauka"
"Xaku ga gatana" ta fada a sanyaye bayan ta duqa tana tsince abinda xai iya
daukuwa a wajen,ta fadi maganarne kawai ba don tana da gatan ko me tsaya mata ba,ta
fada ne kawai saboda bata da abun cewar
"Waye gantanki?" Ya fada bayan sun sheqe da dariya duka su ukun
"Nine gatanta!" Wata kakkausar murya ta ratsa dariyar tasu,cak suka tsaya da
dariyar,basu kadai ba har itama dagowa tayi daga tsintar da take tana laluben ina
mai maganar yake da idanunta,matashin saurayi ne wanda duka duka a qalla bazai
haura shekara ashirin da biyar ba,wankan tarwada ne dogo wanda da alama yana yin
qiba zata boye tsahonsa,yana da kyan fuska mai qayatarwa irin kyan da kama
kallonshi kasan cikin yaren hausa fulani yake,kuma tabbas sahun farko da
kyawawansu,ma'abocin kwarjini da kallom farko kawai zaka yi masa kwarjininsa ya
tabaka,fuskarshi a tsuke take babu alamun annuri a tare dashi yake takowa gabansu
ahmadi,kwarjininsa ya sanyasu tsayawa cak,fargaba ta kamasu,saida yayi gab da
ahmadi kamar zai fada jikinsa don har yana dan take masa qafa yace
"Me tayi muku?" Cikin tsoro tsoro da son nuna jarumta yace
"Raina mana hankali take,kullum ta kawo abincin sadaka sai ta rainama mutane wayo"
a hankali ya waiwaya ya dubi gefanshi inda take tsaye,karon farko idanunsu suka
sarqe dana juna,wani irin nauyi taji da batabtaba jinsa ba sanadiyyar kallon idanun
wani a duniya,kamar yadda shima yaji wani yanayi da baisan na meye ba ya saukar
masa harsai daya lumshe idonsa ya kuma bude cikin sakan biyu,hakan ya sake qara
kwarjininsa da kashe jikin shahida
"A'ah,wallahi ahmadi baku da mutunci" muryar wani dattijo dake xama a wajen lokaci
zuwa lokaci ta katsesu,duk suka maida hankalinsu kanshi sanda ya gama tattare
buzunsa da yake zama yana dinkin takalma,ya qaraso wajen yana nuna su ahmadi da
yatsa
"Yarinyar nan tunda ta soma zuwa wajen nan kuka kafa mata qahon xuqa,da kuka
fuskanci a kintse take shine kuka tsiri takurata,kowa ya shaidi yarinyar nan tunda
take zuwa wajen nan bata da abokin fada,hasalima taimakonmu take,bamu da abin ce
mata sai godiya,kullum daga kwanonta muke ci mu qoshi,bata taba bude baki ta kula
wani ba bare rashin kunya ta biyo baya,dama yau tun dazu na kula da take takenku
shi yasa naqi tafiya gida da wuri har sai ta tashi,ashe kuwa tsiya kuka shirya" a
hankali ya dauke kyawawan idanunsa daga kan dattijon ya maidasu kansu ahmadi da
duka gama tsurewa saboda bayanin da baba isuhu ya kwararo,sosai ya kafesu da ido
wanda har sai da sukaji kallon har cikin lakarsu
"Kubar nan,daga rana irinta yau kada na sake ganinku a nan arean,koda kuna da
abunyi har sai ta gama raba abincinta ta tafi"
"Barema basu da abinyi sai zaman kashe wando" baba isuhu ya dora sharhinsa,da
hanzari suka juya suka soma tafiya,saida suka bada 'yar tazara a tsakaninsu sannan
suka fara gunguni
"Ba wani shege Allah,ke kuma zamu gamu,mu dake ne wallahi......ba wani waye waye"
da kallo ya bisu hannayensa xube a aljuhun wandonshi,idan ka tsirawa fuskarshi ido
sosai qaramin murmushi yake can qasan ranshi,saboda yadda suka nuna raki muraran da
basu tsaya sunyi zage zagen daura dashi ba,ya tabbata da sai sun gane kurensu.

"Allah ya saka maka da alkhairi kaji yaro....kubura maza hada kayanki ki wuce
gida" baba isuhu ya fada yana juyawa wajensa shima yana ci gaba da hada nashi
kayan.

Cikin wani irin nauyi da taji jikinta yayi mata ta duqa tana ci gaba da
tsince abinda zata iya,saiya duqa shima a hankali yana tayata laluben farantai da
cokulanta da suka nutse cikin qasa.
Kusan ma ya fita lalubowa da yawa,hannunshi yayi futu futu da qasa fiye da
nata,baice komai ba ya taka wajen wata roba tata ya zuba cokulan ya ciro d'an
tsumma daga aljihunsa dayafi kama da handkherchief ya goge hannunshi sannan ya
dauki botikin daya rage a wajen ya saka robar a ciki ya rufe ya dauki botikin yayi
gaba,bata gane me yake nufi ba amma saita gaza tambayarsa saboda kwarjinin da yayi
mata,binsa tqci gaba dayi wanda suna kaiwa qarshen titin yadan ja ya tsaya,saita
wuceshi tayi gaba,takunshi ta dinga ji alamun yana biye da ita ne,saidai idan ba
kaga sanda suka taho taren ba ba zaka ce tare suke ba.

Suna karyowa layinsu taji gabanta ya fadi sanda ta kalli gidansu


"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta furta cikin zuciyarta,saboda tuna kalaman
da ummanta ta dinga fada kam mahaifinsu kafin fitarta da abincin sadaka,fatanta
d'aya,Allah yasa zuciyar umman ta sanyaya kafin dawowar mahaifinsu,matuqar bata
sanyaya din ba Allah ne kawai yasan iyakacin abinda zai faru yau a gidan nasu.

Wannan tunanin da kuma tunanin wanda ke biye da ita baquwar fuska ne a


unguwar yasa saura gida biyu ta qarasa qofar gidan nasu taja tunga ta tsaya ba tare
data juya ba,tana jin sanda ya qaraso gefanta ya aje mata botikin
"Duk sanda zaki taho ki dinga samun d'an rakiya namiji babba yana rakoki ya dawo
dake" ya furta cikin wata kwantacciyar murya data tafi da tunaninta cikin lokaci
guda,ta lumshe ido tana jin zuciyarta na qara yawan bugunta,bata motsa ba har sai
data tabbatar ya bace daga layin gana daya sannan ta sanya hannu ta dauki botikin
nata,sai kuma taji haushin kanta ya kamata,ko banza ya cancanci ta bude baki tayi
masa godiya saboda taimakon da yayi mata ba tare daya santa ko yasan daga ina ta
fito ba,yanzun haka babu lallai ta sake ganinsa bare tayi masa godiya,da wannan
tunanin ta qarasa qofar gidansu,sai kuma fargabarta ta dawo sabuwa sanda ta soma
jiyo tashin murya daga cikin gidan nasu,dai dai sanda qanwarta mubina ta fito
hannunta dauke da 'yar tsana da kayan wasa na qasa wanda suka sha fentin pink da
green,har zata wuce abinta da gudu shahida ta cafko rigarta,saita tsaya tana duban
shahidan
"Baba ya dawo?" Ta tambayeta tana fatan tace mata a'a,amma saita amsa mata da
"Eh ya dawo,yana qofar dakinsa ma suna fada da umma" ta bata amsa tana zame rigarta
ta sake sheqawa da gudu ta shige cikin yara 'yan uwanta ko a jikinta.

Jingina bayanta tayi a soron gidan nasu tana jin munanan lafuzan dake
fitowa daga bakin mahaifinta da mahaifiyarta suna jifan junansu dashi,wani qataton
tashin hankali da take tsintar kanta a ciki duk sanda ta riskesu a wannan halin ya
rufto mata,saita sulale ta duqa a soron tanajin ruwan bala'in dake tashi cikin
gidan,wanda ta tabbatar zuwa yanzu dukka maqota kowa ya kasa kunne ya diban
rahoto,ta rasa wannan wacce irin masifa ce?,ta rasa meke haifar da irin wannan
gagarumin yaqi kulli yaumin tsakamin mahaifanta,basa kwana uku cur cikin jituwa da
juna,basa sati cikin salama da walwala,tunda ta taso tayi hankali haka ta rsiki
rayuwarsu,babu ragayya ko kad'an ga junansu,ba wanda ke ganin wani da gashi a
tsakaninsu.

A qalla sun kusa awa guda suna wannan dauki ba dadin a tsakaninsu,wanda har
zuwa sannan hawaye baibar zuba a idanun shahida ba,tilas ta miqe da niyyar shiga
ciki ko Allah zaisa tayi nasarar dakatar dasu,duk da tasan cewa da wuya wai gurguwa
da auren nesa,don idan irin hakan ta faru dukkansu idanunsu rufewa yake basa ji
basa gani.

Ilai kuwa yana zaune bakin rijiya yayin da da umman tata ke cikin
kitchen,har ta qaraci sallamarta babu wanda ya jita a cikinsu,hakan ya sanya ta
dirr botikin ta durfafi dakinta ta bude ta shige sannannta rufe qofar ruf waiko
zata daina jin tashin munanan furucinsu,saidai bata sauya zani ba,haka tq zame ta
zquna gefan katifarta ta hade gwiwarta ta qanqame tana ci gaba da kukanta.

Basu saurara ba har sai da khadija qanwar shahida ta biyu ta dawo daga gidan
kitson da umman ta turata da yunwa,tace umma yunwa amma bata bi ta kanta ba,hakam
yasa ta watsar da takalmanta ta zube dirshan wajen tahau ihun kuka,katsam sai
farouq mai binta ya farka daga baccin da yake shima ya hau tsala nashi kukan jin
ba'a daukeshi ba akan kari,tilas baban nasu ya suri takalminsa ya fice fuu badon
sun gama ba,ita kuma tahau hidimar yaran tana yi tana mita da alamun itama bata
huce ba.

"Au,ita kuma wannan yaushe ta shigo tazo ta yasarwa da mutane botiki kan
hanya salon wani yaci karo dashi ya fadi,inama sauran botikan?" Jin hakan ya sanya
shahida komawa saman katifa ta kwanta luf tamkar mai bacci tana sauke ajiyar
zuciya,hakan ya sanya koda khadija da umman ta aikota tazo ta dubo shahidan tazo
saita koma tace mata umma bacci take
"Bacci?,bacci kuma da wannan yammacin?,k'nnnnn,to Allah yasa ba zazzabinne kuma ya
dawo ba" ta fada tana ci gaba da baiwa faruqu nono.

Takunta ne kawai ke kai kawo a idanunsa sanda yake komawa daga inda ya
rakota,idanunsa ya dinga lumshewa hakanan yanayinta da yanayin tafiyarta yaji ya
burgeshi,sanyinta,yanayin maganarta,da haka har ya qarasa wajen da suka baro
dazun,yanzun babu kowa,har malam isuhu ma ya wuce,kai tsaye ya wuce shagon balarabe
mai saida kayan provision,wanda dama tun asali wajensa yazo.

Hannu ya bawa bala sukayi musabaha,sannan ya zauna kan bencin dake aje daga
cikin shagon saboda custumers daya tarar yana sallama
"Ai na hangoka kaida wadan can yaran marasa kunya,yarinyar da babu sawa ba
fitarwa,ina Allah Allah naje na musu magana naga kaje,ai yarinyar kirkir ce,ba
qaramin taimakon masu sana'a a nan wajen take ba,kowa na yabonta"balarabe mai kanti
yaci gaba da baiwa anwar labarin zamanta a wajen duk da ba tambayarsa yayi
ba,hakanan shima ya samu kansa da saurarensa,duk da cewa bai tofa komai ba cikin
zancan,har sai da balarabe ya gama b'ab'atunsa yayi shuru
"Kana nufin kullum sai tazo nan kenan?" Anwar ya tambaya yana miqawa balarabe naira
dari biyu,yasa hannu yana amsa
"Qwarai kuwa,kullum tana zuwa daga qarfe uku na rana zuwa hudu,hudu tanayi ta gana
rabarwa ta hada kayanta sai tayi gida" baice uffan ba saiya maida akalar tunaninsa
kan me xai saya da d'ari biyun wanda zai riqeshi zuwa sanda zai sake samun wani
kudin
"Me dame za'a baka malam anwaru" d'an tsaki yaja kad'an na alamun dawowa daga
tunani yana murza goshinsa
"Bani kwaki da suger"
"Kuma dai?" Kafadarsa ya dage yadan mari cinyarsa da tafin hannunsa
"To yq za'ayi,rayuwar kenan ai,wataran sai labari in sha Allah"
"Baka yarda ne anwaru....ni na yarda da amincinka,na yarda ka zabi abinda kakeso
cikin shagon na baka bashi kaje idan ka samu ka kawomin amma ka qiya" balarabe ya
fada sanda yake auna masa kwakin a baqar leda,dan miskilin murmushi anwar ya saki
"Idan ka bani naje na samo na kawo maka naji dadi gobe sake karba zanyi,idan kuma
yauna samu abun biyanka gobe fa ina dashi?"
"Ni a wajena ba wata matsala" kai ya kad'a
"A'ah,Allah ne kad'ai baya gajiyawa,amma yau da gobe dole dan adam ya gajiya" kai
malam balarabe yake kadawa,ya jima rabon da yaga matashi mai kishin kai kamar anwar
din,matashin daya dogara da kanshi bai rabu da kowa ba,ya yarda shi din ba kowa
bane,ya kuma yarda da talaucinsa ya kame kansa,yana gama auna masan ya miqa masa ya
karba yayi masa sallama ya wuce.

Muqulli ya ciro cikin aljihunsa ya saka ya bude qofar gidan,ya tura ya


shiga,babu kowa cikin gidan dama bai tsammaci ganin kowa din ba tunda yasan shi
d'aya yake rayuwa a cikin gidan,saidai ga mamakinsa gaba daya dakinsa daya fita ya
barshi a akillace an bibbincike masa,ya saba ganin hakan,yasan kuma bazai wuce
samarin unguwa bane da suka kafa masa qahon zuqa haka kawai ba,yasan baibar wani
abu mai amfani da za'a dauka ba cikin kayan,bama cikin kayan ba cikin gidanma gaba
daya,aje ledar garinsa yayi ya duba agogon dake maqale a bango,saura minti ashirin
asha ruwa,yasan zai isheshi ya gyara wajen,mutum ne da bayason qazanta ko kadan,a
nutse ya gyara komai ya maida muhallinsa,sannan ya wuce kitchen ya bude robar da
yake aje plate da kofi ya dauko ya jiqa garin sannan ya sake fita ya siyo pure
water guda d'aya da naira goman data rage masa,yana shigowa soro aka sha ruwa,a nan
ya balle ya shanye,ya qarasa bakin fanfo ya daura alwala ya wuce masallaci.

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos[6/30, 10:46 AM]


+234 814 691 0795: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI
SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

0️⃣ 5️⃣
*AA*
0️⃣5️⃣

Qarfe sha biyu na rana ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta,siririn
tsaki taha qasa qasa,tun daxun ake maimaita magana d'aya taqi ta qare,da d'ai da
d'ai d'ai take qarewa malaman dake zaune a office din shugaban makarantar ana
tattauna taron da gobe ne za'a gabatar a kuma rufe makarantar don tafiya hutun
azumi,don tsarin makarantar ne basa karatu cikin azumi,suna rufe makaranta ne azumi
saura sati daya ,su dawo karatu bayan sallah da sati biyu,caraf idanunsu suka
hadu,saita janye tata qwayar idanun taja tsakin a sanda yake jifanta da
murmushi,malam musbahu kenan,mutum daya tak daya takura rayuwarta cikin makarantar
fiye da kowacce halitta,itakam shi da nuraddeen batasan wanda yafi wani naci
ba,harma gwara nuran yakan d'aga mata qafa lokaci zuwa lokaci,tun dazun take jinta
not comportable ashe shike kallonta.

Sake duban agogon nata tayi sannan ta miqe lokaci guda,ta kuma nemi izinin
tafiya kan tana da wani uzuri,babu musu shugabannin sashen secondry dana primary
suka bata izini
"Bamuso tafiyarki ba ayanzu miss shahida,saboda yanayin gudunmawar da kike badawa
ta bambanta data kowa" malam musbahu ya fada yana dubanta qasa qasa,bata amsashi ba
har sai data kammala hada takardunta sannan tace
"Ba wanda nafi a nan,kuma duk wata gudunmawa data dace na riga dana bada ita" a
nutse ta juya ta fice bayan tana yunqurin ciro wayarta daga jaka.

Sai data kira anty zubaida ta shaida mata ta wuce gidan anty amina sannan ta
tsaida abun hawa,don idan azumi ya kama bata fita ko ina sai an kammala,in bata
jewa anty aminan ba batasan lokacin zuwanta ba,hakan yasa ta daure zuciyarta ta
yanke shawarar gwara taje din kawai.

Tafiyar minti arba'in kacal daga makarantar zuwa gidan anty aminan,da
sallama ta shiga gidan,saidai hayaniyar yara bai bari anji ba saidata sake wata
sallamar,hamida ita ta soma ji,ta nufi shahida da gudu tana mata oyoyo,kafin kace
meye wannan sun lullubeta,qarin tashin hayaniyarsu shiya ankatar da anty amina dake
kitchen tana shirya musu abincin rana saboda lokacin tafiya islamiyya ya gabato,ta
leqo cikin mamaki tana duban shahidan,bata taba tsammatar ganinta ba,yadda ta saki
baki ya bawa shahida dariya,saita murmusa sanda take ciro alewa daga jakarta tana
barewa qaramin yaron anty aminan faisal
"Ku qarasa ciki ina zuwa" ta fada tana komawa kitchen din,da haka suka qarasa falon
anty aminan suka zube kowa na murnan ganinta,sun kasa qarasa shiryawa ma zuwa
islamiyyar.

Duk sai data raba musu abinda ta ruqo sannan sukaci gaba da hirar kowa tana
biye dashi,ta jima rabonta da walwala irin haka,tunda can maison yara ce dama
ita,hakan yasa taji wani sukuni na musamman na shiga cikin ranta.

"Yayaa,ina uncle kuwa?,yayimin alqawarin sweet har yau bai dawo ya kawomin ba"
sadiq yaron anty amina ya fada yana saka rigar islamiyyarshi,dai dai sanda anty
aminan ta shigo da plates din abinci,cak shahida taji komai ya tsaya mata,ta kasa
hadiye biscuit din data farke cikin wanda ta kawo musu ta d'an soma ci saboda
hamida data takura mata cewa da dad'i,yadda ta tsaya cak haka anty aminan ta tsaya
tana dubanta,don tasan saddiq ya b'arota,yayin da sauran yaran duk suka zuba mata
idanu suna sauraren amsarta,don gaba dayansu suna da buqatar sanin dalilin daina
ganinsa dare d'aya lokaci daya kuma gaba d'aya
"Ya mutu" furucin ya fito daga bakinta kamar mai ciwon baki,idanunta kan saddiq
wanda ya kasa qarasa saka rigar tashi jin abinda shahidan ta fada,harga Allah tana
daukarshi tamkar matacce ne a ruhi da zuciyarta,duk da dama ya dade da mutuwa a
cikin tata zuciyar
"Ya mutu yayaa?"saddiqa ta fada tana zaro idanu,alhini da mamaki ya bayyana qarara
kan fuskar yaran gaba daya
"Kai banason dogon surutu,ke hamida dauki abincinku ki kai muku dakinku kuci a can
ku shirya maza ku fice ku bani waje" cewar anty amina tana musu wuta wuta,don tasan
tabbas ba qaramin furuci bane wannan a wajensu,duba da yanayin sabo dake tsakaninsu
dashi,c gaba fa maganar kuma dai dai yake da hargitsa lissafin shahida da dukkan
walwalar data samu cikin gidan,hakanan yaran suka dinga fita daga dakin jikinsu a
matuqar sanyaye.

Sai da suka gama fita gaba daya sannan anty amina ta qarasa kusa da shahida
ta aje kwanon abincin idanunta na kan shahida data sauke kanta qasa
"Har sai yaushe shahida zakici gaba da rayuwarki kamar kowa?,sai yaushe zaki maida
abinda ya faru kaman bai faru ba?,yaushe zaki rufe wannan tarihin daga babin
rayuwarki?,me yasa wannan lamarin yaqi fita daga ranki kamar sauran abubuwa?" Kasa
bata amsa tayi sai tafukan hannayenta data saka guda biyun ta rufe fuskarta
dasu,ita kanta tana son ta koma normal,tana son ta zama kamar kowa,tanason ta manta
da komai amma ta gagara yin hakan?,me yasa abun yafi tsaya mata fiye da komai?.

A jigace ta dawo gida bawai don tayi wata gajiya ta azo a gani ba,illa dai
zuciyarta data dahu lugub ta kuma saare tun sanda yaran suka jefa mata tambaya a
kanshi,batayi dogon zama a falon ba ta yiwa anty zubaida sallama kan cewa gobe da
wuri zata tashi tana son isa makaranta da wuri don gobene ranar hutunsu.
*1:26 pm*

Tsaye yake cikin wani makeken fili wanda ya qawatu da fareren furanni tas da
jefi jefin koraye,waje ne daya ni'imtu,ya kuma qawatu da wata irin iska mai dadi da
taush take kai kawo iya fadi da girman filin,cakude iskar take da qamshi mai sanyi
wanda ke ratsa zuciya,fararen kayane qal a jikinsa,yana tsaye gaban wata qaramar
qorama mai garai garai,kana iya hangen kifayen dake linqaya da kai kawo daga can
qasanta.

Ingarman bayanshi take iya hangowa,ta zuba mishi idanu tana jin wani bugu da
zuciyarta keyi,tana jin tsoro da zumudin tunkararsa lokaci guda na mamayarta,a
hankali ta dinga takawa gareshi,iska na diban gashinta tana watsashi gaban fuskarta
hagu da damanta,lokaci lokaci tana sanya hannu tana d'aukewa.

Dab da bayanshi ta tsaya taci gaba da kallonshi gabanta na faduwa,tanajin


kamar zata kira sunanshi sai bakinta ya kasa furta komai,ta dan jima a haka sannan
ta miqa hannu da niyyar kama kafadarsa sai ya waiwayo,fuskarshi cike fal da annuri
kamar yadda ta saba ganinsa,yayi kyau ya canza kamar bashi ba,cikin sakan kad'an
dukkan wani annurin fuskarsa ya gushe,ya hade girar sama da qasa,bacin rai ya
bayyana qarara a fuskarsa
"Me kike yi a nan?!" Ya fada cikin tsawa da fusata
"Ban sani ba!" Itama ta maida masa cikin tsawa da fushi,sai kuma ta juya cikin
gaggawa ta bashi baya ba tare data bar wajen ba,ta d'an jima ahaka sannan ta
waiwaya,saidai wayam baya wajen,babu shi babu alamarsa,wani tashin hankali da
batasan na meye ba ya rufto mata,musamman sanda taga duhu ya soma mamaye
wajen,kiran sunanshi ta soma yi a jere babu qaqqautawa,saidai babu alamun yana
jinta bare ta saka ran zai amsa.

A firgice ta miqe daga kwanciyar da take bakinta d'auke da sunanshi kamar


yadda take kiranshi cikin mafarkin,a hankali hankalinta ya dawo jikinta ta fuskanci
mafarki ne,saita sauya sunan nashi da ambaton sunan Allah,yayin da hawaye ya soma
sauka daga idanunta masu zafin gaske,wanne wacce irin jarrabawa ce?,har a mafarkin
ma bazai haqura ya barta ba,tayi shiri hakanan ta tattara dukkan qarfinta tana yaqi
dashi haiqan,saidai ta fuskanci kaman fad'an gwaggo a kofa take.

Sai data gama kukanta son ranta sannan ta sauka a hankali don karta tashi
huda da yau take tayata kwana,ta shiga bandaki ta daura alwala,saidai yau ta kasa
sallar kamar tadda ta saba,saboda wata irin kasala da mutuwar jiki data sakar
mata,abinda ya gudana a mafarkin ya soma dawo mata tar a kwanyarta,duhun da taga ya
soma mamayarta shine abu na farko daya daga mata hankali,me hakan yake nufi
kenan?,saita tuna ranar da suka ga fuskokin juna na qarshe,komai ya soma dawo mata
d'aya bayan d'aya cikin rayuwarta kamar wadda aka kunnawa magijin film.

*_ZAN RAYU DAKE_*

Ranta a matuqar bace take kallon botikanta guda biyu dake shaqe da shinkafa
da waken sadaka wanda tuni suka hadu da qasa suka saje,botikam kuma sukayi fata
fata dasu,sannan ta sake d'aga kai ta dubi ahmadi dake tsaye gabanta shida
abokanshi biyu yana kallonta cikin gadara
"Anzubar kiyi duk abinda zaki,yarinya ba kowan kowa ba sai shegen isa da izza,don
kina raba mana sadaka saikin gindaya mana sharadi,bamu da hannun diba mu zuba da
kanmu?"
"Ni kuka yiwa haka?" Ta fada tana hadiye wani qullutun bacin rai da baqinciki
"Ke aka yiwan,ki dauki duk matakin da zaki dauka"
"Xaku ga gatana" ta fada a sanyaye bayan ta duqa tana tsince abinda xai iya
daukuwa a wajen,ta fadi maganarne kawai ba don tana da gatan ko me tsaya mata ba,ta
fada ne kawai saboda bata da abun cewar
"Waye gantanki?" Ya fada bayan sun sheqe da dariya duka su ukun
"Nine gatanta!" Wata kakkausar murya ta ratsa dariyar tasu,cak suka tsaya da
dariyar,basu kadai ba har itama dagowa tayi daga tsintar da take tana laluben ina
mai maganar yake da idanunta,matashin saurayi ne wanda duka duka a qalla bazai
haura shekara ashirin da biyar ba,wankan tarwada ne dogo wanda da alama yana yin
qiba zata boye tsahonsa,yana da kyan fuska mai qayatarwa irin kyan da kama
kallonshi kasan cikin yaren hausa fulani yake,kuma tabbas sahun farko da
kyawawansu,ma'abocin kwarjini da kallom farko kawai zaka yi masa kwarjininsa ya
tabaka,fuskarshi a tsuke take babu alamun annuri a tare dashi yake takowa gabansu
ahmadi,kwarjininsa ya sanyasu tsayawa cak,fargaba ta kamasu,saida yayi gab da
ahmadi kamar zai fada jikinsa don har yana dan take masa qafa yace
"Me tayi muku?" Cikin tsoro tsoro da son nuna jarumta yace
"Raina mana hankali take,kullum ta kawo abincin sadaka sai ta rainama mutane wayo"
a hankali ya waiwaya ya dubi gefanshi inda take tsaye,karon farko idanunsu suka
sarqe dana juna,wani irin nauyi taji da batabtaba jinsa ba sanadiyyar kallon idanun
wani a duniya,kamar yadda shima yaji wani yanayi da baisan na meye ba ya saukar
masa harsai daya lumshe idonsa ya kuma bude cikin sakan biyu,hakan ya sake qara
kwarjininsa da kashe jikin shahida
"A'ah,wallahi ahmadi baku da mutunci" muryar wani dattijo dake xama a wajen lokaci
zuwa lokaci ta katsesu,duk suka maida hankalinsu kanshi sanda ya gama tattare
buzunsa da yake zama yana dinkin takalma,ya qaraso wajen yana nuna su ahmadi da
yatsa
"Yarinyar nan tunda ta soma zuwa wajen nan kuka kafa mata qahon xuqa,da kuka
fuskanci a kintse take shine kuka tsiri takurata,kowa ya shaidi yarinyar nan tunda
take zuwa wajen nan bata da abokin fada,hasalima taimakonmu take,bamu da abin ce
mata sai godiya,kullum daga kwanonta muke ci mu qoshi,bata taba bude baki ta kula
wani ba bare rashin kunya ta biyo baya,dama yau tun dazu na kula da take takenku
shi yasa naqi tafiya gida da wuri har sai ta tashi,ashe kuwa tsiya kuka shirya" a
hankali ya dauke kyawawan idanunsa daga kan dattijon ya maidasu kansu ahmadi da
duka gama tsurewa saboda bayanin da baba isuhu ya kwararo,sosai ya kafesu da ido
wanda har sai da sukaji kallon har cikin lakarsu
"Kubar nan,daga rana irinta yau kada na sake ganinku a nan arean,koda kuna da
abunyi har sai ta gama raba abincinta ta tafi"
"Barema basu da abinyi sai zaman kashe wando" baba isuhu ya dora sharhinsa,da
hanzari suka juya suka soma tafiya,saida suka bada 'yar tazara a tsakaninsu sannan
suka fara gunguni
"Ba wani shege Allah,ke kuma zamu gamu,mu dake ne wallahi......ba wani waye waye"
da kallo ya bisu hannayensa xube a aljuhun wandonshi,idan ka tsirawa fuskarshi ido
sosai qaramin murmushi yake can qasan ranshi,saboda yadda suka nuna raki muraran da
basu tsaya sunyi zage zagen daura dashi ba,ya tabbata da sai sun gane kurensu.

"Allah ya saka maka da alkhairi kaji yaro....kubura maza hada kayanki ki wuce
gida" baba isuhu ya fada yana juyawa wajensa shima yana ci gaba da hada nashi
kayan.

Cikin wani irin nauyi da taji jikinta yayi mata ta duqa tana ci gaba da
tsince abinda zata iya,saiya duqa shima a hankali yana tayata laluben farantai da
cokulanta da suka nutse cikin qasa.

Kusan ma ya fita lalubowa da yawa,hannunshi yayi futu futu da qasa fiye da


nata,baice komai ba ya taka wajen wata roba tata ya zuba cokulan ya ciro d'an
tsumma daga aljihunsa dayafi kama da handkherchief ya goge hannunshi sannan ya
dauki botikin daya rage a wajen ya saka robar a ciki ya rufe ya dauki botikin yayi
gaba,bata gane me yake nufi ba amma saita gaza tambayarsa saboda kwarjinin da yayi
mata,binsa tqci gaba dayi wanda suna kaiwa qarshen titin yadan ja ya tsaya,saita
wuceshi tayi gaba,takunshi ta dinga ji alamun yana biye da ita ne,saidai idan ba
kaga sanda suka taho taren ba ba zaka ce tare suke ba.
Suna karyowa layinsu taji gabanta ya fadi sanda ta kalli gidansu
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta furta cikin zuciyarta,saboda tuna kalaman
da ummanta ta dinga fada kam mahaifinsu kafin fitarta da abincin sadaka,fatanta
d'aya,Allah yasa zuciyar umman ta sanyaya kafin dawowar mahaifinsu,matuqar bata
sanyaya din ba Allah ne kawai yasan iyakacin abinda zai faru yau a gidan nasu.

Wannan tunanin da kuma tunanin wanda ke biye da ita baquwar fuska ne a


unguwar yasa saura gida biyu ta qarasa qofar gidan nasu taja tunga ta tsaya ba tare
data juya ba,tana jin sanda ya qaraso gefanta ya aje mata botikin
"Duk sanda zaki taho ki dinga samun d'an rakiya namiji babba yana rakoki ya dawo
dake" ya furta cikin wata kwantacciyar murya data tafi da tunaninta cikin lokaci
guda,ta lumshe ido tana jin zuciyarta na qara yawan bugunta,bata motsa ba har sai
data tabbatar ya bace daga layin gana daya sannan ta sanya hannu ta dauki botikin
nata,sai kuma taji haushin kanta ya kamata,ko banza ya cancanci ta bude baki tayi
masa godiya saboda taimakon da yayi mata ba tare daya santa ko yasan daga ina ta
fito ba,yanzun haka babu lallai ta sake ganinsa bare tayi masa godiya,da wannan
tunanin ta qarasa qofar gidansu,sai kuma fargabarta ta dawo sabuwa sanda ta soma
jiyo tashin murya daga cikin gidan nasu,dai dai sanda qanwarta mubina ta fito
hannunta dauke da 'yar tsana da kayan wasa na qasa wanda suka sha fentin pink da
green,har zata wuce abinta da gudu shahida ta cafko rigarta,saita tsaya tana duban
shahidan
"Baba ya dawo?" Ta tambayeta tana fatan tace mata a'a,amma saita amsa mata da
"Eh ya dawo,yana qofar dakinsa ma suna fada da umma" ta bata amsa tana zame rigarta
ta sake sheqawa da gudu ta shige cikin yara 'yan uwanta ko a jikinta.

Jingina bayanta tayi a soron gidan nasu tana jin munanan lafuzan dake
fitowa daga bakin mahaifinta da mahaifiyarta suna jifan junansu dashi,wani qataton
tashin hankali da take tsintar kanta a ciki duk sanda ta riskesu a wannan halin ya
rufto mata,saita sulale ta duqa a soron tanajin ruwan bala'in dake tashi cikin
gidan,wanda ta tabbatar zuwa yanzu dukka maqota kowa ya kasa kunne ya diban
rahoto,ta rasa wannan wacce irin masifa ce?,ta rasa meke haifar da irin wannan
gagarumin yaqi kulli yaumin tsakamin mahaifanta,basa kwana uku cur cikin jituwa da
juna,basa sati cikin salama da walwala,tunda ta taso tayi hankali haka ta rsiki
rayuwarsu,babu ragayya ko kad'an ga junansu,ba wanda ke ganin wani da gashi a
tsakaninsu.

A qalla sun kusa awa guda suna wannan dauki ba dadin a tsakaninsu,wanda har
zuwa sannan hawaye baibar zuba a idanun shahida ba,tilas ta miqe da niyyar shiga
ciki ko Allah zaisa tayi nasarar dakatar dasu,duk da tasan cewa da wuya wai gurguwa
da auren nesa,don idan irin hakan ta faru dukkansu idanunsu rufewa yake basa ji
basa gani.

Ilai kuwa yana zaune bakin rijiya yayin da da umman tata ke cikin
kitchen,har ta qaraci sallamarta babu wanda ya jita a cikinsu,hakan ya sanya ta
dirr botikin ta durfafi dakinta ta bude ta shige sannannta rufe qofar ruf waiko
zata daina jin tashin munanan furucinsu,saidai bata sauya zani ba,haka tq zame ta
zquna gefan katifarta ta hade gwiwarta ta qanqame tana ci gaba da kukanta.

Basu saurara ba har sai da khadija qanwar shahida ta biyu ta dawo daga gidan
kitson da umman ta turata da yunwa,tace umma yunwa amma bata bi ta kanta ba,hakam
yasa ta watsar da takalmanta ta zube dirshan wajen tahau ihun kuka,katsam sai
farouq mai binta ya farka daga baccin da yake shima ya hau tsala nashi kukan jin
ba'a daukeshi ba akan kari,tilas baban nasu ya suri takalminsa ya fice fuu badon
sun gama ba,ita kuma tahau hidimar yaran tana yi tana mita da alamun itama bata
huce ba.

"Au,ita kuma wannan yaushe ta shigo tazo ta yasarwa da mutane botiki kan
hanya salon wani yaci karo dashi ya fadi,inama sauran botikan?" Jin hakan ya sanya
shahida komawa saman katifa ta kwanta luf tamkar mai bacci tana sauke ajiyar
zuciya,hakan ya sanya koda khadija da umman ta aikota tazo ta dubo shahidan tazo
saita koma tace mata umma bacci take
"Bacci?,bacci kuma da wannan yammacin?,k'nnnnn,to Allah yasa ba zazzabinne kuma ya
dawo ba" ta fada tana ci gaba da baiwa faruqu nono.

Takunta ne kawai ke kai kawo a idanunsa sanda yake komawa daga inda ya
rakota,idanunsa ya dinga lumshewa hakanan yanayinta da yanayin tafiyarta yaji ya
burgeshi,sanyinta,yanayin maganarta,da haka har ya qarasa wajen da suka baro
dazun,yanzun babu kowa,har malam isuhu ma ya wuce,kai tsaye ya wuce shagon balarabe
mai saida kayan provision,wanda dama tun asali wajensa yazo.

Hannu ya bawa bala sukayi musabaha,sannan ya zauna kan bencin dake aje daga
cikin shagon saboda custumers daya tarar yana sallama
"Ai na hangoka kaida wadan can yaran marasa kunya,yarinyar da babu sawa ba
fitarwa,ina Allah Allah naje na musu magana naga kaje,ai yarinyar kirkir ce,ba
qaramin taimakon masu sana'a a nan wajen take ba,kowa na yabonta"balarabe mai kanti
yaci gaba da baiwa anwar labarin zamanta a wajen duk da ba tambayarsa yayi
ba,hakanan shima ya samu kansa da saurarensa,duk da cewa bai tofa komai ba cikin
zancan,har sai da balarabe ya gama b'ab'atunsa yayi shuru
"Kana nufin kullum sai tazo nan kenan?" Anwar ya tambaya yana miqawa balarabe naira
dari biyu,yasa hannu yana amsa
"Qwarai kuwa,kullum tana zuwa daga qarfe uku na rana zuwa hudu,hudu tanayi ta gana
rabarwa ta hada kayanta sai tayi gida" baice uffan ba saiya maida akalar tunaninsa
kan me xai saya da d'ari biyun wanda zai riqeshi zuwa sanda zai sake samun wani
kudin
"Me dame za'a baka malam anwaru" d'an tsaki yaja kad'an na alamun dawowa daga
tunani yana murza goshinsa
"Bani kwaki da suger"
"Kuma dai?" Kafadarsa ya dage yadan mari cinyarsa da tafin hannunsa
"To yq za'ayi,rayuwar kenan ai,wataran sai labari in sha Allah"
"Baka yarda ne anwaru....ni na yarda da amincinka,na yarda ka zabi abinda kakeso
cikin shagon na baka bashi kaje idan ka samu ka kawomin amma ka qiya" balarabe ya
fada sanda yake auna masa kwakin a baqar leda,dan miskilin murmushi anwar ya saki
"Idan ka bani naje na samo na kawo maka naji dadi gobe sake karba zanyi,idan kuma
yauna samu abun biyanka gobe fa ina dashi?"
"Ni a wajena ba wata matsala" kai ya kad'a
"A'ah,Allah ne kad'ai baya gajiyawa,amma yau da gobe dole dan adam ya gajiya" kai
malam balarabe yake kadawa,ya jima rabon da yaga matashi mai kishin kai kamar anwar
din,matashin daya dogara da kanshi bai rabu da kowa ba,ya yarda shi din ba kowa
bane,ya kuma yarda da talaucinsa ya kame kansa,yana gama auna masan ya miqa masa ya
karba yayi masa sallama ya wuce.

Muqulli ya ciro cikin aljihunsa ya saka ya bude qofar gidan,ya tura ya


shiga,babu kowa cikin gidan dama bai tsammaci ganin kowa din ba tunda yasan shi
d'aya yake rayuwa a cikin gidan,saidai ga mamakinsa gaba daya dakinsa daya fita ya
barshi a akillace an bibbincike masa,ya saba ganin hakan,yasan kuma bazai wuce
samarin unguwa bane da suka kafa masa qahon zuqa haka kawai ba,yasan baibar wani
abu mai amfani da za'a dauka ba cikin kayan,bama cikin kayan ba cikin gidanma gaba
daya,aje ledar garinsa yayi ya duba agogon dake maqale a bango,saura minti ashirin
asha ruwa,yasan zai isheshi ya gyara wajen,mutum ne da bayason qazanta ko kadan,a
nutse ya gyara komai ya maida muhallinsa,sannan ya wuce kitchen ya bude robar da
yake aje plate da kofi ya dauko ya jiqa garin sannan ya sake fita ya siyo pure
water guda d'aya da naira goman data rage masa,yana shigowa soro aka sha ruwa,a nan
ya balle ya shanye,ya qarasa bakin fanfo ya daura alwala ya wuce masallaci.

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
[6/30, 10:47 AM] +234 814 691 0795: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON
GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ku danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

0⃣ 5⃣
*AA*
0⃣5⃣

Qarfe sha biyu na rana ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta,siririn
tsaki taha qasa qasa,tun daxun ake maimaita magana d'aya taqi ta qare,da d'ai da
d'ai d'ai take qarewa malaman dake zaune a office din shugaban makarantar ana
tattauna taron da gobe ne za'a gabatar a kuma rufe makarantar don tafiya hutun
azumi,don tsarin makarantar ne basa karatu cikin azumi,suna rufe makaranta ne azumi
saura sati daya ,su dawo karatu bayan sallah da sati biyu,caraf idanunsu suka
hadu,saita janye tata qwayar idanun taja tsakin a sanda yake jifanta da
murmushi,malam musbahu kenan,mutum daya tak daya takura rayuwarta cikin makarantar
fiye da kowacce halitta,itakam shi da nuraddeen batasan wanda yafi wani naci
ba,harma gwara nuran yakan d'aga mata qafa lokaci zuwa lokaci,tun dazun take jinta
not comportable ashe shike kallonta.
Sake duban agogon nata tayi sannan ta miqe lokaci guda,ta kuma nemi izinin
tafiya kan tana da wani uzuri,babu musu shugabannin sashen secondry dana primary
suka bata izini
"Bamuso tafiyarki ba ayanzu miss shahida,saboda yanayin gudunmawar da kike badawa
ta bambanta data kowa" malam musbahu ya fada yana dubanta qasa qasa,bata amsashi ba
har sai data kammala hada takardunta sannan tace
"Ba wanda nafi a nan,kuma duk wata gudunmawa data dace na riga dana bada ita" a
nutse ta juya ta fice bayan tana yunqurin ciro wayarta daga jaka.

Sai data kira anty zubaida ta shaida mata ta wuce gidan anty amina sannan ta
tsaida abun hawa,don idan azumi ya kama bata fita ko ina sai an kammala,in bata
jewa anty aminan ba batasan lokacin zuwanta ba,hakan yasa ta daure zuciyarta ta
yanke shawarar gwara taje din kawai.

Tafiyar minti arba'in kacal daga makarantar zuwa gidan anty aminan,da
sallama ta shiga gidan,saidai hayaniyar yara bai bari anji ba saidata sake wata
sallamar,hamida ita ta soma ji,ta nufi shahida da gudu tana mata oyoyo,kafin kace
meye wannan sun lullubeta,qarin tashin hayaniyarsu shiya ankatar da anty amina dake
kitchen tana shirya musu abincin rana saboda lokacin tafiya islamiyya ya gabato,ta
leqo cikin mamaki tana duban shahidan,bata taba tsammatar ganinta ba,yadda ta saki
baki ya bawa shahida dariya,saita murmusa sanda take ciro alewa daga jakarta tana
barewa qaramin yaron anty aminan faisal
"Ku qarasa ciki ina zuwa" ta fada tana komawa kitchen din,da haka suka qarasa falon
anty aminan suka zube kowa na murnan ganinta,sun kasa qarasa shiryawa ma zuwa
islamiyyar.

Duk sai data raba musu abinda ta ruqo sannan sukaci gaba da hirar kowa tana
biye dashi,ta jima rabonta da walwala irin haka,tunda can maison yara ce dama
ita,hakan yasa taji wani sukuni na musamman na shiga cikin ranta.

"Yayaa,ina uncle kuwa?,yayimin alqawarin sweet har yau bai dawo ya kawomin ba"
sadiq yaron anty amina ya fada yana saka rigar islamiyyarshi,dai dai sanda anty
aminan ta shigo da plates din abinci,cak shahida taji komai ya tsaya mata,ta kasa
hadiye biscuit din data farke cikin wanda ta kawo musu ta d'an soma ci saboda
hamida data takura mata cewa da dad'i,yadda ta tsaya cak haka anty aminan ta tsaya
tana dubanta,don tasan saddiq ya b'arota,yayin da sauran yaran duk suka zuba mata
idanu suna sauraren amsarta,don gaba dayansu suna da buqatar sanin dalilin daina
ganinsa dare d'aya lokaci daya kuma gaba d'aya
"Ya mutu" furucin ya fito daga bakinta kamar mai ciwon baki,idanunta kan saddiq
wanda ya kasa qarasa saka rigar tashi jin abinda shahidan ta fada,harga Allah tana
daukarshi tamkar matacce ne a ruhi da zuciyarta,duk da dama ya dade da mutuwa a
cikin tata zuciyar
"Ya mutu yayaa?"saddiqa ta fada tana zaro idanu,alhini da mamaki ya bayyana qarara
kan fuskar yaran gaba daya
"Kai banason dogon surutu,ke hamida dauki abincinku ki kai muku dakinku kuci a can
ku shirya maza ku fice ku bani waje" cewar anty amina tana musu wuta wuta,don tasan
tabbas ba qaramin furuci bane wannan a wajensu,duba da yanayin sabo dake tsakaninsu
dashi,c gaba fa maganar kuma dai dai yake da hargitsa lissafin shahida da dukkan
walwalar data samu cikin gidan,hakanan yaran suka dinga fita daga dakin jikinsu a
matuqar sanyaye.

Sai da suka gama fita gaba daya sannan anty amina ta qarasa kusa da shahida
ta aje kwanon abincin idanunta na kan shahida data sauke kanta qasa
"Har sai yaushe shahida zakici gaba da rayuwarki kamar kowa?,sai yaushe zaki maida
abinda ya faru kaman bai faru ba?,yaushe zaki rufe wannan tarihin daga babin
rayuwarki?,me yasa wannan lamarin yaqi fita daga ranki kamar sauran abubuwa?" Kasa
bata amsa tayi sai tafukan hannayenta data saka guda biyun ta rufe fuskarta
dasu,ita kanta tana son ta koma normal,tana son ta zama kamar kowa,tanason ta manta
da komai amma ta gagara yin hakan?,me yasa abun yafi tsaya mata fiye da komai?.

A jigace ta dawo gida bawai don tayi wata gajiya ta azo a gani ba,illa dai
zuciyarta data dahu lugub ta kuma saare tun sanda yaran suka jefa mata tambaya a
kanshi,batayi dogon zama a falon ba ta yiwa anty zubaida sallama kan cewa gobe da
wuri zata tashi tana son isa makaranta da wuri don gobene ranar hutunsu.

*1:26 pm*

Tsaye yake cikin wani makeken fili wanda ya qawatu da fareren furanni tas da
jefi jefin koraye,waje ne daya ni'imtu,ya kuma qawatu da wata irin iska mai dadi da
taush take kai kawo iya fadi da girman filin,cakude iskar take da qamshi mai sanyi
wanda ke ratsa zuciya,fararen kayane qal a jikinsa,yana tsaye gaban wata qaramar
qorama mai garai garai,kana iya hangen kifayen dake linqaya da kai kawo daga can
qasanta.

Ingarman bayanshi take iya hangowa,ta zuba mishi idanu tana jin wani bugu da
zuciyarta keyi,tana jin tsoro da zumudin tunkararsa lokaci guda na mamayarta,a
hankali ta dinga takawa gareshi,iska na diban gashinta tana watsashi gaban fuskarta
hagu da damanta,lokaci lokaci tana sanya hannu tana d'aukewa.

Dab da bayanshi ta tsaya taci gaba da kallonshi gabanta na faduwa,tanajin


kamar zata kira sunanshi sai bakinta ya kasa furta komai,ta dan jima a haka sannan
ta miqa hannu da niyyar kama kafadarsa sai ya waiwayo,fuskarshi cike fal da annuri
kamar yadda ta saba ganinsa,yayi kyau ya canza kamar bashi ba,cikin sakan kad'an
dukkan wani annurin fuskarsa ya gushe,ya hade girar sama da qasa,bacin rai ya
bayyana qarara a fuskarsa
"Me kike yi a nan?!" Ya fada cikin tsawa da fusata
"Ban sani ba!" Itama ta maida masa cikin tsawa da fushi,sai kuma ta juya cikin
gaggawa ta bashi baya ba tare data bar wajen ba,ta d'an jima ahaka sannan ta
waiwaya,saidai wayam baya wajen,babu shi babu alamarsa,wani tashin hankali da
batasan na meye ba ya rufto mata,musamman sanda taga duhu ya soma mamaye
wajen,kiran sunanshi ta soma yi a jere babu qaqqautawa,saidai babu alamun yana
jinta bare ta saka ran zai amsa.

A firgice ta miqe daga kwanciyar da take bakinta d'auke da sunanshi kamar


yadda take kiranshi cikin mafarkin,a hankali hankalinta ya dawo jikinta ta fuskanci
mafarki ne,saita sauya sunan nashi da ambaton sunan Allah,yayin da hawaye ya soma
sauka daga idanunta masu zafin gaske,wanne wacce irin jarrabawa ce?,har a mafarkin
ma bazai haqura ya barta ba,tayi shiri hakanan ta tattara dukkan qarfinta tana yaqi
dashi haiqan,saidai ta fuskanci kaman fad'an gwaggo a kofa take.

Sai data gama kukanta son ranta sannan ta sauka a hankali don karta tashi
huda da yau take tayata kwana,ta shiga bandaki ta daura alwala,saidai yau ta kasa
sallar kamar tadda ta saba,saboda wata irin kasala da mutuwar jiki data sakar
mata,abinda ya gudana a mafarkin ya soma dawo mata tar a kwanyarta,duhun da taga ya
soma mamayarta shine abu na farko daya daga mata hankali,me hakan yake nufi
kenan?,saita tuna ranar da suka ga fuskokin juna na qarshe,komai ya soma dawo mata
d'aya bayan d'aya cikin rayuwarta kamar wadda aka kunnawa magijin film.

*_ZAN RAYU DAKE_*

Ranta a matuqar bace take kallon botikanta guda biyu dake shaqe da shinkafa
da waken sadaka wanda tuni suka hadu da qasa suka saje,botikam kuma sukayi fata
fata dasu,sannan ta sake d'aga kai ta dubi ahmadi dake tsaye gabanta shida
abokanshi biyu yana kallonta cikin gadara
"Anzubar kiyi duk abinda zaki,yarinya ba kowan kowa ba sai shegen isa da izza,don
kina raba mana sadaka saikin gindaya mana sharadi,bamu da hannun diba mu zuba da
kanmu?"
"Ni kuka yiwa haka?" Ta fada tana hadiye wani qullutun bacin rai da baqinciki
"Ke aka yiwan,ki dauki duk matakin da zaki dauka"
"Xaku ga gatana" ta fada a sanyaye bayan ta duqa tana tsince abinda xai iya
daukuwa a wajen,ta fadi maganarne kawai ba don tana da gatan ko me tsaya mata ba,ta
fada ne kawai saboda bata da abun cewar
"Waye gantanki?" Ya fada bayan sun sheqe da dariya duka su ukun
"Nine gatanta!" Wata kakkausar murya ta ratsa dariyar tasu,cak suka tsaya da
dariyar,basu kadai ba har itama dagowa tayi daga tsintar da take tana laluben ina
mai maganar yake da idanunta,matashin saurayi ne wanda duka duka a qalla bazai
haura shekara ashirin da biyar ba,wankan tarwada ne dogo wanda da alama yana yin
qiba zata boye tsahonsa,yana da kyan fuska mai qayatarwa irin kyan da kama
kallonshi kasan cikin yaren hausa fulani yake,kuma tabbas sahun farko da
kyawawansu,ma'abocin kwarjini da kallom farko kawai zaka yi masa kwarjininsa ya
tabaka,fuskarshi a tsuke take babu alamun annuri a tare dashi yake takowa gabansu
ahmadi,kwarjininsa ya sanyasu tsayawa cak,fargaba ta kamasu,saida yayi gab da
ahmadi kamar zai fada jikinsa don har yana dan take masa qafa yace
"Me tayi muku?" Cikin tsoro tsoro da son nuna jarumta yace
"Raina mana hankali take,kullum ta kawo abincin sadaka sai ta rainama mutane wayo"
a hankali ya waiwaya ya dubi gefanshi inda take tsaye,karon farko idanunsu suka
sarqe dana juna,wani irin nauyi taji da batabtaba jinsa ba sanadiyyar kallon idanun
wani a duniya,kamar yadda shima yaji wani yanayi da baisan na meye ba ya saukar
masa harsai daya lumshe idonsa ya kuma bude cikin sakan biyu,hakan ya sake qara
kwarjininsa da kashe jikin shahida
"A'ah,wallahi ahmadi baku da mutunci" muryar wani dattijo dake xama a wajen lokaci
zuwa lokaci ta katsesu,duk suka maida hankalinsu kanshi sanda ya gama tattare
buzunsa da yake zama yana dinkin takalma,ya qaraso wajen yana nuna su ahmadi da
yatsa
"Yarinyar nan tunda ta soma zuwa wajen nan kuka kafa mata qahon xuqa,da kuka
fuskanci a kintse take shine kuka tsiri takurata,kowa ya shaidi yarinyar nan tunda
take zuwa wajen nan bata da abokin fada,hasalima taimakonmu take,bamu da abin ce
mata sai godiya,kullum daga kwanonta muke ci mu qoshi,bata taba bude baki ta kula
wani ba bare rashin kunya ta biyo baya,dama yau tun dazu na kula da take takenku
shi yasa naqi tafiya gida da wuri har sai ta tashi,ashe kuwa tsiya kuka shirya" a
hankali ya dauke kyawawan idanunsa daga kan dattijon ya maidasu kansu ahmadi da
duka gama tsurewa saboda bayanin da baba isuhu ya kwararo,sosai ya kafesu da ido
wanda har sai da sukaji kallon har cikin lakarsu
"Kubar nan,daga rana irinta yau kada na sake ganinku a nan arean,koda kuna da
abunyi har sai ta gama raba abincinta ta tafi"
"Barema basu da abinyi sai zaman kashe wando" baba isuhu ya dora sharhinsa,da
hanzari suka juya suka soma tafiya,saida suka bada 'yar tazara a tsakaninsu sannan
suka fara gunguni
"Ba wani shege Allah,ke kuma zamu gamu,mu dake ne wallahi......ba wani waye waye"
da kallo ya bisu hannayensa xube a aljuhun wandonshi,idan ka tsirawa fuskarshi ido
sosai qaramin murmushi yake can qasan ranshi,saboda yadda suka nuna raki muraran da
basu tsaya sunyi zage zagen daura dashi ba,ya tabbata da sai sun gane kurensu.

"Allah ya saka maka da alkhairi kaji yaro....kubura maza hada kayanki ki wuce
gida" baba isuhu ya fada yana juyawa wajensa shima yana ci gaba da hada nashi
kayan.

Cikin wani irin nauyi da taji jikinta yayi mata ta duqa tana ci gaba da
tsince abinda zata iya,saiya duqa shima a hankali yana tayata laluben farantai da
cokulanta da suka nutse cikin qasa.

Kusan ma ya fita lalubowa da yawa,hannunshi yayi futu futu da qasa fiye da


nata,baice komai ba ya taka wajen wata roba tata ya zuba cokulan ya ciro d'an
tsumma daga aljihunsa dayafi kama da handkherchief ya goge hannunshi sannan ya
dauki botikin daya rage a wajen ya saka robar a ciki ya rufe ya dauki botikin yayi
gaba,bata gane me yake nufi ba amma saita gaza tambayarsa saboda kwarjinin da yayi
mata,binsa tqci gaba dayi wanda suna kaiwa qarshen titin yadan ja ya tsaya,saita
wuceshi tayi gaba,takunshi ta dinga ji alamun yana biye da ita ne,saidai idan ba
kaga sanda suka taho taren ba ba zaka ce tare suke ba.

Suna karyowa layinsu taji gabanta ya fadi sanda ta kalli gidansu


"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta furta cikin zuciyarta,saboda tuna kalaman
da ummanta ta dinga fada kam mahaifinsu kafin fitarta da abincin sadaka,fatanta
d'aya,Allah yasa zuciyar umman ta sanyaya kafin dawowar mahaifinsu,matuqar bata
sanyaya din ba Allah ne kawai yasan iyakacin abinda zai faru yau a gidan nasu.

Wannan tunanin da kuma tunanin wanda ke biye da ita baquwar fuska ne a


unguwar yasa saura gida biyu ta qarasa qofar gidan nasu taja tunga ta tsaya ba tare
data juya ba,tana jin sanda ya qaraso gefanta ya aje mata botikin
"Duk sanda zaki taho ki dinga samun d'an rakiya namiji babba yana rakoki ya dawo
dake" ya furta cikin wata kwantacciyar murya data tafi da tunaninta cikin lokaci
guda,ta lumshe ido tana jin zuciyarta na qara yawan bugunta,bata motsa ba har sai
data tabbatar ya bace daga layin gana daya sannan ta sanya hannu ta dauki botikin
nata,sai kuma taji haushin kanta ya kamata,ko banza ya cancanci ta bude baki tayi
masa godiya saboda taimakon da yayi mata ba tare daya santa ko yasan daga ina ta
fito ba,yanzun haka babu lallai ta sake ganinsa bare tayi masa godiya,da wannan
tunanin ta qarasa qofar gidansu,sai kuma fargabarta ta dawo sabuwa sanda ta soma
jiyo tashin murya daga cikin gidan nasu,dai dai sanda qanwarta mubina ta fito
hannunta dauke da 'yar tsana da kayan wasa na qasa wanda suka sha fentin pink da
green,har zata wuce abinta da gudu shahida ta cafko rigarta,saita tsaya tana duban
shahidan
"Baba ya dawo?" Ta tambayeta tana fatan tace mata a'a,amma saita amsa mata da
"Eh ya dawo,yana qofar dakinsa ma suna fada da umma" ta bata amsa tana zame rigarta
ta sake sheqawa da gudu ta shige cikin yara 'yan uwanta ko a jikinta.

Jingina bayanta tayi a soron gidan nasu tana jin munanan lafuzan dake
fitowa daga bakin mahaifinta da mahaifiyarta suna jifan junansu dashi,wani qataton
tashin hankali da take tsintar kanta a ciki duk sanda ta riskesu a wannan halin ya
rufto mata,saita sulale ta duqa a soron tanajin ruwan bala'in dake tashi cikin
gidan,wanda ta tabbatar zuwa yanzu dukka maqota kowa ya kasa kunne ya diban
rahoto,ta rasa wannan wacce irin masifa ce?,ta rasa meke haifar da irin wannan
gagarumin yaqi kulli yaumin tsakamin mahaifanta,basa kwana uku cur cikin jituwa da
juna,basa sati cikin salama da walwala,tunda ta taso tayi hankali haka ta rsiki
rayuwarsu,babu ragayya ko kad'an ga junansu,ba wanda ke ganin wani da gashi a
tsakaninsu.

A qalla sun kusa awa guda suna wannan dauki ba dadin a tsakaninsu,wanda har
zuwa sannan hawaye baibar zuba a idanun shahida ba,tilas ta miqe da niyyar shiga
ciki ko Allah zaisa tayi nasarar dakatar dasu,duk da tasan cewa da wuya wai gurguwa
da auren nesa,don idan irin hakan ta faru dukkansu idanunsu rufewa yake basa ji
basa gani.

Ilai kuwa yana zaune bakin rijiya yayin da da umman tata ke cikin
kitchen,har ta qaraci sallamarta babu wanda ya jita a cikinsu,hakan ya sanya ta
dirr botikin ta durfafi dakinta ta bude ta shige sannannta rufe qofar ruf waiko
zata daina jin tashin munanan furucinsu,saidai bata sauya zani ba,haka tq zame ta
zquna gefan katifarta ta hade gwiwarta ta qanqame tana ci gaba da kukanta.

Basu saurara ba har sai da khadija qanwar shahida ta biyu ta dawo daga gidan
kitson da umman ta turata da yunwa,tace umma yunwa amma bata bi ta kanta ba,hakam
yasa ta watsar da takalmanta ta zube dirshan wajen tahau ihun kuka,katsam sai
farouq mai binta ya farka daga baccin da yake shima ya hau tsala nashi kukan jin
ba'a daukeshi ba akan kari,tilas baban nasu ya suri takalminsa ya fice fuu badon
sun gama ba,ita kuma tahau hidimar yaran tana yi tana mita da alamun itama bata
huce ba.

"Au,ita kuma wannan yaushe ta shigo tazo ta yasarwa da mutane botiki kan
hanya salon wani yaci karo dashi ya fadi,inama sauran botikan?" Jin hakan ya sanya
shahida komawa saman katifa ta kwanta luf tamkar mai bacci tana sauke ajiyar
zuciya,hakan ya sanya koda khadija da umman ta aikota tazo ta dubo shahidan tazo
saita koma tace mata umma bacci take
"Bacci?,bacci kuma da wannan yammacin?,k'nnnnn,to Allah yasa ba zazzabinne kuma ya
dawo ba" ta fada tana ci gaba da baiwa faruqu nono.

Takunta ne kawai ke kai kawo a idanunsa sanda yake komawa daga inda ya
rakota,idanunsa ya dinga lumshewa hakanan yanayinta da yanayin tafiyarta yaji ya
burgeshi,sanyinta,yanayin maganarta,da haka har ya qarasa wajen da suka baro
dazun,yanzun babu kowa,har malam isuhu ma ya wuce,kai tsaye ya wuce shagon balarabe
mai saida kayan provision,wanda dama tun asali wajensa yazo.

Hannu ya bawa bala sukayi musabaha,sannan ya zauna kan bencin dake aje daga
cikin shagon saboda custumers daya tarar yana sallama
"Ai na hangoka kaida wadan can yaran marasa kunya,yarinyar da babu sawa ba
fitarwa,ina Allah Allah naje na musu magana naga kaje,ai yarinyar kirkir ce,ba
qaramin taimakon masu sana'a a nan wajen take ba,kowa na yabonta"balarabe mai kanti
yaci gaba da baiwa anwar labarin zamanta a wajen duk da ba tambayarsa yayi
ba,hakanan shima ya samu kansa da saurarensa,duk da cewa bai tofa komai ba cikin
zancan,har sai da balarabe ya gama b'ab'atunsa yayi shuru
"Kana nufin kullum sai tazo nan kenan?" Anwar ya tambaya yana miqawa balarabe naira
dari biyu,yasa hannu yana amsa
"Qwarai kuwa,kullum tana zuwa daga qarfe uku na rana zuwa hudu,hudu tanayi ta gana
rabarwa ta hada kayanta sai tayi gida" baice uffan ba saiya maida akalar tunaninsa
kan me xai saya da d'ari biyun wanda zai riqeshi zuwa sanda zai sake samun wani
kudin
"Me dame za'a baka malam anwaru" d'an tsaki yaja kad'an na alamun dawowa daga
tunani yana murza goshinsa
"Bani kwaki da suger"
"Kuma dai?" Kafadarsa ya dage yadan mari cinyarsa da tafin hannunsa
"To yq za'ayi,rayuwar kenan ai,wataran sai labari in sha Allah"
"Baka yarda ne anwaru....ni na yarda da amincinka,na yarda ka zabi abinda kakeso
cikin shagon na baka bashi kaje idan ka samu ka kawomin amma ka qiya" balarabe ya
fada sanda yake auna masa kwakin a baqar leda,dan miskilin murmushi anwar ya saki
"Idan ka bani naje na samo na kawo maka naji dadi gobe sake karba zanyi,idan kuma
yauna samu abun biyanka gobe fa ina dashi?"
"Ni a wajena ba wata matsala" kai ya kad'a
"A'ah,Allah ne kad'ai baya gajiyawa,amma yau da gobe dole dan adam ya gajiya" kai
malam balarabe yake kadawa,ya jima rabon da yaga matashi mai kishin kai kamar anwar
din,matashin daya dogara da kanshi bai rabu da kowa ba,ya yarda shi din ba kowa
bane,ya kuma yarda da talaucinsa ya kame kansa,yana gama auna masan ya miqa masa ya
karba yayi masa sallama ya wuce.

Muqulli ya ciro cikin aljihunsa ya saka ya bude qofar gidan,ya tura ya


shiga,babu kowa cikin gidan dama bai tsammaci ganin kowa din ba tunda yasan shi
d'aya yake rayuwa a cikin gidan,saidai ga mamakinsa gaba daya dakinsa daya fita ya
barshi a akillace an bibbincike masa,ya saba ganin hakan,yasan kuma bazai wuce
samarin unguwa bane da suka kafa masa qahon zuqa haka kawai ba,yasan baibar wani
abu mai amfani da za'a dauka ba cikin kayan,bama cikin kayan ba cikin gidanma gaba
daya,aje ledar garinsa yayi ya duba agogon dake maqale a bango,saura minti ashirin
asha ruwa,yasan zai isheshi ya gyara wajen,mutum ne da bayason qazanta ko kadan,a
nutse ya gyara komai ya maida muhallinsa,sannan ya wuce kitchen ya bude robar da
yake aje plate da kofi ya dauko ya jiqa garin sannan ya sake fita ya siyo pure
water guda d'aya da naira goman data rage masa,yana shigowa soro aka sha ruwa,a nan
ya balle ya shanye,ya qarasa bakin fanfo ya daura alwala ya wuce masallaci.

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

0️⃣ 6️⃣
*AA*
0️⃣6️⃣

Saida gari ya danyi duhu kadan sannan ya dawo cikin gidan,ya duba garinsa yayi
laushi,ya zuba suger dai dai gwargwado ya zauna gefan 'yar katifarsa ya soma
sha,inda ya kunna redio da wayarsa qarama keypad samfutin tecno yana sauraren
labarai.

Kafin ya kammala an kirayi isha'i,sake miqewa yayi ya fice zuwa


masallaci,don sam baya wasa da sallar cikin jam'i,koda aka idar nan majalisar dake
kusa da gidanshi yadan xauna aka taba hira,bai jima can da yawa yayi sallama
dasu,kasancewar yana da masaniyar gobe yana da lacture ta qarfe tara,kuma dama bai
fiya zama cikinsu ba ba dabi'arsa bace wannan,hakan yasanya wasu kejin haushinsa
tare da yi masa kallon mai girman kai,yakan zauna lokaci zuwa lokaci saboda kauda
wannan zargin daga ransu,bugu da qari ya sani dole kuwa ya fita tun bakwai,don kuwa
da qafarshi yake takawa har zuwa makarantar,zuwanshi mota a abun hawa abune mai
matuqar sa'a,imma wani aikin qarfin ya samu yayi ya samu kudi,ko idan anty usaina
ta d'anyi samuwa ta kirashi ta bashi wani abun,ko Allah ya hadashi da d'aya daga
cikin 'yan makarantarsu ya rage masa hanya.

Allah ya taimakeshi yau cikinsu ba wanda ya shigo masa gida,saboda haka ya


kulle ko ina yayi nafilfilunsa kamar yadda ya saba,ya roqawa iyayensa da 'yan
uwanshi gafara sannan ya kwanta bayan ya sake kunna rediyon yana sauraren shirye
shiryen da sukeyi.

Sannu a hankali tunaninta ya kutso cikin kaiwa da kawowar da qwaqwalwarsa keyi


tun dazu,ya dan saki murmushi yana wassafo kamanninta,yanayinta tsarinta da
tafiyarta,da ganinta zatayi hankali,da ganinta akwai nutsuwa tattare da ita,da
ganinta ba maison hayaniya bace
"Duk taya akayi kasan hakan?" Ya tambayi kansa da kansa,saiya sakarwa kansa
murmushi yana girgixa kai gami da runtse idanunsa,shima baisan ya akayi ya tsinci
kansa da fadawa wannan bigiren ba,saiya juya zuwa daya barin yana son maoda
hankalinsa kan programe din da ake gudanarwa a gidan redio a sannan.

Tun bayan sallar magariba ummantata keta sintirin aiken qannen nata kan ta
fito taci abinci,saidai sam ta qiya,tayi kwanciyarta abinta,ranta ne kawai ke mata
suya,a duk sanda irin wannan balahirar ta faru a gidansu idan da safe ne wuni take
cikin qunci da damuwa,hakanan idan da yammaci ne koda dare kwana take cikin qunci
shima da damuwa,wani lokacin takance inama kurma Allah ya halicceta?,inama
makauniya ce ita ta huta da ganin wannan baqon lamari,wanda ya zama tambarin
gidansu,ya kuma zama abinda jama'ar unguwa ke goranta musu dashi,don babu wanda
baisan irin rayuwar da ake tsakanin uammansu da babansu ba,tayi kuka har sau babu
adadi,tabi hanyoyin gyara bila adadin amma babu alamun ma sauyi bare akai ga gyaran
gaba daya,tayi tunani iri daban daban masu kyau da marasa kyau amma bata samu hanya
mai bullewa ba,tayi yaji tabar gidan batasan adadin sau nawa ba amma sun bita sun
dawo da ita kan alqawarin komai ya wuce zasu gyara amma babu alamun sauyawar
lamuran,ta tambayesu me yasa suke hakan amma su kansu basu san amsa ba,abu d'aya ta
sani shine,dukkaninsu tsakanin ummanta da babanta babu wani mai haquri
acikinsu,ummanta bata da haquri ko kad'an kamar yadda mahaifinta yake,bata raga
masa ko daya,idan ya mata taga bai mata dai dai ba take zata rama,shi kuma yaga ta
rainashi kenan haka zai biye mata suyita yi.

Basu san ciwon da hakan ke mata a qirjinta ba,basu san illar dahakan ke
haifarwa ga tarbiyya yara da tunaninsu da ginuwar hankalinsu,iyayenka a wannan
bigiren na fada da juna kulli yaumin har sauran jama'a su shaida hakan kai me yayi
saura a rayuwarka?.

Saida umman taga da gaske take bazataci abincin ba kamar yadda ta saba a duk
sanda ta samesu suna cecekuceb da suka saba,saita dire faruqu ta nufi dakin nata,ta
yaye labulen tana tsaye daga dokin qofa tace
"Tunda sai abinda kikaga dama zakiyi bismillah,dadin abun cikinki ne ba nawa
ba,yunwa kuwa dai dai take dake matsalarki ce wannan,ki tashi ki gayamin ya akayi
sauran botikaina sabbi suka fashe haka?" Da qyar ta juya daga kwancen da take ta
d'aga kai ta dubeta
"Wasune garin wawaso suka fasa su"
"Botikan duka?" Kai ta gyada mata
"K'nnnn,ai shikenan,Allah ya kyauta" ta fada tana sakin labulen,maida kanta tayi ta
kwantar,inama ace haka takewa mahaifinsu a duk sanda wani abu ya hadosu?,ta
tabbatar da shine tsautsayi irin haka ya faru da yau Allah ne kadai yasan qarshen
fadansu.

Mubina ce ta shigo da kwananon abincin ta dire mata ta juya ta fice,bata dai


kallesu ba tana ci gaba da kwanciyar
"Idan baki tashi kin kama abinci kinci ba na shigo sai nayi mugun saba miki" ta
jiyo muryar umman daga tsakar gida tana gaya mata,hakanan badon son ranta ba ta
sauko ta tanqwashe qafa ta dinga cusa abincin har sai dataji kaman zatayi amai
sannan ta maida murfin ta rufe ta sake kwanciya.

Runtse idanunta tayi tana fatar bacci ya dauketa,sai taga wata fuska data
sanyata saurin sake bude idanunta,dawo mata yayi tar a kwanyarta,bacin ran da take
ciki yasa bata sake tunowa dashi ba sai yanzu,saita gyara kwanciyarta tana kallon
bango,ta dinga tuno fuskarsa da yadda tafiyarsu ta kasance daga bakin masallaci har
zuwa gida,hakanan taji nauyi da bacin ran zuciyarta ya ragu sosai,ta shagala da
tunanin daya d'auketa zuwa bacci mai nauyi.

Qarfe biyu na rana gaba ya tsinci kansa hankalinsa ya tafi bakin masallaci gurin
da ba wajen zuwansa bane idan ba shagin balarabe zashi ba ko wani babban uzurin ya
kamashi na zuwa wajen,sai ya sake tsintar kansa da sake yin wanka bayan ya gama
hutawa duk da kusan dabi'arsa ce a duk sanda ya dawo daga makaranta,amma wannan
karon saiya laluba kayanshi har ya zaro zai saka ya maida ya sauya wasu,abinda bai
taba yi ba,bai taba damuwa da suturar da zai saka,kawai dai yasan dukka kayan
sawarshi a tsaftace suke kullum,hakanan basa rabo da guga,duk da cewa ba wasu masu
shegen kyau da tsada bane,Allah dai yayi masa wata baiwa ta duk kayan daya saka
jikinsa na dauka,hakan yasa matasan anguwar da dama ya tsone musu ido,wanda
yawancinsu dukka sunfishi gata rufin asiri da komai da komai,tsaftarsa tasa baka
gane kaashinsa.

"Ki kulamin da botikai na,karki sake bari su fasamim botiki,kai jamilu idan
ka aje mata ka dawo ka kaimin shara" cewar ummanta wadda take rufe botikin abincin
data gama zubawa almajirin ya qaraso wajen ya dora a kanshi suka fice tanawa umman
sallama.

Har sunje soron gidan hakanan taja ta tsaya,saita juya da hanzari ta koma
ciki
"A'ah,lafiyarki kuwa?" Umman tata da taga wucewarta ciki ta fada
"Lafiya umma ina zuwa" kai tsaye ta dauko dan kwandon kayan kwalliyarta dake saman
akwatin kayanta,ta ciro ruwan madubi mai fadi dake soke a ciki ta kalli fuskarta
"Hoda na miki kyau wallahi shahida,don Allah ki dinga d'an shafawa mana" ta tuna
maganar da qawarta ta gaya mata daxu a makarantar boko,saita samu kanta da ciro
hodar ta bude ta shafa,data sake kallon fuskarta sai taga ta canza din kuwa,sosai
hodar tayi mata kyau ta sake fidda kyau da qyallin fuskarta,murmushi ta saki ta aje
mudubin ta juya ta fice da sauri.

Yana zaune daga shagon balarabe yana kallon duk wani motsinta dake bayyanar
da hankali da nutsuwarta da kuma ainihin ita wace,duk surutu da hirar da balaraben
yake masa baya gane abinda yake fada sam,shi kuma bai fahimta ba bare yaja bakinsa
yayi shuru ya barshi.

Haka ta dinga raba abincin kamar yadda ta saba,saidai tanata dube duben kadan
kadan da batasan meye dalili ba,harta kammala tsaf ta hada kwanukanta waje
daya,haka kawai saitaji ranta ya baci lokacin data gama shirin komawa gida,duqawa
tayi don daukar botikan taga an sako hannu an dauka,da hanzari ta dago don ganin
waye?,ta tsammaci ma su ahmadi ne ma basu gargadin da aka musu jiya ba yau suka
dawo,saidai ga mamakinta saurayin jiya ne,gaba yayi abinsa sai tabi bayansa sukaci
gaba da tafiya ba tare da kowa yace da d'an uwansa wani sbu ba.

Basuyi wani nisa ba ya janye ta koma ita ce a gaba shi yana baya,bata kawo
komai a ranta ba ta tsammaci bazai gane gidan nasu ba shi yasa yayi hakan,kamar
tafiyar jiya har suka je inda ya dakata a jiya ya aje mata botikin,saidai yau din
ta daga ido ta kalleshi,akaci sa'a shima ya kalleta a sannan,wani irin zallar kyau
da kwarjini idanunta suka gani,sai taji wani abu tun daga qwaqwalwarta har tafin
qafarta,mazewa tayi gami da d'auke kai tana jin izzarta ta diya mace na motsawa,a
nashi bangaren ma wani abu mai qarfi yaji yana janshi game da ita tamkar maganadisu
da mayen qarfe,sai bakinsa yayi nauyi,bai furta mata komai ba ya juya ya soma
takawa don barin wajen,daga manyan idanunta tayi tana bin bayanshi da kallo har sai
daya bacewa ganinta,batasan me yasa ba bakuma tasan sanda ta saki murmushi ba ta
daukin botikin nata ta fada gida.

Tsahon kwana uku irin hakan na faruwa tsakaninsu,ba wata magana data taba
shiga tsakaninsu,duk sanda tayi yunqurin yin wata magana saita kasa sabida
kwarjinin da yake mata,tana son tace ya daina rakota saboda ganin yadda idon
sa'idinawan unguwa ya soma dawowa kansu saidai ta kasa furta masa hakan,cikin ranta
takejin nishadi a duk sanda suke wannan tafiyar ta kurame tun daga masallaci zuwa
qofar gidansu,ko sunanshi bata sani ba,sai taga meye nata na tambayar sunansa
ma,aishi ya kamata ya soma tambayarta sunanta,wani sashe na zuciyarta ya
qalubalanceta da a'ah ba haka ake ba,ke yakewa alkhairi,ko godiya baki taba yi masa
ba kan rakokin da yake,ta jinjina kai tana tabbatarwa da kanta rashin
kyautawarta,ta kuma quduri aniyar a gobe zata masa godiya ta kuma tambayi
sunanshi,kai ta girgiza kuma tana sake sakin murmushi,batasan dalilin daya sanya
take yawan tunashi ba,batasan me yasa takejin wani baqon yanayi game dashi ba tun
ranar data soma dora idanunta a kanshi,bata da amsa,tilas ta aje tunaninta a gefe
sanda ta jiyo muryar babanta sun soma rabon halin nasu shi da ummanta,saita miqe a
hankali ta isa bakin windon dakinta,ta yaye dan labulen net din dake maqale jikin
window din tana kallon yadda suke dagawa juna murya kamar zasu yagi juna,batasan
lokacin da wani hawayen baqinciki ya sauko mata ba,baqinciki da b'acin rai ya bata
dukkan wani farinciki data tsinci kanta a ciki,wannan wacce irin rayuwa ce?,ina
zata je ta daina ganin wannan baqincikin da bacin ran?,tabbas da akwai inda zata ta
qauracewa wannan masifar da tuni ta jima da tafiya,tana son mamarta,hakanan tana
son bananta,duk cikinsu babu wanda take goyon baya a cikinsu,batasan me yasa suka
zabi wannan rayuwar ba bayan ga zuria suna tarawa,hakanan kowa yayi musu shaidar
kyakkyawar mu'amala a waje amma me yasa gidan aurensu ya gurbace haka kamar
sansanin yaqi?,haka ta zauna cikin dakin ita d'aya tana rusar kuka harta gaji da
jin sautukansu ta dannan kanta qarqashin filo tana ci gaba da zubda ruwan hawaye.

Kamar kowanne lokaci yauma ta shirya tsaf cikin atamfa riga da zani,sai
hijabi mai hannu da yasha guga,kasancewar ummanta mai tsafta ce,hakan ya sanya
dukka yaranta tun daga kan shahida zuwa faruqu zaka samesu fes dasu,hakanan ma
gidanta da duk abinda ya shafi gidan,sosai higabi mai madauri purpule colour yayi
mata kyau sosai,yau shigar ta musamman ce ita kanta tana jin hakan a jikinta,yau
mai d'aukar matan bai qaraso ba tilas tadan zauna jiran zuwansa,tun tana jin ba
komai harta soma qaguwa,haka kawai taji ra zaqu taje wajen,ta leqo agogo yafi sau
nawa amma shuru yaron bai iso ba,saita kasa zama taci gaba da duba agogo har
ummanta ta fuskanci haka,iya saninta shahida na zuwa kai sadakar abincin nan ne don
kawai tana tsananin jin nauyin uncle isma'il,kusan kullum fuska a hade take tafiya
a haka kuma take dawowa
"Ya akayi ne shahida?,ko tsoron makara islamiyya kike?" Cikin rashin jin dadin
ranta ta kada kanta
"Toko yau zaki zauna kawai idan yazo saiya kai shi?"
"A'ah umma....zan kai bari dai yaxo din" ta fada da hanzari,don bata jin zata iya
jurewa rashin zuwanta wajen
"To ai shikenan" umman tata ta fada tana kwashe shanyar kayan sawarsu da shahidan
ta gama wankewa daxu,ciki harda ba mahaifinta don sam bata da quya ko gandar aiki.

Yana isowa ko zama bata barshi yayi ba ta sakashi ya dauka suka wuce,sai taga
kaman bata sauri,kamar tabar wani yana jiranta,haka dinga ji har suka isa wajen.

Daga nashi bangare shima har ya soma tunanin me ya hanata zuwa har
yanzu?,yana daga zaune cikin shagon bala yana duba agogon wayarshi,sama sama yake
amsawa bala hirarsa,ya daga kai don sake kallon muhallin da take zama din sai yaga
isowarta,wata ajiyar zuciya ya sauke ya zuba mata ido daga inda yake,kaman ance
mata ta waiwayo sai suka hada ido,ta danso ta dirirce amma saita maze,ta samu waje
ta zauna yayin da kowa ya soma fitowa da kwanonshi yana amsa.

Duk motsin da take sai taji kama idanunsa ne a kanta,eh ba kama bane kallon
nata yake,a yau ya hana kansa kallonta,duk da ta kamashi yana kallon nata yafi sau
shurin masaki amma ya gaza dainawa,haka suka dinga hada ido lokaci zuwa lokaci har
abincin ya qare,hakanan yau take jin wani faduwar gaba,ta dinga hada kwanukanta da
sauri tana son yau ta bace masa,saidai burinta bai cika ba,tana gama hadawar ya iso
wajen,ya dauki botikin ya soma takawa,bata da abinyi illa binsa.

Suna isa inda suka saba ta zaci zaiyi yadda ya saba,amma ga sabanin tunaninta
wannan karon sai yaja ya tsaya tsam yana riqe da botikin
"Baki da kirki" taji ya ambata,ba shiri ta dago suka hada ido,qwayar idonta cikin
nasa,yayi.mata wani kallo fuskarsa dauke da murmushin da yasa gudun zuciyarta
qaruwa,cikin hanzari ta sadda kanta jin yadda yake shirin karya lagonta cikin
qaramin lokaci
"Nima na san haka ko baka fada ba....kayi haquri.....na gode da karamcin daka yimin
harna tsahon kwana hudu,Allah ya saka maka da alkhairi"
"Amin...amma bawai kyauta nayimiki ba,nayi miki ne donki biyani" ya fada cikin
salon tsokana,a nata bangaren ta zata da gaske yake,take mummunan tunani ya darsu a
ranta game dashi,baya ta danja kadan sannan tace
"Ni bani da kudin biyanka,tun farko ma bansan biyanka kakeso nayiba da nace ka
barshi" kai yake girgixawa dariya nason subuce masa,dariyar data qara masa kyau har
tasa adam apple dinsa ya dinga motsawa
"Ba kudi nakeso ba 'yammata....zuciyarki kawai nakeso ki mallaka min" ya tsinci
kansa da fada,don ya shagalta da kallonta har baisan maganar da yake qasan
zuciyarshi ya bayyana ba,a bazata taji maganar,don bata taba tsayawa ga da ga wani
namiji ya gaya mata hakan ba ita dashi baki da baki sai wannan karon,ganin ta riga
dataji me yake fada ya sanyashi kada kanshi yana ci gaba da jifanta da murmushi
"Eh zuciyarki nakeso" cikin mintina qalilan kwanyarta ta hakaito mata abinda yake
nufi,wata iriyar kunya da nauyi suka kamata,ta rasa tudun dafaww,saboda haka saita
juya gudu gudu sauri sauri ta shige gida,yana tsaya mana amma ina ba zata iya
ba,bata taba zaton a shekarunta sha biyar akwai saurayin da zai gaya mata wai yana
sonta ba,kalmar tayi mata nauyi da yawa.

Murmushin jin dadi ya saki,ya zauna dakalin dake daura da gidansu,abinka da


d'an makaranta ba'a rabashi da takarda,sai ya ciro qaramar jotter din dake aljihun
wandonshi wanda ya gama duba wani karatu da ita yayi rubutu da basu wuce layi goma
ba ya jefa cikin botikin,ya kira yaro ya bashi botikin shi kuma ya wuce.

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos[7/1, 9:18 AM] ‫اختي‬


‫خفصة‬: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN
KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

0️⃣ 7️⃣
*Alqawarin Allah*
0️⃣7️⃣

Saida umma ta dinga qwala mata kira kan ta fito ta wanke kwanukan ta dauki
abincinta taci kada lokacin islamiyya ya wuce sannan ta taso daga rub da cikin da
tayi saman katifarta,ta harhada kwanukan ta kada ruwan kumfa ta soma sabesu,tanayi
tana tunanin kalmar daya furta mata,ashe kalma ce mai nauyu da dadi haka,lokaci
lokaci ta dinga sakin murmushi ita daya,harta zubawa botikin ruwa ta zubda ruwan
sai taga takardar,ta tsame hannunta cikin kumfar ta dauki takardar sannan ta bude.
Soma fahimta da tayi takardar meye yasa tayi sauri ta shige dakinta,ta samu
kebantaccen waje ta budeta inda zata sha iska ta bushe sosai sannan ta dawo taci
gaba da wanke wankenta.

Kafin ta kammala shirin islamiyyarta saiga qawarta zunnurah ta iso cikin


unifoarm din islamiyya
"Yauwa,dama banason cin abincin nan ni kadai,don Allah bari na dauko ki tayani"
cewar shahida tana nufar kitchen ta fito da kwanon abincinta ta aje a qasa ta zauna
dirshan
"Sauko malama muci"
"Ke nifa a qoshe nake wallahi ba abincin da zan iya ci"
"Ni zakima wulaqanci ko?,zaki sake cewa naci abinci a gidanku" tq fada tana saka
hannu tayi bismillah ta soma ci zunnurah na mata dariya,wai ita zata cewa tana cin
abincin gidansu,matar da nata abincin ma sai ya huce bata ci ba,hira suke jifa jifa
shahida nacin abincin tana kuma duba lokaci kada a fito saga sallah a shiga aji
basu tafi ba,saidai rabi da rabin hankalinta nakan takardarta dake shan iska
"Yauwa shahida....wai waye wanda yake rakoki ne kullum daga wajen sadaka" tsaida
lomar da zata saka a bakinta tayi tana duban zunnuran
"Au har kin samu labari kema?" Harara ta watsa mata
"Uwar labari na samu,waye baya ganinku a tare wai kwana hudu kenan,tunda ansan baki
kula kowa...."
"K'nnnn...nima ban sanshi ba wallahi zunnurah,acan nake ganinsa" dariya zunnurah ta
saki
"Qawata nasan halinki sarai,duk yadda akai wannan din na dabanne tunda har kika
kasa gwada masa halinki" murmushi ta saka,ita kanta tasan na daban dinne nasai
zunnurah ta fada ba,tun kallon farko taji yakai mata ko ina,ganin farko taji wani
qaqqarfan lamari dangane dashi,takan iya raba dare tana tunaninsa,kowanne second
nata da tunaninsa take rayuwa
"Amma fa kinsan shaik hafiz zai shiga wani hali?" Dagowa tayi tana duban zunnurah
kafin ta galla mata harara
"Kamar yaya?,sonshi nake?,ko ce miki yayi yana sona" nan ta zauna tsaf ta kwashe
mata yadda dukkan dalibai suka lura da soyayyar da yake mata,baki ta tabe tana
miqewa daga gaban kwanon,don ita dai tasan ko doguwar magana bata hadata dashi bare
kuma wani abu daban can,fita tayi ta wanke hannunta ta dawo tana ware gogaggen
hijabinta
"Qawata baki da mutunci fa,shaik ke kanki kinsan yammatan makaranta rububinsa
suke,kuma kema kanki qaryarki kice baki san yana sonki ba,maimakon kiyi murna
sainaga ke ko a jikinki labarin bai faranta miki ba ko d'aya"
"Don Allah zunnurah ki qyaleni da zancansa,sai....." Maganar tata ta katse jin
sallamar fiddausi,yarinyar da tsakanin gidansu shahida da nasu gidan layi biyu
ne,tun zuwanta islamiyyarsu shahida takeson qawance da ita,tun shahidan na janyewa
harta saki jiki da ita,saboda ta lura yarinyar itama nada hankali,yawan shuru shuru
da rashin son hayaniya.

Tuni zunnurah ta hade rai,hakanan a duniya taji sam fiddausi bata yi mata
ba,ko kadan jininsu ya kasa haduwa,shahida ta rasa dalili,tun tana sharewa har tazo
tanawa zunnurah fadan ta daina haka,wulaqanta dan adam babu kyau,yarinyar na sonsu
hakanan bata da wata matsala meye abun sha mata qamshi da take
"Hakanan wallahi nidai naji batayimin ba" amsar da zunnurah ta baiwa shahida kenan.

A tsakar gida fiddausi ta duqa ta gaida umma cikin ladabi,ta amsa ba tare data
tsaya ta mata wani cikakken kallo ba taci gaba da sabgoginta(babban kuskure na biyu
da ummanta ta sake tafkawa bayan fada da miji gaban 'ya'ya),fiddausi ta shige dakin
shahida,cikin fara'a suka gaisa ita da shahida,yayin da xunnurah ta kauda kai ta
amsawa fiddausin sama sama,dif zunnurah tayi sai shahidan da fiddausi dake hira
sama sama,har shahida ta gama shiryawa suka fice daga gidan.

Suna gab da shiga gate din makarantar xunnurah ta kamo hannun shahida tayi
baya da ita,duk sai suka tsaya ta hade gira tace da fiddausi
"Me kike jira?,magana zamuyi da ita" sum sum fiddausi ta juya ta wuce ciki
"Wai me yasa kikeson koyon halin daba naki ba zunnurah me fiddausi tayi miki?"
"Shahida,ba haka kawai naji banson yarinyar nan ba,an bani labari fiddausi tana
taba shaye shaye..." Rufe bakinta shahida tayi da hannu tana kallon zunnurah gami
da zaro ido
"Haba zunnurah,haba,zato fa ance zunubi ne,ya zaki jefeta da wannan mummunan kalmar
don kawai tana son mu'amala damu?"
"Da gaske nake miki shahida,daga bakin namiji na samu wannan labarin,kinsan kuwa su
basu fiye munafunci kosa ido ba bare kice,sannan kuma idan zaki lura da kyau zaki
ga yanayin fiddausi ba irin namu bane,yawan bacci da kasala kawai alamune na mutum
yana taba shaye shaye,zaman kadaici rashin so magana da yawa" zame hannunta shahida
tayi daga na zunnurah,don sosai taji babu dadi ta kuma ji ranta ya baci
"Duk abinda kika fada zunnurah baki da tabbaci a kanshi,karki fadi abinda zaki jawo
a tsaidaki a miki hisabi ran gobe qiyama,ni fiddausi ta gayamin bata da cikakkiyar
lafiya,tana da sicklier shi yasa take yawan bacci" kada kai zunnurah tayi
"Shikenan shahida tunda baki yadda dani ba,kinfi kowa amma sanin halina,nidai ina
baki shawara kibi a hankali,don bazanso abinda zai cutar dake ba"
"Babu abinda zai faru in sha Allahu" daga wannan suka rankaya suka shige cikin
makarantar.

Washegari da wuri taje wajen bada sadaka ba kamar yadda ta saba zuwa
ba,hakanan takejin wani nauyi da kunya tunda ta karanta kalaman da yarubuta mata
jikin takarda,niyyarta tayi da wuri ta koma gida ba tare daya sameta ba,saidai
abinda bata sani ba tuni ya rugata ma zuwa,saboda gaba daya ya rasa nutsuwarshi
Allah Allah yake gari ya waye yamma tayi yaje ya ganta,bai taba tsintar kansa cikin
irin wannan yanayin ba,duk yanayin rayuwa da yake ciki hakan bai hanashi bacci
ba,sai gashi a karon farko saboda ita ya kasa bacci daren ranar gaba daya,duk juyin
da zaiyi itace cikin ranshi.

Yana biye da ita bata sani ba,baiyi mata magana ba saida suka gota wajen suka
shiga wani layi
"Yanzu yau kuma haramiyar ladan rakiyar za'a yimin?,wanne irin laifi nayi haka?"
Cak ta tsaya,farinciki da kuma faduwar gaba na cakuduwa cikin ranta,idanunta a waje
har ya iso gabanta yasa hannu ya amshi botikin,ya jera kafada da ita
"Muje" ya fada cikin sassanyar muryarta da kullum take mamakin dad'in muryar da
Allah ya bashi,idan yana magana dole sound dinshi yaja hankalin duk mai sauraro,yau
saitakejin nauyin tafiya dashi,ta kasa yin gaba,ya sake dubanta
"Waiko amsar tambayata itace a'ah akemin irin hakane" wani wal tayi da ido,saiya
dafe qirjinsa da hannunsa daya
"Kiyi haquri karki qarasa tarwatsamin zuciya,wannan zuciyar mai rauni ce akanki"

Fuskarta ta qunshe cikin hijabinta tana dariya qasa qasa,wawiyar ajiyar zuciya
ya saki
"Wai Allah na,alhmdlh,ko iya haka aka tsaya na tabbatar da cewa ina da
nasara...amma dai a gayamin ana sona?" Kai ta kada cike da tsananin kunyarsa,wani
dan tsalle ya saka sannan yace
"Alhmdlh,alhmdlh" yana rungume da hannayensa.

A hankali suka ci gaba da takawa shida ita,saidai ita gaba daya nauyinsa
takeji,yayin da shi kuma yake janta da hira jefi jefi,yau duk masu binsu da kallo
mutanen cikin unguwarsu basu dameta ba,har sai taji ma batason su isa gida yace zai
wuce.

"Kina son wanda bakisan sunanshi ba hakanan bakisan waye shi ba" ya fada
bayan ya miqa mata botikinta,ita sam bata damu da wayeshi ba,sonsa takeji irin
wanda bata taba zata ko tsammatar akwai irinsa ba a duniya,tanajin koma wayeshi
yayi mata hakan
"Ni sunana muhammad anwar aminu,haifaffen kano ne kuma dan kusa da unguwarku ne
ni,maraya ne ni bani da uwa bani da uba,sai 'yar uwata d'aya data ragemin anty
usaina,ina karatu ne a fce kano...kefa?,shahida ko?" Murmushi ta saki tana dubanshi
cikin tausayi jin cewa maraya ne,kai ta kada sannan tace
"Khadija amma shahida,nice ta farko wajen umma da abbana,ina da qanne hudu,nan ne
gidanmu a nan aka haifeni,ina SS 2 yanzu" kai ya kada sannan yace
"Idan nazo anjima za'a barni na ganki" kai ta gyada da sauri,don tasan yadda zatawa
ummanta bayani yadda zata fahimta
"Shikenan zanzo anjima in sha Allahu,inason mu soma mu'amala cikin fahimtar juna
gaskiya da amana...ki shiga gida lokacin islamiyya ya kusa ko?"
"Na gode" ta furta cikin siririyar muryarta data dauki hankalinsa,kai kawai ya iya
gyadawa ya bita da kallo harta shige.

"Waye a waje kuke tsaye dashi?" Tambayar da ummanta ta soma jefo mata kenan
sanda ta aje botikin tana shirin zama,kunya ta d'anji ta kamata,saita kasa amsa
mata da wuri har sai data maimaita
"Ba kowa umm,yadai taba rakoni gida sanda su ahmadi suka fasamin
botiki,shine...shine...." Saita kasa qarasawa,murmushi kadan ummantata tayi,saboda
burinta bai wuce su aurar da shahida ba da zarar ta kammala secondry schl,ita kanta
tasan basa kyauta mata yadda koda yaushe suke cikin fada da juna suna sakata kuka
qunci da baqinciki
"Shine me?" Ta sake tambayarta tana tura mata kwanon da tayi kwadon zogale ta rage
mata saboda tasan tana sonshi,sai data sadda kai sannan tace
"Shine yace wai anjima zaizo idan za'a barni na fita"
"Allah ya kaimu" ta fada tana miqewa don ta wanko hannunta,cikin farinciki taja
kwanon ta soma cin zogalenta,wanda tana gamawa ta shige bandaki ta sake watsa ruwa
saboda ranar da ake,fitowarta kenan daga bandaki dauke kwandon wanka zunnurah ta
iso,tana shiryawa tace
"Zunnu...akwai labari fa yau"bakin zunnnura a washe tace
" ta samu kenan?"kidai muje na baki kisha,ta fada tana zura plate shoes dinta,ta
dauki jakarta suka leqa suka yiwa umma sallama suka wuce.

A hanya ta labartawa zunnurah komai,dariya ta dinga


"Kai amma wannan gayen yayi addu'a tuquru kafin yazo,shahida da babu wanda ya
isheta kallo?,da kinga wata da saurayi ma zakice wannan ai iskamci ne dududu
shekarunmu nawa?,ashe harkin girma" dundu ta dumawa zunnurah
"Banason iskanci qawa,wallahi nayi mamaki nima sosai,dama haka abun yake?,kinji
kuwa yadda nakejinsa a raina?,har banason mu rabu,idan yana kallona wlh zunnurah ni
kadai nasan me nake ji a zuciyata,ban taba tsammanin akwai wani da zanji haka a
kansa ba" dariya zunnurah taketa tiqawa
"Na shiga uku ni zunnu,sati daya kacal amma shine kika zare haka?,Allah yasa to nan
gaba kar ya haukatamin qawa ya cuceni"
"Ba komai idan ya haukataninma zunnu" ta fada tana tayata dariyar,gab da zasu shiga
makarantar sukayi kacibus da fiddausi,da fara'arta take musu magana amma shahida ce
kawai ta amsa suka rankaya suka shige makarantar tare.

Tunda ta dawo daga islamiyya ta kasa zaune ta kasa tsaye,qiyasta da qimanta


yadda haduwarsu zata kasance take,wannan ne karon farko data soma son wani a
rayuwarta,kuma karon farko da zata fara tsayawa zance da wani.

Tuni ummanta ta yiwa babanta bayani,bai kuma ce komai ba,illa ya kirata ya


masa tambayoyi game da shi,ta bashi amsa gwargwadon abinda ta sani game dashi,yace
ta kula kuma idan sun fahimci juna zaiyi magana da yaron.

Ba wani kwalliya tayi ba,tadai saka kayanta masu kyau atamfa riga da skert,ta
kuma yafa wadataccen mayafinta,sanda ya aiko kiranta tare da mubina suka fita,yana
zaune saman yalwataccen dakalin qofar gidansu,daga soron ta tsaya tana qare masa
kallo,yayi kyau sosai fiye da dazun cikin qananun kaya,iya kwanakin kadai da tayi
tana ganinsa ya tabbatar da cewa shi din dan gayune kuma mutum mai son tsafta,bata
taba ganin kayanshi babu guga ba,hakanan bata taba ganinsa da datti ko wani abu
makamancin haka ba
"Daure ki fito princess...saiki kallenin da kyau" habawa,wata iriyar kunya ta taso
ta lullubeta,bata taba tsammanin yana kallonta ba,saita sake lafewa ta kasa
fitowa,tashi yayi yana murmushi ya tsaya a qofar soron nasu yana kallon mubina dake
gaidashi,ya amsa yana shafa kanta gami da yi mata wasu tambayoyi tana amsa
masa,rabi duk a kan shahidan ne,kunya duk ta sake kamata ganin yadda mubina ba
abinda ya shalleta,komai ya tambayeta gaya mishi take,saida suka gama hirarsu
sannan yace
"ALLAH YA TAIMAKEKI...kona koma ne yau ba za'a samu ganina ba?" Dole ta fito ta
saka musu tabarma daga soron nasu,da yake yana da yalwa sosai masu wucewa ba zasu
takurasu ba.

Gaisheshi ta sakeyi ya amsa yana tambayarta gida kaman ba dazu suka rabu
ba,cikin wani shauqi da yake fusgarsu gaba dayansu.
[7/1, 9:19 AM] ‫اختي خفصة‬:
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

ALQAWARIN ALLAH 08

Anwar dinne ya soma cewa"Kamar yadda kika sani na gaya miki daxun cikakken suna
na sannan kuma ni maraya ne,na rasa mahaifina da mahaifiyata da qannena guda biyu
duka rana guda" zaro idanu shahida tayi cike da mamaki da tausayi tana duban anwar
"Eh rana daya,sanadiyyar hatsarin mota da sukayi a hanyarsu ta dawowa daga
qauyenmu"
"Wayyo....Allahu akhbar" ta fada fuskarta na nuna tsantsar tausayi,qwalla na cika
idanunta,tausayin anwar ya kamata,rayuwa ba uwa ba uba ya zata kasance kenan?
"Mu biyu muka rage a gidanmu,ni da yayata kaman yadda na gaya miki,yayata nada aure
tun kafin rasuwar iyayenmu,yanzu haka tana gidan aurenta ni kadai na rage ina
rayuwa a gidanmu,maganar gaskiya shahida zan gaya miki ba boye boye a
tarayyarmu,saboda ina fata Allah ya shiga lamarinmu,niba mai kudi bane,bani da
komai sai abinda Allah ya tsagamin,karki tsammacin samun rayuwa mai tsada,kyauta
mai tsada ko nauyi daga wajena irin wanda samari sukewa 'yammatansu,indai kina
ganin tafiyarmu akwai matsala,duk da tsananin soyayyar da raina ke miki zan iya
haqura na barki da muradinki" kai take girgizawa,sam a batajin zata iya rabuwa da
anwar,qaunarsu dashi daga Allah take,wata qauna ce mai qarfi data kama dukkaninsu
cikin qasa da kwana bakwai,tasan cewa ba qaramin lamari bane a tsakaninsu
"Ni dinma ba wata bace,kaman yadda kake gani rufin asirin Allah ne da dukka bawa
yake qarqashinsa,ina addu'ar yadda muka hadu Allah ya tabbatar damu a haka" sai
data fada kuma taji kunya ta kamata,sun d'an jima kadan suna hira ita dashi,yana
bata labarin abinda yake karanta yanayin makarantar da dai sauransu.
Qarar wayarsa ce ta sa ya dakata da abinda yake gaya mata,ya ciro wayar daga
aljihunsa yana duba mai kiran,gabansa yadan fadi,don sam zuwansa wajen shahidan ya
mantar dashi abinda ya tunkarosa,neman mudin rigestration,hausawa suka ce mai
kurmin ido da wuri yake fara kuka,haka yake duk sanda suka soma exams tun a lokacin
yake fara fafutukar neman kudin,wanda tunda ya soma karatu haka yake,Allah gatan
bawa ne,sai yake bashi kafin lokacin da za'a rufe,saidai wannan karon yana
fargaba,saboda ganin yadda rayuwa ta sake cudewa,fadi tashi ya yiwa mutane
yawa,babu ta sake samun gindin zama a rayuwar al'umma.

