'Kauyen 'Yar Kadde Compt-1

Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 120

[11/5, 9:49 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳 🌳🌳🌳🌳

(Ta'kai taccen labari)

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

Labarina 'kir'kirarren labari ne, haka zalika banyishi don wata ko don wani ba,
idan yay yanayi da labarin ka kayi ha'kuri akasi aka samu😃.

Ya Allah yadda na fara lafia Allah ubangiji ka bani ikon gamashi lafia, Allah sa ya
amfani al'uma amin.

Bismillahir Rahamanir Rahim

1⃣2⃣
1⃣2⃣
1⃣to2⃣

'Kauyen 'yar kadde wani garine dake 'kasarmu ta Nigeria, garine dake jihar
nasarawa, garine da ya had'a mutane daban daban. Ya had'a yaruka da dama, 'karamin
garine wanda ya had'a mutane musulmai da arna, garine mai tattare da zaman lafia,
ga tarin ni'ema. A kwaisu da noma iri iri.

A cikin garin yau na yada zango, gani tsaye a 'kofar wani d'an ma dai-dai cin gida,
gida ne dai irin namu na 'kasa, kusa da gidan kad'an akwai wani 'karamin asibiti,
gaba dashi akwai wani 'karamar primary school.

Shiga gidan nayi domin d'ako muku rahoto.

""Joy yau dai kinsan cewa a kwai Church ko?"" Shiru tayi kamar bada ita uwar take
ba, "" Joy ina magana kina jina, baki tashi tsiyarki sai Sunday, da zarar ance yau
Sunday ne shikenan sai ki kama nu'ku nu'ku, to maza ki shirya ki tadda ni can, time
nata kurewa, saura kuma ki'ki zuwa"" tai 'kwafa tare da tale mata kai.

Har uwan tabar wurin bata tashi ba, tana nan zaune inda ta barta, bata tashi a
wurin ba sai kusan hour1.

A kuma wannan lokacin ne na'kare mata kallo, yarinya ce 'yar karama da ita,
shekarun ta bazai wuce 16 years ba, farace doguwa yanayin fuska kuwa ita ba mummuna
ba haka zalika ba kyakkyawa ba, wato tsaka tsaki kenan.
Tana da diri mai kyau, yanayin ta mai cike da natsuwa, tana sanye cikin kayan barci
Wanda suka zauna d'as a jikin ta.

Cikin natsuwa taje kitchen, d'iban d'umamen shinkafa jallof tayi a kwanan miya
kamar Wanda za'a bawa d'an shekara biyu, koma wa tayi d'aki taci ko gama cinyewa
batai ba taje ta aje tare da sake ruwan wankan a bokiti tayi bayi.

Ta'bata lokaci sosai sanan ta fito, ta shiya cikin wata 'karamar riga da dogon
wando, rigan tad'ame ta sosai wanda ya fito da shape d'in ta.

Gara gashin tada yake ba'ki, mai Kyau dashi tayi Wanda ya kwanta a gadon bayan ta.

Babu wani kwalliya a fuskan ta tad'au Bible d'in ta ta rufo gidan nasu ta nufi
hanyan church, shima Church d'in ba nisa yake dasu ba.

Tafiya take a hankali cikin natsuwa, komai nata masha Allah.

A haka tazo wuce wata wurin wasu samari da talura kullum safe wurin zaman su kenan
koda ana sanyi damuna .

Wani daga ciki tunda ya hango ta yafara had'iye yamu, yana lashe le'be, har tazo ta
wuce su duka zuka zuba mata ido kamar zasu lashe ta.

Lumshe ido yayi saurayin tare da cewa "" gayu al'kur'an yarinyan nan tayi, komai
yaji wallahi ta zata yadda dani hmm da abin ba'acewa komai. Kai dana more"".

Wani cikin su ya sake cewa "" yarinyan badai kaya ba, sai shegen miskilanci da
jijji dakai, ni da zata yarda wallahi da auren zanyi, kaji baza wawa shashsha
madace fah kuma arniya, meye gamun buri da kada? ina laifin mu lalla'bata mu kwashi
ra'ba?"" Wani wanda bakin sa ba'ki'kirin dashi yake cewa haka.

"" Ah Allah yarinyan zatai taurin kai, guma kawai na aura domin na bari ta su'buce
min hmm inaga sai na kusa zaucewa. Wa zai yarda ma har ka aure ta?, ai duk tsiya
indai yarinyan ta yarda ai angama"".

Haka dai suke ta zancen ta, itako bata San ma sunayi ba.

Koda ta'karisa church har an tashi, domin mutane har sun fara fita, da murna ta
saki wani murmushin dake saka kuma tunta lotsawa, hakan kuma na'kara 'kawata fuskan
nata.

Da mamaki nake kallon ta, tana tsaye kusa da church d'in saiga maman ta tafito ita
da wata 'kawanta.

Da mamaki suke kallon ta uwan ta fusata domin gani ta ganta bata ko tsorata ba
saima kafeta da ido da tayi kamar yadda tayi.

Don haka cikin zafin rai ta nufeta tana cewa "" yanzu don ubanki sai yanzu kika
zoko?"" Tai mata ran'kwashi, taji zafi domin harda runtse kyawawan idanuwan ta.

"" Joy mekike so?, meke damun ki? bansan wata irin yarinyan gareni ba Sam baki
maida addinin ki abakin komai ba, baki da hankali sam "".

'Kwanta tace "" madam Gloria kenan ai na fad'a miki indan baki raba yarinyan ki da
watanan musulman ba sai kinyi kuka watarana"".

Haka maman tai ta mata fad'a ko damuwa batayi ba, itako 'kawar maman sai faman
zugata take.
***

"" Mami Allah baza niba, indai ba Dady bazai je yasa su canza ba bazani ba, haba
kamata a rasa inda za'a turani sabis sai wani gari ko nace 'KAUYEN 'YAR KADDE, ina
bazai yuwu ba, i can't believe this"".

Yace cikin zafin rai, murmushi mai ciwo mamin tayi sa'an nan tace ""Auwal kasan
kowe mahaifin ka, idan ya kafe to babu wanda ya isa ya tankwara sa, bai magana biyu
tunda yace sai kaje to kayi ha'kuri kasan baso nakeyi ba don haka sama ranka salama
kaje kawai Allah yaba sa'a"".

Numfasa yayi tare da kwanciya a kushin d'in da yake, zuwa tayi kusa dashi tare da
d'aura kansa a cinyan ta tana shafa masa lallausan gashin kansa yana ta lushe ido,
zuwa can barci ya kwasheshi.

Share
&
Comment

Comments d'in ku zaisa nagane yayi muku

Sai najiku
[11/5, 9:49 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

(Ta'kai taccen labari)

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

Dedicated to my son Muhammad, Allah ubangiji yaji'kan ka yayi maka rahama amin.

Bismillahir Rahamanir Rahim

3⃣4⃣
3⃣to4⃣

Mami na zaune har kusan hour amma bai tashi ba, tana ta faman shafa masa kai, tana
ta kallon yaron nata cike da tausayin shi. Sallaman yayan sa yaron ta na biyu yasa
ta d'ago kai tare da amma sa masa sallah mansa bayan sa matar sace da yarinyan su
mai kimanin shekara biyar da watanni.

Itama d'auke da tata sallamar, "" mami shi kuma wannan lafia? ko shagwa'bar tasace
ta motsa?"" hararan sa tayi tana mai ansa gaisuwan matar tasa.

Yarinya da suka zoda ita ta 'kariso gare su tana mai cewa "" tashi uncle, ka tashi
zan sha ice cream"" tana mai girgiza shi, bud'e idanuwan sa idon cike da barci
domin barci bai isheshi ba, koda yaga bebyn sace a gabansa sai ya tashi da sauri
yana mai cewa "" oyoyo my beby, kece haka da safen nan?, uhum uncle, tashi muje ka
kaini yawo sai mu biya shan ice cream"".

"" Angama my beby bari naje nai wanka, to uncle ina jiranka fah karka dad'e, okay
"" sai lokacin yaga yayan nasa don haka sai ya 'bata fuska domin harda shi a son
yake 'kauye fatar sa ta lalace, ko kula maman yarinyan baiyi ba ya huce. Itako
cikin tsokana tace "" ohni waya ta'ba min maigida nane?" hararan ta yayi tare da
wucewa fau.

Dariya suka kwashe dashi sai da mami ta harare su sanan suka daina.

"" Granny waya ta'ba uncle? waya ya 'bata masa rai? gasu nan kishiyan a gaban ki,
UMMAH kece ko da abbah, kubar 'batawa uncle rai zai mutu idan kuna 'bata masa rai""
mai zasuyi inba dariya ba, harda kakan sai data dara.

Ganin suna mata dariya sai ta fashe da kuka harda birgima.

Ba shiri suka gintse bakin su, mami ta tashi tayi d'akin ta tare da iman.

Itama ikilima ta biyo su tana cewa "" baruwa na mami ni banma autan ki komai ba,
oho dai kwaji dashi daga ke har munafikin mijin ki "".

"" Kai mami ni d'in ne munafiki? eh kai ko bakai ne kaja za'a turamin auta sauro ya
kashe min shiba?"" Shiru yayi yana Sosa kai.

"" Kaban ansa mana"" tace tana mai zama akan sofa dake ciki d'akin nata.

Ya'ki bata ansa domin yasan bai dai gaskiya sai ma wayan cewa yayi da cewa "" bari
na wuce office idan nataso zanzo d'aukan su, oho maka kuma ta Allah bata mutum ba
insha Allah babu abinda zai samamin yaro, kuma mutum yasani nan gani nan bari ehey
mutum ya fita harkan yarona, 'kwarai ma kuwa mami na"" yace yana mai shigowa
d'akin.

"" Ga sojan ki can na hango sa yana parking motar sa, shima karki raga masa mamina
kija masa kunni, harda shi bakin su d'aya Sam basu so suganni kusa dake sai sukama
cewa wai bana abinda ya dace, kome nakeyi mara Kyau oho musu"" ya'karisa yana turo
baki.

Dariya iman tayi tana cewa "" uncle kabar yin shagwa'ba kaga ka girma idan ba haka
ba ko 'kawayena suka ga kana haka dariya zasu ma"" dariya suka soyi, amma sai suka
matse. Domin yadda mami ta had'a fuska zataci 'kaniyan su.

Sun d'anyi shiru na wani lokaci shiko Auwal yana ma'kale kusa da mami kamar zai
shige mata ciki so kawai yake babban yayan nasu ya shigo ayi masa nasa sanan yabar
wurin.

Aiko sai gashi da alama tsaikon nashi yatsaya gaisawa da masu aikin gidan kamar
yadda ya saba.

Aiko daga Auwal har mami suka had'a fuska kamar hadari.
Gaisuwar matarsa kawai ta ansa shiko sai faman hararan sa take.

Murmushi kawai yayi domin yasan kwana nan zancen don haka sai yace cikin ladabi ""
Allah huci zuciyar mami ayi ha'kuri don Allah, mami kuma ma ai taimakon 'KAUYEN
zaiyi, aikin lada zaiyi idan kikaga matsalan doctors da suke saikin zubar masu da
hawaye "".

"" Kum...........,yimin shiru malam, ai ba haka bane kad'ai hanyan da za'a taimaka
musu ba, kuna iya nemo wasu kukai masu ba yarona ba, mami taimako fah kuma ma babu
ruwan mumu bamu muka turasa ba, Allah mami har ina shi'awan idan yagama bautan
'kasan sai mune masa aiki koni nar'inka biya tunda aikin laddane"".

Cikin fad'a "" tace tofar da yamun bakin ka ba'inda yarona zashi ka tura matarka
mana ainaga aikin ta ne"".

Auwal yace "" mami duk nagane su so kawai suke yaronki ya'kara baki wani cuta ya
kama mikini, ba'kin ciki kawai suke dani"" hararan sa yayan yayi ganin zai sake
magana sai yayi kamar zai makeshi sai yayi shiru tare da mi'kewa yana tura baki.

"" Bebyna muje, ke kuma ina Akram da Mufida?" Yace da matar babban yayan tasa,
"suna gidan mu,"" yayi amma aikin san yau nan gidan suke wuni tare dani to shi
kenan na barku lafia "" yace yana mai ri'ke da hannun iman.

***

Haka maman tata tagama mata fad'a ko gezau, haka ta tasa 'keyar ta sukayi gida.
Suna komawa wanke wanke tafara domin batayi ba ta tafi, maman kuma ta tafi kasuwa
domin yo cafenen girki.

Koda Joy tagama ta gara gida sai ta sakayo gidan tayi gidan su Aisha 'kawar ta.

Bayan ta gaida iyayen Aishan sai ta shiga d'akin Aishan, da farin ciki ta rungume
ta kai kace sun dad'e basu had'u ba.

Fira suka farayi duk da Joy ba wani fira take ba domin bata iya surutu ba miskilace
na'karashe, suna tsanani 'kaunar junan su ita da Aisah akwai kyakkyawa fahimta a
tsakanin su.

Iyayen Aisha basu ta'ba karanta ko 'kamanta ba, suna nuna mata soyayya irin ta yada
suke nunawa Aisha domin suna mata 'kwad'ayin musulunci.

Wacece Joy?

Joy dai haifaffiyar Abia state ne, maman ta Gloria 'yar garin abia ne, iyayen ta
haifafun garin ne, su arnane gaba da baya, iyayen ta ita kad'ai suka haifa sai suka
d'au son duniya suka d'aura mata uban ta ba wani mai shi bane sai dai rufin asiri.

A hakan bai hana kulawa da 'yar tasa fiye da tsamanin Kuba masu karatu.

Watarana Allah ya had'a Gloria da wani musulmi, ba'kone ba d'an gari bane , soyayya
suke sosai batare da sanin iyayen ta ba, sanda soyayya tai nisa sanan ta sanar musu
suka nuna basu amince ba, tayi kamar zatai hauka, ciwo riris kamar zata mutu.

Badon iyayen sunso ba suka amince, amma da sharad'in idan wani abu ya taso karta
nemesu, haka ko tayarda batare da tasan asalin mutumin ba sukaje sukai aure.
Auren su da wata uku yayi had'ari ya mutu, tayi kuma kamar me haka ta ha'kura.

Komawa wurin iyayen ta tayi suka'ki kar'banta, don haka sai tabar garin tayo
nasarawa state cikin wani gari mai suna 'YAR KADDE.

Zuwanta garinne tafara laulayi, anane ta haifi Joy don haka joy batasan kowa nata
ba sai maman ta sai gidan su Aisha.

Tare suka gama primary school d'in garin baban su Aisha yane ma musu wani acikin
gari suke tafiya.

Wannan shine ta'kaitaccen tarihin joy.

More comments more typing.

Share & comment pls🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻


[11/5, 9:49 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

(Ta'kai taccen labari)

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

Dedicated to Muhammad Ahmad Bashir

Bismillahir Rahamanir Rahim

5⃣6⃣
5⃣to6⃣

Yau Monday, Monday tushen aiki wanda akace ko bature na tsoron sa, Joy ce zaune
cikin uniform d'inta, mai kalar white and green, karya wa take cikin natsuwa. Tana
idar da karyawan ta d'au bag d'in ta, cikin sanyi murya mai za'ki ta kalli maman ta
tana mai cewa "" mama na tafi, to my dota a kula banda wasa kullum ina mai
gargad'in ki daki kula kiyi karatu domin shine gatan ki idan kika kula yesu zai
dafa miki, kije Allah tsare banda shashshanci.""

Cikin gamsuwa da zancen uwan ta gyad'a kai tare da fita daga d'akin.
A 'kofar gidan suka had'u da Aisha saura kad'an su gwara kai, dariya Aisha tayi
tare da cewa "" inace baki shirya bane, naga har kusan 8pm gashi mashin na mana
wuya anan balle muhau, kisan idan munyi latti basu d'aga mana 'kafa basu duban daga
nesa muke"".

Smile joy tayi tare da cewa "" muje parrot ai ko magan nan naki yasa mu'kara
makara, eh naji ai guma ni, anfi san mutum mai surutu da kurma"" murmushi still ta
sakeyi batare da sake ce da ita komai ba.

Tafiya suke cikin natsuwa, majalisa dai tanan yauma kamar kullum, kuma mafiya
yawancin masu zaman wurin 'yan iskan 'KAUYEN ne, kuma suna zama kawai domin gani
suran jikin dake rikitasu, yake hanasu sukuni, dare ma saboda tsabar jaraba ya
hanasu barci isah ko saboda tsanani son da yake mata yakan sa har yagamsar da kansa
da dare saboda tunanin ta da yake yawanyi.

Yana son tunkaran ta ko nace dukansu ko don bu'katarsu amma kwarjinin da take musu
yake musu shamaki.

Tunda ya hangota yake matse 'kafa, haka suka wuce su basu bar kallon suba, har sai
da suka 'kule musu.

"" Kai wallahi wad'ancan gayun 'yan iskane , sun cika kallon mutane, ina lura dasu
idan suka ganki kamar mayu harda lashe baki suke"" Aisha tayi zance tana dariya,
ta'be baki joy tayi ba tare da ta kokula zancen nata ba, domin sam basa gaban ta.

Itama sarai tana lura dasu sosai.

Sai da suka kusa barin garin sannan suka sami mashin guda d'aya, kamar yadda suka
saba haka sukai wato hawa su biyu.

Sai makaranta, sai muce a dawo lafia su Joy.........

***

Ga Muhammad Auwal kuwa barcin sa kawai yake ta shararawa a safiyar Monday bayan
yasan Dady yace lallai yau ya wuce idan ba haka ba ransa zai mugun 'baci.

Mami ta shigo yakai sau biyar bai tashi ba, haka ma yanzu ta le'ko haka zalika bai
tashi ba, don haka 'karisawa gare sa tayi tare da niyan tada sa, domin tana tsoron
Allah ta tana tsoron mijin ta.

"" Son tashi haka don Allah, tukan Dadyn ka yafarga baka shirya ba"" tace tana mai
girgiza shi.

Mi'ka yayi tare da shagwa'ba fuska tare sauke lumsheshun idanuwan sa a fuskan ta.

"" Mami kin tasheni ina barci na mai dad'i bayan kisan sai one o'clock zan tashi,
please mamina in koma"" girgiza kai tayi tana mai jinzafin ba yadda zatai da mai
gidan nata.

Ganin ta cikin tsananin damuwa sai yaji baiji dad'in hakan ba don haka sai yasakin
mata murmushi tare da cewa "" mamina bar damuwa zan rin'ka dawo wa kullum bashine
damuwanki ba?, a'a son ban yadda ba bason yawan bin mota ga gari mai nisa bari
kawai, kuma ma Dadyn ka yace wai sai Kai five month sanan zaka zo sau
d'aya......ina mami bazan yada ba, bazan iya ba sam, komi dady sai yarin'ka
tsauwalamin, why mami?"" Yace, kwalla na taruwa masa a ido.
Shafa fuskan sa tayi tare da cewa "" yi ha'kuri son tashi kawai mubar maganan nan
tashi maza ka shirya kazo Ahmad ya yakai ka"". Bai sake cewa komai ba ya mi'ke.

Bayan ya fito d'aure da towel a jikin sa, d'aya kuma na hannun sa yana share kai.

Mami ya gani zaune tayi tagumi, yarda towel d'in hannun sa yayi da sauri tare da
nufan ta.

Cire hannun da tai tagumin dashi yayi tare da cewa "" mami kibar damuwa nan don
Allah, idan ba haka ba Allah bazani ba sai dai Dady ya kasheni"" yana mai d'aura
kansa a cinyan ta.

'Digar hawayen sa yasa taji jikin ta yayi sanyi, don haka kauda damuwar dake kan
fuskar ta tayi tare da share masa tana sakin murmushi ya'ke.

"" My boy, yaushe zaka zama jarimin mazane? kuka sam baima wuya, ehey sweetheart
d'ina?"".

Zum'bura baki yayi tare da cewa "" mami nifa jarumine niba ragon maza bane"".

""Okay naji maida wu'kar, nunamin zahiri, maza shirya muje, ka tada hankali sister
d'inka why Auwal? yanzu haka mijin ta yasanar min sai kuka take wai sai tazo
Nigeria"".

"" Oh my god! sorry my heartbeat, mami nakasa jurewa ne, mami banso bata nan ba,
naji bazan iya tafiya ba tare da nasanar mata ba"".

"" Mami na yanzu ya zanyi? oho ma sanda zaka sanar mata meyasa baka tambayeni ba
sai yanzu, kasan dai ciwon ta baisan damuwa da hayaniya ko?, ance kar a gayamata,
kasan lamarin tsakanin ku sai Allah bata son damuwar ka ko kad'an. Yanzu don Allah
mamina bazaki kawo mafita ba, my love na can banso ciwon ta yatashi, kuma ma Allah
mami said a nace mata takwantar da hankali ta, insha Allah babu abinda zai sami
'kanin ta. Ta kuma nunamin ba komai fah"" yace yana mai jin zafi a zuciyar sa.

Tausayi ya bata sosai ga time na tafiya don haka sai ta lallla'bashi tare da cewa
"" maza shirya zansan yadda zanyi, Allah mami na?"" gyad'a masa kai tayi.

Turo baki yayi tare da marai rai ce, "" mami to kirata yanzu"" yace yana mi'ka mata
wayar sa.

Ganin yadda ya marai rai ce, yasa ta nisa cikin tunani domin bata da abinda zata
lallashi Rahama dashi, bata yadda da maganan kowa indai akan 'kannin nata ne, Indai
bashi ne yace ba.

Don haka sai tace "" son kirata kace mata da yadda nka zaka insha shi kenan, ki
tabbata mami zata yadda? Eh mana"".

Don haka bai sake cewa komai ba sai dealing number ta da yayi.

Da 'kar ya shawo kanta, tare da masa fatan alkhairi.

Wani gagarumin nfashi ya sauke.

Tare da rungume mami "" yes mamina ta ha'kuri, to haka dama nakeso maza
shir........bata ko rufe baki ba taji ehun mijin ta.

Don haka sauri ya shirya dama trolley sa tujiya mami ta cika masa da kaya.

Koda suka fito sai fad'a yake, basu ce komai ba illah fita da sukayi gaba d'aya
harda yayan sa Ahmad da zai kaisa........

Fatan alkhairi sukayi masa duka iyayen nasa, Dadyn kansa sai da yayi 'kwallah, shi
kansa bada son ransa zai tura shi ba, amma guma yayi masa haka 'kila ya natsu yasan
ba komai mutum ke samu ba duk kud'i sa.

Kila ya daina 'kaman talaka, yasan talaka shima mutum ne ba abin 'kama ba.

Haka suka d'auki hanya.

***

Bai ta'ba zuwa nasarawa ba sai wannan karan, da fari da yaga garin sai yace yana
mai murmushi ""yaya amma garin nada Kyau fah, shine d'an isakan can yace 'kyauye
zani"" dariya kawai yayan yayi masa bai ce dashi komai ba.

Gani yayi anata tafiyan, sai ya sake cewa "" yaya wai haryan zu?, eh ai munkusa"".

Daga nan suka yi shiru duka sai da sukaje kwanan fiyanku sanan suka d'auki hanya, a
nan ne zuciyar sa ta tsinke da gaske 'KAUYEN zashi.

Bai sake mamaki da ba'kin ciki ba sai da yaga suna sama da 'kasa.

Tafiyan suke kamar zasu tuntsura domin hanyan sam ba Kyau.

Hawaye yaji yana zubo masa don haka cikin kuka yace, "" yaya yanzu 'kiyayyar da
kuke min har takai haka? Yaya nifah 'kannin kune, autan Ku, uwa d'aya uba amma kuke
min 'yan ubanci...........""

Wani gugugum da yaji yasashi yin shiru..........

Camment & share pls


[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳 🌳🌳🌳🌳🌳

(Ta'kai taccen labari)

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

Masoya godiya nake, Nagode da bibbiyan na da kuke, inajin dad'i matu'ka iya wuya
anatare🤝🏻🤝🏻

Antyna kina inah? ga sa'kon dubun gaisuwa ezuwa gareki (Sister Naje'atu).

Bismillahir Rahamanir Rahim

7⃣8⃣
7⃣to8⃣

"" Kutimelesi, yaya ji wuri fisabilillahi, ji wani rami, Allah har na sada'kar
mutuwa zan, yaya please kamaidani, kumin rai Allah mutuwa zanyi, Allah ko sauro sai
ya kasheni. Kaikakai, yaya ji wancan gadan cinyayye, don Allah mu koma, idan ba
haka ba kuma shikenan yaron mami taka ta'kare wayyo autan mami, wayo d'an gatan
Rahamatu, pls yaya mu koma kaga kai kana da masu maka addu'a ni kuma fah?, wanda
zata haifanma ba'a haifeta ba bare azo......., zaci uban kafa, kasan dai niba sa'an
ka bane ko? ko dun kaga kanata iskancin ka ban tankaka bako? to gargad'in mami ne,
bancin haka sai na faffashe bakin rashin kunya, banza shashasha, guma kaje ko maji
sa'kat. Allah ka sake magana sai naci uban ka, don wallahi ka fara isata zan aje
zancen mami a gefe inci 'kaniyan ka, idan yaso idan naje na bata ha'kuri sa'ba mata
danai"" yaja tsaki.

Gum yayi da bakin sa domin yasan ba 'karamar aikin sabane ya sassa'ba masa, don
haka da ganin fuskan nan guma yayi shiru kawai don ba mai 'kautarsa.

Haka koda suka zo gadan rutse ido yayi yana mai jin fad'uwan gaba, suna wuce wa ya
sauke wani nannauyan ajiyan zuciya tare da kallon yayan, harara ko yasamu don haka
bai sake cewa komai ba har suka isa cikin garin.

Aiko yara sai faman tururuwa suke gurin biyo motar manya ko sai kallon motar suke
harda baki da hanci, kai gaskiya 'KAUYEN ci baiyi ba loz.🤭

Shiko Auwal sai faman yatsina yake da harare harare.

Basu zame ko ina ba sai bakin clinic d'in, shiga ciki sukayi sukai parking asibiti
ba wani mai girma bane, 'karamin asibiti ne sosai dagani da d'add'an asibiti ne,
domin pentin duk ya kurkurje.

Koda suka fito daga motan sai Auwal ya kama rufe hanci.

Buge masa hannun yayan yayi tare da gargad'i san nan ya saura rawa kansa.

"" Yaya"" waigo wa yayi tare da hararan sa, bai damu ba yasake cewa ciki marai rai
cewa kamar zaiyi kuka "" yaya inyi magana don Allah, idan kayi sai naci 'kaniyar
ka, basan jin shirmen ka yanzu "".

Turo baki yayi irin na yaran nan 'yan shekaru uku had'u.

""Toni bani ne zanyi maganan ba ai yaya, bakina ne keson yayi maganan"" dariya ne
yaso su'buce ma yayan amma sai ya matse tare da mai kashed'i da ido.

Don haka sai yayi shiru bai sake cewa komai ba.

Office d'in babban mutum dake kula da asibitin suka shiga, domin yayan sai da yazo
satin can suka gama komai da komai da mutumin.

Kawai kawo sa dama yayi.


Domin har wurin kwana ansa mar masa wani gida madai daici mai d'an kyau dashi kusa
da asibitin ne.

Gidan na kusa da nasu Aisha, yana kallon jikin gidan su Joy, sayan gidan yayan yayi
kawai don 'kanin nasa kar ya takura sosai.

Komai na bu'kata ya samar masa harta kayan abinci ya zuba masa wanda sai yafi
shekara anaci sai dai abama wasu.

Don haka koda suka gama da ogan sai suka fito ya rakosu domin kai Auwal gidan sa.

Bayan ya gama duk wani abu da zai masa sai yayi sallama da 'kanin sa tausayin sa
fal a ransa amma guma su masa haka, don haka kila ya sassautawa Kansa.

Suna saran 'kila yayi hankali.

***

Bai dawo gidan ba sai da yaga tashin yayan nasa sanan ya juyo gida ba'kin ciki dam
a cikin ransa.

A cikin gidan parlour ne mai dai dai ci, sai da kwai toilet da kitchen a cikin
parloun, d'aki gudu biyu.

'Daya ne aka saka masa gado mai d'an kyau, sofa da kayan bu'katan d'a namiji,
suturu da sauran su.

'Dayan ko dam da kayan abinci.

Kitchen ma komai yasa masa haka ya zaga ya duba komai na gidan, ya yaba da
'ko'karin d'an uwan sa, domin yasan babu wanda zai masa sai shi.

Don haka wanka yayi tare da kintsa kansa cikin gajeran Wanda da farin singlet,
domin garin da zafi.

Shiga kitchen yayi domin yanaji yunwa, domin sabda maganan tafiyan nan ba wani abu
yake ci ba, baida kwanciyan hankali ci.

Don haka kar yama kansa horo da yawa, sai ya dafa abu mai d'an sau'ki yaci, bayan
ya gama yaji kiran sallah la'asar don haka sai ya saka milk d'in jallabiyan tare da
fito wa daga gidan bayan ya rufe ko inah.

Kalle kallen wurin ya tsayayi na wani lokaci sa'an nan ya nufin masallacin da yake
hango wa nesa da gidan nasa.

***

Tunda ya fito mutane sai faman kallon sa suke, maza da mata, muslmai da arna, ba
wai yau suka saba ganin 'yan birni ba, amma wanann na daban ne, gani ma suke yafi
wad'an can.

Kallon da suke masa haka yana 'bata masa rai.

Har a masallacin ma bai tsira ba, wasu har 'kus'kus suke suna tambayan wanan
baturen daga inah? mai kuma yazo yi?, babu ansa don haka suka 'karici gulman su
sukai shiru.
Cikin 'kan'kani Auwal yayi sallah, ana idarwa ya fito domin tsami kawai yake ta
sha'ka "" wai ai sai cikina ya kumbura, fut"" ya tofar da yamu.

Nufo gida yayi yana mai yatsina, yana gaf da 'karisowa gidan nasa ya hango 'yan
mata biyu suna tahowa da uniform a jikin su, kallon d'aya ya musu ya d'auke kai a
zuciyar sa ko yace "" yanzu dama da makaran ta a garin nan shine 'KAUYEN ci da
gidadanci bai barsu ba? hu'um"".

Aisha tayi gida tana ce da Joy "" besty don Allah gobe banda latti, kinji?"" Kai
kawai ta gyad'a mata ta shige gida itama tayi gida, dai-dai nan shima yazo jikin
gidan nasa bud'e wa yayi ya shiga yana mai ta'be baki.

"" Wow, ashe akwai masu d'an waye wa?"" Domin tunda suka gansa suka d'auke kai.

Basu damu da ganin ba'kon fuskan da suka gani ba.

"" Kai amma faran nan zatai girman kantsiya, matsiyaci ji gidan su, kai zatai
girman kai"" tsaki yayi.

"" Wayyo mami, zufa zai illatani, fanka ne kawai, ga inji ba, yanzu ya zan mami
na? kum.......
'Karan wayar sace tasa yayi tare da zuwa wurin wayar.

Ganin mai kiran nasa yasashi saki lallausan murmushi.

Da murmushi a fuskan sa yace "" My love ya kike?, bros kana lafia dai ko? babu wani
damuwa ko? idan akwai please kagayamin kaji d'an 'kanina, ina sauraron ka, tell me
kaji my boy?"" .

Zum'ba baki yayi yace "" am not a boy, I' m a big man"" smiling tayi ''naji to,
yanzu ka girma ko?" banza da ita yayi.

Da gangan tayi, tasani sarai baison a kirasa da yaro, "" autan mami shalelen Rahama
baka jina ne?, ina sauraron ka, fad'a min mai kake so "".

Turo baki yayi kamar tana gaban sa ya shagwa'be murya "" ba komai, yanzu yaushe
zaki dawo, kimin al'kawarin bazaki dawo da ciwon nan a tare dake ba, please sister
ki warke da wuri 'kaninki na bu'katarki kusa dashi kinji?"" tausayin 'kanin nata ne
ya kamata.

Hawaye taji na sauka akan kyakkyawan fuskan ta.

Sharewa tayi tare da cewa "" very soon zan dawo kaji, okay promise?, y promise "".

"" Yanzu dai kace baka bu'katan komai ko?"" lumshe ido yayi sanan ya jadda mata
baida bu'katan komai.

Sun d'au tsahon lokaci suna waya kamar karsu rabu.

Haka mami ta kirasa itama sun dad'e suna waya ta kuma kwantar masa da hankali.

Kowa na gida ya kirasa, kowa ya nuna damuwa akan sa, hakan yasa ya rage damuwan da
yake ciki.

Don haka wunin ranan cikin kwanciyan hankali ya kwana.

***

Washe gari zai ya d'an tashi da wuri, saboda yasan zashi asibiti, bayan yayi sallah
sai ya koma barci, bai tashi ba sai kusan 7:00am, don haka wanka yayi a sukuni,
yayi break fast ya shirya ciki kayan N Y C E, kayan sun ba'in yin masa kyau, sun
kar'besa sosai.

Kusan takwas saura a fito gidan yana rufe 'kofar gidan su Joy suka fito daga gidan
su Aisha da shirin makaranta a jikin su ko ba'a fad'a maka ba, kasan makaranta
zasu.

Kamar jiya kallo d'aya Aisha ta masa ta d'auke kai, Joy kuwa kallon ma bai samu
daga gare taba.

Shima haka take a gare sa.

Hanyan asibiti ya nufa suma dole tanan ne hanyan su, suna gaba yana bayan su, yana
mai mamakin girman kan yaran.

"" Ji wancan ita kuma bata san tana tana da 'kiba bane ta d'inka kaya yana baiyanar
da suran jikin ta, jifah, anya ba 'yar iska bace, ji yadda take kad'asu, oho god
help me kada damuwa na ya motsa"".

Samun kansa yayi da 'kin kauda idon sa har suka 'kule masa shi kuma ya shiga
asibiti.

Sunyi nisa suna ta ta'ba fira Aisha tace ""besty wallahi ba'kon birnin can ya tafi
da emani na, ya had'u wallahi, banci yafi 'karfina da nace inaso"".

Tsaki Joy ta saki kamar bazatai magana ba kuma sai tace "" amma dai ke banza ne,
kina mace ki zubar da 'kimanki ta 'ya mace, tir miki wallahi "".

Dariya Aisha tayi tare da cewa ""haka kawai sai na cuci kaina bazan fad'i abinda ke
raina ba, wash har naji sa'kin abinda ke damuna saboda na fad'a wa besty na, jiya
fa ko barci na kasa, don ko makaranta dare na kasa zuwa, saboda tunanin sa ya
hanmin 'karfi da kuzari"'.

