Abokin Mijina Completed
Abokin Mijina Completed
Abokin Mijina Completed
😭 ```ABOKIN MIJINA```😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
*DEDICATED TO ZEEYRUMA*
```YA ALLAH KAMAR YANDA NA FARA LAFIYA ALLAH KASA NA GAMA LAFIYA.```🙏🏻
GARGAD'I!
```BAN YARDA WATA KO WANI YA JUYAMUN LABARI BA YIN HAKAN BABBAN KUSKURE NE SABODA
HAKA A KIYAYE!```
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*PAGE 1~5*
"Wai kai sai wani d'oki kake kamar wanda yau aka kai maka matar."
"Abokina bazaka gane bane Wallahi tunda na auri Husna ban ta6a kusan tantaba kai
baka tunanin zan shiga hakk'inta?" Ya k'arasa maganar fuska d'auke da damuwa.
"To ai sai kayi hak'uri tunda kasan tsoro take ji kuma idan kayi bata cire wannan
tsoron ba Wallahi ciwo zaka ji mata kaca-kaca."
"Hmm to Allah yakaimu nan da satin amman Wallahi nikam a matse nake."
Haka dai suka tayi a tsakanin su sannan suka yanke akan sai nan da sati.
Yusuf ne ya rak'oshi har gida a lokacin da suka shigo gidan wani wawan k'amshi
ne ya daki hancin su Wanda sai da gaba d'ayan su suka shiga wani hali.
Zaune take akan d'aya daga cikin kujerun da suka zagaye parlour.
Amsa musu tayi cikin zazzak'ar muryan ta sannan ta tashi tana musu sannu da
zuwa.
Yusuf sake rikicewa yayi da ya kalli halitattar Husna Wanda bai ta6a tsammanin
tana da shi ba.
"Sannun Ku da zuwa"
Yusuf yayi saurin amsawa da cewa
"Yauwa sannu amarya ya kike?"
Murmushi tayi tace "Lafiya k'alau Ya Yusuf, ya Anty Hafsat?" Ta tambaye shi.
"Lafiya ta k'alau gobe insha Allahu zan kawota ku wuni saboda Ku fara sabawa tun
yanzu."
Shikuwa Farooq yana zaune yana kallon amaryar Sa wacce duk kallon da zai mata sai
yaji wani abu a jikin shi.
Wannan kalamai na Farooq ne ya fara 6atawa Yusuf rai hakan ne yasa shi katseshi da
cewa
"Abokina nifa yunwa nake ji muci na gudu nima gida na."
Haka kuwa suka tashi suka nufi dining dan cin abinci amman ina Husna Sam ta kasa
sakewa dan wani kallo Yusuf yake mata hakan ne yasata tashi tabar abinci.
Bayan sun kammala sun koma parlour in zauna Yusuf yace da Farooq
"To Abokina ni zan gudu amman dan Allah kar ka kusanci yarinyar nan Wallahi yanda
na fahimceta har yanzu tsoro ne a ranta kagani dai ko abinci ta kasa ci."
"Eh nima dai hakan nagani amman kasan bazai yu na zuba mata ido ina kallon ta ba,
dole sai nayi abinda yake rai na."
Haka kuwa ya tashi yaje ya kirata suka rakashi bakin motar shi sannan suka dawo
cikin gida.
Sallama yayi ya shiga kamar yanda yayi tsammanin a parlour ya sameta kwance akan
three siter.
"To Allah yasa kar ki iya ki zauna nikam bazan dafa ba" ya k'arasa maganar yana
hayewa sama d'akin shi.
Haka kuwa tabawa Isyaku mai wanki da guga kud'i ya siyo mata tsire kasan cewar
tanada yogurt a friez.
B'angaren Farooq kuwa hankalin shi gaba d'aya baya jikin shi yanda yau yaga
Husna........
*Taku har kullum Momyn musaddiq*✍🏻
💞💞💞💞💞💞💞💞
😭*ABOKIN MIJINA* 😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
*DEDICATED TO SADNAF*
```Wannan page d'in naki ne ke kad'ai My Sadnaf kiyi yanda kike so dashi nabaki
shi kyauta```
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 6~10*
Yanda yaga Husna tana mishi wasu irin salo Wanda bai ta6a tsammanin ta iya irin su
ba haka kuwa shima ya biye mata suka ci gaba da jin dad'in su.
"Eh Wallahi banyi ba amman dai lafiya ka k'irani cikin wannan daren?"
"Lafiya k'alau kawai dai na kiraka muyi hira idan amarya tayi barci."
"Hira kuma nida inada mata kaima kanada me zaisa muyi hira bayan ga matan mu."
"To sarkin iyayi ai cewa nayi idan sunyi barci ko kai naka har yanzu batayi ba?"
"Kai dai kawai bakason muyi amman me zaisa Husna zama har yanzu batayi barci ba."
"To shikenan tunda baka yarda ba to gatanan kaji muryan ta" ya k'arasa maganar
yana mik'a mata wayar.
Wani dad'i ne ya lullu6e Yusuf daman abinda yake nema kenan gashi kuma ya samu.
"Hello Yaya Yusuf baka yarda cewa banyi barci ba?" Ta tambaye shi.
Murmushi jin dad'i yayi yace
"Ina kuwa zan yarda bakiyi barci ba dan nasan wannan lokacin ba abinda zakiyi."
Ba dan yasoba saboda yanzu a rayuwar shi ba abinda yake so kamar yaji muryan
Husna.
"Husna dan Allah inason na miki tambaya ina fatan zaki bani amsa."
"Husna nasan tunda aka kawoki gidan nan kike tsoron had'a shinfid'a da ni shiyasa
nima na barki har sai wannan tsoron ya fita amman kuma naga har yanzu banga kina
buk'ata naba."
"Yaya Wallahi ba wani tsoron ka da nakeji ba, sai dai kasan duk wata mace dole
sai tayi far gaban first night d'in ta."
Wani irin kunya ne ya lullu6e ta wanda ya sata tusa kanta tsakanin pilo.
Bata amsa mishi ba sai ma kara danna kanta take ganin zata 6ata mishi lokaci ne
ya d'auke ta zuwa bathroom.
Alwala sukayi sukazo suka gabatar da sallah sannan ya musu addu'a sosai tukun
suka nufi gado.
Sai Yau Farooq yasan cewa yayi Aure sun faran tawa junan su sosai sai misalin
k'arfe d'aya na dare Farooq ya barta.
Farooq ji yake kamar zai mayar da Husna ciki tsabar yanda yake jin k'aunarta yana
k'ara shiga cikin zuciyar shi.
Ita kuwa Husna taji maza Wanda haka yasata narkewa sai faman kuke-kuke take na
shagwa6a.
Toilet ya shiga ya had'a mata ruwa mai d'umi sannan ya dawo yace mata
"Heartbeat tashi na d'aukeki muje na miki wanka."
"Aa Heartbeat nasan kin wahala bazaki iyayi ba kibari kawai na miki."
" Aa Baby kar kiyi kuka dan Allah tashi ki shiga ina jiranki."
Fitowa tayi d'aure da towel da sauri ya k'araso inda take yana mata sannu yace
mata
"Sannu Babyna zo muje na saka miki sleeping dress."
D'auko kayan yayi yasa mata ya kwantar da ita sai da ya tabbatar tayi barci sannan
shima ya shiga toilet.
B'angaren Yusuf kuwa dad'i yake ji sosai dan kuwa ya tsorata Farooq ko ba komai
burin shi zai cika.
Tashi yayi yaje d'akin Hafsat a zaune ya sameta tana chart hakan ne yabashi
daman k'arasawa.
Washe gari Farroq shida kanshi ya shiga kitchen dan had'a musu breakfast.
Dankali ya soya musu da eggs sai kuma tea.
Bayan ya gama da yadawo d'akin se ya same zaune tasha kwalliya sai k'amshi take
sha ga kuma kayan da ta saka sun bayyana suranta.
Wani irin fari da ido tayi wanda yake k'ara mata kyau sannan tace
"Na warke mana ya Farooq ko bakason na warke ne?" Ta tambaye shi.
```Masoya littafin BARRISTER JANNART ina mai baku hakuri da jina shiru nayi niyan
yimuku shi Yau amman kuma zazzabi ya hanani plz ina mai neman addu'ar ku```
💞💞💞💞💞💞💞💞
😭 *ABOKIN MIJINA*😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
```Wannan page d'in nakine ke ked'ai Momyn sultan kiyi yanda kike so da shi na
bakishi kyauta`
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 11~15*
Sallaman su Yusuf sukaji daga k'ofar parlour dan su ko bude k'ofa basuyi ba.
Farooq ne yaje ya bud'e musu, ganin abokin shi da matar shine yasashi yin
murmushi sannan yace
"Aa Abokina kaine da sassafan nan?"
Gaba d'ayan su a parlour suka zaune itadai Husna badan ranta yaso ba saboda
kwana biyun nan ta kasa gane me Yusuf yake nufi.
Farooq da Hafsat ne suka gaisa cikin mutun ci da girmama juna saboda it a Hafsat
ta d'auki Farooq tamkar yayan ta.
Shikuwa Yusuf sai faman zuba ido yake nason yaga Husna amman ina bai ganta ba
hakan ne yasa yace da Farooq
"Wai kai ina Amaryan ne ko har yanzu bata tashi a barci ba?"
Ita kuwa Husna yanayin kayan jikin ta ne yahanata tashi hakan yasa ta koma gefe
ta zauna.
Yusuf ne yace
"Yauwa nima haka yunwa nake ji kutashi muje mu karya."
Tsayawa yayi cak ko motsawa ya kasa sai faman lashe le6e yake kamar sabon maye ya
zuba mata ido musamman yanda yaga na shanun ta sun kunburo a cikin k'aramin riganda
ta saka.
Farooq ne yace
"Ya katsaya ne bazaka zauna ba."
Ita dai Husna batada bakin magana saboda duk wani iri take jinta.
Sai a lokacin shima ya gane abinda yasa taki sakin jiki bare tayi magana.
Da sauri ya mik'e ya shiga d'aki ya d'auko mata k'aton hijabi har kasa ya bata ta
saka.
Sai a.lokacin tace
"Sannun ku da zuwa Anty Hafsat."
"Yauwa sannu Amarya ya kike?
Ya Amarci?"
Farooq ne yace "to yanzu dai muci abinci ba wai surutu ba."
Haka kuwa sukaci abincin su duk da Husna ba dad'in cin abincin take ba saboda
Yusuf ya zuba mata ido duk motsin da zatayi.
Bayan sun kammala parlour suka koma suka zauna shi kuwa Farooq zan Husna yayi
tace suje ya chanza mata kaya.
Kusan 30 minutes sukayi wajen chanza kaya wanda duk ya dami Yusuf ji yake kamar
ya bisu yaga me sukeyi.
Sanye take da wata atamfa me d'an green a jiki Wanda ya mata kyau sosai duk da ba
wani kwalliya tayi ba,
Rike suke da hannun junan su kana ganin su sai sun baka sha'awa.
Wani bak'in kishi ne ya bige Yusuf wanda yasa zuciyar shi bugawa da k'arfi amman
sai ya danne yace
"Wai kai Farooq bakajin kunya ne dan Allah?
Kana gani a gaban mu zaka rik'e mata hannu kuna tafiya."
Tunda Farooq ya fara magana YusufYa shiga cikin wani hali wanda shi kanshi baisan
dalili ba.
😭 *ABOKIN MIJINA*😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 16~20*
"Kamar ya Yusuf?