Saida aka sake kira ya sami ya daga da sauri,don babu ko ficika a layin nashi
"Ina zuwa in sha Allahu" kawai yace ya latse wayar ya maida aljihu,miqewa yayi
tsaye hannayensa cikin aljihun yana duban shahida qasa qasa,ta masa kyau qwarai,bai
taba ganin macen data masa kyau kaman shahida ba,komai nata mai kyaune,tun daga
yatsun qafarta har kanta,dauke kai yayi da sauri yana kwabar kansa daga kallon
qurillar da yake mata sanda ta dago kai tana dubanshi sanda taga ya miqe
"Allah ya taimakeki zan tafi" ya fada yana qawataccen murmushin daya sake fitar da
sigar kyansa,
"Allah ya tsare hanya...na gode"murmushi ya saki
"nine da godiya,yau an shayar dani irin abinda nake ji abokaina na fada....zumar
soyayya.....dama haka take?,haka akeji?" Dora tafin hannayenta tayi saman fuskarta
ta rufe tana murmushin jin kunya,yayin da ya zuba mata idanu yana kallon zara zaran
yatsun hannunta da suka dauki hankalinsa,ya sauke sassanyar ajiyar zuciya cikin
ranshi yana roqon Allah daya sanya yana kammala karatunsa ya shiga cikin sahun
daliban da suke samun aiki da wuri,don a yanzu jikinsa har ya soma sanyi da irin
kyan daya lura shahida nashi,irin matan da masu kudi ke rububin samu su aure,Allah
kada ya sanya shahidan ta subuce masa,ubangiji yasa rabonsa ce,da ya gama dacewa
nan gidan duniya,tunanin daya dinga yi kenan har sukayi sallama ya wuce.

Koda yaje inda ake kiran nasa ma ba wani biyan buqata ya samu ba,kudin da
yake nema bai samu ba,amma sai sam baiji wata damuwa can ba wadda ya saba ji a baya
duk sanda yaje neman kudin registration dinsa bai samu ba,wannan karon darensa cika
yayi fal da tunaninta da begenta,ya dinga juyi saman katifarsa,ya danna wayarsa
yana zargin kansa me yasa bai karbi number wayarta ba?,sai kuma ya saki murmushi
daya tuna koya karba dinma ina yaga credit din kira?,da gaka ya lallashi kansa yana
addu'ar Allah ya kaimu gobe lafiya.

Tun daga wannan lokacin wata iriyar soyayya mai qarfi ta shiga tsakanin anwar
da shahida,dukkan tunaninsa nata ne,duk wani motsinsa shahida na ciki,tuni labari
ya kai kunnen anty usaina,kallon anwar din kawao tayi tana mamaki,tunda suke dashi
bai taba kawo mata zancan wata yarinya ba,hasalima koda da tsokana tayi masa zancan
budurwa tabe baki yake sannan yace
"Uhmmmm,anty kenan,anata kai wa yake ta kaya?,yanzu kojin labari kikayi ina kula
wata ba zaki tsawatarmin ba?,a wannan yanayin da muke ciki anty mu tsira da
rayuwarmu ma,indai ina da abun kula budurwa na kasa baki ba shakka bani da wani
amfani a rayuwa" tunda har taga yadda anwar ke muradin shahida sai batace komai
ba,tunda haka ta faru tasan cewa soyayya ce tayi masa mugun kamun da bai zata ba
"Su anwar manya,ashe an fada tarko" dariya yayi yana shafa kansa
"Anty,shahida ta dabance,na soma sonta a sanda babu tsarin soyayya a rayuwata gaba
daya,tana da hankali da kamun kai yarinyar,anty koke na kawowa shahida kika ganta
zaki sota,fatana kawai Allah ya dubeni dana kammala karatun nan na samu aiki,na
kula dake anty na kuma samu damar auren shahida" damuwar qaninta tata ce,su biyu
suka ragewa juna a duniya,anwar irin mutanen nan ne jajurtattu,duk da bashi
dashi,duk da shima neman dafawar wani yake amma indai ya samu ko yaya samun yake
saiya tuna da ita,akwai sabo sosai a tsakaninsu,ba wanda ke iya boyewa wani wani
abun,sun zama iyayen juna abokan shawarar juna
"Kullum fatana kenan anwar,ina maka addu'ar wahalar da kakesha a rayuwarka ta zame
maka alkhairi dajin dadin da har iyayenmu dake kwance a kabari xasu ji dadinsa"
"Allah ya amsa anty"
"Yanzu ya ake ciki da kudin resgistratin dinka?" Ta fada bayan ta aje masa shinkafa
kwano guda da wake rabin kwano,wanda aduk sanda ta samu budi take bashi ya samu ya
sauya kalar cimar da yake ci,duk da itama ahalin ni 'yasun take,amma haka suke raba
wuya da dadi tare,kamar yadda idan shi dinne ma hakanne,duk da yana qoqarin boye
mata wasu abubuwa da dama amma takan fuskanci wani abun koda bai gaya mata ba da
bakinsa
"Muci gaba da addu'a,in sha Allahu kafin sannan Allah zai kawo"
"Allah ya dafa mana don isar annabi"
"S A W" ya qarasa mata,daga haka ya miqe,saita kwance bakin zaninta,yasan me take
da nufin yi saboda haka ya dakatar da ita
"Ina da hamsin dina da zan hau mota,bar kudinki" kai ta daga tana kallonshi,tanason
karanto gaskiyarsa ko akasin haka,don ya saba gaya mata haka,qarshe kuma dabawa
yake a qafa har gida duk da tazarar dake tsakaninsu saboda bashi dako sisi,ganin
haka saiya juya da sauri yana mata sallama,bai tsaya saurarenta ba ya fice.

Yana tafe a hanya tunani fal ranshi,shi daya idanunsa sun kada sunyi
ja,fatansa da addu'arsa Allah ya bashi abinda zai sakawa anty usaina dashi,tunanin
shahida daya fado masa a rai shiya dauke duk wani radadi dake ransa,har ya murmusa
shi kadai ba tare daya san ma yayi hakan ba,ya dinga tuna wuninsu na yau,yana zaune
daga shagon balarabe kamar yadda ya saba yana more kallonta,lokaci lokaci sukan
hada ido su sakarwa juna murmushi,wani kallo da yayi mata ya sanya man abincin dake
hannunta ya kware duka cikin botikin shinkafar,kunya ta kamata yayin dashi kuma ya
dinga mata dariya,har a hanyar komawarsu gida ya dinga tsokanarta kan ashe raguwa
ce ita bai sani ba?,anya idan anyi aure zata iya dauke soyayyarsa kuwa?,kunya ta
sakata guduwa ta barshi da botikin,sai mubina ce ta shigo dashi,wannan tunanin na
shahida shi ya hanashi jin nisan tafiyar,har ya iso gida,sai yaji kamar baiyi
tafiyar komai ba,bai zauna ba ya kunna risho dinsa ya dora shinkafar,sannan ya tube
kayanshi ya shiga wanka saboda idan ya fito yaji dadin duba karatun jarrabawarsa.

Cikin wasu 'yan qididdigaggun kwanaki qalilan wata iriyar alaqar soyayya mai
qarfi ta qullu tsakanin shahida da anwar,wata iriyar soyayya mai ban mamaki da
daure kai,zaka rantse da Allah sun doshi shekaru masu tsayi tare,kowannansu yayi
amanna da d'an uwanshi,kowanne ya yarda cewa rayuwarshi ta d'an uwanshi
ce,baqincikin dan uwanshi nasa ne haka farincikinsa,wuya da dad'i basujin zasu iya
rabasu,qaddara kuwa sun jima dayi mata magiyar kada ta shiga tsakaninsu,komai nasu
ya zama iri guda,tunanin da wannan yake a mafi yawancin lokutta zaku samu irinsa
dan uwanshi yake,tamkar tare aka haliccesu haka sukeji,tamkar zuciya daya aka
halitta musu su biyun kowanne bari daya na cikin jikinsa na aiki,anwar kullum
kwanan duniya shike rakota gida,bayajin an halicci wani uzuri a duniya da zai iya
hanashi rakota gida,yakan xauna a rumfar balarabe yana hangota cike da kishi,duk
wani motsinta yana kan idanunshi,baya samun nutsuwa ko sukuni har sai ta kammala ya
tattara mata kayanta ya kaita gida,da ace yana da iko da tuni ya hanata zuwa
wajen,kishi yakanyi kamar xai halakashi duk sanda take zaune tana rabon
abincin,daga bisanima da yaji bazai iya jurewa ba shike amsa ya zubawa kowa,itama a
nata bangaren tanajin shine karsashinta,duk motsi d'aya idan zatayi saita daga kai
ta kalli qwayar idanunshi take samun salama,tana jinsa har cikin jini da
jijiyarta,zata iya sadaukar da komai dominshi,saidai tana mamakin yadda ko sau
d'aya bai taba zuwa ya karbi abincin da take rabawar ba kamar yadda sauran mutane
ke amsa.

Bangare guda kuma bai taba gaya mata yanayin wahalar rayuwar da yake fuskanta
ba,tadai san cewa bamai qarfi bane,hakanan yanayinsa ya tabbatar mata da cewa shi
din mai wadatar zuci ne,don bata taba jin wani qorafi daga bakinsa ba,ko nunawa
kasawa ko gajiya a fuska da jikinsa ba gaba daya,hakan kuma ya sake burgeta
dashi,ya kuma sake saka mata qaunarsa.

Yau bayan ya rakata sunyi sallama ta amshi botikinta ta juya zata shiga gida
taga baquwar mota qofar gidan nasu,tana kallon motar ta tabbatar da cewa sunyi baqi
ne,kuma bata raba d'ayan biyu uncle hisham ne,wanda shine ya baiwa ummanta
kwangilar dafa abincin sadaka da kullum take kaiwa bakin masallaci a rabar,da
farincikinta ta qarasa cikin gidan,don kuwa jininsu ya hadu qwarai da matarshi
aunty zubaida,a tsakar gida ta taddasu,fuskarta washe da fara'a ta aje botikin nata
ta qaraso saman tabarmar da suke zaune anty zubaida na cewa
"Oyoyo 'yammata....sannu da qoqari" tana dariya dariya ta gaidasu,cikin kulawa suka
amsa ta juya tana tambayar yaron anty zubaida na faro farouq yashe sukazo?,
"Sannu da qoqari khadijatu....lallai na yarda ba qaramin qoqari da amana gareki
ba.....gaskiya ali Allah yayi maka baiwa da yarinyar qwarai" cewar uncle
hisham,kanta na duqetana murmushi
"Alhamdulillahi kam,Allah ya azurtamu da diyar qwarai,mu kanmu muna alfahari da
hakan" umma ma kai take jinjinawa,don ita kanta zata iya cewa cikin yaranta
shahidan ta dabance,wani irin hankali da nutsuwa gareta,biyayya da kyautata iyaye
tana sahun gaba,hakanan take qaunarsu,dalili kenan dako yaushe itama take ta
qoqarin daina biyewa mahaifinta suna raba gari shahidan na kallo,sunfi kowa sanin
cewa abun ba qaramin ciwo yake mata ba a rayuwa
"Nawa ake bina ne kudin kai sadaka khadija?" Uncel hisham ya tambaya yana fiddo
kudi daga aljihunsa,dariya ita abun ma ya bata,wanne irin binsa kudi?,mutum mai
tsananin kirki da kyautatawa a garesu?,ko iya kai abincin ma da take ita ta sani
Allah ne kadai yasan ladan da take samu
"Ba kudin da nake binka uncle....nima ai ina samun ladar kaiwa" kai ya gyada
"Na sani,wannan amma dole na baki haqqinki ne"
"Banda abin shahida aiko kayan kwalliya kya saya ki dinga gogawa idan surukin namu
zaizo ko?" Kunya ta kamata ta dan duqar da kanta qasa tana murmushi,mubina uwar
surutu kuwa tayi caraf
"Kullum sai yazo kuwa mamansu faruqu,yana da kirki kullum saiya kawo mana
tsaraba,ko ya bamu goma goma yace mu siya" kunya tasa shahida kasa zama saita miqe
zata gudu,yayin sa antu xubaida ta soma tsokanarta
"Ah lallai,zanso naga wannan surukin namu,na tabbatar shima yana da kyau da nutsuwa
kamar diyarmu..."
"Rabu dasu shahida....dawo ki xauna muyi lissafi" uncle husham ya tare mata,haka ta
dawo tana sunkui da kai ta zauna
"Mu lissafa kwana nawa akayi ana kaiwa?"
"Allah uncle ka barshi kawai"
"Naqi din" ya fada yana soma irga kudin
"Ki fada kona baki yadda naga dama"dariya ta danyi tana basar da maganar,kudi mai
yawa ya irgo yace
"toh gashi"
"Uncle ka bawa umma ta ajemin"
"A'ah a'ah,ba ruwan umma,wahalarkice karbi kiyi duk yadda kikeso dashi...iyakata in
baki shawarar me zakiyi dashi" cewar umman tana miqews don zuwa kitchen ta hadowa
su anty zubaida abinci,hannu biyu ta saka ta amsa tana masa godiya,a nan ta barsu
anty zubaida harta gama shirin islamiyya suna zaune suna hirarsu,tayi musu sallama
ta wuce.

************************

"Malam balarabe ina kayan anwar?" Shahida ta tambayi balarabe mai kanti
lokacin da anwar din ke can yana hada kwanukanta don lokacin komawarta gida yayi
"Gashinan ina aunawa...bari na hada miki harda kwakin"murmushi tayi sanda take
amsar ledar kwakin daga hannunsa
"Anwar...anwar kaina dabanne,ko me zakayi da garin kwaki kuma?"
"Na'am?....ai aikin muhammadu kenan,ba yadda banyi dashi ya dinga sauyawa da wani
abun ba,ya amshi bashi duk sanda Allah ya hore masa ya biyani amma sam sam ya
qiya...gaskiyarki kuwa shi na dabanne,rayuwarsa ma haka,ni tsorona ma kar yayi masa
illa yawan cinsa da yake,bashi da abinda ya wuce gari" sam batasan zancan zucin da
take ya fito fili ba saida taji sharhin malam balarabe fadi ba'a tambayeka
ba,saidai maganar tashi ta taba ta,ko a fuska bata taba ganin wani abu makamancin
haka daga wajen anwar ba,hasalima bai taba karbar abincin da take kawowa wajen ba
ko sau daya kuwa,a gabansa take rabarwa har ya qare iyakarsa ya dauka mata kayanta
suje gida ya aje mata ya wuce,a sanyaye take bin ledar garin da kallo,tausayin
anwar din ya kamata,ta yaya mutum zai rayu da cin gari kullum?,tsananin maraicin ne
yasa haka?,amma indai da gaske ne sun zama abu daya mai yasa bai taba gaya mata
ba?,ta yaya tana cin shinkafa kullum anwar yaci gari?,sosai taji haushin boye matan
da yayi,wasu qwalla suka cika mata idanu,saita dauki ledar kawai ta juya ta fice
daga kantin ba tare data ce komai ba.

Sanda ta isa wajen har ya gama hada komai tsaf yana dube duben
nemanta,fuskarshi yadan tsuke kadan
"Ina kuma kika shiga?,banason ki dinga darawa ko ina daga nan fa,kinsan halin
mutane da shegen kallo da sa ido"
"Ba wani waje naje ba,na karbo maka saqonka ne daga wajen malam balarabe"
"Balarabe kuma?"ya tambayeta yana nazartar fuskarta,fes ya fuskanci yanayinta ya
sauya,ganin bata ce komai ba yasa shi daukan botikin ya soma yin gaba,ga tunaninshi
zata biyoshi amma saiyaga bayansa take bi kamar yadda suka fara can watannin baya
da suka shude sanda suke baqin juna.

Cikin jinin jikinsa yaji sauyin yanayin shahidan bai masa ba,ko shakka babu
akwai abinda ya faru shigarta shagon zuwa fitowarta,zuciyarsa yaji ta tsinke sanda
ta qyasa masa wani tunani game da malam balarabe,baisan sanda yaja birki ba,ya
waiwayo a sukwane,wanda saura qiris suyi karo da juna,baya ta danja kadan tana
duban qwayar idanunshi da suka sauya launi,saiya sake matsowa gab da ita,kanta ta
girgiza qirjinta na bugawa gana duban hagu da damarta,layin tsit yake babu
kowa,yana daya daga ciki layukan da yake da qarancin zirga zirgar jama'a
" me malam balarabe yayi miki?"ya tambayeta da wata iriyar rikitacciyar murya,tuni
qwallar data cike da idanunta ta soma silalowa,rikicewa yayi jikinsa ya soma
rawa,kafin ya sake furta komai ta bude ledar hannunta garin ciki ya bayyana,kallan
garin yayi sannan ya kalleta,tashin hankalin daya sauko masa yaji ya soma
yayewa,hankalinsa ya soma kwanciya ganin ba abinda zuciyarsa ta raya masa bane,ya
saki wata wawuyar ajiyar zuciya wadda ta sanya duk wani qarfi na jikinsa raguwa,har
sai daya jingina da bishiyar da suke tsaye qasanta yana sauke wata qatuwar ajiyar
zuciya
"Me yasa zakamin haka?,wannan abincine yanzu?" Sai yanzu ya sake fahimtar dalilin
sauyawarta,kuka take sosai,saiya amshe ledar ya dora saman botikin daya aje gefansa
"Wannan bai isa ya zama dalilin da zai saka min ke fidda wannan tsadaddun hawayen
ba,wanda duk duniya babu kudin da zasu iya sayen darajarsu a wajena.....ungo nan
share hawayenki" ya fada yana bata qaramin handkherchief dinsa wanda baya rabo
dashi saboda share zufa da yake gwanin zufa ne,hannu ta saka tana goge
fuskarta,tsahon minti biyar ya bata don ta nutsu sannan ya bata damar magana
"Ohk...yanzu fadi duk abinda yake damuwarki"
"Kafi kowa sanin ba haka mukayi alqawarin gina tarayyarmu ba,munyi alqawarin xamu
ji dadi da wuya a tare,kukanka nawa ne,kukana naka ne,haka nan dariyarmu,don me
zaka boyen wannan?" Murmushi mai kyau da qayatarwa ya subuce masa,kullum kwanan
duniya yana jin ana qara masa sonta ne,duk sujjadar da zaiyi saiya roqi Allah yasa
shahida mallakinsa ce daga duniya har lahira
"A ganina wannan ba wani abu bane Allah ya taimakeki,na jima ina cinsa har kawo yau
gashi ina raye ban mutu ba..." Saita mele baki cikin muryar kuka tace
"Zancan mutuwa ma kake?....." Kasa qarasawa tayi ta sake sakin masa wani
kukan,kanshi ya dafe sosai,ya tsani kukanta,idan yana ganin hawayenta ji yake kaman
wani babban tashin hankali ya sameshi
"Ya salam shahidaaah....,Allah ya baki haquri,kin manta cewa mu mutu ka raba ne?"
Da tausasan kalamanshi dake sawa rayuwarta nutsuwa yayi amfani ya lallasheta sannan
suka ci gaba da tafiya,bayan ta sa yayi mata alqawari bazai sake shan gari ba
saidai da marmari.

Sanda suka isa tsaidashi tayi ta shiga gida cikin sauri,bata zarce ko ina ba
sai kitchen dinsu,tasan ba'a rasa abincin a gidan nasu,koda bamai yawa bane amma
za'a dafa,foodflask dinta ta dauka ta cika masa shi da taliya da wake sannan ta
fita.
Yana tsaye harde da hannayensa a qirji,idan ka dubeshi da kyau ya zaka
fahimci ya fada zurfin tunani ne,ledar hannunta ta miqa masa baqa wadda babu ta
yadda za'ayi ya iya gane meye a ciki,saida dubeta ta masa alama da kai akan ya
karba sannan yasa hannu ya amsa
"Ka tafi dashi"
"Meye wannan din?"
"Guba na baka kaci nima naci saimu mutu tare" dariya ta bashi sosai har sai daya
dara,itama sai data fada din maganar ta bata dariya
"Kinsan kuwa zai zame min abun alfahari...kuma babban labarin da zai karade
duniya...masoyiya ta baiwa masoyinta guba donsu mutu tare" murmushin daya qarawa
fuskarta daraja da kyau ta saki
"Zan iya cin guba don tunkudeka daga cinta" girarsa daya ya dage sannan ya sassauta
murya
"Idan babu ke ai babu ni shahida....kina tunanin idan kika mutu kika barni zan iya
qara kwana daya a duniya" wani far tayi da ido wanda ya sanyashi yin baya da sauri
"Inni sa'im...naga alama so kike ki....." Da hanzarinta ta juya masa baya cikin
shagwaba tana dan buga qafa alamun batason ya qarasa maganar da yake
"Shikenan.....sai anjima,na gode" ya fada yana takawa don barin wajen,tana wajen
tsaye harya bacewa ganinta,saita lumshe ido ta saki hannayenta tana sakin siririn
murmushi,tsakanin ita da anwar batasan waye yafi wani son dan uwanshi ba,wannan
amsar kuwa tasan cewa Allah ne kadai masaninta.

Cikin kudinta ta cire dubu uku ta siya qaramar waya sabuwa irinta
anwar,ummanta bata hanata ba bare abbanta,sunsan cewa waya ba damun shahidan tayi
ba,yanzun ma sun tabbatar saboda anwar ta siya,wanda dukkansu zuwa wannan lokacin
anwar ya zama kamar d'a a wajensu,mutum ne da Allah yayi masa baiwar saurin shiha
zukatan al'umma,hakan kuwa baya rasa nasaba da hankali nutsuwa uwa uba tarbiyya da
yake da ita,ko cikin unguwarsu dattawan nan son anwar suke,kusan kowa zakaga yana
janshi a jiki,shi kuwa ya daukesu dukkansu tamkar mahaifansa,dalili kenan daya
sanya wasu daga cikin matasan unguwar kejin haushinsa suka kuma qwafa masa,hakanan
suka daura dambar sake danqwafar dashi,hakanne yasa duk sanda ya samu wani abu
sakakke sai an haura gidan an sace,kama daga sutura zuwa takalma ko d'an kudi,ya
rasa su waye?,baisan kuma meya tsare musu ba,shi da bashi da komai?,bai baiwa kowa
ajiya ba amma ya tsone musu ido.

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos*ZAFAFA BIYAR NA
KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI
TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

0️⃣ 9️⃣
*Alqawarin Allah*
0️⃣9️⃣

Tun daga lokacin ta maida abincin anwar ya zama wajibinta,duk sanda ya nuna alamun
turjiya na bazai amsa ba anan ne zasuyi fada,har hakanma ya zame masa jiki.

Gefe daya kuwa rayuwarshi sai hamdala kawai,kusan duk wani fadi tashi ya zame
ma rayuwarshi jiki,ta fannin kudin registration kuwa ba wani ci gaba da aka
samu,iyakar qoqarinsa bai hada komai ba kaman yadda ya saba,yaqi kuma sanarwa anty
husaina,tun yana jin babu komai harya soma shiga damuwa,ganin lokaci yana
quracewa,sannu a hankali ya soma yanke tsammanin samun kudin ma gaba daya,wanda
hakan ya jefashi cikin damuwa mai tsanani,damuwar da tasa anty husaina ta gane
halin da ake ciki,ta kirashi tayi masa fada sosai,ta kuma saida dan abinda ke
gareta na kudi,saidai kudin basu cika ba,kaso d'aya aka samu cikin biyu,a lokacin
ya rage saura kwanaki makarantar su rufe registration.

A hankali take takowa zuwa cikin soron nasu,niyyarta ta tsoratashi kaman


yadda yayi mata shekaran jiya ya tsoratata,taji tsoro sosai ya koma gefe yana mata
dariya yana fadin
"Ashe farar kura ce ke bansani ba?".

Yau da yazo kan dakalin qofar gidan nasu yaci burki,hakanan yake jin ranshi
babu dadi,wanda hakan ya bayyana har gangar jiki da fuskarshi,saidai duk sanda ya
tuna yanzu zaiga sanyin idaniyarsa sai yaji yanayin da yake ciki din ba komai
bane,wayarshi dage aljihun wandonshi ta dauki qara,ya zura hannunshi a hankali ya
zaro wayar,anty husaina ce ke kiranshi,yasan kuma kiran bai rasa nasaba da cikon
kudin registration dinsa ba,zayaso kunnuwanta su jiye masa ya samu,saidai ba mai
yiwuwa bane yayi mata qarya,abokin kuka shi ake gayawa mutuwa,sannan uwa uba bayaso
wani abu ya kawowa karatunshi tsaiko,babban burinsa a yanzu shine ya kammala
karatunsa ya samu aiki,ya auri shahidansa ya kuma kula da anty husaina,itama ta
huta taji dadinsa
"Yaya dai muhammadu an samu cikon kuwa?" Ta tambayeshi bayan ya gama gaidata,cikin
nuna kasawa da sarewa yace
"Anty ina ganin saidai nayi haquri....wannan karon duk wani qoqarina na samun cikon
kudin na gaza,kudin sunqi samuwa....ina tsoron asarar karatuna..." Tausayinsa ya
kama anty husaina,tasan abune mai wuya ganin karayar anwar
"Kaci gaba da addu'a,ina nan ina nawa qoqarin mu zubawa sarautar Allah ido,in sha
Allahu yana tare da mu"
"A'ah anty.....karki takurawa kanki karki damu,nima zanci gaba da nawa qoqarin...".

A hankali ta koma da baya cikin tsananin mutuwar jiki,ba labe tayi musu ba
amma ta kasa tafiya sanda yake wayar da anty husaina,cikin mutuwar jiki da karaya
take juyawa zuwa cikin gidan,qirjinta ya quntata qwalla ta cika mata idanunta,dama
akwai wani abu da anwar zai iya boye mata game dashi?,da wannan tunanin ta isa
dakinta,gefan katifarta ta samu ta zauna tallafe da kumatunta,batasan adadin
lokacin data dauka a haka ba har ya tarawa wayarta miscal bata gani ba,saida
ummanta ta daga labulen dakin
"Wanne shashanci ne kike haka shahida?,kinsan ba zaki samu fita ba kikabar anwar
qofar gida yana jiranki?" Hannayenta ta sauke tana cewa
"Yanzu zan fita umma" sakin labulen tayi ta juya ta fice tana mita
"To ke kuma ya isa haka malamar mita,tunda ta baki uzuri basai kija bakinki ki
shuru ba?" Ta jiyo abbanta yana fada
"Kaga kar kace zakamin fada,don na mata magana laifi nayi?"
"Ba laifi bane,mitar ne ni banason ji karki cikamana kunne"
"Wai yau cin mutuncin naka ne ya motsa baban shahida?" Ta saki abinda take ta zuba
masa idanu tana tambayarsa,saiyayi banza da ita ya zubda ruwan daya kurkure bakinsa
ya dauki hularsa ya fice,ajiyar zuciya shahida dake tsaye bakin window ta saki,ta
godewa Alla daya taqaita cecekucen nasu baiyi tsaho ba har yaja hankalin anwar ko
yajisu.

Katifarta taje ta daga,kudaden da uncle hisham ya bata ta dauko,ta zauna ta


qirgasu a nutse sannan ta shiryasu,koda batasan nawa anwar ke buqata ba tasan cikon
kudin bazaikai yawan kudaden dake hannunta ba,don kudaden da uncle anwar din ya
bata suna da yawa,don taji ma anty amina na cewa mama su aje a karba a siyawa
shahidan tukunya mai sha biyu a aje mata,lanqwashesu tayi sannan ta miqe ta gyara
mayafinta ta fice.

Sanda ta koma yana zaune kan dakalin,ya zubawa qasa idanu wanda hasken farin
wata ya haske jikinsa yake bashi hoton inuwarsa,a hankali ya dago kai idanunsu suka
hadu da juna,wani sanyi yaji har cikin rai da zuciyarsa,saiya sakar mata murmushi
yana jin kaso tamanin na quncin da zuciyarsa ke ciki ya tafi,kallon farko ana biyu
ya karanci lallai akwai abinda yake damunta,duk sai yaji wani iri,yaji babu
dadi,duk wata walwala da karsashinsa ya shiga yin nashi guri,shi ya amshi daddumar
hannunta ya shimfida ya kuma yi mata nuni data zauna,batayi musu ba ta zauna
din,yana tsaye qyam a kanta yana qare mata kallo,ya samu kanshi da kasa zama
"Mene ne yayi kutse cikin farincikin gimbiyata?"
"Kaine...." Ta fada kanta tsaye,cikin sanyin jiki ya samu dan wani dutse dake daura
da ita ya zauna samanshi
"Bana fatan kasancewar wannan ranar....wane kuskure na tafka haka harya zama
tarnaqi wa farincikin zuciyata?" Hawaye ta soma zubarwa,bana komai bane saina
tausayinsa,zurfin cikinsa yayi yawa,kara da kawaicinsa sun baci,amma ko daya bata
son ya sake boye mata wani abu daya danganceshi,tana ganin kaman hakan wani naqasu
ne tattare da dangantakarsu,zai zama tamkar bai bata muhimmancin da take tsammanin
ya bata ba
"Ashe dukan inda nake tunanin nakai bankai can ba a zuciyarka?"
"Ya salam" ya furta fuskarshi na nuna tsantsar tashin hankalin daya shiga,wanda har
cikin zuciyarshi haka ne,wanda har yanajin ya zarce na rashin kudin registration da
bai samu ba
"Shah......"
"Kar ka sake cemin komai....na kamaka da laifuka guda biyu kawo yanzu,ban taba boye
maka komai daya danganceni ba....amma kai ka boyemin abubuwa har biyu,ban sani ba
ko.matsayina baikai nasan wannan fannin ba...." Sanyi ya dinga ji yana ratsa qasan
zuciyarshi,duk da bai fuskanci me yayi mata ba,dubanta yake cike da qaina soyayya
sa shauqi mai yawa,ta damu da lamuransa fiye da tunanin mai tunani kamar yadda ya
damu da nata,bai tsammaci zata soshi kamar yadda yakesonta ba,ya zaci zata soshi ne
irin son da baikai ya kawo ba,kodon kyau da Allah ya bata,kodon gata data
d'arashi,ko don saboda farinjini da Allah yayi mata
"Yanzu karatunka ba nawa bane?" Ta fada maganar quruciyarta na fitowa fili,hakanan
ta b'ata rai sosai ta kuma tsareshi da ido,murmushi ya saki wanda ya bayyana
fararen haqoranshi
"Nakine my shahida"
"Don me baka gayamin halin da kake ciki ba?" Dan shuru yayi yana tauna amsar da zai
bata,tsahon minti guda kafin yace
"Shahida....kin wuce duk inda kike zato kike tsammani a wajena,tunda Allah ya busan
numfashi ban taba qaunar wata d'iya mace ba saike,nine namiji,ni nake nema,kuma
nine sama dake,bai cancanci ace dukkan wata wahalata tana wuyanki ba"
"Koda bani da abun da zan taimaka dashi ai na sanyaka cikin addu'o'ina ko?"
Idanunsa ya lumshe idanunsa yayi yana sakin murmushi
"Ni na sani shahidana koda banda damuwa ba zata daina sakani a addu'arta ba"
"Ta yaya zan aminta cewar mun zama daya kana boyemin ire iren wadan nan abubuwan?"
"Shahidaa...karki sake tunanin bamu zama daya ba,kin zama muhammad anwar,na zama
rahamatulshahida" sunan ya bata dariya har sai data murmusa,tafin hannunta ta bude
sannan ta miqa masa kudin hannunta
"Ungo qirgamin" amsa yayi yana zolayarta,sannan ya soma qirgawa yana cewa
"Shahidana ta zama hajjaju" sai daya gama qirgawa sannan ya dago ya dubeta yana
gaya mata nawa ne,kai ta gyada duk da tasan nawa ne dama
"Kayi amfani dasu" sak ya tsaya yana dubanta kafin yace
"Shahida...." Idanunta ta ware masa tana dubansa itama,ya gane me take nufiSai ya
saki murmushi
"Aro na baka,amma kayi duk amfanin da kakeson yi dasu"
"Kai amma wannan yarinya kin iya bada rance....to na gode Allah ya bani ikon biya"
daga haka sukaci gaba da hirarsu,saidai rabin hankalinsa dukka yana kan halayen
shahidan,yana sake godewa Allah tabbas baiyi zaben tumun dare ba,hakanan ya
tabbatar bai miqa zuciyarshi inda bai cancanta ba.

Wannan abu da shahidan ta yiwa anwar ba qaramin qara mata qima yayi a idanun
anty husaina ba,wata qauna take mata tamkar diyar cikinta tun kafin ma ta yiwa
anwar hakan,ta yadda ta kuma yi amanna cewa anwar yayi dace da matar aure,ta kuma
shiga sahun masu masa addu'ar Allah yasa shahidan ta zama mallakinsa.

Ta gefan anwar dinma tuni ya shiga bakunan 'yan uwan shahidan musamman 'yan
gidansu da anty amina wadda sukafi dasawa da shahida duk cikin 'yan uwan
mamanta,kasancewar tasu tafi zuwa daya da mamanta,kuma ita daya ke gaya mata magana
itama maman da ita take shawara.

Cikin ikon Allah anwar yayi registration dinsa,komai yaci gaba da tafiya dai
dai,rayuwarsu da shahida kuwa ta zama abar kwatance ga duk wanda ya sansu,kowa
najin jinin danuwansa na yawo a nasa jikin,tun mutane na mamakin yadda sukeson juna
har abun ma ya zame musu jiki,su kansu yadda suke nunawa kansu qauna basusan sunayi
har haka ba saidai a gaya musu.

Sannu a hankali rayuwa taci gaba da juyawa,ta wanni fannin ana samun ci gaba
yayin da wani bangaren yake zamowa koma baya da babban naqasu wajen bawa.

Zuwa sannan shahida sun shiga ss 3 term din farko,a sannan ne Allah ya yiwa
mahaifin zunnurah rasuwa,hakan ya zama silar barinsu garin kano sukayi qaura suka
koma katsina cikin danginsu,dalilin kenan daya sanya kusancin shahida da firdausi
ya sake samun tagomashi mai yawa,ta maye mata gurbin zunnurah,yayin da ita da
zunnurah ya zama sai a waya,lokaci lokaci idan sukayi waya tana sako mata zancan
fiddausin tare da sake ja mata kunne kan tayi hankali da ita,murmushi shahida keyi
yawancin lokaci,ta sake yarda Allah ne kadai.ya isa ya hada zukatan bayinsa,har yau
bata tana ganin wani abu mai kama da abinda zunnurah ke tuhumar fiddausi dangane da
ita ba.

Anwar ya samu ya kammala karatunsa cikin wahala da dagiya da kuma taimakom


anty husaina wadda ta sadaukar da dukkan wani abu nata don ci gabanshi,yayin da
shahida ta zamo mutum na biyu data sadaukar da dukkan wani abu da take ganin ta
mallaka saboda anwar din.

Bayan fitowar sakamakonsa wani yayan abokinsa ya kirasu yayi musu tallar
aikin d'an sanda da za'a soma dauka,rimi rimi sukayi komai da karime karime da
qarfafawar gwiwar shahida data dage kan sai yaje,sai kuma batun tafiya training ya
taso,a nan ne ya sare saboda lissafen lissafen abubuwan da za'a buqata daga
garesu,wanda kusan duka harka ce ta kudi,koda wasa bazai doshi anty husaina da
wannan batun ba saboda yasan cewa wahala ce da nauyi kawai zai dora mata,saiya
shiga neman kudi babu ji babu gani,sai lokacin da tafiyar ta matso sannan ya
shaidawa anty usaina,ta masa addu'a sosai,ranar da zaiyi sallama da shahida ta
dauko baqar ledar viva ta dire masa.

Sai daya gama kalla sannan ya dago yana dubanta,baisan ma da wanne baki zai
mata magana ba,da wanne harshe zai gaya mata yadda take a wajensa?,kaya ne da tasan
cewa zai iya buqata a ciki,wanda ko bata fada ba yasan a qalla zata kashe dubu
biyar,Da hannu ta masa nuni dole yayi shuru,tamkar ba zasu rabu ba ranar,ji yake
kaman idan yaje zaiyi shekara ne bai dawo ba.

Kwanansa uku acan shida wasu mutum biyar suna cin wuya saboda ance sam babu
sunansu cikin list din,bawai kuma babu dinba,yanayin qasarmu ne kawai,an suba
wadanda sukafi kowa rashin galihu an cire sunayensu daga list din an maida gurbinsu
dana wasu,hakanan suka tattara suka dawo gida.

Randa shahida ta ganshi ya dawo ba qaramin jin takaici tayi ba,har kuka ta
kusa yi,shi ya dinga lallabata yana bata haquri
"Duk randa Allah ya horemin abu na farko da zan fara ginawa shahida shine
makaranta,zanyi irin makarantar da yaran masu kudi suke zuwa,irin makarantar da
suke karatuna zuba yaran masu qaramin qarfi,su samu irin ilimin da yaran masu hannu
da shuni suke samu,su samu gata da kulawa irin na yaran masu dashi"shuru shahida
tayi tana karantarsa,har cikin zuciyarsa maganar take fitowa saboda yadda hakan ya
bayyana saman fuskarsa
"Yaran marasa shi suna shan wahala,suna shan wahala matuqa wajen neman ilimi,bayan
sun samu karatun da qyar ya zamana karatun ya kusa zama na banza,sakamakon yadda
aiki ke musu wahala,wanda wasunsu daga qarshe sakamakon karatun nasu kusan dai dai
yake da takardar tsire" nan ma dan shuru yayi yana hadiyar yawu,sosai lamarin ke
sukar zuciyarshi,sun jima suna tattaunawa game da halin rayuwa sannan daga bisani
sukayi sallama.

Anwar bai gajiya ba bai kuma sare ba yaci gaba da neman aiki baji ba
gani,burikansa din nan guda biyu su yake fafutukar ganin ya cimmawa,yana tsoron
shahida ta kammala secondry ba tare daya samu aiki ba,babban burinsa a duniya suyi
aure sanda zata kammala makaranta,ya kuma tsaya mata tayi karatu kaman yadda takeso
harsai tace ya isheta,yana da burin yi mata halacci kwatankwaci koma fiye da yadda
tayi masa.

*BAYAN WATA HUDU*

Kallonshi take tamkar ta zabga masa mari haka takeji,saidai hakan ba


maiyuwuwa bane tunda ba tarbiyyarta bace,dawowarta kenan daga gidan anty amina ya
tsaidata,sam batasan yana biye da ita tun daga qofar gidan anty amina ba cikin
motarsa saida ta iso layin nasu,ta shiga gida da niyyar ba zata saurareshi ba yadda
yaketa zabga aike yasa umma tace ta fita ta saurareshi.

Hakanan cikin jikinta takeji kamar akwai wanda yake kallonta,kamar anwar na
wajen tare dasu,a hankali ta kalli damanta,shine kuwa sanye cikin jibgegiyar rigar
sanyi da wandon jeans,kasancewar ana cikin yanayin sanyi,yayi kyau matuqa,kai kace
wani ne ko dan gidan wani,kyansa ya sake fitowa,fitilun motar daya bari a kunne sun
haskeshi sosai kaman yadda suka haskesu,idanunta cikin nashi saiya ja da baya ya
juya ya soma barin wajen.

Wani tashin hankali ya ziyarceta,da wanne baki zata yi masa bayani?,ganin


yadda hankalinta ya wajen ya sanya saurayin shima juyawa yana kallon wajen saidai
baiga komai ba,bata sake bi ta kanshi ba ta shige gida da hanzari,wayarta ta laluba
ta soma kiran layin anwar din,saidai harta qaraci ringing dinta ta gama bai daga
ba,hakan ba qaramin daga mata hankali yayi ba,ba zata manta ba shekaran jiya suna
hira yake ce mata
"Shahida tsoro nakeji,gani nake kaman zan rasaki,kaman kinfi qarfina" cikin mamaki
tace
"Me kake fada anwar?" Murmushi yayi saidai ya taba har zuciyarsa
"Shahida...kina kallon kanki a mudubi kuwa?,irinki ba qananun mutane ke aurenki
ba....ina tsoron kada wani mai motar yasha gaba na" sosai taji haushi harma ta
shige gida ta barshi ko sallama basuyi ba,da qyar yasha kanta ya waya,to jiya bai
samu zuwa ba kasancewar ya samu dan wani aiki yana kulawa wani da provision dinsa
cikin anguwarsu,ladan da yake bashi ba wani mai yawa bane kasancewar kanti ba wani
girma gareshi ba,amma ya karba yana yi saboda ba mutum ne shi mai raina sana'a ba
komai qanqantarta.

Kusan ranar kwana tayi tana kiran layin nashi amma ko sau daya bai daga
ba,daga nashi bangaren hankalinsa a tashe yake,hakanan zuciyarsa ke wani irin
tafasa,kishi ne ki cinsa sosai,fargaba ta lullubeshi,fargabar kada ace zancansa ne
zai tabbata zai rasa shahidansa,duk sanda ta kirashin bai daga ba sai yaji wani
qunci na sake ziyartar zuciyarsa,bai iya daurewa yana jin kiranta na shigowa amma
ya kasa dagawa,daga bisani tilas ya kashe wayar duka yana fatar ta haqura tayi
bacci.

Kwana biyu ba anwar din ba dalilinsa,hakan ya daga hankalinta don har wajen
kai sadaka bata ganinsa,da yammacin kwana na ukun bayan ta dawo daga kai abinci
wanda yanzu ajewa kawai take wajen baba ado dake wajen ya raba a aiko da botikin
don fir anwar yace ta daina kaiwa,shiryawa tayi ta tadda ummanta zaune tana jan
carbi bayan ta idar sallar la'asar
"Umma....zanje gidan anty amina"kai ta daga ta dubeta sannan ta shafa addu'arta
"gidan amina kuma?,makarantar fa?"kanta tadan sunkuyar tana wasa da farcenta
"hadda ake karba,kuma ni na bada tawa tun jiya" dan jim tayi sannan tace
"Shikenan,ki gaisheta....yauwa....kice mata yaushe za'a fitar da ankon umaiman,ki
gaya mata lokaci yana qurewa fa"
"Tohm umma....saina dawo"
"Zan rakaki yayaa" cewar mubina wada ke shirin islamiyya ta fada bayan ta watsar da
hijabinta wajen
"Babu inda zaki,makaranta zakije" cewar ummanta,tana jiyo ihunta ta saka kai zata
fice tana dariyar rikici irin na mubinan,dai dai lokacin abbanta ya shigo,saita
koma da baya tana masa sannu da zuwa yayin da yake tambayar abinda aka yiwa mubinan
"Wai gidan anty amina tace zata bini,kuma islamiyya zata"
"Ke ina taki islamiyyar?"
"Hadda ake amsa abba kuma na bada tawa tuni..."
"To ma sha Allahu,dama inason ganinki"
"To abba gani" ta dawo tana dawowa saman kujera 'yar tsuguno ta zauna,
"Shahida....ina fatan ba wani abune ya shiga tsakaninki da yaron nan ba anwar?"
"Abba meka gani?" Ta tambaya a sanyaye
"Kwana biyu bana ganinsa yana zuwa" shuru tayi tana tunanin amsar da zata
bashi,dukkaninsu ummanta da abbanta wani irinso sukewa anwar din,halayen anwar abun
sone,nagarta gareshi wadda ta zama tilas ko waye kai ya burgeka
"Uhmmm...bakice komai ba"
"Abba in gaya maka?" Mubina dake goge hawayenta ta fada,harararta shahida tayi amma
hakan baisa ta fasa magana ba
"Wanine mai mota yazo...umma tace taje ta sallameshi,shine yaya anwar ya ganshi ya
tafi"
"Ubanki mai shegiyar magana" umman ta fada tana kai mata duka
"A'ah hadiza barta ta fada....kice kawai kin soma shanshano wani ne....ke shahida
tashi ki tafi,kema zamu gamu dake"
"Duk abinda kaga dama ka fada,tunda dai ba zuciyata ka shiga ka hangi haka ba
shikenan na gode Allah" tun kan ta fice daga soron nasu ranta ya soma baci,saboda
taji suna gab da kaurewa da halayyar tasu da suka saba,saitayi maza maza ta ficema
don kada ta jiyo abinda wunin yau zai sa ta kasa walwala,sam bata iya daurewa duk
sanda wani sabani ya hasu tafi kowa jin zafin abun,tqfi kowa shiga qunci,ta rasa me
yasa dukkansu basu haquri da juna,kowa kaman jiran kowa yake,kamar wadanda aka
sakawa hannu cikin mu'amalarsu.
Ba dadewa ta isa gidan anty amina,ta taddata tana wanki ta saka mata hannu
suka gama tare,tanata tambayarta anwar kwana biyu bai leqo ba batace komai ba,har
sai da suka gama suka zauna dakinta suna ninke wasu kayan da suka soma bushewa
"Anty....nifa zuwa nayi ki mana sasanci da anwar"
"Sasanci kuma,me ya hadaku kenan?,yau kwana uku kuwa da zuwanshi ya gaidani"ana ya
gobe abun zai faru kenan?,shahida ta raya a ranta,batasan ma yazo din ba,jininsu ya
hadu da anty amina,gashi kuma ba wani nisa sosai tsakanin gidanta dana anty
usaina,don har zumunci ma suke yanzu ta sanadinsu,tsaf ta kwashe komai ta gayawa
anty aminan,a take tasa shahidan ta kirashi,saidai harta gama ringing bai daga ba
"kin gani ko anty?"shahidan ta fada idanunta na cikowa da qwalla
"Bari na kirashi da wayata" anty amina ta fada tana daukan wayarta,ringin biyu ya
daga cikin girmamawa
"Anty amina...da kanki?" Ya fara fada cikin girmamawa
"To ya zanyi?,diyata ta dagamin hankali?"dariya ya danyi
"Shahida ko?"
"Ita mana"
"Karki qona katinki anty bari nazo"
"Da kuwa ka taimakeni karta fashemin gata nan ta cika fam" da haka sukayi sallama
tana duban shahidan
"Shima a muryarshi kadai ya isa kasan cewa yana cikin damuwa da kewarki,wanne irin
so kukewa juna shahida?" Kunyace ta kamata saita soma sinne kai.

Ba'ayi minti talatin ba cikakke d'aya daga cikin yaran anty amina suka shigo
suna cewa ga uncle da yake haka suke kiranshi,anty amina ta saka hijabinta tace
suce mishi ya shigo.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*KO KUMA*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARING🙏🏽*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

1️⃣ 0️⃣
*Alqawarin Allah*
1️⃣0️⃣

A nutse cikin sallama ya shigo ta daga kai a hankali ta kalleshi saboda ita kadai
tasan yadda tayi missing dinshi,shi dinma idanunshi na bisa kanta ji yake kamar ya
shekara dari bai ganta ba,amma duk da haka saiya gintse saboda tuno ganinta da yayi
da wani,daya daga kujerun falon ya samu ya zauna suka gaisa da anty amina sannan ta
soma tambayarsa
"Wai me ya hadaka da shahida?,duk ka firgitamin diya?"
"Ta firgitani dai anty...bakiga har rama nayi ba?" Murmushi anty aminan ta
saki,yadda sukeson junan nasu na bata sha'awa,bai boye komai ba ya gaya mata sannan
ya dora da cewa
"Wallahi anty wani irin kishine dani,ina da matuqar kishi kan abinda nakeso,ranar
dana ganta wallahi anty ban iya bacci ba"
"To kayi haquri mr kishi....bari kaji me ya faru" ta shaida masa kamar yadda
shahidan ta gaya mata,nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana jin kaman an sauke masa
qaton dutse daga zuciyarsa,sai a sannan ya sami salama
"A rude nake anty,shahida ba ruwanmu bace mu talakawa,hankalina a tashe yake kada
wani ya qwace min ita"dariya ya baiwa anty amina sosai har sai data dara
"karka damu anwar,shahida taka ce in sha Allah,yo shahida muka bata wani bakaiba ai
inajin fiya fiya zata sha ta mutum" sosai anty amina ta baiwa shahidan kunya,har
sai data diba a guje ta shige dakin anty aminan,shima ya miqe ya fice yana dariya.

A dakin ta taddata ta dubeta


"To laila majnun,saikije ku sameshi tunda na kashe case din,saiki kula a gaba"
"Na gode anty amina ta"
"Eh kyace haka mana tunda na dawo miki da hasken rayuwarki ko?" Dariya ta tuntsire
dashi sannan ta miqe ta zura hijabinta ta fice.

Yana tsaye a soron gidan amma qofar fita yake kallo,tadan tsaya kadan a
bayanshi,a jikinsa yaji tana wajen saiya juyo a hankali idanunsa zube fes a
kanta,takowa yayi har sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sannan ya tsaya,a
hankali cikin wata murya dake cike da mayen so yace
"Nayi kewar wannan kyakkyawar fuskar,wannan ruhin ya hana ruhina samun barci bare
ya samu salama,na cika da fargabar cewa na rasa hasken idaniyata,ashe abun duka ba
haka bane" sosai kalamanshi suka sanyaya mata rai cikin daqiqu kadan,tayi qas da
kanta tana fidda murmushi
"A'ah dago kanki sosai don na samu qwarin gwiwar fada miki albishir din danaso yi
miki tun rannan mai mota ya korani"
"Don Allah ka daina zancan mai motar nan honey haba"
"Na daina" ya fada yana murmushi
"Na samu aikin kamfani Allah ya taimakeki...wani maqocinmu ne ya sama min,kwana
goma sha biyar zan dinga aikin kwana,kwana goma sha biyar aikin wuni,zasu dinga
biyana albashi duk wata dubu sha biyar" sosai fuskarta ta washe da fara'a tana jin
farinciki na ratsata,tana jin burinsu ya soma daukar hanyar cika,rasa inda tsoma
ranta zatayi har sai daya tsaya yana kallonta cikin mamaki,sun jima a soron gidan
anty aminan kafin ya sanyata ta tattaro kayanta tazo su wuce gida,napep ya tsaida
musu har qofar gida,sanda suka sauka ta zaro kudi zata biya ya harareta ya ciro
daga aljihunsa ya biya,dariya kawai tayi,ko yaya idan yana da kudi ko iyakarsu
kenan jikinsa baya yarda tayi masa hidima da kudinta,nan ma sun dan jima kafin suyi
sallama ta wuce gida shima ya wuce.

Cikin taimakon Allah ya soma zuwa aikinsa,saidai babban qalubalen daya soma
fuskanta shine na rashin kudin mota,tafiya ce mai nisa tsakanin unguwarsu zuwa
kamfanin haka yake niqar gari ya tafi,duk da cewa ya saba tun sanda yana makaranta
amma tafiyar bata kai ta makaranta nisa ba,sai kuma abincin da zaici shima saiya
dawo zai jiqa kwakinsa yasha musamman idan aikin dare yayi zai dawo da safe,duka
wannan bai dameshi ba tunda yasan cewa komao lokacine,hakanan bai yarda shahida ko
anty usaina sun sani ba saboda baiga dalilin da yana namiji zai dinga daura nauyi
wa mata ba,a haka ya cinye watanshi guda,saidai kafin cikar watan ya fada yayi
baqi,hakan ya sanya shahida ta sanya ayar tambaya a kanshi.

Ranar daya amso albashinsa yazo da daddare,duka ya zube mata albashin nasa yana
dubanta
"Me zanyi dashi honey?" Ta fada bayan ta gama saka musu albarka
"Inason ki dauki iya abinda ranki yayi miki,a matsayin albashin mijinki na farko"
kai ta girgiza tasan ko tace masa a'ah cewa zaiyi bata isa ba saiya dauka,saboda
haka tasan maganinsa.

Da fari ta ware wasu kudaden tace wannan kudin kayan abinci da zai siyo ya
dinga dafawa yana tafiya dashi kamfani,ta sake ware wasu tace ya sake dinka kaya
kala guda duk wata zai dinka kala daya,ta sake ware wasu tace ya riqe ya kashewa
ne,sannan ta cire wani abu a ciki tace wannan ya kaiwa anty usaina ita yafi
cancanta ta sanya albarka,next month kuma idan ya sake amsa to ya fara ajiya saboda
lalurorin yau da kullum,duk sai data gama kasafin ya cakude kudaden waje daya
sannan yace
"Qurun qus kin gama tatsuniyar taki?,toni ba haka nakeso ayi ba,da safe me mike ci
idan zaki makaranta?"baki tadan cuno
"Kome meye ya samu"
"Good" ya fada yana cire wasu kudi ya aje
"Indomie da qwai nakeson ki koma ci" idanu ta zaro tana kallonshi baki bude
"Honey...me kake fada ne?"
"Abunda kunnuwanki suka jiyr miki.....wannan kuma kudin kashewarki na wata
gud....."
"Kaga...don Allah ka tsaya ka daina wannan lissafin mana" nan sa'insa ta kaure
tsakaninsu,da qyar ya yadda da nata lissafin bayan ta masa alqawarin wata na gaba
ta yadda za'a sata cikin kasafin,saidai duk da haka yayi cancel kudin kashewarsa ya
bata dole ta amsa saboda ya kafa mata sharadi.

Koda ya kaiwa anty usaina ma itama cewa tayi ba zata soma amsa yanzu ba,ya
aje wajensa zata masa magana idan lokacin daya dace yayi,haka ya dawo dasu ya
miqawa shahida
"Shikenan...zan saya banki na dinga tara maka,duk sanda kake da buqata saika amsa"
washegari kuwa ta sayi bankin ta zuba masa harda kudin daya bata,ta nuna masa
sannan ta roqeshi
"Don qaunar da kakemin kada kace a'ah,za'a tara ne ka siya abun hawa ko keke ne,ko
baka fadimin ba nasan tafiyar qafa kake" da qyar ya amince da shawararta,donshi a
son ranta tayi hidimar gabanta kawai dasu.

Wata hudu cif da fara aikinsa komai ya soma tafiya babu laifi,ta wanni
fannin abubuwa da dama sun soma sauqi,cikin godiyar Allah da yadda da cewa komai
lokaci ne.

Cikin haka aka fitar da ankon bikin umaima,wadda take cousin ce a


wajenta,ranar data kawo musu ankon wuni tayi a gidansu,har dare tana nan,sanda ta
tashi tafiya anwar yazo shahidan na wajensa,mubina ce ta rakota tana nanata mata
idan ta tashi dawowa ta kawo mata alawarta,qarasawa tayi wajensu shahidan tana mata
sallama daga bisani tace
"Ina zuba ido saikinzo siyan ankon,kuma wlh baki isa ba ba wani daya da zaki duka
biyun zakiyi"
"To ummata" ta fada tana hararta,don batason ta tada zancan a gaban anwar din,sun
riga da sun gama maganar su tun cikin gida,da haka sukayi sallama umaima ta wuce.

"Wai ina bankin nan kuwa?"


"Yana cikin gida"
"Idan yana kusa daukomin shi idan yana kusa" bata ce komai ba ta shige gidan ta
fito dashi,bankin qasa ne ya amsa saiya sakeshi ya fadi take ya fashe kudin ciki ya
bayyana,baki ta bude tana zaton itace bata bashi dai dai ba ya riqe ya fadi
haka,sai taji yace
"Yauwa yayi dai dai,tayani qirgawa" cikin mamaki ta duqa ta soma tayashi hada
kudin,bayan sun gama hadawa ya miqa mata yace ta irga,cikin murna da mamaki tace
"Da gaske ne kudi wawayene....ban zaci zasu kai haka ba wallahi" murmushi shima ya
saki,walwalar da take kawai ta isheshi farinciki
"Kije ki sayi ankon ko kala nawa ne,saura kiyi dinki,idan ba zasu isa ba kiyimin
magana" ranta ta ba'ta sannan tace
"Me kake fada ne?,kudin keken naka zaka bani kace nayi anko bayan sunkai kudin keke
sabo harda canji?,kuma ma tuni umma tace zatamin daya abba guda daya"
"Duk bansan wannan ba....abinda kawai na sani shahidana zata saka kaya kamar yadda
kowacce mace zata saka...kada kice zakimin musu indai baso kike raina ya baci"
kaita duqar
"Allah ya baka haquri" dole ta fidda kudin ta sayi ankon kala biyu mayafi da abun
daurawa,cikin sati uku suka shiga hidimar biki amma hakan bai hanata ganin anwar
ba,shima hakan ya masa dama tunaninsa rashin ganinta.
Ranar da za'ayi dinner tun safe suna gidan kwalliya,qarfe biyar da rabi na
yammaci ya kirata yazo ganinta tana ina,itama yana ranta don jiya basu samu ganin
juna ba basa unguwar kwata kwata suna can aikin snacks,ta kwatanta masa gidan
kwalliyar,ya gane gidan saboda cikin anguwarsu ne.

Sanda ya iso tuni an gama mata tata,zata wuce kuma gidan bikin ta saka
kayanta kafin a soma dibansu zuwa wajen da za'a gudanar da shagalin.

Dan kwalinta a hannu ta fito soron gidan don kada ya bata mata
kwalliyarta,dubansa tayi yadda yayi mata kyau cikin wani sabon yadi blue
black,wanda aka yiwa dinki irin na matasan zamani,bata mancewa da ita yayi shawara
kafin ya sayi yadin ta kuma zabar masa dinkin qarshen wata sanda aka biya salary ya
cira a ciki yayi,anwar nada wata baiwa ta daban,idan yayi dressing kai kace shi din
wani ne,daga kai yayi daga danna wayarsa da yake yana dubanta,subhanallah ya fada a
sarari,wani azababben kyau yaga ta qara masa,kai kace ba shahidarsa bace,sai yayi
sak yana ci gaba da dubanta,abun ba qaramin dariya ya baiwa shahida ba har sai data
d'an dara
"Yaya anwar wucewa zanyi fa ana jirana.....tun daxun kake kallona sannan kuma kai
baka ce komai ba" ta fada a shagwabe tana langabe wuya,ajiyar zuciya ya sauke
sannan ya dubeta
"Ba inda zan barki ki fita a haka shahida....gaskiya zuciyata ba zata iya jurewa
wasu su kalleki a haka ba a filin Allah wajen bikin dake cakude da maza da mata"
"To a yaya kakeso na fita?" Ta fada tana cuno baki wanda hakan ya sake tafiya da
imaninsa,dan qaramin bakinta mai dauke da pink din labba yasha maroon din jambaki
"Mafita kawai ki wanke fuskarki" idanu ta zaro tana dubanshi
"Haba yaa anwar....haba don Allah" ta fada kaman zatayi kuka tana dan buga
qafarta,fuskarsa ya hade sosai,harga Allah yana da wani irin kishi akan
shahidan,yana jin kaman zai mutu idan wani ya zuba mata idanu bare akai ga batun
furta yana sonta
"Ashe kuwa zaki shekara a soron nan,don na rantse ba zaki matsa ko inaba indai
fuskarki da wannan kwalliyar" tasan cewa da gaske yake saita rasa ya zata
masa,hakan yasa ta juya ciki ta yiwa amarya umaima magana,ita tazo ta roqa mata
alfarma wanda daga qarshe yace saidai ta cire eye lashes din da aka qara mata don
nata ma ya isheta,sannan kuma a goge wasu abubuwan da aka sa mata a fuska,saida
akayi hakan sannan ya qyaleta,duk da haka a gaba ya sakata tana gaba yana
bayanta,sai faman sakin ajiyar zuciya yake,duk da an rage kwalliyar gani yake kowa
ma kallonta yake,adaidaita ya tare mata bai barta ba sai daya rakata har qofar
gidan bikin,yana mata sallama zai juya itama ta tubure kan dole yaje wajen
bikin,yasan da biyu tayi hakan don bai fiya zuwa wajen fate fate ba,to amma abinda
bata sani ba gata tayi masa,don har yanzu hankalinsa bai aminta ba da zuwanta wajen
ita kadai,gani yake tafi kowacce mace kyau,hakanan idanun kowanne namiji yana
akanta
"Zanje na dawo,idan kun gama shiryawa kimin magana" tana masa dariyar cin galaba ta
shige ciki.

Qarfe shida aka soma daukan 'yammatan,a sannan tuni ta yiwa anwar waya,shida
da rabi ya kirata yace ta fito yazo,su biyu ne ita da 'yar anty umma yayar
ummanta,ga mamakinta yana jingine jikin wata qaramar mota mai kyau qirar kia,ya
sauya shigar jikinsa,wannan dinma yadine wanda tare ya siyesu da wancan,saidai
wannan ruwan madara ne lallausa,shima bamai tsada bane amma sai taga kaf mazan
wajen ba wanda ya kamoshi a kyau duk dacewa jayan jikinsu yafi nashi tsada nesa ba
kusa ba.

Shi dinma gaba daya saiya daina ganin 'yammatan dake kai kawo a wajen,ita
kadai take gani cikin dinkin ankon da ya amshi fatarta fiye da zato,kowa idonsa
cikin na dan uwanshi a haka ta qaraso,baice mata komai na sai gaban motar daya bude
mata ta shige,shima ya bude sit din driver ya zauna bayan kubra 'yar anty umma ta
shiga gidan baya ya tada motar.
Saitake jinsu yau kaman rana ta musamman ce a wajensu,wani farinciki taji yana
ratsata,ta samu kanta da addu'ar Allah ya shiga lamarinsu ya buda ma anwar
din,motar tayi masa kyau qwarai da gaske kaman tashi
"Wani abokina ne ya dage lallai lallai yau sai na amsheta na dana,tun tana sabuwa
yamin tayi ban taba danawa ba,kinga kuma bai kamata naqi ba karya dauka wani abun
ne na daban kuma" kai ta gyada yayin daya dinga satar kallonta lokaci zuwa
lokaci,har bintu ta fahimta ta d'an masa tsiya,kunya ta sanya shahida daukan wani
plate data gani ta saka jikin redion motar,tadan qaro volume sanda taji batajin me
yake fita daga cd din,waqa ce ta hamisu breaker waqar jarumar mata,sautin waqar ya
ratsa motar,kidanta ya fita sosai ta speakers din motar ya karade ko ina,har ta
saka hannu zata kashe anwar ya daga mata hannu alamar ta barshi,shuru ya ratsa
motar saidai gaba dayansu waqar na ratsasu ne,ji suke kaman su suke rerawa
junansu,shurun yaci gaba da yi musu jagora har zuwa inda za'a gabatar da bikin.

Sai daya rakata har ciki yayi mata mazauni,ya kuma gaya mata bai yadda da
shiga rawa ba sannan ya fito ya dawo cikin motar ya zauna,wanda ya faka ne a bakin
titi,sai yabar murfin motar a bude iska na shigowa qafarsa daya a waje.

Awa guda da fara gabatar da bikin yana zaune yasa sauraren redio
"Yauwa ga wani can....salamu alaikum" yaji an ambata,kanshi ya dago yana dubanta
sannan ya amsa,matashiyar budurwa ce wadda a qalla ta doshi shekara ashirin da
d'aya,sanye cikin doguwar riga da siririn mayafi,fuskarta saye da tafkeken
glass,gabanta ne yayi mummunar faduwa saboda cika mata idanu da kwarjini da yayi
mata,uwa uba kyau data jima bata ganshi tattare da wani d'a namiji ba,da qyar ta
tattaro miyan bakinta tace
"Don Allah bawan Allah ko zaka taimaka ka duba mana motarmu?" Tayi maganar tana
qare masa kallo ta cikin glass dinta,sai daya kashe redion sannan yace
"Me ya sameta?"yarfar da hannu tayi cikin yauqi
"toh wlh ban sani ba,ina cikin driving ta soma slow sai kuma ta tsaya gaba daya"
dan jim yayi kafin ya jinjina kai ya fito daga motar ya rufeta sannan yayi gaba
zuwa inda motar tata take.

Tsahon wani lokaci yana qoqarin ganin ya gyara saita tashi saita sake
mutuwa,saboda haka ya dago yana goge hannunsa da tsumma
"Gaskiya dole sai bakanike yazo"ya fadiwa nafisa dake gefe tsaye suna qare masa
kallo ita da qawarta mima
"Ya salam...bari na kirashi Allah yasa yana kusa" ta ciro tsadaddar wayarta ta soma
nemanshi,cikin sa'a yace yana kusa ta bashi adress din inda motar take
"Idan ba damuwa ko zamu dan zauna cikin motarka kafin ya iso saboda zama a wajen ba
dadi" nafisa ta fada sanda anwar ke komawa zuwa cikin tashi motar,tsayawa yayi ya
waiwayo,kaman yace a'ah sai yaga mata ne bai kamata ya barsu tsaye ba,tunda motar
tasu ba zasu iya zama cikinta ba,shi kuwa diya mace ako ina take yana da kishi da
qoqarin kare mutunci da martabarta bakin gwargwado koda bai santa ba
"Ba damuwa" ya fada yana sake yin gaba,idanu suka hada da mima ta kashe mata ido
gami da sakin murmushi suka bi bayansa.

Ya tsammaci duka baya zasu shiga,sai yaga mima ce kawai ta shiga bayan,nafisa
ta shiga kujera mai zaman banza,sai data zauna sosai sannan ta waiwayo ta dubeshi
tana murmushi
"Suna na nafisa....kaifa?"
"Muhammad anwar" ya bata amsa a taqaice,idanu ta lumshe
"Nice name...sunan ya dace da maishi" saiya waiwayo ya dubeta kafin ya dauke
kai,murmushi ta sake saki
"Dan wanne anguwa ne kai?,Allah yasa ban matsanta maka ba da tambaya" kai ya
jinjina sannan ya gaya mata unguwar da yake
"Kai ai bamu da nisa sosai" itama tasu unguwar ta fada masa,kusan duk unguwannin
nasu maqotan juna ne,shuru ne ya sake ratsa tsakani yayin data lula duniyar tunanin
yadda zata sha kan anwar,don ba zata cuci kanta ba kallon farko taji anwar yayi
mata,infact ma zata iya cewa ta kamu da sonshi ne kai tsaye.
Isowar mechanic din shi ya katse duk wani tunaninta,hanya daya ta rage mata
saboda haka ta miqa mishi wayarta
"Idan ba zaka damu ba ka sakamin numberka mana,saboda nayi maka godiya" kai ya
girgiza
"Basai kinmin godiyar komai ba" kai ta langabe
"Ya zama dole na gode maka,saboda alkhairi kayi min" baison jan zancan saboda ya
gaji da surutunta,saboda haka ya amshi wayar daidai sanda shahida ke takowa zuwa
inda motar take,tana iya hango komai saboda akwai haske cikin motar,mummunar
faduwar gaba ta samu,saidai ta kasa hana kanta qarasawa wajen,saitaci gaba da
takawa harta isa bakin motar,daidai sanda ya gama saka mata number din ta amsa tana
murmushi tace
"Na gode,sai gani na gaba" ja baya shahida tayi a hankali sanda nafisa ke fitowa
daga gaban motar,idanunsu suka hadu dana juna,kallon kallon suka yiwa juna kafin
nafisan tayi gaba mima ta rufa mata baya,binsu shahida tayi da kallo har suka
bacewa ganinta cikin duhuwar wajen sannan ta dawo da dubanta ga anwar wanda sai
sannan ya lura da tsaiwarta a wajen.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON
GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi
SHARING*🙏🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

1️⃣ 1️⃣
*Alqawarin Allah*
1️⃣1️⃣

"Wacece?,me takeyi a nan wajen?" Ta tambaya tana daga tsaye ba tare data shigo
cikin motar ba
"Motarsu ce ta lalace nayi qoqarin gyara musu,bata ma gyarun ba sai data kira
bakinikensu"
"Shine tazo kusa da kai ta zauna?,har kana amsar wayarta tana jifanka da murmushi?"
"Shigo tukunna sai muyi maganar" ya fadi yana bude mata murfin motar sosai,kaita
girgixa sai kawai ta juya tabar wajen idanunta cike fal da qwalla,cikin hanzari ya
fito don ya cimmata saidai ina tuni ta kutsa cikin mutane ta bace masa bat,haka ya
qaraci nemanta bai ganta ba,dole ya dawo gaban motar ya dinga jera mata kira amma
bata daga ba.

A hankali wajen ya soma yoyewa,ya sake shiga ya dubata amma kome kama da ita
bai gani ba bare ita
"Ya salam shahida....ya salam" ya dinga furtawa a jejjere sanda yake tuqa motar
zuwa hanyar gidansu amaryan,ba qaramin tashi hankalinsa yayi ba,bai samu 'yar
nutsuwa ba sai daya isa gidan yasa aka shiga aka binciko masa aka tabbatar masa ta
dawo gidan nan sannan ya saki ajiyar zuciya,nan kuma ya shiga jera aiken
kiranta,saidai mirsis taqi zuwa,ganin dare ya soma yi ya sanyashi haqura kan tilas
yaja motar yabar unguwar,bai je gida ba sai daya soma kaiwa abokinsa matar,yace
daya barta ma sai sun gama bikin don tafiya ma zaiyi ta sati guda,murmushi ya saki
wanda kusan na yaqe ne,donshi kusan sam baiji dadin hawa motar ba,yana ganin kaman
itace silar faruwar komai,inda ace a motar haya suka tafi shikenan nafisa ba zata
ganshi ba,da amotar haya suka tafi nafisa ba zata rabi wurinsa ba saidai wajen
wani,don bashi da gurin da zata roqi alfarmar zama har shahida ta gansu tare,da a
motar haya ne da tuni tare zasu dawo da shahidanshi su rabu cikin farinciki sa
walwala.

Ta gefan shahida kuwa hankalinta a tashe,gani take kaman za'ayi mata qwacen
anwar din,duk kwanan duniya idan ta kalli anwar din sai taji fargaba ta
cikata,anwar nada kyau kwarjini da cikar zatin da zai zama abun kwadayin mallakar
kowacce mace,kallo daya ta yiwa nafisa ta tabbatar 'yar masu dashi ce,idan hakan
yayi nasarar janye hankalin anwar fa tayi yaya?,da sauri ta kori wannan tunanin
daga ranta,don fatan dorewar hakan,a ranar da qyar ta sami bacci duk da wayarta na
silent tana da yaqinin ta tara miscal na anwar din.

Itama kusan tubure masa tayi yadda ya mata kwanaki,qarshe dai saida suka
dangana da anty amina tayi sasanci kamar yadda ta saba,zuwa lokacin ba qaramin
jigata yayi ba,wanda hakan ya faranta ran shahida ta wani gefe,tunda ko babu komai
ta sake sanin mizanin da zata dora soyayyar da yake matan.

A haka rayuwar wannan masoya take ta kuma ci gaba da gudana,kowanne cike yake
da tsananin so qauna da kuma kishin dan uwanshi,kowannensu cike yake da buri da
fatan farantawa dan uwanshi,har zuwa sanda shahida suka soma shirye shiryen yin
candy,a boye ba tare da saninta ba don yasan zata iya hanashi anwar yasa akayi mata
jaka da memo,yace bazaiyi calender ba bare wani qato ya rataye a dakinsa ya dinga
kalle masa mata,ko memo dinma babu hoto a jiki,yayi mata key walder hakanan ya soya
kayan da zata saka ran walima complete,dukka yayi hakanne bada saninta ba don
yanason mata suprise ne.

_*TAURARUWA MAI WUTSIYA*_

Tsaye take a hamshaqin falonta gaban window,wanda yaji komai da komai na


kayan alatun more ruwa,falone dan qarami saidai ya wadatu da dukkan wani abun
buqata domin hutawa da nutsuwar ruhi,tana sanye da riga da skert wanda iyakar skert
din qaurinta
"Ina jinki mema....na zaqu naji daga gareki,wallahi tun ranar dana soma ganinshi
har yau ban sake samun nutsuwa cikin rayuwata ba....duk iya qoqarina na ganin na
samu zuciyarsa abun yaci tura,yana da wata izza kaman d'an wani,kwarjininsa shike
sake dakusar dani,inajin sonshi ya kaimin ko ina cikin jiki da ruhina" tayi maganar
duka tana tsaye jikin window din ba tare data juyo ba,idanunta na farfajiyar gidan
data wadata da korayen tsirrai.

Tabe baki mima tayi,ita duka mamaki ya cikata,ta yadda feena ta fada qaunar
talaka matsiyaci kaman anwar din,ta kuma fita hayyacinta lokaci guda,haka kawai
tana tsaka da more rayuwarta,to amma ita nata yi mata aiki ta kuma biyata,indai
zata biyata din ai shikenan
"Ba haka kawai kika kasa samo kanshi ba ai feena" meman wadda ke zaune kan daya
daga cikin kujerun falon qafarta daya kan daya tana karkada takardar hannunta ta
fada,da hanzari nafisa ta baro inda take ta qataso gaban feena sannan ta yiwa kanta
mazauni kan wata kujerar daban tana duban feena idanu bude
"Kaman yaya?,meye dalili?" Wani shu'umin murmushi ta saka tana qiyasta kudin da
zata tatsa wajen feena a yau sanadin wannan zazzafar jaridar da zata saida mata
"Zaki iya tuna yarinyar da kukayi kallon kallon da ita ranar da muka zauna
motarshi" yatsanta manuni ta daga sama da sauri kaman maishirin bada amsa cikin aji
"Exactly....na tunata,tun ranar yarinyar na tsaye cikin raina...na rasa wacece mai
shegen kyau da izza haka,da farko nayi tunanin qanwarsa ce saikima naga basuyi kama
ba tako ina"
"Right....budurwarsa ce" gaban feena ya fadi ta zaro idanu
"Wait....da saura fa" mima ta fada tana dariya qasa qasa sannan ta gyara zamanta
"Idan kin taba karanta labarin soyayyar romio da Juliet wannan sun wuce haka,qauna
ce irin wadda zata bawa bahaushen mutum mamaki,son junansu suke kaman tare aka
haliccesu,daya baya komai saida shawarar daya,daya baya iya tafiyat da komai saida
daya,bari dai na baki a taqaice a dunqule,sun narke sun zama abu daya...."
"Dole su rabu su zama abu biyu kuwa...na fahimta,wato saboda itane na kasa cimma
burina kenan?" Ta tambayi mima kai tsaye,kai ta jinjina tana lumshe idanu sannan ta
bude
"Qwarai kuwa....amma saidai karki damu akwai mafita" ta ambata tana warware
takardar hannunta,daki daki ta soma karanta mata abinda shahida tafiso da wanda
bataso har sai da nafisa ta gaji daji ta daga hannu tana dakatar da ita
"Jin wannan abun dame zai qare ni?,qara qonamin rai kikeson yi mima"
"Kina da gajen haquri inda matsalarki take kenan....amma tunda kina ganin haka
shikenan bari na wuce" ta fada tana ninke takardarta,caraf ta kama hannunta
"Mtsweeww,banason ko jin sunanta ne wlh,zauna mu qarasa" bata wani jaa ba ta zauna
din don tana lissafin abinda zata samu ne,taci gaba da karanto mata inda gabar
qarshe take dauke da
"Ta tsani cin amana,ta tsani munafurci,ta tsani ta zauna dakai zuciya daya kai kuma
ashe da zuciya biyu kake tare da ita" tana kaiwa nan ta daga kai tana duban shahida
sannan taci gaba da karatunta,fagen anwar ta shiga,abinda yakeso da wanda bayaso
inda shima tashi gabar qarshe ta zama
"Ya tsani mace mara kamun kai,ya tsani macen dake bin maza,sannan yayi masifar
tsanar mace 'yar shaye shaye" ta sake yin shuru tana duban feena,dan jim tayi
sannan ta gyada kai tana sakin murmushi sosai tana nuna mema
"Shegiya mima,sai yanzu na gane...ko shahidan yana tsoron kaidinki qarashe
bayaninki" sosai taji dadin yadda take sake samun karbuwa wajen feena koda
yaushe,ta ninke takardar sannan ta sake tattara nutsuwarta
"Yarinyar tana da ciwo tana da matsala cikin rayuwarta,duk da har yanzu ba'a gano
wace damuwa gareta ba,amma zamuyi amfani da wannan damar mu sanyata ta zama 'yar
maye,kinga mun samu matakin farko na rabasu,zai zama matakin farko ne saboda wanna
kadai bai isa ya rabasu ba bayan bai kamata da wani laifi ba bayan wannan,itama
bata kamashi ba,bayan ta zaba tantiriyar mashayiya zamu qara mata da sharrin bin
maza...wannan kuma aikin wadanda suka san kan na'ura mai qwaqwalwa ne,zamu saka
mata cewa baya sonta ita kuma yana tare da wata,duk zan kula da yadda komai zai
kasance,naki kawai ki saki kudi ki zuba idanu" murmushin nasara ya subucewa
feena,ji take kaman ta samu anwar ta gama,dukka kudin da yayi saura a jakarta ta
zazzagewa mima,ta kuma yi mata alqawarin wasu
"Ya...zaki dinner dinsu mu'az dinne" idanu ta fiddo
"Me zai hana?,ai har na shirya qaryar da zanwa momy ta barni na fita,kedai jirani
na shirya" cikin mintina qalilan ta fito cikin wasu matsiyatan riga da
wando,hannunta riqe da burmemen hijab da take qoqarin sakawa mima na zaune na sheqa
dariya,ta zuba duk kayan makeup dinta cikin haka ta maqaleta cikin hijabin sannan
ta dubi mima
"Mu hadu a bakin gate,don da mun shiga tare ta ganki zata saka ayar tambaya" haka
kuwa akayi,ta isa wajen momy ta shirya mata qarya ta yadda ba yadda za'ayi ta
ganota sannan ta fice suka hadu da mima,tun a cikin motar ta cillar da hijabinta
tahau tsara kwalliyarta yayin da mima ke driving.

Cikin nasara da taimakon ubangiji ta kammala rubuta jarabawarta kaf,wanda a


ranar sukayi bankwana da dalibai da sauran malamai 'yan uwansu,a daren ranar anwar
yayi shiga ta musamman yazo don tayata murna,ya kuma bata duk wani gift daya tanada
saboda ita,sai data shiga dakinta tana dubawa abun ya sake burgeta,duk da anwar ba
wani mai hali bane amma Allah ya hore masa tsari da iya siyayya,komai daya bata ya
burgeta,ta jima tana kallon wani zobe,duk dana azurfane amma an qawatashi qwarai
dole ya burgeka,zanen heart ne a jiki amma heart din rabi ne,murmushi ta saki tana
sakashi cikin yatsunta,yayi masifar yi mata kyau,saita tattara kayan ta kaiwa
ummanta wanda ita kanta ta yaba da qoqarinsa kaman yadda abbanta ya yaba,hakan ya
mata dadi qwarai,ya kuma bata tabbacin kenan bata da matsala bata da wani shamaki
da zai hanata mallakar anwar,tuna haka cikin jin dadi ya sanyata qanqame filon da
take kai tana hango kanta da anwar dinta a matsayin ango da amarya qarqashin inuwa
guda.

Cikin farinciki da walwala ta gabatar da walimarta,komai ya tafi lpy ya kuna


qayatar sai jiran sakamako,a sannan komai na tafiyar mata lpy,rayuwar tana hangen
nan gaba kadan zata yi mata kyau,komai zai qarasa dai daita musu,anwar ma an masa
qarin albashi wanda hakan dukka su biyun ya musu dadi.

*SANADIYYA*

Ana tsaka da haka gagarumin tashin hankali da yayi sanadiyyar lalacewa


komai,ya zama silar tabuwar rayuwar mutane da dama,yayi sanadin wargajewar wannan
iyali,ya kuma silar tarwatsa rayuwar shahidan...ya zama wani sanadi na dasa
baqinciki mai tarin daci da zafi a rayuwarta ta faru.

Rayuwa tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta rayuwa ce ta rashin haquri,dauke


kai yafiya da juriya da akasan dukkan ma'aurata da yiwa junansu,fada gaban yaransu
wannan ba wani sabon abu bane tun tasowar shahidan,wanda hakan ya sanya bayan
girmanta abun ya zame mata wani ciwo da duk sanda ya taso mata yake mata zafi da
quna a zuciya,dukkan wani mataki da take ganin ya dace ta dauka a matsayinta na
diya mai qarancin iko da abun fada ta dauka harma wanda ya zarta huruminta amma
babu abinda ya sauya,duk da alqawari da qoqarin sauyawar da suke.

Kwatsam dare guda mahaifinta ya jijjigo maganar qarin aure suna tsaka da
rayuwarsu cikin rufin asirin Allah,wanda hakan ya sanya mahaifiyarta tayi tsalle ta
dire tace batasan wannan zance ba,dalilin daya janyo tashin tashina da fadan da
bata taba gani ya wanzu tsakaninsu ba,hakan ya sanya walwalarta da duk wani kuzari
nata ya ragu,anwar ne mutum na farko dayafu kusanci da ita a sannan shiya soma gane
tana cikin damuww,amma baisan dalili ba,taqi kuma sanar masa,ta yaya zata gaya masa
wannan murdaddeb zance?,tun baya baisan halin da gidan nasu ke ciki ba saboda kare
martaba da qimar iyayenta,duk sanda ta fuskanci akwai rashin jituwa tsakanin iyayen
nata bata taba yin zance a gidansu,a gidan anty amina take zancanta,toko yanzu ma
da lamarin gidan nasu ya lalace can take tafiya ya sameta anan,don ba zataso
wataran wani mummunan abun ya faru a gabansa ba duk da yana musu kallon iyayensa
amma asirin ciki sai hanji.

*MAFARI*

Cikin tashin hankalin da bata taba tsintar kanta a ciki ba ta fito daga gidan
nasu tana hawaye,yau a gidansu a gaban idanunta ake doki in doka tsakanin ummanta
da abbanta?,wanne irin iyaye gareta?,ya ilahi ji take kaman zuciyarta zata fashe,ji
takae bugawa zuciyarta zatayi,ita kadai tasan yadda takeji tana jin kaman zuciyarta
ta kumbura ne ta cika qirjinta,zataso ace zunnurah na nan saidai ina,gidan anty
amina takeson zuwa amma babu ko nutsuwar daukan kudin mota a wajenta,ba tare da
tuna nisa da tazarar dake tsakaninsu ba ta hau tafiya cikin fitar hayyaci da tashin
hanakali bacin rai da baqinciki.

Dawowarta kenan daga inda taje ta sauka a abun hawa,tana yunqurjn shigowa
layin nasu ta hangi kaman shahidan,tayi mamaki don shahidan bata taba zuwa gidansu
ba,hakanan bata yowa layinsu don asalan ita bamai yawo bace,sauri ta qara donta
cimmata,sai taga itace dince kuwa,amma a binda ya bata mamaki hawayen data gani
shabe shabe a i fuskarta,hannu tasa ta kamota tana cewa
"Shahida,meye haka kuka kike fa akan hanya" sai a sannan ta kula da fiddausin,sake
fashewa da kukan tayi,ita koma waye ta gani zata iya fada masa abinda ke damunta ko
zataji sassauci a zuciyarta,abun ya mata yawa,wannan damuwar bata shekara daya bace
ko biyu,ganin haka sai fiddausin ta janye shahidan zuwa gidansu,ta tura gate din
gidan suka shige sannan suka nufi dakinta ta qofar baya,sau tari takan iya shigowa
ba tare da an sani ba saboda gidan nada girma babu laifi.

Kuka take sosai tana cewa


"Na gaji fiddausi....na gaji da wannan bacin ran,ina zanje naji dadi,me zanyi na
samu sassauci?" Murmushi fiddausin ta saki,duk da shahidan bata gaya mata damuwarta
ba amma tana ganin sara ne yazo kan gaba
"Ina da maganin damuwa shahida,maganin da zai dauke duk wata damuwa da kike ciki
komai qarfi da girmanta,zaki jiki fresh kaman yau aka haifeki,nauyi da zuciyarki
keji ya sauka kaman bai taba faruwa ba" idanunta dake jiqe da hawaye ta daga tana
kallon fiddausi
"Don girman Allah ki bani kona daina jin suyar da qirjina yakemin"
"Kwantar da hankalinki basai kin hadani da girman Allah ba" ta fada tana zuge jakar
data shigo da ita,kwalabe ta fito dasu ta hada abubuwan ciki ta gauraya sannan ta
miqawa shahida
"Daga kanki ki shanye nina daga wajen likita nake shi ya rubutamin shi yace maganin
damuwa ne" ba tare da kowanne tunani yazo kanta ba,ba tare da tayi lissafin komai
ba,ba tare da ta jinkirta ba ta daga kai ta shanye duka din kamar yadda fiddausin
tace mata,cikin wasu qananun mintina ta soma jin dummm,ta soma ji kamar ana sauyata
daga tata duniyar zuwa wata daban,ta soma daina gane komai,take a nan ta zube saman
gadon fiddausin,lokaci qanqani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita,dariya
fiddausin ta saki tana rufe kwalabenta tare da maidasu haka tana cewa
"WASA FARIN GIRKI YARINYA".

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA
BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu
tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi
SHARING*🙏🏽
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videoshttps://youtu.be/
T9a10h1Apqs
👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽

*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da
buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

1️⃣ 2️⃣
*Alqawarin Allah*
1️⃣2️⃣
A hankali ta farka tana mutstsuka idanunta da taji sun mata nauyi,sam ta mance
inda take saida tayi dan tunani sannan ta tuna,da hanzari ta tashi ta zauna ganin
gari yayi duhu sabanin sanda suka shigo gidan akwai hasken rana,agogon bango ta
kalla sai taga qarfe takwas,hakan yana nuna kenan ta rasa sallar la'asar magariba
dama isha'i.

Da hanzari tayi nufin tashi saidai gaba daya jikinta a mace yake babu
qwari,daidai lokacin da fiddausi ta shigo dakin dauke da plate din abinci,cikin
murmushi take duban shahida
"Sannu kin tashi?,ya kike jin kanki yanzu fresh ko?" Eh to,lokacin da tayi baccin
ta mance komai,saidai yanzu bayan ta farka komai ya sake dawo mata,saidai baccin da
tayi din ya rage mata bacin rai kadan,amma duka ba wannan ba,sallolin data rasa
lokacin da take bacci su sukafi damunta,saboda haka tace
"Banyi sallah uku ba fiddausi,nunan bandaki na daura alwala"ta fada tana jin babu
dadi har cikin ranta,wannan wanne irin bacci ne?,bata taba irinsa ba,hakanan koda
bata da lafiya bata taba hada salloli ba.

Qofa ta nuna mata wadda take cikin dakin gadon nata,nan shahida ta shiga ta
daura alwala,ta fito sannu sannu saboda yadda takejin jikinta sam.babu qwari,gagara
yin sallar tayi a tsaye saboda yadda takejin qafafunta kamar lagwani tilas ta
zauna ta yita a zaune.

Tana gamawa ta miqe don hankalinta yayi gida kuma,don bata taba tsayawa a waje
har wannan lokacin ba bata koma gidan ba
"Ki tsaya kici abinci saiki sake samun qarfin jikinki"
"A'ah fiddausi gwara na wuce gidan,ba wanda yasan inda naje"
"Shikenan....bari na baki wannan duk sanda kike cikin bacin rai kina sha zaki
baccinki ki manta da kowa" sam a cikin ranta batajin zata sake sha,saboda bata taba
bacci irin haka ba,bugu da qari ita babu wani raguwar bacin rai data ji,don kada ta
gwasaleta kawai ta amsa
"Maganin damuwa ne,zaki samu relief,kin ganni nan,ko bacci ne yaqi daukata saboda
wani bacin rai dana sha zanyi baccina hankali kwance" kai kawa i ta gyada,fiddausi
ta rakota har qofar gida ta wuce ita kuma ta koma cikin saurin don ta labartawa
mima komai da yadda abubuwa suka gudaba,sannan ra fara da turo mata kudin data
alqawarta mata,don syrup dinta dama ya qare tana buqatar siyan wasu ta aje.

Tsakar gidan nasu babu wadatar hasje sosai kasancewar babu wutar nepa,bata
nemi kowa ba don bacin rai ke sake taso mata na yadda tabar gidan nasu dazu,uwa uba
kuma wani sabon baccin take ji,gqba daya jikibta jibsa take kaman an tsoma lagwani
a ruwa.

Kan katifarra ta fada rub da ciki tana lumshe idanu tanajin yadda gabobinta
sukayi rauni,idanun nata na arufe taji wayarta na ruri,sam baki daya ta mance da
ita,ta miqe cikin kasala ta daukota daga saman akwatin kayanta,anwar ne yake
kira,take ta dannan ta kara a kunneta
"Ina kika shiga haka shahida?,nazo gida ana nemanki sama da qasa ba'a ganki ba?,na
kira wayarki ya kusa sau hamsin ba'a daga ba" sai data lumshe ido sannan tace
"Babu inda naje fa,ina gidansu fiddausi,wayar kuma na manta ta ne cikin akwatin
kayana,koka kira babu lallai aji sautinta" ajiyar zuciya ya sauke yana jin tashun
hankalin da yaji dazu na sauka
"Karki sake irin wannan fitar,hankalin umma ya tashi sosai"
"In sha Allahu" ta fada amma cikin zuciyarta tana fadin koma meye sune suka ja
"Ya naji muryarki haka?,lafiya kike?" Saidata gyara kwanciyarta saboda baccin dake
fisgarta tace
"Lafiya qalau....kawai...bacci ne yakeson saceni"
"Bacci yau kuma?" Ya tambaya cikin mamaki,sabida yasan a qalla suna kaiwa sha daya
suna waya,a hakama shike datsewa yace tayi bacci,sam bata iya baccin wuri ba
"Wallahi" ta fada a gajarce,saiya raya a ransa jiki da jinine kawai don haka yace
"Alright,asuba ta gari to,tunda yau anmin ruwa gani da jin muryarki" murmushi ta
saki a kasalance tace masa na gode ta datse wayar ta cillar gefe tana maida kanta
saman filo hadi da sake lumshe idanunta.

Mubina ce ta dago labulen dakin ta shigo


"Yaya kizo inji umma...ashe kin dawo tun dazu ake nemanki" juyar da kanta tayi daya
side din cikin muryar jin bacci tace
"Saida safe...kice mata nayi bacci" yau ba 'yan maganar bane akan mubinan don haka
ta fita ta shaidawa umman tasu saqon shahida,sai gata ra taso da kanta
"Ke shahida....ina kika je tun dazu?"
"Gidansu fiddausi" ta bata amsa ba tare data juyo fuskarta inda umman tata ke tsaye
ba
"Tashi ki dauko abincinki a kitchen kici"
"Ba qoshi" ta sake fada cikin muryar bacci,sam umman tata bata lura da sauyin dake
tattare da ita ba,ga tunaninta fushi tayi kaman yadda ra saba a duk sanda wani abu
ya gilma tsakaninta da mahaifinta,saboda haka ta tabe baki
"Indai ba zaki sawa ranki haquru da kauda da kai ba zakita ganin bacin rai,kije ki
hadu da hawan jini a banza,babanku baida haquri kuma baida adalci,ni kuwa bazan
tsaya ya tauyen haqqina ba atoh" tana gama fada ta juya ta fice,sama sama take jin
abinda umman ke cewa,ga mamakin kanta da kanta,maimakon ta sake jin haushi yadda ta
saba sai taji sam maganganun basu d'a d'ata da qasa ba,baccinta ya fiye mata
komai,idanu ta sake rintsewa ba jimawa kuwa wani nannuyan bacci ya kwasheta.

Kwana biyu tsakani suka ci gaba daga inda suka tsaya,a lokacin tana daki zaune
tana turawa anwar tex,tun tana daure zuciyarta harta kasa,ta toshe kunneta duk a
banza,takai ta kawo cikin dakin ita kadai saita fita,haquri ta soma basu tana kuka
kowa idanunshi ya rufe ba wanda ya saurareta bare yayi shuru ya ragawa dan
uwanshi,dare yaui ba damar ta fice daga gidan ta huta,sai kawai maganin da fiddausi
ta bata ya fado mata ta juya da sauri ta koma dakin ta rufo qofar don sautin
tartsatsin fadan ya ragu,ta duba saman madubinta yana aje ta dauka ta bide ta
shanye gaba daya,ta koma gefan gadon ta zauna tana kuja gamida addu'ar Allah yasa
yayi mata aiki,Allah yasa baccin yazo da wuri ya dauketa kota huta dajin meke
faruwa cikin gidan.

Cikin mintina qalilan bacci ya soma zuwa mata,kafin kace ta sheme a wajen,ba
ita ta farka ba sao washegari da safe bayan gari yayi tarwai rana ta take,da
hanzari ta miqe tana tariyo abinda ya farun,sosai taji dadi har ranta da Allah
baisa taji qarshen masifar ba,don haka batasan ya aka qarke ba,ta bude sakatar
dakinta ta fita tsakar gidan nasu,a share yaje fes saidai gidan nasu yayi tsit
alamun ba kowa ko duka yaran basa nan,tasan da hakan don lokacin tafiya makaranta
yayi,saita tari ruwa ta shiga bandaki,wanka tayi don tafijin qwarin jikinta sannan
ta hado da alwala ta fito ta shiga dakinta ta sauya kaya ta tada sallar asuba da
bata samu tayi ba,bayan ta kammala ta wuce dakin ummanta,ta sameta a zaune a
falonta tana tsintar shinkafa,ta dago suka hafa idanu,kallo daya zaka mata kasan
ranta a masifar bace yake,wanda tasan hakan bai rasa nasaba da kace nacen da sukayi
jiya da babanta,gaidata tayi ta amsa sama sama
"Wato don wulaqanci da iskanci da asuba kina ji ana bugun qofarki ki tashi kiyi
sallar asuba kikaqi ko?" Ita sam batasan anyi hakan ba,batasanma yaushe aka buga
qofar tata ba,amma kawai sai tace
"Kiyi haquri umma,bacci ne yaci qarfina"
"Oho ke kika sani,naga alama kin fara goyawa mahaifinki baya,to wallahi kikace haka
zakiyi wahala zakisha" ko kadan ranta bai baci ba sai tace
"Kiyi haquri" banza tayi da ita,sai bayan mintina wajen goma sha biyar sannan tace
da ita
"Saikije ki dauki abun karyawarki a kitcheni,idan kin gama ki kunnan wuta na dora
shinkafar nan"
"Toh" ta fada tana miqewa zuwa madafa.

Tana cin abincin tana tunanin abinda ya farun jiya,gaskiya baqaramin rage
mata radadi maganin yayi ba,ko banza batasan qarshen abun ba,hakanan bata ji wani
bacin rai ba,saita yanke kawai yau ta sake zuwa gidansu fiddausi ta gaya mata inda
ake saida abun ta siya,duk sanda suka soma balahirarsu tasha ta samu bacci ta
qyalesu.

To tun daga lokacin shahida ta shiga ruwa tsundum,batasan illa da giraman


abinda takeyi ba,batasan yadda take rushe rayuwarta ba,kawai ita ta bada amanna ne
tana shan maganin matsalarta,batasan tana sake qarawa rayuwarta matsala bane,tana
tunanin maganin bacci kawai takesha,batasan ta fada shaye shaye bane tsundum,wanda
ba wanda ya kula da sauyawarta banda anwar,lokaci zuwa lokaci idan yazo fira
wajenta da zarar sun fara zata soma gyangyadi,haka zai mata sallama ya tafi,ya
nazarceta sosai baiga wani abu daya sauya dangane da ita dinba bayaga yawan jin
baccin,hakan ya sanya yayi tunanin ko shawara ce da ita?,baiyi qasa a gwiwa ba ya
amso mata magungunan gargajiya harda na sanyi,ta amsa dai kawai ta jibge taci gaba
da sha'aninta.

Zuwa sannan sam abinda ke faruwa tsakanin mamanta da bbanta ya daina


damunta,wani lokaci takan iya shigowa gidan ma ta taddasu sunayi tayi wucewarta
daki ta kwanta abinta tahau baccinta,dukkan wadan nan sauye sauyen basu ganshi
ba,ga ummanta kawai tayi mata shaidar ta koyi nunqufurci tana goyon bayan
babanta,yayin da abban nata yake ganin hankali tayi ta daina damuwa da al'amarin
dake faruwa.

Ta bangaren fiddausi kuwa da akayi amfani da ita don cusa shahida cikin
wannan harkar nasara ce a wajenta,don duk yadda aka tsara abun ya tafi dai
dai,hakan yayi sanadiyyar samun kudade mai yawa daga wajen nafisa,plan dinsu na
gaba shine cusa samari masu kudi 'yan duniya rayuwar shahidan,saidai duk yadda
sukaso ga ganin hakan ya yiwu abun bai kasance ba,saboda sam shahidan tun asali a
jininta yake,bata da kule kule,haka suka qaraci shirya plan din nasu suka
gaji,hakan ya sanya suka sauya dabara,suka sake sabon shiri sabon taku da sabon
tsari,wanda suke fatan shine mataki na qarshe da zai tarwatsa mu'amalar dake
tsakanin anwar da shahida komai qarfinta.

*_SHARRI KAYAN KWALBA_*

Kusan a yanzu babu wata qawa kuma aminiya da shahida ke da ita data wuce
fiddausi,kusan koda wanne lokaci suna tare,hudubar farko data soma yiwa shahida
shine anwar ba son shahidan yake ba,yasha fada cewa mai zaiyi da yarinyar da
iyayenta suka kasance tamkar karnuka saboda fada,sosai xancan ya daki
shahida,saidai iya saninta anwar baisan badaqalar dake faruwa a gidansu ba,don tuni
ta yanke yin zance dashi a gidansu bama gidansu kawai ba unguwar baki d'aya,yanzu
kacokam gidan anty amina take tafiya su hadu a can,saidai kuma akace yau da gobe
tafi qarfin wasa,sai maganar ta dinga tsayewa shahidan aranta,duk da cewa ko daya
bata yarda ba bata gasgata ba,hakanan ba abinda ya ragu game da son anwar daga
zuciyarta,duk sanda taso yin wani dogon nazari kan maganar fiddausi na kadar da
hankalinta ta bata wani abun mayen sai zancan yasha ruwa.

Ta gefan anwar gaba daya hankalinsa ya ta'allaqa ne kan nemawa shahida gurbin
karatu cikin daya daga cikin makarantun gaba da secondry dake jahar kano tunda aka
yi musu qarin albashi,bai gaya mata ba saboda yana sonne yayi mata ba zata,yaci
wahala ya kashe kudi kafin komai ya kammala.

Ana ya gobe zai shaida mata yana gurinta,ranar sun jima tare suna hira,sunyi
hirar da suka jima basuyi irinta ba,kowanne yan jaddadawa d'an uwanshi yadda yake
jinsa cikin jikinsa da zuciyarsa,sun tsokani juna sunyi raha wasa da dariya
sosai,har anwar ta saka ranakun cikin daya daga cikin kundin ranakun farincikinsa
da bazai taba mantawa dasu ba,ta bashi hotunan data dauka musamman sabodashi wanda
ba qaramin kyau tayi cikin hotunan ba,kyanta ya fita muraran,ya qurawa hotunan
idanu yaga kada kai
"Wannan hotunan bazan iya maidasu enlargment ba" dubansa tayi tana narke ido tana
dubanshi
"Saboda banyi kyau ba ko?" Dariya ya saki yana cewa
"Dama akwai wani lokaci da zaki qiyin kyau a idanuna koda wankan kashi kikayi?"
Dariya sosai ya bata har shima ya tayata darawa
"Dama ana wankan kashi ya anwar?" Girarsa ya dage
"Eh waikoda ace anayi din...kyan da kikayi ne shahida yayi yawa,ina kishin mai
aikin budawarma ya ganki" baki ta bude tana dubanshi
"Ya anwar"
"Shahida....kaman har yau kina kokwanton yadda nake sonki da kishinki ko?" Kai ta
girgiza tana dariya
"Xaki fahimta,sai ranar da aka kawoki dakina a matsayin matata" kunya ta sata sadda
kai tana qiyasta ranar a ranta,gata ita dashi a matsayin miji da mata.