"" Besty don Allah idan mun dawo ki rakani wurin sa, na sanar ma ina tsanani
'kaunar sa"".

Wani uban hararan da Joy ta wurga mata yasa ta had'iye sauran maganan ta.

Comment & share pls


[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳 🌳🌳🌳🌳🌳

(Ta'kai taccen labari)

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

Bismillahir Rahamanir Rahim

9⃣1⃣0⃣
9⃣to1⃣0⃣

Yau har suka fita 'KAUYEN basu samu mashin ba, haka suka 'karisa makarantan a
'kasa, domin sai da suka kusa zuwa makaranta sannan suka samu, Aisha zata tsaida,
Joy tace "" Allah baza mu hauba, da yake mu asararrune mukusa makaranta sai mu
hauko? to badani ba, yau akaiwa baba kud'in sa"" dariya Aisha tayi "" kai besty""
bata kulata ba suka cigaba da tafiya har suka 'karisa makarantan, Joy na ba'in
tsoron bulala amma miskilancin ta baisa mutum ya gane domin ba nunawa take ba.

Aiko sunsha dukan late, domin sai da aka musu bulala har goma, ko gezau Joy batayi
ba, Aisha ko sai da tai kuka.

Sai faman tsine wanda ya bugesu take a zuciyar ta, "" basu da imani basu la'akari
da nisan da mutum yake"".

Haka taita 'kun'kunai har suka shiga class.

******Auwal kuwa bayan ya shiga asibitin abinda ya kawo shi ya fara, sai faman
yatsina yake.

3:00pm dai-dai yabar asibitin, gida ya dawo yayi wanka tare da dafa cous cous yaci,
ya kwanta domin ya huta, ko ina na jikin sa sai faman ansawa yake alamun gajiya ne
zaryan atare dashi.

Kai wannan Auwal d'in akwai la'kaumanci, ya saba komai masa ake, sai abinda ba'a
sashiba zaka gansa kan gaba.

Girki kam ko mace albarka, domin sai dai mami bata shiga kitchen ba, indai tana
ciki shi kuma yana gida zagewa yake yana taya ta aiki.

Saboda tayata da yake ba wani nau'in abinci da bai iya ba, banda wanan Auwal bada
son jiki ba, kuma bai iya komai ba bayan wannan.

Amma akwai 'ko'kari sosai ta fannin karatu.

3:45pm ya tashi yayi masallaci, bayan an idar da sallah sai ya fito, zama yayi a
'kofar gidansa yana ganin masu kai da dawo wa, duk wanda zai wuce sai ya kafa masa
ido yana kallon sa kamar zasu cinye sa.

Yana zaune Aisha ta fito daga gidan su, dauke da littafain a hannun ta, ga hijabi
har 'kasa dagani islamiya zata.

Kallo d'aya ya d'auke kansa, wuce shi tayi ba tare da ta kulasa ba.

""To ita d'ayar fah?"" yace a cikin zuciyar sa, can kuma sai ya ta'be baki tare da
cewa "" to ina ruwana"" haka ya d'au tsahon lokaci zaune a wurin nan, domin har
lokacin tashin su Aisha a makaranta yayi ta dawo ta same sa a wurin da ta barsa.

Sai da yayi magriba da i'sha sanan ya koma gida.

***

Yau kwana Kwana uku kenan Joy na fama da ciwon ciki, kuma ciwo irin sosan nan,
miskilanci ya hanata nunawa a fuska balle ta bud'i baki tayi magana.

Saboda miskilancin ta shiyasa sam uwar bata gane ba, da dare yayi haka ta tashi
zata fita.

Har takai bakin 'kofa uwan tace ""where are you going?"" turo baki tayi sanan tace
"" gidan su Aisha zani, kina ganin dare yayi sosai ko?"" d'aga mata kai kawai tayi.

"" Karki dad'e"" shima d'aga kai tayi ta 'kara gaba.

****Auwal zaune a 'kofar gidan sa, yana shan iska, abin dad'i da 'KAUYEN nan sam
basu da sauro, kasan cewan ana zafi shiyasa ya fito yana shan iskan waje.

Dare ne, babu wuta sam a garin amma farin wata kamar rana.

Yana d'an kalle kallen sa, sai yaga Joy tsaye a 'kofar gidan su kamar meneman wani
abu.

Kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai, tare da koran shed'an.

Domin sanye take da guntun vest da gajeran wando, wanda ko rabin cinyan ta baiyi
ba.

"" Anya wanan yarinyan ba karuwa bace kuwa? A fuska kamar MUMMiNA SADI'QA (littafin
sis rukyn Mamah, kuyi maza masoya ku garzaya karku bari abaku labari, domin ta baza
basira da fasaha a cikin mashahurin littafin nan nata)., amma a zahiri abin ba kyan
gani, kai Allah mana tsari da kyan d'an mazuru, tur"".

"" I hate her"" yace tare da to far da yamu.

Itako bata san yanayi ba sam, shigewa gidan su Aisha tayi da sallama d'auke a bakin
ta.

Baban Aisha n da maman ta suna daga d'aki, Aisha ce kawai a tsakar gidan itace ta
ansa mata tare da kallon ta da mamaki d'auke a fuskan ta.

Cikin 'kasa da murya tace "" besty meye haka?"" cikin yatsina ta kalle ta tana
neman 'Karin bayani.

Tashi tayi ta jata cikin d'akin ta, Allah yasa babu 'kannin ta duk sunyi barci.

"" Besty meye haka don Allah? look at you"" ta'be baki tayi tana mai kallon jikin
ta.

Ta gane sarai mai take magana akai amma sai tai biris da ita, neman wuri ma tayi ta
kwanta.

Tana mai cije le'be, domin a wanan lokacin ciwon taji ya taso mata.

"" Besty don Allah kibar irin wanan shigan, domin baida tsari sam ko addini ma ya
han........., tsaya malama, kina manta cewa addini nan da naki ba d'aya bane ko? mu
bamu takura sai kije can ki 'kara malama"" tace cikin masifa.

Da mamaki take kallon 'kawar tata, domin hakan ba halin ta bane sam, komai tace
mata tana binta da idone kawai.

Kuma takan d'auki magana ta da mahimmanci, sa'banin yau.

Gani ta dafe ciki hawaye na zubo mata yasa ta 'karisa da gudu gare ta, tana cewa ""
menene besty? "" shiru bata tanka taba, tana ri'ke da ciki

"" Nine ko?, sorry na bari bazan sake ba, kiyi ha'kuri besty bansan kina irin wanan
shigan sam, domin zai bawa 'yan iska ko wad'an da basu kai zuciya nesa ba yin miki
fayd'e, amma kiyi ha'kuri idan yayi miki zafi bazan sake ba "" tace cikin sanyin
murya.

Shiru bata tanka taba, sai dai tabar hawayen, idon tama ta rufe kamar zatai barci.

Ta d'au tsahon lokaci a haka kafin ta tashi tayi gida ba tare da ta kulata ba.

Addu'a Aisha tayi a zuciyar ta "" ya Allah kaceto wanan baiwa taka"".

Barcin ranan batayi shiba, domin cikin ya matsa mata.

***

Washe gari Sunday, rana da Joy tsaneshi a rayuwar ta bata san meyasa ba, batason
ranan.

Ko nace ta tsani zuwa church, indai maman ta tasa ta sukaje to mudin taje to sai ta
kwana da ciwon kai mai tsanani.

Ranan ne ranan ni'ku ni'kun ta, balle yau ya had'e mata da ciwon mara.

Tuda madam Gloria ta tashi take mata fad'an ta tashi tayi duk abinda zatai, "" yau
banzan d'au iskancin da kikayi na satin can ba,, ki tashi maza"" ko cikan ka batace
mata ba.

Bata damuba domin ta saba da hakan.

Ciwon na cinta ta tashi 6:37am tayi bayi, wanka tayi ta fito, shiryawa tayi cikin
gajeran blue d'in riga, ta wuce guwwa.

Rigan tayi mata kyau sosai, ta fitar mata da shape d'in ta sosai.

Tea uwan ta mi'ka mata "" ki kwana kinasha na tafi karki zo a kan lokaci, yau sai
ma'kota sun 'kwaceki"".

Tayi 'kwafa tare da fita bubble d'auke a hannun ta kannan yasha gashin doki.

Toshi ina Joy ta samo suma ne?😁. gare Ku fan's ina jiran ansa.

Ruwan zafin kawai ta shanye bread d'in ta aje, d'aukan siririn gyalen ta ba'ki ta
yafa ta rufo gidan ta fita.

Tafiyan ta na yau yafi na kullum nawa, daurewa kawai take take taka wan, domin duk
d'aga 'kafan da zatai sai taji cikin kamar ba nata ba.
A haka taje church d'in wurin 8:20am, lokacin har sun fara wa'ke wa'ken su da raye-
rayen su.

Shiga tayi cikin ba'kin ciki.

Uwan na ganin ta ta banka mata harara, bata damu ba taje can baya tai kwanciyan ta
hankali kwance.

Ciwon ranga ranga ya taso mata da kwanciyan ta kad'an.


Bata san sanda ta 'kwala ehu ba.

Ehun ta yasa uwan ta nufota tana surkulensu.

Kan kace me hankali kowa ya dawo kanta, pastor ya fara mata addu'a, yanayi yana
tatta'bata.

Ganin yaune damanshi na 'karshe da zai maida miyonsa yasa yace akaita gidan sa zai
mata addu'a na musamman.

Wani saurayi ne yace akaita asibiti kawai, basu jada maganan saurayin ba suka
kinkimeta sai asibiti.

Pastor nan na tsine ma wannan saurayi a zuciyar sa.

****
Asibiti.........

Sunje aka kar'be su cikin gaggawa, sai dai me wanda zai duba ta baizo ba aka sanar
masu.

Cikin kuka da tashin hankali madam Gloria tace "" ku taimakeni karta mutu kunemoshi
kunji Ku taimaka"" tausayin ta suka ji fita wani yayi ya nufi gidan Auwal duk da
jiya ya sanar zai rin'ka huta wa duk weekend.

Da 'kar da sud'in goshi Auwal ya biyo wanan saurayin suka nufo asibiti.

Sai mita yake.....

Direct d'akin da take yanufa ana nuna masa, yana gaf da shiga maman ta tace "" don
Allah doctor kaceto mini yarinyan yaya,ita kad'ai gareni"" tsaki yayi a zuciyar sa,
"" yanzu akan 'kazaman arnan nan ne banzan can ya tasoni?"" Tsaki yayi ba tare da
ya kulata ba yayi ciki.

Shigo masa da kayan aiki akayi ya fara duba ta batare da yaga fuskan taba.

Koda ya gama ya gano matsalan don haka fita yayi bayan yayi mata aluran da zai rage
mata zugin.

Yace ma maman ta samesa a office d'in shi.

Bayan tazo bayani yayi mata da cewa "" yarki zata fara al'ada ne"" nan dai yayi
mata bayani dangane da damuwar 'yar NATA ya rubu ta musu magungunan da zasu siya.

Godiya tayi masa ta tafi sayowa a cikin asibitin.


****Da alluran barci ya had'a mata don haka bata farfad'o ba har sai bayan la'asar,
bata abinci sukayi sa'anan tasha magani.

Taji dama dama sosai, don haka sukaje suka sanar dashi .

Yazo kwanan da zai sa dashi da d'akin saiga Aisha, kallo d'aya yayi mata ya d'auke
kai.

Shiga d'akin yayi itama ta mara masa baya.

Idonnun sa basu sauka a ko'ina ba sai kan fuskan Joy......................

Ina bu'katan comments sosai my lovely fan's


Luv you all💋💋

Share pls🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

(Ta'kai taccen labari)

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

Dedicated to my fan's

Bismillahir Rahamanir Rahim

1⃣1⃣1⃣2⃣
1⃣1⃣1⃣2⃣
to1⃣2⃣
1⃣1⃣

"" Haba biri yayi kama da mutum, ba banza ba ashe ba musulma bace"" yace a zuciyar
sa. Shanye mamakin sa yayi tare da
Matsewa ya shiga, dudduba ta yayi tare da mata tambayoyi, tana basa ansa yana
rubutawa, koda ya gama tunda yaga ta samu sau'ki sosai kawai sai ya sallame su tare
da cewa yana mai kallon maman ta "" madam zaku iya tafiya, ba wani matsala bane
sosai mata da yawa suna irin wanan ciwon, a kula da shan maganin ta"". Godiya tayi
masa shi kuma ya fita ba tare da ya sake ko kallon taba, tattara kayan su suka bar
asibitin, bayan sun dawo gida uwan ta cigaba da kula da ita, har tasamu lafia, duk
da bawai ya bar mata bane, yana mata kawai dai tana daurewa ne.

Yana tashin mata lokaci zuwa lokaci, shi kuma Auwal da sanin sa ya sallame ta,
domin haka kawai yaji bazai iya juran ganin ta ba, kuma ma wai shine zai rin'ka
duba ta.

Yasan dai in dai suka kula da maganin zataji dama dama, domin mafiya yawancin irin
wanan ciwon sai mace tayi aure take bari.

Ya sallame ta amma bai huta ba sam, domin sallaman kawai yayi amma hankali sa nakan
yarinyan, bai san mai yasa tunanin ta yasashi gaba ba kusan kwana biyu kenan.

Kuma tun daga ranan bai sake sata a idon saba, tunin ta yayi masa yawa wanda har
yana son shafan aikin sa, dare bai da sukunin barci yadda ya kama ta, idon sa
photon yarinyan kawai yake gani, musamman wasu surori na jikin ta dake firgita shi,
duk lokacin da ya tuno wani sura na jikin ta, to tabbas sai yasha magani yake samun
sukuni.

Safe ma haka kai a ta'kaice wuni yake cikin tunanin ta, ya Kuma rasa dalilin hakan.
Yau kusan sati bai sata a ido ba ko 'kawarta bai sake gani ba, don haka wani iri
yakejin sa. Monday ne yau amma sam yaji baisan zuwa asibitin, ko wanka bai ba ya
fito waje ya tsaya daga bakin 'kofar gidan sa, lokacin wurin 7:35pm ne, ko minti
biyar da tsayuwa baiyi ba sai gashi sun fito daga gidan su Joy d'in, jikin su sanye
da uniform, idon ya kafa mata a fakaice ya d'auke kai. Ajiyan zuciya yayi tare da
cewa yana kallon su suna tafiya cikin natsuwa, "" ta rame sosai, kar dai nace ciwon
ne har yanzu?"" yana mai cigaba da binta da mayatatcen kallo.

"" Oh, my god, duk ni naja hakan, laifi nane, bazan cire miki ba, amma da zan iya
kula dake ki samu sau'ki fiye da yadda kika samu. Sorry! "" yace kamar tana gaban
sa.

Bai koma gida ba har sai da suka 'kule masa, shiga gida yayi yana mai jin 'karfi a
jikin sa.

Wanak yayi tare da had'a breakfast sa'an nan ya fito gidan domin wuce wa asibiti.

***

Abu ya zama wa Auwal kamar ibada, kullum sai yazo ya tsaya duk safe yaga wuce war
su makaranta sa'an nan yake samun sukuni, ya rasa maike damun sa game da yarinya,
ya damu sosai da ita.

Yanzu haka kimanin watan sa hud'u kenan a garin kuma tsahon wanan lokacin tunanin
yarinyan ya'ki barin 'ka'kalwar sa.

Satan kallon ta ya zama masa kamar ibada, duk ranan da bai ganta ba bai samun
sukuni.

Sau da dama yakan tsare kansa da tambaya "" meyasa Auwal, meye gamunka da ita?, ba
musulma bace ba"". Ire-iren wad'an nan tambayan dama wasun su yake wa kansa, kuma
har wa yanzu babu wanda yazo duba sa, domin Abba ya hana, tun ya damuwa da 'bacin
rai har yazo ya ha'kura. Yanzu ya saba da garin yana jin dad'in garin sosai, ya
saba da mutane garin, harta madam Gloria suna mutunci sosai da ita, watarana ma har
girki dashi take tana kai masa har gida, kyakkyawa alaqa ke tsakanin su, har
yanajin tana d'ebe masa kewan gida sosai.

Ba musulma bace, bata 'kaman musulmai, domin har yanzu tana tsanani son mijin ta
duk da ya dad'e da mutwa.
Yau weekend, zaune yake a 'kofar gidan sai ga Joy ta fito daga gidan su Aisha,
sanye take da kayan da kusan kullum indai ba makaranta ba yake ganin ta dasu, kayan
da duk yagan ta dasu yanzu yake jin ba'kin ciki sosai.

Riga ne white mai hannun vest, da gajeran wando, kayan sun matseta sosai.

Kallo d'aya ta masa ta d'auke kai, ciza yatsa yayi tare da 'kwafa.

Gida tayi bayan ta yabi da kallo, gauda kai yayi da sauri idanun sa sunrine saboda
ba'kin ciki, "" ita dai yarinyan nan kullum cikin shigan karuwai take"" yace yana
mai da nasanin zaman sa.

Yana zaune madam Gloria ta fito zata anguwa, bayan ta Joy ne ta fito domin mata
rakiya.

Da fara'a a fuskan ta tace "doctor hutawa ake?, eh madam"" yace yana hararan Joy,
"" kutuman uba"" inji Joy.

"" Lafian ki kuwa?, keda wa?"" murmushi tayi domin bata San maganan nata ya fita
ba, "" name mama, na 'kaniyan ki, ba zagi naji kinyi ba?, a'ah, zagi kuma? ni banyi
wani zafi ba"" tace tana rama hararan da yayi mata.

"" Ina wuni"" yace da ita, "" lafia qalu doctor, ya aiki dai?" "lafia qalu, za'a
fita kenan?, eh doctor, to Allah tsare"".

"" Amin doctor, nagode"" tace tana murmushi, shi kuma yayi mata sai ta dawo.

Wuce shi sukai, raka uwan tayi da nisa saida ta samu mashin sannan ta dawo, zata
cikin garine saro kaya domin kayan da take siyarwa duk sun 'kare.

Dawo wa tayi tana zancen zuci, "" shege kawai d'an isaka, haka kawai ban maka komai
ba ka kama hararan ta da shegun idanun nan naka mai kama da na mayu, shiyasa tunda
naga take taken sa d'an iskan yanzu na gummaci ciwo ya kasheni da dai ya duba ni,
ba ta'kaman sa da girman kan sa don yaga shike duba mutum ba?"" tayi 'kwafa.

"" Ai ba kyauta kakeyi ba bare k.........."" Sai kuma tayi shiru tana cije
le'benta.

Kwnan da zatai gida ta had'u da Isah, kallon ta yake kamar maye dama a haushi take
kawai sai tace "" d'an iska lafia kallon? "" "" ni kika cewa d'an iska?, eh ance
d'in idan ba d'an iska bane kai meye na bin mutane da kallon iskanci?"".

Zuciya ta ciwo isah, kawai sai ya biyo ta, guduwa tayi ya bita yana cewa "zan nuna
miki isancina yau dan ubanki, zanga uban da ya tsaya miki a garin nan, wawuya
banza, akwai d'an iska ma irrin uwarki?, ina ubanki yake?, ba cikin shege uwarki
tayi ba ta gudo garin mu? wa yasan asalin ku?"".

Tsaya wa yayi cikin ba'kin ciki da kuka "" tace Kaine d'an iska ba uwata ba, banza
wawa shashsah 'kazami........"" kif ya kifeta da mari.

"" Shegiya angaya miki bamu sani bane, to agari nan ta haifeki, banza yau sai naci
uban ki, ke uwarki zance domin baki da uban. Kuzon an taimaka muku ba'a karaku ba
shiyasa kikewa mutane tsiya da iskanci ko?"".

"" To yau zannu na miki ni cikakken d'an island,yau zan maida kwad'ayi na, inga
uban da zai 'kwaceki duk fad'i garin nan "".

Yace yana janta tana tirjewa, kafiyan tsiyan da da miskilanci ta yasa ta'ki neman
taimako duk da tulun tsoron dake cinta.

'Dukan ta yayi cak yayi bayan gari da ita, tafiya suke yana ta surfa mata zagi tana
ramawa, sai faman kiciniya take domin 'kwatan kanta amma ta kasa.

Ganin suyi nisa ba kuma mutum ko d'aya nane cikin ta ya d'uri ruwa.

Sai asanan ta kama ehu, amma babu mai jinta.

Nan ta yanke shawaran basa ha'kuri, sai dai ta makara, domin lokacin ne ya kawota
dajin da babu maceci sai Allah.

****Auwal kuwa bayan wuce wansu yayi tsaki da cewa "" ni kika harara ko
beb........... "" sai kuma ya kasa 'karisawa, ""zaki zo ki sameni yau sai kin gayan
idan ni sa'anki ne, sai na gara miki zama, har 'yan iskan kayan dakike sawa sai
kinbar skasu badai uwar taki bata ba, hmmm har ciki zanje sai an'kona kayan duka"".

Yana nan zaune sai ga uwan ta dawo da allama wani abu tazo d'auka domin bai isa ace
har taje ta dawo ba.

"" Sannu da dawo wa" "" yauwa Auwal ban maje ba, mantuwa nayi na dawo"" tace tana
shiga gidan ta.

"" Joy, Joy, shiru d'aukan jakanta tayi tafito tana mamaki rashin ganin ta a gidan,
"kuma war haka Aisha na makaranta bare nace tana gidan su, kuma bata shiga indai
Aisha bata sai da 'kau'karan dalili"".

Yana zaune ta fito, ya gama tunanin ina tayi sai ga tambayan madam Gloria.

"" Doctor nace don Allah bakaga yarinya taba?, bata dawo ba bayan wuce war mu?""
tana tambayan tanjin fad'uwan gaba.

Shima fad'uwan gaba ne ya ziyarce shi.

"" A'ah gaskiya, bata dawo ba"" yace yana mai dafe zuciyar sa.

"" A'ah ina tayi?, bata yawo fah, kuma baka a shigan ta gidan nan ba?"" tace tana
nuna gidan su Aisha da kallo.

Kafin ya bata ansa sai ga 'kanin Aisha ya fito daga gidan.

"" Yauwa Muhusin abokina Joy tana gidan kune?"" cewan Auwal, "" a'a bata"" Muhusin
d'in yace.

Kallon mai mashin d'in da ya kawo ta tayi tace "" malam ko zaka tafine? zanje neman
yarinya na"".

Duk da Auwal na cikin damuwa bai hansa dariya ya'ke ba yace "" kije kawai madam
nasan ba nisa taiba 'kila ki ganta yanzu, baza 'bata ba insha Allah "".

"" Nagode yarona, bari naje, idan ta dawo kace mata kada taje ko ina, ta jirani na
dawo please kaji"".

Gyad'a mata kai yayi, ita kuma ta hau suka wuce.

Kasa cigaba da zama yayi zarya ya farayi "" ina yarinyan nan tayi?"".
Gaban sa nata cigaba da fad'uwa ya tashi ya rufe gidan sa, ya jawo masu Joy 'kofar
su yabi hanyan da suka bi.

Duk taku d'aya fad'uwan gaba sa na 'karuwa ne.

***

Kokuwa suka kama, ya yayyaga rigan nata, ganin na shanun ta awaje madai daita dasu
sai faman wal'kiya suke, yasa kwad'ayin sa ya sake tasowa, kamo ta yayi tare da
fara shafosu.

Dukan sa take tana ehu tana basa ha'kuri amma a bazan, kai tamkar ma tana 'kara
zuga sa.

Laushin su ya gigitashi, "" beby dama haka kike, gaskiya beby zaki dad'i, ashe ba
banza ba muje birin wurin kawuna 'kato dashi yake cewa matar sa beby ba"".

Kai bakin sa yayi kan nata ta gantsara masa cizo, ehu yayi ya sake ta da sauri.

Tashi tayi ta fara gudu, binta yayi yana cewa "" shegiya bazan ta'ba bari daman nan
ya wuce ni ba "".

Gudu take yana binta, ranan ko kamar an hana mutanen garin fitowa.

Babu kowa har ta kusa da barin bayan garin, gajiya tayi jiri ya kamata ta yanke
jiki ta fad'i.

Hamdala yayi tare da rufa mata.

Shafata yake ba'ka'k'kautawa, ganin hakan zai 'bata masa lokaci sai yakai hannun sa
maran ta.

Cire mata......

Comment & share please🙏🏻🙏🏻

Luv u all my fan's💋💋💋💋💋


[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

(Ta'kai taccen labari)

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

Bismillahir Rahamanir Rahim

1⃣3⃣1⃣4⃣
1⃣3⃣1⃣4⃣
to1⃣4⃣
1⃣3⃣

Neman keta mata had'i yake da gaske, cikin tsoro tace murya a sha'ke "please kaji
tausayi na, na daina ma rashin kunya" ina bai san ma tanayi ba, 'ko'karin cinkan
burin sa kawai yake. Kuka take kamar ba gobe ta ciza ta yakusheshi ina basan ma
tanayi ba, ya ciro abinsa zai zurma kawai yaji an buga masa 'katon itace a kai.

Ehu ya saki tare da fad'uwa gefe, ita ko idon ta dake rufe ta bud'e sakamakon jin
'karan da taji.

Ganin shi yashe gefe tayi hamdala a zuciyar ta tare da yun'kurin mi'kewa.

Ganin Auwal tayi tsaye ya juya mata baya, ta gane shine saboda kayan jikin sa.

Kasa mi'kewa tayi domin ta wahala wurin yun'kurin 'kwace kanta a wurin isah.

Wani marayan kuka ta saki, baiko waiwayo taba ya fara tafiya ransa na masa 'kuna.

"Please ka taimakeni na tashi" ya tsinci maganan ta, kamar bazai tanka ba, tama
cire ran zai taimake ta sai taga ya mi'ka mata hannu sa, kallon sa tayi sai taga ko
kallon ta baiyi ba.

Mi'ka hannun tayi, taimaka mata yayi ta mi'ke, tana mi'kewa ya fisge hannun sa.

Tare da fara tafiya yana tangad'i.

"Bazan iya tafiya ba, don Allah ka kamani" cikin zafin rai ya waigo yace da ita
yana jifan ta da mummunan kallo.

"Arniyan banza da hofi kidaina had'a ni da Allahn da ya haliceni, kinsan Allah ne?
ai kafirai basu sanshi ba, da kinsan shi da baki rin'ka shigan karuwai ba" yace
yana mai tofar da yamu.

Tafiya ya farayi ba tare da ya sake kallon taba.

"Wayyo mama, mama kizo ki taimakeni" tace cikin mawuyacin hali.

Dawo wa yayi tare da sake mi'ka mata hannun sa d'aya kamar d'azu ta kama.

Tafiya take da'kar, shiko hannun ta dake nasa ji yayi kamar an watsa masa garwashin
wuta.

"Na tsani 'kyauyen nan gaba d'aya" yace a zuciyar sa yana mai share hawaye dake
shirin zubo masa.

Har sunyi nisa sai ya d'an saci kallon ta, gani yadda take yayi matu'kar firgita
sa, ga wani malulun ba'kin ciki da ya rufesa.
Kamar wada akama dole yace yana mai zame hannun sa daga nata "don iskan a haka kike
nufin zamu tafi da yagaggen riga? ko dama ai ba damuwar ki kayan mutunci sukayi ba,
ansaba, hakan ya nuna baki tubaba, baki saduda ba. Hmmm" yaja ga garumin numfashi.

"Bazan iya tafiya dake a haka ba gaskiya, in anbinci kama kekika gayyace shi, kila
bai miki yadda kike so bane shiyasa kike neman wani. Toni ba d'an iska bane, sanan
ban mu'amala dasu, tir, fasi'kanci baiyi ba Sam, Allah tsare mu ya kare mu, amin".

Yace yana mai takawa abinsa.

"Ni nayi nan, Allah had'a ki da dai-dai ke sai aje can a 'karata , misssss".

Ya cigaba da tafiyan sa, kuka ta fashe dashi mai tsanani, ha'ki'ka yaci mata
mutunci tace cikin zuciya, zuciya nata na mata 'kuna.

" Wato nufinsa ni karuwa ce ko? hmmm" tace tana cije le'ban ta.

"Ba komai ba laifin ka bane, kuma nagode da taimako" bai masan tanayi ba domin yayi
nisa.

Tayi nisa cikin tunani sai ta tuna inda take aiko bata san sand ta mi'ke da gudu ba
tama manta bazata iya tafiya ba, duk da taji a jikin ta, amma guma ta tsira da
mutunci ta.

Tafiya take tana tattare yagaggen rigan ta tana rufe 'kirjin ta dashi.

A haka ta kawo har gida mutane nata kallon ta amma ko ajikin ta, hakan bai dame
taba sam.

Tura 'kofar gidan su tayi ta shiga, wurgar da yagaggen rigan tayi ya rage daga ita
sai d'an guntun siket d'in ta.

'Daura ruwan wanka tayi, domin a lokacin babu abinda take bu'kata da ya wuce hakan.

***

Auwal kwance a gadon sa yana ta rafka uban kuka kamar wani mace, kuka ya'ke bil
ha'ki da gaskiya, yayi dana sanin ganin ba'kin abinda ya gani a idonsa.

Zuciyar na masa zafi mai tsanani, da ya rufe idanun sa abinne ke bayyana masa
kamar yanzu ake a gaban sa.

Yana hango abun dake fizgan zuciyar sa gare ta a hannun wani yana sarrafasu yadda
ya gadama.

Wani irin 'kara ya saki tare da ri'ke kansa.

"Duk ita ta janyo ta jama kanta, musulunci yayi, Allah ka 'kara mana imani" yace
tare da dafe zuciyar sa.

"Kullum bata da shiga sai wanda zai hankali mutum gare ta, kai anya ba ita tanemai
ba?" yace yana cije le'be.

Kiran sallah ya tayar dashi, mi'kewa yayi direct toilet ya shiga wankan yayi sa'an
nan yasa white d'in jallabiyan sa ya fito bayan yayi alwallah domin tafiya
masallaci.
Jin idanuwan sa sun masa nauyi yasa shi saka gilasa a fuskan shi, domin baiso a
gane damuwar sa.

Yana rufo gidan sa, yaji motsin tafiya, bayan ya rufe ya juyo domin tafiya, sai
yaga Joy tsaye kusa da gidan nasa, ta jingina da bangon gidan su Aisha, hannun ta
rungume a 'kirjinta.

Idanu wan ta nakan sa tunda ya fito, d'auke kai yayi kamar bai ganta ba tare da
had'e fuska ya fara tafiya.

"Nagode doctor" tace cikin za'kin murya, tsayawa yayi cak, tare da sauke 'boyeyyen
numfashi.

Can kuma mai ya tuno kawai sai ya wuce fauuuuuuu.

Murmushi ta saki tare da lumshe idanuna ta, tana mai bin bayan sa da kallo.

Bata bar kallon sa ba har dai ya kure mata.

Sa'an nan tayi gidan su Aisha.

Manager please

Share please
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

(Ta'kai taccen labari)

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

A fuwan my fan's, bakuyi fushi bako? nama sani baza kuyi ba domin kun kasance masu
ha'kuri dani, ina godiya sosai sosai.

Dedicated to my fan's, luv you guys🥰


*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

1⃣5⃣1⃣6⃣
1⃣5⃣1⃣6⃣
to1⃣6⃣
1⃣5⃣

Shiga gidan su Aisha tayi, maman Aishan ne zaune a kusa da murhu tana fiffita wuta,
"sannu da gida mama" tace tana d'an du' kawa kad'an.
"Yauwa Joy" tace fuskan ta d'auke da murmushi, "mama Aisha ta dawo kuwa?" "a'a,
amma yanzu zaki ganta don zataje islamiya anjima, okay" tace tana mai zama a kan
turmi dake tsakar gidan.

Suna zaune shiru sai ga Aisha tayi sallama, ansa mata mama tayi. Ita dai Joy kallon
ta kawai take.

"Besty yakike" cewar Aisha lokacin da ta'kariso gaban ta.

"Lafia" kawai tace da ita "zo muje ko?" Aisha tace, mi'kewa tayi sukayi d'akin
Aishan.

Kwanciya kawai tayi a katifar Aisha daga shiga d'akin.

Kallon ta kawai tayi ta kyauda kai, domin tunda taga haka to miskilancin ne tsaba
ya tashi.

Sai dai abin mamaki gani kawai tai lokacin da ta waigo tana ta faman murmushi.

Cire hijabin hada tayi tare da d'aukan na islamiya ta saka.

Zama tayi kusa da ita tare da cewa "besty zani islamiya, zanje na dawo nasha labari
domin da alama dai wanan murmushi da ake saki zanji labari mai dad'i".
Ta'ba baki tayi tare da mi'kewa " sai ina kuma besty? inace zaki jirani na dawo
ne?" "Uhu'um" tace da ita tare da riga ta barin d'akin.
Sometimes tana mamakin 'kawar nata, "wata irice ita gadai tanan".
Fito wa tayi lokacin har takai 'kofar gida, 'kofar gidan su ta tsaya tana kallon
gidan Auwal.
Fitowan Aisha yasa ta kauda fuskan ta daga wurin ta maida kan Aishan.
" Besty sai na dawo ko?" d'aga mata kai kawai tayi, ita kuma ta wuce makaranta ta.

"Baki gajiya kedai, kullum makaranta, ina zan iya wannan wahala, ga wani abu
biyabiya dashi".
Tace tana ta'be baki tare da barin kallon 'kawar tata.

Tsawon lokaci tana tsaye a wurin kafin tayi cikin gida.

Koma wanta da kad'an maman ta ta dawo, saukan ta a mashin Auwal ya fito daga gidan
sa, da murmushi ya'ke yace "sannu da zuwa, yauwa yaron kirki" tace dashi "Joy ta
dawo kuwa?".
Wani 'kululun ba'kin ciki ya tokare masa, amma ya daure yace " uhmm".

Shiga gida tayi shi kuma ya wuce inda zashi.

****

Watan Auwal shida a 'KAUYEN 'YAR KADDE, abubuwa da dama sun faru, daga ciki akwai
yawan shige masa da Joy keyi, kamar idan ta gansa ta gaishe sa da dai sauran su, ta
rasa maike damun ta dangane dashi, kuma sau goma zata masa magana bazai tanka taba,
duk sanda ya ganta idan a hanya ne canza hanya yake, idan kuma ta tasame sane sai
ya d'auke kai yayi kamar bai ganta ba.