Dan meyesa kake mun haka ne?
Yau fa aure na wata d'aya amman sai jiya nasamu.".......
"To yanzu tashi muje nifa inason na zauna kusa da mata na ina kallon ta."
"Kai wallahi maye ne kaida kullum kuna tare shine yanzu zakace kanason kallon ta"
ya k'arasa maganar yana kallon shi yana dariya.
"Naji dai tashi mutafi wallahi inason kallon mata ta."
B'angaren su Husna kuwa hiran su suke sosai da Hafsat, itama Hafsat ta sake jiki
da Husna dan taji tanason ta.
Husna ce tace
"Anty Hafsat me kike son kici zan shiga kitchen na d'aura abinci."
"Aa Husna komai kika dafa zanci dan bana sha'awan komai."
Ta tashi zata shiga kitchen kenan sai gasunan sun shigo Farooq ya bud'e baki
zaiyi magana amman Yusuf ya rigashi da cewa
"Aa Husna ina zaki naga kin tashi?"
Farooq ne yace
"Yauwa yayi dai-dai muje muyi girki kai kuma sai Ka zauna wajen matar ka kafin mu
gama" yana k'arasa maganar ya ja hannun Husna sukayi kitchen.
Shikuwa Yusuf wani bakin ciki ne ya lullu6eshi daman shi yazone dan Husna kuma
gashi ta tashi wanne hanya zaibi dan ya dawo da su.
Ai kuwa a take wani abu ya fad'o masa da sauri ya mik'e shima ya shiga kitchen
d'in.
"Haba dan Allah ya munzo gidan ku zaku shiga kitchen Ku barmu a parlour."
Farooq ne yace
"To Idan bamu girka muku abinci ba ya zamuyi kenan?" Ya tambaye shi.
Zuciyar shi cike da Kuna ya dawo ya zauna yana kullah abinda zai shirya.
"Hafsat inason nayi mana gyaran gida kuma bansan ina zamu komaba inason kafin ki
haihu an gyara mana gidan mu."
"Eh nasani Sweetheart bakyason idan anzo suna aga sabon gida?"ya tambaye ta.
"Ai kuwa haka ne to ai ko gidan haya zaka iya kamawa kafin a gama gyaran."
Ita dai kallon shi kawai take dan tasan akwai dalilin wannan maganar nashi.
Su Farooq kuwa suna girki suna zuba soyayyar su haka sukayi har suka kammala.
Rice and stew sai kuma salat da kunun aya wanda yasha kayan had'i
A dining suka jera komai da komai hatta plate da cups sai da Farooq ya d'auko ya
ajiye sannan ya bar wajen.
Kasan cewar suna gamawa aka kira sallan azahar Farooq yaja Yusuf suka wuce
masallaci su kuma sukayi sallahn su.
Gaba d'ayan su suna zaune suna ci Yusuf kam baya magana sai kwasan na gara yake.
Bayan sun kammala cin abincin parlour suka koma suka zauna Yusuf ne yace
"Abokina daman akwai maganar da nake so na fad'a maka."
"Kana gani dai Hafsat ta kunsan haihuwa to banason ayi suna ban gyara mana gidan
ba."
"Yauwa ashe ka gane, to amman banida inda zamu koma da zama kafin a gama gyaran."
"Owhk wannan ba matsala bane zan bud'e muku wancan part d'in sai Ku zauna."
😭 *ABOKIN MIJNA*😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
```Ina kike Anty Khady kizo kema ga naki page d'in kiyi yanda kike so gashi na baki
shi kyauta```
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 21~25*
"Nagode Abokina Allah yasaka maka da alkhairi bansan me zance maka ba banida bak'in
yi maka go"........
Husna kuwa gabanta ne yashiga fad'uwa dan kuwa tasan akwai wani abinda Yusuf yake
shiryawa.
Hafsat ce tace
" mun gode Ya Farooq nima naji dad'i haka wallahi dan kuwa kullum muna tare da
Husna."
Yusuf ne yace
"To yanzu Hafsat ki tashi mu tafi gida mu fara shirye-shirye kinga gobe zamu dawo
nan da zama."
Farooq ne yace
"Kai wallahi kacika gaggawa kabari mana Isyaku ya share muku gidan."
Suna gama maganar Yusuf ya d'auki matar shi cikin farin ciki sukayi gida.
Suna fità Farooq ma ya fita.
Suna tafiya Husna ta shiga gyaran gida tayi shara tayi moping duk da ba wani
kurane da gidan ba.
Kitchen ta shiga ta d'aura abinci nan da nan ta gama kasan cewar tuwon semo da
miyar ku6ewa d'anya sai kuma banana juice.
Wanka tashiga bata wani dade ba ta fito d'aure da towel akwatin k'anan kayanta ta
bud'e.
Wani riga da wando ta fidda ta saka Wanda ba k'aramin kyau ya mata ba.
Rigar pink sai kuma wando white sai ribom d'inta shima pink zama tayi a gabàn
mirror ta fara tsara kwalliya.
Farooq kuwa da yafita gidan Hajiyar shi ya nufa dan sanar da Ita dawowar Yusuf
gidan sa.
Gaidata yayi cikin ladabi da biyayya Ita ta amsa cikin so da k'aunar d'an ta.
"To shi kuma wanne irin gyara zaiyi bayan gidan nashi sabo ne."
"Eh Mummy saboda Hafsat takusan haihuwa shiyasa yake son ya d'an kinkintsa."
"Hmm Umar ba wai na hanaka ba kasan rayuwar yanzu ba tabbas kar ka ajiye abokin
ka a gidan daga baya wani abu yabiyo baya."
"Aa Mummy insha Allah ba abinda zai biyo baya kimana addu'a kawai."
B'angaren Yusuf kuwa suna zuwa gida ya fara had'a musu kaya nan da nan ya had'a
kayan su gabaki d'aya ya saka a bayan motar sa sannan ya koma yace da Hafsat zai
kai kayan su gidan yana zuwa.
Haka kuwa akayi akan hanya magriba tayi mishi sai da ya tsaya a masallaci yayi
sallah sannan ya wuce.
Bayan Farooq yayi sallah ya dawo gida tun kafin ya shiga gidan yaji wani sanyayan
k'amshi ya bige mishi hanci.
A parlour ya sameta zauna tana kallon Arewa24 hakan yasa yak'i yin sallama ya
lalla6a ta baya yaje ya rumgume ta.
Wani irin tsorata Husna tayi dan batayi tsammanin mutum ba murya yana rawa tace
"Dan Allah waye kayi hak'uri ka barni."
Dariya ne ya kama Farooq ganin yanda tayi hakan ne yasa shi juyata ta kalli
fuskan shi.
Farooq ne ya amsa mishi amman ina Yusuf ya tafi wata duniyar ganin Husna cikin
wannan kayan.
"Amarya amman kinyi kyau irin wannan kwalliyar duk Farooq kikayiwa?"
Sake matsowa yayi yana leka ta sai faman kallon kirjinta yake Ita kuwa duk ta
damo Farooq ya dawo dan idan ta tashi wando ya matse ta abin zaifi haka.
Shi kuwa mayen yana nan yana ta faman kalle-kallen shi sai ga Farooq..............
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
```Wannan page d'in naki ne ke kad'ai maryam kiyi yanda kike so na baki shi kyauta
kiyi yanda kike so.```
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 26~30*
Farooq ya fito da sauri ya matsa gefe d'aya kamar mutu min kirki.
"Ya Farooq meyesa Yusuf yake shiga mana cikin gida kamar nasa gidan?"
"Husna kenan, ai Yusuf a matsayin d'an uwa na yake gidan shi da wannan duk d'aya
ne dan yashigo ai ba wani abu bane." Ya k'arasa maganar yana rungumota.
Itadai duk abin ya dameta amman tunda yace haka batada bak'in magana.
*TUSHEN LABARI*
Marigayi Alhaji Ibrahim shine mahaifin Farooq wanda yarasu a wani hatsari da yayi.
Alhaji Ibrahim mai kud'i ne sosai wanda ya rasu yabarwa yaran sa.
Shine Babba sai Khadija sai kuma maryam Hajiya Aisha itace mahaifiyar su.
Hajiya Aisha macece mai hak'uri da mutunta juna kasancewarta ba mai rikici hakan
yasa mutane suke k'aunarta.
Farooq yayi karatu sosai shima yanzu haka yana aiki a bank ba da dukiyar da
mahaifinsu ya bar musu ya dogara ba.
*WANENE YUSUF?*
Yusuf d'an k'awar Hajiya Aisha ne wanda mak'oftaka ya had'asu har suka zama 'yan
uwan juna.
Yusuf da Farooq jinin su ya had'u sosai hakan yasa farooq d'aukan Yusuf ya dawo
dashi gidan su.
Tare suke komai har Wanda basu Sani ba suna cewa uban su d'aya.
Shi kuwa mahaifin Yusuf ba wani k'arfi yak'e da shiba, yanada wani k'aramin shago
a bakin layin su yana sai da kayan tireda.
Haka rayuwar su yakasan ce komai tare har Allah yakawowa Yusuf mata wato Hafsat
ya aura.
Hajiya Aisha ce tayima Yusuf aure hatta sadaki itace ta biya hakan ba k'aramin
dad'i yayiwa mahaifiyar Yusuf wato Habiba ba d'an batayi tsammanin hakan daga
garesu ba.
Bayan Yusuf yayi aure ne Farooq ya samu budurwa wacce ya gani yake so.
A lokacin da Farooq ya bayyanawa Yusuf Husna ya nuna kar ya aureta amman yanda
yaga Farooq ya nace sai ya barshi ya aure ta.
Ranar auren Farooq Yusuf ya sake rikicewa yanda yaga Husna ba hijabi a jikin ta,
kasan cewar bata cire hijabi a jikinta.
Ranar dinner ne Yusuf ya gama haukacewa yanda yaga shigar Husna a wannan lokacin
yayi alwashin raba Farooq da matar shi.
Ranar da suka raka Farooq har sunbaro gidan Yusuf ya kira shi a waya yace kar
yasake ya kwanta da Husna saboda zai iya ji mata ciwo har ta kwanta a hospital
hakan ne yasa Farooq tsorata ya yarda da maganar Yusuf.
Ko wanne rana sai Yusuf ya kawowa Farooq wani karya har tsawon wata d'aya.
*CIGABAN LABARIN*
Washe gari da sassafe Yusuf ya d'auko Hafsat suka dawo gidan su Farooq ko a barci
basu tashi ba.
A cikin barci Farooq yaji ana kwankwasa musu kofa wanda hakan ba k'aramin tsorata
shi yayi ba dan baiyi tsammanin mutum war yanzu ba.
Tashi yayi ya fito ganin Yusuf tsaye ne abin ya bashi mamaki tambayan shi yayi da
cewa
"Yusuf lafiya ko jikin Hafsat ne?"
"Kai wallahi ka cika matsala yanzu fa 6:30 ne shine zaka damu breakfast?
To wallahi ko a barci bamu tashi ba."
"Aa nifa ba haka nake nufi ba, kawai dai nace bamu tashi a barci bane amman dan
shiga gida ne bismillah, ina Hafsat d'in take?"
"Owhk bari na kirata tana mota jirani nazo."
Shi kuwa Farooq mamakin abotarsu yake da Farooq yanda suka saba da wasu abubuwa.
Wayyo hakan ba k'aramin dad'i yayiwa Yusuf ba dan daman Allah Allah yake yaga
Husna.