Daya tashi tafiya saita miqo masa dari biyar bayan wata baqar leda,wadda
daya bude links ne da agogo guda biyu masu matuqar kyau irin wanda tasan yana
masifar so,kallonta yayi itama shi take kallo
"Kada kacemin komai,na fuskanci yau miskini kake baka dako sisi(ta furta cikin
sigar zolaya)"murmushi ya saki,gaskiya ta fada,don duka albashinsa ma na wajen wata
uku ya qare ne wajen sama mata admission,dan abinda yaje riqewa bamai yawa
bane,kudi ya dinga badawa don ta samu gurbin karatun,don yasan cikar burinta kenan
shida ita,hakan bai dameshi ba ko kadan,yana jin zaiwa shahidan fiye da hakanma
indai ita dince
" har saika fada?"ta katse masa tunaninsa
"Ina iya karantar zuciyarka ba tare daka furta abinda ke cikinta ba" ta fada cikin
sanyi da taushi,sun riga da sun zama daya,sai ya saka hannu ya amsa yana murmushi
"Na gode matata" kalmar data yi mata dadi sosai,cikin farinciki walwala da qaunar
juna suka rabu,yana tafe yana tariyar dukka kalamanta,saiyakejin kyautar data masa
tayau din daban take,hakan ya sanya ya kasa fasa kudin ya hau mota,ya taka har zuwa
gida da qafa yana juya ledar data bashi gift din a ciki,gift din data bashine da
sunan tayashi murnar xagayowar ranar haihuwarsa,wanda sam shi ya mance ma da yaune
ranar haihuwarsa.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe biyar na yammaci da 'yan mintuna ta sauke wayar daga kunneta tana
sakin ajiyar zuciya,itakam har cikin zuciyarta sam batajin zuwa ko ina,haka kawai
taji batason fita.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/video

1️⃣ 4️⃣
*Alqawarin Allah*
1️⃣4️⃣

Ta bangaren shahida kuwa mahaifinta ne ya turo qofa ya tsinceta cikin wannan


halin,wanda hakan ba qaramin kadashi yayi ba,bai gane a cikin maye take ba sai daya
kamata zuwa cikin gida yaji tana surutai irin na wanda yasha wani abu ya bugu,saiya
saketa suka zuba mata idanu shida ummanta suna kallonta,kasa tsaiwa tayi saita fadi
luuu ta zube nata ci gaba da surutanta,wanda a nata tunanin anwar take kira ya
tsaya tayi masa bayani,kuka umma ta fashe dashi yayin da abbanta cikin tashin
hankali yace
"Ina kika barmin 'yata taje mariya?"
"Ina kuwa zan barta taje abba?,gaisuwar mutuwa suka je ita da qawarta" ta fada
cikin tsananin tashin hankali da kuma kuka
"Wallahi wallahi ki tabbatar da cewa indai wani mummunan abu ya samu 'yata toki
kuka da kanki" ya fada cikin hargagi yana nunata da yatsa,a ranar dai umma babu
bakin magana ta diyarta take,salati kawai take tana duba jikin shahida daya lalace
da jini,bandaki ta kaita tayi mata wanka wanda shiya sanya bacci ya kwasheta bayan
ta dawo da ita daki.
🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Da salati ta farka tana qarewa dakin kallo,ko ba'a fada ba tasan dakin
ummanta ne,a hankali ta soma tuna me ya faru da ita,tun daga barinsu inda sukaje
zuwa gidan qawar fiddausi,sauketa da saurayin yayi a qofar gidansu,daga nan zaren
tunanin nata ya yanke,tayi tayi ta sake tuno abinda ya faru ta kasa,zuciyarta na
gaya mata taga anwar,wata zuciyar tana ce mata bashi bane.

Muryar umma ta jiyo tana kiranta cikin kakkausar murya wadda tasa hanjin
cikinta kadawa
"Shahida....ina kikaje jiya?" Saita kasa amsa mata,indai har a wannan yanayin ta
shigo gidansu to tabbas bata da bakin kare kanta,kafin ta sake cewa wani abu umman
ta zube dukka kwalaben da suka fado a jakarta wanda tuni ta gama karantawa ta kuma
fahimci kayan shaye shaye ne a ciki,idanun umman jajur tace mata
"Meye wannan shahida?" Kasa hada ido tayi da umman,hankalinta yayi qololuwar
tashi,lafiyayyen mari umman ta sauke mata wanda ya gigitata,sannan yayi dai dai da
shigowar abbanta dakin,wanda tunda ya fita sallar asuba daya daga cikin maqotansa
ya masa jajen anga shahida an kawota qofar gida an yasar me ya sameta bai sake
samun sukuni ba,yasan tabbas maganar akayita tattaunawa a jiya ana kuma sauya mata
kamanni,yasan halin anguwar da 'yan unguwar kaf.

"Ai kibar dukanta bari na gaya miki mariya,koma meye shahida ta zama laifinki
ne,kin zaki baki kin kasa bawa diyata tarbiyya shine yanzu zaki zo kina wani
hargagin banza da wofi?" Cikin bacin rai da shiga zafi biyu ta maida masa amsa
"Indai shahida ta lalace ne kaima akwai laifinka,tunda kaima ubane ai ba'a dauke
nauyin haqqin kula da ita daga kanka ba"
"Au haka ma zaki ce?"
"Eh na fada din,dame kakeso naji ne iye?"
"To mariya nidai tsakanina dake saidai nace Allah ya isa ban yafe ba..." Cikin
qaraji gana zubda hawaye tace
"Nima Allah...." Qarar da shahida ta saki ita ta katse sauran magabar da umman tata
taso furtawa,kuka take sosai hawaye wani yana bin wani
"Ku dainawa juna Allah ya isa kune sila....dukanku ku kuka zama silar koma meye na
koma a yau...ku ku kaini ga afkawa halin da nake ciki a yau,wannan abun da kukeyi
shiya janyo komai,duk d'a na halak bazaiso yaga rana guda tak data zama ranar da
mahaifansa sukai cecekuce ko jayayya ba a gabanshi,sai gashi ni nawa mahaifan a
gabana suke xagin juna,a gabana suke aibata juna,a gabana suke debewa juna
albarka,a gabana suke fada da junansu,duk yadda naso da ganin gyaruwar al'amarin
hakan ya gaza,duk habyar da nabi ta ganin kun gyaru ba wadda ta bulle min,zafi da
radadin haka yasa na nemowa kaina gurbatacciyar mafita,nake shan abinda ni a nawa
tunanin bacci kawai zao sanyi ni,ban sani ba cewa ya shiga cikin abinda annabi ya
haramta tunda zai gusar da hankali,zai saka maye,idan zanyi kuka bazanyi da d'aya
saga cikinku ba,zanyi kuka ne sa dukkaninku,kun kasa fahimtata a sansa ya dace,kun
kasa gane illar abinda kuke aikatawa a gabamu mu 'ya'yanku"daga haka ta miqe ta
miqe jiri da kuma rashin qwarin jiki ya sanya ta dinga layi,amma bata dakata ba har
sai data fice daga dakin zuwa nata dakin.

Dukkaninsu sai jikinsu yayi sanyi,kowannensu ya shiga nazari da dogon


tunani,bai sake cewa komai ba abban ya fice daga dakin,saiya zura takalmansa ma da
niyyar ficewa daga gidan gaba daya.

Yana sanya qafarsa a waje yaci karo da mutum uku cikin maqotansa
"Yauwa malam nuraini...dama yanzu muke neman yaron da zai mana sallama dakai"
qoqarin dai daita fuskarshi yayi ya basu hannu suka gaisa
"Ashe haka abu ya faru?,wallahi sam bamuji dadi ba,yarinyar da kowa ke mata kallon
hankali da nutsuwa" daya daga cikin maqotan nashi da ake kira da malam sallau ya
fada
"Wallahi kuwa malam sallau,amma nidai ina kyautata zaton sharrin qawaye ne tunda
kowa ya shaidi nutsuwar yarinyar....amma cire ciki aiba qaramin abu bane,sanda
haruna ke gayan qaryatashi nayi saida yatabbatar min da kunnensa yaji saurayin yana
fada" a hautsine abban shahida ya dago yana musu wani bahagon kallo,kusan bai
fahimci me suke fada ba gaba daya
"Yata shahida ce tayi ciki harta cire?" Sai suka koma kallon kallo tsakaninsu,malam
sallau ya dubi abban
"Errrhmmm malam nuraini kodai mata sun maka irin halin nasu ne an boye maka bakasa
me yake faruwa cikin gidanka ba?,banda haka wannan zancan ai ya karade unguwarnan
daga daren jiya zuwa safiyar yau"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ya dinga maimaitawa yana dafe da kanshi,me
yayi jama'ar unguwarsu haka sa cikin qanqanin lokaci zasu jefi diyar cikinsa da
wannan sharrin,kansa ya dafe da yaji ya soma juya mishi sai kawai ya juya zuwa
cikin gida
"Allah ya tsare gaba ya kiyaye" ya juyo malam sallau yana fada cikin daga murya,dai
dai sanda shahida data fito don shiga bayi ta kama ruwa ta saki butar hannunta
cikin tsananin tashin hankali ta koma dakinta,dukka jikinta rawa yake,tana tariyar
kalaman da saurayin ya dinga fada bayan ya saketa a qofar gidan,kenan duk abinda ya
fada sun yarda dashi?,kenan yanzu kallon da kowa zai dinga mata?,innalillahi
wa'inna ilaihir raji'un,Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan
minha"shine abinda ta dinga maimaitawa kenan.

Cikin kwana biyu kacal ta rame ta fige ta fita a hayyacinta,bata taba


tunanin akwai tashin hankalin daya wuce na fadan iyayenta ba saiga wanda ya
ninkashi ya risketa,duk ta silar kaucewa wancan bacin ran ashe zata fada wanda yafi
wancan tsanani rusa farinciki dama ruguza rayuwa gaba daya.

Ba ita kadaiba gidanma gaba daya ya zama shuru,baya ga abinda ya faru abbanta
ya kwanta ciwo sosai tun randa su sallau sukazo masa jaje,wanda ba komai bane ya
taba ranshi irin maganar da suka furta,qarshe da aka aunashi jininsa ne yayi mugun
hawa,hakan ya saga hankalin ummanta itama ta shiga wani sabon tashin hankalin da
firgici.

Kwana uku amma shahidar jinta take akwai ya babu,gata nan dai kawai amma komai
ya fice mata aka,ranar kwana na ukun da yammaci wani yaro yayi sallama tsakar gidan
nasu dauke da takarda wanda yace gashi a baiwa shahidan.

Mubina ce ta bita har cikin daki a sannan tana kwance saman abun sallah ta
miqa mata,saita saka hannu kawai ta amsa ta aje saman kanta tana ci gaba da
lazuminta,wanda kusa fiye da rabi istigfari take da salatin annabi.

Sai data idar sannan ta dauko envalope din,tana daga kwance ta


farketa,takarda ce qwaya daya a cikinta ta fado,sai wata azurfarta guda biyu data
siya ta baiwa anwar ajiya,da sauri tasoma warware takardar tana zumudin jin daga
gareshi,don tunda abun ya faru taji dif daga bangarensa,tana zaton wala'alla yazo
ance mishi bata da lafiya,don bata da maraba da mai lalurar,ita kuma wani kunya da
nauyin kiranshi take,gani take kaman daga muryarta zai karanci komai,zai karanci
halin data fada,wasiqace cikin rubutun anwar din mai tsari

_Basai nayi miki sallama ba don baki cancanceta ba,saqo nake son isar miki dama ba
wani mai tsaho ko yawa ba,shahida,sam baki dace dani ba,kuma sam bakiyi dai dai da
rayuwata ba,tuntuni ina zaune dake ne kawai don bani da abinyi kuma bani da wata
qwaqwaqwarar sana'a,gashi ina da buqatar macen da zan di ga rage dare a wajenta,to
zuwa yanzu al'amura son suma yimin kyau,bana jin zan iya ci gaba da zama dake,ki
sani ni muhammad anwar ban taba sonki ko qaunarki ba,na miki alfarma ne kawai a
baya,kuma ki saka a ranki cewa baki taba soyayya da wani mai kama dani ko suna na
bar har qarshen rayuwarki,wasiqar na tafe da guzurin sabuwar masoyiyita wadda nake
da tabbacin ta fiki komai,idan nace komai ina nufin komai da komai da kikasan diya
mace na mallaka_
Cikin rawar jiki ta miqe zaune dungurgur,sannan ta jawo envalope din ta sake
lalubawa ciki,saiga hotuna guda shida rigis sun fado,dukkaninsu anwar ne cikin
hotunan da wata matashiyar budurwa cikin kyakkyawar shiga ta alfarma,kana musu
kallon farko zaka tabbatarwa kanka lallai masoya ne da sukayi zurfin cikin qaunar
juna,saboda yadda kowanne ke kallon danuwanshi cikin fara'a da shauqi,sosai ta
tsurawa fuskar yarinyar ido zuciyarta na wani qara gudu tamkar zata faso
qirjinta,suya zuciyar tata take mata tanason yin kuka amma bataji koda alamarsa ba
bare yazo,nazarin fuskar yarinyar take take ta tuno inda ta santa,ranar bikin
umaima,ranar bikin umma zaune gaban motar daya amso don ya kaita ya daukota,saita
saki hoton tana girgiza kai tare da laluben wayarta duka lokaci daya,tamkar tababba
take zancan a fili ita kadai
"Nasan wasa kake min ya anwar ba zamu taba rabuwa....nasan wani ya kaima labarin
abinda ya faru dani,ranka ya baci ka furta min wannan kalaman saboda kishina da
kake" maganar tata ta katse sanda wayar ta shiga ta soma ringing.

Wata murya daban ta dauka,cikin matuqar sauri da zaquwa tace


"Don girman Allah ka taimakeni ka bawa anwar" dan jimmm yayi cikin tunani,don a
yanzun bayajin anwar din zai iya wata dogon magana,tunda Allah yasa suka miqashi
asibiti yayi kwanaki biyunsa cur ya farfado yace a dawo dashi gida yazo ya dauke
wata envalope dashi kansa muhsin baisan meye a ciki ba ya adana yake zaune waje
daya,kana kallon yanayin fuskarsa kasan ya dulmiya cikin wani qunci,iein quncin
dake kama zukata ya riqe tamau ya dinga yankarta a hankali yana saka rudani damuwa
da baqinciki mai yawa a rayuwa,irin baqincikin dake tasiri kadan kadan daga ruhi
zuwa gangar jiki ya illata mutum ta farat daya ba tare da an ankara ba.

Miqa masa wayar yayi,sai daya daga idanunsa da suke nuna alamun gajiyawa da
damuwa ya dubi muhsin sannan ya maida kan wayar,hannu ya saka a hankali ya
masa,muhsin ya sakar masa yana tashi gami da cewa
"Bari naje gida na dauko wayata na barta a chargy" kai kawai ya iya gyada masa yana
kara wayar a kunnensa.

Abu na farko da tayi kuka ta sakar masa,wanda yake bayyana rauninta


qarara,gajiyawa da rashin samun madafa,idanunsa ya runtse yana jin zuciyarsa cikin
wani inji ana hautsinata sama da qasa ko zata faso qirjinsa ta fito.

*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina
buqatar siya ki tuntubi wannan number*

07067124863

*ko kuma*

09032345899https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

1️⃣ 6️⃣
*Alqawarin Allah*
1️⃣6️⃣

Daga kai tayi ta dubi anty zubaidan maimakon yadda ta saba yi mata a baya duk sanda
ta ganta,takan tashu cikin farinciki tana mata sannu da zuwa dama tambayarta yaushe
ta iso,hadi da tambayarta su faruqu,a nutse anty zubaida itama take qare mata kallo
bayan ta zauna dab da ita,cikin mintina qalilan ta gama karantarta
"Shahida" ta soma kiran sunanta a sanyaye,sake tada kai tayi ta dubeta saita sake
saukewa,shawarar da zuciyarta ta bata tabbas itace mafita,dole ne saita fara tayar
mata da mikin dake zuciyarta don da ala zuciyarta ta riga data daskare,dab take da
rasa feelings,dole ta sata tayi kuka ta rage radadin da yake damun zuciyarta wannan
shine hanya daya na farkar da zuciyar tata,dole ta sakata da kan kanta ta nuna
akwai ciwo a zuciyarta wanda ta wannan hanyar ne kawai zata dawo da feelings da
emotion dinta na fushi,sannan asan yadda gyara zai iya yiwuwa,tana son maida
zuciyarta ne matacciya idan ba'ayi gaggawar gyarawa al'amarin ba
"Shahida!" Ta kirata wannan karon da mugun tsawar data taba zuciyar shahidan,ta
kuma sanyata dago kai tana duban anty zubaida gami da zuba mata idanu,yadda ta
kafeta da idanu shi ya sanya itama tsaiwa tana kallonta
"Shahida bansan ke shashasha bace,ban kuma san ke wawiya bace sai yau,ban raina
wayonki ba sai yau,ashe ke banza ce?!" Shuru tayi kaman wata sokuwa tana duban anty
zubaida,qwaqwalwarta nason tariyo mata meta aikata haka?,ganin yanayinta ya baiwa
anty zubaida qwarin gwiwa
"Shahida....saboda namiji kikeson maida rayuwarki haka?,saboda wani da dacan baki
sanshi ba?saboda wani daya nuna bai damu da rayuwarki ba?,wace iriyar shashasha ce
ke wadda batasan ciwon kanta ba,shi din banza?...waye shi?,kina da 'yan uwa,kina da
mahaifiya...mahaifinki ya rasu,waishin shi da mahaifinki wanne ne yafi miki
muhimmanci,kin rasa mahaifinki ma ya tafi kuma har abada,kun rabu kenan da wanda
yayi silar kawoki duniya,inaga wanda ya tsinceki rana tsaka da
girmanki,shahida!....kisan me kikeyi,ki shiga taitayinki!" A hankali ta soma
girgiza kanta,yayin da hawaye ya cika idanunta,zuciyarta ta soma motsawa,mikin dake
danqare ciki ya tashi,kuka ta saka mai sauti qwarai wanda hatta mutumin dake tsakar
gida zai iya jiyo gunjinta,sai anty zubaidan ta matso da ita jikinta,ba musu ta
kwantar da kanta saman cinyar anty zubaidan taci gaba da gursheqen kukanta,bata ce
mata komai ba hakanan bata hanata ba,shuru tayi tana sauraron yadda kukan nata yake
fita,ta sani duk sanda hawaye daya ya sauka yana sauka ne da wani radadi daga cikin
radadin dake danqare cikin zuciyarta,hannu anty zubaida ta dora saman kan shahidan
ta dinga shafawa a hankali a hankali tana tayata jin radadin.

Aqalla sun shafe awa guda cur a haka,harsai da kukan ya soma sassauta ta soma
rage sauti ya koma sai hawaye,mintina talatin ta sake qara mata zuwa sannan hawayen
ya sake raguwa
"Me ya faru shahida?,garin yaya haka ta kasance?" Bata boyewa anty zubaida komai ba
kanta na saman cinyarta ta warware mata dukkan yadda akayi ta soma shan wani abu da
niyyar rage baqinciki da bacin ran dake damunta,sannan ta zarce da rabuwarta da
anwar sannan ta dora da cewa
"Baqinciki na shi ya kashe abbana anty,shaye shaye yabarmin tabon da har na mutu
dashi zan mutu,na kashe abbana da takaicina!" wanda hakan ya sake bude sabon shafin
kukanta,kai anty zubaida take girgizawa
"Kuskurenki na farki shahida shine da kika saki Allah,kika manta da cewa babu wani
babban abu dake yaye qunci da baqincikin a zuciyar bawa ya samu nutsuwa da
kwanciyar hankali irin kusanta kai da Allah,babu wani abu da zai kawo miki
farinciki da walwala irin karatun qur'ani,shan wani abu a wajen dan adam domin
gusar da baqinciki bacin rai ko kuma damuwa bashi da wani tasiri a gareshi,baya
haifarwa da bawa komai face sake sanyashi cikin damuwar,baya yaye damuwa ta har
abada face ya sake sanyaka cikin wasu sabbin matsalolin,ya haifar maka da ciwuka
masu kai d'an adam ga kushewa,Daga kai tayi ta dubi anty zubaidan maimakon yadda ta
saba yi mata a baya duk sanda ta ganta,takan tashu cikin farinciki tana mata sannu
da zuwa dama tambayarta yaushe ta iso,hadi da tambayarta su faruqu,a nutse anty
zubaida itama take qare mata kallo bayan ta zauna dab da ita,cikin mintina qalilan
ta gama karantarta
"Shahida" ta soma kiran sunanta a sanyaye,sake tada kai tayi ta dubeta saita sake
saukewa,shawarar da zuciyarta ta bata tabbas itace mafita,dole ne saita fara tayar
mata da mikin dake zuciyarta don da ala zuciyarta ta riga data daskare,dab take da
rasa feelings,dole ta sata tayi kuka ta rage radadin da yake damun zuciyarta wannan
shine hanya daya na farkar da zuciyar tata,dole ta sakata da kan kanta ta nuna
akwai ciwo a zuciyarta wanda ta wannan hanyar ne kawai zata dawo da feelings da
emotion dinta na fushi,sannan asan yadda gyara zai iya yiwuwa,tana son maida
zuciyarta ne matacciya idan ba'ayi gaggawar gyarawa al'amarin ba
"Shahida!" Ta kirata wannan karon da mugun tsawar data taba zuciyar shahidan,ta
kuma sanyata dago kai tana duban anty zubaida gami da zuba mata idanu,yadda ta
kafeta da idanu shi ya sanya itama tsaiwa tana kallonta
"Shahida bansan ke shashasha bace,ban kuma san ke wawiya bace sai yau,ban raina
wayonki ba sai yau,ashe ke banza ce?!" Shuru tayi kaman wata sokuwa tana duban anty
zubaida,qwaqwalwarta nason tariyo mata meta aikata haka?,ganin yanayinta ya baiwa
anty zubaida qwarin gwiwa
"Shahida....saboda namiji kikeson maida rayuwarki haka?,saboda wani da dacan baki
sanshi ba?saboda wani daya nuna bai damu da rayuwarki ba?,wace iriyar shashasha ce
ke wadda batasan ciwon kanta ba,shi din banza?...waye shi?,kina da 'yan uwa,kina da
mahaifiya...mahaifinki ya rasu,waishin shi da mahaifinki wanne ne yafi miki
muhimmanci,kin rasa mahaifinki ma ya tafi kuma har abada,kun rabu kenan da wanda
yayi silar kawoki duniya,inaga wanda ya tsinceki rana tsaka da
girmanki,shahida!....kisan me kikeyi,ki shiga taitayinki!" A hankali ta soma
girgiza kanta,yayin da hawaye ya cika idanunta,zuciyarta ta soma motsawa,mikin dake
danqare ciki ya tashi,kuka ta saka mai sauti qwarai wanda hatta mutumin dake tsakar
gida zai iya jiyo gunjinta,sai anty zubaidan ta matso da ita jikinta,ba musu ta
kwantar da kanta saman cinyar anty zubaidan taci gaba da gursheqen kukanta,bata ce
mata komai ba hakanan bata hanata ba,shuru tayi tana sauraron yadda kukan nata yake
fita,ta sani duk sanda hawaye daya ya sauka yana sauka ne da wani radadi daga cikin
radadin dake danqare cikin zuciyarta,hannu anty zubaida ta dora saman kan shahidan
ta dinga shafawa a hankali a hankali tana tayata jin radadin.

Aqalla sun shafe awa guda cur a haka,harsai da kukan ya soma sassauta ta soma
rage sauti ya koma sai hawaye,mintina talatin ta sake qara mata zuwa sannan hawayen
ya sake raguwa
"Me ya faru shahida?,garin yaya haka ta kasance?" Bata boyewa anty zubaida komai ba
kanta na saman cinyarta ta warware mata dukkan yadda akayi ta soma shan wani abu da
niyyar rage baqinciki da bacin ran dake damunta,sannan ta zarce da rabuwarta da
anwar sannan ta dora da cewa
"Baqinciki na shi ya kashe abbana anty,shaye shaye yabarmin tabon da har na mutu
dashi zan mutu,na kashe abbana da takaicina!" wanda hakan ya sake bude sabon shafin
kukanta,kai anty zubaida take girgizawa
"Kuskurenki na farki shahida shine da kika saki Allah,kika manta da cewa babu wani
babban abu dake yaye qunci da baqincikin a zuciyar bawa ya samu nutsuwa da
kwanciyar hankali irin kusanta kai da Allah,babu wani abu da zai kawo miki
farinciki da walwala irin karatun qur'ani,shan wani abu a wajen dan adam domin
gusar da baqinciki bacin rai ko kuma damuwa bashi da wani tasiri a gareshi,baya
haifarwa da bawa komai face sake sanyashi cikin damuwar,baya yaye damuwa ta har
abada face ya sake sanyaka cikin wasu sabbin matsalolin,ya haifar maka da ciwuka
masu kai d'an adam ga kushewa,Kana daukan cuta ne kana laftawa kanka,kana kashe
kanka da kanka,Allah S W T da kansa yace kada ku kashe kawunanku,shan abun maye ba
komai bane face kashe kai,don baka da maraba da mutumin daya dauki makami ya dabawa
kansa,domin kuwa shaye shaye ba cutar da baya haifarwa,lalacewar qoda,lalacewar
hanta,ciwon cancer,ciwon zuciya,yana nakasta hunhu,yana kuma lalata qwaqwalwa wanda
hakan yake jagoranci zuwa ga haukacewa,dukka daya daga cikin wannan cututtuka idan
aka bar mutum dasu sun isheshi azabar nan duniya,sun ishi mai hankali gujewa abun
maye"ajiyar zuciya anty zubaida ta saki sannan ta dora
"A duniyance shaye shaye bai haifar maka da komai sai zubewar qima da
mutunci,mummunar dabi'a ce dako wanda yake yinta yake boyewa,kuma baiso a
sani,dabi'ace dakan gusar da imani da hasken fuska,dabi'ace dake barin tabo cikin
rayuwar wanda ya taba aikatata,sannan ba'a sanyaka cikin sahun managarta mutane ko
mutane masu dattako har abada,saboda kowa kallon mahaukaci yake maka,sannan a
addinance manzan rahama yace dukkan wani abu da zai saka maye haramunne,musulunci
yafimu sanin cewa kayan maye abubuwane masu cutarwa ga lafiyarmu,shi kuma ko yaushe
tattalin lafiyarmu yake,sannan addini ne dake kare mutunci da martabar dan
adam,bambancin mutum da dabba hankali,kinsha abinda zai gusar da hankalin me
sunanki kenan a wannan lokacin?,dalili kenan daya sanya aka haramta mana su,duk
sanda kake cikin maye babu kunya tattare dakai,hakan na nufin ba alkhairi a tare
dakai kenan,saboda ma'aiki ya gaya mana duk inda kaga kunya akwai alkhairi a
wajen,sanda kuma babu kunya tare dakai zaka iya aikata dukkan komai ciki kuwa harda
kisan kai!,tunda kike sha din damuwarki ta taba tafiya gaba daya?" Kai shahida ta
girgaza,don da zarar ta farka dukkan wata damuwa take dawo mata sabuwa fil,harma
tafi ta dazun
"Zaki iya tuna sau nawa kikayi loosing sallah saboda tazo ta riskeki kina cikin
bacci sanadin abinda kika sha?"shuru shahidan tayi tana tunani hawaye masu dumi
nabin fuskarta har cikin kunnenta,kome take komai runtsi sallah bata taba wuceta ba
sai a wannan karon,sai data shiga wannan mugunyar dabi'ar
"Kina tunanin hujjace da zaki gayawa Allah ranar gobe qiyama na dalilin jinkirta
sallahrki?" Ta jefo mata tambayar data sanya shahida fidda sabuwar qwalla,dana sani
da nadama mara misaltuwa na sake shigarta,kaico da rayuwarta da haduwarta da
fiddausi
"Kina da yaqinin sanda kika farka kika ramata Allah zai amsa ya saka miki a mizanin
ayyukanki wajen sallahrki na lokacin bazai tashi blank ba?,bayan kina baccin sabo
ne bana ibada ba?" Sabon kuka shahidan ta sake saki,tsoron Allah na sake
kamata,tana jin kaman yanzu Allah zai amshi rayuwarta,me ta tanada?,wacce amsa zata
bayar?.
"Allah yana karban tuban bayinsa ne matuqar ran bawa baizo gargara ba,sannan kuma
rana bata fito daga mafadarta ba,bai halatta bawa ya jinkirta tuba kan wani aikin
sabo da yake ba,yace har sai Allah ya shiryeshi,don haka yana daga cikin alamar
'yanwuta,kuma alamace dake nuna bawa ya tabe,sannan alamace ta toshewar
basira,anaso koda yaushe bawa ya dinga gaggauta tuba saboda baisan randa ajalinsa
zai riskeshi ba"
"Astagfirullah...astagfirullah" shahida ta dinga maimaitawa a fili har na tsahon
wani lokaci,sai data fuskanci ta samu nutsuwa sannnan ta dagota suna kallon juna
"Shahida...maganar anwar....." wani abu mai ciwo taji ya tokareta,abinda yayi mata
ya dinga yawo cikin idanunta kamar tariyar film,da sauri ta katsi antyn
"Anty...don Allah ki daina kiramin sunanshi....don Allah anty ki dainamin
maganarsa,yanzu bashi a gabana,yadda ya buqaci na barshi na barshi har
abada...yadda ya nuna bai buqatata saboda wani kuskure dana aikata nima bana
buqatarsa har abada" murmushi anty zubaida tayi tana karantar yanayinta da yadda
maganar ke fita daga zuciyarta zuwa harshenta,kai ta girgiza tasan cewa wani bacin
raine dake qonata tun daga cikin jiki zuwa zuciyarta,kowa ya shaida irin qauna da
soyayya dake tsakanin shahida da anwar,koda baka sansu ba labarinsu ba shakka ya
iskeka,bata da tabbaci ko yaqinin kan abunda shahidan ke furtawa saboda ta riga ta
sani cewa soyayya ba qarya bace,ba qaramin dalili ne yake da qarfi da isar da zai
karyata ba,karyawa ta har abada,karayar da ba zata doru ba
"Duk wannan lafazin shahida ban buqatar jinsa daga bakinki,ba'a ciwa soyayya
alwashi kuma ba'a cika mata baki....kiyi addu'a kawai a yanzun,ki tattara
hankalinki waje guda,ki karbi qaddararki,kiyi moving forward,stop worrying about
what u have to loose,and start focusing on what u have to gain,har yanzu yarinyace
ke,shekarunki nawa?,me kika soma gani cikin rayuwa?,akwai abubuwa daya kamata ace
kinyi achieving a rayuwarki,karki bari wani abu guda daya ya tsaidaki waje guda,ya
ruguza dukkan wani kyakkyawan tanadi daya kamata kiwa rayuwarki,wannan abun daya
faru ba komai bane cikin rayuwarki,daya daga cikin challanges kenan na rayuwa,ki
godewa Allah kina da chance,kina da dama,kamar ya baki wata dama ne naci gaba da
gina sabuwar duka rayuwar da kikaso kikaga dama,just choose tobe strong rather than
letting it drown you" wadan nan sune ire iren kalaman da anty zubaida ta dinga
amfani dasu tsahon shekara biyar don dawo da rayuwar shahida cikin nutsuwarta.

Cikin qaramin lokaci taji anwar din ya wanke mata a rai tas,ya sire mata,ya
fice mata daga ruhinta,taji zata iya rayuwa babu shi,taji abune mai sauqi
hakan,saidai baizo mata da sauqi ba yadda ta tsammata,ta share darare da yawa bata
samu bacci ba,ta ga wuninnika da darare masu tsaho da tsauri cikin rayuwarta a
wannan lokaci,ta cika bangon dakinta da shafukan littafanta ta kalaman qarfafa kai
da qarfafa gwiwa akaran kanta,ta siya littafi tayi rubutu mai tsaho da yawa kan
rayuwarta har kawo bigiren da yau take kai,ta tattara duk wani abu da zai iya tuna
mata da anwar ta ajesu waje daya,ta shiga tsara yadda rayuwarta zata kasance nan
gaba,tun saga lokacin ko masoya ta gani sai taji tana tausayinsu,musamman mace idan
taga ta zura jiki da yawa.
Bayan umma ta fita takaba uncle hisham shi ya karbi ragamar daidaita musu
duka al'amuran gidan,sannan suka yanke shawara dashi shahida zata koma hannun anty
zubaidan,tunda har yanzu bata gama daidaita ba,saidai cikin kaso dari an samu sauyi
na kaso shida,rabata da unguwar da duk wani tsohon memory dinta zai sake taimakawa
wajen saita tunaninta,da wannan suka dauke shahidan ta koma wajensu.

Makarantu daban daban anty zubaida ta sakata wanda zata qaru ta fanni da
dama,wasu na koyon harshen larabci wani na koyon turanci bawai don bata iya ba,a'ah
saidon ta maidata busy sosai wanda hakan zai sanya bata da lokacin zama ma ta tuna
wani abu mara dadi daya faru da ita a baya,tayi hakanne kuma kafin wata shekarar ta
zagayo su nema nata admission saboda wannan shekarar ta qwace mata.

Rayuwarta ta soma samun sauye sauye,kullum kwanan duniya saitayi kukan


dabi'ar shaye shaye data ta taba tsintar kanta a ciki,kullum sai tayi nadamar sanin
fiddausi a rayuwarta,sai tayi nadamar sakin jiki ga duk qawar data kutso rayuwarki
sama taka,abune mak wahala da idan ka sake ka jefa kanka da wuya ya fice daga
rayuwarka salin alin ba tare daya haifar maka da nadama da danasani ba,bai kuma bar
maka qatoton tabo ko baqin fenti a rayuwarka ba,ta godewa Allah da yayi gaggawar
fiddata tun batayi nisan da ba zata ji kira ba kamat yadda tagani ta kuma ji labari
da yawa akan wasu,wanda ta shiga bincike ne akai bayan ita Allah ya tsamota,gefe
daya kuwa yaqi take tuquru da kanta game da lamarin anwar,wata irin tsana da bata
taba tunanin tanawa wani dan adam ba ita ke taso mata,duk wani abu da yayi mata da
yadda ya dubu qwayar idanunta ya gaya mata magana,fiddota daga gidanshi da
sauransu,uwa uba hotunan yarinyar da yake gaya mata ya sake ya sauyata a
madadinta,kullum qoqarin goge duk wani tabo ko abun tunawa daya barwa rayuwarta
take,tanason ta nuna masa ta kuma nunawa duniya she can survive without him,tana
son watan watarana yaga cewa shi din ba komai bane da ba zata iya rayuwa babushi
ba.

*Cikin rashin kunya murjewar ido dajin wannan karon dai dai take da kowa,zata iya
karawa da kowa,a shirya take ta rabu da kowa saboda shi,bata jin akwai abinda ya
isa yayi mata hijabi tsakaninta dashi,koda waye,koda mahaifiyarta data haifeta,koda
mahaifinta da yayi silar zuwanta duniya*

*"Allah ya isa ban yafe ba duk wanda yayi silar rabani da Zamab,ko wayeshi bazan
taba yafe masa ba wallahi, dan an haifeka ai ba halittarka akayi ba, kai ma babu
wanda yayi maka auren dole, haka a addinance babu inda Allah yace ayiwa mace auren
dole"*

*kalaman da suka fito kenan kai tsaye daga bakin Basmah zuwa ga mahaifinta Ya
Mu'allim tana dubanshi kai tsaye ba kunya ko rusunawa*

_SAKI RESHE KENAN littafin da zaizo muku daga jarumarku haziqar marubuciya HAUWA A
USMAN JIDDERH_

*WANNAN WACCE IRIYAR DIYACE HAKA?,ME YAKE FARUWA ME KUMA YA FARU?,DON JIN CI GABAN
WANNAN LABARI DAKE QUNSHE DA BADAQALA,SAKIN RESHE DA SAGEGEDUWA ZAKA BIYA NAIRA 300
KACAL TA WANNAN HANYA,BA TARE DA BATA LOKACI BA ZA'A SADAKA DA WAJEN DA ZAKA SAMU
NAKA*

Hauwa Auwal Usman


GT bank
015325259310

*saiki tura shaidar biya zuwa ga wannan number*


07020489340
*katin waya kuma xaku tura 300 ta watsapp ta wannan number*
07020489340

_kar ayi babu ke,maza garzaya ki nemi naki_https://www.youtube.com/channel/


UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina
da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

1️⃣1️⃣7️⃣
7️⃣
*Alqawarin Allah*

Daga gefan anwar kuwa yaso barin garin ne gaba daya,saboda yadda garin yayi
kishi zafi,yaji ya tsani komai,bashi buqatar duk wani abu daya sani,yana buqatar
baqon muhalli,anty husaina ce ta kafe kai da fata kan bata yarda ba,ganin yadda ya
dage kan son tafiya din ta sakar masa kuka,wanda ya sanya dole ya haqura shima yaci
gaba da zaman.

A wannan lokacin da nafisa taga dama tazo mata,taso ta gabatarwa da anwar


kanta ne gaba gadi,taso anwar ya dawo cikin gidansu da zama qarqashin abbanta,ya
bashi gida mota da kuma jari suyi aurensu,saidai yadda labari da halayyar anwar
tazo mata ta tabbatar da cewa aikata hakan babban kuskure ne da zai janyo kwabarta
tayi ruwa,wanda daga qarshe suka gama shawara da mima kan yadda zasuyi.

Alhaji abba kabara mahaifin nafisa mutum ne mai yawan taimako da samawa
matasa ayyukan yi,yana da kamfanoni hakanan yana da shagunan da yake sanya matasa a
ciki,duk matashin da yayu shekara guda riqe da amanar shagon ba tare da an taba
kuka dashi ba alhj abba yakanyi masa kyakkyawar sallama ta hanyar bashi jari mai
tsoka,wani lokaci ma bai duba da abunda aka samu a shekarar,zamanka a shagon iya
karantarshi da amanarka kawai ya nuna idan ya baka jarin ba zasu salwanta
ba,wasunsu kuma yakan daukesu ne ya kaisu kamfaninshi,musamman masu takardun
makaranta,dalili kenan sanya sanya ta samu abban nata
"Uhmm...ya akayi nafi?" Cikin nuna yanayi najin kunya tadan sadda kanta
"Abba dama...dama" sai tayi shuru
"Dama me?" Ya tambayeta yana sauke medical glass dinsa
"Akwai wani marayan matashi ne,abba yana da amana da duk halayen qwarai,ya kammala
karatunsa baida aiki,abba yana shan wuyar rayuwa sanadiyyar haka,idan na masa
magana abba da kaina bazai karbi duk wani abu ba,amma idan kaine da kanka abba
zaifi amsar duk wani taimako" shuru ya danyi yana nazarinta
"A ina ke kika sanshi?"
"Abba...a unguwarsu qawata yake,ita take bani labarinsa,na tabbatar zaka yaba da
halayenshi hakanan zaka tabbatar daya cancanci taimako" kai yake gyadawa sannan
yace
"Ba damuwa,ki turamin adress dinshi,zamu fidda sanarwar daukan ma'aikata a
kamfanina zansa a duba takardunshi sosai"
"To Abba Allah ya qara budi" amin ya fadi yana daukar jaridarsa yaci gaba da
dubawa,yayin da nafisan ta fita cikin farinciki da walwala.
Randa aka kira anwar aka shaida masa sunan kamfanin da sukeso duba
takardunsa yayi mamaki qwarai,don iya yawon neman aikinsa bai taba bi koda ta titin
da kamfanin yake ba,don bai taba sama ranshi cewa zasu daukeshi aiki ba.

Qarfe taran safe na ranar da zaije kamfanin ya gama shirinsa ya fito yana kulle
gidan yaga mota tsaye a qofar gidan,horn aka danna mishi kana aka jawo motar zuwa
gabanshi
"Daga kamfanin alhj abba ne akace muzo mu daukeka" ya kalli motar sosai yaga
tambarin kamfani jiki,hakan ya sanya ba musu ya bishi suka shiga.

Sam bai kula da itaba ashe tana zaune a bayan,sai daya waiwaya suka hada idanu
ta sakar masa murmushi,sam bai ganeta ba,ita ta soma gaidashi sannan ta gabatar
mishi da kanta a matsayin diyar alhj abba,mamaki day ayayi na wanne matsayine dashi
da har za'azo har qofar gida a daukeshi cikin motar kamfani shi da za'a yiwa
alfarmar bashi aiki,bashi da amsar wannan saboda haka shuru shi yafi masa,yana jin
nafisan na bashi labarin abubuwan da suka shafi kamfanin kamar ma an daukeshi aikin
ne,shidai nashi kunne ne,don yanzu baya ga anty husaina baya jin dadin hira da
kowacce diya mace,hasalima bayaso su rabeshi.

Bisa jagoranci da shigewar gaban nafisa ya gama komai cikin kamfanin,aka kuma
bashi babban gurbi wanda ko a mafarki bai taba tsammata ba,koda wasa bata nuna ita
ta roqa masa wannan alfarmar ba saboda tasan ba wani abu bane cikin aikinsa yaqi
amsar aikin gaba daya.

Lokaci kadan da fara aikinsa alhj abba ya tabbatar da duk maganar da nafisa ta
fadi a kansa,yana da gaskiya yana da amana,hakanan yana da aiki tuquru,baya taba
saba lokacin zuwa kamfani hakanan lokacin tashi,gwara ma lokacin tashin idan akwai
wani aikin da kamfani zaici gaba yakan sarayar da lokacin nashi ya gabatar
dashi,dalilin kenan daya sanya alhj abba da kanshi ya danqawa anwar qaramar motar
hawa mai azabar kyau da tsada irin wadda bai kawo zai mallaketa ba nan kusa,sannan
ya nemi daya dawo cikin gidanshi da zama,wanna ne kuma ya bawa alhjin haquri,saboda
yadda nafisa ke shishshige masa sam baya masa dadi,yana karanta mata ne da daga
mata qafa kawai saboda girma da darajar mahaifinta,motat ta sauqaqa masa sauran
ayyuka da zuwanshi ma kamfani gaba daya,hakanan ya dinga barin motar a wani garage
dake farkon layinsu wanda masu abun hawan da basu da muhallin ajesu suke ajewa a
nan su biya wani abu ladan ajiyan.

A sannan rayuwa ta soma mishi kyau,koma ya soma canzawa,kama daga sutura cima
da sauransu,anty husaina ma kanta canji ya soma zuwa mata,a wannan lokacinne nafisa
ta kasa shanye halin ko in kula da anwar ke nuna mata,duk wata alama da ake nunawa
mutum ya gane ana sonshi ta nuna mishi amma a banza wai an mintsini kakkausa,hakan
ya sanya tayi qundunbala taci alwashin sanar mishi wata rana da abbanta ya
gayyatoshi cin abincin dare gidan.

Abban da mamanta sun kammala sun bar wajen saura nafisan da tunda taji
labarin zuwanshi ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta tsara kwalliya ta a mutu,sannan ta
aro duk wani salo da tasan zai iya tafiya da d'a namiji,saidai kuma har ya kusa
gamawa bataga ya nuna wani abu game da ita ya burgeshi ba,hakan ya sanya tayi
gyaran murya
"Anwar....idan ba zaka damu ba don Allah...ina da magana dakai"
"Uhmm...babu damuwa ina jinki" shuru tayi na wasu mintuna sannan ta daga kanta tana
dubanshi sosai
"Tun ranar da Allah yasa na soma ganinka anwar Allah ya dasa min qaunarka...na rasa
ta yadda zan furta maka bansa ya zan gaya maka ka gane ba,wani irin soyayyarka
nakejin har cikin jinina,anwar ina fata da roqon ka soni koda rabin yadda nake
sonka ne" tunda ta soma maganar ya zuba mata idanu yana jin wani abu da baisan meye
ba yana taso masa,ko kusa ko alama baison yaji wannan kalmar daga bakin kowacce
diya mace gani yake duk yaudara ce,ba gaskiya bane qarya ce,yatsunsa ya dinga
bugawa a saman teburin kadan kadan har ita sai data tsargu da kallon da yake matan
ta soma kame kamen abunyi,da qyar ya iya hada abun fada
"Nafisa" ya kira sunanta a kausashe,daga kanta tayi ta dubeshi sosai jin yadda
sunan nata ya fito bilhaqqi daga zuciyarsa
"Inason daga yau wannan tunanin yabar qwaqwalwarki,wannan kalmar ta fita daga
bakinki,ina ganin qimarki data mahaifanki,kada ki jawo abinda bazai mana kyau da
dadi ba ni dake gaba daya"daga haka ya miqe ya dauki maqullan motarshi ya wuce ya
barta a wajen,kuka ta saki sosai,bata taba tunanin lamarin zaizo da haka ba,tayi
tsammanin yadda yake nuna kulawa a gareta kaman qanwarshi zata samu soyayyarshi ta
sauqi,haka ta miqe ta shiga bedroom dinta cikin tashin hankali ta dauki wayarta ta
kira mima ta zayyane mata komai
"Nafisa kenan,dama ke kina tunanin samun kanshi da wuri ne,to kinyi kuskure idan ma
zaki zage damtse kiyi kaman kinayi to" ta jima tana juya zantukan miman a
kwanyarta,inda daga qarshe ta zage damtsen kaman yadda ta bata shawara,saidai gogan
ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa,yadda ya saba mu'amala da ita haka yake babu
abinda ya canza,naci kuwa babu kalar wanda batayi masa ba,inda daga qarshe ma ta
matsawa dadynta ya bata gurbin aiki a kamfanin,ya bata din saidai tace matsayin
secretary din anwar takeso,babu musu ya bata kasancewarta diya mace diya tilo dake
gareshi,anwar din bashi da bakin cewa don me?,haka ya amsheta saidai kusan ba wani
aikin kirki take ba,cikin qaramin lokaci kowa ya fahimci yadda nafisan ke bala'in
so da qaunar anwar din,wannan labarin shi yakai har kunnen umminta,take ta saka
abban nafisan ya karbe gurbin aikin daya bata aka maida shi da wani,fada ta dinga
ma nafisan kan wautar da take nunawa na nunawa namiji irin wannan zallar son bayan
shi baisan tana yi ba,kuka ta dinga duk da ta bata tausayi amma sam bata nuna
ba,don tana sone idan anwar zasiso nafisan ya sota don karan kanshi,ya kuma sota da
datajarta ba tare data zubda qimartata ba wajen neman soyayyarshi ba a matsayinta
na diya mace.

Wannan karbe aikin ya bata ran nafisa matuqa,tana ganin kaman ummin nata bata
sonta ne,banda haka meye aibu a nunuwa anwar soyayya da take,hakan ya sanya ta sake
maida akalar shawararta dai wajen mima,inda ta bata wasu shawarwari da take ganin
anwar din bai isa ya tsallakesu ba dole ya furta mata soyayya da kuma kula koda ba
haka bane har zuciyarshi.

Cikin sa'a kuwa a lokacin aka maka wani gagrumin ruwan sama daya sanya gidan
anwar rushewa,dama yana dab da soma aikinsa ne,dalili kenan daya sanya alhj abba ya
sake nemanshi ya dawo gidanshi da zama har zuwa sanda zai kammala gyara
nashin,tofa,abun nema ya samu wajen nafisa,nan ta zage damtse ta shiga shigewa
anwar din haiqan,har abunma yana wuce gona da iri,don takan iya zamanta bangarenshi
da sunan tayashi hira har tara ko goma na dare,duk wadda kuwa akayi katari cikin
yammatan dake damunshi da kira ta kira nafisan ta samu nasarar dauka hara zata
dauka ranar suyi kace kace da sunan matarshi ce,hakan ya sanya ya qaranta dawowa
gida da wuri,ya qirqirarma kanshi guraren zuwa saiya daida daici sanda tayi
bacci,wani bin ya dace wani bin kuma ya taddata dai tana zaman jiranshi.

Ganin abun yaqi ci yaqi cinyewa tamkar cin qwan makauniya yasanyata amfani da
shawarar mima,inda ta kwanta ciwo sosai suka hada baki da wani likita aka kaita
can,ya dubata ya kuma ce lallai tana cikin damuwa ne,kuma tilas a sama mata abinda
takeso idan ba haka ba za'a iya rasata.

Randa ta farfado daga suman qaryarta anwar na dakin shida alhj abba da
mahaifiyar nafisan,a sannan yana gefan daya gadon da babu kowa a kai yana charting
da wani abokin kasuwanci da suka fara shirin saka hannun jari shi da shi su tashi
nasu kamfanin,sunanshi ta soma kira wanda yaja hankalin dukkaninsu,saiya daga kai
yana dubanta bayan ya amsa,ta wani lumshe idanu kaman gaske tana kallonshi,nauyin
idanun alhj abba da mahifiyarta ya sanyashi barin abinda yake ya taso zuwa kusa da
ita,sai ummanta tabar kujerar da take kai wanda ke gaban gadon ta masa nuni daya
zauna ba musu ya zauna.
Ba kunya ta kama hannunshi cikin dabara ya zame,saita saki kukan qarya
"Don Allah anwar kace kana sona kaji" mummunar faduwar gaba ce ta sameshi yayi
shuru yana jin yadda qirjinsa ke bugawa
"Ina sonki" yayi qundun balar fada saboda ganin yadda take kuka gaban iyayenta
"Zaka aureni?" Ta sake jefa masa tambayar data kusan sa jininsa hawa a take,tanason
daureshi ne wato da jijiyoyin jikinsa.*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don
GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata saita tuntubi wadan nan numbers*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*kuyi subscribing youtube channel dina don samun damar ganin shirye
shiryenmu,subscribe kyauta ne!*👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

1️⃣ 8️⃣
*Alqawarin Allah*
1️⃣8️⃣

Kanshi yaji yayi masa nauyi kaman an dora masa dutse,kafin ya ankara nafisa ta saki
kuka tana roqonshi,dukkansu ya tabbatar hankulansu da kunnuwansu na wajen,haka
yake,don dukansu fata yace ya amince,don sun yarda da hankali da nutsuwar anwar,sun
tabbatar idan ya auri diyarsu ta fada hannun dako bayan ransu basa kokwanto ko
shakka,saidai ta bangarin mamanta magiyar da take ta taba ranta ta kuma bata
takaici
"Meye haka kikeyi ne?,baki da hankali?" Cewar mamarta data matso kusa da gadon a
fusace,ta rasa meye matsalar diyartata,kullum kwanan duniya cikin dorata hanya da
gyara mata kurakurenta take amma a banza wai an tsikari kakkausa,cikin sauri anwar
ya dakatar da maman,ko mutuwa ma tana kunyar idanun mahaifi,hakanan kara da alkunya
ma wani abu ne,kuma shi alkhairi danqo ne baya faduwa qasa banza,nafisa diyarsu ce
kuma fadinma suna sonta bata baki ne,saidai su wasu irin mutane ne masu kunya kara
da kawaici,wanda soyayyar dansu bata hanasu ganin gaskiya
"Qyaleta mama" hakan shi ya tsaida hajiya ta koma da baya tana sauke numfashi,duban
nafisan yayi sosai sannan yace
"To kuma meye na kukan?,ya isa kiyi shuru kinga ba cikakkiyar lafiya ce dake ba"
"Indai kanason shuru na saika yarda kanasona zaka aureni ya anwar" alhj abba ne ya
soma takawa don barin dakin ganin rashin kunyar nafisan na qara gaba
"Zan aureki in sha Allah ki shuru" ajiyar zuciya dukkansu suka sauke wanda su kansu
basu san ta fito sarari ba saida suka hada ido da juna suka tabbatar anwar din yaji
sai kuma sukaji kunya,hakan shi ya tabbatarwa da anwar suma zancan na ransu,basason
tararsa ko tauyeshi ko tilastashi kan abinda bashi da niyya ko ra'ayi.

Wannan abun daya faru sai ya zama kamar wani lasisi nafisa ta samu na nuwa
anwar soyayya ko a gaban waye,wanda hakan ya sanya babu shiri ya qara qaimi wajen
gyaran gidansa,don yana ganin matyqar yaci gaba da zama a gidansu akwai matsala,don
nafisan kaman ta soma fitsare sawayenta,duk da yadda hajiya bilkisu ke taka mata
burki amma sam bataji,hudubar mima gani take itace dai dai don itace dai dai da
ra'ayinta.

Ta dage sosai wajen farauto zuciyarsa,da yake Allah shike sanya soyayya cikin
zukatan bayinsa duk irin kulawa da kyautatawar da take masa bai taba jin wani abu
mai kama da qaunarta ba cikin zuciyarsa,yana mata kallon qanwa tana kuma da qima a
idanunsa darajar mahaifanta da yadda suke sonshi.
Shekara biyu cur rayuwar anwar ta sauya,kai baka ce shine wannan anwar din
ba,kamanni yanayin rayuwa da komai nashi,saida zuciyar nan na nan,zuciyar dai itace
babu wani abu daya sauyata,a sannan alhj abba ya shirya bikin yaye wasu daga
ma'aikatansa wanda su suka buqaci haka don suci gashin kansu,ciki harda anwar wanda
tun dacan dama bai sha'awar zama qarqashin wani,yafison duk wahala yaci gashin
kansa,a lokacin da alhj abba ya yayesu ya danqawa kowanne kudin sallama,saidai
kudin anwar yafi na kowa yawa,ya zauna da alhj abban ya gaya masa zai amsa ya qara
cikin kudadensa,amma in sha Allahu zai dawo da dukka kudin da aka bashi,aljh abba
yace sam wannan kudin kyautane kawai saboda bauta da wahalar da suka yiwa kamfani,
a nutse anwar ya fahimtar dashi manufarsa,shidai yace yaje kawai ya kafa kanshi
din.

Komai na rayuwa wato yana da lokacinsa,hakanan rabon kwado bai hawa sama,anwar
ya tsaya tsayin daka,babu dare ba rana,babu lokacin bacci bana hutu sai daya
tabbatar ya kafu,ya fidda kudin alhj abba ya maida masa,shi kansa alhj abban yayi
mamakin yadda anwar din yayi kafuwar da aqalla kayi shekara goma sha bakayi irinta
ba,saidai yasan komai yassarewace ta ubangiji,shi kansa anwar yasan cewa qarfin
addu'ar iyaye tsayawa kai da fata kan gaskiya da riqe Allah da yayi shi ya kaishi
fa wannan matakin,tuni ya tamfatsawa anty usaina gida,saidai a sanda yace ta zabi
unguwa saita zabi unguwarsu shahida,farkon layinsu wasu gidaje da suka tashi suka
saida,daya tambayeta dalili tace ba ruwansa,ba yadda ya iya haka yayi mata yadda
tace tana so,saidai har aka kammala ginin bai taba taka qafarshi unguwar ba,data
koma kuma sai zuwan ya zame masa dan zani shima,sai daya sanya aka sake fasa qofa
ta bayan layinsu yake shiga ta nan.

Ganin lokaci yana ja anwar yaqi soma maganar aurensu babban burin daya rage
mata a duniya yasa ta soma masa shagube,qwarai ya fahimta saidai har yanzu baiji
nutsuwar zama da nafisa a matsayin matar aurensa ba,duk da ya sani tunda ya furta
dole ya cika amma har yanzu zuciyarsa taqi karban hakan,abinda yaketa yaqi akai
kenan,ita kuma tasan cewa iyayenta ba zasu taba yi masa batun ba,mutum daya ce nan
duniya zata ce yayi ya zame masa dole yayi anty husaina,dalili kenan da yasa ta
wanki qafa bisa shawarar mima taje mata da batun,wanda a yanzu haka akan qadamin da
suke kai kenan yanzu haka(idan baku manta ba a baya kunji inda anty usainan ke masa
maganar kar suji kunya kan nafisan).

Ta bangaren shahida ma kwanaki watanni zuwa shekaru sun soma tafiya,tuni ta


kammala degree dinta wanda ta samu gamasu da qananun shekarun da kowa ya kalleta
sai yayi mamaki,hakanan ta dora da masters shima Allah ya taimaketa ta kammalashi
cike da nasara mai tarin yawa,a sanda sakamakonta ya fito uncle hisham yaso ta
amshi tayin lacturing da jami'o'i suka yi mata tace sam bata ra'ayi,ya tura
takardunta kamfanoni da dama ta samu aiki daga wajensu nanma tace ba zatayi ba ciki
harda kamfaninsu,ba yadda ya iya hakanan ya qyaleta.

Sanda tazo masa da zancan koyarwa a *NOOR INTERNATIONAL* sai daya cire
gilashinsa ya kalleta don ya tabbatar da wasa take koda gaske,hakanan taji kawai
bata da burin daya wuce itama yaran talaka su amfana da karatu ilimi da baiwar da
Allah ya bata,ba haka yaso ba sam,saboda tayi karatu kai kyai wanda ya dace ta
tsaya ta moreshi tayi amfani dashi ta hanyar yin aiki a gurbi da kuma bigiren daya
dace,hanatayi kai tsaye yace maida kai baya ne,ta nace ta dage wansa ya sanyashi
dole ya amince,amma bisa wasu sharudan.

Duk sanda suka mata wani abu da bai gamsheshi ba to ba shakka ta gama koyarwa
a makatantar,kai tsaye ta amince don bata ga ma abinda zai gamota dasu ba bare wani
abun ya faru,kan wannan sharadin ta soma koyarwa cikin makarantar,ta kuma samu
karbuwa daga wajen dalibai har malamai,zama cikin makarantar kuma yayi mata,hakanan
yana mata dadi qwarai.

Wannan shine labarin taurarinmu guda biyu da abinda ya zama sanadiyyar


rabuwarsu ba tare dakowannensu yasan cewa MAQARQASHIYA CE ba.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Zaman bitar rayuwarsu ita da anwar din data tsaya yi daren jiya ba qaramin
taba zuciya ruhi da kuma gangar jikinta yayi ba,tayi kuka irin wanda ta jima ta
jefashi kwandon shara tare da yiwa kanta alqawarin ta daina har abada,dalilin daya
sanyata makara kenan bata kwanta da wuri ba,hakan ya sanyata bata tashi farkawa ba
sai qarfe bakwai na safe,ko sallar asuba ta qwace mata kenan,cikin hanzari ta sauko
daga saman gadonta duk da yadda jikinta yake a matuqar mace,hakanan ya mata nauyi
tun daga gangar jikinta zuwa kanta.

Tana idar da sallar da ake binta tana cikin yin azkar dinta na safiya huda
tayi knocking ta turo qofar,ta shirya tsaf cikin wankakku kuma gogaggun unifoarm
dinta,kai kace yau ne zata soma zuwa makarantar,fuskarta qunshe fal da walwala da
farinciki,saidai tana ganin alamun shahidan bata shirya ba ta turo baki kaman
zatayi kuka
"Anty...bakishirya ba,yaune fa?" Murmushi ta saki tana qarashe salatin annbi guda
goma da takeyi ta shafa sannan tace
"Banajin dadine yau huda"
"Amman zaki ko?" Ta tambayeta da sauri cikin fargabar kada tace ba zata samu zuwan
ba
"Zanje huda...amma inajin zamu makara da yawa fa" qafa ta soma bubbugawa shahidan
ta gane me take nufi
"Kinga...ki shirya a soma kaiki,idan yaso in ya dawo daga kaiki ni saiya
kaini,saimu hadu a hall din hakan yayi?" Kaita kada tana murmushi
"Bari naje naci abinci to" ta fadi tana juyawa a guje ta fita a dakin,sai data
bacewa ganinta sannan ta dauke kanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya,tanajin
inama ace itace hudan,quruciya abu ne mai dadi,baka da matsala baka da damuwa,dukka
ka tsere musu.

A nutse ta cire kayanta ta shige bandaki ta tara ruwan dumi ta soma


wanka,saboda yanayin jikin nata da batajin dadinsa yasa komai nata ma cikin nawaa
take yinsa,hakan ya sanya ta kashe kusan awa guda a wanka da shiryawa.

Ta jima gaban mudubi tana kallon fuskarta kaman yadda ta saba koda
yaushe,dukda idanunta sun dan sauya saboda kukan da tayi daren jiya amma sai taga
fuskarta tayi wasai,farar affaya mai taushi data nade jikinta ta amsheta
qwarai,akwai adon golden jikinta,hakanan taji kaman ta cireta,me yasa ma tayi
shigar ne?,batason dukkan wani abu da zai mata kyau a yanzu har yaja hankalin wani
zuwa gareta,ta saka hannu ta soma cire lullubin laffayar dake kanta anty zubaida ta
turo qofar ta shigo,wanda hakan ya tarwatsa abinda tayi niya
"Me kike haka?,yau lafiyanku kuwa shahida?"koda ta boyewa antyn yadda take qare
mata kallo tasan saita fahimceta,jin tayi shuru saita girgiza kai tana tabe baki
" damuwa dai damuwa dai?,ina zakikai damuwa shahida?,wannan kuma da kike niyyar
cireta fa?,don ta miki kyau?"dole yadda anty zubaidan tayi maganar ya baka
daroya,saita murmusa tana maida lullubin gami da zarar jakarta
"Ina kwana anty?"
"Lafiya lau ni zan fita inason idan ya saukeni saiya wuce dake makarantar basai ya
sake dawowa ya dauki wani ba"
"Tohm anty" tare suka fito daga dakin shahida ta wuce saman dining ta soma tsakurar
abinci,anty zubaida kuma ta koma dakinta don dauko mayafi da jakarta.

Sam abincin ji take bazai ciwu ba,don haka ta hada tea kawai tasha anty
zubaidan na fitowa suke fice tare.
Sun dan sake bata lokaci a hanya saboda cunkoson ababen hawa da suja tarar
a hanya wanda shahidan ta rasa na meye,titi ne da yake da wuya ka samu cunkuso
akanshi,ita kanta data dubi agogonta sai da taga makarar tayi yawa,da qyar suka
samu hanya suka wuce,ta sauke ajiyar zuciya sanda suka isa bakin katafaren ginin
makarantar noor international academy
"Yau ina tunanin zamu iya kaiwa biyu,saboda yaune hutu,idan mun tashi zan maka waya
in sanar maka"
"To babu matsala" ya fada yana tashin adaidaitan,tana tsaye kaman wadda aka dasa
har adaidaitan data sauketan tabar gurin,sannan ta soma takawa a hankali kaman mai
sanda zuwa cikin makarantar,haka kawai taji zuciyarta tayi mata nauyi,qafafunta
kuwa kaman an sare su,bugun zuciyarta na daduwa duk sanda ta qara wani taku guda da
zai kusantar da ita da cikin makarantar.

Harabar makarantar fetal,sai ababen hawan wasu daga cikin malamai da kuma
wasu baqin motoci guda uku da take kyautata zaton na baqonsu ne,shuru makarantar
take,hakan ke nuna mata cewa duk an tafi zuwa hall din da za'a gudanar da taron da
kuma hutun dalibai,ta dan tsaya tana shawarar ta soma kaiwa huda maganinta tasha
kota bari sai sun hadu a dakin taron?
"Malama shahida ya akayi haka?" Taji muryar kausar wadda ta fito daga can wani
sashe wanda zai sadaka da dakin taron,murmushin yaqe shahida tabi kausar dashi
saboda yadda takejin jikinta ba qwari haka kawai
"An sallami kowanne aji saura naki,yau tsarin na daban ne,inviglating ya yiwa
kowanne aji saiya gama dubaka sannan sai ku wuce kai da dalibanka dakin taron"
murya qasa qasa tace
"Yana naki ajin yanzu ku kawai ake jira a soma,kiyi sauri ki riskeshi donma yana da
kirki,nima amakare na iso amma ina bashi uzuri ya karba" kai kawai shahida ta kada
mata sannan ta soma takawa zuwa sashen azuzuwa.

Bayanshi take iya hangowa saboda qofa da ya baiwa baya,tsaye yake gaban
blackboard sanye da suits ash da suka zauna das a jikinsa,fuskanshi na kallon 'yan
ajin da alama wani abu yake saurara daga garesu.

Sautin fitar murmushinsa shi ya soma dukan kunnenta,bisa alama wani cikin
daliban ya fadi abinda ya bashi dariya
"To shikenan...next question....who is the best teacher in dis school?"
"Anty rahama...aunty rahama!" Suka hada baki dukkansu suna fada,abinda ya sake
sashi dariya qwarai,irin dariyar daya jima baiyi irinta ba,baisan wanne irinso
yaran kewa malamar tasu ba,komai anty rahama anty rahama,wai wace anty rahama nan
"Auntyyy" wasu daga cikin yaran da suka hango tsaiwarta bakin ajin suka fada cikin
shauqi da nuna qauna tamkar sunji tambayar da yakewa kanshi,duban yaran yayi sannan
a hankali ya waiwaya yana son yaga wace.

Shahida....shahida ce dai tsaye cikin shigar kamala ta lafaya,jakarta rataye a


kafadarta idanunta saye da farin gilashin daya zamto yana taimaka mata wajen
gani,sakamakon matsalar idanu da taso gamuwa dashi tun shekarun baya saboda yawaita
kukan da take,wani irin abu yaji yana zagayawa saman kanshi,tsigar jikinsa gaba
daya ta zuba,zuciyarsa ta kasu kashi biyu,kowanne sashe na zuciyar tasa da abinda
take ayyanawa.

Gaba daya jin jikinta tayi tamkar an zare dukkan wata laka data yi
saura,,nutsuwa tayi qaura daga jikinta a take,idanunta cikin nashi a hankali taga
yana juye mata daga anwar data sani zuwa wani mutum daban,matashin saurayi mai kyau
kwarjini kamala da haiba,matashin saurayi daya jiqu da hutu da naira,matashin
saurayi mai cikar zati,tsayayyen namiji wanda tambarin ilimi nutsuwa da wata
qasaita ta daban ta bayyana muraran kan fuskarshi,dukkan wani abu daya gani tattare
da ita shekarun baya suka soma dawowa idanunshi daya bayan daya,hotunan da idan ya
tuno dasu suke hanashi bacci duk dare,ganinta cikin halin maye,jinin zubda ciki na
gangarowa daga qafafunta,yaci gaba da kallonta yana takowa inda take tsaye cak,sai
yaga kaman a sannan ne abinda ke jikin hotunan ke faruwa,take cikin 'yan sakannin
da bai wuce ka qirgasu da yatsunta biyu zuwa hudu ba idanunsa ya sauya
launi,jijiyar kanshi ta motsa ta tashi,sai daya zo dab da ita sannan yace
"Kina nufin a haka zaki baiwa yaran mutane tarbiyya?,a haka kike koyar da yaran
jama'a?,na tambayeki ma me kike koya musu?,uhmmm gayamin,?,yadda zasu....." Sai
kuma ya kasa qarasawa ya kaiwa iska wafta da hannunshi sannan ya dunquleshi tsam
kaman zai tatse dukkan jinin dake cikin hannun nashi gaba daya,dai dai sanda
shugaba kula da dukka sashen makarantar ya iso ganin shuru har yanzu bai iso
ba,cikin girmamawa ya rusuna
"Sir....."
"Dakata!" Ya tsaidashi cikin tsawa
"Dama irin wadan nan malaman kuke baiwa yara su koyar?" Cikin mamaki ya dubi
shahida da yake nuna masa,wadda take tsaye qam a wajen kaman an dasata idanunta kan
anwar,tana jin wani fushi na ratsata amma tana ta qoqarin hana hakan tasiri
"Sir.....kodai wani akasi aka samu,amma malama shahida na daya daga cikin malaman
da kaf makarantar nan babu kamarsu a kowanne sashe"
"Sauraramin" ya kuma dakatar dashi wannan karon har yana daga mishi hannu,ya maida
idanunsa cikin nata
"Indai wannan ce malamar da babu kamarta tabbas bakusan abinda kuke ba,babu abinda
ta iya!,bata iya komai ba!,daga yau na koreta!,na koreta cikin malaman makarantar
nan.....kar qafarki ta sake tako mana makaranta,you are fired!" Dukkan wani qwarin
gwiwa da taso tattarowa ya tarwatse da kalmarshi na qarshe saboda yadda sautin ya
fito ya bada amsa kuwwa cikin ajin,qoqarin tattaro abinda zata fada take saidai
bakinta ya gaza fidda sautin saboda karayar da zuciyarta tayi,idanunta suka hada
qwalla fal suna shirin ga gangarowa,saiya sake saka idanunsa cikin nata cikin wani
qwarin gwiwa da yake ji yace
"Uhmm...kina da wani abun cewa ne?....say it....say it mana!" Ya kuma fada cikin
hargagi yana dan dukan qirjinsa da yatsunshi gaba daya,jakar dake kafadarta ce ta
sulmiyo saboda yadda jikinta ya soma rawa,gaba daya kayan ciki suka tarwatse a
wajen ciki harda kwalaben magungunan huda,a kansu idanunsa suka soma sauka,wani
tashin hankali da baisan na meye ba ya rufto masa,saiya daga kai da sauri yana
kallonta,sam ko daya bata da nutsuwar da zata iya tsaiwa ta tattare kayayyakinta ko
ta dauki jakar,hakan yasa ta juya da sauri ta soma takawa,fatanta da burinta kawai
shine tabar makarantar,tabar wajen,tabar inuwar da anwar yake tsaye a
cikinta,burinta shine ta nesanta dashi kawai,ta daina ganinsa ta kuma daina jin
sautinsa
"Ki dawo ki debi wannan kayan zatar naki" maimakon dawowar kamar yadda ya buqata
saita qara sauri kamar wadda aka biyo,don burinta shine ficewa daga makarantar ta
tserewa sautinsa,wannan sautin da ta jima da neman tsari dashi da mamallakinsa.

Titi kawai ta miqa bata ko waiwaye,bata buqatar abun hawa don ji take kaman
qafafunta zasuyi mata aiki fiye da abun hawan,sauri kawai take zubawa wani irin
radadi na keta zuciyarta kamar ana yankarta da reza,anwar dai anwar dai?,tabbas da
tasan akwai wata rana da zasu sake haduwa kaman haka da tuni ta yiwa kanta
kandagarki da ita,wannan wace irin baqar rana ce a wajenta
"Anty shahida...anty shahida" taji ana qwalla mata kira wanda sam bata tsaya ba har
sai da akasha gabanta,shugaban sashe ne riqe da jakarta ya miqa mata
"Don girman Allah kiyi haquri anty shahida,ya dauki hukuncin da dukkanmu bamu isa
mu sauya shi ba"

👑*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai
buqata saita tuntubi wadan nan numbers*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*kuyi subscribing youtube channel dina don samun damar ganin shirye
shiryenmu,subscribe kyauta ne!*👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

1️⃣ 8️⃣
*Alqawarin Allah*
1️⃣8️⃣

Kanshi yaji yayi masa nauyi kaman an dora masa dutse,kafin ya ankara nafisa ta saki
kuka tana roqonshi,dukkansu ya tabbatar hankulansu da kunnuwansu na wajen,haka
yake,don dukansu fata yace ya amince,don sun yarda da hankali da nutsuwar anwar,sun
tabbatar idan ya auri diyarsu ta fada hannun dako bayan ransu basa kokwanto ko
shakka,saidai ta bangarin mamanta magiyar da take ta taba ranta ta kuma bata
takaici
"Meye haka kikeyi ne?,baki da hankali?" Cewar mamarta data matso kusa da gadon a
fusace,ta rasa meye matsalar diyartata,kullum kwanan duniya cikin dorata hanya da
gyara mata kurakurenta take amma a banza wai an tsikari kakkausa,cikin sauri anwar
ya dakatar da maman,ko mutuwa ma tana kunyar idanun mahaifi,hakanan kara da alkunya
ma wani abu ne,kuma shi alkhairi danqo ne baya faduwa qasa banza,nafisa diyarsu ce
kuma fadinma suna sonta bata baki ne,saidai su wasu irin mutane ne masu kunya kara
da kawaici,wanda soyayyar dansu bata hanasu ganin gaskiya
"Qyaleta mama" hakan shi ya tsaida hajiya ta koma da baya tana sauke numfashi,duban
nafisan yayi sosai sannan yace
"To kuma meye na kukan?,ya isa kiyi shuru kinga ba cikakkiyar lafiya ce dake ba"
"Indai kanason shuru na saika yarda kanasona zaka aureni ya anwar" alhj abba ne ya
soma takawa don barin dakin ganin rashin kunyar nafisan na qara gaba
"Zan aureki in sha Allah ki shuru" ajiyar zuciya dukkansu suka sauke wanda su kansu
basu san ta fito sarari ba saida suka hada ido da juna suka tabbatar anwar din yaji
sai kuma sukaji kunya,hakan shi ya tabbatarwa da anwar suma zancan na ransu,basason
tararsa ko tauyeshi ko tilastashi kan abinda bashi da niyya ko ra'ayi.

Wannan abun daya faru sai ya zama kamar wani lasisi nafisa ta samu na nuwa
anwar soyayya ko a gaban waye,wanda hakan ya sanya babu shiri ya qara qaimi wajen
gyaran gidansa,don yana ganin matyqar yaci gaba da zama a gidansu akwai matsala,don
nafisan kaman ta soma fitsare sawayenta,duk da yadda hajiya bilkisu ke taka mata
burki amma sam bataji,hudubar mima gani take itace dai dai don itace dai dai da
ra'ayinta.

Ta dage sosai wajen farauto zuciyarsa,da yake Allah shike sanya soyayya cikin
zukatan bayinsa duk irin kulawa da kyautatawar da take masa bai taba jin wani abu
mai kama da qaunarta ba cikin zuciyarsa,yana mata kallon qanwa tana kuma da qima a
idanunsa darajar mahaifanta da yadda suke sonshi.

Shekara biyu cur rayuwar anwar ta sauya,kai baka ce shine wannan anwar din
ba,kamanni yanayin rayuwa da komai nashi,saida zuciyar nan na nan,zuciyar dai itace
babu wani abu daya sauyata,a sannan alhj abba ya shirya bikin yaye wasu daga
ma'aikatansa wanda su suka buqaci haka don suci gashin kansu,ciki harda anwar wanda
tun dacan dama bai sha'awar zama qarqashin wani,yafison duk wahala yaci gashin
kansa,a lokacin da alhj abba ya yayesu ya danqawa kowanne kudin sallama,saidai
kudin anwar yafi na kowa yawa,ya zauna da alhj abban ya gaya masa zai amsa ya qara
cikin kudadensa,amma in sha Allahu zai dawo da dukka kudin da aka bashi,aljh abba
yace sam wannan kudin kyautane kawai saboda bauta da wahalar da suka yiwa kamfani,
a nutse anwar ya fahimtar dashi manufarsa,shidai yace yaje kawai ya kafa kanshi
din.

Komai na rayuwa wato yana da lokacinsa,hakanan rabon kwado bai hawa sama,anwar
ya tsaya tsayin daka,babu dare ba rana,babu lokacin bacci bana hutu sai daya
tabbatar ya kafu,ya fidda kudin alhj abba ya maida masa,shi kansa alhj abban yayi
mamakin yadda anwar din yayi kafuwar da aqalla kayi shekara goma sha bakayi irinta
ba,saidai yasan komai yassarewace ta ubangiji,shi kansa anwar yasan cewa qarfin
addu'ar iyaye tsayawa kai da fata kan gaskiya da riqe Allah da yayi shi ya kaishi
fa wannan matakin,tuni ya tamfatsawa anty usaina gida,saidai a sanda yace ta zabi
unguwa saita zabi unguwarsu shahida,farkon layinsu wasu gidaje da suka tashi suka
saida,daya tambayeta dalili tace ba ruwansa,ba yadda ya iya haka yayi mata yadda
tace tana so,saidai har aka kammala ginin bai taba taka qafarshi unguwar ba,data
koma kuma sai zuwan ya zame masa dan zani shima,sai daya sanya aka sake fasa qofa
ta bayan layinsu yake shiga ta nan.

Ganin lokaci yana ja anwar yaqi soma maganar aurensu babban burin daya rage
mata a duniya yasa ta soma masa shagube,qwarai ya fahimta saidai har yanzu baiji
nutsuwar zama da nafisa a matsayin matar aurensa ba,duk da ya sani tunda ya furta
dole ya cika amma har yanzu zuciyarsa taqi karban hakan,abinda yaketa yaqi akai
kenan,ita kuma tasan cewa iyayenta ba zasu taba yi masa batun ba,mutum daya ce nan
duniya zata ce yayi ya zame masa dole yayi anty husaina,dalili kenan da yasa ta
wanki qafa bisa shawarar mima taje mata da batun,wanda a yanzu haka akan qadamin da
suke kai kenan yanzu haka(idan baku manta ba a baya kunji inda anty usainan ke masa
maganar kar suji kunya kan nafisan).

Ta bangaren shahida ma kwanaki watanni zuwa shekaru sun soma tafiya,tuni ta


kammala degree dinta wanda ta samu gamasu da qananun shekarun da kowa ya kalleta
sai yayi mamaki,hakanan ta dora da masters shima Allah ya taimaketa ta kammalashi
cike da nasara mai tarin yawa,a sanda sakamakonta ya fito uncle hisham yaso ta
amshi tayin lacturing da jami'o'i suka yi mata tace sam bata ra'ayi,ya tura
takardunta kamfanoni da dama ta samu aiki daga wajensu nanma tace ba zatayi ba ciki
harda kamfaninsu,ba yadda ya iya hakanan ya qyaleta.

Sanda tazo masa da zancan koyarwa a *NOOR INTERNATIONAL* sai daya cire
gilashinsa ya kalleta don ya tabbatar da wasa take koda gaske,hakanan taji kawai
bata da burin daya wuce itama yaran talaka su amfana da karatu ilimi da baiwar da
Allah ya bata,ba haka yaso ba sam,saboda tayi karatu kai kyai wanda ya dace ta
tsaya ta moreshi tayi amfani dashi ta hanyar yin aiki a gurbi da kuma bigiren daya
dace,hanatayi kai tsaye yace maida kai baya ne,ta nace ta dage wansa ya sanyashi
dole ya amince,amma bisa wasu sharudan.

Duk sanda suka mata wani abu da bai gamsheshi ba to ba shakka ta gama koyarwa
a makatantar,kai tsaye ta amince don bata ga ma abinda zai gamota dasu ba bare wani
abun ya faru,kan wannan sharadin ta soma koyarwa cikin makarantar,ta kuma samu
karbuwa daga wajen dalibai har malamai,zama cikin makarantar kuma yayi mata,hakanan
yana mata dadi qwarai.

Wannan shine labarin taurarinmu guda biyu da abinda ya zama sanadiyyar


rabuwarsu ba tare dakowannensu yasan cewa MAQARQASHIYA CE ba.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Zaman bitar rayuwarsu ita da anwar din data tsaya yi daren jiya ba qaramin
taba zuciya ruhi da kuma gangar jikinta yayi ba,tayi kuka irin wanda ta jima ta
jefashi kwandon shara tare da yiwa kanta alqawarin ta daina har abada,dalilin daya
sanyata makara kenan bata kwanta da wuri ba,hakan ya sanyata bata tashi farkawa ba
sai qarfe bakwai na safe,ko sallar asuba ta qwace mata kenan,cikin hanzari ta sauko
daga saman gadonta duk da yadda jikinta yake a matuqar mace,hakanan ya mata nauyi
tun daga gangar jikinta zuwa kanta.
Tana idar da sallar da ake binta tana cikin yin azkar dinta na safiya huda
tayi knocking ta turo qofar,ta shirya tsaf cikin wankakku kuma gogaggun unifoarm
dinta,kai kace yau ne zata soma zuwa makarantar,fuskarta qunshe fal da walwala da
farinciki,saidai tana ganin alamun shahidan bata shirya ba ta turo baki kaman
zatayi kuka
"Anty...bakishirya ba,yaune fa?" Murmushi ta saki tana qarashe salatin annbi guda
goma da takeyi ta shafa sannan tace
"Banajin dadine yau huda"
"Amman zaki ko?" Ta tambayeta da sauri cikin fargabar kada tace ba zata samu zuwan
ba
"Zanje huda...amma inajin zamu makara da yawa fa" qafa ta soma bubbugawa shahidan
ta gane me take nufi
"Kinga...ki shirya a soma kaiki,idan yaso in ya dawo daga kaiki ni saiya
kaini,saimu hadu a hall din hakan yayi?" Kaita kada tana murmushi
"Bari naje naci abinci to" ta fadi tana juyawa a guje ta fita a dakin,sai data
bacewa ganinta sannan ta dauke kanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya,tanajin
inama ace itace hudan,quruciya abu ne mai dadi,baka da matsala baka da damuwa,dukka
ka tsere musu.

A nutse ta cire kayanta ta shige bandaki ta tara ruwan dumi ta soma


wanka,saboda yanayin jikin nata da batajin dadinsa yasa komai nata ma cikin nawaa
take yinsa,hakan ya sanya ta kashe kusan awa guda a wanka da shiryawa.

Ta jima gaban mudubi tana kallon fuskarta kaman yadda ta saba koda
yaushe,dukda idanunta sun dan sauya saboda kukan da tayi daren jiya amma sai taga
fuskarta tayi wasai,farar affaya mai taushi data nade jikinta ta amsheta
qwarai,akwai adon golden jikinta,hakanan taji kaman ta cireta,me yasa ma tayi
shigar ne?,batason dukkan wani abu da zai mata kyau a yanzu har yaja hankalin wani
zuwa gareta,ta saka hannu ta soma cire lullubin laffayar dake kanta anty zubaida ta
turo qofar ta shigo,wanda hakan ya tarwatsa abinda tayi niya
"Me kike haka?,yau lafiyanku kuwa shahida?"koda ta boyewa antyn yadda take qare
mata kallo tasan saita fahimceta,jin tayi shuru saita girgiza kai tana tabe baki
" damuwa dai damuwa dai?,ina zakikai damuwa shahida?,wannan kuma da kike niyyar
cireta fa?,don ta miki kyau?"dole yadda anty zubaidan tayi maganar ya baka
daroya,saita murmusa tana maida lullubin gami da zarar jakarta
"Ina kwana anty?"
"Lafiya lau ni zan fita inason idan ya saukeni saiya wuce dake makarantar basai ya
sake dawowa ya dauki wani ba"
"Tohm anty" tare suka fito daga dakin shahida ta wuce saman dining ta soma tsakurar
abinci,anty zubaida kuma ta koma dakinta don dauko mayafi da jakarta.

Sam abincin ji take bazai ciwu ba,don haka ta hada tea kawai tasha anty
zubaidan na fitowa suke fice tare.

Sun dan sake bata lokaci a hanya saboda cunkoson ababen hawa da suja tarar
a hanya wanda shahidan ta rasa na meye,titi ne da yake da wuya ka samu cunkuso
akanshi,ita kanta data dubi agogonta sai da taga makarar tayi yawa,da qyar suka
samu hanya suka wuce,ta sauke ajiyar zuciya sanda suka isa bakin katafaren ginin
makarantar noor international academy
"Yau ina tunanin zamu iya kaiwa biyu,saboda yaune hutu,idan mun tashi zan maka waya
in sanar maka"
"To babu matsala" ya fada yana tashin adaidaitan,tana tsaye kaman wadda aka dasa
har adaidaitan data sauketan tabar gurin,sannan ta soma takawa a hankali kaman mai
sanda zuwa cikin makarantar,haka kawai taji zuciyarta tayi mata nauyi,qafafunta
kuwa kaman an sare su,bugun zuciyarta na daduwa duk sanda ta qara wani taku guda da
zai kusantar da ita da cikin makarantar.

Harabar makarantar fetal,sai ababen hawan wasu daga cikin malamai da kuma
wasu baqin motoci guda uku da take kyautata zaton na baqonsu ne,shuru makarantar
take,hakan ke nuna mata cewa duk an tafi zuwa hall din da za'a gudanar da taron da
kuma hutun dalibai,ta dan tsaya tana shawarar ta soma kaiwa huda maganinta tasha
kota bari sai sun hadu a dakin taron?
"Malama shahida ya akayi haka?" Taji muryar kausar wadda ta fito daga can wani
sashe wanda zai sadaka da dakin taron,murmushin yaqe shahida tabi kausar dashi
saboda yadda takejin jikinta ba qwari haka kawai
"An sallami kowanne aji saura naki,yau tsarin na daban ne,inviglating ya yiwa
kowanne aji saiya gama dubaka sannan sai ku wuce kai da dalibanka dakin taron"
murya qasa qasa tace
"Yana naki ajin yanzu ku kawai ake jira a soma,kiyi sauri ki riskeshi donma yana da
kirki,nima amakare na iso amma ina bashi uzuri ya karba" kai kawai shahida ta kada
mata sannan ta soma takawa zuwa sashen azuzuwa.

Bayanshi take iya hangowa saboda qofa da ya baiwa baya,tsaye yake gaban
blackboard sanye da suits ash da suka zauna das a jikinsa,fuskanshi na kallon 'yan
ajin da alama wani abu yake saurara daga garesu.

Sautin fitar murmushinsa shi ya soma dukan kunnenta,bisa alama wani cikin
daliban ya fadi abinda ya bashi dariya
"To shikenan...next question....who is the best teacher in dis school?"
"Anty rahama...aunty rahama!" Suka hada baki dukkansu suna fada,abinda ya sake
sashi dariya qwarai,irin dariyar daya jima baiyi irinta ba,baisan wanne irinso
yaran kewa malamar tasu ba,komai anty rahama anty rahama,wai wace anty rahama nan
"Auntyyy" wasu daga cikin yaran da suka hango tsaiwarta bakin ajin suka fada cikin
shauqi da nuna qauna tamkar sunji tambayar da yakewa kanshi,duban yaran yayi sannan
a hankali ya waiwaya yana son yaga wace.

Shahida....shahida ce dai tsaye cikin shigar kamala ta lafaya,jakarta rataye a


kafadarta idanunta saye da farin gilashin daya zamto yana taimaka mata wajen
gani,sakamakon matsalar idanu da taso gamuwa dashi tun shekarun baya saboda yawaita
kukan da take,wani irin abu yaji yana zagayawa saman kanshi,tsigar jikinsa gaba
daya ta zuba,zuciyarsa ta kasu kashi biyu,kowanne sashe na zuciyar tasa da abinda
take ayyanawa.

Gaba daya jin jikinta tayi tamkar an zare dukkan wata laka data yi
saura,,nutsuwa tayi qaura daga jikinta a take,idanunta cikin nashi a hankali taga
yana juye mata daga anwar data sani zuwa wani mutum daban,matashin saurayi mai kyau
kwarjini kamala da haiba,matashin saurayi daya jiqu da hutu da naira,matashin
saurayi mai cikar zati,tsayayyen namiji wanda tambarin ilimi nutsuwa da wata
qasaita ta daban ta bayyana muraran kan fuskarshi,dukkan wani abu daya gani tattare
da ita shekarun baya suka soma dawowa idanunshi daya bayan daya,hotunan da idan ya
tuno dasu suke hanashi bacci duk dare,ganinta cikin halin maye,jinin zubda ciki na
gangarowa daga qafafunta,yaci gaba da kallonta yana takowa inda take tsaye cak,sai
yaga kaman a sannan ne abinda ke jikin hotunan ke faruwa,take cikin 'yan sakannin
da bai wuce ka qirgasu da yatsunta biyu zuwa hudu ba idanunsa ya sauya
launi,jijiyar kanshi ta motsa ta tashi,sai daya zo dab da ita sannan yace
"Kina nufin a haka zaki baiwa yaran mutane tarbiyya?,a haka kike koyar da yaran
jama'a?,na tambayeki ma me kike koya musu?,uhmmm gayamin,?,yadda zasu....." Sai
kuma ya kasa qarasawa ya kaiwa iska wafta da hannunshi sannan ya dunquleshi tsam
kaman zai tatse dukkan jinin dake cikin hannun nashi gaba daya,dai dai sanda
shugaba kula da dukka sashen makarantar ya iso ganin shuru har yanzu bai iso
ba,cikin girmamawa ya rusuna
"Sir....."
"Dakata!" Ya tsaidashi cikin tsawa
"Dama irin wadan nan malaman kuke baiwa yara su koyar?" Cikin mamaki ya dubi
shahida da yake nuna masa,wadda take tsaye qam a wajen kaman an dasata idanunta kan
anwar,tana jin wani fushi na ratsata amma tana ta qoqarin hana hakan tasiri
"Sir.....kodai wani akasi aka samu,amma malama shahida na daya daga cikin malaman
da kaf makarantar nan babu kamarsu a kowanne sashe"
"Sauraramin" ya kuma dakatar dashi wannan karon har yana daga mishi hannu,ya maida
idanunsa cikin nata
"Indai wannan ce malamar da babu kamarta tabbas bakusan abinda kuke ba,babu abinda
ta iya!,bata iya komai ba!,daga yau na koreta!,na koreta cikin malaman makarantar
nan.....kar qafarki ta sake tako mana makaranta,you are fired!" Dukkan wani qwarin
gwiwa da taso tattarowa ya tarwatse da kalmarshi na qarshe saboda yadda sautin ya
fito ya bada amsa kuwwa cikin ajin,qoqarin tattaro abinda zata fada take saidai
bakinta ya gaza fidda sautin saboda karayar da zuciyarta tayi,idanunta suka hada
qwalla fal suna shirin ga gangarowa,saiya sake saka idanunsa cikin nata cikin wani
qwarin gwiwa da yake ji yace
"Uhmm...kina da wani abun cewa ne?....say it....say it mana!" Ya kuma fada cikin
hargagi yana dan dukan qirjinsa da yatsunshi gaba daya,jakar dake kafadarta ce ta
sulmiyo saboda yadda jikinta ya soma rawa,gaba daya kayan ciki suka tarwatse a
wajen ciki harda kwalaben magungunan huda,a kansu idanunsa suka soma sauka,wani
tashin hankali da baisan na meye ba ya rufto masa,saiya daga kai da sauri yana
kallonta,sam ko daya bata da nutsuwar da zata iya tsaiwa ta tattare kayayyakinta ko
ta dauki jakar,hakan yasa ta juya da sauri ta soma takawa,fatanta da burinta kawai
shine tabar makarantar,tabar wajen,tabar inuwar da anwar yake tsaye a
cikinta,burinta shine ta nesanta dashi kawai,ta daina ganinsa ta kuma daina jin
sautinsa
"Ki dawo ki debi wannan kayan zatar naki" maimakon dawowar kamar yadda ya buqata
saita qara sauri kamar wadda aka biyo,don burinta shine ficewa daga makarantar ta
tserewa sautinsa,wannan sautin da ta jima da neman tsari dashi da mamallakinsa.

Titi kawai ta miqa bata ko waiwaye,bata buqatar abun hawa don ji take kaman
qafafunta zasuyi mata aiki fiye da abun hawan,sauri kawai take zubawa wani irin
radadi na keta zuciyarta kamar ana yankarta da reza,anwar dai anwar dai?,tabbas da
tasan akwai wata rana da zasu sake haduwa kaman haka da tuni ta yiwa kanta
kandagarki da ita,wannan wace irin baqar rana ce a wajenta
"Anty shahida...anty shahida" taji ana qwalla mata kira wanda sam bata tsaya ba har
sai da akasha gabanta,shugaban sashe ne riqe da jakarta ya miqa mata
"Don girman Allah kiyi haquri anty shahida,ya dauki hukuncin da dukkanmu bamu isa
mu sauya shi ba"

👑*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina
buqatar siya ki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*kuyi subscribing youtube channel dina don samun damar ganin shirye
shiryenmu,subscribe kyauta ne!*
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos

1️⃣ 9️⃣
*Alqawarin Allah*
1️⃣9️⃣

"sabon abune wannan a wajenmu,abinda bamu taba gani yayi ba tunda muke
dashi,kowa ya shaidai wannan kirkin nasa....anty shahida kodai wani abu kika
masa?,mutumin qwarai irin haka canzawarsa...."da sauri ta yanke masa hanzari
"Na gode malam,haka Allah ya qaddara" gaba tayi da sauri don ita kadai tasan me
take ji,ita daya tasan ya take ji,baifi taku biyar ba adaidaita sahu tasha gabanta
tana tambayarta ina zata je?,sai data shiga sannan ta gaya mishi inda zai kaita,duk
yadda taso daure zuciyarta ta bari saita isa gida saita kasa,ta tattakura ta rushe
da kuka wanda har sai da dan sahun ya waiwayo
"Hajiya...lafiya?,kiyi haquri komai yayi zafi maganinsa Allah" ita dai bata iya
tanka masa ba illa kukanta data ci gaba dayi.

Komao nata ta wurgar tsakar dakinta sannnan ta zauna dirshan tana risgar
kuka,tanajin kaman ranta zai fita ne,duk wata nutsuwarta a yanzu babu ita,anwar dai
shi idanunta suka gani?,anwar shine ya mata wannan tozarcin?,wanne abu tayi mai
munin da har zaikai anwar ya kasa mantawa irin haka ya sake binta da mummunan
shaida da wulaqanci?.

Kusan haka ta dauki dogon lokaci,wanda ita din batasan wadanne awanni ta
shafe haka ba,sai tsintar muryoyin anty zubaida tayi da huda,taso qwarai ta tashi
amma ta kasa saboda wani mugun ciwo da kanta yake mata,da qyar take iya motsawa
bayaga idanunta da suka zama tamkar fulawar da aka zubawa yeast,muryar saddiq taji
yana cewa
"Mummy...tana dakinta" a hankali anty zubaida ta turo qofar tana cewa
"Alhmdlh,shahida kin daga mana hankali,ina kika shiga haka ke kuwa don Allah" ta
qarashe maganar tana qarasowa kanta,zaro ido anty zubaida tayi ganin irin rawar
darin da take yi
"Subhanallahi,ashe bakyajin dadi" ta qaraso gefan gadon shahida ta zauna tana
qoqarin yaye rufar da tayi,da qyar da taimakon anty zubaidan ta tashi ta zauna
sosai,qarya tayi mata kan tana shiga makaranta zazzabi ya saukar mata shi yasa ta
dawo bata kai ga zuwa dakin hutun ba ganin yadda duk suka damu daga anty zubaidan
har su saddiq,farouq anty zubaida ta saka ya hada mata ruwan wanka,saddiq ya zubo
mata abinci,ita taimaka mata ta shiga bandaki tayi wanka gami da daura alwalar
sallar azahar da magariba da duka bata samu yinsu ba,bata bar dakin ba sai data ga
taci abinci ta kuma sha magani sannan.

Tana daga kwancen amma hawaye take sharcewa masu dumi,duk yadda taso ga
kaucewa anwar da shafe duk wani abu daya shafeshi amma haka yaci tura?,wai sai
yaushe?,sai yaushe zaibar rayuwarta zuciyarta da kuma ruhinta ya huta?wunin ranar
gaba daya wani irin wahalallen yini tayi,ba shakka anwar ya zamewa rayuwarta babban
qalubale,har zuwa dare tana cikin yanayi guda wanda da qyar da sudin goshi ta samu
wani wahalallen bacci ya dauketa.

********* **********

A hankali ya daga cup din qarshe na coffe din da yayi saura ya kwankwade
wanda shi kansa baisan kofi nawa yasha ba tsahon awannin daya kwashe zaune a
wajen,idanunsa jajur suke kai kace an badawa idanunsa yaji ne a ciki,saidai yaqi
yarda ko kusa ko alama a kira masa likita ya dubashi,bugu da qari dumin jikinsa ya
qaru sosai har kana iya juyo hucinsa idan ya fidda iska daga bakinsa.

Lumshe idanunsa yayi ya dora hannunsa saman sumarshi mai tauri saidai a gyare
take matuqa yana yamutsata,buri yake inama ya iya kuka idan yana cikin tashin
hankali ko tsanani,inama hawaye zasu fita daga idanunshi ko zai samu sauqin radadin
da yake ji?,cikin sauri ya sake bude idanun shi wanda suka sake kadawa fiye da
dazu,ko yaya ya runtsesu kwalaben da suka zubo daga jakarta yake gani,hakan yana
nuna har yau bata bar dabu'arta ba?,waishin waye ne?,waye ya koya mata wannan
dabi'ar?,babu shakka da zaisan waye shida ita duka saiya hadasu ya hukuntasu,dukan
teburin gabansa yayi da hannunsa ko zaiji sauqin radadin da zuciyarsa ke masa amma
a banza.

Knocking katafariyar qofar falon aka somayi wanda yana ji yayi funfurus,saidai
ya cika ya batse saboda koma waye yana son sake birkita masa lissafi ne,bayan kuma
ya riga da yaja kunnen duka ma'aikatan gidan na kada wanda ya sake yako doshi
sashensa.

Knociking din jinsa yake har qwaqwalwarsa,hakan ya sanya ya miqe a fusace ya


isa qofar ya budeta ya kuma bude baki don zazzagewa koma waye masifa,muhsin ne
bayanshi likita ne tsaye cikin fararen kayan aiki,dole ya hadiye abinda yaso
amayarwa ya saki qofar ya juya zuwa cikin falon ya zabi wata kujerar sabanin wadda
ya tashi daga kai ya zube yana maida numfashi,kallo daya muhsin yayi masa baice
dashi komai ba ya kalli likitan sannan ya maida idonsa ga anwar din
"Zaka iya aikinka" yace dashi,saiyaka jinjina kai ya soma takawa inda anwar ke
zaune ya aje akwatinshi kana ya bude,ya ciro abun gwada B.P ya daura a hannun anwar
ya soma gwadawa,cikin sakannin da basu wuce goma ba ya warware abun daga dantsensa
ya samu kujerar dake daura dashi ya zauna sosai idanunsa a kanshi
"Yallabai....kasan yadda jininka ya sake hawa kuwa?" Ya tambayeshi kanshi tsaye
"Na sani" shima ya bashi amsa bayan ya sake bude dukka idanunshi akan likitan,cikin
mamaki likitan ya maida dubanshi ga muhsin,saiya masa alama daya rubuta magani
kawai ya qyaleshi,hakan kuwa akayi ya rubuta maganin ya baiwa muhsin takardar
sannan ya tattara kayanshi ya yuwa muhsin din sallama ya wuce.

Sai daya tabbatar da fitar likitan sannan ya miqe riqe da takardar maganin ya
qaraso inda anwar din ke zaune,idanu ya zuba masa yana kallonsa wanda hakan ya
sanya anwar kau da kai
"Tsahon shekaru kana fama da wannan damuwar,kaqi gayawa kowa dalilinta,kaqi gayawa
kowa dalilin faruwarta,duk dai amma bazai wuce akan shahida ba,anya kuwa anwar
anya?,me yasa kake shirye shiryen halaka kanka ne babu gaira babu dalili?" Zumbur
ya miqe ya soma takawa don barin gurin
"Kar sake cewa dominta ne,na riga dana shafe babinta kamar yadda na shafe babin
komai daya faru dani a baya" qara sauri yayi ya wuce zuwa bedroom dinsa yanason
baiwa kansa qwarin gwiwa don baison ma anty husaina taji cewa baida lafiya,yanzu
dukkan tsofaffin matsaloli zasu taso,magana wata nabin wata har sai yaji kaman
kanshi zai tarwatse.

Kwananta goma sha hudu tana qoqarin saisaita kanta da maida kanta cikin
yanayin daya dace,yaqi tayi ba dan qarami ba a kwanakin da kanta,ta rame qwarai
saboda jinya tasha sosai,bata fita ko ina,hakanan hatta da wayarta ma a kashe
take,daga daki sai daki,sam anty zubaida batasan meye ya faru ba,saidai dukkaninsu
tattalinta suke har ta soma jin dadin jikinta.