******Auwal kwance yana waya da mami sai faman narke mata yake tana biye masa "mami
don Allah ki ro'ki Dady ya yarda na dawo, wallahi mamina nayi missing d'in ki, ga
'kauyen ko dad'i babu, har yanzu ban saba dashi ba".

" Ga sister zata dawo nan da sati mai zuwa,".


"Ni Auwal bansan yadda zanyi ba, nayi nayi koni nazo na ganka ya'ki, bansan yadda
zanyi ba nima inason naga boy d'ina" tace tana murmushi.

Turo baki yayi tare da cewa "mami niba boy bane gaskiya na girma" "da gaske my son?
uhum".
"Amma mami na haka zanta zama sai na shekara sanan zan ganku?, eh son tunda haka
Dadyn ku yake so".
" Haba sai kace mara gata, mara galihu? hab fisabilillahi kamata haba mami na, do
something ".

" Hmmm, bari zan jaraba Allah sa adace, amin mami na, ko kuma kawai kisa 'yan gaban
goshin sa agaba nasan suna cewa zaiyi na'am".
"To bari suzo muga" "yauwa mamina shiyasa nake tsananin 'kaunar ki, love you mum"
yace tare da sakin masa kiss ta wayar.

Dariya tayi tare da kashe wayar, shiko wani farin cikin da yadad'e baiyyi ba yaji
ya mamayeshi smiling kawai yake.
Tashi yayi daga kwancen tare da shiga toilet yayi wanka, T-shirt mai ratsin baki
da fari yasaka da ba'kin wando, kayan sun matu'kar kar'ban sa.

Kallon kansa yayi a mirror shi kansa yasan ya had'u, smiling yayi tare da cewa
"yaron mami ka had'u" tare da cewa yima kansa kiss ta mirror d'in.

Bayan ya kintsa ya fito domin le'ka asibiti lokacin la'asar ne sakaliya.


Yana rufe gida ya juyo yaga mutum a bayan sa, kauce wa yake ninyan yi ta tare,
tace tana ya mitsa fuska "doctor cikina na ciwo ko zaka taimakamin please?".
Kansa na kallon gefe yace " nan ba asibiti bane, baya ga haka kije kinemi wani
not me".
Kallon sa take ta 'kasan ido, "zaki iya bani hanya na wuce" yace fuskan sa kamar
wanda bai ta'ba dariya ba.

"Kayi Kyau" tace a hankali tare da matsa masa a kan hanya.


Ya fara tafiya yaji kamar ana binsa a baya, bai waigo ba sai da yaje 'kofar
asibiti sanan.
Ganin wace ke bayan sa ya had'e rai tare da shigewa.
Cigaba da bin nasa tayi har 'kofar office d'in sa, bud'e wa yayi tare da shiga, zai
rufe ta turo jikin ta.

"Kibar wurin nan", " doctor nazo fa domin lafia tane, da gaske banda lafia ka yarda
dani" ganin kallon da yake mata yasa tace haka.
Bud'e mata yayi ta shiga, zai duba ta kodon maman ta.
Zama yayi a kujeran sa, ita kuma tana nan tsaye, nuni yayi mata da hannu alaman
ta zauna.
Zaman tayi sa'an nan yayi shiru yana jira daga gare ta.

Tasani sarai tagane nufin sa amma ta share sai ma 'kare masa kallo da take.
Gajiya yayi ya mi'ke domin zuwa duba marasa lafia, itako tana nan zaune ko motsawa
batayi ba.
Fita yayi ya barta ba tare da yace da ita komai ba.

Kallon office d'in take lungu da sa'ko, ba wani babba bane tunda na 'kauye ne, amma
da yake na d'an gata ne ba laifi yayi Kyau.

Tashi tayi taje kan 'karamin bed d'in marasa lafia da yake office d'in ta kwanta
tana mai lumshe ido lokacin ne taji ciwon ya taso mata, don haka sai ta fara
mur'kususu.
Dai-dai nan Auwal ya bud'e 'kofar, ganin bata a kujeran da take yasa shi ajiyan
zuciya tare da cewa "mayya kawai ta tafi......." Bai 'karisa zancen saba yaji nishi
.

Waigawa inda yake jiyowa yayi kwance ya ganta a gadon.

Tana mur'kususu, d'auke kansa yayi kamar bai ganta ba, abinda yazoyi yayi ko ya
gama don haka sai ya tattara abinda yazo dashi domin koma wa gida.

Aje key d'in office d'in ya aje tare da ninyan fita yana cewa kamar mai ciwon baki
"idan kin tashi sai ki rufe musu office d'in su".
Kuka mai had'e da ehu ta saki tare da cewa " wayyo doctor zan mutu kataimakeni
please, mama tace nazo ka dubani".
Dawo wa yayi tare da cewa idon sa na kallon gefe "meke damun ki?" "tunjiya da
dare nan kemin ciwo, ina kenan?" yace ba tare da yajuyo ya kalle ta ba.
"Nan" tace, shi kuma yace cikin gajiya da 'kufula "shi wurin baida suna
ne?" shiru tayi tana mai cigaba da kukan ta.

Haushi yaji zai fita, itako ta dage iya 'karfin ta tasaki ehu mai 'karfi.
Toshe kunnin sa yayi tare da kallon da azafafe ya nufo ta.

Kamar zai bugeta yace "wallahi kika sake min 'kara a kunni sai naci....." sai kuma
yayi shiru.

"Ina kemiki ciwo? yace yana hararan ta.


Maimakon ta bashi ansa sai ta cigaba da kukan ta.

" Tashi kibarmin office yanzun nan kafin ranki ya 'baci" yace yana matsowa kusa da
ita.

Bai aune ba kawai yaji ta kama masa hannun, da mamaki da ba'kin ciki yake kallon
ta.
Bai gama mamaki na yaji hannun sa a lallausan jikin ta.
A han maran ta ta d'aura hannun nasa.

Cikin kuka tace "nan ne kemin ciwo" fisge hannun sa yayi cikin masifa yace yana
tofar da yamu.

"Banza 'kazamiya, amgaya miki kowa 'kazami ne irin ki? ko ance miki ni Auwal irin
karnikan kine 'kazamai Wanda basu san inda yake musu ciwo ba irin ki".

"Zan miki gargad'i da babban murya ni Auwal nafi 'karfin ki, nafi 'karfin 'kazan
taccen jikin ki, kuma ki fita harka ta, idan ba haka ba ki kuka da kanki".
" Banza kawai, Auwal ba jaki bane, kisani koda ni mazinaci ne irinki to bancin
sauran wasu, kina mace mai aji da kima da daraja amma kinzubar dasu, koba abun abun
mamaki bane arna zasuyi fiye da hakan".

Ya sake tofar da yamu idanun sa ya rufe yayi ta surfa mata ba'ka'ken maganganu.
Koda ya gama bai damu da kukan da take da juye-juyen da take ba.

Yabar office d'in tare da sanar da mai gadin wurin idan ta tafi ya rufe masa office
d'in ya'kara gaba.

Tafiya yake yana ganin dishi-dishi domin abinda yafaru yana ganin sa a idanuwan sa
kamar yanzu ake.

Kuma ya tabbatar da zarginsa 'yar iskance ita......

Tofah fan's kunji fan

Kubiyoni domin jin yadda zata kaya, amma hakan bazai samu ba sai naga comments.

Comment & share pls

'Yar Aliyu ce✍🏻


[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*LITTAFAN MARUBUCIYAN:-*
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

*Dedicated to my family*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

1⃣7⃣1⃣8⃣
1⃣7⃣1⃣8⃣
to1⃣8⃣
1⃣7⃣

"Dole na cire ki a raina, kota halin 'ka'ka kuwa, zuciya baki min adalci ba, taya
zaki sa naso wacce bata dace dani ba? yes bata dace dani ba, bata cancan ceni ba.
Ni mai tsaftane ita 'ka zama, ya Allah fitar da ita a zuciya ta". yace yana mai
rintse ido, lokacin yana kwancen a bed d'in sa, babu abinda yake tunani sai ita,
tunani halin da ya baro ta kawai yake.

***Ta d'au tsawon lokaci a wanann yana yin, tana cikin damuwa mai tsananin, abu uku
ke damun ta. Na farko 'kama da Auwal ya kira ta hakan yayi mata zafi sosai, ta gane
cewa yana zargin ta da aika ta fasi'kanci, abinda bai sani ba, zina abune da take
matu'kar 'kama, hakan da ya matu'kar tsaya mata a rai.

Na biyu ciwon maran dake damun ta, ba'kin ciki yasa ya rage mata kaso hamsin na
ciwon.

Na uku tsananin 'kaunar sa da bata san tanayi ba sai yau, gashi Auwal yayi mata
nisa, kalman sa kawai yasa ta gane tsananin kiyayyar da yake mata.

" Ina son ka, wallahi ina son ka, ina tsananin 'kaunar ka, 'kaunar ka shine ajalina
zan rayu da son ka duk da nasan baza ka ta'ba sona ba".

Tace tana mai fashe wa da kuka mai tsanani, a daddafe ta bar office d'in nasa, idan
nun ta nata zubar 'kwallah.

A haka taje gida bata damu da kallon da mutane kema taba sam.

Tana shiga ta tadda uwar ta a tsakar gida, ganin yana yin da 'yar tata ta shigo
yasa ta isa gare ta da sauri ta taro ta.

Tare da tambaya ta abinda ke damun ta, shiru tayi mata tana mai cije le'be.

Tambaya duniya nan uwar ta mata amma ta share ta, ganin haka uwar ta fita harkan ta
duk da yanayin da 'yar tata ke ciki na damun ta.

Kwanciya tayi tana mai tsine ma isah domin shi ya janyo mata tsana da 'kiyayyar da
Auwal yake mata.

••••••••••••••••Yau kimanin kwana hud'u kenan Auwal ya'ki fita ko waje komai a gida
yake yin sa, duk yayi wani iri saboda damuwa dake d'awainiya dashi.

Ta kai ta kawo har da Kuka, kwancen yake yana tunani da ya zame masa abinci domin
abincin ko damuwa dashi baiyi.

"Na sani ina sonki, so mai tsananin ma kuwa amma sai dai ya kasheni da dai na auri
sauran wani, na tsaneki ban sanki daga yau" yace yana maiji zafi a zuciyar sa,
domin tuno cewa ita sauran wanine ya hadda sa masa damuwa fiye da nada.

Wanda har tsanan ta wani sashi na zuciyar sa yake.

'Karar wayar sa ce ta dawo dashi daga halin da yake ciki.

Kallon wayar yayi na wani lokaci kafin ya d'ako, ganin mai kiran sa yasa shi
peaking tare da sakin murmushi da ya kwana biyu baiyi ba.

Kafin tai magana ya riga ta da cewa "sweetheart" yana jan numfashi.

Dariya tayi tare da cewa "na'am sweet bros, yakake d'an 'kanina?" shiru yayi kamar
mai tunani.

"My Auwal kanajina kuwa?" shiru ba ansa ta sake cewa "kana lafia kuwa my bros? talk
to me please " tace cikin tashin hankali.
Sanin halin ta yasa shi
'bata rai tare da cewa "sister ba 'kalau nake ba sam".

" Oh my god!!! what happen?, sister my heart" sai kuma yayi shiru.

"Mai ya same ta?, ciwo take sister, kaje a duba ka mana".

" Na'ki gida kawai nake son dawo wa, mai yasa?" tace dashi, "'kauyen babu dad'i,
ina son na dawo kafin ki dawo, don Allah ki ro'ki Dady na dawo".

" I miss you sister nd mamina, Auwal kenan Dady fa ya kafe ya nace yace sai ka gama
sannan zaka dawo, kuma ma idan nazo dole nazo na ganka".

"Kad'an mafa ya rage maka, sister baza ki gane ba Wallahi ni gida nake so".

"Yanzu ya kake son ayi?, ki ro'ke sa nasan zai amince na dawo kinji tawa".

Shiru tayi ya sake cewa " pleaseeeee" .

"Naji, amma kamin al'kawari zaka koma duk lokacin da aka bu'kaci hakan".

" Na amince" nan dai sukai sallama.

°°°°°

Kwana hud'un nan Joy ta kasance cikin tsananin damuwa, damuwa ba d'an kad'an ba.

Tana son ganin sa, tana son jin murya sa, amma ta yaya? tunda ya'ki fita daga
gidan.

"Inason ganin sa, bazan iya barci ba yau idan ban gansa ba" tace cikin damuwa.

Mi'kewa tayi tare da shirya wa, yau anyi abin arzi'ki, domin shigan dogon riga mai
roba d'in nan tayi.

Yayi mata Kyau matu'kar gaya, har dasu rolling.

Da yake yau Sunday akwai church madam Gloria ta dad'e da tafiya.

Ta fashe jikin ta da turare mai dad'in 'kamshi, tana gama shirya wa ta kulle gidan
sanan ta nufi gidan Auwal gaban ta na mugun fad'uwa.

Tura 'kofar tayi taji ya bud'e, tana jin mugun fad'uwan gaba tayi cikin gidan cikin
sand'a kamar wata 'barauniya.

Tunda ta shigo take jin 'kamshi girki da mamaki ta 'karisa shigo wa.

Babu kowa a tsakar gidan don haka d'akin taga an sakayo ta nufa.

Tura wa tayi wani sanyin dad'i da ni'ima taji, "hmm, komai naka cikin tsarin yake
kuma mai kyau ne. Ina son ka my man".

Shiga tayi babu kowa a parlour, zama tayi a d'aya daga cikin kushin d'in parlour.

Tayi kusan 5mint babu alamar sa, don haka sai ta nufi bedroom d'in sa.

Fito war sa kenan daga toilet, towel d'aure a jikin sa, d'aya kuma yana goge fuskan
sa.
Tana ganin haka ta dawo baya tana mai runtse ido tare da dafe 'kirjin ta dake bara
zanan fashe wa.

Ga wani mugun tsoron sa da taji ya ziyar ce ta, don sai yanzu take da nasanin shigo
masa gida.

" Oh my god!! bari na bar masa gida tunda bai ganni ba, don idan ya ganni Allah
kad'ai yasan abinda zai min".

"Uwa uba zargin sa zai 'kara tabbatar wa" tace tana mai fita daga parlour kamar
yadda ta shigo, haka har ta fita gidan.

Tana fita ta fara sauke numfashi kamar wacce tai gudu, tana cewa "thank god! I'm
safe".

Tana mai dafe da 'kirjin ta.

Jin kamar motsi tabar jikin gidan da gudu ta koma nasu Aisha.

" Ashe ba kowa bane" tace tana dariya da tunda nake da ita ban ta'ba ganin tayi ba.

Kuma dariyan ba 'karamin kyau yayi mata ba.

Tana nan tsaye na kisan 30mint sai gashi ya fito cikin shiga na alfarma.

Farar shadda yasa, shaddar tayi matu'kar 'kar 'bansa.

Bai lura da ita ba sam har ya rufe gidan nasa, yazo zai wuce ne ya gan ta.

Kauda kansa yayi tare da had'e rai, gaban ta taji ya fad'i amma ta daure tace cikin
sanyin murya "doctor barka da safiya" yayi banza da ita.

"Doctor I'm sick" nan ma ya share ta, domin tafiyar sama yake.

"Hmm" tace tare da lumshe idanun ta, tana mai kallon bayan sa har ya 'bace mata.

"Allah tsareka ya kareka my one nd only" tace farin ciki na cika ta.

°°°°Shiko Auwal yaje sayowa su mami tsaraba ne domin anci nasara Dady ya yarda ya
dawo yayi kwana goma.

Saboda farin ciki yasa yaje har cikin garin keffi yayi musu tsaraba na gani na
fad'a.

***Joy ko bayan tafiya sane ta nufi church tana ta faman murmushi, koda tazo uwar
tayi garin ciki sosai domin bata ta'ba zuwa da wuri irin haka ba.

Bata tashi zuwa sai an tashi ko an kusa tashi, duk fitinan uwan da masifar ta bai
sa gobe taje da wuri.

Bayan sun tashi barin uwar tayi tayo gida domin ganin sanyin idanun ta.

Koda tazo bai dawo ba, don haka sai ta bud'e gidan su ta shiga, wanka ta sake
she'kawa .
Bayan tai wanka ta zauna ta tsantsara kwalliya, tasaka riga da wando, rigan mai
dogon hannun sai dai ya kamata cif.

Wandon ma dogo ne amma ya matse ta, a shekarun nan nata tana mamaki girman
halintatan ta, tana ganin wad'an da suka girme ta da shekaru goma ma basu da cikin
halita irin tata.

Komai ta mallaka, jujjuya jiki ta kamayi tana kallon mirror, ta saki wani 'kaya
tattacen murmushi.

"Kai ma nasan kana 'kasa wa, nasan ina burge ka, nasha jin anace wa maza nason
irina".

" Kama kana so ko?" tana mai kashe ido d'aya, dariya ta fashe dashi.

"My man, humm, kana mugun burgeni, kana tafiya da imani nah" tai 'kwal-'kwal.

Cikin tausayin kanta tace "zaka aure ni?, ka aure ni don Allah, wallahi babu wanda
ya ta'ba sanina, ban ta'ba fasikanci ba. Zina! Na tsane sa, abinda baka sani ba
inda tsoro bazan iya bawa wani kai na ba".

" Nasan darajan kaina, ganina da d'an iskan nan da kai Wallahi fyad'e yake son min,
bai min komai ba shine ka ceceni".

"Ka bar zargi na don Allah" ta fashe da wani irin kuka mai tsanani bayan ta gama
surutun ta.

Sai da tayi mai isan ta sanan taje ta wanko fuskan ta, wanan karon powder kawai
tasa sai man baki

Fita tayi waje, ganin 'kofar gidan sa a rufe yasa ta tsaya 'kofar gidan su idon ta
nakan hanya don ganin 'bilowar sa.

Tana nan tsaye Aisha ta fito, ido Aisha ta kura mata kamar wacce bata ta'ba ganin
taba.

Hararan ta Joy tayi tare da d'auke kai, dariya ta bawa Aisha, 'kariso wa gare ta
tayi tana mai cewa "Allah besty kinyi kyau, wanan da dama dama dai, Allah sa kidai
na saka irin wad'an nan ki dawo saka namu".

" Shigan mutunci sai yafi kyau dake" ta 'karsa murmushi d'auke a fuskan ta.

"Bazai ta'ba yuwu wa nasa kaya irin naku ba, ke bazan iya ba sam, haka kawai nasa
kayan da zai rin'ka damuna".

" Uhum'um bazan iya ba, ku muslmai gaskiya addinin Ku da kawai takurawa".

"Muko namu sam babu ta kura, za kai shigan ka yadda kaso".

" Ni wallahi kinzo kina ma damuna, kina samin ciwon kai kina ta sani surutu".

"Allah baki ha'kuri besty nayi nan" ta gane sarai fishi tayi amma ko a gefen gyelen
ta.

Tafiyan Aisha da kad'an sai ga Auwal ya fito daga taxi.

Kayan sa ya fara fito wa dashi, bayan ya gama fito wa dasu tas ya sallami wanda ya
kawo sa.
Waige yayi ko zai sami wanda zai taimaka masa, kawai sai yaga Joy tsaye tana kallon
sa.

'Dauke kai yayi tare da bud'e gidan sa ya fara shiga da kayan.

Ya kai na farko da na biyu duk tana tsaye, ya dawo domin sake kwashe sauran.

Ya kai hannun sa da ninyan d'auka itama takai nata.

'Daga kai yayi tare sa wurga mata wani hararan mai firgitar wa.

Ta tsorata matu'ka amma bata dan dara ba.

Yana d'auakn wanda takai hannun yayi ciki dashi ita kuma ta kwashe sauran ta bisa.

Ya aje kenan ya juyo sukai karo.

Sakin kayan tayi tare da sakin 'kara "wayyo Allah doctor akawai zafi sosai wallahi"
tace cikin shagwa'ba.

Cikin masifa yace "amma dai ke jakace ko?" shiru tayi cikin jin zafin maganan sa
tana kallon sa.

"Dai na kallo na mayyah da 'ki'kiya, ballagaza, shashsha sauran maza".

" To duk mai tanki nafi 'karfin ki wawuya kawai, fice min a gida idan ba haka ba"
yayi 'kwafa.

Kuka ta fashe dashi tare da cewa "ni kazaga?" Yace cikin tabbatar wa "eh dan ubanki
ko kina da abinda zakiyi ne?".

Zuciyar ta taji yana ta farfasa, don haka tace " karka sake zagin ubana idan ba
haka ba zakai nadama".

"Nadamar uwarki zanyi wawuya?, to ance ubanki ke uban naki ma yaci uban sa, kakanki
kenan".

" To wallahi duk maitarki haka zaki bar Auwal, fita maza".

Son da take masa yasa ta kasa yin abinda tai ninya don haka sai ta tashi tabar masa
gidan sa.

Ganin comments zai taimaka matu'ka wurin cigaba da labarin nan.

Amma banyi al'kawarin kullum ba, idan na samu time zakujini. Kuyimin uzuri don
Allah, ba'a son raina bane, ina tsananin 'kaunar Ku masoya na farin cikin ku shine
nawa ngd🙏🏻

Comment & share please


[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*LITTAFAN MARUBUCIYAN:-*
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

*Dedicated to my family*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

1⃣9⃣2⃣0⃣
1⃣9⃣2⃣0⃣
to2⃣0⃣
1⃣9⃣

°°°°°°

Joy tunda ta tashi take jin ta wani iri, haka take shirin makaranta cikin sanyin
jiki, bayan ta gama ta sallami maman ta ta fito, tsaye take a 'kofar gidan su tana
kallon gidan Auwal tana jin fad'uwan gaba mai tsanani a tare da ita. A haka Aisha
ta fito ta ganta, 'kariso wa wurin ta tayi tare da ta'ba ta domin tayi nisa a
tunani, tace da ita "besty muje" figit ta dawo daga dogob tunani da ta tafi.

Har sun fara tafiya ta waigo tana mai sake kallon gidan Auwal, gani take zai fito,
"lafia kuwa kike besty?" Shiru babu ansa sai ma kauda kanta tayi idon ta fal da
hawaye jikin ta na bata cewa wani mummunan abu zai same ta.

Wani zazza'bi taji yana son kama ta, domin fad'uwan gaban ta 'karuwa yayi wanda
har sai da Aisha taji.

Tsayawa tayi tare da ru'ko ta, tana ware ido cikin tsoro da damuwa tace "besty baki
da lafia ne?" kallon ta tayi tare da bud'e baki da ninyan yin magana, amma ta kasa
sai ma fashewa da kuka tayi tare da zamewa ta zauna a dam'ban kan hanya.

Dur'ku sawa Aisha tayi itama har ta fara kuka, domin Allah ya saka mata tsananin
'kaunar Joy d'in.

Kamo ta tayi da ninyan d'ago ta amma ta'ki bata dama.

Cikin kuka tace "besty tashi mu koma gida tunda baki da lafia" girgiza mata kanta
tayi, alamar a'a.
"Meke damun ki besty? kanki d'aya kuwa?, kina ganin inda kike zaune kuwa?" shiru
babu ansa sai cigaba da kuka take mai matu'kar ban tausayi.

Rungume ta tayi suka cigaba da kukan su babu mai lallashin wani, ga garin shiru-
shiru da yake anyi ruwa sama da asuba kowa ya 'boye a d'aki saboda sanyi.

°°°°°

"Ya zanyi na sami motar da zata kaini gida?, shegen 'kauye babu ko taka mamman
mashin bare ka samu mota, wallahi yaya kun cuceni" cewar Auwal da ya gama shiri
tuntuni yana mai burzar da isaka.

"Wayyo mamina ya zanyi yanzu?" d'ako wayar sa yayi tare da dialing number mamin
tasa.

Tana peaking ya fashe da kuka kamar wani yaron goye.

"Menene son?" shiru ya'ki magana sai cigaba da kukan sa yake.

"Na shiga uku son meya faru kuma? yi magana mana, koso kake ka ruguza farin ciki
na? ina murna zaka dawo yau na ganka amma kana kuka, oh Allah na yaushe yaron nan
zai girma".

Cikin shagwa'ba yace " mami babu mota fah a garin nan, yanzu ya zanyi na taho? ko
mashin basu da".

"Jiya da zani cikin gari ba'karamin wahala nasha ba" .

"Yi ha'kuri my son, ka fita kaje cikin gari ka nemo taxi ya kawo ka, ko nawa zan
biya kaji? maza my son".

" To mami na, amma fah da wuya 'kafana bai kumbura ba, jiya mafa 'kafana na taka
har na kusa barin garin sanan na samu mashin".

"Insha Allah bazai kumbura ba, da yarda Allah kana fita zaka samu maza yaron mami".

Kashe wayar yayi tare da mi'kewa ya fita, sanye yake cikin 'kananun kaya kayan
sunyi matu'kar kar'ban sa, saboda sanyin da ake sai ya sanya jacket akan kayan.

Tafiya yake cikin natsuwa, da kagan sa kaga had'ad'an gaye.

Har yanzu suna nan zaune suna ta faman kuka kuma cikin sanyin, fad'uwan gaban ta
yana 'karuwa, jikin ta na bata yana kusa da ita.

Waigen hanyan gidan su tayi ta hango sa gaf dasu, murmushi ne ya su'buce mata, tare
da kafeshi da ido tana share hawaye dake zubo mata.

Da mamaki Aisha ke kallon ta, murmushi da bata ta'ba gani ba a fuskan 'kawar tata
ce ta gani kwancen a fuskan ta.

" Besty kece kuwa? wallahi kinyi mugun kyau, ko dama ke kyakkyawa ce, kin 'kara
kyau" Aisha tace tana mai ta'ba ta.

Ta'ba tan da tayine ya fargar ta ita 'baran-'bara man da take son tafkawa.

Domin tayi al'kawari ko son sa zai kashe ta ko uwar ta baza ta sani ba har sai idan
ya furta mata cewa yana son ta.

Kauda kanta tayi daga kallon sa don kar Aisha ta d'ago wani abu.

Murmushi gefen baki tayi tare da cewa cikin miskilancin ta tana mai kallon sa da ya
kusa inda suke.

"Nagode" tace tare mi'kewa, mi'kewa itama Aisha tayi tana cewa "besty kin 'bata
kayanki, kuma kinsa mun makara sosai mu koma gida tunda haka kike so".

"Amma wai don Allah me yasaki kuka ne haka? kuma lokaci d'aya kin ware?".

Share ta tayi tana mai du'kar da kai 'kasa, domin Auwal yazo dai-dai dasu.

Yana ganin su ya d'auke kai fuska a murtuke, yana wuce wa Joy ta sani numfashi tare
da dafe zuciyar ta.

Tayi shiru na wani lokaci sannan ta fara tafiya, biyo bayan ta Aisha tayi tana
mamakin miskilancin bestyn nata.

Haka suka zo har gida babu mai ce da d'an uwan sa komai.

Aisha ce dai tace da Joy lokacin har tasa 'kafar ta a cikin zauren gidan su " sai
anjima besty" kai kawai ta d'aga mata tare da shige wa gida.

***"Lafia kika dawo yanzu? anya ma kuwa?, bakuje makaranta taba" cewar maman Joy.

Jefar da jakan makarantan tayi a tsakar d'akin ta zauna a kujera tayi shiru na wani
lokaci.

Sannan tace cikin 'kasa da murya "bamu sami zuwa ba. Meya sa to" cewar uwan shiru
nayi bance komai ba sai ma kwanciya ta da nai ina mai lumshe ido.

Girgiza kai mama tayi tare da cewa "ubangiji ya shirye ki" ta shige cikin d'aki.

Murmushi nayi tare da cewa a hankali "ameen, handsome ina zaka ne haka cikin
kyakkyawar shigan dani kad'ai ya cancanta na gani?".

" My man karka kalli kowa please, zama makaho kaji, ka zama kurma kaji".

"Allah sa karsu kallan min kai" tace tana dariya a hankali tare da rufe fuska.

A haka mama ta fito ta same ni, "anya bazan kaki a duba 'kwa'kwalwarki ba?, kwana
biyun nan baki da aiki sai dariya da magana ke kad'ai".

Kallon mama nayi tare da shagwa'be fuska ina mai cewa " lafia ta qalau" na mi'ke,
cire uniform d'in nayi tare da shiga cikin d'aki na d'ako zani na d'aura a 'kirji.

Har zanyi bayi sai mama take cewa "bari na le'ka 'kawata na dawo, tunda yau kin'ki
makaranta sai ki mana abinci" har ta fita ta dawo ta sake cewa "Joy kina ganin
doctor kuwa?" shiru nayi ina maijin sanyi a raina danaji an anbaci masoyina.

"Ina magana kina jina kuma, banson iskanci" cikin sanyin murya nace "a'ah" kawai
nayi toilet.

Ina jinta tana cewa "ko lafia yake oho" ta fice.

Na fito wanak kenan naji 'karan mota, gabana naji yayi mugun fad'uwa don haka
banjira komai ba nayi waje da d'aurin 'kirji.
Mota nagani a dai-dai gidan Auwal, tsayawa nayi tare da kallon gidan inajin wani
yanayi .

Ganin wani ya fito a gidan da kaya yasa nayi cikin gidan.

Karo mukaci dashi, "asshhh" nace ina dafe goshi na.

Kallon sama da 'kasa yayi min tare da tofar da yamu ya ra'ba ta gefe na ya kwashe
kayan da suka zuba ya fita ya barni a wurin.

Shiga cikin parlour nayi naga kaya a tsakar parlour harda akatin kayan sa.

Zama nayi ji'bus tare da ri'ke kaina da ya saramin.

Bansan sanda hawaye ya zubomin ba, ina zaune ya shigo shida mutumin ko yasan Allah
yayi ruwana a wurin kwashe sauran sukayi tasa ina kallo hawaye nata kwaranya.

Bayan sun gama fita da kayan ya dawo don rufe gida, tsaye yake yayi shiru don
baison magana ta had'a su ko kad'an.

Bai aune ba yaji an rungume sa tare da cewa "ina zaka doctor? nine ko? yi ha'kuri
daga yau na bar maka magana don Allah ka zauna" nace ina kuka mai cin rai.

Wani irin mugun abu yaji yana fuzgan sa, domin ta mana masa a bubuwan ta a jikin
sa.

Ji yayi 'kafa funsa suna neman gagaran sa, yun'kurin ture ta yayi amma ina ta
'kan'kame sa.

Cikin wani yanayi yace "don Allah rabu dani tafiya ce a gaba na, nd sau nawa nake
gaya miki ki rabu dani ki fita harka ta?".

" Nifa ba d'an iskan bane" "nima haka" nace cikin kuka ina zare jiki na.

Tsare sa da ido nayi tare da cewa "ina zaka?".

" Inda kika aiken uwata" yace yana hararana.

Murmushi mai ciwo nayi tare da cewa "na takura ka ko?, oho miki, sanan banda
lokacin kini sai kibi wani bani ba don ni Auwal gaba nayi".

Dur'ku sawa nayi gaban sa tare da son ri'ke 'kafar sa, han'barina yayi tare da cewa
" fita min a gida na rufe malama".

Ko motsi banyi ba, wata irin tsawa ya daka min, ba shiri na mi'ke nunamin hanya
yayi tare da cewa "maza barmin gida na, maza ko kuma na caza miki kaman nu".

" Kuma gargad'i na 'karshe ki fita gona ta" yace yana mai sake daka mata tsawa.

Da gudu na fita, domin ya mugun firgitani.

Rufe 'kofar parlour da gidan yayi tare da shiga mota suka bar wurin .

Ina tsaye a cikin zaure ina kallon sanda motar tabar 'kofar gidan.

Kuka na na cigaba dayi na dad'e ina kukan, ban bari ba sai ma shiga gida da nayi
ina cigaba da kuka na, babu maganan girki sam don na manta da lamarin sa, kuka
kawai nake ta...

••••••••••••••••••°°°°°°°°°°°°°•••••••••••••••••

Tunda Auwal yaga sun kusa layin su wani irin farin ciki yakeji, yau dai zai ga mami
zai kwanta a cinyan ta, zata basa abincin ta mai dad'i zata cidashi.

Haka yayi ma mai taxi kwantan ce har suka zo 'kofar gidan su.

Horn driver yayi, mai gadi ne ya fito har wurin motan yazo tare da kallon mai taxi
d'in yana cewa don sam bai lura da Auwal ba.

"Wa kake nema ne malam?" Kafin ya bada ansa Auwal ya fito daga cikin motan.

Hararan sa yayi tare cewa "zaka bud'e ko sai ka rasa aikin ka?" da gudu ya nufi get
d'in yana cewa "yi ha'kuri alhaji bansan kai bane".

Koma wa motar Auwal yayi driver ya tada motar suka shiga, mai gadi na cewa " barka
da dawo wa " hannun kawai ya d'aga masa.

A compound d'in gidan Auwal yace wa mai taxi ya tsaya, yana tsayawa ya fita a motar
.

Mai aikatan gidan dake kai kawo suna ganin sa suka nufo wurin da gudu sauri-sauri.

Sannu da zuwa suka masa ya ansa yana shige wa ciki, yana shiga 'kayataccen parlourn
gidan babba dashi wanda aka 'kawatashi da ababen more rayuwa.

"Mamina where are you?, am back, your handsome is back" yace yana kalle-kallen
parlour don ganin ta ina mamin tasa zata fito.

Da murmushi farin ciki uwar ke sakowa daga steps .

Da gudu ya 'karisa gare ta, yana isa gare ta ya rungume ta.

Cikin farin ciki tace "oyoyo my happiness, godiya ga ubangijin tali kai da ya dawo
min da farin ciki na lafia, welcome back autan mami, jarumin jarumai".

" Fitilar gidan Kabir Mu'azam, farin wata shakallo, sannu da zuwa shalelen Rahama
da mami".

Wani irin farin ciki da natsuwa yakeji jinsa a jikin mamin sa.

Cikin shagwa'ba yace "mamina I miss you so much" kamar zaiyi kuka.

Bubbuga bayan sa tayi tare da cewa "nima haka son, muje kayi wanka sai kaci abincin
ka huta".

Tana ri'ke dashi sukayi d'akin sa, had'a masa ruwan wankan tayi tare da kama sa,
sai da takai sa bayin sanan tace " maza kayi wanka ka fito my handsome " ta fita.

Sai da ta fitar masa da kaya sanan ta sauka, zaune ta tarar da Baraka cikin girmama
wa tace "HAJIYA wanda ya kawo autan ki yana jira a sallame sa".

