Kufan Wuta..Huguma

Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 325

[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 🔥🔥 *_KUFAN WUTA_* 🔥🔥

Free page 01

*TAFIYA DA GWANI ME DADI*

*ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu sababbin tsararru kuma zafafan
labaransu guda biyar kamar yadda aka saba*

RAYUWAR MACE
rano

NOOR ALB
Mamuhghee

MASARAUTA
miss xoxo

BAK'AR INUWA
Billyn Abdul

KUFAN WUTA
Huguma

Zaku samu gaba daya labaran akan naira

1k kacal
2_400
3_500
4_700

*Zaku saka kudin ta wannan account din*

1487616276
BILKISU IBRAHIM MUSA
ACCESS BANK

*SAI KU TURAWA WANNAN NUMBER SHAIDAR BIYANKU*

09032345899

*KATIN MTN KUMA*

09166221261

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
♀️
_MUJE
‍♀
‍♀

️️♀️
‍ ♀️ ZUWA_♀️
‍ ‍♀
‍♀

️️
♀️
‍ ♀️
‍ 🏃🏾‍
🏃
️ 🏾‍🏃
️ 🏾‍️🏃🏾‍️🏃🏾‍️🏃🏾‍
♀️

Dogon layi ne sosai kamar irin na kowacce unguwa ta masu matsakaicin qarfi,hagu da
dama na layin gida jene a jere na masu matsakaiciyar rayuwa,wadanda basu cika mugun
kyau ba,kamar yadda kuma basuyi lalacewa da rashin kyan gani ba,duk da cewa wani
gidan yafi wani kyau,kamar yadda kowa da irin yadda ubangiji S W T ya tsara masa
matakin rayuwar da zai wanzu a kai.

Yawancin gidajen plate ne masu soraye,masu ginin benen daga cikinsu 'yan
qalilan ne,haka nan gaban gidajen akwai kwata wadda tabi ta kowanne qofar
gida,saidai kuma a rufe take da slap,duk da cewa zakaga daya biyu na wani gurbi da
babu slap din,gurbin dake nuni da cewa cirewa yayi ko karyewa,ko kuma an tsigeshi
ne bisa qarfi da da yaji,da kuma qiriniya irin ta yara,wanda bisa dukkan alamu ma
slap din an hada taro da sisi ne daga mazauna layin an ginashi.

Daga can tsakiyar qarshen layin,wanda zaka iya karya kwana ta shiga dakai
wani layin daban,dandazon yarane a tsaye carko carko sunata hargowa,idan daga nesa
ka taho,zaka iya hangen yadda qura take tashi a wajen,alamu dake nuna cewa fada ake
sosai a wajen.

Idan ka duba tsakiyar wajen sosai,yara ne guda biyu,wadanda gaba dayansu


ba zasu zarta shekara goma ba gaba dayansu,'yar baqar dirarriyar yarinyar nata
qoqarin kada abokiyar fadan nata,wadda idan kayi mata kallon farko ba zaka zaci
zata iya dambe haka da abokiyar fadan nata ba,kasancewar bata kai wancar garin jiki
ba,fara ce ba sol ba,kana iya hangen doguwar sumar kanta me santsi yadda ta debi
qasa da yashi na wajen,sakamakon cirewar danwakalin kanta,baya ga hijabinta data ci
damar dashi tun daga sanda za'a fara fadan.

"Iman.....iman.....ga malam nan" wata yarinya ta qaraso wajen bayan taja


birki tana haki,da alama daga wani sashen ta kwaso gudunta ta kuma tuqe a nan.

Sarai iman din ta jita,saita qara himma da hanzarin ganin ta yar da rahama
kafin malam din ya qaraso,ta tabbatar matuqar bata gama ba ya qaraso fadan yazo
qarshe,hakanan kuma babu makawa itace me laifi a wajen malam din,koda kuwa ta fisu
gaskiya.

Saidai bata kai ga cimma burin nata ba taji tsawar malam din a kanta

Dattijon mutum,wanda a qalla shekarunsa sun tasamma hamsin,sanye da fararen kaya


qal,riga 'yar ciki da wando,sai babbar riga malum malum,kansa sanye da farin
rawani,hannunsa dauke da buzu daya nade wani abu a ciki,daya hannun nasa kuma yana
riqene da baqar leda
"Ke hajaru,kinci gidanku!,saketa nace" Ya fada cikin kaushin murya idanunsa duka
bisa yarinyar.

Tunkude rahama hajar iman tayi,ta duqa tana kwasar takalmanta da dankwalinta
da suka turbude cikin qasa,ranta a bace na rashin samun damar tumurmusa rahama da
batayi ba,dai dai lokacin malam ya waiwaya ga yaran yana musu fada,tare da kora
kowa zuwa gida,bayan ya bude ledar hannunsa ya fidda alewa ya rarraba musu.

"Muje gida ke kuma,'yar qaniya" ya fada yana tasa qeyar iman zuwa gida,suna
tafe yana mata sababi har suka isa qofar daya daga cikin gidajen dake jere a layin.

Tun daga qofar gidan zaka karanci cewa gida ne na makaranta,ma'ana gidan da
ake karantar da almajirai,saboda babbar rumfar kwanon da tabarmi dake malale saman
simintin dake qasan rumfar kwanon,tun daga malalen simintin,tabarmin dake shimfide
din zuwa qasar dake gaban gidan a share wajen yake fesss,kai kace lomar tuwo zata
fadi ka duqa ka dauka abarka kaci saboda tsabar tsabta.

Da hanzari almajiran dake zaune a wajen,wadanda basufi biyar ba suka miqe


"Sannu da zuwa malam" duka suka furta,daya daga cikinsu ya matso yana niyyar karbar
ledar hannun malam din,sai ya dakatar dashi

"Yi zamanka habu....inasu haladu?" Ya jefa tambayar ga daya daga cikin mazauna
wajen,wanda ya fisu girma da wayo
"Basu dawo ba tukunna,amma nasan suna hanya" kai malam din ya jinjina

"Shikenan,ku fara shirin sallar magariba,duk wanda ya dawo kada ya fita,inason


ganinku gaba dayanku"

"To malam" suka amsa masa cikin girmamawa,saiya juya ya saka kai zuwa soron gidan.

Faffadan tsakar gida ne mayalwaci sosai,wanda ke dauke da bishiyar


mangwaro da babu kamarta a unguwar,wata iriyar bishiya da Allah ya sanyawa
albarka,me yawan fidda 'ya'ya masu dadin gaske da kusan kowa yake amfana da ita.

Dakuna biyu ne daga hannun damanka wanda suke falle daya da kuma rumfa da
uwar daki,sai wasu da suke kalloka kana shigowa gidan,suma rumfa da uwar daka ne
gaba dayansu,baya ga wani babban dakin falle daya dake a soron gidan.

Gab da soron gidan anan rijiyar gidan take,ma'abociyar ruwa me kyau da


sanyi,wanda koda da rani ne nata qafewa,anan kusan duka 'yan unguwar ke diban ruwa
idan aka shiga yanayi na rani wanda ake yawan samun qafewar rijiyoyi da kuma
janyewar ruwan famfo,bandakinsu na daga can wani dan sakaye sai kitchen dake taqi
kadan daga dakunansu.

Yadda qofar gidan da sorayenshi suke qal haka cikin gidan yake,komai a
killace cikin tsafta a kuma muhallinsa.

Daga qofar kitchen din wata farar macace zaune saman kujera 'yar
tsugono,sanye da wata jar atamfa data qara ma haskenta kyau,duka duka matar
shekarunta na haihuwa zasuyi arba'in,saidai da alama ita din ma'abociyar tsafta ce
da ado.

Kwando ne a gabanta wanda ke cike da alayyahu tana tsinkewa,baya ga albasa


data gama yankanta tuntuni,cikin sauri sauri take aikin,da alama bata saba kaiwa
dare kamar haka bata gama abincin dare ba.

Sau daya tak ta daga kai ta kalli iman wadda fa shigo tana gursheqen
kuka,tabi takalmanta da ta riqo a hannu saboda tsinkewar da yayi,saita maida kanta
taci gaba da aikinta,kamar ma batasan da wanzuwarta ba,abinda ya sake tunzura iman
din,tayi zaman 'yan bori a waje tana aje takalman nata a gefe,tare da sake bude
muryarta tana sakin kukanta.

Ko dagawa ta sake kallon iman batayi ba,saboda irin wannan koke koken da
rigimar ta banza da wofi ba yau ne farau ba a wajenta,kusan kowa na gidan yasan da
zaman wannan,har zuwa sanda malam yayi sallama ya shigo,sai tayi qoqarin rage
sautin kukan nata,ta hau zazzare idanu.

Da malam din ya kalleta dariya ta bashi,amma saiya danne,ya maida kansa ga


matarsa safiya da ake kira da inna,wanna tuni ta miqe tana masa sannu da zuwa,bayan
ta ajjiye aikin da takeyi ta qaraso ta rusuna ta karbi ledar hannunsa.

"Yanzu ke hajaru.....bakya jin fada kenan ko?" Malam din ya fada yana kama
kunnensa da hannu daya

"Sau nawa zan hanaki fada da yara?,.....ina cewa ko sati ba'ayi ba kukayi fada da
asama'u....naja miki kunne,shine har kin manta?" Tsuru tsuru tayi tana raba
idanu,tsoron yadda malam keta fiddo mata manyan idanunsa irin nata ya shigeta,takan
jima har ma ta manta kafin malam yasa hannunsa ya daketa,duk ranar da ya daketa din
kuwa lallai ba shakka ta qureshi ne.....kuma fa zata ji a jikinta
"Daga yau bazan sake miki magana ba,amma zan saki a mari idan baki wasa ba" ya
qarashe maganar yana sakin kunnen nasa.

Inna da tuni ta koma bisa aikinta tana saurarensu,haushi sosai yake cikata
kan yadda malam din bai iya zagewa ya daki iman sosai kamar yadda takeso,saida
yakan gaya mata cewa,duka baya tarbiyya,kuma bashi ke gyara yaro ba,saidai ya
batashi,nasiha da kuma nusarwa sune suka kamata.

Sannu da gida yayi mata kamar yadda ya saba,yana tambayarta kowa lafiya,ta
amsa masa da lpy qalau,wannan kusan dabi'arsa ce,mutum ne shi managarci,wanda yake
matuqar kula da iyalinsa dama buqatunsu,bakin gwagwadon ikonsa,abinci abinsha da
suttura duka bai yarda sunfi qarfin iyalinsa ba,komai qanqantar abu ya daukewa
gidansa,saidai duk da haka bai hana inna sana'a ba,saboda sanin muhimmancinta ga
diya mace.

Gangarawa malam yayi ya daura alwala,ya maida rawaninsa yana shaidawa innar
zai sake fita,bazai shigo ba sai an idar da sallar isha'i

"A dawo lafiya,Allah ya tsare" tasan ya fadi hakanne don kada ta damu da
rashin gamaabincinta akan kari,shi yasa ya fita ya bata sarari don ta samu ta
kammala a nutse.

Fitar malam din kamar dama jira hajar take ta sake bude baki da sabon
babin kuka,abunda ya qule inna sosai,tayita qoqarin danne zuciyarta don kada ta
kaiwa hajar din hannu,amma ko alamun sassauta kukan hajar batayi ba,abinda ya dinga
tunzura inna kenan,taji babu makawa saita jibgi hajar din sannan zataji
sassauci,don haka ta saki dambun data gama hadawa tana maidashi madambaci hawa na
biyu,ta miqe a fusace.

Malam na gyara hannunsa daga qofar fita daga gidan,yana magana da wani
babban dalibinsa sahabi,ya daga kansa a hankali sanda ya fara jiyo muryoyinsu,duk
kuwa da cewa basu kai ga qarasowa inda yake ba,amma kuma har zuciyarsa ta tafi inda
suke.

Su dinne kuwa,matasan yara su biyu ne tafe,suna jere da juna,dukkaninsu


shekarunsu basu wuce sha bakwai ba,yanayin fuska da kuma yadda suke tafe cikin raha
zai iya sawa mutum yace 'yan biyu ne,saidai kuma kamanni da sukayi matuqar shan
bambam a tsakaninsu zaisa ka gane ba twins din bane.

Matashin farko ya dara dan uwansa fari da haske da kuma tsaho kadan,wanda
idan baka da lura ma babu lallai ka gane hakan,yana da zagayayyar fuska da
madaidaicin hanci mai tudu,siraran labba masu kyau da kwantaccen gashin gira,duk da
cewa akwai sauran shekaru masu tarin yawa a gabansa.....amma kuma sai gashi saje ya
fara fito masa sosai,alamun dake nuni da cewa mutum ne me yawan gargasa,don sumar
kansa ma kawai ta nuna alamun hakan.

Wani irin idanu gareshi kamar na mai jin bacci,saidai idan kuma ya budesu
sosai xaka fahimci manya ne suna da girmansu,duk da bai gama girmansa ba,amma kuma
zaka fahimci shi din dogo ne,ya fito daga jinsin yaren da sukafi alaqa da
fulani,yana sanye da riga t,shirt me kwala mai gajeran hannu,sai wani wandon jeans
wanda ya danyi fari kadan,qila saboda yawan morarsa da yakeyi ne,saidai kana kallon
jikinsa kasan gwani ne wajen tsafta,domin kuwa.....duk da wuni da yayi wajen
aikinsa,hakan baisa koda karin gugarsa ya bace ba bare akai ga yin dauda,muhammad
al'ameen kenan.

Saurayi na biyu shima farine,don har yafi dan uwansa fari,hakanan shima ba
baya bane wajen kyau duk da cewa shima shekarun nasa basu gama bayyana komai ba,abu
gudan da ya sake bambanta su....yafi dan uwan nasa garin jiki,shi kuma shadda ce a
jikinsa,duk da cewa ba wata ta azo a gani bace ba,amma shima fes yake,saidai
hannunsa da yayi baqi,sabida aikin gyaran mota da yake koya a wani garage,umarul
farouq kenan wanda ake kira da faruku.

A ladabce dukkaninsu suka qarasa daura da malam,suna masa barka da


yamma,fuskarsa fadade da fara'a,zuciyarsa kuma cike da alfahari dasu yake amsa musu
da

"Yawwa.....ya wajen aikin?"


"Alhmdlh" suka amsa masa a kusan tare

"To ma sha Allah" sai suka miqe suka nufi cikin gidan,wanda al'adarsu ce kowacce
rana,idan suka dawo gida lokaci irin wannan,basa shiga dakinsu dake soron,wanda shi
suke fara tararwa,har sai sun shiga sun yiwa innar sannu da gida sun shaida mata
dawowarsu.

A fusace inna ta ciri wayar radio dinta dake a gefanta,wadda ko awa biyu
ba'ayi da kawota daga gyara ba,aikin da ya kacame mata yasa bata samu tashi ba bare
ta miqa ta daki,sai tayi kan iman cikin fushi tana fadin

"Bari na dakeki da kyau.....sai kiyi kukan me dalili"

"don Allah innarmu" kalmar data ratsa kunnensa kenan,abinda ya sanyata


tsaiwa cak daka dukan iman da tayi niyyar yi,ko da bata juya ba tasan waye,ba yau
ta fara jin hakan daga bakinsa ba,matuqar yana gidan,matuqar kuma yana kusa baya
yarda da adaketan,ya gwammace ya horata ta sassauqar hanya,amma baya qaunar a daga
hannu a daketa.

Kafin innar ta gama miqewa tsaye daga durquson dukan da tayi shirin
mata....tuni har ita iman din ta miqe da hanzari,ta kuma falla da gudu tayi inda
alameen din yake tsaye.

Kafin ta iso ya duqa,ya kuma yiwa jikinsa garkuwa da hannyensa,saboda yasan


tana zuwa din jikinsa zafa fada da shagwabar nan tata,abinda ya jima da yi mata
shamaki da aikatashi,saboda yadda a kullum take qara girma,shekarunta suna daduwa.

Ilai kuwa tana zuwa abinda ta shirya yi kenan,saidai ya sanya hannayensa ya


riqe nata hannuwan,ta sakar masa kuka,cikin sigar lallashi ya fara magana

"Ya isa haka.....ya isa,karki bari aga hawayenki mana" yana maganar ne tare da
sanya gefan dankwalinta yana goge mata fuskarta,sannan ya miqe daha durquson da
yayi ya kama hannunta suna takawa zuwa tsakar gidan.

Tsaki yaji daga bayansa,ya kuma san ba kowa bane illa sadiqu,wanda ya
tabbatar da cewa zuciyarsa yayi matuqar kaiwa nesa,da kuma kara da yayi masa
yau,banda haka tabbas ya sani....da tuni ya jima da kai hannu jikin iman din,kamar
yadda ya saba duk sanda wani abu irin haka ta faru.

Yana riqe da hannunta har suka qarasa inda inna ke tsaye daura da qofar
kitchen,ya russuna yana fadin

"Barka da gida inna" yana kuma ajjiye mata daya daga cikin baqaqen ledoji guda
biyun da ya shigo dasu

"Barka kadai aminu,ya wajen aikin?"

"Alhmdlh inna"

"Ma sha Allah,Allah ya qara albarka" ta fada tana ajjiye kallonta kan Ledar da ya
ajjiye ya tura gaban innar
"Alhamdulillah inna" ya amsa mata,saidai hankalinsa yana kan iman,wadda har yanzu
take kumburi

"Me iman tayi inna?" Lamin ya maida dubansa ga innar bayan ya dauke idanunsa daga
kan iman

Sai da innan ta tabe bakinta sannan ta ja ledar ta fara budawa kafin ta bashi
amsa,amsar da tasan koda ta bashin babu abinda zai sauya zani

"Fada dai fada dai ita da yara,fadan da kuma kai da kanka sai da ka rabashi amma
malam ya ganta da yaran bata haqura ba,ita ba za'a gaya mata ba taji kenan?".

Kansa ya juyar ga iman,wadda ta sake tale baki tana shirin fara wani sabon kukan

"Me yasa iman?,ina cewa ni da malam duka mun raba wannan fadan ko?" Cikin muryar
dake nuni da cewa tana gab da sake sakin wani sabon kukan tace
"To ba sune ba.....da na fito sai su fara tsokanata....bayan kuma ni ban kula su
ba.....wai idona irin na mage" qaramin murmushin da ya sake qawata fuskarshi ya
sake,yana kuma duban qwayar idanun da take magana a kai,tabbas qwayar idanun nata
dama eye lashes dinta ba irin na kowa bane,wannan yasa yara da yawa suke
tsokanarta,abinda ita kuma ta tsana kenan,yake kuma yawan hadata fada da
yaran,tasha sanya kuka kan a cire mata idanun a sauya mata wasu,duk saboda yadda
yaran suke tsokanarta,ko kallonta inna batayi,alameen dinne yake tsayawa ya lalace
bata haquri da lallaminta,tare da qoqarin yi mata bayanin cewa ba ciwo bane.

Cikin nutsuwa ya tattara hankalinsa a kanta

"Sau nawa zaance ki daina damuwa uhmm?,dukanmu muna son ganinki haka,kuma ke me
kyau ce,bakiga duka kin fisu kyau bane?ke ta dabance kinji?,ki daina damuwa da
abinda zasu fada" murmushi ta saka kamar kowanne lokaci idan ya yarrasheta irin
haka,sai ta gyada kai tana murmushi,abinda ya sanya dimple dinta na hagu da dama
lobawa,sai shima ya biye mata wajen sakin murmushin

"aminu.....an kira salla,ka tashi kayi buda baki ka rabu da wanann sakaryar" cewar
inna,tana turo jug na ruwan sanyi data jefawa qanqara gabansa,waiwayowa yayi ya
dauki ruwan kana ya miqe yana duban iman

"Zanje sallah na dawo...."


"Ina tsarabata?" Ta fada a shagwabe tana langwabe wuya tun kafin ya qarasa maganar
da yakeyi,murmushi ya sakamar mata,shi kansa yana yaba rigima irin na iman,shi yasa
babu wanda suke shiri dashi kaf gidan saishi kadai,sai kuma malam wani zubin

"Zan taho miki da ita" ya amsa mata yana shirin daga qafarsa

"Qaniyarki....ke me yasa kullum bakya hankali?"

"Idan na iso wajen saina balla mata dan yatsa,laifinsa da yake biye mata" saddiqu
daya gama daura alwalarsa a bakin famfo ya fada bayan ya zubda ruwan kuskure bakin
da ya guntsa,yana warware dogon hannun rigarsa tare da jefawa iman din harara kamar
idanunsa zasu zazzago qasa

"Amma dai ina cewa ba da kai take ba ko?,to ba ruwanka" alamin ya fada yana watsawa
saddiqun nashi idanuwan,sanda yazo gab da shi zai fice daga gidan,xuwa qofar gidan
don miqawa malam kofin ruwan sanyi suyi buda bakin tare,kamar yadda suka saba,kusan
dukansu suna azumin litinin da alhamis,hatta da iman qaramarsu ta fara,yau dinne
kawai ya zamana shi da malam ne kawai suka samu damar yi,saddiqu yayi zazzabi na
kwana biyu,bai jima da warwarewa ba,abinda ya hanashi yi kenan,ita kuma inna uzuri
irin namu na mata,sai kuma iman wadda tun safe al'amin ya daure mata qarqashi kan
cewa yau akwai rana,tasha ruwa abinta,ta bari sai ranar alhamis tayi,inna tayita
mita har ta haqura ta sanya musu idanu,idan da sabo ta saba da wannan dabi'ar ta
al'amin da iman,bama ita ba,duk wanda ya rayu dasu koda na 'yan kwanaki ne sai ya
fuskanci haka.

_ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha'awa saboda gajiya qarancin
sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa
fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza
kizo ki nema taki_

_CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba


ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA
MAIGIDA_

_GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_

+234 818 401 7452

*Tasted and trusted*👍🏽👍🏽


[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: https://arewabooks.com/book?
id=628235bbb77ff582983d6c6b

*FREE PAGE 02*

_ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha'awa saboda gajiya qarancin
sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa
fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza
kizo ki nema taki_

_CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba


ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA
MAIGIDA_

_GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_

+234 818 401 7452

*Tasted and trusted*👍🏽👍🏽


_____________________________

Basu shigo gidan ba su duka sai bayan sallar isha'i,saboda suna tsayawa daukan
karatu wajen malam cikin almajiransa,hannunsa riqe da baqar leda wadda taketa maiqo
dauke da awara me zafi da tasha cabbage da yaji mai uban yawa.

Dai dai lokacin da iman din ke zaune gefan tabarma tare da innarmu wadda ke
lazumi bayan ta gama tata sallar,abincinta na gefe bata tabashi ba,innar tana
ankare da ita amma bata kulata ba,iman din irin yaran nan ne da ko kadan basa
qaunar abinci,wani lokaci har sai innar ta ajjiye madoki kusa da ita sannan zata ci
abincin,wannan dalilin yasa bata da kumari ko kadan,kusan duka sa'anninta sun fita
girman jiki.

Tana jin sallamar alamin ta miqe daga shirin kwanciyar da takeyi,ya qaraso
gefanta ya zauna yana ajjiye mata ledar awarar,fuskarta a wadace da murmushi ta
janyo ledar ta fara budawa tana cewa

"Na gode yaya alamin" shima murmushi kawai yayi ba tare daya amsa ba,suka bita da
kallo sanda ta miqe zuwa kitchen,da alama plate din da zata juye awarar take nema.
Kusan lokaci daya suka dauke idanunsu shi da inna,sai innar ta ajjiyr
carbin hannunta gefan daddumarta tana cewa

"Zauna aminu" sabule slippers din qafarsa yayi,ya zauna daga gefa,cikin yanayi na
nutsuwa

"Me yasà koda yaushe saidai ka yita biyewa shirmenta?,ta yaya ku da kuke nema ya
kasance koda yaushe baka da aiki sai batar mata daa kudi?,yanzu meye laaifin daambu
da bazata ci ba,saidai awara?" Murmushi ya saki kawai,sannan a nutse yace

"Inna mu din mune dolen imaan,mu ya kamata ace munyi mata daman,idan bamuyi mata ba
waye zaiyi mata,kuma bata roqan kowa a waje saimu da muke yayyenta,kuma ma amfanin
neman kenan inna,iman ba wani abu take tambaya ba da ya wuce dan abun marmari" kai
kawai innar ta raausayar,dama tasan zaa rina indai lamin ne,wannaan ba shine karo
na farko da magana irin wannan ta ratsa tsakaninsu ba,ta rasa wacce irin qauna da
kulawa ce wannan da yakewa imaan din,duk da cewa sun kyautata masa matuqa da
gaske,kyautatawar da duniya ma ta shaida da hakan,amma kulawar da iman ke samu daga
gareshi ta musamman ce.

Koda ta matsa wajen ganin cewa ta hanashi,ko kuma ya rage tasan bata bakinta
ne kawai,lamin din bazai sauya ba,a nata hasashen da ganin kamar ya kamata ya rage
din,tunda ko babu komai akwai yayarsa dake aure a qauyensu,wadda wasu nauye nauye
nata dana yaranta duka ya daukesu bisa wuyansa,kasancewarsa yaro jan gwarxo,mai
himma qoqari da kuma neman na kansa,komai dadi komai wuya,kuma komai rintsi,kwata
kwata baisan wata kalma ta lalaci,son jiki ko kuma qyuya da ganda ba,dukkan wani
aiki da zai samar masa da kudi na halak yana tallafarsa,ya kuma karbeshi hannu
bibbiyu yayi,babu girman kai babu ha'inci ko son jiki.

"Shikenan,Allah yayi muku jagora,yasa albarka a nemanku"

"Ameen inna...ameen" ya fada yana jin dadin addu'arta,uwa ce me yawan addu'a ga


'ya'yanta,kome qanqatar alkhairi idan sukayi,bakinta baya gajiyawa da yi musu
addu'a dare da rana.

Duk sanda tayi masa addu'ar sai yaji dadi qwarai da gaske qasan ransa,ya
rasa mahaifiyarsa tun hankali bai fara riskarsa ba,sai gashi Allah ya musanya masa
da wata makwafinta a sanda baiyi zato ko tsammani ba,a lokacin da ya dauke haso ya
kuma debe tsammani daga samun dukkan wani tattali kulawa ko kuma jin dadi,cikin
tausayi da kuma jin qai na ubangiji ya hadashi da wasu kwafin na iyayensa.

Daga inda take zaune take binsu da kallo,sanda ya karbi awarar da kansa ya
juye cikin farantin robar da iman din ta dauko,sannan ya zauna yana gutsutsura mata
da daya da daya yana miqa mata tana ci suna hira,kallo daya xakayi musu ka tabbatar
da cewa lallai akwai shaquwa me girma a tsakaninsu.

Lumshe idanunta inna tayi,bahaushe yayi gaskiya da yake cewa


"Da da da dukiya babu wanda yasan me morarsu sai Allah" ta Sauke idanunta tana tuna
ranar farko da suka fara sanin lamin,ya kuma shigo rayuwarsu ya zama daya daga
cikin iyalan gidan.

Malam ibrahim khalili shine cikakken sunansa,haifaffen garin


maiduguri,cikakken babarbare wanda ya fito daga gida na ilimi da karatu,asalin
gidansu malam khalili gida ne na malamai,da suka gaji karatu tun daga
kakanninsu,malam khalili yana daya daga cikin yara uku da suka gaji mahaifinsu,duk
kuwa da cewa su biyu rak mahaifiyarsu ta haifa Allah yayi mata rasuwa.
Khalili ya tashi da son karatu da kuma nema tuquru,wannan yana daya daga
cikin dalilan da suka sanya yabar maiduguri,ya shiga duniya neman karatun qur'ani
dama na addini haiqan,daga gari zuwa gari,har ma wasu qasashen da muke maqwabtaka
dasu.

Sosai karatu ya daukewa khalili hankali,bai samu yin aure da wuri ba,har zuwa
sanda ubangiji ya nufeshi da zuwa qasar niger.

A canne ya hadu da fatima buzuwa,tana zuwa daukan karatu makarantar wani


abokinsa,yarinya ce a sannan me qwazo da kuma hazaqa,don lokacin ma ta kusa kammala
haddar qur'ani,tana izifi na hamsin da biyar,tun daga baqara take rubutawa a allo
ta haddace sannan ta wanke a sake yi mata qari,ta samu tarbiyya me kyau da kuma
kulawa,duk da cewa mahaifinta ya rasu,amma mahaifiyarta batayi sakaci da
tarbiyyarta ba,saboda ita daya Allah ya basu.

Lokaci daya soyayya da shaquwa ta shiga tsakaninsu,suka fahimci juna da


kyau,manya suka shiga maganar aka tsaida maganar aure,ba dadewa suka angwance,ya
kuma daukota ya taho da ita garin kano,inda anan ya bude tsangayarsa shima,yana
karbar almajirai daga kowanne gari ko qasa.

Almajirancin makarantar malam khalili ba kamar sauran almjirci bane da


muke gani ayanzu,wada aka watsar da duk wani mutunci da kuma kimarta a yanzu,yara
suke wahala da sunan neman ilimin alqur'ani me girma,wanda sam hakan bashi da tushe
bare asali sam cikin addininmu.

Dukka yaron da zai karba sai ya kasance makusancinsa ne ya kawoshi,zaa


rubuta adreshinka da lambar wayar wanda ya kawoka,sunan gari dana qauyenka da kuma
inda za'a iya samunka,sanna bai yarda a kawo masa yaro babu haka ziqau ba babu
abinda zaici,abun kwanciya da kuma kayan baqatun yau da kullum,saboda shi din bai
yarda da fita bara a makarantarsa ba,karatu aka kawo yaran shi sukeyi,yakan baka
zabi idan ka soma hankali,kana da sha'awar karatun boko?,idan kana dashi zai
shaidawa iyayenka ya sanyaka a makaranta,idan baka buqata kuma zaka kama sana'a
ne,don bai yarda da zama babu sana'ar yi ba,saidai kowacce sana'a kake kana yinta
ne bisa sanya idanunsa da kulawarsa,da kuma tabbatar da cewa sana'ar da kakeyi din
bata sabawa addini da kuma al'ada ba.

Wannan dalilin ya sanya makarantarsa ta kasance mai tsari,mutane da dama


sukeso kawo yaransu karatu nan wajensa,saidai duk shekara akwai adadin da yake
dauka,idan suka cika kuma baya sake dauka sai wata shekarar.

Zamansa da fatima wani irin zama ne me matuqar dadi da kuma ban


sha'awa,khalili wani irin mutum ne managarci,mai halaye da kuma dabi'u masu
kyau,tsayyen akan harkar gidansa da kuma sauke nauyin iyalinsa,idan kaga fatima
zakayi tsammanin tana auren wani me halin ne,saidai ko daya,tsabar kula da take
samu ne da kuma tsaiwar mijinta wajen sauke nauyinta,babu abinda ta nema ta
rasa,tana matuqar jin dadin xama dashi,kamar yadda shima yake yaba mata,yake kuma
matuqar jin dadin xama daa ita,saaboda ita din macace ta gari,mai tarin biyayyawa
mijinta,wadda tasan dai dai ta kuma san akasin hakan,bai taba cewa tayi ta musa
ba,kamar yadda bai taba cewa ta bari taqi ji ba,Shi yasa shima yake qaunarta,da
kuma qoqarin ganin ya hidimta mata iyakar iyawarsa,bata nema komai ta rasa ba cikin
gidanta,cikin wannan yanayin,shekara biyu da aurensa Allah ya albarkaceta da samun
haihuwar santalelen da namiji,aka sanya masa abubakar saddiq.

Daga kan saddiq tayita haife haife suna mutuwa wato WABI,makusanta da wasu
cikin dangi sukayita so malam khalili ya qara aure,amma yace sam baiga dalili
ba,yanajin dadin zama da matarsa,bai nema komai ya rasa ba,idanma ta hahuwa ce,kana
iya haifar yaro guda daya amma ya zame maka me albarka fiye da masu tarin
yaran,indai yana da rabo a haihuwa zata qara,ita kanta a sannan ta bashi dama amma
yace bazaiyi ba,Cikin ikon Allah kuma sai Allah ya basu haihuwar hajar
iman,haihuwar da duka fidda rai da ita,zuwan iman a daidai wannan lokacin ya janyo
mata soyayya mai tarin yawa,saboda tazo a sanda basu zata ba,ta kuma zo a dai dai
lokacin da suke marmari da buqatar qaramin yaron cikin gidan.

Shekarar iman daya a duniya da watanni biyar lamin ya shigo rayuwar cikin
gidan a lokacin.

Yadda jama'a keta yabawa malam khalili kan yadda makaranta da kuma dalibansa
suke a tsare ya sanya malaman wasu tsangayun dake unguwarsu da kuma wasu unguwannin
suka shiga adawa da kuma takun saqa dashi,suke kuma matuqar jin haushinsa,ganin
cewa ya fita daban da sauran malaman tsangayu,babu bautarwa ko azabatarwa ga
dalibansa,kamar yadda bai yadda ya zama cima zaune me matacciyar zuciya ba,sai
abinda iyayen yara suka dauko suka bashi,aah,shima kamar kowa,duk sanda ya tashi
dalibansa shima yana tafiya neman kudinsa,ya dawo kuma lokacin da aka kusa sake
zama ci gaba da karatu,komai nasu na tafiya a tsare ne,kana ganin dalibansa da
yadda yake tafi da komai dole ya baka sha'awa.

Daren wata jumma'a ne,tana zaune tsakar gidanta daya kasance sai ita
daya,sai hajar dake kwance a gefe saman wani abun shinfidarta me hade da katifa
maras tudu,duk kuwa da cewa akwai motsin almajirai da hayaniyarsu daga qofar gida
amma cikin gidan ba kowa,saboda babu wanda ke shigarwa malam gidansa gaba gadi don
suna almajiransa,idan kaga yaro cikin gidan,to qaramine wanda shekarunsa basu wuce
wanda shari'a ta wanzar da hani na shigarsa gidajen matan aure ba,tana da mai mata
aike da maiyi mata wanki ana biyansa duk a cikinsu,bai yarda suyi mata aiki ba tare
daya biyasu ba,saboda yace su din mutane ne suma kamar kowa.

A hankali hayaniyar tasu ta fara raguwa,da alama an gama rabon abincin dare
ne,wanda ake auna cikin abincin kowa a hada,manya a cikinsu su dafa a rabawa kowa,a
wani gida da suke zaune wanda yake daura da gidan malam din,gida ne da wani bawan
Allah ya bayar kyauta su dinga kwana,hankalinta bai wajen sosai,yana can ga tunanin
abinda ya tsaida malam da din bai dawo yadda ya saba ba,shi da saddiqu da yayi masa
rakiya.

"Taho a hankali....riqeshi sadiqu" ta jiyo maganar malam din tun daga


soro,abinda yasa ta ajjiye allon da take rubuta fasayakfika humullah ta maida
hankalinta ga qofar shigowa gidan.

Malam dinne da sadiqu da wani dan farin yaro da bata sanshi ba,ta miqe tana
masa sannu da xuwa,ya amsa hankalinsa yana kan yaron

"Maza dora ruwan zafi innar saddiqu" malam din ya fada yana tsugunnawa a gaban
yaron,yana yage ragowar rigar jikinsa,da hanzarinta ta koma madafa,ta hada ragowar
itacen data gama girki ta kunna ta dora masa ruwan,sannan ta dawo tsakar gidan,inda
malam ke tsugunne gaban yaron yana masa sannu,sadiq na tsaye a saman kanshi yana
kallonsu.

Kujera 'yar tsuguno ta jawo ta zauna,idanunta akan yaron da yake cikin hali
na galabaita ta yiwa malam sannu da zuwa

"Yauwa binta" ya amsa da alamun rashi na a bace ne

"Ki duba maganin zafi don Allah idan akwai,idan ruwan yayi zafi ki juye sadiqu ya
tayashi gasa jikinsa,bari naje na dawo" daga haka malam din ya miqe ya fita.

Duk yadda malam din yace tayi haka tayin,ya gasa jikinsa da kyau,sauran ta
sakashi ya shiga bayi yayi wanka dashi,cikin kayan sadiqun ta zabo wasu ta bashi ya
sanya,don xasuyi kai daya dashi,yana gamawa ta zuba masa abinci,ta koma ta dauki
iman data tashi ta fara rigima ta fara bata nono,daga inda take din tana kallon
yadda sadiqu ya sanyashi a gaba yana kallo,tun dazun shima zuciyarsa a karye take
fuskarshi ta nuna hakan.

Malam ne yayi sallama,ya qarasa gaban yaron yana duban yaron daya ambata da
lamin,ya bashi paracetamol din daya shigo dashi da kuma ruwan tea me zafi a
leda,yace idan ya gama yasha yasha maganin,sai saddiqu ya kaishi daki ya kwanta.

https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥


_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥


_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅


_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥


_Mamuhgee_

Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa


1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼


👇

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________

*KUFAN WUTA*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci
insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina
ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form din kamar
haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with
Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu


https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne
bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu.
Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*

+234 903 177 4742


_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna
sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍😍😊🥰😍 😊 _.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 03

https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ZAFAFA BIYARRRRR*

*_INGANCIN LABARAI_*

*_FASAHA NUTSUWA DA IYA SARRAFA ALQALAMI_*

*_TSARI DA TSANTSAGWARON HIKIMA_*

*_SOYAYYA MAI RATSA ZUKATA DA NARKAR DA ZUCIYA_*

*_JIGON LABARAI DA YASHA BAMBAM DA NA SAURA MAI SANYA ZUCIYA MAMAKI DA TUNANI_*

*_YIN LINQAYA CIKIN DUNIYAR LABARI KAJI KAMAR DAKAI AKEYI DA GASKE NE_*

*DUKA SAI CIKIN GAMAYYAR LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

*_ADADE ANAYI SAI GASKIYA_*

*_HIKIMA KASHIN KWANCE_*

*ABOKAN HIRA NE GA WANDA KE CIKIN KADAICI!*

*ABOKAN TAFIYA GA WANDA KE CIKIN NISHADI*

*WARWARAR MATSALA GAME NEMAN MAFITA*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥


_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥


_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅


_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥


_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa


1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼


👇

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
______________________________

Ajjiye iman inna tayi sannan ta nufi daki,ta dauko babbar tabarmar malam din da
yakan zauna a kai ta shimfida masa,sannan ta gabatar masa da abinci da ruwan wanke
hannu,ta zauna nesa kadan dashi tana ci gaba da shayar da iman wadda ke rigima
saboda bata qoshi ba,ta sakeyi masa sannu da xuwa

"Yauwa sannu binta,ya hidima ya gida"

"Alhmdlhi" ta fada tana dan murmushi,duk data saba da irin wannan kulawar
tashi,amma duk sanda ya tambaya din hakan yana mata dadi,saboda tasan cewa mata da
yawa ne suke neman hakan basu samu ba

"Wannan yaron da kike gani sunansa lamin,na tsinceshi ne a can unguwar da naje nida
saddiqu dubiyar abokina,abinda ya bani mamaki yaro qarami yashe gaban famfon tuqa
tuqa,jikinsa duka tabo na duka,yasha ruwa yanata amansa,wadda ina tsammanin babu
komai ne a cikinsa,yayimin kama da almajiri don haka na matsa kusa dashi,sai daya
dan rage aman na tambayeshi sunansa da kuma inda yake,yamin bayani,ashe almajirin
makarantar malam dan lami ne,sai na tuna kwanaki uku da suka wuce tabbas naji ana
neman wasu cikin daliban,na tambayeshi me yakeyi to a nan,kansa tsaye ya shaida min
guduwa yayi,na masa fada na kuma nemi dalilin da yasa yabar makarantarsu,shi baya
jin tsoron wani abun kada ya sameshi,a yadda na fahimta tsoron malamin da
makarantar yafi tsoro akan duk abinda zai sameshi,abun takaicin kudi malamin yake
sanya musu duk ran laraba,kowa sai ya kawo wadan nan kudaden,idan kuma ba haka
ba,zai ma yaro duka mai tsananin da zai gwammace koma ta yayane ya samo ya kawo
masa,to shi kusan duk sati sai an dakeshi,saboda baya iya kawo komai,don yace bazai
iya yadda sauran sukeyi ba,don cikinsu harda masu sata don kawai su kawo,lamarin ya
dagamin hankali,na daukeshi na maidashi gaban malamin,duk da inajin tausayinsa,amma
babu gatan da xanyi masa da ya wuce hakan,saidai abun mamaki abun takaici kuma abun
haushi,sanda naje ga malamin,tunda ya tambayi waye ni ya fara yimin wani kallo,nasa
ma'anar kallon,tunda sarai nasan waye malam dan lami,yana daga cikin masu adawa da
tsarina,amma ni hakan bai dameni ba,burina da fatana shine kowa ya gyara,tun kafin
nakai ga cewa komai ya soma dakawa lamin tsawa,tare da jifansa da miyagun sunaye da
kuma kalamai,ya kuma fara hanqoran neman manya cikin dalibansa su dauke lamin su
saka masa shi a mari,abinda bai jima da fita daga ciki ba,a nan na nuna masa nima
ainihin xafina,na hana kowa yaxo wajen ya taba yaron,a nan malam dan lami ya tada
husumar cewa dalibinsa ne,kuma babu wanda ya isa ya hanashi yi masa duk hukuncin da
yaga dama,tunda a hannunsa aka danqashi,indai kuwa bazai hukunta laminu ba,saidai
yabar masa makarantarsa,ya koreshi,ya kori yaron ba tare daya tsaya yaji meye zance
ba,bai tsaya yaji me yaron shima zaice ba,bai kuma sanar da magabatansa ba bare
susan ina yaronsu ya koma"

"Na fuskanci tijara yake ji,don haka bance komai ba na tattaro al'aminu,na
wuce dashi chemist saboda yanayin ciwuka da raunin dake jikinsa na tabon bulalai da
duka da kuma mari daya dade a qafarsa ya zame masa ciwo. A hanya nake tambayarsa
wayeshi da kuma qauyensu,ya shaidamin shi din dan birnin kudu ne,mahaifiyarsa ta
jima da rasuwa tun yana qarami,yayarsa da ita ta riqeshi har zuwa sanda ya
tasa,mijin yayar yace bazai iya daukar nauyinsa ba saboda shima bashi da
komai,yayarsa bata da yadda zata riqeshi saboda shi da itan duka marayu ne,hakan ya
sanya mijin yayar ya kawoshi bara,ya damqa shi a hannun malam dan lami,tunda kuma
ya tafi bai waiwayoshi ba,duk da cewa bai wani jima a makarantar ba,azaba ba wacce
bai gani a waie malamin ba,don kusan karatun ma dana tuntuba ba wani mai yawa
bane,azabar da suke sha tafi karatun yawa,wanna dalilin ya sanya na yanke shawarar
kawoshi makarantata yayi karatu,zuwa sanda zai warware kuma mu nemi ita 'yar uwar
tasa ko mijinta mu gaya masa inda yake a yanzu".

Kai inna ta gyada idanunta na kan lamin,zuciyarta cike da tausayinsa,tunda


malam yake kawo almajirai bata taba ganin yaron da taji ya kwanta mata ba kamar
lamin din,a dan awannin da yayi dasu wanda bai wuce awa daya da rabi ba,ta fuskanci
nutsuwar dake tattare da yaron,komai nashi a hankali yakeyi cikin nutsuwa

"Allah ya rufa asiri,ya gyara mana xukatanmu" shine abinda inna ta fada,suka kuma
fara rayuwa da lamin din,wanda cikin kwanaki biyu ya sake da sadiqu,wani irin sabo
sukayi sosai dashi,saika zaci sun dade tare.

Tun farko dama aminu din bai soma kwana cikin almajirai ba,cikin dakin
saddiqu suke kwana,hakanan hatta da suttura ta saddiqun yake sanyawa,kafin daga
bisani malam ya bayar da kudi inna ta samo musu gwanjo masu kyau shida saddiq
din,sosai sadiq ke murnar samun dan uwa,lokaci kadan lamin ya shiga jiki da zukatan
su inna,saboda yarone haziqi,duk wani aiki da saddiq keyiwa inna da malam alamin
din ya daukeshi,sai malam da inna na hanashi suna raba musu kowa ya dauki nasa.

Kusan tare sukayi rainon iman da inna,idan inna tana aiki tofa iman tana
hannunsa,yayita tiri tiri da ita kenan,tun tana masa qyuya har ya zamana duk cikin
gidan babu wanda take yarda dashi Kamar yadda take yarda da alamin,wani lokaci idan
aiki ya kacamema innan idan ya dauki iman sai tayi da gaske ta korashi makaranta
sannan zai tafi,sannu a hankali sai sabo da shaquwa suka shiga tsakaninsu,baya son
kukanta,baya son abinda zai taba iman din,da a daki iman din gwara a dakeshi,koda
malam ya sanyasu makaranta sai ya zamana sai ya fara kai iman sannan shi zai
wuce,koda kuwa shi xaya makara,kudin break dinsa kuwa badai yaci a cikinsa ba,komai
ya gani shi zai kwasowa iman din ya kawo mata,idan kaga yadda yake matan sai ka
rantse da Allah ciki daya suka fito.

Kamanni ne kawai zasu tona asiri,saboda kowa a cikinsu kamanninsa


daban,hasken fata ne kawai ya hadasu,tun iman na qarama ta fita daban,tana da kyan
fuska qwarai da kuma yalwar suma,wadda ta gajeta daga wajen inna.

'yar lele iman take a wajen alamin tun tana da qananun shekaru,zai iya
hana cikinsa ya bata,duk abinda tace tana so to matuqar yana dashi sai ya bata,idan
babu kuwa zai nema mata,abinda yasa ya tashi kenan da zuciyar nema,zama da madaukin
kanwa inji hausawa sukace shike kawo farin kai,tun saddiqu bashi da ra'ayi har zama
da lamin ya sanya ya zama mai neman na kanshi kamar alamin din.
Kusan duk kudin daya samu wajen nemansa fiye da rabinsa siyawa iman wannan
ne siya mata wancan,tun bata isa ado ba yake mata siyayyar kayan kwalliya da qyale
qyale,tun malam da inna na fada,har suka fahimci a jininsa yake kulawa da
iman,bazai iya dainawa ba,dole suka haqura suka sanya masa idanu,saidai innan tayi
masa fada da kuma dabarar ya dinga aje wani abu saboda yayarsa,wadda a yanzu
shekaru ke sake jaa nauyi na dada hawa kanta,tana kuma da buqatar taimako ko yaya
ne.

Alamin shine kewa iman komai,itama duk abinda take da buqata alamin din take
durafafa kanta tsaye,bata ko kallon sadiqu dan uwanta,saboda yana da zafi shi
din,hakanan yanzu yanzu ba wani abu bane yakai mata bugu idan tayi ba dai dai
ba,sabanin alamin.....wanda bashi da daukan zafi a kanta,hasalima yana tare duk
wani abu da yasan xai bata ranta ko ya cutar da ita,idan tayi ba dai dai ba cikin
ruwan sanyi zai nusasheta ya kuma gyara mata,tana kuma daukan maganarsa fiye data
kowa cikin gidan.

Dinki dashi lamin yafi qwarewa,ya iya dinkin mata kamar masifa,har zuwa yanzu
da yake kan shekara ta kusan goma sha shida,wannan yasa iman dake da shekaru goma
sha daya cikin rayuwarta tun a sannan ta zama abun kallo,indai tayi kwalliya kowa
sai ya yaba,tana da kyau sannan kuma alamin din yana fitar da ita da dinkuna sai
kace wata qatuwar budurwa,don idan kaga dinkunan da take sanyawa saika tambaya waye
yayi mata,sau tari idan yayi dinkuna ya samu kudi sosai,yakan je kasuwa ba tare
daya gayawa kowa ba,ya samo mata atamfa falle bibbiyu masu sauqin kudi ya mata
skert da riguna tsala tsala,saboda bata iya daura zani ba har yanzu,abinda yake
hadata da inna kenan,kullum fama take amma har yanzu iman din bata iya ba,koda
yaushe saidai ayi mata riga da skert ko kuma doguwar riga.

Idan kaga iman din saika dauka diyar wani ce,saboda bata rasa komai
ba,kullum tsaf zaka ganta cikin suturu masu kyau.

Amin Abubakar haifaffen garin birnin kudu ne dake jahar jigawa,bafulatani


ne uwa da uba,abinda yasa ya gaji kyau kenan shima tun quruciyarsa,tun shekarunsa
basu fara nuna ba,yaro ne da tun a halittarsa Alla ya masa baiwa masu tarin
yawa,yana da nutsuwa qwarai da gaske wadda ta hade masa da miskilanci,miskilancin
da tun zamanin quruciya ya sanya ba kasafai zaka ganshi cikin wasanni irin na yara
ba,yafi ganewa yana zaune daga gefe yana kallonsu,idan abu ya burgeshi ya saki
murmushi kawai.

Kafin rasuwar mahaifiyarsa ya samu tarbiyya qwarai daga wajenta,wannan tasa


ya zama wani na daban,idan yana wasu abubuwan saika dauka wani babba ne me shekaru.

Yadda malam da kuma inna suka riqeshi abune da bazai manta dashi kafatanin
rayuwarsa ba,sun masa wani gini sun kuma zame masa garkuwa kuma ginshiqi cikin
rayuwarsu,ya fahimci daga inna sadiq da kuma malam dukkaninsu suna qaunar iman,suna
dannewa ne saboda yanayi irin na tarbiyya,shi kuma baiga abinda zaiyi ya faranta
musu ba fiye da kula da abinda sukeso,hakan yasa ya sanyawa kansa bawa iman din
dukkan kulawa,sannu sannu kuma sabo da shaquwa suka shiga tsakaninsu.

Wani lokaci har mantawa yakeyi,yakan kallo iman din a matsayin 'yar uwarsa
ta jini,har sai idan wani abun ya gitta da zai sanya ya tuna cewa ba jininsa bace.

_shimfida kenan......muje zuwa_

_ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha'awa saboda gajiya qarancin
sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa
fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza
kizo ki nema taki_

_CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba


ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA
MAIGIDA_

_GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_

+234 818 401 7452

*Tasted and trusted*👍🏽👍🏽


[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 🔥🔥 *KUFAN WUTA*🔥🔥

NA

*HUGUMA*

Free page 04

*_MASOYA 'YAN QASAR NIJER,ZAKU TURA KATIN WAYA(AIRTEL/MOOV) TA WANNAN NUMBER_*

+22795166177

     Zaune take saman kujera 'yar tsugunno,sanye da uniform na makarantar primary


din da take zuwa,tana ta qoqarin daura takalmin sandal a qafarta,komai nata tsaf
kuma fes,karin guga ya kama uniform din jikinta sosai,shaidar cewa suna samun
kulawa yadda ya kamata,hatta da takalmin sandal din qafarta qyalli yake,kamar yadda
farar safarta take qal kamar baa sakata.

       Wannan kusan duka aiki da horon lamin ne,idan baiyi mata da kansa ba,to ya
riga ya koyar da ita,iman din akwai tsafta kamar yadda lamin din yake,bare ma kafin
ta yiwa kanta wani abu sau daya yayi sau goma,wankinta da nashi duka suna
wuyansa,kama daga uniform dinsu zuwa kayansu na zaman gida.

       Lamin din na tsugunne gefan kitchen yana shirya mata abinci a wani dan
qaramin kwando me kyau,wanda shi da ita sukaje ta zaba ya siya mata,tana ta masa
surutu yana biye mata,wanda duka akan jarrabawar common interence da zata zana ne a
yau,inna na daga cikin kitchen din tana zubawa shi yana shiryawa har ya gama,dai
dai sanda ta gama sanya safa da kuma warin takalmi daya,dayanne ya gagara,don haka
lamin din ya qarasa wajen ya tsugunna ya kama takalmin yana daura mata,sannan ta
miqe tana diban takardunta sabon pencil biro har ma da cleaner dasu sharpener da
lamin din ya siya mata.

         Suka miqe suna yiwa inna sallama,saboda lamin din ne zai kanta har can
inda zasu zana jarabawar da kansa,daidai lokacin malam ya shigo

"A'ah,har kin gama shiryawa kenan,to ai Allah yasa motar bata tashi ta barki ba"
malam ya fada yana danna wayarsa Tecno keypad dake hannunsa saboda yaga lokaci

"Dama ba tare zamu tafi ba,ya lamin ne zai kaini" iman ta fada tana duban malam

"A'ah,wanne irin sakarci ne wannan,ya ga motar makaranta zaki ce saidai laminu ya


kaiki?,ki wuce ki shiga cikin 'yan uwanki dalibai ku tafi"

"Ai malam kada ma ka bata bakinka,babu yadda bayi dasu ba,tun jiya nake sababi,amma
dole ne naja bakina na tsuke,saboda shine yake goya mata baya,wai kada ta shiga
cikinsu uniform dinta ya cukurkude......sai kace tafi kowa" jin inna ta sako baki
ya sanya iman ta fara narai narai da ido kamar me shirin sanya kuka tana duban
lamin din,so take ya sanya baki,kada su malam su hanashi ya rakata.

       Zahiri ita tsoro takeji,saboda yadda taji wadanda suka gama primary wancan
shekarar suke fadan wahalar jarabawar,duk da yadda lamin din ke qarfafa mata gwiwa
tare da nuna mata cewa ba wani abu,suma sunyi fa,iya karatu tasan ta yishi,don a
rana suna kwashe awanni masu yawa lamin din yana mata lesson,tana da matuqar qoqari
da fahimta,saboda haka duk karatun da yake mata tana daukeshi,wannan dalilin ne
yasa lamin din yaci burin tayi karatu mai zurfi,duk sa'ilin da suka zauna suna hira
kuwa rabin maganarsa kenan,wannan abu yayi tasiri itama cikin ranta,bata da burin
daya wuce ta ganta ta gama qaramar makaranta ta shiga jami'a,ta zama likita lawyer
ko 'yar jarida,cikin ukun nan takeso ta zama daya.

"Malam kasan wannan shine karonta na farko da zata fita wani waje tayi jarrabawa
irin wannan,rakatan kuma zai qara mata qwarin gwiwa,tunda makarantar basu hana ba
malam ka bari na kaita" da qyar lamin yasha kansa ya barsu suka fice.

       A soron gidan ya dakata yana cewa

"Bari na tada sadiq ya rakani,tafiya bibbiyu tafi dadi"


"Yaaya,Allah bazaije ba koka tasheshi" iman ta fada tana jan tunga,sai ya waiwayo
ya kalleta,taso bashi dariya yadda ta tsuke dan qaramin bakinta ta marairaice,ya
fuskanci so ne batayi yaje din,don tabbas idan suka tafin tare bazai barta ta sake
ba,duk kuskuren da tayi saiya taso mata da fada hantara ko kyara.

"Ina zuwa dai" ya fada yana saka kansa cikin dakinsu.

       Saidai duk yadda yaso tada sadiq din ya rakashi ya qiya,sai ya cusa kansa ma
qasan filo yana cewa a dawo lafiya,Allah ya bada sa'a,dole ya fito daga dakin ya
barshi.

        Dadi iman din taji,ta dinga boye dariyarta har sai data fito ta dara,harara
lamin din ya watsa mata da lumsassun idanunsa

"Ni kikewa dariya saboda ya yarfani ko?" Sake qyalqyale masa tayi da dariyan

"To ai yaa lamin kai kam baka iya harara ba,hararaka irin ta masu jin bacci ce"
fara'ar fuskarta kadan ta ragu

"Ya lamin,ni dakai me yasa dukanmu bamu da lafiyar ido?" Ta tambayeshi sanda suka
kusa ficewa daga layin nasu tana dubansa,da alamun damuwa cikin muryarta.

       Murmushi ya sake wansa iyakarsa saman lebansa,duk da qarancin shekarunsa


amma yanayinsa kamar wani babban matashi,akwai wani iri kwarjini na daban dake fita
saman fuskarsa.

       Duk da cewa a shekara ta sha bakwai yake amma hankalinsa tabbas yafi na iman
din nesa ba kusa ba,kasantuwarsa namiji ita kuma diya mace

        Cikin harshen da yake ganin zata iya fahimta ya fara mata magana

"Lafiya lau idanunmu suke ni dake,ba kina gani sosai ba?,ko akwai wani abu da bakya
iya gani" saifa girgixa kai alamun a'ah
"To kin gani ba.....nima ina gani sosai,har daga nan ina iya ganin wanda ke tsaye
gaban rumfar malam dalha" ya fada yana nuna wajen da yatsa,abinda ya sanyata tada
kai ta kalli wajen,kawai tazarar nisa a tsakaninsu,don haka abun ya bata mamaki,har
ta fidda idanu,sannan ta waigo gareshi

"Yaaya" kai ya jinjina mata,bata sake kokwanto ko tantama ba,saboda tasan halin
lamin din tunda ta fara wayo,qarya itace abu na qarshe da baya kusantarta a
rayuwarsa kaf,koda ya gaya mata waye a tsayen,da suka isko wajen saita ga shi dinne
kuwa,abinda ya sanyata sakin dariya

"Na yarda Allah yaya,lafiyarmu qalau" murmushi ya kuma saki a maimakon dariya

"Na gaya miki dama,yanayin halitta ce,kowa da yadda Allah ya halicceshi,kamar yadda
yayi wani dogo,wani gajere,wani fari wani baqi,wani me kyau wani akasin haka"

"Wani me suma me kyau irin taka,wani kuma tashi irin ta yaya sadiqu ko?" Wannan
karon dariya ta bashi,har haqoransa suka bayyana

"Zaki bayani duk randa kika fada a gabansa,shima sumarsa me kyau ce sosai
iman....,amma taki tafi tasa kyau sosai" murna ta cikata,tadanyi tsalle kadan

"Don Allah yaya ba na fishi kyau ba?"

"Neeeesa ba kusa ba" ya fada yana duban fuskar dake cike da quruciya,murmushi na
fita daga kan tata fuskar

"To amma me yasa yake cemin me idon mage,mummuna?" Ta tambayeshi tana tura
baki,saiya sake sakin murmushi,indai yana tare da iman din bata bari fuskarsa da
bakinsa su huta

"Ki rabu dashi,kishi yake dake" ta saki qaramar dariya cikin nishadi,tana jin dadin
zama da ya lamin fiye da kowa cikin gidansu,duk sanda zai bata amsa,yana bata amsa
ne ta yadda zata dace da ra'ayinta da kuma abinda takeson ji,indai yana nan baya
bari bacin rai ya zauna saman fuskarta,da irin wadan nan hirarrakin sannu a sannu
har suka samu abun hawa,ya kaisu inda daliban shekarar daga makarantun wannan
qaramar hukumar zasu zana jarrabawar.

        Sai daya tabbatar da shigewarta exam hall din sannan ya juyo zuwa gida,a
qafa ya zabi ya tako zuwa gidan,saboda kudin dake gareshi su isa kawosu gida shi da
iman din zuwa la'asar idan an gama jarrabawar.

        Yana gab da isowa qofar gidan nasu ya hangi yarinyar na tahowa,ubaida 'yar
layinsu ce,ya fuskanci duk sanda xasu hadu da yarinyar saita dinga wani sinqe
sinqe,idan sukayi clashing kuwa haka zata gaidashi cikin girmamawa,duk da cewa
kwata kwata shekarun da ya bata basu wuce biyu ko daya ba,saidai yanayin garin jiki
da kuma kwarjinin da yake dashi,zaka zaci cewa wani babban yayanta ne.

       Yanzun ma yana kallonta tayi wuf ta shige soron wani gida ta buya,saidai
taci gaba da leqensa har ya wuce ta sannan ta fito.

       Yana da yawan gumi,don haka sanda ya isa dakinsu ya jiqe da zufa,ya samu
sadiqu ya fito a wanka daga bandakin da ba'a dade da yi musu ba cikin dakin
nasu,wanda suka hada kudi abinsu shi da saddiqun aka musu,saboda girma da sukaga
sun fara,lamin ne ya kawo wannan shawarar,kuma ta kwantawa saddiq din,da yake dakin
ma sha Allah yana da girma,don ya dauki katifunsu guda biyu bayan leda me kyau dake
malale a dakin,da yake ba wanda yake shigar musu kuma wuni suke wajen sana'a ledar
lafiya lau take,sai kujera guda daya doguwa da kuma kwabet ta katako mara tsaho
amma kuma tana da fadi,anyi mata bangare biyu kowa da sashen kayansa,kusa da
kujerar akwai wani dam teburin na katako da talabijin ta zaune,da receiver a
kanta,wadda suka jona daga maqota,dama ba wani kallon arziqi suke ba,sunfi kallo
sanda ake ball da wani waje,shima kusan sadiq ne me wannan nacin,lamin din yafi ga
sauraren news a redio.

       Suna hada ido ya harari sadiq din wanda yake daura tazugen gajeran wandonsa

"Baka kyauta ba wallahi,abinda kake sam bai kamata ba"

"Allah ya sani bazan iya irin rayuwarka ba,yarinya sai shegen fi'ili da shagwabar
banza da wofi,kamar wata yayayya,ayita riritata,yarinyar da an kusa bude mata
littafin ayyukanta nan da wasu shekaru kadan" sadiq din ya amsa masa yana zura riga
a jikinsa,harararsa lamin ya sakeyi

"Idan bamu kula da ita ba da waye ne zamu kula?,ita kadai ce fa a gabanmu?,kuma ma


ina wani shagwaban yake?,kaidai matsala ce dakai kawai,kuma idan baka canza ba
bazamu taba dai daitawa ba" daga haka yaja towel dinsa dake hannun kujerar ya shige
bandaki,yana jiyo sadiq yanata qananun maganganun indai iman bata canza ba shima
bazai canza ba.

      Kansa kawai ya kada cikin takaici,dukkaninsu har yau sun kasa karantar
iman,kamar shi daya shi da.malam ne suka fuskanceta,ba shakka tana da sakalci da
shagwaba wani lokacin da gabunta irin na yaran da ake haifa daga qarshe,to amma fa
tana da hankali da wata irin nutsuwa,haka kuma tana da fikira da saurin fahimtar
abu,ko yaya ka zauna da ita zaka san cewa uwa ta gari ta taka muhimmiyar rawa wajen
nutsuwarta da dabi'unta,yarinta kuwa har yanzu bata wuce lokacin ba,so dole sai an
dinga mata uzuri ana nusasheta harta wuce lokacin.

       Sanda ya fito lallausar sumarsa mai santsi da zaka zaci relaxer yake sanya
mata tanata digar ruwa,zuwa sannan har sadiqu ya shiga cikin gida ya karbo musu
abun karyawa,kunu ne me zafi sai qamshin lemon tsami yake,sai kuma fanke da qosai
wanda ya tabbatar qosan nashi ne,saboda shi fanken bai dameshi ba,qosai ne koda ya
huce zai cishi a haka yana jin dadinsa,koshi ko alala,sau tari sadiq na tsokanarsa
da cewa

"Wai lallai saika nuna kai cikakken bafullaci ne,qauna ce shadidiya tsakaninku dama
da qosai" wani lokaci yayi dariya ya barshi,wani lokaci kuma ya rama.

       "Yauwa,daga kan plocker dinka akwai saqo gashinan an bani,ka duba" sadiq ya
fada yana qoqarin kai cup din kunun bakinsa,ajjiye towel din da yake goge kansa
dashi yayi ya qarasa gaban locker din,wadda take dauke da tarkacen kayan shafa na
maza,kai kace wani zabgegen saurayi ne,tarin turaruka ne kala daban daban,kama daga
roll-on, sure,body spray,body mist masu sanyi,da turaruka na kaya  shaving cream,da
body cream masu sauqin kudi,man wanki baki da mayukan gashi na maza,sai kuma man
saka takalmi yin qyalli.

         Hannu yakai ya dauki farar takardar da aka nannadeta four corners,ya ware
a hankali,sannan ya zuba mata sleepy eyes dinsa da suke a lumshe,yana bin yadda aka
zane takardar da zanen furanni da kuma tsuntsaye,sannan ya sauka ga saqonnin
soyayyar dake rubuce a tsakiyar wani lafcecen heart (zaku iya tunawa da wasiqar
soyayya da ake rubutawa zamanin quruciya?,ya kai zunzurutun zinaren mazirarin
zuciyata?😂).

        Maida wasiqar yayi sama a qasa yana lalubo sunan marubuciyar,sunan ubaida
ya bayyana,saiya linke takardar,sannan ya waiwaya ya dubi sadiqu

"Yaushe ka mayar dani dan iska ka fara karbo wadan nan abubuwa kana kawomin?,bari
to na ajjiye na kaiwa malam,kada wataran ya kamaka ya zaci bakinmu daya,ko kuma ni
nake aikenka" da hanzari sadiq ya tashi yana danne dariyarsa yasha gaban lamin dake
zura jallabiyarsa ta barci
"Kaga.....ni kada ka yimin sharri,ni ina ruwana?,ina zaune ta aiko qanwarta ta
kawomin,kaga kenan bani na janyota ba ko bare kace" tsayawa yayi yana duban sadiq
din,ya sanshi qwarai da rawar kai,saboda yawancin lokuta idan yaga ana tashi daga
aiki lamin din ya biyo masa ya sakashi a gaba sunyo gida,suna isowa anyi magariba
sunyi masallaci,saga can sun zauna karatu da malam,ana tashi hira cikin abokansu
lamin din baya bari su zarce awa daya zai takura sadiq din kan su shiga gida,ko su
zauna a dakinsu suyi wata hirar,ko suyi karatu,ko su kalli ball idan nepa sun
agajesu da wuta,ko kuma su zauna tare da inna kafin malam ya shigo,yakan yi qorafin

"Waikai.....sai kace wasu mata da Allah,kai ko dan 'yammatan nan da akeyi na layi
bamu da,kana gani su buhari fa,yarinyar nan ta bayan layinmu har dan wasiqa suke
aikawa junansu" kallonsa kawai lamin yakanyi

"Shekararmu nawa ne?"


"Sha bakwai mana,ni harda watanni ma"

"Tabdijan,a shekara sha bakwan har mukai wannan matakin?,meka ajjiye?,me kake
dashi?,wanne mataki ka taka a karatu?"

"Mtseeww,ka gane mana,bafa wai aure zamuyi bafa,kawai irin dai soyayyar nan da kowa
ke tabawa ce,ai abun kunya ne a yadda mukafi dukka samarin unguwar nan kyau amma
ace mune bamu da budurwa"

"Nidai a wajena ba abun kunya bane,amma tunda kai a wajenka haka yake,kaje Allah ya
bada sa'a" daga haka ya maida hankalinsa ga qaramar tvn dake gabansa,wanda suke
hasko wasan da ake bugawa ta gasar nahiyar turai,tsakanin Manchester da Barcelona.

       Yana jin sadiqun yana mitar yanzu kallon qwallon ma sudanje gidan kallo suyi
cikin mutane amma abu ya gagara,kowa yana can ma su suna cikin gida kamar mayu.

        Shi sam irin wadan na shirmen na tashen girma Allah ya tsameshi,baya bashi
sha'awa ko kadan,yadda yake gudanar da rayuwarsa yafi masa dadi,shi mamaki ma yake
idan yaga sa'anninsu suna soyayya,tome zasuce a wadannan shekarun nasu?,dariya suke
masa idan ya fadi hakan,sau tari sukance

"Dama mune muke da kyau irin naka?,kai don bakasan yadda 'yar mata matan nan ke
sonka ba,miskilancinka kawai yasa suke shakkar yi maka magana".

        Hannu lamin ya sanya kan locker din tasa bayan ya gama wannan tunanin,ya
ciro wani man fito da saje da qasumba da sadiq din ya siyo tun rannan,wurgi lamin
yayi dashi saman kujera

"Shi yasa dama ka siyo wannan saboda kayi sauri ka hada gemu kai dole gaka babba
ko?" Yadda lamin yayi maganar cikin jin haushi ya sanya sadiq qyalqyalewa da dariya
dole

"To wai kai din da kaketa haka waliyyi ne kai?,girman nan fa yana tahowa na gaya
maka gaskiya,don ko a yanzu haka habarka ta fara gemu,toni kuma saina zauna a haka
a rainani?,ko kai rannan ina ganinka kanata matse matse?,waye yayi wankan asuba
shekaran jiya?" Ya qarasa fada qasa qasa saboda kar a jiyosu.

        Kafin sadiq ya ankara lamin ya kwada masa wani comb da yake taje sumarshi,a
baki yaso ya sameshi Allah ya taqaita masa ya goce ya samu kafadarsa,sai yayi qofa
yana sheqa dariya

"Kaga kenan gwara ni,kiran girman kawai nake,kai kuwa ya fara samunka,idan ka gama
shiryawa ina jiranka a wajen inna" saboda wajen sana'arsu zasu wuce,don suna hutu
ne saboda sun kammala rubuta jarabawar qualifying,suna jiran wucewarsu S S3,bugu da
qari ma kuma weekend ne.

        Yana shiryawa maganar sadiq na dawo masa,a ranar ya faki idanun sadiq yayi
wankansa ne baisan yana ganinsa ba,bayason sadiq din ya sani,saboda yana kunyar
abinda zaice masa,duk da cewa daga shi har sadiq din ba jahilai bane,tun kafin
zuwan wannan lokacin malam ya musu bayanin xuwan nasa,saidai shi abun naso yazo
masa da wani yanayi na daban,yana jin cewa halittarsa ta dabance,don kusan bai taba
ganin ko ji daga sadiq din ya shiga yanayi irin nasa ba.

       A nutse ya shirya,kamar ko yaushe tsaf dashi,cikin wani yadi mai sanda sanda
me sauqin kudi,yayi kyau,dai dai da matashi mai qananun shekaru.

        A tsakar gida ya samu inna da sadiq din,ya miqe suna yiwa inna sallama,ta
rakasu da kyakkyawar addu'a da kuma fatan alkhairi,ta bisu da kallo tana jin
alfahari da 'ya'yan nata,wanda tsakanin sadiq din da lamin bata banbace wanda
tafiso a cikinsu,tun bayan shigowar lamin din rayuwar gidan.

      Tun qarfe uku ya katse dukkan ayyukansa bayan ya dauki uzuri waje ogansu ya
koma daukar iman din.

       Baifi jiran minti talatin yayi ba daliban daga makarantu daban daban suka
fara fitowa,yana tsaye harde da hannayensa ya hangota,ya zuba mata idanu yana
murmushi ganin yadda take waige waige,ya tabbatar da cewa shi take nema,yadan sake
sakayewa kadan don ya gani ko zata iya ganoshi,saidai batayi wani nisan zango ba
golden eyes dinta ya hango mata shi,saita taho da dan gudunta ma gauraye da
quruciya tana dariya,tana zuwa ta daneshi.

        A hankali yasa hannunsa yana zareta daga jikinsa,ita kuma tana sake
maqaleshi tare da fadin

"Ya lamin mun gama...."


"Imaannn" ya ambaci sunanta yana dan dagewa kadan

"Sakeni mana" turus tayi bayan ta sakeshi tana kallonsa,baki a tabe alamun shagwaba

"Yaya me nayi maka?"ganin yadda fuskarta ta nuna rashin jin dadinta saiya duqa a
gabanta yana duban golden eyes dinta

"Iman.....daga yau kin girma fa,kin zama babba,ko baki gani bane?,kin zana
jarabawar fita daga primary,zaki tafi secondary,duk wanda yaje secondry kuwa ya
girma.....wadda ta girma kuma ba'ason tana taba maza kinji?" Saita tura baki gaba

"Ni bana kula kowa Allah ya lamin,ko mazan ajimu ma Allah,kaine kawai,kuma kai ba
yaya na bane?" Kansa ya gyada yana sake fidda murmushi

"Yayanki ne,amma ko nidinma daga yau na hana kinji?saboda kin zama big girl" Kanta
ta gyada,saidai da alama har cikin ranta bata gamsu ba,yana ankare da ita yadda
tayi kicin kicin da rai,duk yadda yake janta da hira kan yadda taji jarabawar taqi
sake masa ta bashi labari,bai gaji ba yaci gaba da janta da hirar har suka iso
bakin titi don su tari abun hawa.

        Dalibai ne birjik da masu daukarsu,daga gefansa wata 'yar matashiya ce riqe


da hannun wata daliba,da alama qanwarta ce,tunda ya shiga wajen dauko iman ya lura
da yadda taketa satar kalloshi,dauke kai yayi yanzun ma kamar dazu,ya sanya
hannunsa cikin aljihunsa ya fito da baqin glass dinsa da yakan sanya lokaci lokaci.

      Sanyawar da yayi saita sake haska kyanshi cikin farar fatarsa,ya miqa hannu
yana tsayar musu da adaidaita sahu,gaba kadan dasu ta tsaya,ya taka ya tsaya yana
masa bayani inda zai kaisu.
       Yana shirin shiga yarinyar ta qaraso tana fadin inda zata itama

"Shiga muje" mai adaidaitan ya fada mata jin hanya daya ce,abinda yasa fasa sanya
qafafunsa,ya kuma dauke kwandon iman da ya zura a motar yaja baya yana cewa

"Kuje kawai" binsa ta danyi da kallo

"Dukkanmu qannenmu muka dauko,kowa gida kuma yakeson zuwa,kuma tunda yace muje ai
hanya dayace ko?" Ta fada tana dan fara'a,kai ya gyada

"Ga wasu 'yan uwanki can daga gaba,idan hanya daya zaku shikena sai ya cike dasu"
yanayin fuskarta ya nuna bataso ba,amma haka ta saka qanwartata itama ta shiga.

       "Yaya sun tafi fa,dama shiga kawai mukayi" sosai ya kalleta sannan ya amsa
mata

"Babu kyau hada maza da mata guri daya,nima bazanji dadi ba idan kika shiga keda
wani" tadai jishi ne,amma bata fahimta abinda yake nufi ba.

      Basu dade ba suka sake samun wani abun hawan,a hanya ya siya mata tarkacen
alawoyi,abinda ya sanyata sakewa kenan,ta dinga bashi labarin jarrabawar,da kuma
yadda ta amsa kowacce tambaya,don kusan duk abinda ya karanta mata shi taga ya
fito.

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥


_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥


_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅


_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥


_Mamuhgee_

Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa


1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼


👇

*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇

09166221261

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 🔥🔥 *KUFAN WUTA*🔥🔥🔥

NA

*HUGUMA*
*ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

*LAST FREE PAGE*

*_GA WADDA KE BUQATAN BIYAN KUDINTA,ZATA IYA TUNTUBARMU TA WANNAN NUMBERS DIN_*

09032345899
KO
09166221261

Tun bayan zana jarabawarta ya soma mata tanadin tafiya zuwa makarantar gaba
ba tare da kowa ya sani ba,ya siya duk abubuwan da yasan zata iya buqata da kadan
da kadan,zuwa lokacin ya fara canza yanayin kusancinsu,sabida girma daya fara zuwan
mata,a sannan ta shiga shekara ta goma sha uku,duk wasu abubuwa daya kamata ace ta
sani yana koyar da ita cikin dabara da kuma hirarsu,abubuwan da ya kamata diya ta
sani a shekarun fara girmanta,bugu da qari innarta itama ba baya bace,sau da dama
idan ya gaya mata wani abun takan ce inna ta gaya mata,saidai bata fiya daukarsa
serious ba kamar idan shine ya gaya matan,tafi maida hankali idan shine ya fada
mata da kansa.

Cikin sa'a jarabawarsun ta fito,taci wata government school da basu da nisa


da ita,ba bata lokaci malam ya fara mata shiryen shiryen komai,saidai ya tadda amin
yaci rabin aikin,shuru malam yayi cikin mamaki tare da qara qaunar amin din har
cikin jininsa,irin kulawa da iman ke samu a wajensa ko dan uwanta da suke ciki daya
sadiq bata sameta ba.

Bashi da abinda zaice masa banda godiya,godiyar da take saka amin din jin
nauyi da kunya,saboda shikam har yanzu a nasa ganin bai sakawa su malam din da
komai ba,don har kwanan gobe arziqinsu yakeci,sun sanyashi cikin iyalinsu,yana
kwana ya tashi muhalli daya dasu,kuma har kwanan gobe malam din bai daina ciyar
dashi da dauke masa wasu buqatu irin na uba da dansa ba.

Duk da haka malam din ya kwakkwafeshi kan ya dinga adani da tanadi,ya daina
qarar da duka nemansa akan iman din kadai,ya shaida masa yana taru,bai nutsu ba sai
daya samu tabbacin hakan daga bakin sadiqu.

Bangaren inna ma saidai addu'a da fatan Allah ya jiqan mahaifansa,amin din


hannun kyauta gareshi,abun duniya bai rufe masa idanu ba sam,kulli yaumin baya taba
shigowa hannunsa rabbana cikin gidan,wannan dabi'a tasa har sadiqu ya koyeta,hakan
kuma bai sanya ya manta da yayarsa dake garinsu ba wadda tasha dawainiya dashi
ba,duk sanda zaije ganinta yakan riqe wani abu me kauri yakai mata.
Cikin nasara iman ta fara zuwa makarantar,yarinya ce mai hazaqa da kaifin
basira,gefe daya kuma ga alamin,ya soke hirar dare saidai karatu,idan sun gama
karatun ayi hirar kafin inna ta korata ta kwanta,cikin qanqanin lokaci tayi suna
cikin makarantar.

Sannu a hankali rayuwa keci gaba da tafiya musu cikin nasara,iman ta gama
js 1 ta tafi js 2,har ta tafi zuwa js 3,a sannan tuni yammatanci ya fara zuwar
mata,duk wani baiwa da surar kyau na 'ya mace ya fara bayyana a jikinta,wani irin
sassanyan kyau wanda hatta da inna ya sanya take sake saka hankalinta da kulawarta
akan diyartata,don ko ita duk da tashen kyau da tayi zamanin quruciya bata kai iman
din ba,inda Allah ya taimaketa iman din nada wani irin nutsuwa da kuma kamun
kai,bata da hargagi ko hayaniya,ko rawar kan yaran da suke tashen girma.

Ta bangaren alamin ma ya sanya kulawarsa sosai akan iman din,bama shi ba


harda sadiqun da suke ganin kamar bai damu da al'amuranta a baya ba,saboda lokacine
na sabbabin qawaye,kuma lokacine da qananun samari da suma suke tashen girma suke
iya shiga rayuwar yarinya,su sauya ta tare da koya mata dabi'u kala daban daban.

A sannan Allah ya fara sanyawa nemansa albarka,don cikin shagon nasu da suke
dinki a yanzu haka shima ya mallaki keke nasa ma qashin kansa,idan bashi da
makaranta zama yake ya wuni yana dinkinsa,idan kuma yana da lectures sai ya bada
haya wani ya hau,da kudin dinkinsa yake sponsoring karatunsa da komai na
rayuwarsa,ya taimaki yayarsa da a yanxu babu abinda zatace dashi sai
hamdala,hakanan daga inna har malam gajiyar alamin din sukeci sai godiya.

Yana da tsari da kuma bin komai a sannu,bai dauki rayuwarsa da zafi ba,bai
kuma dauki kansa a wani ba,komai nashi moderate yake yinsa tsaka tsaki,babu qarya a
ciki,baya kallon wai collage yake,dole sai yayi abinda wane da wane sukeyi,idan ka
ganshi baka isa ka aibatashi ba ko kai waye,yana da tsafta da sutura ta zamani
bakin gwargwado,saidai duk abinda yasan zai zame masa wahala baya kawoshi cikin
rayuwarsa,hatta da wayar hannunsa mai matsakaicin kudi ce,bai damu da sai ya riqe
babba ba,tunda wannan din zatayi masa komai da babbar zatayi masa,yakanyi tunanin
gwara ya sanya kudin cikin sana'ar dinkinsa,don a yanzu wani keken yakeso ya sake
siya banda wanda yake dashi.

Dukkan wani rufin asiri da kuma kyautatuwar rayuwa ya sameshi,iya shi da


sadiqu a qananun shekarunsu sun tsayawa gidan,sun saukewa malam abubuwa da yawa su
sukeyi,don hatta da harkar karatunsu,kama daga kudin registration da sauransu su
sukewa kansu da kansu.

**********Kamar yadda al'adar gidan ranar kowacce juma'a tuwon shinkafa akeyi miyar
taushe,wannan juma'ar ma hakan take,gefin magariba IMAN ta gama komai,ta kuma
killace gidan kamar yadda ta koya daga mahaifiyarta,saboda a yanzun da shekarunta
suke goma sha biyar,dukkan wani aiki da ada yake wuyan innar yanzu ya dawo
wuyanta,ta horu da wannan tun tana da shekara goma a duniya,don haka sam komai baya
bata wuya a yanzu.

Tsaye take gaban dogon madubin dake jingine,wanda ya kusa rabin qofar
dakinta,gefe da gefansa sama da kuma qasansa an zagayeshi da katako mai kauri
saboda ya bashi kariya,tare da samun damar tsaiwa sosai a muhallin da aka
ajjiyeshi.

Daure take da zanin data fito daga wanka dashi,sai tasa hannu ta zare dan
qaramin hijabin da take xurawa duk sanda zata shiga wankan,take jiqaqqe gashinta
daya kwanta har gadon bayanta ya bayyana,yasha ruwa sosai,saboda wankan tsarki da
tayi na al'ada data gama.

Sai data sanya qaramin towel ta sake goge gashin nata sarai,tadan fifitashi
kadan yasha iska,sannan ta shafeshi da mai,ta kuma sanya cumb ta tajeshi,take ya
dauki sheqi,cikarsa kuma ta bayyana,taja kujera ya qarama da takan zauna akai idan
zatayi kwalliya,ta fara mulke jikinta da mayukanta da take amfani dasu.

A nutse ta gama shafa manta,ta shafe fuskarta da powder,tana yi tana duba


dan qaramin agogon dake manne a saman mudubin nata,wanda lamin ya siya mata,saboda
tashi tafiya makaranta.

Gaban akwatinta dake shaqe da kaya ta zauna tana duba kayan da zata sanya
din,batason ta saka wadanda zasu dameta,saboda zafi da akeyi,uwa uba ma kuma ba
jimawa zasuyi a jikinta ba zata cire ta saka na kwanciya barci.

Garin daga kayan idanunta suka sauka kan wasu kaya baqaqe masu adon farin
zare,da sauri ta sanya hannu ta daukosu tana waresu,sai yanzu ta tuna dasu,kayan da
inna rabi ta bata(yar uwar innarta),kaya ne na buzaye masu kama da saqin
fulani,saidai shi plain zani ne da kuma riga mai kama da buba,wadda iyakarta
cinya,kala biyu ne kayan,akwai jajayensa,dukansu ta ajjiyesu da zummar zata saka
kuma bata saka din ba,sai yanzu data binkito wajen ta gansu.

Miqewa tayi ta fara gwada rigar,ta isa gaban madubi,tar kamanninta suka
fito,baqaqe kayan sun kwanta saman farar fatarta sun qara mata wani irin kyau,sun
kuma tafi da qirar jikinta,duk kuwa da cewa a sake suke,sai ta dan soma jujjuyawa
kadan tana sin ta sake ganin yadda suka amsheta,tana qiyasta ranar da zata sakasu.

Qwalla mata kiran da inna tayi ya dakatar da ita daga abinda takeyin,tana
daga dakin ta amsa tana duba agogi,tasan ba shakka ta gota lokacin da take kaiwa su
ya saddiqu abinci,don haka ta rarumi zanin kawai ta daura,ta yafa dankwalin kayan
saman kanta.

Innar bata tsakar gidan,tabbacin cewa daga rumfarta take mata wannan
kiran,bata kai ga shiga rumfar innar ba ta jiyo muryarta tana fadin

"Ki dauki abincinsu aminu ki miqa dakinsu,ashe tun yammaci ya dawo bashi da
lafiya,bai qaraso ciki ba ya shige dakinsu ya kwanta abinsa,sai yanzu da abubakar
ya shigo yake gayamin" har cikin ranta taji wani rashin dadi jin cewa baijin
dadi,bai kuma gayawa kowa ba,bayan ita idan bata da lafiya bai barinta tayi jinya
ita kadai,tun daga zamanin quruciya har yanzu data fara sanin ciwon kanta,sai ta
amsawa innar da to,ta juya da sauri zuwa kitchen,ya debi kayan abincin data riga ta
shirya musu,wanda dama ba kasafai take kai musu ba,sunfi shigowa su dauka da
kansu,ta nufi soron tana takawa a hankali,cikin ranta tana fatan samun jikin nasa
da sauqi.

Tana dab da bakin qofar dakin nasu sadiq ya daga labulen ya fito

"Ki zubamin a plate ya dan sha iska,yanzu zan dawo" ya fada yana sanya
takalminsa,ta amsa da to kana tayi sallama ta saka kanta zuwa cikin dakin.

Babu kowa a dakin,sai motsin ruwa daga toilet din nasu,ko ina fes yake,sai
qamshin tsintsiyar turare da kuma turarukan da suke amfani dasu daya gauraye
dakin,tanason dakin tun ainihi,saboda yafi kowanne daki dake gidan sanyi da kuma
dadin zama,a zamanin quruciya,tasha shiga dakin ayita nemanta,har bacci yayi awon
gaba da ita.

Table din da tasan suna ajjiye karikicen kayan abincinsu ta qarasa kai ta
dora a nutse,sannan ta bude fa fara zuba lafiyayyen tuwon farar shinkada,da miyar
taushe wadda aka sakawa tantaqwashi,cikin mintuna qalilan qamshi ya bade dakin.

Plate biyu ta zuba harda lamin din,saita koma saman doguwar kujerar dake
dakin ta zauna,tana dakon ya fito tayi masa sannu,duk ranta babu dadi sosai,dama
kusan sati guda suna sabani dashi,basa haduwa sam,inna ta gaya masa yana wasu
dinkunan biki ne,shi yasa yake fita da wuri ya kuma dade bai dawo ba,ga kuma
makaranta.

Tana tausayin yadda yake nema tuquru,ya dauki sana'arsa da muhimmanci,fiye


da yayanta sadiq,don shi wasu lokutan yakan zauna a gida yace bazai fita
ba,musamman idan lectures suka hade masa ranar yasha wuya,amma bata taba ganin
lamin din yana hutu ba,idan tayi magana sai ya saki murmushin dake qarawa idanunsa
lumshewa yace

"Babu wani hutu a nan duniya,namiji kuma da struggling aka sanshi".

Yana da dabi'ar jimawa yana wanka,don haka sai ta tura hannunta cikin
gashin kanta tana dan warashi saboda ya sake samun iska,a hankali har dankwalinta
ya zame daga kanta,saita kamo gashin ta rabashi biyu ta fara kitsa kalba wai ko
zaifi saurin shan iskan.

Sai da ya sanya hannu ya sake sharce gashinsa da kyau,sannan ya kama murfin


qofar bandakin ya murdata ya bude a hankali cikin rashin qwarin jiki.

A hankali idanunsa suka fara sauka a kanta,tayi nisa da kitsa jelar


kalbar,kayan jikinta sun haskata ainun,har suna canza mata yanayi zuwa ainihin
bafulatanar niger kuma shuwa zam.

Bin jelar da take kitsawar yayi da kallo,zuciyarsa ta wani buga,sai ya


lumshe idanunsa kana ya budesu duka lokaci daya,maimakon dauke idanunsa da yayi
niyyar yi daga kanta,haka sai ya gagara,ya maida idanun nasa yana ci gaba da
kallonta

"Anya ko zaka iya ci gaba?,zaka iya daurewa?,zaka iya cika alqawarin daka daukarwa
kanka?" Jerin gwanon tambayoyin da ya jefawa kansa kenan,sai ya sake lumshe
lumsassun idanuwansa da zazzabi ya sake sanyawa suka rusuna suka kuma janye,ya
budesu lokaci guda yana qoqarin hadiye wani abu,kana yayi qoqarin jan qofar
bandakin ya rufe,lokaci guda kuma yana takowa zuwa cikin dakin,yana qoqarin daure
fuskarsa.

Motsin nasa yaja hankalin iman,bata damu da rashin walwalar dake fuskarsa
ba,saboda tasan cewa bashi da lafiya,qila shine abinda ya kawo qarancin walwalar.

"Sannu ya amin" ta fada cikin nuna tsantsar kulawa


"Yauwa" ya amsa mata a dan dake,saita sake zubawa fuskarsa idanu,yau kadai sai take
ga ya canza mata,wani girma da kwarjini da tsahon rayuwarsu tare bata taba gani
saman fuskarsa ba a yau take gani,kodon yaune ta fara yi masa kallon qurilla?,ko
don yaune kadai ranar da zata iya tunawa ya hade mata rai haka?

"Ina dankwalinki?,me yasa zaki bude kanki gaban abincinmu?,ko so kike ki haramta
mana ci?" Yayi maganar still a dake,hannunta ta sanya ta baya ta janyo dankwalinta
ta lulluba saman kanta,tun daga sanda ya horar da ita zama da dankwali,mawuyacine
ka sameta babu shi,maimakon ya zauna sai ya nufi inda kayan shafarsa suke,ya janyo
turaren da yake mulke singalalin hannayensa dasu ya fara shafawar,wannan dalilin
yasa komai nashi qamshi yake,komai nasa kana iya ganeshi saboda qamshinsa na daban
da yake yawan amfani dashi,abu guda daya cikin rayuwarsa da bai daukeshi da sauqi
ba,yana kuma iya sanya ko nawa ne ya siyeshi wato TURARE.

Bayan ya gama ya dauki na jikin ya fara fesawa,cikin lokaci qanqani


sassanyan qamshinsa ya budade dakin,iman dake zaune ta lumshe idanunta tana zuqar
qamshin har cikin zuciyarta,tana mutuwa da mayatar son wannan qamshin tun ba yau
ba,tayi tayi ya siya mata ko ya san mata nashi amma ya gaya mata turaren maza
ne,mata kuma basa sanya turare maza,dole ta haqura,take amfani da wanda ya zaba
mata,har kawo yau.
Bata ankara ba taga ya iso gaban flask din,ya bude flask din data zuba dan
farfesun busashen kifi datayi musu da sauran kifin da malam ya siyo musu tun
shekaran jiya waccar,basu iya cinyeshi ba saboda basu da yawa a gidan

"Ka kawo na zuba maka ya amin" ta fada tana kai hannunta da sauri kan
kwanukan,saidai cikin rashin sa'a sai hannayensu suka hadu waje guda,saboda ya kawo
nasa hannun ne shima don ya zuba,itama takai nata.

Da sauri ya janye nashi hannun,zuciyarsa na wani irin lugude cikin


qirjinsa,karon farko itama a rayuwarta data ji wani shock har cikin
jijiyoyinta,shuru ya ratsa na second guda,kafin ta rigashi sake maida hannunta tana
yunqurin zuba masa,tare dayi masa sannu da jiki,ranta da zuciyarta yana bata cewa
yau miskilanci ne ya hadu da ciwo hala,abinda ta jima bata gani ba tattare dashi.

Idanunya ya sauka kan jelar kalbar datayi guda daya,wadda keya reto gefan
kunnenta saboda tsahonta

"Da sauqi alhmdlh" ya amsa yana janye idanunsa,tare da lalubar kansa,wai yau din me
yake damunsa ne?,kamar yau ne ya fara ganin iman din.

Sosai yayi qoqarin hana idanunsa sake maida idanunsa kanta,saboda ya


tabbatar a yau din akwai wani sabon al'amari dake shigarsa wanda baisan dashi ba

"Shikenan yaya?" Ta fada tana sake nannade jelar kalbar cikin yatsanta guda daya
tana kuma kallonshi

"Eh" ya amsa mata a taqaice

"Allah ya qara lpy" ta fada tana juyawa zuwa hanyar fita,don ta karanci da gaske
yau 'yan miskilancin ne a kusa,ta kuma fi kowa sanin halinsa idan suka motsa
masa,idan ya sauko da kansa zai nemi inda take,ita kuma tayita qorafi kenan a
sannan,saidai yayi murmushi kawai yace baisan sanda shi hakan ta faru ba.

Baisan ita yabi da kallo ba sai da ta fita a dakin,idanunsa suka sauka kan
labulen dake lilawa,saiya dauke idanunsa da sauri,ya zamo daga gefan katifarsu ya
sauka qasa sosai yaja abincin gabansa,yanata qoqarin ganin yaci,saidai duk da hakan
tunani ne fal ransa.

Yana tuna maganar da sukayi da malam tun yana ajin farko a collage,malam
din ya masa kyautar da har duniya ta nade bazai taba mantawa dashi ba,ya shaida
masa ya bashi iman din halak malak,ya bashi ita a matsayin matar aure.