Ranar wata karaba qarfe hudu na yammaci ta fito daga dakinta,gidan yayi
mata shuru haka yayi mata fadi,haka take ji duk sanda su huda suka wuce islamiyya
saisu barta daga ita sai anty zubaida kawai,hakan ya sanyata tunanin samo islamiyya
itama da zata dinga zuwa daukan karatu,don sanda ta fada din anty zubaida dariya ta
dinga mata
"Ohni zubaida,shahida bansan inda zakikai wannan son karatun naki ba" murmushi
kawai tayi
"Anty karatu fa baya yawa,indai ba mutuwa kayi ba ilimi bai yanke maka ba,ba zaka
rasa cin karo da wani abun da baka sanshi ba"
"Gaskiya ne" ta fada cikin nuna gamsuwa.

Sanye take da atampha riga da zani wrapper,sai qaramin mayafi data yane kanta
dashi,ta sake haske haka ta fada,a hankali take takawa har zuwa cikin ainihin
falon,babu kowa kaman yadda ta zata,sabida haka ta juya ta nufi kitchen don tasan a
wannan lokacin anty zubaida tana can.

Da sallama a bakinta ta shiga da dashasshiyar muryarta irin ta marasa


lpy,anty zubaida ta juyo tana amsawa fuskarta qunshe da murmushi
"Patient an taso kenan"
"Wallahi anty...na gaji da kwanciyar nan" ta furta tana jan kujera ta zauna akai
"Ai gwara ki tattaka ko zakiji dadin jikinki" sama sama suke hira ita da anty
zubaidan,inda tana daga zaune ta amshi wasu ayyukan tana tayata,a haka su faruq
suka dawo daga islamiyya suka tarar dasu,zama sukai cikin kitchen din suma,saidai
basu bar bakin anty zubaida ya huta ba,wannan ya buda wancan wannan ya buda wannan
wai duka yunwa sukeji,sudai tunda anty shahida ta soma lalura kawai gidan sai a
slow,waiwayowa anty zubaidan tayi
"Kinga shahida...don Allah debe qannenkin nan ku bani waje na yafe taya aikin
wallahi" dariya shahidan ta bushe da ita sannan ta miqe tana duban su huda
"Oya....lets go" ta furta tana kada hannunta,ba musu suka bita a baya suka fice
zuwa falon.

Haidar ne ya soma canza tasha zuwa mbc bollywood faruq yace sam shi mbc
action xai kalla,huda kuma ta tubure ita mbc three takeso
"Dalla malama matsa kona kwada miki mari" faruq ya fada yana duban huda gami da
zare mata ido
"A'ah wallahi,dalili dame?,bani remote din gaba dayanku na raba gardama
"please anty" faruq ya fada cikin langwabe kai yana miqa mata remote din,ta gane me
yake nufi,saita basar tana cewa
"Babu wanda za'a kamo zabinsa,zabina kowa zai kalla" gwalo kowa kema dan
uwanshi,tana murmushi ta kamo TVC news kwana biyu tayi missing labarai bata samun
kalla,tana jin haidar na gulmarta
"Miss news" ta waiwaya ta kalleshi
"Zamu hadu anjima" da sauri ya dawo ya fasa hawa saman da yake qoqarin yi
"Sorry my aunty kar aji kanmu,niba dake nake ba,Allah kwana biyu dama da baki da
lafiyar nan duk sanda ustaz zai karbi hadda fecewa nake kar 'yammatan ajinmu su min
dariya...ki taimakeni"
"Saika biya cin hanci"
"Na yarda" ya fadi yana dariya,idnunta a kansu sanda suke wucewa dakunansu don
sauya unifoarm dinsu,saida suka bace mata sannan ta janye idanun nata tana sauke
ajiyar zuciya,duk sai taji kaman ita kadai keda matsala,takura da quncin
zuciya,tana son ta rabu dasu amma ta rasa me yasa qoqarinta ya gaza?.

Ganin cewa suma ba labaran suke ba saita sauya tasha zuwa FASHION TV,sabuwar
tasha ce amma tana tashe kuma ta samu karbuwa wajen al'umma sosai,sukan nuna
abubuwa kala daban daban,kama daga sutturu na zamani,bukukuwa,birthday,engagment da
sauransu,wani lokaci tana son kallon tashar saboda takan debe mata kewa,wasu
abubuwan da suke nunawa na burgeta.

Yauma ta tadda suna hira da wata mai gyaran jiki shuwaarab cikin harshen
turanci,shirin ya qayatar da ita sosai,ta bada dukkan hankalinta akai,sai suka
yanke suka tafi talla,tallan farko da suka sako na engagment din wasu igbo ne,tsaki
taja tana gyara zamanta saboda sam bata ji dadin tafiyarsu hutun ba,cikin ranta
tana ganin rashin aikinyi ne kawai da zaka tsaya batawa kanka lokaci saboda an maka
egage da wani,wai itama soyayyar nan gaba daya meye zaqi ko ribarta?,ta sake jan
tsaki sanda aka nunosu suna bayyana yadda suke son juna da farincikinsu da kuma
saqon godiya ga duk wadanda suka halacci bikin engage din nasu,remote ta dauka da
niyyar sauya channel idan sun gama ta dawo,talla na gaba da suka fara haskowa sai
yaja hankalinta matuqa fiye da komai,engage ne na wasu couple da za'ayi musulmai
masu cikakken sunan hausawa,hoton farko na amaryar ne tayi kyau cikin shiga ta
alfarma,wanda kallon farko idan kayi mata zaka tabbatar ta samu gata,hoto na biyu
shi ya sanyata jin wani abu ya tsirga mata,a hankali kanta ya sara,hoton anwar ne a
matsayin shine angon da za'a gudanar da bikin engage din nasu kwanaki goma masu
zuwa,sosai ya fito tarwai,ya cika screen din tvn tamkar yana tsaye ne a
gabanta,sanye da wasu shegun suit,daga sama har qasa shigarsa abar birgewa ce iya
kallon mai kallo,miqewa tayi tsaye ba tare data shiryawa hakan ba,wani abu mai
nauyi na danne zuciyarta kamar ana shirin riqe numfashinta ne,remote din taji ya
mata kadan ta kauda fuskarsa daga screen din tvn,saboda haka bata tsaya ba har sai
data dangane da socket din dake jone da kayan kallon ta kasheshi gaba daya,sannan
ta juya da sauri don barin falon zuciyarta na wani irin gudu tamkar wadda taga wani
abun tsoro.
Sallamar uncle hisham ita ta tsaidata cak,tasan dole ya ganta bai kyautu kuma
ta wuce ba tare data yi masa barka da zuwa ba,daidaita yanayinta taketa qoqarin
yi,kafin afkuwar haka anty zubaida ta fito daga kitchen din,da sauri ta juya don
batason taga fuskarta,ta gwammace ta fuskanci uncle hisham a haka akan anty
zubaida,yanzu zata saka ayar tambaya kan sauyawar yanayinta lokaci guda bayan ba
haka ta baro kitchen ba.

"Sannu da zuwa abbu" ta fada a sanyaye idanunta na kallon qasa saboda tana ji
a jikinta kamar qwayar idanun nata ba dai dai suke ba
"Yauwa rahamatullah(ya kirata da ainihin sunanta),ya jikin naki"
"Da sauqi abbu" ta amsa masa da sauri saboda wani abu dayake qoqarin shaqe mata
wuya
"Ma sha Allah" juyawa tayi da zummar barin falon yace
"Shahida" sake juyowa tayi
"Na'am abbu"
"Anjima inason ganinki"
"Toh" ta fada tana sake juyawa zuwa dakinta.

Takai ta kawo tayi hakan yafi sau babu adadi,hawaye keson fita daga idanunta
amma ta hana kanta hakan,tanason lalubowa kanta dalilin da zai sanyata kuka
"Enought is enought shahida,kinyi kuka a rayuwarki da yawa...ya isa haka,ya kamata
ki kawo qarshen komai,ya kamata komai ya qare" take fadawa kanta da kanta bayan ta
tsaya gaban mudubin tana duban qwayar idanunta da kanta gaba daya saika zaci
zararriya ce,kallon kanta da kanta take tana bawa kanta qwarin gwiwa,saidai ina
hawaye ba'a masa shamaki,saida daya ya ziraro mata wanda ya baiwa dukka sauran
damar samun hanya,ta fashe da kuka sosai cikin sassarfa ta isa saman gadonta tayi
rub da ciki tana cusa kanta qasan filo tana kokawar hana kanta ci gaba da kukan.

Kaman ba zata falon ba amma dole ta qarfafa jikinta ko don saboda abbu da
yace yanason ganinta,ta gyra fuskarta gaban mudubi ta zizara kwalli bayan ta shafa
powder,batason kowa ya fuskanci tayi kuka,a kasalance take kawowa har ta iso cikin
falon,wanda a al'adar abbun dama bayan cin abincin dare yana zama ne cikin yaran
nashi su taba hira kafin ya tattara ya wuce dakinshi.

"Rahama,meye ya faru ranar hutun noor international?" Tambayar da abbun ya


jefo mata kenan bayan ta gama dubawa su farouq haddarsu da wajibul manzil da aka
basu kan tajwidi,a hankali ta dago idanunta ta dubi abbun,daita sunkui da kanta
qasa,tana tuna duk wani cin fuska da anwar yayi mata,tanq tuna kalamanshi akanta
daya bayan daya,wani daci na tasowa daga qirjinta zuwa harshenta,saidai ta dake
zuciyarta,batason ko daya ta sake zubda qwalla a rayuwarta saboda anwar
"Uhmmm..." Abbu ya sake bata dama ganin tayi shuru
"Abbu sun koreni ne"
"Kora kaman yaya?,me kika musu?,wannan wanne irin cin fuska ne?" Anty zubaida ta
fada a hasale,yayin da abbu yayi shuru har sai da anty xubaida takai aya
"Dazu gamayyar malaman makarantarku sun sameni har wajen aikina,sun bani haquri kan
abinda ya faru,na gaya musu banda masaniyar abinda yafarun,sun bayyanamin cewa mai
makarantar ne gaba daya ya sallameki,dukkansu basu da masaniyar ainihn dalilin daya
sanya ya koreki ba,duk da kina daya daga cikin haziqan malaman da suke alfahari
dasu,idan don kamarace bake daya kika makara a ranar ba,amma suna so na baki haquri
in sha Allahu zasu magana dashi master din,kuma sunsan yana da sauqi zai
fahimta,to,duka dai sun gama bayanansu,na kuma ari bakinki naci musu albasa cewa
kema ba zaki koma ba,idan baki manta ba dama kan yarjejeniya na barki koyarwa a
makarantar,yanzu kuma abinda muka gina yarjejeniyar akai ya afku,saboda haka yanxu
kinga nayi winning,dole ki karbi duk aikin dana samo miki kenan" ya qarshe yana
murmushi,don bashi da ra'ayin tursasa dan adam ne,amma dama tun asali ta yaya
shahida me matakin karatun irin wannan zata tsaya koyarwa a primary?,wanne irin
maida kai baya ne
"In sha Allahu abbu,nima bani da sha'awar komawar har abada"
"Shikenam faduwa tazo daidai da zama,Allah yasa hakan shine yafi alkhairi"
"Amin abbu na gode" ta furta idanunta har yanzu na kallon qasa,nan ta yimusu saida
safe da zummar zata sha magani ta kwanta.

Sai data raba dare tana gayawa kanta ya kamata ta motsa gaba,ta watsar da
komai,ta ciyar da rayuwarta gaba,ya kamata ta shafe komai kaman yadda take gayawa
kanta a 'yan kwanakin nan,idan bata manta ba,idan kuma zata iya tunawa,anwar din
data gani dazu da anwar din data gani satin daya gabata ba shine anwar din data
sani shekaru goma baya ba,lallai ba shakka bashi bane,ya kamata aga wata shahidan
ta daban ba wannan ba
"Yes!" Ta fada tana baiwa kanta qwarin gwiwa da tabbacin zata sauya komai.

Washe gari da qwarin gwiwarta ta fito,hakanan tayi yaqin maida murmushi da


fara'arta gaba daya,koda bata samu duka ba taji a jikinta ta maida kaso hamsin
cikin dari,wanka ta soma yi sa'annan ta fito ta shirya cikin kwalliya madaidaiciya
a riga da skert na atamfa don kusan tafi son atamfa saboda tana son kaya cottoon
kasancewarta mutum da batason zafi,feshe jikinta tayi da turarenta na din din
din,ta tsaya gaban mudubi tana kalli kanta,ita kanta tasan tayi kyau,kwalliyar data
jima bata bari ta rabi koda fuskarta ba,murmushi ta sakarwa kanta da kanta tana
sake baiwa kanta qwarin gwiwa,sai taji gaba daya hankalinta ya karkata ga aikin da
abbun yace zai sama mata,batason ci gaba da zama haka
"I need to make my self busy,so i can forget dat am deeply hurt and broke" ta
qarshe maganar tana juyawa cikin hanzari ta dauki wayarta ta fice daga dakin.

A tunanin anty zubaida zata ganta sukuku ko cikin damuwa saboda maganar jiya
amma sai taga sabanin hakan,itama hakan yayi mata dadi sosai,ranar alhamis ce babu
islamiyya,haka ta sake sosai cikinsu huda sukayita buga games bayan sun gama
karatu,ta kira mutanen data jima bata kirasu ba,ta kira zunnurarta sun jima suna
hira,har ita kanta ta dinga tambayarta yau da alama ranar ta musamman ce.

Koda noradden yazo shima yazo yau a sa'a,ta tanqwara zuciyarta ta fita ta
saurareshi ba tare da wani dogon turanci ba,ba laifi kuma ta dan jima wajensa,don
ta dauki mintuna aqalla ashirin abinda bai taba faruwa ba a tarihin
zamantakewarsu,ita kanta yau taji zuciyarta sakayau kaman ta rage mata nauyi daga
cikin nauye nauyen dake takure da ita.*zafafa biyar na kudine,idan kika gani don
GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi wannan number*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*ga mai buqatar littafina da zanyi bayan kammala alqawarin Allah,yaje youtube yayi
searching SAUTIN HIKIMA,zaiga SUBSCRIBE da jan rubutu ya dannan zai koma black,yayi
screenshoot ya turo zuwa ga number da zatazo a qasa,zan sakashi group din da yardar
Allah SUBSCRIBW KYAUTA NE BA'A DAUKAN KO SISI*

07038670166

2️⃣ 0️⃣
*Alqawarin Allah*
2️⃣0️⃣

Zaune yake shi daya cikin dan qaramkn garden din dake bangare raban na gidan
nashi,wanda yasa aka masa shi sannan aka qawata masa,yakan yawaita zama lokaci zuwa
lokaci musamman a sanda yake buqatar kebewa ko yin wani gagarumin aiki da bai
buqatar surutu ko takura,snye yake da t.shirt mai gajeran hannu gami da trouser
light and dark brown,tray ne dan qarami aje a ganshi da butar shayi hadi da qananun
kofuna guda biyu akai,daya kofin yana hannunsa,idanunsa zube kan laptop din dake
kunne gabanshi tana aiki yana kallon wani aiki daya soma tsarawa,inda yake fidda
duk wajajen dake da kura kurai,yayi. Da wani sashen kuma ranshi ke a bace saboda
sanarwar da nafisa ta fitar a fashion tv,baisan ya akayi ba sai saqonnin taya murna
ya tashi dashi fal email dinshi,watsapp dinshi da twitter,angage din ma da ba'akai
ga tabbatar dashi ba.

Qarar bude gate din gidan da mai gadi yayi ya shiga kunnuwansa,sai yayi tsai
yana sauraro,iyakar saninsa yasan dai ya gaya masa kar yabar kowa ya shigo masa
gida idan ba muhsin ba,saboda yana son ya hada hankulanshi waje daya,zuciya da
qwaqwalwarsa ta samu cikakken hutu.

Ba'a wuce minti biyar cikakke da budewar ba ya juyo taku,kamn ya juya saiya
basar yaci gaba da abinda yake,don qamshin turarenta daya rigashi isowa ya gaya
mishi ko wacece.

Ta dauki minti biyar tana tsaye a bayanshi,hannayenta harde a qirji tana qare
masa kalla,ba shakka ta jarabtu da son anwar irin soyayyar da bata tsammaceta
ba,har kwanan gobe kuma bata ji a jikinta zahiri da badini ta samu irin soyayyar da
take kwadayi daga gareshi,haka ta gaji ta saki hannayenta tana fidda ajiyar zuciya
ta taka har inda yake,gabanshi ta zagayo ta tsaya tana dubanshi,fuskarta a narke
haka ta karyar da wuyanta,sai daya mula don kanshi sannan ya dago ya mata kallo
daya,haka kawai yakeji wasu abubuwa marasa dadi akanta,har yanzu baisan a wanne aji
zai sanya nafisan ba,ta kuma qi ta gane taqi ta fuskanceshi
"Baki iya sallama ba?" Sai tadan sassauta kwabw fuskar da tayi,tana son ta koyi
sallama duk sanda ta iskoshi kaman yadda ta fahimci tsarinsa ne amma takan yawaita
mantawa,kuma mima ta gaya mata dole ta siffantu da duk wani yanayi da tasan yana so
yana kuma cikin tsarinsa
"To salamu alaikum" amsa mata yayi duk da har yanzu bai daga kai ya sake dubanta ba
"Ba zakace na xauna ba?" Ta fada cikin shagwaba,ture kofin dake gabansa yayi
"Sai nace ma?,ai ga kujera nan kina gani ko?" Kai ta gyada a hankali taja kujarar
dake fuskantarsa ta zauna.

Hannayenta ta hade waje guda,ta sake sassauta murya


"Dear...don Allah me nayi maka?,me yasa kakeson sanya zuciyata cikin rudani,kasan
ya nake ji duk sanda na kiraka baka daga ba,ko na turo maka saqo baka karanta ko ka
turamin reply ba?" Idanunshi ya daga ya dubeta sai ya sake kautar dasu yaci gaba da
abinda yake,tunu qwalla ta cika mata idanu,ta tsani wannan miskilancin nashi ya
motsa,wahala takesha,tana ji a ranta duk sanda ya soma shariya irin hakan kaman dai
ya tuna tsinanniyar yarinyar da yanzu tsanarta ta ninku a zuciyarta wato
shahida,data sani baya ga rabasun da tayi ta nakastata yadda ko da wasa ma bazai
sake kawota cikin zuciyarsa ba,amma data taba masa zancan ya tunata ne ranar taqa
zallar bacin rai,ya gaya mata karta sake mishi wannan zancan don ba huruminta
bane,sannan kuma karta sake masa maganar wata shahida,abinda ma yasaka ranta ya
danyi sanyi kenan,ta cika da fatan Allah yasa tabar ranshi kenan har abada.

"Meye laifina dear..." Ta fada cikin son fashewa da kuka,saiya tattara dukkan
abinda yake gefe guda ya rufe system din sannan ya daga kai yana dubanta duba na
kai tsaye,yana fata Allah ya yaye mata wannan son da take masa,sam ko kadan shi
hakan baya masa dadi
"Ni na aikeki kona bada daman ki bada sanarwar engage dinmu rana ita yau?" Kai ta
girgiza tana dubanshi hawaye na sake cika idanunta
"Wannan wacce irin banzar dabi'a ce,mu yahudawa ne nafisa?" Nan ma kai ta gyada
saidai cikin ranta tana jin dadi da sauqin radadin da take ji,ta zaci wani babban
laifi ne ta aikata,koya ganta ne ranan nan da saddam randa sukaje dinner din
abokinsu,wanda basu dawo ba sai sha biyu da rabi na dare,ita a ganinta wannan sam
ba laifi ne ba,hasalima saika isa ka qasaita ka amsa sunanka wani sannan za'a ga
wani abu daya shafi event dinku a gidan talabijin din
"Kayi haquri,kuskure ne,bani na biya bama siyama ce tace lallai a saka"
"Siyama....ita tace rana ita yau din kiyi wani bikin engage namu kenan?,ohk tunda
haka ne rana ita yau din ita saita tabbatar da abun kota tursasani" ya qarashe fada
yana janyo wayarshi dake gefe,da sauri ta riqe hannun nashi don tafison a kawo
qarshen komai,bata jurewa fushinsa,jinsa take har zuciyarta,kallonta da yayi ya
sanyata saurin janye hannun nata,yasha mata kashedin tabashi ba sau daya ba ba sau
biyu ba
"Don Allah dear don Allah,wallahi na fasa ba za'a yi ba" yana da tausayin mace
hakanan mutum ne shi da tun asali yake tausaya raunin 'ya mace ko wacece
"Kome mutum xaiyi ya kamata ya dinga duba da abinda bai sabawa addini da al'adarsa
ba,sannan ka dinga dogon nazari da tsinkaye a duk lamarinka kafin aiwatar dashi"
"Kayi haquri"
"Ya wuce" ya fada a taqaice
"Yanzu daga ina kike?" Kame kame ta soma yi,don tun dazun suka fito gantali ita
dasu mima,yanzu haka suna cikin mota su suka rakota bashi haquri,ko hajiya bilkisu
ma batasan tazo ba,ganin ta rasa qwaqwqwaran abun fada guda daya ya dakatar da ita
"Is ok...yanzu ki wuce gida"
"To yaushe xakazo?,kwana biyu ma gaba daya ka daina zuwa ko cin abinci,mama nata
complain" ta fada cikin shagwaba
"Zanzo da zarar na samu dama"
"Can i call you anjima?" Ta sake tambaya,idanunsa ya lumshe kana ya bude,don
maganar ta soma isarsa
"Allah ya kaimu anjima" miqewa tayi ta masa sallama cikin salon nuna qauna sannan
ta juya ta fice daga gidan,ajiyar zuciya ya sauke sanda yaji fitarta,saiya hada
kayanshi gaba daya don zaman gun har ya fita akanshi kuma.

Bacci ya samu yadanyi,qarfe hudu ya tashi,yayi alwala ya fice masallaci,daya


dawo ya shiga wanka ya shirya tsaf cikin dogayen kaya wanda bai fiya sakasu ba,ya
dauki wayoyinshi da maqullin motarsa ya fice,ya yiwa mai gadin sallama ya wuce.

Tafiyar mintuna qalilan ta sadashi da gidan anty usaina,suka gaisa sosai da


mai gadin qofar da yake shiga,saidai qofar ana gyaranta ne saboda gate din yana
masa tauri bai buduwa da sauri,tilas yayi rivers ba don son ranshi ba ya zagaya ta
daya layin.

Idanunshi fes yana iya hangen qofar gidan daga qofar gidan anty usainar,a
hankali ya dauke kanshi yana fidda zazzafar iska daga bakinsa,horn daya yayi aka
bude masa don tuni ya zagayo mai gadin,ya saka motar tashi yayi parking sannan ya
kasheta ya fito.

Anty usainan ya tadda da yaran ta zaune cikin valcony din dake gefan
matattakala hudun da zata sadaka da babban falon gidan,assigment sukeyi,dukansu
suka hada baki suna masa sannu da zuwa cikin girmamawa ya amsa,har ta miqe zasu
shiga ciki taga yana zare sau cikinsa
"Barni daga nan anty na zauna cikinsu nima,sati biyu kenan bamu hadu ba" da d'aya
da d'aya ya dinga bibiyar karatunsu,yammata masu kimanin shekara sha hudu sha biyar
da sha shida,sai namiji mai shekara sha uku,yaji dadin yadda yadda ya samu karatun
nasu na tafiya daidai,wansa daga qarshe ya sallamesu da kyautar dari biyar biyar
suka shige cikin gida suna murna,wajen ya rage daga shi sai anty usainar.

"ya jikin naka?"anty usainar ta tambayeshi bayan sun gama gaisawa,dubanta


yayi
"Waye yace bani da lafiya?"gajeran murmushi ta saki
"kana tunanin zaka iya boyemin ne,tun zuwan da kayi cikin wancan satin nasan baka
jin dadi"
"Don dai karkice na musa miki ne...amma da nace lafiyata qalau,kawai stress ne na
wajen aiki" kai ta kada kawai,tasan dama bazai taba yarda ba,baisan tsohon abu bane
wannan a wajenta,ta karanceshi ciki da bai
"Hakane....Allah ya taimaka to"
"Amin" ya amsa yana ciro wayarsa da tayi qara alamun shigowar saqo,nafisa ce,ya
karanta ya maida mata da thanks sannan ya maida wayar idonsa kan anty usainan
"Dama inason muyi wata magana ce da kai"
"Toh anty,Allah yasa ta samu"
"Eh to.....zancan nafisa,munyi magana da ita ta sanarmin kace rana ita yau kakesan
suje su sami alhj abba,amma saga bangarenka banji kace komai ba har yanzu,ya kamata
fa anwar ka maida hankalinka jikinka,da da yanzu ba daya bane,kullum shekaru qara
yawa suke akan mutum,baya ga haka ma ya kamata mu fita kunyar yarinyar nan da
iyayenta" shuru yayi yana saurarenra idanunsa na kallon carfet din da suke kai,har
sai data kammala sannan ya dubeta cikin nutsuwa da jeranta kalamai
"Anty,har yanzu banji nutsuwa da gamsuwar nafisa ta zama mata agareni ba,har yanzu
ina qoqari da tsarawa kaina yadda zan amshetq,bana son ayi abinda daga qarshe zai
xama wani batu na daban,ina matuqar ganin qimar mama da abbanta,ina ganin mubi
komai a sannu har zuwa sanda komai zai dai daita,zuciyata ta amshi abun dari bisa
dari yadda ya dace"fuska anty usaina ta canza,har cikin ranta tana jin anwar din
zai aikata ba dai dai bane kawai
"Anwar,idan ka sauya ra'ayi ne kawai ka furta,har xuwa yaushe kakeson yarinyar
tayita zaman jiranka?,tun tana kara har takai ga tana takowa ta sameni da
maganar,waishin ma idan bakayi aure ba yanzu sai yaushe xakayi anwar?" Ta jefa masa
tambayar tana tsareshi da idanu
"Duka anty ba wannan maganar bace"
"To wacce ce gaya min?"
"Kamar yadda na gaya miki ne a baya,har yanzu zuciyata ta kasa nutsuwa da yadda da
soyayyar kowacce yarinya,da nafisa zata haqura dani da nafi kowa murna,saboda zanso
mata ta auri wanda yake sonta ba wanda takeso ba"
"Maganata ta tabbata kenan,kawai anwar ka fasa auren nafisa kakeson cewa,ka shirya
butulci wa mahaifanta" cikin bacin rai ta qarashe maganar
"Banason ranki ya baci anty,za'ayi duk yadda kikeso,zanje da kaina na samu kawu
abdulkarim na shaida musu,Allah yayi mana jagora" ajiyar zuciya ta sauke sannan
tace amin Allah yasa ayi a sa'a,ko kadan batason iyayen nafisa su kallesu amatsayin
butulu marasa cika alqawari,marasa kuma rama alkhairi da alkhairi,daga wannan
magana ya miqe
"Har zaka wuce?"
"Eh...ina da aiki da yawa kwana uku ban samu shiga company ba"
"To Allah ya taimaka....amm dama inason gaya maka,cikin satin nan nakeso na shiga
katsina mu gaisa dasu baba furai'ah,ya dace kaima ka ware lokaci kaje ku gaisa,don
ba qaramin jimawa kayi rabonka dasu,tun suna qorafin kayi kudi ka watsar dasu sai
aike har sun haqura ma sun daina" bawai zuwanne wajensu baya sonyi ba,katsinarce
baya son shiga,shi duk wani abu daya jibanci tuna mishi da ita baya qaunarsa
"Zanyi qoqari in sha Allah" tana zaune daga nan har ya isa inda ya aje motarsa tana
kallonsa,ya bude ya shiga ya tayar da ita yabar gidan.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan ya bacewa ganinta,ta fada dogon tunani,abinda


yake dojewa dai yake nuna tsantsar qinsa shine ke wahalar dashi,lamarin da yake
qaryatawa shike dawainiya dashi,itakam a duniya kaf bataga matar data dace dashi
irin shahida ba,har yau yaqu furta nata meye sanadi?,meye dalilin rabuwarsu,har
cikin zuciyarta tana qaunar yarinyar,ta zabi gida kusa dasu ne don tana saka ran
wataran ta dawo mishi da ita cikin rayuwarshi,tarihin soyayyarsu,yadda tayi tambari
ta kuma yi suna bai kyautu ace ta qare a haka a banza ba,ta sani cewa ko yaqi ko
yaso koya nuna koya boye shahidan wani bangare ce na rayuwarshi,ta jima tsahon
shekaru tana addu'a tare da fatan Allah ya shige mata gaba yasa taci galaba duk
sanda ta tasamma tunkarar lamarin,domin cire qiyayya daga zuciyar da ada take cike
da soyayya ba qanqanin abu bane,saidai a jikinta da xuciyarta duka tana jin lokaci
yayi daya dace ta tashi ta gwada tabuka wani abu,koda zaiyi kuka da ita gaba tana
da tabbacin zaya gode mata,duk da batasan meye yayi silar ruguxa wannan kyakkyawar
alaqar da aka ginata cikin fahimtar juna ba.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Cikin lokaci kadan ta soma jin cewa zuciyarta ta karbi canjin da tazo mata
dashi,ba'a dauki dogon lokaci ba uncle hisham yazo mata da upper ta daukan aiki a
companyn *TRIPLE R GEM* kamfanin dake sarrafa duwatsu masu daraja da tsada zuwa
kayan ado da qawa na mata ,irinsu sarqoqi,dan kunnaye,zobuna,abun hannu,munduwa da
sauransu,mallakin *RAYYAN* miji ga *RUMANA DA RAIHANA* (DANGANTAKAR ZUCI).

Sun bata matsayin accountant na wajen gaba daya saboda yarda da amincin uncle
hisham da rayyan yayi yasa ya bashi cigiyar wanda zai riqa masa wannan
matsayin,matsayin da aka bata sai taji yayi mata girma,har taso tace ba zata amsa
ba,uncle hisham ya zauna yayi mata bayani da kyau ya kuma nuna mata Allah ne ya
bata,fatanshi kada ta bashi kunya ta kumayi aiki tuquru,tace in sha Allah.

Duk wani abu da ake baiwa sabon ma'aikaci mai matsayi irin nata sun
bata,saidai taqi amsar gida da mota da suke bayarwa,tace bata da ra'ayinsu,ganin
haka sai suka qara mata kudi kan wanda ya kamata a bata.

Uncle hisham da kanshi ya kaita gidan shugaba kuma mamallakin kamfanin gaba
daya don tayi musu godiya,gida mai dauke da matan aure biyu kuma aminan juna,gida
na farko data ji yanayin rayuwarsu ya burgeta bayan gidan anty zubaida,haduwar
farko jininta ya hadu dana raihana,yanayin rayuwarta nutsuwarta da komai
nata,haduwar farko ta karanci yadda ta iya tattalin miji cikin wani yanayi mai
sanyi da kuma mu'amala,rumana uwargida,mace mai fara'a da saurin sabo itama sunsha
hira da ita,wanda daga qarshe ta tattara kan yara tace zasuje siyayya ne ta barsu
da raihana,yaran da shahida ta kasa tantance wanne ne yaran rumana wanne ne na
raihana?.

Cikin qanqanin lokaci ta kama aikinta sosai,ta kama mutuncinta haka nan
tsakaninta da ma'aikatan sai gaisuwar mutunci da girmama juna,ita kanta idan ka
kalleta zakaga sauyi mai yawa tattare da ita sabanin baya,ta sake fresh hakan
fatarta ta qara kyau da gogewa,kwanciyar hankali da nutsuwa sun samu tare da ita,ta
soma shimfida sabuwar rayuwa,tayi wancakali da dukkan wani qalubale da bacin ran
rayuwa.

_yanzu aka soma,muje zuwa masu karatu_*Zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don
GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata ki tuntubi wannan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

2️⃣ 1️⃣
*Alqawarin Allah*
2️⃣1️⃣

*BAYAN SHEKARA DAYA*

Komai na duniya baya ga qaddara yana tafe ne da lokaci,wanda wannan lokacin


shike qunshe da komai,yake tattare da faruwar komai,shike bayyana komai hakanan
shike haifar da komai din,cikin shekara guda shaheedan ta samu sauyi da canje canje
masu tarin yawa,tayi qoqarin binne duk wani qalubale data taba samu cikin
rayuwarta,ta kaucewa dukkan wani abu da zai tuna mata dashi fiye da baya,ta fannin
rayuwarta kuwa shahidan ta sake zama wata mace mai aji,irin macen da kana mata
kallon farko zakasan ta goge,bawai gogewa ta budewar ido ba,gogewa ta kyau,gogewa
ta iya ado da mu'amala sakamon mu'amala da take da mutane kala daban daban daga
sashe daban daban na qasashen afrika,ta qara wani kyau da kwarjini,hakanan ta
murje,ta gefe guda kuwa a yanzu nuraddeen ya samu kanta babu laifi,aduk sanda ya
kirata zata daga su taba hira,hakanan duk sanda yazo wajenta a gida takanyi qoqarin
fita,wani lokaci ma yakan bita wajen aiki da niyyar daukota,anan ta dakatar
dashi,don babu abinda ta tsana a duniya a yanzu irin shiga motar wani d'a
namiji,duk sanda ta saka kai zata shiga sai abun ya fado mata,wannan moments din ya
kasa barin qwaqwalwarta,shine kuma abu mafi muni cikin dukkan abinda ya faru da
ita,tana mamakin me ta yiwa wannan mutumin daya watsota qofar gidansu cikin cin
mutunci da wulaqanci?,me ta yiwa fiddausi wadda har yau bata bi ta kanta ba ko
neman inda take,hasalima bata sake ganinta ba,to me zatayi mata?,me zata buqata
daga gareta?,koma meye tana roqon Allah yayi hukuncin daya dace.

To ko cikin company ma da baqin dakanzo siyayya kamfanin masoyane suka mata


rubdugu,wani lokaci har haushi kan kamata na yadda ba'a cikakken kwananki uku wani
bai ganta yace yana so ba,ta rasa meye a jikinta haka?,me take dashi wanda yake jan
hankalinsu?,da tasan wannan abun ba shakka data cireshi ta jefar kota huta da
shegen binbinin da suke ma rayuwarta
"Kin hadu ne shahida,kina da komai Allah ya miki baiwar komai,ba zaki gane abinda
nake nufi ba shahida,amma kinyi tako ina,ki bani dama don Allah" ta tuno kalaman
wani alhj wanda tunda yazo kamfanin siyawa matarsa sarqoqi gift na birthday dinta
ya dafewa shahidan,a sannan ta sauko zata je cin abinci,baima san ma'aikaciyarsu
bace.

Gefe daya ta sake yalwata rayuwar ummanta da qannenta,hakan ta yiwa gidansu


gyara ta sake qawatashi,ita kanta a yanzu jin dadin rayuwarta take,abu daya ne data
fuskanci umman nata ta tsiro dashi shine son shahidan tayi aure,don zancan da ake
mubina na ss two ne,kuma ta samu wanda yake sonta,dama yakeso a bashi yaje can
wajen dangin mahaifinsu dake katsina ya gabatar da kanshi.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe hudu suka tashi daga aiki yau,cikin sauri saboda kar lokaci ya qwace
mata ta shiga adaidaita sahun da yake nata ne yake kaita aiki ko wata unguwa da
takeson zuwa,a sanda kuma ya ajeta yaje yayi haya dashi.

Saloon din da take zuwa kitso ya sauketa,ta dubeshi


"Ka dan jirani yau ba dadewa zanyi ba"
"To hajiya" ya fadi yana kashe adaidaitan,ta juya cikin takun nutsuwa zuwa bakin
saloon din.

Yanayin wajen kaman tsarin ciki da falo aka yi masa,duk da qofar cikin mai
fadi ce sai aka saka labule mai shara shara,falon kuma kujerun zaman custumers ne
da kuma kayayyakin siyarwa na kwalliya kamansu ribbom,man kitso man shamfo,beads da
sauransu.

Shagon akwai mutane saidai ba sosai ba,a falon ta tadda mai saloon din tsaye
da wasu mata suna siyan ribboms,cikin fara'a da muntuntawa ta tarbi shahidan,saboda
tasan duk sanda tazo din ba qaramin qaruwa takeyi da ita ba,suka gaisa sannan tace
mata
"Kitso nakeso madam,amma manya nakeso yau ayimin ibra nakeso" cikin juyayyar
hausarta tace
"Ohk madam babu damuwa..saidai akwai wasu da za'a wankewa kai,amma bari na soma
sallamarka su sai su jira"
"A'ah madam,aisun rigani zuwa sallamesu tukunna"
"Ohk maa" ta fada tana juyawa ta duba wani waje da take aje magazines ta zubewa
shahidan sannan ta sallami wadanda suke sayen ribbom ta koma ciki inda take wankin
kan.

Daya daga cikin kujerun dake wajen shahida ta zauna,ta aje jakarta gefe daya
sannan ta cire glass dinta da take amfani dashi lokaci zuwa lokaci saboda ado ta
dorashi saman jakartata ta bude magazine din ta soma dubawa.
Hayaniya da hirar dake tasowa daga ciki ta cika mata kunne har tasa ta daina
fahimtar abinda take dubawar,sai kawai ta rufe magazine din ta riqeta a hannu,hirar
yammatan dake ciki na shiga cikin kunnenta
"Ya hadu iya haduwa,daa wlh ni bai dameni ba saboda a sannan baida wani abun
burgewa,amma yanzu har wani kishi kishinta nakejin yana kamani wallahi,anya nan
gaba kuwa ba za'ayi juyin mulki ba kuwa?" Dariya suka kece dashi
"Mima baki da kyau,daga daukanki sojan haya saiki fadi haka?"
"Ke qyale shegiya,shekara nawa ina mata bauta?,don tana biya na aiba halitta ta
tayi ba" hirar sam bata wa shahida ma'ana ba,saboda haka ta zaro wayarta kawai tayi
kiran ummanta,bayan sun gaisa tace
"Umma don Allah ki saka mubina ta soyamin wainar fulawa ina nan zuwa,na tsaya yin
kitso ne,ta saka min albasa da yawa,ta manja nakeso"
"Toh shikenan,amma saita saukemin tuwona"
"Eh kafin sannan ma na qaraso"
"Allah ya kawoki lafiya"
"Ameen umma" bayan ta kashe kiran noradden ya shigo,ba yabo ba fallasa ta daga
"Yallabiya kin hanani sukuni sai naji muryarki" murmushi ne ya subuce mata ba tare
data sani ba,ita mamaki ke kamata idan nura na nuna yadda yake tsananin qaunarta
"Dariya ma na baki?,don bakiga yadda na gaji tubus ba saboda tunaninki,shahida har
yau kina daukan son da nake miki da sauqi"
"Ba haka bane,kawai dai haka kai ka fahimta"
"Koma yaya ne dai yanzu kin wuni lafiya?"
"Lafiya qalau,kaifa?" Sosai yaji dadin yadda ta tambayeshin,daga haka ya shiga
janta da hira,ta biye mishi kodan ta ragewa kanta lokacin zaman jiran da takeyi.

Minti ashirin 'yammatan da akewa wankin kan daya ta soma daga labulen ta
fito,tana sanye da riga dinkin straight gown wadda tafitar da duk wata sura
tata,shahidan na shirin dauke kai dayar ta biyo bayanta,itama sak irin dinkin dayar
ne a jikinta,har shahida ta dauke kai yadda taga ta zuba mata ido ya sanya itama ta
maida idanunta kanta,da sauri taga ta juya ta koma ciki tana cewa
"Au...madam na manta qawata tace muyi jiranta a nan"
"Ohkey to babu damuwa" ta bata amsa sanda shahida tayi sallama da nooradden ta
maida wayar jakarta sannan ta cire rolling din kanta,ta zare ribbom dinta ta soma
taje kanta.

A gaggauce nafisa tayi parking na motarta a qofar shagon,cikin hanzari da


sassarfa ta nufi qofar shiga wajen kai tsaye.

A sannan anyi rabin kitson da akewa shahida,labulen kawo sukaga an bankado


hakan ya sanya shahida daga kanta ita da madam tawakkaltu dake mata kitson gaba
daya,idanunta ne ya sauka cikin na shahida tana mata kallon fes,itama shahidan
kallonta take,tasan fuskar,fuskace da ba zata taba manceta ba,fuska ce da anwar ya
turo mata da hotunansu a tare yana bayyana mata ita a matsayin masoyiya a
gareshi,ta yaya zata manta wannan fuskar,amma saita dauke idonta ta maida kanta
qasa tana ci gaba da danne danne a wayarta,saidai wani abu yazo ya tsaya mata cak a
qahon zuciyarta.

Madam tawakkaltu ce ta amsa mata tana ci gaba da yiwa shahida kitson,saidai


idanunta na akanta tana neman jin abinda ya kawota wajen,don bata santa ba
"Amm,akwai friend dita mima da tazo wankin kai nan ko?" Nafisa tayi qarfin halin
furtawa,ranta da zuciyarta gaba daya a jagule
"Eh sunaa ciki aeke sukee jira" ta amsa mata cikin gurbatacciyar hausa,kafin takai
ga isa wajen mima ta fito da qawarta lima
"Gani...mu wuce ko?" Ta fada tana karantar fuskar nafisan,kaita jinjina yanayin
fuskarta na sake sauyawa yana nuna rudani a ciki qarara,har sukaje bakin qofar da
zasu fita tana duban shahida wadda bata ma san tanayi ba,saidai jikinta ya bata
hakan
"Madam ko kinsansu ne?" Tawakkaltu ta tambayeta ganin yadda suke kallonta
"Ba wadda na sani a cikinsu" ta amsa mata a taqaice
"Allaho ya kyauta" ta fada tana mamakin irin kallon da sukewa shahidan su duka.

Duka sai komai ya tsayawa shahidan cak,ba bacin rai takeji ba amma ranta da
jikinta sam babu dadi,wayar ta maida cikin jaka ta ciro carbinta ta maqala a
yatsanta ta soma jan HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL,wansa babu jimawa taji komai na
koma mata dai dai.

Dukan sitiyarin motar tayi da qarfin gaske har lima na zaro ido kada fa kan
motar ya lalace
"Ba haka nakeso na ganta ba mima,ya akayi na ganta a cikin kyakkyawan yanayi?,so
nake ta dilmiya ta lalace,so nake tayi nisa cikin shan kayan maye karta waiwayo
komai nisan kiran da za'a mata,kudin dana biyaki bai kamata wasan ya tsaya iya nan
ba,ya akayi haka?" Ran mima yadan sosu kadan sabida yadda nafisan koda yaushe
taqamarta nakan kudin data bata,amma abinka da bariki saita danne
"Abinda ya bani mamaki ya girgizani kenan yasa har nayi kiranki" shuru ne ya ratsa
motar abun na kaiwa nafisa ko ina,maganar mima ta katse mata zaren tunaninta
Ba wannan nakeson jiba,meye mafita?" Ajiyar zuciya mima ta sauke
"Toh....a yanzu dai babu batun saka wani kota bar wani ya shiga jikinta,na tabbatar
ba zata sake barin haka ta faru ba a gareta...amma dai duk da haka,ba'a rasa nono a
riga,ki fidda kudi,zansan aikin daya dace muyi a kanta,amma....kece zakiyi rabin
aikin,ke kike tare da anwar kuma zakici gaba da kasancewa tare dashi,dole ki sake
cusa masa tsana da qinta cikin zuciyarsa,kisan yadda zaki ki mamaye tunaninsa ki
shiga lungu da saqo"
"Kudi ba damuwa bace,successful aiki shine damuwata"
"Karki samu damuwa,kinsan wace ni,nayi kin gani ai" locker motarta ta bude ta ciro
kudi ta irga ta miqa mata,tasa hannu ta cafesu tana sakin murmushi
"Koma sit dina ki jamu,don bazan iya driving ba a yanzu"
"Ohkey" miman ta fadi,sukayi musanyan seat ta kunna motar ta figeta,wata ta sanya
musu nafisa taja tsaki
"Ina cikin irin wannan mode din zaki kunnan waqa,kashe malama ki barni nayi tunani
da kyau"
"Daqiqiya wanne tunani gareki?,bayan duk wani tunaninki nice nake miki" ta fada a
zuciyarta tana cire waqar,yayin da a fili tace
"Am sorry,komai fa zai dai daita".

Qarfe shida ta shiga soron gidansu bakinta dauke da sallama,tsakar gidan nasu
babu kowa sai mubina dake zaune saga qofar kitchen tana suyar wainar fulawarta,fes
gidan yake kamar kullum,cikin gajiya
ta qarasa inda mubina ke zaune
"Sannu da zuwa yayaa"
"Yauwa mubi...ashe kin soma?" Tayi maganar sanda take duqawa ta bude flask din dake
gaban mubina ta gutsiro wainar takai bakinta
"Da tunima na gama ai,maqociyarmu ce ta shigo umma tace a zuba mata shine nake tara
miki wata yanzu"
"Ummmm....amma fa tayi dadi sosai" ta nemi waje kusa da mubinan tana zama ta janyo
yaji ta soma gutsira tana dangwala,mubina na bata labarin bikin wata cousin dinsu
dake matsowa,shirin da akeyi anko da dai sauransu
"Kowa shiri yake yaya sosai,kinsan wanda zata aura din yana da kudi ba laifi"
murmushi kawai shahida ta fitar,wato duk wadda akace yau zata auri me danshi murna
ake mata
"Allah yasa abokin zama ne,ya sanya alkhairi"
"Ameen yaya,naga umma ma tasa an kawo mana ankon,amma bandake" harararta tayi
"Ce miki akayi ni cima zaune ce da za'a min anko?" Dariya mubina ta qyaqyace da ita
"Waya isa yace miki cima zaune,hajiya accountat da kanta"sai data ci ta qoshi sosai
sannan ta isa bakin famfo ta wanke hannunta ta daura alwala ta wuce falon umma.

Da sallama ta shiga,su biyu ne zaune suna hira,ita da wata baquwar fuska da


batasan wace ba,saidai kallo daya ta yiwa matar taji gabanta yayi mummunar
faduwa,itama matar idanunta kan shahida,murmushi kan fuskarta tana amsa sallamar
tata,dauke idanunta tayi ta samu gefen kujera ta zauna
"Sai yanzu kika shigo?"
"Haba tun daxu umma,na tsaya naci waina ne"
"Ashe takice amma umma ta bamu muka cinyeta" cewar matar cikin fara'a,sai shahida
ta juya ta dubeta itama fuskarta ba yabo ba fallasa tace
"Ina yini?"
"Lafiya qalau,mun yini lpy shahida ko?" Ta amsa gaisuwar gami da jeho mata tambaya
daga qarshe,kai ta gyada tana mamakin yadda akayi matar ta san sunanta,bayan umma
bata furta sunan a gabanta ba
"Tunda nake zuwa ban taba ganinki ba sai yau,Allah dai yayi yau zanga yaya shahida"
ta kuma fada tana murmushi,itama murmushin shahidan ta maidata mata,ganin kaman
bata saki jiki ba ya sanya umma cewa
"Maqociyarmu ce nan gaba kadan gidanta yake,tayi wajen wata shida da tarewa sai
yanzu Allah yayi ta leqo mana,gidan nan da faruq yake gaya miki ana sadaka duk
juma'a?" Sai a sannan ta fahimci gidan da take nufi,kai ta gyada tana sake fadada
fara'arta,don mubina tasha bata labarin kirkin matar,daki ta wuce daga haka tana
jiyo hirarsu da umma.

Har ta gama zamanta ta soma shirin tafiya matar tana nan,a nan taci abincin
dare tare dasu umman,mamaki take sosai shahida,a ina suka santa ne?,wace ita?.

A falo tana rataye da jakarta ta dubi mubina


"Cikin kayan da antyn katsina ta kawo miki daukomin na zabi style zankai dinki,yi
sauri ki daukomin,sa'id yayi anguwa mai nisa yace ya barshi basai ya dawo dakata ba
tunda kusa da anguwarsu yake,motar haya zanbi kar dare ya sake yimin"
"Wallahi duka na sakasu yaaya suna wajen wanki" goshinta ta dafe tana jan dan tsaki
cikin rashin jin dadi
"Halinku daya ai indai mubina ce,kowanne kaya da an saka an cire duk kyanshi sai
ruwa,saiki haqura ai har sai ta karbo itama da dan banzan sanabe,ki kama kayanki ki
wanke amma saikin kai wankau" murmushi matar tayi har fararen haqoranta suka
bayyana kan idanun shahida,gabanta ya sake faduwa,matar tana mata kama da
wata,kaman ta taba ganin fuskar
"Kinga qanwata zo muje ki zabi style wanda kikeso kinji"tayi maganar sanda ta miqe
tsaye ta dauki hijabinta dake aje gefe tana sakawa,kallonta shahida tayi,sai taji
tana jin nauyinta sosai,banda haka ce mata zatayi a'ah ta barshi,amma saita kasa
fada,don ita gaba daya ta jima rabonta da sake amincewa da wani a rayuwarta,duk
wata baquwar fuska da zatayi kutsewa rayuwarta kaffa kaffa take da ita.

"umma...ina kuka samota newai?,ni gaskiya ba wani gidanta da zan bita"


shahida ta fada dai dai saitin kunnen umman cikin nuna rashin yarda
"Babu komai matar sananniya ce,hakanan mun dan jima tare,kije kawai" hakanan jiki
ba qwari ta fito ta sameta bakin famfo tana daura alwala,ta kammala ta yiwa umma
sallama suka fice.

Ko a tafiyarma bata yarda sun hada kafada ba,tana gaba ne tana binta a
baya,duk da haka takan juyi jefi jefi ta sako ma shahidan hira,nata eh ko a'ah ne
har suka qaraso gate din gidan,tsaiwa shahidan tayi tana kallon gidan,kaman taso ta
taba ganin anwar tsaye bakin gate din sau daya,saidai bata tabbatar dashi dinne ko
bashi bane,kawai dai tun daga ranar ta tsani kallon qofar gidan ma
"Muje ciki mana shahida saiki zaba a nutse" murmushin yaqe ta saki
"Nan ma ya isa,idan da yara saiki turo su miqo min na wuce,yau nayi dare sosai a
waje takwas ta kusa"
"Yanzu zaki wuce ai,ki shigo ko kuma nace mubina ta fiki kirki dason mutane"
murmushi tayi saita bi bayanta kawai.

Sosai falon ya burge shahida,komai a kammale a tsaftace yana fitar da qamshi


"Zauna gu waje nan shahida" tana nuna mata kujera da hannu,a darare ta zauna din
tana bin falon da kallo mai gwanin sha'awa da burgewa,sanda yake fidda hijabinta
wata 'yar budurwa ta sauko daga sama ta matakalar benan dake falon
"Sannu da zuwa ummi kin dade yau" ta fada tana duban maman tata
"Wallahi sa'ida...yauwa shiga dakina ki bude wardrobe dina,inda na aje dinkunan da
aka kawomin din nan shekaran jiya ki cirosu gaba daya"
"Toh" ta amsa tana shirin juyawa idanunta ya sauka kan shahida,saita sake juyowa da
sauri ta kalleta ta kalli ummin nata,sai kuma ta juya ta sake hayewa saman.

"Ina zuwa shahida kinji" ta fadi tana nufar wata qofa dake nuna alamun kitchen
ne,wayarta dake jaka ta dauki kuka alamun kira ke shigowa,ta cirota tana
dubawa,noradden ne,saita latsa tana karawa a kunnenta
"Ranki ya dade,ya akayi sa'idu yabarmin ke a waje da daren nan?,naje gida baki
nan,na kirashi yace wajen umma yabarki,kuma kince basai ya dawo ba"
"Eh uzuri nayi masa ne" ajiyar zuciya ya aje
"Ni gaki kin fiddoni,kema kinsan ba yadda za'ayi na iya kwanciya kina waje,fito
gani a qofar gida"
"Na fito daga gidan ai"
"Ina kika je?"
"Ina maqota" sai tayi mishi kwatancen gidan yace gashinan,babu jimawa ta fito dauke
da wani dan qaramin faranti da aka dora ruwa da lemo,gefe daya dambun nama da
meatpie ta aje gabanta
"Ga ruwa kisha" murmushin yaqe ta danyi don har yanzu a darare take,hakanan taji ta
kasa sakewa
"Na qoshi wlh anty"
"Da alama dai da gasken shahida baki da kirki" dariya maganar ta bata,saita kuma
sakin murmushi sosai
"Ba haka bane anty,kina gani kusan ma tare mukaci abincin"
"Eh...amma ko albarka kyasa" bata sake cewa komai ba ta gutsuri meatpie din
kadan,dai dai sanda ta qwalawa yarinyar kira
"Sa'ida me kike ne?,kiyi sauri sauri fa take gida zata wuce"
"Gani nan ummi" tana maganar ne sanda take sakkowa daga saman cikin sassarfa
rungume da kayan a qirjinta,a gaban ummin ta zubesu
"Riga daya ce ban gani ba ashe ta shiga cikin wasu kayan
"ok...gasu ki xaba wadanda zasu miki" a nutse take daga dinkunan,duka sun mata
hakanan sunyi bala'in kyau,tana son yace xata dauka duka tanajin nauyinta,saita
zabi uku daga ciki
"Wadan nan ma sunyi,na gode" tura mata sauran tayi
"Jeki dasu gaba daya,mai yiwuwa telan yaga wanda zaifi miki kyau akan wanda ke kika
zaba" haka ta tattara duka kayan ta zuba mata a wata 'yar jaka mai kyau,ta mata
sallama ta fito.

Yana tsaye jikin motarsa wayarsa na hannunshi yana danne danne,ganin


fitowarta ya sanyashi maida wayar aljihu,ya tarbeta cikin fara'a ya amshi ledar
hannun nata sannan ya bude mata gaban mota,dubanshi tayi sosai
"Kaima kariga da kasan qa'idata ko,mu taka zuwa titi ka tsaremin napep" kai ya
langwabar mata yana dubanta
"Kar muyi haka dake don Allah,yau dai daya kiyimin wannan alfarmar na kaiki,tunda
muke dake shahida ko kara babu baki taba shiga motata kosau daya ba,koda batan
hanya" maganar tashi ta bata dariya amma ta maze,ita bata da ra'ayin hakan kwata
kwata,ganin yadda yaketa roqarta gashi dare nayi yasa tayi bismillah gami da addu'a
ta shiga ya zagaya ya rufe ya tada motar.

Farinciki yau fal zuciyar nuran,haka ya dinga sako mata hira,suna tsaka da
tafiya taga ya dauke hanya,idanu a waje zuciyarta na gudu ta kalleshi
"Ina zaka dani malam" dariya yayi
"Karki damu shahida,duk sanda kike tare dani cikin aminci kike,wani waje kawai zamu
shiga,ki rakani zanwa mama siyayya"shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya,duk da haka
hankalinta bai kwanta ba har sai data ga sunyi parking qofar wajen ta bude murfin
motar suka shiga.
A tsaye yake wajen biyan kudi da yake dab da qofar shiga da fita,yana saka
pin dinshi jikin p.o.s machine da ma'aikin wajen ya turo gabanshi,yana gama sawa ya
tura musu donsu ciri kudinsu wanda hakan yayi dai dai da ganin gilmawar wata da
zuciyarsa hakanan ta afu da sanin wacece,suna miqa masa resit ya karba ya soma
takawa don ficewa daga wajen,saiya tuna ya yiwa sa'ida alqawarin turare,tace tana
son irin turarenshi randa yaje gidan,yace mata ba lallai a sameshi qasar nan
ba,amma zai siya mata copy dinshi,yana da wuya yayi alqawari ya saba banda haka da
bazai sake komawa ba,a gajiye ya sake juyawa zuwa ciki ya soma laluben sashen
turaruka.

Tunda ya shiga side din daga nesa yake hangowa kamar shahidan,tana tafe yana
biye da ita a bayanta kaman wani bodyguard,taku kadan zai qara ya hade tazarar dake
tsakaninsu,tana zaban abu tana zubawa a cart din da nuradden ke turawa,ya bata dama
ne ta zabarwa maman komai,da fari taso zuqewa yace indai tayi hakan bata dauki
maman mamarta ba,dole tayi yadda yakeso.

Sanda ta waiwayo don dawowa daya side din fuskarta ta bayyana fes cikin
idanunshi,tana murmushi ne gami da hararar nuradden daya tsokaneta da
"Iyee,ashe madam din tawa an iya siyayya,irin wannan siyayya me aji haka?,gaskiya
idan mukayi aure ke xaki dinga min shopping" dauke kanshi yaso yayi tare da aiwatar
da abinda ke gabanshi amma sai ya gaza hakan kamar wanda aka haneshi,haka kawai
yaji idanunsa na masa yaji yaji,wani abu mai zafi ya sauka a qirjinsa,suna dab da
cimmasa ya juya ya soma takawa don barin shagon gaba daya.

Kallon bayanshi kawai ya haifar mata da mummunar faduwar gaba,duk da batasan


waye ba bata ga fuskarshi ba,haka kawai ta dinga kallon bayanshi har ya bacewa
ganinta nuradden nacan yana zaben zobe,yanayin tafiyarshi da bayanshi kaman anwar
"And so what koda ya kasance anwar dinne?" Zuciyarta ta gaya mata wanda hakan ya
sanyata tabe baki da daga kafada.

Tun kafin ya qarasa ya bude motar,yana zuwa ya shiga ya maida murfin ya


rufe,saiya samu kansa da kasa tafiya,ya sauke glass din side dinsa gaba daya qasa
abinda ba dabi'arsa bace,numfashi yake fitarwa dai dai idanunsa kan qofar fitowa
daga wajen,shi kansa baisan zaman me yayi ba me yake jira oho duka bai sani
ba,saiya duba agogon hannunshi,tara saura,tara saura fa na dare?,sake maida
idanunsa yayi qofar shagon dai ya kafeshi da ido.

Minti goma ya sake duba agogo,tara na dare saura kadan,har yanzu dai shuru?,ya
tambayi kansa
"Lafiyanka kuwa anwar?,wai shin ma me kake jira ne?" Ya tambayi kansa da kansa,tuna
hakan da yayi yasa ya dage gilasan motar da gaggawa ya zura key zai tasheta,dai dai
sanda ya sake duban qofar kanti,sai gasu sun fito fuskokinsu cike da murmushi,yana
riqe da ledojin siyayyar,yayin da ita kuma take riqe da iya tata jakar.

*Ga mai buqatar littafin da zan fara bayan kammala alqawarin Allah,ya shiga youtube
yayi searching SAUTIN HIKIMA zaiga an rubuta (subscribe) dajan rubutu,ya danna sau
daya zai koma black,yayi screenshoot ya turo zuwa wannan number zanyi adding dinsa
a grpup din in sha Allahu 07038670166*

2️⃣ 2️⃣
https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos*Alqawarin Allah*
2️⃣2️⃣

Fasa kunna motar yayi ya tsaya cak yana dubansu ta cikin gilashin har suka isa
bakin motar nuradden din,shi ya bude mata qofar motar ta shiga sannan ya sanya
ledar daya a baya,saiya dora dayar saman cinyarta,runtse ido anwar yayi ganin haka
yana jin wani abu ya dunqule masa a wuya.
Hannu nuradden ya saka cikin aljihun wandonshi ya ciro wani dan qaramin
akwati,ya budeshi yana murmushi ya ciro qayataccen zobe a ciki ya miqawa shahida
yana murmushin,kallonsa tayi sannan ta kalli zoben
"Da zaki miqo min hannunki na saka miki sai nafison haka,ki saka da hannunki
shahida....amma shahida,don Allah zaki aureni?" Maganar ta shiga kunnenta a
bazata,daga idanunta tayi ta kalleshi
"Me ya kawo wannan maganar nuradden?"
"Ban cancanci nayi wannan maganar bane shahida?,kina tunanin akwai wani namiji da
zai kalleki yaji ba burinsa bane ya mallakeki?,ko tsahon zamanmu tare bai kamata
ace na nemi mu zama miji da mata ba?" Bayyananniyar ajiyar zuciya ya saki,gaba daya
ya rusa mata lissafi da plan dinta
"Hakane....amma kayi haquri zamuyi wannan maganar daga baya,kaga yanzu dare yayi
naga kiran anty xubaida ma"
"Shikenan" ya fada yana maida zoben akwakunsa sannan ya miqa mata,ta saka hannu ta
amsa ya zagaya seat dinsa ya shiga ya tayar da motar.

Kashi anwar ya jingina da kujerar da yake kai idanunsa kan motar tasu har
suka fice daga wajen,hakanan yaji ya kasa zama shima ya tada motar tasa ya figeta
yabi bayansu da hanzari,ba jimawa ya cimmasu,haka ya dinga bin bayan motar har zuwa
cikin unguwarsu qofar gidan,gotasu yayi yayi parking din motarsa daga gaban tasu ya
kasheta yana kallon abinda ke faruwa,motar ta bude ta fice ta tura gate din gidan
ta shige sannan nura ya tashi motarsa ya fice daga layin.

Ya kusa a qalla minti goma a tsaye a wajen


"Wanne abu kake ne haka anwar,kana cikin hayyacinka kuwa?" Yaji maganar daga
sama,wani sashe na zuciyarsa na tuhumarsa
"Ya Allah" ya fada shima cikin jin haushin kansa,gami da tuhumar kansa na me ya
kaishi aikata haka,saiya kunna motar yana duban agogon dake gaban motar,qarfe tara
harda minti goma sha shida,yana jin da qyar idan zai iya zuwa gidana anty usaina
yanzu duk da tana can tana jiranshi,kawai saiya wuce gidanshi,zuciyarsa na masa
wani irin zafi haka kawai.

Baiyi nisa a tafiyar ba wayarshi ta dauki qara,ya kalli wayar da ido


kawai,sa'ida ce ke kiranshi,saiya danna sannan ya maidata handsfree yace
"Ya akayi sa'in(shi yakan kirata dashi wani lokaci)"
"Uncle,zaka zo ne?"
"Me ya faru?"
"Uncle wani abu na gani,wata na gani tazo wajen ummi uncle kasan dawa take kama?"
Kai ya kada
"A'ah,dawa take miki kama?"
"Uncle kaman anty shahida nidai haka na gani,amma wannan ta dan fita girma ta kuma
dan fita kyau" gabanshi ne yafadi baisan sanda yace
"Yaushe?" Ba
"Dazu dazu suka shigo gida tare da ummi" dan shuru yayi na dan wani lokaci sannan
ya sauke boyayyar ajiyar zuciya
"Shikenan...yau bazan samu shigowa ba,amma ki bari gobe idan nazo sai muyi maganar"
"Toh uncle,ka siyomin turaren?"
"Zan kawo miki karki damu,ki gaida ummin naki kice mata wani dan uzuri ya riqeni"
"Toh uncle" daga haka dukkansu suka kashe kiran,tunani ya shiga sosai,sai salon
tuqin nasa ya koma slow kaman bazashi gida ba,tunaninta ne ya dawo masa sosai tun
farko alaqarsu irin wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba.

Sai daya kashe wasu mintoci kafin ya isa gida,a gajiye ya isa falonshi ya
fada saman kujera yana lumshe idanunshi kafin ya budesu,yanason manta komai amma
abubuwan nata zarya bisa qwaqwalwarsa,sai kawai ya miqe zuwa bedroom dinshi,ya cire
kayanshi ya daura towel ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi sosai.

Ya jima zaune gefan gadonshi yana neman bacci ya sureshi amma abun yaci
tura,saiya miqe zuwa wani safe na musamman dake dakin,ya saka lambobin sirri ya
budeshi,envalope din daya tsani gani yau da kanshi ya daukota,ya bude abubuwan dake
ciki gaba daya,hotunan ciki suka bayyana,take kanshi ya soma daukan zafi,idanunsa
suka kada jazur dasu,saiya kasa ci gaba da kalla ya soma tattaresu yana tuhumar
shahida cikin ranshi
"Me yasa shahida me yasa?,me yasa za kiyi haka,me yasa kika tarwatsani,me yasa kika
tarwatsa duk wani buri da fata na?" Ya qarashe maganar yana cilla envalope din
cikin abun ya maida ya rufe,saiya fada saman gadonshi yana maida numfashi gami da
ambatar
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil"

*WASHEGARI*

Qarfe goma da minti arba'in ya isa gidan cikin dinkin shadda wadda tayi
masifar masa kyau da fito da kyawunshi.

Dukkansu suna falo suna karyawa


"Uncle sannu da zuwa,ina kwana" suka dinga fada daya bayan daya,fuska a sake yake
amsa musu yana tambayar lafiyar kowa suna amsa mishi
"Ina ummin taku?"
"Tana sama tana wanka" sa'ida ta bashi amsa bakinta fal da zance,turarenta ya ciro
ya miqa mata tasa hannu biyu ta amsa cikin Murna
"Uncle na gode,na gode"
"Yauwa" ya amsa yana duban tashar da suke kallo,hijra tv waqoqi suke sanyowa na
mawaqa daban,sa'ida ce ta tashi daga cin abincin da take ta dawo kan kujerar da
anwar yake kai
"Uncle" ta fada qasa qasa,waiwayo yayi yana kallonta
"Uhmmm"
"Maganarmu ta jiya...." Shuru tayi ta ganin saukowar anty usaina,suna hada ido
tahau rarraba idanu,miqewa tayi tsaye kafin ta iso,ta jefa mata harara
"Ku kwashe farantan nan kukai kitchen,munaya ki hadasu ki wanke,ke kuma uwar zance
ki bita ki daura abincin rana,kafin ki gama laqaqin naki kin gama" duka suka miqe
falon ya zama daga ita saishi,ta zauna tana dubanshi
"Jiya sai kuma na jika shuru,sa'ida tace ba zaka samu shigowa ba" yana shafa kanshi
yace
"Wallahi,jiyan na taho wani uzuri ya tsaidani"
"To Allah ya rufa asiri" a mutunce ya gaisheta ta amsa masa cikin kulawa sannan
daga bisani tace
"Ko a hado maka abincin kari?"
"Eh to...amma bada wani yawa ba" dauke idanunta tayi daga kanshi ta mayar qofar
kitchen din ta kira sa'ida tace ta hado mishi.

Yana karyawan suna taba hiran,a hankali shurunsa yafi maganarsa


yawa,hankalinsa ya karkata kan hijra tv da suka sako waqar jarumar mata,saita dinga
taba ranshi kadan kadan,tana tuna mishi wani lokaci can baya,a nutse ya dauki
remote din dake aje kusa dashi ya sauya tasha,dai dai sanda anty usaina tace
"Anwar....ya kamata fa ace ka soma shiri,biki saura sati hudu amma banga alamun
hakan tattare dakai ba"sai daya hadiye abincin bakinsa sannan yace
"to me zanyi anty bayan wanda nayi"
"Kamar ya me zakayi?,haka zaka aurar musu diya babu maganar lefe babu komai?" Aje
cokalin hannunsa yayu sannan yace
"Nifa anty,da zaki yadda da maganata ayi haquri a qara min wasu watanni"
"Saboda baka da gidan sakata ko baka da kudin yi mata lefan?,ko sadaki ne baka
dashi?" Murmushi ne ya subuce masa ba tare daya shirya ba
"Au dariya ma nake baka ko anwar?"kai ya girgixa dariyar na kubce masa
"ni na isa antyna,kawai dai....naga kina yin nafisa ne da yawa" zamanta ta gyara
sosai,alamun maganar da zata masa nada muhimmanci
"Ba haka bane anwar,ka fahimceni,mutanen nan suna da kawaici da dauke kai,basu da
son zuciya ko tilasta mutum,da wasu ne su yadda suke ganin sun isa dakai dinnan
kawai zasu baka umarnin ka auri diyarsu ne,su saka kuma ranar biki da komai baka
data cewa,uwa uba ina gudun halayyarku ta maza kafa kazo ka murje ido kace ka fasa
ka barmu da kunya" murmushi yayi yana kallon qasa,shikam dama bayajin zai dauki
irin wadan nan abubuwan,dalili kenan da tun farko ya zabi yaci gashin kansa,bai
qasan wani bare ya tilastashi koya tauyeshi,rama halacci dai wannan yasan abune mai
kyau,kuma shine hujja daya,dalili daya da zai sakashi ya haqura ya auri nafisa
"Anty kiyimin kyakkyawan zato,ba abinda zai faru da yardar Allah indai daga
bangarena ne,abinda kawai yasa na buqaci qarin shine,akwai wata 'yar tafiya da
zanyi ta wata uku,kinga zaifi kyau naje na dawo,hankalina ya hadu waje guda,duk
abinda za'ayin ma sai ayin,zan baki kudin da zai isa a hada lefan kafin wucewata da
sauran abubuwan da aka sabayi na al'ada" ajiyar zuciya ta saki
"Shikenan,yanzu ya za'ayi ka shaida musu?"
"Wannan duk ba damuwa bace,zan samu alhj da kaina,baida matsala,yasan da tafiyar
tawa dama"
"Shikenan,Allah yayi mana jagora ya bada sa'a"
"Amin anty" daga haka suka shiga hirar data shafesu,sai wajejen shabiyu na rana ya
baro gidan shima ganin haduwar hadarine,bayan ya tambayesu ya tabbatar basu da wata
damuwa.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Cikin harabar gidan yake zaune cikin motarsa,murfin motar side din da yake a
bude yake,hakanan ya ziro qafarsa daya waje,iska mai dadi dake kadawa tana shigowa
har inda yake,iskar na masa dadi qwarai,,dalilin kenan daya sanya idanunsa lumshewa
yana shaqarta har tsakiyar kanshi,knocking glass din motar yaji anyi,ya ware
idanunsa a hankali suka sauka kan fuskar nafisa dake tsaye cikin kwalliya tana
dubanshi daga sama har qasa,duk da fuskarta qawace take da kwalliya amma annurin
cikinta kadan ne,shigarsa take kallo,yayi kyau cikin qananun kaya baqaqe qafarshi
saye cikin wani booth mai bala'in kyau,quruciyarshi da kyanshi muraran suka
bayyana,sai taji sonshi na sake shigarta,baqinciki da bacin ran daga bikinsu ya
sake mamayeta har hakan ya bayyana kan fuskarta
"Whats wrong with you" ya tambayeta idanunsa qyar a kanta,saitayi narai narai da
idanu,qwayar idonta cike da qwalla,,da alama gab take da sakin kuka,shuru tayi ba
tare data amsa ba,fitowa yayi gaba daya daga motar ya rufe sannan ya jingina da ita
hannayensa shima harde a qirji
"Me ya sameki kuma?"
"Au..baka ma sani ba zaka cemin?" Hannayensa ya watsa yana harde qafafunsa sannan
ya soka hannayensa a aljihun wandonsa
"Eh to,xai iya yiwuwa ni abinda nake tunanin shi zai saki kuka ke a wajenki bashi
bane"
"Me yasa anwar me yasa har qarin watanni uku bayan wata gudan dake gabanmu"
girarshi biyun ya dage yana murmushi
"Au,kice ke kukan aure kike,to saurin na meye?,wata hudu kawai saiya zama damuwa?"
Langabe kai tayi tana dubanshi
"Ni sai ya zama damuwa mana a wajena idan har wajenka bai zama damuwa ba,dama ni na
damu dakai ai na sani" murmushi ya kuma saki,yadan tafa hannunshi kadan
"Abinda ya faru ya riga ya faru,sai a jira zuwan lokaci"
"Ai shikenan,yana iya"agogo ya kalla sannan yace
"Zan wuce" idanu ta zaro
"Duka duka yaushe kazo?,haba ya anwar mana don Allah,hajiyama fa tace ka shigo kaci
abinci"
"Sauri nake nafisa,amma idan na samu chance anjima zan dawo,idan ban dawo ba kuma
sai gobe" ya qarashe maganar yana bude motar,sai daya shiga sannan ta mayar masa da
murfin ta rufe ta daga masa hannu
"Allah ya kiyaye" shima hannu yadan daga mata,har zai tada motar tayi hanzarin
tsaidashi
"Sorry...don Allah ka yimin alfarma mana"
"Allah yasa batafi qarfina ba" murmushi tayi
"Bata fiba,saidai idan ba za'a min ba" dan qaramin murmushi yayi
"Fadi muji"sai data danyi shuru na sakanni sannan tace
"Kamfani triple R Gem nakeso ka rakani don Allah" shuru yayi yana dubanta
"Me zakiyi a can" hannu ta yarfar
"Kai ya anwar,da banso gaya maka ba Allah,amma..."
"A'ah,riqe cikinki" yayi maganar sanda ya tada motar,da sauri ta zaburo
"Bafa wani abu bane,wasu sarqoqi nakeson saya a can" kallonta kawai yake,burin
nafisa yayi girma da yawa,duk sarqoqin garin nan amma sai taje har triple R ta
saya?,iya saninshi wajene dake da babu abun qaramin kudi a can,dutse ne masu daraja
da tsada suke sarrfasu,wanda ba kowa ke iya siyan abun kwalliya ba acan,bayason ya
fiya gwasaleta har taji kaman ya tozartata,sai ya gyada kai
"Alright..amma gaskiya bani da lokaci cikin satin nan gaba daya,saidai ko zuwa next
week"
"Well,yayi indai zaka rakani din" da haka sukayi sallama ya fice daga gidan yabarta
tsaye awajen sonshi na shawagi da ita,sai kuma ta tuna yau akwai partyn da zata
saboda haka da sauri ta juya zuwa cikin gida.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe biyar ta fito daga kamfanin kaman yadda qa'idar lokacin tashinsu
yake,saidai gaba daya hankalinta ba'a kwance yake ba saboda baqin hadarin daya hado
yake kwance a sama yana shirin zub da ruwa.

Kusan mutum uku ne sukayi mata tayin sauketa a gida amma ta doje don kare
mutunci da qimarta,ciki harda alhajin dake nacinta wanda ta lallaba ta fito abinta
ta baroshi a office din rayyan mai kamfanin gaba daya suna lissafin wasu sarqoqi da
sukayi masa,haka ta fito cikin ranta tana addu'a Allah yasa ta isa gida lafiya
qalau.

Titin babu wadatar motoci sai jifa jifa,ko dama can titin bashi da wadatar
wucewar ababen hawa musamman ma na haya,yawanci saina gida,hakan ya sanya ta kusa
kashe minti goma tsaye ba tare da taga gilmawar wani abun hawa na haya ba,cikin
abinda bai gaza minti biyar ba hadarin ya taso sosai,iska ta shiga kadawa ko ina
sama ta sake duhu,fargabarta ta dadu,ta runtse ido tana jin saukar ruwan saman bisa
fuskarta,Allah dai yayi saiya daketa.

A hankali yake tuqin saboda yanayin ruwan dake sauka din,uwa uba yanajin
kaman yayita shawagi saman titi ba tare daya koma gida ba,yakan kasance cikin kewa
da kadaici duk sanda ruwan sama irin haka ke zuba yana cikin gidan shi daya,yakan
tuna masa wata hira da suka tabayi da uta,duk da yadda yakeson bunne komai nata
amma duk lokacin da ake ruwan sama kaman haka sai hirar ta fado masa
"Nafison damina akan kowanne yanayi,tana saka nishadi cikin zuciya,komai yana
wankewa yayi fes,tsirrai zaka ga sunyi kyau ya anwar sunyi kore shar,kosu kasan
suna farinciki da zuwanta,qamshin qasa iska mai dadin da babu kamarta" tayi maganar
ne idanunta na alumshe,saita budesu tar cikin nashi a lokacin da ya zuba mata ido
yana tayata murmushin da takeyi na tuna yanayin da tayi
"Kasan me yaya anwar?" Ta tambayeshi wanda bata kai ga fadin abinda takeson fada
din ba kiran nafisa a sannan ya katsesu,dai dai sanda shima nashi tunanin ya katse
yana hango tsaiwar wata matashiya cikin ruwan saman da har hazo hazo yake,tsurawa
wajen ido yayi yana ci gaba da tuqin a mugun slow kai kace motar na dab da mutuwa
ne,baikai ga qarasawa ba wata farar mota ta yanko daga layin da yake kusa da
ita,dab da ita ta tsaya na cikin motar ya fito riqe da lema ya iso gabanta ya
matsar da lemar zuwa kanta da alamu magana yake mata,idanu ya runtse yana tsaida
motar duk da a tsakiyar titi yake,idanunsa qur akansu,alokaci shahida ta sake ja
baya
"Ka wuce kawai,bani da damuwa nasan ko ban samu mota yanzu ba ruwan daya tsagaita
zan samu"
"Haba yallabiya,ke kuwa yau dai kawai,uzuri ne fa,kiga yadda ruwa ke dukanki ke
daya atsaye anan,uwa uba tsaiwarki a titi irin wannan lokacin hatsarine ga
rayuwarki"kai ta girgixa
"ba komai Allah zai kareni"
"Duk da haka amma kiyi...." Ta gaji dajin kalaman bakinsa,saboda haka kaman adan
hasale tace
"Don qaunarka da mahaliccinka kayi tafiyarka" ya fuskanci kaman tanason hasala ne
don haka yace
"Allah ya baki haquri,naji zan tafi,amma kema don qaunarki da mahaliccinki ki karbi
wannan lemar" batason dogon zance saboda haka tasa hannu ta amsa,ya koma ya shiga
motar ya tasheta ya wuce,ajiyar zuciya ya saki ganin tafiyarsa,duk da haka saiya
kasa tafiya yaci gaba da tsaiwa kaman me gadinta.

Ganin ruwan yadan fara sauqi saita soma takawa don canza wani titin ko zata
dace,shima saiya tashi motar yaci gaba da binta sannu sannu,yana kallon yadda take
digar ruwa har cikin zuciyarsa,saidai bazai iya daukarta amotarsa ba,yanajin wani
abu cikin zuciyarsa,kallonta na tuna masa da ganinta da yayi,fitowarta daga motar
wani,wanda ba qaramin suya yake masa a qirjinsa ba.

*ga mai buqatar littafina da zan fara bayan gama alqawarin Allah,zaije youtube yayi
searching SAUTIN HIKIMA,daga qasa zaiga an rubuta SUBSCRIBE da jan rubutu,ya danna
sau daya zai koma black,yayi screen shoot ya tiro zuwa wannan number,za'ayi adding
dinsa agroup din in sha Allah*
07038670166*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki
sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

2️⃣ 3️⃣
*Alqawarin Allah*
2️⃣3️⃣

Gab da zata tsallaka daya titin mai adaidaita ya taho,ta tsaidashi da sauri,babu
kowa a ciki ta gaya masa inda zata ya dauketa suka wuce,sai da yaga tashinsu sannan
ya saki ajiyar zuciya
"Wai anwar meye damuwarka ne haka?" Wani sashe na zuciyarsa ya jeho masa
tambaya,sai a sannan ya dinga tuno abinda ke faruwa,sam duka baisan yana abinda
yayin ba,kamar wani umarni yaji ana bashi,kai ya girgiza yana jin haushin
kansa,yana ganin ya tsaya ne kawai ya bata lokacinsa,motar ya bawa wuta sosai cikin
gudu ya figeta ya harba titi.

Su duka suna zaune a falon suna kallo,da sallama ta shiga,dukkansu sannu da


zuwa suke mata,anty zubaida na cewa
"Wai wai,sannu rahamatullah" murmushi tayi tana zuge lemar hannunta,huda ta tashi
da hanzari zata tarbeta ta dakatar da ita
"Tsaya huda karki jiqe,don ni da kika ganni yau jalaf nake a kaina ruwan yau ya
qare" tayi maganar sanda take aje jakarta
"Ahto...haka kawai za'a baki mota kika qi,da kinga yanzu ba ruwanki da ruwa ko
rana"
"Wallahi anty to ya za'ayi....faruqu don Allah zazzagemin jakarnan ka duban wayata
ka shanyan abinda kaga ya jiqe" da sauri huda ta amshe cikin shagwaba
"Anty gani sai kice ya faruq kuma?"hararta faruq yayi
"To kishiyata" Dariya shahida tayi
"Auto auta yi haquri,gyaramin bari naje na sauya kayan jikina sanyi sanyi nakeji"
"Idan kin saukoma ga dinkunanki nan an kawo" waiwayowa tayi
"Yauwa,yaushe ya kawo?,jiya fa mukayi waya dashi yace bai gama ba"
"Dazu ya kawo"
"Ya kyauta,don kayan matar data bani aron style nakeson maida mata,kar taga rashin
hankalina...bari naje na dawo saina gani"
"Uhmmm" anty zubaida ta fada.

Sai data soma kunna qwan dakin data kashe dazun da zata fita aiki,haske ya
gauraye ko ina,ko.ina tsaf yana fitar da qamshi kaman yadda ta saba masa,ta kalli
agogo,shida harda rabi na yamma,an kusa kiran magariba kenan,kayan jikinta ta fitar
ta shiga bandaki ta hada ruwa mai dumi sosai tayi wanka hade da alwala sannan ta
dawo daki ta shirya cikin wasu kaya masu dan kauri,sai datayi sallar magariba
sannan ta sake fitowa.

Yanzun ma a zaune ta samesu,saidai da alama faruqu da haidar sunje masallaci


sun dawo,anty zubaidan ma wannan karon da hijabi jikinta,huda dake duqe gaban
socket ta dago tana cewa
"Yauwa anty,yaa nuradden ne ya kiraki"
"Uhmmm" ta amsa tana dubanta,saita ciro wayar ta kawo mata ta karba tana
dubawa,Allah ya taimaketa ba abinda tayi ruwa bai tabata
"Na gode hudallahi" shahida na murmushi ta fada.

Saida sukaci abinci sannan ta duba dinkunan,sunyi masifar kyau ko ba'a fada
ba tasan zasu zauna mata a jiki,saita yanke kawai ta barsu saida bikin da zasuyi,ta
ninke kayan ta kwashesu ta haura sama dasu,don yau da wuri takeson kwanciya har
yanzu kuma yayyafi ake,saboda gobe sammakon fita zatayi akwai ayyuka da yawa.

Tana shirin jan abun rufa kiran nura ya shigo wayarta,ido ta lumshe sannan ta
waresu,ba yadda ta iya haka ta daga
"Ranki ya dade....yau an manta dani kwata kwata ko?,koda yake dama idan ban nemeki
ba saidai na shekara ina jajenki"
"Ba haka bane...ayyuka ne yau sai hamdala"
"Ina fatan dai basu gajiyarmin dake ba?"ajiyar zuciya ta sauke
"Gajiya kam akwaita,don yanzu ma shirin kwanciya bacci nake"
"Da wuri haka?,da qorafi nakira nayi,amma tunda haka ne kiyu baccinki dakyau,ki
gayan yaushe zanzo mu hadu?" Kanta ta juya daya sashen,ta danyi nazari kadan
"Kasan yanayin aikin nawa,wunin office ne,idan na dawo kuma na gaji bacci kawai
nake buqata" tsaf ya gama ramfota,haduwar tasu ne bataso,ita kuma takurawa da
zancan aure da yake a 'yan kwanakin da yadda yake marairaice mata ya sanya bata
fiya son haduwar tasu dashi ba,sakata yake kawai a corner
"Duka ba damuwa bace,ni idan anmin izini saina riskeki har office din lokacin break
mu tattauna abinda zamu tattauna din,karki damu bazan jima ba zan tafi,daga nan har
zuwa next week ina jiranki" numfashi ta sauke,ya gama kamata kenan iya wuya,amma
itama bari ta qure haqurinsa
"Saidai nan da sati daya rana ita yau"
"Allah ya kaimu" ya amsa hakan bisa ga mamakinta,da haka sukayi sallama ta kwanta
tunani fal ranta,tana mamakin yadda nuradden yake iya shanye duk wani hali
nata,bata taba kamashi da rashin yi mata uzuri ko hanzari ba,tanajin nuran na hawa
wani mataki fiye da wanda yake kai a baya,ya kamata ta sake bashi wata damar ko
yaya take,da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.

*BAYAN SATI DAYA*

Turare ta dauka ta fesa abu na qarshe cikin shirin fitarta office,ta kalli
kanta sosai ta tabbatar komai yayi mata,shiga mai kyau da tsari,riga da skert na
swiss atampha wanda suka mata cas da mayafi yalwatacce wanda ta dorashi saman
daurin dankwalinta data dan turoshi gaban goshi,hannunta agogo ne kaman yadda tafi
son sakashi fiye da awarwaro,wuyanta sarqa ce da dan kunnayensu masu azabar kyau
qirar kamfaninsu,wanda gwaji ne akayisu aka bawa masu manyan matsayi a
kamfanin,takalmanta ta jawo rufaffe na mata wanda ya dace da shigarta,tana zuge
jakarta da zata fita da ita taji shigowar saqo a wayarta,saita dakata da abinda
take ga zatonta mudassir ne daya daga cikin abokan aikinta wanda yace zai tura mata
wasu bayanai kan lissafin da suke tayi na wasu siyayya da wani kamfani yayi na
sarqoqi,ga sabanin tunaninta saita tarad da nuradden ne

_Da fatan wannan kyakkyawar halittar ta tashi lafiya cikin amincin ubangiji,yau
sati guda cif cif,Allah yasa banyi azarbabi da yawa ba_

Kyawawan idanunta masu kyau da haske ta juya gabanta yadan fadi,sam ta manta da
zancansu wanda yace ya bata sati guda,saita sauke numfashi data tuna cewa bai taba
zuwa kamfanin nasu ba,asalima bata taba gaya masa inda yake ba,hakan na nuna baisan
office dinta ba,bazai kuma iya zuwa ba har sai ta bashi adress,tuna hakan ya mata
dadi,don idan yazo din bata jin zaya samu amsar da yake da muradi,saboda haka ya
kashe wayarta ta jefa a jaka tana murmushin nasara,ta duqa ta qarasa saka
takalminta ta dago tana rataya jakarta huda ta shigo cikin shirin makaranta
itama,gaida shahidan tayi ta gaya mata sun fito
"Muje hudallah...wannan makaranta anaji da ita" dariya ta saki
"Sosaima anty,kinga randa me makarantarmu yazo,ya bamu labarin wahalar da yayi
saboda karatu,yace mu dake muyi karatu sosai muma donmu zama irinshi" yatsine fuska
shahida tayi saboda yadda zancan ya tuna mata da ranar
"Allah ya kiyaye" shahidan tayi subul da bakan fada wanda yasa buda ta juyi da
sauri
"Allah ya kiyaye kuma anty?,yana da kirki fa,sannan yana da karatu,ya iya turanci
da larabci,gashi kyakkyawa,shiyyasa ranar banji dadi ba da kika koma gida baki
ganshi ba.....kinsan me?,uncle fa muke ce masa,yace duka mu yayanmu ne..."
"Hudaa....a'ah" shahida ta fada tana kallonta,itama sai ta saka ido kawai tana
kallon shahidan
"Oya muje karki sa muyi late dukanmu" dariya ta saki tana tafiya sauri sauri
"Mu yanzu ai ba'a dukan late comers,uncle ya hana" goshinta ta dafe da tafin
hannunta,wato dai hudan ba zata daina mata zancan mutumin nan ba.

Tana mamakin yadda suke ganin kirkinsa haka da yawa,basu san cewa macijin
sari ka noqe bane shi?.

Agurguje kuma a tsaye ta hada tea dan kadan ta kurba,duk yadda anty zubaida
tayi kan ta tsaya tayi break sosai cewa tayi sauri take yau suna da aiki da
yawa,haka ta fice bayan ta musu sallama,aka dauki huda itama ta shiga tata
adaidaitan suka wuce.

A cikin company ya ajeta kaman yadda suka saba ya juya ya fice ita kuma ta
shige zuwa cikin ainihin kamfanin,a sashen kula da baqi na musamman zata wuce cikin
hanzari tajuyi muryar mudassir
"Kin kusa makara fa" waiwayowa tayi fuskarta babu yabo ba fallasa ta dubeshi
"Wallahi,amma na gode Allah da ban makara ba,ina fatan komai ya zama ready"
kafadarshi ya daga yana dubanta,yana da muradin shahidan sosai tana burgeshi,komai
nata abun sha'awa ne amma kame kai da jan ajinta yasa ta masa wani irin kwarjini
daya sanyashi ya kasa kwatanta mata bare ya furta
"Eh tuni ma" ya qarashe maganar yana miqa mata daya daga cikin file biyun dake
hannunshi,hannu ta saka tana buda shafukan farko tana dubawa sama sama,daga kai
tayi sai suka hada ido yana kallonta,hakan ya sanyata dan tsare gida
"Ka sameni a office dina muyi acan inaga zaifi" ta juya abinta ta isa bakin
elevator da xata kaita zuwa bakin ofishinta.

Da sallama ta shiga duk da cewa ya sani babu kowa ciki,a nutse ta qarewa
office din kallo,ko ina tsaf yake yana fidda sassanyar qamshin da ita ta yiwa kanta
zabin kalar freshner din da takeso wadda ta banbanta data kowa,wadda ke mata shara
din ta qwarai sosai,sannan kuma tasan aikinta,hakan yasa takejin dadin aikin da
take mata,tasan ra'ayinta da tsarinta,jakar hannunta da file din ta dora saman
teburinta sannan ta taka a hankali ta isa bakin windows din office din ta bude
kowanne,iska mai dadi da sanyaya rai ta soma kunno kai,irin iskar damina mai taushi
da sanyi,tana son irin wannan iskar,sabida banu iska mai dadinta,fresh ce daga
indallahi,sai data tabbatar ta gauraye office din sannan ta rufe windows din,ta
sauke labulayen ta kunna AC,hakan ya qarawa office din wani dadi da yanayi na
musamman.

Tana zama mudassir ya shigo,yaja kujera ya zauna yana qarewa office din kallo
sanda take kiciniyar futo da system dinta wadda a office din ta kwana bata je da
ita gida ba jiya
"Kai masha Allah,duka kamfanin nan ba office din dake burgeni nakejin dadin
shigoshi irin wannan,komai neat masha Allah" ya qarashe maganar yana sauke idonshi
a kanta,dan qaramin murmushi ta saki sannan ta soma dai daita cumputer din
gabanta,ba tare data sake bashi wata qofar sako wani zancan ba ta soma gabatar masa
da abinda ya zaunar dasu.

Tun tara da rabi suke abu daya har qarfe daya da rabi na rana kafin su
kammala,ta gaji matuqa tayi tubus,ga 'yar banzan yunwa dake damunta,kujerarta taja
baya bayan ta rufe system din tana hamma idanunta lumshewa wanda sam bata kula da
yadda mudassir ya zuba mata ido yana kallonta ba cikin burgewa,tunda suka zauna
qamshinta ke burgeshi
"Yadai madam?" Ya tambayeta har yanxu idanunshi na kanta,sai a sannan ta juyo ta
dubeshi,fuskarta adan hade kaman yadda ta saba idan ta fuskanci kana da shiga sharo
ba shanu
"Da akayi me?,ai mun gama ko?,sauran aikin ya rage naka da nawa,kowa yaje ya tsara
abinsa cikin system dinsa,duk randa zamu gabatarwa da boss kowa yasan me zai fada"
kai ya rausayar
"Ba haka nake nufi ba,naga kaman bakijin dadi ne" miqewa tayi tsaye tana gyara
yafen mayafinta,bandaki takeson shiga sabida fitsari ya matseta gashi yaqi fita ya
bata waje
"No,ba komai gajiya ce kawai.." Ta tura kujera baya sosai yadda zata samu damar
fita daga tsakanin kujerar da teburin.

Gab da zata shige bandakin aka nemi izinin shigowa office din ta
bayar,masinjarta ce cikin girmamawa tace
"Kinyi baqo ne anty(haka take kiranta saboda yadda take ganin qimar shahidan" cikin
mamaki tace
"Baqo kuma?,custumer ne?", ta tambaya duk da tasan bashi bane,don yawanci ba'a
ganinta ita idan ba wata matsala bace akan pyment da custumer zaiyi,koda kuma zai
ganta ma za'a rakoshi ta qarqashin wani office dake kula da shige da fice da kuma
siyayyar kaya a kamfanin
" a'ah,yace yana son ganinki ne personal"tayi tsammanin cikin mutanen dake takura
mata ne,abun saiya qona mata rai,batason abinda zai shafi mutuncinta a wajen
aikinta,sabida haka taja tsaki
"Jeki ce masa lokacin aiki ne yanzu,ya nemeni ta waya ko waye idan na tashi daga
nan"
"Toh" ta fadi tana juya ta fice daga office din,tsaki taja ta dawo don daukar ruwa
ta soma sha tukunna
"Sai haqurifa,kinsan kowanne mutum da yadda Allah yake masa baiwar jama'a"
waiwayowa tayi ta kalleshi,shaf ta mance dashi cikin office din,saita dauke kai
tana sake hade girarta ba tare datace masa komai ba,batason a dinga zama mata cikin
office tafison kuna gama aiki ka kama gabanka,wayarta dakw cikin jakar hannunta
wadda ke saman teburinta tayi qara,a nutse ta qarasa ta zugeta ta cirota,sai taga
number nuradden,fuska tadan yamutsa saboda yadda taji gabanta yadan fadi,ta daga ta
kara a kunnenta
"Allah ya baki haquri gimbiya nine fa,ko nima ba za'a samu damar ganina ba bayan
alqawari aka yimin?" Mamaki ya cikata,ta yaya akayi yasan kamfanin da take
aikin,banda abinki wannan wajen kina tunanin zai xama boyayye ne?,shahararren waje
irin wannan? Wata zuciyar tace da ita,murmushi ta qaqaro
"Ayyah bansan kai bane,minti daya ina xuwa" kiran nashi ta katse ta soma neman wata
number cikin ranta fana dana sani da Allah wadai da kunna wayarta data yi,data sani
tun daxun ta barta a kashe kawai,wani sashe ta kira na kamfanin ta bada umarnin a
rakoshi,daga haka ta kashe wayar,duka sai jikinta yayi sanyi taju qafafunta kamar
an bubbuge mata su,sai ta zauna saman kujerun cushion dake gefe daya na office din.

Sanda ya turo qofar lokacin saddam ya miqe yana fadin


"Bari na samo miki wani abun,na fuskanci kaman yunwa kike ji" bata iya amsa mishi
ba yayin da sukayu clashing da nuradden sanda yake shigowa,suka kalli juna saddam
ya sanya kai ya fice nuradden ya bishi da kallo,sai daya bace masa sannan ya dauke
idanunshi ya qaraso yana rufe office din idanunshi a kanta
"Waye wannan din?" Ya tambayeta kai tsaye,tasan akan wa yake tambaya saita saki
murmushi
"Abokin aiki,aiki muka gama dashi yanxu" dan shuru yayi kishi na cinsa,ji yayi
kaman ya maqure saddam din sabida ya karanci irin kallon da yakewa saddam din shima
irinsa yake masa,kansa kawai ya jinjina yana qarasowa
"Kin kashe wayarki kin tsammaci bazan iya laluboki ba duk inda kika shiga ko?" Boye
dariyarta tayi,batasan ya dagota ba
"A'ah,kasan idan ina aiki banason yawan amsa waya,dalili kenan daya sanyani na
kashe" inda ta tashi ya koma ya zauna yana kallon office din nata,kaman yadda ya
saba burge jama'a shima ya burgeshi sosai
"Sannunka da zuwa" saiya kalleta
"Allah yasa har zuci" qaramar dariya ta saki
"Da ba har zuci ba da tunu na koreka ai" maimakon ya amsa saiya jefo mata wata
tambayar
"Wanne babban baqo haka kukayi a companynku yau?" Dan tunani tayi kadan sannan tace
"Gaskiya ban sani ba,saboda ba bangarena bane" kishi yakeji sosai da fargabar kar
shahidan ta subuce masa saiya sanya idanunsa cikin nata sanda take za a wata
kujerar da take kallon tashi
"Haka manyan mutane ke zuwa wajenku?" Kafada ta dage
"Wajensu dai,abune mawuyaci ni nasan zuwansu ko fitarsu,tubda ba sashe na bane
saidai idan wata matsala da buqatar zuwa wajena ya zama dole"
"Ina kishinki shahida" cak ta tsaya tana kallonsa,kalamansu sunyi shigen kama dana
juna,ya tuna mata dashi dole saboda yanayin yadda yayi furucin,hakan ya sanya ta
miqe kawai ba tare data samu abun fada ba
"Kinsan sonki yake?" Ya jefa mata tambayar sanda take bakin dan qaramin fridge
dinta tana ciro masa ruwa da lemo,saita waiwayo tana dubanshi,murmushi ya qwace
mata
"Wani abu makamancin haka bai taba shiga tsakanina dashi ba,kar ka saka komai a
ranka,kai kanka shaida ne na wace shahida,abu mai sauqi ne samun hanya zuwa
zuciyata kai tsaye har haka?" Maganar tata ta bashi qwarin gwiwa,sai yayi shuru
yana nazarinta,harta dawo ta aje masa lemon da ruwan a gabanshi,yayin dashi kuma ya
dire mata ledar daya shigo da ita
"Ga abinci nan,inajin kamar kina da buqatarsa shi yasa dana tsaya naci nayo miki
naki takeway din,don nasan ko xuwa nayi nace kizo muje muci taren ba zuwa zaki ba"
ya fada cikin jefanta da magana,tasan yana jin haushin hakan,ita kuma ra'ayine sam
bata dashi,sabida haka tayi murmushi kawai,ko yanzun ma ba zata iya cin abinci yana
kallonta ba shina ya sani,amma duk da haka saiya soma bude mata ledar yana cewa
"Kiyi haquri yau dai daya kici a gabana,saimu tattauna abinda ya kawonin,kada
lokacin break dinki ya qare na shiga haqqin company",bai gama budewa aka sake bude
qofar aka shigo,dukansu suka maida hankali ga qofar,saddam ne hannunshi dauke da
ledar gidan abincin dake daura dasu,wanda shahida tafi order abinci acan,fuskarsa
cike da murmushi ya nufosu kai tsaye ba tare daya dubi nuradden ba ya iso
gabanta,dora abincin yayi saman na nuradden daya bude mata yace
"ga favourite dinki nan", wani abu ne ya takorewa nuradden wuya,ya daga kai ya
kalli saddam cikin fushi
"Wanne irin rashin hankaline malam?" Dubansa saddam yayi
"Da akayi me?"
"Ta yaya zaka shigo kai tsaye ba tare daka nemi izni ba,sannan ka samemu zaune zata
ci abinci ka dora wata ledar a sama?" A dage saddam yace
"Matarka ce?"
"Koba matata bace ina zaton tare ka ganmu" cikin halin ko in kula yace
"Auto da sauqi abun,kaga kenan allurar cikin ruwa ce,mai rabo ka dauka" ran
nuradden saiya kai qololuwar baci,hakan ya sanya shahida ta dubi saddam
"Banason tashin hankali saddam,meye haka?" Baison nuradden ya gane cewa bai taba
furta mata kalmar soba bare ya sake samun qwarin gwiwa,hakan ya sanya ya dubeta
"Ba manufata na bata miki rai ba,sai anjima" ya juya ya fice.

Sosai yake jin babu dadi cikin ranshi,saiya dubi shahidan


"Shahida...tsorona da fargabata ta sake daduwa,inajin har cikin raina bani da
tabbas idan har baki amsa min cewa ni kikeso ba kuma ni xaki aura ba" gaba daya sai
lissafinta ya nemi dagulewa,batason ta dauki alqawarin da zai zame mata ciwo ko
nauyin da wuya ta zaiyi wahala ya iya dauka,saboda haka cikin sanyin murya da
kwantar dakai tace
"Tsoron meye haka nuradden,ka kwantar da hankalinka don Allah".