Farooq ne yace
"Gaskiya yanzu Husna barci take saboda jiya daddare bata samu tayi barci ba, sai
dai kishiga kitchen ki girka ko Indomic and egg" ya k'arasa maganar yana kallon ta.
"Haba dan Allah Yusuf na fad'a maka yanzu tasamu tayi barci please kayi hak'uri
mana."
"Owhk Hafsat tashi mu bar mishi gidan sa" yana fad'an haka ya mik'e zai fita
Farooq yayi saurin shan gaban shi yana cewa
"Haba kai kuma daga fad'an haka shine har kayi fishi bari na tashe ta yanzu."
Ita kuwa tana k'ance sai faman shan barcin ta take hankalin ta kwance ba abinda
yake damun ta.
Zuwa yayi ya zauna a bak'in gadon ya zuba mata ido sai da yayi kusan 5mins sannan
ya d'an shafa bayan ta yana wasa da gashinta jin hakan ne yasata tashi ba shiri.
"Owhk ki tashi ga su Yusuf sunzo kuma wai yunwa suke ji please tashi mu shiga
kitchen kunsan yau zan tafi office."
Gaban ta ne yayi mummunar fad'uwa dan Ita yanzu batason Yusuf yazo gidan nan
amman ba yanda ta iya.
Haka ta mik'e ta saka k'atuwar hijabi har k'asa sannan suka fita.
Suna fitowa sukayi arba da Yusuf daman idon shi yana gurin wani murmushi ya sakar
mata Wanda yasa gabanta ya fad'i amman kuma sai ta basar ta watsa mishi nata
hararar.
Allah sarki bawan Allah Farooq yana gefe yana kallon su sai da yaga Husna ta wuce
kitchen sannan ya bita.
😭 *ABOKIN MIJINA* 😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
*DEDICATED TO MY FAN'S*
```Ina kuke masoya ABOKIN MIJINA to ga wannan page d'in na Baku shi kyauta duk da
nadan bazai isheku ba ko WACCE ta d'auki kalma d'aya ```
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 31~35*
Yusuf mik'ewa yayi ya bisu kitchen d'in lokacin da yashiga samu yayi Farooq yana
kissing d'in Husna wani abu yaji ya daki k'irjinsa amman kuma sai ya daure ya shiga
yana cewa
"Yauwa bari nima na tayaku dan mu gama da wuri."
Farooq ne yace
"Haba kai kuwa kabari mana yanzu ai zamu gama kagani fa doya ne" ya k'arasa maganar
yana nuna doyar.
Husna wacce tunda ya shigo ya fara maganar bak'in ciki ya lullu6e ta, ko kallon
sa batayi dan kuwa yanzu ta fara gane shi.
Kallon Farooq tayi Wanda sai faman washe hak'wara yake tace
"To ni zan koma parlour wajen Anty Hafsat kuyi girkin tare."
Farooq yace
"Haba sweetheart idan kika tafi ai kinsan bazamu iya ba please ki tsaya mu
k'arasa."
Bata kulasu ba ta fere doyanta ta d'aura sannan tazo tayi egg sos.
Bata wani d'auki lokaci ba ta kammala amman kuma ko wanne motsi idan Husna tayi
a idon Yusuf dan ko kad'an baya d'auke idon sa akan ta.
Hankalin Yusuf gaba d'aya yana kan d'akin da Husna ta shiga dan kuwa yasan wanka
taje yi.
Bata wuce 30mins ba ta fito cikin wani atamfa mai ratsin pink a jiki Wanda ya
amshi jikin ta ba wani kwalliya a fuskan ta.
Gaba d'aya sune suka zauna a dining Yusuf ne ya zauna a kujeran da yake kallon
na Husna dan ko me tayi yana kallon ta, hakan ne yasa Husna mik'ewa ta zauna akan
cinyar Farooq tana cewa
"Honey ni a baki nakeso kabani bazan iya ci ba" tana maganar cikin shagwa6a.
Wani bak'in kishi ne ya ziyarci zuciyar Yusuf yanda ya sashi ya mik'ewa yana
shirin barin parlour ne Farooq yace mishi
"Yusuf lafiya kuma zaka fita bakayi breakfast d'in ba?"
Da sauri Yusuf ya fita dan idan ya tsaya kallo ta idan baiyiwa Farooq suka ba to
zuciyar shi zata buga.
Bayan ya fita sauka tayi a kanshi tace yaci dawuri ya tafi wajen aiki kar yayi
lett.
Shi kuwa Yusuf yana fita mota ya hau yabar gidan gaba d'aya dan shi bazai iya
zama ba amman wallahi Yau sai ya dawo ya bayyana mata abinda yake ran shi.
Ita kuwa suna gamawa Farooq ta raka mota ya tafi dawowa tayi wajen Hafsat wacce
da halamun barci ne yake damun ta.
Husna tana ganin haka ta d'auki wayan ta ta kira Hajara mai lalle dan tazo yanzu
tayi mata.
Ai kuwa tayi sa'a Hajara bata aikin komai nan da nan tazo ta fesa mata lalle.
Bayan an gama mata tashin Hafsat tayi tace ta tashi itama a mata,
amman sai tace A'a ita zata shiga part d'in ta.
Tana shiga Hajara tayiwa Husna shara da moping duk ta goge mata gidan ta fess.
Shima bata d'auki lokaci ba ta gama tuwon shinkafa da miyar ya kuwa Wanda yasha
kayan k'amshi da nama.
Hanyar d'akin ya kama dan kuwa yau komai zai faru sai dai ya faru.
Ita kuwa tana toilet tana wanka dan bata son Farooq ya dawo bata shirya ba.
Cikin d'akin ya shiga yana du6e-du6e amman ina 6e ganta ba har zai fita sai yaji
motsi a toilet.
😭 *ABOKIN MIJINA*😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
```wannnan Page d'in gaba d'aya shi na Baku shi kyau ta ```
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 36~40*
Wani shu'umin murmushi yayi sannan ya kama hanyar toilet d'in da take.
Bud'ewa yayi a lokacin ita kuma ta d'aura towel a jikin ta kenan sai gashi nan ya
shiga toilet.
Ita bata kula da shiba dan ita sauri take, shi kuwa duk ya haukace a kallon ta.
Juyowan da zatayi sai kawai taga Yusuf a toilet tsaye yana kallon ta.
Wani irin ihu ta saka sannan ta fashe da kuka tana rok'on shi akan dan Allah ya
fita.
Kin fita yayi sai ma kara matsowa inda take yake ita kuwa duk tsoro ya mamaye ta
gashi ba hanyar gudu.
Ita dai Husna ba abinda yake fita a jikin ta ni ba zufa ba, zuciyar ta tana
zugawa Amman kuma sai ta daure tace
"To sai mu fita a toilet mu k'arasa maganar dan naga mai muhimmanci ne."
Haba wa tana fad'an haka yaji wani dad'i a rain shi dan gani yake tarkon shi ya
kamata.
D'aki suka koma, shi kuwa har da zama a bak'in bed ban ji yake shine angon.
Wani kallon tsana ta watsa mishi sannan tace mishi cikin d'aga murya tace
"Tunda jikin na uban ka ne ba,
To wallahi Yusuf ka fita a ido wallahi zan d'au mataki a kanka banza alade kawai
mai bin matar a abokin shi" ta k'arasa maganar tana wani irin huci.
Husna da jin haka ta rikice idanun ta sukayi bak'i bata ganin komai hakan ne
yasa ta d'aukan kwalba ta kwad'awa Yusuf a goshi.
Ita kuwa Husna yana fita ta fad'a kan gado tana kuka sosai dan batasan ya zatayi
ba.
Waya ta d'auka ta kira Mummyn ta amman ina har 3 missed call bata d'auka ba hakan
ne yasa ta sake kwanciya wani sabon kuka.
B'angaren Farooq kuwa hankalin shi duk ya tashi kasan cewar Yusuf yak'i d'aga
masa waya dan yasan fishi yake da shi.
Har magriba Husna tana nan tana aikin kuka tana tunanin ta ina zata lullowa al-
amarin Yusuf dan yaga ba da wasa yazo mata ba.
Tana cikin tunani wayan ta ya fara ringing da sauri ta d'auka ganin Mummy.
"Hello mummy nashiga uku Yusuf zai kashe ni wayyo Allah mummyna ki taimaka mun
dan Allah" ta k'arasa maganar cikin wani irin kuka.
Mummy wacce bata san me Husna take nufi ba tambayan ta tayi da cewa
"Husna lafiyan ki kuwa?
Me aka miki?
Me Yusuf ya miki?"
Duk wannan tambayan tayi mata a lokaci d'aya.
Ai kuwa nan da nan Husna tabawa Mummyn ta labarin abinda Yusuf yake mata tun
randa aka kawo ta.
"Husna wannan al'amarin ba na waya bane, ki tashi kishirya ki saka kayan ki kar
kibari mijin ki ya gane kina cikin damuwa, kuma kar kiyi kurkuren fad'a masa dan
ba yarda zaiyi ba, kiyi hak'uri zuwa gobe zamuyi abu d'aya."
Bayan Yusuf ya tashi daga hospital gida ga dawo, part d'in shi ya shiga ko
sallama babu.
Hafsat ganin ya shigo ba sallama gashi goshi a fashe yasata mik'ewa tana tambaya
lafiya?
Amman ina kin kualta yayi yashiga d'akin shi ya rufe.
Farooq yana dawowa gida part d'in Yusuf ya shiga d'an yasan yadawo gida kuma ga
motar shi a ajiye.
Bayan ya shiga sun gaisa da Hafsat yake tambayan ta ina Yusuf, cemishi tayi yana
cikin d'aki.
Kwankwasa k'ofar yayi sai da ya dad'e sannan ya bud'e mishi yana shiga yagan shi
goshi a fashe da sauri ya k'araso wajen shi yana tambayan shi me yasa me shi.
Suna sallama gaban Husna ya fad'i amman sai ta d'aure ta amsa musu cikin sakin
fuska.
Tashi tayi tanayiwa Farooq sannu da zuwa, cikin sakin fuska ya amsa mata sannan
yace mata
"My angle muje dining kinga Yusuf yayi acceded bai fad'a mana ba kuma yunwa yake ji
yaci abin ci yasha magani."
Suna zaune suna hira shi kuwa Yusuf yana kallon Husna yana tunanin ne ya kamata
yayi mata wani shawara ya yanke Wanda da haka yakama ta ya fara.
Suna cikin hira kawai ya rik'e kai yana ihu wai yana mishi ciwo.
Farooq wanda hankalin shi gaba d'aya ya tashi ya rik'e shi yana addu'a a haka
barci ya d'auke shi a wajen.
Badan ran ta yaso ba taje ta d'auko Farooq ne ya rufe shi suka kashe mishi wutan
parlour suka shiga ciki.
```TURKASHI!```
😭 *ABOKIN MIJINA*😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
```DAN ALLAH JAMA'A KUNÀ MUN HAK'URI KUBARI KUGA INDA LABARIN YA DOSA YANZU NE FA
KUKA FARA JIN LABARIN GABA D'AYA PAGE 9 NE FA MUKAYI AMMAN DUK KUN K'OSA DAN ALLAH
KUYI MUN HAK'URI KUJI YANDA ABIN YAKE```
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 40~45*
Suna shiga d'aki Husna bata wani bata lokaci ba ta d'auki hijabin ta tasaka tana
shirin fita,
Farooq yace mata
"Ina kuma zaki tafi Husna?"