Sosai alamin yaji girma da nauyin kyautar malam din,bazaice baya son iman
ba,kamar yadda bazaice yanajin soyayyarta a ransa ba,soyayya irin ta aure ba,yana
mata soyayya irin ta 'yan uwantaka,saidai shi kansa yasan cewa matsayi ya bata a
zuciyarsa bana wasa ba,matsayin da take dashi a wajensa ba na nan kusa bane,saidai
koma mene a sannan yana ganin tayi matuqar qanqanta ya tunkareta da maganar
soyayya,tunda yaci mata buri da kuma tanadi nayin zuzzurfan karatu,ya karba hannu
bibbiyu kuma ya samu zuciyarsa tayi na'am da hakan,saidai ya barma ransa akwai
ajiyayyen lokaci da zai fara tunkarar iman din da dasa mata soyayyarsa ta hanyar
data dace,ta hanyar da bata kaucewa shari'a tsari da kuma al'ada ba,saboda haka ya
nemi alfarmar malam din bayan ya gabatar masa da qudurinsa,ya shaida masa babu
komai,shidai fatansa Allah ya sake hada kansu,sai gashi a yau rana tsaka ya soma
jin wani baqon lamari game da iman din,tun lokaci bai kai masa Target din da yayi
ba.

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥


_Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥


_Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅


_Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥


_Mamuhgee_

Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa


1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼


👇

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*_DUK WADDA TASA HANNUNTA TAYI MAN SHARING LITTAFI NA ZUWA WANI WAJE ALLAH YA BIMIN
HAKKINA DON ISARSA DA BUWAYARSA_*🤲🏽 🤲🏽 🤲🏽 🤲🏽
🏽🏽🏽🏽

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,ZAKI IYA TUNTUBARMU TA WANNAN NUMBERS DIN*

09032345899
Ko kuma
09166221261

06

Daki ta wuce kai tsaye don cire kayan,tana tafe tana hangen fuskarsa cikin
idanuwanta,bata taba ganin wanda miskilanci yakewa kyau ba irinsa ba,ba tun yau
ba,tun shekarunta basu kai haka ba tasan da wannan.
Sake shanshana hannunta tayi karo na barkatai tana sheqar qamshinsa data
dauko wajen saurin bude masa Flask din abincin,saita saki ajiyar zuciya,haka kawai
yau din take jin zuwan nata dakinsu wani iri,cikin kasala ta qarasa cire kayan,sai
ta zumbula doguwar rigarta kawai,ta dauki littafanta ta tafi dakin inna,saboda yau
ta tabbatar babu zancan karatu,tunda amin din baya jin dadi.

Sanda ta shiga dakin innar ta fita dubo amin din nata,babu jimawa ta
dawo,tana ta mitar yadda ya dawo ya shiga daki ya kwanta da ciwo a jikinsa bai
gayawa kowa ba,motsi kadan sai tambayo sadiqu jikin nasa,bata samu sukuni ba sai
data tabbatar da sauqin.

Wani abu daya tsayawa iman din a rai,yadda ta dinga juyi wajen bacci tana
hango fuskar ya amin din,sai zuciyarta ta dinga raya mata kodai laifi tayi
masa,qamshinsa daya nacewa hannunta ya dinga shiga hancinta,a ranar ta jima tana
juyi kafin ta samu bacci yayi awon gaba da ita.

Washegari abokansu na unguwa da wajen aiki daidaiku suka dinga zuwa


dubashi,abinda zai baka tabbacin yana da kyakkyawar mu'amala da jama'a,dole inna
tasa bayan ya dawo daga makaranta,da zata dora sanwar dare ta qara mudu,ta kammale
komai kafin magariba kamar yadda ta saba,ta shiga bandaki tayi wanka saboda zafin
da ake dan tabawa,sannan ta shirya ta dawo falo wajen inna sukayi sallar magariba.

Tana saman abun salla tana dakon baqin da suka shiga dakinsu ya sadiq din
su fita ta shiga ta dubashi,don da safe da zata wuce makaranta ta samu yana
barci,data dawo tanata aiki ga kuma 'yan dubiya,abinda yasa wunin yau gaba daya
bata ganshi ba kenan,duk sai takejin babu dadi,take kuma ji wani iri,kamar akwai
nisa distance dake shirin shiga tsakaninsu kenan,ta lura tun daga sanda ta shiga
js2 yayi bala'in sauyawa,ko wasa da dariya da zaman hira da suke ada yanzu babu
kaso casa'in cikin dari,saidai kulawar da yake bata babu abinda ya sauya

"Naji hayaniyar ta ragu,ki leqa kikai musu abincin,nasan halin amin,indai yana ciwo
bason abinci yake ba" tsam ta miqe tana gyara yafen mayafinta data yi sallah
dashi,sannan ta nufi kitchen ta debi abincin tayi soro.

Da sallama ta cusa kai soron,wata baqauwar murya ce ta amsa mata,matasa ne


guda biyu da zasuyi shekaru kusan daya dasu sadiq,daya na zaune saman daddumar da
aka shimfida masa saman ledar dakin,dayan kuma na zaune gefan katifar sadiq.

Dan daburcewa tayi kadan saboda yadda taga sun zuba mata ido,sam bata saba
cudanya da maza ba,uwa uba kuma ta zaci lamin da sadiq ne kawai a cikin dakin,saita
taras da akasin haka

"Yana bandaki,yanzu zai fito" daya daga cikin samarin ya fada ganin yadda tayi
turus,saita duqa a hankali ta ajjiye kwanukan,tana samun waje gefe daya ta tsugunna
don jiranshi ya fito bayan ta gaidasu.

Shuru yadan ratsa a tsakani,daya daga cikin samarin da tun dazu yake satar
kallonta ya fara janta da hira,da qyar take amsa masa tambayoyin da yake mata,qasan
ranta haushinsa na kamata,don me zai dameta da wata hira,bayan ita ba itace ta
kawota ba?.

Minti kusan takwas sannan ya bude toilet din ya fito,jikinsa da lema


sosai,har jallabiyar daya sanya tana mannewa a jikinsa.

Da ita ya fara hada idanu,kowannensu ya janye idanunsa daga na dan


uwansa,wani nauyi yau daya taji idanun nasa sunyi mata,rashin fara'arsa ta kwanakin
nan gaba ta sauyashi,ta sanya tana jinsa kamar wani baqo a wajenta.

"Ya amin....barka da dare,ya jikin naka?" Sai daya gyada kai yana hadiye
wani abu daya tsaya masa na haushi da takaicin junaid,saboda ya lura da irin kallon
da yake binta dashi

"Da sauqi alhmdlh..... I hope kinje makaranta?" Yayi mata tambayar dai dai sanda
sadiqu ke shigowa da lemukan fanta masu sanyi a hannunsa,sai maltina ta gwangwani
guda biyu,dama abinda yaje siyo musu kenan,da zummar idan ya dawo yaje ya dauko
musu abincin

"Naje yaya"

"Ma sha Allahu,qanwar saddiq ce da alama?" Junaid ya tambaya idanunsa a kanta yana
washe baki,bata amsa ba saiya gyada kai,ta maida idanunta tana kallon yadin mayafin
dake jikinta kamar ba bata ba

"Tubarakallah......kina aji nawa yanzu?"

"Js 3"

"Kune 'yan placement na bana ko?" Sai ta sake gyada masa kai kawai,don ta ankara da
yadda ya lamin din yayi dif kamar baya dakin,hasalima man shafawarshi yake budewa
zai shafa,saidai fuskarshi a dinke take tsaf

"Muje ki lalubi cokula ki bani" sadiq yayi saurin fada sanda junaid ke qoqarin jefa
mata tambayar,abinda ya sanyata miqewa sadiq yabi bayanta,duk da hakan sai da
junaid din yace

"Kaje ka dawo muyi magan.....ko mu fara da amin kafin ka iso" ya fada yana dariya
dariya,daya dan saurayin yana tayashi,suna dan duban amin da suke zaton zai
tanka,saidai baice dasu komai ba,hakanan yanayin fuskarsa na nan a dinke,abinda
yasa ya musu kwarjini ya kasa maganar dashi,don dama tuni sun dade da sanin
halinsu,tun suna 'yan qasa da shekara sha takwas,lamin din ba kowanne yayin magana
da shirmen magana yake tankawa ba.

Har sadiq ya dawo da spoon din ya zuba abincin suka fara ci yanayinsa bai
koma dai dai ba,yanajin sanda junaid din ke neman izini daga wajenshi ko sadiq din
ya gana da iman,domin yace shikam ta gama yi masa,yadda yaketa kodata da yabata
yasa wani abu yayi masa tsaiwar mashi a wuya,ya dinga jin kamar ya kai masa naushi
a fuska,abinda ya sanyashi miqewa ya fice zuwa qofar gidansu ya zauna saman dakali.

Fayau yau qofar gidan yake,saboda kusan dukkan almajiran malam sun tafi
ganin gida,sau biyu dama yake barinsu suje duk shekara ganin gida,su kuma dawo
lokaci daya sanda ya sanya musu.

Iskar zafi na kadawa sosai ta wajen,sai ya jingina bayansa da ginin


qofar gidan,ya lumshe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya,saman harshensa yana jin
wani daci daya tabbatar bayan na rashin lafiyar da yayi,harda mugun kishin iman din
daya tsinci kansa a ciki.

Baisan ya akayi haka ba,daga jiya zuwa yau gaba daya iman din ta birkita
zuciyarsa,sonta ya taso masa da wani irin qarfi da a baya bai taba jin makamancinsa
ba,daga jiya zuwa yau kuma da abokansu wajen mutum hudu ke taya iman din sai yaji
ya kasa sukuni,shigowarta na qarshe da daddare kawo musu abinci ya sanya yayi mata
kallon qurillar daya tabbatar da cewa eh tabbas ta girma ta kuma fara zama budurwa.

Bai dauka cewa girma zai zowa iman din haka gadan gadan ba,duba da
yanayin jikin fulani da take dashi,to ashe duk ganinta da yake cikim hijabi yasa
yake wannan hasashen,girma da murjewa take ta ciki ba tare da an ankara ba,har ga
Allah bazai iya fadan yadda ya dauki bashi itan da malam yayi da matuqar qima da
daraja ba,saboda kima da mutuncinsu da yake gani,to amma ya sakawa ransa cewa bazai
tunkari iman din da wata magana ta soyayya ba a yanzu,zaici gaba da bata kulawa ne
kamar yadda suka saba a baya,har sai ta shiga ajin qarshe ko na kusa da qarshe na
kammala secondary dinta.

Tun ba'ayi nisa ba ya gane akwai gyaran daya kamata yayiwa tarayyarsu,kamar
yadda suke kusa da juna koda yaushe din nan ya kamata ya janye,ta dinga kallonsa a
matsayin yaya da gaske,don tun farkon girmansa ya fuskanci cewa yana da wata dabi'a
a halittarsa a matsayinsa na da namiji na yawan sha'awa,inda Allah ya taimakeshi me
yawan kamewa ne shi,banda hakan......yadda 'yammata ke mutuwar sonsa.....iya cikin
matan dake kawo musu dinki kawai,banda na 'yan ajinsu a makaranta,gefe guda kuma ga
'yan unguwa da sauransu,wannan ya sanya ya sake janyewa iman din,abinda yaketa bata
mamaki kenan da taraddadin shin me tayi masa ne?,duk da cewa qasan ransa shima
baijin dadin hakan,saidai hakan shine dai dai,kuma zai sanya nutsuwa a zukatan
malam da inna,koda basu nuna masa hakan saman fuskarsa ba.

Tsakiyar tunaninsa yaji hayaniyarsu junaid suna fitowa,suka masa sallama


ya amsa musu sama sama,ya bisu da kallo sanda sadiq ke taka musu zuwa bakin titi
sunata hayaniyarsu irin ta samari,sai ya bisu da kallo har suka dan kaucewa
ganinsa.

Ba jimawa yaga dawowar sadiq din,ya qaraso inda yake zaune ya dafa
kafadarsa

"Tashi mu koma ciki,wajen na akwai sauro,ko gama warkewa bakayi ba kazo ka zauna ka
baza masa jikinka yanata gutsira a banza" yunqurawa yayi ya miqe cikin qarfin hali
yabi bayan sadiq din zuwa cikin dakin nasu.

Sunwa wajen kaca kaca kamar yadda akasan yanayin cin abincin maza samari
yake,yana jin sadiq din ya buda murya ya fara kwadawa iman din kira,yasan kuma cewa
zaiyi tazo ta gyara wajen ta kwashe kwanukan,sai lamin din ya dakatar dashi

"Dakata malam,kuturu ne kai da bazaka iya kai kwanuka ba?,ni idan na gama zan gyara
wajen,daga yau ma banason ta sake kawo abinci indai akwai baqi a ciki,saidai idan
kaine a ciki" waiwayowa yayi ya zubawa lamin din ido,ya karanci tsabar gaskiyarsa
yake fada saman fuskarsa,sai ya saki murmushi ya dawo ya zauna gefan lamin din

"Duk da cewa bani na kar zomon ba....amma zan baka shawara,kada ka tsaya kallon
ruwa kwado yayi maka qafa,diya mace duk yadda kake raina girmanta tasha kan
tunaninka,kana mata kallon kamar tayi qanqanta da soyayya,ka gwada mata bayani kaga
idan bata dauke karatun ba gaba daya,ni na rasa abinda ma kake jira,an maka kyauta
an kuma baka dama amma ka tsaya wani tsari naka?,ka saka kai kawai,Allah ya bada
sa'a" sadiq ya qarashe yana dukan kafadar lamin.

Yana cin abincin yana tattauna zancan shi da zuciyarsa,akwai kunya soyayya
da yarinya tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta,mutanen da yake musu kallon
mahaifansa,abu daya ya yankewa ransa,zai fara bata kulawar data banbanta da irin
wadda yake bata a baya,zai fara dafa zuciyarta da soyayya ba tare da ya furtata
gareta ba,ta yadda da kanta zatayi dako ta kuma zaqu da ranar da zaya furta mata
din,saiya saki wani murmushi wanda ya qawata fuskarsa data dan qara haske kadan
sabida zazzabin da yasha.

*********Kamar kowacce rana da bata da makaranta asabar ko lahadi,yauma haka ta


tashi tayi dukkan wasu aiki na gidan,kama daga shara wanke wanke da kuma dora karin
safe.

Ta gama komai tas inna na daga rumfarta tana sallar walha,ta debo kayan data
bata din zuwa bakin famfo nan tsakar gida,sannan ta koma kitchen tana goge duk inda
ta bata din.
A nutse yake takowa zuwa cikin gidan,sanye da jallabiyyarsa da yake amfani
da ita yawancin lokuta idan ba fita zaiyi ba,hannunsa riqe da ledar da mlam ya
bashi ya kawo cikin gidan bayan sun gama karatun da sukeyi duk safiya da wurwuri
bayan an tashi almajirai.

Kai tsaye ya isa rumfar inna da sallama,ya cire slipper dake qafarsa ya
shiga.

Tana zaune saman abun sallah tana jan carbi,fuskarta ta wadata da murmushi
sanda ya tsuguna a gabanta yana gaisheta,cike da kulawa ta amsa masa tana sake
tambayarsa qwarin jikinsa,duk da cewa ya warware

"Alhamdulillah na warware ai inna,yau ma zan fita aiki in sha Allah"

"Ma sha Allahu,Allah ya qara lafiya"

"Ameen inna...ga wannan ledar,malam ne yace na kawo a dafa masa"

"Tana kitchen ai,saika miqa mata,kace kada ta cika masa yaji da yawa" innar ta fada
bayan ta bude taga meye a ciki,ya amsa da to ya miqe tsam da ledar ya nufi kitchen
din.

Ta bada hankalinta ga aikin da take sosai taga kamar inuwar mutum cikin
kitchen din,abinda ya sanyata zabura kenan,ta waiwayo da sauri,har tsummar hannunta
tana faduwa a qasa.

Idanu suka hada dashi,yana tsaye jingine da jikin qofar,ya zuba mata idanu
yana binta da kallo,gabanta yayi wani mugun faduwa,kamar karo na farko kenan data
taba ganinsa,cikin sanyin jiki ta duqa don ta dauke tsummanta tare da cewa

"Ya lamin.....ka bani tsoro" kusan a tare suka duqa din,shine ya samu nasarar dauke
mata tsumman,suka dago a tare,idanunsu ya fada cikin na juna,yadan ja baya kadan
saboda sunyi kusanci da yawa,ya miqa mata yana ci gaba da kallonta tare da cewa

"Dama can matsoraciyar ce" idanunta ta janye daga nasa,saboda nauyin da taji
zuciyarta nayi,qamshin turaren jikinsa yana busowa zuwa cikin kitchen din,kai
bakace baiyi wanka ba,tsabar abotarsa da turare ne kawai,yayi wani fresh 'yar cutar
da yayi kwana biyu,sai sumar kansa dake adan hautsine saboda bai gyara ta ba,daga
sallah makaranta suka zauna kawai,hakan kuma sai ya qara masa kyau.

"Yaaa banfa zata ba" ta fada da salon shagwabar data saba masa magana a baya,sautin
muryarta yaji ya tabashi,ya kuma saukar masa da kasala,ya sauke boyayyar ajiyar
zuciya,tare da dora ledar hannun nasa kan kantar da take gogewar

"Barka da safiya yaya,ya jikin naka?" Ta furta tana kaucewa kallonsa,saboda wani
yanayi da takeji duk sa'ar data kalleshin

"Alhamdulillah,na warware.....gashi nan,malam yace adafa masa,inna tace karki cika


yaji da yawa" a marairaice ta waiwayo

"Yaaya,na gama komi fa,Allah saura wanke wanke,kwanciya nakeso nayi" yadda tayi
masa maganar ya sake tafiya dashi,sai ya harde hannayensa a qirji ya zuba mata
idanu harta gama,duk da bashi take kallo ba,amma tanajin idanunsa a kanta

"Yanzu idan mijinki yace yanason ki dafa masa abu kamar haka hakan zaki ce?"
Banbarakwai taji maganar tasa,fa waiwayo da sauri sai taga ita yake kallo,fuskarsa
ta wadata da murmshi
"Inna na miki haka ne saboda tanason ki gina gidanki da kulawa,ki shagwaba mijinki
da soyayyar da zatasa ki tsaya masa a zuciya" wata irin kunya ce ta rarrafo ta
rufeta,saboda yanayin yadda yake mata maganar kawai ta sanya taji kamar qasa ta
tsage ta shige,wannan kuwa ya lamin dinta ne?,magana yake mata da wani irin sound
da bata sanshi dashi b,wani irin kallo na daban da sexy eyes dinsa,gaba daya taji
kaman ya zare mata laka,sai ta juya tana ci gaba da aikin a hankali,kunya na
nuqurqusarta.

Bata ankara ba har ya dauki kwanon dake kusa a ita ya juye kifin a ciki
yana cewa

"Tunda raguwa ce ke bari na tayaki" tare suka dawo tsakar gidan,tana wanke
wanke,shi kuma yana gyara mata kifin,gaba daya sai ta jita cikin wata takura da
bata taba jin irinta ba tsakaninta da lamin din,saboda duk wani motsi ko daga kai
da zatayi saita samu tagomashin wani kallo da ta kasa farrasa na meye?,saidai yana
sanya zuciyarta karyewa da kuma yin laushi.

Ya sakankance sosai abinsa,yanata aikata mata da kallon da yake da


tabbacin zai wuce kai tsaye zuwa cikin zuciyarta ne yayi masauki me kyau,koda bai
furta komai a gareta ba,baya da fargaba saboda inna tace zata shiga tadan
kwanta,malam kuwa yayi baqi a waje,wanda yasan yawanci idan sukazo sukan dauki awa
biyu tare kafin su tafi,sadiq kuwa baida matsala dashi,shi ba baqonsa bane bare
yaji kunyarsa.

Kusan tare suka gama komai da ita,sannan ya wuce dakinsu bayan ya sanyata ta
saka masa ruwan wanka.

*HILTI UNISEX CHOCOLATE*

*_chocolate ce ta musamman daga qasar TURKEY_*

*_Maganin matsalarki hajiya keda mai gida cikin tsari babu yane yamen magunguna_*

*Ki tuntubi wannan number don k'arin bayani*

08184017452[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 07

*_ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA'AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR


HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH
YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA KUMA BASU HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI
AMIN._*
__________________________________

_SAKINA VENDIBLES_
_SAKINA VENDIBLES_
_SAKINA VENDIBLES_

_(INDE HARKAR TURARUKA NE MASU KAMA JIKI DA GIDAH KAI HARDA TSUGUNNO. SAKINA
VENDIBLES ITACE KAN GABA)_

_SUNA DA KAYA INGANTATTU MASU MATUKAR KYAU AKAN FARASHI MAI RAHUSA.)_

_KINASON ASAN KIN ISA MACE? WADDA ZAKUYI GOGAYYA DA MASU SAKA DESIGNER TURARE AMMA
KI FUSU KAMSHI? DUK INDA KIKA GIFTA ASAN EH. KEDIN TABANCE , KIN ZARCE SAURAN
MATA)_

_AKWAI KHUMRAH WHITE AND BLACK_


_KULACCAM BLACK (FOR HAIR( AND WHITE FOR BODY_

_WASU DAGA CIKIN KAYAYYAKIN MU SUN KUNSHI👇_

Turaren wuta list*


Queens special
Kajiji mix
Kajiji whole
Gabgab
Brown Hawiii
Special Halut
Sandal balls
Sandal strips
Sandal flakes
Dubai oud
White Hawii
Classy Dufr
Black bange
Black bange
Musky Dorrot(Na tsuguno)
Cous cous

*_DA SAURAN SU DA YAWA_*

*_Handles_*
*Instagram* @sakina_vendibles *Facebook*
@Sakina vendible *Tiktok*
@Sakina vendibles_

Tsaye take gaban mudubin nata tana karanto addu'o'i,bayan ta gama shirinta
tsaf na tafiya makaranta don zana jarabawar placement,kamar kullum,tayi kyau cikin
uniform din da a kullum idan ta saka zaka dauka ta sanyashi ne da nufin gayu ko
ado,saidai sam ba haka bane,qirarta ce,haka Allah ya yita,fatarta na daukar kowanne
irin nau'in dressing.

Lokaci daya gabanta ya dan fadi,ta kuma lumshe idanunta sanda ta jiyo
muryar ya al'amin yana tambayar inna bata fito ba,wannan wani baqon yanayine da
bata jima da tsintar kanta a ciki ba,a duk sanda zataji murya ko motsin ya al'amin
din.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana wara idanunta da suka dauki mintuna
a kulle sanda ta tsinci muryar inna tana kiranta,cikin yanayi na me kama da me
alhini ko tsoron haduwa da ya al'amin din ta zura takalmanta half cover masu
kyau,wanda al'ameen dinne ya siya mata,kamar yadda fiye da rabin komai nata da take
amfani dashi na rayuwarta.

Dashi suka fara hada idanu sanda ta fito tsakar gidan,saita sauke idanunta
daga kanshi da hanzari saboda yanayin kallon da ya jefeta dashi,wanda shi kansa
baisan yayi ba,tayi masa kyau sosai yau din,duk da ya saba ganinta amma yau din
kamar an qara mata girma da shekaru,itama cikin ranta take tadinshi,yayi wani kyau
cikin shadda light blue daketa qyalli,bisa alamu sabuwa ce kar,yau ya fara
sanyata,hakan kuma baya rasa nasaba da daurin auren dan abokin malam din da
zashi,wanda malam dinne ya wakiltashi yaje,saboda a jiya shi ya wuce Niger,can
dangin inna da akayi mata rasuwa zai musu gaisuwa.

Ko kadan bata zargi kanta kan yadda takejin sauyi da baqunta tattare da ya
al'amin din ba,saboda ita kanta tana ganin kamar shima ya sauya,kallo da yanayin
firarsu gaba daya ya canzata,bata saba jin nauyinsa ba idan suna hira a baya,tana
hira dashi kamar yadda takeyi da ya sadiq,amma a yanzu tanajin akwai wani banbamci
a tsakaninsa da ya sadiq din.

Tana qoqarin gaidashi inna ta fara mata fada

"Kinsan yana jiranki zaki shiga ki zauna....."


"Innaaa.....bansan lokaci yayi bafa....girkin nan shi ya cinyemin lokaci" ta fada a
shagwabe kamar yadda ta saba,boyayyen murmushi ya kubce masa,abun ya zame mata
cikin jininta,ta saba maganarta a haka,abinda ke sake daukan hankalinsa dangane da
ita kenan,duk da yana qoqarin boyewa da kuma dannewa
"kaima duk da kai aminu,da tafiyarka,tasan hanya ai,ta tafi da kanta"

Baice komai ba,yadan saki sassanyan murmushin nan nasa,sannan ya matsa


inda ta hada komai nata ya sanya hannu ya dauka yana fadin

"Mun wuce inna,daga wajen daurin auren shago zan wuce"

"Ba zaka dawo ka karba abin karin naka ba" sumarsa irinta buzaye daketa qyalli ya
shafa da hannunsa

"Ina da ayyuka da yawa ne inna.....akwai dinkin wata amarya da nake,nace mata tazo
jibi ta karba,banaso tazo ban gama ba" kai inna ta gyada,ta sanshi da matuqar
qoqari wajen cika alqawari,mutum ne shi kaifi daya,mai matuqar qoqarin ganin ya
cika alqawari,sam bashi daga cikin jerin layin teloli

"Haka ne,to Alla ya dafa ya tsare mana ku,sai kun dawo"

"Ameen inna" suka amsa gaba dayansu,sannan ya sanya iman a gaba suka fice.

Cikin jikinta take jin kunya nauyi da kuma wani irin yanayi,yayin da shi
kuma tunaninsa yayi nisa game da yadda zai tafiyar da koma a tsakaninsu bisa tsari
da tsafta,tafiyar sai tazo da sabon salo,saboda ba haka ya saba rakata zana
jarrabawa ba,sau biyu tana satar kallonsa,ya ganta sarai,amma sai yayi kamar bai
ganta din ba,har zuwa sanda sukayi tsaye a bakin titi suna jiran abun hawa,daga
layin cikin layin da yake facing dinsu,wata mata dake sanye da uniform fari da
ash,wanda hakan ke alamta ma'akaciyar jinya ce wato (nurse) take tunkaro bakin
titin,dukkaninsu sun ganta,har zuwa sanda ta iso titin daga daya tsallaken ta tsaya

"Kamar haka nakeson ganinki.....ina miki sha'awar karatun jinya,ina miki sha'awar
ilimi me zurfi"muryar al'ameen wadda ta fara cika da amo na mazantaka a 'yan
watannin nan ta ratsa kunnen iman din.

A hankali ta daga kanta ta sanya dubanta ga matar,tun ba yau ba dama ta


sani wannan shine burin al'amin din a kanta,ta dade da haddace hakan,kusan kowa a
gidan ya sani,don haka sau tari idan suna irin wannan hirar ma babu me ce musu
uffan,tsakaninsu ne

"Kiyimin alqawarin zaki cikan wannan burin" cikin mamamki kalamansa ta daga idanu
kamar zata klalleshi amma kuma ta kasa,saboda tuna yadda take ji,da kuma yadda
idanuwansa ke mata nauyi yanzun a jiki da zuciya

"Bake da kula kowanne irin saurayi,bake ba soyayya" lafazin nasa ya ratsa ta


tsakiyar tunaninta ya katse mata shi shi wani sauti mai taushi kuma qasa qasa.

Wata irin kunya ce ta dirarta mata,ire iren maganganunsa kenan da suke caza
mata kai,da kuma sake sanyata jin kunya da nauyinsa,maganganun da a baya baya mata
su,tadan sadda kanta qasa,qaramin murmushi yana qwace mata
"Eh,wannan ce hanya daya da zaki taimaki cikar wannan buri nawa,ki bari,idan lokaci
yayi,ni zan zaba miki ɗanɗasheshen miji da zai dace dake" qarasa rufeta kunyar
tayi,sai ta kare fuskarta da hannunta tana cewa

"Ni ban kula kowa ya al'ameen,kuma ma waye zai kulani nima?,dubeni fa?"
Murmushi ne ya qwace masa sanda ya saka hannu yana tsayar musu da wata adaidaita
sahu sannan ya bata amsa

"Kina da kyau imani....ke kyakkyawa cw ta ajin qarshe ko farko zance,irin


kyan dake jan hankalin kowannw namiji....wanda ke ba zaki gane hakan ba,amma a
taqaice,ke sarauniya ce" wanda tun daga ranar ta samu sunan queen daga wajen
al'amin,sunan da ya koma kirata dashi lokaci lokaci,musamman idan ya zamana babu
malam ko inna a wajen,don ta sadiq dama ya maidashi kamar wani kakansa,ba wai kunya
ko nauyinsa yakeji ba,yayin da sunan ya tsayewa iman,yake kuma matuqar yi mata
dadi,zuciyarta nata mata saqe saqe akan al'amin din,me yasa ya canza?,me yasa yanzu
yake tsaye mata a rai?.

Cikin guntar karatun litattafan hausa data fara a boye ya samu amsoshi da
dama,saidai kuma har yau bai furta mata ina sonki iman ba,to hakan meyake nufi?.

*******. ******. ********

Tun dazun data zauna a wajen hankalinta yake rabi da rabi,daya a wajen,daya
kuma ya karkata kan jinkirin shigowar al'amin gidan yau,sau biyu tana tura
almajiran gidansu suna gano mata rumfar karatu ko yana wajen malam sai ace mata
baya nan,tunda ta gama ayyukanta tayi alwalar magariba ta shimfida musu tabarma ita
da inna a nan wajen sukayi sallah take saka ran shigowarsa,amma shuru kakeji,gashi
har qarfe tara na dare na haramar yi,har sadiq ya shigo yaci abincinsa ya sake
fita.

Ta gwada kiransa ta wayar inna kuma sau uku ana ce mata a kashe wayar
take,har inna dake jin radio ta rage sautinta tana jajjabin rashin shigowar
tasa,wanda bata sauke ba sai ga sallamarsa.

Wani boyayyar ajiyar zuciya da batasan daga inda ta taho ba iman din ta
sauke,shi dinma koda ya shigo idanuwansa suna kanta,ta miqe a kunyace a kuma nutse
tana gyara daurin dankwalinta tare da qoqarin yi masa sannu da zuwa tana yunqurin
karbar ledojin hannunsa

"Yauwa Queen" ya furta qasa qasa yadda innar ba zata jiyo ba,saita saki murmushi
tana dora kayan saman daddumar data tashi a kai,inda shi kuma ya qarasa yana zama a
kai tare da yiwa inna barka da gida,ta miqe daga kwanciyar da take tana amsa masa
tare da tambayarsa dadewar da yau yayi,har tana shirin tura sadiq ya dubosa.

Murmushi yayi yana jin dadin yadda har kullum inna ke nuna masa qauna da
soyayya irinbya da da uwa

"Aiki ne yau ya riqeni inna,ban gama musu ba,kuma gobe zasu shigo da safe su
karba,na katse ne na shiga kasuwa,shi yasa dinkin ya kaini har dare" jinjina kai
inna tayi,tana sake jin qaunar al'ameen din cikin rai da zuciyarta,har kullum shi
mutum ne dake sanya cika alqawari gaba da komai a rayuwarsa,ya tsani saba alqawari

"Sannu da qoqari,Allah yayi jagora"


"Ameen inna" .

Iman na daga kitchen tana qoqarin hado masa abincinsa tare da dora masa
ruwan wanka take jiyo hirar tasu,ta hada komai a nutse a kuma tsaftace kamar yadda
inna ta horar da ita ta fito dashi zuwa inda yake zaunen.
"Sannu da aiki autar inna" ya furta cikin kulawa,ta saki murmushi bayan ta
duqa ta aje a gabansa

"Kinga bar abincin nan,zo kiga.....siyayyarki ta tafiya nasreen memorial academy"


sosai maganar tayi mata ba zata,makarantar da inna ta kusa dukanta a kanta,saboda
yadda ta nace ta kafe tanason makarantar,ita kuma inna ta haneta da zancanta,saboda
private school ce da duk term ake biyan kusan dubu goma sha biyar,innan kuma tasan
matsawar alamin din yaji tofa sai ya kaita,shi yasa ta sanyata a daki ta ja mata
kunne,koda ta sanarwa malam murmushi yayi

"Bansan ko tabarar auta ke damu hajar ba,banda haka.....yaci ace wasu abubuwan zuwa
yanzu tafara ragewa,yaron nan hidima da kuma bautar da yake mata ko ciki daya suka
fito iyaka kenan,kinyi dai dai,taci gaba da zuwa ta gwamnatinta yadda ta saba,tunda
ita takeyi tun tasowarta,kuma tana da basirar gane abubuwa,gashi lafiya lau komai
ke tafiya"

Laqwas jikinta yayi sanyi sanda yake fiddo siyayyar da yayi mata yake kuma
shaida mata sati me zuwa zata fara zuwa,an gama koma,idanunta suka ciko rau rau da
qwalla tana satar kallon inna,tana tsoron kada tace itace ta tusashi gaba ka dole
sai ya kaita,ko kuma ita ta gaya masa zabinta.

Ta bangaren innar ma jikinta sanyin yayi,wane irin yaro ne al'ameen din?,ta


tabbatar yinin da yayi har dare a shago kudin wannan siyayyar ya hada ya kashewa
iman din gaba daya,tabi kayan da ya zazzage din da kallo,litattafai ne tari guda,
school bag,takalmi me kyau da 'yan makaranta,biruka da pencils,hatta da uniform din
makarantar gashinan a dinke a goge sai sanyawa kawai.

Fada sosai inna ta rufe iman dashi,wannan karon harda al'amin din,kan me
yasa zai dinga biyewa iman din da duk abinda tace tana so,ita din 'yar wace da
bazata ci gaba da zuwa makarantar gwamnati ba,kamar yadda saura suke zuwa?.

Sosai yaji babu dadi saboda kukan da yaga iman din tanayi,saida inna ta
soma sassauta fadan sannan ya mata magana cikin kwantar da kai,yana mata bayani
zafa fahimta banbamcin karatun makarantun gwamnati da kuma da na kudi,tare da nuna
mata shima yana sha'awar ya canza mata makaranta dama,bawai ita ta sakashi ba,ya
dade yana wannan tanadin.

Saida inna ta tabbatar ba iman ce ta tursasashi ba sannan ta fara


saukowa,saidai duk da haka bata bar mita ba

"Yanzu kai da kake da nauyin 'yar uwarka a ka,ga naka karatun,sanna kuma ka dauka
duk wata lalurar iman ka rungume?" Murmushi kawai ya sake

"Ba komai inna,Allah zaiyi,mudai aci gaba da yi mana addu'a.....sannan don Allah
inna karki sake cewa komai sadiq yaji" ya fada da sauri,saboda jin muryar sadiq din
dake shigowa da sukayi,kuma yaga reaction na fuskar iman,yasan sadiq din dan hada
waje ne,maimakon ya gyara saidai ma ya bata,saidai duk da hakan daya shigo shima
sai daya tofa albarkacin bakinsa,magana dai bata mutu har shigowar malam,shine ya
yayyafawa abun ruwa,ya sanya albarka a ciki,ya kuma ja kunnen iman,sannan ya kebe
da al'amin din bayan kowa ya tashi ya basu waje.

"Yanzu kai malam al'ameen haka za'ayi dakai?" Cikin fargabar ko wani laifi
ya yiwa malam ya daga kai ya dubeshi,malam din ya fahimci abinda ke yawo saman
fuskarsa,sai ya saki murmushi

"Kai da zaka zama magidanci nan gaba,haka zaka zauna sai abinda takeso zakayi
mata?,shifa namiji kullum so ake ya zama tsayayye,yana da kyau a dinga bawa mata
dama kan raayi da zabinsu,amma kuma bafa akan komai ba,qarqashinka zata zauna nan
gaba kadan,to dole tun yanzu ka dinga azata akan tsari da tafarkin da kakeso ta
kasance akai" cikin hikima malam din ya dinga nusasheshi,daga bisani kuma suka fada
hira,wanda wannan ba sabon abu bane dama tsakaninsa da malam din ba,sunawa juna
kallo da da mahaifi ne.

Ya jima yana nazari kan maganganun malam,su suke ganin kamar yana biyar son
ran iman dinne,wanda sam shi ba haka bane,duk abinda yakewa iman....tun kafin ya
soma jinta da wani matsayi daban a cikin zuciyarsa kawo yau,yana mata ne saboda ta
cancanta ta kuma dace yayi mata hakan,sau tari kuma zabu da ra'ayinsu ana samun
arashi yana zuwa daya,iman din ta dabance cikin rai da rayuwarsa,duk da yana ganin
abubuwa sosai tattare da ita,ita dinma kamar ta canza,amma nan gaba kadan zai
qarasa bude mata komai,yana son yabi komai ne bisa tsari na hankali da dacewa,da
wannan ya kwanta a ransa.

*ZAFAFA BIYAR 2022*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_


_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKANFARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE
A TUNTUBE  MU TA_

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa


1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼


👇

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

YAN NIJAR 👇

+227 95 16 61 77

Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number
______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY


INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 08
*_LITTAFIN KUDINE,ZAKI IYA TUNTUBAR WADAN NAN NUMBERS DIN DON SIYAN NAKI_*

09032345899
Ko kuma
09166221261
_______________________________

Misalin takwas da rabi na safiyar ranar litinin din,zaune take saman doguwae
kujerar dake falon principal din nasreen memorial academy,tayi neat cikin shigar
uniform din makarantar da shima ya karbeta fiye da makarantar data baro,idanunta
sunyi narai narai tana kallon al'amin daya miqe yana sallama da principal din,bayan
sun gama komai shi da sadiq sun damqata ga hannun hukumar makarantar,baqunta take
ji sosai cikin wannan makarantar,tamkar yau ne rana ta farko data fara zuwa
makaranta,al'ameen ya waiwayo a nutse ya sanya hannunsa a aljihun wandon lallausan
yadin jikinsa da iya tsahon rigar ya tsaya a gwiwarsa,ya ciro 200 ya miqa mata

"Idan ba zaki iya komawa gida ba ki jirani na dawo,sai na maidake" hannu tasa tana
amsa
"Zan iya yaaya" ta amsa mishi a tausashe,principal din yayi murmushi

"Wannan qanwar taka da alama kana ji da ita" ua fada cikin salon barkwanci,sai
al'amin ya waiwaya ya dubeshi sannan ya saki murmushi

"Auta ce"
"Oh....i see" ya sake sakin murmushi ya musu sallama yabu bayan sadiq suka fice.

Tana zaune nan tana rarraba idanu,har principal din ya kira daya daga
cikin masu goge goge dake aiki a makarantar,tayi masa kiran Assistant monitor din
ss 1,ba jimawa ya dawo yace tana zuwa.

Ba'a rufa minti biyar ba tayi sallama,cikin nutsatsiyar muryarta,tana


sanye da uniform irin na iman din,iman din ta bita da kallo,tana da haske saidai
baikai nata ba,tana da madaidaicin kyau,a qiyasce shekarunsu zasuyi daya da ita

"Ga new student nan,ayi mata seat,sannan a shigar da sunanta cikin register"
"Okay sir" ta amsa a ladabce,sannan ta waiwaya zuwa sashenbda iman ke zaune.

Suna hada idanu ta sake mata murmushi,saita soma takawa zuwa inda take din
tana dubanta,har yanzu kuma murmushin bai bar kan fuskarta ba,ta duqa ta dauki hand
bag din iman din tana cewa

"Taso muje" saita miqe tana dan jan rigarta tabi bayan yarinyar.

Tare suka jera cikin yanayin baqunta,saita waiwayo ta sake sakar mata
murmushi

"Sunana munira hasan......nice assistant monitor na ss 1,monitor dinmu namiji


ne.....kefa,meye sunanki?"

"Hajar ibrahim khalil"


"Yadda kike da kyau haka sunanki yake da dadi" munira ta fada tana sakin murmushi
gami da kallon iman.

Martanin murmushin iman din ta maida mata tana cewa

"Na gode" sukaci gaba da takawa,maganar muniran na maimituwa a ranta,sai ta sanya


hannu ta shafi fuskarta a fakaice,an jima ana fadin ita me kyau ce,saidai ita bata
taba ganin kyan ba a karan kanta,hakanan bata taba baiwa maganar wani muhimmanci
ba.

Kai tsaye munira ta kutsa kai cikin ajin,wanda ya dauki shuru,kowa ya


bada hankalinsa ga allon da malamin dake tsaye yaketa cikashi da rubutu daliban
suna kwafa suna mayarwa zuwa ga litattafansu. Sallamarsu sai taja hankalin kowanne
dalibi dama matashin malamin dake tsaye gaban allo,ta qarasa daura da malami tana
cewa

"Sir,sabuwar daliba ce inji principal,yace a saka sunanta cikin register" kai ya


gyada gami da cewa

"Okay"idanuwansa nakan fuskar iman,wadda ta fara jin wani iri,saboda yadda idanuwa
sukayi mata caa na dalibai maza da mata,musamman ita da banda primary data yi da
maza lokacin bata da wayo, junior dinta ajinau mata ne zalla,kasancewarta
government school

"What is your name?" Malamin ya jefa mata tambayar da harshen nasara,cikin


sassanyar muryarta data sake janyo mata idanuwa ta amsa masa,sai ya jawo register
din kusa dashi ya rubuta sunan,sannan ya bawa munira umarnin tayi mata wajen zama.

Kai tsaye seat dinta ta matsa mata,saboda tsarin zaman duk seat daya mutum
biyu yake dauka,da su biyu ne akai ita da qawarta,to bayan an shiga sabon term sai
aka canzawa qawartata makaranta,hakan ya sanya take zaune ita daya,saboda ba da
kowa ita din take jurar zaman ba.

Ranar farko a makaranta ga duk sabon dalibi rana ce dake cike da baqunta da
rashin sabo,kusan hakan taso faruwa ga iman,saidai kuma kirkin munira ya hana hakan
faruwa,saboda janta data dinga yi da hira,koda aka fita break tare sukayi break
din,aka dawo suka zauna a seat dinsu,tana ta bata labaruka da suka danganci
makarantar da yadda take,har zuwa lokacin da aka kada bell an tashi kenan,iman din
ta saba jakarta tana nufi qofa bayan ta yiwa munira sallama.

A qafa ta fara takawa sabida tadan qara gaba inda babu cunkoson dalibai
sosai,tana tsaka da tafiya taji muryar munira na kiranta,saita dakata ta kuma
waiwayo suka hada ido,kowa ya sakarwa dan uwansa murmushi,ta dakaci muniran har ta
qaraso inda take,suka jera sukaci gaba da tafiya tare,kafin daga bisani muniran
tace

"Ya na ganki kina takawa a qafa?" Waiwayawa iman tayi tadan dubeta cike da mamakin
tambayar tata,to ame takeson ganinta?,kamar taji tambayar da ta yiwa kanta sai ta
dora
"Ko mai daukarki ne bazai samu zuwa ba?,ranar farko a makaranta kuwa ai bai kamata
ya barki kiyi tracking ba". Sai yanzu ta fahimci zancanta,saita murmusa

"Dama can motar haya nake hawa,saidai wataran idan hanya ta biyo da yaa al'ameen ta
qofar makarantarmu ya jirayeni mu koma gida tare" kai munira tadan jinjina,tana
cike da mamaki,saboda kallon farko data yiwa iman,ta mata duba ne na yaran da suka
fito gidan hutu,sam kyan qira da dirin da Allah ya bata tayi zubin gidan yaku bayi
ba,ta tsammaci zata ga wata shimfidediyar mota tazo daukarta ne,saita aje tunanin
nata tana tambayar iman din unguwar da take.

Sanda ta gaya mata idanu ta fiddo

"Ai bamu da nisa da juna,abun hawa daya zamu hau,tunda nima yau shuru ba'azo
daukata ba" ta fada tana saka hannu tana tsayar musu da adaidaita sahu,suka masa
bayani suka shige,iman din na qoqarin neman ragi kan kudin da ya gaya musun,amma
sai taga muniran bata damu da price din da ya fada ba,don haka itama sai tayi shuru
kawai.
Suna tafe muniran na jan iman da hira,a dan zamansu na awanni iman din ta
fuskanci muniran kamar daga gidan masu dashi ta fito,koma ba haka ba to tabbas
gidan data fito sunfi nasu wadata,tadan saki jiki kadan da ita tana biyewa hirar
tata,har aka kawo inda muniran zata sauka,wanda daga nan zuwa gidansu iman baifi
naira 20 ba kudin mota.

Kudin da ya buqata munira ta ciro ta biya musu,iman zata doje tayi gaba
abinta bata tsaya ma sauraren qorafinta ba,mai adaidaita yaja sukayi gaba,cikin
ranta kafin su qarasa gida tana ta yaba kirkin muniran da karamcinta,azamansu na
wasu taqaitattun awanni.

A dan gajiye ta shiga gida,saboda akwai qaerin lokacin tashi kadan a wannan
makarantar kan makarantar data baro.

Da sallama ta kutsa tsakar gidan nasu qarfe biyu da rabi da minti biyar,inna
dake duqe tana baza masarar data wanke don ta samu tasha iska akai niqa ta dago
tana amsa sallamartata,idanunta akanta,ta sabule jakar bayanta ta zauna saman
kujera 'yar tsuguno tana dan goge zufar goshinta tare da yiwa inna sannu da gida

"Yauwa,an taso kenan?" Ta fada tana juyawa zuwa ga aikinta

"Wlh inna,duk na gaji,makarantar tafi waccan nisa"

"Ah to,aishi sa kai yafi bauta ciwo" tasan mita sarai inna zata dorar,don haka ta
saki dariya kawai ta miqe tana daga jakarta

"Amma inna karatun da ake mana a waccar makarantar baiko kama qafar rabin na wannan
makarantar ba"

"To Alla ya taimaka" ta amsa mata.

Kamar zatayi gaba sai kuma ta dakata

"Inna ya al'ameen bai dawo ba?"

"Tunda ya fita dai bai shigo ba" saita daga hannunta duban fuskar siririn agogon
silver dake hannunta tana duba lokaci,wanda yau ta fara sakashi,kuma al'ameen dinne
ya siya mata saboda makarantar

"Amma dai inna ba tuwo zakiyi ba"

"Zanyi ko zakiyi?" Kai ta gyada cikin salo na zaquwa da son jin amsar innar

"To zanyi inna"

"Bashi bane maqiyar tuwo.....dambu nakeso wai nayi" sai fuskar iman din ta dan
saki,don ita gaba ce tsakaninta da tuwo,tunda taji batun dambu kuwa,tasan saboda
malam da al'ameen za'ayishi,don haka tayi damarar zagewa tayishi yayi kyau yayi
dadi ko don al'ameen din,tana matuqar jin dadin yadda yake yaba mata idan tayi
girki,da yadda yake nuna jin dadinsa,koma bayan sadiq dake kusheta,wani lokaci har
sai malam ya shiga sannan zai qyaleta,duk da shima yana yine kawai saboda
tsokana,bawai don bata iya din ba,don ta fannin girki inna ta yarda da ita
dari.bisa dari,tun tana da shekara takwas innar ta fara shiga madafa da ita,tana da
shekara sha biyu kuwa ta sakar mata girkin,saidai ta dinga tayata ko duba mata,zuwa
yanzu kuwa da ake magana fa gama zama cikakkiyar qwararriya.
Ruwa kawai ta watsa tadan tsakuri abincinta kamar yadda ta saba ta fito ta
kama aikin,yau dama babu islamiyya,anyi bikin yaye wasu dalibai da suka sauke
alqur'ani,don haka aka basu hutu,wanda ida an koma su iman dinne 'yan babban
aji,duk da ita dama already tana biyo bayan duk inda aka biya matan da hadda wajen
malam,wani lokaci kuma idan abubuwa sunwa malam din yawa al'ameen ya karba mata.

Cikin karsashi da kuzari take aikinta,tana yi tana yiwa inna surutun


makarantar,wanda ada al'ameen din ta tarawa labaran,saidai tasan ba lallai ta sake
ta bashi labarin sosai ba,sabida kaifi da nauyi da idanuwansa a yanzu suke mata,ta
rasa dawa kuma zata tattauna wannan,qawarta daya a unguwarsu,to itama takan jima
basu hadu ba saboda yanayi na karatu da kuma tsarin tsaron fita a gidan
kowannensu,saidai tanata timing da sanya lokacin da zata fita taje susha hira da
ita.

Ganin ta kammala hada komai,dambun ya hau wuta,kuma tsakar gidansu babu


kowa,saita debo 'yan qananun brassier dinta da ta fara amfani dasu a boye ta zuba a
botiki ta zauna daga bakin famfo,wanda yake daura da qofar shigowa ta fara wankesu.

Ta jima tana ajiyarsu,tun wani lokaci da sukaje nijer,anty raheena 'yar


uwar inna ta bata tace ta ajjiye zasuyi mata amfani,bata aminta da hakan ba sai
sanda amfaninsu ya taso mata,ta rasa wanda zata gayawa tana buqatarsu.

Babu irin wannan hirar tsakaninta da innarta tun farko,ya alameen din
nata kuma koda wasa ba zata iya tunkararsa ta gaya masa tana so ba,sai ta tuna da
ajiyarta, doon haka ta debo abunta ta fara amfani dasu hankalinta kwance,amma
tanata boye boye,don sai irin haka gidan babu kowa take wankesu ta shanyasu a bayan
qofar dakinta,ko idan ta shiga wanka.

Tana wankesu tana dan rera karatun qur'ani da tausashiyar muryarta mai cike
da sanyi nutsuwa da kuma tashen 'yammatantaka.

Daidai lokacin da al'ameen wanda kansa ke ciwo ya shigo cikin gidan,tun


daga soro yayi sallama kamar yadda ya saba,saidai muryarsa bata da wani qarfi me
yawa saboda gajiya da kuma ciwon kai,wanda ya tabbatar stress ne na dinki.

Sam bataji shigowarsa ba,kamar yadda shima ya ganta bagatatan a farkon


qofa,don sam bai kawo samuwar wani mutum zaune a wajen ba.

Saman fuskarta ya fara sauke ganinsa,ta langabe kanta gefe guda,qaramin


bakinta me dauke sa jajayen labba yana motsawa a hankali,sautin karatunta yana fita
da kadan da kadan,gefan da kanta ya karkatan jelar manyan kitso guda hudu dake
kanta sun kwanto ta nan har saman qirjinta.

Tayi masa kyau ainun,fuskarta da maqerin budurci ke aikinsa a kanta tayi


wani fresh tare da annuri na daban,saiya lumshe idanunsa qirjinsa yana bugawa,wani
abu mai sanyi da qarfi da girma ya tsaga qirjinsa ya sauka saman zuciyarsa,ya
tabbatar wani feeling ne me cike da soyayya da kuma qauna ya saukar masa,sai ya
bude idanun nasa yana saukesu zuwa ga abinda take wankewar.

Idanu ya qurawa brasssier din nata yana mamakin yaushe ta fara amfani
dasu,qaramin murmushi ya qwacewa fuskarsa,ya sani tunda can tana da yawan zama da
hijabi cikin gidan,to amma kwanaki yaji yadda inna ke qorafin bata cirewa ko cikin
daki tasha iska,wala'alla yana da nasaba da hakan?.

A firgice ta dago sanda taji sallamar mutum saman kanta,a zabure ta miqe
saboda ba zatan ganinsa,har tana fatali da ruwan wankin da abebaden dake ciki tayi
dakinta da gudu,sai ya bita da kallo,dariya ta qwace masa,ya duqa a hankali ya
kwashe mata abubuwanta da hannu daya ya maida ga botikin,sannan ya tako zuwa cikin
gidan yana aake jaddada sallamarsa,inna dake can uwar daki ya fito zuwa rumfarta
tana amsa sallamar,saiya taka a hankali zuwa rumfar innar yana cire takalman
qafarsa,rabin hankalinsa na ga dakin iman din data turo qofar ya murmusa ya shiga
rumfar innar.

*_HILTI UNISEX CHOCOLATE STILL AVAILABLE, GRAB YOURS NOW,DAB TAKE DA QAREWA_*👌🏽
👌🏽👌🏽👌🏽

08184017452
[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 09

*Game buqatar biyan kudin zafafa biyar,zai iya tuntubarmu ta wannan number*

09032345899
Ko kuma
09166221261
__________________________________

"Tunda ta shigo ta fara tambaya da cigiyarka,nasan kuma labarine kawai cike


taf da bakinta zata baka na makaranta" inna ta fada mishi bayan sun gaisa,tana
ninke abun sallar data bari a wajen ta gashi ta shiga ciki,murmushi ya sake yana
dan shafo kansa,yana funa dramer dinsu ta yanzu yanzu

"Aiki take tayi ai inna,na dauka yau zata huta sabida gajiyar sabuwar makaranta"
dan satar dubansa kadan inna tayu,duk sanda ya nuna wata kulawa kan iman din hakan
namata dadi qwarai,kuma dama shi ba baqon abu bane a wajensa,tana da tabbaci da
yaqinun diyarta qwaya daya tilo ta dace da mijin aure,namijin da yasan abinda
yake,mai yawan tausaya mata da qaunar farincikinta

"Diya macace al'aminu,gwara taci gaba da sabawa akan hakan,na gana nauyun iyalinta
ne zai hau kanta,mace bata da wani hutu da ya wuce tayi abinda ya dace a matsayinta
na mace,to daga baya saita huta din" dan nauyin innar yaji ya kamashi,saiya gyada
kai sannan ya miqe yana yiwa inna sallama.

Koda ya fito tsakar gidan babu ita har yanzu,hakanan babu motsinta,ya
gifta inda ta tashin idanunsa nakan botikin wankinta,ya sake sakin murmushi ya wuce
soro,ya saka key ya bude dakinsu ya shiga.

Saman kujera ya zube yana furzar da iskar daya zuqota tun daga
hunhunsa,hannunsa yana saman kansa yana shafa sumarsa daga gaba zuwa baya a
hankali,yanajin yadda kansa ke sarawa,gefe guda kuma yana qarewa dakin nasu
kallo,yasan hargitse kadan yana buqatar gyara,kwana biyu bashi da isashen lokaci da
zai zauna ya gyara din,dinki yake na jama'a tuquru saboda gabatowar azumi,yanason
ya samu isashen kudi a hannunsa da zai yiwa gidan siyayyar kayan azumi,ya yiwa iman
kayan sallah sannan yaje ya gano yayarsa itama da nata kayan azumin dana
sallah,inna tasha hanashi saboda sadiqu da malam duka suna tasu siyayyar,amma sam
yaqi yarda,inda daga qarshe yace baya jin dadin hakan a ransa,sai yaga kamar innar
ta warshi ne shi,wannan furucin yasa ta qyaleshi,bata sake magana ba.

Ruwa ya fara diba ya shiga wanka ko zaiji dadin jikinsa,bayan ya fito ya


murzawa qofar dakin nasu key,duk da yasan babu me shigo musu kai tsaye,ya sanya
boxer da singlet ya koma ya kwanta saman doguwar kujerarsu yayi rub da ciki.

Idanunsa ya runtse gam,tunanin iman na dawo masa,surorinta na bayyana


cikin idanunsa,wani yanayi na mamayar ilahirin jikinsa,tsigar jikinsa na tashi,sai
ya sake gyara kwanciyar tasa yayi rub da cikin da gaske,ya sake rufe idanunsa a
hankali yana ci gaba da dulmiya cikin tunaninta,murmushi na qwace masa saman
fuskarsa lokaci bayan lokaci,sai daga bisani yaso dakatar da kansa saboda ganin
yadda tunanin ke neman qara ta'azzara ciwon kan nasa,don haka ya haqura da
kwanciyar,ya miqe ya balli paracetamol biyu cikin magungunansa yasha,ya sanya
jallabiya ya jawo qofar dakin nasu ya fito zuwa qofar gida.

Yaci sa'a malam yana nan,an gama karatun yamma yana shirin sallamar
yara,ya cire takalmansa yayi tattaki cikin girmamawa zuwa gaban malam din,yayin da
shima malam ya bishi da kallo wanda ke nuna tsantsar kulawa.

Gefansa ya zauna,bai kuma yi magana ba har ya gama sallamarsu

"Al'ameenu.....lafiya kake kuwa?" Malam ya jefa masa tambaya,sai ya daga kansa


cikin murmushi ya dubi malam,yana yabawa da jinjina qoqarin bayin Allahn,yadda suke
iya hakaito damuwar daje tattare dashi,ta ciwo ce ko akasin hakan

"Kaina ne yake dan min ciwo"


"Subhanallahi.....matso nan" malam din ya fada,saiya matsa gabansa kadan,ya sanya
hannu saman kansa ya kama masa shi da addu'o'i,ya matsa bayan ya gama yana masa
godiya,wanda babu jimawa yaji ya fara sauka,daga bisani ma suka shiga
tattaunawa,har zuwa sansa sadiqu ya dawo dava wajen aikinsa shima ya zauna nan
wajensu yana cewa

"Na biya ta wajen aikinku mu taho tare,saina taras waika taho"

"Kaina ne ya fara ciwo,saina yanke na dawo gida na huta" cikin yanayin nuna alhini
da damuwa yace

"Subhanallah,sannu"
"Yauwa,da sauqi ai,malam ya kamamin ya sauka" ya fada ganin yadda fuskarsa ta nuna
damuwa
"Kaine ma man,ka dinga kwanciya wasu kwanaki kana hutawa,kana stressing kanka da
yawa wallahi" murmushi kawai ya sakar masa ba tare da yace komai ba,shi a karan
kansa a jikinsa yakejin akan struggling bai fara komai ba,namijin duniya dan
gwagwarmaya ne,abinda ya saba gayawa sadiqu kenan.

Basu shiga gida ba anan suka yada jam'in sallar magariba su da sauran
jama'ar dake salla a wajen duk sanda malam ke kusa,aka idar suka sake zama
hira,irin zaman da ba kasafai lokaci ke basu damar yinta ba,saboda baqi da kuma
yanayin aikinsu,daga bisani malam din yayi baqo,suka shiga tattaunawa,hirar sauta
koma ysaka insa da sadiqu,sunaga qus qus dinsu saboda kada malam yaji,saboda hirar
irin tasu ce,yana bashi labarin yarinyar datace tana sonshi,al'ameen din nata sukar
abun,saboda shi sam yana qalubalantar mace tace tanason da namiji a irin wannan
zamanin,daga qarshe malam ya tura daya daga cikin almajiransa su sanya a fito da
abinci,wanda dama da wuya kaga anyi girki a gidan dai dai cikin masu gidan,saboda
baqin da malam din kanyi lokaci zuwa lokaci,sadiqu yacewa yaron ya gayawa iman ta
hado da nasu.

Cikin gidan babu kowa sai ita,don haka inna ta tsaida yaron malam din,ta
taya iman shirya abincin,yaron ha daukar mata wani ita kuma ya dauki wani suka fito
dashi.

Tunda ta doso wajen idanuwansa na kanta,cikin lullubin hijab har qasa,duba


daya zaka yiwa hijabin kasan tsafta ta wadaceshi,don harda karin guga,idan kuma ta
kusanto inda kake zaka iya jin qamshin body mist din da take amfani dasu,'yan 300
ne,saidai suna da sanyin qamshi,tana da maitar son qamshi da turare,don haka tun
kafin ma takai haka ta iya zaben turare, training din al'ameen dince,tun daga
tsafta zuwa son qamshi,girki ne kawai aikin inna.

Har zuwa sanda ta fara isa gaban malam ta ajjiye musu nasu abincin bayan
ta duqa ta gaidashi shi da baqonsa idanunsa na a kanta,girma da 'yammatancinta yana
sake cika sosai,ta zama budurwan gaske,saita qaraso gabansu a hankali,daidai sanda
baqon malam ya furta wata magana data dauke hankalin al'ameen daga wajen kwata
kwata ta maidashi kan hirar su malam din.

"kada dai ace hajarunka ce ta girma haka?" Murmushi malam din yayi

"Itace mana" kai ya gyada

"Ikon Allah,girman dan mutum babu wuya"

"Ka kwana biyu baka ziyarcemu bane shi yasa" malam ya amsa masa gana wanke hannunsa
cikin kwanan wanke hannu dake gabansa wanda inna ta hado dashi

"Lallaifa an kwana biyu" sai yadanyi shuru kadan sannan yace da malam

"Ni kuwa malam khalilu,da zaka amince ai da mun qulla wani alkhairi" daga kai malam
yayi ya dubeshi sanda yake qoqarin bude kwanonin abincin

"Ina saurarenka malam basiru"

"Me zai hana yaron wajena ilyasu yazo yaga hajaru,bamusan me Allah zaiyi ba,kaga
idan Allah ya daidaita tsakaninsu ai mu shikenan,kakarmu ta yanke saqa,tuwona mai
na"

Saura kadan maganar tayi tafiyar yaji da numfashin al'ameen,idanunsa suka


fara laluben iman dake duqe a gabansu tana ajiye musu nasu abincin sabida bacewa
ganinsa da take neman yi,zuciyarsa tayi wani bugawa tare da qara adadin gudunta.

Ajjiye murfin hannunsa malam yayi yana duban baqon nasa

"Zanfi kowa jin dadi matuqar hakan zata kasance,inama ina da wata diyar bayan
hajaru da na baku,kuyimin aikin gafara,tuntuni na bayar da hajar,lokaci kawai muke
jira a zartar da komai nan kusa in sha Allahu".

Nannauyar ajiyar zuciya alameen din ya saki,yana share gumin dake goshinsa
tare da duban tsakiyar blue din qwayar idanun iman din dake haske cikin dan hasken
dake kewaye da wajen,kamar tasan ita yake kallo saita daga kai suka hada idanu,ta
sakar masa da murmushi tana sadda kanta qasa cike da jin nauyi da kunyar abinda ya
faru dazun,abinda ke alamta masa cewa bataji maganar dasu malam ke tattaunawa
ba,nauyin numfashin ajiyar zuciyar da ya saukar ne ya sanyata daga kai suka hada
ido da ita.

Kusan baici wani abincin kirki ba ya tattara ya koma cikin gidan,dakinsu


ya fara shiga saidai ya kasa zama,yanason yin magana da iman din,ba kasafai ya fiya
son kebewa da ita ba saboda kare haqqin sharia sa kuma gujewa shaidan,amma dole ya
zaqulo dalilin da zai sanya su zauna suyi magana da ita,don haka ya dauki sabuwar
wayarsa daya siyo a dazun ya juya da niyyar fitowa,dai dai sanda sadiq ya shigo ya
wuce cikin gidan ya barshi a dakin yana amsa waya.

Dakin malam da ya gani a bude ya tabbata malam din ya shigo cikin


gida,kuma idan ya shigo din inna na tare dashi,hakan ya sake bashi qwarin gwiwar
isa ga rumfar inna.

Cikin saa ya sameta zaune tsakiyar litattafanta,ta bajesu tanata qoqarin


gwada assignment din da aka basu a yau din,wanda zasuyi zanen zuciya ne tare da
fitar da kowanne chamber na cikinta.

A hankali ta daga kanta tana amsa sallamar tashi,sai kuma ta maida kan
nata ta duqar tsakanin qafafunta tana juya abun zanen dake hannunta,ya sake sakin
murmushi,ya qarasa a hankali kan kujerar dake daura da ita ya zauna saman hannun
kujerar,cikin lallausar muryarsa daya ragewa kaifin sauti yace

"Hajar 'yammata" ji tayi tamkar zata lume a wajen,sautin muryarsa a yau din ya zama
na da an cikin kunnuwanta,uwa nauyinsa da takeji ya ninku cikin ranta daga sanda
yaga abinda taje wankewa dazun

"Ina fatan kin kwashe wankinki,saboda banason kowa yazo ya gani" saita saki abun
rubutun ta juyar da kanta ta sanyashi saman kujerar tana boye dariyarta cikin jin
nauyi,ta tabbata zaiyita tsokanarta ne idan batace wani abu ba,don haka cikin
siririyar muryarta tace

"Don Allah ya alameen....don Allah" yasan me takeson fada,saiya saki qaramin


murmushi me dan sauti kadan,ya zamo ya zauna sosai saman kujerar yana cewa

"To shikenan....duk da dai an boyen.....shikenan dai,ungo wannan,sakamin a charge"


a hankali ta juyo tana avoiding hada idanu dashi,tasa hannu biyu ta karba wayar da
yake miqo matan

"Laaaa yaya,taka ce?" Kai ya gyada mata tana juya wayar a hannunta

"Tawa ce" saita narke kadan,duk da bata bari sun hada ido ba

"Don Allah yaya yaushe zaka siyamin nima,kaga fa na shiga senior" ya santa qwarai
da son waya,saidai a yanzu bashi a ra'ayin ta riqe qaya torching kwata kwata saboda
wasu dalilai

"Wannan bata ishemu ba?,abuna ai naki ne"

"Yaaya,idan ka fita fa da abarka zaka dinga fita"

"Zan dinga bar miki ita duk weekend kina danawa,shikenan?" Cikin murna tace

"Yauwa yaya,na gode"

"And....idan naga yanayin performance naki a wannan term din,zan siya miki qaramar
keypad indai inna da malam sun bari" sosai ta nuna murnarta,ta tashi ta fara
qoqarin saka masa a chargyn

"Idan kin gama kizo zamuyi wata magana" ya fada yana saukowa tare da buda takaddan
data fara zanen yana kallon zanen nata.

Tana gama sanya chargyn waigowar da zatayi taga ita yake kallo bayan
hannunsa na riqe da zanenta,wani weakness ya saukar mata,duk kuzarinta na daxu ya
gudu,batasan wane irin power da magnet ne a idanun yayan nata ba,wanda a baya da
babu su sai a yanzu

"Zauna a nan" ya mata nuni da wajen da yake buqatar ta zauna din,inda zai zamana
suna fuskantar juna ne,ta zauna ta lanqwashe qafafunta

"Wa kikeso a zuciyarki?" Ya jefa mata tambayar kai tsaye,abinda ya sanyata daga kai
ba tare da tako shirya ba ta dubeshi saboda jin saukar ba zata da tambayar tashi
tayi mata,idanunsa cikin nata ya jinjina kai
"Yes.....zuwa yanzu kin girma queen,ke din ba yarinya qarama bace kamar yadda kike
kallon kanki,zuciyarki zata iya fadawa soyayya at any time.......wa kikejin kina
so" sosai ya jefata cikin nazari,kafatanin rayuwarta batasan kowa ba bata saba da
kowa ba sama dashi,bata taba kallon kowa ba taji wani abu na daban a kanshi ba sai
shi,inda tasan soyayya ko alamominta,ba shakka zata iya cewa wala'alla shi
takeso,amma yanzun batasan shaquwa ko ganin girma bane,duk bata sani ba.

Maganarsa me nauyi ce,don haka ta girgiza masa kai kawai

"Uhunnn..... talk to me mana,ki gaya min" sake girgiza kai tayi da qarfi,murmushi
me qarfi na son qwace mata,wanda ya cakuda da kunya

"Don Allah yaya,babu kowa fa" kamar yace

"Harda ni?" Sai kuma ya danne wannan a ransa,ya saki nannauyar ajiyar zuciya,ya
sake cooling muryarsa sosai

"Bani aron hankalinki iman" sau daya ta daga kai ta kalleshi ta mayar qasa tana
sake gada nutsuwarta kamar yadda ya buqata

"Inaso ki bani dama guda daya tak a rayuwarki iman,ina da wani tanadi na musamman
cikin rayuwarki"

"To yaya" ta fada a sanyaye.


[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 10

*_Wannan littafin na kudi ne,game buqata zaki iya tuntubar wadan nan numbers din_*

09032345899
Ko kuma
09166221261

"Imannnn" ya danja sunan nata,ta amsa da na'am,har yanzu idanunta suna qasa

"Bana so ki kula kowa,banason kiyi soyayya da kowa..... infact ma,na miki zabin
mijin aure wanda zai dace dake in sha Allah.....kin yarda?" Kai fa gyada tana sake
saukar da kan nata qasa

"Kinyimin alqawari?" Saita sake jinjina masa kan,ya sauke numfashi mai nauyi daga
qirjinsa yana furta

"Alhamdulillah".

Shuru yadan ratsa dakin,yana ci gaba da kallon zanen nata,saidai zuciyarsa


ta rarrabu kashi kashi wajen tunani iri daban daban

"Zanen nan yayi kyau,ina tunanin yadda kika iya zanen zuciya har
haka.....soyayyarki zata kasance me kyau haka" da sauri ta daga kanta suka hada
idanu,wadanne irin manya manya kalmomi ya al'ameen ke mata amfani dasu ne
haka,gashi ya ritsata da idanu yana kallonta,sai ita ta janye nata idanun tana sake
qunshe fuskarta waje daya,ya saki murmushin nasarar da yake hangowa,yana iya
hasashen yadda yake samun ci gaba da kuma galabar narkar mata da zuciya kowacce
rana idan ta bullo kafin ta fadi.

Shi ya zauna ya tayata aikin gaba daya kasancewar science yayi


shima,banda rashin zamowarsa dan wani shi din mutum ne me matuqar qwaqwalwa daya
kamata ace ma zuwa yanzu yayi nisa a karatun likita da yake jarabar so,suna aikin
yana dan janta da hira don ta saki jikinta,tadan sake amma ba kamar yadda suka saba
ba,bai bar cikin gida ba saida inna ta fito daga wajen malam,sannan ya wuce dakinsu
ya barta da tarin tunani cikin kwanyarta.

********WASHEGARI******

Bayan tasowarta daga makaranta wanda shima tare da munira suka taho,ta kuma
sake biya mata kudin mota,bayan tayi wanka ta sauya kaya taci abincinta inna ta
bata dakan garin kunu wanda akewa malam,tace takai bayan layinsu ta tsaya a daka ta
taho dashi

"Don Allah inna zan leqa gidansu bushira" bushiran ba boyayya bace a
wajensu,nutsatsuyar yarinyace da suke taba qawance da iman,wanda tun quruciya itace
kadai ta dauke halayyar iman din,duka sauran irinsu rahama abokan fadanta ne,banda
yanzu da girma da hankali yazo ake gaisuwar mutunci a wuce wajen.

Tana kaiwa mai dakan kudin ta zarce gidansu bushira,wanda gidajen dake
tsakaninsu da gidan dakan bai wuce gida shida ba,tayi sa'a fa sameta a gida,dama
kuma ba inda take zuwan,islamiyya ce,kuma makarantarsu daya,anyi musu hutun sauka
sai wani satin xasu koma

"Wata sabon gani" bushira dake cire lallen data yiwa yatsu hannunta ta fada tana
tabe baki bayan sun shiga dakinta da suke kwana da qannenta,murmushi ima tayi suka
shiga tsokanar juna da hirar duniya,kafin daga bisani iman din fa budewa bushira
abinda ke tafe da ita.

Shuru iman din tayi na kusan minti goma tana juya bayanan da bushira
tayi mata,baya ta gama bata labarin komai,ta dauke hannunta daga kumatunta

"Amma bushira,ta yaya yaya al'ameen zai soni,bayan yayana ne?"

"Yayanki,ciki daya kuka fito?,ko yaya sadiqu ne?" Kai ta girgiza alamun a'ah

"To kuwa kinga ya halatta kuso juna ku kuna qaunaci juna,dama kuma abinda yafi
dacewa kenan,don kusan dama ke din rainonsa ce......kuma ko ke qarya kike kice baki
sonshi munafuka" bushira ta qarashe maganar tana ɗakawa iman duka a cinya gami da
sakin dariya wadda ta sanya uman din dole ta tayata

"Ya al'ameen ya gama haduwa iman,idan ma bakiso wata ce zata daukeshi,yana cin list
na sahun farko na kyawawan unguwan nan wanda babu na biyunsu,duk yadda zan gaya
miki yadda 'yammatan unguwar nan ke sonshi da fatan ya sosu ba zaki gane ba,abu
daya ya rage miki....ki jira sanda zaice kawai yana sonki ki karbi tayinsa hannu
bibbiyu.....idan ma yayi nauyin baki ke ki furta kawai a wuce wajen" duka iman ta
kaiwa bushira a gadon bayanta

"An gaya miki bani da ajine,duk yadda muka taso tare dashi bazan bari ajina ya zuba
ba"

"Gaskiya ne tawan,kema a unguwar yayinki ake,kawai shakkar malam dasu ya al'ameen


din ya hana a fara tareki ko sallama dake,amma ni kaina masu kamun qafa dani a
kanki suna da yawa,harda masu motoci wallahi" miqewa iman tayi tana daure gashinta
mai santsi da ya ware wanda dama babu wuya ya warware din,ta maida hijabinta saman
kanta tana fadin

"Su riqe motocinsu.....kinga na manta shaf da aiken daya fito dani ma"

"Muje na taka miki" bushira ta fada itama tana janyo hijabinta suka yiwa ummansu
sallama suka fito tare.

*******SANNU SANNU******

Kwanaki ke shudewa sa iman cikin makarantar nasreen,zuwa sannan bata da wata


qawa ko aminiya data wuce munira,shaquwa me qarfi ta fara shiga tsakaninsu,duk da
banbancin halaye da kuma dabi'u dake a tsakaninsu,gami da sukunin rayuwa.

Cikin sati uku ta fahimci wace munira,'ya mace guda daya tilo da mamanta
ta haifa bayan yara maza qannenta guda hudu,tana ji da ita ainun,tana bata kulawa
da gata,kusan mafi yawa daga cikin familyn su munira masu arziqi ne masu
sukuni,saidai shi mahaifin muniran rufin asirin Allah gareshi,mamarsu muniran ta
fishi kudi,hakan ya sanya komai na gidan take tafi dashi yadda takeso idan ma
maigidan yayi wanda baiyi mata ba,tana ji da munira sosai,hakan yasa ta daukaki
rayuwarta,tanason rayuwa me tsada sosai,hakanan takan kutsa kanta inda Allah bai
kaita ba,gidajen 'yan uwan mamanta masu dashi ainun babu inda bata sani ba,wani
lokaci idan ta shilla ta debi kayanta ta tafi daya daga cikin gidajen nasu,takan
jima bata dawo nasu gidan ba,har ma sai kayi zaton 'yar gidan ce.

Da yake fara ce hakan sai ya sake qawata fuskarta,ya kuma ja hankalin


samari a kanta,tana da samari sosai,kuma dukkaninsu 'ya'yan manya ne,wayar hannunta
kuwa a lokacin babbar iPhone ce,dukkan abinda take ta'ammali dashi,tun daga sutura
zuwa cima masu tsada ne,komai zatayi saita siya me tsada,saboda mamanta ta tsaya
mata,batason sam taga muniran tata ta shiga cikin danginta an raina ta,hakan ya
sanya take kashe mata kudi tuquru.

Saidai kuma muniran nada kirki daidai gwargwado,hakan shi yake


taimakawa wajen boye da yawa daga halayyarta da basu dace ko kamata ba.

Ba komai na halayenta iman ta sani ba,tunda iyakarsu makaranta,da an rabu


shikenan,sai kuma washegari,iya abunda ta sani muniran tana da kirki da kuma yawan
kyauta,duk da tana zillewa duk wani abu da zaisa muniran ta kashe mata
kudinta,kamar tafiyarsu tare,da yawan lokuta zillewa take tayi tafiyarta saboda
kada muniran tace zata biya mata kudin motar.

*MONDAY MORNING*

Cikin clean uniform dinta da suka dauki karin guga kyakkyawar matashiyar
hajar Ibrahim Khalil ke takowa tana nufar ajinsu,kafadarta daya saqale da
jakarta,daya hannun kuma dan madaidaicin flask din abinci ne a ciki.

Kana duban fuskarta zaka karanci ranta a bace yake,saidai hakan wani kyau
ya qara mata na musamman,sandin bacin ran nata makara datayi,aka kuma shanyasu a
bakin gate har na wajen awa daya cikin rana,wanda wannan shine irin punishment din
makarantar tasu.

Kamar ance ta daga kanta saman varander dinsu,ta daga kyawawan blue eyes
dinta,idanunta sauka ga malamin,sir arabi,malamin daya takurata tun zuwanta
makarantar,da shegen kallo naci da kuma shishshigin shiga harkarta,shike daukarsu
darasin turanci wato English,yammatan makarantar da yawa suna yinsa,saboda motar da
yake hawa,kana kallonsa kasan ba talauci ko babu suka sanyashi koyarwar ba,saidai
ita sam imani hakan bai dameta ko ya dadata da qasa ba,don sam jininsu ita bai hadu
dashi ba,ya fiya jin kansa saboda yaga yana tashen samartaka,yana sanya shaddodi da
hawa mota,ita sam a rayuwarta batason mutum me jin kansa ma,izza da fadin rai,shi
yasa tako ina ya al'ameen yake burgeta.

Yana da wani irin kwarjini gami da aji,uwa uba miskiline naqin qarawa
idan baiso ba,hakan yasa baya daukar raini ko izgili,amma sam baida girman kai ko
dagawa.

Ta sauke nata idanun tana jan tsaki qasa qasa,gami da qare hade ranta gab
da zata shiga cikin ajin nasu,sabida yadda yawanci lokaci irin wannan sanda tazo a
makare mazan ajin ke binta da kallo,abinda ta tsana ita kuma kenan,don haka a dake
ta shiga ajin.

"keda mutumin naki ne?,na hangeshi tsaye upstair" munira ta fada tana danne
dariyarta sanda iman ke zama kusa da ita,tana duba littafin subject din da akeyi

"Shine mana,me shegen kallon tsiya,banason mutum me kallo"

"Tsaurin idanu dai,kwata kwata baki dace irinsa bama,shi bai gani ba kedin kalar
matar manya ce" waiwayowa iman tayi sanda take dora littafin saman table dinta

"Kamar yaya?" Murmushi munira tayi tana ci gaba da copying note dinta

"Kamar har yanzu bakisan baiwar kyan da Allah yayi miki ba,ai kyan kyau irin naki
ki morewa babban gida,inda zaa jiqaki da kudi da mota,fita qasashen waje babu kama
hannun yaro,shine kika mori kyanki,amma ba kowanne irin kalar namijine zaizo ya
tsaya gabanki da sunan yana sonki ba" tsaki iman taja,saboda ta dauki maganar
munira a matsayin shirme,ta bude littafinta ta fara kwafar note din da sauri da
sauri don ta fuskanci ya kusa dawowa ya goge wanda ya fara.

"Am telling you fa,kina ganin kamar wasa ce maganata?,to Allah koni da ban kama
rabin qafarki a kyau ba,zakiga kalar mijin da zan zaba"

"Don Allah ki shiru ki barni da bacin ran da yake damuna" dariya muniran ta saki
tana ci gaba da rubutun,har zuwa sanda malamin ya kammala yayi musu explanation ya
sallamesu.

"Me ya hanaki zuwa makaranta Friday ne?" Iman ta tambayi munira tana maida
littafinta jaka,sai data juya manya idanunta,da alama amsar da zata bayar amsa ce
da take mata dadi cikin ranta sosai sannan tace

"Kinsan biki muke na wata cousin dita,so ran Friday muka tafi garinmu acan zaa
daura aure,kuma ina cikin wanda aka siyawa ticket zasubi flight,kinga ko bazan bari
nayi missing ko damata ta wuceni ba,nayita neman number dinki na gaya maka,sai dana
fara checking wayana naga ashe bamu taba exchanging numbers ba......ki bani number
dinki saboda irin hakan,kinga nama canza sabuwar waya,ranar aka bani gift dinta"
munira ta fada tana saka hannunta a aljuhun rigarta.

Kallo daya zaka yiwa wayar kasan cewa bata qananun kudade bace,hakanan
sabuwa ce fil sai sheqin sabunta take,munira tabi wayar da kallo sannan ta amsa
mata

"Nikam ai bani da waya,ta ya al'ameen nake ara duk weekends nayi game ko browsing"
kallon mamaki qarara munira ta jefi iman dashi,harda dan ja baya

"Kina ss 01 amma ace baki da phone iman, jokes apart please,wasa kikemin ko number
dince ba zaki bani ba?"

"Tunda baki yarda ba ai babu amfani na dage saina gamsar dake,duk yadda kika dauka
hakane"

"Am sorry my friend,Allah na dauka wasa kikemin....amma kuma,ba sani ba wallahi,da


dana canza na baki dayar,sai qanina na bawa wanda yake bin me bina" idanu iman ta
fidda

"Ni shegiya kaza,ya al'ameen bazai bari ba,amma ina saka ran muna gama wannan term
din zai siya min keypad sabuwa in sha Allah,yayi alqawarin idan nayi abun kai zai
siyamin" dariya sosai munira ta saki tana kallon iman

"See you don Allah,wani irin keypad?,to ko 'yan aikin gidanmu banjin akwai me
keypad,don Allah karma ki fada wani yaji,sai ajinki ya zuba,mazancan da kike jawa
aji saisu rainaki,su dauka qaramar yarinya ce ke".

Rai sosai iman ta bata tana dubanta


"To sai me?,ni ina farinciki da duk abinda nake dashi,kuma iya abinda yake ganin ya
dace dani kenan,kuma ina farinciki da hakan"

"Wait mana iman" munira tayi saurin dakatar da ita ganin kamar taji haushi

"Nifa ba abinda nake nufi kenan ba,ki fahimceni.....ina nufin yanzu budurwa
kamarki,ai ya kamata a sakar miki mara a siya miki waya me kyau saboda gudun raini
daga wajen tsararrakinki.....na tabbatar yana da kudin da zai iya siya miki babbar
waya,ko yaya ne kaima kayi dan abun xamanin nan da kowa yakeyi" duban munira kawai
take,tabbas ya al'ameen idan tace tana so zai siya matan,amma a hakan ma babu
lallai su malam su yarda ba,sai tayi shuru bata sake cewa komai ba,saboda isowar
wata 'yar ajinsu da tata wayar,tazo munira ta tuttura mata pics da wasu videos,da
kadan kadan sai ga masu wayar suna zuwa,sunata sending ma junansu abunda kowa keson
sawa a wayarsa.

Tana daga gefe tana kallonsu,kowacce wayar hannunta babbace,wata daga


gidansu wata kuma saurayine ya siya mata,ba shakka tana bala'in son waya da
maitarta,amma ba zata takura ya al'ameen din ya siya mata sama da wadda yace zai
siya matan ba.
[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 11________________

*_Huuuuuum! Idan kaji hanci a sama yayin gittawar mata ƴan ƙwalisa ko shiga
gidajensu kasan maganar ta ƙamshi ce_*

*_Ina magana ne aka kayan ƙamshi ƴan gaske ba saka iska ta hure maka ba_*

*_Ina mata ƴan ƙwalisa ma'abota so da ƙaunar ingantattun haɗin turaruka ƴan gaske?
To kuzo maza ga dama a tafin hanunku cikin sauƙi da sauƙaƙawa._*

*_Ana siyarda Turarukan Wuta na yan Maiduguri Set na amare. Ana bada sari kuma._*

*_Sannan akwai kayan gyaran jiki. Akwai zumar qiba result cikin 1 week. Turaren
daki, jiki, kaya, tsuguno, humra, colacca, turaren wanka, mopping scents, air
freshener._*

_Address Kano, Mariri Maiduguri Road. WhatsApp number 07068145252_.

*Sai kunzo🤳🏻*
___________________________________

Tare suka jero da muniran bayan an tashi kamar yadda suka saba,suna tafe suna
dan hira munira na tsokanarta

"Nikam kullum aka tashi daga makaranta dalibai basa gajiya da kallonki iman?" Tsaki
taja,itama abun yana damunta,don har ta yanke shawarar fara sanya niqabi
"Sai suyita ai,kamar kai dayane mutum,su ba bil'adama bane 'yan uwanka"

"Kin fita daban seriously,shi yasa kike shan kallo" munira ta fadi sanda take nufan
wata mota ash jaye da hannun iman,dakatawa iman din tayi tana qoqarin kuma zame
hanunta daga na munira

"Ina kuma zaki kaini ga hanyar titi?" Waiwayowa tayi tana dubanta,fuskarta dauke da
murnushin nan

"Oops,sorry,na manta in gaya miki,me daukana ya dawo da daukata,dama shike maidani


gida indai naje gidan uncle jibril,yawanci ina bin motar haya ne idan ina gidanmu"
kai iman ta jinjina tana saita hanyarta zuwa titi

"To sai gobe,Allah yabamu alkhairi" da sauri tasha gabanta

"Ban gane ba,bayan ta hanyar unguwarku xamu wuce,ki shigo don Allah,yana da
kirki,zai ajjiyeki unguwarku,cousin dina ne sadam,lokacin tashinmu lokacin ne shi
kuma yake komawa gida cin abinci,shi yasa yaje biyowa ta nan ya daukeni mu wuce
tare" kai iman ta jinjina

"A'ah fa,zanbi adaidaita kamar yadda na saba" dambu taliya ta kada iman amma
taqi,har sau da na cikin motar ya fara mata horn,dole ta haqura tace da ita

"Shikenan,bani number wayar to"

"Idan kin kira amma kice ni kike nema,don ya al'amin ko inna cikinsu wani zai
daga,saboda numbers dinsu ne" dariya munira ta saki

"Allah ya sawwaqe,yanzu inda saurayi kikayi haka zaki gaya masa kenan?"

"Ke kika sani,ni bani da wani saurayi ma" da wani mamakin take duban iman
din,saidai ta share ta soma karanto mata digit's din tana lodawa a wayar tare sa
serving,sukayi sallama tana jajata mata Allah yasa ta samu mota da wuri,saboda
sadam ya gaya mata ana wuyar abun hawa yau din,sakamakon taadar da man fetur
yayi,da yawa wasu masu ababen hawan sun haqura sun ajjiye abun hawan nasu a gida.

Ta samu tulin dalibai kuwa masu jiran abun hawa,haka nan tabi sahunsu
itama,tana fatan su samu da wuri kodon ranar da ake dasawa.

Kusan duk motar da zatazo ta wuce a cike take,wata kuma kafin ta qarasa inda
ta tsaya wasu sun shige sun cikata,tana nan a tsaye tsayin wasu mintuna ta hangi
kamar gilmawar motarsu munira,sai kuma taga ta tsaya taja da baya ta dawo dab da
ita

"Why not ki qyaleta....ba'a dole wajen taimako fa" sadam daya dan hada rai ya
fadawa munira

"Qawatace,banason ganinta tana sha ranar nan,kayi haquri minti daya"

"Ok" ya amsa qasa qasa yana jona wayarsa a chargy,munira ta bude murfin motar ta
fito ta nufi inda iman take.

Da farko musu taso ta sake mata,sai da taga muniran taji haushi,sannan


kuma me motar ya fara buga musu horn sannan ta bita,sanyin ac ya ratsata sanda
jikinta ya shige motar,ta maida murfin ta rufe sanda munira ke mita

"Haka kawai ki tsayar da kanki a wannan ranar babu gaira babu dalili,bayan ga abun
hawa,ai tsaiwa a ranar nan sai dole"
"Ina yini" tayi qoqarin gaida matuqin motar ba tare data amsa mitar da munira ke
mata ba

"Laf....lafiya qalau.... 'yammata" harshensa yadan sarqe,bayan idanunsa sun sauka a


fuskar iman dake ciro jakar bayanta zuwa saman cinyarta ta glass din gaban
motar,gabansa yadan fadi,ya zuba mata idanu na wasu sakanni ba tare daya iya dauke
idonsa daga kanta ba,tunda yake bai taba ganin halittar mace da komai yaji.....ta
kuma tafi da imaninsa irin wannan ba,wani irin kyau mai cika idanun me kallo,abinda
yasa yadan daburce har ya qara mata da kalmar 'yammata kenan ba tare da ya sani
ba,kalmar kuma data dan ja hankalin munira tabi sadam din da kallo,don tasan ba
dabi'arsa bace hakan.

Haka kawai ya samu kansa cikin rashin nutsuwar da yake da tabbacin ya fada
kogin soyayyar iman ne farat daya,ya dinga satar kallonta lokaci bayan lokaci,har
sai da iman din ta ankara,ta kuma tsargu,tare da tuhumar kanta na meye xata shiga
motar wasu,koda rana zata kasheta?,sai ya basar,ya fara soko musu hira,yana kuma
jan iman din din

"Wanne layi zamu shiga?" Ya tambayi iman din kai tsaye,idanunsa na kanta ta cikin
mirror

"Ya isa,anan ma zan sauka" ta fada tana sake gyara jakarta

"A'ah,ai da kin barmu mun cikasa ladanmu ko?" Ya fadi yana dan saki murmushi,munira
ma ta saki nata tana gyada kai

"Aikuwa dai"

"A'ah na gode,babu nisa,zan qarasa da qafata" bai sake cewa komai ba ya fara
qoqarin faka motar,sannan ya saka hannunsa a aljihun gaban motar ya budeshi,ya ciro
wrapper din 'yan dari dari sababbi ya miqa munira

"Bata,tasa kati a waya"


"Ina taga waya,saidai tasha chocolate" munira ta fada cikin sigar zolayar iman tana
miqa mata kudin.

Kememe iman taqi amsar kudin,saima ta soma takawa tayi gaba abinta tana cewa
sai gobe

"Ni nasan ba zata karba ba,amma ka barni da ita,zan kai mata gobe" tace da
sadam,saiya sauke ajiyar zuciya,cikin kasala ya tada motar

"Ban taba ganin yarinyar data yimun ba irin qawarkin nan ba,ki shigemin gaba don
Allah na mallaketa" dariya munira ta saki

"Karka damu,indai zaka saki kudi duk ba zaya gagara ba"

"Mayyar kudi,bansan ina zakikai son kudi ba muni" dariya ta sake

"A'ah ya sadam,kudi fa abun sone,babu meson wahala ko talauci,ko aikin nan da kake
yanzu ba kudin kake nema ba?". Murmushi yayi kawai,don yasan wajen magana badai a
kada muniran ba,gaba daya shi yanzu hankalinsa ya tafi ga iman.

Koda washegari taje mata da kudin makaranta cewa tayi ba zata karba ba
wallahi,harda qarin handset daya siya ya dora mata akai,kusan fada sukayi da iman
din akan hakan,ita ta dage saita karba,dan uwanta ne,kuma babu dadi maida hannun
kyauta baya,yayin da iman din tace sam batasan wannan zance ba,kawai daga haduwa da
mutum sai ta karbi abun hannunsa?,tace waye ya bata ma a gida?. Wani kallo muniran
tayi mata

"Au daman duk yammatan da samari ke musu kyauta nunawa suke a gida suce
wanene ya basu?,kowacce boyewa take tayi amfani dasu abunta,ki karba kawai,don
gaskiya bazan iya maida masa ba,don bansan bayanin da zanyi masa ba"

"Ki riqe na baki kyauta tunda ba zaki iya mayarwa ba"


"Bani ya bawa ba,amma zan ajjiyesu har zuwa randa zaki amsa" ta fada
cikin bacin rai tana zuge handbag dinta ta jefasu ciki,zancan bikin qawayensu guda
biyu dake matsowa da aka zauna yi shi ya raba gardamar,duk da haka muniran bata
sauko ba.

Koda aka tashi tun daga bakin gate ta lura da motar jiya ce tazo daukan
muniran saita zame ta gudu,ta canza hanya ta shiga motar haya tayi gida,washegari
ta dinga mita da qorafi iman din tace da ita

"Kada ma ki soma batawa kanki rai,don Allah bazan sake shiga motar wani a gida baa
sani ba" tasan da gaske take idan tayi magana,don haka bata sake cewa da ita komai
ba,sai kumbure kumbure da take mata alamun tashi fushi,dariya ta saki

"Kyayi ma ki sauko" amsar da iman din ta bata kenan.

********. ******. ********

A nutse ya ajjiye almakashinsa saman keken da yake kai,sannan ya miqe ya


nufo inda iman ke zaune saman wani stool tana fuskantarsa.

Ganin ya dosota saita dauke idanunta a hankali,ya saki qaramin murmushi da


ya sake qawata fuskarsa,ya zauna saman wani keken dake daura da ita,ya dora qafarsa
daya saman wata kujerar roba da babu kowa akai.

Shagon nasu yanzu babu kowa sai wani dan matashi guda daya daketa faman
dinki,da alama masu kayan suna hanya ne,koma bayan sanda ta shigo din da yake cike
da matasan,sunata shirin fita wata ball ta abokinsu,shi dinne yace ba zashi ba,don
ba wani abokinsa bane na kusa,saboda dama ba mutum ne shi me tara abokai da yawa
ba.

"Banfiyason zuwanki shagon nan ba,kina ganin dai yadda kullum yake cike da
mutane" dan turo baki gaba tayi

"To ya alameen,idan ka dawo gida inna ba zata bari muyi magana


bafa.......kuma lokaci yana qurewa,bikin gaba daya saura uku" idanu ya zubawa lips
din da take turowar,kamar ya kama ya tsotse haka yakeji,saiya dauke idanun nasa
yana tattara kansa waje guda

"Me yasa baki kirani a waya ba?" Saita fidda idanunta duka a kanshi

"Ka manta ne,inna ta hanani taba wayarta,tace ina qarar mata da kati"

"Haba da Allah haba,ya zaayi ace budurwa kamanki aron wayar inna kike?,ai kinfi
qarfin haka,wani idan ya ganki zai zaci babbar iPhone ki manya manyan Huawei kike
riqewa" ya fada da salon tsokana.