" Ayyah yana ina?" "yana compound, okay kun bashi abinci kuwa?".
" Eh" "okay ina zuwa" tace tare da wuce wa d'aki.

Kud'i ta d'ebo masu yawa bata damu da ta duba ko nawa bane ta fito.

Har inda yake taje ta basa tare da masa godiyan kawo mata yaro cikin 'koshin
lafia.

Godiya shima yayi sosai yana mamakin karamcin da aka masa, yana mamakin irin kud'in
da aka basa .

Cikin farin ciki yabar gidan bayan ya fitar musu da kayan Auwal d'in.

°°°°Cikin jin dad'i yayi wankan sa, gurje jikin sa yayi sosai da sosai, kai kace
zai sake fata.

Yana fito wa ya wani fad'a bed d'in sa yana cewa "Allah sa mami karta yadda na koma
wanan 'kauyen mai cike da 'kazamai".

Tsaki ya saki domin Joy ce ta fad'o masa a rai.

Tashi yayi tare da shafa mayuka maau tsada sai 'kamshi suke.

Kayan da mami ta fitar masa ya saka tare da feshe jikin sa da turaruka.

Fito wa yayi sak Auwal d'in mami ba na 'kauye ba.

Tunda ya sako mami ta kafe sa da ido har ya 'kariso gaban ta.

Hawaye taji nason zubo mata amma ta matse, ta'ba wuyan sa tayi lokacin ya zauna
kusa da ita.

" Auta ciwo kayi ne wai?" turo baki yayi tare da cewa "mami ba sai da na gaya miki
ba?, ai wanan 'kauyen babu abinda bazai sa mutum ba. Don Allah mami na kada ki bari
na koma idan ba haka ba sai kinyi kuka idan kika ga yadda yaron ki zai koma".

" Kayi ciwon kenan?, a'a kawai 'kauyen ne babu dad'i ga...ga........" sai ya kasa
fad'a.

"Ga me son?" kasa magana yayi.

Cikin damuwa tace "son gaya min don Allah".

" Idan na gaya zaki hansu mai dani?".

"Uhum fad'a kaji my boy" turo baki yayi domin ya tsani a kira sa da boy.

"Mami niba boy bane, don Allah kibar cemin haka dani boy ne aida ba ai yun'kurin
yin min fyad'e ba".

" What!!!" mami tace tana mi'kewa................

Maman kids😍😘🥰 ina godiya sosai.

Comment & share please🙏🏻🙏🏻


[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*LITTAFAN MARUBUCIYAN:-*
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*

*Dedicated to my blood sister (Fatima Aliyu wakili) Allah ubangiji ya'kara miki
lafia keda baby na*

*My fan's godiya a gare ku mai tarin yawa ina matu'kar 'kaunar ku masoya, a koda
yaushe ina alfahari daku, ina jin dad'in yadda kuke bibiya na godiya mara iyaka🙏🏻*

*MY SAHIBA, Allah ubangiji yabaki lafia, masoya muna baran addu'ar ku, don Allah
kusa sahiba a addu'a Allah ya bata lafia😭😭😭😭😭😭*

Sister Rukyn mama ina tayaki murna nan kamla littafin ki mai suna *HUSSAIN* Allah
ubangiji yaba da ladan fad'a sai munjiki a sabon wani littafin nan kusa🥰

*Besty (maman Muhammad) kwana biyu shiru😟Allah ubangiji yasa kina cikin 'koshin
lafia.*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

2⃣1⃣2⃣2⃣
2⃣1⃣2⃣2⃣
to2⃣2⃣
2⃣1⃣

Ya mutsa fuska yayi tare da had'e rai yana cigaba da cewa "da gaske nake mamina,
har cikin gida wata shegiyar arniya tazo min fyad'e".

" Kutumar uban can, waye uban ta shegiya da zata lalata min yaro?, amma dai bata
maka komai ba ko?" shiru ya mata.

Kallon sa tayi na wani lokaci sanan tace tana mai koma wa inda ta tashi "my son
tell me the truth".

Shagwa'be fuska yayi tare da cewa " yanzu mami na baki yadda da yaron ki bako?, tom
shikenan ai inaga sai tamin ciki zaki yadda".

Fashe wa da dariyan babban wansu dake tsaye tun fara shirmen Auwal yayi.

Waiga wa sukayi dukan su suna kallon 'kofar parlourn.

Hararan da mami ta jefa masa ne yasa shi gintse dariyan sa.

"Na shigo?" yace yana mai danne dariyan sa, a zuciyar sa kuwa yana mai mamakin
yadda mamin tasu ke zama tana sauraron shirmen autan nata.

Mai da fuskan ta tayi kan Auwal tare da cewa "oho ma, kuma mutum ya daina mana
la'be ko autana?, uhmm mami na, kuma na sani sarai sai ya kai maganan gaba. kuma
kin san wani abu?" yace yana mai kai bakin sa kunnin ta don kar yayan yaji, nima
bai bani daman jiba.

Sai mamin da take cewa "sun ma isa ne" kawai mukaji.

Tako wa yayi ya shigo ciki, yana mai jefa ma Auwal d'in mugun kallo.

"Mami kin gansa ko?, meka masa daga dawo wan yaro?, ban san fitina fah. A saki ma
yaro na mara yayi fitsari, Allah wanan karon ran kowa zai 'baci a gidan nan".

Gyad'a kai Auwal yayi kamar wani yaro, hakan ma yake jin kansa indai yana gaban
mamin tasa.

" Tashi muje kaci abinci idan ka huta ma 'karisa magana".

"Ku 'karisa shirme dai" cewar yaya nasa murya 'kasa-'kasa, "mai kake cewa?".

" A'ah, ni bance komai ba mami, kama ce " tace tana 'kwafa.

Dining sukayi, jan masa kujera tayi ya zauna yayan na kallon su ta fara feeding
d'in sa.

Ganin ba zai iya jure kayan takaici ba yace "mami ina wuni" "lafia" tace tana mai
cigaba da bama shalelen ta abinci.

Shiru ya zauna kafin ya mi'ke tare da cewa "sai anjima mami" ya fara tafiya.

Cikin d'aga murya tace "dawo" dawo war yayi "shin baka ga auta ya dawo bane?".

" Na gansa, shine ko gasheshi da hanya bakai ba?" zaro ido yayi tare da cewa "kai
mami shine gaba dani koni? tayaya bai gaidani ba ni na gaida sa?".

" Amma ai kasan daga uwa duniya ya fito ko?, sai kabari ya huta idan bai gaida kaba
sai kace amma ba yanzu ba, maza masa sannu da hanya".

Kamar zai kuka saboda ba'kin ciki yace "wallahi abinda kike baki kyau tawa sam
mami".

" To ubana nuna min abinda zanyi" "idan bai nuna miki ba ni gani nazo zan nuna
miki" cewar dady dake shigo wa parlourn.

Shiru tayi kawai bata iya cewa komai ba.

Kar'ban jakar hannun sa yayan yayi sukayi sama suka bar su nan.

"Mamina mai yasa Dady bai sona?" Auwal yace yana mai jin zafin yadda Dadyn ya nuna
halin ko in kula a kansa.

"Mami yau fah na dawo amma duba babu ko farin ciki a tattare da Dady, anya kuwa
mami? anya shi ya haifeni?" yace hawaye na fita daga idanun sa.

"Shishhh autana, dai na zancen nan Dadyn ka na tsananin 'kaunar ka, yafi sonka fiye
da 'ya 'yan da.." sai tayi shiru.

Lallashin sa tayi, bayan ta gama lallashin sa sai suka mi'ke daga dining d'in suka
nufi sama hannun sa sar'ke cikin na mami.

Dai-dai 'kofar part d'in Dadyn tace "muje ka masa sannu da zuwa ko yaron kirki?".

" Hmm" kawai yace sukai knocking suka shiga.

Zaune suka taddashi yana ma Yusif bayanin wani abu.

Zama mami tayi a kusa dashi, Auwal ya dur'kusa kusa da 'kafar ta tare da cema Dady
"ina wuni Dady" cikin sanyin murya.

Da fara'a a fuskan Dady ya ansa masa, tare da cewa "maraba da autan mami shalelen
RAHAMA".

" Yaushe a gari?" turo baki yayi tare da cewa "d'azu".

" Madallah, ya hanya? Alhamdulillah".

"Masha Allah" Dadyn yace yana mai cigaba da abinda suke.

Suna zaune suka gama ya sallami Yusif d'in.

Bayan fitar Yusif d'in ne take cewa "sannu da zuwa alhaji, yauwa madam, ya gidan?".

" Lafiya qalau, ya aikin?". "Sai godiya ubangiji" cewan dadyn. "idan kin sallami
yaron naki sai ki sallameni nima" yace yana nufar bedroom.

Shafo gashin kan Auwal tayi dake she'ki kamar na larabawa.

"Son jeka huta ko ina zuwa na baka labari" murmushi yayi tare da mi'kewa yace "to
mamina, barci ma zanyi idan nai sallan la'asar".

" A'a my son ba kyau barcin yamma ban yadda ba kuma kar ayi".

"Kaji?" "tom first love bazan ba" ya fita daga d'akin.

'Dakin sa ya nufa, bayan yayi alwallah yayi sallah sai ya d'an kishin gid'a yana
kallon t.v, barcin yakeji "amma tunda mami ta hana ba zanyi ba" yace yana mai barin
d'akin gaba d'aya.

'Dakin mami ya shiga, wurin da take aje keys d'in mota yaje, duba nasa yayi bai
gani ba.

Sai ya d'au na RAHAMA guda d'aya ya fito.

Koda yazo wurin motocin sai yaga duk sunyi 'kura da alama dai ba'a anfani dasu
tunda ya tafi, daga nasan har na RAHAMA.

Koma wa yayi ya d'ako na mami ya shiga, bata wuta yayi tare da danna uban horn tun
kan yaje get d'in.
Da gudu mai gadi ya bud'e masa, fita gidan yayi.

Direct gidan wansa Sani yayi, horn yayi aka bud'e masa yayi ciki parking yayi tare
da fita a motan yayi ciki.

Da sallama a bakin sa ya shiga parlour ansawa sukayi yayan har da Ikiliman.

Da gudu Iman ta nufo sa tana cewa "oyoyo uncle" cafe ta yayi tare da d'aga ta sama.

Yace "oyoyo my angle" dariya tayi, zama yayi tare da Iman d'in.

Ikilima tace "oyoyo mijin kwali" ta'be baki yayi tare da cewa "gayi nan a gaban ki,
don nafi 'karfin kwali nine na 'karfen maza azo ayi tarba ta musamman ko kuma mutum
ya koma gidan su".

" Gida kuma? a'a ai mutu karaba nida kai, mai zakaci a kawo maka?".

"Abinda mijin ki yaci"

"Babban magana to ya 'kare" d'auke kansa yayi kamar magidanci yace "a kirka wani
yanzu".

" Wallahi baka isaba dan ubanka, haka kawai kasa matata aiki da yamman nan, sa
Larai ta masa".

Murmushi gefen baki yayi tare da cewa kamar gaske "oh yaya dama kana nan?" bai
tanka masa ba ya 'kara da cewa "ina wuni yaya" bai damu da ansa wan saba ya cigaba
"mun same ku lafia?" nan ma shiru.

Dariya Ikilima ta fashe dashi tare da cewa "Allah shirye ka Auwal, mami ta gama
'bataka wallahi. Antura ka 'kauyen nan ko zakai hankali ne ashe dai akwai aiki".

Murgud'a baki yayi kamar mace yace "'kila da naki nake yawo".

Bata barsa haka ba tace " inaga kuma sa aure kawai idan ya fara tara yara zaiyi
hankali ".

" Maza kuyi" yace yana mi'kewa.

Ganin zai fice tace dashi "dawo 'kanin na dafa maka, banci mamina ta cika min
ciki".

"Daga nan sai inah" banza da ita yayi, Iman ta'ba ta fuska tare da cewa "momy don
Allah Ku daina wa uncle haka" tana mai zum'buro baki ta bisa.

Har ya shiga mota ta 'kariso, "uncle kayi ha'kuri kaji" murmushi yayi tare da janyo
ta ya d'aura ta a cinyan sa.

"Da akayi me baby na?" turo baki tayi irin yadda yakeyi, domin yarinyan tana mugun
kama dashi, idan kuka ga Akram bancin 'karami ne zaka ce shine.

"Ba momy ta 'bata maka rai ba?" .

"Ko d'aya my baby, muje gidan su Mufi, daga nan sai mu wuce duka gidan mami Ku
kwana ko?".

" Yeeeeeeeee, muje uncle " dariya yayi tare da sata a kusa dashi ya tada motar suka
bar gidan.
Zai shiga yayan zai fita ganin motar mami yasa Yusif tsayawa yana mamakin ganin
mami bancin bai dad'e da barin gidan ba.

Ganin Auwal ne cikin motar yasa yayi tsaki tare da ficewa.

Dariya Auwal yayi tare da parking, shiga sukayi Iman ta fara kiran "Mufy" da
'karfi, aiko sai ga Mufyn da gudu.

Akram a bayan ta, tafiya yake sak Auwal, sai dai shi miskiline na 'karshe.

Zuwa yayi ya rungume Auwal tare da cewa a hankali "sannu da zuwa uncle".

" Yauwa yaro na" haka itama Mufy tace.

"Ina Momyn ku?, tana sama" cewar Mufy.

"Okay Ku muje idan na gaida ta sai mu wuce gidan mami don yau gidan mami zaku
kwana".

Mufy ta saki eyhun murna, shiko Akram murmushi kawai yayi sam bai da hayaniya.

Suna hawa tana sakkowa, da murmushi tace " uncle mai yara yaushe a gari?".

"Au mijin ki bai fad'a miki ba? ruwan shi d'azun, barka da zuwa na mami".

" Muje kasha ruwa, Iman ina momy? ".

" Tana gida, ina wuni Anty" "lafia lau ta uncle".


Fridge taje ta kawo musu abu mai sanyi, kur'ba kawai Auwal yayi ya mi'ke "mun tafi"
cewar Mufy.

Kallon Auwal tayi ya d'auke kai sai tace "ina zaku yaran uncle da yamman nan?".

" Gidan grandma okay ku gaishe ta " suka bi bayan Auwal da ya fice da gudu.

Mami zaune ita da Dady a parlourn suka shigo, da gudu suka nufe kakannin nasu.

"Oyoyo, oyoyo amarena, oyoyo abokina" cewar Dady yana runguman su d'aya bayan
d'aya.

"Da zabiya da bilaki, to Ku 'kara gaba banan ba baza ku ta'ba kasuwa ba. Don na
kere Ku babu abinda zaku rud'e sa dashi".

" Can miki me zanyi da tsohon mijin ki? sai dai ko Iman" cewan sarkin tsiwa da
rashin kunya Mufy.

"Iye mijin nawa ne tsoho?, uhum" tace tana turo baki.

"Auta mai kaka wo min rasai tamin a gida?".

" Mami ni yarana duka masu kunya ne ko Mufy na?, eh uncle " suka ce tare da tafawa.

Ta'be baki tayi tare da cewa "zamu had'u idan sun tafi".

Dariya Dady yayi tare cewa "gumma ya kwaye muku ko yaro na yayi hankali, kinbi kin
'bata min yaro".
" Haka ma zaka ce ko?, to mezan ce dama idan ba gaskiya ba".

Share shi tayi tare da cewa tana kallon Akram "miskili kai kenan kullm a haka, auta
kukai yaron Ku asibiti da wuri fah tunkan abin yafi 'karfin Ku".

Ta'be baki yayi tare da mi'kewa " ina zuwa my son?" hanyan steps ya nufa.

Sai da ya hau sannan yace "d'akin ka?" a hankali.

"Me zakyi?, kwanciya. Ka bari sai bayan isha babu kayu kwanciya magrib".

Bai ce dashi komai ba sai dawo wa da yayi ya zauna nesa dasu.

°°°°°°°°°°°°

Kwace madam Gloria ta dawo ta tadda ta sai faman rizga kuka take, da sauri uwan ta
nufe ta.

'Dago ta tayi tare da cewa cikin tsananin damuwa.

Share hawaye fuskan ta tayi tare da du'kar da kan ta 'kasa.

Tatta'ba fuskan ta tayi tare da cewa cikin sanyin murya " what happened? why are
you crying?".

Murmushi ya'ke tayi tare da cewa "nothing".

" Ya zaki ce haka? bayan fuskan ki ya nuna kin dad'e kina kuka?".

"Ina lura dake kwana kin nan kina cikin damuwa, wato kina 'boye min damuwar ki ko?.
Wakike da bayan ni? ashe ban cancanci sanin damuwar ki bako?".

Kukan da take matsewa ne ta fashe dashi.

Ganin bata da ninyan barin kukan yasa uwan tace " kenan ni zaki 'boye wa wani abu?
ba damuwa na bar ki" tace tare da mi'kewa.

Ri'ko hannun uwan tayi tana girgiza kai tare da cewa "a'a mama, nothing of that
sorts".

" To fad'a min " cikin kuka nace "I'm in love with him" sai nai shiru tare da
cigaba da kuka na.

Zaro ido mama tayi tare da cewa "who?".

" Doctor...... doctor Auwal.... " kallon ta tayi cikin mamaki, amma da ta tuno baya
sai mamakin ya gushe.

Hasali ma mikin ta taji yana son tasowa, don haka cikin tsananin tausayi 'yar tata
tace "idan na fahim ta bai sani ba?" d'aga mata kai tayi.

Sauke numfashi tayi tare cewa "kisa same sa ki fad'a masa".

" Ya tafi" nace ina mai sake fashe wa da kuka mai tsanani.

Cikin damuwa tace "ina ?, ban sani ba amma kaya da yawa yasa a taxi suka tafi".
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace " to yanzu ya za'ai? ko ki manta dashi kawai,
kinga soyayyar sa ma zaki rabu da ita ki huta, tunda bamu san inda yake ba".

Hawayen idanun ne suka 'kafe tare da cewa "I can't, I cannot forget him or stop
loving him. I love him mama" nace ina mai fashe wa da kuka.

Cikin tausayi ta tace tana mai ruruguma jin ta tana shafa mata baya alaman rarrashi
"don't cry joy. I am here for you".

" Nasani mama, amma shifa ? bashi baya tare dani".

"Kiyi ha'kuri ubangiji zai duba komai"..................

Comment
&
Share

'Yar Aliyu ce✍🏻


[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

2⃣3⃣2⃣4⃣
2⃣3⃣2⃣4⃣
to2⃣4⃣
2⃣3⃣

Hawaye idanuna ne suka 'kafe tare da cewa "I can't, I cannot forget him or stop
loving him. I love him mama" nace ina mai fashewa da kuka. Cikin tausayi ta, tace
tana mai rungume ta, tana shafa mata baya alaman rarrashi "don't cry joy. I am here
for you", " nasani mama, amma shifa? bashi tare dani, kiyi ha'kuri ubangiji zai
duba komai kinji ".
Gyad'a kai kawai nayi tare da tsayar da kuka na, jin nayi shiru yasa mama ta d'ago
da fuska na, share min hawaye tayi tana murmushi tare da cewa " yauwa yarinyar
kirki" had'e da jan min kuma tu.

Murmushin ya'ke kawai nayi, "kinci abinci kuwa?" Sai lokacin na tuna da cewa mama
ta sani girki, shiru kawai nayi mata.

Sake tambayan ta tayi "nace kinci abinci?" turo baki nayi tare da cewa "a'a" ta
sigan shagwa'ba.

"To mai yasa Joy?, ya tsina fuska nayi sannan nace " ban girka ba" cikin 'kasa da
murya.

Ba tace komai ba sai mi'kewa da tayi, cikin gaggawa ta musu abinci mai sau'ki ta
kawo min har gado.

Ansa nayi tare da mata murmushi nace "nagode momana" jan kuma tuna tayi tare da
jifana da murmushi ita ma.

"Maza kici ki 'koshi 'ya guda, duk da ba wani cin kirki kike ba, shiyasa gaki nan
kullum kaman one".

Dariya na fashe dashi tare da cewa " kai mama nine kamar one?, uhum maza ci ni ina
zuwa" tace tana mi'kewa.

Wanko hannu na nayi a roban da ta d'ebomin ruwa domin haka na fara cin abinci na,
duk loma d'aya sai na dad'e kafin na had'e.

Domin tunanin abin 'kauna yayi min katutu, duk wani dariya da murmushi da nakeyi
inayi ne kawai domin mahaifiya.

Don tafiyan Auwal yayi matu'kar tada hankali na, tuno irin kayan da naga anloda a
motar kuwa na samin fad'uwar gaba mai tsanani.

Haka dai na daure naci kwatan abincin na tura gefe, lokacin ne mama ta dawo d'akin.

Kallon kwanon tayi sanan ta maido da idon ta kaina, tace cikin had'e rai "har kinme
Joy?".

Turo baki nayi tare da had'e fuska don banso ta matsaminci.

Nace " na'koshi" girgiza kai kawai tayi tare da d'auke abincin ta fita dashi.

Zuwa tayi ta 'kara wani akai don mama akwaici ta kamaci.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Auwal kuwa hankali kwance yake rayuwar sa, yama manta da wata yarinya wai ita Joy.

Kwana biyar da zuwan shi yayar sa ta dawo 'kasar tamu, zo kuga murna wurin Auwal,
yanda ku kasan yaron goye haka ya zama, ashe shagwa'ban da akewa mami kad'an ce.

Tsaraba ko yasha shi, kai kace don shi akayi tafiyan, a tsaraban harda na matan sa,
cewar yayan tasa.
Dariya kawai mutanen palon suka kwashe dashi, wanda har sai da Ikilima ta kasa
shiru tace "mutumin da bai da budurwa inashi ina zancen aure, kawai a bamu".

Hararan wasa Rahma ta jefa mata tare da cewa " ba sai kuzo ku danneni ba ku 'kwace,
ai tari zan dunga wa 'kanina har zuwa lokacin da zuciyar mu zata zo. Bare ma jikina
na bani 'kanina ya fara soyayya".

Sai a wannan lokacin ya tuno da wata aba Joy, duk da bawai ya manta da ita kwata -
kwata bane, duk da hakan shine burin shi.

Amma ina can cikin 'kar'kashin zuciyar sa itace ciki male-male.

Tuno ta da yayi ya haddasa masa 'bacin rai sosai, domin har da mummunan ganin da
yayi mata da Isah ya tuni.

Auwal mutum ne mai tsananin kishi, musamman akan abinda yake 'kauna.

Girgiza san da RAHAMA tayi shine ya dawo dashi daga dogon tunanin da ya lula tare
da kafe ta da idanuwan sa

Yanayin yadda fararan idanuwan sa suka koma yasa ta tsorata.

Idanun ta suka ciko da 'kwalla, domin a duniya RAHAMA ta tsani abinda zai ta'ba
mata d'an 'kanin ta.

Lumshe idanuwan nasa yayi na wani lokaci, domin ganin yanayin ta ya sani sarai
yanzu sai ta tada hankali ta ciwon ta yazo ya tashi.

Shiyasa ya lumshe idon don idanun su dai daita.

"Meye Auwal? meke damun ka? mai ya 'bata maka rai?" ta jero masa tambayoyin nan a
lokaci d'aya, kuma cikin kuka.

Jin kukan ta damun sa ta 'karu, amma sai ya danne damuwa nasa tare da bud'e
idanuwan nasa akan ta.

Ya sakin mata 'kayataccen murmushi, ya ri'ko fuskan ta yace "babu komai my love,
bar kukan haka" kallon cikin 'kwayan idanun sa take don tabbatar da zancen sa.

Kauda kai yayi tare da cewa "da gaske babu komai Anty na".

Jan hanci tayi tare cewa " Auwal zaka fad'an gaskiya ko sai ranka ya 'baci?".

Turo baki yayi irin yadda yara keyi yace "kice su fita to" hararan sa ikilima tayi
tare da cewa tana mi'kewa "nayi nan tun kafin a koren".

Itama Momyn su Akram ta bita tana murmushi.

" Sun fita ina sauraron ka" kwanciya a cinyan ta yayi tare da ri'ko hannu ta d'aya
ya dam'ke a nasa.

Zuciyar sa na bugawa, "ina jira fah Auwal" tace gaban ta na fad'i domin da gani
ba'karamin abu bane ke damun sa.

Kuma bai ta'ba 'boye mata damuwar saba.

Jin shirun nasa yayi yawa yasa tace "idan 'karya kake son fad'a min ba gaskiya ba
to kari'ke kayan ka".
Ganin kaman tayi fishi yasa tashi a jikin ta tare da janyo akwatin da tace wa
matar sa ta sayo.

Ya bud'e tare da kallon tulin kayan dake ciki yana nazarin su yana murmushi.

Waigo wa gare ta yayi idon ta na kansa, yace " Anty duka nata ne?" banza dashi tayi
.

Bai damu ba ya fara ciro kayan d'aya bayan d'aya yana kallo tare da murmushi a
fuskan sa.

"Anty zasu matu'kar yin mata kyau amma ban son ta yanzu" yace cikin ransa na
'kuna.

Matsowa tayi kusa dashi tace "ban gane ba?" kallon ta yayi tare cewa "abinda
kikajin nan shine kawai" idanun sa sun 'kara rinewa fiye da dah.

Ganin halin da 'kanin nata keson jefa Kansa yasa tace tana murmushi ya'ke tare da
ri'ko hannu sa.

Kwantar dashi tayi a cinyan ta tare da shafa masa gashin kansa, ta d'au lokaci tana
haka shi kuma yana ta wani irin numfashi.

Zuwa can yayi barci, jin yayi barci yasa ta sauke ajiyan zuciya tare da hamdala.

Tana ro'kon ubangiji a zuciyar ta tace "ya Allah ka San yaya mishi zuciya, idan ba
alkhairi a tsakanin sa da yarinyan ya Allah kaman tar dashi ita, Allah kasa ya
farka bashi da damuwar komai".

Tace tana kallon fuskan sa mai cike da haiba da zati.

" Mai kika masa haka? nasan ba 'karamin abu bane ya 'bata wa Auwal rai".

"Ina kike? ina zan ganki ? inason sanin ki da sanin mai kikawa my 'kani na?"
numfashi taje tare da d'aura kanta a jikina sa.