"Haba Husna mutumin nan fa Bashi da lafiya kina gani kulawan mu yake buk'ata dan
Allah kiyi hak'uri mu kwana,
Kuma ma naga kwana d'aya ne."
"Kaga ya Farooq yanzu bamuda lokacin kace nace kawai kayi abu d'aya ko ni ko
Abokin ka kaza6a."
Wani farin ciki ne ya lullu6e ta dan daman hakan take nema amman kuma bata nuna
yanda Farooq zai gane ba.
B'angaren Yusuf kuwa yana la6e yana jinsu dan kuwa duk abinda sukeyi a kunnen sa
sukayi shi.
Yana jin Farooq ya nufo k'ofa hakan ne yasa shi gudu Wanda har yana buguwa da
gini baya ganin gaban shi.
A daddafe ya zo ya kwanta dan kuwa kan shi ya bugu amman ba damar magana.
Farooq shi kad'ai ya fito dan yau Husna da gaske take ba da wasa ba.
Zuwa yayi ya zauna a bakin kujeran da yake kwance a hankali yake tashin sa
tamkar wani Baby,
Shi kuwa Yusuf yana jinshi amman yayi banza da shi.
Farooq ne yace
"Ayya kiyi hak'uri yanzu ma da zan rakashi."
"Owhk tashi mu tafi."
Wani haushin su ne ya kamashi sannan yace
"Wayyo Hafsat nifa banda lafiya kuma gaskiya ina tsoron gidan nan ni kad'ai kawai
kizo mu kwana a parlour nan."
Wani kallon tara bai cika goma ba tayi mishi sannan tace
"Gaskiya naga alamun rashin lafiyar gaske a tattare da kai,
Gaskiya kan ka ya bugu sosai Wanda har ya kawar maka da hankali."
Yana tafe bayan sun gaisa yake tambayan shi ina Husna.
"Husna tana barci bata tashi ba dan jiya bamu kwanta da guri ba."
Kallon shi Farooq kawai yake dan shima yanzu abubuwan da Yusuf yake ya fara isan
shi.
💞💞💞💞💞💞💞💞
😭 *ABOKIN MIJINA*😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
🎂🏆🎂🏆🎂🏆🎂🏆🎂🏆🎂🏆🎂🏆🎂🏆🎂🏆🎂🏆🎂🏆🎂🏆🎂🏆
```HAPPY ONE YEAR ANNIVERSARY REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS WISHING YOU ALLAH
BLESSING NOW UNITS THEN```
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
````Alhamdulillah, Allah mum gode maka da kakawo wannan rana mai albarka```
```ALLAH UBANGIJI KASA ALBARKA A CIKIN WANNAN KUNGIYAR TAMU, YA ALLAH KA KAREMU
DAGA SHIRRIN MAK'IYA, YA ALLAH KA K'ARA MANA BASIRA DA HAZAKA, ALHAMDULILLAH ALLAH
MUN GODE```
```INA KIKE! YABON GONI YA ZAMA DOLE FATY AZLAND DOLE MU YABA MIKI KECE
SANADIYAR HAD'UWAR MU A WANNAN GIDA MAI TARUN ALBARKA,
ALLAH YASAKA MIKI DA MAFIFICIN ALKHAIRI```
UP🎂
UP🏆
UP🎂
UP🏆
UP🎂
UP🏆
REAL🎂
PURE🏆
MOMENT🎂
OF🏆
LIFE🎂
WRITERS🏆
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
```GABA DAI GABA DAI PURE MOMENT OF LIFE WRITER MUNYI NISA BAMA JIN K'IRA,
MAK'IYAN MU FADAWAR MU MUNA GABA SUNA BINMU A BAYA```
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 46~50*
"Wai kai Yusuf meye sa baka son Hafsat tayi maka abu sai mata ta?
Girki dai ko wacce a cikin su ta iya,
Kuma ma lokacin da banyi aure ba ai nata kake ci, kawai yanzu ka canza kace sai na
Husna meyesa?"
Wani kallo Farooq ya mishi yanda bai fahimmaci me yake nufi ba sannan
"Ban gane me kake fad'a mun ba Yusuf?"
"Kai Farooq kar kanemi fad'a mun magana wallahi zaka sani!
Komai nake fad'a a hankalina nake nasan me nake fad'a saboda kar kayi kuskuren sake
fad'an haka" ya k'arasa maganar yana wani huci kamar tsohon zaki.
Shi kuwa Farooq tsayawa yayi yana kallon shi sannan yace
"Ikon Allah!
Allah yabaka hak'uri."
Yana shiga parlour ya tarar da Husna har tayi shara da moping ta d'aura girki,
Abin ya Bashi mamaki sosai dan tana barci ya fita ya barta.
Wanka sukaje sukayi a tare bayan sun fito sun shirya dining sukaje dan cin
abinci.
Suna gamawa 8:30 ya fita har bakin mota tarashi sai da taga fitan shi sannan ta
dawo cikin gida.
Duk wannan abinda suke a gaban idon Yusuf dan kuwa yana tsaye yana kallon su.
Ko sallama bai mata ba ya shiga cikin parlourn ta tana zaune tana kallo kawai
ganin mutum tayi a tsaye.
"Kai d'an akuya kayi gaggawar barmun gida idan kuma ba haka ba to wallahi zan
maka raunin da yafi wannan na goshin naka."
Wani bak'in ciki ne ya sake lullu6e ta dan yanzu batasan yanda zata mishi ba,
katseta yayi da cewa
"Haba Husna kefa wayayyiyace kina abu sai kace bakiyi makaranta ba ,
Please kizo gareni zan faranta miki idan kud'i kike so zan baki ko nawa ne nidai
buri na kawai ki raba auren ki ko kuma ina zuwa kullum muyi sex sau d'aya kawai a
rana" ya k'arasa maganar yana kashe mata ido d'aya.
"Kai Yusuf wallahi ka fita a idona bazan baka had'in kai ba sai me?
Bak'in alade kawai ni nafi karfin ka sai dai kaje kanemi uwarka dan naga itace dai-
dai kai amman ba niba,
Kuma kayi gaggawar barmun parlour idan ba haka ba zanyi maganin Ka yanzu."ta
k'arasa maganar tana nunashi da d'an yatsa.
Shi kuwa duk wannan zagin da tayi mishi ko a jikin shi sai ma zama yayi a d'aya
daga cikin kujerun parlourn yana cewa
"Nifa yunwa nake ji kikawo mun abin ci."
Ai kuwa yana fita taje da gudu ta sakawa k'ofar key sannan ta dawo ta fashe da
kuka.
B'angaren Farooq kuwa tunda yaje office ya kasa komai sai tunanin maganar Yusuf
yake.
"Me Yusuf yake nufi da haka?
Wato dan na sake mishi shine har yasamu yake mun haka?
To ai kuwa idan har yace haka zai mun wallahi ba mai rabamu da shi sai Allah." Ya
k'arasa maganar yana busar da iska mai zafi.
Hafsat tana zaune a parlour Yusuf ya shigo da gudu kamar Wanda aka biyo shi ai
kuwa itama tashi tayi ta bishi dan ita a tunanin ta wani abu ne ya bishi.
Tana fita ya rude d'aki yasa key ya k'oma ya zauna yana tunanin me zaiyiwa Husna.
😭 *ABOKIN MIJINA* 😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 51~55*
Wani abu ne ya fad'o masa a lokacin ya mik'e ya d'auki key d'in motar shi ya fita
yabar gidan.
Husna kuwa tana nan tana tunanin wanne irin hukunci ya kamata ta d'auka akan
Yusuf dan kuwa idan tayi wasa zai mata abinda batayi tsammani ba.
"Husna nazo ne akan maganar ki ta jiya hankalin mahaifin ki ya tashi sosai shine
ma yasani zuwa yanzu,
Husna me yake faruwa ne?" Ta tambaye ta cikin damuwa.
"Kinga Husna kiyi shiru kiyi hak'uri insha Allah zamuyi abinda ya kamata, yanzu
abinda nake son sani shine mijin ki yasani?"
"To Mummy insha Allah yau zan fad'a mishi duk abinda yake faruwa."
"To shikenan Allah ya taimaka."
Tana tafiya ta sake saka key ta koma ciki dan gabatar da aikin abinci.
Farooq kuwa tunda ya tafi office ya kasa komai sai faman tunani abinda yake ta
tunani shine maganar da Yusuf ya fad'a mishi.
K'arfe biyar yana cika ya tashi bayar wajen aikin dan bazai iya yin komai ba.
Yau kam yasamu kowa a gida sai faman hira suke a tsakanin su.
Ganin Yayan nasu ne yasa su yin shiru dan kuwa tsoron shi suke.
Hajiya ce tace
"Farooq lafiya kuwa na ganka a wannan lokacin?
kuma da alamum fuskan ka akwai damuwa."
"Mama wallahi yau bana d'an jin dad'i ne shi yasa amman ba komai."
"Lafiya k'alau Mama sai dai d'azo mun d'an samu matsala amman ba komai ya wuce."
"Farooq banason ka 6oyemun komai idan wani abin ne ka fad'a mun banason abinda zai
dameka."
B'angaren Yusuf kuwa sabon Sim yaje ya siyo sannan ya dawo gida.
Part d'in Husna yazo amman sai ya tarar a rufe murmushi yayi sannan ya zagaya ta
k'ofar baya.
"Yarinya ni kuma yau nake son na nuna miki cewa bakida wayo ko kad'an, kuma a yau
sai nayi abinda yake rai na."
Wani mugun tsoro ne ya mamaye Husna dan kuwa tasan yanzu ma ba mai taimakon ta sai
Allah, amman ta daure tace
"Yusuf kenan! ai ni bana soron wannan kuma ina tunanin zaka komawa Hafsat babu shi
dan kuwa yankewa zanyi kowa ya huta."
Kin kulata yayi sai ma matsowa yake kusada ita yana lashe harshe ai kuwa tana
ganin haka ta fita da gudu bata tsaya a ko ina ba sai kitchen, biyota yayi yana
dariya yana cewa
"Kina jin zaki tsere mun ne Husna?
Ko ina zaki shiga a gidan nan baki isa kice zaki gudu ban biki ba."
Ai kuwa tana juyawa ta d'auki wuk'a ta tsare shi da shi sannan tace
"Ka tsaya a inda kake kar kasake ka motsa."
Ai kuwa gani nayi Yusuf ya tsaya a waje d'aya kamar wani gunki😂
(Ashe su Malam Yusuf ana tsoron 🔪)
Matsowa ta farayi wajen shi yana ja da baya sai da yazo bakin k'ofa sannan yace
"Husna wallahi bazan cire wannan abin a rai na ba, kuma idan baki amince mun ba
wallahi zan kashe Farooq kuma kema na lalata miki rayuwa sabon haka ki zabi d'aya
ko mutuwar mijinki ko kuma nayi abinda nake so da ke"..........
Ai kuwa bai k'arasa maganar da yake ba Husna tazo da gudu zata yake shi ya kauce
shima fita yayi da gudu ai kuwa a garin bud'e k'ofa sai da ta yanke shi a hannu
sosai tana cewa
" shege maye wallahi kasake dawo wa sai na kashe ka." Ta k'arasa maganar tana kuka.
Jinin da yake jikin wuk'ar da wanda ya dan d'iga kasa k'in gogewa tayi dan
tanason Farooq yazo ya gani.
Yusuf yana shiga part d'in shi kenan motar Farooq ya shigo.
Kwankwasa k'ofar yake sosai amman Husna bata bud'e ba dan batayi tsammanin shi
yanzu ba ta d'auka Yusuf d'in ne har yanzu.