Kallon da al'ameen ya jefeshi dashi yasanya shi jan bakinsa yayi


shuru,kafataninsu sunsan halinsa baya daukar wargi,hatta da ogansu me shagon wani
lokaci kamar shakkar al'ameen din yake saboda kwarjinin da Allah ya zuba masa,uwa
uba kuma mutum ne shi mai tsaiwa akan gaskiya,idan kaga ya dage kan abu,to idan
akayi zuzzurfan bincike shine me gaskiya

"Bani mu gani" ya fada yana miqa mata hannu,sai tabi hannun nasa da
kallo daya nannade hannun rigarsa zuwa gwiwar hannu saboda yaji dadin kallo,cike
yake da gargasa da jijiyoyin da zasu shaidamaka cikin jikinsa a murde yake,kuma
qaqqarfan namijin duniya ne.

Kunya ta kamata sanda ta miqa masa yankin atamfofin guda biyu taga ya
janye hannunsa yana jan hannun rigarsa yana rufe hannayen nasa,idanunsa kuma na
bisa fuskarta,da alama yaga kallon data bishi dashi kenan.

Murmushi ya saki sanda taja hijabinta ta kare fukarta,yana qoqari yaga ya


gujewa duk wani abu da zai sanya taji wani abu tattare da ita,bayason ya raba mata
hankali tun yanzu ko yayi cikakken wasa da hankalinta,saidai lokaci yana nan zuwa
da zai mantar da ita kowa cikin duniya saishi kadai.

Tana miqa masa ta sauka daga kan kujerar don ba zata iya ci gaba da zama
ba

"Qawata zata kawo dinki yaaya don Allah,kada kace aiki ya maka yawa"

"Karta damu,indai ta wajenki ta biyo"

"Saika dawo" ta fada tana masa sallama,bai amsa ba illa binta da yayi da
kallo,kominta a nutse kuma a tsare Allah yayi mata shi,yana jin sara qiris ya fara
tilastata sanya niqab,yana jin ciwo cikin qirjinsa da zuciyarsa duk sansa ta fita
koda makaranta ne,yafi jin dadi da samun nutsuwa udan ya dawo gida ya sameta cikin
gidan.

Wani irin shauqinta yakeji yana fusgarsa har ta bacewa idanunsa,ya sauke
ajiyar zuciya yana sauka dubansa ga qyallen atamfofin data bashi,ya daga kai a
hankali ya dubi matashin daketa aikinsa

"Yahaya......ka dubamin atamfar nan don Allah ka gaya min kudinsu gobe ko jibi"

"An gama" ya fada yana miqewa tare da miqa hannu ya karbesu.

*********. *******. ******

K'arfe hudu da minti ashirin da hudu wayar inna ta kada,iman data kai jug
din data hadawa munira lemo kitchen ta dire da sauri ta dawo ta daga tana amsa
kiran,munira ta tsammata,kuma ita dince,saita aje wayar tana jan babban hijabinta
ta dora saman atamfar dake jikinta,wadda al'ameen ya zauna ya bata lokaci sosai ya
tsara mata dinki na gani na fada

"Inna zan leqa waje na shigo da ita"


"Saikin dawo" inna dake zaune tana qoqarin gyara saitin radio dinta ta fada,tana
son ta kamo freedom radio don jin shirin mu qyaqyata kafin biyar na yamma tayi.
Slippers dinta ta zura ta tako zuwa soron gidansu.

Gab da zata fita shi kuma yana qoqarin shigowa,saura kadan suyi gware,taja
da baya tana yarfe hannu tare da yamutsa fuska,abinda ya taimaka qwarai wajen
fitowar dimple dinta duk sanda ta motsa fuskarta,yayin da shi kuma yaja da baya
yana qare mata kallo.

Yana iya hangen yadda tayi wani kyau duk da cikin hijabi take,yana jin shi
daya ne a duniya yake iya ganin kyanta koda cikin lullubi take,kuma a kanta kadai
yake da wannan baiwar
"Ina zakije?"
"Qawata din nan da zata kawo maka dinki zan shigo da ita"

"Koma ciki" saiya koma da baya ya qwalawa daya daga cikin almajiran gidan kira,yace
ya duba layin,idan yaga wata baquwa tana neman gidan nan ya shigo da ita,ya dawo ya
zarce dakinsu sannan tuni iman ta kona ciki,duk da taso ya barta taje da kanta ta
shigo da ita,saidai ba zata iya yi masa musu ba.

Ba jimawa saiga sallamar munira,iman ta fito da sauri,suka rungume juna


cikin murna,kamar wadanda suka jima basuga junansu ba,kai tsaye suka fada dakin
inna.

Cikin girmamawa ta gaida inna,innan ta amsa mata,sannan ta miqe ta fice


zuwa dakin malam da tun daxu dama takeson shiga ta gyara masa kayan sawarsa ta
barsu su biyu cikin rumfarta.

"Hajar ibrahim khalil" munira ta fadawa iman wadda keta qoqarin zuba
mata lemo da abinci bayan ta qarewa falon nasu kallo

"Munira sulaiman"
"Yaudai gani a gidanku,naga randa zakizo nima namu gidan" hararta tayi cikin wasa

"Aiba zuwana kikayi ba,kawo dinki ne ya kawoki ko?"

"Eh duk da haka,inda hakanne ma ai da shagon zan tambaya nakai musu direct,da qyar
mafa yaron da kika aika ya ganoni" ta fada tana daukan lemon takai bakinta

"Nazo fita mukaci karo da ya al'ameen,shi yace na koma ya tura sa'idu" ajjiye lemon
tayi

"Yaudai zanga ya alameen da zancansa ya cika mana kunnuwa aka hanamu sakat,ya
al'ameen din nan me shegen tsauri da takura,hala ku biyu inna ta haifa kawai" kai
ta girgiza mata tana murmushi

"Mu uku ne,kawai yaya sadiq"

"Amma ban taba ji daga bakinki ba" zamanta fa gyara saman kujera

"Barshi wannan,bamu cika shiri dashi ba" dan dariya muniran tayi suka ci gaba da
casa hirarsu,har ta soma bata labarin bikin wata cousin dinta da zasu fara,wanda
tsiran kwana ukune dana qawarsu amina,wadda ta kawo dinkin ankonta yanzun.

Yadda taketa bawa iman labarin bikin da yadda aka tsara komai ya tabbatar
mata tana matuqar ji da bikin,har ta zolayeta da haka

"Keee,ba dole ba,kinsan manyan mutanen da zasu halacci bikin?,inda naji dadi ana ya
gobe dinner din amina zaayi kamu,ran dinner din amina ranar event din gidansu ango
za'ayi ba namu bane,so babu lallai naje,washegari ne zaa tashi bikin gadan gadan"

"Wai ita aminan dinner zatayi?"

"Eh mana,wannan atamfar ai ita zaa saka ranar" tabe baki iman tayi,saboda ita duk
wata harkar dinner ba zuwa take ba,bata damu da ita ba,koda ta damu dinma tasan ba
dabi'ar gidan bace,babu me barinta

"To inajin babu ni a zuwan"


"Saboda me?,ya al'ameen zai hanaki ko?" Dariya ta kubcewa iman
"Au,sharri zaki masa?har kinyi tafsiri ma?" Itama tana dariyar ta amsa mata

"Eh to ai nasan qarshen zancan kenan,nidai badon yayanki bane Allah cewa zanyi da
wata a qasa,wannan tsanani da boyo haka?,barima dai ya shigo inga ya yake ya alamin
din" maganarta saita dan shigi iman,duk da haka tana dariya ta miqe

"Yama fa shigo gidan amma kin jishi shuru,bari na duba koya gama na masa magana" ta
fada tana ficewa,ta manta bata dauki hijab din nata ba.

*LITTAFIN NAN NA KUDI NE,KI TUNTUBI WADAN NAN NUMBERS DIN DON BIYAN KUDIN NAKI*

09032345899
KO KUMA
09166221261
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 12

_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_

_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_

_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS?
YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS.
KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN
MU_

_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_

_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_

_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_

_ARABIAN OIL PERFUMES_


_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_

_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_

_SKIN CARE PRODUCTs_


_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_

_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN
FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_

_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_

_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_

_instagram:yerwaincense_and_more_*

_WhatsApp: 08095215215_
____________________________________

Tun daga bakin qofar dakin nasu qamshin turarensa ke karakaina,ya cika soron
gaba daya,taja numfashi sosai ta sheqi qamshin,tana matuqar son qamshin
turarensa,har yau kuma bata taba jin kowa da irinsa ba,babu abinda yake kashewa
kudi sosai wajen siyansa irin turare.

Knocking tayi yace a shigo,ta tura qofar a hankali,idanunta suka sauka


a kanshi,yana tsaye gaban mudubi yana ajjiye kwalbar turaren da ya gama fesawar
yana qoqarin dora hula saman kanshi,yayi kyau cikin shadda ruwan makuba,dinkin
zamani daya fidda samartaka sa zallar kyan da Allah ya bashi.

Ta cikin madubin ya kafeta da idanu,abunda bataso,sai ta kauda da kanta


tana cewa

"Yaaya,ta iso tun dazu tana jiranka"

"Ganinan fitowa,wani waje zani na tsaya ne na shirya gaba daya kar na saba
alqawari" ya fada yana daura agogon hannunsa,saita gaza tafiya yaci gaba da satar
kallonsa har ya fuskanci haka,ta basar da sauri,sabida wani iri takeji da ganin
kwalliyar da yayi din

"Yaa ina zaka da yammar nan" sai daya gama daura agogonsa tsaf sannan ya amsa

"Akwai wani da muka hadu da yace nakai takarduna,wala'alla idan da rabo zan samu
scholarship,tunda suna da hanya"
"Allah yasa a dace" tayi masa addu'ar da har cikin ranta haka yake
"Ameen qanwata,na gode" tadanyi murmushi sannan ta miqe ta nufi hanyar waje.

Cikin tattausar muryarsa yayi sallama cikin falon,munira ta daga kanta daga
danna wayarta da takeyi tana amsa sallamar

"Wow"bakinta ya motsa ta furta kalmar qasan zuciyarta,ta gyara zamanta sanda suke
magana da iman

"Karbomin fura wajen inna" ta amsa da to sannan ta miqe ta fita zuwa wajen
innar,dakin ya danyo shuru,saiya qarasa kujerar dake daga bakin qofa ya zauna a
hannun kujerar.

Cikin fara'a gami da mutuntawa munira ta gaidashi,ya amsa kadaran


kadaham,sanda iman din ta dawo da furar a cup ta miqa masa itama ta koma ta zauna.

Sai daya fara kurbar furar a hankali cike da nutsuwa sannan yace

"Muga kayan" saita dauka ledar ta aje masa a gabansa ta fidda kayan tana masa
bayani,baice komai ba harta gama yana shan furarshi,sai data kammala dai dai sanda
ya gama sha ya miqe da cup din a hannunsa

"Imani....ki dauka ki aje wajenki,idan zan fita jibi ki tunamin"


"To yaya" ta amsa masa sanda yake fita.

"Wow....wow,wannan shine ya al'ameen?,badan wani abu ba da na saka kai


wallahi" harara iman ta balla mata

"Ba zaki yaudararmin yayana ba,saboda nasan baida kudin da zaki tsaidashi takara"
dariya ta saki,tabbas abinda ke cikin zuciyarta kenan,saidai ba zata iya fitowa kai
tsaye ta gayawa iman din ba,tako ina al'ameen yakai namiji,abu daya ya rageshi
rashin 'ya'yan banki masu yawan gaske da zasu maisheshi wani,amma banda haka tabbas
gawurtacce kuma isashen namiji ne.

"Yanzu haka maganar ci gaba da karatunsa ce ta futar dashi" iman tadan


bata labari

"Allah sarki yayanmu,Allah ya bada sa'a"


"Ameen" iman ta amsa mata,daga haka suka fada wata hirar.

********. *******Tana daga zaune gefan katifar dake shimfide dakin iman,bayan ta
karbi dinkunanta da sukayi kyau sosai wanda al'ameen din yayi mata,wayarta na
hannunta tana ta danne danne,da yake gwana ce qwarai ita din wajen danna waya,shi
yasa babu inda ke mata wahalar shiga loko da saqo na kowacce irin waya

"Kiyi sauri don Allah muje kada mu samu layi" munira tace da iman wadda ke shiryawa
zasu wuce gidan qunshi,saboda gobe zaa fara bikin qawartasu

"Na gama ai,hijabi kawai xan saka" ta fada tana ware gogaggen hijabinta me kyau

"Kiwa Allah ki aje hijabin nan,wallahi wajen 'yan gayu ne sai kisa a dinga mana
kallon tara saura kwata,ko kamar nawa mayafinne ki saka,tunda kinga dai babba
ne,kuma bashi da shara shara" inan din ta buda baki zatayi magana munira ta dakatar
da ita

"Nasan yanzu zaki kawo karatun ya Alameen,goben ma kenan haka zakiyi?" Murmushi
kawai iman tayi,don kamar ta shiga zuciyartata,maganar al'ameen din ya hanata saka
mayafai zatayi mata,saita aje hijabin,ta bude ma'ajiyar kayanta,ta ciro daga cikin
sabbin lafayar da yagana ta bata,wata 'yar uwar mahaifinta har guda biyar masu
azabar kyau da tsada.

"Kai kai kai,ke kinga kyan datayi miki kuwa,ma sha Alla,da ana musayar
kyau Allah da tuni na karba naki na hadaki da nawa" munira ta fada cikin nuna santi
da yabawa da kyan iman din tayi,wanda zahirin gaskiya gaskiya ta fada,wani kyau
lafayan tayi mata,idan ka kalleta kamar ba zaka dauke ido ba,ita kanta dai data
juya ta sake kallon kanta a madubi ta gasgata hakan.

Tana tsaka da sanya halfshoe dinta da ya alameen ya siya mata 6k wanda ya


dace da lafayar jikinta wayarta da ya alameen din ya bata tecno ta dauki
tsuwwa,munira ta kalli sashen da wayar take,ta tuntsire da dariya tana cewa

"Ana kiranki a rakani kashinki?' sai data manna mata harara sannan ta isa inda
wayar take
"A haka nakeson kayata"

"Amma dai wallahi ba girmanki bane,dressing dinki sam bai kamaci wannan wayar ba"
ta saba da jin wannan lafuzzan daga bakin muniran,don haka tayi banza da ita ta isa
inda wayar take ta daga abunta.

Sai data gama wayar ta dubi muniran


"Su hamra ne,already wai suna wajen,har an fara yiwa wasu,mu kadane bama nan"

"Nasan zaa rina dama,munyi delay da yawa" munira ta fada tana daukar ledar kayanta.

Saida suka biya wajen inna,munira ta yiwa innan sallama da kuma


godiya,ita kuma iman ta karbi kudin qunshin sannan suka fito suka wuce.

AMARYAR KB BEAUTY PARLOR,katafaren wajen gyaran amare da uwayen


gidaje,yammata harma da zawara,waje ne na alfarma wanda ya kasance iya kudinka iya
shagalinka,wajene daya amsa sunansa,duk sanda kaje haka zakaga manyan hajiyoyi suna
karakaina,suna dukkan wani nau'in gyaran jiki da kuma kayan magunguna na gyaran
jiki da aka warewa waje na musamman a ciki.

Amarya sakina itama iyayenta da danshinsu,hakanan wanda zata aura din


shima ba baya bane,tun asali gidansu basu damu da karatun boko ba,kasuwanci sukafi
bawa qarfi,don haka sanda miji ya fito mata ya kuma tabbatar musu zai siya mata
dukkan wani certificate,basu wani jinkirta ba aka cireta daga karatun aka fara
shirin auren nata.

Tun daga shigarsu wajen iman tasan waje ne na matan da suka isa,dukkaninsu
qawaye ne,saidai bata wani saba can dasu kamar yadda suka shaqu da munira ba,don
haka bayan 'yan caftarsu ta qawaye da murnar shigowarsu,sai ta samu waje saman
kujerun da aka tanada a wajen tayi zamanta,tana sauraren hirarrakin dake tashi a
wajen,da kuma shige da ficen 'yan gayu mazansu da matansu.

Hira suke irin ta matasan yammatan dakeji da tashen quruciya,dukkansu


babu wadda ba daga babban gida ta fito ba,kusan ita daya ce ma kawai zaa ce
iyayenta ba wasu masu kudi bane,saidai ita din ma shigarta fes take,kai bakace
hakan ba.

Abu daya ne idan ka lura dashi zaka gane banbamcinsu,manya manyan wayoyin
dake hannun kowaccensu,da kuma irin kudaden dake jakarsu,kowacce ta fito da tata
tana harkar gabanta.

Mutum uku cikinsu saida samarinsu sukazo har qofar wajen suka basu kudin
lallaen da gyaran gashi,kowanne cikin babbar mota,hakan kudin da suka basu sababbin
ne a rafarsu.

Kafin zuwan nasu suka saka gasa,duk wadda kudin da aka bata yafi na
sauran yawa ita zaa fara yiwa,daga qarshe fahima ita ta cinye,dole ita aka saka
za'a bari a fara yiwa.

Ita dai nata idanu,sai wata matashiya dake kusa da ita wadda batafi
sa'arsu ba da aka sawa lalle,tun dazu ake kiranta babu me daga mata,don haka iman
din ta matsa kusa da ita

"Bari na daga miki"


"Yauwa na gode" ta fada a yagance tana murmushin jin dadin hakan da iman din tayi
mata,ta riqe wayar da kafadarta ta fara amsa kiran,murya can qasa,wanda da alamu
saurayinta ne ya kira,don sunyi doguwar waya sosai,har aka gama yiwa amarya sakina
qunshinta da qawarta da sukazo tare,ango yazo daukarta,dukka suka tashi mata
takiya,munira na cewa sai sunje sun gaisa.

Ko alamar motsawa iman batayi ba,amma munira ta finciki hannunta,dole ta


bisu.

Yana jingine jikin fara qal din motarsu,wadda da alama sabuwa ce,su biyune
shida wani matashin saurayin kamarsa,cikin fara'a da barkwanci irin na angwaye da
qawayen amarya,tana tsaye daga gefe tana kallonsu,don ita komai ma sabo ne a
wajenta,saboda wannan shine karonta na farko na bikin qawa a waje,ko cikin dangi ma
ba kasafai take zuwa ba saboda nisa da suka dan mata,daga na uwa har na uban,sai
dai daiku dake nan garin da suke.

Kowa cikinsu ta fara gabatar masa da kanta da kuma sunanta,har aka


gama,munira ta waiwayo

"Matso mana iman" abinda yaja hankalin angon da abokin nasa kenan"

Idanu abokin ya zuba mata sosai,ya furta

"Subhanallah" har zuwa sanda ta iso idanunsa yana kanta

"Itama cikin qawayenku take?" Saurayin me suna hashim ya tambaya bayan ta gama
gaidasu

"Eh....iman,ba kasafai ta fiya son shiga jama'a ba ai"

"That's good" ya fada yana gyada kai,still ita yake kallo,abinda yasa ta takura
kenan,taja da baya tana fadin

"Bari naje kafin ku gama,kada azo kanmu babu kowa"

"Wait iman....ki tsaya ki karba kudin liqi mana" kafada ta daga

"A'ah,na gode sosai wallahi" daga hakata qara sauri tayi ciki tana mita cikin
ranta,gaba daya batasan me yasa mazan yanzu suke da shegen kallo ba.

Basu jima sosai ba suka dawo,sauran su uku kenan da suka rage ba'a yiwa
ba

"Haba iman.....haba da Allah,me yasa kike abu kamar baki waye bane,ke dan samarin
nan ma na yayi da akeyi ki kasa yi,guy iya haduwa amma ki yarfashi ki taho,ke kinga
yadda ya rude da zancanki bayan kin taho,Allah annabi a hadaki dashi?,at last dai
dole muka bashi number dinki" idanunta ta zaro

"Me yasa zaku bashi don Allah,me yasa zakuyimin haka?" Ta fada adan rude,dukkaninsu
suka sanya dariya

"Seriously da gaske nake,yanzu me zance da ya al'ameen idan yaga wani ya kirani?"

"Waima.....wai.ya al'ameen,to meye a ciki?,shi kansa yasan kin isa a kirakin,waima


idan bai bari an kirakin ba,jiqaki zaiyi yasha?,a yadda Allah ya halicceki iman
saidai idan ba zaki dinga fita ba a gida zaki boye kanki" munira ta qarashe bayanan
suka kuma goyi bayanta

"Gaskiya kam,koni da za'a bani dama yaya na zan yiwa kamu" budurwar da ta taimaka
mata dazu ta sanya baki a hirarsu,kowa ya sanya dariya.

Ko a jikin munira ta qara gaba ta cire dan kwalinta don a fara yi mata
gyaran gashi,yayin da iman ta dinga binta da harara tana gasa mata ita.

Daidai sanda aka gama musu wayar muniran ta dauki tsuwwa,ta daga da hanzari

"Ina zuwa.....Allah bazanyi missing ba,gani nan zuwa" shine abinda muniran ta fada
tana maida wayarta jaka

"Don Allah don annabi qawalli ki rakani kamun nan,ban zaci abun haka aka shiryashi
ba sai yanzu da batula ta kirani,ba zamu jima ba in sha Allah zamu taho,kinga hanya
daya zamuyi,gida zan koma zan debo kayana,sai gobe zan wuce gaba daya" da farko
uzuri ta bata kan yamma tayi sosai,kafin suje ma magariba tayi,kuma malam yana fada
idan tayi dare a waje,haka ya al'ameen,da qyar munira tasha kanta,tace zata rakata
har gida ta yiwa inna bayani,zannan ta aminta,nan cikin kayan data amso dinki ta
zabi daya daga ciki ta sauya,ta kuma biya aka mata lite makeup,tayi tayi iman ta
dauki wani a ciki itama ta sauya tace aa,kayan jikinta sun isheta.

Tun daga shigansu wajen iman ta tabbatar lallai bikine na manya,wadanda


sukaci suka tada kai,wani mahaukacin gida ne mai dauki da tafkekiyar haraba,wanda
ama qawata ta da decorations irin na biki,duk yawan jama'ar dake wajen ta daukesu
tsaf,harda ragowar sararin da motocin gidan ke fake abinsu basusan anayi bama.

Tunda suka shiga din iman ta samu seat ta zauna,daga inda take din tana
iya hango yadda komai ke wakana,amarya tayi kyau iya kyau tare da angonta,sai
gudanar da komai ake cikin fariya boko da kuma nuna wadata.

A hankali ta daga kanta ta kalli yadda sama ta fara duhu,alamu suna nuna
anyi kira sallar magariba zuwa yanzu,duk da bata iya jiyo kiran ba saboda tashin
kidan daya karade wajen. Kome take kuma ko a ina take bata wasa da salla,haka aka
tarbiyyantar da ita,don haka ta laluba wayarta ta fara kiran munira babu
qaqqautawa,wanda sai a kira na biyar ta samu ta daga,tace mata gatanan zuwa,ba
jimawa kuwa sai gata,da alamu biki yayi biki

"Nifa zan wucw gida gaskiya,gashi har anyi sallah mu bamuyi ba"
"Don Allah ki bani minti goma kacal,ummi ce zata bani saqo na tafi dashi"
mahafiyace,ba zata iyace mata karsu jira ba,saita rausaya kai

"Idan na koma gida malam ya koroni kyasan inda zakiyi dani,kaini wani wajen nayi
sallah" dariya ta saki

"Ba korokin da zaiyi,ya kori auta ai babu wannan maganar,muje na rakaki" tare suka
jera da ita,saidai duk inda suka gifta sai an kalli iman din,yawanci kallo ne na
baqunta da kuma tsarin surar da Allah yayi mata,wadda ta fita daban data sauran
mata.

Ganin yadda hanyar shiga gidan ke cike da mutane sai iman din ta dakata
da bin munira

"Gaskiya ki samarmin wani gurin inda zan kebe ni kadai nayi sallata,cikin gidan nan
da alama a cike yake,kuma ni babu wanda na sani" tayi qoqarin nuna mata babu komai
ta shiga amma tace a'ah,don haka ta jata can bayan gidan,inda garden din gidan
yake,wanda ke wadace da grass carpet,da kuma famfunan da ake bawa lambun ruwa

"Yauwa,yanzu naji daidai" iman din ta fada tana ware idanunta cikin wajen saboa
yadda ya birgeta,wata iska ta daban wajen yake fitarwa,bugu da qari shuru yake
kamar ba cikin gidan dake cike da hayaniyar biki yake ba

"Ki kirani idan kin gama saimi wuce,ni hutun sallah nake"

"Baki da matsala,amma dana gama zazu zamuyi gida"


"In sha Allahu" ta fada tana juyawa da sauri zuwa ciki,iman ta bita da kallo,cikin
ranta tana mamakin yadda muniran ke bala'in son alaqa da masu kudi,take kuma qaunar
bikinsu,saita dage kafada,qila don ta taso taga haka danginsu yake.

A hankali take takawa zuwa wajen wani famfo daketa zuba shi kadai yana
aika ruwa zuwa sasannin shuke shuken dake fadin lambun,ta tsaya a gabansa cikin
nutsuwa,ta waiga ta tabbatar babu kowa,sai ta fara ware lafayar dake jikinta don
kada ta jiqe,ta ajjiyeta gefe,ta daura alwalar,sannan ta dauketa ta yafata a
matsayin mayafi kawai ta tada sallarta,sai data idar sannan ta miqe,ta zameta daga
kanta ta fara daura abarta a jikinta.

Sau uku tana nadata tana jin batayi mata dai dai a jikinta ba,karo na
hudu taja tsaki ta fara warewa da xummar sake daurawa

"Kawo na tayaki tunda kin kasa" sautin muryar daya daki dodon kunnenta kenan wanda
ya razanata,ta kuma rude gaba daya,ta damqe lafayar tata da hannayenta gaba daya,a
kuma matuqar tsorace sannan a razane ta waiwaya don ganin waye?,daga ina kuma ya
shigo ko ya fito?.

*ZAFAFA BIYAR*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_


_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI
SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa


1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼


👇

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

YAN NIJAR 👇

+227 95 16 61 77

Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number
______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY


INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*13

_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_


_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_

_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS?
YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS.
KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN
MU_

_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_

_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_

_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_

_ARABIAN OIL PERFUMES_


_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_

_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_

_SKIN CARE PRODUCTs_


_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_

_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN
FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_

_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_

_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_

_instagram:yerwaincense_and_more_*

_WhatsApp: 08095215215_

____________________________________

Matashin saurayi ne tsaye a bayanta,fari qal,wanda har wani yellow yake


saboda haske,ma'abocin kyau na gaske,wanda fuskarsa ta cika da baqin gemu da kuma
sumar kai,ba siriri bane kamar yadda yake ba mai qiba ba,jajayen lips dinsa dauke
suke da murmushin da ya bayyana fararen haqoransa,yana sanye da wata muguwar shadda
daketa faman zuba qyalli da maiqo,ruwan hanta wanda ta dace da fatarsa da kuma
fitar da kyansa muraran,hannayensa na goye qirjinsa,wanda hakan ya bayyana muqullin
motar dake soke cikin daya daga cikin 'yan yatsunsa.

Tsoro ya sanya ta sake ja da baya ganin yadda yake ci gaba da


kallonta,murmushi shimfide saman fuskarsa,cikin wata murya mai zaqi ya sake cewa

"Gashi nadin yayi miki kyau sosai da sosai,saidai kuma kuma baki iya daurawa
ba,halan mama ce ta daura miki kafin ki fito?" Rasa amsar bashi tayi sai idanu da
take rarrabawa

"Wannan auta ce da alama" ya sake fada yana komawa da baya a hankali ya zauna saman
kujerar concrete dake wajen,har yanzu bai janye idanuwansa daga kanta ba,hakanan
murmushin da yakeyi baibar kan fuskarsa ba

"Iman.....iman" sautin muryar munira ya fara shigowa wajen,da alama ita take nema

"Uhunnn.....da alama ke suke nema,abokan tafiyarki ne ko?" Ba tare daya jira


amsarta ba ya dora
"ki daura abarki,lemme close my eyes" ya fada yana lumshe qananun kyawawan
idanunsa.

Ta tabbatarwa kanta ba zata iya fita a haka ba,saboda al'ummar dake


harabar wajen sun ninka shi a yawa,saita leqa a hankali,ta tabbatar da gaske
idanunta a rufen suke,don haka cikin sauri ta fara daurawa.

"Are you finished......an min izini na bude idanuna?" Ya fada a tausashe

"Eh" ta amsa cikin sanyi,ya bude idanun nasa tarwai saman fuskarta

"Wow.....wow I didn't realize yadda ta miki kyau kamar yanzu da nake kusa dake,
please ke wanne yare ce?......i think kanuri ne suke amfani da ita ko?" Yadda yayi
maganar har saman fuskarsa ya nuna da gaske so yake ya sani,don haka ta gyada kai

"Eh sune"
"It means ke din kanuri ne?" Kafin tace komai munira ta iskota

"Canza waje kikayi kenan inata bul......" Maganarta fa maqale a maqoshi sanda
idanunta suka sauka a kansa,saita rusuna da sauri cikin girmamawa

"Yallabai barka da yamma" cikin wata dakiya wadda bada ita yanzu yanzu suke magana
da iman ba yace

"Barka" kafin wani a cikinsu ya sake magana wata muryar ta sake cika wajen da kiran
sunan

"Bassam.......bassam"
"Hey guys.....wannan kiran fa?" Ya fada yana daga sautun muryarsa dake da
zaqi,wanda har sai da iman tadan sake kallonshi.

Mutum biyune suka qaraso wajen,dukkansu samari ne da kana musu kallo daya
zakasan sunaji da jini da ajiki da kuma tashen samartaka,kowannensu kalar shigar
dake jikinsa zata fallasa maka wadatar da yake ciki

"Shege....baka da mutunci wallahi,na dauka da gasken kayi tafiyarka" daya


daga cikinsu ya fada yana cika yana batsewa,tare da jifansa da harara,baki ya tabe
kamar yadda mata kanyi

"Gab nake da tafiyan ai,rabo yasa na ratso ta nan" yayi maganar kansa tsaye yana
nuna iman da yatsan hannunsa,dukka suka waiwaya suna kallonta,abinda ya sanyata
gaba daya taji ta tsargu ta kuma takura,

"Rabon samun matar aure" kamar saukar tsawa iman taji maganar,wanne irin magana ce
wannan yakeyi,bayan har yanzu basu zarce mintuna ashirin da fara ganin juna cikin
rayuwarsu ba,batasanshi ba bai santa ba,har yanzu ko kalma daya tak bata furta
gareshi ba,saita rutsashi da kallon mamaki,ganin haka shima ya tsareta da nasa
kallon tare da murmushi mai qawatarwa

"Yes,da gaske nake" ya tabbatar mata yana lumshe idanunsa tare da budesu a lokaci
guda

"Muni......qawarki ce?" Daya daga cikin wandanda suka shigo wajen ya tambaya,cikin
murmushi tare da madaukakin farincikin da muniran keta qoqarin dannewa tace

"Eh yaya ahlan,aminiyata ce......"


"Zaku iya bamu waje mu tattauna?" Matashin da aka kira da bassam ya fada still bai
iya dauke dubansa daga kan iman ba,sai ahalan din yaja da baya

"Baka da matsala,but kada ka dade da yawa"

"Alright" ya amsa a taqaice,dukkaninsu sai suka juya suka fara barin wajen,yayin da
iman ta bisu da kallo cikin taraddadi,tamkar ta bisu amma ta gaza daga qafarta daga
wajen.

"Have a seat please" ta tsinci muryarsa yana tsaye daga bayanta kamar wani
bodyguard da uban gidansa,ya tashi daga mazauninsa ya bata daman zama,bata da abun
cewa illa qarasawa da tayi,a hankali ta zauna kamar yadda ya buqata,saidai bata
wani saki jikinta ba kamar wadda ke dosane saman garwashin wuta.

Qarasowa yayi a hankali,ya shimfida handkerchief a gabanta qasa saman


grass carpet din yayi xaman dirshan,tazarar dake tsakaninsu ba me nisa bace,saidai
bai kusantota da yawa ba,ya aza mata dukka idanunsa sannan ya fara magana da ita.

"sunana bassam balarabe madaki....." Kai tadan daga kadan ta kalleshi,kamar


tasan sunan,kamar tana dan jinsa cikin kafafen yada labarai

"Nine da na uku a wajen mahaifina,da na farko a wajen mummy na,shekarata ashirin da


da takwas,'yan kasuwane mu duk da muna karatun boko me zurfi,hasalima nine jagoran
dukka kamfanonin madaki general enterprises,ban taba aure ba,saidai for now zan
sanya damba,domin kuwa naga matar aure,sai kuma inda qarfina ya qare,ki daga kanki
ki kalleni da kyau kiga nayi miki ko banyi miki ba,saboda ni din mutum ne kaifi
daya,banason boye boye kuma ban iyasa ba....."shuru ne ya ratsa tsakani,bata ko
motsa ba bare ta daga kai ta kalleshi,sai wani bugu da zuciyarta keta
famanyi,saboda tsayin rayuwarta bata taba tsaiwa da wani da sunan saurayi ko
soyayya ba saishi.

Duk yadda yayi kan ta dubeshi ko tace wani abu taqi,har wayarta ta dauki
tsuwwa,sunan inna ya bayyana,abinda ya sanyata miqewa zumbur kenan

"Innata ke kira,tun daxu muka fito,kuma tacemin kada nakai dare a waje" tayi masa
bayanin tana qoqarin bin bayan kiran inna daya katse.

Wayar ya zubawa idanu har zuwa sanda kiran ya shiga,a dan rude takewa innar
bayanin gata nan a hanya,bata saurareta ba sai fada da taketa tsula mata kamar xata
rufeta da duka ta cikin wayar,dai dai sannan munira ta sake shigowa.

"Kije xan rakota zamu fito" amsar daya hawa munira kenan,saidai kafin ya
miqe iman har tabi bayan munira,cikin azama ya cimmata suka jero.
Sai gaba daya ta duburce saboda yadda idanuwa suka dinga yawo a
kansu,suka dinga jan hankalin mutane,ta lura sam ko a jikin bassam,sai hira da yake
janta dashi cikin lanqwashashiyar murya,idanuwansa a kanta duk bayan sakan uku zuwa
biyar,har suka qaraso parking lot na gidan.

Milk color din wata jibgegiyar mota ya bude mata yana fadin

"Bismillah" baya taja,idanunta na nuna alamu na tsoro

"Xan qarasa titi nahau napep" waiwayawa yayi ya kallo munira

"Ke baki gaya mata anguwarnan ba'a samun abun hawa na haya ba?"

"Bata sani ba" munira ta amsa masa cikin wani salo na yauqi irin na 'yammatan da
suke ji da kansu

"Ok,muje na fitar dake titi a motar,amma bisa sharadi daya......idan ba'a samu abun
hawa ba,zan kaiki unguwarku" a jikinta takeji zaa samu,don haka tace masa ta
yarda,saiya gyada kai yana murmushi

"Allah kasa nayi winning", ya fadi harda daga hannayensa sama,tadan dauke kai kadan
yana son bata dariya ganin yadda ya haqiqance bilhaqqi.

Wani sassanyan qamshi ke tashi cikin motar,ko ba'a gaya maka ba kasan
turaren da yake amfani dashine ya hadu da qamshin freshener na mota da kuma sanyin
ac ya bada wani yanayi me mugun dadi,tun daga waje dama zakasan motar sabuwa
ce,cikin motar kuma shi xai qara tabbatar maka da hakan.

Addu'ar bassam itace taci kuwa,don sun jima suna tsumayin samun abun hawa
saidai babu shi,dole hakanan tana ji tana gani suka dauki hanya zuwa
unguwarsu,zuciyarta ta dinga bugun uku uku,ranta cike fal da tsoro da kuma fargabar
kada ta hadu da wani dan gida.

Tunda suka soma tafiya yake janta da hira,cike da nuna tsantsar kulawa da
wani salo dake nuna zallar shauqi,baiji kunya ko nauyin ganin idanuwan munira ba ya
dinga fayyace mata zuciyarsa,kalamansa suka dinga yi mata nauyi aka,har kunya tasa
ko cikakken motsi ta kasa,karo na farko da wani ya zauna yana shirya wasu manyan
kalamai wai duk don saboda ita,ta yadda lallai kamar yadda ya gaya maya ne,shi din
bashi da boye boye ko kuma rufa rufa,a haka har suka iso dab da layinsu,tasa ya
ajjiyeta daga baya baya.

Har tasa hannu zata buda murfin motar da hanzarinta,ya danna mata Lock

"Ya zaki tafi ki barni haka?,babu gamsashshiyar amsa,sannan kuma babu madafa,so
koke gobe ayi jana'izata?"

"Me kake buqata?"


"Phone number dinki" ya amsa mata kai tsaye,so take ya barta ta wuce don haka ta
fara karanta masa yana serving,duk da haka bai barta ba har sai daya kira yaji ta
shiga sannan yace

"Thank God" ya furta yana fitowa shima da sauri dava motar,ya zagayo inda take ya
bude mata cikin girmamawa.

Waiwayowa tayi ganin ya fara take mata baya yana biye da ita kamar wani
bodyguard,ta buda baki zatayi magana,ya ritsata da kallon nan nasa

"Tattaki zan miki angel...."ya amsa mata tambayarta tun batakai ga yinta ba
"A'ah,don Allah ka bari,wallahi na gode,zan qarasa,munira zata rakani" hannayensa
ya sanya ya rufe fuskarsa kadan yana furzar da iska

"Banso kika dakatar dani ba....but,ba yadda zanyi,abinda zuciyarki keso ya zama
kamar umarni ne a gareni.....munira" ya kira sunan muniran da tayi mutuwar tsaye a
gefe

"Ki kulamin da ita,har ku isa gida banaso ku quda ya tabata.....deal" tunda ya fadi
hakan tasan me yake nufi,ko banza yau za'ayi mata yayyafin kudi,tasan a zaune take
wannan,haka suka jera da iman din zuwa cikin layinsu,bassam ya bita da idanu,yana
jin kamar ya hadiyeta,wani wawan kamu soyayyarta tayi ma zuciyarsa,irin kamun da
ba'a taba yi mata irinsa ba,bayajin zai iya haqura da yarinyar ba tare da ya
mallaketa ba.

*ZAFAFA BIYAR*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_


_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI
SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa


1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼


👇

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

YAN NIJAR 👇

+227 95 16 61 77

Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number
______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY


INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 14


_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_
_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_

_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS?
YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS.
KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN
MU_

_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_

_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_

_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_

_ARABIAN OIL PERFUMES_


_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_

_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_

_SKIN CARE PRODUCTs_


_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_

_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN
FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_

_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_

_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_

_instagram:yerwaincense_and_more_*

_WhatsApp: 08095215215_
_____________________________________

Cikin wani irin zumudi da zakwadi munira tayi hanzarin kamo iman suka jera

"La'ilaha illallahu,wallahi kin cika 'yar baiwa iman.....dama ni jikina yana bani
ke matar manya ce,da alama ke zaki zama tararuwar gidanku.....iman,kinsan kuwa waye
bassam a karan kanshi kafin akai ga mahaifinsa?,kinsan yammatan dake layi da kai
kawon kama qafa dashi?,bakya amfani da social medias ne,amma da basai na gaya miki
waye bassam ba" hankalinta duka yayi gida,saidai tana saurara gami da fahimtar
kowacce magana ta muniran ke magana akai

"To sai akayi yaya?"


"Don girman Allah kada kiyi mana baqulu da baqinciki,don wallahi bake kadai
ba,hatta ni na warke,na kuma sake zama babbar yarinya,don Allah kada ki qauron
baki,kada kice baki sonshi,saboda bassam irin mazan da kowacce mace ke buri da
qauna ce" munira ta fada tana marairaicewa

"Nifa tsaya kiji,na yiwa ya al'ameen alqawarin bazanyi soyayya da kowa ba" idanu
munira ta fitar kafin ta maidasu

"Kamar yaya?"

"Eh,yace idan lokaci yayi zai fitarmin da miji" dariya ta saki sosai cikin nishadi

"Dalla can,ashe ke baki da wayo,ya fadi hakane fa a sannan saboda qananun


shekarunki,kada farinjinin da kike dashi maza suyi amfani da kya da kike dashi su
yaudareki,amm kawo yanzu ai kinkai munxalin fara zance ma,tunda dukkanmu zance
muke,ga wasu ma an fara aurarwa,koshi yaga bassam zai miki sha'awarsa,zai kuma so
ya zama surukin gidanku" kai iman ta kada

"Duk abinda ya al'ameen ya fada yana nufin abinda ya fada din"

"Ikon Allah,nifa ban ganewa wannan dagiyar ta ya al'ameen ba,banda yayanki ne ai da


sai nace ko kansa yakewa tanadi ne?" Waiwayawa kawai tayi ta kalli muniran,saita
dauke taci gaba da tafiya batace komai ba,kunnuwanta na sauraren magiyar muniran
kan kada ta tankwabar da soyayyar bassam kamar yadda ta yiwa dan uwata sadam

"Ke kamar bakisan rayuwa ba iman,wasu har rubutu da maganin farinjinin samun mai
kudi ake musu,ke kuma kin samu daga Allah amma zaki wofantar da damarki,ki godewa
Allah wallahi,koda bakison sadam ko qawance kukayi wallahi saikin tserewa sa'a a
cikin dangi da qawayenki,saikin wuce kallon raini,ke ba zakisan haka ba,amma ni
naga abubuwa da dama kuma ina kan gani cikin dangin umma na,saboda mahaifina ba
kowa bane,mahaifiyata tana auren mutumin da ba wani ba" wannan hirar ita ta kaisu
ga qofar gidansu iman,wanda babu mutane sosai,sai dai daikun daliban malam da suka
dawo daga gurare daban daban akayo gida kuma,wasu na cin abincinsu na dare wasu na
hira,saboda yau din ba ranar karatu bace,uwa ba kuma alamu na nuna malam din baya
kusa ma.

Kallon da inna ta watsa mata sanda ta shiga shi ya sanyata ta shiga


taitayinta,munira ta qaraso ta rusuna gaban inna

"Don Allah inna kiyi haquri,wallahi gidan qanwar umma ta rakani,ummance kuma ta
tsaidani zamu amshi saqo mu taho mata dashi,don Allah inna kiyi haquri,laifina ne"

"Allah ya tsare gaba,amma ku kiyaye,kada ku bari ku dinga yin dare a waje,'ya'ya


mata ne ku"

"In sha Allahu inna,ayi haquri,na gode" munira ta fada tana miqewa,suka qarasa
dakin iman din

"Don Allah qawa na roqeki,nasan zai kiraki,koda baki sonshi ki tsaya ki saureshi a
rabu lafiya" munira tace da iman cikin lallabawa sannan ya fito bayan sunyi
sallama.

Kayan jikinta ta fara cirewa ta sanya na zaman gida,sannan ta daura alwalar


sallar isha'i,ta dawo dakinta ta tayar,data idar tayi zaune saman abun sallar,tana
jin gajiya na nuqurqusarta,ta daga kai ta dubi agogo,bataji duriyar alameen ba,da
alama bai dawo bane,da tuni ya nemeta.

Idanunta suka sauka kan ledar da munira ta ajjiye mata me kayan takeaway
na bikin data hadota dasu,ta janyo ta bude ta gani,su souvenir's ne kala kala harda
na banza da rashin sanin ciwon kudi,sai kuma kayan ciye ciye.

Jakarta ta zaro cikin kayan ta bude don ciro wayarta,hannunta ya sauka kan
wasu abubuwa,ta zazzagesu da hanzarinta. Sabbin kudade ne fil a miqe,yan 200 bandir
guda,idanu ta fiddo waje cikin tsoro da mamakin yadda akai kudin suka samu,sai kuma
tayi tunanin na munira ne,tunda jakar na hannunta,don haka ta dauki wayarta ta cire
lock din ta fara qaqarin nemanta,saita ga alamun tex,ta buda don duba daga ina
yake.

Ta zaci daga kamfanin mtn ne,don su kadai ke tura mata saqo,saidai a yau
din akasin hakanne,don kuwa wata tsararriyar number ce dauke da wani zazzafan
saqo,wanda ke cike da wasu shiryayyu kuma tsararrun kalamai dake nuna zallar
shauqin soyayya da ma'abocin saqon ya tsinci kansa a ciki.

Sau uku tana karanta saqon tana komawa farko,sai daga qarshe idanunta suka
kai kan sunan bassam,ta maimaita sunan sannan ta goge saqon da sauri,zuciyarta na
bugawa,ta fita ta kira munira

"Kinyi mantuwar kudinki cikin jakata fa"

"Ba nawa bane,naki ne,bassam yace a baki" kicin kicin tayi da ranta

"Amma me yasa zayimin haka?,kinsan dai bana karbar kudin kowa ko?ko sadam da yake
dan uwanki ban karbi kudinsa ba kin sani,bare wannan da bansan kowa nasa ba"

"iman.....wai me yasa kike haka ne?,kinsan dai babu kyau maida hannun kyauta baya
ko?,ya zaa dinga miki alkhairi kina qin karba?"

"Na karba idan an gani a gida nace me?"

"Dama ni bance ki nuna ba,idan kinsan za'ayimiki fada ki ajjiye abinki ki dinga
zara kina amfani dashi"

"Banaso munira,kizo kawai ki karba abinda ki maida masa" dariya taji ta qyalqyale
dashi

"Toni ina zan ganshi yanzu?,bayan kin fita daga motar naji yana waya,a taqaice dai
a abuja zai kwana ba'a kano ba,sannan na riga da nayi masa alqawarin zame masa
jagora wajen samunki,kinga idan kina tsoro ma kina iya bashi dama yazo gida yaga
malam......hakan zaisa kuyi tarayyarku babu tsoro ko shakku,kiyi amfani da kudinki
kawai malama,sai da safe" munira ta katse wayarta abunta ta barta da waya a hannu.

Karar shigowar kira ya sanyata zabura,saura kadan wayar ta subuce a


hannunta,tayi qoqarin saka wayar a silent sannan ta nutsu ta duba me kiran,idan har
idanunta dai dai suke nuna mata number dazu ce data tura mata saqo,saita samu kanta
da latsa ok,ta kara wayar a kunneta.

Zazzaqar muryarsa ce ta fara dukan kunnenta,a hankali ta amsa masa


sallamarsa

"Kin tafi kin barni da kewarki,inajin kamar ba awannin da suka shude bane muka
rabu,kamar wasu shekaru ne suka raba tsakaninmu....." Yayi maganar cikin salon iya
jan hankalin diya mace,da kuma zallar qwarewa wajen sace zuciyar diya mace

"Don Alla kice wani abu kafin zuciyata ta fashe imani......zuciyata ta kamu da
mahaukacin sonki,wanda har ta fara hasashen yadda rayuwa zata kasance mata babu
ke". Wata ajiyar zuciya cw ta subuce mata saboda nauyi da kalamansa suka fara yiwa
zuciyarta

"Me zance maka to?" Ta samu kanta da furtawa

"Koda bakice komai ba ki saki jiki ki bani dama,don koda baki fada ba na samu
labarin nine mutum na farko da zan fara bude zuciyarki,so inason ayimin alfarma a
kuma bani dama,nayi dashe me kyau,wanda zai bada kyakkyawar yabanya......don Allah
beauty" ya qarashe maganar cikin marairaicewa.

Murmushi mara sauti ya subucewa fuskarta,ashe itama watace,ashe takai a


gaya mata kalamai har haka anema soyayyarta,itama ashe takai,kalaman baqine ga
kunnenta,saboda haka nan da nan ta sake ta bashi kunnuwanta,yayi amfani da wannan
damar ya dinga mata hira me matuqar dadi,yana kodata gami da yabata takowanne
fanni,tare da kuranta matsayin data samu cikin 'yan daqiqu,da kuma yadda zuciyarsa
ta mato mata.

Kiran sunanta da taji inna nayi daga tsakar gida ya dawo da ita daga
nisan kiwon da tayi,cikin hanzari ta katse wayar,ta kuma kasheta gaba daya ta tura
qasan filo,cikin yanayi rashin gaskiya ta kwasa ta yiwo waje da sauri ta tsaya kan
inna

"Gani inna" kallo ta bita dashi a nutse kafin daga bisani tace

"Me kika shiga daki tun dazu kika zauna kinayi ko abincinki baki dauka ba?"

"Sallah nake inna?"


"Qara'insu kikeyi?" Da sauri ta girgiza kai

"A'ah inna,isha'i ce kawai,gajiya tasa dana gama nadan kwanta,kinsan munsha zaman
lalle"

"Yayanki ya shigo,bakiji shigowarsa ba?" Tayi mamaki,don har ga Allah bataji


shigowar tasa ba da gaske,karo na farko da irin hakan ta faru,don babu wani abu
dake shagaltar da ita ta kasa jin shigowar al'ameen din

"Banji ba inna,gyangyadi ya saceni" ta fada tana istigfarin qaryar data sharara

"Dauki abincinsu kikai musu,daga nan ki cewa sadiqu yazo ina kiransa"

"To inna" ta fada tana daukar babban farantin kayan abincinsu tayi dakin.

Kamar ko yaushe sai data tsaya tayi sallama aka bata izini sannan ta cusa
kai,dashi idanunta suka fara karo,hannunsa riqe da wayarsa yana kallon wasu styles
na dogayen riguna daya dora a account dinsa na Instagram,wanda bai jima da budeshi
ba bisa shawarar sadiqu.

Sexy eyes dinsa da suka sake lumshewa saboda gajiya da yunwa ya buda a
hankali ya sauke a kanta,ta qaraso a nutse ta ajjiye farantin

"Sannu da zuwa yaya"

"Yauwa queen.....ya gida?"


"Lafiya lau yaya,ya aiki"

"Alhmdlh,zubamin abincin" ya fada yana zamowa daga saman kujerar zuwa


qasa,hankalinsa akan lallenta baqi da ja wanda yayi masifar zanuwa saman farar
fatarta me haske sosai
"qunshin yayi kyau sosai queen" ya samu kansa da fadi sanda take qoqarin zuba masa
abincin,saita daga kai suka hada idanu,cikin jin nauyinsa tace

"Na gode yaya"

"Amma garin yaya kikayi dare haka?" Dan raurau tayi da fuskarta

"Allah yaya munira na raka wajen event din cousin dinta,kuma ta yiwa inna bayani"

"Ki kiyaye please,kinga ke Queen ce,bai kamata sarauniya guda a dinga ganinta a
araha a waje ba har dare" murmushi ya sake subuce mata,ta gyada kai tana murza
yatsun hannunta,daidai sannan sadiqu ya fito daga bandaki

"Zubamin nima ina zuwa,abu me sanyi yau nake sha'awar sha" ya fadi yana nufar qofa

"Inna tana kiranka ma"


"Tom" ya qarashe amsa matan yana ficewa.

Yana cin abincin yana satar kallonta,sake kyau da zama cikakkiyar budurwa
take,hatta da fuskarta ta nuna hakan balle gangar jikinta,kamar ma so take ta haura
shekarunta,tana dagowa suka hada ido,sa ya mata nuni da wata leda

"Ga mayafinki can" cikin murna ta tashi ta dauko tana dubawa

"An gode yaya,Allah ya qada budi,amma yaya kala biyu ne fa"

"Wannan zai hau kowanne kaya cikin ankon,kiyi amfani dashi,daga baya saina sama
miki dayan" kai ta gyada kawai,amma bataso hakan ba,saboda anyi duka qawayensu kala
daya zasu saka.

Tana maidashi cikin ledar sadiqu ya shigo da lemukan a hannunsa,ya miqa


mata wasu

"Ki dauki daya ki kaiwa inna sauran" ta karba tayi godiya sannan ta fice.

A wajen inna abincinta ta karba tace zataci a daki,hankalinta da


tunaninta duka ya koma kan wayarta,koda ta shiga dakin,kunna wayar shine abu na
farko data fara yi,tana gama kunnuwa saqonni suka fara rigen rigen shigowa a jere
kusan guda biyar,saita koma ta zauna,murmushi na subuce mata tana qoqarin budawa ta
karanta.
[7/19, 10:01 PM] Mummyn Yara: 15
_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_

_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_

_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS?
YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS.
KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN
MU_

_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_
_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_

_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_

_ARABIAN OIL PERFUMES_


_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_

_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_

_SKIN CARE PRODUCTs_


_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_

_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN
FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_

_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_

_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_

_instagram:yerwaincense_and_more_*

_WhatsApp: 08095215215_
_________________________________

Dukkan saqonnin nasa suna tafe da kalaman dake nuna rudun da ya shiga kan
katsewar wayar da kuma jinta a kashe da yayi bayan ya sake kira,magiya yake mata
kan ta taimakeshi ta buda wayar tata,ta daure tayi kiransa,murmushi ta kuma
saki,yanzu kashe wayarta kawai ya sanyashi a damuwa?,wanne irin so ne wannan?,har
ta dannan kiransa ta fasa ta katse,ta ajjiye wayar ta jawo abincinta tahau
ci,saidai tana ci gefe guda kuma zuciya da qwaqwalwarta suna dawo mata da abubuwan
da suka faru wunin yau,tun daga haduwarsu kawo yanzu,duk kyanta da yake fadi gani
take ya fita,saita miqe ta isa gaban mudubi tana qarewa fuskarta kallo,kalamansa a
kanta na dawowa kanta turyan turya,sai ta kuma sakin murmushi,ta juya ta dauki
kwanon abincinta da kayan ciye ciyen bikin da muniran ta hadota dashi don ta kaiwa
inna ko zata iya cin wani abun a ciki.

***********Washegari*******. Da saqonsa tayi karin kumallo,wasu irin shiryayyun


kalamai dake dauke da dandasa dandasan kalaman zallar soyayya,dolenta murmushi ya
subuce mata bayan ta kammala karantawa,yakansa ta shiga mamakin wai ita din me
muhimmanci ce har haka?,itama ashe watace data cancanci samun qauna maqura?,tana
wannan tunanin saiga kiransa,ta sake yin sauri wajen saka wayar a silent.

Sai data katse ya qara kira sannan ta daga


"Beauty.....girmanki ne,amma kuma so kike na haukace na kasa aiwatar da abinda ya
kaini abuja?kinsan kuwa samun hadin kanki shine kawai abinda zai bani nutsuwar
aiwatar da abinda naje yi din?" Murmushi ta saki a boye

"Ni wacece da hakan zata faru da kai?"

"Kina mamakine ko kina tantama?,lallai da alama har yanzu bakisan irin matsayin da
kike dashi a wajena bane,kinsan tunanin kina da wani masoyin da ranki keso kadai
daga jiya zuwa yau ya sanyani nayi zuru zuru,zakiyi mamakin yadda na koma,please
beauty......kicemin ni kadai ne wanda ya fara yaqin neman soyayyarki,duk nasan
mafarkine kawai nakeyi,amma mace kamarki lodi lodin maza nasan ke gware a kanta"
yadda yake maganar cikin laushi da sanyi ya bata dariya,har batasan tace dashi

"Kai kadai ne" ba,wani qaramin ihu ya saki,wanda yake nuna zallar farincikin da
zuciyarsa ke ciki

"Yes.....kice na sanar da mommy a daidai" idanu ta zaro

"Me?" Ta tambayeshi cikin mamaki da fargaba

"Eh, already labarinki yaje wajen mommy,tun a jiyan ban iya barci ba sai dana gaya
mata komai dana sani game da ke,infact ma ita harta matsu taga beautyna,na gaya
mata,ta qara haquri har na shawo kanki tukunna"

"Bassam" ta kira sunanshi a karon farko

"Nifa na yiwa yayana alqawarin bazanyi soyayya da kowa ba, already ma yace shine
zai zabarmin miji" wani mummunan faduwa gabansa yayi,take ya rikice mata,har abun
yayi matuqar bata mamaki,da gaske yake kan duk abinda ya fada,da gaske ne yadda
yake kururuwar sonta

"Please give me a chance beauty,ki bani dama....na miki alqawari indai na kasa sace
zuciyarki da samun soyayyarki zan amshi sunan looser,zan kuma rabu daki,amma na
tabbata yayanki baya nufin abinda ya fada" sai data ce ta bashi damar sannan taji
salama da sukuni cikin muryarsa.

Da hanzari tayi masa sallama tana katse wayar,ganin ya kusa cinye mata
lokacin aikinta,ta cusa wayar qasan pillow,sannan ta janyo dankwalinta ta daure
sassalkan gashinta ta futo tsakar gida,qirjinta cike fal da bitar kalamai da
al'amuran da suke gudana tsakaninta da bassam,tun daga haduwarsu kawo yau.

Tana tsaye a kitchen tana dama kunu,tayi nisa cikin tunaninta,a hankali
ya qaraso bakin qofar kitchen din,idanunsa suka sauka a kanta

"Assalamu alaikum" yayi sallama cikin tattausar muryarsa dake cike da wata irin
nutsuwa ta halitta,ta waiwayo a hankali suka hada ido,sai ta saki murmushi tana dan
motsawa kadan

"Wa'alaikumussalam,ina kwana ya amin"

"Lafiya qalau queen,ki tashi lpy?"

"Lpy qalau....."

"Ma sha Allah,na godewa Allah da queen ta tashi lpy" murmushi ta sake,sai taji
kalamansa na mata kama dana bassam

"Zan samu ruwan dumi?" Tunda taji haka tasan daga motsa jiki ya dawo,shi yasa suk
safiya bata rabo da ruwan dumin saboda shi,matuqar tana kitchen din,tasan yana
shigowa zai nema

"Eh yaya" ta fada da sauri,tana juyawa zuwa inda ta ajjiye flask din ruwan zafi,ta
fara zuba masa,idanunsa na biye da ita.

Daidai yadda tasan zai iya sha ta zuba ta miqa masa,hannu biyu yasa ya
karba

"Na gode" murmushin da ya sake fidda dimple dinta tayi,tana jin kunya ta masa abu
ya gode mata.

Ta zaci fita zaiyi a kitchen din,amma sai taga yaci gaba jingina da
qofar,yana kurban ruwan yana binta da kallo,yana monitoring duk wani motsinta,wutar
qaunarta tana sake ruruwa cikin ransa,yana jin cewa lokaci kadan ya rage komai yazo
qarshe,banda ma delay da ya samu naci gaban karatunsa yadda yaso,da tuni zuwa yanzu
komai yayi nisa,saboda ya riga ya tsara ci gaba da karatun iman din a
gidansa,hankalinsa sai yafi nutsuwa da hakan

"Akwai wani abune yaya?" Ta tambayeshi cikin jin kunya da kuma nauyinsa,miskilin
murmushinsan nan mai cike da nutsuwa da wata izza izza ya sake,ya tashi daga
jinginar da yayi ya tako zuwa kitchen din,ya dora mata cup din kusa da ita

"Babu komai.....kawai ina kallom queen dita yadda take qara girma kullum tana zama
'yar budurwa"

"Kai yaaya" ta fada da sauri tana sunne fuska,shi kuma ya saki 'yar qaramar dariya
mai sauti kadan,ya taka ya fita a kitchen din.

Wunin ranar gaba daya bassam bai barta ta huta ba,kowanne motsi nashi sai
ya gaya mata ga abinda yakeyi,duk wani schedules nasa daga safiya zuwa dare tsaf
sai data sani,tamkar tare suke aiwatar da komai.

Ko wajen kamun surayya haka tayita fama da saqonninsa,yayin da munira ta


hanata sakat da zancansa,batasan ya akayi ba sai ji tayi qawayenta sun fara
tsokanarta da MRS BASSAM,kowacce a cikinsu cewa take

"Gaskiya ba qaramar sa'a kika taka ba,yaro ne matashin saurayi da jini ke zagayawa
a jikinsa,yaro ne da kudi amma hausawa sukance abokin tafiyar manya, friend dina ne
a insta,kije kiga yadda 'yammata ke rushing a kansa,daya daga cikin qawayensu ta
fiddo wayarta,ta shiga account dinsa na Instagram ta buda mata hotunansa ta miqa
mata.

Ta jima riqe da wayar a hannunta tana bin duk wani abu nashi daya dora a
can,ta yadda da duk abinda suka fada din,daga kan hotunansa dake kan shafin nasa
zakasan ba qananun kudi yake riqewa ba,kowannw hoto sutturu na alfarma ne a
jikinsa,rabu da matan social media da kyakkyawan namiji,tarin followers ne dashi
jingim maza da mata,abun ba'a cewa komai,kowanne hoto nasa ko wata magana da
zaiyi,zaka tadda tarin comments da likes rututu a qasanta,ta sake gyara zama tana
bin wallafar tasa.

Ba qarya bane,komai yaji tattare da bassam din,ta sauke ajiyar zuciya tana
sakin murmushi sanda wata 'yar ajinsu da ba wani magana suke da ita can can ba ta
shigo tana tsokanarta itama da mrs bassam

"Ya hadu guy din,bazan boye miki ba,nayi iya qoqarin na sameshi,to amma nasan ni ba
type dinsa bace,shi din sai kyawawa dama irinku,ina tayaki murna gaskiya iman"
murmushi kawai iman din ta bita dashi tana sake maida idanunta kan fuskar bassam.
Kwana biyu sukayi suna casar biki,tana zaune qawayenta nata liqi wa
amarya,saboda tasan ita din bata da kudin da zatayi liqin,sai daga bisani ta bude
jakarta dauko wayarta don duba lokaci,batason ta sake dare kamar na rannan idanunta
suka sauka kan kudin da bassam din ya bata,bata taba komai ba a ciki banda kudin
transport datayi musu ita da qawayenta,saita zari masu yawa a ciki,itama ta isa
saman stage t fara liqawa ango da amarya,take taji kanta daidai da sauran qawayenta
dake wajen,suka dauki ihun sai mrs bassam,abinka da zuciya da kuma aikin dan
adamtaka,sai taji kata yana fasuwa a hankali,sannu sannu sai datayi liqi me yawa da
ya sanya mc kama sunanta sannan ta sauka ta kona gurin zamanta,cin maganinta ya
sanya samari da yawa dakeson kawo mata caffa suka kasa qarasowa inda take.

********Washegari**********
Wunin sakina,ranar ne kuma za'a kaita,saidai dukkaninsu basuje ba sai
yammaci,dukka qawayen suka hadu,cikin daya daga cikin lafayoyinta da bata taba
sanyawa ba ta shirya kanta,duk tafisu tsada shi yasa ta zabi ta sanyata,milk color
ce me haske,sai adon gold a jiki,takalmin qafarta me tsini ne kuma mai tsinin
dunduniya,ta ciki wani lace ta sanya mara nauyi,wanda ya amin yayi mata dinkin
straight skeet da riga me dogon hanu,ta tara gashinta tayi masa nadin alkaki ta
qasan daurinta samfurin ture kaga tsiya.

Fadin kyan da tayi a lokacin bata bakine,saika rantse da Allah daga gidan
wasu hamshaqan ta fito,saboda kulawa da take samu gami da sutura me kyau,kowa kaffa
kaffa da dama dama da ita yake cikin qawayenta,abinda ta lura dashi ya fara faruwa
tun sanda munira ta shaida musu bassam shine masoyinta

"Komai yaji,wanka iya wanka,amma wallahi kika fito da wayar hannunki sai naji kamar
zan nutse" munira ta fada dai dai yadda iman dince kadai zata iya ji.

Sauke wayar tayi tana duban munira,wanda dama ta dauko wayarne saboda
jin qarar shigowar saqo,wanda kuma take da yaqinin ba daga kowa yake ba illa bassam

_"Kinyi kyau iya kyau baby.......,yanzu na shigo gida daga tafiya,amman bazan iya
daurewa ba.....sai nazo naga wannan kwalliyar beautyna"_ wannan shine saqon da taci
karo dashi,wanda mamaki ya kamata kan ta ina ya hangi adonta.

Maimakon ta bawa munira amsar maganarta saita buge da tambayarta

"Ya akayi bassam yaga kwalliyata?" Idanu munira ta wara

"Wallahi ban sani ba,shida baya nan yana abuja?"

"Ya dawo gida yanzu,kuma yana zancan zuwa ya ganni ba tare daya nemi address
ba,bari naga gudun ruwansa,ta ina zai lalubo ni?" Ta fada tana gyara zamanta gami
da gyara rufin lafayarta.

Murmushi munira ta saki


"Har yanzu bakisan waye bassam ba,mai kudin da idan yaso zai iya sanin duk wani
motsi naki,amma bari mu gani,da rabon muje gidan amarya a lafiyayyar mota" munira
ta fada cikin murna,batabi ta murnar munira ba,don tasan babu lallai yazo din,tunda
baisan ina suke ba,saita dan goce kadan ta jingina da kujerar dake daura da ita.

A hankali zuciyarta da qwaqwalwarta suka shiga tunani,suka shiga hasko


mata fuskokinsa data gani cikin hotunansa na ista cikin mabanbantan yanayi da shiga
kala daban daban,tarin tulin 'yammata daketa commenting akai,da kuma qoqarin jan
hankalinsa zuwa private chat,a hankali taji shauqin son ganin fuskar tasa na saukar
mata,saita lumshe idanunta tana bitar lausasan kalamansa da suka zame mata abokai
cikin kwanakin nan,dasu take kwana dasu take tashi,ta kuma hadasu da fuskarsa iya
shiga da tsari na jikinsa,take taji komai yayi mata dari bisa dari,sai ta lumshe
idanu tana sauraren hirarrakinsu,tare da kasa kunne taji xai kirata ko zai turo
saqo ya nema address?.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

16

Taji mamaki sosai sanda yake shaida mata yana qofar gidan,ta dubi munira
duban tuhuma,ta daga hannayenta sama alamun ba ruwana.

A matuqar darare fa shiga motar sanda ya bude mata da kansa ya mata izinin
shigar,shima saboda idanuwan yammata dake qofar gidan ana shirye shiryen daukar
amarya da sukayi musu caa kamar zasu cinyesu.

Nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana shafar qirjinsa

"Thank God,sai yau dana ganki sannan naji kamar an ciremin qaya, beauty,i really
missed you" kunya ce tadan saukar mata,taja lafayanta ta sake boye fuskarta ta
murmushi

"I liked it baby,inason kunyar nan taki,amma dai ya kamata adan fara rageta,a
nunamin soyayya ko?".

Hira yake janta da ita sosai cikin wani salo da yasan yana tafi da zukatan
'yammata,ya hada mata abubuwan sha da ci duka cikin motar saman dan wani abu da ake
janyowa me kama a table,saidai taqi taba komai saboda bata saba ba,ba zata iya cin
komai a gabansa ba,uwa uba kuma a takure take jinta,ga kalamansa daya cikata dasu
wadanda suka yiwa kanta nauyi,taketa jin kunyar yadda yake marairaice mata kamar
zai kwanta aka ta soshi don Allah,yayi alqawarin zai mallaka mata komai.

Abinda bai sani ba tuni ya fara barin burbushin wani abu a cikin
zuciyarta,ya sanya zuciyarta ta fara narkewa da kadan da kadan,hakanan tanajin wani
abu na tabata duk sanda ta kalleshi,ta kuma tabbata kowacce mace ma dole taji irin
wannan,saboda dan gayu ne iya gayu,wanda gayun ga hade da kyau da kuma ilimi
quruciya da kuma wadatar arziqi.

Kafewa yayi kan shi zai kaita gidan amarya,bazai barta tahau motar kowa
ba,nan kuwa ta samu qawayenta 'yan tayi,kowacce tace a motar itama zata,a haka suka
dibi mutum hudu daga cikinsu suka wuce.

Ko a hanya ma bai barta ba,hira yake mata qasa qasa cikin kalaman da zasu
iya wafce ko sace zuciyar kwacce irin mace,idam yaji tayi shuru cikin murya me kama
da rada zaice

"Uhmmm baby......baby kice wani abu mana,don Allah karki haukatani" wani abun ko
bataso saita amsa masa.

Da suka isa ma hanata fita yayi yaci gaba da dasa mata dashe me wuyar
cirewa,su sauran suka shige ciki,sai da yaga an ragu sannan ya mata tattaki har
qofar gidan ta shiga,sannan ya daw jikin motarsa ya jingina yana jiranta.

Tana shiga kamar dama jiranta sukeyi kowacce ta shiga ihu da kuma
zolayarta

"Ku keshan soyayyarku,amma nice nake sumewa" inji zee qawarsu

"Gaskiya gaskiya kika bar wannan guy din kin tafka asara,keee.....me tsada be
wallahi wannan,samun namijin da komai yaji a tare dashi kamarsa ai abune me wahalar
gaske,tabdi,gaskiya kin shiga sahun mata masu sa'a a duniya" daga daga cikinsu ta
sake fada

"Banda zaman amana ake ai ni zanyi wufff dashi" batasan ta jefa mata harara ba sai
da suka kwashe mata da dariya

"Almura,ashe ya fara sace zuciyar da akaqi bawa kowa dama". Haka suka hadu sukayita
yi mata cari.

Duk yadda taso ya barta ta samu abun hawa na haya ta koma gida yaqi ji bare
gani,duk ta gama tsurewa,yayi parking qofar wani babban store ya fita bayan yace
tazo su shiga tare amma taqiya.

A qalla kusa minti talatin ya barsu cikin motar ita da qawayen nata kafin
ya dawo,siyayya yayi mata mai ubansun yawa data sanya iman din tsurewa,ya dubi su
munira yace su shiga ciki su karbo sauran kayan duka nasu ne.

Sai da suka fita ya fidda wasu qananun leda guda biyu,daya daya bude wani
dan qaramin akwati ne me azabae kyau,zobe ne a ciki me bala'in kyau da daukar idanu
ya miqa mata

"Saka,so nake naga yadda zaiwa kyawawan hannuwanki kyau" ya fada yana murmshi,yadda
ya tsareta da kallo ya sanya dole ta saka zoben,ko don ta tsira daga kallon da yake
jifanta dashi

"Ma sha Allah,da dama da nayi kissing wannan kyawawan yatsu,Allah ya mallakamin su"
tsananin kunya ya hanata magana,sai kawai ta janye hannun nata ta boye cikin
mayafi.

Leda ta biyu still shima wani kwalin ne,wanda ke dauke da wata


santaleliyar wayar hannu,wanda ko ba'a gaya maka ba kasan cewa ba qaramar wayar
bace,bawai a girma na jiki ba,a'ah,kudaden da aka zuba kafin a mallaketa.

Miqa mata wayar yayi,ta janye hannunta taqi karba tana dubansa

"Na siyeta ne saboda ke,an saita komai da komai nata,akwai layi a ciki,na siyeshi
ne saboda ni kadai,nafison duk sanda na kiraki na sameki available" babu jan dogon
bayani tace mishi ba zata karba ba,yaji babu dadi har saman fuskarsa,saidai a nata
ganin haka shine daidai,don batasan inda zata sanya wayar ba.

Wannan dalili yasa ta kasa musanta masa sanda ya bata gift na ledar daya
loda mata siyayya,suna tafe munira na mata rakiya kamar kowanne lokaci,saidai
jikinta asabule yake

"Munira,nufar gidanmu fa kike da wadan nan kayan"

"Na sani,ki tsaya ki gani mana" ta bata amsa babu alamun damuwa a tattare da ita.

A bakin famfo suka samu inna tana tarar ruwa a buta,da alama bandaki
zata zagaya,ta daga kai tana amsa sallamarsu,cike da ladabi kamar kullum munira ta
gaida innar,ta amsa mata tana tambayarta mutanen gidan,ta soma gajiya da ganin
yarinyar tare da iman,bata fiyason mu'amalar iman din da baqin fuskar qawaye ba,duk
da dama silar bikin sakina ne ya kawota gidan.

"Inna wai kaya ne da sakina ta bayar a rabawa tsakaninmu qawayenta da


muka yi mata hidiman biki,shine nace ta ajjiye mana a wajenta,idan yaso in an tashi
sai a raba,sai iman din ke tsoron kada ki fada,shine nace bari na roqeki don Allah"

Idanu innar ta sauke kan ledar da muniran ke nuna mata,kowaccensu tayi


shuru tana jiran jin amsar da innan zata bayar,kamar ba zatae komai ba sannan ta
amsa

"Ba damuwa,amma karsu jima,banason ajiyar abinda ba naka ba"

"In sha Allahu inna" daga haka ta miqawa iman ledar,sukayi sallama ita ta juya ta
fice.

Cikin kwanakin gaba daya bassam ya sanya wuta wajen nema soyayyar iman
din,ya kuma ci galaba da gagarumar nasarar da bai taba kawowa kansa zai samu ba,ita
kanta iman din ta fada wani muguwar soyayya da bata taba tunanin zata fada ta
ba,sannu a hankali ta dinga ganin kyan da bassam da kuma sauran jama'a ke
kururutawa tata,ta kuma hango dacewar da sukayi da bassam din. Da kuma dacewarsa da
zamantowarsa miji a gareta.

Ta samu sakewa da dukka kaya da siyayyar bassam sanda taje maiduguri ta


dawo,saita sanya dukka kayan cikin tsarabar da yagana tayi mata,a zuwan ita ta bata
su,ta fidda fella fellan laces din ciki ta bawa al'ameen ya dinka mata.

Haka kawai yaji jikinsa yayi sanyi sanda ya bude laces din xai
dinka,tailor ne shi da yasan aikinsa,ya kuma san kudin kaya masu tarin yawa,a idanu
kawai akace ka yiwa lace din kudi kasan ba qarami bane bare aje ga ainihin
kudinsa,kusan guda uku ne kuma dukka haka suke.

Yagana 'yar kasuwa ce,tana kuma samu sosai da kasuwancinta,to amma kuma
laces din sunyi tsada da yawa,saidai daga bisani ya gargadi kansa,yakuma share
maganar cikin ransa,tunda ya riga ya aminta da wace iman din,rainonsa ce,ta kuma
tsotsi tarbiyya daga inda suka tsotsa,wato wajen inna da malam,ya budesu yayi mata
dinkuna masu kyau,da suka sanya ta dinga murna sanda ya kawo mata su,ta kuma
ajjiyesu,batayi amfani dasu ba sai da bikin murjana,daya 'yar ajintasu.

Ta fita sosai cikin qawayen nata,ta kuma fita daban,ta haska yadda ya
kamata,ta dinga jin kanta yana fasuwa cikin qawayenta,saidai tayi qoqari matuqa
wajen hana kanta jin izza ko girman kai.

Kasancewar bassam ma'abocin tafiye tafiye ne,baya nan akayo bikin


murjana,yaji babu dadi sosai,saboda yaso su kasance tare a lokacin,don har yanzu
abu na gaba da yake buri da buqata shine ta gabatar dashi a gidansu,ya samu 'yancin
zuwa ganinta kai tsaye a duk sanda yaso.

Saidai ita a nata bangaren cike take da tsoro da kuma fargaba,tsoron yadda
zatayi bayani wa malam inda ta sanshi,a inda suka hadu,da kuma yadda akai har suka
saba babu wanda ya sani,ina zatace ta samu lasisi ko kuma umarnin sauraronsa,uwa
uba kuma ta sani,burin ya ami tayi karatu,basuyi cewa zata gabatar da mijin aure a
dai dai wannan gabar da take aji biyar a makarantar secondary ba.

Duk da baizo ba amma tuni wayarsa ta samu baquncin hotunanta tsala tsala
ta hannun jakadiyarsa munira,wanda suka sake haukatashi tare da susutashi,suka kuma
sanyashi qara daura damara da cin burin kasancewa da iman din,da kuma maidata ta
zama matarsa kuma mallakinsa,ko me zaya kashe kuwa.

Tafiyar al'ameen zuwa jigawa garinsu ya sake qulla wani sabon kusanci da
kuma shafin soyayya tsakanin iman da bassam,saboda wayarsa daya bar mata aro kafin
ya dawo,ita kuma tayi amfani da wannan damar,ta bude account na Instagram WhatsApp
da Twitter,yadda zata samu damar ganin bassam din yadda ranta yakeso.

Ta kuwa kalleshin,babu wani hoto nasa data tsallake ba tare data masa
kyakkyawan kallo uku ko sama da haka ba,gayu iya gayu,kudi iya kudi ta gansu,gefe
guda kuma ga ilimi kamar yadda take da sha'awa,daya qyalla idanu ya sameta ta
WhatsApp kuwa kamar zaiyi me saboda murna,hakan ya sanya ta sake zama mayyar
waya,kullum tana manne da ita a daka,Allah Allah take ta gama abinda take ta dauki
wayarta su kasance tare.

Tuni inna ta fara lura da canje canjen dabi'u da kuma halaye tattare da
iman din,abinda yasa ranar da amin ya dawo daga qauye,suna tsakar gida,inna na
saman babbar tabarma,shi kuma yana kan kujera 'yar tsuguno yana bawa inna labarin
ci gaban da qauyensu keta samu,iman din na saman tabarma daban,ta tattara
hankalinta gaba daya saman wayar,abinda yaso jan hankalinsa kenan,duk da suna hira
da inna,amma kusan bayan kowanne minti sai ya daga kai ya kalleta,yasan cewa ba
haka suka saba da ita ba a lokaci irin wannan daya dawo daga tafiya,tana nuna
kewarta sosai a kanshi,abinci na musamman take masa,ta hada da ruwan zafi na wanka
takai masa,yana cin abincin tana damunsa da hirar abubuwan da suka faru bayan baya
nan,shima kuma tana tambayarsa abubuwan daya gani da sauye sauye da aka samu.

Miqewar da tayi yasa inna tace

"Ina zuwa?" Fuska tadan ya mutsa kadan

"Kwanciya zanyi inna,na gaji" idanu ta kafeta dashi

"Me yake damunki ne kwana biyu da kika koyi kwanciyar wuri?"

"Kawai inna,saboda makaranta ma,da shirye shiryen qualifying da mukeso mu fara" sam
maganar bata shigeta ba bare al'amin,wanda ya maida kansa ga qaramar keypad din
daya tafi da ita,yana serving station din da yake yawan sauraran labarai a cikinsu

"Wannan wayar ke daukan hankalinki iman......" Maganar da taso tadan tsoratata,amma


saita dake,saboda tasan halin innar da matuqar bin qwaqwaqwafi

"Games ne da yawa na dauko inna,kuma inajin dadin yi"

"Dole ki maida masa wayarsa,tunda tana neman canzaki" saita marairaice cikin tsoro
da faduwar gaban kada a yanzu yanzu innar tace ta miqa masa abarsa tunda ya
dawo,kafin kuwa ta gama tunanin nata abinda ta zata din ya afku,innar tace da ita

"Bashi wayarsa maza,tunda Allah ya dawo dashi lpy alhmdlh,aikin mori abinda kika
mora,dama kullum malam cikin fadan me yasa ya barta a hannunki yake"

"Don Allah inna........"


"Karki min magiya"

"Zan karba gobe inna,ki qyaleta" al'ameen ya shiga maganar,saboda ko waye mutum
komai qanqantarsa bazaiso irin wannan titsiyen ba,zuciyarsa kuma fes take kan iman
din,baya shakka ko zargin zata aikata wani abu ba dai dai ba,ko kuma ya saba da
tarbiyyan gidan,yadai bata uzuri kan cewa rashin sabo ne,da kuma daukin wayar tunda
ta jima tana sonta.
_________________________________

*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣maza


️ kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku
domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra
domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan
gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata
lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma
mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce
batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu
kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy
beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣ ️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama
duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using
mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi
zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear
bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya
bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left
behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍
👰🏻‍
♀️ ‍️
‍️Glow

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 17

_YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_

_THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_

_DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS?
YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS.
KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN
MU_

_KHUMRAHS_
_KULACCAMS_
_TURARUKAN WUTA_
_NA TSUGUNNO_
_NA KAYA_
_NA GIDAH_
_NA GASHI_

_NA WANKA_
_NA WANKI_
_NA MOPPING_

_AIR FRESHENER_
_CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_
_WARDROBE BALLS_
_SCENTED PEBBLES_

_ARABIAN OIL PERFUMES_


_HAIR SPRAY AND CREAM_
_DILKE AND HALWA SET_

_KABBASA_
_BURNERS_
_KASKO_
_TONGS_
_COAL IGNITERS_

_SKIN CARE PRODUCTs_


_OUR TURARE SAMPLE SETS_
_BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_
_KUJERAR TSUGUNNO_

_SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN
FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_

_MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_

_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_

_instagram:yerwaincense_and_more_*

_WhatsApp: 08095215215_
__________________________________

Washegari bai karba wayar ba kamar yadda yace din,saboda sabgoginsa na dinki
da kuma neman samun damar ci gaba da karatunsa da yaketa fafutuka,saidai a ranar
yanajin yadda inna ke mitar yadda iman din fa tashi a makare ta fara ayyukan
gida,wanda saboda quracewar lokaci bata samu gama aikin ba,inda daga qarshe ta
shirya ta wuce makarantar a makare,innan kuma ita ta qarasa sauran aikin da ya rage
din.

Washegari qarfe takwas saura minti biyar na safe ya fito a shirye zashi
su hadu da mutumin daketa masa fafutukar ganin ya samu tallafin karatu,ya gaida
inna dake dauraye flask din malam na kunu sannan ya tambayeta malam,tace yana qofar
gida,ganin takalman iman na makaranta yasa ya tambayi inna iman dun bata wuce
makarantar ba?

"Ina zata wuce,ta zama abunda ta zama,babu abinda ta iya sai kasala da sakalcin
banza" sai yaji a ransa indai waya ce take sanyata hakan bai kamata ya barta da ita
ba,don ko a jiya da daddare yana jin bambamin sadiqu kamar zai bugeta kan yace
fa.kiqo masa abinci ta shantake,dama kuma can sadiqun zafi gareshi,bai cika haquri
ba,don haka sai ya qarasa rumfar inna da kansa.

Sallamarsa da shigowarsa gaba daya yayita,tana zaune a qas tana saka


farar safarta,ta daga kai tana murmushi gami da amsa sallamar tasa,gabanta yadan
fadi da fari,saboda ganin da tayi ya danyi mata zubi da bassam saboda adon da yayi

"Ina kwana yaya?" Maimakon ya amsa mata sai ya maida mata da tambaya yana dan tsuke
fuska

"Me kike har yanzu baki tafi makaranta ba?"

"Yaya makara nayi wajwn tashi"


"Kin fara wasa da karatunki ko?" Saita girgiza kai

"Aah yaya,bacci ne......"


"Is ok,idan na dawo zan karbi wayata,ki sakamin a charge idan sun kawo wuta tayi
full" a sanyaye ta gyada kanta,sam batason ya karba wayar,saidai......wayarce ta
shiga ranta ko kuma alaqarta da bassam ce bataso ta yanke?.

Tare suka fita shi da ita,sai daya sanyata a abun hawa ta tafi sannan
ya tari nasa yahau,kasancewar ba hanya daya zasuyi ba.

Tun a makaranta ta turawa bassam saqon maida wayar,ta kuma goge duk
wani account da wani abu daya shafeshi,kama daga hotunansa daga tuttura mata,da
kuma saqonnin sms,sai data tabbatar bata bar komai akai ba sannan ta maida wayar
tata jaka,saidai rabi da rabi na karatun ranar ba shigarta yake ba,tana can ga
tunanin yadda zasuyi kewar juna ita da bassam din,ta saba chart dashi,kuma
yafi.mata dadi akan kiran ways,a chart dinne take sakewa sosai ta gaya masa
sirrikan zuciyarta.

*********Goma da rabi na daren ranar,wanda tayi dai dai da kwanaki biyu da amsar
wayar daga hannun iman din,har ya gama shirin kwanciya saboda sammakon da yakeson
yi gobe zuwa shagon dinki don kammala dikunan wasu amare,sai kuma ya miqe ya jawo
locker dinsa sake jikin katifarsa,ya dauko wayar ya sanyata a charge,saboda tunaqa
da yayi zai turawa wani mutum photon wasu takardu nasa.

Gefan katifar ya koma ya zauna yana jiran charge din yadan hau,saboda
bashi da tabbacin akwai charge akai,ya bata mintina goma sannan ya koma gaban
socket din ya zauna yakunna wayar,bayan ta daidaita ya shiga gallery dinsa ya fada
laluben hotunan takardun,tunda already yana dasu,saidai sama ko qasa ya rasasu,ya
dinga kaikawo bai gansu ba,har zai haqura ya sake sabbin dauka,duk da yasan ba
zasuyi kyan wadancan ba,saboda wadancan din anyi scanning dinsu a computer,sai kuma
ya tuna,ya wuce zuwa recycle bin na wayar.

Tun daga farko ya fara cin karo da hotunan da baisansu ba,bai kuma waye mai
su ba,sa'an nan baisan mutumin dake jikin hoton ba rututu masu yawan gaske.

Sosai kansa ya daure,ya dinga bin hotunan da kallo daya bayan


daya,mamaki na sake cikashi ta yadda hotunan suka shiga cikun wayarsa.

Sannu a hankali ya gangaro kan hotunan iman,iman dinsu dai,cikin salo na


gaye da kwalliya,hotunan da sukayi masifar kyau suka kuma fidda duk wani kyau da
Allah ya bata,duk da cewa shigarta bata bayyanar da tsiraicinta ba,amma kyan da
tayi cikun hoton,kyau ne da bai taba ganin tayi irinsa ba a zahiri.

Gaba daya qwaqwalwarsa so tayi ta tsaya da aikin yin kowanne tunani bare
ta bashi hint na abinda ke faruwa,saboda yadda ta dode gaba daya kamar bata taba
wani tunani ba,sai ya koma ya zauna dirshan sanda kwanyarsa ta taimakeshi ta tuna
masa cewa iman itace mutum ta qarshe da wayarsa ta jima a hannunta.

Wani mummunan faduwa gaban al'ameen yayi,har yaji kamar an samu wani abu an
buga masa akai,gudun zuciyarsa ya dadu sosai,sai ya sauka da sauri,ya koma binciken
wayar,bakinsa cike da addu'o'i cikin rudewa.
Duk inda ya shiga babu komai an share,manhajar WhatsApp itace abu na
qarshe daya duba,ba tare da yana da wani yaqini na samun wani abu ko hujja ba.

Ga mamakinsa yana shiga WhatsApp din ya bude sarai,da alamun account din
da akayi amfani dashi shine har yanzu kan wayar ba'a shareshi ba.

Suna da hoton dake kan number farko kuma qwaya daya dake kan account din
gaba daya ya sanyashu furta

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" dukkan wata dakiya da jarumta tasa ta fara


zagwanyewa lokacin da ya fara bin chart history din,yana karanta hirarrakin da
akayi cikin inbox din,wani irin gudu zuciyarsa taci gaba dayi kamar zata faso
qirjinsa ta fado waje,kunnuwansa sukayi dummm wanda ya dauka har tsakiyar kansa,a
hankali cikin wani salon sanda feeling na daina gane abinda ke kewaye dashi ya fara
kutsawa cikin jikinsa,yana aikawa kowanne sashe na jikinsa,a hankali ya daina gane
komai da kowa sai zallar tashin hankalin daya tsinci kansa a ciki,tashin hankalin
da yayi masa ba zata,tamkar zuwan ajali ga dan adam.

A hankali sai wayar ta gagara riquwa a hannunsa,ya zameta a hankali ya


saketa gefansa,ya koma ya zauna sosai yana son fahimtar da kansa abinda ke
faruwa,kamar bashi da idanunsa ya gani ba,saidai kuma wani sashe na kwanyarsa na
gaya masa,ba iman dinsa ba,ba iman dinsa bace,hala ta bada aron wayar itama ga
wani,idan ma ita dince ko dai wasa take?.

A sannan ji yayi babu abinda yake da buqata banda yaga iman a gabansa ya
tambayeta abinda ke faruwa,yana da burin idan ta tashi amsa masa ta amsa da cewa
wasa take,ba da gaske take ba. Ba tare da la'akari ko kuma duba da cewa dare ya
fara yi ba ya miqe da hanzar ya nufi qofar fita,yana so ya sadu da ainihin cikin
gidan.

Garam sukayi karo da sadiq dake shirin shigowa da ledar balangun da ya tafi
siyo musu,saboda dukkanins mutane ne masu son cin dadi a bakunansu,hakan bai basu
matsala ba,saboda kowannensu neman kudi yake tuquru

"Haba mana master......saurin me kake?,gani na dawo,wajen ne akwai layi,kasan ya


iya gashi" ja baya yayi yana duban sadiqun da yake mulmula goshinsa,wanda shi sam
bai ma damu da nasa goshin da ya buge ba,saboda rudanin da yake ciki,gaba daya ma
ya manta wai sadiq din ya tafi siyo musu nama.

Idanu sosai sadiqu ya zuba masa yana masa wani baqon kallo

"Amin.....lafiya kuwa?,wani abu ya faru ne bayan na fita?" Qafafunsa dake a mace


kamar lawashin da yasha rana ya fara janyewa da baya da baya,bayan hankalinsa a
sannan yakai kan agogo,ya kuma tabbatar bazai iya shiga cikin gidan a yanzu
ba,sabosa bai taba shiga din ba idan ba wani abu bane ya taso

"Babu komai" ya amsa ma sadiqu yana zubewa gefan katifarsa,tare da yin hobbasa na
ganin ya saisaita mood na fuskarshi

"Koda naji" sadiqun ya fada yana cire takalmansa ya dorasu saman abinda suke dora
takalma dake bakin qofar dakin sannan ya shigo,ya bude musu naman yana bawa amin
din labarai kamar yadda suka saba duk dare kafin su kwanta.

Idan yace yana gane abu daya da sadiqun ke fada to tabbas ya zabga qarya

"Ya baka cine?,wai anya lafiya kake kuwa?" Kalmar da sadiqun yace dashi kenan yana
rutsashi da ido,abinda yayi silar daya ringa miqa hannu ya a zaqular naman yana
hadiyewa ba tare da ya tsaya cikakkiyar taunawa ba bare ya gane wanne irin taste
gareshi,haka ya dinga tsaya masa a maqoshi kamar wanda ke cusa dan wake,abinda yayi
sanadiyyar qwarewarsa kenan yahau tari,wanda ya sarqafeshi sosai,sai da yasha ruwan
sanyin da sadiqu ya bashi sannan ya lafa,da wannan ya fake yaje ya kwanta,saboda
qirjinsa da ya dauki zafi,sadiq yace may be ko ulcer dinsa ce ta motsa kuma.

Tunda ya kwanta idanuwansa a rufe suke gam,ko qwaqwaran motsi baya qaunar
yaji a kusa dashi bare magana ko surutu,lokaci bayan lokaci yana bude idanunsa ya
sauke ga agogo,yana qididdigar mintunan da suke gabansu kafin wayewar gari.

Zuciya da tunaninsa sunkai sun komo,ya kuma rasa a wanne bigire zai
ajjiye tunani da zuciyarsa,karafkiya qaryata juna da sa'insa babu kalar wadda ba'a
samu ba tsakanin sashe biyu na zuciyar dake qirjinsa,wata zuciyar na rinjayar da
qaryar cewa ba iman bace,haka ba zata faru ba,yayin da wara zuciyar ke tabbatar
masa da iman dince,saidai ta aikata komai ne bisa rashin sani,koma meye ya riga ya
yankewa kansa hukunci kawo qarshen komai,koma meye zai faru ya faru,qirjinsa bashi
da qarfin daukar zuciyar da zata rasa iman haka cikin sauqi,saima ya korewa kansa
wannan tunanin da yake kallonsa a baqi kuma mummunar fata cikin rayuwarsa.

Dai dai lokacin da iman din take can kwance saman tata katifar a zahiri,a
badini kuma tayi matuqar yin nutso kuma me zurfi cikin kogin qaunar bassam,wanda ta
ara masa daqiqa masu dama yana sake karanta mata yadda qaunarta ta tashi zuciyarsa
a aiki,irin girma da kuma matsayin da take dashi,abinda ya sake sawa taji kanta ya
fasu,alfahari da samun bassam da kuma soyayyarsa ta shigeta,ta bude masa tata
soyayar sosai wadda ta narkar da ilahirin zuciyar bassam,ya kuma dauka mata
alqawura masu matuqar nauyi a mizani,girma kima da kuma martaba cikin duniyar
soyayya,wanda daga qarshe sukayi tarayya kan alqawari guda,duk rintsi.....duk
wuya.....suna tare,babu gudu kuma babu ja da baya,dukkan wanda ya sauka daga kai ko
kuma ya sauya,la'ana da kuma hukuncin cin amana yahau kansa.