Duban nafisan yayi fuskarshi a hade" me kikayi haka kenan?,me yasa tun farko
baki duba lafiyar atm din naki ba saida kika gama siyayyar?,bayan kinsan accnt din
aya samu matsala sai xuwa gobe zai soma aiki?"langabe mishi kai tayi
"Please anwar...don Allah kayi magana da mai kamfanin gaba daya,na tabbatar ka
sanshi tunda naji kace bakason yasan ka shigo kamfanin,tunda ka bada rabin kudin
yanzu zai amince ka aiko da saura idan ka koma office,Allah wannan sarqar nasha
wahala na dade ina nemanta,kuma kanaji suma sukace dsign dinta kadai yayi saura,ba
lallai idan na ajeta naje na dawo na sameta" idanunsa ya lumshe kaman bazaice komai
ba,haka kawai yakejin kasala tunda ya tashi yau,hakanan zuciyarsa da jikinsa sam
babu dadi,baice komai din ba ya fita daga wajen da kanshi ya taka zuwa sashen biyan
kudi,suka tarbeshi don tunda ya shigo kamfanin suka gane waye,hakan ya sanya suketa
nan nan dashi,daya daga cikin ma'iakatan ya yiwa magana yana son ganin rayyan
"Ranka ya dade,oga bai shigo ba,amma babu damuwa zaka iya ganin rahama" dan shuru
ya sake yana fidda wayarsa daga aljihunsa ya duba lokaci,sannan ya lalubo wata
number ya kira,bata shiga ba,duka lambobin rayyan din basa tafiya,saiya sake kiran
wata number din,ba jimawa aka daga,ya ambaci adadin kudin da yake buqata ya gaya
masa inda zai kawo masa
"In sha Allah yallabai ina hanya" daga haka ya maida wayar aljihunsa
"Ai...ranka ya dade basai ka zauna jira ba,rahaman kawai zaka yiwa bayani shikenan
zata shigar ne cikin kundin bayanan shiga da fitar kudi na kamfanin" lokaci ya kuma
dubawa,shi kansa baison zaman,saboda jiransa da ake,banda ya riga da yayiwa nafisan
alqawari kuma baison rashin cika alqawari da baiga abinda zai zaunar dashi har haka
ba
"Ba damuwa,bani number din office din"
"To ranka ya dade" ya fada yana gaya mishi cikin sauri kai tsaye ba tare da an
sanar da mai office din ba saboda sanin wayeshi baida buqatar sai sun hadashi da
mai masa iso,a nutse ya juya ya soma takawa
"Ina zaka?" Nafisa dake addu'ar Allah yasa su gama lafiya su fita lpy karya
hutsance mata ta tambaya
"Ki jirani" kawai ya fada yanayin gaba.

Kallon number office din yayi sosai sannan yaja da baya ya kalli qofar,ya
dora hannunshi saman handle din ya tura a hankali wanda hakan ya sanya basuji
alamun bude qofar ba.*zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki
sharing,ga mai buqatar siya zaki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*
09032345899

2️⃣ 5️⃣
*Alqawarin Allah*
2️⃣5️⃣

Tafiyar awa biyu cif ta shigar dashi garin katsina,tuqi yayi lafiyayye cike da
nutsuwa da kuma tunani kala kala,kai tsaye unguwar kakanninsa ya nufa.

Yana qoqarin parking motarsa kawunshi modu ya fito da alama masallaci zashi
saboda yadda yake dan hanzari,bai ganshi ba hakan ya sanya anwar kirayenshi,saiya
waiwayo yana dubanshi cikin murmushi
"Ikon Allah,yau kaine a garin da kanka?" Yana murmushi gami da kashe motar yace
"Wallahi kawu,mun sameku lafiya?"
"Lafiya qalau...mu shiga daga ciki"
"A'ah kawu,gwara na soma yin alwalar tukunna"
"To...to,shiga daga mana saika daura"
"Ah ah kawi,kar naje su tsaidani mu rasa jam'i,idan mun idar ma shuga tare" daya
daga cikin yaran da sukazo wucewa kawu modu ya qwalawa kira ya sashi ya shuga ciki
ya debo musu ruwa a buta
"Dan kuwa yau inna ta samu nayi,kazo yau zuwan ba zata sanda ba'a tsammaci ganinka
ba" murmushu anwar yayi
"Wallahi kawu,Allah ne ya kawo tafiyar haka"mintuna kadan yaron yafito dauke da
'yar matsakaiciyar buta,anwar ya karba suna dan taba hira da kawu madun harya gama
alwalar suka rankaya zuwa masallacin.

"kaine yau kuma?" Inna ta fada sanda yake qoqarin zama kan daya daga cikin
kujerun dake falon,murmushi ya saki yana dubanta,sun riga da sun camfashi baisan
dalili ba
"Nine inna,kaman wanda bai zuwa?,kodai rikicin tsufa ya soma samunki ne kike zaton
na jima sosai banzo ba?" Baki ta tabe tana rufe kwanon shan data gama shan ruwa a
ciki
"Idan ina rikicin tsufa na kasa lissafi ai kawunka ahmadu baiyi tsufan da zai kasa
lissafi ba ko?" Dariya ta bashi sosai har sai daya danyi sannan yace
"To shikenan yanzu Allah ya shiryeni,saime kuma?" Harararshi ta danyi
"Allah yasa"
"Amin inna" gaisheta yayi cikin mutuntawa ta amsa tana tambayarshi su anty usaina
"Lafiya lau take,tana gaisheku dakyau"
"Muna amsawa" daidai lokacin rashida 'yar kawu ahmadu ta shigo da kwanon abinci
guda biyu,cikin girmamawa ta isa gaban anwar ta aje tana gaidashi
"Duba cikin dakina ki dauko kwanon sha ki debo masa ruwan a randa idan zai iya sha"
dariya ta sake bashi,ya fuskanci rikici yau take ji da gaske,saboda wancan zuwan da
yayi tace ya zabi daya cikin yammatan 'yan uwa dake katsina ya hada da wdda zai
aura a kano duka ya aura,yasan yau zai kashe bakin tsanya ne gaba daya shi yasa bai
tada maganar ba ya barta take rikicinta
"Sha kuwa harda shaye shaye...amma ba yanzu zanci abincin bane,zanje wata unguwa ne
na dawo,saqonku na tsaya saukewa don na ragewa motar nauyi" duban rashida yayi dake
zaune gefe tana kallonshi,ji take daman a gidansu yake
"Inasu abdurrashid?"
"Suna qofar gidan malam"
"Maza jeki kiraminsu" da hanzari ta miqe ta fice kawu ahmadu ya sako kai hannunsa
dauke da ruwan roba da lemon roba ya aje gaban anwar yana cewa
"Garin yau ana zuga rana da zafi,ko rashin saukar ruwan sama ne kwana biyu ya saka
haka oho?"
"Ba mamaki kawu,kasan ko yaya hadari ua hadu ba ruwa sai gari ya bada zafi" daga
haka kawun ya samu waje ya zauna suka shiga taba hira kan harkar noma da abinda ya
shafi damina har yaran suka shigo.
Cikin girmamawa suka gaidashi kowa na murnar ganinsa,ya amsa musu cikin
kulawa ya dubi kawu da inna
"Kawu xanje wata unguwa na dawo,Allah yasa zan sameka idan na dawo din,akwai
maganar da nakeso mu tattauna"
"Eh nima inason dan fita in duba shago na yau aike akemin,dalilin ma daya sanya ka
ganni gida ban fita kasuwa ba kenan,amma ba jimawa zanyi ba,zan sallami yaranne na
dawo"
"To ma sha Allah,kafin sannan na dawo,inna zanje na dawo"
"Allah ya tsare hanya" ta fada tana aje carbin hannunta sannan suka fita da yaran
ya bude motarsa ya fito da duka kayan da yake nasu ne,yace sukai cikin gidan,sai
daya tabbatar sun shige sannan ya tada motar ya fice daga layin.

Sassanyar ajiyad zuciya ya fitar sanda yake gab da isa unguwar,qwaqwalwarsa


na masa bitar abinda xaije ya aiwatar din,jiki da zuciyarsa tana gaya masa abinda
zaiyi din shine dai dai,a nutse ya kutsa motar cikin layin,bai tsaya ba sai daya
rage daura gida daya ya isa qofar gidan sannan ya kashe motar,zamansa yayi ciki
yana tunanin ta yadda zai soma shiga gidan,daada zata ganeshi kuwa?,zata karbi
zancansa?,zata yarda da qudurinsa?.

Idonsa ya bude sosai sanda yaga saurayin daya saba aike zuwa gidan lokaci xuwa
lokaci ya leqo ya koma da sauru,addu'a yake Allah yasa ya sake fitowa.

Da hanzari sulaiman ya koma zuwa cikin gida da sauri yana kiran


"Daada,daada" dattijuwar da ake kira da daadan wadda ke zaune cikin rumfarta tana
daura busashshiyar kubewa ta daga kai kawai tana kallonshi har ya iso rumfar tata
"Haba sule,wannan wacce iriyar dabi'ar banza ce haka?"
"Daada wallahi saurayin nan da yake bani saqo lokaci lokaci nake kawo miki wanda
kikace bakisan waye ba kema shi na gani a tsaye a qofar gida,kince duk randa ya
sake zuwa na tsaidamiki shi shi yasa nake sauri na gaya miki kar yana bada saqon ya
tafi"
"Miqo min mayafina....duk abinda ya baka kada ka amsa kace masa lallai lallai ya
shigo inason ganinsa"
"To" sulaiman ya fada yana bata mayafin sannan ya sake fitowa da hanzari.

A nutse yake nufo motar anwar,wanda shima ganinsa yasanshi sauke glass dinsa
har sanda sulaiman din ya qaraso bakin window bakinsa a washe,anwar ya miqa masa
hannu kaman yadda suka saba,yana Murmushi sulaiman ya miqa masa hannu sukayi
musabaha,yana bala'in son musabaha da anwar din,koba komai zai gogi qamshinsa dake
burgeshi yaji laushin fata sannan kuma hannunsa ya shaqi sanyin acn dake cikin
motar kamar yadda sulaiman din ke cewa
"Kwana biyu yallabai?" Sulaiman ya fada yana sosa kai,murmushi anwar din yayi
sannan yace
"Ko zaka yimin iso gurin mutanen gidan?"
"Me zai hana?,dama daadan nason ganinka,ta roqeni ma kan don girman Allah yaudai ka
shigo taga me mata aiken nan" murmushi ya kuma saki yana cire belt din jikinsa
sannan ya maida glass din motar sama ya bude murfin ya fito,sai daya rufe motar
sosai sannan sulaiman yayi gaba anwar din na biye dashi a baya.

A bakin qofar gidan anwar ya coge yana duban soron gidan yana tuna wani abu
daya taba faruwa a wajen shekaru shida baya,a shekarun baya da suka wuce idan aka
ce masa zai sake taka soron saiya qaryata,amma dattako mutunci da qaunar da
dattijuwar ta nuna masa a baya ya dawo dashi yaci gaba da nuna mata nashi
karamcin,sulaiman ya dubeshi
"Ka shigo mana,bismillah" kai ya kada
"Shiga tukunna ka gaya mata zan shigo" anwar din ya masa kwarjini da yawa don haka
ya kasa musa masa,ya saka kai zuwa cikin gidan karo na biyu.

"Tace ayi maka iso" sulaiman din ya fada yana duban anwar,a nutse ya sanya
qafafunsa soron yaci gaba da takawa bisa jagorancin sulaiman.
Qarqashin bishiyar dake gefe daya na tsakar gidan tabarma ke shimfide,nan
sulaiman ya nuna ma anwar,ya sabule saucikin dake qafarsa ya ajesu sannan ya isa
saman tabarmar ya zauna,dai dai lokacin da daada ke fitowa daga rumfarta hannunta
dauke da kwanon sha wanda ke cike da ruwan randarta mai sanyi,idanunta akan anwar
din harta qaraso,duk da ganinta dashi sau biyu ne tak a rayuwa,a lokacin da yafi
haka qarancin shekaru da rashin cikar xati da kamala.

Hannu yasa ya amshi kwanon sanda take shirin xama ya ajeshi gabanta,saida ta
zauna sosai sannan ya soma gaidata
"Mun sameku lafiya?"
"Lafiya qalau alhmdlh....yaro kaike hidima damu haka tsahon shekaru uku amma baka
taba tsayawa na ganka ba ko wani cikin 'ya'yana ya ganka ba bare yayi maka godiya"
murmushi yayi har fararen haqoransa suka bayyana idanunsa a qasa,sai taga ya sake
koma mata anwar din sak,anwar din da har kwanan gobe takeson tasan ina yake?,meya
rabashi da jikartata,amma har yau idan zata tambayi shahidan sau dari bazata tada
kai ta bata amsa ba,harsai ta gaji tayi shuru
"Amma saurayi....sai naga kamar anwaru ko?,anwarun shahida" daga kai yayi yana
duban dadan tare da jinjina ma qoqarinta data iya ganeshi
"Shine daada" gaba daya fuskarta ta washe da fara'a sosai,wani irin farinciki ya
mamayeta,tunda taga anwar din a wancan shekarun Allah yasa mata qaunarsa,ya shiga
ranta sosai,dai daikun ranaku ne da zasu zo su shude bata tuna dashi ba
"Ma sha Allah,Allah abin godiya,kana nan dama anwaru?,har kana iya zuwa guna ka
aikomin da saqo amma ka kasa shigowa na ganka mu gaisa ko sau daya ne?,haba
anwar,me muka yi maka haka?" Murmushin dai ya sakeyi
"Kawai haka Allah ya tsara mana daada,shi ya raba ganawarmu sai yanzu daya qaddara
haduwar tamu"
"Wannan haka yake" ta fada tana jinjina kai cike da gamsuwa,har yanzu bakinta ya
kasa rufuwa
"Ashe daada baki manta dani ba?" Baki ta kama tana cewa
"Ta yaya zan manta dakai anwar,bani bama hatta da qannen mahaifin shahida sun kasa
mantawa dakai,kaiba irin mutumin da za'a manta dashi bane anwaru,gashi shekara
kusan uku kanamin alkhairi ba tare daka bari nasan cewa kai bane....kai sule,zo nan
zoka amsowa anwaru damammiyar fura da nono" tafada tana qoqarin kunce daurin habar
zaninta dake daure da kudi,da sauri anwar ya dakatar da ita
"A'ah daada,don Allah karki wahalar da kanki" dakatawa tayi da abinda take
"Karka tsaidani anwaru,nasan yana daya daga cikin abinda kafison sha rahama ta
gayamin tun lokacin ban manta ba,wannan shine kadai abinda nakejin zan iya maka"
saiya qyaleta ta kunce kudin ta baiwa sulaiman ya amsa ya fice.

"Wanne laifi muka yi maka haka anwaru daka gujemu haka?,ka bace mana bat,ina tsaka
da murnar jikata ta samu nagartaccen miji,tunda har naji isma'ila Allah ya jiqan
rai na yawaita maganarka na tabbatar da nagartarka,dana ganka kuma saina sake
tabbatarwa lallai nagartaccen ne kai,ita kuma waccar almurar koxan kwana kwana
tambayarta ba zata cemin kanzil ba" gyara zamanshi yayi sannan a nutse yace
"Dukkan abinda ya faru a rayuwar bayi ba shakka muqaddari ne daga Allah,kisa a
ranki hukuncin ubangiji ne bacewata daga rayuwarku..."
"Gaskiya ne" ta amsashi tana gyada kai,sadda kanshi qasa yayi sosai
"Zuwa nayi ki bani aurenta daada" kyakkyawan murmushi ya subuce kan fuskar
dattijuwar,cikin ranta tana godewa Allah tare da hamdala,tayi tsammanin shahidanta
ta rasa nagartaccen anwar din nan,sai gashi ya dawo a sanda basu zata ba
"Wannan ai tsohon zance ne anwar,shahida ai taka ce" wani abu ya tsaya masa a
wuya,zayafi kowa farincikin jin hakan da ace a baya ne sanda shahidan take shahidan
anwar ba yanzu data zama ta kowa ba
"Na sani daada,amma wannan karon nazo ne a bani auren shahida da gaske ba kamar a
bayan ba"
"Indai wannan kake da buqata kana iya komawa da aurenta,bamu da haufi kanka
anwaru,koda mahaifin shahida na raye nasan haka zai fadi" hakanan yaji wani sasauci
a ranshi da zuciyarsa,wanda ya danganta hakan da nasarar da zai samu ce ta nunawa
shahida da saurayinta cewa shiba sa'ansu bane takowanne fanni
"Amma duk da haka,ka jira zuwa gobe zan kira kawunnanta na tabbatar musu da aurenka
da shahida"
"Na gode qwarai da gaske daada da wannan karamci,amma inason kimin wata alfarma
guda daya"
"Ba zata gagara ba insha Allahu anwaru"sassauta muryarsa yayi
"mun samu sabani da shahida wanda shi ya zama silar rabuwarmu na wadan nan
shekaru,na dawowa shahida saidai yadda ta dauki zafi fiye dani ta tabbatarmin ba
zata taba karbata a matsayin miji ba..." Yadan dakata a ranshi yana istigfari kan
qaryarda yayi
"Inason don Allah dada a boyewa shahida gaskiyar wanda ke neman aurenta,inason na
gaya mata da kaina mu sasanta kuma kanmu ba tare da kowa ya shigo ciki ba" qanqan
da ido daada tayi cikin masifa tace
"Wato ja'ira tasan komai shi yasa ko zaka kwana tambayarta saita dinke bakinta
ko?,yoni aida ka barni da ita don dakalin qofar gidansu mu gauraya da ita,ja'ira
tana tafe kaman daben masallaci kai kace ba ita bace..." Duk yadda yake jin ransa
saida fadan dadan ya bashi dariya,ya danne yana cewa
"Ki haquri daada karki tasarmin ballina"qwafa taja
"Don dai kace haka ne amma da goben zan gaya mata da kaina,idan yaso ta iskoni
katsina ta hukunta ni" daada na tsaka da fadan dake baiwa anwar dariya yake kuma
sakashi nishadi sabida nasarar daya samu sulaimanu ya dawo da damammiyar fura mai
sanyi data sha suger,sosai anwar ya sake ya dinga sha suna hira da dadan tana bashi
labarai wanda anan yaji labarin rasuwar abban shahidan,sosai jikinsa yayi sanyi
qwarai,ya dinga jin babu dadi har cikin ransa,ya dinga tuno abubuwa da dama
tsakaninsa dashi,yana qaunarshi sosai hakanan yana ganin girmansa,kaman dan cikinsa
ya daukeshi ba suruki ba,yayiwa daada ta'aziyya sosai.

Bata barshi ya tafi ba saida tayi masa irin danwaken da yakeso,wanda ta taba yi
masa zuwansa ziyara wajenta na farko,baici da yawa can ba saboda tuna wani lokaci
da yayi a baya,hakan yasa yaji cikinsa ya cushe,sai bayan la'asar sannan yayi mata
sallama ya wuce.

Daga nan gidan wani abokinsa ya wuce,bashi ya baro wajensa ba shima sai gab
da magariba,koda ga koma unguwar kakannin nasa yana aje motarsa ya wuce sallah
masallaci,acan suka gamu da kawu modu suka rankayo gida bayan an idar.

Inna na zaune cikin rumfarta iskar fankar solar da anwar ya hada duka gidan na
kaiwa da kawowa a falon,bata qure fankar can ba hakanan batayi qasa da yawa
ba,hakan ya sanya iskar ke kadawa dai dai
"Ina ka tsaya haka daga cewa yanzu zaka ka dawo?" Sosai yakejin gajiya da kasala
yadan motsa fuska
"Wallahi inna..nima ban zaci zan dade haka ba" dauke kai tayi ta kalli jijarta
bushira dake xaune tana kallo falon inna tace ta miqawa anwar tuwon darenshi da
mamarsu ta aje masa,cikin sabbin fulasai kaman da plates masu kyau harda ruwan sha
a jug kaman yadda suka saba masa duk sanda yazo.

Qasa ya sauko ya soma zubawa da kanshi duk da cewa ba wata yunwa yakeji sosai
ba,amma saboda innar kar tava dazu baici ba yanzun ma haka taji ba dadi
"Naje gidan daada ne,kakar shah....." Saiya kasa qarasa fadin sunan
"Rahama" ya qarashe fada da ainihin sunanta,wanda baya jin tsahon zamanin da yayi
da saninta ya taba ambatar ainihin sunanta
"Wacece haka?"
"Yarinyar da zan aura..na taba baki labarinta shekara shida baya,wadda ta kasa zuwa
gaidaku?" Murmushi inna ta saki
"Shahida wai?,yarinyar da usaina ke bamu labari wadda ta damu kan rabuwarku?" Kai
ya gyada yana ci gaba da ci tuwon
"Ma sha Allah,amma saidai wani hanzari ba gudu ba,ina maganar yarinyar can nafisa
'yar wajen alhajin nan?,ina cewa duka duka watanni aurenku ya rage?,don dama zuwan
naka nake jira naji ainihin sati nawa ya rage"
"Maganar nafisa tana nan,kuma watanni uku suka rage"
"Anya anwar?,kana nufin auren mata biyu lokaci guda?" Inna ta fada tana
kallonshi,kai ua gyada
"In sha Allah inna,tunda Allah ya hore saidai a tayamu addu'a" shuru ta danyi kadan
kafin daga bisani tace
"Shikenan...Allah yayi jagora,ubangiji ya kore abinqi"
"Ameen"sai daya hadiye lomar bakinsa sannan ya sake cewa
"Na shaidama kakartata gobe su kawu zasu je su tambayamin izini a wajensu,to gashi
ban samu na sanarwa kawun ba,kuma a goben nakeson na koma saboda na baro ayyuka,ban
tsammaci ma yau din zan kwana ba"
"Aiba wata matsala bace,ai ado kawai za'a yiwa waya(qaninta kenan)a sanarwa,shehu
da dahiru suna kan hanya yanzu muka gama waya,sunje duba ta'annabi,idan suka shigo
sai kuyi maganar".

Bashi yabar gidan ba sai qarfe goma na dare,sai daya tabbatar komai ya
kammala ya kuma tsaru sannan ya nufi masauki,yana fitowa daga wanka yana shirin
kwanciya wayar nafisa ta shigo,ya gaji tubus duk da yaga tarin miscal dinta
niyyarsa saida safe zaya kirata saboda bacci yake da buqatar yi,dole ya daga bayan
ya kwanta sosai saman gadonshi
"dear,ina ka tafi ne?,muhsin yace min baka gari"
"Katsina"
"Me kuma kajeyi can dear?"
"Kin manta ina da dangi ne a can?,naje gaida su inna,sannan kuma na gabatar da wani
dan aiki"
"Au haka ne,me yasa baka hadani da ita ba na gaidata?"
"Idan kin matsu kina iya karbar lambarta tunda tana da waya,da can baki gaidata ba
saida nazo zakice na baki?" A shagwabe tace
"Am so sorry dear,ka turomin number din nata saina kirata"
"Saidai gobe idan Allah ya kaimu,yanzun kam na gaji bacci nakeson nayi" da haka ya
samu ya sallameta ya aje wayar tunani nakai kawo cikin ranshi,kenan yanzu idan
lamarin ya tabbata mata biyu zai aure kenan?,juya lamarin yayi cikin zuciyarsa,koda
wasa bai taba kawowa kanshi xai auri mata biyu ba,sai kuma tunaninsa ya juya kan
shahida da nuradden,zayaso yaga fuskar kowannensu a sanda labari ya isa
kunnensa,murmushin mugunta ya saki yana mirginawa hannun damanshi ya soma karanto
addu'ar bacci bayan ya kunna suratul baqara cikin wayarshi ya rage mata sauti
sosai.

*ga mai buqatar littafin da zan soma bayan kammala rubutun alqawarin Allah,zaije
youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,akwai jan rubutu na SUBSCRIBE daga qasa,zaka
dannan sau daya zai koma baqi,sai kiyi screenshoot ki turawa wannan number da
zataso daga qasa,za'a sakaki a group din littafin da yardar Allah*

07038670166*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gansu don GIRMAN ALLAH karki
sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wannan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

2️⃣ 6️⃣
*Alqawarin Allah*
2️⃣6️⃣

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Washegari qarfe tara na safiya ya gama shirinsa tsaf cikin yadinsa na maza mai
kyau da tsada,yayi masifar kyau yadda hularshi ta zauna kanshi sosai kawai ya isa
ya gaya maka ya hada jini da kanawa,hakanan yake jinsa wani sawai kuma fayau
dashi,ya qarasa reception yayi maida musu key din dakinsu ya sallamesu ya wuce zuwa
gidan inna.

Falon inna ya wuce kai tsaye bayan ya isa gidan,ya tadda kawu dahiru da kawu
modu suna rumfar innar suna hira da alama anan sukari karin safe tare,cikin
girmamawa ya gaida inna sannan ya gaidasu yana zama daura da ita,ita ta yunqura da
kanta ta hada masa lafiyayyen kunun tsamiya da sukayi da wainar gero,cikin marmari
yake ci suna ci gaba da hira dasu kawu dahirun,yana kammalawa kawu shehu ya
iso,basu wani jima ba suka miqe gaba daya zuwa gidan daada,shi yaja motar,kawu
shehu da yake shine babbansu yana gaba,kawu dahiru da kawu modu kuma suna baya.

Sanda suka isa gidan sha daya na safe har ta dan gota,hakan yasa suka tadda
kawun nan shahida sun riga da sun iso,sulaiman shi ya musu jagora kamar ko yaushe
zuwa cikin gidan
"A'ah....shehu,kardai kacemin yaron dake neman shahida dan wajenka ne?" Kawu ummaru
wanda yake yaya ne ga mahaifin shahida ya fada yana dariya sanda sukayi musabaha da
kawu shehu
"Yaro na ne,dan wajen qanina ne mai rasuwa"
"
"Kai ma sha Allah,amma naji dadin abun nan qwarai,to ai abunma duk na gida ne,ita
kanta daadan ma bata sani ba,inaga basai anje anata kaiwa da kawowa ba,ayi komai
kawai a gama lokaci guda"
"Kana ganin babu wata damuwa ko matsala?"
"Haba shehu,kaine fa,babu wata damuwa wallahi,dama meye burinmu banda muga yaranmu
sunata aurensu".

A ranar gaba daya kawu ummaru suka amshi kudin auren shahida harda
sadaki,aka kuma tsaida lokacin biki ko ince daurin aure a wajen maza watanni uku
masu zuww,wanda yayi dai dai da watannin da aka tsaida a farko na daurin aurenshi
da nafisa.

Yana tsaye jikin motarshi qafafunshi amatuqar sanyaye,irin wannan lokaci ya


jima yana mafarkin zuwanshi shekara shida baya,ya qiyasta yanayin farinciki da zai
samu kansa a duk sanda Allah ya tabbatar masa a wancan lokaci har baisan sau naya
ya qiyasta din ba,sai gashi abun yazo a bahagon yanayi,yanayin daya kasa tantance
wani iri ne,farinciki ne ko baqinciki?,kansa ya daga a hankali sanda ya soma jiyo
muryoyin su kawu dahiru da alama suna sallama ne dasu kawu ummaru.

Ranar kasa shiga yayi wajen daada duk da yaso suyi sallama,haka ya sake
dibansu kawu shehu ya sauke kowanne a gidansa sannan suka wuce wajen inna shida
kawu modu.

Murmushi ne kawai ke fita a fuskar daada sanda 'ya'yan nata ke gaya mata
yadda komai ya kasance
"haba,ba banza ba nutsuwar yaron ta yimin,naji ya shiga raina sosai,ashe jinin
gidan malam usman ne(sunyi zama na maqotaka ne tun iyayensu da kakanni,zaman da
sukaji dadinsa,kunsan mutanen daa akwai riqo da zumunci da kuma girmama alaqa da
dangantaka komai qanqantarta),na godewa Allah,Allah yasa albarka ya kuma tabbatar
da alkhairi"
"Amin daada" dukkansu suka amsa suna jin dadin hadin
"Yanzu daada za'a sanar dasu kenan?"kai ta girgiza
"qwarai kuwa,ka shaida ma ita uwartata,sannan kuma ka kira can gidan hishamun a
shaida musu,duk da cewa shi ya sani amma sai a gaya masa an karba harda kudin auren
da sadaki,gobe idan ka dawo kai ummaru ka kiramin rahamar ka hadani da ita"
"To shikenan daada" ya fada yana lalubar wayarshi dake aljihun rigarsa.
*_GUDUN QADDARA guzurin taddata....._*

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wadda ta fito tun daga zuciyarta,ta sauke
idanunta kan tafin hannunta tana bitar maganganun nuradden daya gama furta mata
ayanzu,dauta dauko na anty zubaida data gama gaya mata jiya,kusan maganganun nasu
sunyi kamanceceniya da juna,a yanzu bata da wata mafita bata da wani uzuri kaman
yadda anty zubaida tace mata,imma dai ta baiwa nuradden dama wa imma ta sallameshi
hakanan ya daina wahala,ko ga ummanta madai wannan karon ta matsa qwarai kan ya
kamata ta tsaida manemi tayi aure,tunda dai abinda ya farun da ita bawai qarshen
rayuwarta ya kawo ba,saima sabon babin rayuwa daya sake bude mata,idan ta sallami
nuradden bata jin akwai wani qwaya daya cikin samari dama masu auren dake kara
kaina akanta da zata iya kwatanta rayuwarta ta wanzu tare da tashi
"Na amince nuradden....Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi" hannayensa gaba
daya ya hada ya rungume a qirjinsa yana lumshe idanunsa,wani farinciki da baisan a
wanne mizani zai dorashi ba ya shiga dawainiya dashi,sai kawai ya zame saman
gwiwoyinsa a gabanta
"Shahida,ki fadamin me kikeso na baki ladan wannan kyakkyawan albishir din naki?"
Kai ta kada kawai qwalla na taruwa a idanunta,murmushi mai cakude da alamun son yin
kuka na kubcewa saman fuskarta
"Babu abinda zaka bani face nace kayi qoqari karka sa na sake yin nadama da dana
sani a rayuwata karo na biyu"
"Koda baki roqi haka ba wannan duty na ne" da ido kawai ta dinga bishi yadda ya
rasa inda zai tsoma ranshi ya dinga bata mamaki,harta daina mamaki ma abun ya soma
bata dariya,sai daya tabbatar ta dan saki ranta sannan yace
"Yanzu yaushe za'a kai maganata katsina?,shine abu daya da zai sake sawa in samu
nutsuwa a raina,in kuma tabbatar na yiwa duk wani dake da buri ko hanqoran
mallakarki na masa fintikau din da dole ya haqura" murmushi ya qwace mata,tasan
cewa burinsu daada kenan,tana da tabbacin indai nuradden ya isa katsina to magana
ta qare,don ba wani lokaci zasu ja ba ba tare da sun bashi ita ba
"Karka damu duka abun bana sauri bane,next month za'a dauki azumi,sai kayi haquri
mu barwa salla" fuska yadan bata
"Gaskiya yayimin nisa,saidai idan har kin yarda ne ni zan kaiki,qafarki
qafata"hannu ta daga tana murmushi
"Shikenan naji,sai kuma me?"
"Aikin gama min komai nikam,yau nafi kowanne namiji dake fadin duniyar nan sa'a"
yayi furucin a sanda yake kallon sararin samaniya cikin madaukakin farinciki.

Qarfe tara ta shiga gida don bata wuce hakan a waje,duk da dama ba fita take
wajen kowa ba,kusan nuradden din ne kawaima yaci qwallo da har take fita ta
saurareshi,ga mamakinta saita tadda anty zubaida zaune saman kujerar falon hannunta
daya tallafe da kanta,gwiwar hannunta saman hannun kujera,ba kowa falon sai ita
kadai,kallon wani series da suke haskowa a mbc take,sallamar shahidan ya sakata
dagowa da sauri tana dubanta
"Anty,yau yana sameki a nan?" Qoqarin daidaita kanta tayi
"To ya zanyi,uncle dinki yace lallai lallai naga shigowarki na tura masa ke"
murmushi tayi tana zama hannun daya kujerar dake daura da anty xubaidan
"Hala anty kinkai masa qarata ne kan nuradden?,to kisha kuruminki,na riga na baiwa
nuradden dama,zuwa nan da qaramar sallah xai isa gasu daada in sha Allahu" ta
qarashe tana duban anty zubaida,don tasan ta gama mata abinda ranta keso kenan,sai
taga ta murmusa kadan
"Ya za'ayi nakai qararki?,koda nakai dinma ai Allah abinda ya hukunta dole shi zai
faru ko?,yanzu dai kije yana falonshi yana jiranki" sai data miqe sannan tace
"Anty muje tare mana don Allah"
"Ba ruwan zubaida" ta fada da hanzari,dariya ta baiwa shahidan yadda tayi maganar
kamar wata baquwar uncle hisham din,saita juya ta wuce tana cewa
"Ai shikenan anty".
"barka da dare uncle"shahida ta furta sanda ta nutsu a gaban uncle hisham,ya
sauke takardar da yake dubawa ya kalleta
"barka kadai shahida,sai yaushene zakuyi hutun naku kamfanin?"
"Eh to uncle gaskiya ina zaton sai sai dab da sallah,saboda wannan season ne na
yawaita da kuma cunkoson custumers" kai ya jinjina sannan ya danyi shuru kamar mai
nazari kafin daga bisani yace
"Daada ce keda buqatar kije,to ban sani ba ko xaki samu ko weekend ne kije kiji
kiran nata na meye?"
"Shikenan uncle babu damuwa,yau alhamis ranar juma'a tunda da wuri muke barin
kamfani saina shirya naje,idan yaso ran lahadi da yamma saina dawo"
"Hakan yayi,shikenan dama kiran"
"To uncle saida safe" ta fada tana miqewa
"Allah ya bamu alkhairi".

A inda tabar anty xubaida nan ta taras da ita,saita daga kai tana kallon
shahidan,ganin babu sauyin fuska tattare da ita ya tabbatar mata uncle din bai gaya
mata komai ba,zai turata ne kaman yadda dada ta buqata,sallama anty zubaidan tayi
mata ta wuce wajen uncle din,tabar shahidan na sake sabon xaman ganin maimaicin
wani shiri,tana mitar baccin wuri da yau su faruqu sukayi suka barta ita daya,don
bata jin dadin zaman falon ita kadai.

A nutse yake murza motarsa tamkar wanda baison barin titin har zuwa sanda ya
isa unguwarsu anty usaina,cikin nutsuwa ya faka motar sannan ya kasheta ya
fito,cikin wani irin karsashi yake takawa zuwa cikin gidan,haka kawai yake jinsa
kaman mai yawo cikin farin gajimare wanda shi kansa baisan dalilin haka ba,yana
shirin saka qafarsa kan step qwaya daya da zai sadashi da falon gidan ya jiyo
muryar sa'ida na kiranshi,a nutse ya waiwaya,sai ya tsaya hannayensa zube a aljihun
wandonsa yana dakon qarasowarta.

Aladabce ta rusuna tana gaidashi ya amsa yana dubanta


"Daga ina kike?" Sai data dan waiwaya sannan ta dawo da dubanta wajensa
"Uncle....gidansu anty shahida,ummi ta aikeni na amso mata saqo?,kasan me uncle?"
Kai ya girgiza yana dubanta
"Na ganta mafa tazo wajen mamansu,uncle kaganta kuwa kaman ba ita ba...."takun data
jiyo ya sanyata tsuke bakinta,cikin minti daya anty usaina ta bayyana,akwai 'yar
tazara tsakaninsu kadan,ya juya ya dubi sa'idan
"Wuce kafin tazo ta fara miki jajayen idanuwa" maganar ta baiwa sa'ida dariya har
sai data qyalqyale da dariya sannan ta soma takawa don wucewa ciki
"Wato kin dawo shine kika samu waje kika tsaya kina masa wannan dan banzan surutun
naki ko?"kai ta gyada
" a'ah ummi,nima fa yanzu na shigo"harararta tayi cikin ranta tana qissima lallai
ya zama dole ta kwabi sa'ida,donta fuskanci kanta yana rawa tanason ta lalata mata
plan
"Wuce,saura kuma naga qafarki a wajen" da hanzari sa'idan ta wuce,anty usaina ta
bita da kallo harsai data shige sannan ta dauke idanunta,dai dai sanda anwar yake
tsaye daga inda yake,a nutse yana karantar duk wani motsi na anty usaina,murmushi
ya kubce masa,ya gama ganeta tsaf,ya gama karantar tsoronta,ya kuma gane me take
boye masa,saidai baisan nata shirin ba,koma meye nata shirin shi zai mata ba zatan
da bata tsammata ba,idonta ta sauke a kanshi,tana tsaye har ya isketa
"Yaushe kai kuma ka dawo?,daga wuni daya sai kwana har biyu?"
"Tun jiya na dawo,wasu sabgogi ne suka riqeni,duk yadda naso in shigo baiyiwu ba"
bata ce komai ba ta bude qofar falon ta shiga yabi bayanta.

Bayan sun gama gaisawa suka shiga hirar mutanen garin daya baro ya gaya mata
kowa lafiya sannan yace
"Kin tambayeni lafiya na tashi zuwa katsina ba yadda na saba ba" ya fada yana duban
anty usainan dake yankan farcenta
"Eh ai dole,koma waye daya sanka yadda kaqi jinin zuwa katsina dole yayi mamakin
tafiyar taka"
"Neman aure naje,na nema kuma sun bani" saita dakata da abinda take tana kallonshi
sosai,saidai bata ga alamun wasa tattare dashi ba,hakan ya sanya ta gyara zamanta
"Auren wa kuma anwar"
"Shahida" ya fada kai tsaye kuma a taqaice,wani abu taji ya tsarga mata gaba daya
ilahirin jikinta,saita aje rezar gefanta ta zauna sosai tana kallon anwar,tana jin
wani farinciki na ratsata,da gaske ko mafarki take,shahidan da take tayi masa
farautarta?,sun shirya kansu ne koko yaya abun ya faru?abinda ya shiga tsakaninsun
dama baiyi girman da zasu kasa daidaita tsakaninsu ba amma har ya zama silar
rabuwarsu na tsahon shekaru?,ya zama silar lalacewar soyayyar da kowa yake
sha'awa,duka cikin lokaci kadan ya karanci tarin tambayoyin dake yawo a
idanunta,qaramin murmushi yayi yana jin wani ciwo cikin ranshi,inama ace yadda kowa
ya kalli lamarin hakan yake
"Karki damu anty,na rage miki aikin da kiketa yunqurin yine" ya qarasa fada yana
son ganin yanayin fuskarta,ajiyar zuciya ta sauke ta zauna sosai zaman dake nuna ta
soma samun nutsuwa
"Zuciyata ta kasa karbar rabuwarka da ita ne anwar,inaji a jikina bai cancanci ku
rabu ba"
"Shikenan ai....yanzu dai anty abinda nakeso kici gaba da zama a yadda ta sanki har
zuwa lokacin da komai zai daidaita" sai yanayin fuskarta ya sauya
"Komai zai daidaita kamar yaya?,kana nufin baku daidaita ba ka nemi aurenta a
haka?" Kai ya gyada mata
"Eh kusan hakanne"
"Me hakan ke nufi anwar?"
"Babu komai,kema hakan kikeso mu kasance tare fa?"
Eh...amma zanso ace hakan ta faru ne a lokacin da duk wani sabani dakw tsakaninku
ya zama babu shi"
"Karki damu anty" shuru tayi tana nazari,yayin da zuciyarta taji ta mata sanyi
sosao,ta dinga jin farinciki na shigarta,tana ji babu shakka abune mawuyaci anwar
ya samu soyayya irinta shahidan,abune mai wahalar gaske yaso wata kwatankwacin nata
son koda shi yana qaryata hakan tasan wani dalili ne nashi na daban daya rufe masa
idanu har yake qaryata hakan
"Nafisa fa?" Ta sako mishi zancan da take ganin kamar ya manta ne
"Ba abinda ya sauya tsakanina da ita"
"Tasan da wannan maganar?"
"Zata sani anty,zata sani idan lokacin daya dace ta sani yayi"
"Shikenan,Allah ya shige gaba ya kauda dukkan abunqi"mai makon ya amsa saiya soko
wani zancan
"cikin satin nan ne tafiyata,ina ganin ki lissafa duk abinda kuke da buqata don
bazan dawo ba saina gama wata biyun gaba daya,aiki ne mai muhimmanci a gabana"
"Babu wata matsala,don bana tunanin zamu buqaci komai harka dawo din"

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Ranar juma'a qarfe biyu na rana suma gama shirin tafiya katsina,ga mamakinta sai
uncle hisham ya hadasu ita da haidar da faruqu,ganin haka huda itama ta turje saita
je,hakan yasa ta hada kayanta duka suka bar gidan sai anty zubaida kawai.

Tafiyar tayi mata dadi sosai saboda su faruq,har Allah Allah ta dinga yi su
isa,basu jima sosai saman hanya ba suka isa katsina.

Sosai daada tayi farincikin ganinsu su duka,ta rasa inda zata


sanyasu,kowannensu haba haba takeyi dashi,saida suka ci suka sha suka nutsu qarfe
uku na yammaci,a lokacin su faruqu sun fita kewaya 'yan uwa dake nesa,shahida tace
ta gaji ba zata iya fita ba sai gobe,jin haka yasanya huda itama cewa bazata
bisu,nan tayi kwanciyarta saman cinyar daada suna hira abinsu.

Duban shahida daadan tayi bayan ta maida nutsuwarta sosai


"Rahama" ta kirayi ainihin sunanta,saita daga kai daga danna wayar da take ta dubi
daada
"Yau kuma sunan nawa kike sha'awar kira" maimakon ta maida mata yadda suka saba sai
tace
"Maida hankalinki jikinki ki aje wannan wayar" jin hakan yasa ta sauke wayar saman
cinyarta tana kallon daadan
"Abinda yasa nace a turomin ke,inason gaya miki cewa mun bada ke kuma mun karbi
kudin aurenki"

*KIYI SUBSCRIBING,KI TURA WANNAN NUMBER DON SAMUN DAMAR SHIGA GROUP DIN SABON
LITTAFINA DA ZAN SOMA RUBUTAWA BAYAN ALQAWARIN ALLAH IN SHA ALLAH*
07038670166

SAUTIN HIKIMA

https://youtu.be/H7M7h6l6wNMhttps://youtu.be/_XVqJSBXVPI

2️⃣ 9️⃣
*Alqawarin Allah*
2️⃣9️⃣

Da hanzari ta koma jikin wayarta ta cirota,ta koma gefan gado ta rubuta saqo ta
tura masa,saita kashe wayar don ta tabbatar ta barta akunne nuradden bazai barta
tayi barci ba,tunda damar da yake nema kenan gashi ya samu.

Washegari tana kunna wayartata kuwa kiransa ne abu na farko daya soma
shigowa,yadda taji muryarshi ya kasa zaune ya kasa tsaye kaman ance masa an bashi
ita dinne,tun a ranar suka shirya yadda tafiyar zata kaya,ya nemi su tafi tare tace
sam,ya sameta kawai a can ran alhamis din,murmushi ya saka mai sauti
"Bakison hawa motata kwata kwata shahida,don know why....koda yake babu komai saura
qiris in sha Allahu,Allah yakai damo ga harawa dai" murmushi kawai ta saki tana
yanke kiran,bazai gane bane,baisan irin illa tabo da masifar da shiga motar wani ta
sabbabawa rayuwarta bane,tabon da har yanzu bata daina jin dacinsa ba yana zaga
jiki da rayuwarta gaba daya.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe sha biyu da minti arba'in da biyar tayi sallama falon daada,hasina 'yar
gidan qanin abbanta ce zaune ta daga kai cikin mamaki da farinciki ta amsa sallamar
"Mutan kano,yau a gari?,ni har nayi fushi fa,wai shahida kizo har garin nan kwanaki
amma ki kasa leqani,gaba daya kin watsar dani kaman wadda ta miki wani mugun
laifi?" Murmushi shahida tayi tana zama kan daya daga cikin kujerun gami da cire
mayafinta ta aje gefe,iskar fankar da aka qurewa gudu cikin falon tana kadata gami
da shigarta tako ina sakamakon zafin da ake zabgawa da kuma uwar rana
"Kiyi haquri hasina,ba'a son raina ba wallahi,wannan tsohuwr ce ta min laifin daya
shafeku,amma kiyi haquri zanzo in sha Allahu" cikin murmushi hasina ta tabe baki
"Kedai bansan me ya dameki ba,koda yake an auna arziqi da aka samu ma kika ci gaba
da zuwa katsinar da kika yiwa yajin aiki wajen shekaru hudu" murmushin da baikai
har zuci ba shahida tayi tana cire agogon hannunta
"Yanzun ma mawuyacine idan ban koma muku yajin aikin ba ai" ta qarshe fada wani abu
na takore mata wuya idan ta tuna kasassabar dasu daada suka aikata mata,saidai
takanji sassauci idan ta tuna tana da hope a yau,qasa qasa da murya hasina tayi
"Hala ta kusa kwatanta miki abinda taso yimin kenan?" Kallonta shahida take ba
tare da tace komai ba tana son jin qarin bayani
"Wai in gaya miki matarnan daga zuwa mata hutu shikenan tasa aka mata kiran
saurayina qafa da qafa wai ya kamata ya fito hakanan,wannan shekarar ta shirya
aurar da jikokinta,wai basai ya dorawa kanshi wata dawainiya ba yayi abinda addini
kawai yace masa ya wadatar Allah ya sawa auren albarka" tagumi da haba shahida tayi
kawai tana jin wannan bayanin,ita kenan ta mata dakyau ma data amshi kudin
aure,amma gwara hasina da ita sau dubu
"Hasina kukan dadi kike,kinsan me daada tayimin?" Kai ta girgixa tana duban shahida
"Kudin aurena da sadakina suka amsa gaba daya ba tare da na sani ba,kuma ba tare da
nasan waye zan aura din ba,kawai don bincikensu ya basu managarcine suke ganin ya
dace dani" idanu waje hasina ta fito dasu tana duban shahida,kafin tace wani abu
suka jiyo maganar daada daga tsakar gida wadda ta fito da wanka ne tana fadin
"Da kika shigo kika bar akwatin naki rana na duka waye zai dauke miki" dole kowanne
yaja bakinsa yayi shuru harta iso falon,saita kalli idanunsu na 'yan sakanni kana
ta tabe baki
"Magulmatan banza da wofi" daga haka tayi wucewarta daki donta saka kaya,yayin da
shahida cikin dacin rai da baqincikin daya taso mata ta fito tsakar gida ta shiga
bandaki tayi fitsari sannan ta daura alwala nan bakin famfo ta shigo da akwatin
nata.

Qarfe daya da minti ashirin na rana tana tashi daga saman abun sallarta
wayarta ta dauki tsuwwa,hasina ta miqo mata ta duba,nuradden ke kira ko bai fada ba
tasan ya iso ne,gabanta taji yayi mummunar faduwa ta daga idanunta ta kalli daada
data qarawa fura da nono ruwa take sha,saita kalli hasina,suka hada idanu ta mata
signa sannan ta fita tsakar gida,ba jimawa ta biyo bayanta,janta tayi bakin kitchen
ta gaya mata abinda ke faruwa
"Tabdi,kina tunanin akwai abinda zai sauya dada?,amma arashin tayi aka

n bar arha,bari na gaya mata baqo zai shigo" ta juya tana komawa,kafin takai ga
shiga falon yaro ya tamfatsa sallama yana rangada fadin wai ana sallama da
shahida,daada dake zaune a rumfarta tayi katsu tana jiran taji wanda zaiyi magana
cikinsu,shuru sukayi ba wadda ta amsa,sai daadan ta kira yaron ya qaraso bakin
rumfar
"Waye yake sallama da ita?"
"Wani ne,wai nuradden daga kano"
"Kano?" Ta sake tambayar yaron,saiya kada kai alamun eh,shuru na sakanni sannan
tace
"Jeka ce masa ya shigo" juyawa yaron yayi ya fice ita kuma ta kira shahida da
hasina gaba daya
"Xauna nan" ta nunawa shahida gefanta,ba musu ta zauna jiki a sanyaye,ta dubi
hasina
"Bude firinjin can ki ciro ruwa da lemo" ba musu hasinar tayi yadda tace,dada ta
nuna mata shimfidar daddumar data gama salla akai bata kai ga daukewa ba tace ta
dora saman nan.

Cikin minti biyu kacal nuradden ya bayyana cikin falon,yaci manyan kaya
yanata qamshi,bashi kadai bane shida wani abokinsa ko kuma ince amininsa ne,duk da
dan uwanshi ne,cikin girmamawa suka zauna saman shimfidar suna gaida daada,ta amsa
musu kadaran kadaham,yayin da idanun nuradden ke kan shahida.

Tayin ruwa da lemon tayi musu,Sayyid abokinsa ya bude ya zuzzuba musu a


kofi,kusan shi kadai yasha,yana sha suna dan taba jira jifa jifa da daada tana
tambayarshi kano,kasancewar ta dauki shekaru masu dama rabonta da ita,tun kafin
rasuwar babansu shahida.

Sai da suka kammala tasa hasina ta zuba musu abinci,saidai sunce a qoshe
suke,tilas ta rufe ta maida kitchen din,shuru ne ya ratsa na dan wani lokaci sannan
sayyid yace
"Am...daada,abinda yake tafe damu dama magana ce game da shahida da kuma abokina
nura,duk da nasan bata sanar miki da zuwanmu ba"
"Haka yake" a nutse sayyid ya fayyacewa daada komai,tayi gyaran murya tana dubansu
"Nasan cewa kuna da labarin an bada shahidan harma an karbi sadakinta,idan ma ta
boye maka bata gaya maka ba ni ya zama wajibi na gaya maka gaskiyar abinda ake
ciki"
"Ta fadama bata boye ba daada"
"Yauwa...an riga da an karbi sadakin yaron,kuma a shekarun da Allah ya bamu bai
kamata kuma ace muna magana biyu ba,uwa uba sanin kanka ne cewa haramunne neman
aure akan nema,koda ciniki akan ciniki ne haramun ne bare nema kan nema,matar mutum
kabarinsa,Allah ya qaddari haka tun farko shi yasa ya hukunta jinkirin zuwanka
garemu,saboda haka ina mai yaba maka bisa soyayyar daka nunawa jininmu,ina kuma mai
maka fatan samun dacewa da wata matar data fita,sannan ina mai dorawa da baka
haquri,kayi haquri,Allah ya sawa zuciyarka dangana" sayyid ne kawai ke amsawa da
amin,yayin da gaba daya jikin nuradden ya mutu murus,zufa ta dinga yanko masa tako
ina
"Mun gode sosai da karamcin da akayi mana" sayyid ya fada sanda suke miqewa bayan
sun ajewa daada kudi
"A'ah yaro...nifa bazan karba ba,zoka dauka ku wuce Allah yayi maka zabi mafi
alkhairi" qememe suka qi dauka haka suka fice,daada ta juya ta kalli shahida dake
zaune gefanta tana sharbar qwalla
"Saikije ki sallamesu" daga haka ta miqe ta tayi wucewarta daki,sanda ta cimma
qofar gidan tuni su nuradden sun wuce,sai tex daya turo mata na anjima zai kirata
don yanzu baida nutsuwar tsaiwa,sulalewa tayi ta zauna gefan gadon,tana qoqarin
hadiye kukanta.

Shigowar daada dakin ya sanyata daga kai tana kallonta,tana daga tsaye ta
soma magana
"Kin kyauta sosai da kika sanyashi yazo kika toxarta mu,daa can kinsan yana sonki
baki bashi dama ba har saida muka yanke hukunci a kanki?,ko kina tsammanin mu
warware maganar da mukayi kaman qananun mutane?,to idan ma zaki kwantar da
hankalinki ki nutsu waje guda shiya fiye miki alkhairi,ki shirya kuma ki dakaci
zuwan gobe,mijinki da yardar Allah zaizo kuga juna,idan kinga dama kuma idan yazo
din ki watsa mana qasa a idanu" daga haka daadan ta juya tayi ficewarta,sai kawai
shahidan ta bita da kallo ranta na quntata,koma meye shi ya janyo mata,kuma shima
saiyaji a jikinsa da zuciyarsa yadda ya janyo mata bacin rai tsakar rana ba tare
data shiryawa hakan ba.

***** ****** ****** *****

Tunda ta tashi washegarin take kwance abinta kamar ruwa taqi yin komai,saidai
daga nan ta koma can,ha

sina tayi tayi ta tashi tayi wani abun ko taji qwarin jikinta amma ta qeqashe
qasa,ko kallo bata ishi daada ba sangar gabanta kawai take,tana daga kwancen tana
kallon daada,yadda ta cika fridge dinta da fura da nono mai kyau,lemuka da kuma
ruwa,tasa hasina tayi total na kayan fulawa aka siyo komai hasina tayi dan dai dai
aka adana komai,baki ta tabe ta dauke kai bacin rai na cinta sanda daada ta fito da
sabuwar daddumarta da kawu ummaru ya bata sanda ya dawo daga umara ya fesheta da
turare ta baiwa hasina taje ta shimfida a dakin soro.

Saida komai ya kammala hasina ta isketa kwance cikin kujera tana saqa da
warwara ta zauna gefanta
"Ya kamata ki tashi ko ruwa ko watsa kyaji dadin jikinki?" Idanunta da suka sake
girma saboda kwana biyu data yi bata saka musu kwalli ba ta watsawa hasina cikin
salon tambaya
"Me kikeson cewa?,kice kawai na tashi na yi masa kwalliya saboda zaizo,mutuncina ya
qara zuba a idanunsa ko?" Murmushi hasina ta saki tana kada kai
"Niba haka nake nufi ba,kawai nasan yadda kikeson wanka wuni guda kuma ace tun safe
ga azahar ta shiga baki watsa ruwa ba bare kici wani abun ai babu dadi,a qalla
kodon tsaftar jikinki ko?" Saita maida kanta ta kwantar gami da rufe ido sannan ta
amsa mata
"Share kawai" dubanta hasinan tayi na wasu mintunan sannan ta miqe tana cewa
"Allah ya kyauta,ya kamata dai ki sawa ranki salama,tunda kinsan cewa aikin gama ya
gama,kada madai azo gaba kina jin kunya yazo kiga ya miki ki kamu da sonshi,kinsan
wallahi daada ba raga miki zatayi ba"da sauri ta sake bude idon ta dubi hasina
"So,bakisan nayi bikin binneshi ba?" Dariya ta qwacewa hasina ta kama baki tana
kallonta
"Shi kuma wannan da kika kawo fa?,mutunci kuke kenan?"
"Nuradden?..inason in rama halaccin da yayi minne shekaru kusan hudu"
"Tabdi,kice gwara da Allah yasa daada ta zaba miki miji,ashema ba soyayya kuke ba
kenan" kofin dake gefanta shahida ta wafto ta jefi hasina dashi Allah yasa ta kauce
bai sameta ba,har ga Allah taso ta sametan don bata da bakinma ce mata ta fita
saboda wani abu dake takore da wuyanta
"Na rantse da Allah na tashi hasina saidai daada ta fiddaki daga gidan nan" cikin
dariya ta fice tana cewa
"A'ah,a'ah,bani nakar zomon ba,ratayarma kuma ba'a bani ba".

Qarfe uku na rana da 'yan mintina daada ta shigo ta sameta


"Tashi kiyi wanka ko yanzu nasa akaimin ke bandaki na sabeki" ta furta tana nuna da
gaske take,saida ta gama taurin kanta ganin da gaske daadan take sannan ta shiga
bandaki tayi wankan.

Sanda ta fito mai kawai ta shafa sai turarenta oily data gogawa fatarta,tasaka
wasu riga da skert na atamfa ta zura dogon hijabinta daya sauka har saman qafafunta
ta soma da nafila kafin ta gabatar da farillar sallar la'asar.

sanda ta kammala saman abun sallar ta zauna tana jan hasbunallahu wani'imal
wakil,saboda faduwar da gabanta yaketa yi wanda batasan dalili ba.

👑*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina
da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

2️⃣ 9️⃣
*Alqawarin Allah*
2️⃣9️⃣

Da hanzari ta koma jikin wayarta ta cirota,ta koma gefan gado ta rubuta saqo ta
tura masa,saita kashe wayar don ta tabbatar ta barta akunne nuradden bazai barta
tayi barci ba,tunda damar da yake nema kenan gashi ya samu.

Washegari tana kunna wayartata kuwa kiransa ne abu na farko daya soma
shigowa,yadda taji muryarshi ya kasa zaune ya kasa tsaye kaman ance masa an bashi
ita dinne,tun a ranar suka shirya yadda tafiyar zata kaya,ya nemi su tafi tare tace
sam,ya sameta kawai a can ran alhamis din,murmushi ya saka mai sauti
"Bakison hawa motata kwata kwata shahida,don know why....koda yake babu komai saura
qiris in sha Allahu,Allah yakai damo ga harawa dai" murmushi kawai ta saki tana
yanke kiran,bazai gane bane,baisan irin illa tabo da masifar da shiga motar wani ta
sabbabawa rayuwarta bane,tabon da har yanzu bata daina jin dacinsa ba yana zaga
jiki da rayuwarta gaba daya.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe sha biyu da minti arba'in da biyar tayi sallama falon daada,hasina 'yar
gidan qanin abbanta ce zaune ta daga kai cikin mamaki da farinciki ta amsa sallamar
"Mutan kano,yau a gari?,ni har nayi fushi fa,wai shahida kizo har garin nan kwanaki
amma ki kasa leqani,gaba daya kin watsar dani kaman wadda ta miki wani mugun
laifi?" Murmushi shahida tayi tana zama kan daya daga cikin kujerun gami da cire
mayafinta ta aje gefe,iskar fankar da aka qurewa gudu cikin falon tana kadata gami
da shigarta tako ina sakamakon zafin da ake zabgawa da kuma uwar rana
"Kiyi haquri hasina,ba'a son raina ba wallahi,wannan tsohuwr ce ta min laifin daya
shafeku,amma kiyi haquri zanzo in sha Allahu" cikin murmushi hasina ta tabe baki
"Kedai bansan me ya dameki ba,koda yake an auna arziqi da aka samu ma kika ci gaba
da zuwa katsinar da kika yiwa yajin aiki wajen shekaru hudu" murmushin da baikai
har zuci ba shahida tayi tana cire agogon hannunta
"Yanzun ma mawuyacine idan ban koma muku yajin aikin ba ai" ta qarshe fada wani abu
na takore mata wuya idan ta tuna kasassabar dasu daada suka aikata mata,saidai
takanji sassauci idan ta tuna tana da hope a yau,qasa qasa da murya hasina tayi
"Hala ta kusa kwatanta miki abinda taso yimin kenan?" Kallonta shahida take ba
tare da tace komai ba tana son jin qarin bayani
"Wai in gaya miki matarnan daga zuwa mata hutu shikenan tasa aka mata kiran
saurayina qafa da qafa wai ya kamata ya fito hakanan,wannan shekarar ta shirya
aurar da jikokinta,wai basai ya dorawa kanshi wata dawainiya ba yayi abinda addini
kawai yace masa ya wadatar Allah ya sawa auren albarka" tagumi da haba shahida tayi
kawai tana jin wannan bayanin,ita kenan ta mata dakyau ma data amshi kudin
aure,amma gwara hasina da ita sau dubu
"Hasina kukan dadi kike,kinsan me daada tayimin?" Kai ta girgixa tana duban shahida
"Kudin aurena da sadakina suka amsa gaba daya ba tare da na sani ba,kuma ba tare da
nasan waye zan aura din ba,kawai don bincikensu ya basu managarcine suke ganin ya
dace dani" idanu waje hasina ta fito dasu tana duban shahida,kafin tace wani abu
suka jiyo maganar daada daga tsakar gida wadda ta fito da wanka ne tana fadin
"Da kika shigo kika bar akwatin naki rana na duka waye zai dauke miki" dole kowanne
yaja bakinsa yayi shuru harta iso falon,saita kalli idanunsu na 'yan sakanni kana
ta tabe baki
"Magulmatan banza da wofi" daga haka tayi wucewarta daki donta saka kaya,yayin da
shahida cikin dacin rai da baqincikin daya taso mata ta fito tsakar gida ta shiga
bandaki tayi fitsari sannan ta daura alwala nan bakin famfo ta shigo da akwatin
nata.

Qarfe daya da minti ashirin na rana tana tashi daga saman abun sallarta
wayarta ta dauki tsuwwa,hasina ta miqo mata ta duba,nuradden ke kira ko bai fada ba
tasan ya iso ne,gabanta taji yayi mummunar faduwa ta daga idanunta ta kalli daada
data qarawa fura da nono ruwa take sha,saita kalli hasina,suka hada idanu ta mata
signa sannan ta fita tsakar gida,ba jimawa ta biyo bayanta,janta tayi bakin kitchen
ta gaya mata abinda ke faruwa
"Tabdi,kina tunanin akwai abinda zai sauya dada?,amma arashin tayi akan bar
arha,bari na gaya mata baqo zai shigo" ta juya tana komawa,kafin takai ga shiga
falon yaro ya tamfatsa sallama yana rangada fadin wai ana sallama da shahida,daada
dake zaune a rumfarta tayi katsu tana jiran taji wanda zaiyi magana cikinsu,shuru
sukayi ba wadda ta amsa,sai daadan ta kira yaron ya qaraso bakin rumfar
"Waye yake sallama da ita?"
"Wani ne,wai nuradden daga kano"
"Kano?" Ta sake tambayar yaron,saiya kada kai alamun eh,shuru na sakanni sannan
tace
"Jeka ce masa ya shigo" juyawa yaron yayi ya fice ita kuma ta kira shahida da
hasina gaba daya
"Xauna nan" ta nunawa shahida gefanta,ba musu ta zauna jiki a sanyaye,ta dubi
hasina
"Bude firinjin can ki ciro ruwa da lemo" ba musu hasinar tayi yadda tace,dada ta
nuna mata shimfidar daddumar data gama salla akai bata kai ga daukewa ba tace ta
dora saman nan.

Cikin minti biyu kacal nuradden ya bayyana cikin falon,yaci manyan kaya
yanata qamshi,bashi kadai bane shida wani abokinsa ko kuma ince amininsa ne,duk da
dan uwanshi ne,cikin girmamawa suka zauna saman shimfidar suna gaida daada,ta amsa
musu kadaran kadaham,yayin da idanun nuradden ke kan shahida.

Tayin ruwa da lemon tayi musu,Sayyid abokinsa ya bude ya zuzzuba musu a


kofi,kusan shi kadai yasha,yana sha suna dan taba jira jifa jifa da daada tana
tambayarshi kano,kasancewar ta dauki shekaru masu dama rabonta da ita,tun kafin
rasuwar babansu shahida.

Sai da suka kammala tasa hasina ta zuba musu abinci,saidai sunce a qoshe
suke,tilas ta rufe ta maida kitchen din,shuru ne ya ratsa na dan wani lokaci sannan
sayyid yace
"Am...daada,abinda yake tafe damu dama magana ce game da shahida da kuma abokina
nura,duk da nasan bata sanar miki da zuwanmu ba"
"Haka yake" a nutse sayyid ya fayyacewa daada komai,tayi gyaran murya tana dubansu
"Nasan cewa kuna da labarin an bada shahidan harma an karbi sadakinta,idan ma ta
boye maka bata gaya maka ba ni ya zama wajibi na gaya maka gaskiyar abinda ake
ciki"
"Ta fadama bata boye ba daada"
"Yauwa...an riga da an karbi sadakin yaron,kuma a shekarun da Allah ya bamu bai
kamata kuma ace muna magana biyu ba,uwa uba sanin kanka ne cewa haramunne neman
aure akan nema,koda ciniki akan ciniki ne haramun ne bare nema kan nema,matar mutum
kabarinsa,Allah ya qaddari haka tun farko shi yasa ya hukunta jinkirin zuwanka
garemu,saboda haka ina mai yaba maka bisa soyayyar daka nunawa jininmu,ina kuma mai
maka fatan samun dacewa da wata matar data fita,sannan ina mai dorawa da baka
haquri,kayi haquri,Allah ya sawa zuciyarka dangana" sayyid ne kawai ke amsawa da
amin,yayin da gaba daya jikin nuradden ya mutu murus,zufa ta dinga yanko masa tako
ina
"Mun gode sosai da karamcin da akayi mana" sayyid ya fada sanda suke miqewa bayan
sun ajewa daada kudi
"A'ah yaro...nifa bazan karba ba,zoka dauka ku wuce Allah yayi maka zabi mafi
alkhairi" qememe suka qi dauka haka suka fice,daada ta juya ta kalli shahida dake
zaune gefanta tana sharbar qwalla
"Saikije ki sallamesu" daga haka ta miqe ta tayi wucewarta daki,sanda ta cimma
qofar gidan tuni su nuradden sun wuce,sai tex daya turo mata na anjima zai kirata
don yanzu baida nutsuwar tsaiwa,sulalewa tayi ta zauna gefan gadon,tana qoqarin
hadiye kukanta.

Shigowar daada dakin ya sanyata daga kai tana kallonta,tana daga tsaye ta soma
magana
"Kin kyauta sosai da kika sanyashi yazo kika toxarta mu,daa can kinsan yana sonki
baki bashi dama ba har saida muka yanke hukunci a kanki?,ko kina tsammanin mu
warware maganar da mukayi kaman qananun mutane?,to idan ma zaki kwantar da
hankalinki ki nutsu waje guda shiya fiye miki alkhairi,ki shirya kuma ki dakaci
zuwan gobe,mijinki da yardar Allah zaizo kuga juna,idan kinga dama kuma idan yazo
din ki watsa mana qasa a idanu" daga haka daadan ta juya tayi ficewarta,sai kawai
shahidan ta bita da kallo ranta na quntata,koma meye shi ya janyo mata,kuma shima
saiyaji a jikinsa da zuciyarsa yadda ya janyo mata bacin rai tsakar rana ba tare
data shiryawa hakan ba.

***** ****** ****** *****

Tunda ta tashi washegarin take kwance abinta kamar ruwa taqi yin komai,saidai
daga nan ta koma can,hasina tayi tayi ta tashi tayi wani abun ko taji qwarin
jikinta amma ta qeqashe qasa,ko kallo bata ishi daada ba sangar gabanta kawai
take,tana daga kwancen tana kallon daada,yadda ta cika fridge dinta da fura da nono
mai kyau,lemuka da kuma ruwa,tasa hasina tayi total na kayan fulawa aka siyo komai
hasina tayi dan dai dai aka adana komai,baki ta tabe ta dauke kai bacin rai na
cinta sanda daada ta fito da sabuwar daddumarta da kawu ummaru ya bata sanda ya
dawo daga umara ya fesheta da turare ta baiwa hasina taje ta shimfida a dakin soro.

Saida komai ya kammala hasina ta isketa kwance cikin kujera tana saqa da
warwara ta zauna gefanta
"Ya kamata ki tashi ko ruwa ko watsa kyaji dadin jikinki?" Idanunta da suka sake
girma saboda kwana biyu data yi bata saka musu kwalli ba ta watsawa hasina cikin
salon tambaya
"Me kikeson cewa?,kice kawai na tashi na yi masa kwalliya saboda zaizo,mutuncina ya
qara zuba a idanunsa ko?" Murmushi hasina ta saki tana kada kai
"Niba haka nake nufi ba,kawai nasan yadda kikeson wanka wuni guda kuma ace tun safe
ga azahar ta shiga baki watsa ruwa ba bare kici wani abun ai babu dadi,a qalla
kodon tsaftar jikinki ko?" Saita maida kanta ta kwantar gami da rufe ido sannan ta
amsa mata
"Share kawai" dubanta hasinan tayi na wasu mintunan sannan ta miqe tana cewa
"Allah ya kyauta,ya kamata dai ki sawa ranki salama,tunda kinsan cewa aikin gama ya
gama,kada madai azo gaba kina jin kunya yazo kiga ya miki ki kamu da sonshi,kinsan
wallahi daada ba raga miki zatayi ba"da sauri ta sake bude idon ta dubi hasina
"So,bakisan nayi bikin binneshi ba?" Dariya ta qwacewa hasina ta kama baki tana
kallonta
"Shi kuma wannan da kika kawo fa?,mutunci kuke kenan?"
"Nuradden?..inason in rama halaccin da yayi minne shekaru kusan hudu"
"Tabdi,kice gwara da Allah yasa daada ta zaba miki miji,ashema ba soyayya kuke ba
kenan" kofin dake gefanta shahida ta wafto ta jefi hasina dashi Allah yasa ta kauce
bai sameta ba,har ga Allah taso ta sametan don bata da bakinma ce mata ta fita
saboda wani abu dake takore da wuyanta
"Na rantse da Allah na tashi hasina saidai daada ta fiddaki daga gidan nan" cikin
dariya ta fice tana cewa
"A'ah,a'ah,bani nakar zomon ba,ratayarma kuma ba'a bani ba".

Qarfe uku na rana da 'yan mintina daada ta shigo ta sameta


"Tashi kiyi wanka ko yanzu nasa akaimin ke bandaki na sabeki" ta furta tana nuna da
gaske take,saida ta gama taurin kanta ganin da gaske daadan take sannan ta shiga
bandaki tayi wankan.

Sanda ta fito mai kawai ta shafa sai turarenta oily data gogawa fatarta,tasaka
wasu riga da skert na atamfa ta zura dogon hijabinta daya sauka har saman qafafunta
ta soma da nafila kafin ta gabatar da farillar sallar la'asar.

sanda ta kammala saman abun sallar ta zauna tana jan hasbunallahu wani'imal
wakil,saboda faduwar da gabanta yaketa yi wanda batasan dalili ba.

Shigowar hasina dakin ya sanyata daga kai tana dubanta


"Kamar fa baqonki ya iso,ta kamata ki sauya kaya ko powder ki samu ki shafa" harara
ta jefa mata,tana ganin bata amsa ma bata lokaci ne,saita dauke kanta taci gaba da
jan carbinta,dariya hasina tayi
"Kefa bai kamata kice auren dole za'a miki ba,keda zuciyarki babu kowa ciki bare
kice an mishi over taking?"ta qarashe maganar cikin salon tsokana,kasa amsa mata
tayi saboda muryar sulaiman data karade gidan yana shaidawa daadan isowar
baqon,idanunta ta lumshe tana sake maimaita hasbunallahu ba qaqqautawa,tana kallon
hasina ta juya ta fice.

Mintina aqalla goma kyawawa tana kasa kunne ko zata jiyo wani motsi ko wata
magana daga tsakar gida ko rumfar daada amma bataji komai ba,a haka aka share minti
goma tana zaune tana zaman jiran tsammani,jiran da bata da tabbas sai azabar
fargaba da faduwar gaba da suka mata rubdugu,daga labuken da akayi ya sanyata daga
kai tana duban na bakin qofar.

daada ce,tana daga tsaye riqe da labulen dakin tace


"Au,zaman me kike da kika bar mutane a daki su kadai?" Duban daada tayi qwalla na
cika idanunta,wani irin fargaba tana shigarta,saita sauke idanunta qwalla nason
xubowa ta miqe tsaye ta aje carbinta kawai tana gyara zaman hijabinta a jikinta
sanda daada ta saki labulen tayi komawarta rumfarta ta zauna.

Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka tazo ta ratsa falon,hasina da daada
suka bita da kallo,hasina baki bude ta dubi daada saboda ganin yadda shahidan zata
fita ba kwalliya babu komai sai zabgegen hijabi,qwafa dadan ta saka sannan tace
"Rabu da ita ja'iarar kawai shashasha" sarai ta jiyo dadan,haka ta dinga takawa har
zuwa dakin soron,ta saka hannu ta yaye labulen ta shiga.

Babu kowa cikin dakin sai kayan ciye ciyen dake jere a tsare,daga saman daya
daga cikin kujerun kuma hula ce mai azabar kyau da daukar ido da alama ta baqon
ce,to ina ya shiga?,shuru dakin sai uban qamshi daya cika dakin na turaren
baqon,wanda qamshin turaren yaso daukar hankalinta,saita samu hannun daya daga
cikin kujerun ta zauna tana qarewa dakin kallo da idanu kamar yau ta soma
ganinsa,ta dinga qoqarin rage faduwar gabar da takeji tana saisaita kanta da
nutsuwarta.

Kamar a mafarki kamar a wasa ta dinga jiyo murya kamar ta anwar tana doso
dakin,saita ware idanunta ta zubesu duka bakin qofar,yayin da zuciyarta ta soma
qara gudu daga gudun da take yi a dazu,a nutse ya yaye labulen yana sauke wayar
dake kunnenshi,cikin sakan daya idanunsu suka sarqafe cikin na juna,a nutse ya
janye nashi idanun tamkar ba ita ya gani ba,yayin da shahidan ta miqe zumbyr kamar
wadda aka tsikarawa wani abu idanunta dukka a waje saman fuskar anwar wanda ya
jingina bayanshi da bango daura da qofar fita,tafin qafarsa guda daya ya tokare
bangon da ita ta baya dayar kuma yana tsaye a kanta.

"Ki nutsu shahida ki fuskanci komai yadda ya kamata" shawarar farko da


zuciyarta ta soma bata kenan bayan qwaqwalwarta ta dawo daga aiki bayan daukewar da
tunaninta yayi na wucin gadi.

Shuru ya ratsa dakin na tsahon minti biyu tana jira taga shin anwar dinne da
kansa ko wani ya rako?,wajenta yazo ko batan kai yayi?
"Lafiya malam me kake a gidan mutane?" Idanunta a kansa fuskarta na nuna zallar
bacin rai
"Ina cewa kin fito ne don ki gana da wanda ya nemi aurenki?" Ya qarashe maganar da
sigar tambaya fuskarsa a dinke yana dage girarsa qwaya daya idanunshi cikin
nata,cikin tsananin razana da firgici ta fiddo duka idanunta waje.

_kuyi searching tashar SAUTIN HIKIMA dake youtube,daga qasanta zakuga an rubuta
subscribe da jan rubutu,ku danna sau daya zai koma black,sai kiyi screenshoot ku
turo zuwa number wayar da zata zo a qasa,za'a saku group na littafin da zan soma
bayan na kammala rubuta alqawarin Allah in sha Allahu_

07038670166https://youtu.be/H7M7h6l6wNM

*xafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki sharing,ga mai
buqatar siya zai tuntubi wadan nan numbers din*

07067124863

*ko kuma*

09032345899

*Alqawarin Allah*
3️⃣ 0️⃣
3️⃣0️⃣

"Kana nufin kaine mutumin daya kawo sadakina da mudin airena ba tare da sani ko
yardata ba?" Ta furta wani bala'i na cinta,maimakon ya bata amsa da baki saiya daga
mata dukka girarsa biyun yana dubanta kai tsaye ya kafeta da idanunshi,wani tashin
hankali taji ya rufto mata irin wanda bata taba jin irinsa ba tunda maganar aurenta
ta bullo,tashin hankali da ba'a saka masa rana,ko zata yarda da kowa ba zata yarda
da anwar ba,ko zata amince da auren kowa ba zata taba amincewa da auren anwar ba
koda su biyu kadai suka rage a duniyar,murmushin takaici ta saki wanda qasan
zuciyarta ji take kaman zata fashe
"Kaima kasan ka dauko abinda bazai taba yiwuwa ba har abada,tamkar wanda ya mutu ya
dawo ne,kai bakaji kunya ba anwar?,kana tunanin akwai abinda yayi saura?,kana
tsammani akwai wani sauran abinda ya rage tsakanina dakai?,to bari kaji na gaya
maka,ba zaka taba samun yardata ba,ba zaka sake samun soyayyata ba,har abada aure
tsakanina dakai,har abada...." Qawataccen murmushi ya saki,da alamun kwanciyar
hankali kwance kan fuskarshi,sai daya sauke qafarsa ya sauya jinginar da daya
sannan ya rungume hannunsa daya dayan kuma yana shafar sajensa idanunshi a
kanta,fara'ar fuskarshi ta bace bata
"Hajiya shahida....dukka tunaninki bai baki dai dai ba,baije inda ya kamata yaje
ba" sauke qafarsa yayi ya soma takowa inda take tsaye,sai daya rage tazarar dake
tsakaninsu sosai sannan ya tsaya ya soke hannayensa cikin aljihun rigarsa
"Kina tunani ko tsammanin soyayya ce tasa na nemi aurenki?,ko kina tunanin neman
yardarki nake kafin na aureki?"sai ya sake takowa gab da ita kamar zai hadeta da
jikinsa,ya nunata da yatsa
"Zan aureki don na nunawa wancan wawan cewa nidin na girmi qaramin dalili babban
dalili ne ni,sannan nayi isar da zan yanke guntuwar soyayyar da yake taqama da
ita,soyayyar da bai iyata ba,bai gama saninta bama bare ya iya,baisan kanta ba
baisan mece ita ba!" Ya qarasa fada yana dan daga muryarsa gami da nuna qofa da
yatsa kai kace nuradden ne ke tsaye a wajen,saiya sauke hannun nashi yana maidashi
aljihunsa kana yaja baya kadan har yanzu bai dauke idonsa daga kanta ba
"Yana tunanin ya sanki?,yana tunanin yafi kowa saninki koya riga kowa saninki?,ya
gayamin magana yayi tunanin yaci bulus?,inaso yaji ciwo ya kuma ci gaba da jin ciwo
a ransa duk sa'a daya da zata wuce da tunanin wani mai suna anwar ya haramta masa
auren wadda yake iqirarin yanaso,wadda yake iqirarin ba wanda ya isa ya shiga
tsakaninsu" yana kaiwa nan ya juya mata baya,yana jin kamar ana yankar zuciyarsa
"Baki cancanci na qyaleki kici gashin kanki ba,baki cancanci na barki kiyi zabin da
kikaga dama ba,bayan kin cutar da zuciyar da bata cancanci sakamakon da kika bata
ba,kin bata rayuwar da alokacin ya kamata ki tattaleta kodon iyaye da qannenki,kin
bada jikinki ga wani har yayi ajiya a wajen daba muhallin......" Saiya kasa
qarasawa saboda wani dunqulallen abu daya tokare masa maqoshi,ya dinga jin wani
turari tun daga zuciyarsa zuwa fuskarsa,bakinsa yaji ya dauki zafi ya fitar da iska
zazzafa,yana jin wani irin ciwo da qunci duk lokacin daya tuna da lokacin da kuma
abinda ya faru,hotunan dake wajensa da ganin da yayi kaya ido da ido sun kasa
gogewa daga qwaqwalwa da zuciyarsa,yana jin wani irin ciwo mara misaltuwa,tabbas da
yana da iko daya dawo da lokacin ya goge duk wani abu daya faru ko xai samawa
zuciyarsa salama.

Tuni hawaye ya soma wanke mata fuska tana tuna lokacin da abinda ya faru
alokacin daya bayan daya,sai a sannan ta dinga tuna kaman ta ganshi,kaman a
gabanshi aka sauketa,hakan na nufin ya ganta cikin maye?,ya ganta a lokacin da jini
kebin qafafunta?,yaga sanda aka cillo mata pant dinta da kwalabenta?,amma me yasa
ya zama mai qaramin tsinkaye?,mai yasa ya zama mai gajeran nazari?,me yasa ya yanke
mata wannan danyen hukunci farat daya,haka soyayya take?,haka masoyi yakewa
masoyinsa?,sai taji ya sake sireta,daya zama mai dogon nazari da dukka abubuwan da
suka faru yanzu basu faru ba
Ranta ya ninka bacin da yayi,hankalinta taji ya tashi,da qyar ta bude baki cikin
muryar kuka tace
"Mugu azzalumi,ba ruwanka da kowa sai kanka,ba ruwanka da damuwar wani sai taka,ka
tanadi mugun nufi akaina kan abinda baka da cikakkiyar hujja a kai...."
"Wacce huja nake nema baya ga wanda na samu....!" Ya juyo a fusace ya fada
idanunshi da suka kada zuwa jaa suna kanta
"Ba hujjar kake nema ba,kanayin komaine don ka wulaqantani dama,ka shirya komai ne
donka tozartani,to Allah ya fika,ba zaka taba samun nasara a kaina ba,nuradden kuma
idan Allah yaga dama kai baka isa ka rabani dashi ba"itama ta fada cikin tunzura
fushi da bacin rai
"kome zaki fada dai dai ne,duk yadda kika fassara lamarin a ranki ko a bakinki kisa
a ranki haka ne,any ways ma ni nasan na taimaki rayuwarki ne,ko kina tunanin wancan
wawan idan yaji wace ke a baya zaici gaba da haukan da yake a kanki?,kinga
'yammata....koki sawa ranki sauqi ko kar kisa duk uwar ubansu daya" kai take
gyadawa bacin rai na cinta,idanunta fes cikin nashi,ji take kaman ta shaqe anwar
din,a yanzu babu halittar data ji ta tsana sama dashi
"Zan saka salamar duk da bakayimin fatanta ko burin samunta,amma ka sani....tsugune
bata qare ba,don babu abinda zanyi da masoyi irinka nawar!,ka shirya tarbar duk
wani abu da zai tunkaroka!" Tayi lafazin da alama wani abu ya motsa ranta
qwarai,duk da murta na a raunane amma amma fuskarta da qwayar idanunta na bayyana
jarumtarta,wani malalacin murmushi ya saki ya sake matsowa inda take,wannan karon
har qamshin turarensan nan data sanshi dashi yana busowa zuwa hancinta,ya kafeta da
idanunsa,muryarsa can qasa kamar mai shirin furta kalaman soyayya a gareta yace
"A shirye nake,kece zan gayawa ki shirya zama dani idanma ba'a shirye kike
ba,yaushe kikeso wasan ya fara?" Ya fadi cikin halin ko in kula,ganin kallon da
yake mata bacin rai ya sanya ta fashewa da kuka sosai ta zube saman kujerar tana
rufe fuskarta da tafin hannunta,saiya tabe baki yana isa inda hularsa take yasa
hannu ya dauka yana cewa
"Ashe raguwa ce ta gaske,tun yanzu?,wasan namu kuwa zaiyi iri qarkon da nakeso?" Ya
dora hularshi saman kansa sanda ya qarashe maganar,saiya sanya hannunsa cikin
aljihunsa ya ciro kudade sabbabi masu dan yawa ya aje hannun kujerar da take kai
yana cewa
"Ga kudin zance nan,kuma bance a sayi abunda za'a bugu da kudina na,idan aka siya
Allah ya isa na" sosai maganar ta doketa,tana niyyar daga kai ta dubeshi ta
fuskanci ya juya zai fita ne,har yakai bakin qofa sai yasake cewa
"Ammmm..." Yana dawowa da baya,kanta yazo ya tsaya hannunsa daya a aljihun wandonsa
dayan kuma yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa
"Karki manta da sadakina akanki,shaidu kawai za'a tara a daura,ban lamince ki kula
kowanne dan iska ba,ciki harda wannan looser din,idan kuma kikayi hakan shima Allah
ya isa ban yafe ba" saiya sassauta murya ya sauko da kansa qasa qasa gab da ita
"Ina fata har yanzu wasu daga halayen anwar basu bace miki ba daga kanki,mutum ne
mai kishi,ina da kishi kan mace koba wadda ban biya sadakinta ba bare wadda na cire
halalina sa nasha wahalar nema zafi da sanyi nabiya" a fusace ta bude fuskarta
saboda yadda maganganunshi suka isheta,saita ganshi dab da fuskarta,cikin bacin rai
da muryar kuka take cewa
"Sadakinka din banza da wofi,idan kana son nunan kudinka wata tsiya ce kaje ka
karbi sadakinka idan har ka isa cikakken namiji" tsaf ya karanci bacin ran dake
kwance muraran saman fuskarta,saidai yadda yake jin quna yana tunanin bata jin
haka,duk sanda zai kalli fuskarta yana tuna sanda aka sauketa ne a gabanshi,cikin
maye,cikin jini,pant dinta a gabanshi aka cilloshi,wani ya riqe zuwa jikinsa gaban
idanunsa,saiya runtse idanunsa kana ya bata baya ya soma takawa
"Idan kin isa ke kije ki karbo kin kiga idan ban amsa ba,dama taimako nayi kuma na
fuskanci ke bakiga hakan ba" daga haka ya qarasa ficewa daga dakin,sake rushewa da
kuka tayi,ta tsani kalmar taimakon nan,wannan wanne irin cutace?,ita zai taimaka.

Cikin gida ya qarasa,daada na rumfarta a zaune ita da hasina,saiya cire


takalmansa ya zauna saman tabarmar dake shimfide qasan inuwar bishiyar dake tsakar
gidan,daadan tayi tayi dashi ya shigo amma yace wucewa zaiyi,dole ta fito ta zauna
daga gefan tabarmar itama
"Zan wuce daada,ina tunanin rana ita yau za'a kawo lefe,to bansan inda za'a kai
ba,can wajen umma,ko nan garin ko kuma gidan uncle hisham?"
"Babu damuwa akai can hidan hashimun tunda acan za'a yi duka bikin,muma can zamu
tattara ai mu tafi"
"To daada,Allah ya saka da alkhairi ya qara girma" ya furta yana dan sadda kanshi
qasa alamun girmamawa
"Ina kuma ta shiga?" Daada ta tambaya,ya fuskanci shahida take magana,saiya saki
murmushin daya qwata fuskarshi duk da baikai masa qasan ranshi ba
"Tana daki tana kukan bata sona can na barota" kama baki daada tayi tana salati
harta baiwa anwar dariya,harya miqe ya aje mata kudi ma sam bata kula ba tana ta
jajjabi tare da sillewa shahidan hasina na dariya,sai daya sanya takalmansa sannan
ya kalli hasina
"Taimaka kije ki fito da ita daga dakin karta rube" dariya hasina ta saki
sosai,abun saiya qayatar da ita,ya yiwa daada sallama suka fice zuwa soron gidan
shida hasina.

Bakin qofar dakin ya coge ya yaye labulen bayan hasina ta shiga dakin,ta isa
inda take dunqule tana gursheqen kuka
"Saikace yau akace za'a kaiki?,taso da Allah karki tara mana jama'a" hannun hasina
ta buge tana jin takaici yana cikata,duk maganganunsu da daada tana jinsa,tamkar ma
ya raina mata wayo ne,ko yana tunanin 'yar qaramar shahida daya sani a baya ce
wannan?
"Matsa hasina barta,bari na rage miki aikin na dauketa zuwa qofar soro saiki qarasa
shiga da ita ciki,da sauri ta bude fuskarta,idanunta da sukayi jawur zuwa fuskarta
ta kalleshi dasu
"wallahi wallahi ka sake ka tabani sai kayi dana sani!" Ta fada a kausashe
"Meye hakane shahida?" Hasina ta tambayeta tana dubanta cikin mamakin kausasa
lafazin da tayi,dubanta yake sosai,yana son yace shine farau?,amma idanun hasina
yasa ya maida amsarsa
"Wallahi wallahi kinji nima na rantse matsawar baki tashi kin shige ba ko abinda
yafi danasani zanyi saina dangana dake har rumfar daada" saiya maida dubansa ga
hasina dake tsaye tana kallon dramer
"Ina cikin mota a qofar gida,minti biyar na bata idan ta dara hakan bata tashi ba
ki fito ki gayamin" kai ta gyada ya saki labulen ya taka a sannu ya fice daga
soron.

Bata buqatar duk wani abu da zai kawo wani kusanci tsakaninta dashi,so take
ya tafi yabar gidan saboda haka ta miqe tana hada hanya,hasina ta dauki kudin dake
aje inda ta tashi ta bita dasu a baya,ko kallon dada dake tsakar gida tana mita
batayi ba ta shige rumfar daadan ta zube saman kujera,saita dora hannu aka ta fashe
da ihun kuka ko zataji salamar radadin da take ji cikin ranta,hasina kallonta take
idanu a waje cikin rudewa tace
"Meyw haka ne shahida kike kamar wata 'yar shekara goma,ya zaki tara mana jama'a?"
Takai qarshan maganar sanda daada ta runtumo cikin dakin tana tambayar ba'asi
"Au ihu kike?"
"Wallahi daada bana sonshi,shima daada ba sona yake ba bazai gaya muku gaskiya bane
kawai" baki ta tabe tana mata duban sakarya
"Au Allah ko?,ashe tun farkon saninmu dashi mu muka jajibo miki shi ko?,ashe
qiyayya ce ta hadaku a baya ba soyayya ba?"
"Daada baya sona yanzu bana sonshi!" Ta sake fada cikin kuka
"Eh naga alama,shi yasa bai bar kakarki ba yaci gaba dayi mata aike a boye bai bari
nasan wayeshi ba,kuma qiyayyar ce tasa ya tasl qafa da qafa ya nemi aurenki hannun
iyayenki"
"Wallahi daada kinji na ra ntse miki da manufa a lamarinsa"
"Dama akwai auren da babu manufa?,shirme kenan" ganin duka taqi fahimtarta saita
sauko gwiwoyinta qasa tana kallonta
"Daada,don girman Allah ku maida masa kudinsa,ko bazaku bani nuradden ba na amince
ko zabamin ko waye a lokacin da kuka saka na bikin nawa ayi dashi" nazarinta daadan
tayi na wani dan lokaci sannan ta kamata ta miqar da ita tsaye
"Naji,zauna muyi magana" sanyi taji yana ratsa zuciyarta,ta soma jin qamshin
nasara,saita miqe din kamar yadda daada ta buqata suka koma saman kujera suka
zauna.
Saidata bata 'yan mintuna ta nutsu tukunna sannan tace
"Komai da kika gani a rayuwa yana da dalili,inason ki gayamin dalilinki na duka
wadan nan maganganun da tsallen badaken qin auren mutumin da kowa ya shaida kuma
yana da labarin soyayyarku" shuru tayi kawai tana qiyasta ta yadda zata gayawa
daadan komai bayan basusan komai ba akan rayuwar data fada a baya,sannan uwa uba
shi kansa anwar din ta fahimci ba wanda ya taba gayawa ko bashi labarin komai,idan
ta aikata hakan kamar ta dabawa cikinta wuqa,kamar ta yaye mayafin asirin da Allah
ya rufa mata kenan?,ganin tayi shuru sai daada tayi tsammanin ko batason magana ne
a gaban hasina,saboda haka ta korata waje
"Ki gayamin dalilinki,indai matuqar na gamsu,toba shakka a yau basai gobe ba zamu
maida masa komai nashi" tofa ga qoshi ga kwanan yunwa,ta ina zata fara ya
zatayi?,batason tona komai,batason kowa yaji komai,tana ganin kamar ba muhallin
kowa bane ba hurumin kowa bane
Kai ta kada
"Daada baya sona ne,nima yanzu na daina sonshi,kinga babu amfanin aurenmu" murmushi
ta saki tana kada kai
"Banda abinki shahida ta yaya masoya haka siddan zasu daina son junansu?,ai ruwa
baya tsami banza" cikin nuna dagiya da qarfin hali tace
"Hakanan nidai daada muka daina son junanmu,don Allah karku qulla auren qiyayya"
hawaye ta siraro daga idanunta muryarta ta soma rawa,saita sake murmushi tana
kallonta
"Shahida,anyi auren hadin da baki taba ganinsa ba bai taba ganinki ba sai hadi kuma
an zauna lafiya harma yafi na soyayyar qarko,kin ganni nan gani da ran Allah?,to
sanda na auri kakanku sai randa ya shiga dakina nasan shi na aura,saboda haka indai
rashin soyayya ne hujjar fasa aurenki da anwar indai kikaga an fasa to la shakka
mutuwa nayi bana raye,ko bana raye zanbar wasiyyar a tabbatar an daura,don anwar
din ya cika dukkan siffa da kamalar da annabi yace a baiwa mutum aure" daga haka
sai daadan ta miqe ta qyaleta,tashin hankalin data ji a sannan yasa taji zuciyarta
ta bushe gaba daya,hawayen idanunta sun bushe tas,saita miqe itama ta shige daki
tayi rub da ciki tana sakin ajiyar zuciya ko zataji sanyin tuquqin da ranta yake.

Ta shafe a qalla minti talatin a haka kafin daga bisani ta janyo wayarta,ta
lalubo number nuradden ta kira,bugu daya tak ya daga,ajiyar zuciya ya soma saukewa
da alamu hankalinsa shima ba'a kwance yake ba,duk sai taji bacin rai ya sake
shigarta,shi ya janyo komai,shine silar komai
"Ka dawo ka sake neman aurena karo na biyu nuradden,bazan iya aurensa ba" ta fada
kai tsaye ba tare da tayi sallama ba ko tace komai,kafin taji yace wani abu taji an
karbe wayar,da sauri ta daga kai don ganin waye,daada ce,bata ce komai ba ta kara
wayar a kunnenta
"Nura kana jina?" Ta fadi sanda take ficewa daga dakin,saita miqe ta zauna sosai
saman katifar tana bin qofar da kallo.

*muna muku fatan alkhairi tare da fatan zaku gudanar da bukukuwan sallarku lafiya
cikin amincin ubangiji,Allah ya karba mana ibadunmu,ya gafarta mana zunubanmu,yaji
qanmu ya jiqan mamatanmu,yasa mu cikin 'yantattun bayinsa amin umma amin,ZAFAFA
BIYAR na muku fatan alkhairi*

*_karku manta,ku kasance da tashar SAUTIN HIKIMA TV don sauraren littattafan da


zasu debe muku kewa yayin ayyukan sallah a gida*

*kundin qaddarata*
*daurin boye*
*mutuncin mace*

Duka wadanda na rubuta


*fatan alkhairi a gareku*
#zafafa biyar
#sautin hikima tv
#team anwar
#team shahida
#team nafisa

_ma'assalam_🤝🏽🤝🏽🤝🏽_ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsaffin litattafanmu


dama sababbi da zamu fara dorawa nan gaba kadan in sha Allah_

https://youtu.be/H7M7h6l6wNM

3️⃣ 1️⃣
*Alqawarin Allah*
3️⃣1️⃣

Minti goma kyawawa daadan ta dawo,ta miqa mata wayartata tana dubanta,sannan ta
miqa mata kudin da anwar ya bata tana cewa
"Tunda kin zabi zubar mana da qima rahama mu zuba nida ke" daga haka ta juya ta
fice,a sannan ji shahidan take kamar ta dora hannu aka tayita zunduma ihu ko xata
ji sanyi cikin zuciyarta,me yasa ba zasu fahimceta su bata uzuri ba?,me yasa ba
zasu haqura ba?,wai da anwar da itama wa sukafiso ne?,waye nasu a ciki?,kira ne ya
sake shigowa wayarta,ta daga ta duba da sauri sai taga nuradden ne,muryarsa kadai
ta gaya mata cewa ya karaya bashi da wani sauran fata
"Shahida,na rasaki shahida,ta ina zan iya jurewa rashinki?,zan iya tsira daga
hukunci da horon rasaki da zuciyata zata yimin?,ki tayani addu'a bansan ya zata
kayamin ba" daga haka ya yanke kiran,me daada ta gayawa nuradden?,shikenan ta
rabata dashi?,dole ta zauna da mutumin da sam bata ra'ayinsa ne wai?,irin wannan
masoyin zata rabata dashi?,kalamansa kawai sun tabbatar da tsantsar qauna da
soyayyar da yake mata,saita kifa kawai rubda ciki tana lalube da binciken meye
abunyi a qwaqwalwarta,mecece mafita?duk wata dabararta ta qare,wayonta duka ya
qure,daada ta yanke komai.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe bakwai da rabi ne na daren ranar,yana zaune a harabar gidan saman daya
daga cikin fararen kujerun roba dake wajen,shi ya zabi zama a wajen saboda yadda
iskar damina mai sanyi ke busawa gabas da yamma,hakanan qwayayen lantarkin dake
harabar gidan sun haske ko ina harda korayen tsirran dake harabar wajen,sai yake
jin zuciyarsa wasai,hakanan babu nauyi qunci ko wani abu da yakejin ya dameshi a
yanzu,shaqar iskar yake sosai yana fesarwa har cikin huhunshi qamshin iskar da
sanyinta na sake sa zuciyarsa cikin wani shauqi da walwala,fuskarsa fes take a
washe.

A hankali take takowa cikin gayunta,tayi kyau don ba qaramar kwalliya ta


dauka ba,don yau din na daya daga cikin ranakunta na musamman,saboda bako da yaushe
take samun dama irin wannan ba,ace yau anwar din yazo zance takanas saboda ita,zata
iya irga sau nawa hakan ya taba faruwa a tarayyarsu,shi yasa duk ransa zaizo din ba
qaramin tanadi takewa ranar ba.

Gabansa ta tsaya sannan tayi sallama tana kallon yadda yayi masifar kyau cikin
qananun kaya sai kace wanda ya dawo daga europe,ya daga kai yana dubanta sannan ya
amsa,cikin shagwaba shigarsa da yadda yayi kyau yana dada burgeta tace
"Ya bakaci komai ba dear?" Ta qarashe fada tana jan kujerar dake kallonsa ta
zauna,duban tulin kayan ciye ciyen dake gabanshi yayi sannan ya kalleta,shi sam a
ra'ayinsa ba mutum bane mai yawan son ciye ciye,kusan ma babu cimarshi ciki sai
kadan,kafada ya daga
"Karki damu,duka basu da muhimmanci,zuwankin da ganinki ya fisu muhimmanci" wani
farinciki data jima bataji kamarsa ba ya tsirga mata,ta lumshe ido tana sakin
murmushi,ta jima bata ji kalmar data mata dadi matuqa daga anwar din ba irin
wannan,sannan ta budesu idanun nata a kanshi
"Ya gida yasu momy"
"Kowa lafiya suna ma gaidaka" ta fada tana zuba masa lemo sannan ta tura masa,bai
musa ba yaja yadan kurba tana binsa da kallo,batasan wane irin qauna takewa anwar
din ba,jifa jifa take sako hura yana tayata kana ta sako masa zancan
bikinsu,lissafin events da zatayi da sauran abubuwa,yana kurba yana saurarenta sai
daya shanye sannan yace mata
"Next week za'a kawo lefen idan Allah ya kaimu....saidai kuma kafin sannan inason
nayi wata muhimmiyar magana dake,duk da na riga na shaidawa su momy amma naga kece
yafi cancanta ki sani,kuma ni yafi dacewa na sanar miki da kaina" dukka hankalinta
ta bashi ganin yadda ya tara shima nutsuwarshi waje guda gamida soke yatsunsa cikin
na juna yana dubanta sosai
"Uhmm,ina jinka"
"Komai da kika gani a duniya muqaddarine daga Allah,hakanan ba wanda ya isa sauya
tsarin Allah,yadda ya tsarawa bawa haka zai karba,naka kawai ka gode masa,zaka iya
tsarawa rayuwarka abu amma idan baiyi dai dai da tsarin Allah ba zai sauya maka ne
da wanda yake ganin shine daidai da rayuwarka kuma shine mafi alkhairi,to...ina
tunanin ku biyu za'a daura mana aure dasu lokaci guda,na nemi aure watanni biyu
baya da suka wuce Allah ya qaddara kuma an bani,yanzu haka cikin satin da za'a kawo
naki kefen suma za'a kai,lokacin daurin aurenma kusan daya ne,rana ce kawai aka
bambanta,kinga ya kamata ace kin sani saboda kina da haqqin ki sani din,nasan mai
yiwuwa hakan zai bata miki rai saboda halin kishi irin na mata,saboda haka ina mai
baki haquri tare da shaida miki haka Allah ya qaddara dama tun fil'azal shi yasa ya
hukunta faruwar hakan,ina fata hakan bazai dameki ba don kowacce cikinku matsayinta
daban" wani irin abu taji yana mata yawo tsakiyar kaa kamar ana yamutsa
qwaqwalwarta,wannan wacce iriyar mummunar rana ce?,wanne irin mummunan labari
kunnuwanta suke dauko mata?,saita cije lebanta da kyau ga zatonta mafarki take ko
zata farka,saita fuskanci da gaske ne,wani abu ke niyyar toshe mata numfashi,ta
fahimci idan bata bari tayi kuka ba wani mummunan abu na iya faruwa da ita,saboda
haka kawai ta saki hawayen da take qoqarin tarewa suka soma zuba
"Wanne irin abu kake gayamin haka anwar?,kana gayaminne fa kishiya zaka yimin tun
ban shiga gidanka ba,anwar kana gayamin zaka hada soyayyata data wata ne fa,kana
gayamin zamu hada miji da wata,zaka raba soyayyarmu,wai shinma yaushe ka ganta
harkaji kana sonta kaji zaka iya aurenta?"
"Karki damu,ba wata sabuwa bace cikin rayuwata,mun jima tare,rabuwarmu da ita
qaddarar haduwarki dani ce"
"Shahida?!" Ta fada cikin razana da kuma salo na tambaya,saiya zuba mata idanu yana
kallonta tare da mamakin kama sunanta farat daya da tayi kafin daga bisani yace
"Eh,ya akayi kika santa?" Sam batabi takan tambayarshi ba saboda ji take kamar
alqiyamarta ta tsaya,a ina ya tono shahida?,a ina ya ganta?,ya akayi suka
daidaitawa?,ya akayi ta aminta zata aureshi?,ya akayi yaci gaba da kulata?,dama
soyayyarta bata mutu cikin ransa ba?,inaa,har abada ba zata taba yarda ta hada
anwar da shahida ba qarqashin inuwa daya,kuma ta kasance a tsakiyarsu?,ashe data
cika shashasha
"Kacemin kawai ka koma wajen tsohuwar masoyiyarka donka samu damar wulaqantani idan
ka aureni,har abada anwar bazan hadaka da wata ba,bazanyi zaman kishi da kowa
ba,bazan zauna da kishiya ba" ta fada tana miqewa tsaye,cikin hargagi,hannunshi ya
daga mata a nutse
"Ki nutsu nafisa ki samu waje ki zauna"
"Bazan nutsu ba,bazan zauna ba,ka daina kiramin nutsuwa a wannan yanayin,saidai ka
zaba koni ko ita" furucin ya fito hade da kuka mai cike da tashin hankali
"Ba wanda zan zaba hakanan ba wanda zanqi zaba" ya amsa mata kai tsaye tana dubanta
cikin yanayin dake nuna jarunta da mazantaka na jajirtaccen namiji,kai take
jinjinawa hawaye na zuba daga fuskarta sosai yana hadewa da majina,ji take kaman ta
cire ranta,ji take kama ta dauki numfashin shahida da bata tashi dawowa rayuwarta
ba sai sanda ta sakankace take saka ran ta mallaki anwar,tana ganin da tayi faduwar
baqar tasa,data shiga ta zama 'yar kallo gwara ta haqura dashi har abada
"Anwar!...kaje ka auri shahida bazan aureka ba,bazan aureka ba har abada" tana
kaiwa nan ta juya da gudu gudu sauri sauri tayi cikin gida,yayi niyyar dakatar da
ita amma sam bata tsaya ta saurareshi bama bare taji me zai sake fada,saiya furzar
da numfashi,kana ya ture kujerar baya ya miqe yana daukar muqullin motarsa gamida
da handkherchief dinsa dake aje saman teburin ya saka cikin aljihunsa ya nufi qofar
fita,sai daya shiga parking space sannan ya dauki motarsa yayiwa mai gida horn ya
bude masa gate ya fice daga gidan cikin nutsatstsen tuqi.