Ai kuwa nan da nan Husna ta fad'awa Farooq duk abinda yusuf yake mata har yanzu
yau sukayi.
Wani irin kukan kura Farooq yayi Wanda nan da nan ido nunsa suka koma ja
jijiyoyin kanshi gaba d'aya suka bayyana.
Wani irin mik'ewa yayi Wanda bai tsaya a ko ina ba sai part d'in Yusuf.
💞💞💞💞💞💞💞💞
😭 *ABOKIN MIJINA*😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
ɯɛn ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 56~60*
Wani irin mik'ewa yayi Wanda bai tsaya a ko ina ba sai part d'in Yusuf.
Ko sallama baiyi ba ya shiga cikin gidan, Hafsat tana zaune a parlour har ta
tsorata dan batayi tsammanin mutum a yanzu haka ba.
Jikin Farooq ne yayi sanyi dan shi gaba d'aya banyi wani tunanin tambayan Yusuf
abinda ya faru ba ce mishi yayi
"Yusuf kayi hak'uri banyi tunanin tambayan ka ba dan gaba d'aya ido nuna sun rufe
amman dan Allah kayi hak'uri, kuma kana maganar barin gidan Husna gidan ta ne?
Ko ita ta sakaku?
Ban yarda ta bar gidan nan ba, amman ison ka fad'amun gaskiya magana."
"Wallahi tun lokacin da kagabatar dani wajen Husna tun a lokacin nake cin karo a
wasu abubuwan da ban gane mata ba, amman ni nasan mutun cin kai na kuma bazan iya
cin amanar ka ba, kai aminina ne meyesa zan ci amanar ka?
Yau kuma dalilin da yasa na shiga gidan na dawo a hospital kenan sai ga Husna ta
fito tace mun wai kad'angare ya shiga mata parlour naje na cire mata shine ina
shiga ta rufe k'ofa wai sai nabiya mata buk'ata."
Rintse idon shi Farooq yayi sannan ya bud'e idon yayi jajerr kamar jar gauta
sannan yace
"Ni Husna zata ci amana!
Husna ta rasa Wanda zata nema sai ABOKINA?
Kuma bayan nan tayi mishi k'azafin zina!
Wallahi Husna sai kinsan kinyi wannan abin sai na foraki."
Ya k'arasa maganar cikin wani irin yanayi sannan ya tashi ya fita.
Husna kuwa tunda ya fita take tunanin abinda zai faru dan ita tsoro take ji kar
Yusuf yajiwa Farooq ciwo shigowar shine ya katse mata tunanin ta.
Katseta yayi da wata lafiyyar mari Wanda yasa taga walk'iya sannan yace
"Rufe mun baki munafuka ashe duk wannan abinda kike mun munafurci ne to wallahi sai
kinyi da nasani munafukar banza,
Kuma bazaki ta6a rabani a aminina ba."
Ya wuce ya shiga d'akin shi.
Durk'usawa tayi a wajen ta fara kuka sosai dan kuwa yanzu ba mai cireta a cikin
wannan masifar sai Allah.
Har K'arfe goma na dare Farooq bai fito cin abinci ba hakan ne yasa Husna shiga
d'akin dan ya fito ya ci abinci.
Sallama tayi ta shiga amman ina bai amsa mata ba duk da haka bai dameta ba ta
durkusa tace
"Ya Farooq kayi hak'uri ka fito kaci abinci."
Ko kallon ta baiyi ba bare samun wani amsa ta kusan minti biyar a haka wani wawan
tsawa ya daka mata wanda sai da yasata zama gaba d'aya sannan yace
"Ki tashi kibar mun d'aki idan kuma ba haka ba wallahi zaki fuskanci fushi na."
Shi kanshi Farooq baya son kukan ta amman idan ya tuna maganar Yusuf sai yaji
kuma ya tsaneta.
Gaba d'ayan su kwana sukayi basuyi barci ba musamman Husna wacce duk abin duniya
ya ashe ta.
Washe gari da sassafe ta fito ta gama breakfast dan kuwa yau da wuri Farooq zai
fita.
Ta gama komai ta gyara gidan ta ko ina fess sannan taje tayi wanka ta shirya
sannan ta wuce d'akin shi.
Batayi magana ba ta juya ta bar mishi d'akin hawaye yana bin fuskan ta.
Fito yayi cikin wata T-shirt blue da black d'in wando Wanda ya amshi jikin sa
sosai ko kallon inda take baiyi ba ya wuce,
Ya bud'e k'ofa zai fita tayi sauri tace
"Ya Farooq ga breakfast d'in ka fa."
😭 *ABOKIN MIJINA* 😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
```DEDICATED TO MY FANS, no need for long essay you know i💔you💯 one love 💞ana mugun
tare irin totally d'in nan ``` 😍❤
*Masoya na naga sak'onin Ku kuma naji dad'i k'warai da gaske musamman wad'an da
suka kira ni dan jin lafiya da wad'an da suka min text nagode matuk'a kuma ban
barku a baya ba masu bina pc da masu nemana a groups suna tambaya lafiya nagode
nagode k'warai kuma naji dad'in hakan nima yinku 😍 ina sonki ❤irin sosai d'in
nan*👄👄💋💋💞💞💞💞💘💘
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 61~65*
Shi kuwa Farooq ya rasa me yake mishi dad'i dan gaba d'aya jin shi yake wani iri
dan baya son kukan Husna.
B'angaren Yusuf kuwa farin ciki ne fal a fuskan shi dan kuwa tarkon shi ya kusan
kamawa.
Wayan shi ya d'auko da wannan Sim d'in da ya siya ya canza sabon Sim d'in sannan
ya fara kiran wayan Husna.
Tana zaune a inda take tana tunanin yanda rayuwar ta ya koma taji wayan ta tana
ringing da sauri ta d'auko amman sai taga bak'on number har ya katse bata d'auka ba
sai da yayi 5 missed call sannan ta d'auka.
Yana shiga kuwa yayi sa'a a bud'e take hakan ne ya bashi daman shiga ciki.
Ita kuwa Husna tana ajiye wayar barci yayi gaba da ita.
Shi kuwa Farooq har yayi nisa ya tuna yabar wasu takaddu a gida hakan ne yasa shi
guyawa ya dawo.
Yusuf kuwa yana shiga parlour ya saka key sannan ya tunkaro inda yaga Husna kwance.
Tsayawa yayi a kanta yana kare mata kallo sannan yasa hannu ya fara shafar fuskan
ta.
Kamar a mafarki taji ana ta6ata ai kuwa tana bud'e ido taga Yusuf zaune a kusa da
ita wani wawan ihu ta saka sannan ta mik'e da niyar gudu amman ina ba dama ya riga
da ya kamata.
Wani wawan cizo ta saka masa Wanda yasa shi ihu amman duk da haka yaki sakin ta.
Wani irin abu yaji ya ziyarci zuciyar shi dan bai ta6a tsammanin Yusuf zai ci
amanar shi ashe gaskiya Husna take fad'a mashi.......
Maganar Yusuf d'in ne ya katse shi da cewa
"Ai yau gaki a hannu na sai yanda nayi da ke saboda haka gara ki nutsu dan kuwa ba
mai ceton ki.....jin yayi ana k'ok'arin bud'e k'ofar parlourn hakan ne yasa shi jan
Husna cikin d'akin ai ina Farooq da yaji ihun Husna yayi yawa ai tuni ya rikice ta
k'ofar baya ya shiga dan gaba d'aya ya fita a hayyacin shi.
Da gudu ya shiga cikin gidan amman har Yusuf ya shiga da ita cikin d'aki yana
k'ok'arin cire mata kayan jikin ta.
Wani irin wawan shak'a Farooq yayiwa Yusuf Wanda sai da numfashin sa ya d'auke na
d'an wasu seconds sannan suka dawo.
Ai kuwa Farooq wani irin duka yake ma Yusuf dan gaba d'aya idon shi ya rufe duka
yake mishi ta ko ina baya ji baya gani kawai dukan shi yake.
Ita kuwa Husna wacce tasha wuya a wajen Yusuf a gefe ta zauna tana maida numfashi
dan kuwa ba k'aramin wahala tasha ba.
Gaba d'aya Yusuf ya fita a hayyacin sa saboda dukan da Farooq yake mishi duk ya
farfasa mishi jikin sa duk ya gala baita.
Husna ce ta tashi tana bawa Farooq hak'uri akan ya barshi amman ina Farooq baya
jin komai.
Ganin yana ji mishi ciwo kamar Wanda zai kashe shi hakan ne yasa ta kira Hajiya
Aisha a waya akan tazo Yau ba lafiya a gida.
Hajiya Aisha ta rikice gaba ki d'aya dan abinda bata ta6a jiba kenan tsakanin
Farooq da Yusuf amman sai gashi yau sune suke fad'a koma menene wannan babban abu
ne shine kawai abinda ta fad'a.
Koda taje gidan Farooq baya hayyacin shi dan kana ganin shi kamar Wanda kanshi ya
ta6u.
Hajiya da Adamu driver ne suka k'arasa inda suke da sauri dak'yar Adamu ya kwace
Yusuf a hannun Farooq.
Farooq ya fara magana cikin wani irin murya da bai ta6ayin irin ta ba, yace
"Yusuf ni zakaci amana?
Na amince da kai Dari bisa Dari amman k'arasa da me zaka saka mun sai da neman mata
ta?
Kama bayan hakan nasani na zalunci baiwar Allah da batasan komai ba wallahi Yusuf
kacuce ni."
Wani irin kuka ne ya kufce mishi.
Hajiya dai batasan meye ya faru ba dan gaba d'aya kalaman Farooq sun rikita ta.
Yusuf dai yana jikin Adamu driver dan kuwa yasha duka sosai ba daman magana.
Hajiya ce tace
"Kai Farooq yanzu ba wannan ba Ka tashi mu kai Yusuf hospital dan kuwa yana jin
jiki."
Hajiya dai ta rasa bakin magana dan bata ta6a jin wad'an nan kalaman a bakin
Farooq ba.
😭 *ABOKIN MIJINA*😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
*DEDICATED TO MY FANS*
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 66~70*
"Wai kai Farooq bakada hankali ne kake fad'a mun wad'an nan maganganun?
Ko kamanta wanene Yusuf kake fad'an haka akan shi."
"Mama ni nasan Yusuf kuma nine sanadin komawar shi haka amman ya rasa da me zai
saka mun Mama sai da Neman mata ta!"
Wani irin zabura Hajiya Aisha tayi tana kallon su dan maganar ba k'aramin razata
yayi ba sannan tace
"Subhallahi!
Farooq me kake fad'a ne nifa har yanzu ban gane ba."
"Mama ba yanzu ya kamata muyi wannan maganar ba sai kowa da kowa an had'u yanzu
zanje gidan su Husna na d'auko iyayen ta dan kuwa abin har su ya shafa Mama."
"Too Farooq amman ai koma menene sai ansamu Yusuf ya dawo hayyacin sa dan kuwa
yanzu komai za'ayi baya hayyacin sa."
"Wannan dai shi yasani sai dai mahaifiyar sa tazo takai shi hospital amman dai ba
tawa uwar ba."
"To yanzu dai Farooq hak'uri zakayi mukai shi dan kowa yana Neman taimaka."
Haka sukayi tayi da Hajiya Aisha dak'yar ta samu ya amince amman hakan ma da
sharad'in ba shine zai kai suba kuma ba driver ba sai dai su hau napep dan bashi ya
siya mishi motar ba.