Wannan kusan itace hira mafi dadi da sukayi da bassam a wajenta tsahon
tarayyarsu,domin kuwa ko bayan ya sauke wayar sun rabu kasa runtsawa tayi,murmushin
dake kan fuskarta cikun duhun dakin yaqi barin fuskarta,hirarraki muryarsa da gwala
gwalan kalamansa sukaqi barin qirji da zuciyarta,ta dinga tariyarsu tana jin wani
dadi qauna da shauqi yana sake kamata,zuciyarta jaririyar zuciya ce,wadda ta fara
soyayya ta zahiri a karon farko,don haka komai baqo ya kasance mata,sai daga bisani
fa samu baccin yayi awon gaba da ita,cike da mafarkan bassam,wanda a ciki har ya
zama miji a gareta.

Kwata kwata baccin da yayi tsahon daren dukansa bai wuce na awanni uku
ba,suma din a tsitstsinke,a kunnuwansa akayi kiran asubahi,yayi alwala suka fice
masallaci tare da sadiqu,wanda hakan al'adarsu ce,kuma acan suke tadda malam.

Miqewa sadiqu yayi ya dubeshi bayan an idar da sallar,wasuma har syn fara
watsewa

"Nikam yauma idan zaman azkar dinkan nan zakayi saidai mu hadu a gida,don wallahi
jiya kwata kwata bacci bai isheni ba" ya fada yana miqa

"Shikenan,saina taho" ya amsa masa yana sake maida kansa qasa,don bayason sadiq din
ya fahimci bai samu bacci ba.

Yana kallon sadiq ta qasan idanunsa har ya fice,hakanan yaji bazai iya
komawa cikin gidan ba,ya kintata wani lokaci ne da zai cimma iman,duk da cewa yau
tana da makaranta alhamis ce.

Cikin wani nishadi da walwala take zuba kunu da awarar data soya cikin
cup da plate don taci ya wuce makaranta,ta gama shirinta tsaf,kana duban fuakarta
zakasan wani nishadi takeji,bassam ya raya darenta ya kuma qawata mata safiyarta da
kyakkyawan saqon barka da safiya.

Ta juyo zata fito kenan yayi sallama bakin qofar kitchen din,idanunsu
suka shiga cikin na juna,sai ta hangi baqon yanayi tattare dashi,saidai bata kawo
komai ba cikin ranta ta zarce da gaisheshi,ya amsa mata yana nazarinta

"Akwai ruwan dumi?" Ya tambayeta yana jingina da qofar kitchen kamar yadda ya
saba,tsaiwarsa kwnan duk sanda zai karba ruwan,duk da yawanci a gajiye yake shigowa
dama saboda exercise da yakeyi,sabanin yau,da babu execise din da ya iya
fita,saidai zuciyarsa a jigace take qwarai,wanda hakan yayi tasiri har zuwa gangar
jikinsa,ya matsu ya kuma damu ya fidda abinda yake zuciyarsa da ransa komai da
komai ma ya huta

"Yaaya...gashi" ya tsinci muryarta tana masa magana,da alama tun daxu ta zuba ta
miqa masa,sai ya karba ya fara kurba a hankali,bayan ya matsa mata hanya

"Idan kin gama ki dauko litattafanki ina jiranki" har tadan dakata sai kuma ta amsa
da to tayi gaba,kasancewar ta saba lokaci lokaci yakan rakata,koda ba har makaranta
ba to xai kaita bakin titi,saidai a kwanakin nan abun yaja baya.

*_LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_


_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI
SE A TUNTUBE  MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa


1487616276
Access bank

Number shaidar biya👇🏼


👇

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261

YAN NIJAR 👇

+227 95 16 61 77

Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number
______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.


TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 18

Jerawa yayi da ita kafada da kafada sanda suke takawa a hankali,idanunsa


qur saman hanya,zuciyarsa na taraddadi da fargabar abubuwan da zayaji.

Satar kallonsa ta sakeyi a karo na barkatai,ganin sun nufi hanyar


makarantar tasu kai tsaye ba tare da ya tsaidan mata da abun hawa ba

"Yaya,a qafa zumuje?,ka manta?,kawai dan nisa fa?,naga munbi ta layin nan" lokaci
ya kalla a hankali kafin ya sauke hannunsa ya kuma sake rage speed na tafiyar,ya
zaro wayar dake aljihun hagunsa ya miqawa iman idanunsa cikin nata

"Karbi ki dubamin" cikin rashin fahimta ta miqa hannu ta karba wayar,ta kuma bude
kamar yadda ya umarceta.

Abinda ta gani din shi ya birkita kwanyarta cikin sakanni,duk da tasan da


wanzuwarsa,amma bata tsammaci yaci gaba da wanzuwa cikin wayar ba,take rudewa suka
bayyanar mata,saidai tayi qoqarin bawa kanta dakiya da qwarin gwiwa,tunda babu wani
na sabo ko rashin tarbiyya kaf cikin charts dinsu,bugu da qari ma tana jin lokaci
yayi da zata bayyanawa duniya bassam dinta

"Waye wannan?" Amin ya fada yana kallon wayar kafin ya maida dubansa ga fuskar
iman. Har cikin ranta taji tambayar kamar tazo mata a dai dai,don saboda dama ya
amin dinne kawai take tunanin zatayi maganar dashi,ya kuma fuskanceta har ya kai
zancan gaban malam,to saidai shima duk sanda ta yunqura zata yi masa maganar sai
taji ya mata wani mugun kwarjini,amma yanzun komai zaizo da sauqi.

Sunne kai tayi irin na alamun jin kunya

"Saurayina ne ya amin"ta fada tana rufe fuskarta da tafin hannu.

Hasbunallahu wa ni'imal wakil,ita yayi qoqarin zuqowa saga mafitar


maganarsa zuwa saman harshensa,sannan yayi azamar dafe wata bishiya da tafiyarsu ta
ratso dasu ta gefanta don neman agajin tsaiwa sa qafafunsa.

Kasancewar sautin addu'ar tashi bai samu fitowa ba illa maqalewa da yayi
saman harshensa.......wannan ya sanya sam batasan me yake faruwa ba,cikin wani irin
tashin hankali yaci gaba da kallon iman duk da fuskarta a rufe take da hannunta

"Iman......ina alqawarin da kika yimin ba zakiyi soyayya da kowa ba?,ina alqawarin


da kika yimin na bani damar zabar miki miji na gari?" Yanayinta ya sauya kadan
cikin boyayyar fuskarts,duk da bata kalli tasa fuskar ba amma ta fuskanci sauyun
sauti sosai fiye dana dazu

"Yaaya.....kayi haquri,na saba maka wannan alqawarin,amma shima ina da tabbacin


irin mijin da kakeson zabarmin dinne,kuma zaka yaba da zabina yaya,ya shiga
rayuwarta ne katsam" qara dafe bishiyar yayi da kyau saboda jin jiri na dibansa da
yayi,babu sauran kwana kwana ko boye boye

"Iman......nine mijin da na yi miki tanadi,ni ya amin dinki nine mijin dana zaba na
kuma killace kaina saboda ke,iman.....ni amin nike sonki iman,zuciyata ta girma da
sonki ta kuma rayu da sonki tsahon shekaru masu yawa". Kamar wadda aka jibgawa wani
abu a saman kanta haka taji,ta yaye fuskarta da sauri da kuma hanzari don tana da
buqatar tabbatarwa kanta ba shirin film akeyi a wajen ba,tana son ta gani da gaske
ya amin ne?,kuma ba wasa yake mata ba?.

Saidai kuma.....kallon farko ta karanci zallar gaskiyar dake fitowa tun


daga zuciyarsas shimfide saman fuskarsa muraran,abinda ya sake firgitata,ta danyi
baya kadan tana jin tashin hankali yana rufto mata,ta yaya haka zata faru?,ta yaya
zaice wai da sonta ya rayu?,me yasa bai gaya mata tun da can ba sai a yanzu data
riga tayi alqawari da wani,data riga tayi nisan kiwo cikin duniyar soyayyar
wani?,ta yaya zata gane yaren da yakeson koya mata bayan bashi ta iya ba?,meye yake
shirin faruwa?.

"Ya ameen,da gaske kake?,nice fa iman dinka?"kai ya gyada mata yana


kallon tsakiyar idanunta kai tsaye

"Na sani,iman dita ce,shi yasa nake gaya mata halin da zuciyata take ciki,ina sonki
iman......burina kuma na aureki,in fact,malam ya jima da bani ke!" Maganarsa ta
qarshe saura kadannta wargaza kwanyarta

"Me?!" Ta furta da wani sauti me kauri da amo

"Eh,malam ya bani ke tuntuni" ya fada yana gyada mata kai tare da tabbatar mata.

Kanta ta soma girgizawa,sam sam kwanyarta ba zata dauki wannan batun


ba,wacce iriyar magana ce haka mara dadin saurare?,ta yaya zaizo mata da wannan
maganar?,tsahon zamansu da rayuwar da sukayi a muhalli guda bai taba tunkararta da
maganar ba sai yanzu?sai daidai wannan lokacin?.

Ci gaba tayi da gigixa kanta tana koma da baya,kafin ta juya cikin wani
irin hanzari ta nufi hanyar gida,ya miqe da sauri yabi bayanta yana qwala mata
kira,saidai ko waiwayawa batayi ba bare ta saurareshi,har ya fara rufa mata
baya,sai kuma ya tsaya cak bayan ya yiwa kansa birki ya kuma gayawa kansa gaskiya
kan bai kamata ya bita ba din,jama'a suna kallonsu,sannan kuma gida zata shiga a
hakan,shigarsu tare cikin wannan yanayin su duka biyun bai kamata ba,kuma yana biye
da ita,sai ya dawo a hankali cikin wata kasala da mutuwar jiki ta gaske,ya duqa ya
dauki jakarta data sulale a wajen ya soma takawa a hankali shima zuwa hanyar
gidan,kwanyarsa na juyawa,tunaninsa yana hautsinewa,yaya iman ta dauki maganar?,me
ya sanyata firgicewa haka?,wadan nan sune tambayoyin da ya dinga maimaitawa kansa
su wanda bashi da amsoshinsu.

A hanya komai kama kamar iman bai gani ba,hakan ya alamta masa ta jima da
isa gida kenan?,wannan yasa daya dawo shima bai shiga gidan ba,dakinsu ya wuce kai
tsaye,ya zame saman katifa yayi rub a ciki,bayajin akwai wani abu da zai iya
tabukawa,saboa ya jin kamar qafafunsa ba zasu iya daukar gangar jikinsa ba.

Yadda batasan a gida ya wuni ba itama shima baisan tana kwance cikin
dakinsu ba,dukkaninsu wani irin yini sukayi mai wahala qunci da kuma takura,tunanin
dake qirjin kowannensu ya nauyayar masa,wani irin yanayi mara dadi na zulumi da
kuma fargaba,fargabar data kasance mai tarin banbamci a tsakanin iman da ameen.

Sai magariba da ya shiga cikin gidan inna keta mamakin dama yana
ciki?,saboda sadiqu nada aiki da yawa a ranar a garejinsu,abinda ya sanyashi fitar
wuri sannan kuma har zuwa lokacin bai shigo ba

"Banajin dadi ne inna,kuma banaso na gaya miki nasan zakiyita damuwa ne" amsar daya
bata kenan

"Ikon Allah,don iman bata jin dadine itama,nasan da dole zata bincikoka,nayi mamaki
nima da banji motsinka ba ashe jikinne.....don Allah aminu ka daina zama da ciwo
baka fada,babu kyau,a qalla ya kamata ko leqaka a dinga yi ko ana ganin yanayin
jikin naka,baka zauna a daki kai kadai ba kamar babu kowa cikin gidan uhmmm"

"In sha Allah inna,kiyi haquri" ta amsa masa sa babu komai,yanayin sanyi da
yanayinsa ya koma saita azashi da cewa don bayajin dadin jikinsa ne,daga bakin
qofar dakin iman din ya tsaya yayi mata sannu saboda wanzuwar inna a wajen kada
taga ya wuce,ya jiyota can qasa sosai ta amsa masa,sai ya sake wucewa zuwa dakinsu.

********. ****. ********

Munira ce rike gam da hannun iman din sanda suke zagayawa zuwa bayan
ajujuwansu,bata sakar mata hannu ba sai da suka dangana saman wani dan tudu wanda
asalinsa tarin qasa ne saboda jimawa a wajen ya koma kamar dutse.

"Tunda kika shigo na tabbatar ba lafiya ba,gashi jiya na dinga zura idanu
an bani saqo na baki amma baki shigo ba" munira ta fada tana duban iman dake zaune
ta rungume qafafuwanta a qirjinta.

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke,a.hankali ta fara magana cikin sautin da


sai ka dauka wani babban ciwo tayi

"Rayuwata na neman fadawa garari munira......na shiga rudani me zurfi daga jiya
zuwa yau,irin wanda ban taba hasasowa ba" matse fuska munira tayi tare da sake
tattara hankalinta waje daya

"Rudanin me?,me ya faru?rabuwa kukayi da bassam?" Kai ta girgiza

"Muna gab da rabuwarne wala'alla"

"Karki gayamin wannan mummunar kalmar mana iman,kina haukane?,bassam din zaki bari
ya subuce miki?"

"Munira.....ya ameen ke sona" saita firfitar da idanu waje

"Yayannaki da kuke ciki daya?,wanne irin hauka ne wannan?"

"Ba ciki daya muke ba,riqonshi inna tayi,kuma almajirin malam ne,dalibinsa ne" sak
munira ta tsaya tana kallon iman,tarin mamaki ne fal saman fuskarta,sai iman ta
gyara zama ta gaya mata duk yadda akayi.

Fuska munira ta yatsina

"To don yana sonki shine me?,kawai saiki zauna a rabaki da wanda zuciyarki
takeso?,wanda zai zama hutun rayuwa a gareki matuqar kika aureshi,karki
manta,'yammatan wannan zamanin SHI SUKE BURI" Kai iman ta girgiza tana jin tashin
hankali na sake ninkuwa cikin ranta

"Munira.....bakisan halin malam ba,na tabbatar baya magana ta tashi,kuma wallahi


wallahi indai ya ameen ya tabbata yana sona malam ya sake fahimtar hakan babu wanda
ya isa ya hanashi bashi ni duk duniya" murmushi munira ta saki,sai ta matso kusa da
iman din sosai

"Kinga,ayi me baro baro kawai a wuce wajen......ki bude bakinki malama,karki cuci
kanki,ki gayawa kowa kina son bassam,kuma shi kike da burin aura,ki gayawa ameen
bassam kikeso kanki tsaye,idan kikace zaki tsaya kunya ko kara,to wallahi kina ji
kina gani za'ayi babu ke,ni dama na dade ina zargin sonki yake,shi yasa ya tajura
rahuwarki ya hanaki sakewa kamar kowacce diya,abu daya ne ya ciremin zargina da
kika gayamin cewa yayanki ne.....amma Allah na tuba,me na sama yaci ballantana ya
baiwa na qasa,ki duba surarki da kyau....banda ma yiwa kai kasada me zaisa yace
yana sonki a irin wannan lokacin da arziqi ya qwala muku kira?,me yake dashi da zai
riqeki iman?,ina cewa makarantar da zaici gaba ma kokawa suke shi da ita da
fafutukar ganin ya sameta,idan kika auri bassam.....bashi kansa ba,hatta da
abokansa dana kusa dashi.....danginsa na qauye rankatakaf sun huta,amma shikenan
saboda ya dankwafe rayuwarki sai yace wai yana sonki saboda cuta da mugunta,yana da
kyau yana da kwarjini na daukar hankali,amma magana ta domin Allah bashi da
sinadarin riqe mace kamarki.......da dinki zaici da ke?,koda karatun da bashi da
tabbacin samunsa?ke rabu da gaibu fa ki kama dahir,kuma shima matuqar yana sonki ai
zaiso ci gabanki ne,bawai ya aureki ku dankwafe waje daya babu ci gaba ba" ire iren
maganganun munira kenan data ci gaba dayi,kamar zata ari baki.

Iman tana saurarenta tsaf,ita ba wannan bace damuwarta,babbar damuwarta


soyayyar bassam da zuciyarta ta saba da ita,kuma batajin zata iya jurewa rasashi.

"Gashi inji bassam......,jiya ya aiko yaranshi ya kawo min da daddare


saboda ya kikkiraki jiyan bai jiki ba,ya damu sosai,shi kansa yaron nasa idan kinga
motar da yake hawa ko......hmmmm" tayi zancan sanda take fidda waya sabuwa dal tana
miqa mata.

Wannan karon batayi musun karba ba,jiki a sanyaye ta amsa,saboda tana jin
wannab shine lokaci mafi dacewa da su kasance tare da juna da bassam din.

Nan da nan labari wayar ya karade cikin qawaye da classmates dinta,tanajin


mazan ajin suna fadan kudin wayar,mamaki ya kamata,ta jujjuya wayar a hannunta tana
mamaki yadda mutum zai iya narka kudi kamar haka ya siya waya qwaya daya jal.[7/19,
10:02 PM] Mummyn Yara: 19

Cikin jiki zuciya ruhi da kuma idanu ya tabbatar akwai matsala,irin matsalar
da duk sanda zuciyarsa ta gaya masa akwaita yana qoqarin qaryata kansa da
tunaninsa,komai da komai din na iman ya canza kuma ace ya janye daga muhalli da
bigiren da ya santa ada,duk dacewa ba mazaunin gida bane shi.....amma kuma gaba
daya iman din ta yiwa idaniyarsa qaura,ya daina ganinta,walau da safe koda
dare,tamkar wasan buya ta tsiro dashi a tsakaninsu a tsanake,yasha ganin wucewarta
wuf a duk sanda ta karanci motsinsa a waje ki tahowarsa izuwa wajen.

Iman din dake tiri tiri da dukkan wani abu da ya shafeshi a yanxu ba ita
bace,iman din dako yaushe take shiga kokwanto da wasi wasi duk sanda wasu awanni
suka shude bataji motsinsa ko gilmawarsa ba,dukka a yanzu sun kau,kwanaki biyar din
da suka biyo bayan maganarsu bai sake sanyata a idanunsa ba,koda muryarta zai iya
cewa baifi sau uku ya jiyota ba tsayin kwanakin.

Wata iriyar rayuwa yake a kwanakin wadda shi kansa baxaice ga inda ta
dosa ba,saboda rashin gane ainihin abinda iman ke nufi,ina tasa gaba?,meye
alqiblarta?, Duka bai sani ba,tarin damuwar dake danqare cikin zuciyarsa ta bayyana
cikin ayyukansa na yau da kullum,ada idan gana dinka riga goma a wuni daya,a yanzu
biyu yake iyayi,sauran duka tunani ya cinyeshi.

_wannan kenan_

K'arfe takwas na dare bayan kammala sallar isha'i ya shigo gidan,wanda


direct daga masallaci gidan ya nufo,tunda dama can shi ba ma'abocin zaman majalissa
bane,koda ya zauna din baya wuce minti goma zuwa ashirin zai sallama dasu ya wuto
gida yaci gaba da sabgoginsa.

Sanda yake sanyo kai cikin gidan tare da sallama a bakisa yaga kamar
wani abu ya gifta wuf zuwa daki,inna ta daga idanunta tabi iman da kallo wadda ita
dince tayi hakan,cikin mamaki tana amsa sallamar amin din,ta fuskanci wasu sauye
sauye sosai game da alaqar ameen din da iman,yau dinne kuma idanunta suka ganeta
real,zuciyarta tadan tsinke kadan,tana fatan kada ubangiji ya sanya wata matsala ce
ta afku tsakaninsu komai qanqantarta,don basa fatan hakan,saboda ko a jiya sun jima
ita da malam suna tattauna batu akan aminu da iman din

"Barka da dare inna" amin ya fada cikin murmushin sannan me sanyi da


akullum yake fuskantar innar dashi,fuskantar da da zai yiwa mahaifiyarsa cikin
girmama a tarin ladabi.

Cikin nata salon kulawar da kuma nuna qauna ta sakar masa fara'a

"Yauwa aminullahi,sannu da qoqari,an samu shigowa?" Ta qarashe maganar tana


tura masa kujerar tsuguno,sai ya zame ya zauna kan shimfidar abun sallar da iman ta
tashi yanzu akai,ya zauna sosai akai ya tanqwashe qafafunsa yana gaidata kamar
wanda ba tare suke gida daya ba.

Cikin kulawa ta amsa masa,sai 'yar hira ta shigo kan wajen aikin nasu,aduk
sanda wata matsala ko ci gaba suka sameshi kam aikinsa,da ita yake shawara,da ita
yake tattaunawa,su kashe su binne,inna takanji matsalarsa dari yayarsa dake jigawa
bataji guda daya ba.

Duk wannan hirar fiye da rabin hankalin inna yana kan dakin iman,tana
zuba idanu tare sa saka ran ganin fitowar iman,tana fara'a gamida nuna kulawa dayi
masa sannu da zuwa,ta kuma debo abincinsa ta gabatar masa kamar yadda suka
saba,sabanin haka shuru kakeji.

Hankalin inna ya dan daga kan,ranta kuma sosu,ta kasa jurewa sai data
daga murya cikin sauti mai qarfi ta qwalawa iman din kira.

Kai tsaye kuwa kiran ya isa kunnuwan iman,wadda ke kwance rub da ciki
kan katifarta,ta nutsa cikin duniyar chart da bassam,wanda har bata iya jin hirar
dake gudana tsakanin inna da bassam dake zaune daga qofar dakinta.

Da hanzari ta danna wayar qasan pillow,tunda dama babu wanda yasan da zaman
wayar,koda yaushe kuma a silent take,ta tashi da wani irin reaction na rashin
gaskiya ta fito waje tana gyara daurin dankwalinta.

Tamkar batasan ya shigo gidan ba,tamkar ba dalilin shigowarsa yasa tabar


tsakar gidan ba ta gaidashi,duba daya yayi mata yasan lallai mawuyacine abinda
zuciyarsa keta gujewa ba shine ya afku ba,iman din dake marmarinsa a yau ita ke
gaidashi babu wani doki babu komai,fara'a da ya santa da ita babu kaso casa'in
cikin dari.

Da wani mugun bin qwaqwafi inna ke karantarsu gaba dayansu,saita danne


tace da iman

"Wanne irin sakarcine wannan,ki wuce ki dauko masa abincinsa,kin kama kin wani qule
daki?,haka kawai kin koyi nunqufurcin banza da wofi na zaman daka?,inacewa baki
jima da fitowa ba?,me kika koma yi a ciki ko wutar nepa babu?" Gabanta ya fadi
saboda tasan halin inna sarai,tana matuqar qoqari wajen kiyayewa duk wani abu da
zaisa inna ta zargi akwai wata a qasa amma a banza,mutum ce ita me mugun kula da
kuma tsantseni

"Inna kayana na fito dasu na manta zan gyara na barsu a waje" ta fada cikin
marairaicewa

"Saiki wuce ki debo masa abincin" ta sake maimaitawa tana miqe qafafunta da sukeso
su fara mata ciwo,dama kwana biyun daurewa kawai takeyi

"Zan fara watsa ruwa,kamar nan da minti ashirin sai a kawomin"


"To shikenan....,idan zaki hada masa ga kwadon xogale can ragowar na malam
da yayi buda baki dashi saiki hada masa dashi" da to ta amsa tana nufar
kitchen,saidai ranta a bace yake sosai,kawai saboda amin din innan ta sakata a gaba
take mata fada,yadda innar ke nuna masa kula da tattalinsa koda yaushe ko ya sadiqu
bata yi masa haka,abincinma sai an wani hada masa kulli yaumin kamar wani
magidanci,rana dai daine zai shiga kitchen ya dauko da kansa yaci.

Tunda take dashi bata taba ganin aibun hakan ba sai yau,sai yau da
zuciyarta ta karkata zuwa wani hanya daban ba wadda a baya take kai ba.

Kwata kwata bata qaunar su kebe da amin din baki daya,wannan shine babban
dalilin da haduwarsu cikin gidan ma ta haramatata,saboda batason ya sake dauko.mata
magana makamanciyar wadda yayi mata a rannan,shurunsa da rashin nemanta da baiyi ba
shima a kwanakin ya sauqaqa mata dukkan wani tsoro da kuma zulumi nata,koda bata
buda baki tayi magana ba tana kyautata zaton ya zuwa yanzu ya gane inda ta dosa.

Tana hada abincin tana mita qasan ranta,fuskarta a hade,hakanan bakinta


yana ta motsawa,tasan yayi hakkanne kawai don ya samu damar magana da ita,kuma
batajin zata sake bashi wannan damar.

Data gama hadawar saita koma daki dauko hijabinta,hasken wayarta dake
alamta shigowat saqinnin bassam ya zaunar da ita,ta saki murmushi sanda ta fara bin
saqonnin nasa,saita manta da aikin da zatayi ta shiga maida masa amsa.

Ya jima tsaye gaban mudubi gana sharce kansa yana kuma duban
fuskarsa,kwanyarsa na masa bitar tarin maganganun dake cunkushe daga zuciyarsa zuwa
bakinsa,mamakin yadda komai yake qoqarin sauyawa cikin qanqanin lokaci yakeyi.

Cikin jallabiyya ya shirya bayan ya feshe jikinsa da turarensa kamar


yadda ya saba,hatta da boxer na ciki bai tsira ba,sai ya koma saman kujerar dakin
ya zauna yana duba lokaci,tayi delay sosai,amma sai ya bata uzuri,kamar hadda hali
da dabi'ansa yake,mutum ne shi mai yawan bada uzuri,zaiyi wuya karon farko ya
kamaka da laifi,sai ya dora hannunsa saman sumarsa da har yanzu danshin ruwan dake
jikinta bai bushe ba,yana shafata a hankali daga gaba zuwa baya,yana jin yadda
damuwa ke sandar jiki da zuciyarsa.

Wayarsa ya maida gefe ya ajjiye yana furzar sa zazzafar iska daga bakinsa
sanda yayi kiran layinta yaji busy,wani abu ya tsaya masa a maqoshi ya kuma tokare
masa maqogaro,a hankali yaci gaba da shafar sumarsa yana lallashin kansa da
kansa,sai ya lumshe idanunsa yana sake fitar da iska mai tsaho wai ko zata rage
masa nauyin da yakeji cikin qirjinsa.

Kiran wayarsa da akayi shi ya dauke masa hankali,ya kuma zuqe yawan
mintunan data dauka bata kawo masa abincin ba.

"To ba damuwa,bari zan kira idan na duba" amsar da ya bayar kenan sanda yaji
motsinta,da kuma sallamarta a bakin qofa cikin zazzaqar muryarta,ya bata izinin
shigowa yana qoqarin sanya wayarsa a silent,wanda kafin ya gama ya daga kansa harta
ajjiye abincin ta juya

"Iman" ya qwala mata kira,ta waiwayo tana jin ba dadi a zuciyarta kan tsaidatan da
yayi

"Zo ki zauna......magana zamuyi"

"Yanzu zan dawo" ta amsa masa a taqaice,saiya gyada kai lumsassun idanunsa suna
zube saman fuskarta,yana ganin sauyi muraran daga iman dinsa zuwa wata iman din ta
daban,ta juya da hanzarinta ta fice,cikin ranta tana jin saidai suyi maganar da
wata amma ba ita iman din ba.

Amma kuma tana saka qafarta a tsakar gida inna dake fitowa daga daki
ambaci sunanta

"Wai wanne irin baqin hali kika koyo imani?,wannan zobon da kika ajjiye ya gama
hada sanyinsa babu mesha ba zaki kai masa ba,bawan Allah azumi yakai fa?" Kamar
zata dora hannu aka ta zunduma ihu haka ta dauki jug din zobon ta nufi soron
dashi,bata taba jin inama tana da qanne ba irin yau,da babu shakka saidai fa ta
tura daya daga cikinsu ta samu ta dawo,domin har a jikinta tana jin bassam nacan
yana jiranta,haka fa tura qofar dakin ranta a bace sallamarta a ciki,daidai sannan
nepa suka kawo wuta,hasken farin qwan lantarkin dake dakin ya mamaye ko ina,ya kuma
taimakawa ameen qwarai wajen ganin yanayin fuskar iman din.

Can nesa ta samu ta zauna bayan ta dire masa jug din,kanta a qasa kamar
wata surukarta tace gani.

Baiko motsa ba sabda tayi maganar,sai kafeta da yayi da lumsassun


idanunsa na wasu daqiqu,sannan ya miqe cikin nutsuwar nan tasa,ya taka a hankali ya
rage tazarar dake tsakaninsu,a hankali ya zame saman carfet ya zauna saitinta,ta
yadda zasu iya ganin juna yadda ya dace.

Dakakkiyar muryarsan nan me cike da amo na mazantaka ta fara fita,yau din


cikin wani irin yanayi na sany da laushi,duk da cewa dama can ita iman din wannan
amon ta saba ji daga gareshi,bai fiya kausasa mata a magana ba

"Iman.....a duniya idan akwai wanda zai fadi halayyata bayan inna da yayata to kece
ta ukunsu,banajin ko sadiqu ya sanni yadda kika sanni" sai ya sanyi shuru yana
sauke numfashi gami daci gaba da kallonta sannan ya dora

"Kwanaki biyar da suka shude,munyi magana dake.....na bayyana miki komai,saidai


kuma har yau na kasa karantar me wannan iman din take nufi?,ina ta fuskanta?,ina ta
sa gaba?iman baki sona ne?,ko ya amin din naki bai miki ba?,idan banyi miki ba iman
ki fito ki gaya min,saboda ni ba baqonki bane......"ga fada maganar cike da qwarim
gwiwar samun akasin abinda zuciyarsa ke raya masa,saida amsar da iman din ta bashi
tayi matuqa girgizashi,ta motsa masa zuciyarsa fiye da yadda ya zata ko kuma ya
tsammata......amsar da bai taba kawowa koda cikin mafarkansa zai jita daga bakin
iman din ba,bai taba zaton zata iya furtata ba

"kayi haquri ya amin........bassam nakeso" ta amsa masa,tamkar dama jira


take a bata wannan damar.

Dukkan wata jijiya dake kai saqo jini da kuma iska a jikinsa zuwa
muhallansu sai da ta tafi hutu na sakanni,kafin ya samu nasarar zuqo
numfashinsa,bayan ya tabbatar numfashin ya koma saman qirjinsa yadda ya dace,sai ya
fara kokwanton duniyar zahiri ce ko ta mafarki,saboda haka yayi qarfin halin
motsawa kadan

"Iman.....sake maimatawa naji". Yayi maganar sautin muryarsa na fidda wani amo
wanda zai alamtawa mai sauraron da kunnensa da kuma qirjinsa ya cika da hikima cewa
lallai akwai wani abu mai tsananin nauyi da yake shirin danne zuciyar da wannan
sautin ya fito daga gangar jikinta......
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: .20

"Kayi haquri ya amin......basai na maimaita maka ba,abinda na fada din,hakan nake


nufi har tsakiyar zuciyata" wannan karon shigar da maganar tayi masa tafi wadda
tayi masa dazu,domin kuwa a take launin fari dake qwayar idaniyarsa ya juye zuwa
ja,saukar wasu abubuwa masu kama da mãsu yakeji tako ina a jikinsa.

Bai taba hasashen rashin samun nasafa kamar wannan a rayuwarsa ba,bai
taba tunani ko hangen failure irin haka ba kafa rayuwarsa,sai gashi kalar tashi
faduwar tana son ga riskeshi kan yanayi mafi muni,kan iman.....iman din da duk
duniya babu wani abu da yakejin yana da lasisi qwarin gwiwa da tabbaci a kansa
kamarta,saboda rainonsa ce,halittar da yaso yake kuma qimantata cikin kafatanin
rayuwarsa.

"Zuciyata da gangar jikina ta rayu dake a matsayin wata makusanciya,kuma


halitta mafi da kima a idanuna,sannan daga bisani dukka wadan nan suka narke suka
koma soyayya me nauyi da kuma qarfi,irin qarfin da zai iya fasa zuciyar duk wanda
ya kama......ima,daga ranar da malam ya bani ke daga ranar na laluba zuciyata,sai
na tarar ashe yarin sonki ne zallah shimfide a cikinta,dashi ta rayu tsahon zamanta
cikin gidan nan,ban fahimci haka ba saboda kallon qanwa ta jini da nake miki kuma
muharramata,sai ranar da malam ya tunsar da ruhina halaccin abun sannan na tabbatar
da haka.......iman" ya kira sunanta da wani irin taushi da ya sanya gangar jikinta
zubawa

"Ki yarda ki soni,ki karbi soyayyata iman,ina miki albishir din cewa,zaki sameni a
matsayin cikakken miji GARKUWA INUWA KUMA MAJINGINA ga matarsa,zan maidake abar
kwatance cikin mata,zan gatantaki da dukkan wani nau'i na gata da alqaluma suka
rubuta aka kuma adanashi da sunan GATA".

Tabbas jikinta yayi sanyi da jin fitar wandan nan kalaman daga bakin ya
amin din,tunda bata tana jinsu daga bakinta ba,saidai kuma idan fa waiga ta
waigo....zuciyarta ta maimaita mata kabar amin dai dai yake da rasa bassam muddin
ranta,sai wani rauni na musamman ya lullubeta,taji ba zata iya ba,ba zata iya
barinsa ba,ba zata iya rayuwa babu shi ba,jaririyar zuciyarta ta saba da
soyayyarsa,kunnuwanta na iya sake tariyo mata kalaman da ya gama gaya mata yanzun
nan,tamkar yasan abinda ke shirin faruwa kenan,cikin karyayyar murya dake nuna
karyewar zuciyarsa,baya ya gama roqonta ta barshi yazo gidansu haka nan,ta barshi
yazo ya gabatar da kansa wajensu malam,amma tsoro ya sanyata tace aa

"Karki yaudareni iman don Allah,ki soni yadda nake sonki koma fiye da haka,duk
randa kika kwatanta rabuwa dani,ba shakka sunana gawa" yayi maganar kamar zai fashe
mata da kuka.

Kai take girgizawa a hankali tana dubansa

"Kayi haquri ya amin,bazan iya ba,inason bassam,ina son bassam,zuciyata tana sonshi
ya ameen,ka taimaka ka mara min baya mu samu cikar burinmu" sosai yaji hankalinsa
ya sake tashi,ya sake kawo kusanci tsakaninsu yana dubanta sosai

"Look iman.......kinsan me kike fada?,ya ameen dinki kike cewa ya barwa


wani ke?,bazan iya ba iman.....ki bani dama na wanke wancan daga ranki nayi miki
sabon dashe me kyau da ma'ana" ji tayi kamar ya kwara mata ruwan zafi,saita miqe da
sauri,wani abu me kama da tsoro da kuma fusata suna cudanya cikin ranta

"Bazanyi maka qarya ba,bazan iya ba......inason bassam.....ina sonshi"


wannan kalaman data furta su suka sanyashi runtse idanunsa katamau ya gaza budesu
har tabar dakin,fitarsu daga bakinta zuwa kunnuwansa sun aikawa sa zuciyarsa wata
irin guba me tasiri da saurin illata dan adam

"Iman....iman" ya dinga maimaita sunan cikin kwanyarsa,kamar sunan baqo ne a


wajensa,mamakin yadda iman din ke magana dashi haka kai tsaye,babu haufi......babu
kara ko alkunya,iman dinsu ce wannan?,idan itace me ya canza ta?,meye ya sauyata
haka?,tabbas akwai abinda ke faruwa ko kuma ace ya riga ya faru,waye wannan bassam
din?,yaya akayi yayi nasarar canza iman din gaba daya?.

Wadannan sune abubuwan da suka taru sukayi masa rubdugu,suka saukar masa da
wani matsanancin ciwon kai cikin mintuna qalilan,wanda hakan ya tilasta masa
kwanciya,yana sauke numfashi a hankali,tafin hannunsa daya dafe da goshinsa.

Abu kamar wasa ciwon kan ya zaunar masa sosai ya kuma sanya masa
jinya,kusan kowa na gidan ya damu da yadda alamin din ya kwanta ciwo haka lokaci
guda,babu ma kamar inna data tabbatar ranae lafiya lau ya shigo,abunda ya tsaya
mata a rai,haka kawai taji bata yarda da iman din ba,musamman da taga qarancin
damuwa kan ciwon alamin tattare da ita,abinda bau taba faruwa ba tsahon rayuwarsu
tare,ita tafi kowa shiga damuwa da dimuwa duk sanda bashi da lafiya,tafi kowa
zamantowa kusa dashi,ta kumafi kowa sake maida hankali da kula da al'amuransa,amma
dukka yanzu babu wannan.

Kasa daurewa inna tayi,saboda lokacine da suke gab da cika burinsu ita da
malam,lokacine da suke son fahimtar juna da shaquwar dake tsakaninsu tafi tada,amma
sai ga wani baqon lamari na kuma shirin bullowa a sanda bai kamata ba,bai kuma dace
ya bullo din ba.

Kiran iman tayi ta rufeta da fada kan halin ko in kula data lura yana
faruwa,duk da cewa sai mai tsananin kula da sanya idanu zai karanci hakan

"Inna,shirin zana jarabawar qualifying muke fa,kuma ina da buqatar nayi karatu
sosai,shi kansa da kansa yake korata yace na dinga zama waje daya ina karatu" salon
qaryar data shararawa innar kenan,haka kawai taji bata gamsu ba,kuma hujjar bata
ratsata ba,don haka batace mata komai ba ballantana ta amsata.

Misalin qarfe takwas na dare ne,yana zaune qasan ledar din,ha jingina
bayansa da doguwa kujera guda daya dake dakin,qafafunsa na miqe sambal,wanda hakan
ya sake bayyana baiwar tsayi da Allah ya bashi,sambala sambalan qafafunsan yayi
crossing nasu waje guda,yadan daga kansa sama kadan,saidai idanunsa a runtse suke.

Idan ka sanshi kallo daya zakayi masa kaga yadan fada,ba kamar yadda yake
ada ba,dakin babu kowa saishi kadai,sai tv daketa faman yi,albarkacin wutar NEPA da
ake da ita.

A mintunan da suka shude dazu shida sadiqu ne,wanda ya zauna ya sanyashi


a gaba cike da damuwa kan sai yaji mene ne damuwarsa?,amsa daya yake bashi

"Bani da wata damuwa sadiqu,na gaya maka,ciwo ne kawai daga Allah" kansa ya girgiza
masa gana dubansa alamun bai yarda ba

"Haka dai ka fada,amma kuma ban yarda,saboda bani kadai ba,duk wanda ya sanka idan
ya kalli fuskarka yasan akwai damuwa qasan ranka" murmushin qarfin hali ya sakar
masa

"Mutumin da bashi da lafiya har a tambayeshi batun damuwa dama?,ina damuwa ne kada
na mutu na barka kai kadai" dariya ya sanya ta qwacewa sadiq din,duk sanda yayi
masa irin wannan zolayar a sanda bashi da lafiya dariya yake bashi

"Kaga.....ka samomin abun sha me sanyi mana please kaji?" Yace da sadiqun,saboda
yadda zuciyarsa ke masa zafi,wala'alla idan wani abun me sanyi yabi ta maqogaronsa
ya ratsa qirjinsa ya samu sassauci,dalilin fitar sadiqun kenan,shi kuma ya lula
duniyar tunani,dason warware tarin tunane tunanen da suke cunkushe a kansa.

Sallamarta ta sanyashi bude idanunsa da sauri cike da mamaki,yau kwanaki


biyu kenan rabonta da dakin,saidai ya jiho muryarta daga tsakar gida,ko kuma idan
zata fice.
Daga sallamae bata sake cewa komai ba,ta wuce tana ajjiye abincin,shima
sai ya maida idanunsa ya rufe,amma yana iya gani da kuma bibiyar motsinta ta qasan
idanunsa,yadda idan ka shigo ma zaka tsammaci idanunsa a rufen suke,koma bacci
yake.

Sosai ya lura da yadda taketa tsutsuke fuska da kuma bata rai,dukkan


alamu suka nuna dole akayi mata ta kawo abincin,sai data gama shirya komai ta juya
da zummar ficewa,cikin zafin nama ba tare da duba yanayin jikinsa ba ya miqe da
hanzari ya tareta.

Kallon kallo suka yiwa junansu,kowa yana duban dan uwansa cikin
mabanbancin emotion,ita ta fara kauda idanunta daga kansa,ta kuma ja da baya sannan
a hankali tace

"Fita zanyi,inna tana jirana" ba

"Iman,idan har da wasa kikemin......kiyi haquri ki janye maganarki,idan har gwadani


kike iman,ki sani wallahi bazanci wannan jarabawar ba" kan nata yana can daya
bangaren ta amsa masa,batason ta dubeshi don kada taji nauyi ko rashin kamata

"Wasa kuma?,ka taba yimin wasan furtamin kana sona?" Kansa ya girgiza

"Yadda baka taba min ba.....haka nima da gaske nake bassam nakeso,kayi haquri shi
nakeso,shi nakeso,na riga na kamu da sonsa" ta qarashe maganar tana zuba masa
qwayar idanun nan nata da a shekarun baya zamanin quruciya yara ke tsokanarta dame
idanun mage.

Cikin jikinsa yaji ya kamata ya kauce ya bata hanya,hakan kuwa yayi,yaja


jikinsa gefe a hankali,hakan ya bata dama ta daga labulen,ta kuma tura qofar ta
fice,zuciyarta na ganin baiken ya amin da yake sake tararta da wannan
maganar,maganar da take ga ya isa ya barta hakanan,tunda dama tun asali babu irinta
a tsakaninsu.

Yadda ta wuce fuuu zuwa dakinta ya sanya inna dake daura alwala bakin
famfo ta saki abunda take ta miqe ta bita da kallo,lallai ya kamata ta tambaya,ta
kuma sanya tuhuma tsakanin bassam da iman din.

******Yana zaune daga gefan malam din,saman babbar dardumar dake malale a babban
falon malam din,wanda babu komai sai dardumar da labulaye,da filalluka sample din
tuntum.

Karin safe malam din yakeyi suna dan taba hira da sadiqu da amin
din,yayi matuqar qoqari wajen ganin ya sake jikinsa ta yadda ba zasu fahimci komai
ba,amma shi kadai yasan me yakeji a zuciyarsa.

Tashin muryar inna suka fara ji daga tsakar gida cikin tsawa,abinda ya
sanyasu su dukka yin sak suna sauraro izuwa tsakar gidan,saboda gaba dayansu baqon
abune a wajensu tattare da innar,basu taba jin wani abu makamancin haka daga gareta
ba

"Me yake faruwa ne?" Malam yayi tambaya a fili,kamar yana buqatar ansa daga wajensu
sadiqu

"Leqa sadiqu,me ya samu binta haka" malam din ya sake fada cikin jimami da
mamaki,sai ya miqe yabi bayan sadiqu saboa kasa zama da yayi.

Duk muryarta da suke jiyowa tana daga cikin dakin iman ne,malam ya
qarasa a hankali ya sanya kansa cikin dakin,abinda ya manta rabonsa da yayishi,sai
ya samesu cirko ciro a tsaye,hannun sadiq riqe da waya yana juyata

"Lafiya binta?" Malam ya sake tambayar inna,wadda ke tsaye a kan iman,ranta a mugun
bace,bata amsa masa ba,sai wayar hannun sadiqu data karba ta miqa masa,yasa hannu
yakarba shima ya shiga juyata

"Ta waye wannan?" Malam din ya tambaya

"Ta iman ce" sadiq ya amsa masa

"Iman kuma?" Malam ya maimaita cike da dimbin mamaki

"Ita" inna ta amsa with confidence wanda ke cakude da wani irin zallar bacin
rai,maida dubansa ya sakeyi ga iman da kanta ke qasa

"Ya akayi kika samu wannan wayar?" Tambayar data fadarwa da iman din gaba,saboda
bata shirya amsata ba kwata kwata

"Tambayarki nakeyi" malam ya sake fada

"Malam,tun kafin ka shigo na tambayeta bata cemin komai ba,kamata......" Hannu


malam ya daga mata,sai tayi shuru tana saukar dakai,abinda bata taba yi ba iman din
ta sanyata yinsa yau

"Iman,karo na qarshe....ina kika samu wannan?"

"Wanine ya bani" dukkansu sai da maganar ta daki kowa a cikinsu,ta kuma sanyasu a
cikin rudani

"Wani fa kika ce iman?,wayeshi?"

"Saurayina ne" ta fada da low tune cike da fargaba,saidai zuciyarta na gaya mata
wanna shine last option da take dashi.

Shuru dakin ya dauka,kowa yayi dif a cikinsu,malam yana ci gaba da juya


wayar,yayin da kansa ha daure,mamaki kuma yake sake nuqurqusarsa

"Muje rumfata" ya basu umarni yana yin gaba da wayar a hannunsa,suka mara masa
baya,sadiqu na satar kallon iman din,yana jin kamar a bashi dama ya zabga mata mari
ko sau daya ne,saurayinta?,a gidansu kuma wai?,iman din?.

Sallamar malam tasa amin dake zaune a waje bai motsa ba bai kuma tashi ba
tunda suka fita,ya daga kansa yana amsawa,tunda suka fitan jikinsa ya bashi akwai
wani abu dake shirin faruwa,duk da bayajin abunda suke fada daga can din.

Shiru ne ya ratsa falon na wasu sakanni,har zuwa sanda malam ya jefawa


iman tambayar

"Waye saurayin nata?,a ina suka hadu" tambayar data qular da inna da kuma sadiqu,ta
kuma sanya amin ya sake saukar da kansa,abubuwa da yaketa qoqarin boyewa da kuma
dannewa zasu fasu kenan.

Sosai ta bawa kanta qwarin gwiwa,da kuma jin yaqinin cewa ba zasu
tilastata kan abinda bata ra'ayi ko kuma bata so ba,tiryan tiryan ta fayyace musu
waye bassam din,da kuma lokacin da suka dauka a tare

Wani abu ya yiwa sadiqu tsaye a wuya tunda ta fara amsawa malam
tambayoyinsa,huci yake fitarwa yana jin kamar ya tashi ya rufe iman din da
duka,idanunta har sunyi soyewar da zata yi wannan bayanin a tsakankaninsu su
hudu?,ameen kam ko motsawa bai yi ba,saboda wani nauyi da yaji qirjinsa yayi.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" malam ya fada qasa qasa,saiya miqawa


iman wayar

"Ki kirashi kice inason ganinsa,yazo yau yau din nan,daga yanzu zuwa magariba,idan
kin gaya masa ki dawomin da wayar" dukkansu sai sukai saroro da jin maganar da
malam din yayi,banda amin da babu wani abu da yaji,saboda yasan waye malam,duk wani
hukunci da zai yanke tafe yake da hikima a cikinsa,kuma yana da manufa,sadiqu da
inna duka suke zaton zaya rufeta dashi,amma sukaga akasin hakan....saidai koma meye
zasu zuba ido suga meye matakin da malam din zai dauka.

Wayarta ta karba ta miqe ta fice tana qoqarin aiwatar da abinda malam din
umarceta,tana ji cikin ranta akwai nasara tattare dasu.

K'arfe takwas saura na dare bassam ya iso qofar gidansu iman,bayan ya


samu cikakken kwatance daga iman,cikin shiga yake ta alfarma da nuna irin dukiyar
da Allah ya bashi,hakanan motar da yazo cikinta,tafi kowacce mota da yake hawa
tsada.

Yana tsaye daga jikin motar bayan ya bude Boot na motar,ya kira wasu daga
cikin daliban malam dake rumfar gidan suna daura alwalar sallar isha'i dake
gabatowa ya sanyasu suka fara kwashe kayan ciki suna shiga cikin gida dasu.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: ''21

Saidai kuma ko sakanni goma ba'ayi ba,sahun farko na yaran da suka fara
shiga gidan da kayan suka sake fitowa dauke dasu a kawunansu,kai tsaye suka
nufoshi,ya tsaya cak yana dubansu

"Inna tace malam din baya nan,a ajjiye kayan a a waje har sai ya dawo" yasan sunan
inna a bakin iman,ya tabbatar ummanta ce,sai ya ciro wayarsa don kiran iman din
yayi mata bayanin cewa shine ya aiko,saidai kuma koda ya kira wayar a kashe
take,don haka dole ya maida wayar aljihun nasa,ya kuma sa aka lode kayan cikin
rumfar.

Ya bude motar yana shirin shiga ya zauna ya jirayi malam din saiga bullowar
malam din,ya fahimci hakane saboda yadda daliban nasa keta masa sannu da
zuwa,dawowarsa kenan daga wajen saukar qur'ani da akayi na daliban wata makaranta.

Kallon farko yaji malam yayi masa wani mugun kwarjini,dama kwarjinin malam
din ba sabon abu bane ga duk wanda ya sanshi,saboda yadda qur'ani da tsoron Allah
ya ratsashi,saiya qarasa ya russuna yana gida malam din,ya amsa gana binsa da kallo
saboda baisan waye shi ba

"Dan samari daga ina?"


"Bassam ne" ya amsa yana shafa qeyarsa

"Ma sha Allah,to yayi kyau,ka qarasa masallaci muyi sallah,idan an idar sai ka
sameni a qofar gida" kira malam din yayi yasa aka kawo masa ruwan alwala.

Sam sadiqu da suke shigowa layin a lokacin shi da amin bai lura da canzawar
salon tafiyar al'amin din ba,tunda suka shigo layin yake hangen baquwar
motar,zuciyarsa na gaya masa bassam ne,ilai kuwa ya hangi fuskarsa sanda yake
alwala daga tsaye,duk ya rikice ruwan nata dawo masa yana bata shaddar jikinsa

"Ina zuqa sadiqu,nayi mantuwa" amin ya fada yana juya ya koma da baya,sam bazai iya
hada numfashi da bassam din ba,bazai iya kallon fuskarsa ba,yana jin wani kishi na
sukar zuciyarsa,hakan yasa ya yanke shawarar ya kauce daga wajen.

"Ina aminu ne?" Tambayar da malam ya yiwa sadiqu kenan sansa sadiq din ke
zama gefan malam,wani side din ba wanda bassam yake zaune ba

"Tare muka shigo dashi,amma yayi mantuwa a shago ya kuma tun dazun" sai kawai malam
ya gyada kai,ya gabatarwa da bassam ruwan randa me sanyi da aka kawo masa a kwanon
sha,saidai bassam din yace ya qoshi,ba kuma komai ya kawo hakan ba,saboda sam bazai
iya shan ruwan daba na roba ba.

"Malam bassam.....naji dadi da amsa kirana da kayi,ni din nan nine


mahaifin iman,kuma a yadda al'ada ta tanadar.....da kuma addininmu,a duk sanda
saurayi yaga yarinya yana so,zai fara turo magabatansa ne,saboda kiyayewar mutunci
kima da kuma daraja ta kowanne gida,idan an bawa magabatansa dama.....zasu sanar
masa yazo yaga yarinya,to a taka tarayyar da hajar duka babu wannan,banga laifinka
ba,saboda bansan waye kai ba,ban kuma san daga inda kake ba,na tattara laifin na
dorashi ga hajar,saboda ita tafi kowa sanin irin gidan data fito da kuma waye
mahaifinta,kayi kusakurai da yawa,ka yita hidimawa diyata ba tare da sanina
ba,wanda hakan kansa ya sabawa qa'ida da tsari,saidai nata laifin a idanuna yafi
naka ...to duka ba wannan ba,abinda yasa nace maka kazo shine,inason shaida maka na
dakatar dakai daga mu'amala da hajar,saboda nayi mata miji tuntuntuni,ko ita kanta
bana jin ta sani,da haka ba zata faru ba,don haka nake baka haquri....wadan nan" ya
janyo ledar gefansa da sadiqu ya shigo da ita

"Duka abubuwan daka taba bata ne,ciki harda wayar hannu,ka duba idan akwai abinda
ka taba bata da babu shi a nan wajen kayi magana".

Wani gumi ne yake yankowa bassam,saboda bai taba tsammani ko kawo cew
maganar da ta sanya malam ya kirashi kenan ba,wato rabasu zaiyi?,cikin tashin
hankali ya motsa baki ya fara roqar malam din kan kada ya aikata haka,ya bashi
daman gyara kuskuransa ya kuma bashi iman din ya aura

Murmushi irin na cikakkun dattijai malam ya sake,koda babu al'ameen


bayajin zai iya baiwa iman bassam din,aure yakeso yayi mata na mutunci da siyawa
kai daraja,auren qwarya tabi qwarya,kini sai kininsa

"Kayi haquri samari,na riga na bada hajar kamar yadda na gaya maka,kuma bama magana
mu tadata,saboda shi alqawari abun tambaya ne ranar gobe......idan ka tashi tafiya
ga kayanka nan,bama buqatar komai cikin abinda ka kawo din,ka sauka lafiya" daga
haka malam ya miqe yayi cikin gida,sadiqu ya mara masa baya ransa fari qal,wannan
abinda malam din ya aikata shine dai dai.

Sai da malam din ya gama duk abinda ya saba yi bayan shigarsa gida sannan
yasa innar ta turo masa masa iman,wadda ta kasa ta tsare dama tana ta jiran jin
abinda ga faru bayan xuwan bassam gidan,tunda a yanxun duka wayoyinta suna hannun
malam,ana kiran nata kuwa kamar na tsikarinta ta miqe ta fito.

Cikin kwantaccen harshe malam yayi mata bayanin komai,ya kuma gaya mata
cewa ita din an bayar da ita ga aminu tuntuni,shi ya nemi abar abun a hannunsa shi
yasa suka qyale

"Nasan lamarin xai iya zamar miki mai wahala,to amma matuqar kika maida komai ba
komai ba,zakiga komai din yazo miki da sauqi,tunda dai aminu ba baqonki
bane,shaquwa sãbo da kuma fahimtar junan dake tsakaninku yasa mukayi sha'awar hakan
ma,saboda haka ki tattara hankalinki waje daya,ku sake fahimtar juna,aminu kamar
dan uwanki na jini yake,hakazalika bana jin zaki samu mijin aure tamkarsa,munsan
halinsa ciki da bai,hasalima kusan fiye da rabi na halayyarsa rainonmu ne" kai inna
ke kadawa cike da gamsuwa,itama sai yanzu hankalinta ya kwanta da hukuncin da malam
din ya zartas
"Banason na sake ganin wani shirme ko kuskure makamancin wanda kikayi a yanzu ya
sake maimaituwa,tunda na gama magana da yaron,na kuma fahimtar dashi,Allah ya sake
hada kanku,ya tabbatar mana da alkhairi,tashi kije,ki kuma yita addu'a".

Da qyar iman ta iya riqe kanta sai data shiga dakinta,wani irin kuka ta
saki mai sauti da amo,wanda saura kadan su malam din su jiyota,ta yaya zata iya
fara rayuwa da bassam?,ta yaya zata iya rabuwa dashi?,yaya akayi bassam ya amincewa
rabuwa da ita?,ina dukka tarin alqawuran da sukayiwa junansu shi da ita, just
recently,me yasa malam zai mata haka?,me yasa ya amin za'a hada baki dashi a rusa
farincikinta?,me yasa ya dage sai ya aureta?,wadan nan up ta kwana tana yiwa
kanta,gefe daya sai ta samu kanta dajin matsanancin haushin amin,shine ya jawo
komai,banda ya nuna yana sonta....banda ga karba kyautarta da malam yayi masa da
za'a barta ta zabi wanda takeso,ta tabbatar da hakan.

Ta gefan al'ameen kuwa shima daban malam yayi kiransa

"Kayi saken da wani ya shiga gurbinka ya fara yiwa kansa aiki,yanzun dole sai kayi
aikin gogeshi,duk da inaji a jikina cewa akasi ne aka samu,saboda haka aikin
bazaiyi maka wani wahala ba......,ka sake kula da kyau,banda ka roqi alfarmar
abarta ta qarashe makarantarta saboda watanni ne suka rage,da bana jin zaa rufa
watan nan ban daura aurenku ba,ko a yanzu babu tabbacin hakan ba zata faru ba,Allah
ya sake kiyayewa,ya hada kanku". Da wadan nan maganganun malam yayi tunanin cewa ya
gyara komai,kuma komai zai hau kan hanya da kuma tsari,saidai ina.......akwai
guguwa a gaba mai tarin qura,guguwar data jirkita gidan da duk wani tsari nasa gaba
daya.

WASHEGARI.....kamar ba zataje makaranta ba don har qarfe shida da rabi tana kwance
tana share hawayen da tun daren jiya ya gaza tsaiwa,daga bisani taji damuwa kamar
zata fasa mata zuciya,ko banza idan taje din zata samu koda aron wayar da zasuyi
magana da bassam din,taji ya akayi aka haihu a ragaya,sannan kuma tana da tabbacin
samun shawarar wari daga munira,don haka ta sauko daga kan gadonta,ta fita zuwa
tsakar gida,taja ruwa a rijiya,ta cika botiki takai bandaki,bata ko damu da tsaiwa
ta kashe sanyinsa ba.

Sanda ta cewa inna ta wuce makaranta ba tare da tayi dukka ayyukan data
saba ba ba kuma taci komai ba inna batace da ita komai ba,saboda tasan dole damuwa
zata biyo baya,amma suna hange da hasashen tarin alkhairin da zai dorarma
rayuwarta,damuwar tadan lokaci ce qanqani.

Cikin sa'a suka hade a bakin gate na makarantar kowa na shirin shiga,suna
hada idanu kawai kuka ya qwacewa iman din,abinda ya tashi hankalin munira kenan,ta
kama hannunta da sauri ta jata bayan ajujuwansu.

Kuka sosai take mata muniran tana kallonta bata ce mata komai ba,kamar
yadda bata tsaidata ba,har sai data yi me isarta ta fara tsagaitawa sannan muniran
ta magantu

"Ya kamata koma meye ki daure zuciyarki ki gayamin,saboda bazan taba sanin
yadda zan kamo bakin zaren ba idan baki gayamin matsalar ba"

Handkerchief din data fito dashi daga aljihunta ta sanya ta share


fuskarta,wadda ta hada ja sosai saboda kukan data kwana tanayi,kaf ta kwashe duk
abinda ya faru ta shaida mata.

Tsaki munira taja,ranta yana suya da sake baci,haushin ameen ya kamata


matuqa
"Babu wanda ke miki maqarqashiya da son ganin koma bayanki face amin,shine kanwa
uwar gami,haka kawai mutum ya shigo gidanku ya muku kane kane ya rabaki da
iyayenki,duk soyayyar da suke miki,ni ban yarda zasu iya tirsasaki ki auri wani
haka kawai bisa radin kansu ba,sai don su faranta masa,idan zaki zage ki karta masa
rashin mutuncin da zai cire duk wata soyayya taki dake zuciyarsa ki zage" kai iman
ta girgiza

"Ni duka ba wanna ba,mafita kawai nake nema,banason na rasa bassam"

Gyara zama munira tayi cikin seriousness tace

"Akwai plan guda uku....,zamu bi kowanne a ciki,idan na farko baiyi aiki ba zami
tsallaka na biyu har zuwa na uku.....na farko,zaki sanya bassam ya turawa malam
iyayensa kai tsaye,su roqarma bassam ke,wala'alla girma da kimarsu yasa su cika
mishi idanu ya kasa musa musu......idan wannan biyi aiki ba.......zaki je ki roqi
ameen ya shaidawa malam ya janye,ki kwantar dakai sosai,ki masa dukkan wata kala ko
kama ta ban tausayi......idan wannan baiyi ba,babu wani sauran option sai guda
daya" ta furta tana daga yatsarta,idanunta akan iman

"Wanne ne?" Iman din ta tambayeta tanason jin qarashen bayanin muniran

"Maganata da na fara yinta a farko,ki rufe idanunki ki karta masa rashin mutuncin
da zai tsigeki daga zuciyarsa,yaji bayason koda hada inuwa dake bare har igiyar
auratayya ta hadaki dashi" kai iman din ke girgizawa

"Ba za'a kai nan ba in sha Allahu,kiramin bassam" ta fada tana tattara hankalinta
kan jakar munira da take kyautata zaton wayar tana ciki.

Wayar ta miqa mata bayan ta cirota ta cire mata password din,da sauri da
sauri ta zuba numbers din bassam din ta danna masa kira.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 22

Fitar sautin muryarsa cikin sallama kadai ya tabbatar mata ya kwana cikin
damuwa ne,saboda yadda muryarsa tayi can qasa sosai,amsa masa tayi cikin nata
laushin,ya kira sunanta da dan qarfi,abinda ya sanya zuciyarta ta qara karyewa,sai
ta miqe ta matsa kadan daga inda munira take,hawaye na qoqarin silmiyo mata.

******BAYAN KWANA HUDU*********

Lokaci mai tsaho take batawa suna hira da bassam a wayar munira duk
sanda taje makaranta,hakan ya rage mata damuwa sosai,a nan suka gama shirya ranar
da zai turo mutanensa wajen malam,ta saka masa lokacin data tabbatar idan sunzo din
zasu malam.

Ranar tun yammaci ta kasa sukuni,tana tsakar gida tana yankan alayyahun
miyar taushen data dora,mahadin alkubus da sukayi a daren amma hankalinta gaba daya
baya jikinta,inna da suke aikin tare tana lure da ita,tana mamakin yadda gaba daya
iman din ta sauya kamar wadda aka yiwa juyen qwaqwalwa,har yanzu ta fuskanci babu
alamun gyaruwar mu'amala tsakanin iman din da lamin,abun yana damunta sosai,saiai
ta duqufa da addu'a,tana ta gayawa Allah,koma meye Allah ya kawo qarshensa,ya
warware cikin sauqi.

Zuwa sanda ta kammala sallar magariba kuwa kamar sabuwar sojar dake koyon
parade a karon farko,taji shigowar malam,ta kuma ji fitarsa,amma daga nan bata
sakejin kowanne motsi ko kuma tashin wata maganar ba har zuwa wayewar gari.
A washegari a gurguje ta dinga komai,so take ta isa makaranta ta kira
bassam din a wayar munira taji me ya faru?,ko baqin basu zo ba?,saidai sanda ta
jefa masa tambayar ya tabbatar mata sunje,amma babu wata nasara,domin kuwa,kalar
bayanin da yayi masa shi dashi irinsa ya maimaita musu.

Hankalinta ya tashi qwarai,amma ta danne ta dinga kwantarwa da bassam din


hankali,inda daga qarshe yace sunyi shawara da abokinsa ya sake turawa dai kamar
bayan kwana bakwai.

Hakan kuwa akayi a karo na biyu,abinda ya faru wancan lokacin yanzun ma


shi ya sake faruwa,still dai malam ko kiranta baiyi ba bare yayi mata wata
magana,daga bakin bassam din taji sunzo,a ranar kusan qaramin hauka sukayi ita da
bassam din,daga qarshe suka sake yankewa cewa zai sake dai turawa a karo na uku.

A ranar ne tun bata tambayi bassam ba tasan lallai sunzo,wani qaton


kuskure suka tafka a wannan karon,siyayya suka shirgowa malam.din ta fitar hankali
kamar za'a bude shago,abinda yayi matuqar bata ran malam din,bashi kadai
ba.....harda sadiqu,yayi musu fata fata 'yan aiken,sannan ya dawo ciki ya sanya aka
kira mishi iman din,jikinta a sabule ta shiga rumfar malam din,saita taras da
al'amin a zaune a gefansa,kanshi a qasa.

Dauke kanta tayi daga inda yake,tana jin wani abu me kama da haushinsa
yana kamata,shine sila,shine ya jawo komai,yanzun kuma me yakeyi a wajen malam
din?,saita samu waje ta zauna a hankali itama kanta a qasa.

"Tsahon zamanku dashi baki shaida masa waye ibrahim khalilu ba?,to idan
bai sani ba ina fatan saqon dana aike masa dashi ya riskeshi,hajar.....idanma abun
duniyarsa yake rudarki gwara ki fiddashi daga zuciyarki,ni khalilu ba makwadaici
bane,kima da darajata itace gaba da komai,daga yau........indai nine mahaifinki na
soke makarantarki.......sannan kuma na sanya ranar aureku keda aminu wata biyu masu
zuwa,sati takwas kenan,sadaki kawai nakeso kaje ka hada,daga dubu ashirin zuwa
abinda Allah ya hore maka".

Malam din yana kaiwa nan ya miqe cikim bacin rai yana gyara malum malum
dinsa,taju daya yayi baiyi na biyu ba iman ta miqe hadi da sakin qaqqarfan
kuka,sannan ta sulale a wajen,ko waiwayota malam din baiyi ba yaci gaba da takawa
ya fice a rumfar,hakan ya baiwa inna damar yunqurowa,hannunta dauke da murfin
samira data sakawa malam abinci,wanda ko kusa iman din bata ankara da tahowarta ba
bare abinda ke hannunta ba sai qarar saukar murfin a hannun amin da yayi hanzarin
tare bugun da hannunsa bayan ya ankara da tahowar innar,daidai qashin tsintsiyar
hannunsa,ya hadu ya bada wani sauti qwalll!.

Idanunsa ya runtse saboda yadda zafin bugun ya ratsashi,sai a sannan iman


ta ankarata,cikin azama tayi bayansa saboda samun mafaka ta tsaya tana rarraba
idanu tare daci gaba da kukanta,wanda ya hasala inna,ta sake yunqura ta wurgawa
iman din murfin,ya kuwa daki kanta

"Gafara aminu ka bani waje.....banason abinda bai shafeka ba na hada dakai,matsa ka


bani waje,imani......ashe ke BUTULU CE KUFAN WUTA?,sakayyar da zakiwa aminu
kenan?,kukan auren aminu kike saboda tsantsar butulci?" Inna ta fada cikin tsananin
bacin rai,hankalinta a tashe kan hannun amin data buga

"Don girman Allah kiyi haquri inna,bada zafi za'a fahimtar da ita ba" da qyar ya
lallaba inna ta fita daga rumfar malam din,saidai fada take sosai kamar zata ari
baki,abunda basu saba gani daga gareta ba.

Shuru dakin ya dauka bayan ficewarta,babu komai sai sautin kukan iman
din,a hankali ya matsa gaba ya bada space a tsakaninsu sannan ya waiwayo insa take
tsayen,kuka take sosai kamar zata hadiye da zuciyarta,suna hada idanu ta sulale ta
durqusa gabansa,cikin madaukakin kuka harshensa yana hadewa tace

"Don girman Allah ka janye ya amin,don Allah ka gayawa malam ka fasa,ka barmu mu
auri juna nida bassam" suka sosai kalamanta sukayi masa qasan zuciyarsa,ya lumshe
lumsassun idanunsa sannan ya budesu,bayajin zai iya zuwa ya tunkari malam yace masa
ya fasa aurenta,bazai iya wannan aikin ba,amma kuma a yanzun baisan ta yadda zai
lallabata ta daina wannan kukan dake ci masa zuciya ba

"Ya isa iman,ki daina kukan haka,kije zamuyi magana" wani abu ta hadiye
tana dan jin relief yana saukar mata,sai ta tashi a hankali kamar yadda ya buqaceta
ta fice daga dakin,yayin da shi kuma ya bita da kallo.

Idonsa ya runtse gam tare da kama gashin kansa ya riqe da qarfi,wani radadi
ciwo da zafi yakeji tsakiyar qirjinsa,bai taba yarda da cewa son maso wani azaba
gareshi ba sai yanzu,bai taba yarda da wannan maganar ba sai a yanzun,inama zai
iya,inama zai yiwu,da tabbas ya cire wannan bassam din daga zuciyar iman din ya
dasa kansa,bai taba kawowa ko a mafarki iman din zata gujeshi ba.

Cikin kwanakin gaba daya gidan ya zama wani iri,da sadiqu da inna gaba
daya fushi suke da iman din,yayin da malam keta qoqarin ganin abubuwa sun daidaita
ta hanyar nusashshe da ita da kuma janta a jiki,ta bangare daya kuwa ita gaba daya
bata wannan take ba,tanata qoqarin komawa ne kamar da tsakaninta da amin din saboda
ta samu yayi mata abinda takeso,ya tausaya mata ya janye ya barta da bassam,tana da
tabbacin furtawa janyewarsa ce kadai abinda zai samu dama da kuma lasisin kasancewa
tare da bassam a matsayin miji da mata.

Koda yaushe idan ta tada maganar yana cewa ta bari zasu tattauna,dawo da
kusancinsu da take ta qoqarin yi ya masa dadi,saboda ya sanya a ransa ta wannan
hanyar zai sanya kansa cikin zuciyarsa a sannu a sannu,sannan idan tafiya ta fara
nisa zata haqura haka yake fata,don haka ta bangare daya ma tuni ya sake dawowa da
aikinsa haiqan na dinki,duk da malam yace sadaki kawai yake buqata,amma bazai qyale
iman dinsa babu sabbin sutura kamar kowacce amarya ba,uwa uba yana son ya samar
musu gidan da zasu zauna da kanshi bawai malam din ya basu ko ya samar musu ba,don
haka ya fidda ajiyarsa da yaketa yi,wadda yake saka ran amfani da ita idan ya samu
gurbin karatun da yaketa fafutuka,daya duba kuwa kudade ne masu yawa sa zasu
isheshi yayi abubuwa masu yawa dasu.

Sam iman bata gane wasa kawai yake mata da hankali ba sai da ya shigo da
wasu atamfofi ya kirata yace ta zaba guda biyar a ciki.

Atamfofin ta kalla sannan ta sake dubansa gabanta yana faduwa

"Na menene kuma had biyar?" Murmushi ya saki yana dubanta

"Ta ya zaayi ina tailor guda nabar amaryata babu sabon kaya?" Zumbur ta miqe hawaye
na cika idanunta,hankali take take dubansa

"Ashe dama yaudarata kakeyi?,ashe ba zaka iya yimin abinda nakeso ba?" Zaiyi.magana
cikin daga murya tace

"Kada ka sake kacemin komai kaji malam" daga haka ta juya da gudu zata fice,sukaci
karo sa sadiqu,saita gewayeshi ta fice,ya qaraso dakin a fusace

"Me yarinyar nan take gaya maka?".

Ganin a zabure sadiqun yake,sanna ransa a bace yake,zai iyayi mata komai sai
yace
"Ina ruwanka?,zancan miji da matarsa?" Kai ya girgiza ba alamun wasa a fuskarsa

"Tsawa fa naji tayi maka daga shigowata tun dahga farkon soro"

"Koma meye babu naka a ciki" amin din na kaiwa nan sadiqu bai saurareshi ba yayi
cikin gidan,amin ya miqe yabi bayansa,saboda ya tabbatar yadda ran abubakar ke a
bace kwanakin akan iman din,dama kawai dama yake buqatar samu a kanta lallai akwai
abinda zai faru.

Dai dai sanda ya isa kuwa tuni ta samu marin farko daga wajen sadiqu,yana
shirin qara mata na biyu amin din ya riqe masa hannu,yana zuwa dakin dama ya saka
kanshi da sauri,abinda ya mata rabonsa da aikatawa,saboda sam babu wanda ke shiga
dakinta sai inna.

Qarar data qwalla ita ta fito da inna dake uwar dakanta,dafe da kuncinta
amin ya sameta hawaye wani nabin wani,zai sake kai mata mari na biyu amin ya riqe
hannunsa cikin bacin rai,sadiq din na qoqarin qwacewa yana sababi,tsaiwar inna
kadai a wajen ta fahimci abinda yake faruwa

"Ka barshi aminu yayi mata dukan tsiya,shashasha BUTULU,koda baikai ga dukanta ba
ni gab nake da na saka ua daketan dama ai,duk irin takunki ina sane dashi,idanuwa
kawai na zuba miki" inna itama ta dora da nata sababin,da qyar ya fiddasu daga
dakin kowa ya koma nashi ranshi a bace,sannan ya tsaya bata baki,amma ko kallonsa
batayi ba har ya gama ya fita,yana fitan ta sakawa qofarta sakata ta koma ta
kwanta,tana kin haushi da tsanar amin na shigarta,ko babu komai shine yayi silar
dukanta da ya sadiqu yayi,sabida ta manta rabon da ya sanya hannu a jikinta ya
daketa.

A daki ya cimma sadiqu yanata huci

"Baka kyautamin ba sam sadiq"

"Nikai baka kyautamin ba,dama irin abinda take maka kenan baka taba gayamin ba?"
Kai ya girgiza

"Bata taba yimin ba,kuma kota taba din ma meye naka a ciki?,ina ruwanka,tun asali
dama baa shiga tsakaninmu ai kafi kowa sani" kansa ya kada

"Wannan abun ba irin tarayyarku ta baya bace amin,ka daina maida wannan abun ba
komai ba"

"Wannan ai ba dabara kayi ba,duka babu abinda zai gyara saidai ma ya lalata,zaka
sake dasa mata qin abunne a zuciyarta maimakon ta sassauto"

"Tayita qin mana,ina ruwan wani,aure ne dai sai anyishi,ko tanaso ko bataso,ko
gawarta ce sai an kai"

"Subhanallah" amin ya fada yana jin babu dadi har cikin ransa

"Kada ka sake fadin haka,ita zata zauna zaman auren ba wani ba,dole idan taci gaba
da qi a haqura a qyaleta,ko cikin addini babu auren dole"

"Eh,amma akwai auren cancanta ko?,kai kana tunanin malam zai janye maganarsa
ne?,daga gurinka take samun fuskar yin dukka wadan nan iskace iskancen wallahi"
daga haka sadiq din ya miqe abunsa ya tura toilet dinsu ya shige.

Zazzafar iska ya fitar daga bakinsa,gaba daya kansa ya daure,zuciyarsa


babu dadi,komai ya daure masa waje daya,iman din tayi sauyawar dako a mafarki yaga
hakan za qaryata,wai dukka soyayyar waninsa ce data danne tasa a zuciyarta ko kuwa
akwai wani abu na daban da baisan dashi ba?.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 23

MATAKI na sauyawarta ta dauka, option na qarshe da take ganin tana dashi,tun


daga lokacin ta soke gaisuwa tsakaninta da ameen,ko magana bata bari ta hadasu
saidai idan a gaban malam inna ko sadiq ne,bai taba gayawa kowa ba,sai yama tsiri
fitar wuri wajen dinkinsa,ya wuni har dare a can yanayi sannan ya dawo gidan,hakan
ya aake qaranta haduwarsu,ya kuma zame masa alkhairi,saboda nan da nan yayi dinkuna
masu tarin yawan gaske,kudi kuma suka dinga shigo masa.

Duk wata hidima da take masa a yanzu ta sabule hannunta,babu abinda yake
hadata dashi,hatta da abinci ta daina kai masa,babu irin abunda inna batayi mata ba
kan batun kai abinci amma ta qeqashe,ita kanta innar kallon iman din take kamar an
canza mata ita,saidai bakinta bai fasa addu'a akan iman din ba.

********Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana ajjiye kwalbar turaren da ya gama


fesawa a jikinsa,sai yanzu yaji dadin jikin nasa bayan yayi wankan,saboda gajiyar
da ya hadawa kansa yau din tana da yawa.

Da baya ya koma yana shirin zama yaga an dage labulen,iman ce dauke da


kwanukan abincinsu guda biyu,bazai iya tuna ranar yaushe bane rana ta qarshe da ta
shigo dakin har ya ganta kamar haka,amma ko a yanzun idan ka dubi fuskarta da kyau
zakasan cewa tilas akayi mata.

Tana ajjiye kwanukan ta juya abinta zata fice ba tare data ce masa kanzil
ba,kusan ha saba da wannan sabuwar dabi'artata,gaaba take dashi sosai,don ko kallon
inda yake batayi,to amma ayau din yanason suyi magana ta qarshe kuma ta fahimta
dashi,don gaba daya salon rayuwar da takeso su shimfida batayi masa ba,don haka
cikin zafin nama irin ta zaratan maza yayi wuf ya isa gabanta,ya kuma sanya qafarsa
ya tura qofar dakin,ta kuwa rufe ruf,jamlock ya shige

"Meye haka?" Ta fada cikin wata iriyar tsiwa tana dubansa kai tsaye

"Ta yaya zaki tafi kibar angonki?,bayan kwana da kwanaki bai samu kun kebe ba,kuma
koda kun hadu a tsakar gida ba'a kallonsa ko a gaisheshi?"

"Wai gaisuwata dama kake zaman jira?,aiko wallahi zaka bushe baka sameta ba,ka
matsamin na wuce" wadan nan ba baqin kalamai bane a wajensa,saboda tuni ya saba
jinsu,amma a yanzun shi ba wannan bace a gabansa

"Ni ban taba ganin inda ake soyayya dole ba,duk inda aka ce ba'a sonka ya kamata
kayi aiki da hankalinka ka gusa daga wajen tun lokaci bai qure maka ba,naci babu
abinda zai haifar maka,wanda bai sonka kawai bai sonka,saika qara gaba ka lalubi
wata ai ko,ka matsan na wuce ina da abunyi". Sosai yagi qoqarin hadiye
maganganunta,tare da danne duk wani reaction da zasu bada saman fuskarsa

"Babu inda zaki,amaryata nakeso gani da gaske" wata irin harara ta watsa masa kamar
idanunta zai fado

"Wace amaryar taka?" Saita zubda yawu gefe

"Allah ya kiyaye ya tsareni,ni in aureka?,na aureja nace na auri meye?,wallahi da


na aureka gwara na mutu,kai koda an daura an kaini saina caka mana wuqa dani dakai
din duka mu mutu" dummn kansa yaji yayi da kalamanta ba qarshe,ya lumshe idanunsa
ya furta
"Ya salam,Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla" a fili,saidai muryarsa can
qasa,wai dama haka mata suke?,haka suke canza alqibla lokaci guda?,iman ce fa
wannan,iman din da ya gama sanin quruciyarta,ya koya mata ababe masu yawa cikin
rayuwarta,yau ita take iya tsaiwa a gabansa ta gaya masa wadan nan maganganun.

Wani irin matsawa yayi da baya cikin fushi da hanzari,ya sanya hannunsa
ya dauko kakkaifar wuqar da yasha lemon fata da ita tunda safe,ya dawo gabanta ya
lalubi hannunta ya sanya mata wuqar a zafafe

"Bismillah,ki fara aiwatarwa tun yanzu,ga wuqar nace,ki nunawa duniya ke cikakkiyar
mara hankali ce mara qwaqwalwa ta gaske" ya fada cikin wata irin tsawa data kada
hanjin iman din,ya ritsata da idanuwansa da suka sauya launi saboda bacin ran
maganarta da yadda zuciyarsa ke tafasa,jikinta ya dauki kyarma,sai ya sanya hannu
ya fisge wuqar ya kuma yi jifa da ita,taku uku ya qara zuwa gabanta,tazarar dake
tsakaninsu tayi qaranci qwarai,har suna iya shaqar numfashin juna

"Ko a yau aka daura mana aure dake zan iya datse igiyar aurena dukka ukun dake
kanki.......tunda har zaki iya daukan rai lallai ba shakka na tabbatar wancan
mutumin ya cire dukka imanin dake zuciyarki tausayi da kuma jin qai.....ba abun
mamaki bane tunda tuntuni ya cire miki ganin girman maganar iyaye. Tun farko bani
da sha'awar auren macen da bata sona koda kuwa wanne irin so nake mata,rashin
zarrar da zan bijirewa maganarsu malam saboda su din iyayena ne ya sanya na haqura
da tsarina na dauki nasu......badai saboda ina sonki ne ya sanya kike dukkan wasu
abubuwa da kike ba?,ki bude kunnenki.....daga yau,ni muhammad amin,na rabu dake har
abada,idan kinso kije ki auri billgate" daga haka ha kewayeta cikin wani irin zafi
da har tan jin wani irin huci sanda ya giftatan.

Cikin daren juyi ta dinga yi tana hango abinda ya faru tsakaninta


dashi,wani irin fushi da bacin rai data hanga daga gareshi

Washegari da safe saiga kiran malam,a lokacin ta samu bacci ya dan


dauketa bayan ta shaidawa bassam duk abinda ya faru,ya bata qwarin gwiwa tare da
kwantar mata da hankalin lallai nasara tana zuwa.

Tun kafin takai ga zama da dogon hijabinta malam din ya fara sauke mata
ruwan bala'in fada,fadan daya rudasu gaba dayansu ita da amin dake zaune a wajen

"Idan ma ita ta tursasaka ko ta sakaka kazo ka fadi cewa ka janye a bata wanda
takeso.....to inamai shaida maka daga kai har ita baku isa ba,bazan kuma fasa
abinda nayi niyya ba,dakai da ita din gaba daya mu zuba nida ku,tunda haka kuka
zaba,ku tashi ku bani waje shashan banza" wannan itace magana ta qarshe da malam
din yayi dasu.

Sati guda a tsakani suka wayi gari da baquncin yaa gana,yayar malam
kenan,dukka gidan babu wanda baiyi mamaki ba,banda al'ameen da yasan da zuwan
nata,hasalima yasan maqasudin zuwan nata,tunda shine sila,rabonta da garin kano an
jima,a qalla ba'a qasara an kusa shekara biyar ko shida.

Daga inna har iman data rame ta fada saboda damuwar da take ciki suka
tashi haiqan wajen tarbarta da abinci da sauran abubuwa,hira sosai suka sha da inna
harma da iman din mutuniyarta,saida la'asar bayan iman din ta zuba mata ruwa a buta
tazo ta sanar mata sai ta dubeta

"Wai duk meye silar wannan ramar ta hajar?" Ta jefawa inna tambayar,tabe baki innar
tayi

"Gatanan,ki tambayeta" maida dubanta tayi ga iman,saita sunkui da kai hawaye suka
fara tsatstsafo mata,tana jin ranta yana suya
"Ke na tambaya ai ba hajar ba"

"Dan uwanta za'a bata,aminu,wanda suka taso gida daya,cikin mutunci da girmama
juna,wanda yasan darajarta,tayi tsallen albarka ta dauko wani bare,wanda dukiyar da
yake da ita ko ubanta baida rabin rabin rabinta tace shi takeso,ban sani ba ko abun
hannunsa ke rudarta" inna na kaiwa nan iman din ta juya da hanzari ta fice a
dakin,hawayen da take riqewa suna sauko mata,wato kallon da suke mata kenan?,babu
wanda ya kalli cewa soyayya ce sila a cikinsu?.

Batasan yadda suka qare da inna ba,don bata fito daga dakin ba kwata
kwata sai da zata daura alwalar magariba,shima tanayi ta koma dakin,sai wajen qarfe
goma na dare har tana shirin kwanciya taji anyi knocking qofarta daga tsakar gida

"Ki fito inji malam ki sameshi a rumfarsa" muryar ya sadiqu ta ratsa kunnenta,take
ciwon da kanta yake ya sake hauhawa,haka ta miqe a daddafe ta zura hijabinta ta
fito zuwa rumfar malam din,gabanta na wani irin faduwa.

Daga gefe guda ta rakube jikin yagana,kamar wadda zata shige cikinta,dukka
al'ummar gidan ce cikin fakon,kallo daya malam din yayi mata ya dauke kansa,sannan
ya fara magana

"Allah ya sani nayi dukkan iya bakin qoqarina don ganin na baki
ingantacciyar rayuwa,na kyautata gobanki amma ban samu hadin kai ba kwata kwata
daga gareki ba,kin sanya kwalli kin murje idanunki,kin kuma gaza gane ko fahimtar
abunda mu muke hangar miki........shikenan,zan miki yadda kike so din saboda
darajar yagana dashi kansa aminun da yakai qarata wajenta yakuma jajibota ta taso
ta taho,zan baki yaron da kikeso,amma ba bisa zabi ko son raina ba......zan bashi
aurenki amma bisa sharadai kamar haka,sharadi na farko,aurenki dashi babu yaji,babu
saki,sharadi na biyu,idan kika saka qafa kika bar gidan nan banason ganin
wulqawarki a gidan nan bare naga kina zirga zirga da sunan ziyara,mun yafe masa
ke,na uku babu ruwanmu da duk wata matsala da zata taso miki ko ta tunkareki,idan
ma hakan ya faru to ki nemi wani gidan amma dai ba nan ba......."

"Amma malam....." Amin yayi qoqarin datsar malam din,saboda jin girman sharadin da
yaketa yankowa iman din,da sauri malam ya dakatar dashi

"Idan kace wani abu sau ranka ya baci,tunda kun gama naku kun tursasani saiku barni
nima nayi nawa" maganar ta sanya alameen komawa yayi laqwas,saboda bai taba jin
malam din ya gaya masa hakan ba sai yau,karo na farko kaf tsahon rayuwarsu
tare,yagana.batace komai ba,duk da.sharuddan sunyi tsauri da yawa,tana fatan iman
din taji girma da.nauyin sharuddan tace ta janye,wannan dalili yasa batace komai
din ba.

"kin yarda kin amince?" Malam ya tambayeta da kakkausar murya,dukka sai


idanu ya koma kanta,kowa fatansa a wajen tace a'ah,kowa addu'ar da yakeyi cikin
zuciyarsa kenan.

A hankali zuciyarta ke wassafa mata tare da tariyo mata kalaman


bassam,irin soyayya da Zai nuna mata,kulawa da kuma qauna tare da daukaka darajarta
a cikin mata,ta tuna yadda suke begen juna ita dashi,saita daga kanta a hankali
zuwa sama alamun

"Eh" wani irin runtse idanu amin yayi wanda ta saukar masa da ciwon kai lokaci
guda,saboda yadda jijiyoyin kansa suka harba sanda ya tsinkayi amsar da iman ta
bayar,yana iyajin wani zazzafan huci da sadiqu dake kusa dashi ya fitar,alamun
zuciyarsa zafi kawai takeyi,kamar anyi ruwa an dauke haka wuta ta daukewa kowa dake
dakin,kalaman malam suka sake ratsa shirun

"Ki kirashi ki shaida.masa cewa......rana ita yau yazo da sadaki a daura muku
aure,yazo da shaidunsa biyu sun isa,daga nan ya daukeki ku wuce" ba iman ba,hatta
da ya gana saida maganar malam din ta girgizashi,wanne irin hukunci ne haka
tsattsaura bayan wanda ya furta kuma dazu,a rude iman take bin malam din da
kallo,tana jin maganar tasa kamar a mafarki,a sadaka malam zai bada ita kenan?

"A'ah malam,ba za'ayi haka ba,don bakason mijin data zaba hakan ba shine zai sa ka
bada diyarka baka binciki waye shi ba,sannan ka dauketa haka ziqau ka bada ita babu
komai kamar sadaka,ba lefe babu dukka wasu kayyayaki da al:ada ta tanada" duban ya
gana yayi

"Me zan aikata kuma bayan wannan?,kina tunanin a yanzu akwai wanda zaka tunkara kan
neman sanin sahihiyar halayyar me kudi ya gaya maka gaskiyarsa tsakaninsa da
Allah?,abune mai wahalar gaske,kaya kuma ya gana da kike magana a kansu,keda kanki
kikace al'ada,al'ada kuma ba addini bace,dama a addinance shine zai bata wajen
zama,wajen zama kuwa ya hada harda kayan daki"

"To amma ita binta ai zata sanarwa danginta zata aurar da diyarta ko?"

"Babu wanda zan gayawa,yadda ta zabarwa kanta kenan,don haka bazan dagawa kowa
hankali ba,tunda shi ta zaba kuma an bata me yayi saura?,wanne muhimmanci muke
dashi?,me zamu tsinana mata" inna ta fada tana miqewa tsaye,ta fara takawa tana
barin falon,batason taci gaba da zama bare hawayen da takejin suna tsatstsafo mata
su samu zubowa,tun dazu take dannesu,batason su zubo bare su zamewa iman din bala'i
cikin rayuwarta,tausayin iman din takeji na yadda soyayya ta rufe mata idanu,tun
bata gama sanin duniya ba,na yadda tabar lu'u'lu'u ta dauki jan qarfe,bata jin a
duniya iman din zata samu mijin da yakai amin nagarta da komai da komai,tabbas
diyartata ta tafka babbar asara,a yau kuma a karon farko cikin zuciyarta taji ta
buraci inama ace tana da wata diyar bayan iman,da babu ko shakka koda batakai
munzalin aure ba ta wanketa ta bawa amin ita,kallon fuskarsa da tayi sau daya bata
qara marmarin kalla ba,tabbas dukkan abinda yayi yayi shine saboda tsabar juriya da
qarfin hali irin nasa,amma idan kayi nazarinsa da kyau zaka karanci zallar tashin
hankali da gigita da ya tsinci kansa a ciki.

Inna na fita sadiqu ya miqe ya mara mata baya,al'ameen ya miqe a daddafe


shima yana lalubar hanya malam ya zaunar dashi

"Duk da irin qiyayyar da hajar ta nuna maka.....amma ko sau daya baka taba nuna
bakason auren nan ba,baka taba musu damu ba,hakanan baka taba bijirewa umarninmu
ba,kai da kake bata tsatsonmu ka fito ba,babu abinda zance dakai saidai nace Allah
yayi maka albarka,ya baka mace ta gari wadda zakayi alfahari da samunta" kansa a
qasa ya amsawa malam din,sannan ya miqe a hankali yana ficewa,ya gana tana binsa
itama da addu'a,ranta duk babu dadi,saboda duk wanda yasan iman a dangi yasan
al'ameen,yasan kuma nagarta irin tashi da halin dattakonsa.[7/19, 10:02 PM] Mummyn
Yara: 24

        Ba qaramin kai ruwa rana akayi da malam ba kafin ya amince ya saurari ya


gana,ya qara bikin zuwa sati uku masu zuwa,don ya rantse ya maya cewar ba zata qara
masa wata guda a gida ba,saboda shi kam bazaici gaba da zama da yarinyar da tafi
qarfin umarninsa ba,wannan furuci shike daga hankalin iman,bataso ko sau daya taji
malam ya fadi hakan.

         Munira da tasan yadda komai ya wakana da sauran qawaye da basu sani ba


duniya sabuwa,duniya ta samu,nan take aka soma shirin biki gadan gadan,bassam ya
sakar musu komai,yace su tsara komai,su fadi dukkan abinda suke buqata kada suji
shayi ko wani abu,ya sakar musu bakin aljihu iyaka, events events sai da suka tsara
na kwanaki bakwai curr,kuma kowanne kudi za'a kashe ba qarami ba,saidai duk wannan
abun malam yace ba cikin gidansa ba,hakanan ya gana ta dauki ragamar komai ta maida
gidan wani dan uwansu dake daura da unguwarsu,ya bawa iman din daki guda,sai data
koma gidanne ma taji tadan ware,saboda ta daina ganin mugun kallo daga inna,wanda
take aika mata dashi duk safiyar duniya har zuwa faduwar rana,suka kuma zame
hannunsu daga duk wani abu daya danganci bikin,don malam ma yace bashi da kudin da
zai siya mata kayan daki a lokacin bare kayan kitchen,yadai siya katifa botiki buta
tsintsiya da labule,ya kuma siya mata fulasai da tukwane.

           Munira ce ta tseguntawa bassam abinda ake ciki,ranar saiga kira daga


bassam din cikin sabuwar dalleliyar iPhone 13 pro max

"iya abinda suka siyamin din ya isheni,dashi kuma zan tafi" amsar data bashi kenan
ta katse wayarta abunta,ranta ya baci sosai kan me yasa muniran zatayi mata
haka?,koda tazo take mata maganar cikin bacin rai sai tayi dariya

"Wallahi wallahi ya zuba miki komai a gidanki,kuma ina da yaqinin babu wanda yasan
shine yayi miki,to meye a ciki wai?,ai shima yasan basuson auren ne shi yasa akayi
miki haka,amma ki kwantar da hankalinki,komai zai wuce" kai iman din ta gyada,duk
da cewa wani lokaci idan shna hidimarsu takan manta ta yadda za'ayi auren nata,amma
duk sanda ta tuna sai taji jikinta yayi sanyi

"Inajin kamar na fasa auren nan munira,gaba daya daga inna har malam sun jingine
ni,kamar ma basa sona" idanu munira ta fitar

"Ashe baki da hankali?,don fa zaki aura,to idan baki sani ba bari na gaya miki,kudi
sune qare magana,idan kana da kudi zaka iya siyan komai,zaka iya mallakar
komai,ciki harda soyayyar mutane da farinjini,ke har mutunci a yanzu a wannan
zamanin kudi suna saiwa mutum shi,bari ki gani,wuyarta ki shiga gidan,sukaga kuna
zaune lafiya qalau,kuma abubuwa na shiga da fita daga hannunki komai zai canza,zai
zama tarihi kamar ba'ayi ba"

"Na yadda lallai bakisa waye malam ba......babu abinda ke iya canzashi a duniya
idan ba gaskiya bace" ta maidawa munira amsa tana kallonta

"Kinga,kada fa ki damu,yau da gobe bata bar komai ba,matso kiga kayan da bassam ya
zabar muku,tunda ke kinqi sakin jiki aje a zabi komai dake" ta bude wayarta tana
nuna mata kayan masu azabar tsada daya tilar mata da sunan lefe,gefe guda kuma ga
kayan dukka events din guda bakwai din,kowanne anko sukayi ita da bassam din,kuma a
dinke suke,kana gani kasan anci mutuncin naira a wajen.