Yana tuqin yana furzar sa iska mai dumi daga bakinsa,wai me yasa mata dukka
harkarsu matsala ce?,don kawai yace mata ba ita daya za'a daurawa aure dashi ba
shine xata masa wannan jinnun?,to xaya zuba ido yaga iya nata gudun ruwan.

Wayarshi dake aje gefe ta dauki rura,yadan juya ya kalleta,ganin number anty
usaina ce ya sanyashi dagawa,ya saka handsfree ya aje gefansa
"Kana wajen ta ina ne?"
"Ina hanya anty"
"To shikenan saika iso"bai amsa ba ya katse kiran ya aje wayar ya maida hankalinsa
ga tuqinsa,duka hannayensa na zube saman sitiyarin,yayin da rabin tunaninsa ya tafi
ga abinda nafisan tayi yanzu,me take tunani?,zaita binta ne yana lallashinta?,ko
yace ta taimaka ta aureshi?.

Yana fitowa daga motar su sa'ida suka shigo gidan,dawowarsu kenan daga
makarantar dare dake can daya bangaren na unguwarsu,ba yadda anwar din baiyi ta
qyalesu ba amma tace sam batason zaman banza,zaman kallon bayan sallar magariba
daga waccar tashar a koma waccar,dukansu suka iso suna masa sannu da zuwa ya amsa
ya shiga cikinsu suka shige cikin gidan.

Qaramin falon anty usaina suka shiga suka bar yaran a babban falo,idanunsa
nakan tauraruwa tv anty usaina ta shigo ta aje masa abinci,kallon abincin yayi
" banajin yunwa anty"tana shirin zama tace
"Kaci a gidan abinci kenan?,gwanda dai kayi auren nan suma sa huta da ganinka"
murmushi ya saki yana shafa kanshi,zama tayi suka gaisa
"Ya za'ayi da kayan lefen?,na ina za'a fara kaiwa?" Tsaki yaja can qasa sannan yace
"Ni kaina ban sani ba,ina tunanin iya nasu za'a kai,don nafisa tace ta fasa" idanu
anty usaina ta fiddo
"Ta fasa kamar yaya?"hannayenshi ya watsa sannan yace
"Oho,na shaida mata kawai su biyu ne dalilin da yasa tace ta fasa kenan" saita
sauke ajiyar zuciya tana dubanshi
"Don tace ta fasa bawai yana nufin ta fasa dinne ba,kishi ne kawai da bacin
rai,lokaci qanqani zata sauko,saboda haka ba za'a fasa shirin komai ba,zuwa gobe ka
kirata ka bata baki duk yadda kukayi saika sanarmin" kai kawai ya gyada yana mita
qasan zuciyarshi,yadan jima anan suna tattaunawa sannan daga bisani yayi mata
sallama ya wuce.

A guje nafisa ta shiga falon gidan nasu ta wuce momy dake zaune tana kallo ta
haye sama dakinta,da kallo momyn ta bita harta shige,saita dauke kai tana sauke
ajiyar zuciya,dama ta sani za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,yadda nafisan ta
dora burinta da rayuwarta duka kan anwar din tasan za'a sha gwagwarmaya duk sanda
labarin ya shiga kunnenta,qyaleta tayi bata bi ta kanta ba,ta barta ta gama kukan
zuciyarta ta huce tukunna.

Tamkar zata zauce haka taji,ta kai ta kawo ta kasa zama kamar wadda ta hadiyi
tabarya,wannan wacce iriyar masifaffiyar shahida ce?,wanne irin mayen anwar ne?,ace
duk yadda takai ga rabasu haqanta ya gaza cimma ruwa?,iya abinda ya kamata tayi don
rabasu tayi amma ace bayan shekaru shidda sun sake dawowa sun jone?,idan ma kisa ba
batasan me zatayi don rabasu ba,wayarta ta rarumo ta kira number mima,saidai
hartayi quginta ta katse bata daga ba,haka ta dinga kira ba qaqqautawa amma bata
daga ba,cillar da wayar tayi cikin muryar kuka mai cike da bacin rai da qunan
zuciya tace
"Shegiya mahaukaciya,wai ina kika shiga ne?!" Ta qarasa fada cikin qaraji wanda
banda sautin tv dake aiki ba abinda zai hana momyn jiyo sautinta.
Haka ta dinga qaramin hauka ita kadai cikin dakin har sha biyu saura na dare
sanda wayarta tahau kuka,ta daukota da hanzari tana tsammanin mima ce,maimakon mima
anwar ne,aje wayar tayi kawai tana kallonta harta qaraci kukanta ta gama,sai daya
kira sau uku bata daga ba tana zaune da kallon wayar ruwan hawaye na fita daga
idanunta,tana ganin hakan da zatayi kawai shine zaisa anwar din ya janye qudurinsa
ya haqura shahidan.

Washegari qarfe goma na safe tana gaban mudubi a zaune tana kallon yadda
fuskarta ta qojale saboda kukan data kwana tana yi wayar ta sake burari,wannan
karonma anwar ne a maimakon mima,bata da mafita tilas ta daga wayar ta sake gaya
masa kalaman da zasu tabbatar masa da cewa ta rabu dashi kp hakan zai tsoratashi ya
janye nufinsa
"Karka sake kirana matsawar kana kan qudurinka na hada aurena da wata macen
daban,na gaya maka tun jiya nikam nafisa bazan aureka ba anwar muddin kana a
matsayin mijin mace biyu,na haqura dakai har abada" daga haka ta yanke kiran,saiya
furzar da numfashi daga bakinsa ya baiwa banza ajiyarta,ya aje wayarshi yaci gaba
da shirinsa,shikam ya yankema ransa babu sauran wata mace da zata sake bashi
wahala,bazai sake son wata ba bare ta gasa mishi zuciya yadda ya faru dashi a
baya,ya saki qaramin murmushi sanda ya tuna cewa da sonta yake da tuni yanzu yana
cikin tashin hankali da dimuwa a sanda tace bata sonshi,yanzun kam hankalinshi
kwance yake jinsa,saidai kuma wani bari na zuciyarsa yana dan jin damuwa,musamman
idan ya tuna da mahaifanta yadda zasu dauki maganar,da wannan tunanin ya gama
shirinsa ko abinci yau bai saurara ba ya dauki muqullinsa ya fito,kafin ya tashi
motarsa ya tsaya ya turawa anty usaina yadda sukayi da nafisan,don baison kiranta
ma bare ta bijiro da wani abun da zai hanashi uzurinsa nayau.

***** ****** ****** *****

"Wannan sakarcin banza ne ai sakarcin wofi,ta isa ta haramta abinda Allah ya


halatta?" Alhj abba mahaifin nafisa ya fada cikin fushi da bacin rai yana duban
mummy mahaifiyarta,kai ta gyada itama,sau tari tana mamakin halayen nafisan,ta rasa
inda take debo wasu baqaqen halayen,abubuwa da yawa ita dai ta sani ba halayyarta
bace kota mahaifinta ba
"Atoh,nayi mata magana daxun da safe ta nunamin tana kan bakanta" mummy ta baiwa
alhj abba amsa,shikam anwar yana daga gefe kanshi a qasa cikin girmamawa yana
saurarensu,baice komai ba sai a sannan
"Kuyi mata uzuri,duba da yadda zancan ya sameta a qurarren lokacin da bata zata
ba,ni kaina bani da masaniyar abun zai kasance haka sai gab da zanyi tafiya,sai
naga yafi kyau idan na dawo na shaida mata mu fahimci juna,to sai kuma aka samu
sabanin fahimta"
"Qarancin hankali da tunani dai,ita zata zauna maka da ita?,ko ita haqqin kula da
ita yake kanta?,bilki....kiramin ita maza" a nutse hajiyan ta miqe ta fice zuwa
dakin nafisan.

Kwance take rub da ciki tana aikin kuka,tana son anwar tana tsoron rabuwa
dashi,tana tsoron yaqi janye qudurinsa,don itakam ba abinda zai sata ta sauka daga
kan bakanta,matsawar ta yarda ta aureshi to yaqin da tayi shekara da shekaru tana
yi,kudinta data kashe,lokacinta data fansar duka sun tashi a babin badinuhu bataci
riba ba kenan
"Kin hadu da aiki kuma kin gama kanki da wahala wallahi,tunda kin daukama kanki
aqidar banza da wofi,ki tashi kije mahaifinki nason ganinki" cewar mummy daga haka
bata qara ba ta juya tayi ficewarta.

Sanda ta isa falon anwar ta soma gani,kishinsa ya sake lullubeta ganin yadda
kamar ma sake kyau da fresh yayi abinsa tsakanin kwanakin da ita take fama da
quncin zuciya,gefan abban nata ta zauna ya dubeta
"Nafi,wanne irin shashanci da sakalci kike shirin aikatawa haka?,saboda Allah ya
halatta masa auren daga daya zuwa hudu saikice ba zaki aureshi ba saboda haka?,zaki
sauya hukuncin Allah kenan?,koke kikayi kanki?to kar naji karna gani,banason wannan
shirmen banza,yana da damarma yace biyu zaiyi kece ata uku" Kuka ta saki sosai
"Abba...wallahi bazan aureshi ba,bazan iya zama dashi da wata ba"baki bude alhj
abba ya watsa mata daquwa
"Kinci gidanku,kajimin fitinanniyar yarinya?,to saikin aureshin naga wanda ya isa
ya hana" miqewa tayi cikin kuka
"Wallahi abba zan gudu,zan barku idan aka aura min shi" mummy na shirin kai mata
duka saboda takaici ta fice a guje daga falon.

Shuru ne ya ratsa falon,kunya da takaici na kama alhj abba da hajiya


bilkisu,sai suka rasa ta inda zasu kama zancan,sunsan halin nafisa sarai sai
addu'a,karta aikata wani abu da zai zama musu illa nan gaba,anwar ya fahimci
shurunsu saboda haka yace
"Alhj,karka damu,Dukkaninmu ni da kai da mummy bamu da ikon da zamu sauya mata
ra'ayi,sannan duk yadda mukaso abin itace zata zauna,dole saida gamsuwarta sannan
komai zai tafi yadda ake buqata"ajiyar zuciya suka saki dukansu kusan a tare cikin
bacin rai da takaici
"Yarone ka haifeshi baka haifi halinsa ba,kayi haquri anwar" cewar alhj abba yana
jin babu dadi har cikin ransa,yana jin kaman ya muzanta
"Haka Allah ya qaddara" anwar din ya furta kanshi a qasa,shima yana jin babu dadi
saboda yadda sukejin laifin kaman a kansu yake.

Tana zaune har yanzu inda ta zauna tana rusar kuka a haka mummy ta tura qofar
dakin ta sameta,da hanzari ta daga kai cikin fargaba da razani tare da taraddin
furucin da zai fito daga bakin mummyn,tana son anwar tana fata ace ya karbi
muradinta
"Shikenan ko?,burinki ya cika?,saikije ki samo wani mijin wanda yafi anwar" daga
haka ta juya abinta ta fice tabar mata dakin,cikin tashin hankali ta miqe kaman
zata bi bayan mommy don samun qarin bayani,sai kuma ta dawo da baya qwaqwalwarta na
gaya mata ma'anar maganar mummyn,anwar ya barta?,anwar ya zabi shahida
akanta?,wahalarta ta tashi a banza kenan?,kai ta shiga girgizawa tana fadin
bazaiyiwu ba,ta dauki wayarta ta soma kiran layin mima ba qaqqautawa don tana da
buqatarta a yau fiye da kullum,saidai amsar dai daya ce wayar a kashe take.

A qalla ta kwashi awa kusan biyu a haka,bata da wata mafita ayanzu banda ta
kira anwar,ta soma laluben number dinsa ta kira.

Fitowarsa kenan daga kitchen dauke da cup na coffe wanda ya shiga ya hada
da kansa,cikin mamaki yake duban mai kiran,saiya samu daya daga cikin kujerun falon
ya zauna yana amsa wayar
"Ni zaka yiwa haka anwar?,ni nafisa zaka gujewa saboda wata banzar shahida da bata
kama qafata wajen qaunarka ba?,idan baki sani ba bari yau na fada maka,ni nafisa
nice silar duk wani arzqinka,nice silar duk wani matsayi daka taka a yau,nice silar
zamantowa abinda kake a yanxu,amma sakayyar da zaka yimin kenan?,ka zabi wata
akaina?"
"Kin gama?" Ya furta a nutse yana saurarenta,jin batace komai ba yasa ya dora
"Na farko ba wani bawa daya isa ya azurta wani bawa dukkaninmu muna cine cikin
taskar ubangiji,abu na biyu banyi zabe ba hakan ban fifita ba,kece wadda kika
zabarwa kanki haka,ko a yanxu kika yarda da abinda nazo dashi,kika amince da cewa
qaddararmu ce gaba daya ina maraba da hakan,saboda haka zabi ya rage game shiga
rijiya" daga haka ya datse kiran ya aje wayar gefanshi,yadda yake tsammanin zai
damu ko zaiji ciwo saiyaga duka ba haka bane,abu daya cikin daruruwan daya sanya ya
kasa baiwa nafisa koda digo daya cikin dari na so ko qauna a zuciyarsa kenan,bata
da lafazin magana,bata da tarbiyya yiwa kai waigi a duk sanda rai ya baci,ya godewa
Allah daya sanya ya maida dukkan kudaden da kamfani da kuma alhj abba ya bashi a
wancan lokacin ya zabi yaci gashin kanshi ba tarema da yasan waye yayi silar
zuwanshi wajen ba,saiya dauki coffensa a hankali ya soma kurba ba tare daya ji wata
gagarumar damuwa ba.
Kira ya sake shigowa wayar tashi,ya dauka itace dai sai yaga anty usaina,ya
amsa wayar bayan sun gaisa ga gaya masa komai ya kammala kuma jibi ne zasu miqa
lefan
"Shikenam babu damuwa,Allah ya nuna mana,saidai na nafisa ki ajesu wajenki,zan
shigo gobe zamuyi magana"
"Allah ya nuna mana" ta amsa masa.

Wayarsa ya dauka yana duba jerin numbers din dake cikin wayar,kaf wayar babu
number dinta,ba abun mamaki bane don yasan dama da zaman hakan,rabonshi da number
dinta ta rabi wayarshi cikin xamanin da yake amfani da waya keypad,wayar da har
yanzu bai rabu da ita ba,hakanan baisan dalilin qin rabuwa da ita ba,saiya koma
neman number wayar sulaiman,bugu uku ya daga,suka gaisa ya gaya masa ya kaiwa daada
wayar,ya shaida masa yana kusa da ita,sabida haka ya miqa mata wayar,bayan sun
gaisa cikin mutunta juna sun dan taba wasa irin na jika da kaka da suke lokaci zuwa
lokaci,don jin anwar din take kamar jikanta na jini
"Jibi xasu miqa kayan daada,na nemi number dinta ban samu ba,ko zaki nemi wani
cikin gidan a shaida masa"
"Karka damu,sule nada lambar zubaida,yanzu zansa ya kirata ya gaya mata" hira suka
dan qra tabawa kadan yana tsokanarta sannan sukayi sallama.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana kurban coffensa idanunsa saman tv da aka
ragewa volume sosai,tunani nason fisgarsa yana jefashi wata duniya can,zamanin da
dukkaninsu shida shahidan keda buri da fatan mallakar junansu,zamanin da kowannensu
yake kwana ya kuma tashi da marari soyayya da begen dan uwanshi,a sannan dukkan
mafarkinsu da fatansu ya ta'allaqa ne akan lokacin da zasu zama mallakin
juna,lokacin da dukansu shida ita quruciyarsu ta ninka ta yanzj qwarai,bai mantawa
wani lokaci daya je hira suna hirar qawar shahida da aka kaiwa lefe,ganin yadda
yake nuna buri da fatan yiwa shahidan lefe mai yawa na kece sa'a yasa tace
"Nifa yaa anwar,basai ka takura kanka ba,nifa ba wani lefe da zakamin,ni ba kaya
nakeso ba..."
"Me kikeso...?" Ya fada yana tsareta da ido cikin wani salon kallo da baisan yana
mata ba saboda shagwabarta data tafi dashi,yasandai cewa sanda yake kallonta din
soyayyarta da qaunarta na narkewa tana sake kwaranya cikin magudanan jininsa,kallon
da yake mata ya sanyata jin kunya harta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana
dariya
"Kai nakeso ni"
"Na sani shahida,amma kullum burina shine na daga darajar shahida cikin mata,kullum
burina shahida tafi kowacce mace a duniya,indai ina dashi dole shahidana ta fita
daban,kita min addu'a shahida,idan na tashi zan miki lefe irin wanda kowacce mace
xatayi burinsa" idanunta ta zaro tana kallonshi
"Ya anwar?,ranar kuwa zanyi bacci?,ya anwar dina yayimin kaya irin haka ranar
kowacce mace saidai ta biyo bayana"
"Qwarai kuwa,wannan dan qaramin bakinkin ya iya furta kalmomi masu zaqi da tsayawa
a rai" dariya sukayi a tare tana kife fuskarta akan cinyarta.

Yana kawowa nan wani qaramin murmushi da bai shirya ba ya subuce saman
fuskarsa,saiya aje cup din,lokaci guda wani abu yayi kutse cikin farincikin daya
tsinci kasa,ya soma juyawa zuwa bacin rai,da sauri ya soma furta la'ilaha illa anta
subhanaka inni kuntu minazzalimin,saiya miqe ya dauki cup dinsa ya haura sama inda
bedroom dinsa yake dashi.

***** ******* *********

"Ina kwana anty" shahida ta fada sanda take sanya kanta cikin kitchen tana
daura agogon hannunta,anty zubaida ta amsa hankalinta na wajen siyayyar da akayi
mata tana dubawa,sai data gama daura agogon sannan ta daga kai,turus tayi yadda
taga kitchen din ga kacame da kayyaki
"Anty,wadan nan kayan kuma fa?" Ajiye dan qaramin botikin butter din data duba tayi
"Kayan aikin abincin masu kawo lefe ne" wani mummunar faduwar gaba taji ta
ziyarceta,duk wani dan kuzari data samu ta sauko dashi yau ya soma yin nashi
waje,saita dan dafe kujerar dake kusa da ita
"Lefe kuma?" Kai anty zubaida ta kada tana karantarta
"Eh,jiya da dare daada ta gayamin" sai kawai ta kada kai tana qoqarin hadiye wani
abu,ba tare data ce komai ba ta juya ta fice a kitchen din,ko abincin break dake
saman tebur bata saurara ba ta fice daga gidan,ta samu mai adaidatanta na jiranta
ta shiga ta zauna yaja suka bar gidan.

Ko data isa office rufe kanta kawai tayi ba tare data bar kowa ya shigo ba,ta
rasa shin kuka zatayi ko kuwa,idan tayi kuka babu mai sauraren kukanta,idan bore
zata ci gaba dayi wanda zatayiwa borenma bata ganshi ba,wannan wanne irin cin
zaline anwar ya shiryawa rayuwarta?,me yasa zai bibiyi rayuwarta da irin wannan
sakamakon na daban,tunda bai ra'ayinta ya barta tayi rayuwarta cikin salama,irin
rayuwar da zata samu nutsuwa mana,saiya shigo don ya rusata?,ya rusa dukkan walwala
da farincikin data jima tana tattalinsu da rainonsu?.

Kusan haka ta wuni cikin kamfanin babu cikakkiyar madafa ko mafita,don haka
suna tashi ta yanke shawarar zuwa gida,donkarta koma ma ta tadda su anty zubaida na
aikin kayan masu kawo lefe,lefen da takeji kamar ta cinnawa mai lefen da lefan

3️⃣ 2️⃣
kanshi wuta.*AA*
3️⃣2️⃣

Sallama tayi a tsakar gidansu,khadija dake qofar kitchen tana tankadewa umma
dake cikin kitchen garin tuwo ta amsa,a matuqar kasalance kamar wadda tayi aikin
shekara ta tsaya da qofar kitchen din tana gaida umman,ta waiwayo ta dubeta sannan
ta amsa tana karantar yanayinta,khadija na gaidata ta amsa mata tana shigewa
falonsu,jakarta ta aje waje daya sannan ta cire mayafinta ta dora akai,ta samu daya
daga cikin kujerun falon ta kwanta tana sauke numfashi a hsnkali,saita tashi ta
sake qaro gudun fankar dake sama tana juyawa ta sake dawowa ta kwanta a riginginen
dai,haka kawai zuciyarta tayi wani rauni,hawaye ya soma bin kumatunta yana zirarowa
gefan fuskarta,ta dinga shareshi akai akai,duk sanda ta tuna anwar zata aura sai
taji zuciyarta ta quntata,a ganinta bata dace dashi ba,bata cancanci mutum kamarsa
ba,tunda a baya ya iya guje mata a gaba babu abinda zai hanashi aikata hakan,bugu
da qarima gaba daya auren manufa zaiyi da ita,yayi ne don kawai ya rusa walwalarta
ya rabata da nuradden.

Umman ta dan jima tana kallonta ba tare data sani ba kafin tatako zuwa cikin
falon,ta samu kujera daya ta zauna sai a sannan shahidan ta ganta,miqewa tayi daga
kwanciyar kuka na balle mata sosai,baki ta sake umman tana dubanta sannan tace
"Saikace qanqanuwar yarinya zaki tasani gaba kina kuka?,meye hakan?" Zamowa tayi
daga saman kujerar da take kai tayin kneeldown a gaban umman ta kama hannayenta
"Don girman Allah umma ki dakatar dasu,ke daya ce burina na qarshe,wallahi umma
bana sonshi shima baya sona,ku aura min koma waye umma amma banda anwar?" Idanu ta
saka tana kallonta,a iya saninta abinda ya faru tsakaninta da anwar ma laifi nata
ne,iya abinda ta saninma baiyi zafin da zata rikice hakan ba harta rasa sukuni da
walwala ba,Yayin da khadija wadda shigowarta kenan ta tsinci xancan ta dafe baki
gami da zare ido cikin mamaki,har batasan sanda tayi subutar bakin cewa
"Yaaya?,ya anwar ne fa?" Daga kai umma tayi tayi mata nuni data fice,haka ta fita
cikin dimbin mamaki,ta zaci antyn tata zatayi farinciki da dawowar anwar rayuwarsu
fiye da yadda su sukayi,amma ga sabanin hankalinta sai taga ba haka bane sam.

A nutse umma ta zuba mata idanu,cikin sanyin murya wanda ke nuna har jikinta
ma a sanyaye yake tace
"Ashe so kike ki tona mana asiri shahida bayan lullubin sutura da Allah yayi mana?"
Ta qarasa maganar wani abu na taba zuciyarta wanda ya bayyana har a muryarta
"Shahida ashe baki qaunata?,ashe ba rufin asiri Allah yayi miki ba damu kanmu daya
dawo miki da anwar?,meye a zuciyarki shahida?,bakison farincikina ashe da
walwalata?"kai shahida ke girgizawa kuka na qwace mata
"ba haka bane umma,umma bana sonshi kiyi haquri umma,wallahi banajin sonshi kwata
kwata"
"Shahida indai nice na haifeki ina....."
"A'ah,karki qarasa don Allah umma" sukaji wata murya da sako kanta kenan dakin ta
tsinci zancan shahida na qarshe da lafazin umman ta fada,dukkansu suka juya suna
kallonta,anty usaina ce,ta qarso inda suke zaune,wajen shahida ta nufa kai tsaye ta
kama hannayenta sannan ta zauna gab da ita,hankalin umma yadan tashi kadan don ba
zataso shahida tacigaba da magana kan anwar ba,don tana da tabbacin batasan wace
ita a wajenshi ba
"Idan kika fadi haka kamar kin mata qarfa qarfa ne ai" tana kallon umman tayi
maganar,wani sanyi shahida taji cikin ranta,tana fatan Allah yasa zuwan matar ya
zame mata haske
"Idan kuma tana da hujjarta fa wadda tafi taku qarfi?,ki barta aji hujjarta da
dalilanta tukunna".

Miqewa umma tayi


" bata da wata hujja ko dalili usaina"
"A'ah bari naji ta bakinta tukunna"
"Koda kinji ta bakinta na riga na yanke matuqar nina haifeta ina bata umarnin auren
anwar" daga haka umma ta fice daga dakin tana mamakin wauta da sakarcin da shahidan
takeson tafkawa,kamar batasan meya wakana cikin rayuwarta a baya ba,bata taba
tsammanin ma anwar zai sake waiwayar shahida yace zai aureta ba sabida abunda
idanunshi suka gane masa a zahiri ba labarj,dama tazo mata tanason tayi wasa da
ita?,koda taqi anwar din batajin zata samu kamar anwar din,mutumin da tun wancan
lokacin ya samu karbuwa cikin kaf danginta na uwa da uba,badon komai ba sai kyawun
halayyarsa da kyawawan dabi'un da Allah ya huwace masa.

Maido dubanta kan shahida tayi bayan ficewar umma,suka hada idanu,hakanan
shahidan taji gabanta ya fadi,ta dauke nata idanun tana matsar qwalla,cikin taushin
murya ba tare data saki hannunta ba tace
"Shahida....inason naji meye matsalarki dashi wannan din da umma tace saikin
aura,indai naji dalilanki masu qarfi ne nayi alqawarin tsaya miki harsai an warware
komai" shuru na 'yan sakanni ya ratsa tsakaninsu,batajin zata iya furtawa wani
komai,yin hakan kamar ta dabawa cikinta wuqane,tana ji ceqa wani sirri ne agareta
ga duk wanda baisan meye faru ba,a hankali ta motsa labbanta sannan tace
"Kawai bana sonshi,shima kuma baya sona,hasalima mun rabu dashi a qalla shekara
shida kenan,ba wanda keda muradin wani" shuru anty usaina tayi tana nazarin
kalamanta,ba shakka akwai wani abu,amma dukkansu amsa kusan guda ce,jiya jiya ta
titsiye anwar din kan meye sanadin rabuwarsu da shahida amma ya kasa bata amsa daya
qwaqwqwara,kowannensu bayason fallasa asirin dan uwanshi,hakan na nufin akwai
ragowar wani abu da yayi saura game da zukatansu qarqashin zukatansu kenan koda su
basusan da hakan ba?
"Amma shahida....ya akayi kikasan baya sonki?,kuma dama an taba rabuwa hakanan babu
wani dalili?"tambayar taso kaita maqura saboda rashin amsa
"Miji da mata ma kan iya rabuwa haka kawai ya saketa badon ta masa komai ba,saidon
qarewar wa'adin zamansu da Allah ya qaddara musu" saitayi shuru tana hadiyar zuciya
tana neman amsa ta biyu da zata bata wadda zata gamsar da ita,da qyar ta iya hada
abun fadi bayan anty usainan tace
"Uhmmm,ya akayi kikasan baya sonki?"
"Duk wani abu na nuna kulawa ko xiyara da zai nuna saurayi yana son budurwa babu
shi tattare dashi,sau daya ya taba zuwa wajena,shima bamuyi ganawar dadi dashi
ba,ta yaya zance yana sona?" Ta qarasa maganar badon abinda ta fada ya dameta koya
dadata da qasa ba,a'ah,ta fada ne kawai donta riqeshi hujjar da anty usaina zata
taimaka mata ta rana wannan auren da take kallonsa a matsayin qarfen qafa mai wuyar
kwantuwa a gareta.

Lallai ya zama dole ta shiga alaqar shahida da anwar,tana fata nan gaba
dukkansu suyi dariya,tana fatan ko meye silar shiga tsakaninsu nan gaba ya zama
tarihi,rayuwarsu ta koma kamar yadda take a baya
"Naji dadi da kika kasance yarinya mai biyayya wa iyayenta,ina mai miki kyakkyawan
fatan ba zaki toxarta ba in sha Allahu,biyayyarki zata kai miki da ixinin ubangiji"
da wannan kalaman sukayi sallama,ta fice daga gidan bayan ta samu umma ta roqeta
kan karta gaya mata dangantakarta da anwar,donta tabbatar hakan zai baiwa shahidan
kunya.

Tun a kan hanya ta soma gwada number anwar din,saidai bata sami wayarshi ba
akashe take,da alama yana muhimmin wani abune,dole ta katse kiran ta isa
gida,saidai lokaci lokaci tana gwada number tashi ko xata dace ta shiga.

Tana idar da sallar magariba ta soma shirin barin gidan,umma ta dubeta


"Amma da kin dan jinkirta tafiyar tukunna,saboda garin a dinke yake da hadari ga
iska ta soma kadawa"
"Idan ya sauko bansan ranar da zai dauke ba,anty zubaida kuma zataji shurun yayi
yawa,don ban gaya mata ma ina nan ba"
"Shikenan,Allah yayi miki albarka,yasa albarka a rayuwarku"
"Ameen" ta amsa tana maida qwallar dakeson fitowa,haka ta baro gidan tana tafiya
kamar wadda batason taka qasa,wanda bai sani ba sai ya zaci salo ne ko tana
sane,amma ba komai bane sai tsabar damuwa dake cinta a rai,tana jin yadda hadarin
ya taso sosai sanda takai tsakiyar layin nasu,iska ta dinga kadawa tana ratsa
jikinta,saidai sam bata damu ba,bata damu da ruwan ya sauko ya daketa ba,hakanan
bata damu data koma gida donta samu mafaka ba.

Daidai lokacin da motarsa ke tsaye qofar gidan anty usaina wadda ta buqaci
ganinsa a yau basai gobe ba,yana zaune cikin motar baikai ga yiwa mai gadi horn ba
bare ya bude masa,ya tsaya ne amsa waya,dukka gilasansa a rufe suke ruf kamar yadda
al'adarsa take yawanci idan yana cikin mota,bugu da qari kuma ma sabida iskar
dayaga ta taso sosai,wanda yasan ba za'a rasa qura ba cikinta,gefansa ya kalla
kamar wanda aka fisgi hankalinsa,sai yaga kaman itace ta wuce,yaci gaba da amsa
wayar yana kallon bayanta,tabbas ita dince,amma me take har war haka duhun magariba
ya mamaye gari bata koma gida ba,idanunsa suka ci gaba da kallonta har lokacin data
dan bada tazara daga inda yake,yana shirin janye idanunsa yaga yayyafi ya soma
sauka ta gilashin motarsa,yaso ya dake yaso ya dauke kai ya saka motarsa cikin
gidan anty usaina amma saiyaji kaman umarni,a zafafe yace
"Oh god" yana zare belt din jikinsa,cikin zafin nama da kuma jin haushin kansa da
kansa ya bude murfin motar ya fice.

Yana kuzari da halittar ba daya bace,hakan ya sanya cikin qididdgaggun taku ya


cimmata
"Daga ina kike haka?" A nutse ta waiwayo tana dubansa sanda take gab da qarasa
bakin titi,saita juya da niyyar ci gaba da takawa ba tare data amsa shi ba
"Wai sanda zaki fita ma kin tambayeni ne?,saboda tsabar rinton zunubi?" Kalaman sun
mata ciwo,wato tun yanzu yake nufin xai mulkata kenan?,hakan yasa ta tsaida tafiyar
tata ta juyo ta dubeshi
"Kai waye da don zan fita saina tambayeka?"
"Kinfi kowa sanin ni waye ai ba buqatar na maimaita miki,banason dogon zance wuce
muje na taimaka miki na saukeki,amma kafin sannan idan kina da niqab ki saka a
fuskarki kar mutanen unguwa su ganmu tare su zaci nima dan harka ne" ya kai qarshen
zancan yana dage girarsa duka biyun,wanda hakan ya masa kyau ainun duk da fuskarshi
a murtuke take,sosai kalaman suka fusatata wanda hakan ya sanyata ta juyo gaba daya
ta watsa masa idanunta da suka sake budewa saboda bacin rai,hakan ya tilasta masa
dan qanqance nashi idanun gami da damqe hannayensa dake zube a aljihu
"To hell with your taimako...Allah suturu buqui,har abada bana son
taimakonka,sannan kuma aikin banza kake harara a duhu,da kake gudun kar a ganmu
tare me ya kaika neman dauramin igiyarka,idan da gaske kake qyamata aiya kamata ka
gujeni da gaske ta yadda ko qasa daya ba zaka hada dani ba bare inuwa daya,indai ka
cika kai anwar ne ka aikata hakan" qaramin murmushi ya saki daya sake fitar da
kyansa,ya dage dukka kafadunsa
"Ba zaki taba samun yadda kikeso ba,niba qaramin yaro bane bare kalamanki su
tunzurani nayi miki yadda kikeso,abu daya kawai na sani shine,na riga dana biya
sadakinki,saboda haka ina da power a kanki ko kinqi ko kinso...saboda haka ki wuce
muje" dogon tsaki taja wanda ya ratsa kunnuwansa,sannan ta watsa masa harara ta
juya taci gaba da tafiya,bai fasa binta ba shima har suka isa titi.

Adaidaitan farko data tsaida ya sallameshi da dubu daya yace yane abinsa,na
biyu ma haka,na uku kuwa da yame dattijone yace masa baba kaje matata ce yaji
takeson yi,na bata haquri taki haqura,nan yasa bawan Allahn ya tsaya yana mata
nasiha,inda daga qarshe ya sallameshi da dubu uku ya amsa yana godiya,ta hudu kuwa
ya samu sauayi maiji da tashen girma yaso masa gardama.kan saiya dauketa tunda
itama tana son shiga
"Kana sha'awar xaman gidan kaso kenan?" Harya karkata baki zai masa diban albarka
saiya nutsu ya qarewa shigarsa kallo,tun daga takalminsa,kayan jikinsa zuwa
agogonsa,aibabu shiri yaja abun hawansa ya fece,bacin rai ya taru ya rufeta ruf
sanda ta kalli titin ta ganshi fayau ba wani sauran abun hawa na haya kuma nan
kusa,ta waiwayo zata gasa masa magana ko xataji sanyi,kadan ya rage fuskarsu ta
gwaru,sam batasan yana bayanta ba a tsaye,da alama kuma duk tsahon lokacin kallonta
yake,baya yaja yana bata fuska
"Ke baki da kunya ne?,akan titi kike neman ki rungumeni?,toki maida qwalamarki,ni
ba naki bane" kawai saita fashe da kuka ba tare data shirya ba,saboda ya gama
cutarta,bata ga wani kalma da zata fada masa ba wadda zata rama abinda ya gaya
mata,minti biyu kacal ruwan sama ya soma sauka,ya kalli sama sannan ya kalleta
"A karo na qarshe nake gaya miki ki wuce mu tafi" baya taja saman wasu tayoyi da
masu faci suka tashi suka barsu a wajen ta zauna,ta gwammace ruwan yayi mata koma
meye data bishi kota shiga motarshi,ganin ta zauna dafa'an ya sanyashi juyawa ya
koma cikin layin don dauko motartashi zuwa nan bakin titin dukda yadda ruwa yake
dukansa.

Yana isowa wajen yaga tashinta cikin adaidaita sahu,qaramin murmushi ya sube
masa,wato dama tana da taurin kai kenan?,saiya sake baiwa motar wuta harsai daya je
daya side din na adaidaitan,ya tabbatar ta ganshi sannan ya barsu suka wuceshi,a
baya yaci gaba da binsu har xuwa sanda yaga shigarta gida sannan ya karya kan motar
ya koma gidan anty usaina.

Sanda ta shiga gida baqinciki da takaici ya sake cikata ganin yadda gidan
har baqi yadan samu,hakanan ga kayan amsar lefe a kammale gobe kawai suke
jira,hasina ma ba'a barta a baya ba,ganun zata saka mata ciwon kai da tsokanarta
yasa tayi zarcewarta daki ko tsayawa a wajen batayi ba bare ta zauna,gaban
mudubinta ta tsaya tana kallon yadda ta jiqe gaba dayanta,haushinsa ya sake
cikata,taji kaman ta sake fashewa da wani kukan,duk shi yaja mata,da ta shiga
adaidatan a lokacin daya dace da duk hakan bata faru da ita ba,haka ta ringa cire
kayanta daya bayan daya ta daura babban towel ta shige bandakinta ta hada ruwa mai

3️⃣ 2️⃣
zafi tayi wanka.*AA*
3️⃣2️⃣

Sallama tayi a tsakar gidansu,khadija dake qofar kitchen tana tankadewa umma
dake cikin kitchen garin tuwo ta amsa,a matuqar kasalance kamar wadda tayi aikin
shekara ta tsaya da qofar kitchen din tana gaida umman,ta waiwayo ta dubeta sannan
ta amsa tana karantar yanayinta,khadija na gaidata ta amsa mata tana shigewa
falonsu,jakarta ta aje waje daya sannan ta cire mayafinta ta dora akai,ta samu daya
daga cikin kujerun falon ta kwanta tana sauke numfashi a hsnkali,saita tashi ta
sake qaro gudun fankar dake sama tana juyawa ta sake dawowa ta kwanta a riginginen
dai,haka kawai zuciyarta tayi wani rauni,hawaye ya soma bin kumatunta yana zirarowa
gefan fuskarta,ta dinga shareshi akai akai,duk sanda ta tuna anwar zata aura sai
taji zuciyarta ta quntata,a ganinta bata dace dashi ba,bata cancanci mutum kamarsa
ba,tunda a baya ya iya guje mata a gaba babu abinda zai hanashi aikata hakan,bugu
da qarima gaba daya auren manufa zaiyi da ita,yayi ne don kawai ya rusa walwalarta
ya rabata da nuradden.
Umman ta dan jima tana kallonta ba tare data sani ba kafin tatako zuwa cikin
falon,ta samu kujera daya ta zauna sai a sannan shahidan ta ganta,miqewa tayi daga
kwanciyar kuka na balle mata sosai,baki ta sake umman tana dubanta sannan tace
"Saikace qanqanuwar yarinya zaki tasani gaba kina kuka?,meye hakan?" Zamowa tayi
daga saman kujerar da take kai tayin kneeldown a gaban umman ta kama hannayenta
"Don girman Allah umma ki dakatar dasu,ke daya ce burina na qarshe,wallahi umma
bana sonshi shima baya sona,ku aura min koma waye umma amma banda anwar?" Idanu ta
saka tana kallonta,a iya saninta abinda ya faru tsakaninta da anwar ma laifi nata
ne,iya abinda ta saninma baiyi zafin da zata rikice hakan ba harta rasa sukuni da
walwala ba,Yayin da khadija wadda shigowarta kenan ta tsinci xancan ta dafe baki
gami da zare ido cikin mamaki,har batasan sanda tayi subutar bakin cewa
"Yaaya?,ya anwar ne fa?" Daga kai umma tayi tayi mata nuni data fice,haka ta fita
cikin dimbin mamaki,ta zaci antyn tata zatayi farinciki da dawowar anwar rayuwarsu
fiye da yadda su sukayi,amma ga sabanin hankalinta sai taga ba haka bane sam.

A nutse umma ta zuba mata idanu,cikin sanyin murya wanda ke nuna har jikinta
ma a sanyaye yake tace
"Ashe so kike ki tona mana asiri shahida bayan lullubin sutura da Allah yayi mana?"
Ta qarasa maganar wani abu na taba zuciyarta wanda ya bayyana har a muryarta
"Shahida ashe baki qaunata?,ashe ba rufin asiri Allah yayi miki ba damu kanmu daya
dawo miki da anwar?,meye a zuciyarki shahida?,bakison farincikina ashe da
walwalata?"kai shahida ke girgizawa kuka na qwace mata
"ba haka bane umma,umma bana sonshi kiyi haquri umma,wallahi banajin sonshi kwata
kwata"
"Shahida indai nice na haifeki ina....."
"A'ah,karki qarasa don Allah umma" sukaji wata murya da sako kanta kenan dakin ta
tsinci zancan shahida na qarshe da lafazin umman ta fada,dukkansu suka juya suna
kallonta,anty usaina ce,ta qarso inda suke zaune,wajen shahida ta nufa kai tsaye ta
kama hannayenta sannan ta zauna gab da ita,hankalin umma yadan tashi kadan don ba
zataso shahida tacigaba da magana kan anwar ba,don tana da tabbacin batasan wace
ita a wajenshi ba
"Idan kika fadi haka kamar kin mata qarfa qarfa ne ai" tana kallon umman tayi
maganar,wani sanyi shahida taji cikin ranta,tana fatan Allah yasa zuwan matar ya
zame mata haske
"Idan kuma tana da hujjarta fa wadda tafi taku qarfi?,ki barta aji hujjarta da
dalilanta tukunna".

Miqewa umma tayi


" bata da wata hujja ko dalili usaina"
"A'ah bari naji ta bakinta tukunna"
"Koda kinji ta bakinta na riga na yanke matuqar nina haifeta ina bata umarnin auren
anwar" daga haka umma ta fice daga dakin tana mamakin wauta da sakarcin da shahidan
takeson tafkawa,kamar batasan meya wakana cikin rayuwarta a baya ba,bata taba
tsammanin ma anwar zai sake waiwayar shahida yace zai aureta ba sabida abunda
idanunshi suka gane masa a zahiri ba labarj,dama tazo mata tanason tayi wasa da
ita?,koda taqi anwar din batajin zata samu kamar anwar din,mutumin da tun wancan
lokacin ya samu karbuwa cikin kaf danginta na uwa da uba,badon komai ba sai kyawun
halayyarsa da kyawawan dabi'un da Allah ya huwace masa.

Maido dubanta kan shahida tayi bayan ficewar umma,suka hada idanu,hakanan
shahidan taji gabanta ya fadi,ta dauke nata idanun tana matsar qwalla,cikin taushin
murya ba tare data saki hannunta ba tace
"Shahida....inason naji meye matsalarki dashi wannan din da umma tace saikin
aura,indai naji dalilanki masu qarfi ne nayi alqawarin tsaya miki harsai an warware
komai" shuru na 'yan sakanni ya ratsa tsakaninsu,batajin zata iya furtawa wani
komai,yin hakan kamar ta dabawa cikinta wuqane,tana ji ceqa wani sirri ne agareta
ga duk wanda baisan meye faru ba,a hankali ta motsa labbanta sannan tace
"Kawai bana sonshi,shima kuma baya sona,hasalima mun rabu dashi a qalla shekara
shida kenan,ba wanda keda muradin wani" shuru anty usaina tayi tana nazarin
kalamanta,ba shakka akwai wani abu,amma dukkansu amsa kusan guda ce,jiya jiya ta
titsiye anwar din kan meye sanadin rabuwarsu da shahida amma ya kasa bata amsa daya
qwaqwqwara,kowannensu bayason fallasa asirin dan uwanshi,hakan na nufin akwai
ragowar wani abu da yayi saura game da zukatansu qarqashin zukatansu kenan koda su
basusan da hakan ba?
"Amma shahida....ya akayi kikasan baya sonki?,kuma dama an taba rabuwa hakanan babu
wani dalili?"tambayar taso kaita maqura saboda rashin amsa
"Miji da mata ma kan iya rabuwa haka kawai ya saketa badon ta masa komai ba,saidon
qarewar wa'adin zamansu da Allah ya qaddara musu" saitayi shuru tana hadiyar zuciya
tana neman amsa ta biyu da zata bata wadda zata gamsar da ita,da qyar ta iya hada
abun fadi bayan anty usainan tace
"Uhmmm,ya akayi kikasan baya sonki?"
"Duk wani abu na nuna kulawa ko xiyara da zai nuna saurayi yana son budurwa babu
shi tattare dashi,sau daya ya taba zuwa wajena,shima bamuyi ganawar dadi dashi
ba,ta yaya zance yana sona?" Ta qarasa maganar badon abinda ta fada ya dameta koya
dadata da qasa ba,a'ah,ta fada ne kawai donta riqeshi hujjar da anty usaina zata
taimaka mata ta rana wannan auren da take kallonsa a matsayin qarfen qafa mai wuyar
kwantuwa a gareta.

Lallai ya zama dole ta shiga alaqar shahida da anwar,tana fata nan gaba
dukkansu suyi dariya,tana fatan ko meye silar shiga tsakaninsu nan gaba ya zama
tarihi,rayuwarsu ta koma kamar yadda take a baya
"Naji dadi da kika kasance yarinya mai biyayya wa iyayenta,ina mai miki kyakkyawan
fatan ba zaki toxarta ba in sha Allahu,biyayyarki zata kai miki da ixinin ubangiji"
da wannan kalaman sukayi sallama,ta fice daga gidan bayan ta samu umma ta roqeta
kan karta gaya mata dangantakarta da anwar,donta tabbatar hakan zai baiwa shahidan
kunya.

Tun a kan hanya ta soma gwada number anwar din,saidai bata sami wayarshi ba
akashe take,da alama yana muhimmin wani abune,dole ta katse kiran ta isa
gida,saidai lokaci lokaci tana gwada number tashi ko xata dace ta shiga.

Tana idar da sallar magariba ta soma shirin barin gidan,umma ta dubeta


"Amma da kin dan jinkirta tafiyar tukunna,saboda garin a dinke yake da hadari ga
iska ta soma kadawa"
"Idan ya sauko bansan ranar da zai dauke ba,anty zubaida kuma zataji shurun yayi
yawa,don ban gaya mata ma ina nan ba"
"Shikenan,Allah yayi miki albarka,yasa albarka a rayuwarku"
"Ameen" ta amsa tana maida qwallar dakeson fitowa,haka ta baro gidan tana tafiya
kamar wadda batason taka qasa,wanda bai sani ba sai ya zaci salo ne ko tana
sane,amma ba komai bane sai tsabar damuwa dake cinta a rai,tana jin yadda hadarin
ya taso sosai sanda takai tsakiyar layin nasu,iska ta dinga kadawa tana ratsa
jikinta,saidai sam bata damu ba,bata damu da ruwan ya sauko ya daketa ba,hakanan
bata damu data koma gida donta samu mafaka ba.

Daidai lokacin da motarsa ke tsaye qofar gidan anty usaina wadda ta buqaci
ganinsa a yau basai gobe ba,yana zaune cikin motar baikai ga yiwa mai gadi horn ba
bare ya bude masa,ya tsaya ne amsa waya,dukka gilasansa a rufe suke ruf kamar yadda
al'adarsa take yawanci idan yana cikin mota,bugu da qari kuma ma sabida iskar
dayaga ta taso sosai,wanda yasan ba za'a rasa qura ba cikinta,gefansa ya kalla
kamar wanda aka fisgi hankalinsa,sai yaga kaman itace ta wuce,yaci gaba da amsa
wayar yana kallon bayanta,tabbas ita dince,amma me take har war haka duhun magariba
ya mamaye gari bata koma gida ba,idanunsa suka ci gaba da kallonta har lokacin data
dan bada tazara daga inda yake,yana shirin janye idanunsa yaga yayyafi ya soma
sauka ta gilashin motarsa,yaso ya dake yaso ya dauke kai ya saka motarsa cikin
gidan anty usaina amma saiyaji kaman umarni,a zafafe yace
"Oh god" yana zare belt din jikinsa,cikin zafin nama da kuma jin haushin kansa da
kansa ya bude murfin motar ya fice.
Yana kuzari da halittar ba daya bace,hakan ya sanya cikin qididdgaggun taku ya
cimmata
"Daga ina kike haka?" A nutse ta waiwayo tana dubansa sanda take gab da qarasa
bakin titi,saita juya da niyyar ci gaba da takawa ba tare data amsa shi ba
"Wai sanda zaki fita ma kin tambayeni ne?,saboda tsabar rinton zunubi?" Kalaman sun
mata ciwo,wato tun yanzu yake nufin xai mulkata kenan?,hakan yasa ta tsaida tafiyar
tata ta juyo ta dubeshi
"Kai waye da don zan fita saina tambayeka?"
"Kinfi kowa sanin ni waye ai ba buqatar na maimaita miki,banason dogon zance wuce
muje na taimaka miki na saukeki,amma kafin sannan idan kina da niqab ki saka a
fuskarki kar mutanen unguwa su ganmu tare su zaci nima dan harka ne" ya kai qarshen
zancan yana dage girarsa duka biyun,wanda hakan ya masa kyau ainun duk da fuskarshi
a murtuke take,sosai kalaman suka fusatata wanda hakan ya sanyata ta juyo gaba daya
ta watsa masa idanunta da suka sake budewa saboda bacin rai,hakan ya tilasta masa
dan qanqance nashi idanun gami da damqe hannayensa dake zube a aljihu
"To hell with your taimako...Allah suturu buqui,har abada bana son
taimakonka,sannan kuma aikin banza kake harara a duhu,da kake gudun kar a ganmu
tare me ya kaika neman dauramin igiyarka,idan da gaske kake qyamata aiya kamata ka
gujeni da gaske ta yadda ko qasa daya ba zaka hada dani ba bare inuwa daya,indai ka
cika kai anwar ne ka aikata hakan" qaramin murmushi ya saki daya sake fitar da
kyansa,ya dage dukka kafadunsa
"Ba zaki taba samun yadda kikeso ba,niba qaramin yaro bane bare kalamanki su
tunzurani nayi miki yadda kikeso,abu daya kawai na sani shine,na riga dana biya
sadakinki,saboda haka ina da power a kanki ko kinqi ko kinso...saboda haka ki wuce
muje" dogon tsaki taja wanda ya ratsa kunnuwansa,sannan ta watsa masa harara ta
juya taci gaba da tafiya,bai fasa binta ba shima har suka isa titi.

Adaidaitan farko data tsaida ya sallameshi da dubu daya yace yane abinsa,na
biyu ma haka,na uku kuwa da yame dattijone yace masa baba kaje matata ce yaji
takeson yi,na bata haquri taki haqura,nan yasa bawan Allahn ya tsaya yana mata
nasiha,inda daga qarshe ya sallameshi da dubu uku ya amsa yana godiya,ta hudu kuwa
ya samu sauayi maiji da tashen girma yaso masa gardama.kan saiya dauketa tunda
itama tana son shiga
"Kana sha'awar xaman gidan kaso kenan?" Harya karkata baki zai masa diban albarka
saiya nutsu ya qarewa shigarsa kallo,tun daga takalminsa,kayan jikinsa zuwa
agogonsa,aibabu shiri yaja abun hawansa ya fece,bacin rai ya taru ya rufeta ruf
sanda ta kalli titin ta ganshi fayau ba wani sauran abun hawa na haya kuma nan
kusa,ta waiwayo zata gasa masa magana ko xataji sanyi,kadan ya rage fuskarsu ta
gwaru,sam batasan yana bayanta ba a tsaye,da alama kuma duk tsahon lokacin kallonta
yake,baya yaja yana bata fuska
"Ke baki da kunya ne?,akan titi kike neman ki rungumeni?,toki maida qwalamarki,ni
ba naki bane" kawai saita fashe da kuka ba tare data shirya ba,saboda ya gama
cutarta,bata ga wani kalma da zata fada masa ba wadda zata rama abinda ya gaya
mata,minti biyu kacal ruwan sama ya soma sauka,ya kalli sama sannan ya kalleta
"A karo na qarshe nake gaya miki ki wuce mu tafi" baya taja saman wasu tayoyi da
masu faci suka tashi suka barsu a wajen ta zauna,ta gwammace ruwan yayi mata koma
meye data bishi kota shiga motarshi,ganin ta zauna dafa'an ya sanyashi juyawa ya
koma cikin layin don dauko motartashi zuwa nan bakin titin dukda yadda ruwa yake
dukansa.

Yana isowa wajen yaga tashinta cikin adaidaita sahu,qaramin murmushi ya sube
masa,wato dama tana da taurin kai kenan?,saiya sake baiwa motar wuta harsai daya je
daya side din na adaidaitan,ya tabbatar ta ganshi sannan ya barsu suka wuceshi,a
baya yaci gaba da binsu har xuwa sanda yaga shigarta gida sannan ya karya kan motar
ya koma gidan anty usaina.

Sanda ta shiga gida baqinciki da takaici ya sake cikata ganin yadda gidan
har baqi yadan samu,hakanan ga kayan amsar lefe a kammale gobe kawai suke
jira,hasina ma ba'a barta a baya ba,ganun zata saka mata ciwon kai da tsokanarta
yasa tayi zarcewarta daki ko tsayawa a wajen batayi ba bare ta zauna,gaban
mudubinta ta tsaya tana kallon yadda ta jiqe gaba dayanta,haushinsa ya sake
cikata,taji kaman ta sake fashewa da wani kukan,duk shi yaja mata,da ta shiga
adaidatan a lokacin daya dace da duk hakan bata faru da ita ba,haka ta ringa cire
kayanta daya bayan daya ta daura babban towel ta shige bandakinta ta hada ruwa mai
zafi tayi wanka.*Alqawarin Allah*https://youtu.be/alR4jOvvQUc

3️⃣ 3️⃣
*Alqawarin Allah*
3️⃣3️⃣

Washegari da wuri tabar gidan fiye da yadda ta saba fita,ko a kamfaninma masu gadi
kawai ta taras,ta bude office dinta ta shiga ta zaun donko mai maita shara ma bata
iso ba.

Sanda aka tashi ta tsaya tunanin inda zata,don tasan wala'alla dai dai
lokacinne ma gidan yake a cike,yankewa kawai tayi ta tafi gidan oga rayyan,ba bata
lokaci ta gayawa mai adaidaitanta ya wuce can da ita.

Sosai taji dadin zuwa gidan,a rayuwa gidan yana burgeta qwarai,yanayin
mu'amalar jama'an gidan,nan wajen raihana ta zauna suka sha hira sosai,sai bayan
sallar magariba sannan tayi haramar tafiya,nan ta cikata da turaruka tana cewa
"Gashi amarya,naji oga yace kin kusa shiga daga ciki,ki fara amfani da wadan nan
kafin lokacin xan kawo miki na amare"
"Hmmm" kawai tace tana dan fitar da murmushin da baikai zuci ba daga fuskarta.

Tun daga harabar gidan zaka san cewa ansha baqi a gidan,bata yarda tabi ta
qofar falo ba saita bi ta qofar baya tayi shigewarta dakinta,kayan hannunta ta aje
ta rage kayan jikinta ta shiga wanka,bayan ta fito ta murza manta mai qamshi ta
saka riga mara nauyi,ta ciro wayarta daga jaka kenan taga miscal din zunnurah,sai
fuskarta ta washe da fara'a,ba bata lokaci tabi kiran,bugu biyu ta daga,abu na
farko data fara shine guda ta sakar mata,bacin rai ya bijirowa shahidan,wato
kiranta tayi donta tsokaneta kenan?,sai kawai ta yanke kiran,ta nufi gadonta ta hau
ta kwanta rub da ciki tana lumshe idanunta,dai dai nan hasina ta turo qofar
"Au yaushe kika shigo?" Banza tayi da ita kamar bata ji ba,hakanan taqi bude
idanunta,don tasan qarshenta itama tention xata qara mata kawai
"Shahida" hasina ta sake fada tana matsowa dab da gadon,ta dora hannunta saman
filon tadan daka,sai a sannan ta ware idanunta tana dubanta
"Bacci nakeji,don Allah ki barni na huta" murmushi hasina ta saki
"Amma na miki jaje da zaki kwana bakiga kayanki ba wallahi,kallo ya barki" qur ta
mata da idanu kafin taja qaramin tsaki ta maida kanta daya barin tana rufe
idanunta,dariya ta sheqe sosai da ita sannan ta juya ta fice tana waqar amarya.

Da sauri ta diro daga saman gadon ta isa bakin qofar ta saka key ta kulle
sannan ta sake dawowa ta kwanta,tana gyara kwanciyar tata tana mita ita daya gami
da jan tsaki lokaci lokaci,rigingine ta kwanta tana kallon roofing din
dakin,idanunta a kulle gam tanason tilasta kanta tayi bacci.

Haka aka dinga mata knocking tana ji ta share,donko hasina yau saidai ta
kwana wani dakin amma ba nata ba,kadaitaka kawai yau take da buqata.

Sai sha daya da wani abu na dare sannan bacci ya soma fisgarta,qarar
wayarta yasa ta bude idanunta ahankali kan wayar dake aje saman cikinta,ta daga
wayar tana dubawa,lambace babu suna,kaman ba zata daga ba sai kuma ta daga kana ta
kara a kunneta gamida yin sallama,can qasa taji an amsa sallamar har bata tantance
muryar waye,shuru ya ratsa da wasu sakanni
"Nuradden" ta canki sunan
"Shahida,na rasa ta ina zan fara koyawa kaina haquri dake" idanunta ta lumshe tana
jin bacin rai na ratsata
"Kayi haquri noradden,duk ni na jawo mana komai,da ace banyi jinkirin hanaka zuwa
gidanmu ba da guni hakan duka bata faru ba"
"Ki tayani addu'a kawai,Allah ya yayemin,don ba lallai bane na daina sonki" daga
haka wayar ta katse,a sanyaye ta ajiye wayar ta mirgina daya barin nata,harga Allah
bata tausayin kanta kamar yadda take tausayin nuradden din,ya riga ya fada da
yawa,ta kuma son ciwo da radadin soyayya,musamman a sanda ka rasa abinda kake
tsananin so ka kuma saka ranka dashi,a hankali kalamanshi suka fado mata,baya neman
yaradarta,bata cancani ta rayu cikin farinciki ba ta zabi wanda takeso,zai aureta
ne don ya nuna mata ya isa,lebanta na qasa ta cije tana rarrabe maganar da abinda
yake nufi,auren manufa zaiyi da ita kenan?,zaiyi ne don cimma wani boyayyen nufi
nashi?,lallai zata nuna masa yayi ganganci,akwai banbanci tsakanin da da yanzu,ta
jima ahaka tana saqa abubuwa da yawa tare da tunawa da al'amura masu yawa kafin
bacci yayi nasarar saceta.

Washegarima kusan fitar wuri tayi,tana tsaye a kitchen tana shan ruwan dumi
anty zubaida ta taras da ita
"Ba zakiga kayan ba kenan zaki fita" agogonta ta kalla sannan ta sauke hannu
"Sauri nake anty"
"Hakan yasanya jiya nace a tasoki ki gani ai" baki ta tabe a fakaice tana tuna
haushin da hasina taso tura mata ajiyan da yadda ta matsanta mata,kayan da bataga
abinda anwar zai zuba a ciki da zasu burgeta ba
"Idan na dawo na gani,saina dawo anty" ta fada cikin hanzari bayan ta dauki jakarta
data aje ta rataya tana ficewa da hanzari,kasa cewa komai anty zubaida tayi sai
binta da kallo kawai da tayi harta fice sannan ta girgiza kanta tana tadi ita da
zuciyarta,ko ba'a fada ba tasan ganin kayanne bata sonyi.

Kwana uku tana cewa anty zubaidan zata gani amma bata yarda taje inda sukebama
bare ta gani,dole ta gaji ta zuba mata idanu,a haka har akaci kwana goma sha
biyu,ga tsammanin anty zubaida shahidan zata dauki hutu wajen aiki,saidai taga ko
ajikinta bata fasa fita aikin na,sake qara mata kwana biyu tayi taga ko zata dakata
da fitar,saidai ranar daya rage biki saura kwana bakwai cif da safe anty zubaida ta
sameta a falo tana karyawa ta gama shiryawa tsaf,kallonta sosai take taga da gaske
take fita aiki zatayi?,kallon harya sanya shahidan itama yin sak tana kallon anty
zubaidan,saidata soma dan tsuke fuska sannan tace
"Ina zaki haka da safe?" Tambayar tadan baiwa shahida mamaki,ko maqota sunsan inda
taje zuwa daga safiya zuwa yammaci bare anty zubaidan,don ita bata kawo tambayar
tata nada alaqa da aurenta ba
"Office mana anty" ta fada cikin son gamsar da ita,kai anty zubaida ta girgiza
"Bakisan aurenki saura kwanaki bakwai ba ko lissafi ne ya qwace miki?,ko kuma duka
kina sane saboda kinha na zuba miki ido ne?"wani abu ya taba zuciyar shahidan,ba
zancan data tsana a yanzu irin zancan aurenta,tana sane saura kwanaki bakwai su
qullashi to amma ita meye nata a ciki?,me zata zauna gida tayi
" to anty,ni menene nawa a ciki?,me zan zauna nayi a gida?"
"Eh babu komai naki a ciki tunda zubaida ce zatayi aure,so kike duniya ta zagemu
ko?,tunda kike kin taba ganin amarya budurwar da aka aurar salin alin?,to banason
sakarci,babu ruwana da wani abu daya taba gittawa tsakaninki da anwar ni aikina
zanyi kawai,rawata zan taka,saboda haka ki koma ciki daga yau zansa abban huda ya
dauka miki excuse,su baki hutun sati uku" kaman ta zunduma ihu haka taji sanda anty
zubaida ke maganar,abinda ta dauka wasa ne gashi yana neman tabbata,ba damar musu
da ita saboda yadda ta tsare gida sosai,haka shahidan ta soma takawa don komawa
dakinta
"Eheennn...jimana" anty zubaida ta sake fada,saita tsaya gami da waiwayowa tana
dubanta,sai data kallo agogo sannan tace da ita
"Qarfe sha daya na rana zamu fita dake,ki zauna cikin shirin" kai ta gyada kamar
kazar da qwai ya fashewa cikin cikinta,haka ta dinga tafiya harta isa daki,ta
watsar da duka kayanta kanta na daukar zafi,me yasa anwar yake son ya soma da
nasara da sa'a a kanta?,me yasa anwar ya dawo cikin rayuwarta bayan bata da
buqatarsa?,haka ta dinga yiwa kanta tambaya ranta na zafi.

Sha dayan da 'yan mintina suka fita ita da anty zubaidan kawai,bata tambayeta
ina zasuje ba har saida suka isa gidan sannan ta fahimci wajen gyaran jiki ta
kawota,tamkar wata doluwa haka ta dinga bin anty zubaida da kallo har suka gama
gaisawa da matar da gabatar da shahida wajen matar a matsayin amaryar da za'a yiwa
bikin
"Kai tubarkalla masha Allah,wannan badon hausawa suna cewa idan kana da kyau ka
qara da wanka ba ai bata buqatar komai,saida nasan gyaran ba qaramin hawanta zaiba
zubaida" tana jinsu harta gama surutunta ta soma hada kayayyakin gyaran jikin ta
buqaci shahida ta sauya wani zani na daban data dauko.mata,fuska ta bata tana duban
anty zubaida ranta na baci ta wani gefan,yanzu saboda anwar ne aka kawota nan wajen
"Anty,don Allah abar abunnan,batamin kaya kawai zaiyi" dago idonta tayi daga
wayarta da take dannawa ta watsawa shahidan harara,hakanan tana ji tana gani ta
sauya zanin aka shiga mata gyaran,bakinta gum tana bin matar da kallo kaman ta
mangareta saboda yadda takebin fatarta da kayyakin tana shafeta dasu.

Tana ganin kawai bata lokaci da bata kudi ne.

A qalla sun kusa kashe awa biyu cur ana abu daya,bin jikin nata take da kallo
yadda ya soma wani santsi sulbi da sheqi na musamman,tabe bakinta tayi data tuna
saboda me akayi mata,sai taji gyaran sam bai burgeta ba,tana maida kayanta wani
qamshi na tashi daga jikinta duk sanda ta motsa,turarukan qarshe da aka murje mata
jikinta dasu.

Basu jima ba suka isa gida,a falonta zauna cikinsu huda wadanda ke
kallo,faruq ya kalleta
"Anty harkin fara canzawa,kaman bakeba akan dazun da kuka fita'binsa tayi da ido
kawai ba tare datace komai ba,kafin ta gama tunanin da take ta jiyo muryar huda
"anty...zamuyi kewarki,tafiya zakiyi yanzu ki barmu?"ta qarasa fada a shagwabe
kaman zata saki kuka,nan take ran shahida yaso ya sake baci da tuna hakan da
tayu,anty zubaida ce ta katse komai tana tambatar faruq me suka dafa musu,yace
white rice ne bazai iya miya ba,hararsa tayi
"Daga kai har haidar din a rasa wanda zaiyi miya?" Huda na gefa na musu dariya,kai
ya langabar
"Allah ummi shi yasa nace ki samo mai aiki fa" tsaki taja sai shahida ta miqe
"Bari na hada" tafurta tana yin gaba zuwa kitchen.

Kayan miya ta diba ta soma gyarawa sannan tayi blending,dukka rabin


hankalinta da nutsuwarta nakan tunani,data hada miyar saita zauna cikin kitchen din
tana duban agogo,tasan zuwa sanda zata gama hudu tayi saita da alwala kawai gaba
daya.

Miyar na soyuwa haidar ya shigo yana shaida mata tazo inji anty zubaida,saita
rage wutar can qasa yadda ba zata kama ba kafin ta dawo ta fito zuwa falon,a zaune
ta sameta da tulin kaya a gaba da alama sabbabi dinkuna ne tana dagawa tana kalla
gami da ware wasu gefe
"Kije waje kinyi baqo"gabanta yadan fadi,tadan bata fuska
" waye haka da la'asar din na"
"Ban sani ba nima,idan kinje zaki gani" hakan yadan kwantar mata da hankali jin ba
wanda ta tsani ganin bane,nan kan kujera ta dauki mayafinta data dawo dazu dashi ta
yafa sannan ta fice.

Matashin saurayine mai kyau da aji tsaye jikin motarsa,sanye yake da shadda
riga da wando dinkin tazarce,hankalinsa duka nakan wayarshi a haka ta kusa
cimmasa,bata sanshi ba amma sai take ganin tasan fuskar a wani waje daban ko can da
dadewa,sallama ta masa ganin baisan da isowarta ba,ya daga kai da hanzari yana
amsawa fuskarsa ta fadada da fara'a
"Barkanki da yamma kin wuni lpy"
"Lafiya alhmdlh" ta amsashi a taqaice
"Ya mutanen gidan kowa da kowa lafiya?"
"Lafiya qalau" ta sake amsawa tana mamaki ina ya santa tare da zurfafa tunaninta ko
zata iya tuna a inda ta sanshi,murmushi ya saki
"Nasan baki sanni ba,ni sunana muhsin,aboki kuma aminin anwar" lokaci daya maganar
ta sauka a zuciyarta,sai yanayin fuskarta ya soma sauyawa,fuskarta ta soma
tsukewa,duk da haka tadan dake hadi da qoqarin sassautawa,shima dubanta yake yana
karantar sauyawar yanayinta lokaci kadan,bai sake cewa komai ba ya bude murfin
motar da yake jingine a jiki ya zura hannu ya ciro wata babbar envalope da qarama
ya miqa mata,kallon envalope din tayi sannan ta dawo da kallonta kanshi alamun
neman ba'asi
"Katin gayyata ne na dinner ko zaki gayyaci qawayenki,wannan kuma kudine ko zaki
buqaci wani abu" kai ta girgiza tana danja baya,a fuska tana ganin mutuncinsa amma
baya ga haka so take taci masa mutunci ne shida wanda ya aikoshin,amma duk da haka
ba zata kasa bashi saqo ba
"Ka maida masa dukkan kayansa,ka gaya masa aurensa baya buqatar wani shiri tunda a
shiryensa aka qulla shi,kudi kuwa baiyi kudin bani ba a yanzu har zuwa nan gaba,ka
gaida na gode" daga haka ta juya zuwa cikin gidan tana takawa a nutse,da kallo ya
bita qwaqwalwarsa cunkushe da tunani da mamaki,kullum kwanan duniya sake mamaki
yake kan meye haka mai girma daya raba kwanunansu ya tarwatsasu haka zuwa pieces
suka kasa kuma daidaita tsahon shekarun?,amsar daya kasa samunta kenan haryau daga
wajen anwar duk da sanda rabuwar ta afku shine mutum na farko daya sha wuya da
anwar din kafin rayuwarshi ta daidaita,saiya xagaya ya bude murfin motar tasa ya
shiga yana tuna yadda sukayi da anwar sanda zai ya shirya kudin da katin yace zai
kaimata da sunanshi,har kusan haurawa sukayi kan koda zaikai din yakai amma bada
sunanshi ba.

Iska ya furzar daga bakinsa lokacin da muhsin ke zaune kan daya daga cikin
kujerun office din yana sake tambayarsa wanne laifi ya aikatawa shahida haka?,ya
dubi envalope din daya fita dasu ya dawo dasu kamar yadda suke,hakan na nufin bata
karba ba kenan
"Bata karbi kayan daka kai din ba kenan?" Anwar ya tambayi muhsin kai tsaye yana
dubanshi,kai ya kada
"Ni duk ba wannan na tambayeka ba,inason gyara wannan barakar ne shi yafi
damuna,banason alaqar taci gaba da tafiya a haka"
"Me ta gaya maka sanda kaje?" Ya sake jeho masa tambaya ba tare daya damu da nashi
bayanan ba
"Batace komai ba" murmushin yaqe ya saki,takowa yayi kusa dashi kujerar dake
fuskantarsa ya zauna
"Ta fadi maganganu a kaina,takuma ce ba zata karba bata buqata right?" Idanunsa
cikin na muhsin ya fada,kauda idonsa muhsin yayi saboda shi kansa wasu lokutan
anwar na masa kwarjini da yawa
"Kaga malam nidai bance maka haka ba,banason tone tone" miqewa yayi yana jijjiga
kai
"Ta fada,na santa kamar yunwar cikina" gaban envalope din ya qarasa,ya farke dayar
ya cire kudaden ciki ya janyo locker din office din nasa ya zubasu ciki,sannan ya
janyo daya locker ya ciro wasu ya musanyasu dasu ya maidata ya manne muhsin na
kallonsa,ya kwashesu duka ya aje masa key saman teburinsa
"Idan ka gama ka rufe ko ina" daga haka ya juya yana takawa sannu sannu zai fice
daga office din
"Wait mana malam,ina zaka je?" Murmushi ya jefa masa ya fita ba tare daya amsashi
ba.

Gidansa ya soma isa ya bude sashensa ya shiga,ya aje kayan hannunsa,bandaki


ya shiga ya tara ruwan wanka mai dumi ya sake wanka sannan ya nemi abinci yaci ya
qoshi,wardrobe dinsa ya bude ya zabi kayan da yaje gani sun dace da irin wannan
lokacin ya sanya,ya tsaya gaban mudubi yana taje kansa gami da kallon kansa yadda
kayan suka amsheshi,tuna abinda ya faru tsakaninta da muhsin yayi,saki yaja,wato
ita mai taurin kai ko?,har yau bata kallon laifinta sai wani take dorawa alhakin
faruwar komai ba tare data duba nata laifin ba,aikawa yaso yi direct inda dole ta
karba saqon,amma hkanan yaji yana son yaje yaga hawayenta ya takaleta ya kuma tsone
zuciyarta,saiya aje cumb din yana daura agogon fata sannan ya zauna ya daura
takalmansa ya feshe jikinsa da turare ya dauki key din motarsa ya fito.

A hankali yake tafiyar kaman bazaije ba,karon farko da zai fara zuwa gidan
anty zubaida kenan,yadan yi nauyi a hanya hakan yasa bai isa ba sai qarfe shida
mintina hamsin suka rage kenan a yi sallar magarib.

Maigadin gidan anty zubaida ne ya iso ya bashi hannu don suyi musabaha,cikin
tantama yadanyi jim don yana ganin bai kamata suyi hannu da hannu ba
"Mu gaisa mana abokina,bakason ladar ne" da sauri ya miqa masa suka gaisa
"Inason magana da wata yarinya shahida a gidan nan ne" cikin washe baki yace
"Au,kaddai kaine angon?" Murmushi kawai yayi sannan ya sake cewa
"Idan ka shiga matar gidan zaka sanarwa zuwa na,sannan ka turomin faruqu ko haidar"
"Toh...toh" ya fada yana juyawa zuwa ciki.

Sanda saqon kiran ya sameta tana daki tana shiryawa bayan ta gama mitar
wankan turaren da anty zubaida ta kafa nata dokarshi,turaren na nata dadi da qamshi
amma tuna dalilin yinsa ke qona mata rai da dagula mata lissafi,tsaki taja sanda
huda ta gaya mata ana kiranta,ta shiga mita
"Wai wanne irin kirane da baqi haka tun dazu ba za'a bar mutum ya huta ba?,haka
kawai kana zaman zamanka daada ta tada zaune tsaye cak,ni wallahi na gaji da wadan
nan abubuwan,daga wannan sai wancan?" A haka ta shirya ta zari hijabi ta fito
"Baqon na waje ai" anty zubaida tace da ita sanda taga ta tsaya ta mata turus,haka
ta juya ta fita kaman zata fashe.

Faruq ta soma hangowa cikin dakin saukar baqi na gidan baki na motsi da
alama hira yake zubawa,harara ta zabga masa duk da bai ganta ba,a haka ta isa ta
yaye labulen,tare idanunsu suka sauka cikin na juna,yawun bakinta ya tsaya
kowannensu na kallon dan uwanshi ba tare daya dauke ido ba,gani yayi kamar ba
ita,fatarta ta sake sauyawa kyanta kaman an matso shi,qamshinta ya soma cika
wajen,shima kwarjini taga yayi mata,shigar ta amsheshi,yayi kyau ya sake zama
cikakken mutum da hankali da ilimi suka ratsashi,ita ta soma janye idanunta,ranta a
hade tsaf ta taka zuwa ciki tana duban faruq,saiya miqe,anwar yace
"Zan nemeka kafin na wuce kada kayi nisa"
"To yaya" ya fada yana ficewa,sai da taga fitarsa sannan ta zauna hannun kujerar
dake a dab da bakin qofar fita,tanason tsareshi da ido donta karanci me ya kawoshi
amma batasan me yasa takejin rashin qwarin gwiwa ba,ta maida idanunta kan tafin
hannunta tana murzawa ba tare data ce masa uffan ba,hakan ya bashi damar kafeta da
ido,ya soma kallonta tun daga yatsan qafarta zuwa saman kanta,yana jin wasu
tagwayen abubuwa na fada cikin zuciyarsa,daya nason yaqar daya gami da
rinjayarsa,inda daga qarshe dayan yayi galaba,saiya runtse idanunsa yabar kallonta
saboda wani bacin rai dakeson shaqeshi,kullum kwanan duniya yana son sasautawa
kanshi,yana son ya daina ganin baqinta da baqin abinda ta aikata,yana son abinda
idanunsa suka gane masa da hotunan daya gani su bace daga idanunsa ko zai samu
salama da rangwame amma hakan ya faskara,sai komai yayi kaman zai goge saiya sake
dawowa sabo fil a ransa.

Walwalar da yake jin kaman zata samu a ruhinsa ta dusashe,sauran faragar


fuskarsa ta bace bat.

Zaman kurame ne yaci gaba da wanzuwa tsakaninsu harna tsahon wasu mintuna,sai
daya gama zamanshi don kanshi sannan ya miqe,cikin wani taku ya isa dab da ita ya
tsaya akanta,kana ya ranqwafa gefanta har tana iya jiyo qamshin ya aje envalope din
hannunshi,ba tare daya dago ba yace mata
"Baki iya gaisuwa ba saikace a gidan mashaya inda kowa yake ogan kanshi,karki
tsammaci xaki gidana da wannan dabi'ar ki tsira,ga saqon da muhsin ya kawo miki
daxu kika maidashi nina dawo dashi,idan kin isa karkiyi amfani dashi yadda ya dace
kiga yadda zata kaya mana nidake,tunda na fahimci cikin halayen da kika koyo kala
daban daban harda taurin kai ko?,good....inason wannan sabon halin naki,idan kin
tashi gayyatarki karki sake ki kwaso min tarkacen 'yan maye,ko tarkacen qazaman
tsaffin samarinki" daga haka ya dago yana shirin wucewa zuciyarta taje iya wuya,ta
kasa daurewa
"Idan ba haka bafa?,me zakayi?" Ta fada a tsiwace cikin fushi da fusata,saiya sake
dawowa gabanta ya tsaya,ya dubeta na wasu mintuna sannan ya saki murmushi
"Ki aikata din sai kiga sakamakon" miqewa tsaye tana masa kallon tara saura kwata
sannan tace dashi cikin salo na masifa dake cin zuciyarta
"Baka isa ka sakani abinda banyi niyya ba,baka isa komai ba idan ma kana tunin ka
isa" murmushi ya sake saki wannan karon mai sauti,yadan buga qafarsa sannan yace
"Ko a haka aka tsaya ai inga irin tawa isar ko?,hukuncin da zan miki ba isata kawai
zai nuna miki ba,izzar aure da izzar anwar namiji"
"Namiji shine zai tsaya takara da abokan adawarshi ya kuma samu nasara,ba wanda zai
wafta koya biyo ta bayan gida ba,koya taka wani tsani don kaiwa wannan bigiren,ka
daina batawa kanka lokaci wajen kiran kanka da namiji,ba namiji bane kai saidai
mata maza" idanunsa ya qura mata qir sanda take maganar cikin dakiya da rashin nuna
tsoro,hakanan bilhaqqi da gaske,ganin takai aya saiya soma takowa inda take
tsaye,ta tsaya cak don ganin iya gudun ruwanshi,saidai harya iso gab da ita bai
daina takowa ba,hakan na nufin zai hade gap din dake tsakaninsu kenan,don haka ta
soma ja baya ga zatonta zai tsaya amma ina,bai barta ba sai daya tabbatar ya hada
bayanta da bango,qafarshi dake saye da takalmi saman tata qafar wanda yana iya jin
zafi zafi na tudun takalminsa daya take mata qafa,kusancin dake tsakaninsu yayi
yawa,tana iya ganin fuskarsa tarwai wadda kyau ya cikata gamida iya gyara,idanunsa
sai suke juye mata irin na anwar dinta na wancan lokacin sak,janye qwayar idanunta
tayi gabanta na bugawa da sauri da sauri,tsoro da fargabar me zaiyi mata na
shigarta,saitaga ya daga hannu kaman yana shirin marinta,ta runtse idonta da sauri
tana wassafa me zata masa ita bayan ya gama marin nata,ji tayi yaja baya da sauri
cikin kaushi yace
"Sai na saki kinyi nadamar lafazinki,tsautsayi kuma yasa bakiyi yadda nace miki ba"
daga haka ya juya da sauri sauri ya fice daga dakin,cikin hanzari ta daga murya
"Idan ka isa ka tsaya mana ka dakenin kaga yadda akeyinta" gab da zai fice ya
waiwayo yace
"Aiba a gidan syrup muke ba" kalmar ta tsaya tana fassarawa,take wani abu ya cushe
mata maqoshi,cikin qanqanin lokaci hawaye ya ballewa idanunta,tana jin zafi a
zuciyarta duk sanda yayi wani lafazi dazai iya tuna mata da abinda ta aikata a
baya,sulalewa tayi ta zauna a wajen,ba shakka ba'a bari a kwashe duka,shaye shaye
ashe wani tabone da tambarinsa bai barin jikin maishi?,koda kowa ya manta ba'a rasa
burbushi,ta jima a wajen tana jin ciwo kala kala kafin ta miqe ta fice daga
dakin,ko kallo envalope din basu isheta ba bare ta dauka.

A falo anty zubaida tace ta tsaya ta duba dinkunanta na biki wanda ita batasan
ankai bama,don ko kayan har yau bata kalla ba bare ta gane me takeso a ciki har
tayi tunanin kaiwa dinki?,bata cikin yanayin da zata iya zama cikinsu saboda haka
tabawa anty zubaidan uzurin kanta na ciwo zata duba zuwa safiya da haka ta wuce
dakinta.

Washegari sun fito da anty zubaida zata koma gidan gyaran jiki tanata kumbure
kumburenta da mita cikin ranta na yadda aka takura mata ba gaira babu dalili faruq
dake sharar dakin da uncle hisham ya sakashi sabida zaiyi baqi ya fito da envalope
din yana miqawa anty zubaida
"Anty wannan a dakin na gansu,kaman na anty shahida ne don jiya na gansu a hannun
uncle anwar" hanu tasa ta karba sannan ta waiwaya tana duban shahidan
"Me yasa kika barsu a dakin?,abinda kikayi dai dai kenan?" Saita langabe kai,ita
abun goma da ashirin,komai tayi batayi dai dai ba,saita saka hannu kawai ta amsa
suka wuce,suna shiga mota ta kasa daurewa ta saki kuka tana kife fuskarta saman
cinyarta,anty zubaida batace komai ba saidai ta dora hannunta saman bayan

3️⃣ 4️⃣
shahidan,saida tayi kukan na wani lokaci sannan anty zubaida tace mata.......
3️⃣4️⃣
"Abubuwa da yawa da mukeso muke qwallafa rai a garesu ba alkhairi bane ga
bawa,kiyi qoqarin rage wannan kaifin qiyayyar kamar yadda annabi yayi umarni saboda
kada ta juye miki zuwa soyayya mai zafi daga baya,kiyita addu'a Allah yasa abinda
zai faru dake ya zama shine mafi akhairi a rayuwarki duniyarki da lahirarki" da ire
iren wannan nasihar suka isa wajen gyaran jikin.

Anty zubaidan ita ta karbi envalope din ta bude taga abunda ke ciki,saita
amsa ta aje tana jiran hasina tazo ta raba cikin 'yan uwa,don shahidan a yanzu bata
da wata qawa banda zunnurah da take sokoto,tunda abun ya faru gaba daya ta cure
qawa daga tsarin rayuwarta,saidai gaisuwa kawai ta mutunci,sabida card din bashi da
wani yawa sosai,da alama dinner ce da akayi selecting iya adadin mutanen da zasu
shiga.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Gaba daya ta susuce cikin kwanakin ta fita hayyacinta,idan ka ganta saika dauka
ba ita bace ba,gashi daga mummy har abban nata ba wanda ya sake bi ta kanta koya
tanka mata dangane da hukuncin data yanke na ba zata auri anwar ba bare ta fadi
abunda yake ranta ko zataji dadi,kullum kwanan duniya kamar ibada kuwa saita kira
number mima sau babu adadi amma tana a kashe amsar kenan kullu yaumin,ko fita yanzu
ba kasafai take ba,kishin anwar da sauran kwanakin daya rage ya zama mallakin
shahida su take lissafi,sanda taga kwanakin na qaratowa kuma bata da madafa ko
makoma saita soma dana sani da nadama tana tuhumar kanta anya kuwa batayi kuskure
ba?,anya bata aikata ba dai dai ba?,da wannan tunanin ne a yau daya rage saura
kwanaki hudu biki ta sake jan wayarta tana gwada lambar mima karo na wajen dari
biyu da wani abu.

Kaman a mafarki taji ta shiga,saita miqe zumbur tana kaiwa da kowawa ita kadai
tana fadin
"Ki daga mima,ki daga ki daga don Allah" gab da zata katse ta daga din kuwa
"Ina kika shiga don Allah?,ina kika tafi?,don Allah duk inda kike ki dawo a yau"
"Lafiya?"
"Ba lafiya ba mima,nace na fasa auren anwar saboda zai aureni nida shahida mima
kina ina,ina buqatar taimakonki"
"Shahida kuma?" Ta tambaya cikin mamaki
"Eh ita dai" wani malalacin murmushi mima ta saki sannan tace
"To ai kinyi dai dai da kika ce kin fasa,hukuncinki shine dai dai"
"Kaman yaya mima,nifa ina qaunar anwar har yanzu ina jin soyayyarsa cikin raina,ina
jin bazan iya rabuwa dashi ba" dan bata rai mima tayi sannan tace
"Duk da haka dole kiyi haquri ai yanzu bake ba shiga gidan saikin shirya,sabida
haka kici gaba da walwalarki har zuwa sanda zan dawo karki damu komai zai gyaru
yadda kikeso"
"Ina cikin damuwa mima,burina yanzu kawai shine na mallaki anwar,sai zuwa yaushe
zaki dawo"
"A'ah fa,aikina kinsan babu gaggawa sai biyan buqata,saboda haka idan gaggawa kike
kawai ki nemi wata mafitar bani ba"
"Shikenan saikin dawo"
"Yauwa...am idan ba damuwa kimin transfer mana,ina da buqatar wasu yan kudi"
"Babu damuwa,kaman nawa kike da buqatar?"
"Dubu dari uku ma sun isheni in jalauta"
"Ohk,accnt dina ya samu matsala bazaiyiwu inyi miki trasfer ba,amma zanje banki na
tura miki"
"Shikenan saina jiki,karki wuce la'asar"
"Ba case" daga haka suka aje wayoyin,duk sai taji salama na shigarta tamkar
matsalarta ma ta yanke kenan tunda sukayi magana da mina,saidai kuma har yanzu
zuciyarta cike take da kishin anwar da tsanar shahida,da kuma jun babu dadi duk
sanda ta tuna kwanaki qalilan ya rage su zama ma'aurata,amma idan ta tuna mima
tasan cewa data dawo komai yazo qarshe,don so take kafin ita ta shiga gidan ta fara
yin waje da shahida.

Kai tsaye ta sauqo qasa don zuwa kitchen ta samu wani abu da zata ci,yunwar
data tarawa kanta tsahon satittika sai yanzu take taso mata,a falo taga mummyn
tata,saita bi nafisan da kallo ba tare data ce mata komai ba harta shige kitchen
din,lokaci daya ta fada ta rame,yarinyar Allah ya zuba mata taurin kai da
kafiya,duk sunsan tana son anwar amma ba yadda suka iya sabida ta nuna ba zata
aureshi ba,sun fita jin zafin rabuwarsu sabida sun shaida nagartarsa,basu da sauran
abunyi bare su tursasata tunda basu zasuyi mata zaman auren ba.

Sai data ci ta qoshi sannan ta shiga tayi wanka,tayi 'yar kwalliya sama sama
ta dauki muqullin motarta da kudaden da mummyn ce ta bata ajiya ta irga dai dai
yadda mima keso ta fita bankin donta tura mata.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

File na qarshe ya qarasa dubawa ya rufe yana fadin wash gami da miqar da
bayansa jikin makarin kujerarsa da yake kai yana cire agogon hannunsa gamida ajeshi
gefa,duban muhsin yayi
"Uhmm ina jinka" ba tare daya ce komai ba ya ciro wata 'yar guntuwar takarda ya
tura gaban anwar din,sannan ya aje wata a tsakiyarsu,wadda ya tura masan ya dauka
yana dubawa,sai daya gama karantawa sannan ya kalli muhsin alamun yanason qarin
bayani
"List na kudin dinkin kayan angwancinka ne,bazan biya wannan ba kai zaka biya"
qaramin murmushi ya saki,gaba daya muhsin din ya hana kanshi sakat kaman shi zaiyi
auren,hatta shi kansa sabbin kayan daya dinka saboda auren suna da yawa
"Ni malam dama bannce maka ina buqatar sabon kaya ba,saboda haka kayi sadaka" shima
murmushin ya saki yana hararshi
"Baka isa ka sani sadakar da babu niyya ba,nadai ranta maka kuma zaka biyani"
dariya ya dan saki yana daukar ruwan da muhsin din ya zuba baisha ba ya soma sha a
hankali daidai sanda muhsin ya sake tura masa daya takardar daya aje a
tsakiyarsu,aje ruwan da yakesha yayi yana sake dubanta
"Oh god,muhsin wai kana nufin da gaske dinner zakuyi?"a kaikaice ya kalleshi
"au...kai da kana nufin an buga katinne kawai saboda burga ko wani abu?,dinner ne
na gama tsara komai ka duba gashinan ka gani,ka saka mana sunayen qawayen amarya"
aje takardar yayi yana furzar da iska daga bakinsa
"Sai kaje ka tambayeta ai,nikam ban sani ba,ina zaman zamana lafiyar Allah zaka
tayarmin da zaune tsaye ka tsiri hada dinner"
"Aikin banza aikin wofi,qaryar banza,ina cewa duka kwanakin nan saboda auren nan
gaba daya ka canza,walwarka da fara'arka,duk wanda ka gani bakinka har qeya yake"
tilas muhsin din ya sanyashi sakin dariyar da bai shirya ba
"Bakasan dawar garin ba muhsin,kasan auren dole?" Ya tambayeshi bayan fara'ar
fuskarsa ta ragu
"Qwarai kuwa"
"Toshi zanma kaina" dariya sosai muhsin ya fashe da ita yana kallonsa
"Gayawa qaramin yaro da baisan abinda yakeyi ba...waima don Allah,ka gayamin meye
ya hadaka haka da shahida,shahidan da a baya duk duniya baka da kamarta?"
"Tsarin Allah ne" ya bashi amsa ba tare daya dubeshi ba,fuskarsa na bayyana akwai
radadi da ciwon dake cikin zuciyarsa,sai muhsin yayi shuru yana dan karantarsa
kafin daga bisani yace
"Duk abinda zakayi kabishi a hankali anwar,ba dukka zatone yake zama gaskiya
ba,daukan hukunci cikin zafi yana haifar da dana sani,ka dauki komai da sassauci
karka yarda ka tsaurara dayawa,don tsauri bai har da komai sai cakudewar lamura da
rashin samun gyara ko ci gaba" baice komai ba ya miqe yana rufe sauran takardun
gabanshi sannan ya nufi toilet dake cikin office din.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Duk wani abu dake faruwa ganinsa take tamkar mafarki ne bawai gaske ba,tuni ta
sare taci gaba da zubawa sarautar Allah idanu kawai,cikin kwana biyu da suka biyo
baya gidan anty zubaida ya soma samun baqi 'yan biki,komai tana yinsa ne kan tsari
da shirin anty xubaida,saura kwana biyu a fara biki akaje akayi mata jeranta,sanda
su hasina suka dawo suna yaba kyan gidan tsarinsa da kyansa,itadai nata ido ne da
kunne,shiri sukewa bikin sosai takowanne fanni,baga gidansu ba baga gidan anty
zubaida ba,ba daga katsina ba,kaman dama kowanne jiran lokacin auren nata
yake,hakan baya rasa nasaba da yadda take mutum mai kirki ga kowa,sannu a hankali
kuzarinta ya dinga raguwa,karsashinta ya dinga raguwa,bata sake sallamawa ba sai
ana ya gobe za'a fara gudanar da bikin sanda ta dawo daga qunshi,wani irin qunshi
ne da aka shimfidawa hannu da qafarta kai kace zanene saboda kyau da haduwarsa,ba
lallen ba gaba dayanta ta canza,duk wanda ya kalleta saiya kuma,gyaran kuma ya hadu
da kwarjinin amarci saita zama kamar wata zara cikin wata,duk da yadda take fama da
rashin kuxari da walwala.

Ranar da za'a yi kamu da wuri anty zubaida tasa ta koma a qarasa gyaran jiki
na qarshe,itada hasina da wata coursin dinta suka je,daga can suka biya gidansu
saboda daada data sauka a can tace tana son ganinta.

Gidan nasu ma baqine kota ita kasancewar wannan shine karo na farko da
ummantata zata aurat da diya,tun daga soro aka soma sakin mata guda,wanda hakan
yasa taji kanta ya sara,tadan tsuke fuska suka wuce ciki,a rumfa suka samu
dadan,duk da tsufarta ita dinma amma sai data lallaba jan lalle wanda yayi mata
kyau,tana zaune cikin matan 'ya'yanta da jikokinta shahida da hasinan suka
shiga,guri daya ta samu ta zauna don ba zata iya maida tsokanar da ake mata ba da
kiranta amarya da ake faman yi,tana jinsu har sukayi suka gama suka qyaleta.

Da daya da daya kowa ya fice ya barta a rumfar daga ita sai dadan,ta dubeta
sosai gami da gyara zamanta tana kallonta
"Abinda yasa nace a turomin ke tun yanzu saboda bani da tabbas din xamu samu zama
kamar haka idan kuka fara wadan nan bidi'o'in naku" baki shahida ta tabe,su waye a
gaba idan ba goshi ba da zata ce haka,duk basu suka tada aurenba,suka tayar da
zaune tsaye,sosai daada ta zama cikim seriouse ta soma magana tana duban shahida
"Kafin rasuwar mahaifinki Allah shine shaida cewa ya baki tarbiyya bakin gwargwado
ya baki duk kulawar data dace,hakanan mahaifiyarki itama ta baki tata tarbiyyar
bakin gwargwado,abinda nakeson cewa shine,kinar gani ko karki duba cewa anwar mun
lanqwasaki ne kan dole kin aureshi,ba ruwan Allah da wannan,yi masa biyayya ya zama
miki wajibi,dole kiyi idan yace dole ki bari idan yace,sauke dukkan haqqinsa ki
sani ya rataya a wuyanki babu fashi,ruwanki ne kije ki masa tsiya ruwanki ne ki
kyautata,koma meye kikayi abinda za'a soma fada shine tarbiyyar gidanku ce ta uwa
da uba kenan,idan kinso kija musu yabo,idan kuma kinso kija musu zagi,Kiyi
biyayyawa mijinki sauda qafa,yi nayi bari na bari,anwar ya riga ya zama mijinki
Alqawarin Allah ne wannan daya cikashi"a fakaice ta sake tabe baki sannan ta miqe
tsam tana cewa
"To,na gode" ta soma yin gaba zata fice daga falon,a tsakar gida ta samu hasina
tana tsakiyar mutane suka kwasar cafta,da hannu kawai tayi mata inkiya ta
fice,hasinan ta tashi ta bita bayan ta yiwa su umma sallama.

Qarfe hudu na yammaci harabar gidan maqotan anty zubaida ta cika ta tumbatsa
da jama'a,wanda shahida dake zaune cikin dakinta anty zubaida ta kasa ta tsare mai
kwalliya na mata takejin surutun jama'a da hayaniyarsu har tsakiyar kanta,babbar
harabar gida ce wadda aka qawata da decoration me kyau da tsari wanda ya dace da
sutturar da amarya zata saka,kota ina mutane ne dangin shahidan na uwa dana
uba,manya da yara da yammata,wajen a tsare yake duk da yawan mutanen da suka
halacci kamun.
Anty zubaida ita ke riqe da ita har mazauninta inda aka tanada saboda
ita,bata barta ba sai data duqa ta mata gargadin karta sake ta bata musu taro ta
hanyar yin wani abu na daban,hakanan cikin mayafinta da aka lullubeta har saman
kanta ta dinga hadiyar wani abu mai tauri a maqogaronta,ta dinga kokawar maida
kukanta,duk wanda yazo a haka zai mata liqi ya wuce taqi ta daga kaima bare ta
tantance su waye a wajen,a haka har lokacin soma kamu yayi,tana jin sanda dangin
mahaifiyarta dana mahaifinta suka iso inda take zaune,aka buqaci dangin ango su
matso
"Ga turaren da za'a yiwa amarya kamu dashi inji angonta" taji wata murya wadda
kamar ta santa tana fada,aka saki dariya gaba daya,wata mai azabar murya ta rangada
guda wadda shahida taji kaman ana sakatar qwaqwalwarta,ta runtse idonta hawayen da
take boyewa suka gaza riquwa,sai suka silalo suka zubo har saman tafin hannunta
dake aje saman cinyarta,feshin farko na turaren da aka mata gabanta yayi mumunan
faduwa,tabbas wannan qamshin anwar ne,turarensa ne,sake rintse idanunta tayi
tanajin radadi a zuciyarta,waishin me yasa kowa ya kasa fahimtarta ne?,basa ganewa
ne?,me yasa kullum kwanan duniya suke jawo abinda zai sake kusantata dashi ne?,a
haka har aka qare fesheta akayi addu'a sannan akaci gaba da saka kidan
qwarya,dangin ago suka buqaci yi mata liqi,haka anty zubaida tazo ta dagata zuwa
amma ba tare data bude mata fuskarta ba suka shiga mata liqi,kowa sai daya tsaya ya
kallesu ya qara.

Qarfe sha daya da rabi na daren ranar bayan taron kamu ya watse tana tsaye
gaban window din dakinta dake bude iska na shigowa sosai mai sanyi na alamun dare
ya soma nisa,iskar dake shigowa cakude take da turaren da aka yi mata barinsa daxu
a jikinta wanda duk da wankan da tayi kusan aikin banza ne qamshin bai rabu da
jikinta ba,kusan a yanzu ba wannan ne ya dameta ba,saqon anty zubaida data gaya
mata kafin shigowarta dakin shine babban abinda ya hanata sukuni a yanzu,dinner da
za'ayi gobe tsakanin ango da amarya da abokansu,ta yaya zata zauna bigire daya da
anwar din a matsayin amarya da ango?,yadda anty zubaida ta tsume take ja mata kunne
kan goben ta tabbatar kome tayi a laifi yake,ranta a bace yake sosai,ga mari ga
tsinka jaka?,itakam me anwar zaice da ita?,ya jima da rusa dukka wani farinciki
nata yanzu gashi ya sake dawowa yasa hannu ya takwabe wanda yayi saura,bata da wata
mafita gashi ta gaji da tsaiwar,saboda haka ta saki labulen ta dawo cikin dakin
wanda su uku ne duka duka a ciki don tace ba zata kwana da kowa ba,tsallakesu tayi
wanda tuni sun fara barci ta shiga bandaki ta daura alwala sannan ta dawo ta kwanta
tana fatan bacci ya dauketa.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Duk yadda taso ta taushi kanta ta kuma qwararawa kanta gwiwa donta fita ga
motoci hudu na anwar dake jiranta a qofar gidan hakan yaci tura,a dakin baqi na
uncle hisham dake dab da qofar fita ta shiga ta zauna.

Ran hasina ya baci it hankalinta ya tashi na kada ta bada su,ga zunnurah


tayi gaba tuni a motar mai gidanta da yace bai yarda tahau motar kowa ba bare ta
mata magana ko shahidan zataji maganarta,irin kudaden da aka kashe mata kawai a
ranar donta fito ba kadan bane,ta kuwa fita din tayi kyau,irin amaryar da duk wanda
ya kalleta sau daya saiya maida kanshi ya mata duba na biyu,gashi dukka wanda ya
dace hasinan ta yiwa magana kan yasa shahidan ta fito sunyi gaba,kusan su suka rage
kawai,bata da wata dabara dole daga qarshe ta fita ta shaidawa muhsin da suke zaman
jiran fitowarsu.

Kai ya jinjina kawai sannan ya juya ya nufi daya daga cikin motocin datafi
kowacce kyau da girma,bude gidan baya yayi ya shiga inda anan anwar ke
hakimce,cikin dan bacin rai yace
"Wai zaman me muke muhsin,haka kawai ka kawoni cikin mota ka aje bayan kasan inada
abunyi da yawa"
"Kaga saurara....wayarka zaka dauka ka kira mana amarya ka lallabata ta taimaka ta
fito" cikin rashin gane me yake nufi yace
"Kaman yaya?" Girarsa muhsin ya dage
"Eh to....qila sarautar tasu ce ta motsa,tana ciki taqi fitowa" dan jim yayi na
wani lokaci sannan ya saki wani tsaki da qarfi
"Koma meye kaika jawa mutane wallahi" ya qarasa fada yana kokawar cire babbar rigar
shaddar dake jikinsa wadda taci aiki tayi bala'in yi masa kyau,ko ba'a fada maka ba
kana kallonshi kaga ango
"A'ah,meye na cire babbar riga kamar me shirin dambe?" Sai daya bude murfin motar
ya saka qafarsa daya a waje sannan yace
"Damben zanyi" ya qarasa fita yana rufe murfin motar,yanajin muhsin din na cewa
nifa kiranta nace kayi a waya ka fiddota fa ba wani abu ba,ko kallonshi baiyi ba ya
wuce abinsa,dukka 'yammatan dake tsatstsaye suna jiran fitowat amarya donsu wuce
dakin taron sai dayaja hankalinsu,kowacce idanunta bisa kanshi,b wadda bai burge ba
cikinsu,a hankali yaci gaba da takunsa harya shiga gidan ya nufi dakin baqin kai
tsaye ya tura qofar.