Haka kuwa suka d'au shatar napep har zuwa wani k'aramin hospital Wanda yake kusa
da unguwar su.
Magunguna aka bashi sai kuma aka mishi allura guda biyu sannan suka dawo gida.
Koda suka dawo yaji saukin jikin sa dan yanzu baya jin ciwon da d'azu yake jin
shi.
Shi kuwa Farooq suna fita yasa Isyaku ya tattara komai da yake na Yusuf ne yakai
mishi gidan shi baya son ganin su a gidan shi.
Komawa part d'in shi yayi ya sami Husna zaune tana kuka wani sabon sonta ne ya
lullu6e shi da tausayin ta dan har baya son ya tuna irin abinda ya mata tsakanin
jiya da yau.
K'arasowa yayi wajen ta jiki a sanyaye sannan ya zauna ya zuba mata ido cikin
dashashiyar murya yace
"My Angle dan Allah kiyafe mun wall".........katse shi tayi da cewa
" A'a Ya Farooq dan Allah karka rok'eni akan abinda kamun, nasan cewa duk laifi
nane da ban sanar da kai abubuwan da yake faruw.".......
Shima katseta yayi da cewa
"A'a Husna karki d'aurawa kanki laifin da ba naki ba,
Kinyi k'ok'arin fahimtar da ni amman na nuna miki ba haka ba dan Allah kiyi
hak'uri da abinda nayi miki abin takaici ma shine nasa hannu na mare ki Husna."
Sai kuma ya fashe da kuka yana jin wani irin abu yana ziyartar zuciyar shi da kuma
tunanin abinda ya kamata ya kara yiwa Yusuf dan ba wannan kad'ai ya kamata yayi
mishi ba.
B'angaren Yusuf kuwa Hajiya Aisha gidan ta ta wuce da shi sai da yasamu yayi
wanka sannan yace mata zaije ya dawo.
Ce mishi tayi
"A'a Yusuf daman yanzu ma kawai dalilin da yasa na kawo ka gidana,
Ina son ka fad'a mun gaskiyar abinda ya had'a ka da Abokin ka?"
Hajiya Aisha baki bud'e ta bishi da kallo dan bata ta6a tsammanin irin wannan
rashin kunyar a wajen Yusuf ba.
Yàn fita gidan su ya shiga a kan taburma ya sami Inna zaune tana tsintar shinkafa
ko sallama baiyi ba ya shiga.
"A garin yaya yaji kama irin wannan raunin naga fa duk jikin ka ya kunbura?"
"Wai Inna akan nace inason matar shi ai naga matar ba dan shi kad'ai akayi ta ba."
"Inna ki bari kawai goyon bayan ki nake buk'ata idan kin amince mun da nayi komai
shikenan ni burina ya cika."
"Na amince Yusuf kuma Allah yayi maka albarka ai banga dalilin da zaisa ayi maka
irin wannan dan banzan dukan ba."
Anan duk ta fad'a mishi irin abubuwan da ya kamata yayi dan wannan ba abin wasa
bane.
Hajiya Aisha ce ta kira Farooq a waya tace sazo tare da Husna tana son magana da
su.
Nan da nan suka amsa kiran ta dan basa wasa da kiran Iyayen su.
Suna fita sai ga Yusuf shima ya shiga Isyaku ne ya k'arasa inda yake yace mishi
" kayi hak'uri Ogana yace kar nabarka kashiga cikin gida,
Kuma duk wani kayan Ku an mayar muku dashi gidan ku. "
Ai kuwa Yusuf yana jin haka ya fito a cikin motar ya fara nausar Isyaku,
Nan da nan suka fara dukan junan su,
Ai daman Isyaku kamar nema yake suka yayiwa Yusuf sosai dan kuwa har fasa mishi
hanci yayi.
```Kuyi hak'uri da wannan wallahi yanzu haka kaina ciwo yake dan kar kuce banyi
muku ba shi yasa nayi muku.```
😭 *ABOKIN MIJINA*😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
```Wannan page d'in naki ne ke kad'ai Ummu Farhana soyayyar ki gareni yafi karfin
misaltawa ba abinda zance sai dai Allah yabar mu tare😍❤
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 71~75*
A parlour suka samu Hajiya zaune tayi tagumi tamkar wacce aka aiko mata da mutuwa,
Sallaman su ne ya dawo da ita daga tunanin da take.
Farooq ne yace
"Mama lafiya kika mana k'iran gaggawa?"
"Mama nayi k'ok'arin sanar da ya Farooq amman sai ya nuna mun ba haka ba hakan ne
yasa nayi shiru ban sake maganar ba amman na fad'ama Mummyna tasan komai duk abinda
yake faruwa tasani."
"To Alhamdulillah daman haka nake son ji dan kuwa wannan ba k'aramin al'amari
bane ace Aminin mijinka yana Neman ka ai kuwa abun sai addu'a,
Kai kuma Farooq kayi wauta bai kamata ka sakewa Yusuf haka ba,
Kuma lokacin da Husna take k'ok'arin sanar da kai ai da Ka tsaya ka saurareta dan
kuwa zaman aure ba abin wasa bane, bare kuma Neman aure ciki aure kaga wannan
babban abu ne."
"Haka ne Mama lokacin ido na ya rufe bana ganin laifin Yusuf ko kad'an,
Amman yanzu nayi nadamar hakan kuma insha Allah hakan bazai sake faruwa ba."
"To shikenan amman a yanda naga Yusuf yabar gidan nan kamar a fusace ya fita dan
nima sai da ya fad'a mun magana."
Cikin zafin nama Farooq ya d'aga kai yana kallon Hajiya sannan yace
"Mama me Yusuf ya fad'a miki?"
Hajiya ce tace
"A'a Farooq ban yarda kaje kana tashin hankali da Yusuf ba, duk da shi bai d'auke
mu a bakin komai ba to mu mu d'auke shi."
Wani irin kallo Farooq yayi Wanda ban ta6a ganin yayi irin ta ba sannan yace
"Husna Yusuf ne yace miki zai kashe ni?"
Hajiya Aisha kam suman zaune tayi dan bata ta6a tsammanin Yusuf zai musu haka ba
bare ma akan mace.
Ai kuwa Husna ta Kuna musu wannan d'aukan duk abinda Yusuf ya fad'a mata duk
sunji.
Wani abu ne yazo ya bugi zuciyar Farooq Wanda yasa shi mik'ewa ba shiri,
yana shirin fita suka jiwo muryan Habiba daga waje tana ta faman zuba masifa.
Ido nunsa gaba d'aya sunyi ja cikin wani irin murya yace
"Haba Mama so kike wad'an nan mutane su kashe mune kamar yanda suka fad'a?
Dan meyesa zakice nayi shiru akan kuma mu akan cuta?
Haba Mama abinda suke mana yayi yawa gaskiya,
Ko wannan shine saka mak'on halaccin da muka musu?" Sai kuma ya kasa k'arasa
maganar dan har Habiba ta shiga cikin parlour.
Hajiya kam rasa bakin magana tayi dan bata ta6a tsammanin Habiba zata fad'a mata
irin wannan maganganun ko a bayan idon ta, amman sai gashi a gaban idon ta, a gaban
Sirikar ta take fad'a mata.
Bak'in ciki ne ya ishi Farooq hakan ne yasa shi fita yabar gidan gaba d'aya idan
kuwa ya tsaya zaiyiwa Habiba ba dad'i.
B'angaren Yusuf kuwa gidan shi ya koma yaje tayi wanka ya canza kayan shi sannan
ya d'auki key d'in motar shi ya fita dan kuwa yau bazai bar Farooq ba.
Ai kuwa Yusuf sake komawa yayi gidan Farooq amman sai ya tsaya a bak'in gate dan
ya tabbatar idan ba a gidan ba bazai same shi ba.
Bai dad'e da zuwa ba sai ga motar Farooq ta tafo tamkar wanda yake tseren gudu
bud'e mishi gate Isyaku yayi ai kuwa Yusuf da gudu shima ya shigo dan yabar motar a
waje.
Farooq yana fitowa kawai yaji an rik'e shi ta baya ana dukan shi.
Ai kuwa Yusuf dukan Farooq yake dan kuwa ya shak'e mishi wuya sosai yayi yayi ya
k'wace ya kasa ai gani nayi Yusuf ya zaro wata sabuwar wuk'a yana k'ok'arin
yank.........
😭*ABOKIN MIJINA* 😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
*DEDICATED TO MY FANS*
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 76~80*
Gani nayi Yusuf ya zaro wuk'a yana k'ok'arin yankewa Farooq mak'ok'oro.
Isyaku ne ya k'araso wajen su da gudu ganin abinda Yusuf yake shirin aikatawa mai
gidan shi,
Wani k'aton itace Isyaku ya d'auko ya k'wad'awa Yusuf a baya wanda sai da yasa shi
ihu sannan ya sake Farooq ya jefar wuk'an da yake hannun shi.
Sai a lokacin Farooq ya samu hankali sannan shima ya shak'e shi yana fad'in
"Yusuf kashe ni zakayi?
Yusuf ni Farooq kake shirin yankawa?
Wannan shine abinda zaka saka mun?
To Wallahi baka isaba sai dai ni naga bayan ka tunda kai ba d'an halak bane."
Isyaku ne yazo ya fara k'ok'arin rabasu amman ina ya kasa saboda Farooq ba
k'aramin shaka yayiwa Yusuf d'in ba.
Shi kuwa Yusuf yaji mutuwa sai faman zare ido yake sannan cikin dashasshiyar
murya yace
"Dan Allah Farooq ka yafeni na tuba kabar mun wuya na Zan mutu."
"To bari kaji wallahi yanda nadau alwashin sai na kashe wallahi ba abinda zai
hanani" Yusuf ne ya fad'a hakan bayan Farooq ya sake shi.
Isyaku da yake gefe tsaye yana kallon ikon Allah sannan yace
"Yusuf kanada hankali kuwa?
Ko kasan irin kalaman da suke fita a bakin ka?
To kayi gaggawan".........
Yusuf ya katse shi da cewa
" kai dallah Malam kamun shiru munafuki kai ma bazan barka ba tunda naga bakin ku
d'aya, kuma ina mai tabbatar maka kai ma sai naga bayan ka."
Yana fad'an haka ya fita yabar su baki bud'e dan shi Farooq gaba d'aya ya kasa
yarda Yusuf ne yake mishi wannan abin.
Haka dai suka d'an tattauna sannan Farooq ya fita yabar gidan.
B'angaren Yusuf kuwa yana fita motar shi ya shiga waya ya d'auka ya kira Hafsat.
"Ke kina ina ne?" Ya tambaye ta.
"Ina gidan mu amman yanzu zan dawo, wani abu ne?"
"Yauwa to ki zauna kar ki dawo sai na nemeki dan yanzu bana buk'atar ganin ki."
"Ban gane me kake nufi ba Yusuf."
"Eh abinda kikaji na fad'a miki shine abinda nake nufi." Yana gama fad'an haka ya
kashe wayar sa bai tsaya a ko ina ba sai gidan Inna.
Tana zaune a bakin kitchen nata da alamun dai abinci take da fawa.
Bai kula su ba ya shige d'akin sa danshi gaba d'aya baya shiga harkar su.
A nan dai Habiba duk tabawa Yusuf muna nan shawarar warinta sai da aka kira
sallah magriba sannan yayi mata sallama ya tafi.
Farooq baizo gidan Hajiya ba sai da yayi sallah isha'i sannan yazo d'aukan Husna.