          Kudi sosai ya ajjiyewa iman din na gyaran jiki da sauransu ta hannun


muneera,da kudaden tazo a hannunta tana nunawa iman din

"Yanzu ina zamu ayi miki gyaran jiki sharp sharp na kwanakin nan da suka rage,yadda
zaki sake fita"

"Amaryar kb global enterprises"

"Inane haka?" Muneera ta tambayi daya daga cikin qawayensun da tayi magana

"Ai babu inda zamu samu fiye da yadda mukeso irin kamfanin AMARYAR KB GLOBAL
ENTERPRISES"

"Babu wasa fa,kinsan mrs bassam ce,duniya zata daukaki bikin nan,dole ne mukaita
inda zaa fita kunya,wadanda suka san abinda sukeyi"

"Haba malama,kinfa sanni,ita ta yiwa sakina gyaran jiki?"

"Yes.....nafa tuna,sakina tasha kyau gaskiya......anyita maganar yadda jikinya yayi


kyau wallahi cikin qawaye,ga yadda jikinta ya dinga ya dinga fidda wani irin
qamshi,ni kaina sai da na tambayeta wanne turare ne,amma kamar tana saida kayan
amarya set na kayan qamshi ko?"

"Abubuwan da suke samarwa fa suna da yawa,kinga suna da


Turaren wuta from chad

Sandal flakes
Kajiji                
Yellow sandal
Mufaddal.       
Senegalese Kajiji
Couscous.         
Green sandal.     
Sudanese mix.     
Shek Bakhur.        
Sandal coconut.   
Dorot                      
Hadut.                     
Gabgab.                  
Sandal rose.          
Green fruity.             
Sandal bange.         
Kajiji balls.                
Sandal balls.             
Aroosa.
Khumra
VIP Khumra
Royal princess oil perfume ne
Hair kulacca
Sudanese kulacca na jiki
Sudanese scrub and dilka
Bath fragrance (turaren wankan)
Carpet and curtains perfume
Wardrobe balls

Sai kuma kayan gyaran mata kamar

Maganin infection
Maganin mata 👇🏽
👇
Tsimi
Tula syrup
Tabaje
Kurman namiji
Pussy dessert
Silky syrup
Bata gaban kishiya
Hatsabibin gari
Zumar Chad
Tsimin tula
Tula juice sweetener
Ciccibi
Kaza
Zumar bita zaizai

"Kai,amma matar ta hadu,duk ina kikasan wadan nan kayan nata?"

"Kai kayanta ai dar ne,auty na duk wani qamshi ko gyara da zakiga tayi a maryar kb
takeyi,duk sanda mijinta zai dawo daga spain acan ake mata gyaran jiki,karkiso kiga
gift din da mijn ke bata idan ya dawo" shewa suka sanya,muneera tace

"Bani number dinta,can zamu kai tamu amaryar a hada mana ita"

"Ok,08067558902". Nan take muneera tayi serving.

          Sanda yagana ta tashi komawa maiduguri taje ta dawo kafin satittikan


bikin su cika,da kanta ta kira iman din ta sakeyi mata jirwaye da kamar wanka,don
sanyi jikinta yayi sanyi,amma kuma babu alamun zata janye daga auren bassam

"Karki dauka kamar na daure miki gindi ne kije ki auri wanda kikaga
dama,a'ah....nayi hakane saboda yadda na tsani auren dole,saboda shi yagi
sanadiyyar rasuwar jikata balaraba,babu abinda yafi bin umarnin iyaye dadinkoda
kuwa ka fisu gaskiya" da wanna kalaman ta tafi tabar iman.

**********Katafaren falone wanda idan ka kirashi da aljannar duniya bakayi kuskure


ba,saboda yadda ya wadata yaji dukkan wani kayan alatu na rayuwa,wani abunma idan
ka kalla kasan harda nuna fariya a cikinsa,duk kuwa da cewa arziqinsu yakai suyi
koma meye,amma falon sak samfurin irin falukan da masu kudin qasashen larabawa ke
ginawa kansu.

         Babbar macace mai tsaho da kuma kauri,sanye da wani dandatsetsen lace da


yasha ruwan stone tun daga sama har qasa,qafafuwanta sunsha jan lalle har zuwa
yatsun hannunta,tana zaune saman kujerun alfarma dake falon ta dora qafa daya kan
daya,'yan aikine keta hidima da ita,saidai babu wadda ta daga idanu ta kalla,ta
bada himma kan canza channel tv daga wada take kai zuwa wata,fuskarta kwata kwata
babu annuri ko kadan.

           Kyawawan labulayen parlor din aka daga gami da sallama cikin muryarsa me
zaqin nan,zaqin da har yaso yayi yawa ta fita daga ta maza zuwa sigar muryar mata
irin masu dan babbar muryar nan.

          Bassam ne sanye da qananun kaya,idanunsa sanye da qwabjejen baqin glass


daya haska farar fatarsa,ya doso inda matar take zaune yana sallama.

          Ciki ciki ta amsa masa,yana zama dukka masu aikin suka watse,suka barsu
su kadai cikin falon

"Barka da hutawa" ya fada cikin sigar dake nuna boko tayi matuqar ratsashi,sai data
ajjiye remote control din a gefanta,sannan ta tattara dubanta a kanshi,cikin wata
murya dake nuna a ciki take dashi tace

"Ashe abinda kaje ka jajibo mana kenan?" Ta jefa masa tambayar tana qanqance idanu

"Kamar yaya mom?"

"Yanzu bassam ka rasa yarinyar da zaka auro sai 'yar gidan almajirai?,'yar
matsiyata,masu ci da allo da tawada?,wadda iyayenta basu ajjiye komai ba?,duk tulin
'yammatan da kake dasu,babu irin jinsin yaren da qabila da kuma 'yan qasar da babu?
babu kalar matsayin da iyayensu basu dashi?, recently 'yar gidan commissioner of
finance tazo gidan nan takanas saboda kai,ringidi ringidi ina murna kamar
gaske,ashe kai idanunka wata suka hango maka?" Kansa ya shafa yana bata fuska

"Munafukan nan su fahima da sukaje kai lefe ne suka gaya miki,wallahi dama nasan
za'a rina" tsawa ta daka masa

"Kai dalla banza shashasha,wanda baisan ciwon kansa ba,su kishin dan uwansu suke
idan kai baka kishin kanka,wannan 'yar gidan matsiyatan dama tuntuni kaketa yiwa
ruwan kudi,kake rawar jiki kana barnatar musu da kudi,kudin da basusan darajarsa
ba,kudin daka zubar musu inda da tabbacin har ubanta ya mutu bazai hada jarin da
yakai yawansu ba,wallahi wallahi banda magana tayi nisa ko zaka mutu ba zaka aureta
ba,so kake kawai ka tozartani cikin qawaye da abokan gaba 'yan baqinciki da
mahassada?" Ciki ciki yace

"Am sorry mom,amma yarinyar ai tayi,nasan zata fiddaki kunya shi yasa na zabeta,don
kaf cikin wadanda kike lissafawan babu wadda ta kama qafarta a kyau,kawai talakawa
ne dai,amma shi kansa babanta da qyar ya bada ita"

"Kai dalla can matsa,au da qyar ya bayar?,to ai daya riqe abarsa,kada Allah yasa ya
bayar din,saboda Allah ya taimakeshi ma zai hada jini damu?" Sake hasala hajiya
hafsatu tayi wadda suke kira da mom,da qyar bassam yasha kanta kafin ta sauko

"Wannan gidan naka ka bata ta zauna ba?" Kai ya jinjina mata

"To ban lamunta ba.....me zasu iya zubawa a wannan gidan har ya cika?,matuqar
kanason aurenta duk uban abinda suka jera din,a kawoshi nan part din hajj a
shareshi a jera" idanu ya fitar

"Haba mom,why?,nifa gaskiya inason sakewa da matata" haiqan ta sake taso


masa,saboda tasan halin bassam din,zuma ne saida wuta

"Gidan ubanta yakai parlour daya dake part dinka kima ne?,idan kanasonta ta dawo ta
zauna damu,idan kuma ba haka ba,to saidai ka fasa auren nata,wannan gidan sai ka
tashi sake auren abokin burmin qwaryarmu sannan za'a shigeshi,amma ba zaka saka min
diyar almajirai a ciki ba" daga wannan ta miqe abunta ta nufi stairs ta haye
abunta.

          Abunda ya sanya inna ta kasa riqe hawayen da taketa qoqarin


tsaidashi,ranar da al'ameen ya sauke motoci guda biyu shaqe da kayan gado da kuma
kayan kitchen na ban mamaki,dukka wani tanadi nasa da yayi don kansa ya qarar dashi
akan iman din kamar yadda ya saba,babu yadda baiyi da sadiqu ya siya mata
freezer,home theater da sauran kayan wuta ba amma fafur yaqi,yace sisinsa bazai
kashe mata ba,tunda mai kudin duniya zata aura,shima da yasan haka zai qarar da
komai nashi lallai da bazai bari ya siya mata komai ba,shikam.kamar bashi da
zuciya,ya manta abinda iman din tayi masa ne ko kuwa?.

          Murmushi kawai yayi ya kada kai,cikin nutsuwarsa da muryarsan nan mai


dauke da wani irin sound yace

"Ko a lahira wani yana cin albarkacin wani bare gidan duniya,diyar data fito daga
tsatson inna da malam tafi qarfin na rama mata sharri da sharri,koda abunda tayimin
yafi haka girma da muni,aurenta ne bataso nayi.....kuma na yiwa kaina wannan
alqawarin yadda bataso har abada aure tsakanina da ita,Allah ya tabbatar da ita
gidan mijinta,ya basu zaman lafiya me dorewa" binsa kawai da kallo sadiqu
yayi,yanajin kimar amin din tana daduwa cikin ransa da idanunsa.

         Daga ita har malam din rasa bakin magana sukayi,saboda ko su ba zasu iya
yi mata kayan da suka kama qafar haka kyau da tsada ba,kunya duk ta cikasu,imanndin
ta qishi,shi kuma ga abinda ya saka mata dashi nan,daga qarshe yaa gana ce tasa aka
yiwa bassam magana kan za'a zo ayi jere,yace ya gama komai,sam ya gana tace sai an
jera mata,ya debe wasu daga cikin nashin,hakanan aka kai kayan gidansu bassam,inda
mom tace anan zata zauna.

        Duk da cewa kayan sunyi iya qurewar gatan yarinyar da iyayenta ke da


matsayi irin nasu malam,amma su fahima da suke qanne ga bassam da kuma yayunsa tabe
baki sukayi sanda sukaga zatin kayan,saidai kuma sauran da bassam din yayi wanda
basusan shine yayi ba shi ya hanasu tankawa.
           Biki aka shiga gudanarwa gadan gadan,irin bikin da yake burin 'yammatan
yanzu,bikin da ya dauki hankula,yaja magana a social media qwarai da
gaske,hotunansu suka dinga shiga wayoyin jama'a,loko da saqo,biki bassam din yayi
na kece raini,yayi barnar kudi kamar baisan ciwonsu ba,abinda ya bata ran momy
qwarai,tsana da kuma haushin iman ya cikata tun bata kai ga shigowa gidan ba,ta
yaya yarinyar da bata isa ba,bata kai komai ba bassam din zai xauna ya dinga kashe
mata kudi haka?.

        K'arfe tara na dare ya samu ya kutso zuwa dakinsu dake soro,hannunsa riqe
da baqar leda,wadda ke dauke da dinkin riga da wando da 'yar ciki na dakakkiyar
shaddar da ya zuba kudade masu nauyi ya siyeta,ya kuma kashe kudade masu yawan
gaske akayi mata aikin hannu gabanta da bayanta.

         Duk yadda inna taqi taro amma hakan bai hana gida samun baqi ba,saboda
wasu da yawa sun rugi sun taho bikin ne saboda labarin irin mijin da zata aura da
ya kai musu
#zafafabiyar
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: *25 A*

_AM SORRY,ASHE AN SAMU TSALLAKE,GA MISSING PAGE DIN NAN,AMMA NA YAU DANA GOBE NA
BAKU KENAN,ASHA KARATU LAFIYA_

25

Cikin matuqar dauriya da juriya yaketa attending baqin da sukazo domin


malam,da yawa mutane sunata yi masa Allah ya sanya alkhairi,ga zatonsu shine
angon,ya buga kyau babu qarya,don dole idan kazo wajen ka zaci shine angon da gaske
din.

Kusan a idanunsa tawagar bassam suka iso,cikin tawagar motoci na kece


raini,hadi da tarin dubban al'umma,wanda hakan zai tabbatar maka ba qaramin gangami
angon yayi ba,ya dauke idanunsa daga sashen da suke,zuciyarsa na qara yawan adadin
bugawarta.

Shuru yayi yana jin tamkar ana dura masa hayaniyar jama'ar dake wajen
cikin kansa sanda lasifiqar dake wajen ta yada muryar mutumin dake sanarwar cewa an
biya sadakin hajar ibrahim khalil wato iman din naira dubu dari da hamsin da kuma
galleliyar sabuwar mota,daga nan liman ya zarcw da sigar daurin aure.

Kamar wasa yaji qafafunsa sun gaza daukarsa,a hankali yaji kamar yana
sulalewa,duhu ya soma sauka a idanunsa,abu na qarshe da ya iya gani fuskar sadiqu
daya taroshi yana qwala masa kira,daga haka komai ya tsaya masa cak......

********Tunda suka fito daga gidansu take wani irin kuka,bayan ta gama kukan da
saika tsammaci wa'adin rayuwarta ne ya qare,har zuwa sanda ta zame tana roqon inna
ta gayawa malam ta fasa auren,don sam bata samu ganin malam din bama,saboda yana
can asibiti wajen al'ameen,ita kanta innar

"Allah ya bada sa'a" kalmar data gaya mata kenan,tana qoqarin yafa mayafinta don
wucewa asibiti wajen al'ameen da aka kwantar tunda safen.

Ko a cikin motar kukan take kamar babu gobe,gaba daya komai yafita a
ranta,hakanan hankalinta a tashe yake,saidai dukkan wanda zasu bata baki sunyi iya
abunda zasu iya,basusan dawar garin ba,saima suka hau mata shaqiyanci kan gobe iwar
haka inda zakaje gidan ragal da ita,su bazasu iya ba,angon ya qarasa rarrashinta.

Babu wanda bai gigita da irin kyau girma da tsaruwar gidansu bassam
ba,don duk yadda suke hasashe ya wuce nan,kai tsaye suka nufi part din mom da
ita,kamar yadda yake a al'ada,kaiwa uwar miji matar danta,matuqar basu da nisa da
juna ko kuma cikin gida daya kamar haka.

Saidai kuma dab da zasu qarasa qofar sashen aka taresu kan su wuce da ita
sashenta,basai an kawo mata ita ba.

Kallon kallo aka hauyi,kowa da abunda ya fahimta,hakanan kowa da abinda


yake saqawa cikin ransa ko kuma shifa abokin tafiyarsa,haka suka juya da iman din
zuwa sashenta kamar yadda mom ta buqata.

*_BAYAN AWANNI UKU_*

A hankali hawaye keci gaba da sauka daga idanunta,wani irin mutuwar jiki
da bacin rai dukka sun mamayeta,musamman idan ta tuna irin sallamar da sukayi da
inna,malam kuwa dama bataga idanunsa ba bare ya sadiqu,uwa uba kuma lamin dake
asibiti batasan a wanne hali yake ciki ba,saidai kuma ta wani sashen ranta yakanyi
mata sanyi,musamman idan ta tuna da irin alqawuran da bassam yayi.mata da tanadin
kulawa a irin wannan daren.

zuwa lokacin sashen nata yayi tsit,saboda kowa ya watse ya kama gabansa,babu
qarar komai saita babban engine da ake zubawa disel wanda shike bawa dukkan gidan
wuta,tana

Tun tana sharar hawayen tana kuma dakon shigowarsa,har hawayen suka
kafe,tsoro kuma ya mamayi shurun,saita sake curewa waje guda tana sake sakin wasu
sabbin qwallar.

Tun tana daga idanu tana duba lokaci har idanun nata suka fara nauyi,sabida
gajiyan data tara a jikinta na kwanaki bakwai,a hankali baccu ya rinjayu juriyarta
yayi galaba a kanta,ta sulale nan gefan lallausan gadonta ta fara bacci ba tare
data sani ba.

Can cikin barcinta taji kamar ana taba qafafunta,abunda ya zaburar da ita
kenan ta farka a firgice,suna hada idanu da bassam dake kanta saita sunkui da kai
qasa,yana tsaye riqe da babbar rigarsa ya zuba mata idanu,saidai akwai yanayi a
launin idanunsa,kamar wanda yayi barci ya farka

"Bacci zakiyi baki sauya kaya ba,hala kin gaji da jirana ko?,abokaina ne suka hada
wani dinner iya mu imu,ga wannan,nidai bacci nakeji,saida safe" yayu maganar yana
ajjiye mata ledar daya shigo da ita ya nufi saman gadon ya fada akai.

Waiwayawa tayi da kanta gefan da ya kwanta din,yayi dai dai saman gadon,da
alama da gaske yake bacci zaiyi,don har ya cusa kansa qasan pillow abinsa ya fara
sauke numfashi d'ai d'ai.

Mamakine ya cikata sosai,wanne irin ango ne haka?,ko 'yar sallar nan ta


daren farko ma bai damu yayita ba?,ta maida dubanta ga ledar da ya shigo da ita
din,sai ta matsar da ita kawai gefe,ta miqe ta lalubi toilytayi fitsari sannan ta
daura alwala,ta dawo saman gadon tankwanta daga ca daya gefan.

Ta jima zuciyarta tana mata saqe saqe kafin bacci yayi awon gaba da ita.

Koda ta farka da asuba saita taras har yanzu baccinsa yake,tayita qoqarin
tashinsa yana sake juyi yana kwanciya,daga qarshe fincikota yayi cikin jikinsa ya
matseta,tayita kiciniyar qwace kanta amma ta kasa,haka ta haqura,tana ji tana gani
daga shi har ita sallar asuban ta wucesu.

11:02 AM
Ko ina na gidan tabi tadan kakkabe inda yayi qura ta kuma badeshi da
turaran wuta bayan tayi wanka ta kuma sabunta kwalliyarta cikin atamfa,ganin har
sanda ta gama din babu wani abu da zasu karya dashi saita shiga kitchen,ta soya
qwai ta dafa ruwan tea,tana jerewa saman dining ne bassam.ya fito yana amsa
waya,daga shi sai singlet da gajeran wando,tadan waiwaya ta kalleshi,sai ta dauke
idanu taci gaba da abinda take,da alama bai jima da farkawa ba sannan yayi salla.

Inda take ya qaraso,ya jata jikinsa ya rungume yana ci gaba da amsa


wayar,wannan ya bata damar jin muryar wanda suke wayar dashi,muryar macace,saidai
bata iya jin me take gaya masa,suna a haka har ya vama wayar,ya ajjiye nan saman
table din da suke tsaye daura dashi

"Amarya bakya laifi"


"Ina kwana" ta gaidashi cikin girmamawa

"Lafiya lau,me aka dafa mana" yayi maganar yana miqa hannu ya bude kwanukan

"A'ah,ba'a kawo abinci daga cikin gida ba?"


"Eh gsky,ban sani ba ko ina ciki an buga anji shuru" daukar wayar tasa ya kira mom.

Ciki ciki ta amsa gaisuwar tasa,ba tare data bari ya dora da maganarsa ba
tace

"Ku ba'a isa ku shigo ku gaida mutane ba kenan"


"Yanzu muka tashine mom,na tambayeta ma an kawo abinci tace a'ah"
"Waye bawanta?,idan zata tashi ta girka ta tashi ta girka da kanta" saita datse
wayarta abunta

"Oh shit" ya fada yana cije baki,ya sake aje wayar sannan ya saketa ya zagaya ya
zauna yana cewa ta hada mishi tea din.

Kadan kadan take kurba cike da baqunta,shi kuma wanda zai sanyata ta saki
jikin tunda suka zauna yake amsa waya kala daban daban,har sai daya kusa gamaw
sannan ya sauke wayar,ya dubeta yana murmushi

"Saifa kinyi haquri,nidin mutum ne mai jama'a,mai kuma busy sosai,mutane na ne na


Media suke congratulating dina" dan qaramin murmushi kawai ta saki tana gyada kai.

To a yanayin gidan amarya da yake da farinjini banda gidan iman din,don


kuwa babu kowa a sashen nata,koda kuwa 'yan cikin gidansu bassam din,shi kansa daga
bisani kiransa akayi daya daga cikin abokansa,ya shirya cikin dakakkiyar
shaddarsa,yayi kyau sosai kamar kowanne lokaci,tana dubansa bayan ta gama tayashi
ya shirya tana fesa masa turare

"Ya kamata mu shiga ciki kafin ka fita mu gaida mom ko?"


"Sai na dawo tukunna"
"Zaka biya ya wajensu inna ne?" Ta tambayeshi,don tana zaton zasu gaisuwar surukai
ne kamar yadda al'ada ta tanada

"Kai,bana jin haka gaskiya" da wannan amsar yayi gaba bayan ya danyi kissing bayan
hannunta,tayi masa a dawo lafiya,saidai tana mamakin me yasa bazai qarasa gidan
nasu ba.

Shuru ita daya a sashen,sai tv dake aikinta,duk da cewa gidan sabone a


wajenta,amma ko sau daya batayi sha'awar bari ta tashi ta zagaya taga ya gidan yake
ba,haka kawai takejin jikinta a mace,sam babu wani karsashi ko walwala tattare da
ita,ta dauki waya ta kira inna ya kusa sau biyar amma bata daga ba,so take taji
dama yaya jikin lamin,ganin bata dauka ba saita maida akalar kiran wayar sadiqu,shi
wayar tasa ma a kashe take,malam shine na qarshe data kira,cikin sa'a kuwa ya
daga,saidai daga gaisuwa bai sake barin wani abun ya hadasu ba ya kashe wayarsa.

Tana cikin wannan yanayin su munira ita da qawayenta suka iso,abunda yadan
motsata kenan,har ya rage mata damuwar da take ciki,cikin lokaci kadan suka cika
gidan da hira,sunata tsokanarta gami da zolayarta kamar dai yadda akasan qawayen
amarya kanyi idan sunzo gidan qawarsu sabon aure.

Su munira ne kan gaba,aka shiga kitchen aka shiga dafe dafe,lafiyayyen


abinci sukayi,aka fidda kula aka zubawa bassam nashi,daya daga cikin qawayen nasu
ce tace

"Amma dai ki dinga saka sanwa da mamansa,duk da suna da wadata da dadi ki dafa ki
aika mata" harara munira ta jefa mata

"Kinjiki da wani abu,su masu kudi ina sukasan wannan,babu ruwansu,dadin auren gidan
wadata kenan,nasuma basi gama cinyewa ba bare su saurari na suruka".

Ta sake sosai taci abincin a cikinsu muniran,ta sake wanka tayi


kwalliyarta dakyau,wanda hakan yayi masifar fidda kyanta,kamar ka saceta ka gudu,ga
kyan quruciya da halitta ga na amarci.

"Kannensa sun shigo kuwa?,suna da kirki ko?"munira ta tambayi iman sanda


suka kebe,abinda yaketa bawa iman din mamaki kenan tun dazu,babu wanda ta gani daga
cikin gidan,ko don itadin bata shiga bane

"Ko fuskan mamansa ban sani ba har yanzu"


"Karki damu tunda zaku shiga anjima,kinsan su masu kudi basu danu da rayuwar kowa
ba,surukutar ma ba kasafai ake yinta ba,musamman aka hadu da 'yan boko,su kuma duk
sun hada" amsar muniran tadan kwantar mata da hankali.

Suna tsakiyar hirar bassam ya shigo,ya zuba mata idanu saboda yadda tayi
masifar yi masa kyau,ya bude mata hannayens babu ko kunyarsu munira,hakanan itama
ta isa gareshi saboda kada ta kunyatashi,ya rungumeta tsam a jikinsa yana fadin

"Kinyi kyau beauty,kina da kyau baby" ba shiri su munira suka fara lalubar jaka
zasu tafi,kudi masu tsoka ya basu wanda ya sake gigitasu,ya kuma sanya driver ya
maida kowaccensu gida.

Ita taimaka masa yayi wanka kamar dazu ya kuma shirya yaci abinci,a lokacin
ta sake matsa masa su shiga ciki su gaida mom,yace ta dauko mayafi suje.

Tun daga shigarta ta tadda qannensa kafin fitowar uwar gayyar wato mom tasan
cewa bata karbu ba,ba'a kuma maraba da ita,'yammata hudu ta samu a parlor din suna
kallo,saidai kaf dinsu babu wadda tayi mata duba biyu bare ta saka ran zasu
gaidata,hakan baisa ta kasa gaidasu ba,saboda ta lura biyu daga cikinsu zasu girme
mata,biyun ne zasuyi sa'anni.

Sama sama suka amsa kamar wadanda aka yiwa dole,bassam din ya jefesu da
harara

"Wanne irin iskancin banza ne wannan,kunaji ana gaidaku" daya daga cikinsu ce wadda
ke riqe da tab tana ta faman danne danne ta waiwaya ta masa wani irin kallo

"Tunda mun amsa ai fine"


"Shut off......" Yadan fada mata a tsawace,sai kawai ta miqe ta sauko daga saman
kujeran da take kai tana quna quni tayi ciki abinta,sauran ma sai suka fara binta
daya bayan daya,kafin daga qarshe mom ta fito.
Kallo daya zakayi mata kasan cewa hamshaqiyar macace da taci ta tada
kai,takeji da izzar kudi da kuma isa
"Sai yanzu kuka ga damar zuwa gaisheni?" Mom ta fada tana zama cikin luntsuma
luntsuman kujerun da ta kusa nutsewa a ciki
"Tunda na fita ban dawo bane sai yanzu" ya amsa mata hankalinsa nakan wayarsa
"Ita 'yar mulkin ba zata iya zuwa da kanta ba saika sanyota a gaba kamar 'yar gidan
sarakai?" Tayi furucin bata ko dubi sashen da iman din ke zaune na,mummunar faduwa
gaban iman yayi,fargaba ta saukar mata,jin bassam baice komai ba saita motsa,cikin
girmamawa ta qarasa gabanta ta duqa tana gaidata cike da surukuta da girmamawa,wani
kallo ta debo tayi mata shi sama da qasa,duk da cewa a zaune take,kana ta amsa mata
da amsawa guda daya tak,sannan ta dauke kanta ta tattara hankalinta kan danta suka
shiga hirarsu abinsu,kamar ma sun manta da ita,kamar ma Allah baiyi wanzuwarta a
wajen ba,sai data gaji don kanta qafafuwanta suka fara tsami sannan ta nemawa kanta
wajen zama.

Awa daya babu wani abu a ciki sannan mom ta waiwayo inda take

"Da Allah dan kauce daga nan,muna magana" jikinta a mugun sanyaye ta dan dubi
bassam,sai taga hankalinsa yana kan wayarsa,ta miqe a hankali cikin girmamawa tace

"Sai anjima mom" ci kanki batace mata ba,saima dogon tsakin data bita dashi sanda
take fita daga falon,don kyau yarinyar tana da kyau,saidai kuma ta samu tawaya ta
fuskoki biyu,na farko gidan data fito din bai cancanci ace kamar bassam ya auri
diyar gidan ba,na biyu kasancewar mahaifinta malami,batason ya zamana bassam din ya
auri matar da zata mallake mata d'a,wanan dalilan yasa gaba daya taji iman din
batayi mata ba.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 26

Kwanciyarta tayi daga gefe guda na dakin bayan ta gama addu'o'inta,tana jinsa
yanata motsi har zuwa sansa ya jawota jikinsa

"Wai fushi ma kikeyi?"kanta ta girgiza

"Idanma nayi fushi nima ban kyauta ba dana daga maka waya,kayi haquri,amma maganar
hijabi,bazan iya daina sakashi ba,dashi aka tarbiyyanceni" tsaki taji yaja

"Su tarbiyya manya,nidai indai kinason farantamin ga abinda nace dake nan" abinda
ya fada kenan,daga haka dukansu kowa yaja bakinsa yayi shiru. Daren ranar
jagwalgwalan da ake matan ma ba'a yishi ba,itama hakan sai yafi mata dadi,saboda ko
babu komai ta kwana cikin salama.

To tun daga waccar ranar ya koyi yawon dare,idan ya dawo daga aikinsa,yaci
abinci wanka kawai zai sakeyi ya fice,bashi zai shigo gidan ba sai qarfe daya na
dare wani lokacin har biyu yakan iya kaiwa,wani lokaci ko sallar isha'i sai ya dawo
zaiyi.

Abun ya shiga cikin jerin abubuwan dake dagula mata lissafi a rayuwar
gidan,ta kuma rasa inda yake zuwa,tayi masa duk abinda ya dace don tasan inda yake
zuwa amma amsa daya ce,aikine yake riqeshi,daga baya ma data dameshi sai ya daka
mata tsawa,ya kuma ce mata shi ba danta bane,kada ta sake gigin masa wannan banzar
tambayar,sanda yake gaban mom ba ba'ayi masa wannan sanya idanun ba bare yanzu da
yake da 'yanci

"Ni banason takura da sanya idanu,wannan ne yasa na auroki tun kina sha takwas
bakikai ashirin ba" wannan maganar tasa ta tsaya mata a wuya,me yake nufi?,me
maganarsa take nufi?,bata da wani abokin shawara duk duniya sai munira,amma a
wannan karon sai ta gaza furtawa muniran abinda yake damunta cikin gidan nata,koda
yaushe idan suna chart gaya mata take komai lafiya
"Shegiya iman,an samu duniya,muma Allah ya sanyamu a danshinku,Allah yasa kada ki
canza qawaye nan gaba matan manya a manta damu,inason zuwa amma jarabawa ta
hanani,umma ta dage sai na fidda result masu kyau idan inason aure bayan candy" sai
a lokacin taji wata kewa ta makaranta ta kamata,ya akayi tayi sakacin da maganar
karatunta tasha ruwa?,ta tuna irin yadda ya al'ameen yasha gwagwarmaya akan
karatunta,gwagwarmayar da ko nashi karatun bai maida hankalin ya yiwa ba,ta sauka
daga chart din,ta lalubo number wayar inna a karo na barkatai ta kirata.

Daf da zata tsinke aka daga,don har ta fitar da rai da za'a daga
din,satinta biyar da xuwa gidan,amma sau daya tak ta taba kiranta ta amsa sai
wannan karon.

Tanajin sallamar innar hawaye suka sauko mata,cikin rawar murya ta fara
gaidata,innar ta amsa a dake kamar anyi mata dole,daga haka shuru ya biyo baya

"Sai anjima" inna ta fada tana datse wayar,saidai can wani saqo na zuciyarta taji
yana matsewa,muryar iman dinta ba haka take ba,tabbas ta canza.

A lokacin suna tare da al'ameen wanda ya ajjiye takardun daya shigo


dasu gaban innar

"Amintacce......da alama bakinka akwai labari" inna ta fada cikin fara'a


sosai,saboda ta hangi wata walwala mai yawa a fuskar al'amin din,abubuwan da suka
farun sai suka sake zama kamar wani mabudi na qarin kusanci da fahimtar juna
tsakanin alameen din da inna

"Allah yayi inna....na samu tallafin karatu zuwa qasar dubai" idanu inna ta fitar
sosai,gaba daya bakinta yaqi rufuwa

"Kaiii....Alhamdulillahi,Allah mun mun gode maka,Allah kaine Allah,Allah ka qarawa


annabi muhammad daraja,aminu?,abun ya tabbata?" Kai ya gyada murmushi cike fal
fuskarsa

"Wallahi inna,don har na haqura na fitar da rai"

"Rabon kwado ai baya taba hawa sama aminu,kuma ita addu'a babu abinda ta bari" sai
taja takardun ta dudduba iya abinda zata iya ganewa a ciki,tayi masa addu'a sosai.

Sun dan jima suna tattaunawa shida inna kafin ya dauki takardun ya wuce
daki,saboda yace tun yanzu zai fara shiri,don tafiyar tasu ba zata wuce sati hudu
masu zuwa ba in sha Allah.

Iman ce mutum ta farko data fara fado masa a rai sanda scholarship din ya
samu,amma yayi gaggawar tsigeta daga ransa ya ajjiyeta a gefe,saboda ya riga da ya
yiwa kansa alqawarin sake sabuwar rayuwa da zai shafe babin iman kwata kwata daga
cikinta,tun sanda aka sallamoshi daga asibiti bayan baqar wahalar da yasha ta sati
daya,ya kuma dawo gida yayi jinyar sai biyu.

*******jaye take da trolley dinsa tana biye dashi a baya,yayin da shi din
kuma yake sanye da wasu rantstsun suits masu bala'in kyau da daukar idanu.

Tana biye dashi tana mamakin yadda sam hankalinsa bai kanta,a matsayinsa na
magidanci kuma sabon aure wanda bai dorar da komai cikin rayuwar auren ba,zaiyi
tafiya ta wata guda cur,amma babu ko alamun damuwa tattali ko nuna kulawa saboda
zai tafi yabar amaryarsa agida,sai faman amsa waya ma da yakeyi,har suka isa inda
motar da zata kaishi airport ke jiransa.
Sai daya shiga motar kafin ya rufe sannan yadan dage wayar daga kunnensa

"Allah ya kiyaye,ya bada sa'a,Allah ya kaika lafiya"

"Ameen.....ba wata matsala ko?"

"Eh to,waye zai tayani kwana,shine maganar da tun jiya nakeyi maka ita baka amsamin
ba"

"Ki shiga cikin gida ki roqi fahima ko fairuza wata tazo ta dinga tayaki......idan
akwai wata damuwan kada ki damu,ki bude locker din cikin dakina ta gefan gado,key
din na jiki,ki dauki adadin abunda yayi miki,saina dawo" daga haka yaja murfin
motar ya rufe.

Kasa daga qafafunta tayi daga wajen,sai hannyenta data goya tana bin motar
da kallo kawai,inama yadda yake sakar mata kudi farinciki yake bata haka?,inama ace
nutsuwar zuciya da ruhi take samu har haka gurinsa,sam kwata kwata batajin wannan
ruhin na matan aure cikin jikinta,tana jinta wani salaf tamkar tana
gida,kai......akwai tarin bambance bambance ma a yanzun kan zamanta a gidansu da
kuma wannan gidan,saidai kuma.....ta yaya zata daidaita wadan nan al'amuran?,ta
yaya zata koma tana jin kanta da ruhinta kwatankwacin yadda kowacce mace takeji
cikin gidanta,kamar yadda takejin matan aure na hira cikin group nasu na WhatsApp?.

Sai data shiga sashen nata sannan ta tabbatarwa kanta mawuyacine ta iya
kwana ita daya kamar yadda ta kwatantawa ranta,saidai kuma.....ta yaya zata tunkari
wadancan mutanen,wadanda suka kaita gefe daya suka ajjiye,sam basa tuna ma akwai
wata halitta me rai ta dan adam a wajen?.

Tana tsaka da wannan tunanin sallamar munira ta katseta,taji matuqat


mamakin ganinta,suka saki juna bayan sun gama murnar ganin juna,muniran na qare
mata kallo

"Me zan gani haka?,ke ko 'yar qibar nan ta amare da akeyi ke babu ke?,sai kyau
kawai da fatarki ta qara" baki kawai iman din ta tabe tana miqewa

"Me zan kawo miki?"


"A'ah muje,yau saina zaba na darje,sai nayi qara'in abinda na dade banci ba" tayi
maganar tana miqewa,dariya dukka sukayi suka rankaya kitchen.

Tsaye tayi kawai daga gefe tana kallon yadda muniran ta rude,taketa santin
babu ce kawai babu cikin kitchen din,ita batasan ko sau daya daga alatu har cimar
dake cikin kitchen din ba dai dai da rana daya bata taba ci ko amfani dashi ba taji
ya tsarga mata ba ko yayi mata dai dai

"HANGEN DALA FA BA SHIGA BIRNI BACE(huguma) munira" cikin rashin fahimta ta waiwayi
ta dubeta"

"Kamar yaya?" A wannan gabar taji ta kawo maqura kuma iyakar da dole kwanyarta ita
kadai ba zaya iya wannan ayyukan ba,don haka ta fayyace mata komai,illa ta suturta
maganar rashin iya yin komai a gado da bassam din bayayi.

"Mtseww,ni wallahi idan nice ke wannan ba matsala bace a wajena,indai zanci


nasha na qoshi,nayi wadaqa da kudina duk su suka jiyo,ke kuwa cikin wadan nan
abubuwan dana lissafa babu wanda kike da matsalarsa,yawon daren bassam,yawan
mu'amala da waya fiye dake,rashin baki isashen lokacinsa,wannan duka damuwoyin
kansa ne ba naki ba,wasu danginsa sa sauransu ba case dinki bane kowa yayi ta
kansa,tunda babu abinda kika waiwaya kika rasa" girgiza kai iman dake goye da
hannuwanta tayi
"Ba zaki gane bane munira,zaman ya wuce ya baki abinci sutura da kudi,wannan duka
wani tunaninmu ne ashe na rashin sanin ciwon kai da kuma quruciya,kinsan da miji ya
baki naira dubu gwara ya baki minti dayansa?,ya kalleki duba na so qauna da
soyayya?,ya saurareki saurare na girmamawa da jin qai.....amma fa,duka wannan ga
macen datasan ciwon kanta ne,wai kuwa kinsan har yanzu bazan iya banbance miki mene
bassam yakeso ba da kuma abinda bayaso?,saboda har yanzu ban samu wani isashen zama
dashi da zai kaini ga fahimtar hakan ba?,ya tara kudin amma har yau nema yake,ya
kasa zama ya huta ko qaqa"

"Gwara yayita nema muku ai keda yaran da zaki zazzago masa" munira ta amsa mata
tana tura qatuwar lomar shinkafa wadda fiye da rabinta naman kaza ne data masa
gutsi gutsi.

Amsar da muniran ta bata yasa ta qare mata kallo a fakaice,saita gane


cewa muniran ba fahimtarta take ba,ba kuma zata gane ba,saboda ba'a cikin system
din take ba,don haka ta sakin zancen kawai,ta qyale muniran.

Sanda zata tafi ta bata kyautar dubu biyar,sosai muniran taji dadi

"Kai.....dadin auren me kudi kenan,yanzu irin wadan nan kina dasu nasan
bila'adadin,kiyita tara abinki kina aikawa dasu gida a sarrafa miki,kiyi kiyi kema
nan da nan ki kama qasa" munira ta fadi tana danna kudinta a jaka,murmushi kawai
iman din tayi,suka fito tana taka mata.

Da zasu wucw tayi tayi muniran ta rakata su shiga wajen mom fa tambayo
fahima ko fairuza tayin kwana munira tace bata shiga,saboda idan ta shiga suka mata
kallon banza ba zata bari ba,haka ta barta ta wuce,data dawo daga rakiyar saita
wuce sashen mom din ita daya.

Tana kutsa kai cikin falon gabanta na tsananta faduwa,saboda yau kuma
batasan da wacce fuskar zasu tarbeta ba,wacce magana zasu yayyaba mata,a haka dai
ta daure tayi sallama cikin lallausar muryarta tana saka kai cikin falon.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 27

Taci sa'a za'ace ko rashin sa'a,ta samesu su dukka hudun suna nan,uku
fahima,fairuza da nasma suna can saman dining suna cin abinci,ikram na zaune qasan
carpet cikin falon tana aiki cikin system,da yake ita din ta fara aiki a babban
kamfanin gidansu,momi ma na daga gafe tana fama da kallon news,idanunta saye da
glass din da iman din tafi kyatata zaton medical ne.

Kamar ko yaushe d qyar ta amsa sallamarta ta dauke kanta,ikram ma dake aiki


kallo daya ta mata taci gaba da aikinta bayan ta amsa sallamar,a haka duk cikinsu
ta fisu sauqi,kuma itace babba cikin matan,su kuwa sauran dake saman dining suna
kaiwa ciki suna hirarsu kamarma basusan ta shigo ba.

Ikram din ta fara gaidawa,ta amsa babu yabo babu fallasa idanunta akan
aikinta,saita qarasa ta gaida mom,ta amsa tana kallon tv abinta.

Shuru ya biyo baya kamar babu wata baquwar halitta a wajen,tamkar kaya suka
aje ko kuma kashi,bakajin komai sai sautin tashin hirar su fahima.

Sai data gaji da zaman kuramen sannan cikin yanayin dari dari da kuma
tsoro tace

"Amm....mom dama zuwa nayi na roqi alfarmar fahima ta dinga zuwa tana tayani kwana
kafin ya bassam ya dawo"

"Wait!....wait.....me nake jiyowa?" Muryar fahiman ta ratso tun daga inda take
zaune,sai iman din ta dubi sashen cikin mamaki,saboda ta zaci tun shigowarta
basusan ta shigo ba,ashe sunajinta.

Da wani irin taku fahiman ta sauko daga wajen,ta qaraso gaban iman ta tsaya
tsam a kanta,ta jefeta da wani irin kallo na raini da qasqanci sannan ta fara
magana cikin fada

"Lallai na yarda ni kadai kika raina cikin gidan nan,yanzu don Allah ki dubeni daga
sama har qasa......" Tayi maganar tana nuna kanta

"Kamar ni.....in tafi gidanki tayaki kwana?,ko don kina ganin kanmu daya?,to ai
hausawa sunce abanza wai talaka ya girmi sarki,ni ba tsararki bace,sunanki ya fita
daga bakina" hannu mom ta dagawa fahima

"Yafi da Allah" sai data ja mata dogon tsaki sannan tayi gaba taba gunagunan
maganganu

"Ke kalleni nan" mom ta fada tana duban iman din sosai

"Ina cewa a gidanku ke kadai kike kwana a dakinki,dakin da babu cikakkiyar qofa
ma,kinga nan gidan" ta fada taba nuna falon da yatsanta
"Kaf katangunsa dogaye ne masu qwari,babu inda ya zaizaye ko ya cinye,baya ga haka
akwai guards a gidan nan,sabida haka idan zaki wuce ki bawa mutane wake kije ki
koyi kwana ke kadai ki koya,don bassam ma bai fara tafiye tafiye ba idan
shine,banason wani iyayin banza da kwainane" jikinta babu laka ko kadan ta
miqe,tana takawa a hankali ranta a bace jikinta a matuqar sanyaye,tana iya jiyo
dogon tsakin mom din,sannan tace

"Gayyar tsiya arna a idi" kalmar data sanya hawaye suka silalo mata masu zafin
gaske.

Hakanan kuwa ta kwana ita daya a sashen kamar mayyar,fargaba tsoro da kuma
baqinciki sukayi mata qawanya,wani abu me kama da nadama ya fara sauko mata,har
yanzu har kuma kawo yau ba zata iya dorar da wani abu guda daya da zata ce ta samu
naci gaba ba a gidan farinciki ko walwala,banda tarin kudi da yake ajjiye mata
wanda batajin dadinsu ko kadan,sannan bata da abunyi dasu.

A haka a haka bassam ya kwashe sati biyu da yin tafiyar tasa,wanda tsahon
sati biyun nan idan tace sunyi cikakkiyar waya sau uku to qarya takeyi,kwata kwata
kiran da yayi matan ma sau ukunne,idan kuma ita ta kirashi sai yace mata yana wani
aikin,ko kuma yana kan hanya ko kuma zai kirata,kiran da bazaiyi mata shi kenan
ba,idan ta gashi ta online kuwa,ta tura saqo,sai iya kaiwa kwanaki biyu bai buda
ba,hakanan zai gama zamansa online baisan ko sallama ya turo mata ba,amma haka ta
dinga danne ranta tana gayawa kanta da gasken ne aikinne yayi masa yawa.

Ashe motsin mutum ma awaje koda ba zakuyi magana ba rahama ne,batasan da


wannan ba sai a yanzu da bassam din baya nan,su mom ta fuskanci ba kallon
cikakkiyar 'yar adam sukeyi mata ba,don har tafiya sukayi ta kwanaki hudu bata sani
ba,randa zasu dawo ta fita tadan tattaka cikin gidan saboda gajiya da tayi da zaman
waje gudan taga shigowar motarsu ana mata sannu da zuwa,batayi qasa a gwiwa ba ta
qarasa itama ta siga cikin 'yan sannu da zuwan,saidai ko kallon tsiya bata samu ba
bare tasaka ran samun na arziqi,haka ta juya ta koma sashenta gwiwa a sanyaye.

Sati na hudu da tafiyarsa gaba daya ta sake zabgewa,ta kuma rame,sai fari
data qara da kuma kyau da sheqi da fatarta keyi,a sannan ya turo wani mutum da zai
dinga zuwa yana koya mata mota duk yammaci cikin gidan,haka kuwa akayi,sati biyu
kacal iman din ta qware sosai,hannunta yafada,har ta fara hawa saman titi tana
shawagi titunan gefannin unguwarsu ta dawo,hakan shi ya fara rage mata kadaici da
kuma dauke mata hankali,saidai kuma tana shan kallo,abinda yasa tasa aka maida mata
gilasanta tint.

Ranar ta gwada kiran bassam tace masa zataje gida,domin zuwa lokacin
haqurinta ya qare ya gaza,innarta kawai takeson gani,tana shiryawa amma kuma
fargaba ce fal ranta,saboda batasan irin tarbar da innar xatayi mata ba,hakanan fa
shirya tsaf cikin wani lafiyayyen lace na alfarma,ta debi kudi masu dama ta zuba
ajakarta.

Tana tafe tana duba hanya,harta riski wannan babban store,anan ta tsaya ya
loda siyayya me yawa ta kayan abinci me yawa,da kayan maqulashe,irin abubuwan da
tasan malam da inna naso sannan tayi hanyar gida.

Tun daga nesa ta fahimci yau ba'a zauna karatu ba,saidai kuma akwai
dalibai dai daiku cikin rumfar gidan nasu suna harkar gabansu,a hankali ta sako
motarta cikin layin nasu,ta daidaita motar daidai qofar gidan,sannan ta bude ta
fito.

Da murna daliban malam din sukayo wajenta,musamman wandanda suke dan dasawa
dasu suke mata wanki da sauransu,ta fidda jakarta tayi musu rabon 'yan 200 sababbi
fil,sannan tabar musu booth din motar a bude,tace su debo duka kayan ciki su shigo
mata dashi ciki.

A hankali idanunta suka sauka a qofar dakin dake garqame da muqulli,ta


tsurawa qofar dakin idanu har zuwa sanda tazo zata gifta qofar dakin,ta lumshe
idanu gabanta ya fadi saboda wani qamshi data shaqa,qamshin turaren ameen ne da ya
kama dakin fiye dana ya sadiqu yake ratsowa ta labulen window din dakin dake
bude,taci gaba da saka kai zuwa cikin gidan gabanta naci gaba da faduwa har ta
bayyana a tsakar gidan.

Fes tsakar gidan yake kamar kowanne lokaci,tsahon watannin yana nan yadda
yake,babu wani abu daya canza,don ko lokacin bikinta ko fenti ba'a yiwa gidan ba
bare wani abu makamancin wannan.

Sallama biyu tayi,ana ukun ta jiyo inna daga rumfarta tana amsawa,taci
gaba da tafiya har zuwa bakin rumfar,ta sabule takalmanta,ta saka kanta ciki
bakinta dauke da sallama.

Sak inna dake saka ruwan pure water a sabuwar qaramin fridge dake kusa
da qofa ta tsaya tana duban iman din,da alama tayi mamakin ganinta,sai kuma ta
share,ta hade fuskarta waje guda taci gaba da abinda takeyi,kamar bata ganta
ba,babu wani reaction najin dadi akan fuskar innar.

Har ta qaraso ta zame tana gaida innar bata bar abinda take ba,ta amsa mata
dai taci gaba da saka ruwan,dakin ya dauki shuru,sai motsin yara dake shigo da kaya
a tsakar gidan,wanda inna batace komai ba tunda tasan muryoyinsu,ta dauka wani abun
suka shigo yi.

Tana gamawa fa rufe fridge din,ta dawo saman daya daga cikin kujerun ta
dauki carbinta,sai tayi hanyar fita abinta ta fita daga dakin zuwa kitchen ta kama
ayyukanta.

Wasu zafafan hawaye ne suka tsattsafowa iman tana daga zaunen,yanzu


innarta ce tayi mata wannan shakulaton bangaron?,innarta da suke zama suyi hira da
ita?,innarta dake bata kulawa?,innarta dake gaya mata yadda zatayi
kewarta?.....kece sila.....ke kika ja. Wannan itace amsar da zuciyarta ta
bata,saita miqe cak tabi baya innar.

"Kawo inna na wanke miki" ta fadi tana qoqarin amsar kwanukan dake hannun
inna
"Ni shegiya.....rufamin asiri,barni da kayana,ina ni ina saki aiki hajar?" Kalaman
sai suka yiwa iman din girma a kanta,gaba daya saita kasa ci gaba da riqon
kwanukan,ta samu gefe ta sulale ta zauna.

Sam inna bata lura da kayan ba sai data gama zata koma kitchen

"Ke meye haka?waye ya kawo wadan nan kayan?"

"Nice inna" ta fada bakinta nadan rawa,tana addu'ar Allah yasa kada innar ta
wofantar dasu taqi karba

"Maza maza kafin ma malam ya shigo ya sabar miki kisa a fita dasu daga gidan
nan,don bamu da gurbin ajjiyesu,jiya jiya aminu kafij ya tafi yabar mana abincin
rabin shekara,babu abinda muke buqata,shida sadiqu sun ishemu rayuwa"

"Ina ya ameen din ya tafi?" Tambayar data fara zuwa mata ka kenan,bata ta
sababin da innar keyi,sai daga bisani da fadan innar ya tsananta hankalinta ya dawo
kai

"Don Allah inna kuyi haquri,don girman Allah" wani kallo ta watsa mata

"Haqurin me?,me kikayi mana?" Kasa bata amsa tayi,sai qas datayi da kanta hawaye na
sauka,lokaci daya gaba daya duniya ta daina mata dadi,ta daina jin wani dandano ko
dadi nata.

Duk sababin da inna keyi hakan bai sanya ta tashi tasa an kwashe kayan
ba,har zuwa sanda ta jiyo muryar malam yana sako kanshi cikin gidan,mummunar faduwa
gabanta yayi,ta ambaci sunan Allah tana daga kanta a gigice sanda taji ya ambaci
sunanta,kafin ya iso ta miqe tsaye tana dakon isowarsa.

"Zoki wuce ki koma gidanki,can ne wajen zamanki,mu basai kinzo kin


gaishemu ba,wadan nan kayan da kika zo dasu kuma bamu da wajen ajjiyesu,abunka da
gidan talaka me nema,uwa uba kuma ya hadu da yaro me hazaqa daya cika masa dan
rumbunsa da abincin watanni shida,don kada ya tafi ya barshi da yunwa.....ungo
wannan" ya fadi yana miqa mata 'yan 200 din tari,wanda tana ganinsu ta gane wadanda
ta rabawa almajiran ne,kenan karbosu yayi

°°"200 ce babu a ciki,wadda kika bawa habu,ya fita aiki,amma ga wata


madadinta,saidai ita din tsohuwa ce,idan kuma bakison tsaffin kudi kiyi haquri,idan
ya dawo zan karba na ajjiye miki sabuwarki,duk randa Allah ya hadamu saiki karba"
sulalewa tayi a wajen tana sakin kuka tare da roqon malam ya barta ko azahar ne ta
qarasa kaiwa,amma baibi ta kanta ba,hasalima yaran ya kira,yasa suka dinga jidar
abincin suna maida mata boot din nata,inna na kitchen,yadda batace tak ba,hakanan
bata waiwayosu ba,har ta gama roqarsa,ta sanya mayafinta da takalminta ta fita.

Tana tuqin tana sharar hawaye,har taso ta tafka shirme,sai da tayi parking
gefan titi tadan daidaita kanta sannan taci gaba da tafiya.

Koda taje gida kwance kawai tayi taci gaba da kukanta,ba wanda ya damu da
ita bare ta saka ran zaiyi cigiyarta,hasalima sanda tacewa mom din zataje gidan
cewa tayi me zatayi mata,kudine?....idan shi take buqata ta tabbatar danta ya
ajjiye mata su,tunda tasan dama nan sukafi kauri,maganar data sanyata cikin
alwashin ba zata qara gayawa mom din ba din zata fita zuwa gida.

hatta da kayan cikin motar ta barsu batabi ga kansu baba ita ta tashi ba
sai gab da magarib,tunda dama tana fashin sallah ne.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 29
Lokacin da bassam din ya shaida mata dawowarsa tayi dukkan wani shiri na
tarbarsa,kama daga gyaran jiki qunshi da kuma gyaran gashi,hakanan ranar daya
shaida mata cewa jirgin qarfe hudu xasu sauka ta shirya lafiyayyen abinci kala kala
duk na taryarss,saidai tun sanda ya shigo din,banda qarar shigowar motocinsa babu
abinda ta sake ji,tun tana duban hanya har ta sare,don da alama sashen mom ya wuce
direct.
A hankali abincin data jera zafinsa ya zagwanye,kwalliyarta ta fara
sulalewa tana yin nata guri,har bayan sallar isha'i,tayi kwance lamo saman doguwar
kujera ita daya tana hadiyar zuciya.
Sha daya saura na dare taji ya turo qofar ya falon,tana daga kwance ta daga kai
kawai ta dubeshi,bacin rai ya hanata mata motsawa bare ta tarbeshi,sai taci gaba da
kwanciyarta kawai,har zuwa sanda ya qaraso kanta ya tsaya
"Ke!" Ya kirayi sunanta da kakkausar murya,a mamakance ta daga kanta ta dubeshi
"Kina jin mutane,su dawo daga doguwar tafiya irin wannan amma ki kasa zuwa ko sannu
ki musu,me kike nufi?" Gani tayi ya gama raina mata hankali ma,daya shigo baiko
kula da yanayin daya sameta a ciki ba zai dirar mata da fada,saita miqe ta zauna
sosai saman kujeran
"A ina na gankan banda yanzu?"
"Ok....amma kinsan ina sashen mom ko?,ba zaki iya shiga can ba ki sameni,da gaske
mom take kenan da tace baki qaunar rabarsu,don baqin halima tsahon watannin da nayi
amma ace ke daya kike kwan?" Kanta ne ya daure sosai,maganar ta bata mamaki,wanne
sabon salo ne haka kuma aka fito dashi cikin gidan,me dame mom ta shirya masa na
maganganu,sai zuciyarta ta bata shawarar ta sauko ita,saboda batasan me dame ta
gaya masa ba wanda zai iya tunzarasu shi da ita
"Ba haka bane,tunda naga kayi can nasan kana da buqatar ku kebe,ban kuma dauka zaka
dauki tsahon wannan lokacin baka shigo ba,duba can abincinka ne har ya huce"
dubansa yakai ga dining din,ya hangi kwanukan a jere,tabbas yana da buqatar
girkinta,don tunda ya tafi yayi missing taste din abincinta,ko daya dawo ma da
zumudin yazo yaci girkinta ya dawo,saidai kuma ya samu tarba daga mom,da kuma
nau'ikan abinciccika kala kala,ta kangeshi kuma da nau'in hirarrakin da suka jima
basuyi ba.
Saukowa yayi ya sassauta fusatar da yayi,ya miqa mata hannu
"Is okay.....muje ki bani abincin naci,ince dai shikenan ko?" Itama qoqari tayi ta
sake danne nata fushin,ta bashi hannun ya dagata,suia qarasa dining din,tayi
serving nasa,ta zauna opposite dinsa,yana ci yana bata labarin tafiyar da
yayi,mutum ce ita mai zurfi da kaifin gabe abu,ta fuskanci akwai wani abu guda daya
behind tafiyar tasa da yaketa ciccirewa yana sauya masa lamiri.
Ruwa ta hada masa me dumi yayi wanka,sai daya shirya ya kwanta sannan ta
dawo gyara wajen,zuciyarta na raya mata wala'alla yau wani abu ya wakana a
tsakaninsu,ta gama gyara wajen ta shirya itama.
Saidai ko data je bedroom din already ma bacci yayi awon gaba dashi,saita zauna
daure da bedside drawer tana addu'o'inta,dai dai nan wayarsa ta kada alamun kira.
Idanunta taka kan screen din wayar,sunan linda ya bayyana,sai hotonta dake
blinking,ko bakaga sunan ba hoton kawai ya isa ya gaya maka qabila ce kuma ahlil
kitabi wato kafura,kiran yadan dauki hankalinta,saidai kafin takai ga yin komai
taji ya motsa,ya kuma kai hannunsa ya dauki wayar da sauri ya kara a kunnensa
"Goodnight,am tired" abinda taji ya fada kenan ya kashe wayar gaba daya ya jefata
qasan pillow dinsa,ya koma kwanciyar rub da ciki yaci gaba da barcinsa.
Sosai kiran ya tsaye mata a rai,ta lura ko sati daya ba'a rufa ba da
aurensu ta gane yadda 'yammata ke yawan kiransa a waya,iya abinda idanunta suka
gane mata kenan,don bata taba daukar masa waya ba bare tayi bincike,tun ranar da
abokansa sukazo tsautsayi yasa ta dauka,hakan kuma ya haifar musu da sabani.
To ashe wasa farin girki,tunda ya dawo sai abubuwan suka sake rikicewa,daga
bangarensa har zuwa bangaren mom,ita mom tunda ya bata kyautar danqareriyar mota
wadda kudinta ya tasamma miliyan goma shikenan suka sanyata gaba ita dasu
fahima,ada basa shigowa bangarenta,amma a yanzu sai suka tsiri shigo mata,kai tsaye
zasu fada mata bedroom dressing room ko kuma kitchen dinta,duk abinda sukaga dama
zasu dauka,su tafi dana tafiya,su barnatar dana barnatarwa,duk da cewa Allah ya
wadatasu da komai,babu abinda suka nema suka rasa,bata taba daga idanu ta kallesu
ba,amma duk da haka bata tsira da baqar magana da kuma habaici ba,abinda ta lura
dashi shine. sun dauki aqidar qwarya tabi qwarya,gaskiya ne da ake cewa idan kaga
diyan talaka na aure gidan masu arqizi to ba shakka rabone ya rantse,ko kuma su din
irin mutanen nan da ake cewa daya cikin million ne,don zaiyi wahalar gaske kaga
hakan,kowa irinsa yake aure,sun maida abun jari hujja.
Bata sake gasgata hakan ba saida matan yayun bassam din sukazo gidan su
biyu,dukkansu gudajen iyayensu masu maiq ne kamar gidansu bassam din,haba haba mom
take dasu,babu raini tsangwama ko wulaqanci irin wanda suke mata ita,tsakaninta da
faccalolin nata dai baina baina,babu yabo hakanan babu fallasa.
Ta bangaren bassan kuwa,tun tana kawaici da yadda mata ke yawan kiransa
harta qosa ta fara qorafi akai,abinda ya sanya kenan yake yawaita saka wayansa a
silent.
Abun sai ya zame mata biyu,ga lalurarsa da bai taba tsayawa yayi mata
wani gamsashen bayani akai ba,ga kuma wannan dabi'a tasa,hasalima kamar ma damuwar
da yakeyi a baya akan al'amarin yanzu taja baya sosai,kawai da ya kasa yake tashi
yayi wanka yaci gaba da sabgarsa.
K'arfe sha daya saura na dare take takowa zuwa parlor dinsa na musamman
dauke da butar shayi mai hade da tray da qananun kofunansu,sanye take da kayan
bacci masu kauri riga da wando da suka saukar mata ash color marasa turuwa,sai
gashin kanta mai santsi data matse waje daya yanata sheqi a hasken qwan
lantarki,duk inda ta gifta sai tabar sauran qamshinta a wajen.
Da sallama ta shiga,yana saman kujera a zaune yana ta aiki da
system,kansa ya daga ya kalleta,ya zuba mata idanu,tayi masa kyau sosai a
idonsa,iman din badai kyau ba,wani irin kyau ne da ita da baya dusashewa,ko don
yanzunne take kan tashen shekarun quruciya da kyan nata?,komai nata daban
yake,komai nata na musamman ne.
Sake maimaita sallamar tata tayi sanda ta iso gabanshi,duk da cewa ba
wannan ne karon farko,ta saba da halinsa na rashin damuwa da amsa sallama,idanunsa
ya lumshe yana amsa mata,yana da feelings sosai akanta wanda har yanzu bai kasheshi
ba,saidai kuma ya rasa abinda yasa duk sanda yazo gareta haka tae faruwa dashi,ita
kadai.....baisan daga ina matsalar take ba,tun yana damuwa har takai ma ya rage
damuwa akai.
"Wannan kwalliyar tayimin,ya kamata na biya farashinta" murmushi ta
sake,tana jimawa bataji kalami mai dadi daga bakinsa ba,har takan manta da cewa
akwai wasu kalmomi masu dadi da sukayi saura a tsakaninta dashi da zasu iya furtawa
juna
"Na gode" ta ambata tana ajjiye masa shayin.
System din taga ya ajjiye ya laluba wasu takardu ya ciro cheque,rubutu yayi akai
sannan ya miqa mata
"Na biya kudinta" ya fada yana miqa mata cheque din.
"Na gode" ta ambata tana karba,ta juya tana duba abinda ya rubuta
ajiki,naira dubu dari ce.
Gefanta ta ajjiyeta tana tatara hankalinta akansa,don ba wannan ne a
gabanta ba,sam yanzu ire iren wadan nan kyaututtukan nashi basa damunta balle ma su
burgeta,saboda ta rasa dukkan wani abu daya kamata ace ta samu daga
gareshi,kulawarsa da kuma lokacinsa dukka samunsu sun zame mata wani kayan
gabas,tana yunqurin bude baki ta fara magana kira ya shigo wayarsa,kamar kowanne
lokaci tabi wayar da kallo,bacin rai da baqinciki suna cikata,bata da wani sakewa
dashi matuqar wayarsa zata kasance a bude.
Shima kamar wasu lokuta da dama haka ya daga wayarsa abunsa a
gabanta,briefly yace zai kira idan ya gama abinda yakeyi,ta bishi da kallo ranta
yana quna,bayajin kunyar daukar wayar duk wadda ta kirashi a gabanta,yau din dai ta
kasa cinyewa
"A gabana bassam.....a gabana kake daga wayar wasu?" Fuskarsa yada tsuke,saboda ya
tsani tayi masa qorafi akan hakan Ai bai kamata ace kina damuwa ba,tunda dai kinsan
mutum kamata bazai rasa masu tayawa ba,suna nan jingim da yawa,a cikinsu kuma na
zaboki" ranta je taji ya sosu da abinda ya fada,sai kawai ta miqe,yana yawan fadin
magangun da bai kamata ace ya gaya mata su ba
"Na godewa Allah da bani na taya ba,nice wadda aka taya" daga haka tayi gaba
abinta,tana jiyosa yana faffadar maganganu amma tayi banza dashi,daga baya bayan
wasu mintuna data koma dauko wayarta,saita sameshi ya bararraje abinsa yanata
hirarsa,kana masa duba daya zakasan da mace yake waya,wani abu ya tokare mata
wuya,tana komawa sashensa ta shige toilet tasha kukanta sannan ta wanke fuskarta ta
fito.
Tana da tarin matsalolin da batasan dawa zata tattauna ba,waye zai bata shawara,a
yanzun bata buqatar shawarar munira,saboda abinda ta fuskanci madubin hangen
nesarsu a yanzu ya bambanta dana juna,kowanne a cikinsu da irin abinda yake hangowa
daya saba dana danuwansa,a yanzun munira na cikin rudu da gushewar gano abinda gobe
zata iya haifarwa kamar yadda itama ta tsinci kanta a ciki watannin baya,wanda sai
a yanzunne hijabin daya rufe kwanya da idanunta yake yayewa sannu a hankali,wani
baqin gani mara kyau da kuma dimuwa yake bayyana a gareta.
Al'ameen shine sunan daya fado mata a rai,saita lumshe idanunta hawaye
suna saukar mata,tana da yaqinin idan da ace aurenta kamar kowanne irin aure
ne.....shine mutumin da zaiyi ruwa yayi tsaki wajen shiga matsalolinta da
damuwarta,ta tabbatar da babu yadda za'ayi ya tsinci kanta a kadaici irin haka,ba
zata rasa mafita ba,ba zata rasa abokin shawara ba,tun ranar daurin aurenta bata
sake ganinsa ba,bata sake sanin a wanne hali da yanayi yake ciki ba,hasalima bata
san ina hake ba,don kusan zuwanta gidan uku bayan aure da daddare,duk da ba jimawa
take ba amma bataga koda gilmawarsa ba,taga sadiqu kuma yaci ace shima ta
ganshi,zuwanta na farko taji anyi xancen ya tafi wani waje to ina yaje?,bata sani
ba,bata kuma dame amsa mata.
Bai shigo dakin ba sai wajen qarfe daya saura na dare,har a sannan tana kwance
kanta na mata wanu matsanancin ciwo saboda tunane tunane da suka cika mata kwanya,a
hakan zaka tsammaci bacci take,saidai idanuwanta biyu,har ya gama abinda zaiyi ya
haye gadon yaja bargonsa abinsa,ba jimawa taji tashin munsharinsa.
Idanunta ta runtse,wasu hawaye masu dumi suka gangaro mata,a haka munira take cewa
ta share tayi sabgar gabanta?,ta dauka cewa samun kudi da sutura da cima kadai sune
dadin aure kamar yadda a baya dukkaninsu qwaqwalensu suka basu?,ba shakka tana kan
kuskure,wanda bata fata yayi mata jagoranci zuwa rayuwar data tsinci kanta yanzu
ita a ciki.
Watansa guda da dawowa ya sake shirya wata tafiyar,wadda zai dauki a qalla wata
biyu acan kafin ya dawo,tafiyar data zama mabudin budewar komai,da kuma wani irin
rikici daya sake sanyo rayuwar aurenta a gaba.Ya tafi ya barta kamar kowanne
lokaci,babu kulawa daga kowanne sashe,sai azabar kadaici da zaman shuru,wata daya
da sati biyu da tafiyarsa safiyar wata lahadi30 safiyar lahadi
Tunda gari ya waye tana kwance bata tashi ba,tunda ta idar da sallar asuba,saboda
tasan cewa babu wani abu da zatayi koda ta tashin.
Ciwon ka take fama dashi matsananci sosai,wanda ta kusa a qalla wata daya
tana fama dashi,tun bayan tafiyar bassam din,koda ba'a gaya kata ba tasan yana da
qaqqarfar alaqa da yawan tunani da kuma damuwa da take kwana ta wuni a
cikinta.Babbar damuwarta yanzu a rayuwa yadda zata dai daita da inna da kuma
malam,ta sani cewa mutum daya ne a rayuwa a yanzu zai iya daidaita tsakaninsu
AMEEN,wanda shi kuma a yanzun batasan a wacce duniyar yake ba,ko giyar wake tasha
tasan bata isa ta fuskanci ya sadiqu ba,tana da yaqin ranta sai yayi matuqar baci
fiye da abinda inna da malam zasuyi mata,dukka danginta ba'a kusa suke ba bare taga
wasu,wadanda ke a kusan basu wuce su biyar ba,su dimma babu sa'anninta ko masu
qananun yara yammata da zasu kawo mata ziyara bare su rage mata kewa.
Da qyar ta sauka daga saman gadonta,kanta kamar xai fado,ta shiga kitchen
ta hada ruwan tea ta riqo a mug ta dawo dakin,gefan gado ta zauna,ta jawo wayarta
ta fara laluben number munira,saboda shekaran jiya tace mata zata zo,tanaso ta
tabbatar zata zo din.
A kashe wayar tata take,sai ta bude data taba fatan samunta online,tunda
wani lokaci akan sameta ta WhatsApp,koda layinta bai shiga ba.
Ta sama take kallon notification na wayarta,saqonni keta
shigowa,idanunta suka fada kan wata baquwar number,wadda ta turo jerin hotuna har
guda shida,batasan number din ba,hakan ya sanyata ta fara bude saqonta.
Rubutune kamar haka daga farko
hi me gadin gida,ina fatan wadan nan hotunan zasu debe miki kewar wuninki na
yau,asha kallo lafiya_
Mamaki ya cikata,ta dannan hotunan cikin sakanni suka bude mata,tarwai
kamar gilashin madubi.
Mummunan faduwa gabanta yayi,Har mug din hannunta yana subucewa daga
hannun nata,ya fadi a qasa ya tarwatse shida ragowar tea din dake ciki,innalillahi
wa inna ilaihi raji'un ta shiga furtawa hannayenta na rawa,zuciyarta na bugawa da
gudu kamar zatayi tsalle ta faso qirjinta ta fito waje,tuni ta dade a tsaye tana
bin hotunan da kallo daya bayan daya,duk da yadda hannunta ke rawa amma bata fasa
binsu daya bayan daya ba,saboda tana jinta ne kamar a duniyar mafarki ba a gaske
ba.
Wasu irin qazaman hotunane na bassam shi da wata qedara wadda babu alamun digon
musulunci tattare da ita,hotuna ne da babu abinda suka boye na tsiraicin dake jikin
dan adam,wasu hotunan suna kwance saman katafaren gadon da dakin yafi kama da
hotel,wasu a bakin beach harda wadanda akayi a toilet cikin bathtub,abun babu ko
kyan gani.
Jiri ne ya debeta yana shirin kayar da ita,tayi hanzarin komawa ta zauna,wayar ta
sulake gefe,sai ta saka duka tafukan hannunta saman fuskarta,ta lullube
fuskar,sannan ta fashe da wani matsanancin kuka,nadama da dana sani tana cin
zuciyarta.Kuka take haiqan cikin tashin hankali,babu me rarrashinta ko bata
baki,tunda take a duniyarta bata taba ganin abinda ya daga mata hankali irin wannan
ba,ashe dama haka bassam din yake?,neman mata yakeyi?,kenan lafiyarsa qalau?,ita
yake rainanawa hankali ko kuma me?.
Cikin matsanancin hali ta wuni ranar,zuwa dare saiga wani saqon da yafi
wancan muni,gajeran video da yasanya numfashinta wucewa,bai dawo ba sai bayan wasu
sakkanni,ta dauki wayar tayi wurgi da ita tana gunjin kuka mai sauti,kamar ta tsaga
qirjinta ta fidda zuciyarta haka ta dinga ji.Kwananta uku cikin wannan halin ita
daya,ta fede ta rame ta lalace ta kuma zabge,depression ya fara kamata,kamar wata
mai matsala a qwaqwalwa wani lokaci,ita kadai zata tsaya gaban madubi tana zantuka
da kanta tana kuka.
A kwana na hudu munira tazo,ba zata iya gaya mata komai da komai
ba,tsairaicin mijinta ne,kai batajin ma muniran zata iya bata shawarar da ta
dace,don daga isowarta gidan ta fara surutu kan motar da aka yiwa iman din
kyautarta,motar da tunda ta hauta sau daya bata qara hawanta ba,hasalima bata ita
take ba,ta kanta takeyi a yanzun,bata buqatar dukkan wani abu daya fito daga hannun
bassam din,komai nashi a qazanta take kallonsa,tadai gayawa muniran abunda ke
faruwa sama sama,sai ya dan tabe baki
"Shine kika zauna kika fige haka?,to don Allah ta yaya zaki raba mutum irin bassam
da yammata da matan waje?,kina ganin yadda Allah yayishi,bai rasa komai ba,su
sauran matan dake gidan wadata an gaya miki haka suke zaune basu da matsala,tunda
dai.baki rasa komai ba ki barshi yayi sabgarsa kema kiyi naki sha'anin,tunda ya
sakar miki mara,bai takuraki ba,wadda take miki ture turen aurenki takeson kashewa
kawai" shuru tayi tana mamakin munira,lallai wanda Allah ya ganar dashi ya
huta,saita rabu da ita ita da banzan tunaninta.Cikin rahama da jin qan ubangiji,da
wani yammaci tana kwance a bushe kamar wadda ta shekara jinya,ubangiji ya aiko mata
da bushira,qawarta tun zamanin yarinta.A gigice ta miqe ta nufi bushira,suka
rungume juna
"Bushira,ya akayi kikasan gida na?,yaushe kika dawo?" Tambayar data fara jefa mata
kenan tun kafin ta zauna,murmushi tayi tabi iman da kallo
"Amarya hala laulayi kika fara,irin wannan dashewa haka?" Maganar sai ta taba
zuciyar iman din sosai,har rauninta ya bayyana saman fuskarta,duk.yadda takai ga
dannewa saiga hawaye suna ambaliya kan fuskarta,rudewa bushira tayi sosai
"Subhnallah,meye haka iman?,daga magana?,ko na miki ba dai dai bane?" Kai ta
girgixa ta qanqame bushira tana fashewa da kuka
"Ina cikin tashin hankali bushira,tunda nayi auren nan ban taba jin dadinsa na
kwana uku ba,Allah ya mallakamin abinda na nace akansa,amma kuma sai ya barni da
iyawata"
"Zauna muyi magana a nutse" bushira ta fadi tana zaunar da ita saman kujera
hankalinta a tashe,babu haufin komai ta shaidawa bushira duk yanayin da take
ciki,saboda a duniya a yanzu cikin ranta tana jin babu qawar data kai qawar
quruciya,qawar islamiyya,qawar da aka tashi a unguwa tare,qawar kusa da gida wadda
ta fito daga gidan tarbiyya,ki qaraci tara sabbin qawayenki,daga makarantu ko
ma'aikatu,qasashe da garuruwa,mawuyacine ki samu irinsu,sun saki kin sansu ciki da
bai.Bushira ta jina jinjina tarin matsalolin da suka dabaibaye iman din watanni
kadan da aurensu,ba shakka akwai wata a qasa,saita daga kai ya dubeta
"Me ya kawo rashin aurenki da ya amin,don na tabbatar nayi imanin yana sonki,sonki
yakeyi kamar yadda nayi miki hasashe" kai tsaye ta amsa mata da furucun dake fita
daga bakinta cike da tarin nadama qarara
"Ya ajjiye duk wani abu a gefe ya kalleni ya gayamin yana sona,amma nasa qafa na
shure,na shaida masa bana sonshi bassam nakeso,saboda a lokacin soyayya ta rufemin
idanu,ina ganin bassam ya fishi cancanta Duk abinda ya biyo baya ta gaya mata tsaf
"Subhanallah" bushira ta maimaita sau uku sannan ta dora
"Dukkan wata matsala da kika ci karo da ita,kece kika kirawa kanki ita,tun inaca na
fara jin wai wai 'yan gidanku basuson aurenki,na tabbatarwa kaina akwai abinda yake
faruwa iman,bakisan ba'a musu da iyaye ba?,bakisan bayan bautar Allah kada ka
hadashi da abokin tarayya babin iyaye shine abu na biyu da Alla yake fadi
ba?,saboda girmansu ya hada haqqinsu da bautarsa?,bakisan koda kin fisu gaskiya da
hujja qarara mabayyaniya mawuyacine Allah bai jarrabeki ba?,abar ta batun ya
alameen tunda yanzu wani kike aure amma inason na gaya miki,kin tafka babbar
hasarar da bazaki maida gurbinta har abada ya alameen?,kusan shi ya raineki,baya ga
inna da malam yafi kowa sanin ciwonki,yafi kowa sanin me kikeso da kuma abinda
bakiso?,yafi kowa tattalinki?,shine karatunki suturarki da duk wata walwalarki,koda
qiyayya kike masa azuciyarki haiqan....iyaka wadan nan abubuwan basu isa su
tsaidashi a mizanin wanda ya cancanci aurenki ba?.iman.....ina tunaninki ya tafi da
har kika zaci samun wani makwafin ya alameen a duniyarki?" Fuskarta ta kifa gaba
daya saman pillow,tana jin tsakiyar kanta kamar ana yamutsa mata kwanya ko ana mata
hajijiya a tsakiyar kanta.
Yanayin yadda ta shiga rudu da yawa ya sanya bushira sassautawa,ta fara
kwantar mata da hankali da kalamai masu taushi,bayan ta sanyata ta sauke dukka wani
social network dake wayarta,ta kuma shaida mata ta jirayi dawowar mijinta,ta bibiyi
maganar a nutse,kada tayi hanzarin yanke hukunci gudun nadama ko dana sani,saboda
zai iya yiwuwa sharrin mace ne da kaidinta,muhimmin abu kuma na qarshe da taja
hankalinta shine,ta nace ta kuma dage ta dai daita tsakaninta dasu malam
"A yanzu babu abinda nake da buri sama da na ganni a tsakiyar mala da inna,saidai
abunda nake fuskanta a duk sanda naje ganinsu da sunan ziyara ya tursasa min zama
gefe guda,abunda ke cikin idanuwansu da irin kallon da sukeyimin,sun gaza fahimtar
ba dukiyar bassam bace ta jani ga aurensa,koda akwai tasirin dukiyarsa wallahi
bushira bame yawa bace,amma rannan inna cemin tayi,wai na matsa da zuwarmusu
gida,ta zaci zan canza wasu iyayen ne ai masu wadata,tunda sudin basu da komai,basu
kuma ajiye komai ba Kai bushira ta jinjina
"A irin wannan situation din ba kowa ne zaki gaya masa haka ya yarda ba,amma
hakanan zaki ci gaba da zuwa kina fuska tarsu da dukka maganganun da xasu gaya
miki,yawan maganganun da zasu gaya miki yawan dafi da tsatsar dake wankewa daga
zukatansu a kanki kenan,a haka a hankali a hankali komai zai dinga wankewa daga
zuciyarsu" kai ta gyada,qwarai taga hikimar hakan,hasashen bushira yayi dai dai
"Amm sannan kuma" bushira ta fadi baya tayi gyaran murya,da alama maganar da zatayi
tadanyi mata nauyi
"Maganar matsalar mijinki,ya kamata ki tuntubeshi ku tattana,zama haka bazai yiwu
ba,duba da cewa haqqinki ne a kanshi" ta qarashe maganar tadan murmusawa kadan. Dan
qaramin tsaki iman taja
"Manta da wannan bushira,ana ta kai wa yake ta kaya?,a wannan yanayin da nake
ciki?, infact ma gaba daya Allah ya zaremin abun daga zuciyata,sau tari ka nakan
tambayi kaina ko bani da cikakkiyar lafiya ne?,ko romance din da muke na gaza jin
wani cikakken wani abu akansa......ni bushira ban ma yarda baida lpy ba zuwa
yanzu,idan har hakane,me yakewa ita wannan karuwar data turomin hotunansu cikin
qazamin yanayi?,jagwalgwalon da yakemin itama yake mata?" Tayi maganar wani abu me
daci da tauri yana tsaya mata a maqoshi.
Girgiza kai bushira tayi
"Kada ki zargi haka,karuwa ce,indai yana da kudi koda bashi da mazantaka zata iya
zama dashi,matuqar zai kashe mata abinda yake dashi,dama ba abunda sukeyiwa kenan
ba?" Kai iman ta gyada mata,tana dan samun relief cikin zuciyarta,ita kanta
bushiran tasan ta gaya mata hakanne kawai saboda ta kwantar mata da hankali.
Cikin yanayin quncin da take ciki kaso dari kaso hamsin ya zagwanye,bushiran
ce ta tada girki da kanta ta shiga kitchen,ta shirya lafiyayyar jalop rice,ta zuba
musu tare,ta hilaci iman din sai data ci mai dan dama,saidai har zuwa sannan kanta
na mata ciwo,tana daurewa ne,sannan ta danji qwarin jikinta abincin da taci.
Ya kamata shima kije kiga likita,bai kamata kita zama da ciwo me naci irin haka
baki nema magani ba" bushira ta bata shawara sanda ta shirya zata tafi,kamar ta
hana bushiran tafiya haka taji,zuciyarta ta dinga yi mata rashin dadi,batasan tayi
missing childhood friend dinta ba sai a yanzu. Haka ta rakata har qofar gate,bayan
ta saka mata kudi masu yawa a jakarta,wanda sai da tasha qwarbai da bushiran sannan
ta karba,a take ta hangi bambamci qarara mai kuma tarin yawa tsakaninta da muneera.
"Anya da bushira ce muneera zata barni na auri bassam na qyale ya ameen?"
Tambayar data dinga yiwa kanta kenan sanda take dawowa zuwa sashents
"Muneera qaunata take ko kuma qina?" Tambaya ta biyu da tazo kanta kenan,wadda ta
kasa tantance ta.
Tana sanya kai a parlor din nata taga shigar fahima dressing room dinta,cikin
mamaki tabi bayanta,duk da tuni zuciyarta ta gama gaya mata abunda ya shigo da
fahiman,tunda ba yaune karonsu na farko da suke mata irin hakan ba.
Dai dai sanda ta shiga fahiman tayi nisa a dudduba laces dinta dake rataye
jikin hanger,sau daya ta juyo ta dubi iman din taci gaba da abinda takeyi,kai
bakace gidanta kuma dakinta ta shigo mata kanta tsaye ba tare da saninta ba.
Daya daga cikinsu ta ciro daga hanger din,ta kalli jikinsa sosai sai ta
ninkeshi,ta matsa sashen takalma ta fara dubawa suma.
A yau din ranta a matuqar bace yake da rainin hankali da kuma iskancin
da suke mata,abun ya fara wuce makadi da rawa,sun kuma fara wuce iyaka,don haka ta
bude bakinta da dan qarfi tace
"Wai lafiya kiketa yimin dauki dai dai cikin kayana?" Juyowa tayi ta watsa mata
wani kallon banza
"Kayanki ko kayan yayana?,ins kukaga arziqin da zakizo da wadan nan kayan daga
gidanku" maganar ta sake tunzura iman,a fusace ta qarasa cikin dakin,bata tsaya
wata wata ba ta fusge lace din dake hannun fahiman
"Duk da yayan naki ne ya siya na hana bazan bayar ba,matuqar da sunana yayan naki
ya siya to babu wanda ya isa ya dauka ko ya tabamin kaya babu izinina,ki fita ki
bani waje tun zuciya bata debeni na miki matsiyacin dukan da za'a sake ganeki"
tabbas a yadda taga idanun iman din sun sauya kala tana kuma bubbudesu da
kyau,furucinta ke nuna tsantsar tunzurarta,tunzarar da bata taba ganin tayi
makamanciyarta ba tabbas zata iya aikata abinda take fadi,don haka ta saici hanya
tana dubanta Zakisan dani kike,sai kinyi nadama
"Na jima banyi nadamar ba,wacce nadamar ce ta ragemin banda wadda nake ciki,yi
waje!" Sai fahiman ta juya tana ficewa daga dakin,iman din kuma ta zube a wajen
dafe da kanta da takeji kamar zai tarwatse[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 31
Da qyar ta kawo lanta parlor dafe da kan nata da yake sara mata kamar xai
fado,tana zaune anan taji anata fama knockin
"Madam ki bude.....hajiya ce take kiranki" abinda 'yan aikin da mom din keta
aikowa taxo suke fada kenan ta window dun parlor,saidai babu wanda ta saurara a
cikinsu bare ta bude musu qorar.Muryar mom dince daga qarshe ta bayyana da kanta a
qofar falon,saidai a sannan sama sama ma take iya jin abinda take fada,saboda yadda
kunnuwanta sukayi dimm gaba daya,ta daina gane komai kamar wadda ta suma,irin suman
nan na ido biyu,kamar kuma wadda ta tafi duniyar mafarki Sanda ta koma normal data
duba agogo awanni ta diba a hakan,ta miqe da qyar ta koma bedroom tana kiran sunan
Allah.
Wannan ya sanya a washegari dole ta miqa kanta asibiti,dr ahmad Abdullahi shine
likitan da take gani,yayi mata gwaje gwaje sosai,bayan ya kammala dubata,sakamakon
da ya bayyana shine ta kamu da hawan jini,don jininta yakai 190,mamaki sosai ya
kama dr ahmad,ya sake daga kansa ya kalleta,sannan ya duba shekarunta dake rubuce
jikin file dinta na asibitin.hajiya aqananun shekarunkin nan bai kamata ace jininki
ya hau har haka ba,ya kamata ki sakawa ranki nutsuwa da salama.....ko meye yayi
zafi maganinsa Allah,kiyi qoqarin kwantar da hankalinki ko domin lafiyarki,hawan
jini mummunan ciwo ne dake da hatsari da kuma barazana ga dukka sassan jikin dan
adam" wani abu me nauyi taji ya sake saukowa saman qirjinta,ta kwantar da fuskarta
saman hand bag dinta,tana jin kamar ta gayawa dr Ahmad matsalolinta,mutum ne mai
bala'in nutsuwa haiba da kamala,wanda tun farkon zuwanta asibitin ta zabi ta dinga
ganinsa,saboda alamomi na riqo da addini dake damfare dashi
"Kiyi haquri hajiya,at younger age naki irin wannan. ko 20yrs baki kai ba bai
kamaci kibar wani abu ya gadar miki da ciwon da zai tarwatsa lafiyarki ba" bai nemi
sanin halin da take ciki ba,amma yayi aikinsa na likita ya kwantar mata da hankali
da kalaman da suka dace.Sosai tayi masa godiya,ta kuma sawa ranta zatayi qoqarin
bin komai a sannu kamar yadda bushira da dr ahmad suka bata shawara.Daga asibitin
gidansu ta wuce,ta dauki aniyar yau koda zasu koreta kamar yadda suka saba ba zata
ko ina ba,yadda innar ta saba tarbarta haka yau dinma tayi mata,saidai yau din da
sassauci bata nemi ta koma gida ba,qarin wani ci gaban yau din bata raba wajen zama
da ita ba,saidai babu ruwanta da ita,kamar ma babu wata halitta a dakin sai ita
daya.Ko iya hakan ma ya yiwa iman din dadi,tayi kwanciyarta kan doguwar kujerar
dake falon tana bin innar tata da kallo,abinda yadan sake mata dadi,yadda kusan sau
uku suna hada ido da innar sanda innar take satar kallonta,addu'a take cikin
ranta,ubangiji ya sassauta mata,ya sauko mata da zukatan iyayenta ko zata samu
salama ta wani bangaren.Shima malam din daya dawo yau data je ta gaidashi babu
abinda yace da ita,sai da yana alwalar sallar magariba sannan yace idan ta idar da
salla ta wuce gidanta,kamar ba zata tafi ba,kamar tayita zamanta da iyayenta,kamar
ta dawo da rayuwarta ta baya haka taji,saidai bata da wani zabi,bata kuma da yadda
zatayi,tunda ita ta siyawa kanta ta kuma biya,tafiya ta kamata dole.Daga ranar ta
samu.nayi,duk sanda taje asibiti checkup saita zarce gida,ba zata koma gidansu ba
sai magariba,wannan ya sassauta mata damuwarta qwarai da gaske,sai taji duka sauran
matsalolin dake tsakaninta da bassam minus ne,duk da suna qasan ranta suna cin
zuciyarta,bacin rai yakan dawo mata a duk anda ta tuna da munanan hotuna da videos
din da aka tura mata.
A wannan karon batasan bassam din zai dawo ba saboda ta ajiye wayarta gaba daya,a
yanz ta sake tsanar wayar kwata kwata,ta fita daga kanta Ranar bayan ta idar da
sallar azahar,ta dama yoghurt na L&Z da lallausar furar data debo daga wajen inna
da ko ci kanki batace da ita ba sanda tasa hannu ta diba furar,ta damata da yoghurt
din tasha,bata fiya girki ba,saboda a yanzun sam bata da appetite,kome zata dafa ba
dadinsa zataji ba,ta fidda hijabin kanta ta koma saman doguwar kujerar falonta ta
kwanta rigingine,hannunta daya saman kanta,idanunta a lumshe,qira'ar shaik shary
al_afasy data kunna jikin tv na ratsa falon a hankali,tana bin qira'ar da boyayyen
sauti,saidai kuma kana iya ganin yadda qaramin bakinta yake motsawa.
Alamun bude qofar falon bai sanyata ta bude idanunta ba,don bata raba dayan biyu su
fahima ne,duk da cewa tun ranar da abun ya faru babu wadda ta sake shigo masa
sashe,saidai yadda taji alamun ana tahowa inda take ya sanyata ta bude idanun
nata,ta zubesu saman guskar bassam dake sanye da suit ash colour,blue din qwayar
idanunta suke fitowar ta saboda rashin kwalli da kuma kodewa da idanun nata sukayi.
Fuskarsa a matuqar murtuke,ta danne zuciyarta ta miqe daga kwanciyar datayi sanda
taga ya iso kanta ya tsaya,ta dauki remote ta rage sautin karatun ca qasa sannan ga
furta masa sannu da zuwa.
Ciki ciki ya amsa mata yana ajjiye trolley dinsa idanunsa nabin parlor din da
kallo.yana sassauta tie dinsa,kamar me neman wani abu
"Me ya samu wayarki?,inatason in sanar miki dawowata amma ba'a samunki"
"Matsala ta samu" ta amsa masa a taqaice tana kaucew kallon qwayar idanunsa,saboda
wani tsanarsa data ji ta saukar mata lokaci guda sanda yayi mata zancan waya,wani
baqi take gani yayi mata a idanunta,dukk wani kwarjini kyau da qaunarsa da takeji
ta laluba taji.babu ko guda daya
"Meye amfanin kudin dana bar miki da bazaki iya dauka ki sayi wata ba" haushi
tambayar tabata qwarai,idan kuma tace zata bude baki ta bashi amsa maganar ba zata
fita da dadi ba,don haka sai ta miqe kawai a maimakon ta amsa masa,tasa hannu taja
trolly din nasa zuwa dakinsa,dakin da tunda yasa qafa ya tafi bata sake shigarsa
ba,dakinta da aka zuba mata kayan ameen tafi jin dadin xama cikinsa sau dub
Dukka motsinsa tana ankare dashi,sai wani ciccin magani yake da bata fuska kamar
wadda tayi masa wani abu,abunda ya sake bata mata rai da dugunxumata yadda wayarsa
ta fara harbawa da kira don masifa,ko awa guda biyu da shigowa cikin gidansa
ba,kiran yana shigowa yana katsewa.
Banason hauka..just two hours?,ba haka mukayi dake ba,karki sake kirana,ki barni na
huta" sune kalmomi na qarshe da taji daga bakinsa sanda take fitowa daga bandaki
bayan ta gama hada masa ruwan wankan da ya buqata.Maganganun da suka tsaye mata a
rai kenan,suka kuma sake fama mata mikin dake ranta,ta dinga hadiyar yawu da
qyar,ko baya data gama hada masa abincin gaggawan data shirya masa takai masa daki
parlor ta dawo tayi zamanta,bata tashi daga wajen ba saida lokacin sallar la'asar
ya gabato,sannan ta koma dakin.
Bacci ta sameshi yana yi haiqan kamar wanda yayi tafiyar qasa,kamar ya shareshi ta
wuce sai kuma taga bai kamata ba,a qalla akwai hakkin salla a wuyansa,don haka ta
qarasa ta fara qoqarin tadashi,saidai juyin duniya yaqi tashin yace ta rabu
dashi,ba tun yau ba,bai cika damuwa ba da lokacin sallah saboda ya kubce masa.
Kwarai taso dauke kanta daga wayarsa daketa blinking,da alama a silent ya
sakata,saita dawo da baya,zuciyarta na rinjayarta kan ta duba wayar ko zata samu
haske kan abinda yaqi gushewa daga zuciyarta,yake kuma kai komo.
Sofa din dake dakin can wata corner ta koma ta zauna akai,hannunta na rawa
zuciyarta tana bugawa ta bude wayar,babu nambobin sirri,hakan ya bata damar wucewa
kai tsaye zuwa WhatsApp dinsa.Charts ne burjik da 'yammata iri iri,wasu hausawa
wasu yare,harda 'yan wasu qasashen,dukka hirace dake nuna qauna da soyayya
tsakaninsu,sai kuma receipt na kudaden da yake turawa wasu daga ciki.Harta gota
sunan ta dawo da baya,tabbas yayi kama da sunan wadda ta tura.mata saqo wancan
watan,ba tare da bata lokaci ba ta danna ta shiga.bata tsaya duba saqon qarshe ba
tayi scrolling zuwa sama,saboda tana son sanin meye tsakaninta dashi tun daga farko
zuwa yanzu,sai data je qarshe sannan ta fara bin saqonnin,wanda suka fara ne ran
uku ga wata,data duba date yayi dai dai da kwananta guda a gidan bassam din,saqon
farko shine ya fara tura mata shi kamar haka
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 32

_Baki da hankali ashe jessica?, Da gaske kike dama sai da kika aikata
din?,ta yaya zaki haramtamin matata ta sunna?_

Emoji na dariya ta fara aiko masa sannan tace

_mahaukatan ai biyu ne,wato ni da kaii,ta yaya kake da tabbacin bazan aikata abinda
na niyyata din ba?,ta yaya kake tunanin zan sake barwa wata diya mace kai?,shekara
biyar?,cikakkun shekaru biyar kana yaudarata kan zaka aureni,to na gaji da
alqawarin banza,daga yau din kai nawa ne ni kadai,naga macen da zata sake morarka
bayan ni_

Bayan wasu sakanni da basu da yawa ya maida mata amsa

_karkiyimin haka?,ki fadi ko nawa ne zan biyaki_

_banason komai daga gareka,aurena nakeso kawai kayi_

_kinsan me kike cewa?,addininmu ba daya bafa?_

_eh,kowa sai yayi addininsa ai ko_

Sauran maganganun da suka biyo baya gaba daya ciki bacin rai yake
mata su,da kuma barazana,daga qarshe saqonnin suka yanke,suka shiga wani kwanan
watan na daban.