_ku ziyarci tashar SAUTIN HIKIMA dake youtube,don sauraron litattafanmu tsaffi da
sababbi,dama wadanda zasu muku nan gaba wadanda babu su a duniyar watsapp,karku

3️⃣ 5️⃣
manta kuyi subscribe don sanin cewa mun dora sabon shirinmu_*Alqawarin Allah*
3️⃣5️⃣

Tana kwance saman doguwar kujera ta juyawa qofar shigowa baya,hakan ya sanya
sanda taji an bude qofar ta waiwayo ta saddaqar da cewa anty zubaida ce,saidai
wanda ta gani din yana shigowa ya sanyata bude manyan idanunta da suka sake
qawatuwa da kwallin da me makeup ta sanya musu tana dubanshi,fuskarta a yamutse
alamun tambaya tacj gaba da kallonshi sanda shi kuma yake takowa cikin dakin,yayin
da wani sashe na zuciyarta ya karkata wajen kallon adonshi cikin shaddar jikinsa
mai azabar kyau da daukar ido,ta zauna masa das kai kace saboda shi kadai aka
yita,shima ita yake kallo,duk yadda yaso kwabar kansa da hana kanshi yabata saida
zuciyarsa ta zarme ta gano kyawun da tayi masa,tayi wani kyau na musamman,duk da
ramar da tayi amma hakan bai hana kyawunta fitowa ba.

Nesa da ita kadan ya tsaya ya harde hannayensa yanaci gaba da kallonta,yace da


ita sanda ta waiwaya tana niyyar sake juya baya ta koma kwanciyarta abinta
"Mudin kin tsammaci abokan wasanki ne?,ko ce miki akayi bamu da abunyi?,sauko maza
ki wuce mu tafi tun ban aikata abinda nayi niyya ba" idan ta tanka to sauran
kujerun dakin sun tanka,saima sake gyara kwanciyarta data yi kamar bada ita yake
ba,hakan ya bashi haushi,shi zatama kunnen uwar shegu tana jinsa?,saboda haka bai
sake ce mata komai ba ya taka har inda take kwancen a hankali ba tare data sani
ba,ya isa bayanta ya ranqwafa gaba daya ya sanya hannunsa ya soma ciccibarta,cikin
matuqar mamaki tayi yunqurin tashi gami da zillewa cikin zafin nama,ta zauna sosai
fuskarta cike da bacin rai take dubanshi
"Me hakane?,karka kuma kuskuren tabani malam kaji na gaya maka"girar sama data qasa
a hade ya maida mata amsa idanunshi cikin nata
"wannan sharadinki ne ba nawa ba,baki isa kuma ki kafamin shi ba,a banza ma wani ya
taba bare ni?mema kike gudu ne?,meye abun killacewar?"ya qarashe furucin wannan
karon yana tuna sanda nuradden ya kama hannunta a office yana niyyar sanya mata
zobe,idanunta ta daga ta kalleshi cikin mamaki,kamar yaya wani ya tabata?,shi wai
abu nawa ya gani?,abu nawa ya sani dangane da ita wanda ita bata da masaniya akan
ya sani din?,ba abinda ya fado mata a rai sai sanda ta fada jikin mutumin da
fiddausi ta kaita siyan kayan maye,anya bai wajen koya ganta ne yake mata gugar
xana?,wani bacin rai ya sauko mata a take fiye da wanda take ciki,tsaki taja qasan
ranta zuciyarta na mata suya,ta kwashe qafafunta da garin sauri ta saukesu qasa
bata ma sani ba,yabi qafafun nata da suka sha lalle da kallo harta tanqwashe su
tana niyyar sake kwanciya
"karki kuskura...wannan karon idan na iso inda kike banga abinda xai dakatar dani
daga fitar dake ba da hannuna"baki ta tabe karon farko ta jefa masa harara,ji take
kaman ta tashi tayita dukansa ko xataji sassaucin haushi da zafinsa da take
ji,kansa ya nuna da yatsa
"Ni kike harara?"
"Saime don na harareka,kai waye?" Tayi furucin tana son ta tunzurashi ko hakan
zaiyi sanadin da zaiyi zuciya ya fita ya qyaleta,don itakam ko daya bata da muradin
zuwa ko ina,hannun nasa dake harde a qirji ya sauke yana sake takowa inda take
idonsa akanta,kafin ya qaraso tayi zumbur ta miqe tsaye gami da kaucewa gefa
"Na gaya maka babu inda zani,ko ana dole ne?idan ka aureni dole baka isa kamin
dolen zuwa wajen taro ba"
"Haka kika ce?"
"Eh" ta bashi amsa kai tsaye,wannan karon qwaqwalwarta bata gama bata shawarar
abinda zatayi ba caraf taji ya sureta gaba daya ya fice da ita,sosai ta
tsorata,kunyar jama'an da zasu tarar haushi da takaicinsa suka cikata
"Ka cikani malam,ka saukeni,wannan wanne irin wulaqanci ne haka?,baka ganin
mutane?,a haka zaka fita dani har waje?" Bai saurareta ba harsai da sukaje daf da
gate din sannan ya direta,hakanan ya babbake qofar ya tsareta da ido yana son yaga
iya gudun ruwanta,daidai sanda wayar hannunta ta soma ruri,tana hadiye bacin ranta
ta duba sunan mai kiran,anty zubaida ce ta daga ta kara a kunnenta
"Wai me kuka tsayane kuna ina har yanzu baqi sun gaji da jiranku?" Bata da wata
dabara saita yanke wayar ta gyara tsaiwarta,takalman qafarta takeon gyarawa amma
batason duqawa,ya tsareta da ido dole ta sunkuya a hankali da niyyar sake daure
igiyoyin jiki,daidai nan shima ya duqa goshinsu ya gwaru,ta miqe tsaye da sauri
dage da goshin nata tana jin zafin gwaren da sukayi,bai dago ya duqa,ya sanya
hannunsa a nutse ya tattara igiyoyin ya soma daure mata su idanunsa kan farar
qafarta data sha jan lalle har saman qafar,qoqarin qwace qafar ta shiga yi amma a
banza sai daya gama sannan ya miqe,yaja da baya fuska a matuqar tsuke,sai data
kalleshi sannan ta soma takawa ta fice daga gidan ya mara mata baya.

Dukkansu xaman kurame sukayi shida ita cikin motar,kowa ya kama owners corner
ya hade fuska kaman zasu masgi juna,ta cikin glasa muhsin ya qare musu kallo,dariya
ta cikashi,ya girgiza kai kawai,shikam wannan abun yafi masa kama da fadan
masoya,sai shine daya gaji da shurun ya soma sako musu hira don gudun xaman
shuru,ba wani hadin kai ya samu daga wajensu ba na tayashi hirar ba,har gwara ma
anwar akan shahidan ta takejin wani abu ya tokare mata wuya,tunda suka shiga motar
sai kace bai santa ba,kai bakace shine a daxun ke shirin mata daukan amarya ba.

Sanda duka isa muhsin shiya fara ficewa a motar,tana shirin budewa itama ta
fita anwar ya danna lock,waiwayowa tayi ta dubeshi,batason wata magana ko gajerace
bare mai tsaho saboda haka ta kalleshi kawai daidai sanda shima ya kalleta
"Saurin me kikeyi?,kina gudun jerawa ne dani,saidai ni na fiki gudun na jera dake
don kar a dauka nida ke Ali yaga Ali ne"
"Ai baka cika wanda yake gudun jerawa da 'yar maye ba tunda zaka iya aurenta" ta
maida masa amsa idanunta akanshi,saiya dauke kanshi yana cire belt din
jikinsa,hakanan ya samu kansa dajin zafin kalmar 'yar maye data fada din.

Sanda suke shiga wajen babu wanda basu burge ba,duk wanda ya dora idonshi
akansu saiya shagala da kallonsu,perfect martch da yawa suke fada,yayin da duka
jama'ar dake wajen suka miqe don nuna girmamawa a garesu,da yawa wadanda sukasan
tsohuwar alaqar dake tsakaninsu kuwa irinsu anty usaina zunnurah da maqota
fuskokinsu sunqi gushewa da murmushi
"Lallai *ALQAWARIN ALLAH BAYA TASHI* ba wanda ya isa ya canza alqawarin Allah"
zunnurah take fada a bayyane tana kallon maigidanta sanda shahida da anwar suka
zauna a muhallin da aka tanadar musu,tana tuna tsahon zamanin da suka dauka basu
tare,tana tuna yadda kowanne yaqi dan uwansa yake nesanta kanshi dashi,dai gashi
cikin qanqanin lokaci ubangiji ya nuna buwayarsa,ya sake dawo dasu cikin rayuwar
juna duk da yadda kowannensu ke tsaye kai da fata akan qudurinsa amma Allah yayi
nasa hukuncin.
Sanda aka fara gabatar da komai akayi kiran dangin ango anty usaina ta fito
sai abun ya baiwa shahida mamaki,ruwan kudin data musu yasa ta sanya ayar tambaya a
kanta,wace anty usaina?ta tambayi kanta lokacin data tsaya gefan anwar suna magana
qasa qasa yadda shahidan bataji,gabanta ya fadi cikin ranta tana addu'ar Allah yasa
ba abinda take zato bane.

Saidai kuma addu'ar tata batayi tsaho na aka ware fili na musamman saboda
babbar yayar ango aka bata dama,cikin qananun hawaye da suka kasa riquwa a idanunta
ta miqe ta isa inda anwar da shahida ke zaune,tasa hannunta ta tashesu tsaye gami
da dan matso dasu gaban step din da suke kai kadan yadda kowa zai iya ganinsu,ta
karbi abun magana tayi taku biyu gaba kadan dasu sannan ta tsaya
"Yanzu da zan tambaya cewa suwa kuke gani a tsaye a nan wasunku zasuce amarya da
ango,wasu zasuce masoya,eh....masoya ne saidai ba ordinary masoya da kowa ya sani
ba,masoya ne da kalar soyayyarsu ta bambanta data kowa,masoyan da Allah zai cika
alqawarinsa a kansu koda ba wanda yaso hakan,nasan zaku yarda dani idan kukaga
wannan" saita juya ta kalli masu gabatarwa,cikin sakannin da basu wuce goma ba
majigin dake kafe a bango daban dake hall din ya soma haske wanda hakan yaja
hankalin kowa,ciki harda anwar da shahida,cikin qanqanin lokaci hotuna suka soma
bayyana kansu daya bayan daya,hotunan anwar da shahida shekara biyar zuwa shida
baya,mamaki ya kama anwar ni na a ina anty usaina ta samo wadan nan hotunan?,hotuna
ne da sukan dauka lokaci zuwa lokaci shida shahidan idan yaje zance sanda ya siyi
waya torching ya siya mata itama,tana ainihin shahidarta yana ainihin anwar
dinsa,nan fa murmushi ya cika fuskokin al'umma kowa nabin hotunan daya bayan daya
da kallo,abokan tsokana suka samu nayi,yayye da iyaye suka dinga dariyar
hotunan,wasu da hijabai a jikinta,wasu ta sunne kai,shi kuwa yana dan tsirit dinsa
babu wata cika ko kumari tattare dashi,a hankali hotunan suka dinga shiga zukatansu
suna tuna musu wani lokaci can baya,lokutan da sukafi kowanne dadi cikin
rayuwarsu,hoto na qarshe ya soki zuciyarsa shida ita,dukkansu basu manta ba,wannan
shine hoto kusan na qarshe da suka dauka tsakaninsu dab da mai afkuwa zata
afku,idanunta ta runtse hawaye nason saukowa tana hanashi,turota da anwar yayi daga
gidansa shine abinda yazo mata a rai,daidai sanda shima ya dauke kanshi daga kallon
hotunan,suna qarewa gurin ya rude da hayaniya da kuma tafu gami da sowa,saida mc ya
daidaita komai sannan anty usaina taci gaba da magana
"Zuwa yanzu nasan kowa ya gasgata maganata ko?"
"Eh..." Duka hall din ya amsa,kaita jinjina sannan ta sake komawa gabansu tana
dubansu har yanzu abun magana na hannunta
"Inason ku sake tabbatarmana da cewa zaku kula dakanku,zaku kula da amanar juna,ga
shaidu nan suna kallo" ta qarashe maganar tana fidda murmushi gami da fatan hakan
ya kawo sauyi tsakaninsu komi qanqantarsa,anwar ta fara miqawa abun maganar tana
tsareshi da ido,dole ya amsa yakai bakinsa,sassanyar muryarshi mai cike da
mazantaka ta cika hall din wanda hakan ya taso da tsohon mikin dake danqare zuciyar
nafisa dake maqale ita da mima a wani sashe na hall din,ji tayi kaman zuciyarta
zatayi bindiga,sonshi da qaunarshi ya sake narkewa cikin zuciyarta,taji inama tun
farko batayi sakin bakin cewa ta fasa aurenshi ba?
"In sha Allah zan kula da ita,zan sauke duk wani haqqi nata dake wuyana..."
"Kayi mana qwange....zaka bata soyayya da kulawa?" Anty usaina ta tari numfashinsa
ta fada cikin sauri ta sigar tambata,kasancewar ba abun magana a hannunta yasa
wadanda ke zaune gaba gaba abokanshi su kadai sukaji me tace sai kuwa su,idanu ya
fiddo yana kallon antyn ya tabbatar qure takeson yi masa,cikin qasa qasa da murya
yadda su kadai zasuji yace
"Idan naga ta cancanta ba" yana miqawa antyn abun maganar,duka takai masa wanda ta
manta ma a inda suka saboda jin haushi ya goce yana dariya,abun ya baiwa mutanen
dake wajen sha'awa suka saka dariya gami da sanya musu tafi,harara ta jefa masa
sannan ta juya ta miqawa shahida abun maganar
"Uhmm...uwar gidan anwar,ina naki alqawarin" murmushi ta qaqalo sannan ta jefawa
anwar harara wanda har cikin zuciyarta ita tayi hakan,yayin da sauran mutane suka
tsammaci soyayya ce
"Alqawarin daya dauka baiyimin ba anty,ba abinda ya iya,baisan haqqin soyayya ba
baisan mutuncin masoyi ba,baisan komai ba a soyayya bai iyata ba" tsit kowa yayi
yana saurarenta cikin mamaki,gaban anty usaina ya shiga faduwa,hasina da zunnurah
dake zaune cikin mutane ji sukayi kaman su rugo da gudu su qwace abun maganar daga
hannunta,yayin da nafisa ta tsaya cak farinciki na ratsata,me zai farune?,ba hadin
kai tsakaninsu kenan ko jituwa
"Haka kikeso anty na fada irin kalaman da wata amarya da aka yiwa auren dole ta
fada?,idan ban yabi masoyi kamarshi ba me zance?,bashi da buqatar yabo ko daukan
alwashi a kansa,shi yasan komai,duk alqawarin da zan dauka anan na fallasa sirrin
soyayyarmu ne,alqawarin daya dauka duka namu ne mu biyu basai nayi maimaici ba,ni
dashi duka abu daya ne" ta qarashe fada tana murmushi saman fuskarta can qasan
ranta kuma tana jin ciwon lafazinta,sowa da ihu wajen ya kaure dashi,ba wanda ya
fuskanci me take nufi daga anty usaina saishi uban gayyar,sai zunnurah da
hasina,kowa ya zaci cewa abinda ta fada din zallar soyayya ce da qauna,miqawa antyn
abun maganar tayi,tana juyowa suka hada idanu dashi saita dauke idonta gefe guda.

Sosai dinner din ta qayatar ta sanya farinciki cikin zukatan al'umma da


dama,takuma burgesu,komai ya gudana yadda anty zubaida tayi fata shahidan bata bada
matsala ba,tayi qoqarin kula da duk wani motsi nata da action nata.*Alqawarin

3️⃣ 6️⃣
Allah*
3️⃣6️⃣

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Daurin auren da za'ayi sha daya na safe amma tun takwas na safe gidan ya soma
cika da 'yan uwa,a sannan tana kwance daga saman gadonta tana kallon yammatan nata
hada hadarsu abinsu suna breakfast,ko sha'awar abincinma batayi bare takai
gaci,babu yadda hasina batayi da ita ba amma ko kallonta batayi ba bare ta
tashi,sai juyi take daga nan zuwa can,ji take kaman zazzabi zai kamata,har goma
saura tana kwance tana kallon masu wanka nayi masu kwalliya nayi.

A sannan ne anty zubaida ta shigo tana dubanta


"Wankanne yau baki da niyyaryi ko kuwa?" Bata amsa mata ba illa miqewa da tayi ta
zauna sosai saman gadon tanajin jikinta a matuqar mace,haka zuciyarta a
cunkushe,kanta a qasa anty zubaida ta aje ledar hannunta
"Ki tashi kiyi wanka ki shirya,mai kwalliya zata shigo tayi miki"
"Anty.." Ta kira sunan anty zubaidan zuciya a karye,juyowa tayi tana kallonta
"Don Allah ki qyale mai kwalliyar nan yau,don Allah" dan shuru tayi sannan tace
"Shikenan zata koma,hasina ta shafa miki ko powder ne" daga haka ta fice daga
dakin.

Dariya hasina tayi sosai tana qarasowa inda shahida ke zaune tana tare
qwallar idonta,idan da hali yau batason ko sau daya tayi kuka
"Hajiya shahida,nikam na rasa me kike nufi,don Allah yammata ba kukan dadi wannan
matar take ba?" Ta tambayi sauran yammatan dake dakin tana watsa hannaye,dariya aka
sanya sannan ta dora
"Allah ya baki miji irin wannan da yaji komai da komai amma ki tsaya kina wani nuna
qiyayyar banza,ke idanunsa kawai aka kallah Allah ansan dan soyayya ne na
qarshe,baku lura da yanayin kallonsa bane?" Ta sake jefawa 'yammatan dakin tambaya
"Ashe bani kadai na gani ba,nida daada ta fadamin tun farko aini zan sako kai akwai
amanta da batunki" daya daga cikin cousin sis din shahida ta fada,muryarta kamar ta
mutumin daya tashi yanzu a bacci tace
"Yanzu ma lokaci bai qureba,da zasu taimakeni da sun maida daurin auren kanki,don
Allah ki shaida musu" daya daga cikinsu ta saki dariyahatda qyaqyacewa
"Kuna ganin idonta kunsan qarya take,wannan aka qwace miki shi idan baki kuka ba
yanzu gaba sai hawan jini ya kamaki" dukka suka sheqe da dariya,abun ya bata haushi
ganin wai basu yarda da ita ba
"Nikeson anwar?,amma kun yaudari kanku" daga haka ta zira takalmanta ta shige
bandakin ganin suna sake turata.

Kafin sha daya na rana layin ya dinke tsaf da jama'a,hayaniya ta kowanne


sashi,yayin da fargaba da faduwar gaban shahida suka dadu duk sanda wani minti ko
sakan ya shude,idanuwanta kan agogo,duk surutan da ake cikin dakin bata jinsu bare
ta fahimci me suke fada.

Sha daya da minti goma sha biyar qanwar ummanta ita da wasu yan uwan babanta
su uku suma shigo dakin suna sakin guda wadda ta firgita shahida gamida saka
zuciyarta gudu da matsanancin sauri,inda take zaune suka qaraso hannun daya daga
cikinsu na dauke da turare ta dunfarota tana cewa
" *Alqawarin Allah* ya tabbata,yau Allah yayi,shahida ta zama matar anwar"wadda ke
tsaye a bakin qofa qanwar abbanta tace
"Allah ya jiqan habibu,Allah baiyi zaiga aurenki ba shahida,duk qaunar da yake miki
Allah bai nufa ba,Allah ya jiqanka habibu yakai haske kabarinka" kalaman da suka
sake tunzura zuciyar shahida kenan sanda suke fesheta da turaren,ta saki kuka sosai
mai sauti wanda ya tunawa da abbanta yasa taji auren ya sake fice mata daga
kai,karo na biyu tun bayan lokacin da al'amarin ya faru da taji ba zata iya yafewa
fiddausi ba wadda ita ta zama sila kuma jagorar afkuwar komai a rayuwarta,me ta
yiwa fiddausi haka dataso tarwatsa mata rayuwa?.

Daada ce ta shigo dakin jin hayaniya da gudar dake tashi a cikin dakin,yawan
kukan da taga shahidan nayi yasa daadan ta fitar da kowa daga dakin taja mata
qofar,tayi hakanne donta bata damar yin kuka sosai ko zataji sanyi a ranta.

Daidai lokacin da nafisa ke kaikawo kaman wadda ta hadiyi kunawa tana


zufa,bata tabajin cewa tayi kuskure ba sai yanzu da labarin tabbatuwar auren
shahida da anwar ya ratsa kunnenta
"Anya banyi ganganci ba kuwa mima?"
"Gaganci kuma na nawa?" Ta fadi a zuciyarta,amma a fili saits iso inda take ta dafa
kafadarta
"Babu wani ganganci da kikayi,badai gani na iso ba?zaki shiga gidan anwar a sanda
ya dace dake,ki sawq ranki kamar kin sameshi kin gama" sanyi ya ratsa ranta ta saki
ajiyar zuciya
"Please mima,duk wani shiri da zakiyi karkiyi na dogon lokaci,kiyishi a gajeran
zango,don zuciysta ba zata iya jurar tunawa da zan dinga cewa anwar nacan ya kebe
da wata macen ba bayan ni"
"Baki da damuwa fa hajiyata,kisa ido kisha kallo" mima tayi lafazin tana daukan
jaka da dan yalolon mayafinta ta fice daga falon.

*5:00 pm*

Qarfe biyar na yammaci cikin dakin nata da aka gama kwashe komai nata take
zaune saman kujerar madubi,da kanta a yanzu take shiryawa don tasan me afkuwar ta
riga data afku,komai ya qare mata,babu sauran wani abu da zai tasiri koya hanata
shiga gidan anwar,ta gama yankewa kanta gwara ta sassautawa zuciyarta,ta yadda da
hakan ta kuma sallama,taci alwashin samawa kanta walwala da nutsuwa,saidai hawayen
da har yanzu ta kasa cin galaba akanshi gaba daya duk da ya ragu,amma lokaci lokaci
yakan sako kai tasa hannu ta daukeshi.

Tsaf ta gama shirin nata hasina da anty xubaida na gyara mata wasu abubuwan
har komai ya kammala,lallai amarya amarya ce,gaba daya kaman sauya shahidan akayi
da wata sabuwar halittar,tayi wani kyau na musamman gami da kwarjini,anty usaina ta
zauna daga bakin gado tana dubanta
"Za'a soma kaiki wajen umma,daganan kuma akaiki gidan yayarshi,za'a barki a nan shi
zaizo ya daukeki ku wuce,munyi magana da ita ta gayan dalilanta nayin hakan kuma na
gamsu,shahida,zamana dake zamane mai dadi wansa nake alfahari dashi,kuma dukkan
abinda ya kamata na gaya kiki koki sani kin riga dakin sani na kuma sake miki
tishinsa,abu na qarshe kawai da zan rufe dashi shine ince miki,shi aure bautar
ubangiji ne,hakan ya sanya dadinsa bai rufewa mace ido ta manta da
mahaliccinta,haka dacinsa ma bai sanya mace ta manta da cewa bautar Allah
take,Allah yasa kin shiga a sa'a,ya sauya zukatanku da manufofinku cikin qanqanin
lokaci,ina maraba da tambaya daga gareki duk sanda wani abu ya shige miki duhu,amma
ki sani,dole ki zama jaruma,dole ki koyi hadiye wasu abubuwan ba tare da kowa ya
sani kokin gayawa kowa ba,ciki badon tuwo kawai aka yishi ba,Allah ya sadamu da
dukkan alkhairinsa" daga haka anty zubaida ta miqe don batason tayi qwalla ko daya
don karta sake karyawa shahida gwiwa tunda ta fuskanci kamar ta aro dakiya da
juriya,daidai sannan huda ta shigo da sauri,ta isa gaban shahida ta rungumeta,zata
fara kuka anty zubaida ta zare mata ido gamida korata don karta karyawa shahidan
gwiwa,a haka aka fita da ita zuwa gidansu.

Can dinma gidan cike yake da jama'a 'yan yinin biki,uwar dakan ummanta aka
ajeta,'yan uwa suka dinga shigowa aka dinga gaisawa ana yi mata Allah ya sanya
alkhairi,tayi qoqarin tarbar kowa cikin mutuntawa,tunda kusan dangin ummanta ne
duka,ba wani bare ko baquwar fuska.

Sai gab da magariba sannan umma ta zauna da ita ita da sauran


yayyenta,fadane dai irin wanda uwaye kewa diyarsu,daga bisani kuma umma ta taba
nata,ta nemi yafiyarta cikin kuka tana tunawa da abbanta
"Bakiyimin komai ba shahida,saidaima ni nace ki yafe mana nida mahaifinku" kukan da
bataso ba a yanzu shi take haiqan,kaman ba zata fita daga gidan ba haka ta tako
suna riqe da ita aka fito da ita,saitaji wani qauna da kewar mahaifiyarta na
ratsata,taji kaman karta tafi,taji kaman taci gaba da zama dasu,a yanzu bata
buqatar anwar sam,bata da buqatarsa cikin rayuwarta.

Tun daga harabar gidan anty usainan zaka gane wata walima ake ta daban
saboda yadda harabar ta qawatu,uwa uba ankon da yake jikin duk wanda ke farfajiyar
dama cikin gidan cikin wata atamfa mai azabar kyau da tsari.

Sabon shagali na walimar da dangin ango suka hada aka bude,nan aka zaunar da
shahida suka dinga mata barin liqi tako ina,ba'a tashi ba saida akayi sallar
magariba,anty usaina bata bari an shiga da ita cikin gidan ba,can wani babban falo
dake da daki da bandaki aka kaita,babu kowa wurin da niyyar ko zatayi sallah,aka
aje mata abinci aka barta ita daya donta sake,tuni 'yan uwanta suka koma gida ba
wanda ya zauna,fashin sallah take hakanan abinci bata sha'awarsa,kuma batajin zai
iya wucewa ta maqoshinta,saboda haka ta zauna kawai idanunta kan tv din dake aiki
ita daya,volume dinta can qasa don ba'ajin ma me ake cewa,sam ba tv dince a gabanta
ba,sabuwar rayuwar da zata fuskanta itace a gabanta,abu na gaba tsakanin kunyar
anty usaina,ta yaya zata kalleta?,idan ta tuna kalaman data gaya mata na batason
dan uwanta sai taji duk nauyi ya sauko mata,batasan itace wannan yayar tashi qwaya
daya da bashi da kamarta ba,da duk yadda take qin abun ba zata yarda bakinta ya
fada ba,addu'a take cikin ranta Allah yasa kada ta shigo.

Bakwai da rabi zuwa takwas na dare taji hayaniyar gidan ta ragu sosai,da
alama masu tafiya sun tafi kenan,masu shigewa cikin gida sun shige,turo qofar da
akayi shi yaja hankalinta,ta dan dage mayafinta kadan tana kallon mai
shigowar,sa'ida ce saidai ita batasanta ba,fuskarwa a washe ta qaraso falon tana
takowa a hankali tana waigawa,da alama ba'asan tayo.nan ba,dab da shahida ta zauna
tana kallonta
"Anty,saike kadai?,nayi nayi da ummi tabarni nazo tace a'ah zamu takura miki kina
hutawa ne,da qyar na samu na sallabo" murmushi shahida tadan saki tana duban sa'ida
"Ina yini anty,ya gajiyar biki"
"Lafiya lau,me sunanki"
"Sa'ida,'yar anty usaina ce ni,kuma qawar uncle anwar" girarta shahida ta dage duka
biyun tana dubanta alamun tambaya,dorawa tayi
"Wallahi kun dace sosai anty keda uncle,uncle ya samu mata me kyau" tana murmushi
sosai ta fada tana kuma sake kallon fuskar shahidan data ji tana burgeta,murmushi
shahidan ta kuma saki
"Ko?" Tace cikin sigar tambaya,kaita kada
"Qwarai kuwa,amma anty,don Allah ki kularmin da uncle dina,wallahi inason uncle
anwar,yana da kirki sosai,yana sonmu shima,yana kula damu sosai da sosai,don Allah
anty" saita tsaya tana sake dubanta kafin ta kuma sakin murmushi,ta dora hannunta
saman hannun sa'ida
"Uncle din naki nima zai iya kula dani ne sa'ida?" Dariya ta saki
"Tabdi,sosai kuwa anty,kinsan uncle anwar kuwa?,ai matarshi ta caba" saitayi qasa
da murya
"Na zaci fa zai iya aurena harna cewa ummi ina sonshi,ranar saida na daku
sosai,ashe babana ne" dariya ta kubcewa shahida da sa'idan duka,da sauran dariya a
fuskar shahidan tace
"Babanki ne sa'ida,amma kita addu'a Allah ya baki wanda ya fishi nagartar halaye"
"Akwai wanda yafi uncle dina kuwa?" Ta fada cikin tantama da tunani,kaita jinjina
"Qwarai kuwa,duk wanda kika gani kome kika gani a duniya akwai wanda ya fishi akwai
wanda baikaishi ba akwai dai dai dashi"
"Tohm shikenan......" Bata qarasa maganar ba suka jiyo taku ana nufowa wajen,saita
fiddo idanu
"Na shiga uku anty,Allah yasa ba ummi bace" riqe hannunta tayi
"Karki damu,zance nina kiraki ki tayani hira" shuru sukayi suna jiran ganin wanda
zai shigo din.

Sallamar mutum biyu ce,ummin sai muryar anwar daga bayanta,mummunar faduwar
gaban data sanya shahida maida kanta cikin mayafi ta saukar mata,ummi anty usaina
ce a gaba sai anwar din daga bayanta,idanunta akan sa'ida nashi idanun nakan
shahida da kanta ke sunkuye lullube da mayafi,kama baki tayi
"Na shigesu ni usaina,sa'ida...sa'ida ki shiga hankalinki da wannan rawar qafar
taki,dama da akacemin ba'a ganki ba nan kikayo?,to tashi ki wuce ki bama mutane
guri" da sauri ta zame hannunta cikin na shahidan sannan ta miqe,duk da haka da
zata gifta anwar din saida tace
"Uncle,kayi kyau sosai yau,amma wallahi in gaya maka gaskiya?,anty shahida ta fika
kyau ashe" anty usaina batasan sanda dariya kubce mata ba,yayin da murmushi ya
subuce masa shima ya bita da kallo harta fice daga dakin,ba ruwanta hakanan
take,idan taga gaskiya saita fada,kusan halayenta suna kamanceceniya dana
mahaifiyarsu,duk cikin yaran anty usaina tasu tafi zuwa daya,kusan sanda aka haifi
sa'ida tare sukayi rainonta shida anty usainan tun lokacin mahaifansu suna
raye,idanunsa ya sake saukewa akan shahidan a hankali duk da bai ganin
fuskarta,yana tsaye a wajen har anty usaina ta zauna
"Zauna daga can" ta fada tana masa nuni da inda takeso ya zauna din,kujerar da
shahida ke kaine,duk da cewa mai yalwa ce amma saiya zauna a hannun kujera,cikin
hikima da nutsuwa ta soma magana dasu
"Alhamdulillahi rabbil Aalim,komai na rayuwa a tsare yake zuwa daga wajen ubangiji
mai kowa da komai,basai na tsaya wani tambaye tambaye ba don nasan ba amsa zan samu
daga gareku ba,abunda nakeson na fada shine,wannan auren naku ya isheku dama sauran
mutane ishara,kun rabu da juna kun guji juna ba tare da dayanku ya sake tunani
Allah zaiyi ikonsa ku sake haduwa a wannan bigire ba na aure,wannan kadai ya isa ya
nunawa bawa yana tashi ne Allah yana tasa,ta Allah kuma itace dai dai,saboda haka
ku sanyawa zukatanku salama,ku zauna da juna cikin aminci da bin umarnin
mahalicci,kada ku yiwa Allah butulci wanda ya baku aron rai da lafiya ya kawoku
wannan lokacin koda cikin zukatanku bason hakan kuke ba,dubunku na nan na fatan
samun kamar takun,ya sake hadaku a sanda kowannenku rayuwarsa ta sauya ta samu ci
gaba,ta yuwu hikimar rabuwar daku dama don kowanne ya cimma gacinsa ne,wanda
wala'alla idan kuna tare da zaku cimma wannan abun ba,ku kauda hayaniya da tashin
hankali ku ajeshi idanma kun daura azamar hakan,kuyita addu'ar Allah ya baku mafita
ya sanyaya zukatanku" saita waiwaya ta dubi anwar
"Kai kaine babba sannan kaine shugaba,kai keda hankali fiye da mace,sabida haka
fiye da rabin nauyi da yanayin yadda zamanku zai kasance ya ta'allaqa a wuyanka
ne,kasan komai basak na fada maka ba,iyayenmu kafin su rasu makarantace a gareka,ka
dauki matarka ku tafi daga kai sai ita,ina muku fatan alkhairi,shahida...Allah ya
bamu alkhairinsa kinji" kasa magana tayi kunya na kamata,ta fuskanci hakan sabida
haka tayi murmushi taga bari kawai ta murje mata kunyar a wuce wajen
"Ki daina kunyata,don kincemin bakison anwar wallahi banga laifinki ko daya
ba,hasalima burgeni kikayi,donko nice kw abinda zanyi kenan,kawai saika rabu dani
tsahon wasu shekaru ka zagaya ta bayan fage ka aureni haka akeyi?" Ta qarashe
maganar tana duban anwar gamida harararsa
"Kuma ka nemi yafiyarta kukan daka sa ta dinga yi da aurenka data yi bayan bata
shirya ba bata amince ba" murmushi ya qwace masa mai dan sauti,itama antyn tana
murmushin ta fice ta barsu.

Shuru ya ratsa dakin na wasu mintina masu dan dama,idonsa akanta da yake
lullube,zuciyarsa na masa bitar wasu shekaru can baya,yasha kwana idanunsa biyu
yana wassafa yaya zai kasance duk randa shahida ta zama mallakinsa,yasha raba dare
yana tsara ranar da irin abubuwan da zasu faru a lokacin,ga komai yazo ga lokacin
yazo saidai cikin bahagon yanayi da dabaibayi,ajiyar zuciya ya saki a bayyane
sannan ya furta cikin sanyin murya
"Tashi mu tafi" yi tayi kaman batajishi ba,yayi tsai yana dubanta,ya tabbatar
taji,har tsahon minti guda sannan yace
"Kin sani sarai tun da can banason musu da taurin kai ko?,indai zaki dauki wannan
dabi'ar zakisha wuya a wajena" daga haka ya miqe yayi gaba,tasan idan ta bari
yafice batasan hanya ba,dole ta miqe itama ta bishi".

Bangaren ajiye motocin gidan suka isa,yasa muqulli ya bude motar ya


shiga,saita soma qoqarin bude gidan baya da zummar zata shiga,lock ya sakawa qofar
ba tare daya waiwayo ya dubeta ba,hakanan ta gaji da tsaiwa ya yunqurin budewar ta
matso gidan gaba ta bude,a hankali ta shiga ta zauna sosai sannan ta kame jikinta
waje daya bayan ta sake jan mayafinta ta rufe fuskarta,karon farko bayan wasu
shekaru masu tsayi ta sake hada mazauni dashi cikin mota,gaba dayansu jinsu suke
banbarakwai,kowa yanaji kamar yana tare da baqonsa ne,ya dage dukka gilasan ya
kunna ac dukda sanyin dake dan kadawa a garin,ya tashi motar suka fice daga gidan.

Wani tuqi yake kaman bazasu gida ba ko kuma yana lallaba kwalta,duk da titin
da sukabin fetal yake babu yawaitar jama'a sai haske fitilun titi tako ina,shuru ya
ratsa motar babu me cewa komai har suka isa wani waje da sukeda saida kayan ciye
ciye,kama daga ice cream,burger shawarma kaza da tsire da sauransu,saida yadanyi
gaba kadan inda babu mutane sannan yayi parking,ya kashe motar ya fita.

Bai jima ba ya dawo hannunsa dauke da leda ya sakata a sit din baya,sannan ya
tashi motar sukayi gaba,hannunsa ya saka ya kunna rediyo freedom wanda minti biyar
ya rage su fara shirin siyasa na kowanne gauta,waqar jarumar matace ta soma
plying,waqar tana taba zuciyarsa sosai,yana son ya kashe amma saiya samu kanshi da
barinta tana ci gaba da tashi,sautin na karade motar yana shiga kunnuwansu cikin
sauti madaidaici gami da haifarwa da kowa yanayi na daban.

Ta gefan ido ya saci kallonta,tayi laqwas cikin sit din motar,idanunta a


lumshe,zara zaran gashin idanunta sun fito sosai,juyawa yayi duka yana kallonta
sosai,daidai sanda ta bude nata idanun,saiyayi hanzarin dauke kanshin ya maida ga
titi yaci gaba da tuqa motar cikin nutsuwa da qwarewa.

_zaku iya jina shuru gobe saboda wani uzuri daya tasomin,amma idan na samu dama
zaku jini in sha Allah_
😊 _kuci gaba dai dayi mana uzuri,kana taka ne Allah na tashi,ta Allah itace dai
dai,har kullum burinmu mu sauke nauyinku dake kanmu,muna godiya_ 🙏?*Alqawarin

3️⃣ 8️⃣
Allah*
3️⃣8️⃣
Kafin ta sauka qasa ta dan jima a tsaye saman step na kusa da qarshe tana dai daita
yanayinta sannan ta sauka a hankali.

Ana qwala kiran sallahn ya sauko cikin jallabiya mai gajeran hannu fara sol da
ita,bisa dukkan alamu sabuwa ce,jikinsa na tashin qamshin turare mai sanyi kaman
wanda yayi wanka dashi,zuciyarta taso yadan fisgeta ta kalleshi amma tayi ta maza
ta dake kaman bata ganshi ba har ya fice masallacin.

Ba'a jima can da idarwa ba ya dawo,ya zauna saman kujerar falon suna dan taba
hira da anty amina kafin su kammala kintsawa,da suka tashi tafiya saita rasa me
zata basu,qarshe data shiga dakinta wajen akwatunan lefanta ta isa ,karo na farko
data budesu ta kuma kalla abinda ke ciki,guda biyu ne masu dauke kayan sawa taf
daqyar aka rufesu don ba abinda aka taba a ciki,ta dinga daga kayan daya bayan daya
tana kalla,kan wata shadda lace ta tsaya,ta kalleta sosai,tun daga colour har
design din choice dinta ne,tasan duk duniya kuma babu wanda yasan hakan sai
anwar,hakan ya saka ta sanya hannu ta cirota,ta kalleta sosai,iya kyau ta mata kyau
qwarai,kuma kana ganinta kasan babbar ce,saidai ba zata iya sanyata a jikinta
ba,tasan anwar ne ya zabeta,ta yanke ta baiwa anty amina ita,sauran manyan su uku
ta zaba musu atamfofi,yan yaran da yan matasan kuma ta diba musu kayan kwalliya,ta
zaba kayan gararta da yawa ta hada musu.

Anwar yana tsaye ta miqawa kowa,ta miqo ledar anty amina yafi kusa da inda
take tsaye,saboda haka ya zira hannu ya karba ya buda yana gani sannan ya rufe,daga
kai yayi tasan ita zai kalla saboda haka ta dauke kai,ilai kuwa itadin ya
kalla,haka kawai yaji kyautar ta masa ciwo,bawai saboda kudin abarba,a'ah,yafi
qarfin kudinta hakanan anty amina a wajenta tafi qarfi wannan,yasan cewa da biyu
tayi kyautar itama ta san da hakan,abinda ya bata ranshi kenan.

Har bakin mota tayi musu rakiya,anwar yace a matse sukazo hala,su ragu wasu
su shiga motarsa ya kaisu,ta musu sallama ta koma cikin gida,harsun gama shiga yace
yana zuwa,ya buda murfin motar ya koma cikin gidan.

Tana tsaka da tattare wajen taji shigowarsa,ta daga kai ta dubeshi saita
basar taci gaba da abinda take kaman bataga shigowarsa ba,bayanta kadan ya
tsaya,kaman bazaiyi magana ba sannan daga bisani yace
"Duk yadda kikeji a zuciyarki game dani kusan nima haka yake koma fiye,amma,karki
sake gangancin da kikayi yau,duk kayan dana siya nasan wa na siyawa shi,idan da
buqatar bada kyautar irinsu a siyo daga waje ba daga cikin akwati ba" idanunta ta
watsa masa sannan tace
"Ina ruwan wani?,ina cewa kayana ne ko?"
"Alright,hakane fa,amma keda kayan qasan wa kuke?"
"Oho" tace tana ci gaba da aikinta,shuru yayi yana kallonta,saiya jinjina kai
sannan yace
"Zaki gane kurenki" ya juya ya fice saboda tunawa da yayi yabar mutane a mota,tsaki
taja taci gaba da aikinta tana cewa
"Na dade ban gane kuren nawa ba"

A gurguje ta gama duk abinda zatayi ta dauki duk abinda take buqata ta shige
dakinta,wanka ta soma yi sannan taci abinci,ta jawo wayarta ta fara amfani da
ita,kama daga kiran waya,da duba saqonnin wayarta ta watsapp,bataji shigowarsa ba
sai wajen qarfe goma na dare,dai dai sannan ta miqe ta kashe qwanta ta koma gado
tayi addu'ar bacci tayi kwanciyarta.

Shika koda ya shigo dakinsa ya wuce abinsa,baibi kota kan abincin dake kan
tebur ba.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Washegari ma ta samu baqi ba laifi duk da basu kai na jiya ba,abinda ya debe
mata kewa kenan har wata washegarin,saidai randa ta cika kwana na hudu dif
kakeji,duk sai taji gidan babu dadi,haka ta wuni ita kadai,daga kwanciya sai kallo
sai latse latsen waya,har zuwa dare data kammala abinda take tayi shigewarta daki.

Tunda ta gama yin baqi bai kuma sakata a idanunsa ba,kafin magariba ta gama
komai tayi shigewarta daki,bata fitowa sai washegari shima idan ya fita a
gidan,zatayi abincin safe haka na dare ta aje masa,saidai shima bai bata taba
abincin ba,yadda ta jera haka zata kwashe abinta,kusan hakan na faruwa ne saboda ya
koma aikinsa gadan gadan,bai samun damar dawowa gidan dawuri,hakanan da wuri yake
fita.

Sati biyu cur aka suka kwashe a haka,idan ya dawo bai ganinta,hakanan idan zai
fita ma haka.

Zaman taji ya isheta,kadaicin ya mata yawa,tayi kallo har ta gaji,tayi chart


ya isheta,saita yanke shawarar ta sameshi tayi masa magana kan komawarta office don
tana da buqatar hakan.

Sai data idar da sallar magariba yau sannan ta shiga tayi wanka,ta shirya
cikin wani cotton material baqi da aka yiwa adon purple wanda yadan ciza,ta gyara
gyara gashinta sannan ta feshe jikinta da turaruka yadda ta saba,duk da ko batasaka
turaren ba qamshi kayan suke bayarwa na turaren wutar da take turare kayan nata
dashi,nan bakin window din dakinta dake fuskantar harabar gidan ta tsaya,ta yaye
labulen tana kallon harabar gidan kawai,duk da babu kowa sai mai gadi dake zaune
can bakin qofar gidan,amma ko ina gauraye yake da haske tarwai kaman rana,haka
gidan yake da wuta 24hrs.

Ta jima tsaye tana saqo tana warwara,har ta soma gajiya da tsaiwar ta saki
labulen da niyyar komawa ta zauna taji horn,saita tsaya tana ci gaba da kallon qofa
sanda baaba ya tura gate din anwar ya sako motarsa cikin gidan,tabi motar da kallo
har zuwa harabar da yake ajesu,tana kallo baban ya qarasa bakin motar bayan ya
maida qofar ya rufe,ya tsaya daga bakin window din da alama magana suke sannan ya
juya ya tafi.

Tayi zaton bazai fito daga motar ba jin shuru na wasu mintuna,kana daga bisani
taga ya bude murfin motar ya fito,sanye da mens blazzer ruwan blueblack da baqin
takalmi sau ciki,yanayin takunsa kawai zai gaya maka a gajiye yake,idanunta akanshi
har ya bacewa ganinta sannan ta saki labulen tana sauke ajiyar zuciya,hannunta
saman kanta tana son tuna wani abu tana tursasa zuciyarta kan kada ta tuna mata.

A qalla sai data bada minti talatin kyawawa sannan ta yafa mayafinta ta
fito,sam bata ko sha'awar hawa samansa amma dole ce xata kaita,taso ace yana zama a
falo ta cimmasa a can.

Yauma da zata gota table din sai data kalla,komai yana nan akai kamar yadda ta
dora,saita tabe baki tayi gaba cikin zuciyarta tana cewa
"Kai ka jiyo,nidai na sauke haqqina ko".

Yana zaune saman kujera one sitter,sanye da boxer da short sleeve shirt
farare qal,fitowarsa kenan daga wanka,yayi relaxing bayansa a makarin
kujerar,idanunsa na lumshe ya hada yatsun hannanunshi cikin na juna,haka kawai
yakejin gidan ya masa shuru tamkar shi kadaine a cikin gidan,yunwa da gajiya suna
damunsa,yana buqatar abubuwa da yawa amma ya rasa wanne zai fara tunawa cikin
zuciyarsa,cikin haka yaji kaman an buda qofar falonsa,da mamaki ya ware idanunshi
da suka dan kada saboda yadda ya jima da rufesu yana kallon qofar,qwarai yayi
mamakin ganinta,amma ya shanye mamakin yana ci gaba da dubanta sanda take takowa
ciki,bazaiyi qarya ba ta masa kyai cikin yadin jikinta,saiyaji wani bangare daya
cunkushe a zuciyarsa yana budewa,tunanin da yakeson yi ya soma dawowa,kwanaki yau
kusan goma sha uku kenan bai sanyata a idanunsa ba,ko motsinta bazai iya fadin
yaushe rabon daya ji ba,tana sake matsowa qamshin jikinta na shiga ta qofofin
hancinsa,qamshin daya sanyashi lumshe idanunsa ya sake budesu a kanta sanda ta samu
hannun daya daga cikin kujerun dake can nesa dashi ta dosana ta zauna kan
wuta,shuru ya ratsa dakin bayan sallamar data yi na wasu daqiqu sannan tace
"Inason magana dakai" idanunshi ya daga ya kalleta na wasu sakanni kafin ya janye
duban nashi daga kanta ya maida idanun nasa ya rufe kaman yadda suke dazu,don shine
mafita kawai a wajensa
"Uhmmm" yace da ita a taqaice
"Inason na koma aiki idan Allah ya kaimu ranar monday" da sauri ya bude idanun nasa
ya zubesu fes a kanta,saitaji ya mata kwarjini saboda haka ta janye idanunta daga
kanshi
"Labari kike bani ko umarni?" Ya tambayeta kai tsaye,yanayin tambayar daya mata
yasa dole ta kuma kallonshi,tadan sake tsuke fuska
"Shaida maka nake"sai ya maida idanun nashi ya rufe sannan yace
"Tunda ba umarni bane ba zaki koma ba,kin gama aiki a triple r gem,bama nan ba
kawai,kin gama kowanne aiki ako ina idan ba cikin gidan nan ba" haushi takaici da
baqinciki suka cikata,me yake nufi kenan?,yana nufin ya rabata da aikinta,cikin
hasala tace
"Me kakeso kace?,bayan duka qarfa qarfan daka yimin bai isheka ba har saika qara da
wannan?,toni ban yarda ba in gaya maka gaskiya,ai bamuyi haka dakai ba" miqewa tayi
tsaye ta soma tafiya
"Dama na gaya maka ne donkar kazo ka tarar bana nan kace ban shaida maka ba".

Tana dab da fita ta tsinceshi a gabanta,suna hada ido ta kauda kai saboda
yadda qwayar idanunshi ta sauya launi
"Bazan taba lamunta ki fita wani waje mahada jama'a maza da mata ba da sunan
aiki,ki gogayya da maza kiyi magana dasu,ki fita da safe ki dawo da yammaci,idan na
barki kika koma lallai na tabbata wawa,kuma abinda nayi baiyi riba ba,kina nufin
komawa office din danaga wani ya kama yatsarki zai saka miki zobe?,Karki soma gigin
aikata kuskure irin wannan,idan ba haka ba zaki gane baki da wayau,idan kuma baki
yarda ba bismillah" daga haka ya kauce daga hanya ya bata waje yana komawa
mazauninsa,da gudu gudu ta fice daga falon ta soma sauka qasa,tayi nasarar riqe
kukanta batayi agabansa ba sai data danga da dakin gadonta,wani irin tuquqi takeji
cikin qirjinta da zuciyarta,sam bazata yarda ba,ba zata lamunci ya sake cin galaba
a kanta ba bayan wadda yaci,idan yayi haka aiya tauyeta da yawa,tayita zama kenan
cikin wannan gidan da zaman cikinsa harya soma gundirarta,zaman da bai mata ma'ana
ba sam?,gobe kam saidai ayi duk wadda za'ayi,idan yaso yace ta wuce gidansu.

Iska yake furzarwa daga bakinsa mai dumi bayan fitarta yana murza tafin
hannunshi kan hannun kujerar da yake kai,yanajin bacin rai nason taso masa yana
danneshi,ta yaya zai barta ta koma aiki?,aikin da tun ranar daya ganta cikinsa bai
sake samun nutsuwa ba sai daya tabbatar ta daina zuwa ta sanadin aurenshi,randa
yaga nuradden din cikin office dinta da qyar ya samu ya saisaita kansa,ji ya dinga
yi kaman hawan jininsa zai tashi,sannu sannu ya dinga ambaton sunan Allah har ya
samu zafin da yakeji ya sauka,yunwar da yakeji ta dawo masa sabuwa fil,bashi da
mafita illa slipper dinshi daya zira ya sauka zuwa qasan.

Karon farko da zauna kan dining din,ya jawo warmers din ya soma budewa daya
bayan daya,take qamshi ya cika wajen wanda ya qara qaimin yunwar tasa,tun kafin ya
soma ci a ido abincin yayi masa,sanda ya soma ci kuwa saiya samu kansa da lumshe
idanunsa,dadin girkinta ya ninka fiye da wanda ya sani a baya,a nutse yaci
abincin,ya kuma yi qoshin daya manta rabonshi da yayi irinsa,baibat abincinba sai
daya diba wani yayi guzuri ya haura sama dashi.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Bayan ta idar da sallar asuba bata koma ba ta soma gyara dakinta,sannan ta
fito falo,ga zatonta zata dauki fulasan abincin kamar yadda ta saba kowanne lokaci
amma saita tarar anci fiye da rabin abincin,harara kwanukan abincin tayi kaman su
suka mata laifi
"Dan rainin hankali,nina kwana ina baqinciki,shi kuma ashe zuwa yayi ya cika
cikinsa,bacin raina dadi ma kenan yake masa,bai taba cin abincina ba sai yau daya
fuskanci a bacin rai nake kenan,aikuwa bazan yadda ba nima" da wannan tunanin ta
gama komai na gidan,ta kuma shirya abincin safe ta jera yadda ta saba sannan ta
shiga wanka.

Tara saura ta gama komai,ta shirya tsaf cikin laffaya data nade jikinta fes
da ita,qafarta sanye take da takalmi me tsinin dunduniya,ba qaramin kyau tayi
ba,kana kallonta kasan sabuwar amarya ce.

Tana tsaue bakin dining tana break don ko zama batasonyi bare ta makara taji
takun takalmi da alama ana saukowa ne daga sama,tasan shine don haka taqi daga
kanta bare ta dubeshi,daga saman step din ya tsaya yana dubanta cikin mamaki,tana
nufin fita kenan zatayi da gaske?,a ina shahida ta sauyo hali ta koyi musu da
kafiya?,bari ya zuba ido yaga iya gudun ruwanta,dole ya nuna mata shine mijin itace
matar,zata ga qarfin qwanji yau kuwa idan batayi wasa ba.

Bai qara taku daya ba yana tsaye yana kallonta harta gama,ta ciro paper daga
jakarta tayi rubutu ta ninke ta aje anan sannan ta tattara jakarta ta zuge ta riqe
a hannunta ta soma takawa don ficewa.?*Alqawarin Allah*
39

"Karki kuskura ki fita" ya fada yana daga tsayen yana dubanta,kamarma bada ita
yake ba haka taci gaba da takawa.

A nutse ya gama saukowa sannan ya saka hanzari irin na ingarman


namiji,kafin kace meye wannan ya cimmata,yasa hannu ya maida murfin qofat falon ya
rufe idanunshi cikin nata ya bata umarni kai tsaye
"Wuce ki koma ciki" dubansa tayi itama
"Kaman yaya?,bayan na gaya maka tun jiya aiko?"
"Ki koma ciki kawai nace" saita dubeshi na tsahon minti daya,ta karanci da gaske
yake,ita kuma na zata yarda yaga lagonta ba bare yaci gaba da sanyata yin abinda
batayi niyya ba kuma bata shirya ba,saita sake dora hannunta kan handle din qofar
da niyyar budewa,caraf ya riqe hannun nata,tana shirin masa tsiwar ya saketa bata
ankara ba taji an sureta gaba daya daga ita hat jakar hannun tata,ya juya ya soma
taka matakalar da zata sadashi da sama,sosai ta soma qoqarin zillewa ranta na quna
na yadda ya maidata kaman wata karmami,ya dagata ba komai bane a wajensa kamar ba
mutum ba?,sai kace wata 'yar baby
"Meye haka ne?,ka saukeni don Allah bana son irin haka,ka saukeni,ka saukeni bana
so" abinda ta dinga fada kenan tana qoqarin qwacewa daga daga hannunsa,baiko bi ta
kanta ba hakanan bai fasa hawa saman ba har sai daya dangane da bedroom dinsa
sannan ya cillata saman lallausan gadonshi yana maida numfashi,fuskarshi a
daure,ranshi a matuqar bace wanda ko ba'a gaya maka ba zaka fuskanci haka ta
idanunsa da suka soma sauya kala,nunata yayi da yatsa cikin bambami dake nuna
ranshi ya baci
"Na fuskanci cewa sassauci na yana neman kawo raini a tsakaninmu,barinki kiyi yadda
kikeso yasa kikejin kece mijin nine matar ko?,to daga yau komai zai sauya,zaki gane
wane shugaba tsakanin ni da ke" daga haka ya maida muqullin dakin ya rufesu shida
ita gaba daya,cikin hanzari take saukowa daga saman gadon nashi tana cewa
"Ka budemin qofa,ya zaka rufeni anan,wai me yasa ka fiya son kanka ne da yawa?,me
yasa kake zalunt...." Maganar tata ce ta katse sakamakon yadda ta sauko qafafunta
qasa da hanzari da cogenta,sai akayi rashin sa'a qafar tata ta turgude da tsinin
takalminta,maimakon ta qarasa maganar da take saita buge da sakin qara,ta koma tayi
zaman dole bakin gadon tana duba qafarta.
Towel din dayake daukowa ya rataya a wuyanshi sannan ya waiwayo yaga me ya
sakata yin qarar,idanunsa ya sauka a qafarta da take dafe da ita,a hankali ya
qarasa ya duqa gabanta,ya saka hannu zai taba qafar ta janyeta baya da sauri tana
ci gaba da dafe wajen,ya gane me take nufi,tana nufin batason ya taba nata qafa
kenan,saboda haka ya qyaleta ya juya abinshi yayi shigewarsa wankansa.

Azabar data dinga ji cikin qafar ya tabbatar mata mawuyacine idan ba targade
tayi ba,batasan ya zatayi da qafar taya ba,hakanan ita daua cikin dakin ta dinga
dafe qafar tana jin zugi na ratsata.

Sai daya kwashe awa guda cur sannan ya fito,a shiryensa kaman ba shine ya
shiga wanka da towel da jallabiya ba,ya isa gaban mudubi ya dauki turarukansa ya
fesa,ta cikin madubin yaje dan kallonta yadda ta soma hada gumi,tuni harta cire
yafen lafayar jikinta,idanunsa ya sauka kan lallausar t.shirt din dake jikinta fara
sol mai dogon hannu da rufaffen wuya,wadda ta lafe sosai a jikinta ta fidda shape
din albarkatun qirjinta,saiya dauke idanunsa daga kanta da sauri,ya gama fesa
turarensa ya taje kansa sannan ya juya ya sake takawa inda take ya tsugunna gabanta
karo na biyu,zata sake janye qafar yayi caraf ya riqeta sosai,ta saki ihun azaba
sanda ya gama zare takalmin ya soma mammatsata,take ya gane targade ne,ya kuma gamo
wajen,sai daya faki numfashinta ya kama wajen sosai wanda babu shiri ta qwalla wata
irin qara tana qoqarin tureshi,saidai ko gezau baiyi na yaci gaba da gyara
wajen,tun tana masa masifa tana jin girman kan ta roqeshi ya qyaleta harta soma
roqon nashi tana hadashi da Allah,ta hada gumi jagaf kafin ya gama,yana sakinta ta
saki ajiyar zuciya,sai kuka ya qwace mata,dama zuciyar na akusa,gani take kaman
yana sane ya taba ciwon da yawa yayine kawai saboda mugunta.

Baiko dubeta ya juya ya isa bakin qofa yabude zai fice,taso yunqurawa ta miqe
ta bishi a baya da hanzari ko xata samu nasarar ficewa amma ina babu damar ta taka
qafar,tana kallo yaja qofar,saidai wannan karon bai rufeta ba,abinda ya sanyata
sakin ajiyar zuciya kenan,ta maida kanta jikin filo ta jinginar tana lumshe
jiqaqqun idanunta da duka jiqe da ruwan hawaye.

Tun tana sauke ajiyar zuciya tana shaqar qamshinsa daya kama dakin har bacci
ya soma fisgarta,ta dinga dagewa don bata son yin bacci saman gadonshi amma ina
yafi qarfinta.

Qarfe biyu na rana ya sake dawowa saman,duka yau ba inda ya fita,duk da yaso
yayi fitarsa ya qyaleta amma saiya kasa,sanin cewa mawuyacine ta iya tabuka komai
saboda targaden data ji din ba kadan bane.

A hankali ya turo qofar dakin,yayi tsammanin samunta zaune,sabanin hakan


saiya sameta a kwance a rigingine tana bacci sosai,ya qarasa a hankali ya tsaya
kanta hannunsa rungume a qirji ya zuba mata ido,irin kallon daya jima baiyi mata
irinsa ba,abubuwa biyu na kokawa cikin zuciyarsa,ya samu ya kauda su,ya isa gefan
kanta yadan bubbuga filon da take kai a hankali,bude idanunta tayi sannu
sannu,saita tuna inda take,saboda haka ya ware idanun nata da sauri gami da miqewa
zaune sosai tana masa wani kallo da yafi kama da harara
"Ki tashi ki sallah" ya fada yana aje mata takeaway,sannan ya goya hannunsa a baya
ya tsaya yana kallon yadda take kokawar miqewa cikin dabara,da alama tana shan zafi
amma taqi nemon taimakonsa,data gaji da kanta ta koma ta zauna tana lumshe ido
saboda zafin da wajen yake mata,gami da sauke numfashi
"Ki tashi na taimaka miki badon halinki ba"
"Banaso" ta fada da hanzari,sai ya daga kafadunsa alamun bai damu ba ya soma takawa
zai fice,ta kalli agogo ta tabbatar idan ya fita da matsala,lokaci zai iya qwace
mata,ita kuma idan tace zata tashi da kanta zata sha wahala,saboda haka kaman wadda
aka yiwa dole tace
"Dawo ka tayani,amma karka soma tabamin jiki don zaka rakani alwala"
"Riqe jikinki na riqe taimakona" ya bata amsa sanda ya tura qofar kamar xai
fita,tana kallo ya sake ficewa,sai wani abu ya tokare mata maqoshi,ita zaiwa
wulaqanci?.

Sau uku tana gwada takawar amma zafi da tsoro ya hanata,dole ta koma ya zauna
tana kallo lokacin sallah na sake wuceta,baqinciki kamar tayi yaya.

Turo qofar da aka sakeyi yasata daga kanta,shine dai ya sake dawowa dauke da
wata roba dake fidda tururin ruwan zafi,hannunsa dayan riqe da towel,gabanta ya iso
saitin qafar ya aje robar sannan ya jawo wani qaramin qawataccen stool dan gajere
ya dora robar akai,bai kalleta ba ya kama qafar ya dora saman robar,zafi yasa ta
saki 'yar qaramar qara zata riqe hannunsa sai kuma tayi saurin janyewa,tana ji ya
dinga tsoma towel din yana matsewa gami da danna mata wurin,tun tana jin ciwo harya
soma sake mata,radadin ya ragu,tunda ya soma aikin bai daga kai ya dubeta ba,lokaci
lokaci idanunta kan fada kansa ba tare data shirya ba,amma ko sau daya taci sa'a
basu hada ido ba,tsahon mintuna sannan ya miqe ya dauki towel da robar ya fice
dasu.

Sake gwada miqewar tayi wannan karon saita dan taku,a daddafe ta samu ta tura
qofar da zata sadaka da falonshi don dakinta takeson tafiya,sam bata qaunar zaman
dakin nasa,a bakin qofar falon wadda zata sadaka da matattakalar benan suka kusa
karo yana dawowa tana shirin sauka,fuskarnan a tsuke kaman baisan meye dariya ba
yace
"Ina zaki haka?"
"Inda nafi wayo" ta amsashi tana duban ta inda zata rabashi ta wuce
"Koma ba inda zaki,kin dawo nan kenan harsai kin gane kece matar nice mijin,don na
fuskanci baki banbance tazarar dake tsakaninmu ba" wani kallonsa tayi
"Ba inda zan koma,dakina xan koma" girarshi ya dage
"Ashe?,tunda kin yarda dakinki ne can ashe nine mai gidan ko?"
"Oho?" Tace tana juya masa baya gami da turo baki,anwar din yakai mata ko ina,ya
soma quret,ta fuskanci duk abinda zaiyi ya qureta ya iya,saita soma qoqarin
rabeshi,qyaleta yayi harsai data raba tsakiyarsa sannan ya cukukikuyeta gaba daya
cikin qirjinsa ya mata wani kyakkyawan ruqo,karon farko shida ita a rayuwarsu,ihu
ta saki kaman wadda taga abun tsoro tana qoqarin qwacewa,daukarta yayi cak kamar
yadda ya saba mata,abinda tafi tsana kenan,saboda idan yayi hakan gani take kaman
ya raina mata wayo,bai sauketa ko ina ba bandaki,ya ajeta saman toilet sit,ta bude
baki zatayi magana yasa yatsa ya dalle mata bakin gami da cewa
"Shshshs,karki sake ki mana surutu a bandaki" yana maganar yana zaro ido kaman
wanda yakewa qaramin yaro,bacin rai ya hanata magana,saita qyaleshi tana kallonsa
ya daura mata alwalar,zai sake sungumota ya fito da ita ta zille,ta tashi tana
dingisawa ta fito,fafur taqi zama a bedroom dinsa sai a falo,a nan tayi sallarta.

Daidai sanda ta idar wayarta tayi tsuwwa,lokaci daya idanunsu suka sauka kan
jakar,ya rigata saka hannu ya dauki jakar ya zuge ya ciro wayar,zai daga ta dubeshi
"Karka daga min waya,bani abata" fuska a tsuke ya daga kai daga daga wayar da yayi
niyya yi
"Saboda baki da gaskiya?" Saita ware ido tana kallonshi
"Eh bani da gaskiyar,duk abinda zakace kace,ka fadima abinda yafi hakan idan
kaso,bakinka rayuwarka kuma zuciyarka ba tawa ba" ta qarashe cikin hasala,yana
tsaye cak yana kallonta saiya saki murmushi ya dauke idanunsa daga kanta
"Ko baki fada ba dama ai haka yake,dama ai zuciyata ce ba taki ba,haka rayuwata
vata taba zama taki ba ki rubuta ki aje" daga haka ya daga wayar ya kara a
kunnesa,hakanan taji kalaman sun samata ciwo,saita jefa masa harara ta dauke kanta
wani sashe daban
"Lpy qalau....eh,to" kawai taji ya fada ya latse wayar,yana shirin maidata wayar
jakar aka sake kira
"Triple R company" ya furta a fili,ta waiwayo da sauri ta dubeshi,da alama kira ne
daga kamfaninsu,saita samu kanta tana addu'ar Allah yasa ba daga cikin maza abokan
aikinta bane,bata gama wannan tunanin ba tajishi yana bada amsa
"Maigidanta zaishigo ya samu boss dinku,zamuyi magana dashi" daga haka itama ya
yanke wayar,tana kallo ya juya wajen da layi yake ya ciroshi,ya fidda layin saiya
soma lanqwasashi
"Karka karyamin layina" ta fada cikin hanzari,saidai ina tuni ya karyashin ya
watsashi cikin dan qaramin abun sharar dake kusa dasu sannan ya dubeta
"Namiji ne ya kiraki yana tambayar ba'asin rashin zuwanki aiki yau,baisan kina da
aure ba?,ko baya ga haka dole ki rabu da wannan layin,bazan lamunci kici gaba da
amfani dashi ba" ya qureta matuqa ta kasa daure bacin ranta ya bayyana muraran
"Wai me ya dameka da rayuwata ne?,ina ruwanka dani?,me yasa kakeson shishshigema
rayuwata bayan ni bayan ni gana shigewa taka?,bayan ni ban damu da taka rayuwar
ba?,me na tsare maka?,ohk....alwashinka kakeson ka cimma ko na quntatawa rayuwata
shine kake aiwatarwa yanzu?" Tsaf ya xuba ido yana kallonta ba tare daya motsa ko
yace wani abu ba,mamaki take bashi idan tana masifa wanda ko iyawa ma batayi
ba,batasan me yake ji cikin zuciyarsa bane,batasan wanne hali yaje ciki ba,da yana
da ikon maida bara bana daya dawo da ita ya goge dukkan wani tabo da aibu,ba zata
fahimci komai ba,ba zata gane komai ba,tanata amfani da zahiri ne ba tare data
binciki me badinin ta haifar ba,saiya saki hannuwansa kawai gami da fidda qaramin
murmushi,indai ba tunzurata yayi ba bazai taba jin muryarta ba,idan bai tunzurata
ba yasan halinta sarai ba zata taba yin magana dashi ba ko zasu shekare a
haka,yasan halinta tsaf,baijin baya ga mahaifanta akwai wanda yasan halinta sama
dashi
"Donke baki damu da rayuwata ba saime?,akwai dubbai da suka damu da ita,don na
taimakeki ma na rabi rayuwar taki shine kike wani zaqalqalewa kina zaton ke watace
a wajena?" Ido da baki duka ta saka tana son tantance me yake cewa,daidai lokacin
da qararrwar dake nuna akwai baqi can falon qasa ta soma kadawa,saiya miqe kawai
yana tabe mata baki ya fice ya sauka qasa.

Daada ce ita da mubina da khadija,su sukayi waya dazu kan zasu rakota,tun
bikin daada bata koma ba umma tace saitayi sati uku,sai yanzu ta soma shirin
komawa,zuwanshi gidan wajen daada hira babu adadi,ta fuskanci abubuwa da dama game
da zamansu ba tare daya gaya mata ba,da batayi niyyar zuwa gidan ba sam,amma taga
ya kamata ta danyi gyara ko yaya ne kafin ta wuce karta tafi tabar baya da qura,don
tasan umman shahidan koda wasa ba zata taba taka gidan shahida a yanzu ba,donko
hira ake bata sanya baki,yaji qishin qishin din zata zo din yau dalili kenan dayasa
ya tsare shahidan a sama don kar daada ta ramfo komai,don hausawa sunce babba babba
ne,abinda zai gano ko kahau bishiyar rimi ba zaka hangoshi ba.

Shi ya tarbesu daada tahau baza ido


"Ina ita waccar ja'irar,kaine kake tarar baqin ita kuma tana me?" Murmushi ya saki
"A'ah a'ah,kawai yaune na karbata,tana sama batajin dadi ne,ta samu targade a
qafarta"
"To ce mata ta sauko,don tayi targade saboda tsabar son jiki shine zata hau sama ta
nade?,oh ni habiba,yaran yanzu saidai abarsu,kamar wadda ta karye"
"Yi haquri daada karki rudamin mata,kin manta ke mai laifi ce dama?" Ya fada cikin
tsokana,da ido ta bishi baki sake
"Iyeeee....au wato harka soma bin bayan matarka?" Murmushi ya saki sosai sannan
yace
"Yi haquri daadarmu,so so ne amma aisonkai yafi ko?" Kasa amsashi tayi,cikin
zuciyarta tanajin sanyi da dadi na yadda ta fuskanci.yana kulawa da jikarta,ta cika
da fata da addu'ar Allah yasa itama haka take masa kada ta basu kunya,kada kuma ta
watsa musu qasa a ido,mubina yasa ta shiga kitchen ta hada musu abin motsa baki,sai
dayaga ta shirya musu komai sannan ya zqri muqulli don zuwa ya sama musu abinci
"Ku hau saman daada ku sameta kafin na dawo"
"Kaga nifa ba zama zanyi ba,mai motar daya kawomu ma yana qofar gida yana jira in
fito ya maidani,don yau ni kam kwanan garinmu zanyi" qememe taqi barinshi ya
fita,tace saidai yahau sama ya sauko mata da shahida
"Kiyi haquri daada ki hau,ba zata iya saukowa ba"
"Ita sabon qashima taqi saukowa bare ni tsohon qashi za'ace nayi tattaki
nahau,tunda goya mata baya kake tayita narkewa kaga tafiyarmu" daqyar ya lallaba
daadan tahau saman,inda mubina da khadija sukayi xamansu nan falon suna kallo.
Har yanzu tana zaune saman abun sallah a haka daada ta shigo,sai taji dadin
zuwan daadan,tana ganin tazo a daidai,ita ta qulla komai saboda haka dole ta yiwa
anwar magana ya barta ta koma bakin aikinta,ba yabi ba fallasa ta gaidata,ta amsa
tana qare mata kallo,bawani sauyi data gani tattare da shahidan na mace me
aure,saita tabe baki,zata fara magana shahidan ta rigata cikin sautin wanda keson
fashewa da kuka
"Daada ki masa magana ya barni na koma aikina,kinga tun asali da aikina ya
ganni,sannan kuma baice min bazanyi ba sai jiya da nake gaya masa zan koma yace
waina gama aiki,daxun nan kan ku shigo ya dauki wayata ya ballamin layina waina
daina amfani dashi" rashin sani yafi dare duhu,wani kallo daadan ke mata
akaikaice,sai data gama tsaf sannan tace
"Yo ai ni banga wani abun azo a gani dakika tabuka ba daxai nuna kinsan ma kina da
aure,daga ke harshi banga wani sauyi tattare daku ba"
"Kai anwaru" ta kira sunanshi tana zare ido,ya amsa mata ta masa nuni da kusa da
shahida
"Xauna nan" ba musu ya zauna yana qunshe dariya,daada sarkin rigimammu,da alama
akwai magana a bakinta
"Tunda kuka tare ta taba maka kwanan turaka?" Ta jeho masa tambayar kanta
tsaye,take qwaqwalwarsa ta gaya masa abinda take nufi,kunya ta rugo ta
rarumeshi,bai taba tunanin tambayar da zata masa kenan ba,cikin hanzari yace
"Daada ai...."
"Aime?,idan baka da amsa to bari na amsa maka,bata taba ba,kalli qafafunta da
wuyanta,idan tace ma eh to qarya take,oh la'ilaha illallahu muhammadarasulillahi
sallallahu alaihi wasallam" ta debo salati tana tafa hannuwa

_afwa masu karatu,kunsan yadda sabgogi ke kutso kai ciki*Alqawarin Allah*


40

"Ni habiba naga abinda ya isheni.....rahama?!" Tayi kiranta da sunanta na


ainihi,daga ita har anwar din sai sukayi tsuru tsuru suna kallon daada yadda ta
dauki abun,kunya da daurewar kai duk suka cikasu
"Kinason ki gama lafiya kuwa?,kinsan tsinuwar mala'iku kuwa akanki?,so kike ki
shiga wuta da qafafunki?,to wallahi kishiga taitayinki karki jawowa kanki masifa ki
jawo mana,rahama!" Ta sake kiran nata cikin kambama abun,yadda daadan ke magana da
yadda shahida ta soma turo baki fuska a hade cikin bacin rai saiya so baiwa anwar
dariya,shi tuni a nasa shekarun ya fahimci tayine tana sane donta tsorata
shahidan,ta kuma sake kawo gyara a zamansun gaba daya
"Yanzu daada fisabilillahi waya gaya miki wannan maganar?,shi yace miki haka?ko
kuwa ni?" Daquwa ta watsa mata
"Kinci gidanku,don gyatumarki a tsufana ni akwai abinda za'a boyemin?,to wallahi
wallahi tun muna shaida juna ni dake ki gyara duk abinda na gane da wanda ma ban
gane ba,duka kin fini sani ai basai nayi filla filla ba,kin ganni nan bana daukar
sakarci,ba abu bane me wahala na miki dukan tsiya cikin gidan nan kibar ganin kina
da igiya a kanki,girma kuwa ban ganshi ba bare ya hanani dakarki,aiki kuma ba
zakiyishi ba haihata haihata...."
"A'ah daada....ba'ace haihata haihata ba" anwar ya dakatar da daada yana boye
dariyarsa wadda shahidan ta fuskanci hakan,ta sake qulewa sosai,wato ita tako ina
bata da nasara,bata da rinjaye kenan?
"Zatayi aiki idan tanaso....amma ba bisa qarqashin kowa ba sai qarqashina,zatayi
aiki a nawa companyn kuma a office dina" ya qarashe zancan yana duban daada ba tare
daya dubi shahida ba,don yasan kai tsaye cewa zatayi ba zatayi ba,amma ga mamakinsa
sai yaji ta amsa da
"Na amince zanyi" ta amsa masa idanunta qyar a kansa,tasan yayine don ya qureta
yayi da manufa,ita kuwa tacu damarar takura masa itama tunda har ya bullo ta wannan
hanyar,sai daya gama karantarta ta qwayar idanunta sannan ya girgixa kai
"Well,hakan yayi,daga yau daga yanzu ma na daukeki aiki,za'a dinga kuma baki salary
kamar na kowanne ma'aikaci dai dai da matsayinka,salary dinki shine salary na farko
dayafi na kowanne ma'aikaci yawa duba da matakin aikin dana baki" kaita juyar tana
hadiyar bacin ranta,cikin ranta ba haka taso ba
"Shikenan ma,shine daidai,kaga kuna tare ko yaushe,tuwona maina,yamafi tsari" daada
ta fada tana ware hannaye,daga haka daadan ta miqe bayan ta sake kwakkwafar
shahidan,ba yadda anwar baiyi ta zauna ba tace sam,daqyar shahida ta iyayi mata a
sauka lafiya,ya fita rakata.

Cikin kwanakin hakanan shahidan naji na gani ta zauna saman nashi,saidai


kwana uku rak tayi wanda ta jita kaman akan wuta take,a falo duka tayi xamanta,sai
shima ya shareta kawai ya shiga sabgarsa,randa taji dama dama a qafarta ranar ta
sake tarkatawa ta koma dakinta.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

A hankali take takowa zuwa bakin dining din donta samu tadan dumama
cikinta,bayan ta gama shirinta tsaf kamar yadda ta saba duk lokacin da zata je
office,madaidaiciyar kwalliya tayi wadda ta qawatar da ita matuqa,ta sake fidda
kyawunta,kallo daya xaka mata kasan macace mai aji tako ina,wannan itace ranar
farko da zata soma zuwa office din anwar da sunan ma'aikaciya.

Shi dinma yana tsaye daura da teburin yana kurbar tea gami da jefa soyayyen
chips a bakinsa,kacokam idanunsa nakan wata takarda dake saman teburin kusa da
farantin chips dinsa,wanda ke dauke da zanen taswirar wani gini da gwamnati ta basu
kwangilarsa da xasu soma yinsa cikin satin.

Takun daya soma ji shi yaja hankalinsa,har yakai kofin bakinsa ya janye ba
tare daya kurbi tea din ba,daga sama zuwa qasa ya qarewa kwalliyar tata kallo cikin
taqaitattun daqiqa ya kauda kanshi yaci gaba da shan tea dinsa.

Qarasowa tayi itama ta fara hada nata ba tare data dubeshi ba tace
"Gd mrng" fuska a tsuke
"Mrng" ya amsa mata a taqaice shima yana juya fasalin takardarsa ba tare daya
dubeta ba,wani abu ke tsunkulin zuciyarsa,shigarta sai yaga ta bayyana ado da
yawa,duk da ko ina a jikinta rufe yakr ruf ba wani abu nata daya bayyana,amma sai
yake ganin kamar kallonta za'a yita yi idan suka je,dana sanin cewa tayi aiki a
kamfaninsa ya kamashi,inama ace cewa kawai yayi ba zatayi aikin ba gaba daya,gashi
ya ruga ya furta babu damar ya canza,yin hakan zai nuna qarantarsa ne kawai.

Sai daya gama tas ya dire cup din yana cewa


"Wannan shigar batayi ba,kije ki canza wata ki sameni a mota,idan kuma kika makara
to cikin albashinki" daga haka ya juya ya soma takawa,ya dauki handkherchief dinsa
da muqullin mota dake aje saman daya daga cikin kujerun falon,ta bishi da kallo
galala baki sake harya fice,sai daya bacewa ganinta sannan ta dauke idanunta tana
lumshe ido,takaici nason kamata amma tana daurewa.

Yana daga xaune cikin motar,ta baqaqen gilasan da batasan yana kallonta ba
ya xuba mata ido,karo na biyu kenan daya sake maidata ta sauya shiga amma shi har
yau baiga wani abu na kyanta daya buya ba,bayyananniyar ajiyar zuciya ya
sauke,tunda can yasan cewa haka take halittarta ce,duk kayan da zata saka suna mata
kyau gami da dacewa da ita komai rashin kyau ko tsadarsa,agogon dake daura a
hannunsa ya kalla,dole ya haqura ya qyaleta su tafi hakanan,zuwa yanxu ya cinye
sauran lokacin da suke dashi.

Tana zuwa gidan baya ta shiga,baice mata komai ba yaja motar suka fice daga
gidan,suna dab da ginin kamfanin ya tsaida motar,ba tare daya juyo ya dubeta ba
yace
"Dawo gaba" jim tayi sai kuma ta fito don batason ma ta yawaita magana dashi.
Tun daga harabar kamfanin ta karanci yadda suke ganin qima daraja da
mutuncinsa,wannan karon baiyi parking inda kowa yake ba,sai dayaje gaban ginin
sosai sannan ya tsaida motar suka fito,basu shiga ta gaban ginin ba saita bayanshi.

Kallon office din babu abinda ya tuna mata dashi face nata office din,kusan
tsari yanayi da kuma zubinsa kamar nata office din,take kewarsa ta kamata,ta lumshe
idanunta sanda take zaune kan cushion din office din tana jira ya kaita nata
ofishin.

Abinda ya bata haushi da mamaki shine bai wuce yadda taga yayi zamansa kan
tashi kujerar ba ya shiga ayyukan daya taras kan teburinsa ba,yayin da take zaune
shuru bata wani aiki.

Ganin sun cinye awanni biyu cur a haka ya sanyata gyara zama sannan ta dubeshi
"Ban gane manufar ajeni cikin office dinka ba,ka mantane aiki nazo yi?" Sai sannan
ya daga kai ya dubeta,saiya maida kan cumputer dinsa yana cewa
"Na fiki sanin ai aiki kikazo yi,gaggawar me kike?,zakiga aikin naki ai" daga haka
ba wanda ya sake tankawa wani,saidai sau uku tana daga kai sai taga kaman kallonta
yake,daga kanta yasa ya kauda nashi kan,saidai har yanxu bata kamashi dumu dumu ba
shi yasa bata tabbatarwa da ranta hakanne ba.

Minti talatin bayan nan yace


"Hadamin coffee,ki bude can ki ciromin cake guda uku" duk yayi maganar ne ba tare
daya dubeta ba,karon farko daya fara bata umarni irin haka tunda sukayi aure,saita
miqe din tayi yadda yace ta dawo ta zauna.

Ba'a jima ba sosai ya sake cewa ta dauko mishi ruwa,ta dauko ta aje masa
saman table din,saiya daga kansa ya kalleta sannan ya maida kan computer dinsa yaci
gaba da aikinsa,awa biyu tsakani yace ta dauko mishi lemo a fridge,idanunta ta juya
cikin nuna qosawa,ta sauke numfashi sannan taje ta bude ta dauko masa ta aje
"Ba wannan kalar nakeso ba,ki duba akwai wani daban shi zaki dauko min" hadiyewa
tayi ta juya din ta maida ta dauko masa ta aje,saiya dubeta ya kauda kai
"Waishin haka ake bawa mutum abu,a dire masa kaman dutse,baza'a bude masa ba bare a
zuba masa?" Hannayenta ta goya a qirjinta ta zuba masa ido
"Wai na tambayeka?,aiki nazo yiwa kamfani ko kai nazo yiwa aiki?" A nutse ya dubeta
sannan ya ture cumputer din gefe kadan ya hada yatsunsa cikin na juna
"Bakisan cewa nine kamfanin ba gaba daya?" Ido ta fiddo alamun bata gane ba,girarsa
ya daga mata
"Eh,aikin kamfani xakiyi,kuma nine kamfanin gaba daya,babu aikin dayafi nawa
aikin,wannan aikin shine aikinki a office dina,zan biyaki albashi kamar kowa
albashinma daya fi na kowanne ma'aikaci,ba shikenan ba?" Idanu kawai ta zuba masa
tana kallonshi yana fidda qaramin murmushi,tsantsar raina mata wayon da yayi kawai
ya isheta bacin rai,saita juya kawai ba tare data tanka masa ba ta nufi qofar fita.

Gabanta yasha ya tsate hanya


"Ina zaki?,lokacin tashi baiyi ba madam"
"Aikinne na fasa bazanyi ba gaba daya" duka kafadunsa ya daga,hakan ya masa
shima,don baisan ta yaya zai dinga barin mutane na shiga masa office ba alhali tana
ciki
"Fine and good....saiki jira sai lokacin tashi yayi saimu wuce gida" daga haka ya
juya zuwa wajen wayarsa da tunda suka fara taqaddamar ta soma ringing,daga wayar
yayi yana dubawa,wannan shine kira na dari da biyu daya samu da lambar daga farkon
satin xuwa yau,tunda ya daga yaji muryar nafisa bai sake daga wayar ba,don baisan
me kuma zata ce masa ba,me yayi saura tsakaninsu?.

Wayar ta wurgar a gefanta ta fada saman kujera tana yamutsa gashinta,sam ta


kasa jurewa da rashin anwar kamar yadda mima ta shawarceta ta jira sai zuwa wani
lokaci da ita miman ke shirya mata,ta rasa ta yaya zata iya jurewa,daga qarshe dole
tabi zabin ranta ta soma neman khalipha baji babu gani,tana neman hanyar da zata
gyara kurenta,kullum ranta soyuwa take ta gaza sukuni idan ta tuna yanzu haka fa
yana can suna rayuwarsu shida shahidan?,me yasa kishi ya rufe mata ido haka ta
tauyi rayuwarta?,ta yaudari kanta akan ba zata iya aurenshi ba?,bayan tasan cewa ka
ta kawai ta yiwa qarya,ta ina zata soma gyara wannan babban kuskuren data
tagka,tasan cewa abune ba mai sauqi ba musamman idan ta tuna da yadda ta samu
soyayyarshi a baya,saidai koma meye tanajin zata jure harsai haqarta ta cimma
ruwa,sai taga abinda ya turewa buzu nadi,zata aje mima a gefe wannan karon,zatayi
yaqi ta samawa zuciyarta abinda takeso kota yayane ma,idan yaso ta nemi miman daga
baya su dora daga inda suka tsaya.

Dirowa tayi daga saman gadonta ta shiga bandaki ta dauraye fuskarta sannan ta
yafa qaramin mayafi saman kanta ta fito.

Dakin mahaifiyarta ta wuce,ta sameta zaune tana waya,saita samu waje tana
jiranta garta kammala,kusan tunda abun ya faru ta sake dauke mata wuta,a baya ta
sani amma ta nuna kamar abin bai dameta ba,tunda tana tsammanin abinda ta aikata
shine dai dai
"Mommy,zuwa nayi na baki haquri" dubanta tayi sannan tace
"Akanme?" Shuru tadanyi sannan daga bisani kanta a qasa tace
"Nasan na bata muku kan qin auren anwar da nayi,amma a sannan idanuna ya rufe,don
Allah momy kuyi haquri,ki tayani baiwa daddy haquri" tabe baki mommyn tayi tana
miqewa
"Aike za'a baiwa haquri,name zaki bamu haquri tunda kin aikata dai dai,rayuwarkice
fa kuma kika zaba mata abinda kike ganin yafi davewa da ita" daga haka mummyn ta
bude qofar dakin nata ta fice,da kallo ta bita kafin daga bisani ta janye idanunta
tana sauke ajiyar zuciya,lallai aikine ba qaramiba a gananta kafin ta soma shan kan
iyayenta,wanda sune tsaninta na nasararta Wajen anwar,saita miqe kawai tabi bayan
mummyn,sai inda qarfinta ya qare kam.

Lokacin sallar azahar taga ya sanya rigarshi ya fita,hakanan ta miqe itama ta


shiga bandakinsa dake nan cikin office din ta shiga tayi alwala tazo ta tada sallah
kan abun sallarsa dake cikin office din.

Bai wani jima ba da yawa ya dawo dauke da takeaway,ya aje mata nata ya bude
nashi ya wanke hannunsa ya soma ci,ta gefan ido take satar kallonsa,wato har yau
halinshi nacin abinci da hannu dai yana nan.

Ranar haka suka wuni har lokacin tashi,yana aikinsa tana zaune waje
daya,saidai sam taqi zama saitin da zata ga fuskarshi koshi yaga tata,tayi
danasanin karbar tayin aikinsa da biyoshi kamfanin datayi yafi sau shurin
masaki,kome za'ayi kam ba zata taba iya aiki dashi ba,ta gwammace tayita zaman
gidan akan zamansu qarqashin inuwa daya,suna musayar numfashi daya kusa da juna
sosai har kamar haka,ta saurari muryarsa data wulaqantata wulaqancin da har yau
yaqi gushewa yabar zuciyarta,duk sanda ta nutsa duniyar tunani saita tuna kalamansa
da har yau bataji kalaman da suka yiwa kunnuwanta muni kamarsu ba.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Qarfe shida da minti ashirin da biyar na yammaci ya shigo gidan.

,yana zaune a falon yana sauke gajiyar daya tarawa kansa yau,ji yake kaman
bazai iya hawa samanshi ba,da ido yake bin kowanne sashe na falon da kallo,ko ina
fes yake ba alamun datti ko qura,hakanan yana fitar da sassanyan qamshi mai ratsa
zuciya,amma saika rantse ba wani dan adam cikin gidan,sai qarar na'urori kawai dake
fita kadan kadan,ya janye idanunshi kenan yana shirin miqewa yaganta tana
fitowa,sanye take da doguwar rigar atamfa mai gajeran hannu,wadda tafitar da shape
dinta sosai,kama dafa damammen cikinta,qirjinta da yake das cikakku,zuwa mazaunanta
da suka dace da qirar jikinta,kanta babu kallabi sai gashinta dake daure waje
daya,tayi kyau kamar wata 'yar tsana,fatarta ta sake fresh na zama waje daya,da
alama ta fito daukan wani abune,suna hada idanu tayi turus kamar zata juya,sai kuma
ta maze taci gaba da takowa,dab da zata giftashi tace
"Sannu da zuwa" ciki ciki kamar wadda aka turawa tsumma a baki,wanda banda
kunnuwansa dake dukka wajen ba bazai iya jin me tace ba,hakanan yaji yana da
sha'awar ya takaleta,kwana biyu da bai ganta ba saiyaga kaman ya jima bai ganta din
ba,saboda haka ya hade rai qyam sannan yace
"Zonan" yadda ya kirata cikin gadara da bata haushi,amma saita tuna koma meye itace
a qasanshi,saboda haka ta sassauta ranta ta tako inda yake zaune ta tsaya
gefanshi,saiya daga kai yana kallonta
"Me haka?,zaki samin ciwon kai rage tsahonki" dubansa tayi sosai kaman zata tanka
saita shareshi,ta zauna hannun kujerar da take daura dashi,samun kanshi yayi da
qare mata kallo,idanunsa suka tsaya kan qirjinta kamar wani mayen qarfe ke
janshi,idanu ta zaro data fuskanci inda yake kalla,saita goye hannayenta a wajen
abinda ya fargar dashi cewa kallonshi ya zarme da yawa,saiya maze yana sake hada
rai
"Haka kike zama dama idan bana nan?" Ya jeho mata tambayar,mamaki ya kamata,ta kasa
gane me yake cewa?
"Kamar yaya?,ban gane ba?" Ta tambayeshi itama tana kallonshi bayan ta kalli kanta
"Wannan shigar gaskiya bata dace ba" mamaki ya sake kamata
"Waini da waye cikin gidan?"ya gane sam maganarsa bata da makama saboda haka yace
"tunda haka kika zaba shikenan,bani ruwa nasha tunda baki iyaba har sai mutum ya
roqa" ta gane sarai neman abun fada yake,saboda haka ta miqe kawai ba tare datace
masa komai ba ta wuce kitchen din,saiya waiwaya ya bita da kallo,karon farko da
yaji wani abu yana ratsashi tun daga tsakiyar kansa zuwa tafin qafafunsa,ya lumshe
ido yana ambaton sunan Allah,baqon feelings yakeji sosai wanda har yaso danne
gajiyar da yakeji.

Idanunsa ya bude sanda take aje masa ruwan,idanunsa kuwa sukayi kyakkyawan
gani,saiyaji kaman yakai hannunsa kamar ana janshi ne,ya samu da qyar yayi
controlling kansa sanda qamshin turarenta ya soma rarraba mishi hankali,yana kallon
tasoma takawa don barin wajen ya kasa magana sai binta da idanu,da qyar yasamu cewa
"Nace ki tafi ne?" Waiwayowa tayi tana kallonshi fuska a turbune
"Zo nan" ya sake fada,ba yadda ta iya don batason ta saba da dabi'ar musu da
gardama data soma masa ya zame mata jiki
"Zubamin" ya fada yana nuna mata ruwan,haka ta sake duqawa tana zuba masa,ta gama
ya amsa yana nuna mata wata leda daya shigo da ita
"Kaimin dakina" ya dora qafarsa daya kan daya ya soma shan ruwan,baki take turowa
ciki ciki,ya soma kaita bango,ta dauki jakar ta soma hawa saman,nan ma da kallo ya
bita yadda mazaunanta ke juyawa kai kace tana sane takeyin hakan,ajiyar zuciya ya
sauke bayan ta bacewa ganinsa,ya dire cup din da hanzari ya miqe ya rufa mata
baya.n rayuwa_🙏🏽*Alqawarin Allah*
41

_ku ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsofaffi dama sabbabin littafanmu,da
sababbin ma da bakusan dasu ba wadanda zasu fara zuwa muku ta tashar nan gaba kadan
da ixinin ubangiji_

https://youtu.be/-tPtW9YtNpU

Tana shirin fita yana shirin shigowa sukayi kacibus,tadanja da baya tana
neman hanyar wucewa
"Waye ya miki karatun yadda ake zama da mijine?" Yayi tambayar yana dubanta,dagowa
tayi cikin mamaki ta kalleshi,saiya dage mata gira guda daya
"Eh,gaskiya bata iya komai ba kaman yadda na lura,saboda bangani a qasa ba" ya fada
yana takowa zuwa inda take tsaye,yanajin bazai iya barinta yadda ta rikitashi taci
bulus ba ba tare da shima yau yadan taba koda fatarta ba yaji yadda akeji,baya ta
soma ja tana kallonshi,bata fahimci me yake shirin aikatawa ba saida ya kusa qureta
jikin madubin dakin,idanunta cike fal da tsoron da takeson boyewa tace
"Meye haka kakeyi?"
"Abinda kika gani" ya bata amsa bai fasa nufota ba,cikin dan tsoro tace
"Karka tabani" cak ya tsaya yana kallonta
"Tunda kwartone ni?" Ya amsa mata ta sigar tambaya,bai kuma bi ta kanta ba yaci
gaba da nufarta,don baijin zai iya haqura din shima bai d'aana ba,ko ina ta kalla
ya riga daya kangeta,a haka ya hade gap din dake tsakaninsu,ya zagaya hannunsa ta
qugunta ya janyota sosai cikin jikinsa,fuskarsa ya sauko da ita dokin wuyanta yana
kai hancinsa,ta soma juye juye tana son ta qwace daga hannunshi
"Banaso,meye haka,ka sakeni"
"Ni kuma inaso" ya fada yana fidda numfashi saboda yadda abun ya soma masa
dadi,wayarsa dake saman mudubin ta dauki haske da qara,wanda hakan yaja hankalinsu
gaba dayansu,a tare idanunsu ya sauka a tare kan screen din wayar,sunan NAFISA ya
bayyana saman screen din,dauke idanunshi yayi yaci gaba da abinda yake,hakanan taji
wani abu yadan sosa mata rai kadan,amma saita dauka yadda ya tarfata ne yake yadda
yaso da ita,sosai yake shinshinar kowanne lungu da saqo na jikinta yana fitar da
numfashi,ko ina jikin shahidan rawa yake itama,karon farko da irin hakan ya soma
faruwa da ita a rayuwarta,tsoro da haushin anwar din ya cikata ganin da gaske yake
yau ba wasa bane,kaman wanda aka tsikara ya saketa da sauri gami da turata baya
shima yaja baya da hanzari yana zama gefan gado ya dafe kanshi dayaji ya sara masa
lokaci daya
"Ya Allah" ya furta yana ci gaba da dafe kan nashi,hanqota kawai yayi sanda take
rungume jikin wani,bayaso ire iren wadan nan tunanukan su dinga dawo masa
kwanya,saboda haka saiya dinga maimaita
"Hasbunallahu wani'imal wakil" tana zuge zif din rigarta tana mamakin yadda lokaci
guda yasaketa haka,yanayin da taga ya shiga din,saidai itama ba'a nutse take ba
saboda haka tana gama jan zip din nata ta soma tattaki cikin hanzari zata fice
"Dawo nan!" Ya fada cikin kakkausar murya,ba musu tadawo din ta tsaya cak saidai
bata dubeshi ba,fuskarshi a dinke take tsaf babu fara'a ta sisin kwabo
"Shiga ki hadamin ruwan wanka" jikinta a mace take takawa zuwa bandakin,ta hada
mishin ta fito ta shaida masa,saiya miqe kawai ya zari towel
"Karki tafi saina fito" ya fada yana shigewa cikin bandakin,tsayawa tayi cak,ta
jingina da madubi tanajin yadda qafafunta suka mutu,jikinta babu qwari sam,ta soma
tuna yadda taji daxun da yadda abun ya kasance,saita lumshe idanunta tana tuns
komai,qamshin jikinsa daya goga mata yana zarya cikin hancinta har zuwa
qwaqwalwarta,kasala na sake saukar mata,qarar da wayar tashi ta sakeyi ita ta katse
mata duk tunaninta ta sanyata bude ido,bata tabata ba sai dubanta data kai kan
wayar,sunan nafisa ne dai again,saita ci gaba da kallon wayar harta katse,tana
shirin dauke idanun nata wani kiran ya sake shigowa.

Ci gaba tayi da kallon wayar har kiran ya sake katsewa,duk kiran daya shigo
din kan idanunta ya dinga shigowa yana katsewa,wanda a qalla kafin ya fito din an
kira yakai sau goma sha biyar,kuma ba'a fasa kiran ba,bata dauke idonta ba itama
saida taji ya soma qoqarin bude qofar bandakin sannan ta kauda kai tana tunanin
wace wannan haka?,meye ya faru take jero kira haka ba qaqqautawa?,bakin mudubin ya
tako saita matsa gefe tana sake dauke kanta wani sashen,towel ne daure a jikinsa
iya qugu,sai wani daya ratayo wanda duka duka bai gama rufe jikinsa ba gaba
daya,wani nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,gabanta ya dunga faduwa
sosai,ta sake dauke kanta yadda ko inuwarsa ba zata gani ba,baice mata komai ba ya
daga wayar ya duba mai kiran,duka nafisan ce,cikin zuciyarsa yaja tsaki yana
tambayar kanshi me zata masa?,ya aje wayar yana cewa
"Kije ki shirya,zamuje duba anty usaina batajin dadi" waiwayowa tayi cikin faduwar
gaba da fargaba,bala'in kunya da nauyin anty usainan takeji,yanzu kuma zai kaita
gidanta?,saidai a kamatance ma bai kamata ta musa masa ba kodon karamci irin na
anty usainan da qaunar da take gwada mata.

Tana shiryawa amma kiran wayar ya tsaya mata arai,ta rasa dalili,kiran sai
takega kamar yayi yawa,a haka ta gama shiryawa tsaf cikin wani lace,ta yane kanta
da yalwataccen mayafin daya dace da shigar tata,saidata dubawa anty usainan abinda
zata kai mata ta saka cikin jakar hannunta sannan ta fito,a falon qasa suka
hadu,saita tsinci kanta da satar kallonsa duk da bata shiryawa hakan ba,anwar badai
wanka ba,tunda can tun lokacin da bashi da komai mutum ne mai tsafta da kwalliya ma
gaba daya,yayi kyau cikin yadin kufta na maza,dubanta yayi sosai wannan karon
kanshi tsaye babu boye boye
"Wannan qamshin yayi yawa" yana takowa zuwa gabanta,tuna abin daxu daya mata tayi
saitayi hanzarin jaa da baya kada ya maimaita,don har yanzu jikinta a mace
yake,tsayawa yayi cak saiyayi murmushi cikin ranshi,ya gane me take gujewa,itakam
ba wani turare ta saka ba bayan na jikinta,juyawa yayi ya fice ta mara masa baya.

Zata shiga baya kamar yadda ta saba masa taji qofar taqi buduwa,haka tayita
qoqarinta na budewar amma taqi da alama lock ya saka,dole ta dawo gaba ta bude ta
shiga.

Horn biyu maigadin ya dage masa gate din ya saka motar,ya qaraso suka gaisa
da anwar din sanda yake fitowa daga motar,suka soma takawa zuwa cikin gidan,suna
gab da valcony din da zata sadasu da qofar falon tana fitowa cikin doguwar riga da
yalolon mayafi,hada idanu sukayi da anwar,saita kasa dauke idanunta daga
kanshi,gabanta na faduwa qaunarshi na sake ratsa zuciyarta fiye dada,sai taga kaman
an qara masa kyau da haske,ga wani kwarjini na musamman da gake fitarwa,shi ya soma
janye nashi idanun ya soma yin gaba,suka hada idanu da shahida dake
bayanshi,kowacce nata idon cikin na 'yar uwarta,sake kallon shahidan nafisa take
sama da qasa,kishinta na ratsata,ta sake kyau da aji fiye da daa,duk da cewa ba
zata taba mance fuskarba,duk da cewa ta ganeta amma saita janye idonta daga kanta
ta rufawa anwar baya,tana jin wani abu na sukar zuciyarta,da kallo tabi bayan
shahidan har suka wuce,sannan taja qwafa ta wuce,tanajin a zuciyarta wannan karan
kam ba zatabi shawarar mima ba,zuciyarta takai maqurar da bazata iya jurewa ba.