Nan itama barci ya kwashe ta.

~~~~~~~~~~~~

Damuwa yayi wa Joy yawa kullum kwana nan duniya baza ido take tana kallon hanyan da
Auwal zai dawo, tunanin ya zame mata jiki, kuka ko shine abinci ta a halin yanzu,
tun maman na lallashi har ta kai ga yanzu ta zuba mata ido, makaranta kuwa yanzu ta
sauke sa saboda bata son Auwal ya dawo bata.

Yadda take son mai da kanta da rayuwar ta na matu'kar damun 'kawar ta da mahaifiyar
ta.

Kuma saboda zurfi ciki har yau kusan satin Auwal d'aya da kwana biyu Aisha bata san
meke damun 'kawar taba.

Tayi tayi ta sanar mata ta'ki , tayi fushi akan haka har takai ga ta sakko domin
tasan waye 'kawar ta akan zurfin ciki.
Kwance take da wurin 'karfe 11:00pm idon ta kuri kamar kowacce dare tun bayan barin
Auwal garin.

Tana abinda ta saba wato kuka.

"Shin yanzu idan kabar ni ina zan sa raina?, yaushe zaka dawo? ji yadda na rame
dama ba akauki ne dani ba. Tunani da fargana bazaka dawo ba yana mugun d'agamin
hankali, yanzu ne nagane irin tsanani son da nake maka, inaga kuma shine ajalina
mudin baka dawo gare niba . ka aminta dani don Allah shine burina . Kada kabarni
doctor kada ka gujeni kasoni kada ka'kini".

" Idan kabar ni bansan inda zansa raina ba, yaushe zaka zo gare ni kace ina soki
Joy? " tace tana 'kan'kame filo tare da fashewa da kuka.

Kuna ta tambaya to gashi na daur nayi, yadda na faran ta muku inason nima Ku sani
farin ciki.

Comments d'in Ku shine 'kwarin guwar mu mu writer's.

Sai naji Ku, idan ba haka ba kuji shiru.


[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*My fan's godiya marar adadi, Allah bar 'kauna*

*Dedicated to Heart beat🥰*


*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

2⃣5⃣2⃣6⃣
2⃣5⃣2⃣6⃣
to2⃣6⃣
2⃣5⃣

Auwal ya riga RAHAMA tashi, jin motsin sane yasa ta farka tare da d'aga sa, kallon
sa tayi shima ita yake kallon bayan ya tashi a jikin ta, murmushi ta sakin masa
shima ya mayar mata.

"Anty kema barcin kikayi?, eh d'an 'kanina" tace tana jan mai kuma tu.

"Har kun tashi?" a tare suka wai ga, mami ce ke tambayan su, "eh mami munsha barci,
ko ban ninyan barcin ba ga wanda ya sani nan" cewan RAHAMA tana kai masa dungurin
wasa.

Dariya mami tayi tare da cewa "ai kun saba dama ba yau bane farko, maza tashi kije
sashin ku tun d'azu mijin ki ke mana safa da marwa".

Turo baki tayi tare da cewa " kai amma gaskiya Salisu nada neman magana, meye kuma
na sintiri?, toni gaskiya ina tare da 'kanina ban gaji da ganin sa ba".

"Banson shashanci maza tashi kije" ba don taso ba ta mi'ke tare da kama hannu
Auwal.

Kallon ta mami tayi tare da cewa "ina zaki kuma dashi?" .

"'Bangaren mu mana" janye hannu sa yayi tare da cewa "Anty ni bazani ba gaskiya,
saboda mai?".

"Kawai" yace da ita tare da koma wa gadon 'yan matamcin ta ya kwanta tare da lumshe
ido.

Kallon sa tayi tare da cewa tana mai maida idon ta kan mami "mami kice masa ya
tashi muje, yaje ina? ina tunda kika dawo kuke tare? maza bar nan banson
shashanci".

Fita tayi ba don ranta yaso ba, tana fita mami ta nufo wurin d'an nata.

Zama tayi gefen gadon tare da cewa " meye damuwar ka yaro na?" shiru yayi kamar mai
barci amma tasani sarai ba barcin yake ba.

"Da kai fa nake kanaji na ina magana kai banza dani" bud'e idanun sa da sukai masa
yaji-yaji saboda hawayen dake cikin sa.

Sunyi ja jazur dasu yana kallon ta dasu "lafia Auwal?" tace tana mai d'ago sa.

Bai shiryawa zuban hawaye ba kawai sai gashi sun zubo masa.

"Mami na" yace cikin in ina, "ya akayi ne d'an mami ? fad'a kada kai shiru zaka
samu sau'ki kaji?".

" Mami inason ta ina 'kinta, mami ki nake kamar zan mutu na kuma manta da ita, amma
zancen Anty yasa na tuno ta, don barcin nan da nai har mafarkin ta nai".

"Mami zan koma gobe" daga haka yayi shiru yana mai dafe 'kirjin sa yarasa taka mai
man maike damun sa.

"Auwal ban gane zancen kaba, ban gane inda maganan ka ta dosa ba, mai kake nufi?".

" Fad'a min wacecce kake so, kuma wacecce kake 'ki".

"Duk itace" yace yana mai kallon mamin.

"Fahimtar dani, yaro na ya fara soyayya? kome?".

Ganin ta kafesa da ido yasashi kauda kai tare da sanar mata da labarin komai na
dangane dashi da Joy.

Amma koda yazo zancen fyad'e ya kasa fad'a kuma hakan ya'kara masa zafi a zuciya
fiye dada.

" Yaka tsaya? inajin ka, shikenan ai mami" bai fad'a wa mami cewan ba musulma
bace.

"To meyasa baka fad'a mata ba?" shiru na wasu d'aki'ka yayi sannan yace "yarinya ce
sosai mami shiyyasa ban sanar mata ba".

" Yarinya kamar ya? bata isa aure bane?. tukunna dai mami bata wuce 16 years ba
fah, yanzu haka ina tunanin JS3 take".

"Ai ta isa aure kam, sai dai kace kawai baka son ka auri yarinya, to mai zai hana a
d'aura aure ta ta dawo nan da zama? idan yaso daga baya sai ayi biki bayan ta gama
secondary d'in ta".

Turo baki yayi tare da cewa " kai mami to meye ma'anar haka? baki tunanin ta'ki
maida hankali a karatun ta?".

"Kuma mani a'a sai ta girma, don bazan bari ayi taje kuma.....kawai.......umm ni
dai a'a kawai".

" Shikenan tunda hakan yafi maka, amma shawara ta ka sanar mata tunda wuri ".

" Humm" yace kawai tashi tayi ta fita ta barsa, shi kuma kwanciya yayi yana tunani.

°°°°°°°°°°

Washe gari samakon tashi Auwal yayi, da shirin sa tsaf na tafiya ya fito, lokacin
da ya fito babu wanda ya fito sai masu aiki dake kara kanya.

Don duka daga sallan asuba kowa ya koma barci amma banda shi.

'Dakin mami ya nufa duk da yasan ba lalai ya same ta irin wannan lokacin a d'aki
ba.

Koda ya shiga babu kowa a ciki, kiran layin ta yayi sai da yakira yafi a 'kirga
kuma yana ringing ba'a d'aga ba.

Ganin time na tafiya yasa ya zari key d'in motar sa da kayan sa ya fita a d'akin.

Wurin ma'a danar motocin gidan ya nufa, motar sa ya bud'e tare da jefa kayan sa
yayi ciki.

Tada motar yayi ya bar gidan ba tare da sanin kowa ba sai dai masu aiki tsiraru da
mai gadi suka gansa.

Sai muce Auwal Allah tsare hanya........

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

"Joy ki tashi haka mana, barcin ya isa haka" tashi nayi ina tura baki had'e da
mi'ka.

"Mama Allah kin cuceni ina cikin barci na mai dad'in gaske kin katseni" nace a
cikin zuciya ta.

"Tashi kinji yau bikin Bola, tashi kishirya muje, ba inda zani" nace ina ninyan
koma wa na kwanta.

"Tashi ki karya to, ba yanzu zan karya ba, kinsan ko 'karfe nawa ne yanzu kuwa?".

" Um'um, 12:30pm ne yanzu, maza tashi ki karya saiki wanka ki kwanta ni Narasa wani
tsiya kika tsiro yanzu, da dare baza'a barci ba sai safe yayi akama barci".

"Kibarni please mama ki tafi abunki" nace tare da gyara kwanciya na.

Girgiza kai kawai tayi tare da cewa "sai na dawo, ah" nace ko wai gawa banyi ba.

------------------------

11:00am yayi wa Auwal a 'kofar gidan sa na 'YAR KADDE, parking yayi a jikin gidan
fito wa yayi a motan tare da rufewa bayan ya ciro kayan sa.

Bud'e gidan sa yayi ya shiga tare da tura 'kofar yayi ciki, kallon gidan yake duk
yayi datti.

Bud'e 'kofar shiga d'akin yayi jefa jakar kayan sa yayi tare da tu'bewa ya fara
gyara gidan.

Tsaf ya gyara ko'ina gida ya fito shar dashi, lallai yaron mami yayi 'ko'kari.

Bayan ya kamala gyaran gidan yayi wanka, shiryawa yayi cikin 'kananun kaya , kayan
sun kar'besa sosai, a lokacin ne yaji anfara kiran sallan azahar don haka sai yayi
alwallah tare da fita don zuwa masallaci.

Bayan an idah salla ne ya fara tunanin mai zaici, fito wa yayi daga masallacin yayo
gida.

Joy ta fito daga cikin gida da nufin shiga gidan su Aisha sai taga mota a jikin
gidan Auwal.

Kallon motan take kamar shine a ciki, a zahirin gaskiya bata ta'ba ganin mota irin
wannan a cikin 'KAUYEN ba.

Motan ta bala'in d'aukan hankalin ta, zuciyar ta na raya mata cewa Auwal d'in ta ya
dawo.

Farin cikin da na dad'e bangani ba a fuskan ta shine kwance har da darinyan ta.

Ji take kamar ta zura da gudu tashiga gidan sa, amma ina a wanan lokaci ne
miskilancin ta ya tashi, tsaye kawai tayi tana kallon gidan.

Tana tsaye Auwal ya dawo, tun daga nesa ya hango ta, tafiya yake kawai amma idanun
sa ita yake kallo.

Murmushi ya saki lokacin da ya 'kariso, idon sune ya sar'ke ana juna.

Kallon junansu suke na tsahon wani lokaci, Joy ne ta fara jenye nata tare da juyawa
gida.

Dariya ya fashe dashi kuma tajisa sarai tai shige wanta, "'yar rainin wayo kawai,
sai da tagama kalle kyakkyawan mami tsaf kamar ta lashe, kuma hakan take marmari
nagano tsaf, wai ita miskila ta wani juya fuw tayi gida".

" Dawo ki cigaba da kallon abinki " yace yana murmushi tare da shige wa nasa gidan
yana girgiza kai "hmm, yarinya kenan wai ita aji, bari ya tsinke muga sai inga ta
tsiya".

Yace dai-dai da iso warsa farfadan gidan, zama yayi a fararen kujerun sa dake gefe
a tsare a gidan.

Yamitsa fuska yayi tare da cewa " ta rame wallahi, ta rame sosai Allah sa dai ba
ciwon cikin bane, ko......." sai yayi shiru yana nazari.

Murmushi yayi tare da cewa "kai so ba'ine, so masifa ne, yunwa fa nakeji amma
sakamakon ganin masoyiya ya tafi. Hmmm"

•••••••••••

Dariya nima nayi lokacin da na dawo cikin d'aki, don sai lokacin tazo "jishi kamar
aljani saboda kyau, Allah yayi wa Auwal kyau tamakar shi yayi kansa".

" Allah sa ya dawo ne yace yana sona, wuw da nayi farin ciki mai tsanani ".

Kwanciya ta nayi tare da lumshe idanuwa na.....

Share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*Dedicated to my lvly fan's*


*Musamman*
*MY besty (maman Muhammad)*
*Bilqess*
*Maman Aliu*
*Fauxy*
*Fulani Gal*
*Maman Inteesar*
*Jidda h garba*
Da dai sauran su ina tsanani 'kaunar Ku fan's , much luv sisters iya wuya ana
tare🤝🏻🤝🏻

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

2⃣7⃣2⃣8⃣
2⃣7⃣2⃣8⃣
to2⃣8⃣
2⃣7⃣

6:10pm na sake rangad'a wankana na zauna na tsantsara 'kwalliya na, nayi masifar
kyau, kamar a sace a gudu, ina zaune a far fada, ina duba notebook d'ina. Sai ga
mama ta shigo tunda na d'aga kai na naga ita ce na mai da kai na a littafi na, na
cigaba da nazari.

Ban sake d'ago wa ba sai da naji tace "shigo mana doctor", sa'an nan na d'ago gaba
na na fad'i na jin ankira rayuwa ta.

Shigo wa yayi muka had'a ido dashi, hannu sa ri'ke da kaya, idon sa na kai na yace
" a ina za'a aje?" mama tace "bani nan yaron kirki na aje".

Murmushi yayi mai 'kaya tarwa tare da cewa " nu namin kawai na aje" yace yana mai
kauda fuskan shi daga kallon na.

Murmushi gefen baki nayi tare da cewa "sannu da dawo wa mama".

" Yauwa Joy sannu da gida", ban ansa ba ina kallon sa tage fen ido mama ta nuna
masa inda muke aje kayan abincin mu ya aje.

"Sannu kaji? nagode fa, bari na kawo maka ruwa kasha, ko Joy kawo masa bari na duba
cincin mu ya rage sai na bashi yau ya dawo yace, gashi bamu dafa abinci ba sai ya
faraci kafin na d'aura yanzu".

Kamar ba dani take ba, ko motsi banyi ba, don kamar maye haka ya kafeni da ido.

" Joy ba magana nake ba" mi'kewa nayi ba don naso ba nayi kitchen.

Cup mai kyau na d'ako tare da d'ebo ruwan randa na fito.

Ina zuwa na aje a gaban sa na wuce, lokacin ne mama ta fito da ba'kin leda a hannu
ta.

"Joy ansa ki sayo masa zo'bo mai sanyi ya rage yunwa kafin na dafa abinci"

Kar'ba nayi tare da nufan hanya, shi kuma ta mi'ka masa cincin d'in. Ransa idan
yayi ba'ki ya 'baci, babban matsalan shi da Joy kenan shigan banza.

Kuma shine sulan 'kwad'ayin wasu, ko yau da dama-dama.

Bin bayan ta yayi mama tace "kabari ta kawo yanzu zata dawo".

Murmushi ya'ke yayi tare da cewa " idan ta dawo na kar'ba" don Allah Allah yake
yaje ya han ta tafiya.

"Auwal kenan kai wai har yanzu baka saki jiki damu ba, jeka to" murmushi ya sakeyi
tare da rufa mata baya.

Koda ya fito da yake ba sauri gare taba ya tarar da ita tana gaf da gidan zo'bon,
domin daga gidan su, gida uku ne sai na masu zo'bon.

"Joy" ya 'kwala mata kira, wai gowa tayi don jin muryan sa, fuska d'aure ya kauda
kansa ganin ta juyo.

Tsaye take daga inda take tana kallon sa, ita ba tai gaba ba, ita ba tai baya ba.

Ido kawai ta zuba masa, jin shiru bata dawo ba kuma tasan sa rai kiran ta na nufin
ta dawo ne .

Sai ya wai go don ganin tsayuwan da take kuma gashi gaba da gidan da take tsaye
majalisan maza ne.

Wani sa'in harda d'an iskan saurayin ta (Isah), ya tofar da yamu tare da tsaki.

Kallon sa kawai take, ganin zai waigo yasa na kauda kai na tare da d'aga kai don
cigaba da tafiya.

Cikin jin haushi yace "dawo bansha" yadda zataji, "to ai bakai ka aikeni ba bare ka
hanani tafiya" nace a zuciya ta tare da cigaba da tafiya ta bako wai waye.

Cije le'be yayi tare da girgiza kai, ransa ba'kin 'kirin, yana hangen yadda samarin
'kyauye suka kafe ta da ido.

Wani har da hanci wurin kallon.

Shige wa gida yayi don ba'kin ciki tare da buga 'kofa garau.

Zama yayi a fararen kujerun sa na far fada, tare da jingina ya rintse ido, tuno
ranan da yayi mummunan ganin yayi.
Dafe zuciyar sa yayi saboda yadda take mugun bugawa.

•••••••••••••

"Mama gashi" cewar Joy a bakin kitchen, waigo wa mama tayi tare da cewa "baki gansa
waje ba?, uhum" kawai nace.

"To taimaka ki mi'ka masa a gida, nasan yana nan".

" To" nace tare da fita gidan, koda naje 'kofar gidan nasa na dad'e ina tunanin
yadda zan shiga.

Kudum bala nayi na daure na tura 'kofar gaba na na fad'i.

Shiga nayi na gansa zaune idanun sa a rufe, jin motsin tafiya yasa ya bud'e idanun
sa dasu kai jajazur dasu.

Ganin itane yasa ya maida ido ya rufe, zuwa gaban sa nayi na aje zan juya ba tare
da nace dashi komai ba.

Yace "d'auki" kallon sa nayi still idon sa na rufe, juyawa nayi don tafiya ta.

"Nace ki d'auka ko?" cikin tsawa, niko taurin kai sai nai kamar banji sa ba nasa
kai.

Banyi taku uku ba naji an ri'ko hannu na, waigo wa nayi ya wurgamin wata
matsiyaciyan harara tare da sakin min hannu nawa, yayi min nuni da zo'bon da na
aje.

Tura baki nayi ina cewa "mama tace na kawo ni, amma kafin ki sayo mai na sanar
miki?".

Ya tsina fuska nayi sa'an nan nace kamar mai ciwon baki " gani nayi ai bakai ka
aiken ba" tare da zum'bura baki.

"To sai ki d'auka kisha, don ni banshan 'kazan ta" kallon sa nayi shima ya d'ago
daradaran idanuna sa.

"Eh, yadda kikajin nan" "ummm, hakan yayi" nace tare da matsawa na d'au zo'bon zan
wuce.

"Shanye shi anan " yace fuska a d'aure kamar wanda bai ta'ba dariya ba.

Tsoro ne ya kamani na kafa kai bayan na bud'e goran .

Bige goran yayi ya zube min a jiki, sanyin zo'bon har cikin kaina.

Kallon sa nayi shima ni yake kallo, fuska babu walwala yake "duk ranan da na sake
ganin ki da irin wad'an nan tsuma ko makaman tansu, tabbas rai zai mummunan 'baci".

" Fita min a gida" yace cikin tsawa daya firgitani, da gudu na fita.

"Sai yanzu naji sa'ki a zuciya ta, na fanshe haushi na" yace tare da shige wa
d'aki, alwallah ya gaba tar don anfara kiran sallan magariba, ya fito don tafiya
massalaci.
•••••••••••••

"Mugu kawai" nace lokacin da na shigo gida, "kada wa Joy?" cewar mama daga kitchen.

"Ba kowa" nace tare da nufan d'aki ina jin ta tana cewa "kin zama mahaukaciya ba ai
dole" bance komai ba na bud'e gana mazgo na don canza kayan jikina.

Kallon kayan nayi ina tunanin maganan sa, don gaskiya na tsora ta sosai.

Ganin haka bai min ba na zazzage kayan ciki kaf a tsakar d'akin.

Da 'kar na samu wani dogon riga mai gajeran hannu ya wuce guwa nasa ina mai cewa
"ka nunan kayan da zam saka tunda kasayo min" ina mai murgud'a baki kamar yana gaba
na.

°°°°°°°°°°°°

Shiru- shiru har 9:30pm mama bata gansa ba, don haka tace "tashi ki kaima doctor
abincin nan".

Zabura nayi tare da cewa " Allah mama bazani ba, doctor d'in nan fiti nan nene"
zata sake magana sai ga Aisha ta shigo.

"Yauwa tunda ban isa da d'ayan ba nasan wannan baza ta'ki ba" ya tsina hanci nayi
tare da ta'be baki.

Dariya Aisha tayi tare da cewa "waya ta'ba min besty? eyeh? mai mukayi ne mama" duk
cikin tsokaana tayi.

Hararan ta nayi tare da gyara kwanciya ta.

"Uhum mama bani sa'kon mai zan miki kiga cika aiki yanzu tunda wata bata son
albarka".

Tsaki nayi mama tace " ma'kocin ku likitan nan zaki mi'kawa abinci".

"Aiko yanzu na barsa waje yana shan iska, yauwa kai mai" mama tace tana mi'ka mata.

'Kar'ba tayi ta fita, bata jima ba ta dawo ko nace suka shigo tare hannu ta d'auke
da kwanon abinci.

Waiga dukan mu mukayi kallon d'aya na masa na d'auke kai da sauri saboda hararan da
yayi min.

Duk da dare ne akwai farin wata kamar rana.

Turo baki nayi, "Auwal ya haka?" lokacin da Aisha ta aje abincin.

Murmushi yayi tare da cewa "nagode mama naci abinci ko?" yace yana zama kusa dani
kad'an.

Cikin 'kasa da murya yadda babu wanda zaiji yace "bakijin magana ko?" kallon su
mama nayi naga hakalin ta naga abincin da aka aje Aisha cema naga tana kallo na.

"Bani da wasu sai irin su" nace a hankali, zaiyi magana mama tace "yanzu ka
kyauta?, haka mukayi da kai?".

" Ayi ha'kuri gobe zanci" yace yana murmushi kad'an, "to nayi".

Fira suka d'an ta'ba da mama ya tashi yayi mata sai da safe ya fita, ba tare da ya
kalleni ko ya sake kulani ba.

Kamar ma baiji mai nace ba..

Washe gari ina cikin barci safen da na saba, naji muryan sa yana ce da mama " mama
yanzu naga waccen yarinyan da suke tafiya makaranta da Joy ta tafi, nace lafia bata
tafi ba, ko ta riga ta gaba ne?".

"Wai Joy ai tayi kwana biyu bata zuwa, nayi nayi ta'ki, kuma ko jiya bayan kafita
maganan makaranta yarinyan tazo mata, amma fir tace baza taba, ko naji tana ce da
ita next week zata".

" To mai yasa?, oho gata can bata da sana'a kullum sai barci, don ko church yanzu
taba tafiya, nai magana har bakina yayi tsini amma ta'ki haka ma zuba mata ido".

Inajin su sukai ta magana, har takai ga yace mama ta tasoni, zuwa ko tayi tashi na
d'in nayi kamar ina barci.

Kiran suna na ta fara, da yake ban cika nauyin barci ba da safe, nafi barci harda
minshari da dare, don saboda tsaban barci kana iya saceni ka gudu.

Tayi kira yakai uku na'ki ko motsi, sai ta fara jijjigani amma ko didim.

Auwal na tsaye yanaji gashi ya tsaida Aisha a waje .

Don haka sai ya shigo d'akin kawai yana cewa "mama bani ruwan sanyi kawai" bata
musa ba kuwa tace "to tare da shiga bangi da don d'ako masa.

Bata jima ba ta kawo, jin tace " gashi" yasa na mi'ke a zabure, ina zare ido fuska
ta a had'e.

Dariya mama tayi tare da cewa "dama ai nasan kinaji na, dakin cigaba da 'kaliya ai
dakin ga aiki".

Turo baki nayi tare da zuro 'kafafuna a 'kasa, shiko kamar wani ubana yana wani
kauda kai ya had'e rai yace " tashi kisa uniform mu tafi" kallon sa nayi tare da
hararan sa.

Zuwa can nace "ai nayi latti , sai kuma gobe".

" Baki isaba tashi kisaka uniform nace" "uhum banyi wanka bani, ba'a bu'kata wuce
ni kina 'batan lokaci" yace tare da barin d'akin.

Yana daga waje yace "ina jira minti biyar na baki, kika wuce rai ya 'baci".

" Kiji fa mam, sai kace wani ubana, to wai meye ruwan shi dani".

Bugen baki mama tayi tare da cewa "karki shirya ki tsaya yau naga duka" daga haka
ta fita itama.........
Comment & share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*Dedicated to Safiyya A W fan's club, kuna bani nishad'i godiya mai tarin yawa*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

2⃣9⃣3⃣0⃣
2⃣9⃣3⃣0⃣
to3⃣0⃣
2⃣9⃣

Bayi na shiga, wanka ta nayi sannan na fito, koda na fito ganin kayan makaranta na
da school bag d'ina a gefen katifa da kayan shafa, nasan duk aikin mama ne.

Janyo kayan shafan nayi ina hararan uniform d'in kamar shine ya min laifi, shafa
mai nayi kawai na d'au kayan na saka, fuka babu komai na fito, tunda na fito ya
kafeni da ido.

Kauda kaina nayi daga gare sa tare da tsaki a zuciya ta, nufan hanya fita nayi ba
tare da na kula mama koshi ba.

"Baki sallame taba", kamar ba dani yake ba na 'kara gaba.

Girgiza kai kawai yayi mama tayi murmushi tare da cewa " nagode yaro na, ubangiji
ya taimake ka" "ameen" yace tare da bin bayan na.

Ina fito wa naga Aisha tsaye, muna had'a ido na d'auke kai na.
Cikin masifa ta nufo ni, tana cewa "ai da baki fito ba, da ya barki, kinje kin
shanya mutane, kuma muje yau sai kinsha duka biyu, gana rashin zuwa gana latti".

Kamar ba dani take ba na nufi hanya, lokacin ne ya fito motar sa ya bud'e, yana mai
cewa Aisha " shiga muje na kai ku" da farin ciki ta nufi motan.

Ina jin su ban ko waigo ba, tana shiga ya tada motan.

Ya fara tafiya a hankali, don garin namu hawa da sauka ne, ga wasu shegun duwatsu,
har da uban ramu ka, gomnati ta'ki kawo tallafi. Koda yazo dai-dai inda nake sai ya
tsaya ba tare da yayi magana ba.

Ganin haka na bud'e bayan motan na shiga tunda Aisha na gaba.

Ajiyan zuciya ya saki tare da lumshe idanun sa na wani lokaci, kafin ya nisa ya
bud'e a hankali ya sauke su akan fuska ta.

Ta madubin motan, wani irin nishad'i naji yana tsarga 'kashi da 'bargo na, shima ta
'barayin sa hakan ne.

Aisha ko washe baki take ta shiga motan da bata ta'ba shiga ba.

Fara tafiya yayi, a hankali yake tu'kin mota shiru kamar kurmaye, sai aukin kallo
kamar zai cinyeni.

A haka har muka fito bakin titin shiga cikin gari, yana ganin sa a kwanlta yace
yana mai kallon gefen da Aisha take "inane hanyan makaranta?" .

"Nan hanyan zaka bi" ta nuna masa gefen dama, daga nan ne ya fara tu'ki cikin
kwarewa, da taimakon Aisha ya kawo mu makaranta .

Yana parking muka fita, kiran Aisha yayi don yaga sai faman had'e rai nake tunda
muka fito.

Dawo wa tayi tare da le'ka kanta ta gilas d'in motan, kud'i ya mi'ka mata yace
"kuyi break" godiya tayi masa sa'anan ta biyo bayan na da nake ta tafiya ta ba
tare da na jira ta kona waigo ba.

Yana kallon na har na shiga class sa'anan ya bar wurin cike da tsanani 'kauna ta.

"Wai besty yau Allah ya d'aga mu, kuma Allah ya cece mu, da yanzu muna can hanya
muna cin kwakwa, amma gaskiya yana da kirki, kalli kud'in da ya bamu, da har inajin
haushin tsaida ni da yayi", kallo d'aya nayi na d'auke kai na, " ga naki, banso"
nace.

" Kai amma guy d'in nan ya had'u, idanun sa farare 'kar dasu, gashin giran sa masu
tsanani kyau da tsari, inama inama besty ohhhhhh Allah na" tace tana rugune hannun
ta a 'kirjin ta

Esha ke cewa bayan mun zauna, zancen ta na sufan tamin habibi yayi ba'in 'bata min
rai amma ban nuna ba nabar abin a raina yana cin raina, bamu dad'e da zuwa ba aka
fara tsaron latt, malami ya shigo muka fara karatu.

****************

Muna fito wa daga cikin makaranta muna tafe Aisha sai zuba take ita d'aya kamar
kad'anya .

Bamu lura dashi ba sam, sai jinsa nayi dai-dai saitin kunni na yace "ku nake jira"
cikin daddad'an muryan sa.

Bugawa zuciya ta tayi, na d'an juya kad'an na gansa gab dani, yana cikin kyakkyawan
shiga, Aisha dajin muryan sa ta washe baki tare da cewa "sannu da zuwa yaya".

" Kutumar uban can" nace a zuciya ta, murmushi yayi mata tare da cewa "yauwa 'kanwa
ta, kun tashi lafia? ya karatu dai?".

"Lafia qalu, alhamdulillah" "masha Allah, muje ko?" yace yana mai nuna mana inda
motar sa take.

Tare muka jera yana ta gefen hagu na, koda muka zo shiga motan bayan ya bud'e .

Zan shiga baya kamar yadda nazo da farko ya daka tar dani, tsayawa nayi ina kallon
sa har iso gareni.

"'Kanwa ta koma baya" yace da Aisha data hakince a gaba.

"To" tace tare da fita ta koma baya, "shiga" yace yana tsaye tare da kallo na, ban
ce komai ba na shiga ya rufe 'kofar tare da zaga yawa ma zaunin shi na drive ya
shiga muka d'au hanya.

Kamar tafiyan farko haka mukayi wannan ma.

Bai tsaya a ko ina ba sai 'kofar gidan mu, bud'e 'kofar motan mukayi a tare kowa ya
fita.

Aisha na cewa "mungode yaya, Allah ya saka", " ameen" yace yana murmushi idon sa na
kaina da nake ninyan shiga gida ba tare da na waigo ba.
"Tsaya 'kanwata ki kar'ba" bud'e but d'in motan yayi tare da ciro ledan shopping ya
mi'ka mata.

Godiya tayi tana kallon sa cike da sha'awa a zuciyar ta tana raya "ashe yana da
kirki?" tayi gida tana waigen sa.

Shiru yayi bayan shige wansu yana sosa kai da key d'in hannun sa.

Kallon kayan dake dam motar yayi, yana na zarin yadda zai kwashe su.

Ganin babu mafita yasa ya fara fidda kayan yana ajewa a zauren gidan, yana cikinyi
'kanin Aisha ya fito, kiran sa yayi tare da mi'ka masa wani leda yace "shiga min
dashi kaji aboki?".

" To" yace ya shiga gidan su Joy dashi ya mara masa baya, Joy ne zaune tsakar gidan
lokacin da ya shigo zaune da d'aurin 'kirji ga bokiti a gaban ta tana ta faman ya
tsina fuska.

"Sannu da dawo wa Anty Joy" Muhusin yace, d'ago da kai tayi tana kallon sa tare da
cewa "yauwa yaro kirki".

Aje kayan kusa da ita Auwal yayi shima Muhusin yayi hakan.

Haka Auwal ya kwaso kayan nan tasa tana zaune yana shigo wa dashi ba tace dashi ci
kanka ba.

Duk da taso cewa wani abu, bakin tane yayi nauyi shiyya sa.

Sai da ya shigo dana 'karshe ya sallami Muhusin tare da zama kusa da ita.

Kallon sa tayi da mamaki domin wurin da 'kura amma ba tace komai ba.

Jan nufashi yayi murya can 'kasa yace " Joy" ido kawai ta tsira masa.

"Ina son ki" sai yayi shiru, murmushi ne ya su'buce min a take, kallo na yayi shima
ya saki murmushi tare da kauda kai yace "alhamdulillah, don alamu sunnuna itama
tana son sa".

Cigaba da cewa yayi " ina tsanani 'kaunar ki, kuma ina da kishi mai tsanani akan
ki, ga kaya nan don Allah kirin'ka sawa kibar sa wad'an kike sawa don zuciya ta na
'kuna duk lokacin da nagan ki dasu".
"Duk da nasan addinin mu ba d'aya ba, amma zuciya ta tafi na'am da kayan mu, ki
daure ki saka su".

Juyo wa yayi gaba d'aya yana kallon ta, yace " kina sona?" babu kunya na d'aga masa
kai ina murmushi.

Farin ciki na ya'ki 'boyu, kallon na yake cike da 'kauna .

"Har da irin wannan zaman a dai na please" yace yana nuna d'aurin 'kiri dake jikin
ta.

Rufe fuska tayi tare da cewa "wanka zanyi shiyya sa" a hankali.

"Zaman me kike to baki shiga bayin ba?" shagwa'be fuska tayi tare da cewa "na gaji
ne shiyya sa" dariya yayi tare da mamakin ta.

Kafeshi da ido tayi kamar zata lasheshi, "kallon fa?" yace yana mai gintse dariyan
sa .

"Kafi kyau idan kana dariya, Allah ko?" yace yana 'kale mata ido d'aya.

Kallon a gogon hannun sa yayi tare da cewa "muje na miki ankusa kiran sallah" zaro
ido tayi tare da cewa "a'a, na yafe, hmmm, shikenan ai aukau lokacin da ko kince
bazan bari ba. Mama fah?, tana barci" tace tana kallon cikin idanu wansa.

"Ta kyau ta, ki dai na kallo na haka idan ba haka ba akwai babban matsala" dariya
nayi tare da cewa "tom, bari naje nayi wankan Allah har da yunwa nakeji, nima haka"
yace yana shafo cikin sa.

Cikin tausayawa tace "bari na kawo maka kaci" tace tana mi'kewa, yamu ya had'iye
kut tare da kauda kai da sauri.

Bata 'bata lokaci ba ta dawo hannun ta d'auke da tire, dire wa tayi a gaban sa tare
da zama.

Bud'e kwanon tayi, shinkafa ne da miya, gaskiya bazai iya cin wannan shinka fan ba.

Don haka sai yace "kici kawai bari naje masallaci" 'bata fuska tayi ba shiri ya
fasa mi'kewa.

Tura masa kwanon tayi gaban sa, kallon ta yayi ta masa nuni da yaci.

"Bani to" yace yana bud'e baki, kallon tsabtataccen bakin sa tayi, yayi matu'kar
burge ta.
Babu damuwan komai ta saka cokali ta d'ebo ta nufi bakin sa dashi.

Ta bashi kusan sau biyar aka kira salla, don haka ya dakatar da ita.

"Maza kiyi wanka kafin na dawo mu cigaba da fita" yace yana gab da fita.

"Oho har da abinci kici kinji?" d'aga kai nayi ina mai jefan sa murmushi, shima ya
mayar mini.

Comment & share pls


[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*Tell my mistake to me, not to others. Because my mistakes are to be corrected by


me, not by others.*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

3⃣1⃣3⃣2⃣
3⃣1⃣3⃣2⃣
to3⃣2⃣
3⃣1⃣

Bayan fitan sa na kwashe kayan da ya sayo min na kai d'aki na aje na fito, dawo wa
nayi inda na tshi na zauna, wani irin farin ciki naji yana mamayeni, kasa tashi
nayi daga wurin har na tsawon wani lokaci, ina nan zaune sai faman murmushi nake
Aisha ta shigo, kallo na take tunda ta shigo, nayi nisa bansan ta shigo ba.
"Besty! Besty!! Besty!!!" sau uku duk banji taba, gashi sai faman murmushi nake ina
karkad'a kai.

Jin kiran sunana da tai tayi shine ya farkar da mama, fito wa tayi tana cewa "kun
dawo yaushe Aisha?" .

"Tun d'azu, mama anya 'kwa'kwalwar besty lafia yake kuwa?" dariya mama tayi kad'an
tare da cewa "mai kika gani?".

" Matso kiga mama, wallahi tunda na shigo take a haka, kuma nakira sunan ta bata
san inayi ba".

"Joy" mama ta kira ta da 'karfi, firgit na dawo daga duniya ta nida hubby na,
kallon Aisha nayi dake gaba na.

Murmushi da tunda nake da ita bata ta'ba ganin nayi wa wani ba bare ita taga na
mata.

"Besty wannan fara'an fah? da murmushi fah?" rungume ta nayi ina ta faman sakin
murmushi.

"Shafa min mana besty mai muka samu bayan dawo war mu?".

" Am very happy today my 'kawa" nace ina kallon ta, itama ni take kallo fuska ta
d'auke da murmushi.

"Really?" d'aga mata kai nayi tare da sake rungume ta, mama na tsaye tana ganin
ikon Allah.

"Burina, farin ciki na, rauwata, anashuwa na, walwala na" sai nayi shiru.

"Uhum, ina sauraron ki fad'a min na tayaki murna sosai" cewar Aisha.
Lumshe ido nayi na bud'e su, basu sauka a ko ina ba sai a kan kyakkyawan fuskan sa