Hoton passport dinta ne da aka bugawa visa ta qasar daya ce mata zaiyi
tafiya a sannan,idanu iman ta fitar tana jin wani tashin hankali,dukka saqonnin sun
bayyana mata cewa dukka tafiye tafiyen da zaiyi da Jessica yake tafiya,ita ta zame
masa madadinta.
Tashin hankalin da ba'a saka masa rana,wato daman watace tayi masa
sihirin da bai iya aikata komai idan bada ita ba garin biye biye da neme nemen
matansa?,wannan wacce irin masifa ce,dama tafiyar da yakeyi tare suke tafiya,ashe
shi yaba samun abunda yakeso shi yasa ya jingineta,ya daina damuwa da situation
dinsa,ashe ba lalura gareshi ba?.

Kamar yasan meke faruwa yayi juyi cikun barcinsa da zummar gyara
kwancinyarsa,idanu suka hada tana riqe da wayarsa hawaye sun mata face face saman
fuska,sai yadan miqe da hanzari ya zauna saman gadon

"Me kikemin da waya?,miqo min wayata" yayi maganar yana hade rai,cikin sautin kukan
data kasa controlling dinsa ta fara magana

"Ashe dama haka kake bassam?,ashe kai din baqin kumurcin maciji ne?,ashe dafin da
yake tattare dakai kenan?,manemin mata ne kai wata kake dauka kuyi tafiya nisan
duniya wata da watanni kabar matarka ta sunna a gida?baya ga tulin yammatan da
kakewa hidima bassam,har wata ka ajiye?,dadironka......." Tsawa ya daka mata

"Dalla malama dakatamin mana,ni zaki saka a gaba kamar dan cikinki kinamin wanna
titsiyen?,ko uwata bata isa ta bimin qwaqwaqwafi haka ba bare ke,abinda yasa tun
farko banson aure saboda banason bin diddigi da takura,kema da nake ganinki me
mitsi mitsin shekaru har kinsan bin diddigin spouse dinki?,yaushe kikayi wannan
wayon?" Cikin bacin rai ta fara maida masa amsa

"Ko yau nafado duniya matarka ce ni,kuma ka dade kana wasu abubuwan a gabana ka
manta?"

"And so what?,eh matatace ke......me kika rasa?,ci sha suttura ko kudi?"

"Basu nake buqata ba,don ba don saboda su na aureka ba" wata dariya ya saki yana
zuro qafafunsa qasa idanunsa cikin nata

"Zuqi ta malle inji bahaushe,shi yasa naga kinqi dan uwanki ko.....ke,bari na gaya
miki,tarrr idanuna suke kallo kowacce mace,a zamanin nan dama mace tana maka
soyayyar gaskiya ne?,duk wadda tace tana sonka saboda Allah qarya take maka,shi
yasa nake amfani da damata,in kashe miki kudi nima na amfana dake,na sakar miki
komai......saboda haka banason takura ko kuma sanya idanu,ki barni nayi rayuwata
yadda na saba,banason takura" cikin xafi da tsananin fushi ta miqe

"Amma ka shayar dani ruwan mamaki bassam...."

"Bakiga komai ba,abinda kika gani kika maqalen shi sauran suka gani suke tare
dani,kalleni sama da qasa......wanda bai kaini komai da komai ba ya tara yammata
bareni da babu abinda Allah ya rageni dashi, relax 'yammata,kici arziqi kibar
arziqi a inda yake,idan kina tunanin zan zauna nayita lallabaki yanzun kina batawa
kanki lokacine kawai,i already won the election.......so no need naci gaba da
campaign,kin gane?"

"Amma ka zalunceni,ka cutar dani,kakuma cutar da zuciyata......".

Dif wuta ta dauke mata saboda saukar wani zazzafan mari saman
kuncinta,wanda ta manta a duniyarta rabonta da irinsa saboda gata da kulawa da take
samu

"Stupid kawai........don kinga na qyaleki bayan iskanci da wulaqancin da kikayiwa


mahaifiyata?,ina da labari fa amma na dage miki qafa,ko kin dauka nima bansan kima
da darajarta ba kamar yadda bakisan kimar naki ba?to ki kiyayeni wallahi, you worth
nothing to me,ni mace ba kayan gabas bace a wajena,yanzu yanzu ina iya wullar da
ita na canzata da wata" Kalamansa sun matuqar girgizata tare da taba mata tunani,ta
kasa koda qwaqwaran motsi bare ta aiwatar da komai,hannayenta saman kuncinta har ya
zura slippers dinsa yana jan tsaki bayan ya dauki wayarsa ya fice daga dakin.

Komai tsaya mata yayi cak,ta daina gane komai ta kuma daina fahimtar
komai,batasan me zatayi ba,kamar yadda batasan meye abu na gaba da zai sameta
ba,saida jikinta ya bata amsa ta hanyar daukar rawa,wanda a take zazzabi yayi mata
kirif,jikinta gaba daya ya fra shaking,qafafuwanta suka gaza daukarta,ta sulale a
wajen ta cure waje daya.

Wani mugun zazzabi mai uban huci ne ya rufeta,ta jima zaune a wajen
kafin taja jikinta zuwa nata dakin,tayi curewar alkaki tsakiyar gadon.

Maganarma ta hana kanta kuka bata taso ba,duk da yadda takejin kanta yana
barazanar rabewa gida biyu,ji take kamar duniyarta zata tashi,nadama iya
nadama,dana sani mara iyaka wadda ta ninka wadda takeyi a baya tun 'yan kwanaki da
aurenta da bassam,ashe ita din banza ce?,ashe ita din wawuya ce?,ashe itadin bata
da hankali?,dukka a ture abubuwan da suka faru gefe,a dauko maganar sanin ya kamata
dangane da iyaye,tabbas ta tozarta su malam da inna,ta kuma ci amanar ya alameen,ta
tabbata BUTULU KUFAN WUTA kamar yadda inna ta kirata dashi,kallonta kawai bassam
yakeyi?,amma yayi mata shuru tun a sannan bai gaya mata gaskiya ba saboda burinsa
na aurenta?.

Ya tabbata bassam fasiqi ne........haka dabi'arsa take ko daga baya ya


sauya,sam sam wannan ba bassam din data sani bane,ba shine bassam din da tayi
soyayya dashi a waje bane,shi kadaine hakan?,ko dukka maza haka suke?.

Kafin wani lokaci yanayin da take ciki ya ta'azzara,taji kamar ranta na


shirin fita ta numfashinta ne,ta tabbatar taci gaba da zama a haka komai zai iya
faruwa da ita,asibiti yafi kamata taje,to amma waye zai kaita?,waye xai
tallafeta,bushira da munira sukazo kanta,bushira bata iya tuqi ba,munira ta fita
wayewa ta wannan fannin,duk da a yanzun bataso ko qaunar alaqarta da munira taci
gaba,amma dole ita din xata kira.

Tana tsaka da yi.mata bayani numfashinta ya fara seizing,wayar ta sulale


mata,ta runtse idanunta tana ambaton sunan Allah.

Sanda munira ga qaraso tuni ta fara ficewa daga hayyacinta,haki take


sosai,muniran ta kamata bayan ta duba key din motarta,suka fito ta sanyata a motar
suka fice ba tare da kowa ya sani ba.

Cikin sa'a suka taras dr ahmad ne on duty,cikin gaggawa ya karbeta ya


shiga bata taimakon gaggawa,hankalinsa yayi matuqar dugunzuma da ganin yanayin da
take ciki,at her age bai kamata ace tana shiga mummunan yanayi haka ba,shekarunta
sunyi qanqanta da yawa,don haka bayan ya daidaita komai ya shaidawa munira yana
buqatar ganin iyayenta ko mijinta.

Washegari ta tashi jikinta da dan dama dama,saidai kuma babu qarfi sam,

"Tun jiyan na gayawa bassam kinga har sha biyu na rana na shirin yi bai shigo ba"
inji munera dake danne dannen waya,kai ta kada,sam batayi mamaki ba,saboda gaba
daya tasan cewa bassam ya sauya,ba shine bassam data sani ba,abun tambayar ina
tulin soyayyar da yake mata?,ina tulin soyayyar daya dinga nuna mata?,ina tayi

"Bani waya na kira inna" shine abinda tace da ita maimakon tsayawa su tattauna
batun bassam din,ta miqa mata,ta saka numbers din inna data dade da haddacesu ta
soma kira.
Bugu biyu ta daga,cikin raunanniyar muryarta ta fara gaidata,innar ta amsa

"Inna bani da lafiya,ina asibiti"

"Allah ya sawwaqe,ya baki lafiya" ta amsa mata kai tsaye,sai shuru yadan biyo
baya,iman din tayi ta maza tace

"Inna,ba zakizo ki ganni ba?" Maganar tadan taba innan,amma sai tayi kamar bata
jita ba,qarshe ma dif ta yanke kiran.

Hawaye ne ya biyo kuncin iman din,ta tabbatar lallai tana neman


taimako,tana neman sanya hannun wani babba cikin al'amarinta,idan ba haka ba za'a
wayi gari a samu baqinciki ya kasheta.

Ba bassam ne yazo ba sai dare,koda yazo dinma fada ya fara yi mata wai
kan me zata saka qafarta ta fice daga gidan bata shaida masa ba?,ai ba zaman kanta
take ba,abun ya daure mata kai,don haka ta bawa banza ajiyarsa,ana tsaka da haka dr
ahmad daya dawo zaiyi night round ya taras dashi

"Banda abinka,ai kone patient irin wannan yayi ba'a masa fada a yanayin da take
ciki,gaskiya ku kula da.lafiyarta,saboda matuqar za'a bar irin wannan abun na
yawaita faruwa da ita zai iya tana zuciyarta,ko ya sanyata ta shiga mummunan
yanayi" sake duddubata yayi ya rubuta mata sallama da magunguna,tare da yi mata jan
kunne kan ta kula da lafiyarta.

Ko a cikin mota babu wanda ya kula dan uwansa,tuqinsa yake ita kuma ta
maida kanta saitin window,hadiyar zuciya kawai take tana qoqarin hana kanta shiga
bacin rai saboda warning din da dr ahmad yayi mata.

Suna isa gida ta bude motar ta fice abinta,dakinta ta shiga,ta cire kayanta
ta fara shiga ta watsa ruwa,ta hado da alwala tayi sallar magrib data kubce mata ta
hada da isha'i,sai taji nutsuwa 'yar kadan ta saukar mata,sannan ta miqe ta fara
laluben wayarta.

Batayi duba me yawa ba ta ganta,ta koma gefan gadonta ta zauna tana


lalubar number wayar ya gana,ta tattara dukka nutsuwarta. Wayar na ringing
zuciyarta na dade karyewa,rauni yana cikata,tana sake qwararawa kanta gwiwa,cike da
fatan ya gana zata shiga lamarin nata,ta kuma samar mata da mafita.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 33

Ba jimawa muryar yagana ta bayyana da sautin sallama,muryarta na rawa ta


amsa mata sallamar tata,da fari ya gana bata fahimta komai ba cikin muryar iman din
ba,saima fara tsokanarta da tayi da cewa

"Ja'ira,tunda na miki haji da ummara kika manta dani sai yau da kika gama sheqe
amarcin watannu shida?"

"Uhmmm" kawai iman tace,don idan tace zata bude baki ta bada qwaqwarar amsa kuka ne
zai kece mata

"To ya gidan,ya angon naki?,ina fata anata biyayya ko?" Tamkar wannan tambayar
kukan yake jira sai kuwa ta fashe dashi,a rude ya gana ke tambayarta lafiya,saidai
ta kasa cewa da ya gana komai,sai sautin kukan dake fita daga bakinta,wanda ya faro
ne tun daga qasan zuciya,yana bayyana tsantsar quncin da zuciyarki ke ciki.

Bata hanata kukanta ba,sai da tayi mai isarta sannan ta fara labartawa
yagana komai,babu abinda ta boye mata a ciki.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" wannan kalmar yagana ta dinga


maimaitawa cikin rudewa,hankalinta yayi matuqar tashi

"Kiyi shuru hajar,ya isa" ya gana keta fada

"Wannan shine abinda su malam ke guje miki, shine abinda muke guje miki gaba
dayanmu" ta fada feeling her guiltiness,tana ganin kamar itama me laifi ce, da nata
kason da ta sanya baki malam ya sauka daga qudirinsa,duk da cewa haka yaran
sukaso,duk da cewa babu wanda yasan gaibu,ba wanda yasan hakan zata kasace sai
Allah jalla wa 'ala.

Kwantar mata da hankali ta dunga yi da kalamai masu taushi,tare da nuna


mata illar saka damuwa a ranta a situation din da dr yace tana ciki a yanzu,daga
bisani ta bata shawarwari da kuma jan hankali

"Kowanne gidan auren akwai nashi qalubalen hajar,ki zama jajirtatta ki aiki tuquru
ki gyara gidanki,zanzo kanon zan zauna da malam da binta din,suma dole zuwa yanzu
su sauki ai su tayaki da addu'a,idanma sunqi na tabbatar cikin zukatansu babu wanda
zai kaisu dakuwa da halin da kika shiga" ba maganar data sake sa mata nutsuwa irin
wadda yagana din ta gaya mata na zata sasanta tsakaninsu dasu malam din.

Sun jima kan waya tana bata addu'o'i da shawarwari,har sai data tabbatar da
ta samu nutsuwa.

Ta sake kiran bushira ta shaida mata,itama ta shiga damuwar,saidai


shawarwarin data batan sunyi kusan kamanceceniya dana yagana,duk abinda suka fada
ya dace kuma dai dai ne,saidai abu daya da takeji cikin ranta,bassam da aurensa
gaba daya sun fice mata fit a rai,kamar fitar kibiya daga cikin baka,wannan ya bata
salama,ta tattara hankalinta wajen shan maganinta,tsakaninta da bassam saidai
kallo,sai kuma idan sun hadu a parlor,wannan yasa ya dauka fushi take dashi shi
yaaa ta watsar dashi,shi kuma sai ya dauki aniyar quntata mata,hakan yasa ya sake
fidda ainihin halayyarsa,yake baje kolinsa na hira da 'yammata barkatai,da kuma
fiya joint joint dasu yana musu barin kudi,bata duk wani chart bare ta gani ranta
ya baci,whatsApp kawai takeyi,shima kuma already tayi mute na status din nasa.

A yanzu kallon kanta take a matsayin me gadin da gaske cikin gidan


bassam din,komai nashi ya daina damunta,hakanan ta tattara rayuwarta waje daya,kama
daga suttura da dakin kwana ta koma amfani da wanda tazo dashi daga gidansu,sai
abunda ya kama dole zatayi amfani da nashi.

A hankali ta fara samun sauqi da nutsuwar rai da ruhi,musamman data


maida alqur'ani abokin hirarta,gaba daya ta zama wata iri,wani irin sukuku,ba hirar
nan ba kuzari me yawa,babu kuma wani ado na azo a gani,saidai bata yada tsafta da
kuma qamshi ba,saboda dashi aka raineta.

Bata damu ba sam,tunda yanzu ta samu matsayin kiran malam da inna su


daga,ta kuma gaishesu,hakanan idan taje sun daina korota gida,iya wannan ya isheta.

Bushira na dan zuwa mata,itama idan taje unguwar takan qarasa gidansu
susha hira sosai,ta janye jikinta sosai da munira,idan tazo kadaram kadaham,ta
daina gaya mata kowanne yanayi da take ciki,hakanan ta daina shawara gaba daya da
ita.

*_WATA SABUWA......inji 'yan ca ca_*

Da yammacin ranar litinin,bayan ta idar da sallar la'asar ta fito parlor


zuwa kitchen don samarwa kanta abinda zata sanya a cikinta,don rabonta da abinci
tun breakfast da tayi da tea da two slices na bread.

Rasa me zata dafa tayi,saboda cikinta ne ita daya,tuntuni ta sauke dafa


abinci da bassam,don baya shigowa gidan sai dare ya tsala,sha biyu da rabi daya har
biyuma wani lokaci.

Busashen kifi ta gyara hade d wake,ta tsaida sanwar jalop din taliya da
wake da busashen kifi,saita koms parlor sanye da hijabin sallarta,hannunta maqale
da carbun nan counter wanda a yanzu bata rabo dashi.

Ta gama lazuminta zaman shurun ya mata yawa,saita kunna tv,abinda yakan


jima batayi ba kenan,ta fara kallon wani film na tarihin sahabbai daga wata tashar
da pure larabci,saidai kuma akwai subtitle na turanci.

Film din ya dan dauki hankalinta,saboda ta kwana biyu bata saka tv a


idanunta ba,har sai da sanwar ta jima tana tafasa sannan ta farga,ta miqe da
hanzari ta koma kitchen din,ta hada komai sannan tayo hanyar parlor din.

Cak ta tsaya ganin baqin da bata barsu a parlor din ba amma ta dawo ta
taras dasu,wasu a tsaye wasu a zaune,wasu kuma daga bakin qofa.

Mom ce ita da fahima fairuza da nasma,sai kuma anty billy wadda take
qanwa ce ga mom,shahararriyar mara mutunci ce,wadda bata dauki talaka a bakin komai
ba,tunda suka taba haduwa da iman sau biyu iman din bata sake bari sun gamu da ita
ba,saboda zallar kallin qasqanci da take jifarta dashi,ta lura ma kusan anty billyn
tafi mom zaqewa akan auren iman din da bassam.

Cikin dakiya da sanyawa ranta nutsuwa ta qaraso falon

"Sannunku da zuwa" ta fada a nutse,babu wansa ya kalleta ko ya tanka mata a


cikinsu,saima tsaki da Anty billy taja,tana mata wani irin kallo kamar zata sheqa
mata mari.

Batabi ta kanta ba tunda ita din ba dolenta bace,saita dubi mom

"Mom ku zauna,ga guri"


"Rasa wajen zama nayi tun daga cikin gida na da zanzo nan na
zauna?......kai.....David" ta qwala kira,saiga wasu daga cikin qattan ma'aikata
maza na gidan su hudu sun shigo

"Ku shiga store din gidan nan,ku fiddomin dukka wani kayan abinci da abinsha dake
ciki ku kawo min shi nan" tak iman din bata ce ba,sai ta koma gefe ta basu hanya
kawai tana kallon ikon Allah,gami da tambayar kanta abinda yake faruwa.

Kusan mintuna goma suka kwashe suna fidda kayan,hadda buhun shinkafar da
aka bude aka fara amfani dashi,matsowa tayi gaban kayan,ta nuna shinkafar da aka
fara amfani da ita tace a maida store din,amma dukkan wasu sauran abubuwan amfani
da kayan alatu,kama daga waken gwangwani,kifin gwangwani,indomie,madara lemuka
ruwan roba kai hatta da kifi da nama dake cikin fridge tasa an fiddasu,duka aka
tattare mata su tace akai sashenta.

Dubanta tayi sosai bayan sun fice


"Nasan zaki ta yiwa kanki tambayar dalilin da yasa na aikata haka ko?,to ba komai
bane illa gajiya da nayi da ganin ana ciyar da banza wofi,wata shida da aure amma
banga alamun samun qaruwa ba,dan tofe tofen yawu da amai da zazzabin dare duka
babu,to meye amfanin ci dake?,dadin ai yayi miki yawa,ki kwana a ac,kici me kyau
kisha mekyau,ku saka suttura me tsada amma baby wanu alfanu da kike kawo
mana........"

"Wallahi ya hafsa sakar mata maqoshin da kukayi ne ma yasa kwanaki can ta fara
yunqurin soma rashin mutuncin nan" kai mom ta girgiza tana kallon billy
"Ai ni ba'a haifi matar da dana zai auro ta rainani ba,kosu mimi da ake gani muna
zaune lafiya bina suke su da iyayensu suke wasu,wanda idan ama fadi sunansu ansan
da zamansu,idan ita ban isa da ita ba ai na isa da dana ko?......saboda haka" ta
fada tana maida dubanta ga iman

"Ki kwana da sanin bassam aure xaya qara,yarinyar da zai aura din tana nan zuwa
cikin gidan nan don su fahimci juna,wannan satin ko kuma sati na sama" daga haka
suka juya suka fice daga sashen nata.

Shuruuuuu tayi bata iya tanka musu da komai ba,bakinta ya riga da yayi
nauyi,idan ma tace zata tanka din me zatace musu?,kowa ya siya rariya yasan zata
zubda ruwa,kome ya faru da ita ta jawa kanta,idanunta keta radadin yajin tara
hawaye amma ta daure ta hana kanta,bata dawo saiti ba saida hancinta ya fara jiyo
mata qaurin girkin data dora,kamar wadda babu laka a jikinta ra nufi kitchen din,ta
kashe gas din gaba daya ba tare data damu ta duba ya dahu ko bai dahu ba,illa dai
ta bude tukunyar,tabi abincin da kallo kamar wata shashasha,so take taga meye
abinda bata ci a gidansu?,meye malam bai ciyar da ita ba?,meye yayyenta basa siya
mata idan tace tana da buqata?,wacce cima ce sabuwa a wajenta cikin abinciccikan
dake cikin gidan?malam da 'yan uwanta ba ragwage bane,basu yarda taga wani kalar
abincin a wani gida tayi sha'awarsa ba'a girka shi a gidansu ba,saita saki murfin
tukunyar,ta sulale a wajen,ta kuma saki kukan da taketa faman hana kanta yi,abincin
da bata ci ba kenan.

A kwanakin ta fahimci abinda mom din ta aikata da sanin bassam,tunda


gaba daya duk wani abu na buqata idan yanaso sassan mom din yake tafiya abinsa ya
dauka yayi sha'anin gabansa dashi,idan kuma na amfanin koda yaushe ne,sai yake
zubawa cikin freezer na falonshi yake amfanin da abunsa.

Koda wasa bata taba daga kai kota nuha ta damu ba ko ta gane abinda yake
aikatawan,a yanzun saukowar iyayenta yafi komai dadada mata rai,hakanan ta fannin
abinci dama a yanzun ba wani shiga cikinta yake sosai,so duk abinda ta samu ci take
ta kwanta,idan bai mata ba kuma tana fiddawa cikin kudinta tayi magana da masu gadi
su siyo mata,ko kuma ita din idan ta fita,musamman ranakun ganin likitanta,ganin
likitan da babu abinda ya shalli bassam dashi,komai ita ke kashewa kanta cikin
abinda yake ajjiye mata ada,don a yanzun ya daina ajjiye mata komai,tasan kuma duka
daga umarnin mom ne,da kuma shima halinsa da ya bayyanar mata qarara a yanzu.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 34

Tun tana bedroom dinta take jiyo motsi da kai kawo cikin falonta,da fari
tayi tunanin bassam ne,to amma jin motsin na sake matsowa dakunan kusa da ita ya
sanyata ta zura gyara zaman hijabinta,ta ajjiye alqur'anin data qulla qawance dashi
ta leeqo don ganin abinda ke faruwa.

Mamakine sosai ya cikata ganinsu fahima na wucewa da kayayyaki dakin dake


bashi da tazara da nata,sai ta jinjina kai,batace musu komai ba ta juya zuwa
ciki,don dama basu ganta ba,saidai kuma har yanzu tana tunanin abinda zasuyi cikin
dakin,dawowa sukayi part dinta ko kuwa?,saita aje tunanin a gefe guda,ganin cewa
bazai amfaneta da komai ba,ita dake lallaba lafiyarta a yanzun.

Ta jima tana jin motsi da buruntunsu amma duk da haka bata tashi ba,taci
gaba da zarafin gabanta,har zuwa sanda ta gama abunda takeyi din,ta fita zuwa
kitchen don ta laluba ko zata samu abinda zata iya ci.

Ta qofar dakin tabi,an jashi an kulleshi,saidai kana iya jiyo qamshin


freshner dake tasowa daga cikin dakin,saita kauda kai ta qarasa kitchen din.

Dube dube ta tsaya yi,sai a sannan ta tabbatar lallai bata da wani


sauran abinda zata iya ci cikin gidan,shinkafar data rage itama a yanzun babu
ita,duk kyau girma da qayatuwar kitchen din dama gidan gaba daya amma babu abincin
da dan adam zaici?,wani abu ya tsaya mata a wuya,tsahon rayuwarta a gidansu,bata
taba bude ido a ma'ajiyar abincinsu taga babu shinkafa sama da kwano biyar ba,sai
gashi yau a gidan aurenta,gidan da kowa yakema kallon ta samu aljannar duniya,gidan
da ake ganin koda da dawisu da talo talo taso zata ciyar da kanta,a yau shinkafa
gwangwani daya ta gagareta,ruwan famfo shine ruwan shanta musamman idan tayi saken
da pure water dinta ya qare,ita kanta batasan suna ko ma'anar auren nan nata
ba,saidai kawai tana so tayi biyayya ga abinda yagana tace,ko Allah zaisa ta zame
mafa hujja kuma shaida a nan gaba.

Ruwan Lipton ta hada da kuma bread ta dawo dakinta,tana lissafa kwanakin


da suka rage da zata koma ganin likita,daga can zata siyo abubuwan da suka samu
kafin ta samu ganin bassam ta shaida masa,sabida a yanzu bata da guarantee na
lokacin ganinsa.

Abunda yake bata mamaki yadda sam mom bata damu da irin daren da yake
kaiwa ba kafin ya kawo cikin gidan,abinda ta fuskanta shine,hakan yana yiwa mom
dadi saboda kawai a cusgunawa iman,bata damu da illar da hakan take dashi ba,bata
damu da me sakamakon hakan zai haifar ba.

********. *******. *******

K'arfe biyu na rana tana zaune a falon tana yankan farcenta,sanye take d
wasu blue black material wanda aka yiwa dinkin doguwar riga bubu,saiya yane kanta
da babban dankwalin rigar,ta zauna anan dinne saboda tadanyi kallo fa ragewa kanta
kewa da zaman kadaici,wanda dr ahmad ya gargadeta da hakan,baisan cewa zaman
kadaici ya zama wani bangare na rayuwarta ba.

Kamshin turarensa daya fara busowa sosai cikin falon ya sanyata dago da
kanta,bassam dinne yayi kwalliya sosai cikin qananun kaya,yayi kyau babu
qarya,kasancewar yana da wannan baiwae ga daukar ido duk sanda yayi ado,rabonta da
ganinsa idan bata manta ba zata iya cewa yau kwanaki bakwai ko takwas kenan,saita
dauka kanta taci gaba da abinda takeyi,yayin da shi kuma ha qaraso inda take
zaunen,idanunsa a kanta.

Sosai tayi masa kyau,duk biye biyensa har yau bai taba haduwa da mace me
sassanyan kyau haka me tafiya da hankali ba irin iman din,duk da cewa ba wata
zuzzurfar mu'amala bace take shiga tsakaninsu amma yayi missing skin nata mai
taushi da wani irin qamshi,yasha kwatanta yadda zai tsinci kansa idan ya shiga
duniyarta ta zahiri.....yanaji a ransa lokaci ya kusa da zai sanya jessica koda
bata qaunar Allah ta kawo qarshen abindata aikata masa.

Wannan sharetan da yayi yanaji a ransa shine hanyar da zaibi kawai ya


hukuntata,ya kuma nade tabarmar kunyarsa tsaf da hauka,sannan ta yaya kamar shi,shi
din da mata ke Rububi mace kamar iman 'yar tsakuwa a cikin 'yammatansa,sabida tayi
fushi ya zubda ajinsa ya lallasheta ko ya bata haquri?,yayin imanin dole tata zata
kawota,a nan zai jata a qasa ya kuma nuna mata iyakarta,ta yadda nan gaba ko kara
ya sanya ba zatayi sha'awar tsallakewa ba,shi yasa yaji dadin kwashe kayan abincin
da mom tayi,ko iya su zasu ta kawo kanta gareshi.

Ya zaci zata furta wani abu,amma sai yaga ko sashen da yake ma bata
kalla ba,har ya qaraci tsaiwarsa da gyara tie da kuma hannun rigarsa ya soma
ganganrawa zai fice,mamaki fal ranshi,wanne irin miskilanci gareta,ya zaci kawo
yanzu zatayi laushi tazo ta nema sulhu kamar yadda abokansa ke bashi labarin yadda
sukeyi da matansu idan suka kamasu da laifi makamancin haka,sai gashi ita sake
dauke masa wuta ma tayi gaba daya.

Karamin tsaki taja sanda ya fita,tana jin yana sake sire mata a rai,ji take
kamar ta tattara kayanta tabar gidan,saidai kuma bataso tayi kunnen uwar shegu da
maganar yagana,abinda ke sake taka mata burki kenan.

Tana nan zaune a wajen tana ta so ta tashi,amma wani film da ake


haskawa ya tsaidata,ta dauke idanunta daga kan tv zuwa bakin qofar falota sanda
taji hayaniya,ana kuma qoqarin shigowa falon.

Fahima ce kan gaba dauke da trolley,tanata faman zuba hira da mutanen


dake bayanta,don har waiwayawa take,sai fairuza daga bayan nata,da kuma wata
baquwar fuska na wata fara qal din matashiya.

Dukkansu sun hada ido da ita,amma sai kowa yayi kamar bai ganta ba,suna
takowa zuwa cikin falon tare da ci gaba da hirarsu,wanda rabinta cikin harshen
turanci sukeyinta.

Dab da zasu giftata matashiyar cikinsu wadda itace baquwar fuska a


cikinsu a wajen iman ta sake kallon iman din sosai,sannan suka wuce,qofar dakin
dataji motsinsu a jiya taga fahima tasa key ta bude sun shiga gaba dayansu.

Ko zama basu gama yi ba ta sake jin motsi,saiga bassam ya shigo,tabi


hannuwansa da kallo,yana riqe da wata qaramar jaka mahadin trolley din dasu fairuza
suka riqo,daya hannun nashi kuma babbar leda ce,wadda duk da baka iya ganin abinda
yake ciki xaka fahimci takeaway ne,walau na abinci ko na kayan maqulashe.

Duk da dakewar da yayi amma yanayinsa yadan sauya,kamar bai danji dadin
ganinta a wajen a zaune ba,kafin ya qaraso ma saita miqe abinta tana daukar
hijabinta dake aje gefe ta wuce dakinta tabar musu falon.

Aqalla awa wajen uku tana ci gaba da jin hirarrakinsu da darunsu daga can
dakin,tun tana jurewa har suka fara cikata,saita qarasa bakin qofarta ta rufeta ta
murza key,abinda yasa gaba daya ta daina jiyo motsinsu.

Duk yadda taso kauda tunani da mamakin abinda ke faruwa cikin gidan amma
hakan yaqi yiwuwa,ta gaza fahimtar komai,idan banda jahilci ta yaya za'a sauki baqo
cikin gidanta amma a gaza gaya mata?,wanne irin tsarine wannan.

Ranar gaba daya a dakinta ta qarar da wuninta,har zuwa dare,ta gama


karatunta da sallolinta ta kashe fitila ta kwanta,bayan ta saita alarm saboda
tanaso gobe ta tashi da dan wuri zata asibiti ganin dr ahmad.

********Karfe goma na safiya ta gama shirinta tsaf cikin abaya,wanda mafi yawa tafi
sanyata idan zata fita,duk da yada ta sauya,duk kuma da yanayi na rashin kwanciyar
hankalin da take ciki amma hakan bai hanata yin kyau ba,kamar wata balariya haka ta
fito,ta murza key din da tun yammacin jiya ta sanyashi bata bude ba sai yanzu.

Tana isowa falon qamshi ya daki hancinta,koda ba'a gaya mata ba tasan
cewa daga cikin kitchen dinta qamshin yake fitowa,idanunta suka sauka a qofar
dakin,qofar a bude take,saidai ba gaba daya ba,an dan sayata ne,labule kuma ya qara
rufe sauran gurbin da qofar bata rufe ba.

Tana iya jiyo sound na murya na tashi daga cikin dakin,sai ta dinga jiyo
kamar muryar bassam,amma zuciyarta taqi aminta da hakan,saboa bataga abinda zai
kaishi dakin ba ida ana magana na abinda ya kamata,tayi qoqarin dannen zuciyarta,ta
qara takawa zuwa gaba tana duba gurbin data ajjiye milkshake dinta jiya tana fatan
Allah yasa bai lalace ba,sabida shi kadai ya rage mata a gidan.

Balle murfin tayi takai bakinta,dai dai lakacin da qofar dakin ra


motsa,labulen ya daga,tana shirin dauke idanunta bassam na fitowa daga dakin,bai
kuma lura da ita ba yayi gaba zuwa kitchen,saiga yarinyar jiya na biye dashi,sanye
da kayan bacci masu sulbi,wadanda suka bi jikinta suka kwanta,sumar kanta kuma a
bayyane saboda rashin saka dankwali.

Saura kadan ta qware Allah ya taimaketa ta dawo dashi zuwa bakinta,sai


ta dire kwalin kanta yana sarawa,ta daure a hankali ta juya tana laluben hanya ta
fita daga parlor din.

Sai data kusa minti talatin zaune cikin motarta tana qoqarin daidaita
kanta,kuka take sonyi amma kuma ya kasa zuwa,sai zafi da zuciyarta keyi,cikin zafin
nama ta kunna motar ta kuma tasheta ta figeta da gudu.

A minti talatin take zuwa asibitin dr ahmad,amma a yay minti ashirin


ne ya kaita,tana zuwa mutum biyune a gabanta,saita zauna kawai tana bin kowa da
idanu har zuwa sanda akayi kiran sunanta.

Kallo daya dr ahmad din yayi mata ya tabbatar bata rabu da matsala ba

"Lafiya kike kuwa hajjaju?" Kamar jira take dama ya tambayeta,sai kawai ta fashe
masa da kuka,ta gaza riqe wajjaj damuwar,abun yana neman fin kwanyarta.

"Subhanallah......subhanallah" ya dinga maimaitawa cikin


nutsuwarsa,idanunsa na kan yatsun hannayensa yana dubansu,saboda babu tayadda zai
kalli fuskar matar wani,duk da taja mayafin abayarta ta lullube fiye da rabin
fuskarta.

Sai daya tabbatar ta rage dafin dake cikin zuciyarta,sai ya miqe ya


qaro gudun acn dake office din,sannan ya isa bakin fridge dinsa,ya debo ruwa da
lemo da cups,ya dawo bakin table din,ya zuba kowanne a cup ya ajjiye mata a
gabanta,sannan ya koma kujerarsa ya zauna yana cewa

"Bismillah,dauki kisha" tabbas tana da buqatar ruwa saboda yadda maqogoronta ya


bushe tas,duk da cewa bataci komai ba,amma sai ta dauki ruwan ta kurba,har sai data
ji bushewar maqogaron nata ya ragu sannan ta ajjiye.

"Nasha gaya miki,indai kinason lafiyar zuciyarki ki guji abinda zai bata
miki rai"

"Bani nake batawa kaina rai ba dr" a wannan karon kasa boye masa komai tayi,ta
bashi labarinta gaba daya,tana ji a ranta kamar ya al'ameen dinta ne a gabanta take
gaya masa matsalolinta.

Da farko fada ya sakeyi mata akan kuskuren data tafka tun farko kamar
yadda duk wanda yaji yake mata

"Iyaye ba wasa bane,saba musu da bujire musu shine kuskure mafi muni da dan adam
zaiyi a rayuwarsa,kome zaki gani yanzu cikin rayuwarki sakamakin bata musu ran da
kikayi ne,amm alhmdlh,tunda sun fara saukowa ki sanya ran samun raguwar
jarrabobinki.......inda ace ni isasheshene da zai iya yanke hukunci kan
al'amuranki,da na haramta aurenki da mijinki saboda bayyanar fasiqancinsa,amma bani
da wannan hurumin,shawara daya ce zan baki,ki tsananta addu'a babu ji babu gani
akan ubangiji yayi miki mafita mafi alkhairi,amma damuwa bata warware damuwa saidai
ta qara maka damuwa,ta kuma gadar maka da cututtukan da zasu iya naqasa rayuwarki"
kalamai masu kyau da ma'ana ta samu daga bakin dr ahmad,wanda hakan ya sanya ta
qara ganin kima da mutuncinsa a idanunta,yayi checking nata sosai,ya sake dorata
akan magunguna sa shawarwari,kafin tabaro asibitin ta samu relief sosai,sai kawai
ta wuce gidansu,ko banza idan taga inna zata sake samun wani sassaucin.

Bata koma gidan ba sai dab da isha'i,tana shiga suna cin karo dasu,suna
zaune dashe dashe a parlor dinta,yarinyar da har yau batasan sunanta ba,cikin
dressing din da bai kamata wani wanda yake ba muharraminta ba ya ganta da irin
wannan shigar ba,babu kowa a sahen daga shi sai ita suna kallo.

Sam ba tabarmar kunyar da bassam din ke nadewa ne ke damunta ba,ko kuma


yadda tazo ta samesun ba,don a yanzun ta sanya bassam din a ajin BABU,dashi da babu
duka daya haka ta saka a ranta,ita din kamar mai zaman jiran wa'adinta
ne........yadda mom ta bada dama aka kebance da danta na cikinta,aka basu dama suka
kadaice,bata ko kishin tarbiyyarsa,ama ture ta tata da suka raina,suke ganin bata
kai komai ba......wanda tana da yaqini da kuma tabbacin babu matar auren da zata
lamunci ayi mata haka,saidai ita din bassam ba shin a gabanta ba,shi da babu duk
daya take kallonsu,don haka ko kallon tsiya basu samu ba bare na arziqi,ta sanya
kai tayi ciki abunta,yayin da bassam.ya dage yana aika mata da miyagun maganganu
cike da fada da rashin daraja.

"Calm down baby..,..karka bari ta bata mana jin dadinmu mana" yarinyar
wadda ake kira da seema ta fada,saidai zuciya nata tunzurashi akan kada ya qyale
iman din,sai ya miqe

"Ina zuwa baby" yabi bayan iman din cikin fushi da jin cewa iman din ta
wulaqantashi.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 35

Towel ta daura ta kuma zura hijab,tana shirin shiga wanka bassam din ya
shigo,saidai kuma suna hada idanu kaifin abinda ya shigo dashi din ya ragu

"Ke.......kina jina ina miki magana saboda kin rainani kika shigo kika barni?wato
ga banza shasha mahaukaci ko?" Maimakon ta tanka masan kamar yadda yakeso
dinndai ,sai ta sake bawa banza ajiyarsa,ta qarasa ta dauki man wanke gashi ta
sakeyin gaba.

Sake fusata yayi sosai,ya daka mata tsawa yana cewa

"Na yarda da gaske kin rainani kamar yadda mom tace,saboda kinga kin dan fara riqe
kudade,kina cin mai kyau kisha me.kyau ki kwana a ac"

"Kul!" Ta fada itama cikin daga murya,abun sai ya bashi mamaki,ya buda idanunsa
yana kallonta,itama sosai ta bude nata idanun cikin nashi

"Karka kuskura ku zarme cikin maganganunka,shurun da nakeyi bawai yana gwada bansan
ciwon kaina ko bani da wayo ba,ina sane da komai,hakanan a shirye nake da faruwar
kowanne abu,ina cin me kyau?,ina abun yake?,ina qudan yake ballantana romonsa?,na
tabbatar sanda ka daukoni daga gidanmu ba haka nake ba,hakanan ba dusa muke ci
ba,maganar kwana a ac kuma kai kanka kasan ka fada ne don kaji dadin bakinka,ac ba
shine arziqi ko kuma kyau ba,inda shine......ni hajar bazanyi kyan da ka gani a
tattare dani ka nace sai da ka auroni ba......ka rabani da kowa nawa,kazo kana
gasani kuna nunamin baqin halayen da babu arziqi ko dattako ko kadan a cikinsa,na
rantse da Allah daga yau duk wanda ya sake takani saina takashi ko wayeshi,ka
gayawa sauran" tasowa yayi kamar xai daketa,wani jarumta tazo mata,ta dauki fitilar
gefa gado ta daga sama

"Duk randa ka sake ka kwatanta dukana,koda da wasa ne,wallahi wannan abar bata da
muhallin da zata fashe ta kuma tarwatse illa kanka" sake birkicewa yayi da
maganganun tabarmar kunya,ta bawa banza ajiyarsa ta shige bandaki ta murza key.

Famfo ta kunna saboda batason yaji sautin kukanta,ta dinga kuka sosai
tana kiran sunan Allah,daga nan tana jiyo yadda yake bin duka lockers dinta yana
kwashe kudaden da suke ciki yana fadin

"Zanyi maganinki,zakisan cewa bani da kyau,saboda kinga na sangartaki shi yasa kike
dukka iskancin da kikaga dama".

Cikin ikon Allah kafin ta baro bandakin zuciyarta tayi sanyi,data fito din
saita kulle dakinta,ta shirya ta jawo takeaway din data shigo dashi ta fara ciba
wani da yawa taci ba ta ture saboda yaddaa taste din bakinta ya dauke gaba daya,ta
ballo maganinta tasha ta kashe fitila ta haura gado ta kwanta,don ta hana kanta
tunani saita janyo wayarta,cikin karatuttukan malamai da take download ta ajjiye ta
buda daya ta fara sauraro,a hankali ta sake samun nutsuwa,ta tattara dukka
hankalinta akan karatun tana fahimtar kowanne lafazi dake fita daga bakin malamin.

Wata irin rayuwa ake gudanarwa cikin gidan musamman sassan iman din,kamar
wasu maguzawa ko kuma wadanda basusan addininsu ba,seema diyace ga tsohon
ambassador din nigeria a England,kuma 'yar qawace ta kurkusa a wajen mom,cikin
manyan qawayenta makusantanta,an dauko cancankat an kawota gidan da sunan su saba
da bassam kafin maganar aurensu,an kawota sashen iman din ba tare da neman yarda ko
amincewarta ba,basa yiwa iman din kallon komai face qasqantacciya wadda bata da
wani daraja ko kima saboda bata fito daga gidan nau'in mutane da suke da abun
duniya ba wato kudi.

Dukkan abinda suka ga dama yi suke a sassan nata,idan ka shigo zaka


tsammaci seema ce matar gidan,saboda gaba daga iman din ta tattara tabar musu
gidan,tayi qaura zuwa dakinta tana aiwatar da al'amurata,idan kaga ta fito tofa
saidai idan wani dalili me qarfi ne ya fiddota,tana gamawa kuma zata koma,bama
kasafai zaka ganta din ba,tunda babu kayan abinci bare tace xatayi girki,kayansu
lemuka da madara kawai data tara a dakinta sune abincinta,wanda suma suna kan
hanyar qarewa.

Hausawa sukace ba'a bawa kura ajiyar nama,a nan kuwa na bawa bassam,gaba
daya bassam ya ja iman ya ajjiye gefe,ko cigiyarta baya yi bare nemanta,domin kuwa
ya samu dukkan abunda yake buqata daga wajen seema,tsula tsiyarsa yake,ya samu
lasisin fiye da yadda yayi tunani,don zuwa lokacin ya samu makarin lalurarshi ba
tare daya bari jessica ta sani ba,babu abinda ya banbanta seema da matarsa,dukkansu
basu da wata damuwa ko tunanin ranar nadama.

*_KOMAI NISAN DARE gari zai waye_*

Tunda gari ya waye yau sashen nata shuru yake,babu motsin bassam bare na
seema,ko ba'a gaya mata ba kuma tasan sun fita ne tare,don wannan din ba wani baqon
lamari bane tattare dasu,hakan ya bata damar fitowa parlor ta dan zauna,saboda ta
rage muguwar kewa da zaman kadaicin dake damunta,zuwa yanzu ta fara qosawa,ta kuma
fara gajiya da abinda idanuwanta suke gani,sau tari zuciyata tana gaya mata ta
gudu,ko tayi yaji,saidai dukka haqurin da take tana yine saboda ta kafa hujja ya
kuma zame mata hujja,ba'a wajen yagana kadai da kullum take sake tausarta
ba,a'ah.....har sauran al'umma da duk mutumin da zai qalubalanceta a duk sanda
ubangiji yaga damar zartar da hukuncinsa akan zamanta.

"Salama alaikummm" sautin muryar dake dauke da gurbatacciyar hausa ya samu mazauni
a kunnuwan iman,cikin mamaki ta daga kai don jin daga inda sallamar ta fito.

Zabgegiyar macace sanye da mini skirt wanda inda zatayi kyakkyawan tsuguno
ba abinda zai hana bayyanar tsiraicinta,sai armless chiffon shirt v neck shape daya
bayyana kusan rabin qirjinta,kanta yasha lodin attach,yayin da hannunta yasa fixing
na faratan kanti,takalmin qafarta me igiya ne,mai azabar tsinin dunduniya kamar
wadda ta shirya tsokane idon duniya,tafkeken sun glasses din daya kusa cinye rabin
fuskarta na riqe a hannunta tana kallon iman,kamar yadda iman ke kallonta,tana son
tuna a inda ta taba ganin fuskarta,da kuma abinda ya kawo wannan halittar cikin
gidan

"Zan iya shigowa?" Ta tambayi iman tana ci gaba da kallonta,bata da zabin daya wuce
ce mata

"Bismillah" tana nuna mata wajen zama,saita qaraso cikin taku kamar zata karye
saboda tsinin takalminta,ta zauna saman kujerar tana ajjiye jakarta gefe,har yanzu
kuma idanunta yana kan fuskar iman,wanda har kallon ya soma sanyata ta tsargu.

Kaf sashen nata bata da wani ruwa bare lemo na roba da zata iya bata,don
haka ta gyara zamanta tana duban matar

"Kene matar bassam ko?" Ta tambayeta tana dage girarta

"Eh nice"

"Woww......a fili kafi kyau akan hoton daya nunamin" turus iman din tayi,kada dai
ace kwashe kwashen bassam ne har yakai suka fara biyoshi har cikin gida,lallai zai
kai gabar da kuma ba zata iya ci gaba da zuba masa ido ba"

"Am jessica.....oh....sorry ....ya taba gayamin baki karatu ba,ko secondary school
baki kammala ba ko,bari nayi magana da ausanku" sosai maganar ta daurewa iman
kai,saidai kafin ta gama wannan tunanin ta sake jefata a wani

"Da fariko......nazo wajenki ne da kyakyawan zuciya,zuciyana babu haushi a


kanki,abinda yasa nayi shawaran zuwa na fitar dake daga duhu shine,na farko ke
yarinya ne,bakasan komai akan duniya ba,na biyu kuma baka taba tsokanana rigima ko
wani abu ba mara dadi tsakanina dakai......ba kamar matan bassam na baya ba"

"Mata kuma?" Iman din fa fada a bayyane cikin mamakin daya fito fili ya bayyana
qarara saman fuskarta.

Kai Jessica ta kada tana dan qaramin murmushi

"Yes,wives na bassam ba,nasan baki sani ba......but keep calm,zan miki bayanin
komai .......idan zaki iya tunawa watanni da suka wuce an taba toro miki da pics na
mijinki shi da wata,to nice wannan din" zumbur iman ta miqe cikin bacin rai

"Tashi ki fitarmin a gida annamimiya arniyar banza,me kikazo kuma yimin?,saboda


kinga wancan lokacin na qyaleki ban kulaki ba,shine kikayo tattaki har cikin gida?"
Hankali kwance Jessica ta dubeta

"Karki tashi hankalinki mana,koda na tashi na tafi,tafiyana babu abinda zai


canza,saima wargaza miki naki rayuwan,ki tsaya ki saurareni,daga qarshe koma meye
saika fada" wani sashe na zuciyarta taji yana umartarta ta bata dama,saita koma ta
zauna tana huci,saidai ba cikin kujerar ba,a hannun kujera ta zauna wannan karon,da
shirin kota kwana,ko zata kawo mata rainin hankali,idan seema ta samu daurin gindin
mom tana abinda taga dama.....ita kuma jessica fa?,na meye zata sakewa sauran?.

"Kamar yadda na gaya miki sunana,ni din ba 'yar garin nan bace,abinda
ya kawo nan din karatu ne,shekarata goma tare da bassam muna soyayya dashi,asalin
fara soyayyarmu kuwa ya nuna min zai aureni ne,nayi masa tuni da bambancin
addininmu yace babu matsala,shi wannan ba matsala bane a gidansu,tun a sannan
mahaifinsa yana da rai,ashe bassam ya fada ne kawai saboda ya samu kaina ya
lalatani,ni kuma a sannan ban sani ba,na bashi amanar kaina da rayuwata sai yadda
yayi dani,na sani tu a lokacin bassam yana da farinjinin 'yammata,wanda yawancinsu
kudi da kyau da yake dashi yake rudarsu,to ban damu ba sosai saboda ban zaci yana
nemansu bane kamar yadda yake nema na,sai daga bisani na gane hakan,mukayita tashin
hankali dashi,daga baya na haqura na qyaleshi saboda na fuskanci a jininsa ne,bazai
daina kulasu ba,naci gaba da biye masa tare da nace masa kan maganar aure na,amma
har muka dibi shekaru biyar bassam yaqi yarda da maganata,a haka muka shiga shekara
ta shida,a sannan ne na samu ciki,wadda na tabbatar da cewa bassam ne yayimin
shi,tunda a sannan babu wanda nake kulawa saishi,qememe yace a zubar dashi ko na
rabu dashi,ni kuwa naqi,saboda a tamu al'adar mu ba abun ku ya bane don kina tare
da saurayinki kinyi ciki kin haihu,kina iya tara yara hudu biyar har fiye da haka
da saurayi,sai daga bisani idan kuna tare a daura muku aure da yaranku.

Barazanar daya shiga yimin yasa na tattare na koma qauyenmu,ya daina jin
duriyata da labarina gaba daya,acan nayi rainon cikina na haifi yarinya mace,sai
data isa yaye shekara daya da rabi na dawo rayuwar bassam,nayi gyara na musamman
saboda nasan lagonsa,ina dawowa kuwa ko takan cikina baibi ba aka dora da
sabgogi,abinda bai sani ba lamfo nake masa ina bibiyar duka rayuwarsa,saidai ashe
nima lamfo yayimin,sanda na dawo masa da maganar aurenmu yace shi Allah ya
tsareshi,me zaiyi da ragowar wasu,maganar ga batan rai,tunda ko ragowar wasunne ni
ai shine ya fara nunan hanya,a sannan munyi bacin rai dashi irin wanda bamu taba yi
ba,na tattare komai nawa muka rabu,amma a raina akwai shirin daukan fansa,saboda
haka na fara binciken abubuwan da suka shafeshi da yake boyewa,wanda idan suka
bayyana zasuyi destroying dinsa.

Cikin abinda na gano kuwa harda aure da yayi na mata uku,daya ya


saketa,biyu yana zaune dasu ba tare da kowacce tasan da 'yaruwarta ba,sannan
mamanshi ma batasan da auren ba,saboda auren sirri yayi abunsa na watanni,idan ya
gama morar yarinya saiya rabu da ita ya koreta.

A sannan daya daga cikinsu nada ciki,kishi yasa na dawo rayuwar bassam,na
fara nunawa matansa cewa akwai wata fa tare dashi,sai muka shiga gwabzawa dasu,inda
daga qarshe basu cimma nasara ba,lokacin daya diba na sakinsu yayi ya rabu dasu.

Unfortunately ba'a dauki dogon lokaci da rabuwarsu ba na tsinci labarin


xaiyi aure,dana tareshi da zancan kansa tsaye yacemin eh aure zaiyi,abun ya
girgizani ya kuma bani mamaki,na dinga son insan wacece wannan data sauya ma bassam
ra'ayi lokaci daya,ya kuma aminta zai aureta?,saidai ban samu wannan damar
ba,saboda gida dana koma can garinmu,'yarmu da bassam baisan da ita ba bata da
lpy,inacan kuma ban dawo ba har ya rage saura kwana uku daurin aure,wannan shi ya
wargazamin duka plan dina,amma dana bawa sister na labari,saita kawo shawarar na
kassara mazantakansa,tunda dai shine taqamar kowanne namiji,ta yadda babu wata mace
da zai iya tsinanawa komai indai bani ba,a wajena ne kawai zai iya kasancewa
namiji,wannan itace hanya guda daya da zata mallakamin shi,tasa ya dawo tafin
hannuna"

"Sosai shawarar ta yimin,ta kuma faranta min rai,ana ya gobe daurin aure
na tura masa Tex,na tayashi murna,nayi masa kuma albishir din abinda ke shirin
samunsa,ya kirani ya zazzageni,yace shi zan yiwa barazana,ni kuma nace masa maji ma
gani.

Bayan yaje ya tabbatar da abinda na gaya masa,wannan shine abunda yayi


sikar dawowarsa wajena,muma sake zama kamar miji da mata ni dashi,yaso kasancewa
tare dake qwarai da gaske,saboda yadda zuciyarsa ta cika da sha'awarki tun sanda ya
fara ganinki,don ko lokuttan da yake tare dani ke yake ambata......yaso yayi
mu'amala dake da farko kamar yadda yakewa kowacce mace,bansan me ya gamo ya kasa
aiwatar da wannan ba,ya juya manufar zuwa ta aure a kanki,amma daya daga cikin
dalilan da na sani shine......ya aureki ne don ya bunne barnar da yake
aikatawa,saboda kedin kina da qananun shekaru akanmu,ba zaki takurashi ko hanashi
yayi yadda yakeso ba.

At last saqon da nazo dashi gareki na ceton rai ne,saboda ni na riga na


fada,no way out......bassam ya fara harka da wata yarinya serah,yarinyar da nake da
dukkan tabbaci da yaqinin tana da cutar HIV,ban kuma ankare da hakan ba saida suka
fafa nisa a mu'amala,zuwa sannan kuma me afkuwa ta afku......anan ne kuma na
fahimci cewa ya warke ya samu makarin sihirin da nayi masa,idan kinsan har yau bai
nemeki ba......to ki kubutar da kanki.....ki tseratar da quruciyarki,idan kuma an
riga an gamu......sai nace miki ina miki jaje,ni ban damu ba da kaina,saboda ko
babu komai na hada iri dashi......." Saita miqe tana maida glass dinta

"Dukka cikin kalamaina babu qarya ko daya,idan akwai ubangiji ya hukuntani,na fada
miki ne sabida nayi ceto ga innocent soul,na barki lafiya".

Zata iya cewa inuwar jessica itace abu na qarshe data iya gani,sai bude
idanunta tayi taga daya daga cikin ma'aikatan gidan mata a gefanta[7/19, 10:02 PM]
Mummyn Yara: 36

Sai data sake bude idanunta sosai taji tana yi mata sannu sannan ta fahimci
suma tayi a wajen,a hankali qwaqwalwarta ta fara tariyo mata abunda ya faru zuwan
Jessica da kuma abubuwan data shaida mata,kuka sosai ta fashe dashi,sannan ta miqe
da sauri ba tare data kalli matar dake gefan nata ba,tsanar gidan da tsanar duk
wani abu da kuma duk wani mutum dake gidan tana darsuwa a
ranta,bassam?,bassam.......ashe shidin furen kan juji ne?,ashe baqin maciji ne shi
mai dauke da mugun dafi?,irin dafin da idan ya tsartu ga gangar jiki yake ɗai ɗaita
jiki,ya kuma haifar da mummunar illar da bata warkewa.

Takai ta kawo yafi sau shurin masaki,ta rasa wacce shawara ya kamata ta
yanke?,meye abu na qarshe daya kamata tayi?,don dai tabbas indai ya tabbata dukka
abinda jessica ta fada haka yake.....babu wani sauran zama tsakaninta da bassam har
gaban abada.

Fitowa na ukun da tayi zuwa falon kamar me neman wani abu,yayi dai dai
da shigowar bassam da seema,saidai wata irin shigowa sukayi,tana gaba fuuuu yana
binta a baya

"Haba mana seema....tun a hanya nake fama dake ki tsaya ki saurareni.......na


rantse miki babu wani abu da yake tsakanina da ita fa?" Ko juyowa ta kalleshi seema
batayi ba ta shige dakinta,kana ta fito ta sake wuceshi,ya soma takawa zai bita
yana kiran sunanta,saidai tuni ta fice abinta.

"Damnit" ya fada yana yarfar da hannuwansa,da alama abun baiyi masa dadi
ba,wasu hawaye masu dumi suka saukowa iman tana kallon fuskarsa ba tare da ya sani
ba,babu abinda take hangowa sai lokacin da ya yaudareta,ya kawota duniyarsa bisa
kyakkyawan zaton zata samu dukkan wata kulawa data dace da diya mace,ta miqa masa
dukkan yardarta,ta zama butulu kufan wuta ga ya ameen dinta,mutumin da ya sota fiye
da kowa a duniya

"Ke kuma meye kika wani tsaya kina kallon mutane kamar baki sansu ba" cikin muryar
kuka ta fara magana

"Ina kallon mayaudariya kuma maha'inciyar fuska,azzaluma wadda bata damu da gobenta
ba bare na wani,fuskar da take iya fuskantar kowanne zunubi,take iya mu'amala harda
kafirai maqiya Allah da ma'aiki irinsu Jessica" sosai taha reaction na fuskarsa ya
sauya sanda ta ambaci sunan Jessica din

"Ke!,banason hauka da rashin hankali fa?,kisan me bakinki yake fada,to sai


meye?,sai mene?,babu abinda zan nema ban samu ba cikin rayuwata,sai na kasa jin
dadin rayuwata?,sana ragi kaina?,bazai yiwuwu ba,kinga....ni ba kalar mazan da suke
daukan raini daga matayensu bane"

"Raini shine abu mafi sauqi da zaka samu daga gareni idan na yarda na zauna
dakai......"
"Ba sai....." Maganarsa ta tsaya sanda yajiyo muryar mom tana qwala masa
kira,hankalinsa ya tashi,saboda ya tabbatar seema qararshi takai wajen mom,ba'a
cika sakanni ba mom din ta bayyana cikin parlor din,kamar kullum cikin takun
qasaita take takowa cikin falon,taku dai dai kamar qasa ba zata iya daukarta
ba,saboda jin izza da kuma isa

"Me ka yiwa seema?" Tambayar da tayi masa kenan tana cika tana batsewa,gami da jefa
harara ta musamman ga iman,wadda take tsammanin kamar tana da hannu kan bacin ran
seeman data hada kayanta tana iqirarin tafiya

"Bab....ba komai fa mom....kawai......"

"Bassam" iman ta kirashi a kaurare,saboda a yanzun idanunta basa ganin kowa,bacin


ranta kuma yana ninka na baya ne

"Wuce muje sassa na daga kai har seeman" mom ta fada tana tsareshi da idanu,da
hanzari iman tasha gabansa ganin yana yunqurin fita

"Dakata malam.....yau zamana dakai ya qare a gidan nan,bazan iya zama da fasiqin
namiji ba"

"And so what?.....ga hanya nan ki tafi,ke kika rasa bani ba,don na taimakeki,na
miki gata,na kawoki rayuwar wadata shine zaki dinga fiffiqemin kina min wannan
fitsarar" ya fada a tsawace.

Baya tayi tana girgiza kanta,zuciyarta kamar zata fado,sai kuma ta juya da
gudu tayi dakinta,duk da gunjin kukan da take amma tana jiyo muryar mom tana cewa

"Ko bata fada ba zamanku ya qare,a gabana saboda ita din ba 'yar gidan mutunci
bace?,dama ni na gaji da wannan auren,gwara ayi komai a gama tsakaninka da
seema,nima sai hankalina yafi kwanciya"

Ma'ajiyar jakankunanta ta nufa ta fara hargitsosu tana dubawa ko zata


dace da wadda keda kudi a ciki,saboda ta tabbatar a yau din ta tashi bata da komai.

Saidai har ta gama bincikenta bata samu kudin da takejin zasu kaita inda
take lissafa zata je din ba,abu daya ta sani,koda a qafa ne.....koda me zaya faru
ba zata sake kwana cikin wannan gidan ba,gidan da dashi da maqabarta a wajenta
bashi da maraba.

Hijabin da take sala ta janyo ta zura,sannan ta sanya slipper din da take


yawo dashi tsakanin bedroom dinta zuwa parlour,taku daya biyu sai ta tsaya cak,ta
kuma sauke ajiyar zuciya,ta dawo da baya da hanzari ta buda wata locker ta sanya
hannu,saiga atm ta fito dashi,tsahon xamanta a gidan ta manta dashi,saboda koda
yaushe akwai kudi available kuma cash,qaramar purse da batayi niyyar dauka ba ada
ta koma ta dauka,ta jefa atm din da wayarta a ciki,cikin wani irin hanzari da kuma
sauri kamar wadda za'a kama ko ace dawo ta qara gaba.

Karo na farko a rayuwarta data doshi tasha da sunan tafiya wani gari,kai
tsaye ta nema motar dake lodi zuwa maiduguri,bayan ta tsaya a wani atm machine ta
cira kudaden da tasan zasu iya kaita duk inda ta nufa,tun cikin napep akan hanya
tasan cewa bata da wani qwarin gwiwa da zata doshi inna malam ko uwa uba yaya
sadiqu da wata matsala data shafi aurenta,matuqar ba dan saukowar da sukayi bane
takeso ta rushe wannan sassaucin a tsakaninsu,a yanzu bata da kowa.....bata da
wanda zata dosa idan ba yagana ba,ita kadai ce madafarta,ita daya ce takejin zata
tallafi wannan raunin nata.

Tafiya mai cike da wahala da quncin zuciya tayi,don tunda suka tashi daga
kano har suka isa maiduguri......tsahon awannin batakai koda ruwa bakinta ba,a
hakan a lexirouse taje......saidai yadda takeji kanta dama jikinta kamar wadda ta
tafi a kori kura ko kuma 'yar qurqura,wahala tako ina,don ko bayan sun sauka da
qyar ta samu me abun hawan daya amince zai kaita unguwarau yagana sabida dare da
yayi,uwa uba shi daya ne ya gane kwatancen da taketa yi masa da qyar,ya tsula mata
kudi kuwa sosai,amma bata damu ba,don ba wannan bace matsalarta,burinta shine ta
ganta gata ga ya gana,ta kuma karba mata 'yancinta,ta rabata da auren bassam a
kanta.

Tsoro ne ya kama yagana sanda taga iman din,daga bisani mamakin ya maye
gurbin tsoron

"Hajaru.....daga ina haka a wannan daren?" Maimakon ta bata amsa saita fashe da
wani irin kuka,tamkar rarraunan marayan daya rasa uwa da uba duka a lokaci guda.

"Subhanallahi,hajar wani ne ya rasu acan kanon?" Kai ta girgiza mata


alamun a'ah saboda ganin yadda hankalinta yayi mugun tashi

"Ki lallabata a hankali" alhj bukari mijin yagana ya fada bayan ya gama tausar iman
din,ya fice ya basu waje.

Sai data rama sallolin dake kanta,ya gana ta gabatar mata da abinci duk
da cewa dare yayi,amma sai ta kasa ci,abinda yasa ta hada mata abu me ruwa ruwa da
kuma zaqi wanda take ganin zata iya sha.

Ba wani da yawa tasha ba ta ture,bata matsanta mata ba ta dauka ya


rufe,sannan cikin kwantar da hankali ya gana ta sake tambayarta.

Kamar wancan karon.....babu abinda iman din ta rufewa yagana,cikin matuqar


tashin hankali take tafa hannaye tare da dauko dogon salati

"Allah mun gode maka daya kare mana ke,Allah abun godiya,wato shi yasan manufarsa
da tun farko yaaa farkarsa tayi masa sihirin da ya zama hoto,da tuni yanzu wani
zancan ake akanki kenan iman ba wannan ba?" Yagana ta fadi tana dafe kanta cike da
zallar kaduwa da kuma tsoro.

Kai iman din ta jinjina hawayen mai radadi da zafi suna sake sauka akan
kuncinta

"Ki kwanta kiyi bacci,kada ki sanya wata damuwa cikin ranki,aure kamar an rabashi
an gama,ai zama ya kuma qare,babu wani zancan gyara ko sasanci,da wannan cutar?,mu
godewa Allah daya tsayar ma iya nan,yanzu zanje mu tattauna da alhaji,don musan ya
za'a bullowa abun,dole khalilu ya sani shima,tunda abune daya shafi jininka" sai
data tabbatar iman ta kwanta sannan ta yunqura ta miqe ta fice zuwa dakin mai
gidanka.

Idan tace tayi cikakken barci a daren tayi qarya,juyi kawai ta dunga yi
tana tariyo rayuwarta,tun daga sanda ta fara mallakar hankalinta har zuwa
yanzu,abubuwan da suka dinga faruwa,musamman lokacin aurenta da bassam,da yawa
gangancinta ne ya janyosu,ta runtse idanunta tana jin wani ciwo a qirjinta tana
hango kanta tsaye gaban ga ameen tana zazzaga masa rashin kunya dukka akan
bassam,ta fashe da kuka mara sauti bayan tayi qoqarin rufe bakinta,tana jin wani
irin kaico da muguwar nadama suna shigarta,jikinta ya dinga kakkarwa,kadan ya rage
hawan jininta ya dawo da mugun qarfi,cikin taimakon Allah ta dinga ambatar sunan
Allahn,yakawo mata dauki komai ya daidaita,gab da asuba wani wahalallen bacci mai
mafarkai barkatai marasa dadi yayi awon gaba da ita.

Lokacin data farka don yin sallar Asubar kanta yayi wani mugun nauyi,ta
lallaba cikin toilet din dake dakin ta daura alwala tazo ta bada farali,ta dan jima
saman abun sallar tana addu'o'i na tuba neman rahama gafara da yafiya da kuma sauqi
a dukkanin rayuwar da zata risketa a nan gaba.

Sai data tabbatar ta gaji da zaman sannan ta janyo wayarta don duba
lokaci,sai idanunta suka fada kan envelope dake fuskar wayarta,wadda ta fado da
sunan bassam,tasa hannunta ta bude wayar sannan ta bude envelope din ta fara duba
saqon

*_Ni Bassam balarabe madaki,na saki matata iman saki daya_*

Sau biyu gabanta ya fadi lokaci guda bayab ta gama karanta gajeran
saqon,ta duba da kyau tabbas number bassam dince,saita lumshe idanunta tana sakin
wani numfashi me nauyi daga qirjinta,wanda bayan fitar numfashin......sai taji
kamar ya fita ne tare da dukkan wani nauyi daya jima a qirjinta,nauyin da taji ya
saukar mata tun ranar da aka daura mata aure,watanni tara baya kenan cikin na
goma,bata ji kuma ya sauka ba sai a yau din,maimakon taji dimuwa ko kuma
damuwa,a'ah ,sai ta jita sakayau,a nan taja pillow ta maida kanta ta kwanta,tana
lumshe kyawawan blue eyes dinta,cikin zuciyarta da kuma labbanta dake motsawa tana
fadin

"Alhamdulillah....alhamdulillah,Allahumma salli ala sayyidina muhammadin wasallim"


tun tana fada da qarfinta har wani irin bacci ya rinjayi qwayoyin idanuwanta suka
rufe ruf,ta lula duniyar bacci.

"iman.....iman" taji ana kiran sunanta sama sama,saita buda idanunta,suka


sauka kan yagana dake tsaye gefanta,qarasa bude idanun nata tayi ta miqe ta zauna
tana ambaton sunan Allah,sai a sannan yaagana ta samu waje ta zauna tana dubanta

"Inata tararrabin baki samu barci ba,yanzu kuma na koma tararrabin baccin lafiya
kuwa kikeyi?,tun daxu ko motsawa bakiyi?,kayan abincinki tunda duminsu har sun
huce" gefanta taga jeran kwanukan abincin,mamaki ita kamta ya kamata,saboda bata da
wani nauyin bacci,amma kuma ace har an shiga an fita sau nawa bata ji ba

"Alhaji ne zai fita,ni kuma banason ya fita ba'a tsaida matsaya ba" ba kasafai iman
din ke magana ba idan ta farka daga barci batayi brush ba,saboda haka ta cewa
yaagana tana xuwa,ta shiga bandaki,ta wanko bakinta sannan ta dawo

"Ya sauqaqewa kowa wahala yaagana,da asuba ya aiko da sakin ma ta saqon waya" duk
da cewa yaagana taji haushin hakan sabida rashin mutunci ne da rashin kima,a rasa
ta yadda zaa saki mace saboda son a wulaqantata saita saqon waya,amma kuma jin
dadinta yafi yawa,jin cewa komai yazo qarshe,batayi qasa a guiwa ba ta shaidawa
alhaji,saidai ya girgixa kai

"Dole sai an kirashi anji ta bakinsa,saboda haka ina ganin zuwa gobe ko jibi,ku
shirya sai mu wuce kanon tare,akwai wasu kayana da sukazo dama,suna kasuwar kantin
kwari" da wannan maganar suka tsaida matsaya,ta kuma shaidawa iman din,kai kawai ta
kada kana tace

"Allah yasa muna da rai".


[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 37 Kwana biyun da tayi gidan yaagana sai taji kamar
an canzata ne,duk wani takura da quncin zuciya da takeji babu shi,abu daya ne yake
sanyata faduwar gaba zuwa biyu,yaya malam da inna zasu kalli abun?,zasu karbeta
kuwa?,idan sun karbetan alaqarsu zata koma kamar yadda take da?,ko kuma ta
tabarbare kenan?,wadan nan tambayoyin suke cin ranta,suke kuma takurata lokutta da
dama idan ta tunasu Randa suka tasamma kanon sammako sukayi,saboda haka goma na
safe acan tayi musu,basu sauka gidan malam ba,sai da suka fara biyawa gidan kawu
muntari,gidan alwalin iman din,wanda ta koma gidansa da zama lokacin aurenta da
bassam din,sannan suka qarasa gidan malam din.
Kamar wata baquwa haka ta zama,ta kasa sakewa gaba daya,motsi kadan sai ta kalli
inna,ita kanta innar tayi mamakin ganinta tare da yaagana da kuma alhaji,saidai
bata ce komai ba,ganin harda kawu muntari Basu xauna gidan kawu muntari ba,don
haka a gidan inna suka karya aka kuma dora abincin rana,zuwa lokacin mazan suna
rumfar malam din,da alama kuma tattaunawa sukeyi,daga bisani ne malam din ya leqo
yayi kiransu su dukka suka isa rumfar tasa.Hajaru..inason ki sani cewa duk abinda
ya samu bawa muqaddarine daga ubangijinsa,yanzu yanzu muka gama magana da
mijinki,mun kirashi kuma ya tabbatar mana da sakin da yayi miki,to amma kuma shi
malam mahaifinki ya kafe kai da fata kan bai aminta da abinda kika zo dashi
ba.munaso ki bude baki ki gaya mana,tsakaninki da Allah meye ya hadaku dashi?"
Kanta a qasa,hawaye ya cika mata idanu,tanajin quna da zafi a ranta,ta gaji da
zancan bassam da tarin matsalolinsa,tunda dai har ya sahale mata ya kamata a rufe
babinsa hakanan,to amma hakan ba zata yiwu ba,dole saita gaya musu abubuwan da suka
wakana. A nutse ta labarta musu komai,ya gana data zame mata kamar shaida itama ta
gaya musu duk abinda ta sani,parlour din ya dauki shuru,sai sheshseqar kukan iman
din. Gyaran murya malam din yayi
"To yanzu yaaya mu me xamuyi?,muda bamu isa komai ba?,ai saidai muce Allah ya
kyauta na gaba,riqon hajar kuma yanzu ai yafi qarfinmu,bamu da muhalli da irin
abincin da take ci,saidai ko a cigita cikin dangi ko akwai inda zata iya zama dasu"
sosai maganar malam din ta girgiza iman,sautin kukanta ya qaru,hankalinta ya sake
tashi fiye da yadda take a da,ta waiwaya tana ruqon inna,sai innar itama taja
jikinta gefe tana cewa
Wa?,ni binta,yo zantukan malam dukka akan hanya suke" tausayin iman ya kama alhaji
da yagana,ran yagana ya baci sosai,ta kalli iman
Tashi ki shiga ciki" ta miqe tsam tana jin jiri yana dibanta,har sai data bace
sannan yaagana ta dawo da kallonta kansu
Duk wannan zantukan da kuke kai da binta zancan banza kuke,wai ku dole saikun
nunawa duniya bakwason imani,fushi kuke da ita,zancan banza ne kuke,wallahi wallahi
kuka sake na tafi da hajaru maiduguri saikun manta kalarta" alhj mijin yaagana ne
ya karba
Malam ni a tunani na kaine zaka yi mana wannan fadan bamu xamuyi maka ba,ka taba
ganin inda hannunka ya rube ka yanke kayar?,bayan haka kuma.a yanzu dai inajin babu
sauran kalar nadamar da ta rage hajar bata yita ba,babu ita,kuma dama ance ba'a
qwace garma a hannun yaro ko?,idan ya gaji yaji wuya da kansa zai cillar da
ita,saboda haka,ina mai aron bakinta nima,kuyi haquri ku manta da komai,kalar tata
qaddarar da kuma jarrabawarta kenan,Allah yasa kuma ta cinyeta Kiranta yaagana
tayi,kowa da kalan nasihan da zaiyi mata,cikin kuka da zubda hawaye ta sake duqawa
ta nema gafarar inna da malam,dukka suka amsa da cewa sun yafe mata,saidai malam
yace aje ayi mata gwaji a ranar,don a sake tabbatar da lafiyarta,haka kuwa
akayi,result ya fita cewa bata tare da wani ciwo banda hawan jinin data samo a
can,shima kuma likitan ya bada tabbacin indai zata samu kwanciyar hankali da
nutsuwa zata rabu dashi, tension ne ya kawo mata shi. Ya saddiqu kuwa har yanzu
jiya iyau,mu'amalarsu sam bata koma kamar ta baya ba,har sai da malam ya kirashi ya
masa fada sannan ya sauko,ya rage daure mata fuska. Batasan cewa sabawa umarnin
iyaye koda kai keda gaskiya ba indai ba sabon Allah suka umarceka ba babban bala'i
bane sai yanzu,ranar da sadiqu yasa motoci a gaba akaje aka kwashe kayanta
rankatakaf daga gidan bassam.a ranar tayi wani irin ni'imtaccen bacci,baccin da
rabonta da irinsa tun ranar data sanya qafa tabar gidan nasu,bacci harda makara,a
ranar data sake tabbatarwa da cewa babu ita babu bassam kenan,sunyi hannun riga har
abada. Iya furniture din da taje dasu gidan da kuma motar hawanta data zo cikin
sadakinta kadai ya sadiq din ya dauko,banda wannan tsinke nasu bai shigo cikin
kayan ba Shawara yayi da ita ya tarkata kayan furniture din aka saida,motar
kuma tace a ajjiyeta,don ko son ganinta batayi,don haka sai ya jata ya kaita garage
dinsa,don shima yanzun ya bude nasa qaramin garage din gyaran motocin,har ma ya
dauki yaran unguwa su hudu suna koyon aiki a wajen,suna kuma taimaka masa
bayan wasu watanni Sanda ta samu nutsuwa abu na farko daya fara zuwa kanta
shine karatu,a yanzu bata da burin daya wuce ta dawo da karatunta,ta shaidawa
malam,ya aminta da hakan,saboda tun farko yasan burin ameen kenan a kanta, ya
sadiqu ma yayi murna sosai da har yanzu karatun bai bar kanta ba,kuma shine ya
shige mata gaba,ta samu takardun qualifying da secondary School certificate,sannan
ta samu damar zana jamb dukka cikin shekara guda,komai nata ya hadu yadda ya
kamata,ya sadiqu ya daye tuquru wajen sama mata makaranta,har ta dinga mamakin
yadda ya maida kai,saboda har yanzun 'yar tsama suke,saidai katsam sai gashi
makaranta ta samu,muma course din data nema,murna kamar tayi me? Tun ana saura
kwana bakwai ta fara zuwa din babu irin fada da hudubar da bataji ba kan
qawaye,daga bakin inna ne,daga bakin malam ne uwa uba kuma daga uban gayyar ya
sadiqu. Zuwa yanzu itakam aita gurzu,ta kuma gane duniya,ba sai an mata ma
magana aka qawaye irinsu munira ba,munirar da suka jima suna gaisawa amma bata taba
gaya mata aurenta ya mutu ba,sai ranar data wanki qafa taje gidan da sunan ziyara
sannan ta samu labari,daga nan kuwa tayo gida wajen iman din cikin tashin hankali.
Saidai kuma yadda ta samu iman din qalau cikin walwala yasa jikinta ya danyi
sanyi,ganin munira a gidan sam bai yiwa iman dadi ba,don ita yanzu bata qaunar
dukkan wani abu da yake da alaqa da bassam,ko kuma zai tuna mata dashi,a yanzu
rayuwarta dadi take mata,tana jin kamar an tariyo mata da rayuwarta ne,saidai akwai
abu daya da tasan ta rasashi,akwai abu daya da takeji cikin zuciyarta cewa tayi
missing,tana jin akwai wani babban bangare abu mai muhimmanci kuma jigo cikin
rayuwarta data rasashi wato ameen..abunda ke daure mata kai kuma shine,babu wanda
ya taba yin zancansa a gabanta..da kunnenta dai bata taba ji ba,babu wanda ya taba
yi mata maganarsa,tunda tazo gidan bata taba ji anyi labarinsa ba,ita kuma bata
taba tambaya ba,inaaaa .ina ta isa tayi zancansa ita din?,bata da wannan qwarin
gwiwar sam,saita tattara komai ta ajjiyeshi gefe guda,bawai don ta manta ba. Tun
munira na zuwa iman nayi mata hannunka mai sanda.tana daure mata fuska da rashin
sake mata,har takai ga ta fito gaba da gaba da gaya mata
Tunda na fito munee ban taba zuwa gidanku ba nikam.inaga ba.me zai hana mu haqura
da wannan ziyarar,muci gaba da gaisawa kawai a waya idan da yiwuwar hakan?" Sosai
taga rashin dadi qarara samn fuskar munira,saidai ya zamar mata dole tayi mata
hakan,saboda ta fuskanci abinda ya sameta munira ce ta bada gudunmawar afkuwarsa
kaso saba'in cikin dari,shi yasa ta gwammace su nesanci kuna gaba daya ita da ita,a
yanzu mutum daya take tare da ita,suke kuma shawara wato bushira,saboda ta tabbatar
ita din qawa ce ta arziqi,data fito daga gidan dattako da sanin ya kamata. Fara
zuwan iman makaranta taci qwal ubanta ba kadan ba,taji jiki ta jigata,saboda shi
karatu ko yaya ka barshi,to shima saiya maka nisan da baka taba tunani ba,saidai
naci da jajircewa sune tushen dukkan wata nasara,haka ta sakawa ranta himma naci da
kuma jurewa,da kadan kadan sai gashi ta fata ganewa,ana kuma dan tafiya da ita babu
laifi,saidai ba kamar sanda take kafin aurenta ba,bata damu da hakan ba,ta sama
ranta tafi tafi wataran zata dawo da kanta wannan matakin da ikon Allah.
bayan shekara biyu Turare shine abu na qarshe data fesa saboda cike kamalar
kwalliyar tata,ta maida turaren saman madubi ta ajjiye tana kallon fuskarta jikin
madubin dake dakin. Kyakkyawar fuskar hajar ibrahim khalilu iman fuskar da a
yanzu tafi cikar kamala fiye da shekara biyu baya,fuskar data cika da tarin annuri
da kuma alamu na qarin shekaru,alamun da suka qara ma fuskar tata cikar kamala,kyau
da kuma haiba,sai cikar haduwar hankali da kuma sanin ciwon kai da suka bayyana
akan fuskarta,a hankali ta gyara daurin kanta hagu da dama ta tabbatar yayi,ta
murmusa har dimple dinta ya lotsa daga dukkan kumatunta
Alhamdulillah.ta fada a bayyane,kamar yadda ya zame mata jiki a duk sanda ta kalli
kanta,taga kuma ubangiji ya saita mata rayuwarta,ta fara maida abubuwan data rasa a
baya a rayuwarta masu yawa,tana godewa Allah da miyagun qaddarorinta basuyi nisan
zango ba,tana godewa Allah da bai dubi halinta ko kuma abinda ta aikata ba. cikin
rahama tausayi da jin qansa ya wadata rayuwarta da abubuwa masu kyau. Cikin
kayanta ta laluba mayafin daya dace da shigarta da 'yar jakar hannu da take dura
takardunta,ta yafa ta hada da takalmi sannan ta fara takawa zuwa tsakar
gidansu,cikin wani taku da ba nata ba,wanda wala'alla sauyin yanayi da kuma rayuwa
ya sanya dukkan dabi'unta na ainihi sake fitowa. A hankali ta tako zuwa tsakar
gidansu,qamshin turaren wuta na kaya yana surarowa daga jikinta saboda tsabar yadda
ya kama jikin nata,ya hade da sassanyan body mist da take amfani dashi Tsakar
gidan nasu tabi da kallo,gaba daya ta rasa meke shirin faruwa a gidan da inna ta
kasa zaune ta kasa tsaye,kwana kusan uku kenan innnar tana yiwa gidan kwalema. Iya
tuquru da iman din ake aikin,kasancewarta wadda dukka ayyukan gidan suna wuyanta
dama,ta riga ta saba,saidai sam ta kasa tambayar innar dalilin kwalimar. Ko yanzun
ma kallon innar take ita da mufida sunata sauke kayan kitchen din innar ana fitowa
dasu,yarinyar cikin dangin inna na nijer take,tazo mata hutu ne,saboda gama zana
jarrabawar common entrance da tayi,da iman din aka fara aikin,amma ganin lokacin
makaranta yayi yasa ta saki aikin taje fa shirya.
Sannunku da aiki ta fada tana qarasowa inda suke tana rataya jakarta
Yauwa.kin fito Inna tafada tana dan dubanta kafin ta maida kanta taci gaba da aikin
da takeyi
Eh inna,harma naso na makara" tayi maganar tana duba agogon fata mai azabar kyau
dake daure a tsintsiyar hannunta. Tana daga kai suka hada idanu da mufida,ta saki
murmushi yarinyar
Wannan kallon fa? Iman ta tambayeta itama fuskarta a sake
Wallahi kinyi kyau yaa iman,haka nakeso idan na qara girma nima na shiga jami'a,na
kuma zama 'yar gayu irinki
Yar gayu,'yar gayu,'yar gayu,bakinki baya gajiya da gayamin wannan sunan?" Dariya
mufidan ta saki
Don Allah inna yaa iman ba 'yar gayu bace?,kuma kyakkyawa
Oho muku,wannan zancan naku yafi qarfina.ungo nan inna tayi maganar tana daukar
dari biyar daga kudaden dake gefanta ta miqa iman din
Idan kin fito ki biya ta kasuwa ki samomin turaren bakhur
Bakhur kuma inna?"Ta tambayi innar cikin mamaki
Eh shi,laifi nayi kika tsareni haka da kallo?Kai ta kada
A'ah inna,gani nayi kina da turaruka,harda wadanda baki amfani dasu ba,ko wancan
satin ma na kawo miki wani turaren wuta Wannan din shi nakeso..ki wuce ki tafi ko
kuma ki bani aikena
Sai na dawo" iman din tafada zuciyarta na motsawa,tuna mata da sunan turaren tamkar
wani fami ne a rayuwarta,sunan kawai ya tuna mata da wani abu jigo,haka ta ratso ta
soron gidan dan fita qogar waje Sauka idanunta yayi kan dakin ya sadiqu,nan ma
dai kamar cikin gidan,an fidda komai na cikin dakin,babu komai a cikinsa da alama
shima kwalemar ake,tanason ganin ya sadiqun,amma sai taji ba zata iya shiga dakin
ba,don haka ta saka kai zuwa waje zuciyarta na mata wasu wasi Kofar gidan dukka
babu daliban malam din,da alama kowa yayi jasa waje,don dama sha daya tayi lokacin
tashinsu kenan,babu kowa sai malam din dake zaune saman kujerar da yaje
karatu,snaye da farin yadi qal da kuma farin rawani na wani lallausan plain yadi
Malam din badai tsafta da kuma kwalliya ba,duk qwaqwarka ba zaja taba rasashi cikun
tsafta da qamshi ba,duk kuwa da cewa mafi yawan kayan sawarsa harma da rawaninsa
yafi tu'ammali da farare,amma ko yaushe qal zaka gansu kuna fes,hakanan malam din
baisan saka tsumma ba,tun a lokacin ma da bashi da mataimaka koda yaushe cikin
kyakkyawar shiga yake bare yanzu Sai data duqa tama mallam sallama,ya kuma
sallameta da kudin mota kamar yadda ya saba,duk da sana'ar da takeyi amma sam shi
bai damu da wannan ba,ta raba a hankali taci gaba da takawa zuwa titin
unguwarsu,kwanyarta cike fal da tunanin aiken innar har zuwa sanda fa samu abun
hawa ta wuce makarantar.
Daga bakin gate ta sauka ya biyashi,itakuma ta soma takawa zuwa cikin
makaranta.huguma
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 38
Kamar ko yaushe daga shigarta ta fara fusgar hankalin maza da dama,duk inda ta
ratsa binta ake da kallo,tun abun yana damunta harma ya zame mata jiki,ba mazan
ba,hatta da wasu matan suma kallon suke binta dashi a yawancin lokuta,saidai babu
fuskar da zaka tunkareta da wata magana,saboda sam bata barin fara'a saman fuskarta
har dangane da ajinsu,shi yasa mutane ke kiranta da mabambantan sunaye. Wasu na
mata kallon miskila,wasu na mata kallon me girman kai,wasu nacewa ta isa tayi,ai
tana da kyan da zata nunawa kowa,mata da yawakuma na kishinta ne sabida tana da
kyan dake fusgar hankalin samari ko abokan huldarsu. Itakam bata damu ba,saboda
abunda ya kawota kawai takeyi,kuma darajar addua da takewa kanta da rayuwarta,Allah
ya tsareta daga dukkan sharri na miyagun malamai harma da daliban,so bataga abunda
zai dameta ba kuma. Awa uku kawai dama ke gareta cikin makarantar,saidai a tsahon
awa ukun aiken inna ya tsaye mata a rai,bata kuma san dalili ba,kawai dai tasan ta
tuna mata da ya amin,saboda shi daya ne a gidan ke mayatar son turaren bakhur,don
haka ana tashi ta wuce kasuwar ta siyama innar aikenta,sannan ta zarce
asibiti,saboda yaune ranar da zataje taga dr,don duk bayan wasu watanni tana
zuwa,saboda gudun dawowar matsalarta,shawarace dr din ya bata,kuma taga alfanunta.
Mutum biyar ne a gabanta,tana zaune tana ta juya turaren a hannunta har zuwa sanda
aka kirata,saita maida jakarta ta ratayata,sannan ta nufi office din. Da sallama
abakinta ta tura qofar ta shiga,ya daga kansa yana amsa sallamar tata,sai fuskarsa
ta zarce da mayalwaciyar fara'a,ya maida kansa yana qarasa rubutunsa cikin file
amma kuma yana cewa
"Hajjaju,yau kece a gari?" Fuskarta da dan nata murmushin ta amsa masa sanda take
zama
"Nice dr
"Marhaban dake" saita sake murmushin tana cewa
"Na gode dr" rufe file din yayi,ya tattara dukka hankalinsa akanta,suka gaisa
sannan ya fara mata tambayoyi,daga bisani ya gwada komai.komai normal yake,ya
ajjiye kayan gwajin da murmushin nan dai na fuskarsa
Alhamdulillah,hajjaju lafiya ta samu,saidai duk da haka mu bamu gaji da ganinki
ba,sannan ba zamu bada shawarar ki daina zuwa ba,koda sau daya.ne ko biyu a
shekara" ya fada yana rubutu a file dinta
Tunda komai ya zama normal dr inaga.ai no need naci gaba da zuwa din ko?" Kai ya
gyada
Idan hakan yayi miki fine godiya tayi masa sosai sannan ta buqaci amsat file din ta
maida reception,saidai yace
Noo..barshi a nan hajjaju,kawai abinda nakeso na duba a jiki
Ok dr,na gode" ta sake masa godiyan tana nufar qofa ba tare data kawo komai cikin
ranta ba
Ammmm.hajjaju taji ya ambata sanda ta murda hannun qofar zata fice,waiwayowa
tayi,suka hada idanu,idonsa fes bisa kanta
Kice hadiza sabi'u ta shigo
Ok dr ta fada a ranta tana mamakin kallon da ya bita dashi a yau,karon farko.
Tana zaune cikin dakin nata daga bakin katifarta,ta ware fanka sosai iska na
shigarta tako ina,sanye take da wata buba ta wani yadi mai sulbi,sai dankwalin inna
data dauka ta daura shima mai sulbi,hannunta riqe da biro tana bin assignment din
data gama da kallo cike da nazari tana dubawa,tare da bin qwaqwafin inda tayi ba
dai dai ba.
Motsim shigowar mufida ya sanyata daga kai tana duban yarinyar,tun dazun suketa
aikinsu ita da inna,yau din ko nemanta ba'ayi ba,duk kuwa da cewa aikin abinci
innar takeyi,abincin ma wanda iman din ta qware sosai akai,wato hadin wainar
shinkafa Agogo iman din ta fara kalla tana duban mufida data dauro alwalar sallar
magariba tana qoqarin saka hijabinta,kawaicinta a yau ya qare,ta rasa gane abinda
ke wakana cikin gidan
"Wai nikam mufida..inna baqi garega gobe cikin gidan nan?"
Au baki sani ba?" Yarinyar ya fada,da alama tana zumudin bada labarinne
Ban sani ba mufeeda" iman din ta fada tanayin wani kalar tausayi
Duk gyaran nan da akeyi har dakin yaya sadiq?,baqone zaizo gobe,inna tacemin d'anta
ne zaizo daga qasar waje,kullum sai ta bani labarinsa,tace tunda ya tafi can baizo
ba sai yanzu,tace yana da kirki sosai.sunansaaaaa.ummmm,ya aminu" matsananciyar
faduwa da gabanta yayi har sai da biron hannunta ya subuce ya fadi,dama ya amin ne
zai dawo?,kowa a gidan ya sani amma banda ita?,indai hakane kuwa kenan basu haqura
ba,har yanzu akwai haushinta qasan ransu. Kafin ta sake wani tunani kiran sunanta
da ya sadiq yake qwallawa daga qofar dakin nasu ya katseta,saita miqe da
sauri,saidai kuma yadda dukka wata laka ta jikinta ta mutu ya sanyata cin
tuntube,saura kadan ta fadi,ta dai daita kanta tana amsa sannun da mufida take
mata,ta qarasa qofar dakin,ta yaye labulen tana cewa
Yaya sadiqu gani"
Ungo don Allah,hadamin shi,yanzu nakeso nasha" ya fada yana miqa mata yar babbar
baqar ledar,data buda sai taga jayan fruit ne, fruit salad yakeso ta hada masa
kenan Kitchen ta wuce kai tsaye ta fara aikin,tana aikin tana kallon yadda aka
gyara kitchen din,ga jerin kayan abinci nan da aka rage ayyukansu,gobe kenan za'a
qarasasu. A sanyaye ta gama hadawa,ta miqa inna din ta fara diban nata,sauran ta
ajjiyewa ya sadiq din ta komo daki,data shigo dinma litattafan ta tattare waje daya
ta haye katifarta,bata da qwarin gwiwar ci gana da duba assignment din gaba daya,ta
rasa mene yake mata dadi,wanne yanayi take ciki,ya amin zaizo?,yaya haduwarsu zata
kasance?,da wanne ido zata kalleshi? Tanajin mufida na tashinta tasha nata fruit
salad din amma tace mata ta qoshi,wani irin fargaba mutuwar jiki gami da kasala ke
dibanta,wanda ita kanta batasan dalili ba,saidai jikinta ya gama mutuwa murus,cikin
wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita. Can cikin barcinta hancinta ya dinga
debo mata kalolin qamshin girki,ta bude idanunta a hankali,ta juyasu cikin dakin
nata,wayam yake babu mufida,da alama tuni ta fice,sai ta miqe da hanzari tana duba
agogon wayarta. Qarfe tara ne na safe,yau din lecture daya gareta,itama kuma
kamar ta jiya ce,sha daya na safe su gama qarfe daya,saita aje wayar,ta zamo daga
katifar tata ta isa bakin qofa tana dan dage labulen tana kallon tsakar
gidan,tsakar gidan nasu dako yaushe yake a tsaftace yau a kacame yake,ta saki
labulen,ta koma da baya ta dauko set na kayan wankanta sannan ta sake fitowa. Sai
data gaida inna dake ta faman loda waina a cooler,tadan tsokani mufida dake da son
aiki bata gajiya sannan ta karbi ruwan zafi ta wuce wanka,tana shiryawa tana
mamakin yadda kowa bai bi ta kanta ba bare ayi maganar zuwan ya lamin a
gabanta,banda mufida ta gaya mata,ta tabbatar babu wanda zai gaya matan. Tsaf ta
shirya cikin dinkin bubu na atamfa,wadda tayi mata kyau qwarai,jikinta sai fidda
wani sihirtaccen qamshi yake kamar kullum,ta hada duk abinda zata buqata tayo
tsakar gidan
Ba zaki tsaya ki karya ba." Kai ta gyada
Sai na dawo dai inna
Allah ya kaimu Wucewa dakin malam tayi,yana zaune da qur'ani gabansa da aka rubuta
da jar tawada jikin wasu farin papers
Tun kwanaki naso a rubuta miki qur'anin nan ki wanke ki qara ruwa ki dinga
sha..amma zan saka ayi miki keda mufida" malam din ya fada bayan sun gama gaisawa
yana miqa mata kudin makaranta
"To a bani wannan malam tunda na gani?" Ta fada tana langabe kai,don a yanzu sau
tari tafi jin dadin hira da malam din akan inna. Kai ya girgiza
"Wannan?,banda wannan,na muhammadu aminu ce" dif wuta ta dauke mata,sai ta miqe
gwiwa a sanyaye tana yiwa malam sallama,idanunta suka sauka kan wata qanqareriyar
shadda da hula tangaran,harda takalmi duka sabbi
Kilan duk na zuwanshi ne?" Ta tambayi kanta,sai ta fita tana mamakin yadda suka
daukaki zuwan nasa,sunata shirye shirye kamar wadanda zasuyi wani biki. Ta
dakinsu dake soro ma koda bata shiga ba tasan lallai dakin yasha gyara sosai,tana
jiyo muryar ya sadiqu da alamu waya yake,sai ta saka kai ta fice a hankali Kusan
karatun yau din gaba daya bata wanu fahimceshi dari bisa dari ba,tadai tsinta iya
abinda zata tsinta,batasan me yaketa raba mata hankali da kuma dauke mata hankali
ba,don koda aka tashi sai data jima kafin ta baro makarantar Tana cikin napep
amma duk matsawar da zasuyi gaba zuwa gida sai taji wani iri
Don Allah idan ba damuwa juya dani kabuga" ta baiwa mai adaidaitan umarni
Ba matsala,amma zaki biya
Ka fadi nawa ne zan biya in sha Allah" ba musu ya gangara gefe,sannan ya juya kan
motar suka koma baya. Haka kawai taji ba zata iya tunkarar gidansu ba,ba zata iya
shiga gidan yanxu ba,ta sauke wani numfashi me nauyi tana lumshe idanunta,tana jin
yadda iskar hanya ke bugun fuskarta,ta tabbatar a yanzun idan ya ameen din baya
gida to ya kusa isa gidan,shi yasa ta yanke tafiya gidan kawu muntari wajen umma
hassana. Suna isa ta fito ta miqa masa abunda yace ta bashi,ta saka kai cikin
gidan bakinta dauke da sallama. Ta samu yaran gidan sunata shirin tafiya
islamiyya,tana taya umma hassana shiryasu suna taba hira,har ta sallamesu,gidan
yayi shuru ba kowa,sai yaron da take goyo Bandaki ta shiga ta canza pad din
jikinta,sannan tayi alwala,duk da ba sallah zatayi ba,don dai kawai taji dadin
jikinta,kafin ta fito umma hassanan ta zuba mata abinci,ta zauna tana ci suna hira.
Bata jima sosai da cin abincin ba jikinta dukka ya mutu,taji tana jin bacci,saita
kwanta umman ta bata waje ta fita qarasa ayyukanta,bata jima ba kuwa bacci yayi
awon gaba da ita. Ba ita ta farka ba saida akayi sallar la'asar,shima qarar
shigowar text a wayarta dake saman kanta ya farkar da ita,ta miqe zaune tana
salati,ta jawo wayar ta duba,sai taga saqon daya shigo da number dr ahmad
ne,gajeran saqo ne kamar haka
Barka da warhaka hajjaju,cewa nayi bari na gaisheki,fatan kin wuni
lafiya,bissalam_*
Dr ahmad kuma?" Ta tambayi kanta cikin mamaki tare da maimaita karanta saqon,abunda
ta kawo kawai a ranta shine yayi mistake na tura saqonne,saboda haka saita ajjiye
wayar kawai,ta gyara daurin dankwalinta daya zame sakamakon santsin gashinta,ta
miqe zuwa tsakar gida wajen umma hassana. Ta sameta tanata hada hadar yin
dambu,gashi yayi mata yammaci,ta kama mata,nan da nan suka dora,ta tayata suka
tsaftace wajen sannan suka koma daki suka dora hirarsu. Sai bayan an dan jima da
idar da sallar magriba,harma.taci abinci sannan tayi ma umma hassana sallama,tana
ta mamakin zuwan iman din da kuma dadewarta,har tana tsokanarta da cewa
Allah yasa ki dore da wannan zumunci" murmushi kawai iman din tayi,saboda ita kanta
tasan ba zuwan Allah da annabi tayi ba. A hankali kamar wata tsohuwar barauniya
take takawa sannu sannu,tun daga qofar gidansu zuwa cikin gidan,ta saki ajiyar
zuciya sanda ta fuskanci dakin soron a rufe yake,saita qara sauri amma kuma cikin
takatsantsan,ta samu ta shige dakinsu tana sauie ajiyar zuciya,duk da cewa bataji
motsin wani abu ba. Jakar hannunta ta ajjiye,ta cire kayan jikinta tana canzawa
mufida ta shigo
Yaa iman,yaushe kika shigo,yanzun nan inna ke maganar dadewarki
Kaina ne yake ciwo mufida yanzu na shigo..ina innar?"Tana rumfarta a zaune
"Ita kadai ce?"Eh,ai.babu kowa agidan,tun la'asar su ya sadiq da baqon baturen da
suka zo dashi suka fita,basu dawo ba kuma bayanin yayi mata dadi,don haka ta fita a
gurguje tayi duk wani uzurinta da zai fiddata tsakar gida ta dawo daki
abinta,itadai haka nan takeji..batason su hadu da yaa ameen,batasan kuma me yasa ba
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 39

Washegari ma tashin wuri tayi,ta shirya a gurguje,ta cimma inna a dakinta tana
zaune tana sauraren labaran siya, volume din can qasa,ta tadda zata iya jin duk
wani motsi.