Hajiya ce tace
"Farooq ina fatan wani abu bai faru ba?"
Ai kuwa nan da nan ya basu labarin abinda ya faru har yanda akayi Isyaku ta
taimaka shi.
Ita kam Hajiya kuka ta fara dan bata ta6a ganin irin wannan masifar ba, ace mutum
da matar sa amman wani yana Neman k'wace masa har yana neman d'aukan ran shi.
Husna tace
"Ya Farooq gaskiya ni ina tsoron komawa gidan can kabar ni anan kawai kuma kai ma
ka dawo nan da zama."
Khadija ce tace
"Yaya lalle Yusuf ya d'auko ruwan dafa kanshi dan wallahi bazan barshi ba."
"To naji kubari sai gobe na dawo mu tattauna dan yanzu dare yayi."
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
```DEDICATED TO DEE``` 💘
```Ina kike surukata Dee💘wannan page d'in gaba d'aya shi naki ne nabaki shi kyauta
```
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 81~85*
Farooq bai damu ba sai ma wani murmushi da yayi dan daman yasan so sake had'uwa.
Ai kuwa tafiya suke Yusuf yana binsu har sai da suka isa gida sannan ya tsaya.
Suna shiga Farooq yace da Husna ta shiga cikin gida yana zuwa.
Yana fita ya ganshi tsaye kamar wani sabon mahaukaci dan irin shigar da yayi abin
dariya ce amman da yake shima Farooq d'an kansane sai yasha kunu ya k'arasa inda
yake.
Isyaku da duk yaji abinda suke fad'a ne ya k'araso inda Farooq yake yace
"Yallabai nidai wannan al'amarin Yusuf ya fara bani tsoro kuma fa akan matar ka ce!
Gaskiya wannan sai kunje kotu dan ba k'aramin abu bane."
"Isyaku ni kaina al'amarin Yusuf ya fara isata amman inason na nuna masa ni ba
sa'an sa bane, kuma idan ni ban nuna masa nafishi haukaba zai mun abinda yafi haka,
shiyasa nake so nima na nuna masa nawa halin."
"Kuma fa haka ne Yallabai, kaga fa d'azu da yazo na hanashi shiga wallahi sai da
mukayi fad'a da shi."
"Sai hak'uri Isyaku mutane ne kowa da halin shi."
Yana gama fad'an haka ya shiga cikin gida yabar Isyaku yana mamakin wannan abin.
Washe gari haka suka wuni kowa da abinda yake sak'awa a zuciyar sa,
Musamman Yusuf wanda yanzu haka shirye-shiryen kashe Farooq yake.
Ita kuwa Husna kuka kawai take dan gaba d'aya ji take itace ta jawo wannan
masifar ga kuma wani masifaffan zazzabi da ya zuba mata.
Farooq yayi-yayi su tafi hospital amman firr Husna taki dan yanzu ita ji take ta
tsani komai.
Husna dai jiki ba dad'i sosai dan ko iya tashi batayi ga kuma tasa tunani sosai a
ranta ganin haka ne yasa Farooq yaje ya d'auko doctor dan ya gaji da ganin ta haka.
Wayyo kuzo kuga murna a wajen Farooq dan har kyauta yayiwa Doctor.
Ai kuwa wani irin gata Farooq yakewa Husna dan yanzu ba k'aramin so yake mata
ba.
B'angaren Yusuf kuwa yana zaune yana jiran Farooq ya saki Husna dan ko ba komai
yayi masa bara zana a tsammanin sa Farooq zai saki Husna.
Yusuf yan zaune har sati baiji wani labari ba hakan ne yasa shi zuwa gidan
Farooq.
Yana zuwa yayi sa'a Isyaku baya nan Farooq ya aike shi.
Shiga cikin gidan kawai yayi ba ko sallama.
A parlour ya tsaya amman baiga kowa ba hakan ne, motsi yaji a cikin d'aki ai kuwa
da sauri ya k'arasa ciki.
Husna tana toilet tana ta faman kwara amai Farooq yana kanta yana mata sannu sai
ganin mutum sukayi a kansu a tsaye.
Wani Uban ashar Yusuf yayi sannan yace
"Farooq kana nufin Husna ciki ne da ita?
To wallahi baka isa ba sai na zubar da sh"...........
Wani shak'a Farooq yayi mishi ya had'a kan shi da bango duka kawai yake mishi ba
gaggauwata sannan ya fara cewa
" Yusuf Uban wa yabaka daman shiga gidana har cikin d'aki na?
Wa yabaka izeni ina tambayan ka." Ya sake shararamai mari.
Ina Yusuf yaji duka sosai ya kasa magana sai faman zare ido yake dan bai ta6a jin
irin wannan dukan ba.
Sai da Farooq ya fara sassauta dukan sannan Yusuf ya samu ya k'wace jikin shi
sannan ya fara cewa
"Wallahi sai na zubar da cikin nan ai daman na fad'a maka kar kabari tayi ciki
shine ka bari ko?
To wallahi sai na rabata da shi."
Ganin Farooq yana tunkaro inda yake ne ya sashi fita da gudu yabar d'akin Farooq
ma ya bishi.
😭*ABOKIN MIJINA* 😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 86~90*
Komawa cikin gida Farooq yayi samun Husna yayi zaune tayi tagumi dan ita gaba
d'aya hankalin ta ba a kwance yake ba.
"Haba Husna dan meyesa zaki damu kanki akan wannan al'amarin?
Dan Allah na rok'eki ki daina sa wannan abin a ranki ko kin manta kina d'auke da
ciki ne?" Ya tambaye ta.
Zuwa yayi ya zauna a kusa da ita ya d'an kwantar da ita a jikin shi sannan yace
"To naji dan Allah ki daina kuka ko kina son cikin da yake jikin ki shima ya shiga
damuwa?"
Alama a'a tayi mishi da kai
"To ki daina tunani insha Allah ba abinda zai same mu sai abinda Allah ya rubuta
mana saboda haka kiyi hak'uri ki cire komai a ranki" ya k'arasa maganar yana shafar
fuskan ta.
"To insha Allah na daina." Sannan ta goge hawayen da suke bin fuskan ta.
Yusuf kuwa gidan su ya nufa yaje yayiwa mahaifiyar sa bayanin duk abinda sukayi
sannan ya sanar mata Husna tana d'auke da ciki.
Habiba ce tace
"Ciki fa kace Yusuf!
Ai kuwa yanzu sai ka hakura tunda tana d'auke da juna biyu."
Duk wannan maganar da suke a kunnen Mahaifin shi dan shi gaba d'aya baisan abinda
yake faruwa ba sai da yaji suna fad'a.
Gaba d'aya jikin shi yayi sanyi dan bai ta6a tsammanin haka halin d'an shi yake
ba, duk da daman halin Habiba amman bai ta6a tsammanin zata sa mutum ya kashe su
ba.
Fasa shiga gidan yayi ya juya ya fita ya koma shago dan gaba d'aya jikin sa rawa
yake.
'Yar k'aramar Nokia sa ya d'auka ya fara Neman number Farooq.
Manager shi yayiwa magana akan an kirashi amman yanzu zai dawo bazai dade ba.
Motar shi ya hau bai tsaya a ko ina ba sai a k'ofar shagon Baba.
Haka suka shiga cikin gida a babban parlour suka zauna sannan Baba yace
"Yauwa to inason ka kira mun Hajiya dan itama inason taji abin a kunnen ta."
Farooq baiyi musu ba ya tashi ya shiga cikin gida dan kiran Mama.
Allah sarki bawan Allah Farooq shikam kasa magana yayi dan zuciyar shi ji yake
kamar zata buga.
Ai kuwa Hajiya ta Bashi gaba d'aya labarin da ta sani, shi kanshi sai da abin ya
bashi tsoron dan bai ta6a tsammanin haka Yusuf yake ta'addanci ba.
Hajiya Aisha kam in ba kuka ba ba abinda take dan ita tunda take a rayuwanta bata
ta6a ganin irin wannan masifar ba.
Bayan sun yanke hukunci sukayi sallama da Malam ya fita duk jikin shi a sanyaye.
B'angaren Yusuf kuwa yana fita wani unguwa ya tafi inda asalin yan daba suke zama
yaje ya same su sai faman shaye-shaye suke a nan ne ya basu address d'in Farooq da
number gidan har photo Farooq sai da ya basu akan aikin kud'i million d'aya.
Haka kuwa ya dawo gida cikin farin ciki dan yau burin shi zai cika.
😭*ABOKIN MIJINA* 😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 91~95*
Ai kuwa D.P.O ya bashi mutane mota biyu dan su kama su akan laifin da suke son
aika tawa.
Godiya ya mishi sosai sannan ya dawo gida Isyaku ya fad'awa komai dan baya son
Husna taji labarin abin.
Isyaku kam gaba d'aya ya tsorata dan kar yaje a garin kafin azo a kamasu su kashe
sa hakan ne yace
"Yallabai gaskiya nikam na tsorata da wannan al'amarin ni yanzu zan tafi gida idan
Allah ya kaimu gobe sai na dawo."
Shima Farooq abin ma dariya ya bashi dan yaga alamun Isyaku tsoro yake ji sannan
yace
"Haba Isyaku ya zaka bani kunya dan Allah gaskiya banyi tsammanin tsoro a tattare
da kai ba."
"Kai yallabai wannan al'amarin rai ne kaga kuwa ba'a wasa da shi."
"Kaga fa suma yan anayin sallah'n isha'i zasu zo kowa ya samu wajen b'uya ai sai
anyi shiri, kai yanzu abinda nake so kawai kabar k'ofar gidan a bud'e har yan
sandan suzo."
Bayan haka kuma cikin gida ya shiga dan duba jikin Husna.
Tana zaune a parlour tayi wanka tayi kwalliya Yau kam ba laifi tad'an ji saukin
jikin ta sosai.
Haka suka ci abinci cikin so da kaunar junan su, Farooq ko kad'an bai nuna gani
abu a tattare a fuskan shi ba bare kuma Husna tasan halinda ake ciki.
Yusuf kam shiri yake sosai dan dashi yace za'a tafi gidan Farooq d'in dan yana so
ya harbi Farooq da hannun sa.
Haka kuwa duk ya shirya har ya saka kayan da suka bashi da fuskan da zai saka
saboda kar a gane shi.
Misalin karfe goma na dare 'yan sanda sukazo suka zagaye gidan Farooq dukan su ko
ina sai da suka b'uya sannan suka boye motar su a gaba da gidan saboda kar 'yan
fashin su gani.
Ai kuwa misalin Karfe goma sha biyu yan fashi suka zo gidan Farooq har da Yusuf
shine yake jagoran su cikin gidan.
Suna zuwa sukayi sa'a k'ofar gidan a bud'e yake hakan ne ya basu daman shiga
cikin gidan cikin hanzari.
Isyaku yana d'akin shi zaune dan gaba d'aya ya kasa barci ji yake idan ya kwanta
zasujo su kashe sa duk da ga 'yan sanda ta ko ina a gidan.
Suna zuwa direct part d'in Farooq sukayi sauran biyu kuma suka tsaya a wajen
Isyaku.
Suna shiga d'akin Isyaku wasu police su biyu sukaje suka kama su.
Suna shiga parlour a zaune suka sami Farooq akan sallaya da alama sallah ya idar
yake addu'a.
Gaba d'ayan su rikicewa sukayi dan basu tsammanin haka zai faru da su ba.
Yusuf kam sai wani muzurai yake da ido dan kuwa baisan ya akayi haka ya faru ba.