Yana gaba tana binsa a baya cike da kunya har cikin babban falon anty
usaina,gaba daya yaran suke miqe suna musu sannu da zuwa,sa'ida ta soma tare
shahida ta rungumeta
"Oyoyo anty,uncle,amma bakacemin zakuzo da anty ba yau"
"To ai gata kin ganmu" ya bata amsa yana zama saman daya daga cikin kujerun,yayin
da maibin sa'idan ta haura sama donta shaidawa anty usainan zuwan sun tana cewa
"Yanxu ma tahau saman,anty nafisa ce tazo dubata" cikin shi da shahidan ba wanda
yace komai ba,itakam nunawa ma tayi kaman bata santa ba bare ta ganeta,sunata taba
hira da sa'idan,yayin da shi kuma ya shiga tunanin me nafisan tazoyi gidan anty
usainan?.

Dawowa tayi ta shaida musu tace su hau saman,shine dai a gaba tana binsa a
baya har suka bayyana wani falon dake daman,anty usainan na zaune qasan carfet suka
shiga da sallama,fuskar anty usaina wadace da fara'a takewa shahidan lale kota
anwar ma bata biba,a kunyace ta zauna gefan anty usainan tana jin anwar na tambayar
antyn fitilun harabar gidan da wasu suka mutu
"Ka qyalesu hakanan tunda dai gidan da haske ai shikenan" saita sake maida kanta ga
shahida wanda kanta ke sunkuye a qasa,gaidata tayi a kunyace anty usainan ta amsa
cikin kulawa,Shahidan ta mata sannu da jiki ta amsata
"Aina warware alhmdlh,shine sai daya tattagoki" qaramin murmushi ta saki kanta a
qasa cike da jin kunya da nauyinta,daidai lokacin sa'ida ta shigo dauke da tray
wanda ta cikashi da kayan ciye ciye,kai tsaye ta aje gaban shahidan,ta durqusa tana
zuba mata duk abinda ke cikin farantin,qasa qasa shahidan ke kallonta tana dariya
idanu a waje yadda su anty usaina bazasujiba tace
"Sa'idah,wannan duka?,aisai cikin antyn taki ya fashe"
"A'ah anty kici wallahi,yauke baquwarmuce ta musamman"
"Mu kuma aisai a koramu ko?,yauni aka yiwa danwaken zagaye saboda kin ganta ko?"
Tana dariya sa'idan ta daga kai daga shiryawa shahida cake da take cikin plate ta
kalleshi cikin dariya
"Ba haka bane uncle nina isa?,kawaidai nasan ka gayamin cewa kaida anty abu guda
ne,kaga idan na bata kamar kai na baiwa" murmushi yayi yana daga mata hannu yana
satar kallon shahidan,shi sam ya mance daya gaya mata hakan,ya fada ne a gaban anty
usaina don sake kwantar mata da hankali da amintar mata tunaninta,saidai ya manta
sa'idan bata mantuwa,ta kammala zubawa shahida komai ta miqe tana duban anty usaina
"Na gama ummi"
"Shikenan,idan kin sauka ki shiga kitchen ki tafasa min maganin nan,ki samu botiki
mai murfi ki xuba a ciki kidan sabashi yasha iska kafin na sauko shi xansha"
"Tohm" tajuya ta dubi shahida
"Anty kici sosai don Allah ki cinye duka" murmushi kawai tayi tana dubanta,sosai
yarinyar take sonta da burgeta.

Inda shahidan ke zaune ya sauko,ya zauna sosai a gabanta,farantin dake


tsakiyarsu ne kawai ya raba tsakaninsu,idanunsu suka shiga cikin na jina,kowanne ya
zare nashi idon daga cikin na dan uwanshi yana jin yarrr cikin jikinsa saboda
kusancin da sukayi da juna yayi yawa,saiya sanya hannu ya dauki kofin gabanta yana
cewa
"Tunda niba wanda yayimin tayi bari nayiwa kaina"
"A'ah..ban yarda da wannan juyin mallakar ba,aje mata,kaidin baqo ne da bazaka
dauka da kanka ba?" Murmushi ya saki yana tsaida kofin da yayi nufin kaiwa bakinsa
"To ai anty itama ba zata sha ba idan bansha ba" ya qarshe maganar yana waiwayawa
ya dubi shahidan yana kashe mata ido,sadda kanta qasa tayi saboda wani abu dataji
ya saukar mata saman zuciyarta mau nauyi,yakai bakinsa ya kurba lemon ya miqa mata
suna magana da anty usaina,qin amsa tayi har ya gama maganar ya juyo yana dubanta
"Karbi mana,kosai na baki da kaina?" Harara ta cilla masa a fakaice ta saka hannu
takarba ganin yana kai kofin bakinta,ya xuba mata ido sanda takai kofin nata
bakin,tana sane ta juya daga wajen daya sha ta sauya gurbi,murmushin mugunta ya
saki ya waiwaya wajen anty usaina yana tambayarta
"Me yarinyarnan tazoyi gidan nan?,na ganta sanda muke shigowa"
"Nafisa?....waitaji banji dadiba shine tazo dubani,amma tazomin da wata magana da
nace saikazo naji ta bakinka tukunna" ta fada tana dan dubam shahida,batason yin
maganar a gabanta,amma kuma tana ganin yin maganar a gabantan kamar xai bada wani
alfanu game da kawo gyara kan yanayin mu'amalarsu da anwar,don har yanzu bata gamsu
da yanayin zaman nasu ba,tana ganin yadda suke abu kaman baqin juna
"Tace na baka haquri akan kuskuren datayi a baya,tana son idan da hali ka dawo
ka....." Daga kai anty usaina tayi tana duban shahida wadda ta miqe tsaye
"A'ah,ki zamanki shahida mana?"murmushi tadan saki,don tunda aka ambaci sunan
nafisa zuciyarta ta gaya mata ba kowa bace illa wannan wadda suka gani dai sanda
zasu fita,fuskar da anwar ya aiko mata da ita cikin envalope din data baiwa suna da
baqin saqo,hotunan da har yau ta kasa rabuwa dasu dukda yadda suke qona ruhi da
zuciyarta duk sanda ta tuna dasu,ko kuma duk lokacin data kallo gefan da suke aje
"Zan saukane wajensu sa'ida"
"To shikenan,nima ganinan zuwa,ai bamu gama hirar ba"
"Toh anty" ta fada ta juya tana fice daga dakin,anty usaina ta bita da kallo
farinciki na ratsa zuciyarta,tanason karanto wani abu game da shahidan,saita maida
dubanta ga anwar,wannan karon shiya soma magana
"Don Allah anty karki shiga maganar nan,an riga da an wuce wajen tuni,na godewa
Allah da bani na soma gudunta ba bare aga butulcina,ta ruga data gayamin manufarta
tun rannan,kuma kullum kwanan duniya saita aikomin da saqo kan hakan" ajiyar zuciya
anty usaina ta saki,itakam a duniya yanzu ba abinda ya rage mata illa taga kan
shahida da anwar din ya hadu kawai,ta tabbatar idan hakan ta faru babu kuma sauran
wata matsala
"Shikenan Allah ya zaba abinda yafi alkhairi,nikam yanzu bani da burin daya wuce
naga kanku ya hadu yadda ya kamata kaida shahida,yarinyar tana da nagarta
anwar,kayi qoqarin gyara zamanku,gashi kuna qoqarin cinye wata na biyu amma a
karatuna banga hadin kan da nake buqata ba,ajiyar zuciya ya saki yana dan
kashingida kadan,cikin zuciyarsa yana fadin antyn ba zata gane ba,shi kadai yasan
me yakeji kullum kwanan duniya,a raye yake amma zuciyarsa matatta ce,ya gaza gano
dalilin daya sanya shahidan aikata dukkan abinda ta aikata a rayuwarta,meye
sila?,meya janyo haka?.
Shahida na qasa suna hirarsu dasu sa'ida anty usaina ta koro anwar qasan
takuma ce ya turo mata shahidan,sanda taje kusan karatun xama da miji tayi mata
sosai ba kunya ko nauyi tsakaninsu
"Shahida...kiyi haquri da yadda rayuwar aurenku taxo muku ahagunce kuma a
kaikace,farinciki gamida walwalar gida a hannun matar gida take,tana da ikon maida
gidanta aljannar duniya ko kuma akasin haka,duk yadda namiji keda taurin kai,taurin
zuciya da kuma kafiya abune mai sauqi matarsa ta canzashi matuqar tayi karatu mai
yawa akanshi da halayyarshi,kiyi haquri kiyi qoqarin canza gidanki,ki zama mace
sosai,kiyi amfani da hikima da basirarki,kaf dinmu makusantanki dana anwar ba wanda
yake fata ko burin rabuwarki dashi,kinga kenan babu ranar da zaku rabun,tome zayasa
abinda babu ranar yankewarsa maimakon ka gyarashi kaji dadinsa ka amfaneshi saika
zabi dawwama cikin karkatacciyar rayuwa maras dadi?,duk lokacin da rayuwar
auratayya ta kacame ta lalace babu wanda yafi cutuwa a ciki,yafi quntata,yafi zama
cikin wahala baqinciki da bacin rai irin MACE,namiji nada tarin hanyoyin da zai
debewa kansa kewa ya ragewa kansa baqinciki da bacin rai,ba kamar ke mace ba da
taki damar qwaya dayace wannan mijin da kike aure,kome anwar ya miki,duk da bansan
girman cutarwar da yayi miki ba abaya,ina mai qasaqantar da kaina da roqa masa
alfarmar ki yafe masa,ki tashi tsaye ki gyara gidanki,ki masa kyautatawar da
girmanta zaisa yayi nadama yayi danasani,ya kuma ji kunyar aikata miki dukkan
abinda ya aikata mikin,ita mace tana da wannan power,zuciyar namiji a wajenta ba
komai bace horewa ce ta ubangiji,nasan zaki iya din ina kyautata miki wannan
zaton,ina roqar alfarma zakiyimin shahida?"cikin jin kunya da nauyi gamida gasgata
kalaman anty usaina ta gyada kai
"Xan miki anty,zanyi in sha Allahu" ajiyar zuciya ta saki tana lumshe idanu
"Na gode qwarai,amma kafin sannan,ki nutsu ki mu'amalanceshi ta yanayi da sigar da
yake mu'amalantarki gudun kadda kisha wahala,ina fatan kin fahimceni?" Kai ta gyada
mata alamun ta gane,hakan ya yiwa anty usaina dadi sosai,da kanta ta bude cupboard
dinta ta ciro mata wasu rigunan bacci masu shegen kyau da sulbi guda shida,ta hada
mata da turarukan bedroom suma guda hudu masu kyau da tsada,ta amsa tayi mata
godiya sosai,saita danyi jim,anty usainam ta fuskanci akwai maganar da
takesonyi,saboda haka tace da ita ta fada kada taji nauyi ko kunya
"Anty aron sa'ida zaki bani don Allah tayimin ko sati guda ne" baki anty usaina ta
bude
"Keda zaki shiga yaqarmin tunanin dan uwa na hadaki da sa'ida ta hana ruwa gudu?"
Kunya ta sata sadda kai tana dariya
"Shikenan,amma ba zata wuce kwana uku ba"
"Don Allah anty ki barta tayi sati" daqyar ta yadda da hakan,sa'ida murna kaman me
ta hada kayanta ta bisu.

*11:30 pm*

Doguwar rigar bacci ce a jikinta mai sulbi wadda takai har qasa da dogon
hannu,sai baby hijab data sanya wanda iyakarsa saman kafadunta,duk motsin datayi
qamshi ne yake tashi harta iso matatattakalar qarshe wadda daga ita sai qaramar
baranda da zata sadaka da falon samanshi,cak ta tsaya tana ajiyar numfashi,shida
kanshi ya mata magana kafin su shigo gidan kanta taho samanshi saboda sa'ida kada
ta karanci yanayin zamansu,baiso anty usaina ta fahimci komai,baisan yayi sara bane
kan gaba,ta riga data gama shirinta dukda ciwo da takeji a qirjinta da nauyin
alqawarin data dauka,anya zata iya saukewa?,takewa kanta wannan tambayar,duk sanda
fuskar nafisa ta gilma mata a idanu,yadda ya cillota da girman kalaman daya sossoka
mata saitaga gaba daya yayi mata baqi a ido,koren shaidan tayi sannan tayi
bismillah taci gaba da takawa ta tura qofar falon ta shiga.*Alqawarin Allah*
42

https://youtu.be/-tPtW9YtNpU
Yana zaune saman kujera ya miqe qafafunsa gaba daya,sanye yake da gajeran wando
iya gwiwa da vest,hannunta riqe da wayarshi yayin da rabin hankalinsa ya tafi ga
kallon labaran da ake a VOA,bude qofar yaja hankalinsa,ya daga idonsa ya dubi
qofar,hada ido sukayi da ita,ta janye nata idon saboda nauyin ganinsa da take a
haka,yayin dashi kuma yaci gaba da kallonta har zuwa sanda ta iso inda yake,ga
mamakinsa sai yaga tayi wucewarta bedroom dinshi rungume da kaya a hannunta ta tura
qofar ta shige,sai a sannan ya janye idanunsa yana lumshesu gamida budesu duka
lokaci guda hadi da zuqar qamshin turaren data wuce tabar masa,saiya sake miqe
bayansa saman kujerar,ya aje wayarshi saboda kasalar data saukar masa,ya tattara
hankalinsa duka kan tvn yaci gaba da bibiyar labaran.

Idanunta ta waro tana sarawa kanta abinda tayi na farko na wuceshin da tayi
kaman dakinta,ta kalli gadon nashi,fes dashi kaman gadon mace,ta tabbatar shike
gyara abinsa,ta bude ma'ajiyar kayan sawarshi ta aje kayan data shigo dasu a
hannunta,bata kwanciya saida ruwa,saboda haka dole ta fita ta samu ruwa,ta zare
hijabin jikinta ta gyara dankwalin kanta ta rufe gashinta sosai sannan ta soma
takawa ta fito daga bedroom din.

Baiji fitowarta ba sai gilmawarta ya gani zuwa saqon da fridge dinsa ke


ajiye,yaso yiwa idonsa shamaki amma ya gaz,yana kallonta qasa qasa wanda ahaka
saika tsammaci bacci yake ta ciro ruwan gora daya ta juya ta koma zuwa ciki.

Duka addu'o'inta tayi,ta shafe jikinta da su sannan ta dauki remote ta qaro


gudun acn,sannan ta kashe qwan wutan ta koma ta kwanta.

Sha biyu saura yaji zaman ya isheshi,duk da yawancin lokutan yakan wuce haka
azaune ya riga daya saba,saiya kashe duka kayan wutar ya tattare komai ya tura
qofar dakin ya shiga,duhu ne ya masa maraba,ya laluba ya kunna wutar,can ya hangota
saman gadon nashi a kwance abinta,ta tattara dukkan filallukan,wani ta dora kanta
wani qafafunta,wani ta takore bayanta kamar mai ciki,duvet din nashi ma hannunta ta
dora akai don ba rufe tayi ba,hakanan ta raba gadon biyu ita bata gefe guda kuma
bata tsakiya gaba daya,saiya tattare hannayensa kawai ya tsaya yana kallonta,yana
tunanin ta ina zai kwanta?.

Qarar wayarshi ta katse masa tunani,ya cirota daga aljihunsa ya duba,tsaki


yaja ganin wadda take kiran,saiya maida wayar aljihu,ya qarasa side bed ya dauki
remote na ac ya rage sannan ya nufi bandaki ya daura alwala,sallah yayi raka'a biyu
yana saman abun sallah yana addu'a wayartashi ta sake ruri,tsakin dataji yaja tuni
zuciyarta ta gaya mata wacece,gyara kwanciyarta tayi ta soma gunguni qasa qasa
yadda tasan zai iyaji
"Haka kawai a takurawa mutane da waya,sannan a kashewa mutane iska bayan zafi
sukeji" daga kai yayi daga tasbihin da yake qirgawa da yatsun hannayenshi yana
kallonta,saidai bai samu nasarar kallon fuskarta ba,sai bayanta daya hanga wanda
rigar baccinta mai sulbi tabi ta lafe,sake maida kanshi yayi yaci gaba da
tasbihinta ba tare daya sake daga kanshi ba,saida ya kammala komai,ya sanya kayan
baccinsa sannan ya tsaya yana tunanin ta inda zai kwanta,ya jima yana kallonta ta
rigar baccin dake jikinta wata kasala na saukar masa,saiya zauna gefan gadon
qafafunsa a qasa,hannu ya sanya ya dan daki gefan filon da take kai,shuru ta masa
kaman batajiba,saida ya sake sannan ta juyo gaba daya a fusace,cikin rashin saniiii
wuyan rigarta yadan zame,saman qirjinta ya fito bata sani ba,idanunsa suka soma
kaiwa nan,yayi hanzarin janye idanunsa,saiya tsuke fuska
"Bafa wai zaki dinga zuwa min da duk shigar da kikaga dama bane,saboda haka ki
tashi ki saka hijabinki" saidata koma arub da cikinta ta juya masa baya sannan tace
"Ina cewa dai duka gidan nan gidana ne ko?,ko bayaga haka ma ni ban saba kwana da
hijabi ba,ban iya ba saidai kayi haquri kam" daga haka bata sake waiwayoshi ko cewa
komai ba,hakanan ya qaraci zamanshi,dole ya kashe wutar ya dawo daga gefe daya
kaman wanda ya roqa ya kwanta,gamida hade hannayenshi yayi matashin mai dasu karon
farko tsahon shekarun da suka wuce dabazai iya tunawa ba.
Qamshinta shine abu na biyu daya ringa takurashi,ya juya baya a banza,yayi
kai da qafa amma banza,saida bacci yayi masa mugun kamu sannan ya samu salama.

Sanda ta bude idonta ta fuskanci bacci yayi awon gaba dashi,saita miqe ta
sauka daga gadon ta koma saman kujera tayi kwanciyarta,abinda bata sani ba shine
tunda ta motsa ya tashi,kusan ya saba kwana shi kadai,ya jima rabonshi daya kwana
da wani,hakan ya sanya tunda suka kwanta yakejin banbarakwai baccin bai sama dai
dai yadda ya saba ba.

Cikin duhun taji an sureta gaba daya,ihu take shirin saki taji bakinsa cikin
nata,bai ajeta ko inaba sai saman gadon,qarfinsa ya aza mata,qasa qasa yace da ita
"Tunda kika fara saikin sauke,anan zaki kwana kamar yadda kika tattare min filo da
abun rufa"
"Ce maka akai tsoro nikeji?,kawai banda muradin hada gado dakaine"
"Nasan da hakan,kuma saboda sanin baki da muradin yasa na dora mikishi a matsayin
wajibinki" ya fada sanda yake komawa inda ya tashi,saita yunqura zata sake sauka
"Idan kika sauka ban yafe ba" a hankali ta dawo ta kwanta inda ta tashi,jikinta
yayi sanyi da kalmarsa,tasan tabbas idan ta sauka din ba ruwan Allah sai Allah ya
isanshi ta bita.

Washegari data sauko tuni har sa'ida ta kusa kammala kintsa gidan,rainon anty
usaina na wasa na,dama ko a gidan duk yalwar gidan nasu babu mai aiki,ita da
yaranta suke kula da gidan,sai masu share can harabar gidan,saita tsaya ta hada
breakfast, sunayi suna hirarsu harta kammala,cikin dakinta ta shiga tayi wanka,ta
shirya cikin atamfa riga da skert.

Sama ta sake komawa da zimmar dauko wayarta,ta turo qofar bedroom din ta
shiga,saita sameshi xaune gefan gado tana latsa wayarshi,kai ya daga suka hada
idanu,saiya kasa dauke idanunshi
"Ya salam" ya furta can qasan ranshi,sosai kayan suka fidda kamarta,ta dauke kenta
zata gotashi tana gaidashi,baisan ya akayi ba ya tsinci kansa dakai hannunshi ya
fincikota,bata zata ba saboda haka jikinsa tayo gaba daya cikin tsoro,saiya riqrta
gam,ta dinga yunqurin qwatar kanta amma qoqarinta ya gaza,wani irin abu yakeji yana
zagaya jikinsa,idanunsa ya saka cikin nata cikin qanqanin lokaci ya kashe mata jiki
gaba daya,saidai duk da haka bata bari hakan ya nuna ba,hade ranshi yayi sannan
yace
"Bana gaya miki cewa ba kowacce shiga nakeso ba?" Ranta a hade tana sake son qwace
kanta tace
"Nifa gidana ne,kuma sai an kafamin dokar yin dressing?" Girarsa duka ya dage
"Au haka kika ce?,bari na koya miki hankali,gobe idan na hanaki kya sakeyi" daga
haka ya juyata qasanshi ya aza mata dukka qarfinsa,yanayin yadda yake matan saiya
soma bata tsoro,jikinta ya dauki rawa gaba daya ta zaro ido tana kiran
sunanshi,harga Allah yasone kawai ya razanata saboda zuciyarshi da jikinsa ba zasu
jure ci gaba da ganinta a haka ba,zaifison taci gaba da kaikawonta cikin hijabi,don
bayason dukka abinda zai dinga daga masa hankali yana zaman zamanshi,amma sai gashi
yana niyyar wuce gona da iri.

Cikin second daya bacin rai ya rufto mishi,saiya mirgina gefe sannan ya
tashi ya zauna yana dafe da kanshi daya sara masa,zuciyarsa ta cunkushe bacin rai
ya mamayeshi,fuskar saurayin ta bayyana muraran,zayaso ya sake ganinsa a
rayuwarsa,ba shakka duk randa ya sake katarin ganinsa baiga abinda zai hanashi
daureshi ba,me yasa ya shiga rayuwar shahida?,me yasa ya haifar da gibi a rayuwarsu
da har yau ya kasa cikewa?,saiya miqe kawai ya nufi bandaki ba tare daya sake
waiwayarta ba,cikin tsoro ta tashi ta gyara gashinta ta dauki dankwalinta da sauri
ta fice daga dakin.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
Cikin kwanakin duk wata hanya da tasan zatabi ta raunana zuciyar iyayen nata
sai data bi,ta kwantar dakai sosai da kuka da magiya kansu yafe mata,to hausawa
sunce tsakanin daa da iyayensa sai Allah,hakance kuwa ta kasance,suka yafe matan
tare da sake jan kunnenta kanta sake aikata sakarci makamancin wannan,ta kuma nuna
musu ta tuba,farinciki sosai ya cikata ganin ta cimma nasara a matakin farko,saita
bijiro musu da magana ta biyu bayan 'yan kwanaki.

Anan ne kowa yacoge a cikinsu,abban yace sam da kunya a idanunsa bazai nemi
anwar ya dawo ya aureta ba,,ganin abba yaqi saita waiwaya tana hawaye ta dubi mummy
"Mummy don Allah" kaita girgiza
"Wa?,ni?,toba dani ba sa lallen karya,idan anwar ya dawo yau yace zai aureki sai
nafi kowa farinciki saboda sanin nagartarsa,amma a yanzu dai ina bayan
mahaifinki,keda kika bata ke zaki gyara abinki" sosai hankalinta ya sake tashi
ganin ga qoshi amma tana neman tayi kwanan yunwa,anwar kam tun kafin ta tunkari
kowa shita soma tunkara amma*_43R_*

*Alqawarin Allah*
43

Wani irin murdawa mararshi tayi wanda hakan ya sanyashi duqawa riqe da cikinsa,ya
tako a haka a hankali zuwa gefan gadon,idanu ta zaro jikinta ya dauki rawa,ta tako
ta tsaya daga bayanshi amma ta kasa cewa komai,da qyar cikin rawar murya tace
"Sannu,baka da lafiya" kallonta kawai da yayi da qwayar idanunsa da suka kada zuwa
launin jaa ya tabbatar mata da bashi da lafiyar kenan,ta juya zata futa da niyyar
ta kira anty usaina ta shaida mata,saiya dakatar da ita
"Jirani na shirya,zanje naga likita".

Hannu likitan ya saka ya cire abun abun awon jini daya sanya a dantsen
anwar din yana kallonshi
"kamar yadda na tsammata ne,jininka yahau sosai,kamarma yahau fiye da kowanne
lokaci,gaskiya anwar bazan boye maka ba,wani lokaci sai naga kamar kana wasa da
lafiyarka ne,bansan meya hanaka kwantar da hankalinka ba ka samu jinin nan ya sauka
gaba daya,sai yayi kaman ya sauka saiya sake hawa,bansan daga inda matsalar take
ba" murmushin qarfin hali yasaki,ya lumshe idanunsa kana ya bude
"Share kawai khalid" likitan mai sunan khalid ya waiwaya ya dubi shahida wadda ke
zaune wata kujerar daban,hannayenta rungume a qirjinta,ta zubawa anwar ido ba tare
da yasani ba,kallon mamaki take masa na bayanan da taji daga bakin dr khalid,wanne
irin hawan jini?,yaushe anwar din yasamu hawan jini?,iya saninta dashi kaf
tarayyarsu anwar baida hawan jinin,yaushe ya gamu da wannan matsalar?
"Madam" ya kirata wanda hakan yaja hankalinta zuwa kanshi
"Bayan hawan jini gaskiya abokina na buqatar kulawa,don Allah ki kulamana
dashi,nasan kinfi kowa sanin mutumin kirki ne,lalurarshi ba zata yiwa mutane da
yawa dadi ba" kai ta gyada likitan ya miqe yana cewa
"Ruwa naso indan saka maka,amma nasan hali ba zaka taba yarda ka zauna ba,bari na
rubuta maka wasu magungunan na bayar a karbo maka,madam sai a kula da bashi akan
lokaci" kai ta sake gyadawa tana duban anwar din,saita kauda kai sanda taga ya
waiwayo suna shirin hada idanu.

Suna tafe a hanya motar ta dauki shuru,kowa da abinda yake saqawa cikin
zuciyarsa,tambayar ta yiwa shahida tsaye a rai na hawan jinin anwar,yayin data
gefan anwar din maganganun dr khalil suka dinga kai kawo a qwaqwalwarsa,tabbas ba
shakka shine mutum na farko da zaifi kowa son rabuwa da cutar,zaifi kowa son ganin
ya cire kome cikin ransa,zaiso ace ya goge kome dake damunsa,amma saidai shi kansa
yasan hakan bame yiwuwa bane,shahida ce,idan da wata macen ce daban ha tabbatar da
tuni ya cireta daga rayuwarshi irin fitar da mai rai kanyi daga duniya wanda har
abadan bazai dawo cikinta ba,amma akan shahidam hakan ya gaza,ya sani cewa koda zai
fada a baki koda zai nuna a aikace shahidan bata dameshi ba yayiwa kanshi
qarya,karon farko dayakejin inama inama,inama ace bai kalli hotunan ba,inama ace
ranar baije gidansu zance ba bare yaga abinda ya gani,inama ace shahidan bata fada
halin data fada ba a baya,da wannan tunanin suka isa gida,da kanshi wannan karon
yasha maganin sannan ya shiga bedroom dinsa ya kwanta kozai samu relief.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

A kasalance yake shiryawa cikin farar shadda,riga iya gwiwa mai gajeran hannu
da dogon wando,kana ganin yadda yake shiryawar kasan cewa ba wani dadin jikinsa
yake ji sosai ba,yana daura agogon hannunshi ta turo qofar dakin da
sallama,hannunta riqe wata butar shayi me kyau,da mamaki take dan dubanshi saidai
bata tanka ba ta aje butar
"Ya jikin?" Ta tambaya a taqaice,daga kai yayi ya dubeta yadda ta juya baya ya
maida kansa yaci gaba da daura agogonsa sannan yace
"Alhamdulillah" tadanyi taku biyu sannan ta sake tsaiwa,ya fuskanci akwai magana a
bakinta saiya amsa
"Tun jiya akwai alqawari. Haduwarmu dashi,jiya banjin dadi,so yau nakeson nacika"
yana gama fadi ta taka ta sauka daga saman,dama tanson jin fitar zaiyi amma tanajin
nauyin tambaya.

Tun jiya take zuba idanun ganinsa,ta kasa zaune ta kasa tsaye,tun bakwai na
dare take zirya tsakanin harabar gidan,falon abbansu zuwa nasu falon da dakinta ma
gaba daya,ganin goma na dare tayi hankalinta yayi mummunan tashi,Allah yasa abba
bai gane ba,Allah yasa anwar bai kira abba ba ya sanar masa yaji yana nemansa ba
abba kuma yace bashi bane,daga daren zuwa safiyar ranar ji tayi kaman ta zare,duk
motsin shiga da fitar mota a gidan yana kan idanunta,saida dare yayi ta tabbatar
babu wani sauran wanda ka iya zuwa a wannan lokacin sannan ta haqura.

Da safema haka ta dasa abun zama cike da fata da kuma buri,qarfe goma da
rabi da minti takwas aka saki horn mai gadi ya doshi qofar don ya bude,gabanta wani
mugun faduwa yake haka tamiqe tsaye tana duban qofar gidan,kusan shidewa tayi
sanda taga fitowarsa daga motar,idanunta qur akanshi yana sake burgeta duk wani
motsi da yayi,tana kallon aka masa iso cikin falon daddyn,cikin wani mugun hanzari
ta diba tayi cikin gida kai tsaye ta wuce dakinta,hijabi ta lalubo ta zira saman
kanta sannanta sake fitowa da hanzari don kada lokaci ya qwace mata.

Sanda ta shiga mummynta na tare da daddyn,hakan yayi masifar yi mata


dadi,sait tayi qoqarin daidaita nutsuwarta ta taka zuwa cikin falon da sallama.

Dukkaninsu suka amsa mata,ta isa gefan daddyn inda anwar ke zaune qasan
carfet saboda girmamawa suna gaisawa,nan ta duqa kan duka gwiwoyinta,ta saki kuka
sosai wanda ya karade ilahirin falon,duka sakin baki sukayi suna kallonta,mummy ce
cikin hade rai tace
"Kewai meye haka?,wanne irin shashancine wannan kawai zaki shigo kisa mutane a gaba
da kuka?" Cikin muryar kuka tace
"Don girman Allah mummy ku yafemin,ku yafemin,ku roqamin ya anwar shima ya yafemin"
"Me ya dawo da wannan maganar data riga tawuce kuma nafi?"
"Gafarar ya anwar nake nema" gaba daya kanshi ya kunce,shi sam.bai dauki abunda
tayi a matsayin wata matsala ko abun bacin rai ba,tuni ya riga daya wuce wajen,tun
a lokacin da abun ya faru shiya tattara komai daya shafi wannan fannin ya ajeshi a
gefe,baison zancan yayi tsaho saboda haka yace
"Ya riga ya wuce har abada" ranta taji yayi,wani mugun sanyi,alamun nasara na
tabbata kenan a gareta,saita sake sunkuyar da kanta qasa sosai sannan tace
"Bansan cewa nayi wauta ba kuma nayi kwaba saida na rabu dakai,nakai kukana ga abba
da mummy amma kowannensu yaqi mara min baya ka dawo cikin rayuwata,sunce idan ka
amince suna murna da hakan,saboda sunsan cewa idan sukayi maka magana ko bakaso
zakace eh,gani a gabanka anwar don girman Allah inason ka sake dawowa rayuwata karo
na biyu,ka yiwa iyayena dake shauqin son ganin haka alfarma wanda alkunya da
kawaici yasa suka kasa gaya maka"
"Ke nafi!" Abbanta ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsaw,a,bataji komai ba don
idanunta da zuciyarta sunyi nisa wajen son ganin cikar muradi da burinta,saita daga
kai ta dubi abban sannan ta sake sunkuyarwa
"Abba na fadi masa gaskiyar abinda yake faruwa ne,na tabbatar da zaka iya da kaine
xaka nemi ya aureni karo na biyu....anwar,ka duba wannan alkunya da kara ta iyayena
gami da girman soyayyar da nake maka" baqinciki ya kama mummy na yadda sam halayen
nafisan suke wadansu irin mabanbanta daban,ta kawo mata duka anwar ya dakatar da
mummyn cikin sauri
"Rabu dani na mata duka,baki da kunya nafisa ko kadan?,a gabanmu kice kin fasa
aurensa,sannan ki dawo a gaban namu dai kice ya aureki?,wace iriyar yarinya ce ke?"
Cikin kuka sosai nafisan tace
"Kuskure ne mummy yanzu kuma na gane kuskuren da nayi,wallahi idan babu anwar
rayuwata ba zata taba dai daita ba,mummy ku tayani bashi baki"
"Ce miki akayi baida zuciya da zaki gujeshi yanzu ki dawo masa saboda rashin ta
ido?,kema kinsan bazai taba yiwuwa ba" mummy ta amsa mata tana jifanta da harara,so
take kawai ta samu dama ta daki bakin nafisan ya fashe ko zata samu sassauci
takaicin dake cikata
"Na amince zan aureta" anwar ya furta,lafazin daya girgizasu dukka su ukun,basu
taba zata ba sam ko a mafarki,sunyi tsammanin bazai taba yarda ba,cikin hikima yake
karantar yanayin fuskar alhj abba da munny bilkisu,ko basu fada masa ba ya gama
karantar yanayin da zukatansu suka shiga,alhj abba da mummyn suna da daraja a
idanunshi,ya sani cewa tsantsar kara kawaici da alkunya ne dasu,amma da qauna kowa
ya sani suna matuqar qaunar nafisa,me yasa shi bazai iya musu kara ba ya auri diyar
su wanda yasan shine cikon muradinsu,ba shakka da nafisan diyar wani ce da ya barta
kenan har abada,amma ko a lahirama wani yana cin albarkacin wani bare nan gidan
duniya.

"Bazaiyiwu ba anwar,ka tashi kawai kayi tafiyarka" cewar alhj abba,don harga
Allah bayason su xama sila na yiwa anwar din dole,wani tashin hankali ya saukowa
nafisan,ya ga qoshi ga kuma kwanan yunwa tana shirin yi?,me yasa abban nata zaiyi
mata haka?,girgixa kai anwar yayi cikin qarfin hali
"A'ah abba,ba za'ayi haka ba,nafisa qanwa take a gurina idan da kara da
kawaici,abinda ya wuce ya riga daya wuce tunda ta gane kuskurenta,Allah ya yafe
mana gaba daya ya kuma kiyaye gaba" murna farinciki kaman ta taka rawa a
gabansu,saidai yanzu ba lokacin hakan bane,sake kwantar dakai tayi sosai ta sake
neman afuwa gamida nuna tsantsar nadamarta,itakam hajiya bilkisu miqewa tayi ta
fice tabar falon,tana jin ciwo cikin zuciyarta sosai duk lokacin da nafisan ke
roqar soyayya,ta rasa wacce irin diya Allah ya bata?,zataso ace nafisan ta auri
wanda shi yake mutuwar sonta ba ita take mutuwar sonshi ba,ta rasa meye matsalarta
meye damuwarta?,ba kalar saurayin da bata dashi wanda kowa neman yardarta kan ya
aureta yake amma sam ita ta qwallafa rayuwarta kan anwar,eh anwar ya isa mutumin da
za'aso a zama mata a gareshi,amma duka hakan a ganin mummyn xaifi kyau idan har
shine yazo da kanshi ya nemi hakan.

Tunaninsa ne ya dinga kasuwa kashi kashi,abinda ya faru yanxu cikin gidan alhj
abban,tabbas shi shaidane kan irin son da nafisan ke masa wanda sautari hakan yakan
bashi mamaki qwarai,karbar aurenta da yayi yasani shi kadaine abunda zaiwa alhj
abba ya saka masa dimbin alkhairin da yayi masa da kyautatawa a rayuwa,da yadda
yake kallonshi tamkar danshi,saidai ko daya zuciyarsa babu nutsuwa ko jin dadin
karbar da yayi,bayajin wani daidaito ko daya kan batun nafisan,duk da agefe guda ya
sani yana da buqatar kulawar mace,amma,ta yaya wata zata sanyo kai cikin rayuwar
gidan alhali ga yadda take?,ta yaya zai kawo gyara?,tuninsa ya sake tafiya kan
hotunan dake aje har yanzu suna yankawa gami da qona zuciyarsa duk daqiqa ko sa'a
daya da zata shude,duk lokacin da idanunsa suka kai kai,yaha shahidan tsirara tare
da wani sai yaji kaman mai shirin haukacewa,duk sanda ya kallo hoton yaga shahidan
rungume qirjin daya daga cikin masu saida kayan maye sai yaji dama makaho ne
shi,Allah ne kadai da qarfin addu'a suka sashi ya rayu har yakai bigiren da yake
kai a yanzu.
Sassanyar ajiyar zuciya ya saki sanda yake kashe motar shi,ya daga hannunsa
ya kira maigadin,cikin girmamawa ya qaraso
"Baqi indai ba 'yan uwa bane na jiki duk wanda yazo kace musa bama nan"ya qarashe
maganar cikin muryar dake nuna jiki da zuciyarsa duka babu qwari
"To ranka ya dade" ya wuce ya koma bakin qofa yayin da shi kuma ya fito,ya dinga
takawa a hankali zuwa cikin falon.

Shuru yake kaman koda yaushe,saidai ya hangi abinci a shirye saman


dining,hakanan yayi sha'awar xama a falon,idonsa kan wata tasha da suke nuno
fasahar zamani da qere qere,suna wani shirin kan na'ura mai qwaqwalwa,tsohon
mintuna idanunsa nakan allon talabijin din,wani bayani da baqon nasu yakeyi ya
dauki hankalinsa matuqa,yadda ci gaban xamani yazo da sauye sauye,yadda za'a
qirqiri abu a idanunka kaga haka yake,amma da za'a sanyashi a na'ura sai kaga abun
ba haka yake ba,tsahon minti ashirin yana bayanin wanda yayi matuqar daukan
hankalinsa.

A hankali tunaninsa ya karkata ga abunda zuciyarsa keson tuna masa tun


daxun,saiya miqe da hanzari ya soma haurawa saman cikin sassarfa,bai tsaya ko inaba
sai bakin safe din nashi,cikin sauri ya tsugunna,ya soma saka lambobin sirrin ya
budeshi,envalope din ya ciro kaman ko yaushe ya zazzage hotunan ciki duka suka fado
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta kaman yadda ya saba sanda yake binsu da
kallo daya bayan daya,duk sanda zai gansu yakanji kaman duniyarshi sama ta kona
qasa ne,kullum yanajin kamar ranar ya soma ganinsu,saiya zauna sosai zuciyarsa na
fata da kuma burin samun mafita,xuciyarsa ta cika da fatan dama ace ba haka
bane,dama ace ba ita bace,dama ace ba shahida bace a jiki shine bai ganin dai dai
duk sanda zai kalla,saiya sake gyara zamanshi sosai,ta ina zai fara?,bashi da wani
qarfin sani ta wannan fannin,idan kuma yi masa za'ayi duk duniya bayajin akwao wani
mahaluki da zai iya bari yaga hotunan,koda mahaifiyarshi data haifeshi ce inda tana
raye.

Sake miqewa yayi da sauri saboda tunawa da yayi da makarantar computer da


sa'ida ta mishi xancan ummi ta musu register xasu fara zuwa,idan bai manta ba ta
gaya mishi akwai online classes da special classes da za'azo har gida a koya
maka,system yayi nufin kunnawa,sai yaga kamar ba zata masa sauri ba,ya ciro
wayarshi daga aljihunsa ya kunna data sannan ha fada google ya soma rubuta sunan
makarantar,bai manta sunanta ba saboda kusan ma'abocin siyayya ne a shagonsu na
yanar gizo wato www.rahamalls.com,bakin gado ya koma sannan ya rubuta sunan
makarantar *RAHA COMPUTER INSTITUTE* ,cikin qaramin lokaci ya samu dukkan
bayanai,kuma tsarin ya gamsar dashi,ya dauki number dake cikin bayanan ya kira.

Cikin sanin daraja da mutuntaka tadan adam ya sake samun bayanan da yake
buqata,cikin abinda bai gaza awa guda ba yayi register dasu da komai da
komai,ajiyar zuciya ya sauke sanda komai ya kammala,ya duba agogo yaga lokacin daya
kwashe,ya miqe a hankali yana fidda kayan jikinsa,ya sauya wasu marasa nauyi,wando
iya gwiwa sai jallabiyya daya fitar ganin lokacin sallah ya kusa,ya shiga bandaki
ya daura alwala,sanda ya fito wayarshi na ruri,gab da zai isa gareta ta katse,saiya
duba mai kiran,nafisa ce,miscal na shida kenan daga sanda ta fara kiransa zuwa
yanzu,sai a sannan ma zancan ya dawo masa,ya duba saqon data tura masa wanda na
godiya ne da kuma ya yaje gida,aje wayar yayi ya isa inda magungunansa suke ya cira
yasha,sannan ya fesa turare ya qarasa bakin gado ya dauki jallabiyyarsa ya
saka,hakanan yakejin kaman wani nauyi ya ragu daga zuciyarsa.

Cikin mamaki ta dubi table din sanda ta fito daga dakinta,taji kaman ya
shigo amma bataga alamun hakan ba,kaman zata share sai kuma taba hakan bai dace
ba,kodon jikinsa takega ya kamata ta duba,idan lafiya lau shikenan babu buqatar
sake damuwa ko saka ido.

Zai fita ita kuma zata shigo,kusan lokaci daya suka murda handle din,baya
tadanja kadan bayan ta dubeshi ta dauke idanunta,sai taga kaman ya fada kadan daga
jiya zuwa yau da kuma fitar daya sakeyi da dawowarsa,ganin alamun fita zaiyi sallah
saita juya ta soma sauka tana cewa
"Sannu da zuwa"
"Yauwa" ya amsa yana tsaye cak yana dubanta sanda take sauka din,yanajin kaman ya
rintse ido ya bude yaga duk abinda ya farun da wanda ke faruwa a mafarkine,bai taba
kwana ya kwatanta a ranshi ko sau daya rayuwar zata iya zuwa musu da wannan salon
ba,dai gashi lokaci daya komai ya canza,komai ya tabarbare,komai yazo da cikin wani
bahagon yanayi.

Karon farko tun bayan rabuwarsu dayaji wani abu mai kama da tausayi tausayi
akanta saboda tuna cewa nan gaba kadan nafisa xata shigo gidan a matsayin kishiya a
wajenya,ya tuna yadda mata ke komawa duk sanda zance makamancin haka ya shiga
kunnensu yatuna yadda nafisa ta birkice a sanda labarin wanzuwarta qarqashin inuwa
guda ya shiga kunnenta,a sannanma bata zama qarqashin ikonsa na,basu taba kwana
qasan rufi guda ba,inaga ita?,duk da bashi da tabbacin cewa zataji wani abu ko zata
damu,saboda dukkan dalilin dake sawa mace tayi hakan babushi tattare da ita.

"Kidan samu kifi ki dafaminshi idan ba damuwa,zanje sallah na dawo" ya fada


cikin laushin murya wanda har hakan yaso bata mamaki,saita juyo tana kallonshi,suka
hada idanu ta sake dauke kai ganin yadda ya kafa mata idanu,taji kallon nata har
cikin jikinta,sai taba baiken kanta data sanya kaya irin wannan ta zauna haka ko
mayafi babu bare hijabi,amsa masa tayi da to tana ci gaba da sauka daga benan,har
sai dayaga bacewarta sannan ya sauko shima yawuce masallacin.

Sai data soma shiga daki ta samu dan qaramin hijabi ta saka sannnan ta wuce
kitchen din har yanzu tana mamakin irin salon da yayi mata magana dashi,ta ciro
kifi ta gyarashi,ta kauda wancan tunanin na farko ta fada tunanin yadda zata
sarrafashi ta yadda zai dace da yanayinsa,wani gashi ta tuno mai kama da romo romo
da takanga anty xubaida bayi,ba bata lokaci ta soma hadashi,wanda cikin mintuna
qalilan ta kammala,qamshi kuwa ya cika gidan ko ina,ta gyara komai a kitchen din ta
gogeshi sosai yadda ta saba sannan ta fito don barin kitchen din.

Tunda ya dawo yana falon a zaune yana shaqar qamshin kifin har cikin
zuciyarsa,da mamaki tadan dubi sashen da yake din,don iya zamanta a gidan batace ga
sanda ta ganshi zaune haka sosao cikin falon ba,kamar yasan da tsaiwarta shima ya
waiwaya yana dubanta,yabi hijabin jikinta da kallo,shima hakan yayi masa don tamkar
gata tayi masa,baisan me yasa takeson ta zame masa tamkar wani maganadisu ba ko
mayen qarfe aduk sanda ya ganta?,baisan me yakeson sauyashi haka ba,bayan a baya
yasan bai damu da dukka shigarta ba,amma cikin abinda bai gaza sati biyu ba yanason
sauyawa gaba daya?.*Alqawarin Allah*
44

Komawa tayi da baya kitchen din ta shirya komai ta dauko kan tray sannan ta
sake fitowa
"A'ina za'a aje maka?" Nuni yayi kata da gabanshi,ta qaraso nan ta aje ta shirya
komai ta dauko sauran na wajen dining shima ta shirya masa,tayi sarving dinsa
sannan ta yunqura zata miqe saiya dakatar da ita yace ta zauna,ba musu ta koma ta
zauna din,saidai duka bata jinta dai dai,baiyi magana ba harya qare cin abincin
sannan ya soma da cewa
"Da can kafin aurenki ina tare da wata yarinya nafisa wadda har an saka mana rana
lokacin biki ya rage saura sati uku,to wasu abubuwa suka biyo baya wanda ya zama
silar fasa auren namu a wancan lokacin,a yanzu maganar ta dawo wanda ina tunanin
duka ba za'a wuce sati uku ba nan gaba" bata taba tunanin zataji irin abinda taji a
zuciyarta ba'a yanzu,tunda ya ambaci sunan zuciyarta da idanunta suka haska mata
ita,saita dinga binsa da kallo kawai sanda yake bayanansa,gaba daya saita daina
fahimtarsa,duka bayanan da yake kawai tana ganin yana yine saboda radin
kanshi,yarinyar daya aiko mata da hotunanta sanda take tsaka da radadin rashin
mahaifinta?,yarinyar daya turo mata da fuskarta sanda take tsaka da jimami da
alhinin rabuwa dashi?,yarinyar daya kawo mata hotonta ta gani cewa ya samu wadda ta
fita?,ya sauya wata a madadinta,a yanzu ita zai aura ya kawo gidan?,shine yake wani
rufa rufa dason yiwa zancan kwaskwarima?,tana ganin abu mafi sauqi kawai ya fito ya
gaya mata zai cika muradi da burinsa ne,yanzune manufar da yasa ya aureta zai
bayyan muraran baro baro,me yayi saura?,me xata xauna taji daga bakinsa,ai komai ya
qare hakanan komai ya fito fili,sai kawai ta miqe sanda yake tsaka da bayanin
nashi,binta yayi da kallo ganin ta soma tafiya zuwa hanyar dakinta ba tare data ko
waiwayeshi ba,kiran sunanta ya soma yi abinda ya jima rabonshi dayin hakan,saidai
ko daya bata saurareshi ba bare taji me yake fada,da hanzari ya miqe ya bi
baya,taji takun tafiyarsa,saboda haka tana shiga dakin ta saka key,ta samu gefan
gadonta ta xauna ba tare datasan me zata tuna ba,wani kuka ne mai sautu ya qwace
mata wanda ta kasa tsaidashi,hannunsa saman kanshi yana yamutsawa jin sautin
kukanta dake ratso har inda yake tsaye
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta yana kallon qofar dakin da yayi juyin
duniya ta bude taqi,bai taba xato ko tunanin xata damu ba ko sau daya,me yasa ta
damu?,me yasa ranta yw baci?,bayan ta gaya mishi cewa bata qaunarshi ko kadan?.

"Me yasa kike kuka shahida?,kukan me kike?,kins kukane saboda mutumin da kika
dainaso xai qara aure?,ko kina kuka ne saboda mutumin daya daina sonki xai auro
wadda yakeso?,muradin zuciyarsa?,haske rayuwarshi?,meye abun damuwa a ciki
shahida?,har yanzu anwar na cikin zuciyarki ko kuwa?" Tambayoyin da zuciyarta ta
dinga mata kenan wanda yasa ta soma tuhumar kanta da kanta.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Duban nafisan mima takeyi sosai da wani irin banzan kallo,cikin ranta ji take
kaman ta tashi ta shaqe nafisan,cikin ranta tana ala wadai da sakacin da tayi har
ta bari tunanin nafisa yakai gata nemi anwar karo na biyu,tabbas da tasan da irin
wannan ranar da tunu ta saka almakashi ta datse alaqar da tayi saura tsakanin anwar
din da nafisan,koda yake a yanzu ma bata baci ba,saidai kuma ba haka taso ba,dole
ya saka taka tsantsan da nutsuwa dinta wargaza tsakaninsu,don a yanzu bata da burin
daya wuce ta ganta itama gidan anwar din a matsayin matarsa,sake duban nafisan tayi
a karo na biyu yadda taketa faman fara'a,bakinta kamar zai hade da kunnenta,irin
kallon da miman ke mata yasanya jikinta yadan soma sanyi
"Ko bayi dai dai bane hajjaju?,bafa zan iya haqura da anwar ba matuqar ina raye
shima yana raye" baki miman ta tabe tana ci gaba da dubanta
"Dama aida kin jira ni nidin xan miki wannan aikin,abinda yasa kika ji shuru ba'a
kai gabar bane,naso mu gasashine harsai ya kawo kanshi da kanshi ta yadda koda kin
shiga saikinfi daraja da qima a idanunsa,amma a yanzun yadda kikayi wallahi qimarki
ta zube qasa warwas,kuma haki da wata fuffuka da xakiyi idan kin shiga
gidan,hasalima ba baiyi matsuwar shigowarki gidan ba kinga baki da abun cewa sawa
ko hanawa koda kin shiga gidan" sai jikinta ya danyi sanyi,taji maganar mima tabbas
tana kan hanya,shigen maganar da mummynta ta gaya mata kenan,ita kuwa a rayuwa
yanzu burinta na gaba shine ta shiga gidan anwar ta zama ita ke fada aji,ita zata
sa ayi ta hana kuma a hanu,wanda daga qarshe take fatan shahidan ta fita tabar mata
gidan gaba daya taci gaba dayin yadda takeso.
"Gaskiyar magana mima banason nayi rayuwar da bani zance ayi ba cikin wannan
gida,saboda har yau ina tsoro kuma ina shakkar soyayyar dake tsakanin anwar da
wannan mayyar yarinyar" abun nema ya samu wajen mima,hanyar da zata wargaza rayuwar
auren nafisan cikin sauqi,duk da haka saita sake tsuke fuska ta kuma gum da bakinta
harsai da nafisan ta sake magantuwa cikin mitar tayi mata shuru,fuska ta yatsina
"In sake shiga sabgarki ki watsamin qasa a ido?,ina qoqarin fiddo miki da daraja da
martabarki amma ke baki gani,gwara kawao na qyaleki kici gaba da samawa kanki
mafita" harara ta watsawa miman
"Banason wulaqanci wallahi mima,haba don Allah,sau daya dai don nayi amfani da
shawarar kaina saiya zama matsala?" Sai data gama shan qamshinta sannan tace
"Shikenan,zaki samu yadda kikeso,zaki mulka anwar ki kuma juyashi shida waccar
yadda kikeso matuqar zaki jure ki kuma bi doka da qa'ida,zan dawo next week randa
kikacemin zaki fara rabon IV zakiji sauran qarin bayani" kamar ta goya mima haka
nafisa taji,kudade masu yawa ta baiwa miman sannan ta rakata.

Dariya mima ta saki bayan ta gama irga kudaden,mota takeson sauyawa,kuma ba


shakka lokacin da zata sauya motar da takeso din yayi,a jikin nafisan zata hada
kudinta tsaf,daga qarshe kuma ta tashi a tutar babu,ba anwar din ba kuma
kudinta,daga haka ta tada motarta taci gaba da tafiya tanabin waqar dake tashi
cikin motar cikin nishadi gami da tsara yadda zata mallaki anwar ita kadai bayan ta
fitar da shahida da nafisan ma daga gidan dukkansu.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Kaman a mafarki take jiyo sallamar anty xubaida cikin falon nasu,da sauri ta
sauko daga gadon wanda ta maidashi wajen rayuwarta,idan kaga ta fito tota tabbatar
anwar ya fita baya gidan sannan zata fito tayi aikace aikacenta a gaggauce ta
koma,sam bata qaunar haduwa dashi ko daya,Suna shirin yiwa kansu mazauni ta fito
fuskarta a washe
"Anty yau a gida na?,ashe xakixo?"
"Kamawa ai take,gashi ta kama shahida naxo" cikin walwala da farinciki ta tarbesu.

,sun jima sosai ranar,sunata hira dasu huda,duk sai yaji kewar gida ta sake
kamata,kaman ta koma gidan haka takeji.

Saida suka dan kebe sannan anty zubaidan ta gaya mata abinda ya
kawota,zancan auren anwar,kebe fuska shahidan tayi cikin nuna halin ko in
kula,saidai can qasan ranta wani abu ke tsinkulinta,maganganu sosai anty zubaidan
tayi mata,gami da jan hankalinta,suna gama cin abincin rana tace zasu koma,kaman
shahidan tayi kuka amma hakan ta haqura,taso sosai antyn tabar mata hudan amma
qememe taqi,haka suka tattara tanaji tana gani suka tafi.

Zuwan antyn yasa tadan sake ranta,ta koma sabgoginta kamar baya,saidai ta sake
janye sosai daga anwar din,sati biyu da faruwar hakan anwar ya shigoda set din
manyan akwatina guda hudu,da farko tayi burus amma daga bisani tayi tunani kada ya
tsammaci kishinsa take saita karba ta masa godiya,yayin daya bita da kallon
mamaki,da gaske bata jin kishinsa? Hakan na nufin bata sonshi?.

Cikin kwanakin ka'in da na'in ya maida hankalinsa ga koyon abinda yasa gaba
daga raha computer instute,ya ware lokaci har gida yake iskeshi malamin,baisan me
yasa abun ya tsaya masa a rai ba,bai san me yasa ya maida hankali fiye da yadda ya
xata ba,wanda yake da tabbacin cewa cikin wata uku ya cimma abinda yakeso ya cimma
din,ta bangare guda guda kuwa yayi qoqarin kawo sauyi ko yaya yake tsakaninsa da
shahidan,don ko kusa baida burin nafisa taxo ta fuskanci komai dangane da
zamansu,duk da qoqarin nasa sau da yawa yakan cimma tasgaro,saboda rashin samun
cikakken hadin kai daga shahidan.

Ta bangaren amarya nafisa kuwa shirye shirye sun kankama ka'in da


na'in,dukkan wani abu da aka sani na bidi'ar biki ba wanda bata tsara xatayi
ba,harda ma wanda ba' saba gani ba,ko sauraren abinda anwar din zai bayar
batayi,sha'aninta kawai take.

Qarfe shida saura malamin da suke karatu tare ya tafi,yarage saura shi kadai a
dakin,ya shiga cumputer din sosai yayi shige da fice wanda ya tabbatar masa lallai
ya soma nisa,hakanan yana cimma abinda ya nufa din,saiya kasheta yana sakin
murmushi wanda yayi dai dai da shigowar kira a wayarshi,duban wayar yayi sai yaga
nafisa ce,ya manta shaf cikin satin zasuxo jeran kaya,bai daga ba harta katse,saiya
janyo wayar yana laluba inda ya aje numberta,cikin sauyin da aka fara samu wanda
ada bashi da ita.
Har tayi ringing sau biyu tana katsewa ba amsa,sai ana ukun sannan ta
daga,shuru tayi tana sauraren muryarsa wadda ko mutuwa tayi ta dawo ba zata kasa
gane muryar waye ba
"Bakisan ina cikin gidan bane?" Ya tambayeta ganin tsahon zamansu baiji motsinta ko
gilmawarta ba,shuru babu amsa saboda haka ya kautar da wancan zancan
"Ki sameni a dakin karatuna....am yana nan daga baya kaman zaki shiga qofar kitchen
ta baya" ya sake mata bayani don ya sani bata sani ba,tunda bata taba zuwa ba.

Wayar ta sauke tana jin wani haushinsa na kamata,tome zaiyi mata,kiran me


kuma yake mata?.

Har sai daya zaci ba zata zo ba yaci gaba da aikinsa sannan yaji an murda
murfin qofar,ya daga kai yana kallon bakin qofar,itace cikin jar doguwar riga wadda
ta yane kanta da qaramin mayafinta,idonsa ya dauke wani abu na tsirga masa,ba
kwalliya a fuskarta amma tayi masifar amsarta rigar wanda ya kasa kubuta daga
qyasata da zuciyarsa tayi.

Daga sallama bata sake cewa komai ba,ta samu gefansa ta zauna,saiya kashe
wayar tashi da yake dannawa,ya juyo gaba daya suna fuskantar juna sosai yatsunshi
sarqafe da juna idanunshi cikin nata,fuskarsa na nuna zancan da zaiyi mai
muhimmanci ne,sai taji kallon da yamata nauyi,ta kauda kanta gefe guda
"Gobe jibi gata masu jeren amarya zasu zo...."
"Me zanyi musu to?,meye amfanin gayamin din?,Allah ya kawosu lafiya" ta fada cikin
zafi zafi wanda ita kanta batasan ta aikata hakan ba,idanu ya zuba mata har takai
aya sannan yace
"Babu abunda xaki musu,kawai inason ki kwashe kayanki xaki koma dakunan sama"
waiwayowa tayi tana dubanshi,me zataje samanshi tayi masa,dai kawai ta miqe ta soma
takawa tana cewa
"Na barwa amarya,inda nake nan ya isheni na qarasa kwanakin da suka ragemin" bai
fuskanci me kalmarta ta qarshe ke nufi ba,amma ganin zata fice sai yace da ita
"Umarni na baki ai ba shawara bace bare ki gayamin naki ra'ayin" daga haka shima ya
juya abinda shida kujerarsa,saita waiwayo tadan dubeshi kadan sannan taci gaba da
takawai ta fita daga dakin.

Tana shiga nata dakin taji kuka ya qwace mata,duk yadda taso hana kanta abun
yaci tura,batasan me yasa takejin bacin rai da damuwa ba,kuka tayi sosai kafin taji
zuciyarta tayi sanyi.

*BAYAN KWANA UKU*

Tana kwance rub da ciki saman gadonta,sanye da wata doguwar riga na wani yadi
me sulbi wanda yake kama da yadin satin,hakan yasa yabi jikinta ya lafe,gajeran
hannu ne dashi gami da wuyan half shoulder wanda ya fitar da wuyanta da wani sashi
na qirjinta sosai,kanta babu dankwali kana a tsefe yake,hakan yasanya gashinta da
bata kamashi da ribbom ba ya biyota shima ya kwanta saman filon da take kai,gama
wayarta kenan da ummanta tana nazarin maganganun data gaya mata taji an murda qofar
dakin,wanda hakan yaja hankalinta zuwa kallon qofar,yana shigowa idanunshi cikin
nata,mamaki ya sanyata miqewa ta zauna sosai saman gadon,tama mance da irin dinkin
da yake jikinta,idanunta fal da alamun tambaya,jingina yayi daura da qofar ya goye
hannayensa a qirji yana qare mata kallo,sai a sannan ta tuna da rigar jikinta,tabi
kanta da kanta da kallo saita daga kai tana hade fuskarta tsaf,miqewa tayi ta nufi
wardrobe dinta ta soma lalubar mayafi,yana tsaye still yana kallonta har yanzu
baice komai ba,harta gama yafa mayafin ta dawo gefan gadonta ta zauna
"Ki shirya gobe qarfe tara na safe xamu fita tare xan saukeki gida" fuska a tattare
ta bishi fa kallo har ya fice,saita ja qaramin tsaki ta koma ta kwanta tana tunanin
ina zai kaita?,kuma me zata fita tayi.
Tara saura tana tsaka da shirinta wayarta ta shiga ruri,ta qarasa inda take
aje ta daga tana duba mai kiran,anty usaina ta gani,a ladabce ta daga suka gaisa
sannan tace
"Na kasa samun layin anwar,inata kira busy,taimaka don Allah ki gaya masa idan zai
fito ya fito da wadan nan takardun"
"Toh anty" ta amsa mata a ladabce tana aje wayar,qarasa shiryawa tayi sannan ta
fito ta haura saman nashi,tana shiga yana aje wayar gami da miqewa ya tura qofar
toilet ya shige,bata masa magana ba don qyashin hakan takeji,saita barshi ta samu
saman kujerar mudubi inda ya tashi ta zauna tana dakon fitowarsa.

Wayar daya aje saman mudubi wanda take dab da ita ta dauki ruri,idanunta kai
kan me kiran,nafisa ta gani,ta riga data haddace sunan,saita dauke kai saidai
hankalinta ya kasa daukuwa daga kai,tana jin sautin ringing din har cikin kanta
harta katse,aka sake kira ta sake katsewa,ba jima wani kira yasake shigowa,batasan
sanda taja wani mugun tsaki ba ta finciko wayar ta kasheta gaba daya ta dangwarar
da ita awajen,tana tuna sanda ta shigo waya taga ya gama,wala'alla ma shi yasa anty
usaina ta gaza samunshi wayama yake kenan
"Ina ruwana da wayarshi" ta gayawa kanta tana sake tsuke fuska ita kadai,daidai
lokacin daya fito daga bandakin jikinsa jiqe da lema,da alama wanka yayi,fuskarta a
dinke tsaf cikin kaushi tace dashi tana miqewa
"Anty tace karka manta ka fito da takardun nan" daga haka tayi gaba,binta yayi da
kallo,tana gab da ficewa yasha gabanta,ya murza key ya rufe qofar,saita danja da
baya tana dubanshi,kuka takeson tayi amma batasonyi a gabansa,don tasha alwashin ta
daina yi din yana gani yana jin dadi
"Ka budemin na fita na qarasa shiryawa" ta fada cikin sanyi,wanda ba haka taso,taso
tayi maganar ne cikin kaushi da zafi,saiya kada kai yana duban idanunta wansa hakan
yaso mata tasiri,saita zare nata idon gami da kauda kanta wani sashen daban.

_Dadai zakuyi haquri harmu cimma manufar labarin,don kowanne labari yana da manufar
da akeso a cimma,idan kuma kunason shortcut shikenan_

Mai yiwuwa gobe kujini shuru,idan kuma Allah ya bada dama to.

*karku manta kuyi wekend dinku da tashar SAUTIN HIKIMA dake youtube,ku saurari
littafanmu ba tare da kunsha wahalar karatu ba kuna daga kwance*💃🏻

*Asha weekend lafiya*🤝*Alqawarin Allah*


45

"Zuwa yanzu ya kamata ki fara koyan wasu abubuwan,saboda karta shigo ta rainaki" ya
fada yana son dawo da salon tsokanarshi.

Wani kallo ta watsa masa da idanunta sanda yake komawa zuwa bakin mudubi,wani
abu ya tokare mata wuya
"Wace zata shigo din?,bani ya kamata ka gayawa wannan maganar ba,don ni ba kallon
mijina nake maka ba" saiya waiwayo yana zare idanu
"Da gaske?,lallai kinci tuwo da yawa,wait....waima kallon me kike min?" Harara ta
sake watsa masa ganin yanason maida abun shirme kamar yadda ya saba,baisan yadda
ranta ke tafasa ba
"Oho,koma meye ba damuwarka bane,ka budemin qofa kawai na wuce,abu daya na sani
shine,daga kai har ita kada wanda ya sake yashiga hurumina" baki ya kama yana
kallonta,sau tari yakanso yaga tana rashin kunya,sai dan qaramin bakinta yayita
burgeshi,don a tsahon xamansu na baya bai taba ganin tana tsiwa ba sai yanzu
"Idan kuma akaqi fa?"
"Raine zai baci" ta amsashi kai tsaye,qaramar dariya ya bushe da ita
"Kinga...kawai ki fito kice kishi ne yake damunki ko?,to kiyi haquri,na miki laifi"
sake hararshi tayi,tanajin kaman ta makeshi ko zataji sauqi
"Ni na gaya maka duka wannan na damuwata bace,bama kallon miji nake maka ba bare
nayi kishinka,ka budemin na fice kawai"
"Aiko kin makaro,dakin yadda kawai da hakan yanzu zan bude miki qofar salin
alin,amma tunda kika musa to sai na gama shiryawa tsaf sannan zan bude ki mu sauka
tare" tanaji tana gani yayi funfurus yahau shiryawa a gabanta ko kunya baiji,haka
ta zauna ta kallo bango harya gama ya budeta.

Har daki yabita ta gama daukar abinda zata dauka kaman wani body guard,tana
kumburi tana komai amma bai kula ba ta fito suka fita.

Gidansu ya soma kaita,ta cika da mamaki sanda suka isa taga ya sake cikinsu
sosai kaman yadda suka saba a baya,sai taga kamar ma sunfi zumudin zuwanshi akan
nata,hira suke abinsu da umma kamar danta,baqinciki yasa ta kasa sakewa ma bare
tayi hira,basu bar gidan ba sai qarfe daya da rabi na rana bayan yaje masallacin
layinsu yayi sallah sannan yace ta taso,kaman ba zata tashin ba,don ita sam lokacin
bai isheta ba,amma yadda umma ke jifanta da harara yasa dole ta miqe tabi bayanshi.

Daga nan gidan anty zubaida sukayi,can dinma haka suka gaisa da antyn cike da
sabo,sannan ya yiwa anty zubaidan sallama kan zaije anjima zai dawo ya dauki
shahidan.

Kusan fiye da rabin hirarsu ya ranar jirwaye me kama da wanka anty zubaidan
ta dinga mata da gugar zana,ta kuma fahimceta sarai saidai tayi kaman bata gane
ba,duka dai kan zamantakewarsu ne da nafisa dake shirin shigowa gidan,wanda duka
ita tana ganin wannan ba matsalarta bace,dubanta anty zubaidan tayi sanda suke
tsaye cikin kitchen tana tayata yanka cabbage zata hada coleslow
"Ranar yaushe zaki yinin naki ne banji kince komai ba,yaufa alhamis,lahadi kuma
daurin aure" baki ta tabe bayan ta dubi anty zubaidan
"Ko nawa bikinma ban tsaya wani tsara wuni ba bare bikin wasu" ta fadi cikin
qunquni,murmushi ya subucewa anty zubaida saita kada kai,lallai yaro yaro ne,ga
zallar kishi na bayyana kan fuskarta da kalamanta amma taqi yarda da cewa kishi
take
"Wancan daban wannan daban,bakyace ba zakiyi ba kodon idon mutane,kuma kema zaki
buqaci wadanda zasu tayaki karbar amarya"
"Waini zan karbeta ma?" Ta fada tana nuna kanta da wuqar hannunta
"Eh mana,haka akeyi ai" saita jijjiga kai tana ci gaba da yankanta
"Lalllai kam" anty zubaida ta fuskanci zancan ciwo yake mata ba tare datasan da
hakan ba,sai kawai ta shareta suka shiga wata maganar daban.

Bayan sunyi sallar la'asar anty zubaidan tace tazo ta rakata kitso,ba musu
ya dauki mayafinta suka fita a motarta,huda tace zata bisu antyn yace sam tayi
zamanta,suna tafe a motar antyn na nuwa shahidan wasu robobi masu dauke da gumba ta
kwakwa da dabino,wanda idan kanaci zaka xaci an hada kayan qwalamane kawai sai aiki
a jiki,wadda takan jima jikin mace bata bar jikinta ba,ta dinga mata dabara kanta
dandana mata taji,haka ta dinga ci suna hira,antyn tana tuqi a hankali har sai
dataci da yawa,ta sake nuna mata wata roba wadda ke cike da tsumi tace
"Sha kiji wannan fa"dan bata fuska shahidan tayi
"Wainikam anty wadan nan ba irin kayan nan naku bane na matan aure?" Harara ta jefa
mata
"Ke matar shika ce?" Sai zancan ya bawa shahidan dariya,ta bude robar ta ta soma
sha,zaqinsa da dadinsa yasa sai data sha rabi,abun har ya baiwa anty zubaida dariya
tace
"Ya haka?"
"Wannan kam yayi dadi sosai shima"
"Tsumin maman farida ne,jiya aka aikomin shi daga zariya"tana rufe robar tace
"Amma yayi dadi wlh ya tsumu" dariya ta sake baiwa antyn.
Bata gane inda sukazo ba saida anty zubaida tayi parking,wajen da aka mata
gyaran jiki ne na aure,saida suka shiga ta gane wai ita antyn ta kawo ayiwa,narke
mata tayi don ita sam bata sha'awa,hasalima tasan cewa asarar kudi kawai za'ayi
"Don Allah anty,iya qunshinma kawai ya isa" daga qarshe dai da qunshi kawai aka
tsira ja da baqi,itama antyn aka mata jaa sannan sukayo gida,zuwa lokacin har anyi
sallar magariba,saboda haka tana shiga salla kawai tayi,ko abinci bata ciba ya iso
suka wuce.

Tun daga falon qasa taga gidan gaba daya kamar ba nata ba
"Sama zaki wuce" ya furta mata yana zama saman daya daga cikin kujerun,bata
kulashiba ta shige,saidai tayi tayi qofar dakin nata ya budu amma sam yaqi,haka ta
dawo falon tana raba ido zuciyarta fal qunci,da gaske kenan ya maidata saman ya
saka nafisan a nata dakin?,zuwa yanzu baya falon,haka ta gaji da zama a falon bacin
rai na sake cikata,tilas ta haura saman.

Dakin da yake kallo nashi ta tura,komai na dakin sabo ne kaman yadda kayan
falon saman ma suke sabo dai dai dana qasan,abu daya yasa ta gane dakinta ne
takacen kayan makeup dake jere saman mudubinta gasunan jere saman sabon
mudubinta,ta jima tana qarewa dakin kallo yadda yatsaru yayi wani kyau,dukka
colours din ciki masu kyau da kwantar da hankaline,sai data gaji don kanta sannan
ta cire kayanta tafada wanka,tana wankan tana kallon lallenta wanda yayi kyau sosai
ita kanta ya burgeta.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Kallo daya zaka yiwa fuskarta ka tabbatar da cewa yau din rana ce ta musamman a
wajenta,hakanan farincikin da take ciki ayau din shima farinciki ne na musamman.

Ta kasa boye duk wani jin dadi da walwalarta,duk da cewa yadda taso ba duka
haka anwar yayi mata ba,dinner daya yaje mata a gaggauce,hatta yau da yake daurin
aurensu tana da labarin a makare ya iso wajen,bai kuma jima ba ya koma,saidai duka
wannan ba damuwarta bane,da taimakon mima tasan cewa komai zai daidaita,zata kuma
samu yadda takeso.

"Qawata jimana" mima dake tsaye dankwali gaban goshi ta fada bayan ta gama
yiwa duk yarinyar dake madaidaicin falon nafisan kallon tara saura
"Kowa zaici uwasa" ta fadi a ranta,shigowarta kenan ita dinma batazo da wuri ba,ta
jima tsaye daga waje tana kallon yafda nafisa ke wani rawar kai kamar zata taka kan
shege
"Gani,ta samu ne?"
"Eh kusan hakanne,amma qawata,bayan sauran event da ango baizo daurin aurenma ance
a makare yazo ko?" Tabe baki nafisa tayi da alama tadanji haushin abun
"Hmmmm,wallahi in gaya miki mima,ban sani ba ko waccar matar tashice ta tsaidashi
Allahu a'alamu"
Sake tabe baki mima tayi
"Waxai hanashin idan ba ita ba?,kinga abinda nake gaya miki aiko?" Sanyin jikin
nafisa yayi,saita zubawa mima ido kawai tana kallonta,da alamun neman mafita
take,hakan yayi dai dai da tsarin miman,saboda haka tasa hannu cikin jikirta ta
fito da wani qullin baqar leda ta soma warwareta,layune tafka tafka guda biyu wanda
jikinsu yake wani iri babu kyan gani ta nuna mata
"Wannan,ki tabbatar ayau ko gobe idan an kaiki kin maqalata gefan gadonki" ta ajeta
ta dauko wasu baqaqen garin magunguna da wani mai kama da man shafawa saidai kore
sharr yake
"Wadan nan kuma kin gansu?" Tafada tana duban nafisan sosai,alamun maganar da zata
gaya mata babba ce
"Kin gansu dakyau ko?"ta sake jaddada mata,gyada kai nafisan tayi tana kallonsu
tana kallon mima
"qananu ne amma amfaninsu yawa ne dashi,wadan nan da kike gani idan kikabi doka da
tsarinsu to rayuwar gidan aurenki zata inganta ta tafi yadda kike fata,idan kika
tsallake doka daya ko sharadinsu to kuwa babu shakka kjn wargaza komai,kuma komai
zai iya biyo baya" cikin nuna zaquwa da qaguwa ta gyara tsaiwarta tana cewa
"In sha Allahu ba abinda zai faru,gayamin ya amfaninsu yake" sai data daure ta miqa
mata sannan tace
"Daga randa za'a kaiki gidanki zaki jiqa kowanne kiyi tsarki dashi,mai kama da man
shine na shafawa,zakiyita amfani dasu har tsahon watanni uku cif cif,sharadinsu
sune,idan kika soma amfani dasu babu maganar kwanciyar aure harsai kin
kammala,kinga kenan daga randa xaki shiga gidanki harki kammala amfani dasu ba zaki
bawa anwar kanki ba harsaikin gama amfani dasu,ammafa daga randa kika gama amfani
dasu yasanki a 'ya mace ko?" Sai tayi shuru tana juya idanunta sannan tace
"Uhmmm.....abun ba'a magana kawai" ta furta murmushi na qwacewa fuskarta,shuru
nafisa tayi tana nazari,da alamu ta shiga damuwa,cikin zuciyarta tana jin babu
dadi,ba qaramin buri ta cuwa first night dinta ba,tayi alqawarin saita hana shahida
bacci a ranar saboda tayi tayi anwar ya kaita gidansa na alfarma data sani wanda da
yake zaune a ciki amma yaqj,gidan da xai kaitan sam yayi mata qanqanta
"Yanzu har watanni uku kenan ba wani mu'amala tsakaninmu?"
"Eh...indai kinanson samun yadda kikeso,idan kuma ba haka ba,kina iya bani maganina
na juya dashi,saiki shirya fuskantar duk wata rayuwa da zaki gani" da sauri ta
janye maganin ganin mima ta miqo hannu tana cewa
"A'ah,Allah na tuba don dai wata uku kawai?"
"Ah to nima shi na gani,kuma gidan nan bake kadai bace bare kice akwai matsala,idan
ya matsu ya tafi wajen dayar" harara nafisa ta watsa mata cike da kishi
"Tabdi,lallai ma,to bari kiji,nijin kaina nake ni kadai nake wallahi" dariya mima
ta kwashe da ita harda tafa hannu tana duban nafisan,yayin da nafisan ta taka tayi
gaba ta koma cikin mutane yana yiwa miman godiya,juyawa tayi mima ta fice daga
gidan tana sakin murmushi don tace mata ba zata zauna ba akwai inda zata,amma
anjima da ita za'a kai amarya.

🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍

Sake dawowa yayi jikin qofar karo na babu adadi,tun kafin ya fita daurin aure
take cikin dakin kuma taqi fitowa,yayi juyin duniya amma taqi tabude mishi,ko bata
fada ba koda bai sani ba jikinsa ya bashi kuka take,dalilin daya sanyashi makara
baije akan kariba kenan,bayan yaje ya dawo kuma nanma ko reception din da aka
shirya bai tsaya ba yayo gida saidai jiya iyau,daga qarshe badon yaso ba ya yanke
tilas ya kira anty xubaida ya gaya mata.

Sakin ajiyar zuciya tayi tana aje wayar bayan gama doguwar waya da sukayi
da anty zubaida da kuma zunnurah,ita kanta tanason tayi controlling kanta amma ta
kasa,wani irin bacin rai da baqin ciki ke taso mata,tadan dauki wasu mintuna a
zaune a wajen sannan ta miqe ta shiga bandaki,ta hada ruwan wanka mai dumi sosai
tayi wanka,already ta riga data sauko ta gyare gidan tun sanda taji fitarsa,shi
kadai dinne kawai batason gani,amma dole ta haqura ta dauki maganar anty zubaida da
zunnurarta,donta wuce komai a wajenta.

'Yar madaidaiciyar kwalliya tayi cikin wani sabon coffe lace me adon silver
pink da golden,sosai ta dinkin ya tsaya mata,hakanan lace din yahau fatarta
qwarai,ta saka awarwaro dan kunne da sarqa duka silver ta wadata jikinta da turare.

Dai dai nan taji ana sake knocking,ta kalli qofar ta dauke kanta,sannan
ta soma takowa ta bude ba tare data tambayi waye ba,anwar dinne yana tsaye qofar
dakin sanye da rigar da wando na shadda blue ruwan sararin samaniya,fuskarsa sam
babu walwala,hannunsa goye a qirji ya zubawa qofar ido,wanda tana bude qofar
idanunshi suka sauka a kanta,rabon daya sanyata a idanunsa tun ranar dinner din
nafisa data matsanta mishi sai yazo,sanda ya shirya zai fita tana falon qasa tana
kallo,abinda kusan ba dabi'arta bace,zai mata magana bata tsaya saurarenshi ba ta
tattare wayoyinta da kayanta ta haura saman ko waiwayoshi batayi ba,sai yaji sam
baiji dadi ba,tunda ba dabi'arta bane zaman falo mai yiwuwa yau tayi sha'awa ne
gashi ya bata mata yanayi,koda yaje a gurguje ya dawo,amma saiya tadda ta garqame
kanta,tun ranar rabonshi da ganinta sai yau.

Bata ankara ba har ya iso gabanta,saiki tayi ta riqe dukka hannayenta cikin
lallausan tafin hannunshi,runtse ido tayi tana son zamewa amma ya riqe gam,saita
soma qoqarin ganin ta qwace din,gaba daya ya janyota sai gata cikin jikinsa,saura
kadan numfashinta ya dauke,ta dinga qoqarin zuqoshi hadi da shaqar qamshin daddadan
turarenshi
"Babu dadi ko?,kiyi haquri" ya gaya mata muryasa qasa qasa,tsigar jikinta ta zuba
sosai,saita soma kokawar cire jikinta tana tureshi da dukka hannayenta
"Ina ruwana?,meya dameni?,ka sakeni don Allah bana son irin haka"
"Ko baki taba sona ba shahida dole kiji haushi,dole kiji kishi,nasan halin mata fa"
yayi maganar yana sakinta daga jikin nashi,saiyadan jaa baya kadan
"Kije qasa kina da baqi" daga haka ya juya ya nufi dakinsa,yayin data gyara daurin
dankwalinta sannan ta sauka zuwa qasan.

Mubina ce khadija da huda sai sa'ida da qanwarta ,fuskarta a sake ta


karbesu,nan suka sake sosai abinsu cikin gidan,sa'ida ta gaya mata anty usaina na
gaidata,can gidan anty usainan dole ta hada wuni saboda 'yan katsina da sukazo duk
da basu da yawa,amma wannan karon harda inna kakar anwar,wanda ta manta rabonta da
kano,shi yasa wannan karon anwar din ya matsa sai tazo,tunda ta fuskanci shahidan
bata da ra'ayi hada wani taro sai ita ta hada a gidanta,saidai sa'idan ta gaya mata
anjima zasuzo karban amarya.

Kaman babu abinda yake damunta haka suka dinga sabgoginsu da yaran,anwar din
yana daga sama,wani lokaci ya leqo yayita kallonsu bata sani ba,wani lokaci kuma
yana daga daki yakejin motsinsu,shi ya aika akaje aka dauko yaran yasa aka kawo
mata,yasan koba komai zasu hanata zaman dakin daya tsira,ta kuwa ji dadin zuwan
nasu,duk wata damuwa da take jinta liqe da ranta sai takejin ta ragu.

Ko data gama abinci iya ita da yaran suka zauna sukaci,bayan sun gama tasa
suka kwashe suka kai mata kitchen zata wanke,tana tsaye a kitchen din ta soma
dauraye kwanukan ya shigo,ta waiwaya ta dubeshi ta dubeshi sai kuma ta dauke kai
tana ci gaba da wanke wankenta
"Ni ban taba ganin ango irin wannan ba,ba abokai ba komai,ka dawo gida ka samu waje
ka zauna?" Take tadin ita da zuciyarta,wanda harya iso bayanta dab da ita bata sani
ba,kallonta yake hakanan qirarta da shape dinta yake daukan hankalinsa fiye da
qima,saiya dinga tuna baya can da bai taba ganin komai nata ba,saboda a sannan
ma'abociyar sanya hijabi ce,a lokacin da yake cike da buri da fatan Allah ya bashi
kudin da zai aureta ya mallaketa a matsayin matarsa,yanzu gata a matsayin
matarsa,amma wani abu ya ma rayuwarsu karan tsaye,saiya kauda wannan tunanin yace
"Ni ba za'a bani abincin ba?" Gocewa tayi gefe jin maganarsa dab da ita,da alama
tsaye yake kenan a bayanta
"Ban dafa dakai ba" ta amsa masa tana ci gaba da wanke farantan ba tare data juyo
ta dubeshi ba,shuru yayi yana dubanta,bata taba hanashi abinci ba sai yau,sai baice
komai ba ya matsa gefe kusa da inda tukwane suke,ya dauki daya ya dauraye ya ya
tari ruwa a fanfon dake kusa da ita,ya hada kayan qamshi ya dora ruwan shayi,ya
jingina da jikin kwabar kitchen din yana kallon ruwan yana jiran ya tafasa,duk
abinda yake tana kallonshi ta gefen ido,ta rugashi gamawa don haka ta fita tabar
masa kitchen din,suna falon yazo ya wucesu da ruwan shayin,harya soma hawa saman
saiya waiwayo yana dubanta,hankalin yaran duka nakan arewa24 yace
"Banfa ji haushi ba,wanda ma aka dinga bani a baya Allah ya amfana ko?" Ya qarashe
maganar yana daga mata gira,kauda kai tayi yadda ta saba kaman bata ganshi ba,yayin
dashi kuma yaci gaba da hawa saman.

Da yammaci suka sake gyare gidan tsaf suka cikashi da qamshi tako ina,har
turarukan da bata taba amfani dasu ba sai ranar,kama daga na labule carfet da wanda
kebin iska,sun gama kenan sai gashi ya sauko cikin shadda brown sabuwar qarr,kyau
uya kyau yayishi,sai taga kamar wannan shigar ta musammance,duk da dama shidin koda
yaushe cikin saka sabbin sutura yake,hakanan taji wani abu ya tokareta sanda suka
hada ido ya dage mata gira guda,saita aje pillow din hannunta ba tare data bari ya
iso inda suke ba ta shige kitchen,tana jinshi da yaran suna uncle kayi kyau,ya gama
dan hirarsu dasu ya fice daga gidan bayan ya dauki daya daga cikin
motocinsa.*Alqawarin Allah*
46

Sanda takoma dakinta da niyyar shiga wanka taga wayarta na haske,ta jawo ta
bude sannan ta duba,saqone daya shigo minti biyar baya
"Haka kike kishina?,ki rage kishina wallahi" kalmar da aka rubuta kenan,tsaki tadan
ja tana ture wayar,tasan ba kowa bane sai anwar,batasan me yasa yake wasu abun
kamar da gayya ba,sautari yana hakanne kawai donta biyeshi ko yaji tabakinta
musamman idan yafuskanci batason magana ko batason kulashi.

Bayan ta fito ta shirya kanta cikin wani lace mai azabar kyau da
tsada,qirar qasan switherland,wanda anty zubaida tun a sannan taso ta sakashi ranar
da za'a kawota nan gidan amma taqiya sam,blueblack ne me yarfin adon peach a jiki
da green dan kadan kadan,gaba daya baki yaran suka saki suna kallonta sanda ta fito
kafin daga bisani kowa yahau sharhi,saida suka saka ta koma ta sake kallon kanta a
mudubi,ba qarya sukayi ba,kamar amaryar haka ta koma,ga uban qunshi dama hannu da
qafa,saita kalli kanta ta sake juyawa ta kalla,har batasan sanda murmushi ya qwace
mata ba.

Tana daga dakin ta jiyo 'yar hayaniya,mubina ta shigo ta gaya mata su anty
usaina ne suka zo,saita laluba mayafin da zai dace da kayan ta saka sannan ta fita.

Cikin girmamawa suka soma gaidawa,kanta a qasa don harda inna a ciki,karon
farko data soma ganin innar a ido,har qasa ta tsugunba ta gaidata,innar ta amsa
cikin walwala saboda yadda suka samun shahidan wanda basu tsammaci zasu ganta haka
ba,ta gabatar musu da abinci amma sukace a qoshe suke,ganin magariba ta gabato suka
soma yin alwala,wanda a sannan anty usaina ta samu ta kebe da shahida,maganganu ta
mata masu kwantar da hankali da saka nutsuwa,wanda hakan ya qara mata nutsuwa
qwarai.

Suna idar da sallar ayarin amarya suka qaraso,saboda yawansu yawanci a qofar
gida wasu motocin suka tsaya,a sannan idarwarta kenan da salla tana saman abun
sallarta,wani matsananciyar faduwar gaba taji saidai bata bari ta dirirce kota rude
ba,saita dinga ambatar la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu
minazzalimin,Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahla,wa'anta taj'alil hazna iza
shi'ita sahla,bata miqe ba hakanan bata yi magana ba tana zaune a wajen tana
sauraren hayaniyar mutane.

Mubina ce ta shigo ta sameta


"Yaya wai ki fito,ga baqin nan sun iso" amsa mata tayi tana miqewa mubina tafice ta
barta,sai tayi tsai gaban mudubi kawai tana duban kanta,faduwar gaba da fargabarta
na qaruwa,powder ta dauka ta sake shafawa,ta fesa turare sannan ta gyara daukin
dankwalinta,ta dauki mayafinta daya dace da kayan ta saka ta zira plate din takalmi
sha daya shiga da kayan,tanayi tana addu'a sannan ta fito.

Kusa da ita anty usaina ta matsa mata tace ta zauna,basu da wani yawa
mutanen cikin falon,sai tayi shuru kawai tana sauraren yadda zuciyarta ke
bugawa,wanda ita kanta batasan dalili ba.

Gudar data karade gidan yasanya suka gane motar amarya ta iso,sai anty
zubaida dake zaune a daya barin na shahidan ta kalleta
"Kina addu'a dai ko?" Kai kawai ra gyada mata saboda yadda taji jikinta yayi sanyi
kamar an zare mata laka,dukkansu hankulansu nakan qofar har aka shigo da nafisa.
Kanta na lullube kaman kowacce amarya,tana riqe hannun qanwar mummy suka
qaraso da ita inda su inna ke zaune,aka gaisa sannan suka damqata a hannun shahidan
kamar yadda al'ada tanada,anty zubaida ita tayi musu addu'a sannan suka qarasa da
ita gefanta.

*10:30 pm*

Ruwa mai azabar dumi ta hada tayi wanka dashi wanda hakan ya taimaka wajen
saukar gajiyar jikinta,ta dawo gaban mudubi ta zauna,sannan ta bude manta ta soma
shafawa,tanayi tana sauraren yadda gidan yake shuru,kusan kowa yatafi,daga ita sai
nafisa sai wasu daga cikin qawayenta da suka kafe kai da fata kan ba zasu ko ina ba
sai ango ya shigo an siyi baki,kusan kafin ya haura samanta tana jiyosu sunata
shaqiyancinsu da iya shege,nan ta tattara ta wuce tabar musu qasan,duk abinda take
ba cikin kasala da mutuwar jiki takeyinsa,haka kawai takejin zuciya da ruhinta babu
dadi.

Cikin mintina qalilan tagama komai,ta mulke jikinta da cream perfume,ta cire
sabuwar rigar baccinta cikin kayanta mai santsi da kwantawa a jiki ta zirata ba
tare data buqaci bra ba,don jin qirjinta take kaman yana mata ciwo kadan kadan,ta
kashe qwan wutar dakin nata tabi lafiyar gadonta,saidai fafur bacci yaqi zuwa,haka
ta dinga raba ido cikin duhu tare da tunani barkatai cikin zuciya da
qwaqwalwarta,harta gaji da ruf da ciki ta koma rigingine.

Sha daya saura na daren taji shigowar motarsa,ba jimawa taji shigowarsa
cikin gidan da fitar 'yammatan amaryar suna mita,ta runtse idanunta sanda taji
qarar rufe gate din gidan gaba daya,saitaqi bude idanunta tabarsu a rufen tana fata
da addu'ar zuwan bacci.

Ta cikin rufaffun idanunta taga haske ya gauraye dakin,cikin mamaki ta bude


idanunta da sauri,saita waiwaya tana duban bakin qofa,sam batasan sa'adda daya bude
dakin ba.

Yana tsaye qyam goye da hannunshi,sanye da kayan daya fita dasu


dazun,idanunshi zube fes a kanta yana qare mata kallo daga sama har qasa,surarta
cikakkiya ta gama bayyana cikin rigar baccin data lafe a jikinta ba tare data sani
ba,wani abu yaji yana tsirga masa daga kanshi har qafa,sai ya kasa dauke idanunsa
daga kanta,kauda idonta tayi da sauri sannan ta soma lalubar mayafi donta lullube
jikinta,bata ankara ba ta jita cikin jikinsa gaba daya ya rungumota ta
baya,zuciyarta tahau bugawa da sauri da sauri,kafin tace komai ya rigata
"Wai me yasa kikemin haka ne?,ko don kinga na qyaleki?" Ya fada da muryarsa wadda
tayi laushi,saita kasa aiwatar da komai maimakon daa da tayi niyyar qwace kanta,a
qalla minti uku sukayi a haka sannan ya janye jikinsa yayi baya ganin idan baiyi da
gaske ba zai saki layi,baison hakan kuma ta kasance a lokacin dabai dace ba,ledar
daya aje a baya ya dauko ya aje mata a gabanta sanda ta sulale ta zauna a gefan
gadon tana tattare jikinta waje daya,don bata da kuzarin dauko mayafin nata,dubanta
yake cikin tsakiyar idanunta sannan yace
"Kika samu waje kika zauna,waye zai kaini dakin amaryar?" Ya fada can qasa,so take
tace masa kada Allah yasa yaje din indai itace zata rakashi,amma saita kasa
fada,tayi banza dashi kawai,harya gaji da kallonta da kuma jiran amsarta,saiya saki
ajiyar zuciya yana qoqarin yaqi da abinda yakeji a kanta
"Shikenan,saida safe" ya furta yana takawa zai fice daga dakin,har yakai bakin qofa
sannan ta bude bakinta tace
"Karka sake shigomin daki bada izinina ba" fasa bude qofar da yake shirin yi
yayi,saiya sake takowa yadawo cikin dakin,sai dayazo gab da ita sannan yace
"Maimaita abinda kikace,banji ba" banza tayi dashi tana kauda kai,saboda yadda ya
tsareta da ido,uwa uba kuma kusancinsu da bataso wanda ke haifar mata da wani
yanayi wanda yake saka wani abu dake kama da kishi yana taso mata daga ranta,wanda
itasam batason hakan,ya tsaya gab da ita da yawa,idan kuma ta biyeshi tasan zai
jima bai fita mata a daki bane,wala'alla ma daga qarshe saiya jangwalo abinda xaisa
ta bige da kuka
"Ashe ana tsoron iya inji dan mayya,zanyi maganin bakinkin nan" ya fada yana kai
yatsanshi lebanta,saitayi saurin kauda kai tana balla masa harara,ya gani sarai
wanda har baisan sanda murmushi ya subuce masa ba
"Yaushe wai shahida ta zama mara kunya me tsiwa ne?,shahidan dana sani mai
kunya,idan naje zance bata iya......" Kasa qarasawa kuma yayi,sam ya mance baisan
yana sakin layi ba sai dayaga ta tattara dukkan hankalinta kanshi ta zuba mishi
ido,dukkaninsu kowa yaji cikin jiki da zuciyarshi,ya tuna musu wani abu ya kuma
famawa kowannensu tabo da miki,har ya futa daga dakin yaja mata qofar bai iya sake
cewa komai ba.

Dakinsa ya tura yashiga,ya zube bakin gadonshi yana fitar da iska daga
bakinsa,bayajin karsashi ko wata walwala ko kadan tattare dashi,yabi dakin da kallo
kamar yau ya soma ganinsa,sannan ya miqe ya soma cire kayan jikinsa,ya hada ruwan
wanka mai zafi ya dauki towel yashige.

Dai dai lokacin ta hauro saman,tsam ta tsaya tana qarewa falon saman
kallo,ya qawatashi matuqa wane falon qasa?,wani kishu bacin rai baqin ciki da
tsanar shahida suka cikata,takalli sashen da akace mata dakin shahidan na nan ta
zuba mishi harara kamar shahidance a tsaye,sannan taja wata doguwar qwafa kana tayi
gaba,tura qofar dakin nashi tayi ta shiga,ko ba'a gaya mata ba tasan wanka yake don
ta jiyo qarar ruwa,ta qarasa bakin gado inda ya tube kayanshi ta dauka tana
shinshinawa,qamshin kayan ya ratsata kamar ba kayan daya cire ba,ta lumshe ido tana
sakin murmushi,ba shakka zata morewa rayuwarta da miji dan gayu,inama ace mima
batazo yau da wannan maganin ba,yau da sai tayi ihu iya ihu,ihun da zai hana
shahida bacci,idan banda tsabar wulaqanci ta ina amarya na qasa uwar gida na
sama?,ita zata yiwa bariki,baridai magani ya kammala abubuwa su fara daidaita yadda
ta tsara,kowa zaizo hannu ne,da wannan tunanin tasaki kayan,ta isa bakin mudubin
dakin tadan jaye yalolon mayafin data yafawa kanta,tana kallon kanta da kanta ta
mudubi cikin rigar baccin data saka,juyawa tayi baya ta tabbatar ko ina yafito,taso
ace ma ta tadda shahidane a falo tazo ta wuceta tana kallo kuma babu yadda ta
iya,amma babu komai ajuri zuwa rafi da tulu
"Toke daba kwanciya zakuyi ba inake ina wannan shigar?" Ta tambayi kanta da kanta
tana riqe haba,saita saki murmushi tana baiwa kanta amsa
"Ko babu me gaba daya ai ba'a hanamu romance ba ko?" Tuna hakan yasake faranta mata
ranta,lallai yau zata morewa jikin anwar,saita kai maqura a romancing dinsa.

Tana tsaka da karanta wannan wasiqar jakin yaturo qofar bandakin yafito,sak
yayi cikin mamaki yana dubanta,murmushi ta sakar masa tana dan sadda kanta alamun
kunya tana tsaye a wajen,sai daya gama qare mata kallo da suturar dake jikinta
cikin sanyin jiki sannan yajuya ya rufo qofar bandakin ya soma takowa zuwa cikin
dakin,ita tasoma magana
"Na jika shuru ne inata jiran kuma naji ban sake jin motsinka ba" yana shafa mai
sanda take qarewa qirarsa kallo tana hadiyar yawu,ta qagu ya qaraso kodan rungumeta
ne yayi amma saiya zauna shafa mai,sai yabata amsa dacewa
"Da kinyi zamanki ma,zan qaraso nan din ai" bayanshi ta tako ta tsaya,ta miqa hannu
ta dauki man shafawar ta soma shafa masa a baya,wanda hakan yasa wutar jikinsa ta
dauke gaba daya,yaci gaba dayi masa magana cikin shagwaba
"Na kasa jira ne,so nake naganka,yau sau daya fa na ganka" sam kasa amsa mata yayi
saboda gaba daya jikinsa yadauki wuta,saiya ture hannuwan nata ya miqe don baiso ta
sakashi abinda baida niyyar yinsa ayau,ya isa ma'ajiyar kayan sawarshi yacire wasu
kayan bacci yakoma bandaki yasanya.

Tana tsaye har yanzu,ya karanceta a nutse,ya fahimci yanayinta,amma ta yaya


zaiyuwu su zauna saman shahidan na nan?,hakan saiyake ganin kamar anci fuskarta
ne,saboda haka ya dauki ledojin yace da ita
"Muje" saita narke
"Nan fa?,ni nafison wannan dakin" kaiya girgiza yana kewayeta yayi gaba,dole ta
biyoshi,amma taso su zauna nan din ko motsin qarya tayi duk da babu wani abu da
zata yadda yafaru tsakaninsu tasan zata matuqar baqanta nata rai tare da barinta
cikin tunanin ko komai ya wakana?.

Ta fannin shahida kuwa qur'ani ta saka a wayarta qira'ar shaik shuraim


wadda ta karade dakin gaba daya ta ratso har falon,hakan yasanya mata nutsuwa
qwarai,har taji bacci yasoma fisgarta,sanda zai gifta dakin karatun yaratsa
kunnuwansa,a karon farko tun bayan wasu shekaru yaji tausayinta ya ratsashi,a haka
suka sauka shida nafisan zuwa qasa.

Amaryar zamani ta yadda da wannan sunan ta kuma yiwa kanta laqabi


dashi,saboda haka bata yiwa kanta qauro ko cutar kanta ba taci kazarta
sosai,hakanan da suka kammala shirin kwanciya ma,abubuwa suka soma tafiya ta zage
sosai tana aika da nata wasannin,tunda tasan cewa ba zata yarda komai ya wakana
ba,to ba shakka zatayi iya bakin qoqarinta ta ragewa kanta zafi ta wannan
hanyar,uwa uba a nata tunanin gwara ta rikita anwar din,ta yadda ko wata shida tayi
bata barshi yayi ba bazai iya haqura ba bazata fita daga ranshi ba,zaita bibiya ta
yadda duk randa akace komai zai wakana zai zamto tamkar salla a wajensa a ranar.

Mamaki qwarai yakama anwar din,yadda take tafi da lamuran nata ba kunya
ciki,amma bashi da wata hujja dazai hanata,tunda haqqinta ne ta kuma nema,ko a
wajen Allah idan ya hanata yayi laifi,saboda haka ya bude mata nashi salon wanda
yakusa tafiya da ita har taso mance sharadin maganinta,saidaga baya data ankata ta
tattakura ta tureshi gaba daya,wanda yatafi luu saboda dukka qarfin jikinsa
babu,gaba daya hankalinsa yana gab da tafiya shima,da farko ya zaci tsoro takeji
yabi hanyar da zai amintar da ita amma furrr taqi,dole daga qarshe ya miqe dukka
jikinsa rawa yake,yakai wani stage da shine na qarshe,yakai matakin da yakejin ya
kamata ace shima ya wuce sahun samartaka,shi yasa yadda tazo mishin ya tabashi
sosai,amma bazai sake taba koda yatsarta ba ayau tunda bata da muradi,saiya bude
toilet din dakin ya shiga ya budewa kansa shower tun daga saman kanshi,sanyin ruwan
na ratsashi yana qoqarin controlling kanshi,ya jima ahaka kafin ya samu yanayinsa
ya daidaita sannan yayi wanka ya fito,a sannan ya sameta zaune,ba alamun tsoro ko
kunya a fuskarta,ta maida rigar baccinta tana shirin kwanciya,gefen gadon ya samu
shima ya kwanta yana sakin numfashi,ta matso da niyyar rungumeshi ya kada mata
yatsa,don ba shakka idan ta sake ta tabashi a yanzun komai zai iya wakana,shi kuwa
baijin zai yiwa nafisan dole,don badon tun farko ta nuna aniyarta bama ba abinda
yayi niyyar nema daga gareta,har sai lokacin da zuciyarsa ta gama gamsuwa da aminta
da ita,haka takoma can qarshe tana kallonshi,baisan me take ji bane,tanajin ta
fishi buqatuwa zuwa gareshi,amma dole tabi sharadi saboda tacika muradin zuciyarta.

Qarfe goma da rabi na safe ya tura qofar dakinsa ya fito,dai dai lokacin da
shahida ke haurowa saman bayan ta gama kintsa inda zata kintsa din ta dafa abubda
zataci dai dai cikinta,don batajin zata iya musu wani abinci suci daga nafisan har
anwar din,hada idanu sukayi,ita tana dubanshi ne cikin mamakin me yake a
dakin,yayin dashi kuma yake kallonta saboda yadda tayi masa kyau matuqa gaya cikin
wasu riga da skert,kanta babu dankwali saboda saurin da take ta gama komai tahige
dakinta,don batason ganin kowa cikinsu,take abun jiya ya taso masa,har sai daya
rintse ido gami da dunqule hannunsa yana dan cije lips kadan
"Ina kwana" ta gaidashi tana niyyar wucewa,qamshin nan nata mai sanyi ya cika wajen
gaba daya
"Lafiya lau" ya amsa da wata irin muryar datayi laushi,yadda tamasa maganar bai
masa ba,yana buqatar fiye da hakan,don haka yabi bayanta tana shiga shima yana saka
qafarshi.

You might also like