Binta da kallo innar tayi sanda take gaya mata zata wuce makaranta

"Allah ya kiyaye hanya,saikin dawo"

"Ameen" ta amsawa innar tana ficewa sa dan hanzari,cike da fargaba da kuma tsoron
kada su hadu din,shima dai a ranar bata dawo ba sai bayan magrib,tana gidansu
bushira,amma ta aikowa da innar yara kan tana can din.

Kayan jikinta kawai ta cire ta sauya wasu,ta zauna gefan katifarta jin
shigowar saqo bayan ta jawo wayar tana dubawa

_Amincin Allah ya tabbata a gareki yake kyakkyawa,da fatan kin yini cikin koshin
lafiya_

"Dr ahmad?" Ta sake tambayar kanta cikin mamaki,anya ko yana sane yake tura
mata wadan nan saqonnin?,ko yauma mistake din yayi?. Bata lalubo amsa ba mufida
tayi sallama ta shigo,iman ta daga kai tana dubanta,shadda ce a jikinta me kyau
qwarai,dinkin doguwar riga,da alama sabuwace,don bata cikin kayanta kwata kwata da
tazo dasu

"Yammatan inna,wannan kyau haka?,ina kikaje?" Iman din tadan tsokaneta,dariya tayi
itama tana zama a qasa kusa da iman din

"Taro akayi fa yau,wallahi yaaya iman kinyi missing,baqon inna dan


balarabe.......au,ashefa tace danta ne,yaya ameen,shine ya hada taro,ya bude wani
qaton shago nayin dinki,kinga kyan da wajen yayi yaa iman?,sai naji inama ni tailor
ce,kekunan dinki,injin stone,keken waiving komai dai yaya iman,baki gani ba
wallahi".

Sallamarsa ce ta gauraye tsakar gidan,cikin muryarsa mai nauyin


nan,wadda a yanzu ke bayyana cikar mazantaka nutsuwa da kuma kamala a tattare
dashi,lumshe idanu iman din tayi,wani abu mai nauyi yana tsarga mata,kamar yasa
zancansa suke,saita dubi mufida

"Dukanku yau kuna can kenan"


"Eh mana,harda inna da malam fa,wai dan balaraben nan ashe ya iya dinki,sai gashi
yahau keke shima yaa iman?" Mufida ta fada cikin alamun mamaki,harda kama baki,duk
da yanayin da jiki da zuciyarta ya shiga amma sai tadan murmusa kawai

"Tsohon tailor ne" daga haka ta sake bude wayarta ba tare da tana da abunyi ba

"Yaa iman.....na kawo miki abincinki?" Kai ta girgiza mata,bata jin zata iya cin
wani abu

"Na qoshi mufida,kedai sannunki,na gode" sai yarinyar ta matsa wajen kayanta ta
canza kayan jikinta,sannan ta fice daga dakin.

Iska mai nauyi da zafi iman din ta fitar tare da sauke ajiyar zuciya,tana
ci gaba da taba screen din wayarta,zuciyarta na lulawa duniyar tunani,wanda muryar
mufida ta katseta

"Yaa iman kizo inji inna" dokawa qirjinta yayi,ta daga kai da sauri,tana son
tambayar mufidan waye da waye a falon,amma tuni yarinyar ta shilla abunta da gudu
ta koma.

Sunan Allah ta kiraya kafin ta tashi,saita zari dogon hijabinta ta zura,ta


ajjiye wayarta ta fito ta doshi falon,zacuyarta na harbawa da sauri.

Tana yaye labulen wani irin kwantaccen qamshi ya cika mata hancinta,ta
bude bakinta a hankali tayi sallama,muryar data amsa mata sallamar ta sake sanyata
ta daburce,kanta na a qasa ta kasa dagashi,batasan waye da waye a falon ba,batasan
kuma inda zata zauna ba,don haka ga zame mata dole ta daga idanunta ta zabi wajen
zama.

Karon farko idanunta suka sauka a kanshi,yana zaune saman center carpet
saboda aka shimfida falon innar,wanda iman din kanta batasan yaushe aka sakashi
ba,sanye yake da shadda ruwan hanta,sai maiqo take da qyalli tare da fidda
qamshi,baqar sumar nan tasa ta ainihin bafillace tana nan a kansa,ta qara kyau cika
da kuma wani qyalli da sheqin baqi,duk bata iya ganin fuskarsa sosai,amma tana iya
hagen wani lafiyayyen gemu daya zagaye ya kuma qawata fuskarsa,ya qarawa fuskar
kyau da kuma cikae kamala da kwarjini,da amaa sunansa na cikakken namiji,da hanzari
ta dauke kanta daga wajen,duk da har yanzu hankalinsa nakan mufida,da alama akwai
wani zance da sukeyi daya dauke masa hankali,kamar ma labarin qasarsu take bashi.

Cikin sauri ta samawa kanta waje,sai a lokacin ta lura da baraka(yayar


alameen wadda ta riqeshi) daga gefe tana sallah,da yake falon na inna akwai
yalwa,sai kuma ya sadiqu dake gaban kayan kallo da batasan sanda aka kawosu ba
shima yanata qoqarin hadasu.

"Ina yini yaaya,an dawo lafiya?" Waiwayowa yayi a hankali ya dubeta sau
daya,sai ya kautar da idanunsa,yadan saki gajeran murmushi

"Bazan amsa ba,saida kowa ya gama yimin sannu da zuwa sannan ke?" Sadda kanta tayi
qasa,cikin mamakin yadda ya amsa mata a sake,kamar wani abu bai faru ba,kamar babu
abinda ya gitta tsakaninsu,kafin ta bada amsa muryar baraka ta ratsa tsakani

"Banda abinka aminu dan makaranta ai bashi da wani sukuni,babu zama ko iman?" Nauyi
ya kuma saukar mata,ita kanta yaya barakan kunyarta da nauyinta takeji,saita gyada
kanta ta daga kai ta kalleta

"Ina yini yaa baraka,ya hanya?"

"Lafiya lau imani,gamu yau a kano,ya gida ya makaranta?"

"Alhamdulillah" ta amsa mata tana murza yatsun hannunta,tanaji kamar zata


nutse,musamaman sa kwanyarta take mata tariyar abinda ya shude shekarun baya,duk da
cewa ba wata magana data yana hadata mara dadi da yaa barakan ko a baya,amma ta
tabbatar tana da labarin komai.

Hirace qasa qasa mufida da amin sukeyi,sai yaa barakan dake janta da
hira,yayin da sadiqu ke nashi aikin,kafin daga bisani ya saki aiki yaja tsaki

"Nafa gaji gaskiya,kaga ka taso muje kawai na rakaka,kaga dare yayi,idan mun dawo
ko zuwa gobe a qarasa"

"Alright" ya amsa a taqaice yana miqewa

"Idan na dawo maci gaba ko" yace da mufida,ya tako a hankali ya gifta iman
din,idanunta ya sauka saman qafarsa daa sake haske da fresh,zaratan yatsunsa sun
cika da gashi

"Yaaya zamuje mu dawo"


"To kwace ina gaisheta" suka saka kai suka fice,yayin da yabar qamshinsa mai yawa a
hancin iman din,ya kuma bar zuciyarta da tunani da kuma wasi wasin inda zasu,duk da
yadda take jan zuciyartata amma ta nace dason sanin inda suka tafin,har sai da inna
ta shigo sannan ta samu sasauci,ta bata abun shara tace ta gyara spare dakin dake
kusa da nata,baraka zata kwanta a ciki.

Haka kawai ta dinga kasa kunne taji shigowarsu,bata samu jin shigowar
nasu ba kuwa sai wajen sha daya da rabi na dare,ta sake lumshe idanunta tana jin
muryarsa daga can nesa yana magana,da alama yana daga soron,bai shigo cikin gida
ba,ta sauke numfashi tana gyara kwanciyarta zuwa daga side din.

Basu sake haduwa ba ita dashi tun daga ranar,washegari dama yaya
baraka ta koma,ita kam sunyi sallama.

Satinsa biyu taji labarin ya koma daga bakin mufida,abun da ta danji


ya mata susa a ranta kenan,lallai tabbas duk wata alaqa dake tsakaninsu da amin din
ta lalace kenan,banda haka......inda yadda ya dauketa a baya yanzunma hakanne,ba
shakka itace mutum ta farko da zata fara sanin komawarsa.

A bakin mufidan takejin labarin nan da wata shida zai gama karatunsa ya
dawo gaba daya,yace ma a nan za'ayi bikin salla qarama dashi,mufidan ta dauko wayar
inna da tace shine ya siyawa innar,ta nunnu mata sabon shagon da tace sunje bikin
budeshin.

Shagone mai kyau na dinkawa da kuma saida kayan sawa,sutturu kala kala
daga na maza har na mata,ba wani qatoto bane,amma kuma yana da yalwa da kuma
girma,bugu da qari yadda aka tsara wajen dole ya burge mutum,an tsara komai bisa
tsari me qayatarwa,sannan ya sadiqu shine shugaban wajen da zai dinga kula da
gurin.

Kanta ta jinjina,har yanzu ya amin bai rabu da dinki ba kenan,yana nan


cikin jininsa?,saita miqawa mufida wayar tana murmushi tare da cewa

"Gaskiya yayi kyau wajen"


"Wallahi yaa iman saima kinje,yace ayimin dinkin sallata acan ma,har ya zabarmin
atamfofi,wallahi dan gidan innar nan yana da kirki sosai sosai yaa iman" murmushi
ya subuce mata,mufidan ta tuna mata da wani abu,ta tuna mata sanda take kamarta a
shekaru,sanda ya amin din yake nata take tashi,sanda yakeji da ita,yake kula da
komai.nata cike da kulawa da takatsantsan

"Sosai ma kuwa" ta amsa mata tana jijjiga kai,sai mufidan taci gaba da bata labarin
ya amin din da kirkinsa,ita kuma ta bata lokaci tana sauraren yarinyar.

Ko a washegari tana ta kasa kunne taji ko inna ko ya sadiqu ko malam wani


zaiyi maganar amin da ita,saidai babu wanda yace mata komai,abun sai ya bata
mamaki,amma kuma ita a qashin kanta ta gayawa kanta,suyi mata maganarsa suce mata
meye?,a sanda ta yankewa kanta hukunci ba wanda tayi shawara dashi,sannan a yanzu
duka rayuwar amin da mu'amalarsa bai shafeta ba,indai zata yiwa kanta adalci,ya
kamaci ta tsame kanta,da wanna ta sanya abun wani sashe can na cikin ranta,duk da
ta sani abune mai yiwuwa ace ta mantar da kanta al'ameen din.

*_BAYAN WATA UKU_*

Tsaye take a parlor din inna tana hada tea,bayan ta gama duk wani shirinta
na tafiya makaranta,don hatta da jakarta ma tana falon innar,sai data gama hadawa
tsaf sannan tafara kurba tana tsaye kusa da fridge.

Labulen uwar dakan inna aka daga,innar ta fito cikin atamfarta mai kyau
England,tayi tsaf da ita,kana ganinta kasan tana cikin jin dadi da samun kulawa
sosai,don tsufanta da shekarunta basu wani bayyana ba sosai,musamman da yake ba
wani haihuwa tayi me yawa ba,mayafinta a hannu iman ta kalleta

"Au fita kema zakiyi inna?"

"Eh amma yanzu zamu dawo ai,cewa mufida tayi hanzari ta fito" sai ta ajjiye cup din
hannunta tana daukan jakarta da mayafinta itama

"Naji ya sadiqu yana magana dame adaidaita,idan hanya daya zamuyi ku saukeni a
makaranta mana,na huta fita titi tarar abun hawa"

"Bari sadiqu yazo muji" inna ta amsa mata tana zura hijabinta,dai dai lokacin
sadiqun ya shigo,shima a shirye tsaf cikin wani tattausan yadi da al'ameen ya kawo
musu iri daya shi dashi

"Inna game adaidaita yana qofar gida yana jira"

"Ya sadiqu idan hanyatace ku saukeni nima"

"Muje,amma sai mun fara biyawa ta inda zamu din kan a qarasa makarantarku"

"Ba matsala idan ba dadewa zakuyi ba,nima akwai sauran lokaci" da haka suka dunguma
suka fita gaba daya,bayan ya sadiqun ya kulle gidan,saboda babu kowa,malam ma ya
fita.

Sam bata fuskanci inda zasu ba sai da suka dauki hanya taji ya sadiqu yana
yiwa inna bayani

"Yayi qoqari gaskiya sosai,shi yasa kudin hannunsa suka kusa yankewa,filin babba
ne,ya siya kayan gini da yawa,farawa zasuyi"

"Aminu badai qoqari ba,Allah yaci gaba da dafa masa"


"Ameen inna,gaskiya dai kam,yayi dabara da bai saki sana'arsa ba,kinsan wasu
daliban idan suka fita qasar waje,sai suga ai faduwa ce suyi sana'a,zama suke cima
zaune sai abinda gwamnati ta aiko musu dashi,sanda ma.basu samu ba haka zasu
rungumi hannu" kai inna ta jinjina

"Kaga kuwa wannan aiba dabara bace,ni nasan aminu da zuciyar nema,bazai taba zama
haka ba dama" kaman bata a cikin motar haka tayi,saidai kunnuwanta na tare dasu,har
zuwa sanda suka qaraso unguwar suka soma shiga cikinta.

Sababbin gidaje ne a unguwar,kana gani kasan mazauna cikinta duka basu


jima da fara tarewa ba,saida akwai gidaje ba laifi,unguwace me kyau da tsari,a
hankali har suka qaraso bakin wani kango,wanda zagayeshi kawai akayi da doguwar
katanga.

Cikin adaidatan tayi zamanta,ganin babu wanda yayi mata tayin ta fito
din,bayan wajen minti talatin sai gasu sun sake fitowa sun ci gaba da
tattaunawa,bakin inna cike fal da addu'a akan amin din,har sanda suka qaraso bakin
motar ya tayar suka tafi.

Bayan watanni biyu shirye shiryen daukar azumi ya kankama,rana daya


taga an fara gyaran gidan nasu,an gyara tsakar gidansu an shimfida marbles,parlor
din inna an sassaqe an masa tiles,haka rumfar malam ma,bandakin gidan shima ba'a
barshi a baya ba,sai dakinsu ta sadiqun shima da aka maida shi tiles da tiles har
jikin bango,sannan akabi gidan aka yi masa fenti.

Dama can gidan nasu gini ne tsayayye me qwari da kyau,ga kuma innar
gwanar tsafta,sai gashi ya sake dawowa sabo fil,aka shirya komai a muhallinsa,cikin
qanqanin lokacin gidan yayi wani haske gwanin sha'awa.

Cikin taimakon Allah da huwacewarsa aka dauki azumin ramadan,sannu a


hankali kwanakin suka fara shurawa,har aka shiga goman qarshe,sai gashi ana zancan
jibi sallah,a ranar ne iman din suka tafi qunshi da gyaran kai ita da
mufida,yanayin cikowar sallah daban wajen masu lallen da gyaran kai,wannan yaja
musu basu suka dawo gida ba sai bayan sallar isha'i.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 40............Inna a bani abinci,kamar banci komai ba
wallahi" iman ta fada tana tuje dankwalin kanta,sassalkan gashinta da yasha gyara
ya bayyana,ta zauna saman kujera tana jawo flask din data gani,ta bude ta tsiyayi
kunun ciki Anan parlor din inna taci abincinta ta qoqarta tayi sallar asham,qarfe
tara da wani abu saiga ya sadiqu,mufida ta anshi ledar hannunsa bayan tayi masa
sannu da zuwa,ya amsa yana zama,iman ma tayi masa,sai mufidan ta matso tana shirin
ajiye masa ledar
A'ah dauke,ai ba tawa bace,kayan sallarku ne aciki" murna sosai ta kama mufida,ta
miqawa inna ledar,innan ta fara fidda kayan ciki tana dubawa. Atamfofine kala uku
a dinke na manya,dinki me kyau da tsari,sai kuma lace guda daya,sai na mufida kala
biyar itama,atamfa uku lace biyu,dukkaninsu kana ganinsu zasu burgeka,daga dinkin
har kayan kasan wanda yasan kan abunne ya zabesu
Wannan inji al'ameen,saiki zaba kalolin hijaban da kukeso gobe idan na fita sai
nasa a dinko muku,da size na takalmin mufida,ke dama 38 ne ko?" Ya fada yana kallon
iman,kanta ta gyada gami da amsa masa da
Eh". Godiya inna taci gaba dayi kamar ameen din yana wajen,yayin da sadiqu ya soma
bata labarin yadda shagon daya bude keta samun hubbulowar jama'a
Wallahi inna baki gani ba,yadda kikasan an yiwa wajen yayyafin farinjini,sai yanzu
nake gasgata dabarar ameen din,daa inata cewa kar ya bude,ashe shi ya dade da sanin
albarkar dake cikin dinki"
Banda abunka ai tsohuwar sana'a ce da qasar hausa ta gajeta,mutane ke raina
sana'ar,amma duk wata sana'ar hannu ai albarka gareta,har yanzu akwai manyan
gidajen da basu bar gadonsu ba,saidai sun zamanantar da ita kamar yadda aminun ya
zamanantar da ita shima
Gaskiya dai,ai na gani" ya sadiqun ya fada,yana rufe bakinsa wayarsa ta dauki
ringing
Kinga shine ma yake kira" sadiqu ya fada yana duban inna
Dan halak kenan,yaqi ambato" ta fadi tana murmushi,suna gama gaisawa ya miqawa
inna,bayan sun gaisa tayi masa godiya sosai,sannan ta hadashi da mufida,a nan ne
suka dan jima suna magana,da alama zolayarta yaketa yi tana dariya. Tsam iman ta
miqe,ganin yadda koda yaushe suke sake maidata kamar wata bare ko baquwa a
cikinsu,saita wuce dakinta ta barsu a parlor din. Kira ne ya shigo tata wayar
sanda ta gama wanka ta dawo don sauya kaya,bata samu dagawa ba har sai da aka sake
kira,ta qarasa fesa turarenta ta ajjiye ta qaraso ta dauki wayar tana duba me
kiran. Dr ahmad ne,ta danji mamaki,don bai taba kianta ba,iyakarta dashi tex,shima
iyaka gaisuwa ce,ita kuma ta maida masa masa da thanks,ko tace masa na gode sosai.
Tana daga tsaye ta daga kiran,sallama yayi mata daga bangarensa ta amsa masa
Har na fara tunanin ba zaki daga wayata ba
Saboda me?,nasani ko wani maganin ka samomin?" Dan qaramin murmushi ya saki
Wannan karon idan akwai wanda za'a bawa maganin ma nine" bata gama fahimtar
maganarsa ba ya sake sako gaisuwa
Ya gida ya ibada"
"Alhmdlh,ya akaji da marasa lafiya?"
Gamu nan,mun godewa Allah" shuru ne yadan ratsa,kafin daga bisani ya sake magana
Inata miqo gaisuwata hajiya amma bana samun wata gamsashshiyar amsa banda ta
godiya,ni kuma ba godiyar nan nakeso naji ba"
Toooo..to me kakeson ji dr?" Dan murmushi ya saki
So nake a tambayeni dalilin yin gaisuwar" dan murmushi kawai ta sake,saboda yadda
yayi maganar ya bata dariya
Ai nasan akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin likita da mara lafiyansa ko?"
Duk da hakanma..amma yanzu wannan likitan yanason sake qarfafa alaqa da dangantakar
dake tsakaninsa da patient dinsa,bayan waccar alaqar" ya zuwa yanzu ta sansano wani
abu a cikin maganganunsa,amma sai tayi kamar bata fahimta din ba
Idan babu damuwa,inaso ayimin izini nazo yawon salla,koda ba za'a bani barka da
sallah ba" Dr ahmad yana da kima da mutunci a idanunta,amma saidai batajin zata
bashi wannan damar,ita a yanzun gaba daya ta sare da lamarin maza,tsoro suke
bata,to ta bawa dr ahmad din damar zuwa malam ya ganshi tace masa meye?
Kayi haquri dr.ba yanzu abubuwa sunmin yawa
Sai yaushe kenan?" Ya ritsata da tambaya,kasa gano amsar daya dace ta bashi
tayi,sai kawai bakinga ya subuce da fadin
Nan gaba kadan zan saka ranar" ajiyar zuciya ya sauke,duk da ba haka yaso ba amma
yace
Allah ya nuna mana lokacin" kasancewarsa bame zafi ba,hakanan bashi da
tsawwalawa,yana da sauqin kai da kuma saurin fahimta.
A sauqaqe yadan jata da hira,bai kuma matsa da yawa ko ya kaita bango ba yayi mata
sallama,suka katse wayar dukansu. Tana ajjiye wayar ta waiwaya wajen mufida wadda
ta shigo rungume da kayanta,har yanzu akwai farinciki qarara saman fuskarta
Yaaya iman..wannan sallar xan sha kwalliya wallahi,irin taki da daurin nan da
kikeyi xakiyimin" murmusawa tayi
Aikam dai ya kamata" ta amsa mata a taqaice,saboda haka kawai takejin batason
magana. Kwanaki biyu a gaba musulmi suka sauke azuminsu,washegari akayi idi,ranar
sallar suna gida,saidai sunyi kwalliya gaba dayansu,sunata baqi jifa jifa inna na
saukarsu da tuwon sallaj da basa fashin yinsa duk salla,a ranarma taga inna nata
shirye shirye,kamar wancan karon na zuwan ameen din,ta tabbatarwa ranta shi dinne
zaizo,saiai bata sani ba,gobe ne ko kuma jibi.
Karfe sha daya na safe ta gama shirinta tsaf cikin kwalliya,cikin daya daga cikin
sababbin atamfofinta,sam bata da matsala sutura koda shekara nawa zatayi bata
siyeta ba,hakan ya sanya zaiyi wuya ka ganta da kaya ka sake ganinta dasu a
kurkusa. Tsaf ta gama shirinta,saidai tana dubawa yaga mufida da zasu fitan tare
bata shirya ba
Wai meye haka mufida?,tsaiwa zanyi jiranki?"
Nafa fasa zuwa yaa iman,yaya ameen ne zai dawo yau" sai da taji qirjinta ya
amsa,amma ta dake ta amsa mata da to ai shikenan,ta yiwa inna sallama ta wuce gidan
kawu muntari.
Wuni guda hankalinta a rabe yake gida biyu,idan alameen ya dawo yanzu ya dawo
kenan,ta yaya zasu rayu gida daya tare ita dashi?,wannan tambayar itace ya hanta
sukuni,harta qaraci wuninta ta dawo gida. Koda takoma gida boyon kanta tayi a
daki,ta kuma fake da ciwon kai,ta tilastawa kanta baccin wuri,washegari kuma still
ta sake fita,data dawo dinma ta qunshe kanta a daki,a rana da uku ne yunwa ta
sanyata tashin wuri,bataso amma dole haka ta fito,tana sanye da doguwar rigar bacci
mai kauri da taushi,sai baby hijab data dauran saman kanta,ta tsallake mufida dake
bacci ta fito tsakar gidan nasu ta zarce kitchen. Gidan shuru ba motsin kowa,da
alama basu tashi ba,don haka take komai cikin takatsantsan karta tashi wani,kitchen
din nasu ba kasafai ya fiya dattin dare ba,sabida suna gama girki inna ke sawa a
wankeshi kota wanke da kanta saboda gudun zaunuwar qwari,don haka dan sake goggoge
shi tayi,ta duba abinda suke dashi,ta dora breakfast din,cikin ranta tana danjin
marmarin yin girkin,saboda tadan kwana biyu bata shiga kitchen din ba.
Tana aikin tana lissafin inda zataje yau din,taga miscal na munira,saidai bata bi
ta kanta ba har yau,muniran nata nacin ci gaba da qawancensu,da kuma son wanke
kanta game da aurenta da bassam,tana gaya mata itama batasan haka bassam yake ba,da
bazata bari ya samu iman din ba,ita duka wannan yanzun ba shine a gabanta ba,an
riga an wuce wajen,tunda dai qaddararta tazo da sauqi tana godewa Allah,kawai dai
sam a yanzun bata sha'awar qawancensu da muniran baki daya,shi yasa taketa ja baya
da ita,layinta na yanzun ma sabo ne data canzashi baya ya fara zuwa
makaranta,batasan ya akayi muniran ta samu number ba.
Wani mummunar faduwar gaba ce ta ziyarce tana kwashe kaskon qarshe na chips din
data soya,daga dan nesa kadan take jiyo muryarsa,da alama yana bakin qofar shigowa
tsakar gidanne,a hankali muryar take kusantota,bugun zuciyarta na qara daduwa,duk
da haka ta aro jarumta tana ci gaba da kwashe dankalin don kar ya qone,har zuwa
sanda taji muryar tasa fa fito sosai,da alama yana baki qofar kitchen din kenan a
tsaye,sai a sannan ta fahimci waya yake,waya kuma cikin taushi da Idan ban takuraki
ba zan iya samun ruwan dumi?" Ya fada cikin laushin muryar san nan da ya sanya wani
abu ya tsarga mata,sa'annan ya kuma tuna mata da wani lokaci acan baya,lokaci me
matuqar dadi cikin rayuwarta,lokacin da duk safiya yakanzo ya tsaya kamar
haka,yakanzo yana mata hira tana aiki,ko yana tayata..idan kuma da idanun inna
yakanyi monitoring dinta.
Ci gaba yayi da wayarsa hankali kwance yana kallon wani wajen,saita juya jikinta
na dan rawa kadan,ta debo masa ruwan zafi,tunda ba kamar baya bane da take da
yaqinin zaizo,wanda take debo ruwan ya samu ya huce kafin yazo sha.
Gashi" ta fada tana miqa masa,sai a sannan ya waiwayo,itama kuma sai a sananan taga
fuskarsa tarwai,ya sake hada wani kyau cikar kwarjini da kamala,gashin da ya barwa
fuskarsa ya sake maidashi cikakken matashi mai jini a jika,kyansa kamar ya ninka na
baya,saboda ya cakuda da ilimi hutu da jin dadi,ba kamar na baya ba dake hade da
fita nema a kullum,cikin zafi rana ko ko kuma ruwa. Batasan yadda akayi ba ta saki
kofin ya sube,sai ga cup din shi sa ruwan da yake dauke dadshi sun zama pieces
qasan tiles.
Subhanallah" ya fada da hanzari yana cire wayar da yakeyi din daga kunnensa,cikin
sauri ya duqa yana cewa
Garin yaya haka?,ai ban karba ba,bakiji ciwo ba dai ko?" Kanta ta girgiza alamun
a'a,sai ta juya da sauri zuwa cikin kitchen din nemo tsintsiya a rude
A hankali mana" ya fada da dan sauri,saboda yadda yaga tana tafiya da sauri
sauri,har tana shirin taka fasashen tangaran din
Move ya fada yana qarasawa kitchen din,a hankali ya maida wayarsa aljihu,sannan ya
matsa inda dust bin da tsintsiyan yake,ya daukosu,ya duqa a hankali ya sharesu ya
zuba a dust bin din,sannan ya matsa kusa da flask din,ya bude ya zuba wani ruwan
zafin ya fice a kitchen din yana cewa
Ki dinga lura Gaba daya ji tayi jikinta ya sake,ta kasa ci gaba da aiwatar da
komai,ta koma jikin cabinet na kitchen din ga jingina tana sauke numfashi,har yanz
rawan da jikinta yakeyi bai dai daita ba,ta kusa minti goma sha biyar a haka,sannan
ta motsa taci gaba da aikin,wanda ba jimawa mufida ta tashi,ita ta kama mata wasu
ayyukan,don gaba daya wani karsashi na jikinta babu shi ya gudu. Har ta kammala
aikin bata sake ganin wulgawarsa ba,sai kawai ta zarce da wanka,ta fito ta shiga
dakinta ta shirya tsaf,sosai tayi kyau cikin wani lace da aka yiwa dinkin riga da
skert, color din lace din ta haskata sosai da sosai,lite makeup tayi kamar yadda ta
saba,fatar fuskarta nada kya da sheqi,hakan yasa yawancin lokuta koda lite makeup
tayi zakaga tai masifar yin kyau,koda lio gloss kawai ta shafawa lebbunanta,ko
abincin bata iya ci ba ta dauki mayafinta da jaka ta nufi dakin inna. Daga bakin
qofar falon tadan tsaya,gabanta ya fadi saboda jiyo muryarsa da tayi daga cikin
falon,kamar ta koma,saidai kuma babu yadda za'ayi hakan ta kasance,saidai cikin
biyu ayi daya,ko tayi shahada ta shiga ta nema izinin fita,ko kuma ta koma fa
haqura da fitan,wanda a zahiri tana buqatar ta fita din. Mayafin kayan ta ware ta
yafashi saman kafadunta,sannan ta dan runtse idanunta kafin ta sanya hannu ta bude
labulen ta shiga da sallamarta. Ameen dinne ya amsa hankalinsa nakan hada
tea,yana zaune saman center carpet da kayan breakfast a gabanshi,yayin da inna ke
saman kujera can gefanshi suna hirarsu. Bai daga kai ya dubeta ba har tazo ta
gotashi zuwa gefan innar,murya a qasa tace "Inna zan fita...yau zanje gidansu
Au,ai na tsammaci aiki kika samu" cira kai tayi ta dubi innar
Aiki kuma inna?"Eh,da naga kina sintirin fita kullum..halayyar da kika tsiro da ita
kenan iman?" Ajjiye cup din yayi ya miqe a hankali ya fice daga parlor din,hakan
ya sanyainna ta maida hankalinta sosai ga iman,fuskarta a dinke tsaf fiye da daxu.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 41

*_KU BIBIYENI TA AREWABOOKS DOMIN SAMUN SABBIN PAGES DA DUMINSU_*

https://arewabooks.com/chapter?id=62beaa7c93b638ade30a0e93

41

"Baqin hali da baqar zuciya kika koyo?,daga ina?,duk fice ficen da kike ina
sane fa,nayi shuru ne na zuba miki ido naga gudun ruwanki.....tun zuwan aminu na
farko na karanci take takenki,bakyason ganinsa saboda ya miki laifi?,bakyason ku
hadu ko?,duk wata sabga data shafeshi ko ta shafi uzurinsa baki saka hannu babu ke
a ciki,shine yanzu kika tsiri fita saboda ya dawo gida,to baro kiji,saidai ke kibar
gidan,saboda aminu ya dawo gida kenan,idan ma baqinciki kikeyi saidai ki yishi ki
gama ke kadai......mara tunani kawai" tunda inna ta fara fadan kuka ya kubce
mata,haquri kawai take bata,tama rasa da bakin da zatayi mata bayanin da zata
fuskanceta,sam abinda innar ta fahimta ba haka bane......sai ta miqe da sauri sauri
ta fice daga parlor din,ganin innar ta kasa fahimtarta.

Dakinta ta isa,ta fada kan katifarta tana sakin wani sabon kukan,ta yaya
zata fahimtar da inna kunyar alameen takeji?,yaya zata ganar da ita nauyinsa
takeji?,tana nadamar furucinta a kansa ne na baya?,tana nadamar ayyukanta na
baya,da kuma jin kunyar lafuzanta,duk sanda ta ganshi saita tunasu,saitaji kamar a
yanzune take ce masa bata sonshi,kamar a yanzune take furta me zatayi dashi,kamar a
yanzune take fadin Allah ya kiyaye ta aureshi,bata gaba ko fushi dashi......saboda
bai cancanci tayi ba.

Haka ta dinga kukanta ita daya,mufida ta jima a kanta cikin rashin jin
dadi tana bata haquri,kafin ta wuce ta bar mata dakin.

Ta jima ahakan,kafin daga bisani bacci ya dauketa,baccin da tayi na awa


biyu,bata farka ba sai qarfe daya saura,kai tsaye ta daura alwala,ta dawo ta sauya
kayan jikinta zuwa masu sauqi wadanda ba zasu dameta ba.

Kitchen ta zarce ta fara musu shirin abincin rana,tayi alqawarin faranta


ran innar da dukkan wani abu da tasan tanaso,zai kuma faranta mata,indai kula da
amin ne damuwarta zata gyara in sha Allah,saidai tana tunanin yadda hakan zata
kasance,tana tunanin yadda shi kansa zai karbeta ta koma kamar da.

Lafiyayyen girki ta tsara,wanda ta jima batayi irinsa ba,sannan ta hada


lemo,don a yanzun basu da matsalar wajen sanyi,fridge biyu keda innar,daya a
falonta,daya na rumfar malam,ta saka a ciki don yayi sanyi.

Kamar yadda ta saba haka ta hada tray guda na abincinsu takai parlor din
inna,sannan ta koma daki ta zuba nata taci,abincin bai shiga da yawa ba,saboda
yadda ranta yake babu dadi,haka abincin bai mata taste a baki ba,tadaiyi qoqarin
dora walwala akan fuskarta saboda innar,data gama ci ma sai ta dawo parlor din ta
zauna suka kunna kallo,saidai gaba daya hankalinta bashi a wajen

"Kinga mufida.....nasan yayunki na hanya sun kusa isowa,dinga daukan abincin nan a
hankali kina kaiwa dakinsu,ga muqulli ki bude" inna ta fadi,mufidan ta tashi ta
karba muqullin,duk iman din sai taji ba dadi,saboda aikinta ne,amma ta bari,tunda
mufidan zata iya,ta dinga diba da kadan da kadan harta gama din,bayan minti wajen
goma iman ta tuna da lemon,tasan basu fiya son abu yayi sanyi da yawa ba,gwara a
cire musu shi a kai musu,kafin suci din xai huce,don haka ta miqe,ta cire lemon ta
nufi dakin bayan mufida ta gaya mata sakaya qofar kawai tayi bata rufe ba.

Hankali kwance ta tura qofar,saboda tasan babu kowa a ciki,wani sanyin


dadi ya bugi hancinta,dakin ya sakw wani girma kyau da haske,tunda akayi gyaran
bata taba shigowa dakin ba sai yanzu,ko ina tsaf tsaf,tiles din nan yasha
guga,mamakin ma wanda ke gyara musu dakin haka ya kamata,ta duqa a hankali tana
ajjiye jug din,dai dai lokacin da ameen ya fito daga toilet.

Da sauri ta miqe,har jug din na rawa kamar zai biyota,saida ameen din
yace

"Kula fa" batayi zaton yana dakin ba,hannun rigarsa a nade zuwa gwiwa,ya cire links
din rigar,fuskarsa zuwa hannun da qafar tasa duk jiqe da lema,da alama alwala
yayi,hakan ya bawa kwantaccen gashin dake hannunsa damar sake kwanciya lif,sai taja
da baya tana shirin fita,ya sadiqu ya sako kai.

Dubanta yayi sosai


"Yau kuma a gari inji maqi baqo?" Binsa tayi da kallo,yana qarasawa gami da bude
kwanukan abincin

"An gama nunqufurcin kuma yau anyi abinci kenan" ameen dake ware hannun rigarsa
bayan ya shimfida abun salla ya xuba mishi idanunsa

"Xakazo muyi sallar tukunna ko sai ka gama sharhin?"

"Da alwalata fa,amma dai bari na sake wata.....idan kin shiga ki cewa inna mun
dawo" wannan ya bata damar juyawa da hanzari ta fice,tana godewa Allah da bai samu
damar sauke mata nashi kason ba.

"Wannan abun sam banajin dadinsa ba sadiqu" amin din ya fada sanda sadiqun
ya fito daga alwalar

"Me akayi?" Tsaiwarsa ya gyara

"Ya za'ayi a takura yarinya haka?,dazu dazun inna ta gama yi mata fada,sannan kai
kazo da naka zaka dora?,duka takurar ta meye ne?,kowanne bawa da kalar tasa
qaddarar,kuma duk yadda ta riskeshi haka zai karbeta,don ban auri iman ba a baya ba
wani abu bane,ba hakan na nufin dukka wata kyakkyawar alaqa dake tsakaninmu ba ta
yanke,bata sona ne.....kuma ba wanda zai zauna mata dani,ta samu rabonta nima kuma
na samu nawa,komai.ya qare a tsakaninmu,ba wata sauran alaqa,amma kuma har yanxu
tana nan a matsayin qanwata.....to kuma meye na tsananin?"

"To akaramakallahu......tayar mana da sallah" sadiqu ya fada yana jinjina karamci


irin na amin din,yana tuna irin wahalar da yasha a asibiti shekarun baya sanda iman
din ta zama ta wani,amma ko a sannan nunawa yake ba silarta bane,muqaddari ne daga
Allah.A yanzun kuma yana qoqarin sake share komai tsakaninsu,da kuma yunqurin maida
matsayinta irin nada,lallai iman din tayi asara iya asara,asarar da bayajin zata
maida kamarsa,tunda kusan zaice mai rabo ta dauka......

Ranar wuni tayi cikin gidan,kuma cikin parlor din innar,babu inda taje,duk
don ta faranta ran innar,sai kuma taga ma gaba daya ma baya zama a gidan,daya shigo
yake fita,da alama akwai wani abu me muhimmanci da yaketa aiwatarwa,wanda ya
hanashi zaman.

Hudu ga sallah ya shirya zuwa jigawa wajen yaya baraka,mota har qofar
gida mai kyau ya dauka shata shi kadai,batasan mufida zata bishi ba,sai gani tayi
tana shiryawa,tayi shuru tana tuna shekarun baya da suka shude,a irin lokaci irin
wannan itace kan gaba wajen tafiya jigawan,idan sukaje a qalla sukanyi kwanaki uku
acan,yaaya barakan tana lelenta gami da ina ka aje da ita.

Tana parlor tana yiwa inna moping ya shigo parlor din,sanye yake da
wata danyar shadda ruwan sararin samaniya,wadda ta dinku ta kuma zauna a
jikinsa.hakanan ta dace da jikinsa,kansa babu hula,hakan ya bayyana kansa daketa
qyalli,da alama ta samu gyara ainun,hular tana riqe a hannunsa kawai,da alama baida
sha'awar sakata,kallo daya zaka yi masa kasan cikakken dan gayu ne,wanda yasan
ma'anarsa,bawai a baki kawai ba,har a aikace,duk indanya gifta kuma sai ya bar
tsarabar qamshinsa mai sanyi a wajen.

Kallo daya tayi masa ta sadda kanta qas,wani kwarjini yake mata a yanzun
sosai fiye da shekarun da suka shude,bata sani ba ko a yanzun yafi cika idanu
ne,shekaru da cikar sametakarsa da suka bayyana muraran oho

"Ina kwana?" Ta fada kanta a qasa,don tasan ba zata iya hada idanu dashi
ba,waiwayawa yayi yayi mata kallo daya ya amsa da

"Kin tashi lafiya?" Yasa qarasa takawa zuwa ciki,idanunsa kan agogon bangon parlor
din innar

"Alhmdlh" ta amsa masa a gajarce,saboda sam bata saba da irin wannan gaisuwar tasu
ba,baquwace a gurinta,kuma sun fara irinta ne tun sanda komai ya lalace a
tsakaninsu.

Kamar ko yaushe ya tsugunna a ladabce ya gaida inna,ta amsa tana cewa

"Tashi aminu karka bata jikinka,wajen a danyace yake bai bushe ba" sai ya saki
murmushi kawai yana cewa

"Inna zamu wuce"


"To ma sha Allah......sai yaushe kenan?"

"Eh to,ina jin ba zamu wuce gobe ba,saboda cikin satin nan nake saka ran fara shiga
office,kuma har yanzu ban gama shirya komai da komai ba"

"To madalla,madalla......bari na baka saqo ka kaiwa barakan" sai inna ta miqe zuwa
cikin dakinta,tsalelen agogon hannunsa mai tsada ya kalla,sai ya sauke hannunsa
yana sake gyara zamansa,yana dan tsokanar mufida da lallausan muryarsa,akan yadda
ta zaqu su tafi,har zuwa sanda inna ta dawo da leda babba ta miqa masa,ya amsa suka
sake sallama

"Allah ya kiyaye hanya" kalmar data amsawa mufida da ita kenan sanda take ce mata
sun tafi.
A ranar tayi zaton zata sake sosai,saboda dodon nata baya nan,amma sai
taji sam ba haka bane,hasalima gaba daya sai takejin wani kewa da rashin dadin
zaman gidan,daga bisani ta alaqanta hakan da rashin mufida,tunda zuwa yanzu sun
saba sosai,har inna na shawarar daukota gaba daya,tunda tasan da gudu iyayenta zasu
bata ita.

**** *WASHEGARI.......* Samun kanta tayi da tsara abinci me kyau,abincin ma kalar


wanda tasan ya amin din yanaso,tunda taji sunyi waya da inna,ya tabbatar mata zuwa
yamma zasu taho,yasan zasu qaraso kafin magariba,tunda tazarar dake tsakanin
jigawar da kano bai wuce awa biyu da rabi ba.

Sosai innar taji dadin abunda tayi,itama hakan sai ya faranta


ranta,tunda dama tayine saboda innar,burinta kuma ya cika,innar ta dinga janta da
hira,abunda ya jima bai faru a tsakaninsu ba.

Sai hudu na yamma ta gama komai,ta fada wanka sannan ta shiga dakin don
ta kintsa jikinta.

Tsaye tayi a bakin madubi tana kallon fuskarta,ita kanta tasan yau fuskar
tata ta cika da annuri,hakan kuma yana da alaqa da yadda suka wuni yau da inna
cikin dadin rai,sai ta samu kanta da yiwa kanta alqawarin lallai zata ci gaba da
yin hakan,kodon ta samu irin wannan kulawar data rasa a baya.

Barin gaban mudubin tayi da sauri ganin lokacin sallar la'asar na nemam
qwace mata,ta isa ma'ajiyar kayanta,ta fitar da wata doguwar riga mai budadden
hannu,wuyan me kwala ne,haka nan qasar rigar a bude yake sosai,ta saka ta shafa
powder da lip gloss,sannan ta saka hijabinta ta tada salla.

Tana idar da sallar ta fara azkar dinta na yammaci,kamar jira wayar tata
take ta idar din ta dauki kida,ta miqa hannu ta dauko tana duba me kiran,dr ahmad
ne,kuma ko shekaran jiya ya kirata ya gaisheta kamar yadda yace,saita daga wayar ta
kara a kunneta hadi da sallama.

Cikin sakewa da sauqinsan nan ya amsa mata,sannan ya fara gaidata,abunda


yake dada sakata jin nauyinsa kenan,shi bai wani damuwa da ta gaisheshi,mutum ne
mai.matuqar sauqin hali da sauqin kai,saita maida.masa gaisuwar,ya amsa sannan ya
fara janta da hira.

Tadan saurareshi,saboda tana kunyar qin tsayawar,don sau biyu yana kira
tana taras da miscalled kuma.bata bi kiranka,kuma ko a yanxun bai mata qorafin
rashin daga wayar ko kuma qin biyo kiransa ba.

"Har yanzu lokacin baiyi ba da za'a bani dama nazo?" Kanta ta girgiza kamar
tana gabansa,amma a furuci sai tace dashi

"Kayi haquri" ajiyar zuciya ya sauke

"Inata haquri hajjaju......amma zan gaya miki gaskiya,kawaici kawai nakeyi,inason


nazo mu tattauna seriously,zuciyata kullum qara ragwancewa takeyi,kada naje ina
zaune ayin overtaking" duk da ta gama gano manufarsa a kanta,amman yanzun da ya
fara bayyanawa sai da abun tajishi wani iri,batasan me ya dauki dr ahmad ya fada
sonta haka ba,amma koma meye tanaso su rabu lafiya,saboda mutum ne daya girmamata
qwarai da gaske,ya kuma taimaki rayuwarta sa shawarwari da kuma kulawa ta musamman
irin ta likita,amma zance na gaskiya ita a yanzu kwata kwata babu wanu tsari ko
maganar aure a ranta,batajin akwai wanda zata iya bawa filin zuciyarta ya shiga.
"Akwai lokaci"
"Ya ubangiji,ka nunamin wannan lokacin" taji ya fadi da confidence dinsa,saita sake
masa murmushi kawai.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 42

Ana idar da sallar magarib da hijabin jikinta ta shiga falon inna,ta sameta
itama ta kammala sallar

"Inna kinga su mufida shuru har yanzu"

"Zancansu nake nima a raina,ke nake jira kizo ki kamo min su a waya"

"To" ta amsa dashi,saita zauna ta fara lalube a wayarta,cak ta tsaya daga


bisani,tunawar da tayi alameen inna keso a kira mata ba ya lamin na shekarun baya
ba,sai ta sauke wayar tana dan duban inna,saboda bata da number wayarsa a halin
yanzu,batason kuma ta fadi inna ta tunzura,saita miqe a fakaice,ta dauko wayar inna
ta saka numbers din ta fara kira.

Dab da zata tsinke taji ya daga,muryarza fes,da wannan sautin mai nauyi da
kuma taushi yayi sallama,saida gabanta ya fadi sannan ta amsa sallamar a
hankali,shuru ya ratsa tsakani na aqalla sakanni goma,daga can bangarensa yayi
shuru yana saurare,duk da zuciyarsa ta gama shaida masa wacece,amma ko afuska baiyi
alamun da zai nuna ya gane din ba

"Wace?" Ya jefa tambayar kai tsaye,zare wayar tayi daga kunneta a hankali,wani abu
yana mata susa a qirji,dama bai kamata ta kira ta kama wayar ta qanqame ba,saita
miqawa inna tana cewa

"Gashi"
"Yauwa" inna ta fada tana karba,miqews tayi ta matsa gaban kayan kallo ta maida
gaskiya plus wanda suke gabatar da shirin zamantakewa,sai da innar tace

"Gashi" sanna ta juyo ta karba wayar,tana shirin sakata a charge ya sadiqu ya shigo
falon

"Inna kinjisu al'ameen shuru ko?"

"Eh yanzu muka gama waya dashi,ashe mota ce ta basu matsala a hanya"

"Haka yace wallahi,ya kirani"

"To Allah yakiyaye,ya kawosu lafiya"

"Ameen ameen.....me kuka dafa ne inna,inaso zan fita" yayi maganar yana kallon
iman,kafin ta amsa masa sai kuma yace

"Yi sauri ki zubomin,na makara" miqewa tayi ta zuba ta kawo masa,yana ci suna hira
da inna,har ya gama ya miqe zuwa dakinsu da sunan zaiyi wanka,iman din na kallonsa
tanason tsokanarsa kan zance ya fara zuwa ne,saidai ganin yana sauri yasa ta barshi
har ya fice.

Ba'a rufa awa daya ba sallamar mufida ta fara iskowa cikin gidan,ta shigo
dakin innar bakinta a washe,tana janye da wani babban buhu da yafi qarfinta

"Inna mun dawo" ta fada tana sakin buhun gami da zubewa

"Lale maraba da mutanen jigawa tarin Allah" tsokanarta iman ta fara yi,daidai
lokacin da muryar amin ta bayyana a tsakar gidan shima yayi sallama,gabanta ya fadi
kamar ko yaushe,ta lumshe idanunta tana kiran sunan Allah,sai kuma muryar tasa ta
gauraya data ya sadiqu,dukkansu suna yunqurin shigowa parlor din

"Kaima ance ka siya mota kaqi,ka tsaya wani noqe noqe,kullum baka da aiki sai
shatar mota,kana zaune zan siya mota,ka zauna kallo,ana gama maganar gidansu
yarinyar nan motar zan hara" ya sadiqu ya fada sanda suke shigowa falon,yana kan
gaba,sanye da wata dakakkiyar shadda ruwan hanta,ya kafa hula abunsa yayi kyau
sosai,shima sadiqun a wadan nan shekarun sai hamdala,saboda tuni ya daina aikin
gyaran mota,ya fara sana'ar siyar da sabbin spare parts na motar,kuma samu yake
sosai

"Zan siya,komai a hankali ake abinsa mr sadiq" ameen dake shigowa rataye da jaka a
bayanshi ya bashi amsa,ya zarce da sauke idanunsa a fuskar iman wadda keta qoqarin
gyara zamanta ba tare da dalili ba.

Ita ta fara masa sannu da zuwa sannan ta zame jikinta tabar dakin,duk
sanda yake waje batajin sakewa kwata kwata,sai taji kamar ya cika dakin,bata iya
wani qwaqwaran motsi.

Takusa minti arba'in a zaune gefan gadonta,suna musayar text da dr ahmad


daya matsa mata ta tayashi hira,mufida ta shigo janye da wata leda ta miqa mata

"Gashi inji yaa baraka" ajjiye wayar tayi ta janyo ledar tana cewa
"Toooo,me muka samu?" Cikin ranta tana mamakin yadda yaa barakan ta aiko mata da
saqo haka?

Mangoro ne mai kyau da yawa,wanda a wajen fatarsa kore ne,amma ta ciki ya


nuna,irin mangwaron da take matuqar so,sai gyada mai bawo dame gishiri mai yawa
kowacce a qulle daban,sai dinya da yawa.

"Kai duk wannan nawa ne?" Kai mufida ta gyada

"Tace sanda kuke zuwa da ya amin sune kayan da kika fiso" wani nauyi da kunya suka
kamata,tabbas haka ne,a sanda take mutum kafin ta zama BUTULU KUFAN WUTA,ashe yaa
barakan bata manta ba?,hakanan abunda tayiwa dan uwanta bai sanya ta gaza aiko mata
da tsarabar ba?,wanne irin karamci ne har haka?.

Fita tayi da kayan ta adanasu,ta diba gwargwadon yadda zai isheta ta dawo
daki.

*************Daga tsaye take cikin parlor din innar daga wajen bakin qofa,
breakfast take hannu baka hannu qwarya saboda gab take data makara,sanye take da
wata abaya saqar qasar dubai,wadda ya dace da jikinta,tayi mata kyau matuqa,saika
zata daga wanca jinsin ta fito.

Ta jiyo takun takalmin daga tsakar gida,amma bata kawo komai ba saboda
hankalinta bai wajen,sai da aka yaye labulen falon,haske ya cika falon tare da
sassanyan qamshinsa sannan ta ankara da waye.

Al'ameen ne,cikin wasu irin suit masu matuqar kyau da aji,idanunsu suka
sarqe cikin na juna,take bread din da take qoqarin hadiyewa ya tsaya mata a wuya,ta
hadiyeshi da qyar,sai kuma qwarewa ta biyo baya.

Dagowa yayi a hankali daga qoqarin cire rufaffun takalmansa daketa qyalli
saboda yadda suke fes babu ko digon qura a kai yadan dubeta

"Ki nema ruwa kisha kafin abinda kikaci ya dawo" ya fada a hankali cikin nutsuwar
nan tasa,yana qarasa fidda takalman,ya tako zuwa cikin falon bakinsa dauke da
sallama,daidai sanda inna ta bude labulen uwar dakanta ta fito tana cewa

"Wannan gaggawar da kike ba dole ki qware ba.....ba'a yiwa abinci haka


ai.....aminu......ka fito?" Cikin girmamawa ya gaidata ta amsa masa cikin kulawa

"Ina kwana?" Ta gaidashi tana daukar jakarta,wani irin kunya ce ta kamata,bataso


yaga kamar ganinsa yasa ta qware din

"Kin tashi lafiya?" Ya maida mata

"Alhamdlh.....inna na wuce" ta amsa masa hadi da yiwa inna sallama,saboda tana da


tabbacin matuqar taci gaba da tsaiwa cikin falon bata isa ta yiwa idanunta shamaki
da kallonsa ba.

"Ka zauna kaci wani abun mana" inna tace dashi bayan fitar iman,saiya
girgiza kai

"Ana jirana inna,kuma yau zan fara shiga office din,bai kamata naje a makare
ba,sannan ma kuma akwai abubuwan daya kamata ace nayi settling a yau din" addu'a
sosai innar ta kwarara masa,ya miqe cike da jin dadi da kuma qwarin gwiwa ya
fita,yana jin dadi da kuma farinciki mayalwaci cikin qirjinsa,ko babu komai,ya samu
wadda ta zame masaadadin mahaifiya,yake kuma samun da ɗaɗan addu'o'in da yake ganin
tasirinsu cikin rayuwarsa,lallai babu ko shakka,inna nada wani madaukakin matsayi
da kima a idanunsa.

Already akwai mai napep dinsa,yana qofar gida yana jiransa,yana shiga ya
gaidashi cikin girmamawa,sannan yaja motar suka fara gangarawa zuwa bakin titi.

Har sun gota yatsaidashi,ya sanyashi ya koma da baya,iman dince a tsaye tana
duba agogon hannunta,sam bata kula da tsaiwarsu ba

"Shigo mu saukeki" muryar amin din ta cika kunnenta,ta daga kanta da sauri ta
saukesu a kanshi,ba ita yake kalla ba sanda yayi maganar,wayar hannunsa yake
latsawa,ta janye idanunta daga kanshi ta fara takowa a hankali ta shiga motar,sanna
yaja suka fara tafiya..

Shuru ne ya ratsa motar,ba qarar komai saita iskar dake shiga tana
fita,da kuma daddadan turaren jikkunansu daketa gauraya cikin motar,duk juction din
da suka tsaya sai idanuwa sunyi musu ca,shi kam idanunsa nakan wayarsa baisan me
ake ba,tana tajin qarar tura saqo na watsapp.

A junction din qarshe wata budurwa ta ratso ta tsakiyar motocin ta yiwa


mai adaidatan magana tanaso ya sauketa a gaba,ya girgiza kai alamun a'ah,murmushi
tayi,idanunta nakansu iman din

"Hala ango da amarya ka dauko ko?,nice couple,wallahi kun dace,tun acan baya na
hangoku,kun burgeni sosai" dubanta sosai iman din tayi,yayi da amin ya daga kai
yayi mata,sai aka rasa mai bata amsa,harta ratsa ta cikin motocin ta bace musu.

Tsaiwa maganar tayi cikin zuciyar iman din,zuciyarta ta dinga azalzalarta


ta kalli yadda suka dace din ita da ya amin ta madubin motar tana qoqarin kaucewa,
lastly dai daga qarshe haka zuciyarta ta rinjayi idanuwanta,takai dubanta ga
madubin,cikij rashin sa'a ya daga kansa yana duban hanya saboda jin sun koma tafiya
slowly......karaf idanuwansu suka hadu,cikinbl wani irin hanzari da waskewa ta
kauda idanun nata. Qaramin sauti taji ya fita daga bakinsa,wanda idan har ta canka
dai dai murmushi yayi mata,gabanta ya fadi,kada dai ace ya ganta,tun daga lokacin
bata sake wani qwaqwaran motsi ba har suka sauketa yaja sukayi gaba.

Wunin ranar a makaranta babu abunda take tunawa illa wannan dan zaman nasu
da sukayi a tare,wani lokaci sai taji kamar jikinta yana tashin qamshin irin
turarensa ne,ranar gaba daya bata da wani kuzari sam a jikinta har aka tashi.

********Aiki sosai alamin ya kama babu kama hannun yaro,babban kamfani ne da suka
bashi babban matsayi,kamfani ne dake kula da gine gine da kuma qawar gidaje,suna da
rassa iri iri a fadin qasar nan,babban reshensu yana a china,albashi suka sanya
masa mai tsoka,amma duk da albashin da zasuke bashi.....da baiyi niyyar yin aiki
dasu ba,hankalinsa yafi karkata ga bunqasa harkar dinke dinkensa,kamar xasuyi fada
da sadiq ka hakan,saidai daya zauna sukayi shawara da inna da malam,malam ni ya
nusashe dashi alfanun karbar aikin,zaiyi amfani da albashinsa ya bunqasa wajen ba
tare da yabar aikin ba,wannan shawarar tayi masa,ya kuma gamsu da ita dari bisa
dari,don yasan cewa abinda babba ya hango,yaro ko yahau bushiyar rimi bazai
hangoshi ba.

*******A hankali ta gyara yafen mayafin doguwar rigar da take jikinta,sannan cikin
sanyi ta dauki tray din dake jere da abincinnasu ta soma takawa zuwa dakin nasu,don
dai babu yadda zata yine,amma gaba daya batason wani abu da zai kawo kusanci ko ya
sanya su kebe da ya amin din.

Idanunta ta lumshe tana zuqar iska sosai zuwa huhunta sanda ta tsaya
qofar dakin,ko ina na jikinta kamar an zare masa laka,ta tabbatar ya sadiqu baya
nan,yatabbata zance yake zuwa,don kuwa magana har ta fasu cikin gidan,a yau dinma
yana can,saboa haka tana da yaqinin ameen dinne kadai cikin dakin,tunda ya dawo ba
zata iya tuna sanda ta shiga kai masa abinci yana shi daya ba,yawanci ma a yanzu a
falon inna yakeci,idan kuma a dakin nasu zaici,mufida ke tsayawa daga soro tayi
musu knocking su karba ta koma ciki,to yau mufidan tana dan zazzabine,bata jin dadi
sosai.

Sallama tayi daga bakin qofar dakin

"Shigo" taji muryarsa tarrr yana bata umarni,wani abune mai qarfi cikin muryar
lamin din,wanda duk sanda yayi magana koda bada ita yake ba sai taji ta saukar mata
da nauyi saman zuciyarta da wani irin yanayi mai wuyar fassarawa,bataso ta shiga
din,bata qaunar hakan,saboda haka tayi kamar bata ji ba ta sake maimaita sallamarta

"Come in" ya sake fada daga cikin dakin,a yanzu kam idan taci gaba da tsaiwa yasan
cewa tayi ne tana sane,bata da wani sauran chance illa kutsa kai zuwa cikin
dakin,idanunta sauke a qas,saidai tana shiga natural sanyin da dakin yake dashi,da
kuma mayen qamshin nan nasa yayi mata sallama.

Yana zaune saman daya daga cikin kujerun dake gefe daya a dakin,wandda
tayi kyau sosai a mazauninta,saboda yadda dakin ya qara kyau fili da kuma
qayatuwa,sanye yake da wata baqar jallabiyya bai gajeran hannu,wadda tayi masifar
haska fatarsa,kamar wani balarabe cikin jinsin wadanda basu cika hasken fata
ba,sumarsa na nan a kwance cikin tsafta da burgewa,kai zaka dauka ba shine mutumin
da bai jima da dawowa daga office ba,wayace maqale a kunnensa,yayi relax cikin
kujerar sosai,babu lallai ka iya jin abinda yake fada.

Bata yarda ta kalli sashen da yake ba,qarasa a hankali wajen da suka ware
saboda cim abincin tana dora tray din

"Miss you too.....i will call you" kalmar da taji daga bakinsa kenan,wadda taji
kamar zuciyarta zata tsinke ta fado

"Zo nan" taji ya fada cikin wata murya dake nuni da umarni kai tsaye,cak ta
tsaya,sannan ta waiwayo a hankali,dai dai sanda yake sauko da qafafunsa qas tare da
matsowa zuwa gaba kana ya zauna sosai.
*_Arewabooks link_*

https://arewabooks.com/chapter?id=62beab3c93b638ade30a1fc7

_please follow me_


@HUGUMA
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 43

*_follow my account @arewabooks as HUGUMA,for latest pages_*

"Dage curtains din" ya sake fadi kafin ta qaraso inda yake,sai ta koma a
hankali zuwa bakin qofar ta yaye labulen yadda ya buqata,waje ta bayyana tarwai,ta
yadda duk wanda zaya wuce zai hangi cikin dakin,sannan ta tako inda yake,tana jin
qafafunta kamar sun lanqwashewa,kamar ba zasu iya daukarta ba.

"Uhmmm,zauna a nan" ya fadi yana pointing mata wajen da yakeso ga zauna din,wajen
ta kalla,a qa'ida yayi mata kusanci dashi da yawa,bata da yaqinin idan ta zauna
kafin ga tashi zuciyarta ba zata fashe ko ta tarwatse ba,ko kuma wani abun bazai
sameta ba,dole taja qafafunta ta zauna a hankali a wajen,saidai a matuqar takure da
kuma dar dar

"Iman..." Ya kira sunanta da wani irin heavy sound,wanda banda ta riqe numfashinta
da kyau ba shakka zata samun daukewarsa na wucin gadi,duk da haka bata tsira ba,sai
daya haifar da wani yanayi na daban cikin zuciyarta

"Me yasa kike qoqarin canzawa?,ko kuma nace kika canza?" Ya dakata a nan,ya zuba
mata idanunsa dake da nauyi da kuma dafi a kanta

"Yanzu meye hakan?,kalli yadda kika zauna?,dodo ne ni ko meye?,duk wani abu da yake
cikin idanunki ina iya karantarsa cikin lokaci qanqani......,bcoz.....nine mutum na
farko da zan gayawa duniya wace ke,idan don abunda ya faru ne ki aje wanna issue
din a gefe,ya wuce har gaban abada.....inaso ki saka a ranki da zuciyarki,babu wata
kalma data taba shiga tsakaninmu dake makamanciyar wannan,ki sawa ranki har yanzu
ya lamin dinki ne,wanda bai gurbata alaqar da take tsakaninku ba......idan hakan
shi ya haifar da wannan ciwon,ki manta dashi,ki dawo iman dana sani a baya,na
sani......kina takura kanki kan abinda ya shude har abada.....ki canza ki kuma
gyara,ran inna yana baci,idan kuma kikaci gaa da wannan silly behavior
din......ranki zai baci" yana kaiwa nan hawaye suka sauko mata,hawaye masu
dumi,wasu maganganun nasa sun dada maga,wasu kuma sun tashi hankalinta,sun kuma
sakamata shakku,tare da wani yanayi na tsaka me wuya.

"Ehnnnnn.....idan kin gama kukan kya iya tafiya" ya fadi yana komawa
baya,yayi relaxing jikin kujerar ya janyo wayarsa yana dannawa.

Cikin dauriya da juriya ta goge hawayen fuskar tata,sannan tayi magana


cikin harshen dake nuna anyi kuka

"Kayi haquri,zan gyara"

"Da kyau,Allah ya tashemu lafiya" ya amsa mata yana ci gaba da danna wayar
still,saita miqe,tana takawa a hankali har tabar dakin.

Ita kadai tasan me takeji a cikin zuciyarta,ita daya tasan yanayin da


maganganunsa suka jefata

"Su koma kamar da?,kamar yaya lamin da iman din inna?,kamar wata alaqa bata taba
hadasu ba,hakan fa yana nufin yankewar komai da komai a tsakaninsu kenan" wadan nan
maganganun ta dinga juyawa cikin ranta,barci kuma ya qauracewa idanunta,tana jin
wani suya cikin qirjinta,har sai bayan da dare yayi nisa sannan ta samu baccin yayi
gaba da ita.

*******Cikin kwanakin taga abinda ya fada mata din a aikace,da gaske ya maidata
iman dinsa tada,ya dawo da caring irin na yaya da qanwa dake tsakaninsu,saidai a
wannan karon akwai jan girma a ciki,wani lokaci harda wannan dadadden miskilallen
halin nasa,ya koyi yi mata fada idan tayi ba dai dai ba,ba kamar baya ba da kome
tayi zai dinga qoqarin bata kariya a idanun mutane,akwai haduwar jini tsakaninsa da
mufida,don haka 'yar gidansa ce ita din,yadda zaiwa mufida hakanan yake mata,babu
wani banbanci a tsakani,tayi qoqarin ganin ta warware itama,ta ajjiye komai a gefe
ta koma yi masa kamar daa,saidai akwai wani strong feeling cikin zuciyarta,mai
matuqar qarfin da itakanta take kasa controlling kanta a yawancin lokuta,sau tari
sai ta bude WhatsApp dinta ta ganshi a online,kota duba dp dinsa,duk da ba
ma'abocin saka hotonsa bane,a dp din,duk wani movement nashi hakanan ta samu kanta
da interest akai,saidai babu wani abu data gani na daban tattare da alamin din,face
fsohuwar alaqar da take tsakaninsu zalla da ya sabuntata.

Rana daya ta kalli kanta a madubi taga tana ramewa,abunda ya bata


mamaki,ta kalli kanta ta sake kalla,tasan akwao stress na karatu,amma koma behind
it akwai wani abu da ake kira rashin sukunin zuciya.

Tun da bata da wani aboki ko qawar shawara saishi,a yanzun kuma batajin
zata tunkareshi da wannan batun,abu me matuqar saka jin kunya ga duk wanda aka
budewa karatun,bushira ce kawai tazo ranta,duk da suna haduwa a chart suyi hira da
ita,amma a yanzu ba shakka tana buqatar ganinta,tasan cewa ita kadai ce zata bata
gamsashshiyar shawara bisa amana da kuma sirri,wannan yasa ta kirata tun safe ta
gaya mata tana zuwa,da yammaci tayi qoqarin gamawa inna komai,ta shirya tsaf cikin
atamfarta riga da skert,ta dora babban hijabi me hannu da ya saukar mata har qasa
ruwan makuba neat dashi abun burgewa,kalar ta farare ce,hakan ya sanya yayi mugun
mata kyau,don ko ita data tsaya gaban mudubi ta gani,tana godewa Allah kan tarin
baiwarwakin da yayi mata,babu wanda zai kalleta ko a mafarki yace ta taba aure,duk
da auren a suna ne kawai,bai amsa sunansa ba.

Gayu da qamshi sun matuqar zaunar mata,don haka ko zama kayi sosai kusa
da ita kana iya diban tsarabar sassanyar qamshinta,wanda sai kana gab da ita ne
zaka jishi.

A parlor ta tadda ina ta shaida matan zata fita gidansu bushiran,bata


hanata ba,bushira sananniya ce,sannan tana yawaita ziyartar iman din,ta kalli
mufida dake bacci a kujerar falon inna

"Ga 'yar rakiyar tawa tayi bacci"


"Eh saidai ki maza kije ki dawo"

"Yanzu kuwa inna in sha Allah" ta amsa mata tana sanya plate shoes dinta daya dave
dace da shigarta ta nufo waje.

Kamar ko yaushe cikin nutsuwa tsari da kamun kai take tafiya,duk da yadda
idanuwa kan mata caa idan ta fito amma bata daga kai bare ta damu dasu,tasan ita
din wace,ta kuma san mutunci da darajar kanta,cikin mintina qalilan ta isa gidansu
bushiran.

Ta samu gidan ba kowa sai ita,tana ta wainar fulawa,wadda qaninta ya roqeta


tayi musu shida abokansa,kujera taja ta zauna zata tayata

"A'ah,wallahi bakiga yadda kikayi kyau ba,kada ki bata jikinki da manja,rigimar


alqasim ce kawai ya tsiri na musu waina,ni da nake karatun exams,kedai bari na saka
miki kici kawai" saita zaro plate ta saka matan,tana ci tana bude mata flask din
tana zuba wadda ta soyu.

"Naji kince akwai magana,tun dazu nake dakon shigowarki" ta tambayi iman
din bayan ta gama ci,yanayin yadda fuskarta ya koma kawai ya gayawa bushira she's
serious kan maganar daya kawota.

"Magana xamuyi dake bisa yarda dake da amincin da yake tsakaninmu,duk


duniya ba wanda zan iya gayawa wannan maganar saike,na dauki tsahon darare da
kwanuka ina qaryata kaina,saidai kuma kan nawa shima qaryatani yake,har kuma ya
rinjayeni.....bushira na kamu da son ya alameen" ta qarashe maganar cikin wani
rauni,har idanunta suna tara hawaye.

Tsoro mamaki ko razani ta tsammaci gani daga fuskar bushira,amma sai


murmushi da nutsuwa akasin wadancan ababen ya bayyana,abunda ya bata mamaki,ta
tsaya tana duban bushira.

A kalla minti biyu suna a haka sannan bushira ta magantu

"Na baki mamaki ko?,to ai hajiyata wannan maganar a bude take,ke kika yaudari kanki
kika kuma ha'inci kanki,kin dade kinason ya alameen.....rudar kanki kikayi,da kuma
salon taki qaddarar data jefo miki da bassam,ya rikita qaramar zuciya da
qwaqwalwarki dake ginuwa a lokacin.....kika dauki son da kikewa ya amin kika bawa
bassam,a zatonki bassam din kikeso,bayan kuma bashi kikeso ba......bassam ya taka
sahun barawo ne kawai a hausance" dif iman din tayi,tana jinjina kaifin basira da
hangen nesa irin na bushira,ta karanta tsaf abunda ta jima tana surantawa a ranta
da tunanin yadda zata fito dashi.

"Me kike jira da baku koma bigiren da kike akai ba keda ya ameen a yanzu
tunda kuna da dama?" Kanta ga girgiza cikin alhinantawa kanta

"Mun koma......amma ba irin bigiren dake kike hasasowa ba......na koma matsayina na
qanwarsa ne kawai,yakuma gayan iya hakane buqatarsa"

"To shine me?,zama zakiyi kina kallo ya zama rabon wata?,ko bari zakiyi ya subuce
miki,a wannan zamanin da nagarta tayi wahala,samun miji na gari yake neman zamewa
diya mace garari?,idan zaki tashiga ki maida kanki zuciyarsa cikin
siyasa......bazan boye miki ba,randa na sake ganin ya amin nima ya tafi dani
wallahi,kawai don nasan ajiya ce ta amana shi yasa na basar kawai" dole bushiran ta
bawa iman dariya

"Da gaske nake miki,ki qoqarin daidaitawa kafin kiji sold out" wannan karon dariyar
iman din sai data fito,ta daki cinyar bushiran

"Wai sold out kamar kaya"

"Tabdi,irin ya alameen ai kayanne masu tsada"

Wannan maganganu da kuma tattanawa da sukayi da bushira ta dade tana


juyasu cikin ranta,tana aunasu a mizanin dacewa da kuma rashin dacewarta,tabbas
soyayyar al'ameen ta yiwa zuciyarta wani wawan kamu da batasan yaushe hakan ta
kasance ba?,idan har zata budi idanu taga ya zama rabon wata ta auna ta kuma
gwadawa zuciyarta zata iya jurewa?,bataga mafita kota ina ba,to amma kuma ta yaya
zata dorashi akan irin mizani da saitin da bushira ke mata nuni?,akwai abubuwa masu
tarin yawa dake sanya zuciyarta cikin kunya nauyi da kuma shakku duk sanda zata
daga kai su hada ido da ya ameen din,a fuska take qoqarin maida komai ba komai
ba.....kamar yadda ta gaya matan shi a nashi sashen haka yake,saidai ta sani
abundan ya farun wani abune da zai matuqar wahala ya gogu a zahiri.
Zuwa yanzun zuciyarta na gaya mata kamar ya alameen din yafi
qarfinta,tako ina qofofin samu da kuma na arziqi ne suke bude masa,sabon shafin
wadata da arziqi wanda suka bayyana hatta da saman fatarsa,zaka dauka cewa ba cikin
gidan nasu yake rayuwa ba,duk da cewa gidan nasu a yanzu a layin yana cikin sahun
gidaje dake da kyau da kuma tsari,can qasan ranta zuciyarta tana rawa tare da kwana
da kuma tashi da fargabar kada ya kamo zuciyar wata ko shi a kamo tashi.

Bai cika shekara da kama aikinsa ba kawai yazo da takardun gida,gidane


me kyau da kuma tsari daya siyawa malam din,da sunan su tashi daga nan,a barshi a
mazaunin makaranta,su kuma su koma sabon gida,da farko malam ya fara fada

"Yaya zakayi haka aminu?,wanne irin bahagon tunani ne wannan kayi?,kai da kake da
fili kake kuma gini?,muke saka ran ku gama kai da sadiqun kuyi aure kwana kusa?"
Lafazin auren da malam ya ambata shi ya sanya iman miqewa tsam ta fara takawa tabar
wajen,saboda ambaton kalmar dai dai yake da bugun guduma a tsakiyar kanta,batasan
ya suka qare ba,daga bisani dai ta tsinci maganar tabbatuwar tashinsu,ta fara hada
kayanta kamar yadda taga kowa yanayi,ranar wata alhamis bayan sallar magrib suka
bar unguwar,bayan sunyi sallama da kowa.

Ginine me kyau irin na zamani,gidane madaidaici,wanda bai cika girma sosai


ba,hakanan ba qarami bane,kamar gidan amarya,an tsara komai bisa tsari da kyau da
kuma burgewa,duk wanda yazo sai ya yaba gidan,hakan 'yan rakiya da sauran 'yan uwa
suka dinga fatan alkhairi tare da fatan tarewarsu a sa'a.

***********"Wayyo" tadan fada can qasan maqoshinta,tana miqewa daga durquson da


tayi,har yau dakunansu basu gama zama ready ba,gyaran gidan suketa yi,wuni na uku
kenan,saidai zuwa yau alhmdlh komai ya kusa kammala.

Ja da baya tayi tana kallon kanta a sabon madubinta,ta fito tar,duk da


cewa batayi wanka ba amma ba zaka iya gane hakan ba,tana sanye da wata doguwar riga
me zubin A shape,ta wani black cotton material ce mai touches na white,kanta kuwa
siririn mayafin rigar ne ta daure kanta dashi,amma qanqantarsa ya sanya baifi rabin
gashinta ya rufe mata ba.

Kishirwa take ji,don haka ta ajjiye sabbin kwalaben turarukan data siyo
bayan ta gwada fesa daya,ta taka a hankali zuwa parlor din gidan don ta dauka ruwa
a fridge tasha,kasancewar yau garin akwai hucin rana babu laifi,duk da cewa yamma
liqis ne yanzun.

Sai data shaqi qamshin dake parlor din na sabunta da kuma turaren da suka
kunna wanda tuni har ya gama cinyewa,saidai qamshinsa yana nan,ta qarasa fridge din
ta bude ta dauko pure water guda daya ta bula ta fara sha,sannan ta juyo a hankali
da nufin komawa dakinta.

Tsaye yake cikin parlor din,sanye da suit dinsa,hannunsa riqe da brief


case,bata tsammaci ganinsa ba ko kadan a irin wannan lokacin,wannan yasa ruwan da
take sha ya zarce mata take kuma ta qware,ta hau tari sosai.
https://arewabooks.com/chapter?id=62beaa7c93b638ade30a0e93
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 44

"Ya salam,garin yaya?" Ta furta sanda yake qarasowa inda take tsayen,kasa daga kai
tayi bare ta bashi amsa,tana jin haushin kanta na yadda duk sanda zasu hadu sai
tayi misbehaving,batason taci gaba da yin abubuwan da zasu janyo ta bada kanta

"Sannu" ya fada yana ja da baya kadan,kafin takai ga amsawa yace

"Ina inna?"
"Tana daki" ta amsa masa ba tare data iya daga kai ta dubeshi ba,qamshin turarensa
ke haifar mata da wani abu cikin zuciyarta
"Qyaleta" ya fada yana juyawa zuwa qofar da zata fiddashi daga parlor din,ta kuma
sadashi sa sassan su shida sadiqu,a sace tabi bayansa da kallo,kullum sake kyau
yake da kuma sake zama wani na daban,cikakken namiji me aji,hutu jin dadi da
kwanciyar hankali na sake bayyana muraran,tun daga kan fuskarsa har saman fatarsa.

Kadan ya rage ya kamata sanda take kallonsa,cikin wani irin hanzari ta


dauke kai lokacin da ya waiwayo

"Me kuka dafa?" Yayi mata magana kamar yadda ya saba yi mata ayanzu,cikin dakiya
shariya wani lokaci tare da burbushin halayyarsan nan miskilanci

"Tuwo ne" sai yadan murza goshinsa da yatsunsa

"Zan iya samun wani abun nadaban,wanda bazai wuce rabin awa ba" kai ta gyada
masa,sai ya juya yaci gaba da takawa,maimakon itama ta koma dakin,sai kawai ta
zarce kitchen,a yanzu bata da burin daya wuce yace yana buqatar abu kaza,wanda ita
kuma a yanzu ba kasafai hakan ke hadasu ba.

Cikin minti talatin din da ya buqata ta gama shirya komai,ta dauki


wayarta ta laluba number dinsa,sai datayi kamar zata kira sai kuma ta fasa,kada ta
zaqe da yawa,don haka ta dawo parlor tayi zaune kawai bayan ta kunna tv din dake
aiki cikin parlor din,hannunta riqe da wayarta tana duba wasu hotuna da sukayi biki
a nijer watannin baya da suka wuce.

Tun kafin ya qaraso qamshinsa ya cika wajen,abinda ya qara gudun zuciyarta


kenan,tana ga qoqarin hana kanta daga kai ta kalli qofar,wani sashe na zuciyarta
kuma na azalzalarta,a haka sallamarsa ta cimma parlor din lallausar muryar nan
tasa.

Sanye cikin wani lallausan farin yadi mai shara shara,wanda har kana iya
hango singlet dinsa ta ciki,Hannunsa daya saye cikin aljihunsa,daya hannun kuma
yana amsa waya dashi.

Fadin yayi kyau ma bata baki ne,wani sassanyan kyau mai tafiya da aji da
kuma nutsuw,sumarshi tasha gyara sosai,lallai ta yarda ameen data sani a yanzu ba
shine alameen din data sani a baya ba,komai ya saka yi masa kyau yake,ado mai cike
da tsari da tafi da hankali.

Karamin dining da aka sawa innar a parlor wanda taketa mita akanshi ya
nufa,har yanzu wayar yake amsawa,yayin da iman din ta gaza tashi daga inda take
zaunen,saboda ta tabbatar idan taje din sai tayi wani abu da ba dai dai ba kamar
yadda ta saba.

Parlor din ya dauki shiru bayan ya gama wayar,sai qarar plate da spoon
dinsa daya fara cin abincin bayan yayi serving kanshi,cikin nutsuwa yake kai
abincin bakinsa,fitowar inna ta katse shurun da ya wanzu a wajen,ta qarasa inda
yake tana tambayar yaushe ya shigo

"Tun dazu inna,har na shirya zan sake fita ma,nasan aiki kike shi yasa nace a
barki" tana daga kan kujerar amma kunnenta na wajen,fiye da rabin hankalinta yana
kan hirarsu,tunda ya shigo din hankalinta ya gaza kwanciya,shigar da yayi ta
tabbatar mata fita zaiyi,abun tambayar shine ina zashi da yammacin nan lis?.

"Don Allah inna idan sadiqu ya shigo kice ya jirani,na kira wayarsa ban
sameshi ba"

"To shikenan,a dawo lafiya"


"Ya ameen a dawo lafiya" mufida itama ta fada,dole itama tabi sahu,ya amsa ba tare
daya duba sashenta ba ya fita.

Kamar ya fita da dukkan wata walwala tata da kuzari,sai taji duk zaman
parlor din bai mata dadi,wayarta na a hannunta tana chart,saidai kuma a hankali ta
daina fahimtar abunda take dubawa cikin wayar

"Na zuba mana abinci yaa iman?" Mufida ta tambayeta,sai ta kashe datar tana
kallonta

"Banajin yunwa yanzu kam,ci abincinki,sai zuw anjima" tayi maganar tana zamewa
saman doguwar kujerar falon,bayan ta saka mufida ta miqo mata remote ta canza
tasha.

Duk da kallon da take yadan dauki hankalinta,saidai hakan bai hanata duba
agogo ba duk bayan wasu mintuna,suna nan zaune a parlor har sanda malam ya shigo
inna tayi wajensa,falo ya zama daga ita sai mufida,da yake yarinyar mayyar kallo
ce,takwas tara goma duka tayi a idanunta,babu alamun shigowar ameen din,a hankali
ta dinga jin zuciyarta tana takurewa waje guda,wani abu ya tsaya mata a wuya,a
hankali zuciyarta ta fara yi mata zafi,saita lumshe idanunta kawai tana sauraren
bugun zuciyarta.

Sallamarsa ce ta ratsa tsakar gidan har zuwa parlour din,saita maida


idanunta ta lumshe,tana jiyoshi lokacin da yake shaidawa inna ya dawo,sai kuma
muryarsa cikin taushi yake kiran mufida wadda ta fara gyangyadi,bata da dogon
bacci,hakan ya sanya yana kiranta ta miqe ta fita waje,saita buda idanunta tabi
mufida da kallo har zuwa sanda yarinyar ta dawo parlorn.

Dauke take da wata baqar leda mai adon zaiba,bakinta har kunne ta fara
magana

"Ya iman,tashi ki gani" qarasowa tayi gaban iman din ta tsugunna ita da ledar tana
qoqarin ciro kayan ciki

"Ya ameen ne ya bani,zance yaje yau,yacema tace tana gaisheni" tabbas inda mufida
tasan yanayin da zata shiga da ba zata bata wannan labarin ba,gaba daya tun daga
cikin kwanyarta zuwa tafin qafarta kamar an xuba mata kiyashi haka ta dinga jin
wani abu,kamar ana yamutsa kwanyarta,tana daga kwancen ta kasa amsawa mufida kamar
yadda ta kasa tashi,da idanu tabi kayan da yarinyar ke fitowa dasu da idanu,pepper
chicken ne sai meat pie da samosa,sam bata fahimtar abunda mufida ke fadi,taga dai
tana miqo mata kayan bayan ta kaiwa inna ta dawo,abu daya ta iya shine girgiza mata
kai,sannan ta kira sunan Allah can qasa ta yunqura ta sauke qafafuwanta qasa,ta
fara takawa a hankali zuwa dakinta,saidai tana jin kamar qafafuwanta ba qasa suke
takawa ba,kamar gangar jikinta ba zata iya kaita daki ba.

Tana shiga ta murzawa dakin nata key,ta kuma sulale a qasa a hankali ta
saki wani kuka mara sauti,saidai mai cin zuciya da kuma gangar jiki gaba daya,don
gaba daya ta cure waje daya,jikinta kuma ya kama rawa,sanyi take ya lullubeta,saita
sake qanqame waje daya,ta tura kanta tsakanin cinyoyinta.

Wani irin zafi zuciyarta keyi,wanda ya sanya hatta da hawayen dake fita a
fuskarta masu zafi ne,indai har da gaske mufida take,indai har ameen ya fara zuwa
zance,hakan na nufin ya fara son wata?,hakan yana nufin zuciyarsa ta fara qaunar
wata ba ita ba?.

Ya ilahi zata iya jurewa?,zuciyarta zata iya dauka?,bata da tabbas.....bata


da tabbacin hakan,amma ta sani cewa gagarumar matsala da damuwa ke fuskantota,ta
yaya zata tunkari ameen da batun soyayyarsa?,ta yaya zata bayyana masa abunda take
ji a zuciyarta,ta yaya zata gaya masa tun da can da yanzu shine dai cikin
zuciyarta?,shine ya mamaye dukkan wani sashe na zuciyarta da kuma rayuwarta?,saita
xame a wajen ta kwanta gaba daya saboda yadda kanta yake sara mata,bata damu da
sanyin da yake busowa ta wajen ba.

Sau biyu mufida tana knocking qofar amma saidai tayi mata gyaran murya,daga
bisani data gaji bata qara bugawar ba.

Tayi kuka a ranar iya son ranta,kukan da sai daya sanya taji kanta
kamar an saqala mata dutse saboda nauyin da yayi mata,batasan yawan lokacin data
dauka kwance a wajen ba,illa dai daga bisani taja jikinta zuwa saman gadonta ta
kwanta da qyar,jikinta saboda zafi kamar ana hura wuta,a zahiri kuma wani irin
sanyi takeji sosai a jikinta.

Tayi sa'a sallar asuba bata kubce mata ba,saidai tana rawar dari tayi
alwalar tazo ta tada sallar,bayan ta idar saita bude key din data sakawa dakin,ta
dawo ta kwanta tana sake curewa sosai,saboda azabar zazzabi da sanyin dake ratsa
mata qasusuwa,ta lumshe idanunta,har yanzu tana jin qunci da zafi da zuciyarta take
mata.

K'arfe bakwai mufida ta shigo dakin

"Yaa iman....ya iman" baccin wahalar daya fara daukarta ya katse,sai ta bude
idanunta a hankali tana duban yarinyar

"Ki fito,kizo kiga motar da ya lamin ya siyo,haddadiya,yanzu yaje ya daukota,kinga


yadda tayi kyau kuwa?" Taci gaba da bata labari,ba tare data lura da yadda idanunta
suka sauya ba

"Ki taso ki gani inji inna"


"Bazan iya tashi ba mufida" cak ta tsaya tana kallonta sosai,ta matsa kusa da ita

"Jikinki hucin zazzabi yakeyi yaa iman,dama baki da lafiya?,sannu......bari.naje na


gayawa innar" mufidan ta fada fuskarta cike fal da damuwa,sai ta juya da hanzari ta
fice daga dakin.

A 'yar qaramar farfajiyar gidan motar ke fake,inna sadiqu da kuma lamin


din kansa suna tsaye jikin motar,sadiqu na qoqarin budewa ya shiga ya
kunnata,saboda yace yanason yaji ya kafiyar engine dinta yake kamar yadda aka
tabbatarwa da lamin din,motace da bata cika girma ba,amma sai azabar kyau da daukar
ido,ta tsaru sosai,duk wanda ya kalleta sai ta bashi sha'awa.

"Inna....inna" mufida ta fara kiranta kafin qaraso,dukka sai suka waiwayo

"Inna wallahi bata da lafiya,bakiji zafi a jikinta ba" sake murfin motar lamin yayi
ya maida hankalinsa ga mufida dake bayani,sadiqu kuwa tuni ya shige cikin motar
yana qoqarin kunnata.