da shigo wansa kenan, ya dawo daga masallaci ko gida bai shiga ba yazo yaga ko tayi
wanka taci abinci.

'Kayataccen murmushi na masa, 'bata fuska yayi tare da harara na.

Fuuu naji gaba na ya fad'i, ido na zuba masa shiko ya d'auke kai.

"Shigo mana doctor" cewar mama, murmushi yayi mata tare da 'kari sowa ciki yana
cewa "sannu da gida mama, nazo kina ta barci".

" Hmmm, kai dai bari wallahi jin jikina nayi duk a gajiye bayan na gama girki
shiyasa na kwanta na huta har basan su Joy sun dawo ba " tace .

Kallon sa nake har yazo ya wuceni ko kallo na baiyi ba.

Shagwa'be fuska nayi tare da shashsha'ka, kamar zanyi kuka.

"Lafia ke kuma?" cewar mama, "ai ba lafia yau mama inaga sai yaya na ya duba ta
dai, jifa yanzu take fara'a da farin ciki, amma lokaci d'aya ta canja" cewar Aisha.

Hararan ta nayi tare da turo baki ina waigo wa, had'a ido mukayi ya kauda kai.

Cikin shagwa'ba nace "bashi bane" nace ina le'ka fuskan sa da ya juya dashi gefe.

"Wake nan?" inji mama, jin haka yasa ya waigo mi'kewa nayi tare da cewa "ba gashi a
gaban ki nan ba".

Zaro fararen idanuwan sa yayi yana kallo na, murmushi na sakin masa tare da 'kale
ido nayi cikin d'aki.

" Ban son sharri daga shigo war sa, zaki wani 'bata rai kice shi" cewar mama "aiko
dai, mai yaya na zai miki? muna zaune muna gani ya shigo ko kallon ki baiyi ba,
dama besty kin iya sharri ban sani ba?".
Jin bai ce komai ba yasa na fito, tsayawa nayi akan sa, lokacin mama ta nufi
kitchen, kallon sa nayi tare da cewa " ka rantse baka kalleni ba daka shigo, kuma
ka rantse sharri nake maka baka min komai ba ".

Kamar ba dashi nake ba yayi banza dani, bubbuga 'kafa na farayi a 'kasa da fara
shashsha'ka.

Kallo na yayi tare da mi'kewa yace a hankali yadda Aisha baza taji ba " wallahi
nafi ki iya rashin kunya, a gaban mama kikewa saurayi shagwa'ba?, to Allah zan
kunya taki".

Turo baki nayi tare da cewa "to bakai kaja ba to" "niko?" yace yana matsowa kusa
dani.

"Uhum, lallai wannan shine a dake ka a hanaka kuka, mai nace miki fisabilillahi
kafin na tafi masallaci?".

" Wanak da cin abinci" nace ina turo baki, kallon bakin yayi tare da runtse ido
had'e da cije le'be.

Yace cikin wani yanayi "to mai yasa baki ba?" far nayi da ido, wanda saura kad'an
ya fad'i yayi maza ya dafa bango tare da cewa a cikin zuciyar sa "yarinyan nan zata
kashe ni idan banyi wasa ba".

Matsowa nayi gaban sa, dai-dai nan mama ta fito hannun ta ri'ke da abinci.

Ganin zan ta'ba sa yayi maza ya kauce, ban ha'kura ba na sake matsoshi ina mai cewa
cikin damuwan da na shiga take ganin zai fad'i "maike damun ka?".

Kafin ya bani ansa mama tace " wani abu ya same shi ne?" tana mai aje abinci a kusa
da kujeran da ya tashi.

Turo baki nayi cike da shagwa'ba zanyi magana yayi saurin cewa "ba komai mama".

Wani irin kallo na masa, yayi saurin d'auke kai a zuciyar sa yana cewa "bazan iya
kasance wa kusa dake ba, musamman idan mu kad'ai ne, idan ba haka ba sai nayi
sa'bon Allah, yanzu dama haka yarinyan nan take kana ganin ta shiru-shiru?".
" Ga abinci ka doctor " murmushi yayi tare da cewa "naci ai mama d'azu kina barci".

" Kai my.............." da sauri ya kallo ni, gar gad'i yayi min, Allah saura
kad'an nayi dariya na gintse, ko meye tsoron sa oho.

Don haka na murmusa tare da cewa "mama ina sabulu wanka yake? na duba kwando bashi
inda kike ajewa kuma ban gani ba".

Kafin ta bani ansa sai da tace da doctor " ka 'kara to" bai son mata gaddama yace
"to" tare da bismillah ya fara ci.

"Wai wanka zakiyi ne?" cewar Aisha, "uhum" nace da ita ido na nakan doctor da
yafara cin abinci.

"Kafin ki shiga bani littafin Husna da kika ara zan duba wani abu, to" nace da ita
tare da shiga d'aki na d'ako na bata.

"Yauwa bari naje kiga, mama sai anjima, yaya sai anjima" tare suka ansa shida mama.

Ido na nakan doctor da ya d'ago yana kallo na yana min magana da ido, wai naje nai
wanka nazo muci.

Tura baki nayi tare da cewa "mama sabulun" "sabulun nan sai dai kisiyo" tace tana
shiga d'aki.

Kafin ta d'ako kud'in na zana kusa dashi har guwana na ta'ba nasa, da yake mama ta
shinfid'a masa tabar ma.

Runtse ido yayi tare da cewa "meye haka?, mai nayi" nace ina dube dube.

"Ansa kisiyo" na kar'bi kud'in tare da mi'kewa, tara tafiya nayi bai ninyan magana
ba yace "amm......." sai kuma yayi shiru, waigo wa nayi tare da cewa "kana magana
ne? duba kayan nan akwai" daga haka ya gintse bakin sa.
Yana mamakin ta sosai, yace a zuciyar sa "yanzu ba don nace ba da haka zata fita
duk mazan garin nan su gama gane min ita" tsaki yayi tare da cewa "musulunci yayi
gaskiya".

Kallon mu mama tayi duka, tana mamakin sauyin da ta gani a tare damu duka, amma
taje baki tayi shiru.

'Daki naje na bud'e kayan d'aya bayan d'aya ina mamaki da alajabi, har naga wanda
sabulun wankan yake ciki.

Wani irin sonsa da 'kaunar sa naji ya 'kara nunkuwa a zuciya ta.

Gaskiya Auwal ya kashe kud'i, ya narke kud'i kamar bai so.

Cikin sanyin jiki na mai da kayan sannan na mi'ke.

Suna zaune da mama na fito, suna d'an ta'ba fira, ya bar macin abinci.

Kallon sa nayi koya waigo, wuce wa nayi na d'ebi ruwan zanyi bayin tsakar gidan.

"Mama yanzu ruwan sanyi zatayi wanka dashi?" daga ni har mama juyo wa mukayi muna
kallon sa.

Ganin kallon da mama take masa yasa ya kauda kai yanajin kunya.

Murmushi mama tayi tana kallo na, nima kallon ta nayi tare da d'age mata gira ina
murmushi.

Numfasa wa tayi da fara'a a fuskan ta tace "gata nan dai hanata yau 'kila ta bari,
don naga tana ganin ka da gashi".

" Tafi shekaru uku tana wanka da ruwan sanyi" zaro ido yayi yana kallo na, "wuce ki
dafa ruwa sai kiyi wanka" yace yana d'aure fuska.
"Inama da ruwan d'umi a kitchen d'in" cewar mama, ban musa ba na dawo nayi kitchen.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*********************

Washe gari tun da asuba na tashi kai kace sallah zatai nace da ita, kallo na tayi
tare da cewa "sorry Mrs ba addinin mu d'aya ba bare kiyi tunanin haka, saboda son
ganin masoyi na yasa na tashi da wuri, don yau basai antasheni ba" Dariya nayi tare
da cewa "a'a kinji 'kawan kwanta ruwan sanyi na jira" murgud'amin baki tayi tare da
cewa "aniyanki ta biki, don yau na tabbata ko makaranta nace ba zani ba babu abinda
zai min, ban cin karki ce nai rashin kunya da nagaya miki yadda zai tasheni ko ban
tashi ba. Oh da gaske?" d'an kai tayi kawai tare da cigaba da sabgan gaban ta.

Don sai a wannan lokacin ne take bitan abinda aka koya musu a makaranta.

6:30am ta gama wanka tsaf ta shirya, wanda ganin ta shirya yasa mama koma wa barci
bayan ta aje mata break fast.

Koda na gama shirya wa banko tashe taba na fito gidan a bina, tsaye nake a bakin
zauren gidan mu ina kallon yanayin anguwan namu tsit kamar ba mutane.

Ko na abin mamaki bane, idan nai la'akari dako 'karfe nawa ne yanzu.

Murmushi na saki ina kallon gidan su besty da yake a rufe, alaman basu bud'e ba.

Kallon na sahibi nayi naga shima a rufe, ga motar sa a gefe.

Nufan 'kofar gidan nayi, tura wa nayi naga 'kofar ta bud'e, murmushi na saki tare
da shiga ciki.

Komai tsaf kamar yadda yake haka komai na gidan yake a tsabtace a gyare.

Ga inji a kunne daga gefe kanajin karatun Qur'ani na tashi.


Zuwa nayi 'kofar palon, itama a bud'e take, nayi mamaki matu'ka .

"Bai tunani azo a sace masa?" nace a zuciya ta, shiga nayi babu kowa a palon, nufan
bedroom d'in sa nayi, ina zuwa d'aga labule nayi, hango mutum nayi kwance a
lullu'be akan gado.

Girgiza kai nayi tare da aje jaka ta akan sofa na nufi katifan ina dariyan abinda
zan mai.

Ina zuwa nai tsalle na fad'a kansa, "innalillahi" yace tare da fara bud'e idonun
sa, ai bai san sanda ya bud'e suba gaba d'aya yana kallon agogon bangon dake
d'akin.

Mai da idonun sa yayi kai na tare da harara ta, niko na fashe da dariya, muskutawa
yayi tare da cewa "d'aga ni, wai ma meye na zuwa tashi na da sassafen nan?".

Turo baki na nayi dake gaf da nasa ina kallon cikin 'kayan idanuna sa, nace "
makaranta zaka kaini".

Kauda fuskan sa yayi don yaga kamar tana ninyan had'e bakin su yace "makaranta ne
da uwar safen nan?, uhum, gari fa ko gama haske baiyi ba, ba ina ganin yadda kuke
tafiya ba?".

" To naji, nazo na ganka ne" "hmmm, d'agani tom" 'kin d'aga san nayi, don haka sai
ya fido hannun sa daga cikin abin rufan yace cikin lallashi "d'aga ni Queen d'ina
kinji" ma'ke ka fad'a nayi.

Shiru yayi yana kallon yadda ta had'a fuska, "Allah barci bai isheni ba, jiya kin
kanai nayeni kin hanani moruwa, ko asibiti fa banje ba".

"'Dagani kinji baby na" sauka nayi tare da kwanciya a gefen sa "oh Allah" yace yana
runtse ido.

"Tashi kijirani a Palo yanzu zan fito, a'a muyi barci kawai" nace ina mai d'aura
hannun na a jikin sa.

"Barcin ya tafi kuma ai, jeki yanzu zanzo" ma'ke kafad'a nayi tare da rufe ido
kamar zanyi barci.
Rasa yadda zaiyi yayi, don haka sai shima ya rude ido, domin har ga Allah bai son
kusancin nan nasu haka, don komai na iya faruwa, 'karin dad'i daga shi sai
guntulallen wando.

Jin shiru yasa na d'ago tare da cewa "ka koma barcin ne?, a'a, ai na gaya miki ya
tafi, kije palo kijiran nayi wanka mutafi, kin maci abinci kuwa?".

" A'a, mai yasa to?" yace yana mai bud'e ido, "tare nake son muci".

" To jeki kitchen kima kafin na fito wanka" mi'kewa nayi tare da fita a d'akin.

Ri'ke kai yayi tare da cewa "zan sha aiki" ya mi'ke bayan ya yaye
bargon.................

Comments nake da bu'kata, idan ba haka ba sai bayan sati biyu🥰

Luv you all my fan's❤❤


[11/5, 9:53 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

3⃣3⃣3⃣4⃣
3⃣3⃣3⃣4⃣
3⃣3⃣3⃣4⃣3⃣3⃣
3⃣3⃣➡3⃣4⃣
3⃣4⃣

Jallabiya ya nema ya saka, ya saka kenan ta dawo cikin d'akin kallon ta yayi kamar
yadda itama idon ta ke kan nasa, d'aga kai yayi alaman ya akayi ne, sai da ta
'kariso ciki gab dashi sannan tace "ina kitchen d'in yake?" kallon ta yayi tare da
cewa "kai Habibaty, kitchen d'in ne baki gani ba?, uhm," nace ina kallon sa, don
gaskiya bana gaji da kallon hasken idaniya ta.

"Muje na nuna miki tun kafin ki cinye ni da wad'an nan idanuwan naki" murmushi nayi
ba tare da na bar kallon nasa ba.

"Muje nace, time na tafiya, gashi ko wanka banyi ba, kuma inason na le'ka asibiti
da safen nan".

"To muje" nace ina dawo wa kusa dashi, girgiza kai yayi tare da d'aga 'kafan sa
yafara tafiya, nima na fara.

Yana d'aga 'kafa d'aya nima haka, waiga gefen daman sa da nake yayi yace "wai ni
kakan kine baby?".

" Kamar ya?" gaba yayi ba tare da ya bani ansa ba, ni kuma na bisa, kitchen d'in ya
nuna min zai juya nace "mai za'a dafa maka?".

" Abinda zaki iya ci, don da ganin wannan shafaffen cikin babu komai a cikin sa".

"Hmmm, my heart kenan" kallo na yayi yana mai jin matsanancin farin cikin sunan da
nakira sa dashi.

"Ina son ki" yace yana mai lumshe idanu wan sa, "nima haka" ba tare da na bud'e
baki ba, lab'bana ne kawai suka motsa, kallon su yayi tare da jin wani irin yanayi.

Barin wurin yayi ni kuma nayi cikin kitchen d'in, tunani na fara "shin mai zan
masa?" nai shiru ina nazari.

Ban iya kunna gas ba sai na kuna stove, d'aura ruwan zafi nayi, kafin yayi zafi na
fere doya, yana tausa na juye, soya doya nayi da 'kwai.

Ina gama wa na fito, lokacin shima ya fito a lokacin ya fito 'kamshin shi ya cika
ko ina na palon, ganin kallon da nake masa kamar wa wuya yasa ya saki wani
had'ad'd'an murmushi.

Mayar masa nima nayi tare da nufo sa, cikin shagwa'ba nace lokacin da na iso gaban
sa "gaskiya doctor kamin wayau" zaro ido da ya zama kamar al'adanshi yayi tare da
min magana da ido, "name?".
Turo baki nayi tare da cewa "kasani ma break fast bayan nayi wanka, kana 'kamshi
niko sai wari nake" nace ina shinshina jiki na.

Matsowa gab dani yayi yana murmushi tare da cewa "muji" yana kamo hannu na, tare da
rankwafawa ya kai hancin sa a wuya na, yace "hunnnn, 'kamshi, kinji 'kamshin dakike
kuwa baby?".

Fincike wa nayi don nasan tsokana ta kawai yake, murmushin gefen baki yayi tare da
cewa " da gaske 'kamshi kike, zo na'kara ji".

Bibbiga 'kafa na farayi a 'kasa ina cewa "Allah ban wani 'kamshi ni na sani, kuma
ni wanaka zan sakeyi yanzu na fesa turaren ka".

"Zo HAYATI, zo kinji" banza dashi nayi, shi kuma yana tsoron Allah yana tsoron
abinda Joy za tayi.

Ko kallon sa banyi ba nayi hanyan d'akin sa "oh my god" yace tare da d'aura hannu
aka, niko ina shiga nayi toilet d'in sa, wani irin 'kamshi bayin yake, tu'bewa nayi
na d'aura towel d'in sa, na fito da uniform d'ina a hannu palon na fito.

Jin motsina yayi tunani ko na fasa ne ya d'ago da kai don kallo na.

Da sauri ya kauda kai, murmushi nayi tare da mamakin sa, sai kace yaga wani abun
tsoro.

"Ga uniform d'ina ka ninke min kafin na fito, yadda ba zai ya mutse ba" nace tare
da ajewa kusa dashi.

Bai ce komai ba har nabar wurin, kuma ko sake kallo na baiyi ba.

Wanka na nake cikin nishad'i, da ruwa mai 'kamshi, "nima yau zan zama 'yar gayu"
nace ina sakin murmushi.

Bayan na fito na 'kwala masa kira don ba mirror bansan inda kayan 'kamshin sa suke
ba.

Yanaji ya kasa magana, don yana nan inda ta bar sa, a daskare yake don ko uniform
d'in da tace ya nunke mata baiyi ba.

Sake 'kwala masa kira nayi amma shiru babu ansa, don haka sai na fito tunani na ko
ya fita ne, ina zuwa na gansa zaune inda na bar sa.

Cikin shagwa'ba na nufo sa, banyi wata wata ba na d'ane cinyan sa, d'ago da
runannun idanuwan sa yayi tare da cewa cikin ma wuyacin hali.

Da sanyin murya "please kibar abinda kike, Allah addinin mu yahana haka, haramun ne
abinda muke aika tawa, hakan zai kamu ga aika ta mummunan abu, ki bari kinji".

" Ki adana su zuwa bayan auren mu" yace yana kauda kai, kallon sa nayi da mamaki,
nace "meye abinda nake mara kyau?" shiru yayi bai ce komai ba.

Hannaye na nasa tare da juyo da fuskan sa, ina kallon cikin idon sa nace "meye
laifin abinda nayi?, kaban ansa".

Saka hannu sa yayi tare da zame hannu wana yace " addinin mu ya haramta ke'bance
war mu haka".

'Dage gira nayi tare da girgiza kai "to d'an d'agani please, kije kuma kisa kaya mu
karya zaku makara fah, kalli" yace yana mai nuna min agogo.

Takwasa saura minti goma na gani, mi'kewa nayi tare da cewa "ina ka aje kayan
'kamshin ka?" bai ce komai ba ya mi'ke, d'akin ya nufa nabi bayan sa.

Muna shiga ya mi'ka min wani jaka "gashi, please kiyi sauri muje" yace tare da fita
bayan na ansa.

"My heart d'an kawo min uniform d'in" zuwa yayi bakin 'kofa ba tare da ya d'aga
labulen d'akin ba .

Yace "gashi" turo hannu sa kawai yayi, murmushi nayi ina mamakin wani irin addinine
haka mai shegen ta kura?.

Saka kaya na nayi na fashe jikina da turarukan sa masu shegen 'kamshi, amma abin
takaici banji 'kamshin kamar na jikin sa ba.

Fito wa nayi, kallon sa nayi tare da kallon break fast d'in bai ko ta'ba ba.

"Ya bakaci ba?" kallon na yayi tare da cewa "ke nake jira" ya tsina fuska nayi tare
da cewa "kaci kawai na 'koshi".

Mi'kewa yayi ba tare da yace dani komai ba ya nufi 'kofa, da mamaki na kira sunan
sa.

Waigo wa yayi yana kallo na ba tare da ya ansa ba, " bakaci ba ".

" Na 'koshi ne nima" murmushi nayi tare da nufan inda yake tsaye, kamo hannu sa
nayi .

Bai ce dani komai ba har na zaunar dashi, bud'e wa nayi tare da zuba wa a plat, na
had'a masa tea duka nace "muci" tare da saka hannu.
Bai ce komai ba ya faraci, kad'an yaci yace ya 'koshi tare da mi'kewa.

Nima na mi'ke, kallo na yayi tare da cewa "ci inajiran ki waje" .

"Na 'koshi, kin tabbata? uhum".

" Shikenan muje 8:10am har yayi 'kila 'kawan ki ta tafi" fita yayi na bisa a baya,
ina fita ya saka key ya rufe 'kofan.

Mukayo waje ya rufe gidan shima, rana ya fara fito wa mutane nata kai da dawo wa.

"Shiga kira ta" bace komai ba na nufi cikin gidan nasu.

Mama na tarar a tsakar gidan, gaishe ta nayi itako tana kallo na da mamaki a fuskan
ta bata ansa min gaisuwan ba.

"Baku tafi ba?" tace, cewan ta haka ne ya ganar dani cewa Aisha ta tafi, don haka
sai nai tsuru tsuru na kasa bata ansan tambayan ta.

"Joy dake nake fah" sosa 'keya na farayi sai na dake tare da cewa "mantuwa nayi
shine na dawo, to na duba d'akin mu ban gani ba shine na tuna jiya tazo ta 'kar'ba,
shine nazo duba wa".

Shiru tana kallo na kamar bata yadda da abinda nace ba, sai daga baya tace " me
kenan?".

"Litafin wata 'yar class d'in mu, shiga ki duba, amma ai da kun dawo tare ta barki
ke d'aya kin dawo".

" Amma a mashin kika dawo ko?" tace ina gab da shiga d'akin.

"Uhum" nace kawai tare da sa kai.

Kallon d'akin na tsayayi kawai har kusan minti biyar sannan na fito, ganin bata
tsakar gidan na saki ajiyan zuciya tare da falfalawa da gudu.

Ina fita na bud'e mota na fad'a cikin tare da sauke numfashi.

"Lafia?, ina 'kawar taki?" yace yana kallo na.

Ban sa ansa ba nace "muje kawai" bai wani matsa ba ya tada mota muka bar wurin.

Mun fara nisa sannan nace "Aisha fa ta tafi, kuma nasan ta shiga gidan mu nema na".

"Yayi, kinga mai himma kenan" turo baki nayi tare da cewa "naji ni ban da himma".

" A'a ni bance ba" banza dashi nayi shima bai matsa ba ya cigaba da tafiyan sa.

Yana parking na bud'e 'kofa zan fita, "ansa" yace .

Waigo wa nayi tare da kallon hannu sa, "ki ansa nace" hannu a dun'kule.
"Me zan ansa?" nace ina le'ka sa'kon hannu 'kara dam'kewa yayi tare da sa d'aya
hannu sa ya janyoni tare da kar'be jaka ta yasa min tare da saki na.

Zanyi magana yace "oyo wuce kin makara, maza aji kar a ta'ba min lafia jikin ki"
murmushi nayi tare da fita daga motan.

'Daga min hannu yayi nima haka nayi cikin makaranta.

Sauri ya tada motan yabar wurin bayan yaga shiga ta aji.

Ina shiga Aisha ta tsare ni da ido, murmushi nayi tare da cewa "lafia kallon
malama?".

"Ina kikaje ne besty? naje gida mama tace kin dad'e da fita".

" Gidan doctor " nace murya 'kasa 'kasa, don malam ya shigo lokacin.

Zaro ido tayi tare da bud'e baki, murmushi nayi tare da cewa gab da kunnin ta "rufe
bakin, kinsan wannan malamin mai rainin wayau ne, ki bari sai ya fita sai ki sake
wani tambayan".

Aiko kamar wa wuya ta kasa magana rufe bakin tayi muka natsu aka fara darasi.

Yana fita Aisha ba ta barni na koda matsa ba ta jefomin tambayan.

"Mekikai a gidan doctor fisabilillahi da girman ki da 'kiman ki?" .

"Tashin sa a barci nayi, bayan haka na masa break fast".

San'kare wa tayi a wurin.

Niko dariya nayi, in banda abinki Aisha ina ruwan arne........

**********

Rayuwa tama su Joy dad'i soyayya kawai suke kamar ba gobe, suna tsananin 'kaunar
junan su da kulawa da junan su
Sosai.

Amma fa Auwal bai sake sakacin barin 'kofar gidan sa a bud'e ba, don yana tsoron
Allah yana tsoron Joy.

Duk da haka bai tsira ba, a hakan tana yawan ta'ba sa, ko son shige masa jiki.

Wani abu da ta tsiro shine zuwa asibiti duk bayan ta dawo daga makaranta, sai tazo
tawani kanai naye shi.
Haka suke ta tafiya har wa yau, yanzu haka saura jibi Auwal zai koma garin sa, ya
gama sabis d'in sa, ya rasa yadda zai sanar mata.

Ganin cewa suna ta faman jarabwa, don bai son ya tada mata da hankali ko kad'an.

A haka har kwana uku tayi ba tare da yasan yadda zai ya gaya mata ba.

Can Abuja su mami sun kasa sun tsare suna jiran dawo wa Auwal shiru har washe gari
bashi ba labarin sa.

Sun kira wayar sa a kashe, shiko yayi hakan ne saboda bai san mai zaice masu ba.

Sati d'aya da gama wan sa saura kwana biyu su Joy su gama jarabawa, yana zaune a
'kofar gidan sa kawai sai hango motocin gidan su yayi guda biyu suna taho wa.

Farin cikin ganin 'yan gida da fargaba suka taru suka diran masa a lokaci d'aya.

Mi'kewa yayi daga farin kujeran da yake zaune, dai-dai nan sukai parking, nufar
motan sister d'in sa yayi.

Da farin ciki ya bud'e 'kofar motan, ita ce hakin CE a bayan motan sai Akaram.

Ko bari ta fito baiyi ba yace "oyoyo sis, oyoyo my son".

Harara ta maka masa, tare da cewa " shiga mota muje" d'aure fuska yayi tare da cewa
"kai Anty wani irin in shiga mota daga zuwan ki?".

" Auwal ban wasa da kai nace ka shiga mota mu tafi" bud'e d'ayan motan da akayi ne
yasa shi waiga wa.

Ba kowa bane illah Dady da kan sa, sai yaya wato Wanda ya kawo sa.

Ga farin ciki ga far gaba, amma hakan ya matse yayi musu barka da zuwa.

"Son mai kake a garin nan bayan ka gama abinda ya kawo ka?" cewan Dady ba tare da
ya ansa sanu da zuwan da yake masa ba.

Shiru shima Auwal yayi, ganin zai 'bata lokaci yasa Dady yace "shiga muje" rasa
yadda zaiyi yayi tunda Dady da Kansa yace haka.

Kamar zai kuka yace "Dady kuje kawai gobe zan.........." bai 'Kari saba sakamakon
wani matsiya cin harara da Dady yayi masa.

Bai dan dara ba yace "Dady bari na had'a kaya sai muje".

" Bama wani ka wuce muje" "akwai takadduna fa a cikin gidan".

" Jeka maza rakasa" yace da yayan nasa, bai so hakan ba amma haka yayi gaba yayan
yabi bayan sa zuwa cikin gidan.

Tarka ta takkdun yayi kaf tare da abubuwan sa masu mahimmanci suka fito, amma kafin
su fito ya faki idon yayan ya rubuta leta ya aje a kan kujera d'aki .
Suna fito wa saka kayan a bot d'in motan yayi tare da kallon gidan yana mai jin
wani iri a cikin ransa, gashi Joy suna makaranta yau bai san yadda 'yar rigiman sa
zatai ba.

"Dady bari na bawa gidan nan key d'in nazo".

" Ga wani can bashi ya kai musu kana 'bata min lokaci " waiga inda dadyn yai nunin
yayi.

Aiko ganin Muhusin ne yasamu kwanciya hankali.

Matsawa kusa dashi yayi tare da cewa cikin 'kasa da murya yana mai tura masa abu a
aljihu "'kani na, don Allah ga wannan wayan da kye d'in nan Joy na dawo wa kaba ta,
kace nace don Allah tayi ha'kuri zan zo bayan kwana biyu".

" To yaya insha Allah zan gaya mata, yauwa 'kanina nagode" yace tare da juyawa
wurin motan .

Shigan sa keda wuya suka bar wurin....................


.

To fah, wata sabuwa inji 'yan caca🤨😅

Comment & share pls


[11/5, 9:53 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

3⃣5⃣3⃣6⃣
3⃣5⃣3⃣6⃣
5⃣3⃣6⃣
➡3⃣ 3⃣
3⃣6⃣
3⃣5⃣
6⃣

Tun shad'aya suka gama jarabawan su, tafe suke suna d'an fira har suka zo inda
Auwal ya saba zama don jiran su, don basu ta'ba jiran saba kullum shike jiran su.

"Abin mamaki Aisha yau my heart bai zo da wuri ba" cewan Joy tana mai kafe wurin da
ya saba parking da ido.

Aisha tace" Allah sa dai lafia, amin" nace ina maijin fad'uwan gaba na ya'karu fiye
da yadda nakeji tun da na tashi a yau.

"Mu zauna daga nan mu jira shi besty" ba tare da nace komai ba na bita muka zauna a
wata gindin bishiya.

Shiru muke zaune amma idanuna na hanya, muna zaune har na tsahon wasu lokaci babu
doctor babu labarin sa.

Mune har 2:00pm babu shi, a lokacin kuwa zo kuga idanuwa na, idanuwa na fal da
'kwalla, gabana sai faman bugawa yake.

Nayi zurfi cikin tunani mai ya hanasa zuwa d'aukan mu, fatana dai ace yana cikin
'koshin lafia idan ba haka ba akwai matsala babba ma.

"Tashi mu tafi besty kinga rana tayi da uban yunwan da nakeji" cewar Aisha tare da
mi'kewa tana kamo hannu na.

Dojewa nayi na'ki tashi, kallo na tayi tare da cewa cikin marai rai cewa "please ki
tashi nasan wani babban uzuri ne ya tsayar dashi, don haka mu tafi kawai".

Gamsuwa da zancen ta nayi don haka sai na mi'ke, tare goyin mukayi muka nufo hanyan
'kauyen mu.

Tafiya muke amma gaba na na cigaba da fad'uwa, 'karuwan fad'uwan gaba na shine
sanda muka zo muka cimma babu motan Auwal a inda ya saba ajeta, don sam bai zuwa da
ita ko'ina da ya wuce kaimu makaranta.

Sai wasu lokutan da idan bai da wani abun anfani sai yaje cikin gari ya siyo. Kuma
bai tafiya sam ba tare da ya sanar dani ba.

Barin Aisha nayi da sallaman mai mashin ni kuma na nufi 'kofar gidan sa, duk da na
gansa a rufe.

Bubbuga gidan na farayi kamar mara kai, zuwa Aisha tayi tajani ina turjewa don jiki
na ya bani ba lafia ba.

Da 'kar ta jani cikin gidan mu, mama ce zaune a tsakar gidan da alamu dai shan iska
take, don zaune take da 'yar single a jiki ta sai faman fifita take.

Ko inda take ban kalla ba nayi hanyan d'aki, Aisha ce ta gaida ita tare da fita a
gidan.

Ina shiga d'aki nayi wurgi da jakan makarantan, za gaye d'aki na farayi.

A haka mama ta shigo ta cimmini, kallo na tayi tare da cewa" lafia kuwa Joy? "
kallon ta nayi tare da kauda kaina.
Gajiya da zaga d'akin nayi don haka na fad'a kan katifa tare da cewa" wayyo" da
'karfin gaske hawaye kuma suka fara ambaliya akan kyakkyawan fuska ta.

Da sauri mama tazo inda bake tare da d'ago ni tace" what happened Joy ".

" Mama ina doctor yaje yau bai gaya min ba?" Nace ba tare da naba ta ansan tambayan
ta ba.

Wani irin kallo na tayi tare da cewa" lallai doctor nada aiki tunda zai auri matar
da bazai ta'ba fita ba sai da sanin ta da kuma izinin ta" ta had'a da tsaki tare da
tashi tabar d'akin.

Eyhu na sake saki ina cewa " wayyo doctor na ina kashiga ne zuciya ta zata fashe?"
tare da rushewa da kuka.

Ranan babu zancen abinci, to yaya zakaci abinci ma bakaji yunwa ba? Toni ranan nama
manta da wani abinci sam.

6:15pm Muhusin ya shigo gidan mu da uniform d'in islamiya a jikin sa.

Gai da mama yayi tare da cewa bayan ta ansa "Anty Joy na nan?"

"Eh tana nan shiga ciki" tace dashi, hanya d'akin yayi.

Ina kwance da uniform d'ina kuma har lokacin kuka nake ya shigo, naji motsi ban
damu da sanin ko waye ba shiyasa ban waigo ba.

Ji nayi ance "Anty gashi inji yaya farin nan na kusa da gidan mu" ai da sauri na
waigo hard murmushi na.

Nace ina kallon hannu sa "yana ina?" mi'ka min kye yayi tare da cewa" ya tafi gashi
harda wayan nan yace na baki" yace yana bud'e jakan islamiyan tasa.

Gaba na ya fad'i na kalle sa tare da cewa" ina ya tafi?" Ina jujjuya kye d'in hannu
na hawaye naji ya fara zubowa a fuska ta.

"Ban sani ba, wasu ne dai 'yan birni suka zo a motoci da yawa ya shiga suka
tafi" .

Yace tare da mi'kamin wayar doctor, kar'ba nayi shi kuma ya fita.

Bin wayar nayi da ido ina jujjuya shi har na tsahon wasu lokuta.

Dana wayar nayi ta kawo haske, photo nane ya bai yana a fuskan wayan, ban san sanda
akai photo ba amma yayi matu'kar kyau.

Tashi nayi da kye a hannu na nayi fito daga d'aki, nufan hanya fita nayi mama na
kallo na batace dani komai ba.

Gidan nashi naje na bud'e, shiga nayi har ciki.

Tun daga yanyin yadda falon yake naji wani iri tsoro da fargaba.

Shiga bedroom d'in sa nayi, kaya ne na gansa a hargitse, kuka na saki tare da
d'aura hannu aka.

"Wayyo doctor na, wayyo! Wayyo mai yasa zaka min haka?, mai yasa zaka tafi ka
barni?"

"Baka min adalci ba" nace tare da fad'a wa katifan sa ina mai cigaba da kuka na.

Haka na kasance a gidan nan har dare kuma baci basha sai kuka kawai. Bani na bar
gidan nan ba sai 9:00pm.

Koda na shiga gida banyi takan mama ba na kwanta kawai ina mai cigaba da kuka na.

Da fitana mama ta biyo bayana, ganin inda na shiga yasa tai zargin wani abu.

Gidan su Aisha ta shiga bayan na shige gidan doctor, bayan sun gaisa da maman Aisha
sai ta nemi Muhusin, tambayan sa tayi yayi mata bayani ita kuma tabar gidan.

Shiyasa bata ko nemeni ba, ganin kukan ya'kici ya'ki 'karewa yasa ta matso cikin
tausayawa ta kamoni tare da lallashi na.

Ta d'au lokaci mai tsayi tana lallashina, da'kar na dai na kuka.

Baccin ranan ban samu yin saba sam.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Auwal lafia suka kai gida, baiyi magana da kowa ba har da mami. Fushi sosai yake da
kowa na gidan.

Duk wani gata da tarairaya da mami da uwar gayan suke sam bai burgesa, bai sa ya
saki jiki ba.

Abinci sai anyi da gaske yake ci, kullum yana cikin d'aki, bashi da abinso dake
saka shi nishad'i da jin dad'i wanda in har yana cikin yanayin zaka ga yana dariya
ko murmushi, shine tunani masoyiyan sa.

Hakan da ya mai da kansa yasa damuwa mai tsanani a zukatan iyayen sa da 'yan uwan
sa, musamman mami da Anty RAHAMA.

A haka har akai sati biyu, a sati biyun nan ko yayi muguwan rama kai kace wanda
yayi ciwon shekara.

Kuma a yaune yasha alwashin koma wa 'KAUYEN 'YAR KADDE tun da nanne farin ciki sa
yake.

Shirya wansa yayi ba tare da ya sanarwa kowa na gidan ba.

Bayan ya gama shirya kansa cikin 'kananun kaya wando na'ki da jan riga mai rane jah
da fari sai wani zane na 'baki kad'an wanda yayi matu'kar 'karawa rigan kyau.

Kayan sun matu'kar kar'ba sa.


Fita yayi daga d'akin sa yayo main palon gidan. Da yake yau Saturday ne kowa na
gida, zaune ya gansu duka, mami, RAHAMA, Dady har da yayyun sa maza.

Gai dasu duka yayi a cikin ciki ba tare da ya kallesu ba, ansawa duka sukayi idon
su na kansa.

Sunji dad'in adon da yayi a tunani su ya kwantar da hankalin sane basu san ko
kad'an ba hakan bane, domin kwanciya hankali sa shine yayi arab da za'bin ransa.

Gani sukayi ya nufi hanya barin palon, duk cikin su sun kasa masa magana.

RAHAMA ne kamar mai tsoro ta kira sunan sa, tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba.

Tashi tayi tare da zuwa inda yake.

Dafa kafad'an sa tayi tare da cewa" ina zakaje habibi?" Banza da ita yayi tare da
zare hannu ta daga kafad'an sa ya bar wurin.

Wurin ajiye motocin gidan ya nufa, 'barayin da motocin sa suke ya nufa.