Tunani yake ya akayi Farooq yasan abinda yake shiryawa amman ina ba amsa aka
kwashe su.aka kai su station.
Husna da tana cikin d'aki tana barci hayaniyar da tajine yasata tashi.
Gaba d'aya abinda Yusuf yake fad'a taji a kunnen ta ba k'aramin razanata abin
yayi ba.
Kukan ta Farooq yaji da sauri ya shiga d'akin dan baisan idonta biyu ba.
Lallamin ta yake sosai amman tak'i yin shiru gaba d'aya Farooq ya fita a hayyacin
sa yanda yaga tana kukan har cikin ran shi yake jin kukan ta.
Washe gari kuwa aka shigar da su Yusuf kotu Wanda aka yanke musu hukuncin zama a
gidan yari na shekara d'aya tare da hukunci mai tsanani.
😭*ABOKIN MIJINA* 😭
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*✍🏻
````DEDICATED TO MY FANS, no need for long essay you know i💔you💯 one love 💞ana
mugun tare irin totally d'in nan``` 😍❤
```TA FARKON SU (S) KHADIJA 'YAR KHUWAILID, BAYAN TA YA AURI MATA GUDA GOMA (10)
SUNE:
(S)AISHA 'YAR (S) ABUBAKAR
(S) HAFSAT 'YAR (S) UMAR
(S)ZAINAB 'YAR JAHASH
(S) MAIMUNA 'YAR HARIS
(S)SAFIYYA 'YAR HUYAYYI.```
*KUYANGUNSA*
*Amman kuyangunsa su gudu (4) ne.*
*(S) MARIYATUL-KIBDIYYAH*
*(S) RAIHANATUL-KIBDIYYAH*
*DA WATA KUMA GUDA D'AYA WANDA (S) ZAINAB 'YAR JAHASH TA BASHI KYAUTA.*
*TA HUDU (4) KUMA YA SAMETA NE DAGA WANI SASHIN NA RABATATTU.*
*DUKKAN SU DAGA (S) KHADIJA SUKE SAI (S)* *IBRAHIM SHI DAGA (S)* *MARIYATUL
KIBDIYYAH YAKE, WADDA MUKAUKASU YA BASHI ITA KYAUTA.*
🔚 🔚💞
🔚. 🔚💞
🔚. 🔚💞
🔚 🔚💞
# [email protected]
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 96~100*
Washe gari kuwa aka shiga da su kotu aka yanke musu hukuncin zama a gidan yari na
shekara d'aya tare da horo mai tsanani.
Mahaifiyar Yusuf tayi kuka sosai dan bataso hakan ya faru da tilon d'an ta ba.
Farooq jikin shi duk yayi sanyi dan shi yana son Abokin shi tsakani da Allah
amman ina Yusuf ba haka ya d'auka ba.
Yusuf kuwa kuka yake sosai yanayin nadamar abinda ya aikata ya cikin kukan shi ne
Dauda Wanda shine babban 'yan daban yazo yace da shi
"Haba Maza wallahi ka bani kunya banyi tsammanin haka a tattare da kai ba, yanzu
kana nufin dan ankawo ka nan na shekara d'aya shine duk kabi ka damu kanka har kake
kuka?
To bari kaji ni da yau zuwana uku kenan kuma ina fita sai naje nayi abinda nayi
niya saboda haka ina baka shawarar kar kabari kud'irin ka na kashe Farooq ya fita a
rain ka."
Shi kuwa Dauda dad'i yaji dan so yake ya d'aura shi wani hanyar.
Farooq yana ji ya rikice gaba d'aya waya ya d'auka ya kira Mama ya fad'a mata ce
mishi tayi ya jirata tana zuwa amman kar ya sanar da mahaifiyar Husna, da to ya
amsa mata yaje yasa Husna a gaba yana ta faman yi mata sannu.
Basu wuce minti goma da waya ba sai gata nan tazo cewa tayi
"Farooq d'auko kayan haihuwa mu tafi hospital."
Ai kuwa daman sun had'a kayan su tun ba yau ba alkwatin ya d'auka suka fita sai
Aminu Kano hospital daman anan take awu.
Suna zuwa aka shiga da ita kasan cewar haihuwar tazo ta.
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e Farooq sai da yayi sujjada ya godewa Allah
sannan ya mik'a hannu dan kar6an Babyn.
"To me kike so ki fad'a mun idan baifi k'arfi na ba zan baki shi."
Hajiya kam tana tsaye tana kallon Farooq abin ma dariya ya bata dan kamar film
take kallo take ji.
Sai da yagama yiwa Babyn addu'a sannan ya wuce wajen Maman sa.
A lokacin Farooq ya kira gidan su Husna ya sanar da su wayyo kuzo kuga murna ta
ko ina kan nace me mutane sun cika hospital.
Farooq kuwa sai kiran 'yan uwa da Abokan arziki yake yana fad'a musu haihuwar
Husna.
B'angaren Yusuf kuwa ba k'aramin azaba suke shaba duk ya rame yayi bak'i fuskan nan
duk gashi dan idan ka ganshi ma bazaka gane shi ba duk ya canza kamanni ga abinci
ma sau d'aya ake basu a rana shima ba isarsu yake ba.
Tunda aka saka Yusuf a gidan yari mahaifin sa bai ta6a zuwa ga duba shi ba sai
mahaifiyar sa itama lokacin taje duba Yusuf a garin dawowa gida sukayi accident
k'afan ta ya karye duk d'aurin da aka mata bayayi har aka hakura aka bari gashi
yanzu haka za'a yanke farar amman ba kud'in aiki.
Yusuf yayi nadama sosai yayi da nasanin abin da ya aikata amman yana fara nadama
sai Dauda yazo ya canza mishi tunani.
Ai kuwa yana d'aukar maganar Dauda dan ba k'aramin yarda yayi da shi ba.
Husna kuwa ba k'aramin kulawa take samu ba ta ko wanne b'angare dangin mijinta
suna matuk'ar kaunar ta bama da sukaji labarin abinda ya faru a cewar su da wata ce
ai tuni Yusuf yaci galaba akan ta.
Ranar suna yarinya tace sunan Hajiya Aisha anyi taro sosai dan Wanda bai sani ba
cewa zaiyi aure ake.
Da yamma akayi walima wanda Malama Khadija tazo tayi musu wa'azi akan zaman
takewar aure.
Washe gari ne za'akai Husna wanka amman ina Farooq yace shi baisan zancen ba dan
shi baiyar da Husna taje gida wanka ba.
Akayi-akayi Farooq yabar Husna ta tafi amman yace shi bai yarda ba sai da Hajiya
tasa baki sannan ya bari badan ransa ya so ba.
Haka aka d'auki Husna aka tafi da ita wanka amman kullum sai faru yaje sau biyu ko
sau uku a rana.
Yau yake su Yusuf zasu fito a gidan yari Yusuf sai Allah Allah yake yaje gida yaga
me yahana mahaifiyar sa zuwa d'auka shi.
Ko wannen su yayi shirin tafiya dan duk yawancin su sunada mata harda yara.
Shi kuwa Yusuf bai damu da rayuwar Hafsat ba bare kuma abinda yake cikin ta.
Haka kuwa suka rabu bayan Dauda ya zuga Yusuf ya canza mishi tunani.
A zaune ya sameta akan tuburma tayi tagumi tana tunanin wannan rayuwar da take
ciki.
Sallama shi da taji ne yasata d'aga kanta da sauri tana kallon shi.
Ai kuwa nan da nan Inna ta bashi labarin abinda ya faru da ita da rashin kud'in
aikin gashi k'afar ta ru6e.
Gidan duk yayi kura duk ya 6aci a haka ya shiga bedroom d'in yayi wanka ya fito
ya shirya cikin kanana kaya sannan ya d'auki key motar shi ya fita.
Su Farooq kuwa soyayya suke sha sosai da matar shi ga 'yar su wacce suke kira da
Samha hankalin su kwance ba abinda yake damun su.
Yusuf kuwa yana fita wajen wani yaje yace mishi yana so yaje ya cire birkin motar
Farooq zai biyashi da kud'i mai yawa.
Yusuf gidan su ya wuce dan bai sanar da mahaifiyar sa abinda yake kullawa ba.
Farooq ma gidan su yazo dan gaida mahaifiyar sa Bala ya ganshi ya biyo bayan shi.
Buya yayi har sai da Farooq yayi parking motar shi sannan ya fito ya tunkaro inda
motar yake.
Lokacin da yazo wajen motar cikicewa dan Yusuf ma anan ya ajiye motar sa kuma duk
iri d'aya ne hatta color iri d'aya.
Sai da Bala ya gama karewa motocin kallo sannan yazo ya cire birkin d'ayar motar
sannan ya tafi.
Cikin jin dad'i Yusuf ya amsa da to ya tashi yabar Inna ya fita ya hau mota ya
tafi.
Sai da Yusuf yahau babbar kwalta ga wata k'atuwar mota tana tunkaro shi ina yayi
-yayi yataka birki amman ina babu haka wannan motar tazo ta taka Yusuf.
Motar Yusuf tayi rugu-rugu wanda bazakayi tsammanin da mutum a ciki ba.
Haka aka cire Yusuf jikin shi duk jini aka ajiye shi a gefe.
Farooq kuwa ya tashi a gidan su zai dawo gida yaga kamar motar Yusuf ce take ci
da wuta, da sauri tayi parking ya k'arasa wajen da gudu abinda idon shi ya gane
mishi ne ya razana shi.
Da sauri ya k'arasa inda aka kwantar da Yusuf mutane sai magana suke dan 'yan
wajen basu sanshi ba.
Ai kuwa Farooq ana tafiya ya d'auke shi yasa shi a motar sa bai tsaya a ko ina ba
sai Hospital.
Wani Doctor ne ya fita yace da Farooq yana son ganin sa, haka suka shiga office
d'in doctor.
Bayani ya mishi sosai.akan k'afar Yusuf ba zata kara aiki ba sai ba an yake dan
tayi rugu-rugu.
Farooq ba k'aramin razana yayi ba dan baiso haka ta faro da abokin sa ba amman ba
yanda ya iya haka Allah ya k'addara masa.
Kud'in aikin Farooq ya biya akayi mishi duk wani abinda ake buk'ata Farooq ya
biya sannan ya koma ya sanar da Hajiya Aisha.
Mahaifiyar sa kuwa tanajin labarin accident da d'anta yayi a lokacin hawan jini
ya bigeta ta rasu.
Yusuf na gani akan keken sa zaune yayi tagumi sai faman hawaye yake yayi nadamar
duk.abinda ya aika ta.
Gidan Farooq yazo ya nemi gafarar su akan su yafe mishi kuma duk ya sanar da su
abinda ya aika ta.
Farooq kuwa ya yafe mishi duk abinda yayi sannan yayiwa Allah godiya da ya shirya
Abokinsa.
Farooq yana taimakawa Yusuf sosai dan yanzu bashida aikin yi sai zama kan keke.
*Alhamdulillah!*
*Alhamdulillah!!*
*Alhamdulillah!!!*
*Alhamdulillah!!!!*
*ALHAMDULILLAH ALLAH NA GODE MAKA DA KABANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN KUSKUREN
KE CIKI ALLAH KAYAFE MUN ALKHAIRIN DA KE CIKI ALLAH KA BAMU LADAN SHI*
*MASOYA WANNAN LITTAFI NA GODE DA NUNA KAUNAR KU GARENI NAGODE! NAGODE!! NAGODE!!!*