Rufe suke ruf d'aga wa yayi d'aya bayan d'aya, gani yayi duka sunyi kura.

Cike da masifa yake 'kwala ma mai wankin motocin kira.

Da gudu ya nufo sa, ma'kaitan kaf sunji kiran nan har 'kwa'kwalwan su.

Hatta su mami sai da suka fito suga dalilin uban wannan kiran.

Abinda bai ta'bayi ba fuska babu walwala yana zuwa ya dur'kusa tare da cewa" gani
yalla'bai" .

Ya bashi wani irin mari tare da cewa cikin masifa "wani irin iskanci ne zaka barmin
motoci da 'kira eyeh?"

Yace yana 'kara masa wani, cike da girmamawa yace" yalla'bai go kwana hud'u baya
sai da na wanke".

"Sai akace maka kuma jiya ko yau karka wanke ko?"

"Maza wanke min wancan jan yanzu na baka minti biyar kuma ya fita, idan ba haka ba
yau sai kabar gidan nan" yace tare da tsaki ya juya.

Kamar d'azu suna kallon sa ya wuce ta gefen su baikoyiwa wani daga cikin su magana
ba.

Da mamaki RAHAMA tace idanun ta cike da ruwan hawaye "Dady don Allah muje mu bashi
ha'kuri muji meye damuwar sa, idan ma zaman 'KAUYEN yake so sai mu barshi ya koma
idan yaso muyi masa ginin zamani a can. Sai ya rin'ka zuwa duk sati gida yana
dubamu komu murin'ka zuwa".

Tunda ta fara maganan yake hararan ta har ta idda maganan ta.

Yau da badon 'yar gaban goshi bace tai maganan nan ai da tasha mari.

" Baki da hankali ko RAHAMA? ni kike so naje na bawa d'ana ha'kuri to bai zai ta'ba
yuwu wa ba, don bashine ya haifeni ba, don ko uban sa.........."
Sai kuma yayi shiru "to bari kiji babu wata 'KAUYEN da zai koma, nd kwanan nan zai
fara zuwa asibitin sa, don an gama komai bikin bud'e wa za'a sai ya fara aiki kinji
ko?" Daga nan yayi tsaki tare da barin wurin.

"Kema dai inajin mahaukaciya ce ke, wai da bakin ki kike cewa Auwal ya koma 'KAUYEN
da zama. Hmmm to bari kiji ko zuwansa sabis saboda ya rage wasu abubuwa da basu
dace ba shiyasa muka dage kai da 'kafa ya tafi".

" Don sam bamu soba ke har Dady kan sa, saboda yayi hankali ne kawai muka kai sa"
cewan babban wansu.

Kuka ta fashe dashi tare kallon mami da tai shiru .

Matsawa inda take tayi ta rungume ta tare da cewa" mami yanzu ya zanyi ya zanyi my
brother ya dawo kamar da?" shiru tayi domin ita kanta abin na damun ta sosai.

Suna tsaye su biyu domin sauran sun bar wurin sai gashi ya fito.

Wuce su yake sonyi mami tace cikin matsawa da d'aure fuska.

"Ina zaka?" tsayawa yayi shiru ba tare da yace komai ba.

Tsawa da bata ta'ba masa ba shine tayi masa "dakai fa nake kayi shiru".

Fukan nan a had'e yace" nasarawa zani " daga haka yayi shiru.

"'KAUYEN nan zaka ko?" Shiru yayi ba tare da ya bata ansa ba.

"Wai shin Auwal meye kakeso? Meye kake nema a 'KAUYEN nan?" Still bai bata ansa ba.

"To tunda baka da ansan tambaya ta koma ciki" wani iri juyo wa yayi cikin tashin
hankali yake kallon mamin.

Zaiyi magana tace" daga yau na sake jin sunan 'KAUYEN nan a bakin ka bare kace zaka
sai na.............................

Comment nd share

Luv you all my fan's💋💋💋


[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*


🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*

*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*My ❤, my kaka, my Hafsatuwa😉, my Hafnan is back.💃💃💃💃💃💃💃💃💃ina masoya ku fito, ga


shahararriyan Marubuciyan nan da ta saba nishad'an tar daku, wato Marubuciyan, SHI
SO 'DAYA NE, FATALWAN MIJIN NA da kuma HIBBATULLAHI. ta dawo muku da wani
shahararran littafin ta mai suna KAICON SO! Masoya ku hanzar to kar kubari a baku
labari Hafsat Mustafah (Hafnan) ta shirya tsaf domin nishad'an tar daku,
wa'azantarwa da ilimantarwa. Da abaka labari gumma ka bayar, saboda haka masoya ku
fito 'kwai da 'kwar'kwata domin wanke idanuwan Ku, karrrrrrr
kubari.....................*

*you will never brave, if you don't get hurt. You will never learn, if you don't
make mistakes. You will never be successful, if you don't encounter
failure..................Good morning😉🙏🏻

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

3⃣7⃣3⃣8⃣
3⃣7⃣3⃣8⃣
7⃣3⃣8⃣
➡3⃣ 3⃣
3⃣8⃣
3⃣7⃣
8⃣

"Wayyo Allah na, wayyo mami na. Wallahi mutuwa zanyi, mami in............" Sai kuma
yayi shiru, kallon sa tayi tare da cewa "indai na isa zan gani" daga haka taja
hannun RAHAMA suka wuce ciki, Kamar zaiyi kuka ya tsaya kallon hanyan da suka bi.
Yana tsaye ba'kin ciki fal a cikin ransa, amma ya ya iya, haka ya gama tsayuwan sa
yayi ciki, ko kallon inda suke baiyi ba san da ya shiga.

Sati na zagayo wa akai gagarumin bikin bud'e asibitin, Dady yayi 'ko'kari matu'ka
ya cika uba na gari wanda kowani d'a zai alfaharin kasancewan sa uba a gare sa.

Ya zuba masa duk abinda ya kamata, had'a dasu manyan doctors, kayan aiki na zamani
tun daga 'kasanr waje da dai sauran su.

Amma abin mamaki koda na waiga inda mutumin ku yake sam babu alaman farin ciki a
tare dashi, fuskan nan a murtuke.
Angama taro lafia sai dai fatan Allah sa albarka.

Ya fara aikin sa cikin nasara, yana samun girmamawa ga duk ma aikatan, suna
matu'kar girma mashi, aiki sosai suke a asibitin ciki tsantsan 'kwarewa.

Lokaci 'kan'kani asibitin yayi suna, sun sami lambobin yabo daga wurare daban, don
gaskiya doctor Auwal 'kwararrene.

Kimanin wata hud'u da bud'e asibitin sa, amma Auwal bai ma kowa magana sai ta kama
dole, walan gida ko asibiti.

Haka zalika fuska a d'aure, mata na son sa kamar zasu mutu amma babu fuska balle su
san'kafa mai tayin soyayyar su.

Duk wata mace maiji da kanta da isa, burin ta Auwal ya kula ta.

Amma hakan bai samuwa sam, Auwal ya zama wani irin mutum.

Auwal ya zama fitinan nane 'karfi da yaji, abi kad'an kayi kuskure zaka sha masifa
ko kuma ya kore ka, gida ko asibiti. shiyasa duk wani mai son kansa da arzi'ki yana
gujewa 'bacin ran Auwal.

Ba gida ba ba asibiti ba kullum kwanan duniya ka sake kayi kuskure kad'an yanzu zai
'kore ka, haka zalika ko sakon baka 'karawa a wurin.

***********

Zaune yake a bakin bed d'in sa sai faman kiran wayar sa da ya bawa Joy yake da ya
zame masa kullum kamar ibada amma bata shiga.

Kamar zaiyi kuka yace" why my happiness? Kullum sai na kira layin nan yafi abinda
yafi, ko ba'a baki bane? Kai inah nasan yaron nan sosai bazai 'ki baki ba".

"To amma meye na kashe waya?".

" Oh Allah na help me" yace tare da sake gwada layin, still dai abu d'aya baturiyan
nan take ta nana tawa.

Cikin fushi yayi wurgi da wayar, kwanciya yayi a gadon tare da runtse idanu.

Bai ankara ba kawai sai ga hawaye masu d'umi suna zubo mishi, bai hansu su zuba ba
har sai da suka bar zuba don kan su.

Dai-dai nan yaji ana knocking, tsaki yayi tare da tashi ya nufan 'kofan, bud'e wa
yayi.

Ganin wacce ke tsaye yasa ya mai da 'kofa ya rufe, abin mamaki fanz RAHAMA ce fa
akai wa haka, lallai abin babbane.

Kuka ta fashe dashi, yana jin kukan har cikin ransa amma yayi biris da ita, da yaji
kukan na damun sa ma sai ya tashi ya shige toilet abinsa.

Kuka tayi sosai kafin tabar wurin, daga nan ta zarce part d'in mami.
Da gudu ta nufe ta, tace cikin kuka "mami don Allah kuyiwa my brother abin da yake
so, don Allah ku barsa ya tafi can d'in don samun kwanciya hankalin mu. Mami bai
magana da kowa, baicin abincin gidan nan sai da matsi".

" Mami jifa, ni na raine sa da hannu na, na kula dashi kamar uwan da ta haifesa,
shine abokin shawarata, abokin firata, shine kesani nishad'i. Shike sani farin ciki
fiye da kowa, baya son ya ganni cikin damuwa ko d'an 'kan'kani ne, ya tsani ganin
'bacin raina. 'Kanina na sona, kullum......." Sai ta fashe da wani irin kuka mai
ban tausayi.

Rarrashin ta mami take, tace cikin lallashi "ki fita harkan Auwal idan ba haka ba
ciwon ki na gab da dawo wa".

"Mami ina fita harkan Auwal fa kika ce?" Tace cikin zaro idanu "amma mami bakiyi
tunani ba sam, Mami Auwal fah d'anki ne na duniya da lahira, maraya ne kin sani
sarai, mami kina tunanin share sa da kuke hakan ya dace? har yau kun'ki zama dashi
kuji meye damuwar sa meye yake so?".

" Shin haka ya dace kuyi ma maraya? kunyiwa maraya adalci kuwa? mami kamar bake ba,
mami kiyi tunani da kyau shin abinda kukayi dai daine? Auwal d'ane d'an gata,
saboda iyayen sa ma 'yan gatan kune. Mami kiyi tunani ".

" Mami kamar bake ba, mami Auwal d'inki ne fah, yaron Anty ne fah. Anty baza ta
ta'bajin dad'in ace yau ga yayan ta tabar mata d'a cikin wannan yanayi ba, kin bar
mata yaro cikin damuwa".

"Mami kin manta wannan shine jinin Anty 'kwalllin 'kwal? Shine ita fah tunda bata,
mami ina son da kike mata ya tafi? wai yau da bakin ki kike cewa na rabu da jinin
Anty na? Bayan Anty na itace uwata.".

" Anty da Abbey mutanen kirki ne sosai ke kanki sheda ce, uwa d'aya uba d'aya kuke
mami ko kin mata Abbey 'kanin mijin ki ne uwa d'aya uba d'aya? ".

" Auwal jinin mune gaba da baya, da mamaci na magana da tabbas Anty ta sanar miki
bata jin dad'in yadda kika bar mata yaro kamar mara gata ba, Anty ta mutu tana
murna da murmushi na tabar farin cikin ta a hannun ki, saboda tasan bazaki ta'ba
wofin tar mata dashi ba".

RAHAMA ke zancen nan cikin kuka mai tsanani.

"Mami kije kiji mai d'anki yake so, mai yake bu'kata. Ki nemo yadda zakiyi Auwal
yayi farin ciki, Anty ta baki amanan d'anta tana tunani kece kad'ai wanda take da
ya'kini tilon d'an ta zai samu farin ciki daga gare ta".

Daga haka ta tashi tabar d'akin mamin, jikin mami yayi sanyi sosai, don gaskiya
maganan RAHAMA ya shige ta sosai.

Su uku ne, amma kuma itace abokiyan shawara firan ta duka, tace tana maiji kewan
'yar uwan ta ta.

Tashi tayi cikin sanyin jiki ta fito daga d'akin nata, bata zame ko inaba sai
'kofar d'akin Auwal.

Knocking tayi tayi amma Auwal ya'ki bud'e wa don a tunani sa RAHAMA ce ta dawo, don
duk abinsa yana ganin girman mami fiye da kowa a gidan, shiyasa ita kad'ai yake
d'aga wa 'kafa.

Haka ta d'au tsahon lokaci tana bugawa amma ya'ki bud'e wa.

Kiran sunan sa ta farayi amma shiru kakeji tamakar bashi a d'akin.

Haka ta gaji ta ha'kura akan sai da safe.

°°°°°°°°°°°

Washe gari kuwa tsiro da wani abu yayi, suna idar da sallan asuba Dady na kallon sa
yabar gidan a guje kamar zai tashi sama.

Dama yayi wanka sannan yayi alwallah, da mamaki baki sake Dady ke kallon hanyan da
yabi.

Girgiza kai kawai yayi tare da shigo wa ciki.

Wurin break fast ne mami taje neman sa ta tadda bashi shine Dady ke samar mata da
akan idon shi ya fita.

Jikin tane yayi sanyi, RAHAMA ma tashi tayi gaba d'aya tabar dining d'in mijin ta
yabi bayan ta .

Mamin kanta kasa karyawan tayi, kiran layin sa tayi bai shiga, don haka ta buga
uban tagumi hawaye na kwaranya akan fuskan ta.

Dady ya matso kusa da ita tare da bata baki sannan tabar kukan.

Auwal ko daga gida asibiti yayi, koda ya bud'e office d'in sa kwanciya yayi kawai
tare da runtse idanun sa.

Wanene Auwal??????

Asalin sa, ko nace tushen sa.

Alhaji Bashir da malam Isma'il ma'kotan junane, kuma aminan juna. Idan ba wanda
yasan su tuntuni ba zai tsammanin 'yan uwan junane, don yadda suke mu'amala ya wuce
ka kira su da aminai, domin sun zama 'yan uwan juna.

Yadda mazajen suke haka ma matan su.

Alhaji Bashir mutumin kirkine, yana da arzi'ki dai-dai gwargwado, arzi'kin sa bai
rufe masa ido ba sam, yana matu'kar taimakon talakawa, yana daraja ma'koci, matar
sa d'aya itace HAJIYA Umma, macece mai kirki da zumun ta.

Sun d'au tsahon lokaci Allah bai basu haihuwa ba, tun suna damuwa har ya zamana
sun fawalawa Allah.

Watarana suna zaune abokan junan nan suna fira, sai Bashir ya dubi Ismail cikin
damuwa yake cewa" na rasa wani laifi nayi wa ubangiji na" sai kuma yayi shiru.

Sai Ismail yace" d'an uwa mai yasa kace haka?" numfasawa yayi sa'an nan yace"
wallahi rashin haihuwan nan na matu'kar damuna, ka duba tsahon shekaru goma sha da
auren mu amma har yanzu shiru bamu ta'ba ko 'bari ba, ga fitinan dangi".

Murmushi Ismail yayi tare da cewa" bai kamata kasa damuwa a ranka ba, duk bawa bai
wuce jarabawan ubangiji ba, wannan shine jarabawan mu nida kai, saboda haka kar mu
gaji, mu cigaba da addu'a Allah na sane damu, Allah ya bamu ikon cin jarawan nan".

Magagganu mai dad'i Ismail yayi masa, maganan ta shige sa, don yayi aiki da ita.

**********

Bayan wata biyar da maganan su sai gashi Allah ya bawa matan Bashir ciki, zoka ga
murna wurin iyalan nan

Bayan wani lokaci ta haifi d'anta mai tsanani kyau aka samasa suna KABIR.

KABIR nada shekaru biyu ta sake samun ciki, wannan karon itama matan Ismail ta samu
ciki. Sai dai wannan cikin yazo ma matan Bashir wani iri domin yana bata wuya
sosai.

Kullum cikin ciwo, ranar da ta haihu na biyu tace ga garin ku nan.

Wannan karon ma namiji ta haifa, Bashir yayi kukan ba'kin ciki sosai malam Ismail
ne yaba shi baki yazo har yasama zuciyar sa salama.

Bayan rasuwan ta da kwana uku yaro ya fara neman abinci, hankalin Bashir ya tashi
sosai.

Fara zaga dangi yayi don neman mai shayar masa da yaro ya biya amma daga nasa har
na matar sa anrasa.

Don mursisi suka'ki, damuwa yasa duk yabi ya zaganye, ga jariri anrasa mai kar'ba
ga kuma yayyayye babu mai kulwa dashi.

Ismail ne ya share masa hawaye ya kar'bi jaririn ya bawa matar Amina ta had'a ta
shayar dashi tare da yaron ta Muta'ka don itama bata dad'e da haihuwa ba.

Tsakanin su kwana biyu, yayi farin ciki matu'ka sosai gaya, don haka zumuncin su
ya'kara 'kaimi.

Malam Ismail bai tsaya nan ba har da KABIR ya kar'ba yaba wa matar sa ta cigaba da
kulawa da nata da nasu bata ta'ba nuna banbanci ba sam.

Bayan shekaru shida yara su uku maza sun taso kusan kai d'aya cikin gata da
soyayyar iyayen su uku.

Alhaji Bashir ya had'a su kaf ya sasu makaranta boko, na addini kuma ko dama malam
Ismail na koyar dasu shida matar sa.

Yarane kyawawa, ana haka umma ta sake haihuwa kamar yadda suke kiran ta, macece aka
samu zokaga farin ciki wurin iyayen da kuma yayyin yarinyan, ranan suna yarinya
taci suna MARYAM.

MARYAM 'yar gata 'yar gaban goshin wannan ahali, kowa bai son kukan ta.

Shekaru uku da haihuwa MARYAM aka sake haihuwan 'ya mace ita kuma Bilkisu .
Yara sun taso cikin gata da soyayya ga tsantsan tarbiya.

Bayan wasu shekaru Bashir ya kwanta ciwo, hakalin Ismail da yara yayi mugun tashi.

Haka ya kaisa asibiti, haka aka d'au tsahon lokaci ana jinya maimakon sau'ki kullum
abin 'karuwa yake.

Kawai sai shima yace ga garin ku nan, Ismail yayi kuka, yayi ba'kin cikin rashin
d'an uwan sa.

Kafin ya rasu ya basa amanan yaran sa, kuma ya kar'ba.

Haka Ismail ya cigaba da kulawa da yaran nan bisa gaskiya da amana, kuma komai da
zai musu da dukiyan sa yake, bai ta'ba ta'ba nasu ba.

Sai dai yana jujjuya musu, a haka yara har suka girma bayan gama karatun samarin
nan uku sai suka fara aiki.

Baba Ismail na cigaba da kulawa musu da dukiyan su, yayi yayi suyi suwanci fir
suka'ki waisu basu shi'awa.

Lokacin ne kuma KABIR ya fara soyayya da MARYAM, shima 'kanin ba'a barsa a baya ba
ya fara shima yace yana son Bilki.

Mukutar dai bai sami budurwa ba shi.

Baban nasu yaso abin baiso ba saboda surutun mutane.

Amma yara sun kafe, ba don yaso ba aka saka ranan auren su.

Gidan 'kerarre suka tamfatsa a Abuja wuse. Da yake nan dukan su suka sami aiki.

Bayan biki suka tare da matan su.

Shi kuma Mukutar a Abia yake aiki.

MARYAM ta haihu auren su da shekaru biyu, bayan nan ta 'kara haihuwa kuma duka
maza.

Rashin haihuwan Bilki na matu'kar damun zukatan su, haka yayi bala'in ta'ba zuciyar
miji da matan nan saboda Allah ya jarabesu da masifan son 'ya'ya.

Duk da yaran yayin su babu shamaki a tsaknin su amma suna masifan son na kansu.

Shekaru goma baya MARYAM ta sake haihu wannan Karo mace ta haifa.

Hakan sai da zuciyar Balki ya buga, haka sukai fama da ita suna ta jinyan kusan
shekaru biyu.

Koda MARYAM ta gano damuwa 'yar uwan ta sai tabata 'kautan 'yar RAHAMA.

Bilki tayi farin ciki sosai, a lokacin ne aka canzawa mijin ta wurin aiki zuwa
Kaduna.

Haka suka d'unguma suka tafi da 'yar su.


RAHAMA ta taso cikin tsanani soyayya da gata, ba'a son damuwa ta haka ma fishin ta.

Bilki na matu'kar 'kaunar RAHAMA kamar ranta.

Allah bai basu haihuwa ba sai da RAHAMA takai shekara goma shara biyar.

Zoka ga farin ciki wurin su, RAHAMA ma ba'a barta a baya ba murna take sosai za'a
mata 'kani.

Komai taci ta rage ko ta samo sai tace" momy gashi kibawa 'kanina".

RAHAMA har tafi su son cikin nan.

Bayan wata tara Bilki ta haihu, ta haifi santalelen d'anta Auwal.

Tunda ta haifi Auwal ta kama ciwo, Auwal bai shekara ba ta rasu.

Batun zaiyana muku irin ba'kin cikin da wad'an ahali subakyi 'bata bakine.

Mutum ya ta'ba zuka tansu sosai, bayan wata biyar aka 'kara musu jarabawa da
mutuwan mijin Balki AL'kasim.

Sunyi shekaru da yawa kafin ciwon nan ya warke a zukatan su.

Amma na RAHAMA shine 'kila ajalin ta, don itama kawai za'ace akaima wa mutuwa.

Wannan dalilin ne Auwal ya zamo d'anga tan kowa.

Musamman mutane biyun nan RAHAMA, mami.

Saboda soyayyar da RAHAMA kema Auwal yasa da takai minzalin aure ta'kiyi saboda
bata son a rabata da Auwal.

Sai da 'kar tayi sai da Wanda zata aura ya yadda da zaman gidan su tukuna.

Wannan shine ta'kaitaccen tarihin su.

Comments & share pls🙏🏻


[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*


*we are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all.........DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*Wallahi kuna matu'kar bani haushi, mutum baiji wahalan muku typing ba. Amma ku
kuna jin 'kashin kuma mutum comments. Sai mutum bai ba a isheshi da tambaya, to
billahillazi nagaji, idan baku so babu dole kusanar dani sai na aje kawai ba nai ta
ti'kin banza ba🤨. Inga gyara daga wanna idan ba haka ba na aje, kuma wanna ma badon
ku nayi ba, saboda masu mun comments nayi, idan baku gyara ba ina iya bari kuma ko
kin tambaya idan kikaji shiru bazan ko kalle kiba bare kisa ran ansa😏 kuyi ha'kuri
idan maganana ya 'bata muku rai gaskiya ta na fad'a🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

3⃣9⃣4⃣0⃣
3⃣9⃣4⃣0⃣
9⃣4⃣0⃣
➡4⃣ 3⃣
4⃣0⃣
3⃣9⃣
0⃣

*******

Joy kuwa rayuwa tama ta zafi, kullum cikin tunani take, duk tabi ta rame, ta zama
kurman 'karfi da yaji. Dama abinka ga miskila, abin sai ya'karu fiye da da. Kuka ya
zama shine abincin ta, shine kullum dare rana. Anyi lallashi har angaji an barta,
domin kamar 'kara zuga ta suke. Magana daga eh sai a'a idan ta gada ma taso, idan
bata soba to sai dai d'aga kai ko ta girgiza maka, ko tayi kamar ba da ita kake ba.
Makaranta ma barin zuwa tayi maman tayi tayi ta'ki zuwa Aisha tayi amma a banza.
Jarabawa haka suna kallo ta'ki zuwa ta'kari sa. babban takaicin ta na'kin kula kowa
da'kin zuwa makaranta shine saboda har kwana biyu da barin sa bai kira taba har
wayar ta mace saboda rashin charge. Da wanna dalilin yasa kowa haushi yake bata,
wayar ma ajeshi gefe tayi don tace bai da anfani.

Rayuwa tayi mata wani iri bata jin dad'in shi sam, kullum addu'a take ubangiji dawo
mata dashi lafia.

Haka aka d'au kusan sati, wata, shiru babu Auwal. Wanda a wanna lokacin ne sukayi
hutu kuma har sun dawo, amma Joy ta'ki makaranta fir.

Koda yaushe bata da aiki sai tunanin da kuka, har tsawon wata hud'u.

Maman ta fara nema mata taimako daga wurin 'yan uwan ta arna, shine aka fara
samun sau'ki, don alhamdulillah yanzu tabar kuka, tunani ma ta rage sosai.
Makarantan dai ta'ki, ganin sau'ki na samuwa yasa basu matsa mata ba.

Rashin 'kin makarantan Joy ba 'karamin ba'kin ciki Aisha tayi ba.

Don Aisha ita kad'ai ke tafiya makaranta haka ma dawo wa.

Lokaci na ta tafiya, yanzu haka Aisha na SS2.

Joy na gida har yanzu, ganin yanzu ta kwantar da hankalin ta, yasa Aisha tazo har
gida taro'ke ta har da kuka akan ta koma makaranta shine fa ta amince zata koma.

Tako koma d'in amma JS3 ta koma, ta mai da hankali sosai tana karatun.

Lokacin jarabawa nayi ta zana, koda sakamako ya fito sunyi farin ciki sosai.

Daga nan ta fara cuku cukun neman cigaba, ta kuma samu ta fara SS1 d'in ta cikin
kwanciyan hankali.

Lokacin Aisha na SS3.

Karatu suke ba wasa don sun mai da hankali sosai.

Kada kuyi tsammanin cewa wai joy ta shafe babin Auwal a zuciyan ta.

Ko d'aya yana nan daram, kuma kullum bata cire rai da cewa zai dawo gare taba
watarana.

Kuma kusan kullum sai tashiga gidan nasa, watarana ma a can take wanka da dai
sauran su. Mama bata ta'ba hanata ba, don tasan zafin so, don shine silan rabuwan
ta da iyayen ta.

Gidan na matu'kar d'ebe mata kewan shi sosai, yana rage mata wani abu.

Haka take tafiyar da rauywan ta cikin tsananin begen doctor d'in ta.

Amma dai-dai da rana d'aya bata ta'ba nuna ko a fuska tana damuwa dashi ba.
Nunawa take tama manta dashi, hakan ya faranta ran bestyn ta da maman ta.

Anzo anfara registration na waec da neco, sai Aisha tace ma baban ta ya biya musu,
ya ansa akan zai biya, saboda haka da murna tazo gidan su Joy ta sanar mata.

Tace" besty an fara registration fah" shiru ta mata kamar ba da ita take ba.

Ta sake cewa" haba besty ina magana kina banza dani kamar ba dake nake ba" tare da
ta'ba ta.

'Dago dara daran idanun ta tayi ta kalle ta ba tare da tayi magana ba.

Aisha ba tai zuciya ba ta sake cewa" besty an fara registration na waec da neco,
nama baba magana akan ya biya mana don banson na barki a baya".

Ta tsaya tana kallon ta tare da jiran abinda zata ce.

Murmushi gefen baki tayi tare da cewa" ban bu'katan haka gaskiya, na fison nayi
karatuna a tsari, banso wuce ba".

Daga haka tai shiru tare da kauda kanta, juyo da fuskan nata Aisha tayi tare da
cewa cikin 'bata fuska" meye nufin ki wai?" shiru ta mata, tace" nufin ki na samu
baba nace masa me bayan yace yau zaije ya biya? da yake tun jiya nayi magana".

"Bazan yiba nace miki" kuka ta fashe dashi tare da cewa" shikenan tun da ke ba'a
iya miki sai abinda kike so shikike so kikeyi " .

Daga haka ta mi'ke ta fara tafiya da ninyan barin gidan.

Sai da takai 'kofa sai taga bata kyau ta mata ba, don haka tace" kiyi ha'kuri na
amince".

Waigo wa tayi cikin tsantsan farin ciki tana kallon ta amma kamar ba ita tai
maganan ba.

Fuska d'aure kuma kullum haka yake.


Dawo wa tayi da murna ta rungume ta.

*****

Lokaci nayi suka zana jarabawan su cikin nasara da kwanciyan hankali.

Alhamdulillah sunyi nasara don certificate yayi kyau sosai.

Daga nan sai aka fara shirin jam.

Shima sunci don haka suka samu gurbin karatu a jami'an nasarawa.

Kowa fanni da ta za'ba aka bata, Aisha low, Joy fanin habibin ta ta za'ba.

Karatu suke cikin kwanciyan hankali, a lokacin duk kannin halitan cigakkun mata sun
bayyana a tare dash, ko dama can Joy ba bata ba tana da komai.

Kyawawan 'yan matane ajin 'farko, Joy dai farace kamar yadda kuka sani siririya
doguwa, mai yalwataccen gashin kai. Ga bakin ta madai daita, masu d'aukan hankali.
Ga fararen idanu.

Akwai diri mai d'aukan hankali, komai nata ya 'kara cika da fitowa, ba shakka Joy
had'ad'd'iyar budurwace mai kimanin shekaru 20.

Kyawun ta mai d'aukan hankali ne, don a halin yanzu samari sun fara zarya ba kuma
'kananun mutane ba, a'a irin 'ya'yan manyan mutanen nan.

Bata sauraron su ko kad'an. Aisha ma babu laifi tana da nata kyau d'in dai-dai ita.
Itama tana da samarin amma ba irin na Joy ba.

Kuma itama bata kula su karatun su kawai suke .

Da taimakon baban su Aisha suke karatun su cikin rufun asiri, yana matu'kar
'ko'karin ganin basu rasa komai ba na bu'kata.

Dai-dai na talaka.

°°°°°°°°°°°°

Lokaci ba 'karya bane, don a yanzu haka Joy ta gama karatun ta, Aisha ta riga ta
gama wa tunda course d'in su ba d'aya bane. Aisha tayi service har ta gama, saura
Joy. kuma dai-dai da sarannan Aisha ita da wani d'an mai kud'i.

Bata so haka ba amma bata da yadda ta iya saboda nacin wanna d'in da kuma mahaifin
ta, don yace tunda angama karatu sai aure kuma.

Wata d'aya kacal aka sa, taso Joy ta tsai da wani a cikin maneman ta idan yaso a
had'a ayi tare amma fir ta'ki.

Don da ta matsama tunda takama kuka sai da takwana uku bata magana da kowa ko
abinci ta'kici shiyyasa ta ha'kura.

Shirye-shirye suke ba kama hannun yaro, daga 'bangaren angon har amarya kowa shiri
yake.

Biki ya rage saura sati biyu ango yazo musu da albishir d'in ya sai musu gida a
cikin gari can G R A keffi, iyayen Aisha sunyi murna sosai.

Tare wa washe gari don a can za'ai biki.

Kuma gidan yace parts uku ne har da maman Joy, itama tai murna tayi godiya sosai.

Koda Joy ta samu labari fir tace babu inda zata, don bata son Auwal yazo bai same
taba..

Don bata cire rai akan cewa zai dawo gare ta ba.

Sai da maman ta ta nuna 'bacin ranta sosai sannan ta yadda suka bar 'kauyen sai
faman kuka take.

Gida yayi sosai ba laifi, wani babba bane amma ya burgeni sosai.

Bayan tare wansu da sati aka fara gudanar da biki, tun daga wanna lokacin Aisha ta
fara kukan rabuwa da Joy .

Babban tashin hankali ta shine ba a gari zasu zauna ba, don angon d'an abuja ne,
can ma yake aiki.

Ana shirin biki Aisha na ciwo, tun tana a tsaye har ta kaima kwanciyan a gadon
asibiti.

Tashin hankali sosai wad'an nan a halin suka shiga, likita kuma yace a mata abinda
take so, idan ba haka ba komai na iya faruwa.

Don haka iyayen ta suka tambaye ta damuwa ta a gaban angon da kowa nata.

Tana kuka take cewa" so nake Joy ta bini" koda aka tambaye ta ina baki shakku tace
abuja.

Iyayen sun ga rashin yuwan haka da dace wan abin.

Amma angon yace babu damuwa da haka Aisha ta warke aka cigaba da shagali, Joy taso
'kin yadda amma ganin halin da 'yar uwan ta take ciki yasa ta amince.

•••••••••••••••••

Rana bata 'karya, wanna haka yake domin yaune aka shaida d'aurin auren Aisha da
Abudurrahaman.

Ayi cikin kwanciyan hankali kuma a yau d'ine daga d'aurin aure suka wuce da amarya.

Sai dai muce Allah basu zaman lafia.

-------------------------------

Zaman Joy a Abuja....

Zama ne cikin jin dad'i da walwala, bata da matsalan komai da kowa.

Sai dai tunanin Auwal da take lokaci zuwa lokaci, maganan tafiya service d'in ta na
tashi KD suka tura ta, sai ta nuna bata shi'awan can.

Saboda haka sai Abdurrahaman ya mata cuku cuku aka barta a Abuja, don haka bata da
matsalan komai.

Don sosai Aisha da mijin take 'ko'karin faran ta mata da sata farin ciki.

Kullum cikin tarairayan ta suke, itama tana 'ko'karin kyauta ta musu, tana bama
mijin Aisha girma sosai tamakar wanta ta d'auke shi.

Zaman ta a Abuja ne Aisha tayi mata sha'awan musulunci, nuna mata tayi bata da
ra'ayi. Don haka babu wanda ya matsa mata akan hakan.

Joy ta samu kwanciyan hankali don haka ta'kara wani mugun kyau.

Samari ko sai dai bata fita ba, ko kallo basu ishe taba, sabgan gaban ta kawai
take, a haka har ta kammala bautan 'kasan ta cikin kwanciyan hankali.

Don haka sai ta fara zancen aiki babu 'bata lokaci Abdurrahaman ya nema mata aiki a
wani aisibiti babba ta fara tafiya.

Aisha taso itama ya samun mata, amma yace shi bai da shi'awan iyalen sa da aiki
kome take so ta fad'a masa zai mata.

Don haka sai ta bu'kaci jari, bai ko jah ba ya bata ta fara kasuwanci.

Watarana Aisha da mijin ta na zaune ranan weekend ne har Joy na gida, Africa TV3
suke kallo su biyu sai ga Joy ta fito, shirin yara ake a lokacin.

Zama tayi cike da shi'awan yaro d'an 'karami dake karatun al'qur'ani mai girma.

Murmushi kawai take, bata tashi ba har sai da aka cire shirin.

Tun daga wanna ranan shirin nan bai wuce ta. Yawan kallon shirin yasa taji tana
matu'kar son musulunci don tana shi'awan itama ta iya karatun al'qur'ani.

Rana tsaka ta samu Aisha har cikin d'akin ta lokacin Abdul bashi ya tafi wurin aiki
ita kuma night duty take da.

"Besty har kin tashi?" tace da ita lokacin da take shigowa.

Bata bata ansa ba illah 'karisowa da tayi ta zauna kusa da ita fuskan ta d'auke da
murmushi.

Ri'ko hannun ta tayi tare da cewa" Aisha inason na musulunta" daga haka ta tsuke
bakin ta.

Waro ido Aisha tayi tare da cewa cikin tsantsan farin ciki" da gaske my besty?"
d'aga mata kai tayi.

Don haka Aisha ta rugume ta cikin tsantsan farin ciki, har da hawayen ta.

Babu 'bata lokaci Aisha ta kira mijin ta ta sanar masa, babu 'bata lokaci yace suje
wurin limamin anguwan su.

Koda sukaje ba'a wani 'bata lokaci ba ta'kar'bi musulunci.

Aisha ta za'ban mata Suna Fatima, wani irin natsuwa da kwanciyan hankali taji yana
wanzuwa a gare ta.

Ga wani irin farin ciki da takeji.

Fatima wanda suke kira da (Zarah) tana d'aukan abuabuwan addinin musulunci da ake
koya mata fiye da tunanin ku.
Babu abinda tafiso a ciki rin Qur'ani, don haka ta mai da hankali sosai tana koya,
saboda 'kwa'kwa da kuma son abun.

Cikin wata hud'u tayi sauka, zo kaga murna da farin ciki wurin ta da uwan uba
Aisha, don haka gaga rumin walima aka shirya mata.

Sai dai abinka da boko da kuma ansaba shigan 'kananun kaya nana sai ma wanda ya
'karu sai dai na d'an d'aura 'karamin mayafi.

***************

Fatima mai farin jinine tun tuni balle ta musulunta don haka abin sai ya 'karu.

Maza da mata kowa nason ta kulasa tayi mu'amala da ita.

A haka ne tayi wata 'kawa a ma'kotan su mai suna Husna, Husna yarinyan nacin
masifa. Kad'aci ke damun ta, da yake basu dad'e da tare wa ba. Kuma su biyu ne
kawai 'ya'yan gidan daga ita sai wanta, da wannan dalilin yasa take shige-shigen
ma'kota. Shine Allah ya had'a ta da Fatima taji ta Shiva ranata, sai ta maida gidan
su faty ma kamar nasu tai ta shige mata. tun Fatima na 'kalleta har sai da yazo
suka fara 'kawance domin sam bata da zuciya.

Tana zuwa gidan su Zarah sosai, amma ita dai-dai da rana d'aya bata ta'ba shiga
gidan nasu ba.

••••••••••••••••••••••

"Don Allah ki rakani yau mana" cewa Husna suna zaune kan gadon Zarah bayan sun gama
cin abinci.

"Kiyi ha'kuri gaskiya babu inda zani" cewar Zarah.

"Haba Zarah kullum nazo miki da bu'katata sai ki 'kimin, bansan mai yasa kike min
haka ba. Wallahi ba kyau wula'kanci, har yanzu kin'ki sakin jikin ki dani. Wallahi
Faty ina matu'kar 'kaunar ki har cikin raina, keko kin'ki sani a zuciyar ki ko
kad'an".

"Meyasa? wallahi hakan bai dace ba".

" Allah baki ha'kuri tunda baki sona baki aminta dani ba nayi nan nagaji haka,
kullum ni kenan nan nai ta bibbiyan ki kamar wata sarki to nagaji ba dole 'kawance"
tace cikin fushi tare da mi'kewa idon ta cike da hawaye don tana matu'kar 'kaunar
Zarah.

Amma ga dukan alamu ita bata son mu'amalan su.

Kamo hannun ta tayi tare da cewa" idan ba zamu dad'eba muje don inason naje wurin
aiki 2pm dai-dai".

Dawo wa tayi tare da rungume ta tana maijin farin ciki.

"Ki muje idan ba haka ba na fasa".

" A'a muje hajiya ta mai ajin tsiya sai har dani za'a rin'kama wa?, gidan su
hayati zani Maman sa ke nemana kinsan biki ya taso sauran sati uku, zani na kur'bi
tsumi, kai matan nan Allah ya samata son d'an nan kamar shikenan mata".

"Bata gajiya sam wurin gyrani yanzu haka sati mai zuwa zamu India a min gyara na
musamman, wanna kuma yayar sace ta d'au nauyi".

Ta'ba baki nayi tare da cewa" muje ni kada 'batan lokaci na'ki zuwa kimin kuka".

"Don idan na biye miki takan mutumin da bai San kinayi ba zamu iya kaiwa dare".

" Wallahi ni har mamaki kike bani ace wai macce kamar ke ki mutum ma mutumn da Sam
bai ra'ayin ki, wallahi ko shine autan maza sai haka" ta 'karisa tare da sakin
tsaki.

"'Karin kayan takaicin bai zuwa sai dai ke kije gidan su ku zanta, anya wannan
auren za'a sami kwanciyan hankali kuwa?"

Murmushi mai ciwo Husna tayi tare da cewa" baza ki gane ba yarinya gayen ya had'u,
yadda kika san ba mutum ba saboda kyau, ni tunda uwata ta haifeni ban ta'ba ganin
kyakkyawan mutum irin saba".

"Oh really?"

"Allah kuwa idan kika gansa zaki ce na gaya miki, don gayen 'karshe ne".

Ta'ba baki tayi tare da girgiza kai ina mama kin ta, sai tace" muje fah kada na
'bata lokaci kije ki fasa rakani".

Fito wa daga cikin d'akin Joy sukayi suka mufi na Aisha kwance take tana duba wani
littafin.

Sallaman su yasa ta kauda fuska daga littafin tare da zuba musu ido tana mai ansa
musu sallaman.

Tashi tayi daga kwancen tana mai cewa" sai ina kuma 'yan mata?"

Husna tace" anty Aisha zata rakani wuse ne gidan 'kawar momy".

"Hummmm kice dai gidan siri kan mu" murmushi kawai tayi tare da cewa" sai mun
dawo".

"Besty baki sallameni ba" cewar Aisha ganin Husna ta jata zasu bar d'akin.

Murmushin ta mai burgewa ta jefe ta dashi tare da cewa" sai mun dawo to" daga haka
suka bar d'akin, ita kuma ta bisu da addu'a dawo wa lafia.

A compound d'in gidan suka tsaya Zarah tace" jeki d'ako motar ki ina jiran ki a
nan".

Shagwa'be fuskan ta tayi tare da cewa" don Allah my Zarah yau mu fita a sabon motar
can ta'ki".

Hararan ta tayi tare da cewa" na'ki" marairai ce mata tayi, ba don taso ba haka
tasa aka fito mata da motar suka Shiga.

Tare da barin gidan, bata son hawa motar ne saboda wani saurayin ta mai nacin tsiya
ya sayo mata.

Motar babu 'karya ta had'u.

Husna ke driving d'in sai faman santin motar take.

Wani tamfareren gida suka shiga, parking Husna tayi Tare da kallon Zarah tace"
Zarahty ya kikaga gidan surukan nawa?" don taga tun daga get d'in gidan take kallo
har suka shigo gidan.

Yatsina fuska tayi tare da cewa" gidan yayi".

"Muje to" tace tare da 'ko'karin fita daga cikin motan.

Rufe motar Suka yi tare da shiga ciki, sallama sukayi a bakin 'kofan babban falon
gidan, shiru babu ansa.

Don haka suka shiga daga ciki, part d'in mami suka nufa, a nan suka tadda mamin.
sallama sukayi ta ansa fuskan ta d'auke da fara'a.

Shiga sukayi har gaban ta suka gaida ta, ta ansa idon ta nakan Zarah da tunda ta
gan ta taji wani irin fad'uwan gaba.

Idon ta nakan Zarah tace " Husna 'kawar kice wannan?"

"Eh mami" tana murmushi tare da kallon Zarah taga kanta a 'kasa kamar wata muna
fuka.
Mami tace" sannu ko" take ce da Zarah.

Ansawa tayi sai mamin tace" tashi ku zauna a cushion mana, nasha gaya miki Husna
kibar irin haka bakiji".

Tashi sukayi Husna na murmushi tace" Allah huci zuciyar mamin mu baza mu'kara ba".

"Allah sa, ya momyn naki?"

"Tana nan lafia qlau, tace a gai daki".

" Masha Allah, bari a kawo muku abinci" .

"Mami mun 'koshi" mamin tace tana hararan ta" dama nace baki 'koshi bane? kullum
dama ke a 'koshe kike zuwa gidan iyayen naki".

"To yau sai kinci" tace tana 'ko'karin mi'kewa. Cikin murya mai dad'in amo da
sauraro cike da natsuwa Zarah tace" mun 'koshi mami, don abinci muka gamaci muka
fito".

Gaban mami ne ya sake fad'i dajin wannan muryan, tsayawa tayi cak tare da waigo wa
tana kallon gefen da Zarahn take.

Had'a ido sukayi still fad'uwan gaba ne, murmushin ya'ke mami ta sakin mata tare
gyara zama.

"Husna amma 'kawar nan naki ba 'yar nan bace ko?"

Murmushi Husna tayi tare da cewa" 'yar nasarawa ce, amma tana zaune a ne a garin
nan".

"Oh sannu" tace da Zarah.

Ansawa tayi dai-dai nan RAHAMA ta shigo Auwal a bayan ta da sallama d'auke a bakin
su.

Amma na RAHAMA ne ya fito, na Auwal kuwa sai idan ka kalli bakin sane zaka gane
yayi sallama.

'Karisowa inda su mamin ke zaune tayi, shiko dodon mutane tsayawa yayi daga bakin
'kofar shigowa yana mai cewa" mami mun dawo zan tafi office sai na dawo" daga haka
ya juya.

RAHAMA ko zama tayi tare da cewa" wassh mami nagaji walla............" bata samu
zarafin 'karisawa ba sakamakon fuskan Zarah da tagani.

Idon ta da 'kwallan da ya taru cikin sakonni tace" mami kina ganin abinda nake
ganin kuwa?"

Mami tasan me take magana akai amma tayi mata shiru.

Taso wa tayi tazo ta dur'kusa kusa da mami tare da kamo hannun ta tana mata nuni da
Zarah tace" mami anty ce fah nake ganin, sai dai kuma jikin ta ya nuna na yara ne,
dama idan ka mutu ka dawo yaro kake koma wa?"

Shirun mami yasa tace lokacin hawaye ya fara zuba" mami anty ce ko?... Itace ta
dawo gare muko? dama ina mafarkin ta mami bata mutum ba, kullum haka take gaya min
a mafarki, tana cemin zata dawo. Zata dawo ta rayu da Auwal d'in ta ".

" Mami taso, taso" tace tana janta, fizge hannun ta tayi tare da cewa cikin tsawa"
RAHAMA ba ita bace, kina haukane? a ina kika ta'ba ganin mutum ya mutu ya dawo?
Kuma ma idan itace sai tazama yarinya? kin manta tana da d'an da ya isa aure da
yayi da wuri idan Allah ya albarkaci auren da yaran sa biyar ko hud'u".

"Idan kina mafarki ne ki farka don ba ita bace" mami ta 'karisa idon ta na zubar da
hawaye .

Tun da suka fara zancen su tsoro ya shigi Zarah, don haka mi'kewa tayi ba tare da
ta kalli inda Husna take ba zata fita.

RAHAMA tace" mami kalli zata gudu anty don Allah ki dawo kada ki barmu muna
tsananin bu'katar ki.. Munyi kewan ki sosai. Ga habibin ki zaiyi aure kinga ga
matar da zai aura nan, Husna jeki, jeki ga mahaifiyar mijin ki can".

Kan Husna ya 'kulle shiru tayi tana binsu da kallon musamman ma RAHAMA da take
tunanin ta haukace.

Mami ne ta tsinke RAHAMA da wani uban mari mai zafi tace" ki farka RAHAMA ba ita
bace, wannan da kika gani tare da Husna suka zo. 'Kawar tace".

Marin ya shige ta sosai, natsuwa tayi tana sauraron mami da ta cigaba da cewa" kama
ne RAHAMA, ba'a mutuwa a dawo".

Matso wa tayi kusa da mamin tare da rungume ta, ta fashe da matsanancin kuka.

Rarrashin ta mami ta kamayi ta dad'e tana rarrashi kafin ta fara a jiyan zuciya.

Mi'kewa Husna tayi tabi Zarah da tai gaba, koda ta fito bata kuma ga motar ta a
ajiye.

Shiga motor tayi ta fad'a tare da barin gidan.......

Inason idan nayi kuskure fan's d'ina su gaya mini, nayi kuskure a page d'in baya,
wata tamin magana ta PC kuma naji dad'in hakan sosai, don har ga Allah na sani
kuskure ne aka samu.
Kuskure kuwa shine da nace bayan kakan Auwal namiji da matar sa ta mutu kakan sa na
wurin uwan ya kar'bi jaririn da matar abokin sa ta haifa ya bama matar sa ta had'a
ta shayar dash tare da jaririn ta da suka haihu tare, to kunga idan ta shayar dashi
babu aure a tsakanin 'ya'yan su don addini ya haram ta hakan, sorry to sai ba haka
naso rubutawa ba akasi aka samu. Madara ta basa ba nono ba.

Don gara, kuskure ko shawara👉🏻08105039568 'kofa a bud'e take ngd, and mata kawai.

*COMMENTS*
*&*
*SHARE*
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*

*we are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all.........DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

4⃣1⃣4⃣2⃣
4⃣1⃣4⃣2⃣
1⃣4⃣2⃣
➡4⃣ 4⃣
4⃣2⃣
4⃣1⃣
2⃣

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Tafiya nake ba tare da sanin inda nake jefa 'kafata ba. jefa 'kafa kawai nake. Har
na kusa barin layin sai ga Husna, parking tayi tare da fitowa daga cikin motan,
bata ce dani komai ba illah jan hannun na da tayi. Bata saken hannun ba har sai da
ta danganani da motar, zaunar dani tayi tare da rufe sead d'in ta zagayo mazau nin
ta ta shiga tare dawa mota key muka bar wurin.

Tafiya muke babu maice da kowa komai, don kowa na fama da tulun tunanin a cikin
ransa.

Har muka zo gida tai parking, sake jana tayi ta fito dani tare da shigewa dani
cikin gida, niko binta kawai nake kamar ra'kumi da akala.

Babu kowa a falon, don haka d'aki na tayi dani, zaunar dani tayi a gefen gado tare
da barin d'akin ba tare da tace dani komai ba.

Niko ina nan zaune inda ta barni har na tsahon wani lokaci, tunanin nake shin ma
wai meye asalina?, waye ubana?, ina dangin mamana da na babana suke?

Anya ma 'yar halasace ni?


Tun da nake tunanin hakan bai ta'ba zomin ba sai yau, kuma mama bata ta'ba bani
labarin wani nawa ba. Don haka yau ina da bu'katan son sanin meye asalina?

Farko ma dai waye ubana?, ban ta'ba tambaya ba tunda nake, don na taso na ganni
tare da uwata ce kawai.

Ban ta'ba ganin wani yazo wajen ta da sunan d'an uwan ta kona babana ba.

Kai anya kuwa? da dai sake, da kawai alaman tambaya.

Dagani sai ita kawai, babu dangi ko guda d'aya.

Akwai sanda aka ta'ba min gorin asali amma ko kad'an banji wani abu akan haka ba.

Don da naji wani abu dana tunkari mama da maganan tun a lokacin, da yake lokacin
bansan ciwon kaina ba.

Na d'au lokaci mai tsayi ina ta faman tunanin da zancen zucci, wanda har kaina ya
fara min ciwo.

Tashi nayi na shiga toilet tare da sakin ma kaina ruwa, hakan yasa naji d'an sanyi
kad'an.

Don haka sai na fito bayan na cire kayan jiki na tare da d'aura towel a jiki na.

Goge jikin nayi ba tare dana shafa komai ba na bud'e wardrop na d'au dogon riga
mara nauyi nasa .

Kwanciyan nayi tare da cigaba da tunani na.

A haka barci ya d'auke ni, ranan na manta da zancen wani office.

Don duk ringing d'in da waya ta take tayi banji ba Sam.

Bani na tashi ba sai bayan la'asar, kuma ma Aisha ce ta shigo ta tasheni.

Mi'ka nayi da sallati, sa'annan nayi addu'an tashi daga barci tare da kallon Aisha
itama ni take kallo.
Murmushi tayi min tare da cewa" yaushe kuka dawo?" ya mutsa fuska nayi tare da
cewa" d'azu".

"Shine koki fad'an kin dawo? ina can inta faman tunanin har yanzu baku dawo ba.
Tunanin zuwa d'akin nan nayi shine na shigo na cima kina barci, gashi la'asar ta
wuce bakiyi salla ba. Sai ki hanzar ta".

Sauke 'kafafuna nayi a 'kasa ba tare da nace da ita komai ba.

Toilet na nufa, wanka nayi tare da d'aura alwallah na fito.

Tana nan zaune inda na barta a bakin gado, wuce wa nayi na d'akko wani dogon riga
ba'ki na zirah tare da saka hijabi.

Shimfid'a dadduma nayi tare da fara sallah, cikin natsuwa take komai nata.

A haka ta gaba tar da sallan azahar da la'asar, duk Aisha na kallon ta har ta idah
tayi addu'a.

Bayan ta gama sai ta jingina kanta a jikin gado tare da rintse ido, hawaye taji
yana son zubo mata matsewa tayi batai ba.

Sakkowa daga gado Aisha tayi tare da zama kusa da Zarah dafa ta tayi tare da cewa"
besty meke damun ki?"

Shiru tayi bata bata ansa ba, "besty ina magana kinmin shiru".

"Mai ya faru?" bud'e runannun idanun ta tayi. Kallon Aisha tayi tare da cewa" babu
komai".

Ganin yadda idanuwan nata suka rine ya'kara tayar ma Aisha da hankali, don haka.

Cikin lallashi Aisha tace" yanzu bazaki sanar min da damuwan kiba ko? haba my
Zarah, don Allah gaya min, ni kad'ai kike da duk fad'in garin nan, idan baki gayan
ba waza ki fad'a mawa? idan kuma so kike nai kuka kuma shikenan ".

Ta'karisa tana majin damuwa a zuciyar ta.

" Aisha kin ta'ba ganin baba na? kin sanshi? ko kin ta'ba jin labarin sa? wai ma
anya ina da uba?" tace hawaye na zubowa daga cikin idanun ta.

Sakin baki Aisha tayi da mamaki tana kallon ta har ta idah zancen ta.
Tace" wani shegen yace baki da uba? eyeh!" .

"Waye? nace waye?" Aisha tace cikin masifah.

Kamo hannun ta nayi tare da cewa" ba kowa, babu wanda yace bani da uba. Nine nace
ma kaina, domin ban ta'ba ganin uban nawa ba, ban kuma san asalina ba shiyyasa nace
haka".

"'Karya kike akwai dalilin da yasa kika ce haka ban yadda da abinda kikace ba, idan
kince haka mai yasa tuntuni baki ta'ba zancen nan ba sai yau da rana tsaka?"

"Husna ce tamiki gorin uba ko kuma wani matsiyaci ne?"

Murmushi nayi tare da cewa" nace miki babu kowa, wallahi babu wanda ya tambayeni
ubana".

Ganin ta'ki yadda da zancen tane yasa ta kwashe abinda ya faru a gidan su surukan
Aisha ta fad'a mata, ta'kara da cewa" Allah jikina na bani inada ala'ka dasu".

Shiru Aisha tayi don bata san mai zatace ba.

Don gaskiya bata san mahaifina ba, don 'kawayen ta na 'kauye sunsha ai bantani a
gaban ta bata ko kulasu sunsha cewa ta rabu dani donni shegiyace bani da uba.

Don iyayen su sunce da ciki uwan na tazo garin ita da wata 'kawanta kuma bata wani
jima ba ta haifeni, ana tunanin tayi cikin shegene iyayen ta suka koro ta.

To me zata ce?

Ganin Aisha tayi shiru yasa tace" gobe zan tafi keffi insha Allah, don inason nayi
magana da mama ina son sani ni wacece? meye asalina? tun kafin lokaci ya kuremin".

Numfashi Aisha ta sauke tare da cewa" Allah kaimu, idan Hubby ya dawo sai na mai
magana idan yaso sai mu tafi tare".

Gyad'a mata kai tayi ba tare da tace komai ba.

Zama sukayi shiru-shiru babu mai magana a cikin su, kowa tunani ne fal a zuciyar
sa.

**********
Husna bayan tabar gidan su Zarah gidan su ta shiga, zuwa tayi har d'akin momyn ta
ta same ta.

Momyn nace da ita" har kun dawo?" ita kuma nace da momyn" momy dama ba Hajiya
MARYAM bane ta haifi Auwal? "

Da mamaki uwan ke kallon ta, sai tayi murmushi tare da cewa" ba ita bace ko momy?"

"Injiwa ya fad'a miki haka dan ubanki?"

"Su da kansu".

" Da kansu kamar ya?" tace fuskan ta cike da mamaki.

Nan Husna ta kwashe abinda ya faru tasanar mata.

"Eh hakane ba itace ta haifesa ba".

" To momy waye mahaifiyar sa?"

"'Kanwan MARYAM d'in Balki itace ta haifesa, yayin da 'kanin mijin MARYAM d'in
yanka sance shine uban Auwal d'in".

" To ina suke momy?"

"Bakiji mai RAHAMA take cewa ba? koke da'ki'kiya ce? to ta rasu tun Auwal na
jariri".

" To mahaifin nasa fah?"

"Ke ubanki tashi ni duk kin isheni da tambaya, maza bar nan wurin".

Cikin sanyin jiki ta tashi tabar wurin.

'Dakin ta dake kusa dana momyn ta ta bud'e ta shiga, zubewa tayi a kan cushion tare
da buga uban ta fumi.

Tace" meye al'kansu da Zarah? tabbas akwai dangan taka na jini a tsakanin su, domin
ban ta'ba lura ba sai yau akwai kama a tsakanin Zarah da Auwal kama ma na'kin
'karawa. Sai dai tafi Auwal hasken fata, shi kuma ya fita kyau".

"Tabbas akwai cakwakiya".............


*************

Bayan natsuwa ya zoma RAHAMA ne sai tace da mami cikin sanyin murya" mami anya
kamace kawai tsakanin anty da yarinyan nan babu wani abu ba bayan shi?"

"RAHAMA kibar maganan, domin bamu da wani al'ka da yarinyan nan, domin daga jihar
nasarawa ta fito kuma bamu da kowa namu dake can. Ikon Allah ne kawai" daga haka
tayi shiru.

RAHAMA dai bata wani gamsu ba tace" anya kuwa mami? a dai bincika, don wannan kaman
ya wuce misali".

Shiru mami tayi ba tace komai ba.

Ganin haka yasa itama RAHAMA tayi shiru.

***********

Abdul bai dawo ba sai wurin 'karfe shida da rabi, don sai da yayi sallan magariba
sa'annan ya shigo cikin gidan.

Zaune ya taddasu jigum jigum, da mamaki yabisu da kallo dukan su, da alamu ma
basuji sallaman saba.

Ta'ba kafad'an Aisha yayi firgigif ta dawo duniyar mu, kallon sa tayi tare da
mi'kewa had'e da murmushin ya'ke tace" hubby sannu da zuwa".

Bai ansa mata ba sai ma cigaba da kallon ta da yake famanyi.

Shagwa'be fuska tayi tare da cewa" hubby ina magana kamin banza".

Kamo hannun ta yayi suka nufi cikin d'aki, har lokacin Zarah bata dawo ba ita, ta
tafi can duniyar tunani.

Koda suka shiga d'aki zaunar da ita yayi akan sofa shi kuma ya du'ka a gaban ta
tare da kallon cikin idan uwan ta yace" maike damun matana da har zan shigo bata
san na shigo ba?"

Hawaye ne ya zubo mata, zaro ido yayi tare da tara hannun sa hawaye na d'iga a
ciki.

Yace" My Esha lafia kike min asaran hawayen ki?"


Kwantowa tayi kansa tare da cewa" don Allah hubby kada ka matsamin na san sani
abinda ke damuna, domin sirrin besty nane. and gobe tace zata keffi don Allah kamin
izini muje tare".

Numfashi ya sauke tare da cewa" shikenan amma don Allah abar kukan nan, a rage
damuwa don za'a shiga ha'kina gaskiya ".

" sannan magana tafiya Ku bari sai jibi Saturday sai na kaiku".

Cikin murna takai masa sumbata a goshi daga nan ta taimaka masa yayi wanka suka
fito cin abinci.

Kwana biyu nan Zarah tayi sane cikin za'kuwa da damuwa kai har da fargaba ma.

Ranan da zasu tafi ta riga kowa shiryawa.

Bayan sun kintsa suka d'auko hanya....................

*COMMENTS*
*&*
*SHARE*
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*

*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*

*we are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among
all.........DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*

*Dedicated to my lovely fan's*


*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

4⃣3⃣4⃣4⃣
4⃣3⃣4⃣4⃣
3⃣4⃣4⃣
➡4⃣ 4⃣
4⃣4⃣
4⃣3⃣
4⃣

12:40pm yayi musu a 'kofar get d'in gidan su Aishan, horn yayi mai gadi ya le'ko.
Da sauri ya koma ya bud'e suka shiga.

Parking yayi Zarah ta fita daga cikin motan tabar Aisha, part d'in su ta nufa.

Zaune ta tarar da maman ta a cikin palo tana kallo tashan su na arna.

Jin motsin mutum yasa madam Gloria wai gowa, ganin Joy cikin wani irin yanayi kuma
a baza ta yasa ta mi'ke tare da nufo ta.

Rungume uwan tayi tare da fashewa da matsanancin kuka.

Shafa bayan ta tayi alaman rarrashi har na tsahon wani lokaci, sa'an nan ta d'ago
ta tare da cewa" mai ya farune Joy? lafia kuwa?" a lokaci d'aya ta jefo mata
wad'an nan tambayoyin.

Kallon uwan tayi face to face tace" mama waye ubana?"

Kallon ta tayi da mamaki kwance akan fuskan ta tace" wani abu ya farune?"

Bata nata ansan taba ta sake cewa" nace waye ubana? yana ina? don ina bu'katan
mahaifina a halin yanzu. Inason sanin dangina".

Kauda kai madam Gloria tayi tare da cewa" ya rasu".

"Ya rasu fa kikace? to naji ina 'yan uwan sa? ko nace dangin sa?"

Tace" bansan inda suke ba".

"Wani irin magana ne wannan mama, anya kuwa taya ma hakan zai kasance?, hakan ba
mai yuwuwa bane".

" Mama banson wani 'boye 'boye nazo nan ne saboda inason nasan wacecce ni?"
"Joy nace miki baban ki ya rasu, ya rasu naji bai da 'yan uwane?"

"Eh" tace tana hararan ta, kallon uwan tayi na tsahon wani lokaci tana nazarin ta.

Can ta jefo mata wani tambayan tace" mama ina iyayen ki suke? tunda baki san na
mahaifina ba ".

" Bani da" tace cikin masifa tare da cewa" banson ki sake min wani magana anan haka
kuma ya isa".

"Bai isa ba mama, ko dai cikin shege kikayi kika haifeni ya raboki da iyayen ki?".

Hawaye ne ya fara kwaranya akan fuskan mama.

Cikin ihu tace" mama ba kuka nake da bu'kata ba, sanin ko wacecce ni nada matu'kar
mahimmamci, kodai daga sama na fad'o?"

Mari uwan ta wanke ta dashi tare da cewa" ya isah, ya isa, haka Joy ".

Tana ri'ke da kuma tunta tace cikin d'aga murya" bai isaba, ba kuma zai ta'ba isaba
waye ni mama? ki fad'a min koni wacecce ke ko cikin shegene kikayi ki sanar dani".

"Joy ni kike ma magana na rashin kunya? am your mom fah?"

"Nasani ai, nasan koke wacecce amma bansan waye ubana ba, to a fad'a minin ko nakai
'kara".

" Joy nice fah? kalli kiga mom d'in kice fah" tace tana mai juyo da Joy d'in tana
fuskan tan ta.

Zarah tace" na sani nasan kece uwata shiyasa nake tambayan ki ubana, don bai yuwuwa
macce tayi ma kanta ciki ba tare da namiji ba".

"Da namiji ake had'u a samar da ciki, mama ina ubana, d'an uwan mu'amalan ki?"

"Kada ki damu sanar dani bazan miki komai ba, ko shi kan shi kawai dai inason sanin
shine, idan bashi ai yana da 'yan uwa. To sanar dani ina suke?"

Kuka mama ta fashe dashi mai tsanani, niko idona ya rufe bai dameni ba, don babu
abinda nakeso a halin yanzu ko ta halin 'ka'ka.
Cikin kuka ta fara zaiyano minin da asalin ta har zuwa auren ta da babana da kuma
sa'kon rasuwan sa da ta samu da kuma yadda sukayi da iyayen ta har tabar garin ta
(idan baku manta ba na baku labarin maman Joy tun a farkon labarin).

Kuka suke dukan su babu mai lallashin wani, sun dad'e suna kuka kafin Zarah ta
tsaigai ta tare da cewa" mama yanzu tunda kike dashi bai ta'ba gaya miki garin
suba? ko wani nasa guda d'aya baki sani ba?"

Shiru tayi tana tunani kafin ta nisa tace" bai ta'ba gaya min ba, don a wani
masallaci a Abia aka d'aura mana aure" .

Bata hakurin abinda namata nayi bayan hankali ya natsu.

A nan ne nake sanar mata da cewa na musulunta, bata wani damu da hakan ba tunda
ubana ma musulmi ne.

*****

Aisha bayan fitan Zarah ta bita da kallo tare da girgiza kai idanun ta cike da
'kallah.

Dawo da idanun ta tayi kan mijin ta taga ita yake kallo.

Ganin tana son yin kuka yasa ya girgiza mata kai, had'iye kukan tayi tare da cewa"
muje ciki to?" fita sukayi daga cikin motan tare da nufan part d'in Umman Aisha.

Sallama sukayi a bakin 'kofan shiga falon, aka ansa musu, ba kowa bane illah
Muhusin dake zaune yana home work, shigo wa sukayi yana arab da fuskan sister d'in
shi ya taso da gudu yazo ya rungume ta.

Tare da cewa" oyoyo anty Aisha? " murmushi tayi tare da cewa" sannu yaron Umma ina
umman?"

"Tana ciki" yace tare da kallon Abdul yace" sannu da zuwa yaya Abdul".

Hararan wasa ya jefa masa tare da cewa" ban ansawa, sai yanzu ka ganni?"

Murmushi yayi tare da sunkuyar da kai yace" yi ha'kuri yaya".

"Nayi to oyah zo" zuwa kusa dashi yayi ya rungume sa tare da masa yadda yaga Aisha
tayi.
Dariya Aisha tayi tare da cewa" bari naje na kira Umman".

"Barta bari naje na d'an huta yanzu haka barci take kada a taso ta".

" Yauwa hubby ka amince mu kwanan ko?"

"To basai kisa na amincen ba, komin dare yau zamu koma tunda kuka taso tafiyan da
ba'a shirya ba".

Yace yana hararan ta, murmushi tayi tare da cewa" Allah baka ha'kuri mijin Aisha to
muje na rakaka".

"Barshi na hutar dake, maza kuyi abinda zakuyi saboda mu koma da wuri".

" To" tace dashi tana tsaye har yabar falon sannan taja hannun Muhusin sukayi ciki.

Sallama sukayi a bakin kofan Umma ta ansa musu, shiga sukayi.

"A'a wa nake gani kamar Aisha na?" turi baki tayi tare da cewa" waye to Umma idan
bani d'in ba?"

Murmushi tayi tare da cewa" maraba da mutan Habuja, lale marhabun da amare".

Murmushi mai 'kayatarwa Aisha tayi tare da nufan inda Umma take tare da zama kusa
da ita.

Tace" ina wuni Umma" "lafia lau, ya kuke?"

"Lafia qalau Umma" "to ya mai gidan naki?"

"Yana lafia, gashi can ma tare mukazo".

"Maraban ku, ina d'ayan amaryan?" cewar Umma cikin sigan tsokana.

'Kwala ya taru mata a idanu fuskan ta ya canza.

"Menene Aisha? ina take?"

"Tana part d'in su, lafia take?" tace kamar za tai kuka" eh".

"Anya kuwa Aisha? nafa sanki musamman akan Joy, yanzu haka wani abu ke damun ta".

" Lafia qalau take Umma, sai dai wani abu dake damun ta shine mukazo mama ta fad'a
ma".

"Kuma ma ta musulunta yanzu Fatima take muna cema ta Zarah".

Washe baki Umma tayi tare da cewa" kai masha Allah, alhamdulillah. Amma nayi mata
murna sosai, Allah kasa maman ta itama ta musulunta ".

" Ameen Umma".

"To meke damun ta kuma?" shiru tayi ba tace komai ba sai ma wasa da yatsun hannun
ta da take.

Ganin haka Umma ta gane bata son sani don haka bata matsa mata ba sai ma cewa da
tayi" Allah ya yaye mata damuwan to".

"Ameen Umma" tace cikin sanyin murya.

"Tashi kije ki kaima mijin ki ruwa da abinci".

Tace" yaje ya dawo" da mamaki Umma tace" yaje ya dawo kamar ya? daga zuwa kuma ko
ruwa bai shaba, ki barsa ya fita amma dai babu hankali a lamarin ki".

"Sai ki kirasa a waya kice yazo yaci abinci".

" To Umma" tace tare da ciro waya a cikin jakan ta.

Koda ta kira sanar mata yayi bashi a kusa, don haka sai ta fad'a ma Umma, Umman
tayi mata fad'an kada ta sake haka.

******

2:10pm Zarah ta shigo part d'in su Aisha ita da maman ta, Zarah ta gaida Umma.
Aisha ta gaida maman Zarah.

Sai suka kama fira kuma, suna firan ne Abdul suka shigo tare da baban Aisha da yake
Umma ta kirasa to ya dawo kenan shima Abdul ya dawo suka had'u a compound d'in
gidan shine suka shigo tare.

Gaishe da su Umma yayi cikin girmama wa, su Zarah suka gaida baba.

Daga nan baba yayi musu nasiha na zama lafia da ha'kuri da juna.

Daga nan sai Abdul yace bayan baba ya sallame su" idan kun gama ina jiran ku saboda
kada muyi dare" daga haka yayi musu sallama suka ya fita.
Yana fita yasa mai gadi shigo musu da kayan abinci ya kira Aisha ya'kara musu da
kud'i, albarka suka sa masa sosai sa'anan suka mai godiya.

Basu suka bar gida ba sai da sukayi sallan la'asar sannan suka d'auki hanya.

********

Saura sati biyu bikin Husna aiki yama Zarah yawa ga shirye-shiryen biki ga aikin
office, haka take ta fama, komai za'a sai Husna ta nemo ta. Tsare-tsaren biki itace
kan gaba.

Anfara gudanar da biki tun biki ya rage saura sati d'aya, yau wannan bidi'an gobe
wancan.

Kuma har yau Zarah bata ga ango yazo ba, daga 'kawayen amarya sai abokan ango aketa
gudanar da abubuwa.

Da kyau dinner da za'ayi ana gobe biki bayan walima, sai Husna ta shiga damuwa na
rashin halattan ango duk wurin shagulgulan biki, ta kuma gaji da tambayan da
'kawaye suke mata na rashin ganin angon, tun tana 'karya yanzu haka 'karyan ya
'kare kuma a rasa mai zata ce dasu.

Zaune take jugum a cikin d'akin Zarah ta buga uban ta gumi, har Zarah ta shigo bata
san ta shigo ba.

Zuwa kusa da ita Zarahn tayi ta zauna tare da dafa ta.

Waigo wa tayi jin an ta'ba ta, ganin Zarah ne yasa ta rungume ta tare da fashewa da
kuka.

Bubbuga mata baya Zarah tayi tare da cewa" lafia Husna? mai ya faru? mai akai
miki?"

Cikin kuka tace" Zarah Auwal bai sona, da da yadda zanyi dana cireshi a cikin raina
na huta. Zarah ina tsananin 'kaunar sa".

"Ni kad'ai nake haukata tunda aka fara shirin bikin nan, dai-dai da sau d'aya ya'ki
halattan biki ko guda d'aya da aka gudanar. Gashi a halin yanzu 'karyana ya 'kare".

" Ya zanyi Zarah? ki gayamin, gashi anjima za'ai dinner ban san yadda zanyi yai
attending ba".

Tace tana mai fashewa da matsanancin kuka.


Itama yanzu Zarah ta fara jin haushin abinda angon nan yake, mai yake ta'kama
dashi?

Mai yasa baison Husna? Husna yarinya ce kyakkyawa, fara doguwa ga hanci ga zarara
zaran yatsu, idanu.

Jiki ma masha Allah komai akwai, babu abinda tarasa na wanda d'ana miji yake so.

Uwa uba ilimi boko da na islama.

Ya fara bani haushi inason sanin abinda yake ta'kama dashi.

'Dago Husna daga jikin ta tayi tare da cewa tana mai kallon cikin idan uwan ta
had'e da share mata hawaye.

"Husna tashi muje mu same shi" zaro ido tayi tare da cewa cikin tsoro" gaskiya
bazan iya zuwa ba inajin tsoro gaskiya ".

Tsaki Zarah tayi tare da cewa" tsoro ya kasheki ya kuma kaiki ya baro".

"Tashi dallah muje" tace tana mai jan hannun ta.

Girgiza kai tayi idanun ta cike da hawaye tace" bazan iya ba, ya Auwal bai da
mutunci nemo wani mafitan kawai amma ba wannan ba".

"Kirasa a waya to" tace" ko nakira sa ba zai d'auka ba".

"Bani number wayar sa" tace tana mai d'ako wayar ta.

Karanta mata Husna tayi ita kuma tana rubutawa.

Dialing number tayi, yayi ta ringing ba'a d'au call d'in ba.

Sake kira na biyu tayi sai da ya kusa tsinkewa sannan aka d'aga amma ba ai magana
ba.

"Hello!" Zarah tace.

Zaune yake zumbur ya mi'ke tare da cewa" my baby, my


Joyyyyyyyyyyyyyyyyyy"..................
*COMMENTS*
*&*
*SHARE*

Luv you all my fan's💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋

You might also like