"Dama bata da lafiya amma ta shige daka ta kwanta,a gidan nan dama ita da aminu ke
wannan shashancin banzan......,kice mata ta fito taci abinci ta samu magani tasha"
amsawa mufida tayi ta koma ciki,babu jimawa ta dawo

"Inna ta kasa tasowa fa" yarinyar ta fada fuskarta cike fal da damuwa

"Ko zaki duba ki gani inna,ciwo baya yiwa iman ta dadi tun ba yau ba" lamin ya
fada,fuskarsa na nuna alamun kulawa

"Zan iya dagata ne,idan ka bibiya langwai ne fa kawai irin nata" ya sani sarai kara
kawai inna keyi,don haka saiya qwanqwasa baqin glass din motar,sadiqu ya sauke.
Yana qoqarin gaya masa engine me kyaune sosai ya rigashi yana cewa

"Ka shiga ciki ka duba iman mana"

"Me ya sameta kuma?" Ya tambaya yana dan yamutsa fuska

"Kamar zazzabine haka mufida tace"


"Master qyaleta,tasowarma ba zatayi ba sai an dubota?,ita har yanzu kallon yarinya
takewa kanta" qas yayi da muryarsa yadda inna baza ji ba

"Ni kakeso naje na fiddota?,me hakane sadiqu?" Fuskarsa ya kalla saiya sheqe da
dariya,ya kunce seat belt din daya daura ya fara qoqarin fitowa yana cewa

"Inason wannan mood din naka,idan ka zama serious ko?,u are looking wani
boss....banda ni dinma nine tsoro zaka dinga bani kenan ko?" Murmusawa yayi kawai
da salon murmushinsa mara zurfi,ya ciro kansa yana amsa mishi

"Kai dinne wani lokaci kamar na makeka,bakasan me ya dace ba kwata kwata?" Shidai
ciki yayi yana cewa

"Sai kayita yi kuma,da wasu shanyayyun idanunka a wajen" murmushi ya bishi


dashi,hakan daya fada sai ya tuna masa da quruciyarsu,sanda yake tsokanar iman dame
idanun mage,idan shi din ya shigar mata kuma,shima ya karbi rabonsa dame shanyayyun
idanuwa.

Minti kusan goma ya bayar da rata saboda ya basu daman yin duk abinda
zasuyin,sai ya fara takawa zuwa cikin parlour din,jikinsa sanye da baqar jallabiyya
me sulbi,ya boye hannayensa cikin aljihunta.

Saman daya daga cikin kujerun parlour din take zaune,ta dafe kanta da
tafin hannunta daya,wandata dogare hannun nata da gwiwar hannunta a hannun kujerar
da take kai,dan kwalinta me sulbi daya janye baya saboda sulbinsa da santsin gashin
kanta ya bayyana gaban gashinta sosai.

Yana shiga inna na fitowa daga kitchen

"Zan kintsa dakin malam,idan ruwan yayi dumi ki gwadawa mufida ta sauke miki,ki
samu kisha kiyi wanka ko zakiji qwarin jikinki,amma da wayonki kina zaune da
ciwo,ko kamar mufida yanzu ba zata zauna ba" ta juya ta fice tana qananun mita.

Tabbas taji shigowarsa da tsaiwarsa a wajen,koda bataji ba qamshinsa data


riga ta haddaceshi ya riga ya gama gaya mata wanzuwarsa a wajen,amma tana sane taqi
waiwayowa,bataso ta juyo ta kalli idanun nan masa masu wani irin qarfi da kuma
tasiri a tattare da ita,batason ta juya su hada idanu har yaga raunin da ya
mamayeta.

Tana jinsa sanda ya tako zuwa side din da take,sai ta zabi sauke qwayoyin
idaunta zuwa qasa,har zuwa sanda ya samu mazauni dab da qofarsu ta kitchen,ya zauna
hannun kujera

"Ina kwana" ta gaidashi da dasashshiyar muryarta

"Lafiya ya jikin?"
"Da sauqi"
"Ma sha Allah" ya amsa yana janye idanunsa daga kanta bayan ya mata duba guda
daya,koda batace komai ba...ko bai kalleta sosai ba ya san jiya zuwa yau din da
gaske taji jiki,cikin gidam yafi kowa iya karantar ciwonta.

Waiwayawa yayi inda mufida ke zaune yace ta duba ruwan yayi zafi,ba jimawa
ta dawo ta amsa masa,sai ya miqe da kansa ya shiga kitchen din.

Farin ruwa inna ta dora,ya laluba da kansa ya nemo kayan qamshi ya watsa a
ciki,ya bari ya tafasa sannan ya hada tea din ya bawa mufida takai mata,shi kuma ya
dora wani ruwan ya tafasa farin ruwa yadda ya saba,ya juyeshi a mug,ya fito dashi a
hannunsa yana jiran ya huce zuwa matakin dumi yasha yadda ya saba.

Idanunta a lumshe take kurban tea din,zafinsa na ratsawa sassan


cikinta,kamar wadda ke shan magani haka take jinsa,batason yiwa inna musu ne
kawai,ya qarasa ya rage fankar parlor din,dai dai sanda wayarsa ta fara fitar da
wani daddan busar sarewa.

Hannunsa ya sanya a aljihun gaban rigarsa ya zaro wayar

"Morning.....how was your night?" Abunda ya fadi kenan,sai yayi shuru yana saurare.
Ci gaba tayi da riqon cup din,ta kasa ci gaba da shan tea din,cikin rashin sa'a ta
saci kallonsa,murmushi yake fitarwa saman fuskarsa,koda batasan wanda ya kirashi ba
tayi hasashen hakan,saita sauke kanta,ciwon kan nata yana sake qaruwa

"Ba wani labari.....gaskiya zaiyi wuya,autarmu ce babu lafiya" batasan me akace


masa ba taji dai yace

"Ok....bye" ya katse wayar ya saka a aljihu,shuru ya kuma ratsa wajen,ya maida


hankalinsa ga ruwansa hankali kwance yan auna zafinsa,jin bai huce ba har
yanzu,saiya fara yin hanyar barin parlor din

"Kiyi qoqari ki shirya muje kiga likita,ba'a zama da ciwo haka nan,Allah ya
sawwaqe" bin bayansa tayi da kallo ba tare data shirya ba,hawaye na tara kansu zasu
biyo kuncinta,yaushe ta fara wannan dakon?,yaushe kuma zata saukeshi?,wanne irin
qoshin wahala ne ya sameta haka?,sai tayi hanzarin dire cup din,ta kuma miqe da
hanzari zuwa dakinta duk da yadda kanta yake sara mata,don batason tun a nan wajen
hawayen su fidda kansu.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 45

Duk yadda taso kaucewa tafiya asibin tare dashi bata yiwu ba,saboda bata da
wata hujja da zata bayar na aiwatar da hakan,tafuyarsun tare tasan babu abinda zata
haifar mata illa fama mata wani tabo da miki dake tsaka da ciwo da kuɗa,yake kuma
jan ruwa mai zugi cikin tsokokin zuciyarta,haka nan ta shiga tayi wanka,ta shirya
kanta cikin doguwa riga saqar k'asar turkey,wadda take a bude sosai me hannun
roba,two colors brown da baqa,tayi mata kyau sosai,duk da yadda fuskarta ke cikin
yanayi,a haka idan ka kalla zaka zaci straight skart ce daga qasa sama kuma ta dora
baqar half gown,da mayafin rigar ta yane kanta ba tare data tsaya rolling ba,ta
saka wani black plate half cover shoe,wayarta kawai ta fito.

A parlor ta yiwa inna sallama ta fice,tun daga qofar falon ta hangi


mufida,ta shirya tsaf abunta,anata murna zaa fita da ita.

Ta maida idanunta kansa,duk da bayansa kawai take iya hangowa amma sai
daya haifar mata da faduwar gaba,shaddace a jikinsa me tsada ko a idanu,amma an
mata dinki yarbawa,iya gwiwa mai gajeran hannu da manyan aljihu hagu da dama,sai
dogon wando,shima half cover ya saka irin na maza mai asalin kyau da tsadan,daga
nesa kadai kana iya gane tsaftarshi qwarai bare ka matso kusa dashi kayi arangama
da sassanyan qamshinsa,ganin yana qoqarin juyowa sai ta dauke kanta zuwa wani
sashen daban....kafin ta qaraso har ya bude qofofin motar,da kansa ya budewa mufida
front seat yana tsokanarta,tana murna kuwa ta shige,ya maida ya rufe ya zagaya
nashi seat din ya shiga,daidai sanda iman din itama ta shiga baya.

Bismillah yayi ya tada motar,yayi reverse sannan ya daidaitata cikin


layin suka dauki hanya.

Hirarsu suke shida mufida abinsu,kamar ma babu wani cikin motar sai
su,kanta yana jingine da murfin motar,idanuwanta a lumshe,duk wata kalma ko harafi
da zai futa daga bakinsa tana saurare,duk wata magana da zaiyi mai ma'ana ce,wadda
ke nuna zallar hankali tare da nutsuwar wanda furucin ke fita daga bakinsa,da alama
ita kanta yarinyar tana ji dashi sosai,tana kuma jin dadin hirar tasu,cikin
excitement take bashi amsa,duk da ba cikin lafiyarta take ba,amma jirar tasu saita
dinga burgeta.

"Akwai asibitin da kike zuwa inji inna,meye address din?" Ya fada yana
karkata akalar motar tashi zuwa babban titi,ta cira kai a hankali,tana mamakin
yadda ya iya tuqi haka cikin nutsuwa da qwarewa,ta dade da saninsa,shi ba mutum
bane me karban aron abun hannun abokai,tun a wancan lokacin akwai abokansu da yawa
dake da mota,babu yadda basuyi dashi yazo ya koya ba ko ya dinga aran tasu amma
yace sam,zaman wajen dinkinsa yafi masa wannan yawace yawacen.

Hakan kawai taji batason kaishi asibitin,amma tunda ya riga da yasan nan
din take zuwa ba yadda zatayi,a hankalibta fada masa sunan asibitin,tayi zaton zai
tambayi hanya sai taga yaci gaba da hirarshi,tafi tafi sai gasu a asibitin.

Cikin nutsuwa yayi parking,ya kashe motar yana fadin


"Alhamdilillah" ya zare belt dinsa ya fita ya budewa mufida qofa.

Tabbas son yara cikin jininsa yake,had yanzu kuma bai barshi ba,daga
yadda yakewa mufidan zaka gane hakan,ta tabbatar matsayinta mufidan ke shirin
hawa,gurbinta take nema mayewa,ta kalli yadda yake riqe da hannun yarinyar,sai taji
wani abu ya taba ranta,dab da zasu qarasa entrance na asibitin ta danyi kiranta,bai
juyo ba amma ya zame hannunsa daga nata,sai yarinyar ta tsaya shi kuma yayi gaba,ta
qarasa ta kama hannunta,sannu tayi mata,ta dauka ko tafiyar ce bata yi mata dadi
shi yasa ta kirata ta tsayata.

Tafiyar tasu ba daya bace koda lafiya take bare yanzu da bata jin
dadi,don haka kafin ta qarasa har an fidda file dinsu yana biyan consultation fee

"Hajiya iman....wani aure kika qara ne?,gaskiya kina da sa'a,duk mazanki babu na
yarwa,harma wannan yafi wancan kyau ma sha Allah,duk da kema ba baya bace,shi yasa
kike samo irinsu" wata nurse halima ta fada,irin matan nan ne masu barkwanci da
kuma shegen surutu,kafin iman din tace wani abu ta sake duban alameen

"Yallabai inafa tayaka murna,ka dace da mace gaskiya" ta gefan ido take satar
kallonshi tana son taga ya yanayinsa yake,saidai bata gane komai ba,hasalima
sabgarshi yake da wayarsa kamar ma bay wajen

"Wata nawa ne cikin?za'a saka jikin record din kadin nayi miki bp da kuma weight
dinta yallabai" sai a sannan ya daga kai ya dubu nurse din,tun asali bayason mace
me yawan surutu shi kam,ko don ba kowanne lokaci ba kuma da kowa magana ta cika
damunsa ba,ya tabbatar da sadiqu ta samu saidai ya matsa ya basu waje

"Sorry madam,ba matata bace,ba awo tazo ba,just tazo ganin likitanta ne"

"Ayyah sorry,kuyi haquri,dr ahmad ne,yana ciki ma,amma akwai mutum kusan shida a
gabanku,idan sun fito sai ku shiga" bai bi ta kanta ba ya fito da kudin ya ajjiye
mata a gabanta,ta dauke ta fara rubuta musi receipt ta saka a file din nasu.

Mabanbantan wurare suka zauna suna ci gaba da hirarsu da mufida,har zuwa


sanda layin yazo kansu.

Shine a gaba suna bayansa,da sallama ya shiga,dr ahmad na rubuce rubuce


kan wani file ya daga kai yana amsawa,har zai maida kansa ya hangi shigowar iman
din,hakan yasa ya ajjiye biron da yake rubutu dashi,murmushi kwance saman fuskarsa
ya miqe tsaye,hakan ya sanya alameen waiwayawa ya dubi iman din.

"Bismillah,ga wajeku zauna"yayi musu izinin zama bayan sunyi musabaha da


ameen,mufida ma ta gaidashi,ya amsa mata cikin sakin fuska.

"Yaya?,jikin ne?" Dr ahmad ya tambayeta cike da kulawa,ya tattara dukka


hankalinsa da nutsuwarsa a kanta,kai ta gyada a hankali saboda jin da take kamar
zai cire

"Subhanallah" ya fada adan rikice


"Jikina ya bani dama,tunda nayita kira jiya babu amsa,haka tex ma......garin yaya
haka ta faru hajiya?" Ya sake tambaya fuskarsa a narke cikin matuqar kulawa,abunda
ya sanyata jin wani iri,ta daga idonta a hankali zata saci kallon alameen dake
tsaye,hannayensa duka zube cikin aljihun rigarsa,tunda suka shigo dama bai zauna
ba,yana jingine da bangon office din,yayi crossing legs dinsa.

Taci sa'a tsimammun idanuwansa suna kanta shima,suka hada idanu,sai ya miqe
ya tsaya sosai bisa qafafunsa yana cire hannayensa daga aljihu ya maidasu qirjinsa
ya harde,cikin wata qasaita yayi magana

"Eheenn....ki bude baki ki masa bayani,ko kuma na baku space,tunda akwai sirri
tsakanin likita sa patient ko?" Ya fada a hankali yana raba bayansa da
bangon,sannan ya fara takawa,murmushi dr ahmad ya saki

"Kawai dai naga alama tana tsoron yayan nan namu,but she can explain ai ko a
gabanka dinne"

"Kada ka damu abokina.....idan kun gama ina waje" yayi maganar yana sake bashi
hannu,sannan ya nufi qofa,mufida ta tashi ta biyo bayansa,sai ya dakata yace da ita

"No,ki xauna ku fito tare"


"To" ta amsa masa tana komawa ta zauna.

Wani abu mai tauri ne ys tsaya mata a wuya,kunnuwanta na jin takun


fitarsa daga office din,wato ko oho?,bai damu da ita ba?,baya kishinta kenan,har
zai iya fita ya barta da dr ahmad din,bayan ta tabbatar da duk wanda yaga reaction
na dr ahmad zai gane cewa akwai wani manufa mai qarfi a zuciyarshi dangane da
ita?.da gaske babu komai a zuciyar ameen a kanta ko kuwa me?,yana son tabbatar mata
ta fita daga kansa?.

A dabarance ta janye idanunta tare sa sauke ajiyar zuciya,ta maida ga dr


ahmad daya taso daga seat dinsa,ya dawo kujerar dake opposite dinta,bayan ya turata
baya kadan,cikin sanyin murya yake mata magana

"Meye damuwar?,can you share it with me?" Yayi tambayar yana kallonta,sanya nata
idanun tayi itama cikin nasa,tana karantar damuwa da yayi qarara da
lamarinta,sabanin alameen din,da bata tsinci kowanne sauyin yanayi dangane dashi
ba,illa dai zallar nuna tausayi,wanda dama ko ba'a kanta kadai ba,shi mutum ne mai
tausayi,musamman ga na qasa dashi

"Banaso ki koma yanayin da kika baro a baya,ina fargaban komawar taki,saboda babu
lallai abun yazo da kyau,kada ki sanyani yin asarar da ban shiryata ba" idanunta ta
dauke daga kansa,tana jan numfashi tare da sauke ajiyar zuciya,ta maida bayanta
jikin kujera ba tare datace komai ba.

Wayar land line dame office din ya janyo,nurse ya kira kamar yadda ta saba
don tayi mata awon BP,ya maida wayar ya ajjiye yana tattara nutsuwarshi a kanta.
Tunda suna doso wajen hankalinta ya dauko ga ameen,hannunsa riqe da wata
leda mai dauke fried plaintain,guda daa kuma yana hannun mufida tana ci,zuna zaune
daga saman motar tashi,da alama labari take bashi kamar yadda ta saba,fuskarsa na
fidda wani qaramin murmushi,yayin da yake dan cilla qafarsa kadan.

Yanayin yadda yayi fresh da kuma yadda motar ta dace dashi dole ya dauki
hankalin kowacce mace,komai isa kyau da kuma taqamarta,don babu abinda baya dashi
wanda zaija hankalin,kwarji na musamman yake dashi,ita kanta tana mamaki wani
lokaci, totally ba lameen din shekarun baya bane wannan,wani rauni taji yana cika
zuciyarta,tana ji a jikinta alamun faduwarta kan samun soyayyarsa da rashin nasara
dake tunkarota.

A hankali ya sauka daga saman motar,ya ajjiye abunda ke hannunsa,fuskarsa


a sake ya miqawa dr ahmad hannu suka sake musabaha

"Kun gama dr"


"Mun gama yayanmu.....Allah yasa na canki dai dai" murmushi kawai yayi masa ba tare
daya amsa ba

"Don Allah ayimin alfarma a kulamin da ita,akwai damuwa cikin ranta dakeson tada
ciwonta" sauke idanunsa yayi akan iman din dake gefe guda,sai ya ciro key din motar
daga aljihunsa yana dauke idanunsa daga kanta,sannan ya dannan ya bude musu motar
yana cewa

"Ku shiga ciki ku jirani". Sai daya tabbatar sun shiga sannan ya maida hankalinsa
ga dr ahmad

"Thank you Dr,amma kuma...wanne damuwa ne haka?"

"I tried to get the information daga gareta amma bata gayamin komai
ba,please....kune kuke da kusanci sosai da ita,kuyi qoqari wajen relieving mata
damuwarta"

"Ok" ya amsa masa a taqaice

"Can i say goodbye to her?" Ya tambayi alameen,sai ya daga kafadunshi yana takawa
zuwa gaba

"Why not?"

"Na gode" ya fada shima yana biyo bayansa.

Tana jinsa ya buda motar ya shiga,saidai bata dago kanta ba,idanunta naga
yatsun hannunta tana murxasu a hankali,sosai qirjinta yake mata zafi,kalmar

"Hajjaju" ta shiga kunnenta saitin window din da take zaune,ta daga kai ta kalli dr
ahmad dake mata murmushi,a hankali kuma ta saci duban alameen,sai taga wayarsa ma
yake qoqarin sakawa a charge

"Allah ya bada lafiya,an hanani address bare nazo nayi dubiya ko?" Murmushi ta
fitar na yaqe,wanda bahaushe yace yafi kuka ciwo

"Shikenan,hope to visit you soon,sai munyi waya.....,yallabai.....godiya nake" ya


fadawa alameen

"Don't mention it" ya amsa masa,sai ya kunna motar abunda yasa dr ahmad ja baya
kenan yana kallonsu har suka fice a asibitin.
Ajiyar zuciya ya sauke yana komawa ciki,har ga Allah yana bala'in son iman
din,tun farkon zuwanta asibitin,a sannan ma bai gane matar aure bace sai daga baya
da matsaloli sukayita kunno kai,yasan wala'alla wahalar data sha a aurenta na baya
yasa ta kasa sake masa,amma yasan a hankali in sha Allah komai zai kawo qarshe,zai
kuma shawo kanta.

Ta tafas batace ba tunda suka shiga motat,hirarsu suke shida mufidan


kamar dai dazu,hawayenta taketa riqewa,bataso su zuba ya gani,ita kadai tasan ciwon
da qirjinta yake mata,wanne irin cin fuska ne ya lamin din yayi mata haka?,ko
yaya?....sam babu wani digo na kishinta ko kuma soyayyarta akan fuska da
ayyukansa?.

Sai daya tsaya a hanya a wani guri ya siya fruits masu yawa,bayan ya
tambayi mufida dame dame sukafi so sannan suka wuce gida,a 'yar harabar gidan dake
dauke motar tasa yayi parking,mufida ta fara ficewa da ledojin,rashin qwarin
jikinta yasa take komai slowly,ta buda murfin motar zata fita taji yace

"Wait" saita dakata din kamar yadda yace,hannunsa ya sanya a hankali ya saita
mudubin gaban motar zuwa saitin fuskarta,ta daga idanunta a hankali tana kallon
wajen,saiga fuskarsa tarwa,tsimammun idanunsa a kanta masu nauyi da kwarjini.

Ita ta fara janye idanun nata kamar kowanne lokaci,kafin daga bisani
muryarsa ta ratso kunnenta

"Wacce damuwa ce a ranki haka?" Yayi tambayar a dake,cikin ginshirar nan tasa,koda
bata kalleshi ba tasan fuskarsa babu alamar wasa,to amma a nata ganin bai kamata
yayi mata wannan tambayar ba,tayi imani cewa yafi kowa sanin amsar tambayarsa,koda
bata buda baki tayi masa bayanin komai ba,hakan da yake mata kamae titsiye ne.

Bata amsa ba,kuma bata da niyyar cewa komai,shi kuma bai fasa kallonta ta
cikin mudubin ba,hakanan ta dunga jin idanunsa na yawo cikin jikinta kota
ina,tsahon wasu mintuna kafin ta sake ji yake

"Alright.....shikenan,abu daya zance miki.....lafiya abace mai daraja,saiki


kula,zaki iya tafiya" daga haka ya soma cire belt din dake jikinsa,ta saka hannunta
a sanyaye ta bude motar ta fito,tana tafiya kamar iska na yawo da ita haka takejin
jikinta,zuciyarta a quntace waje guda,kwanyarta cunkushe,a hankali kamar ba zata
qarasa ba ta cusa jikinta zuwa parlor dinsu.

*FOLLOW ME ON AREWABOOKS DOMIN SAMUN CI GABA,SABBBABIN PAGES GALLA GALLA*

*_KUFAN WUTA_*

*SABABBIN PAGES DA DUMINSU SUN SAUKA*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


👇👇👇👇👇

https://arewabooks.com/chapter?id=62bc3f8a7660dfc79da17d20

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar
haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with
Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*


https://arewabooks.com/chapter?id=62bc3f8a7660dfc79da17d20

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu


https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne
bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu.
Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN
NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna
sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍😍😊🥰😍 😊 _.

*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


👇👇👇👇👇

*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.

*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin
kasuwar ArewaBooks.

*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.

A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba
"Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku
zaishiga account dinku kaitsaye (instant).

--------

Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:

*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*

Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din,


amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number
ArewaBooks.

_Account No_ - *1220077999*


_Account Name_ - *Arewa Books Publishers*
_Bank_ - *Zenith Bank*

Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:

Amount Paid: - Nawa aka tura?

Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa

Transferred time: - lokacin da aka turo

Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi

Deposit date: - ranar da aka turo

Sai ayi SUBMIT.

*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank
Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna
amsar:

MTN,
9Mobile
Glo
Airtel

Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin
akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.

*WANNAN SHINE BAYANAN*[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 46

Sanarwa da inna kawai tayi ta dawo ta wuce daki,ta zube saman katifa tana
maida numfashi,kwanyarta na tariyo mata duk abunda suka faru,tana shakka zuciyarta
kuma nason tabbatar mata,ta juya ta gyara kwanciyarta tare da runtse idanunta,tana
son ta mance da komai ko zata samu sauqin azabar da takeji tun daga gangar jikinta
zuwa zuciyarta,saidai bayan kowacce daqiqa tunanin ameen ne a rai da
zuciyarta,azabar da takeji kuma tana sake qaruwa,bata samu sassauci ba.

Fruit da magungunan da mufida ta ajjiye mata tace ya ameen ne yace ta


tabbatar tasha ta bisu da kallo,me yasa yake bata fake caring?,me yasa yaketa
pretending?,bayan tasan ba haka bane?,a yanzu ba wadan nan abebadan take buqata
ba,koda taci ko tasha tasan babu wani magani da zasu iya yi mata,zuciyarta shi
takeso,shi take da buqata,shine magani kuma abincinta,amma me yasa yaketa avoiding
dinta?,yanata nuna bai gane komai?,yanata nuna a yanzun yaren dake kan fuskarta
bashi yake ganewa ba?, pillow ta jawo ta cusa kanta a qasa gami da qanqameshi tana
fatan Allah ya kawo mata barci ko zata samu sassauci.

Addu'arta kuwa taci,dogon barcin daya dauketa har gefin magariba sannan
ta farka,ta ambaci sunan Allah da sauri ta shiga bandaki,ta daura alwala ta dawo ta
fara bada bashin sallolin dake kanta,bata tashi ba sai datayi sallar magariba.

Tadan samu relief kadan,ta jawo ledar magungunanta ta dubasu,saita fara


shirin miqewa,dai dai lokacin mufida ta shigo
"Yauwa,ashe kin tashi ma,bari na gayawa innan"

"Tsaya mu fita tare" ta fada tans miqewa tare da tambayarta

"Ba kowane a gidan?" Dan dubanta tayi cikin rashin gane ma'anar tambayar tata,amma
duk da haka tayi qoqarin amsa mata

"Yaa sadiqu ya tafi zance..." Gabanta ya doka,tana fargabar jin amsa ta gaba

"Ya alameen kuma tunda suka fita unguwa da malam basu dawo ba" saita jinjina
kai,tayi gaba mufida ta biyo bayanta.

A parlor ta cimma inna,tana zaune tana gyara saitin stations na radio


dinta,akwai tv,amma sam bata wani damu inna ba,idan sun kunna takan kalla,amma idan
basu kunna ba saita wuni a kashe ba tare data kunna ba.

Daga kai tayi tana yiwa iman din sannu,ta amsa tana zama saman kujera

"Kinsha magungunan naki?"

"Yanzu dai zansha" ta amsa mata,sannan tace mufida ta samo mata abincin dan kadan a
kitchen.

Tana tsaka daci taji sallamar malam,already mufida ta gaya mata tare suke
dashi,hakan na nuna sun dawo kenan,sai ta ajjiye farantin gefe saboda yadda taji
abincin ya tsaya mata.

Ballar maganin tayi ta riqe cikin tafin hannunta,ruwan na riqe a cup amma
tana wassafa yadda zata tanqwara kanta tasha maganin,saboda tun asali bata qaunar
magani,sai an sha fama da ita takesha.

Shigowar malam ta sakata ajjiye cup din,taci gaba da riqon maganin a


hannunta tana masa sannu da zuwa,sai idanunta yakai kan wanda yake bayansa,ameen ne
tsaye sarqafe da hannayensa a qirji,hada ido sukayi,saiya dauke kansa kanshi tsaye
bayan ya kalli hannun ta,koda ba'a gaya masa ba yasan yadda zatasha maganin take
taraddadi,ya juya a nutse ya fice daga parlor din,yana amsa wayarsa da aka kirashi
sanda ya juya din.

Miqewa tayi itama ta koma daki ta barwa inna da malam parlor din,duk da
cewa malam din yana da tashi rumfar,amma qila a nan yayi sha'awar zama.

Ko data koma ciki ta taras da miscal din dr ahmad masu yawa,daga bisani
kuma taga tex dinshi,duka yana mata sannu da jiki ne,tare da bata qwarin gwiwar
kauda damuwa daga ranta,aje wayar kawai tai bayan ta gama karantawa,indai sai
damuwa ta fita daga ranta,to tabbas bata da guarantee din ranar warkewa.

Washegari ma haka nan ta wuni,jikin da sauqi,amma babu wani kuzari sam


tattare da ita,a dakinta tayi kwanciyarta,bata yarda ko sau daya ta fito sun hadu
dashi ba,saidai duka taji muryarsa sanda zai fita,ta lumshe ido wani abu na tsarga
mata sanda taji ya ambaci sunanta yana tambayarta,har zuwa amsar da mufida ta
bashi,hakanan sanda ya dawo ma taji shigowarsa,hatta da zaman cin abinci da sukayi
a parlor shi da sadiq,da fitarsa daga parlor din sanda wayarsa ta dauki ruri,sai
zuciyarta ta cilla ta bishi bayan fitar tasa,tana ji a jikinsa da wata zaiyi waya.

Kasa nutsuwa zuciyarta tayi,daga qarshe ta dauko headphone dinta tayi


connecting da wayarta,ta kunna suratul baqra cikin qira'ar sheik khalilul kusari,ta
rage volume dai dai yadda bazai dameta ba,wannan ya taimaka matuqa wajen janye
hankalinta,har ta samu barci ya fara fusgarta.
*****A kwana na biyu ne taji qwarin jikinta,ranar ta wuni a kwance,ta samu
barci kuwa sosai yadda ya kamata,hakan ya sanya koda ta tashi fresh ta jita,ta fito
parlor tana laluben inna,sai a sannan mufida ta gaya mata ta tafi karben lefen 'yar
gidan kawu muktar,ta jinjina kai tana mamakin baccin da tasha,saita koma daki ta
cire kayanta ta fada wanka.

Tsaye tayi gaban mudubi daure da towel tana kallon fuskarta,ta fada tayi
fayau da ita,sai haske data qara,blue eyes dinta sunyi tas dasu,manta ta jawo ta
fara qoqarin shafawa mufida ta shigo

"Ya iman kinyi baquwa"


"Baquwa kuma?" Ta tambaya cikin mamaki

"Eh" shuru ta danyi sannan tace

"Baki santa ba?" Kai ta girgiza

"Ban santa ba,amma dai 'yar gayu kamarki" murmushi iman din tayi,har fararen
haqoranta suna fitowa

"Ke kam akwai ki da son gayu mufida,jeki kice mata ina zuwa" ta amsa da to ta juya
ta fita tana dariya.

A nutse ta shirya kanta cikin wani Cotton material,ash colour ne mai zanen
manyan flowers,dinkin riga da skert ne me kyau daya zauna a jikinta,comb tasa tana
taje kanta mai laushi da tsaho,ta duba ma'ajiyar ribbons dinta ta saka daya ta kame
gashin nata dashi,ta kalli gashin nata ta cikin madubin,sai takejin ya mata datti
tana buqatar zuwa a wanke mata shi,duk da ba wani datti bane me yawa,jikinta tabi
da turarenta mai taushin qamshi ta feshe,saita dauki wayarta da zummar idan ta gama
da baquwar ta kunna data ta duba group na ajinsu taga me ake ciki,don kwana biyu
bata hau ba,daxun kuma tana tsaka da bacci wata abokiyar karatunta da suke mutunci
sosai ta kirata,ta bata haquri kan zata kira idan ta tashi.

Sanda ta qarasa parlor din idanunta na kan wayar,sai data shiga sannan ta
cira kanta tana yin sallama.

Sanye cikin wani lace orange da aka yiwa dinki bunu na zamani da aka
wadata da stones masu walwali,ta yane kanta da mayafi medium,wanda tadan jashi
baya,daurin kanta daya fara daga gaban goshinta ya zauna das,ya kuma sake qawata
kwalliyarta,matashiyar budurwa ce wankan tarwada,wadda a qalla shekarunta baxasu
haura ashirin da biyu ba,tana da doguwar fuska da siraran labba,sai gashin gira
wanda ya zarta gashin idanunta cika,tana da kyau irin wanda ake kira da matsakaicin
kyau,a wasu guraren kuma direct za'a kirata da sunan kyakkyawa,shigarta kadai zata
gaya maka a waye take,hannunta riqe yake da wayarta tana latse latse,gefanta kuma
wata matashiyarce,itama cikin doguwar rigar atamfa,saidai ita din batakai wannan
kyau ba,kamar yadda a ido kawai zakasan bata qarasa shekarun wancar din ba.

Idanun iman qur bisa fuskokinsu take takowa,saboda duk cikinsu babu
fuskar wadda ta sani

"Sannun ku" ta fada da tattausar muryarta,zuciyarta na raya mata batan kai


sukayi,ba gidan suke nema ba

"Yauwa sannu" matashiyar dake sanye da lace ta amsa murya qasa qasa,idanunta fes
bisa fuskar iman wadda tuni ta qaraso wajen tana dauke idanunta daga kansu karo na
barkatai da batasan adadin ba..

Cikin zuciyarta iman take mamakin kallon da baquwar ke binga dashi,mutum ce ita
data tsani kallon qurilla,balle ga baqo....baqonma irin wannan da batasan daga ina
take ba,kuma me take kallon oho.

A nutse ta samu one sitter ta zauna ta dauke pillow din dake kai ta maida
saman cinyarta

"Sannunku ko?" Iman din ta sake maimaitawa,sai matashiyar dake gefe ta amsa wannan
karon

"Ina gajiya ya gida?" Iman ta maida musu gaisuwarsu,sannan ta miqe,har yanzu dai
tana mamakin su waye,daga inda kuma suke din.

A nutse ta wuce zuwa kitchen don ta gabatar musu da ruwa,kamar yadda suka
saba al'adar gidan,koda basusan baqo ba,kallo suka bita dashi,kafin daga bisani su
janye idanunsu kusan a tare

"Wai itace autar?" Matashiyar dake gefe ta tambayeta

"Nima dai ina doubting......banga suna kama ba,amma......bari na kirashi kawai"


saita dauki wayarta data ajjiye a gefe,ta fara zuba numbers dinsa cikin wayar,wanda
ta jima da haddace digits din.

Tabe baki iman tayi bayan ta gama guntun tunaninta akan su waye cikin
kitchen,koma su waye kansu suke batawa lokaci idan suka gane ba gidan da suke nema
sukazo ba,ta qarasa ta samu babban tray ta zuba robobin zobo mai sanyi da sukeyi
suna zubawa a fridge saboda sha,ta hado musu da pure water shima mai sanyi sosai,ta
dora cups ta nufo falon.

Tun kan ta qaraso ta fahimci waya take,saidai ba zaka iya jin me take fada
ba,har ta qaraso din kuwa bata iyajin komai ba,saboda yadda take maganar kamar
wadda ke rada

"Eh......dama mamaki na shirya baka,idan baka yarda ba ka qaraso muna cikin gidan
ai" ta fada da wata iriyar murya can qas.

Qarasa dire musu plate din kawai tayi ta koma seat din data taso ta sake
zama,ta fuskanci dai gidan nasu sukazo,to amma wajen wa?,for now dai ai ya kamata
su fadi wa suke nema,to amma koda waye taji tana waya yana da alaqa da gidan nasu.

Sosai qirjinta ya harba sanda zuciyarta ta raya mata idan ameen ne


fa?,siriryar iska mai zafi ta futar daga hunhunta wai ko zaga samu relief,iya
wannan tunanin ya sanyata jade girar sama data qasa,ta tsuke fuskarta tas,tsohon
tsimammen miskilancinta ya motsa,ta maida qafarta daya kan daya,sannan taja wayarta
ta bude,ta fara bin charts din group din ajinsu,gefe daya zuciyarta na qwarara mata
gwiwar bata da alaqa da ameen,ba yadda za'ayi tana surukar gidan ta iya tunkarar
gidansu.

Parlor din ya dauki shuru,iman din ta maida hankalinta ga chart


dinta,sai qarar tv dake tashi kadan kadan,sam taji baquwar batayi mata ba,ta yaya
zakizo gidan mutane ki samu guri ki zauna,ki kasa fadin wacece ke?,jin kai ne ko
meye?.

A karo na kusa hudu daya abokiyar tafiyan tata ta dubeta,tadan tabata


kadan,kafadunta ta dage kana ta daga gira sama ta sauke,ta aje cup din ruwan data
sha

"Sunana samha" a nutse iman ta daga kanta ta kalleta

"Wannan kuma qanwata ce subai'a,muna neman iman ne,qanwar alameen" a nutsen ta amsa
mata,ambatar sunan al'ameen din da tayi sai da gaban iman din yayi wata mummunar
faduwa.

"Gani" kallonta samhan tayi sosai sannan ta dan saki murmushi

"Ayyah,ban san fuskarki ba,shi yasa ban ganeki ba,ya jikin naki?"

"Alhamdulillah"
"To Allah ya qara sauqi"

"Ameen" ta amsa mata a taqaice ta maida kanfa ga wayarta,har yanzu qirjinta bai
daina bugawa ba,wani irin fargaba ce ta dinga saukar mata tana kashe mata gabban
jikinta,duk yadda samhan taso ta dinga janta da hira amma hakan ya faskara,banda ma
bata da tabbacin wacece ita?,kuma wajen wa tazo.....da babu abinda zata zauna yi a
parlor din.

Ganin bata samu sakewa da iman din ba yadda ya kamata saita koma hirarta da
mufida,da yake mai hira ce mufidan saita sake mata suka taba hirara.

*_Assalamu alaikum,fatan kowa yana lafiya,don Allah ina neman alfarmarku,wani


muhimmin abu ya tasomin cikin satin nan har zuwa satin gaba,zaku dinga ganin
1page,idan kuma na samu sarari zaku dinga ganin guda biyu har zuwa sanda uzurin
nawa zai kammala,ina fatan za'ayimin afuwa,na gode_*👏🏾👏🏾👏🏾
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 47

Zaman gaba daya ha gama gundurarta cikin parlor din,sam babu wani armashi ko
ma'ana,ta gama yanke iya mintocin da idan suka cika zata tashi daga zaman da sam
bashi da wata fa'ida a idanunta.

Sallamarsa ce ta ratsa tsakar gidan,cikin husky voice dinsa,wadda duk


sanda zata jita sai ta haifar da wani abu mai nauyi dangane dashi a gangar jiki da
zuciyarta,don ko a yanzu ma lumshe idanunta tayi tana jin yadda ko wane sashe na
jikinta ke amsawa,bude idanunta kuwa yayi dai dai da zare rufaffun takalmansa da
yayi ya sako kai zuwa parlor din.

Tsaye yayi daga bakin qofa,hannyensa boye cikin aljihun wandon suit
dinsa,idanunsa saman fuskar samha,yayin da fuskar samhan ta wadata da murmushi tana
dan jan mayafinta tana rufe rabin fuskarta

"Suby'a har da ke?" Ya fada yana sakin hannayensa tare da takowa a nutse zuwa cikin
parlor din,cikin murmushi suby'a din tace

"Ya zanyi mata yaya,indai batazo dubiyar nan ba babu zaman lafiya,tunda taji auta
babu lafiya ta hanani sakat"

"Da kyau" ya amsa yana qoqarin maida idanunshi kan iman,wadda ta miqe zumbur kamar
wadda aka tsikara,sannan ta wuce kanta tsaye zuwa kitchen ba tare data waiwayo ko
kuma ta saurari kowa ba.

Da idanu ya rakata kafin ya janye dubansa daga kanta cikin mamakin


reaction dinta,sauke kallonsa yayi ga samha wadda itama ta bishi da kallo,suka hada
idanu

"Are you okay?" Ta tambayeshi yanayin fuskarta yana dan canzawa akan yadda ta
kalleshi lokacin da ya shigo parlor din,ta hanyar dage mata girarsa ya amsa mata
yana sake qarasowa don samun kujerar da zai zauna akai,mufida tayi masa sannu da
zuwa,ya amsa yanabin ruwa da drinks din da aka ajjiye musu da kallo.

Bata tsaya ba sai data dangane da jikin cupboard din kitchen din,ta dafe
hannuwanta dasu tana qoqarin saidaita gudun zuciyarta saboda hakin da yakeson
sarqafeta,koda baice komai ba ta gama karantar komai din,samha budurwar ameen ce,ta
kuma zo dubata saboda taji bata da lafiya,hakan yana nufin batasan tarihin abinda
yake tsakaninsu ba,wannan shike tabbatar mata da gaske ya ameen ga wanke dukka wata
tsohuwar alaqa da dangantaka data taba hadasu da gasken gaske kamar yadda ya taba
furta mata.

Kokari take ta fitar da hawaye daga idanunta ko hakan zaisa ta samu


sassaucin wani abu mai tauri daya tsaya mata a wuya,ta sunkuyar da kanta qasa a
hankali sanda kukan ke zuwa mata,ta kuma saka hanunta guda daya ta toshe bakinta
dashi don kada ta fallasa kanta,wasu hawaye masu dumi suka fada kai kawo saman
fuskarta,sai taji tsaiwar na neman gagararta,ta sulale ta tsugunna sosai tana cusa
kanta a tsakanin cinyoyinta,tabbas ta rasa ya ameen,ta rasashi rashi na har
abada,babu abinda idanunta ke hango mata a yanzun sai fuskarsa tare data samha,daga
nan inda take tana iya jin muryan samhan,duk da bata iya fahimtar me suke fada,sai
tasa tafin hannuwanta ta danne kunnuwanta dasu tana runtse idanunta.

Kuka take wanda ke tafe da qunci nadama da kuma dana sani,bata taba
tunani a rayuwarta zuciyarta na qaunar ya ameen ba har haka,bata taba kawowa akwai
lokacin da nadama da tashin hankali kan barin ameen zasu risketa ba har irin
haka,dama da gaske ne da ake cewa dama sau daya take zuwarma dan adam a
rayuwa,itakam da alama ta rasa tata damar,me yasa ya ameen bazai kalli qwayoyin
idanuwanta ya karanci meke cikin zuciya da ruhinta ba kamar yadda ya saba mata?,me
yasa zai barta ita daya sonshi yana wajigata ta duk inda yaga dama?,idan ma horo ne
ya zuwa yanzu zuciyarta ta gama horuwa,koda yadda zuciyarta ta cika fa tumbatsa da
qaunarsa kawai ya barta tabbas ta karbi dukkan sakamakon daya kamata.

Batasan sanda innata shigo gidan ba,saidai kawai ta tsinci muryarta tana
doso qofar kitchen din tana kiran sunanta da alama nemanta take.

Da hanzari ta miqe,ta kuma juyawa qofa baya tana fuskantar sink na


kitchen din,ta kunna famfo ta tara hannayenta ta fara wanke fuskarta,dai dai sanda
innar ta qaraso tana fadin

"Me kike haka a kitchen ne tun kusan rabin awa?" Rasa amsar da zata bawa inna
tayi,batason ta buda baki da zummar magana innar ta gano tayi kuka,amma dole ta
amsa matan indai baso take ta zagayo taha fuskarta bane

"Kokarin dora abinci nake inna"

"Bansan ma me kuka zauna yi ba har yanzu ace ba'a dora abincin dare ba,ki fara
samun wani abun me sauqi ki dorawa baqin nan,nace sai sun dakata mun gaisa sosai
tunda yanzun na shigo ni"

"To" din da zatace ta maqale mata,ta kasa kunne taji takun fitar innar amma bataji
ba,a maimakon hakan sai taji innar tana takowa zuwa cikin kitchen din,abunda ya
kidimata kenan ta fara kame kame,sam bata qaunar wani ya fahimci halin da take ciki
akan ameen din,matsala ce da ita ya jawowa kanta da hannunta ita kadai,ita kadai
din kuma ya cancanci tayi kuka da ita,a sanda dukka masoyanta suke jiye nata zuwan
wannan rana....a sannan din ita kuma nata idanun suka rufe,bata ji bata gani,bata
hango aibu dacewa ko kuma rashin dacewa.

A gabanta inna ta tsaya,ta kasa daga idanunta balle ta kalli innar tamkar
wata mara gaskiya,taji lokacin da innar ta motsa bakinta da niyyar yin magana,sai
kuma taji ta maida ta rufe,ta kuma ja da baya taba cewa

"Karki dauko girki mai wahala don kada su qosa da jira" daga haka ta juya a hankali
ta fice daga kitchen din.
Lafiyayyar taliya tayi data wadata da kayan lambu,ta shirya komai a
tsare,sannan ta kira mufida daga nan inda take din tazo ta dauka,ba tare data fito
parlor din ba ta zarce da dora abincin dare na gidan gaba daya.

"Well-done" ya furta a nutse sanda mufida ta ajjiye tray din abincin a


gabansa sanda yake zaune saman carpet din parlor din yana amsa wayar
bashari,shugaban babban shagonsa da a yanzu yaketa qoqarin ganin ya maidashi
company,parlor din babu kowa yanzun,don inna ta basu waje tunda taji iman ta gama
abincin.

Da hannu yayima suby'a alama kan tayi serving nasu,tayi yadda yace
din,saidai samha ta maqale kafada alamun ba zata ci ba,miqewa yayi tsaye bayan ya
cire wayar daga kunnensa

"Ku kammala kafin na fito,kiyi tasting girkin ki fadamin abinda kika ji" daga haka
ya maida wayar kunnensa sannan ya taka a hankali ya fice daga falon.

Sai daya bacewa ganinta ta janye idanunta daga kanshi tana sauke ajiyar
zuciya,suby'a ta zungureta

"Wai meye hakan?" Murmushi samha ta saki

"Farkon ganina dashi.....ban taba tunaun wata rana zai soni....ko xan sameshi ba
suby'a,matan dake sonshi sunyi yawan da har nake ganin ni bazan samu ba" baki
suby'a ta riqe,tana mamakin samhan,miskilace ta haqiqa,wadda ba kasafai namiji ke
burgeta ba,tana da kyan da yasa ba kowanne namiji take tsayawa ta kula ba,bare har
ta buda baki tace tana sonshi,alameen na cikin namiji na farko data taba furtawa da
bakinta tana sonshi,har kuma take gaza boye son,bata wasa da sanya da dukkan wani
abu daya shafeshi.

"Amma suby'a,anya ko yarinyar nan jinin man ce?"

"Kamar yaya?" Suby'a ta tambayeta tana kallonta cikin rashin fahimta

"Basa kama kwata kwata,saidai kowanne cikinsu da color din nashi kyan,na biyu kuma
jin kanta yayi yawa...... infact ma,sai nakeji a raina bata yimin ba,innarsu ta
fita kirki" murmushi suby'a tayi

"Kinga,kice dai kawai bata yi mikin ba,amma idan batun jin kaine ina kika baro man
din naki?,ko kin manta saboda yanzun kin sameshi?"

"Manta kawai,bani abincin na dandana naji abunda yakeso naji din" ta fadi tana
kallon taliyar yadda ta shiryu a idanuma,tun ba'a kaita baki ba.

Tabbas taji different aroma and taste,tasan kuma duk hannun da yayi abincin
yasan abunda ake kira da girki,saidai batasan me yasa zuciyarta taqi gamsuwa da
harshenta ya yabi girkin ba,daga qarshe ta ajjiye spoon din,ta koma da baya ta
zauna tana turama ameen saqo.

Sai daya gama wayarshi tsaf sannan ya tura qofar parlor din nasu,babban
parlor din daya wadatu da kyau da kuma tsafta,ko ina a shirye yake da kayan alatu
masu kyau da daukan hankali,kusan komai na cikinsa black and white ne,ya sauke
wayar yana fadin

"Alhamdulillah" har sau uku qasa qasa amma a fili,shi kansa yasan nasibi da budi da
ubangiji yaketa yi masa abune da ba kowanne bawa bane ya samu hakan,cikin shekaru
kadan amma ya fara riqe dukiyar dako a mafarki bai taba kawowa kansa zai mallaketa
ba,yaci gaba da takawa a hankali zuwa daya daga cikin qofofin bedrooms guda biyu
dake parlor din,har ya qarasa tasa,ya tura ya shiga.
Dakin kwanane wanda zai burge duk wanda ya ganshi,komai dake cikinsa
fari ne,da alama wannan shine zabin mamallakin dakin,komai tsaf a kammale kamae
parlor din,qamshi ne kawai ke fita daga cikinsa da kalolin qamshin air freshener da
kuma turarukan da yake amfani dasu wanda suka fara kama bedroom din nashi.

Saman mirror dinsa dake cike da kayan shafa na maza ya isa ya dora
wayarsa akai,ya balle belt din jikinsa ya fidda wandon,sai boxer daya rage,sannan
ya fara balle rigar jikinsa ya fiddasu daya bayan daya,take faffadan jikinsa wanda
ke murde yake kuma cike da gargasa daga qirjinsa zuwa hannuwansa suka
bayyana,matsawa ya sakeyi gaban mudubin ya dauki towel yana nutsa yatsunsa saman
sumarsa,gami da furzar da iska mai zafi daga bakinsa,abinda ke nuni da cewa a
gajiye yake lallai.

Wata qofar ya buda ya shige,sannan ya maidata ya rufe.

A qalla mintuna ashirin cif yayi cikin toilet din daidai sanda wayarsa
ta fara tsuwwa,yana cikin nau'in mutanen dake dadewa a toilet,ya fito sanye da
rigar wanka data tsaya masa iya singalalin qafafunsa da suka jiqe da ruwa,gashin
dake jikinsu suka kwanta luf,hannunsa dayan riqe da towel yanata goge sumar kansa
da kyau,jikinsa ba abinda yake sai fidda qamshin shower gel din da yake amfani da
ita.

Yana ci gaba da goge kan ga qarasa ga wayar tasa,ya zuba mata idanu a haka
ba tare daya taba ba,yana karanta saqon samhan daya shigo wayarsa ya kuma bayyana
saman screen din

"I ate,what next?" Qaramun murmushin gefan baki yayi,sai ya ajjiye towel din daga
gefe,ya dauki wayar yana maida mata amsa

"Ina da son abinci.....if i said that......ina nufin different types of food,so get
ready....." Yana sending mata ya ajjiye wayar,ya daga idanunshi ya maida kan
fuskarsa data bayyana tarwai a fuskar madubi da dan sauran danshi a kanta.

Idonsa ya dan rufe kana ya bude,fuskar iman ta gifta cikin kwanyarsa


haka kawai, different reactions nata a mintunan da suka gabata suka fara dawo
masa,sai ya dauki tunanin ya cilla gefe,ya dauko body cream dinsa ya fara shafawa
bayan ya saita wayarsa yadda zata karanto masa saqonnin da yake dasu ta email
dinsa,tunda ya baro system dinsa a office bai taho da ita ba.

Ta fara nisa da aikin abincin,kamar yadda tunaninta yayi nisa da gangar


jikinta taji inna na kiran sunanta,ta ajjiye albasar da take qoqarin yankawa ta
waiwayo tana amsawa,duk da qwalla ce qasan idanunta,amma kuma a nata ganin zata
kaucewa kowacce tuhuma saboda zata kafa hujja da albasar da take yankawa.

Dan zuba mata idanu innar ta sakeyi

"Idan akwai sauran abincin can da kika dafa kibari basai kin dora wani ba,malam
yayo waya,bazai samu tahowa yau ba,zai kwana a can"

"To" tace tana tattare kayayyakin

"Lafiyarki kuwa?" Inna dake shirin fita ta dakata ta tambayi iman din,bata da wata
amsa da zata bata,don haka ta gaya nata yanayin da takeji kawai

"Kaina ne yake ciwo" jim kadan inna tayi

"To basai ki lalubi maganinnki kisha tun yanzu ba?,Allah ya sawwaqe"


"Ameen" ta amsa mata tana sake danne zuciyarta,ta tattara komai a tsaitsaye saboda
yadda ciwon kan keta qara gaba ta wuce daki.

Alwala tayi tayi sallah,saidai ta kasa tashi daga saman abun sallar,tayi
imani a yau idan batasha maganinta ba akwai matsala,ta miqe a hankali tana duba
ma'ajiyarsu cike da dauriya,saidai ta taras babu komai,ta dafe goshinta tana kiran
sunan Allah.

Tasan dole ta nemo maganin indai tanason samun sassaucin radadin da take
ji,matsalar su daya,a yanzu basu da dan aike a gidan,duka almajiran malam an barsu
a tsohon gida,yanzu acan suke karatunsu,unguwar tasu kuma wata iriyar unguwa
ce,wadda idan kana neman abu sai kayi tattaki ka fita daga cikinta,bata da sauran
option face ta fita din,don haka da hijabin jikinta ta zura slipper ta dauki
wayarta ta fito.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 48

Har yanzu suna parlor din,saidai zuwa yanzu sun miqr tsaye,da alama suna
shirin tafiya ne,kanta ta kawar tayi hanyar dakin inna,ta samu innar tana hada wasu
kayayyaki a leda,da alama baquwar tasu zata bawa

"Yaya?" Innar ta tambayeta tana dubanta

"Maganin ciwon kan nan zanje dubowa inna"

"To....amma kuma darene ai,ko kuma bari na yiwa aminu magana,idan zasu fita ya fita
dake" bataji dadin abunda inna tace ba,batason hada tafiya dasu kwata kwata,inda
tasan tafiyar tata ma zatayi dai dai da tasu da bazata fito ba har sai sun wuce,a
yanzu kuma tattalin duk abinda zai bata ran innar takeyi,saboda haka babu damar
musa mata,sai ta amsa mata da to,tabi bayan innar sanda take fita daga dakin riqe
da ledar.

Suna fitowa zuwa parlor din yana daga labule shima yayi sallama,kallo daya
iman tayi masa ta janye idanunta zuwa wani sashe na daban,saboda wani kishi da taji
yana shirin shaqe mata kafar iska,wani mugun kyau taga yayi mata cikin qananun
kayan da ya saka,sun daukeshi fiye da yadda za'a gaya ma mutum,kana masa kallo daya
zaka san cewa hutu wayewa da ilimi sun ratsashi qwarai da gaske,idan dai batayi
kuskure ba tana iya ganin yadda samha ta kafe ameen din da idanu,fuskarta kuma na
aika masa da saqon murmushi,saita janye jikinta a hankali zuwa baya,ta lalubi
kujera daya ta zauna akai,tana qoqarin controlling kanta.

Duk sallamar da sukewa inna tana jinsu,da ledar da suka ajjiye da sunan
kayan dubiyarta

"Al'aminu.....xaka biya da iman da Allah zata duba maganinta,kanta ke ciwo"

"Ya salam.....sannu,jikinne ya dawo?" Samha ta fada cikin nuna kulawa,fuskarta na


bayyana damuwa.

Kanta kawai ta gyada mata ba tare data dubeta ba,tana iya jin idanun lamin
din a kanta,har zuwa sanda ya janyesu yana amsawa inna,suka qara sallama dukka
sukabi bayansa tana zaune a wajen ko motsawa batayi ba.

"Tashi kije kada su jiraki" inna dake neman wajen zama ta fada,saita gyada kai

"Zan tashi inna,so nake kan yadan dai daita" ta fada tana tallafe kan nata da tafin
hannunta

"Sannu....Allah dai ya sawwaqe wannan ciwon ya yayeshi"


"Amin" ta amsa qasa wasa muryarta na dan rawa saboda hawaye da suke qoqarin taruwa
cikin idanunta.

Bata motsa ba har sai da mufida data musu rakiya ta dawo tace ya lamin yace
ta fito sannan ta miqe tana ficewa,ita kuma yarinyar ta fara tattare wajen.

Shuru cikin motar ya dauka bayan wucewar mufidan takai saqon da alameen
din ya aiketa dashi,shi yana qoqarin saka frequency na gidan radion arewa zaiji
labaran dare da yake mayen jin news ne.

Ajiyar zuciya samha ta sauke,tana dan kada yatsunta,ta waiwaya a hankali


zuwa sashen da lamin ke rage volume tana duban fuskarsa daga side daya,ta lumshe
idanunta kanata bude,daga cikin abubuwan dake burgeta tattare da lamin din yanayij
nutsuwarsa da kuma komai nashi bisa tsari da aji,lumsassun idanunsa da kuma
kwantaccen gashin dake habarsa zuwa gefe da gefan fuskarsa,wanda ko sau daya babu
wanda zaice ya taba ganinsa ba'a tsare ba

"Man" ta kirashi kai tsaye da wata kwantacciyar murya,kansa ya daga suka hada
idanu,sai ta sakar masa murmushi,sexy eyes dinsa suna sake tsuma soyayyarsa dake
zuciyarta

"Dakai da iman,waye ne yafi miskilanci ne?" Karamin Murmushi ya saki,yana relaxing


bayansa da kujera da yake kai,sannan ya gane tafukan hannayensa waje guda yana
dubanta

"Ni din miskili ne?" Ya tambayeta yana dage dukka girarsa sama,abunda ya qara masa
kyau da kwarjini kenan,sai ta lunshe idanunta sannan ta gyada kai

"Kwarai kuwa,don har yanzu ban manta abubuwan da suka faru ba kafin na sameka"
murmushin gefen baki ne ya kubce masa,sai ya gyara zamansa sosai ya na fuskantar
gaban motar,dai dai sanda iman ta fito daga ciki,tana kuma takowa a hankali,iska na
kada hijabinta daga hagu zuwa dama,dama zuwa hagu,jikinta ba kuzari abinda ya
qarawa tafiyarta slow kenan,idamunsa fes a kanta,sai ya dora hannunsa daya kan
sitiyarin motar daya hannun kuma ya fara qoqarin tayar da motar sannan yace

"Wala'alla kiga dabi'u masu tarin yawa dake kamanceceniya tsakanina da


iman....saboda ita din raino ce" da sauri samha ta kalleshi

"Rainonka?,amma kuma man....sai nake ganin kamar ba sister dinka bace ta jini,ina
nufin uwa daya uba daya"

Dubanta yayi kafin ya dauke kansa ya mayar gabansa

"Me yasa kikace haka?"


"Kawai zuciyata na rayamin haka,kuma akwai tarin alamomin tambaya akan fuskarka
data iman"

"Ba lallai sai kowa ne da kuka fito ciki daya bane take zama 'yar uwarka ai,ko
suby'a a yanzu ta zama 'yar uwata,ko ba haka bama,musulunci ya kulla dangantaka ta
'yan uwantaka a tsakanin kowanne musulmi,bare inna da malam,inda akwai wani matsayi
daya gota na uwa da uba,tabbas sun cancanceshi.....ko kinsan lamin ba kowa bane
face almajiri?"

"Almajiri?" Ta tambaya cikin mamaki tana dubansa da kyau,saiya gyada mata kai ba
tare daya waiwayo ba

"Yes,hala kinyi mistake da kika fara soyayya da almajiri ko?" Ya fadi wani ciwo na
motsuwa cikin ransa na abunda ya shude shekarun baya can,murmushi ta saka
"Ko kadan,koda akwai matsayin da kake ganin yafi na almajiri muni ni bai dameni
ba,kuma baya gabana,saboda muhammad al'ameen din gundarinsa nakeso" lafazinta ya
sanyashi waiwaya ba shiri ya kalleta,lokaci daya yaji matsayinta ya qaru a ransa,a
da yana wani hasashe da kuma d'ari d'ari a kanta,amma a yanzu ta wanke komai.

Kafin ya amsa mata iman ta qaraso,ta bude gidan baya daya side din ta
shiga,suby'a ta amsa sallamar tata tare da yi mata sannu,yayin da samha a wannan
karon batace da ita komai ba,lokaci daya wani kishin iman din taji ya kama
zuciyarta da mugun qarfi,duk wata soyayya da kulawa da take qoqarin bata babu ita
ta zagwanye,kishi ya maye gurbinta,itama iman din bata lura da wani sauyi daga
samhan ba,saboda dama ba wai qaunar shishshigin da take mata take ba,ta tattara
dukka hankalinta ta mayar ga window,tana kallon gine gine da kuma titunan da suke
giftawa.

Kasa kasa take iya jin hirar da samha kewa amin,amma ba zaka iya jin me
take gaya masa ba,idanuwanta ta mayar ta lumshe kawai,tana jin sautin bugun
zuciyarta da qarfi,addu'a take sukai inda zata sauka ta fita a motar,don ko meye
za'a bata ba zata yarda ta dawo a cikinta ba.

Bata tashi bude idanunta ba sai da taji sun sauka daga titi suna
gangarawa zuw cikin wani layi,ta bude idanunta a hankali tana kallon unguwar.

Kofar wani gida ya tsaida motar,gidane mai bene hakanan mai girma tun
daga yanayin katangarsa ta waje,yana da tsaho a fuskar gidan ma,gininsa a tsaye
yake,ko ba'a gaya maka ba kasan masj gidan akwai abun,duk da yanayin ginin na nuna
ya dan kwana biyu.

Suby'a ce tayi mata magana tana shirin fita

"Allah ya qara sauqi,sai anjima"

"Ameen,na gode" ta amsa da muryarta data cakuda da sanyi,tana sake maida kanta gefe

"Man....shikenan?,sai yaushe?" Samha ta tambaya a narke tana duban ameen,idanunsa


na kallon gaban motar,yayin da ya yiwa sitiyarin motar qawanya da hannuwansa duka
biyun

"I will see you soon"

"Ka tabbata?" Saiya jinjina kai wannan karon bayan ya kalleta

"Na tabbata"
"Is okay,byee,qanwarmu,Allah ya bada lafiya" ta fada tana kama murfin motar ta bude
sannan ta fice,iman din ba zata iya tantance ta amsa mata ko bata amsa ba,illa dai
tasan tayi qoqarin motsa labbanta,amma batasan sautin ya fita ko maqalewa yayi
ba,samhan ta zagaya a hankali yana tsaye har zuwa sanda ta bude murfin qofar gida
ta shige bayan ta tsaya tayi waving masa hannunta.

Shuru ya ratsa motar na wasu mintuna

"Taso ki dawo gaba" umarni ya fita kai tsaye daga bakinsa,umarnin daya sake tattaro
dukka wani kishinta da bacin ranta waje daya,abunda ya matsa mata qwallar da take
dannewa ta gangaro mata,sai tasa gefen hijabinta ta tsaneta,sannan ta bashi amsar
da ita kanta batayi tsammani zata iya bashi ba

"A'ah,a nan zan zauna" shuru ya sake ratsawa na second biyar kafin taji ya saka
hannu ya buda murfin motar,ya fito a nutse yana takawa zuwa side din da take
zaune,hannu yasa ya buda murfin motar
"Fito" ya fada da dakakkiyar muryarsan nan wanda duk sanda yayi amfani da ita wajen
yi mata magana......maganar ke shiga har cikin qashi da bargonta.

Kamar yadda yace haka taja jikinta a matuqar mace ta fita,ta bude gaban ta
shiga,ya maida murfin bayan ya rufe,ya zagayo seat dinsa ya shigo ya maida mufin
shima ya rufe.

Takure jikinta tayi gaba daya waje daya,tana jin wani mugun kusanci a
tsakaninsu,zuciyarta na sake canza yanayim bugunta,qamshin turarensa ya mamayeta
gaba daya,kai kace tayi mayafi ne da suturarsa,kwantar da kanta tayi saman cinyarta
bayan ta rungume gwuiwoyinta cikin jikinta,tana fatan hakan xai bata dukka wani
qwarin gwiwa da take nema,xai kuma hana hawayen dake idanunta zuba.

Tanajin sanda ya tashi motar,hawaye suka silalo mata masu dumi,wane irin
hukunci ya ameen din yake mata haka?,saita kifa fuskarta kawai tana ta gayawa kanta
cewa bai kamaci tayi kuka ba a yanzu,a jikinta takeji kowacce rana zuciyarta na
sake samun rauni ne,raunin da ta tabbatar indai haka zata ci gaba da
kasancewa......watan watarana zata gaza,zata gaza ci gaba da daukar komai.

Basuyi tafiya mai nisa sosai ba taji ya sake tsaida motar,ya fita ya zagaya
seat din baya ya dauki kwalin maganin daya sulale a hannunta ya shiga pharmacy din
dake gabansu,bai jima ba ya fito,ya sake shiga motar yana dan sauke numfashi sannan
ya tada motar,dai dai sanda wayarsa ta dauki ruri,ya daga wayar ya sakata a
handsfree yana ci gaba da tuqinsa

"Kana ta inane?" Muryar ya sadiqu ta cika motar

"Na fita maida baby......daga nan kuma zan shiga ayimin aski,bana jin dadin kaina
haka" kalmar babyn tayi matuqar yiwa iman din zafi,ta runtse idonta gam tana
ambaton sunan Allah

"Oh okay,yanzu zan qaraza gida nima,idan ka dawo ma jone"

"Ba case" ya amsa masa yana kashe wayar,saiya ajjiyeta a tsakaninsu ya maida dukka
hankalinsa ka tuqin da yake,saidai lokaci zuwa lokaci wani abu na dan dauke masa
hankali.

Ko qwaqwaran motsi taqiyi,har cikin ranta takejin kamar da biyu ameen din
yake komai,ta yaya zai dinga pretending ne a kanta,bayan duk duniya shine mutum na
farko dayafi kowa karantar zahiri da badinin zuciyarta,shin ina wannan karatun?,ko
shina ya zagwanye tare da dukka soyayyar daya gwada mata a baya?,ko shima ya tafi
tare da dukka wata qauna tata dake ran ameen din?,baisan wani irin ciwo me zafi
yake dasawa ranta da rayuwarta ba,baisan yana kasheta bane deep inside her.

Katafaren gidan aski ne na isassun maza wanda ya amsa sunansa,koda sau


daya ka dubi wajen kasan waje ne dake tafe da tsari da kuma ilimi gwanin
burgewa,baya ga aski har manicure and pedicure,duk inda kaga yaje aski ko gyaran
farce a kano to babu yadda zaiyi ne,yafi ganewa na nan wajen,ya cire belt dinsa ya
buda qofa a nutse ya fice.

Tunda ya fita idanunta na alumshe,saidai qarar da wayarsa ta fara yi akai


akai ya fara damunta,dole ta juyo da fuskarta a hankali zuwa sashe da wayar take
wadda keta haske kiran na sake shigowa.

Sign na heart ne kawai ke blinking akan screen din,ta zubawa screen din
wayar idanu,zuciyarta na ci gaba da bugawa a hankali,haka wayar taci gaba da
shigowa tana kuma yankewa har kusan sau uku.

Tana shirin dauke idanunta don ragewa kanta bugun zuciyar saqo ya shigo a
karo na qarshe maimakon kira

_"Nasan duk yadda akayi driving kake man,duk da na qiyasta for now yaci ace ka isa
gida,hala kun tsaya wani guri ne, anyways..... take care of yourself"_

Wani abu me matuqar zafi cakude da bacin rai ne ya tasowa iman,me wannan
matar ke nufi?,batasan waye ameen a wajenta ba?,koda babu komai batasan shi din
yayanta bane?,batasan sunfi kusa ba?,kalamanta na nuni da tuhuma da kuma shakka a
fakaice,saita daga hannunta a zafafe da niyyar kashe hasken wayar don ta daina
ganin gilmawar saqon a idanunta,dai dai lokacin da ya bude motar,idanunsa ya sauka
a kan wayar,kana ya janyesu ya maidasu kan fuskar iman,qwayar idonta ta shiga cikin
tashi,saita janye idanun nata tana kuma qoqarin maida fuskarta daya side din dai
dai sanda ya jefa mata tambaya

"An kirani ne?" So take ta cire masa shakkun abinda ya gani din,kada ya dauka
damuwa tayi da wayar yasa har haka,saboda zuwa lokacin ya dauki wayar yana buda Tex
din

"Kararta ce take damuna,am trying to mute the sound" murmushin gefan baki ya saki
mara sauti,wanda ita kanta iman din bata ankara da hakan ba,shuru na wasu sakanni
ya sake ratsa wajen da alama saqon yake karantawa,kafin daga bisani yace........

GIRMA DA KIMAR IYAYE TA WUCE WASA,A DUK SANDA KA SABAWA MAGANARSU KODA KA FISU
GASIYA,INDAI BA KAUCEWA FADAR ALLAH BANE,KO YAYA...KO YAYA SAI KAGA BA DAI DAI
BA,DUK WADDA TA ZABA IRIN ABUNDA IMAN TAYI,ZATA IYA GAMUWA DA SAKAMAKON DA YAFI NA
IMAN,wallahi wallahi iman nata da sauqi,da Allah yaga dama sai ta hadu da cutar hiv
din daga jikin bassam har qarshen rayuwarta,sabawa umarnin iyaye yana daga cikin
gagga gagga laifuffuka da bai kamata ayi sakaci ko sasauci wajen fadakarwa a kansu
ba,littafi yanzu ya zama kamar wani madubine da al'umma suke kalla su gyara wani
abu da ba dai dai ba,Allah yasa mu dace

*please follow me on arewabooks*


HUGUMA

Add my story to your library for more latest pages

https:/arewabooks.com/chapter?id=62bff720a306c9b48f09f552

Thanks.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 49

"Fito ki duba cikin biyun wanne ne zai miki maganin,an samu different colors"
ya fadi mata yana juyawa, trying to call number samha din.

Gaba yayi tana binshi a baya,tana jin sanda yake baiwa samhan excuse,tare
da alqawarin kiranta idan ya gama abunda yake,tabi bayansa da kallo ta cikin hasken
fitilun dake wajen,wani abu mai nauyi na sake ratsa qirjinta da zuciyarta.

Dab da zasu shiga wajen saiya rage saurinsa,harta cimmasa suka dai daita
tazarar dake tsakaninsu sannan suka shige,babban store ne,wanda bayan magunguna
suna saida abubuwa iri daban daban na ciye ciye.

Da hannu yayi mata nuni da area din magungunan suke,ta fara takawa a
hankali tana shiga wajen,idanunsa na biye da ita,kafin daga bisani ya janyesu yana
qoqarin dai daita kansa.

Tana duba magunguna amma kuma hankalinta na wani waje na daban,zuciyarta


ta nace maimaita mata duk abubuwan da suka faru tun daga zuwan samha har zuwa
tsaiwarsu qofar wajen

"Wow....wacce iriyar sa'a na taka yau din?" Da sauri ta waiwaya jin muryar data
sani na magana,kuma daf da ita ake maganar,dr ahmad ne,yana sabe da wata baby girl
wadda aka yiwa kwalliya dai dai gwargwado,gashinta yasha adon ribbons masu kyau.

Bakinta ta washe masa kamar yadda hake binta da murmushi,don dai ita din
ba zata kira abunda tayi masa da sunan murmushi ba

"Dr,barka da dare"
"A'ah,ki barni na fara gaisheki mana hajjaju,banyi tsammanin ganinki a yanxu ba a
wannan wajen,sai gashi Allah ya dubi idanun bawan Allah" murmushi ne yaso qwace
mata ganin yadda yayi,ta miqa hannu don ya bata yarinyar tana cewa

"Zo baby....ya sunanki?" Ba qyuya kuwa yarinyar ta taho wajen nata,duk da batasanta
ba,sai dr ahmad ya buda baki yana kallonta

"What?,lallai kin ciri tuta wajen milha" ya fada cikin mamaki,saita dauke idaunta
daga fuskar yarinyar,wadda ganinta sak fuskar dr ahmad din

"Me kenan?"
"Bata yarda da kowa sai wanda ta saba gani,zaiyi wuya kiga taje wajen baquwar
fuska" murmushi tayi kawai maimakon amsa maganarsa,ta rasa abun cewa don haka tace
dashi

"Kana tana yawon dare kenan?" Da sauri ya daga hannayensa sama

"Rufamin asiri hajjaju,wallahi ba haka nake ba,kada a kashen kasuwa" murmushi ya


kubce nata ganin yadda ya haqiqance har da saurin rantsuwa

"Maganin hajiya ne ya qare shine na fito nemo mata" saita gyada kanta tana ci gaba
da yiwa yarinyar wasa,yarinyar taji ta burgeta,ta kuma kwanta mata a rai,duk da
dama itadin mayyyar yara ce,saboda yadda ta taso itace qarama a gida,bata da qani
ko qamwa,idanun dr ahmad a kansa,yana fargabar ya zamana wani ne ya kawota ba,ya
hadiye abunda ke taso masa ya daure ya tambayeta

"Kefa?,Allah yasa ba 'yan overtaking bane sukayi overtaking din dani" qaramin
murmushi ta maida masa itama,sannan ta amsa mishi

"Nima maganina na fito nema,ni da ya ameen ne"

"Oh... okay" sai taga kawai ya dauki kwando ya fara zuba daukan kaya yana
zubawa,bata kawo komai a ranta ba,tunda tasan cewa yana da iyaye,sannan uwa uba
mutum kamar dr ahmad din bazai kasa shigowa guri kamar wannan ba ya fita bai dauki
komai ba.

Mintuna kusan takwas ya sake dawowa inda suke,ya cika kwandon da kaya

"Muje na biya kudi,daga nan sai mu gaisa da yayan namu ko?" Kamar tace mishi
a'ah,sai kuma wani abu ya darsu a ranta,don haka kai tsaye tace masa

"Ok,ba damuwa" yaso amsar milha amma tace masa a'ah

"Ina ka samo baby ne me kama da kai?"

"Magana ce daya kamata ayita a nutse,bazan gaya miki komai akai ba,har sai randa
aka bani dama nazo ni dake muka zauna sosai.....don Allah ki tausayamin ki
gajarcemin wannan jiran da bansan lokacin yankewarsa ba" ya fadi yana
marairaicewa,yanayin maganar tasa yasa murmushi kubce mata,dai dai sanda ameen dake
tsaye yana jiranta ya daga kansa daga wayarsa da yake dannawa,idanunsa kuma basu
sauka ako ina ba sai a kansu,kallon second uku yayi musu ya sauke kan nasa again
akan wayar tasa,kamar bai sansu ba,ko bai gansu ba,yaci gaba da latsa wayarsa.

Daga can qasan zuciyarta taji wani dadi ya zarta mata kadan kan ganinsu tare
da ya amin din yayi,duk da ba haka taso ba ace ya dauje idanun nasa da wurwuri
haka,ta tsurawa fuskarsa idanu sanda suke takowa inda yake tsayen,zuciyarta cike da
hope din ya sake daga idanu ya gansu taren,saidai kuma addu'arta bata ci ba,don har
suka qaraso wajen tamkar baisan Allah yayi ruwan halittarsu ba,har sai da dr ahmad
yayi masa sallama sannan ya daga kansa yana amsa masa,suka miqawa juna hannu.

Ci gaba tayi da satar kallon fuskarsa sanda suke gaisawa da dr ahmad,wai


ko zata karanci wani abu na sauyawarsa ko kuma wani yanayi na daban,saidai duk
qwaqwarta ta kasa gane komai,tilas ta kama kanta daga nacin kallon da take
masa,qwaqwalwarta ta shiga searching,daga bisani ya karba milha daga hannunta,ya
matsa kadan daga inda suke tsaye yana ta yiwa yarinyar wasa,sai kuma ya fara takawa
a hankali yana komawa cikin store din,yana tafe yana daukar mata kayan wasa da
sauran kayan ciye ciye na yara.

Bai tashi dawowa ba saida uban siyayyan kayan wasa dana ci kala kala,dai
dai sanda aka gama yiwa Dr Ahmad lissafi ya kuma biya da cash,shima ya matsa aka
lissafa ya basu atm dinsa suka cira,don bau wadataccen kudi a hannunsa.

Tare suka jero da dr din suna taba hira,saika dauka sunsan juna ne,hirace
irin tasu ta maza data shafesu,tana biye dasu a baya,saidai gaba daya ya ameen din
ya gama kwance mata duk wani lissafi nata da yayi saura,duk wata hanya da zata saka
masa tarko ko kuma ta gane wani abu ya tosheta.

A seat din gaban motar dr ahmad din ya ajjiye yarinyar,ya kuma ajiye mata
ledarta a gefanta,sannan ya sha sumarta ya cewa

"Byee baby"
"Byee uncle"ta amsa masa tana dariya tare da kada hannunta,ya maida murfin ya rufe
mata,sannan ya nufi motarsa.

"Bamuyi haka dakai ba dr,yanzu nacewa ya ameen me?,kawai daga haduwa


saika hau yimin siyayya,shi kansa ya amin din ai bazaiji dadi ba" iman tace da dr
ahmad,wanda ya jajirce sai ta karba uban siyayyar da yayi da sunanta

"So nake innar dama ta tambayi waye ni,qilan hakan zaisa a bani damar bayyana
kaina,amma maganar ya ameen na tabbatar bashi da matsala,muje kawai" yayi gaba riqe
da ledar.

Tsaiwa tayi ta kasa binsa kamar an riqe mata qafafu,inda tasan haka zata
faru da bata tsaya ba,tana kallonsa har zuwa sanda ya isa bakin motar amin din,ya
zagaya ta window yayi magana,sai taga ya dage booth din motar ya saka ledar ya
rufe,sanna ya waiwayo inda take tsaye,ya sakar mata murmushi yana daga hannuwansa
biyu,alamun komai yayi dai dai,sai a sannan ta fara takowa a hankali kamar kazar da
qwai ya fashewa a ciki.

"Matsoraciya kawai,kina da yaya mai sauqin hali da kuma fahimta amma


bakisan hakan ba" yafada yana dariyar tsokana,itadai bata iya cewa komai ba,sai
yayi gaba ya bude mata murfin motar,ta zura jikinta a hankali,tana ji dama baya ya
bude mata ba gaba ba,ya maida ya rufe yana cewa

"Na gode hajiya.......yallabai godiya nake" yaja da baya don ya bashi damar tada
motar,kafin ya juya zuwa tashi motar.
Shuru shine abinda ya wanzu a motar,daga ita har shi babu wani da yake
cewa da dan uwansa komai.

Inda so samu ne kuka takeson tayi ko zata samu relief,kuka irin sosai din
nan,duk wannan abun da tayi tayi ne saboda ya ameen din,tayi ne di ta caje
zuciyarsa ko zata tsinci wani abu da zai bata qwarin gwiwa,saidai da alama babu
komai a ciki da yake da nasaba da ita,hawayen sun taru ta maidasu har batasan adadi
ba

Wani tuqi yake ba irin wanda yayi daxu ba,ya qara speed na motar fiye da
dazu sosai,hakanan ya tattara hankalinsa da idanunsa kan titi fiye da dazun dai,a
haka suka qarasa gida,yayi parking sannan ya kashe motar

"Ki daga booth ki kwashe tarkacen can.....don idan kika barsu zanyi sadakarsu ne"
wani kallo ta watsa masa da yafi kama da harara,yau inda akwai wasa tsakaninsu
saita yaba masa maganganun da wala'alla zuciyarta zata sassauta,bata taba yardarwa
kanta ameen kwata kwata bata gabanshi baya kishinta ba sai yanzu,qafafuwanta suna
rawa ta soma takawa cikin gida ba tare data tsaya diban kayan ba,saboda hawayen da
taketa riqewa daya balle mata.

A zafafe shima ya fita daga motar yabi bayanta,taku hudu qwarara ya


cimmata ya kuma sha gabanta,cikin wani irin zafi yake duban fuskarta

"Abokin wasanki ne ni?.....nace ki kwashe kayanki ki taho kibarsu cikin


motata?,inyi me dasu?" Ya fada cikin muryarsa da tayi nauyi,take kuma cike fal da
fada.

Gudun hawayen fuskarta suka qaru,sai kuma a sannan ya lura


dasu,sassauci ya sauki saman fuskarsa ba kamar dazu ba,yaja numfashi yana qoqarin
danne kansa

"Wadan nan hawayen kuma na meye su?,me akayi miki?" Yafadi yana hade girarsa waje
guda,qas tayi da kanta ba tare data iya cewa dashi komai ba,tsahon wasu sakanni
sannan ta bude baki a hankali

"Ciwon kaina ne ya dawo" idanunsa ya dauke daga kanta,daga can bakin qofa ya hangi
sayyadi,yaron da malam ke aikowa gidan wasu lokutan ya kawo sakonni,cikin kaurin
murya ya kira yaron,ya qaraso da hanzari a ladabce,saiya nuna masa motar

"Jeka ka bude bayanta zakaga leda ka daukota gaba daya"

"To" ya amsa mishi yana juyawa.

A hankali ya dauke idanunsa daga kan yaron ya maida fuskar iman din,sai ya
hade hannayensa a qirjinsa ya zubawa fuskar tata idanu yana iya ganin yadda hawaye
yake diga yana faduwa qasa,kallonsa yana da matuqar dafi da kuma tasiri a jikinta
da zuciyarta,saiya qara mata wani weakness daya sanya ta kasa dogara da kanta sai
data jingina da bangon hanyar da zata sadaka da parlor din,ta kuma boye fuskarta
cikin hijabi.

Dawowa sayyadi yayi da ledar a hannunsa,ameen ne ya karba ya ajjiyeta a


gefe,taku uku ya qare ya rahe tazarar dake tsakaninsa da iman din,yatsaya gab da
ita sosai,cikin wani irin lallausan murya yace

"Yanzun ciwon kan kikewa kuka haka?" Batasan me zatace dashi ba,shima bai jirayi
amsarta ba yace

"Ki qoqari ki tsaya haka,don ciki zaki shiga,ni kuma ba zamu shiga tare ba kina
wannan kukan inna ta dauka wani abune ya faru" sai ya saka hannunsa a karon farko
tsahon rayuwarsu yaja hijabin data duqunqune fuskarta dashi ya fara qoqarin
wareshi.

Kam ta riqe hijabij,qaramin murmushin da iyakarsa fatar baki ya saki,ya


gwada mata irin nasa qarfin,tashi guda ya cireshi gaba daya,har hakan ya kusa
haifar da fadawarta jikinsa,saidai ya tareta da hannunshi kana ya matsa baya.

Hannayensa ya zuba a aljihun wandonsa yana kallonta,ya tsare gida sosai


kamar bashi ba

"Zagaya muje ta bayan gida" ya bata umarni kai tsaye,dole kayi shakkansa yadda ya
sauya fuska lokaci guda,ta fara takawa kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki shi
kuma yana biye da ita suka bi ta hanyar bayan gidan.

Saida yasa ta wanke fuskarta a bakin famfon wajen,ya miqa mata handkerchief
dinsa mai cike da sassanyan qamshi ta dauke danshin fuskarta dashi sanna ya mata
nuni data wuce,ta taka a hakali zuwa ciki ya rakata da idanunsa.

Babu kowa a parlor din sai tv dake aiki,ta qarasa cikin qarfin hali ta
kasheta,sannan ta nufi dakin inna,labulen tadan daga kawai ta gaya mata ta
dawo,zata wuce tasha magani ta kwanta,innan tayi mata sannu ta zarce dakinta tana
jin sanyi cikin ranta na yadda innar bata ga fuskarta ba,kota kan kayan da suka
baro waje bata sake tunawa ba,tabi lafiyar katifarta bayan tasha maganin tana sauke
ajiyar zuciya,taji relief a cikin zuciyarta qwarai,hakan kuma bai rasa nasaba da
dan caring da ya ameen ya nuna mata,duk da bai taka kara ya karya ba,ta rufe
idanunta tana hango yadda lumsassun idanunsa suka bude da kyau sanda ta kusa fadawa
jikinsa ya kuma ja baya da sauri,saita sauke ajiyar zuciya tana tura kanta qasan
pillow.
[7/19, 10:02 PM] Mummyn Yara: 50

Da gaske ta dinga yaqi da zuciyarta cikin kwanakin don ganin ta samarwa da


zuciyarta nutsuwa,saboda yadda takejin yanayin jikinta komai zai iya faruwa da ita.

Duk wata hanya da zasu hadu da ita tayi qoqari ta tosheta,saidai duk da
hakan bata tsira da jin muryarsa da kuma tunani da zuciyarta ke yawan kawo
mata,wanda take yaqi qwarai wajen kawar da wannan,saidai kusan a banza wai man
kaza,data kore tunanin batasan lokacin da zai mamayeta ya dawo ba.

A haka ta dinga juriya tana dannewa,tayi qoqari ta maida hankalinta kan


karatunta,saboda karatune da ko yaya damuwa ta shiga cikinsa sai kaga ba dai dai
ba,hakanan tana shekarar qarshe,kada ya rage mata ta zama cikakkiyar nurse.

*********Safiyar wata lahadi,a ranar bata da wani uzuri da zai fiddata waje,don
haka bayan ta gama komai na ayyukan gidan tayi wanka ta sake komawa ta kwanta,babu
jimawa barci ya debeta.

Can cikin barci yunwa ta tasheta,ta sauko a hankali daga gadonta,ta miqe
ta shige toilet,bakinta ta sake wankewa ta dauraye fuskarta ta tsaneta da towel
sannan ta fito,ta jawo hijab dinta iya gwiwa ta zura,saboda yau din weekend,tasan
ba za'a rasa mazan gidan a kusa ba.

Parlor babu kowa,saidai tana iya dan jiyo muryoyi daga parlor din
malam,sai ta zarce dakin inna taga ko zata sameta?.

Bata ciki,ba kowa ma a ciki,ta dan kalli dakin,sai taji ya kamata ta sake
kintsa mata shi,duk da atsaftace yake,amma wasu kayan ba guraren daya kamata a
ajjiyesu kenan ba.

Ta rufe dakin tana juyowa sukayi kacibus da inna


"Yanzu na dubaki ban ganki ba"
"Eh ina wajen malam,muje ciki dama inason ganinki" gaban iman din ya fadi,saboda a
yanzun babu abinda taqi jini irin ta batawa inna ko malam rai,tun bayan kuskuren
data tafka a baya,jikinta babu qwari tabi bayan inna.

Atsaye ta sameta tsakar dakin

"Wannan kayan na waye?,tun rannan sayyadi ya shigo dasu,yanayin jikinki yasa ban
miki zancansu ba,na manta dasu ma a dakin sai daxu ina neman wani sabon rawanin
malam" idanunta takai ga ledar,gabanta ya sake faduwa,ta tuna da ita,shaf ta manta
da ita sai yanzu,ta dubi inna taga yadda ta tsareta da idanu,koda bata yi mata
hakan ba babu wani 'yar boye boye tsakaninta da inna,tayi wannan alqawarin daga
sanda mai faruwa ta faru,har zuwa randa ita ko innar wani zaibar wani a duniya

"Dr ahmad ne ya bani"


"Wayeshi?" Ta tambayeta yanayin fuskar innar yana sauyawa

"Likitan dake dubani tun ina gidan bassam,ranar dana fita siyo magani muka hadu
dashi a store din"

"Kina nufin a gaban aminu?,kuma ya sani?" Kai ta gyadawa innar a sanyaye,shuru ya


ratsa dakin na kusan minti guda

"Shikenan,kije,dama malam yace yanason ganinki" gaba daya sai gabbanta suka saki,ta
kasa motsawa,ta kuma kasa hadiye tambayarta sai data jefawa inna ita

"Malam kuma inna,wani laifin nayi?" Kallonta tayi,sai taji tausayinta ya tabata,don
haka tayi mata murmushi

"Babu wani laifi,shikenan babu ganawa ko tattaunawa tsakanin uba da diyanshi sai ya
zamto wani laifi suka aikata masa?" Ajiyar zuciya ta sauke,ta samu relief yanzu,don
haka ta juya ta fita a dakin innar,innar ta bita da kallo a sace harta qarasa
fitar,saita sauke ajiyar zuciya,ta laluba gefan gadonta ta zauna tana fadin

"Ya Allahu,ya Allah ka shiga wannan lamari,Allah ka kawo mafita ya rahman,Allah kai
kasan yadda zakayi da bayin nan naka,ya Allahu" murya qasa qasa,qafafunta gaba daya
sunyi sanyi,ta jima a zaune kafin ta miqe ta shiga abunda ga kawota dakin.

Yankewa tayi kawai ta fara shiga kitchen ta samu wani abun ta toshe yunwar
dake sakadarta kafin ta wuce wajen malam din,haka kuwa akayi,ta biya ta can ta hada
tea tasha,ta samu ragowar soyayyan qwai tana murmushi ta fara gutsira tana ci,da
alama na mufida ne,sabida tafi kowa son soyayyen qwai a gidan,tadanji cikinta yayi
mata dai dai sannan ta wuce wajen malam din.

Tun kafin ta shiga rumfar malam din ta fara jiyo muryarsa mai cike da nutsuwa
da taushi,da alama wani bayani yakewa malam din,ta tsinci kanta cikin faduwar gaba
kamar kowanne lokaci,ta zuqi iska sosai sannan ta fesar,ta tabbatar shigarta parlor
din sai yabar baya da qura,basu taba hada wajen zama dashi ba bata tsinci zuciyarta
cikin wani sabo kuma mahaukacin sonshi ba,abun kamar jarrabi a gareta,haka ta
tattaro dukka wata jarumta da juriyarta ta yaye labulen tare da yin sallama.

Idanunsa ya dauke daga kan paper din dake hannunsa ya saukesu a kanta,ya
motsa labbansa yana amsa sallamar tata kafin ya janyesu ya sake maidawa kan
takardar gami da dakatawa da bayanin da yakeyi.

Tun hada idanun da sukayi dashi karo na farko ta janye daga kallonsa,tun
kuma a sannan ya sakar mata wasu dafi masi qarfi xuwa kowanne sashe na jiki da
zuciyarta,yayi azabar kyau cikin shadda wadda aka yiwa wani irin dinki,yar ciki me
dogon hannu da wata daga sama kamar top,taji aikin hannu da zare mai kauri,dinkin
ya zauna masa kamar yadda shaddar tayi bala'in tafiya da qirarsa da kyan surar da
Allah yayi masa,sumar kansa a kwance sai qyalli takeyi,kwanakin data dauka bata
ganshi ba sai taga kamar an qara masa kyaune,wani abu mai sanyi ya ratsa
zuciyarta,idan hancinta ba qarya yayi mata ba qamshinsa ne kawai cike a falon,wani
sihirtaccen qamshi da batasan da wanne kalar turare yake amfani ba,tun yana lamin
dinsa asal qamshinsa na dabanne,gwani ne wajen iya zabar kalar turare

"Maraba da autar inna,hajaratu ayar Allah" malam ya tsokaneta da suna da kuma salon
da a baya yake tsokanarta dashi,murmushi ta saki,saboda abun yayi mata dadi
sosai,abune data jima rabon data jishi daga bakin malam din,wannan dalilin ya sanya
ta zabi zama kusa da malam din,saita zarce mazauninsa,ta zauna dai dai qafafunsa a
qasan carpet ta soma gaidashi.

Cikin kulawa ya amsa mata,ta maida dubanta ga lamin

"Barka da safiya" hankalinsa na kan takardun gabansa ya amsa mata,hakanan ya sadiqu


shima takardun dai yaketa dubawa yana shiryasu.

Ita d malam suke dan taba hira,yayin da sadiqu da amin din suka karkata
da hada takardun,suna kuma dan musayar maganganu a tsakaninsu,duk da hirar da suke
da malam din amma hankalinta na kanshi,a sace take kallonsa ta gefan idonta,glass
din da ya sanya a yau din ya qara masa kyau da kwarjini na musamman,ta yarda sanya
abu ma ya karbeka baiwa ce,shikam yana daga cikin baiwarsa,tun zamanin da yawancin
suturunsa ma ba masu tsada bane,bare yanzu da kudade suka fara zaunar masa.

Ta lura da yadda wayarsa keta haske yana kasheta,da alama kira ne yaketa
shigowa,sai taji rata ya raya mata samha ce,take zuciyarta ta jagule,karo na qarshe
yadan saki siririn tsaki ya kashe wayar gaba dayanta wanda cikin rashin sa'a ya
kamata tana kallon nasa,da wani mugun hanzari ta dauke kanta kamar bashi take kallo
ba,tana iya jin siririn murmushi mai qaramin sauti daya fitar,yaci gaba da aikinsa.

Kusan mintuna talatin sannan suka kammala

"Komai yayi dai dai,rana kawai mukeso malam ya sanya mana da za'a bude company din"
alamin ya fada a ladabce da nuna tsananin girmamawa,daya daga cikin abubuwan da
suka sanya malam din yakejin bala'in so da qaunar alamin din,wani irin yaro ne da
Allah ya zuba masa sanin ya kamata,mai matuqar ladabi biyayya tausayi da kuma
girmama na gaba,ba shakka duk da iyayensa basu mori komai daga kyakkyawar haihuwar
da sukayi ba,amma kuma sun barwa duniya kyakkyawan iri abun misali,mutane da
yawansu basusan ba malam bane ya haifi lamin din ba,sai dalili ya kawo,kai malam
din ya jinjina

"Ina ganin mu barwa ranar juma'a ko?,bayan saukowa daga sallar juma'a,tunda kace
akwai masallaci daura da ma'aikatar"

"To Allah ya kai mana rai da lafiya" ya amsa a ladance

"Ameen ameen" malam da sadiqu suka amsa

"Sanna kuma...." Ya sake magana yana motsawa

"Akwai wani abunda na soma nema yanxu haka,shirye shirye nason bude compy na saida
spare parts na motoci da kuma maida tsofaffin motoci zuwa sababbi wanda nake saka
ran sadiq zai ja ragamarsu,abun yana da wahala ne malam da kuma buqatar kudade,to
amma kuma cikin ikon Allah da muka fara aiki kan abun,sai komai yake zuwa mana da
sauqi,mun samu manyan mutane da suke da sha'awa kan abun,kuma zasu zuna share
dinsu,yanzu haka muna saka ran nan ba da dadewa ba shima za'a gama komai yafara
aiki"
"Allahu akhbar,Alhamdulillah,mun godewa Allah,ubangiji ya qara sanya albarka cikin
lamuranka kai da 'yan uwanka,ba shakka wannan babban abun alfahari ne a
garemu.....ke hajar,kiramin innarku" ya fadi yana duban iman,tarin walwala da
farincikin dake saman fuskarsa ba zasu misaltu ba.

Ko minti daya bata cika ba inna ta shigo,ta ajjiye wasu kwanuka gaban malam
din,ta koma gefe daya ta xauna tana sauraren bayanan malam.

Ita kanta kasa boye murnarta tayi,tayi musu addu'a sosai tare da fatam
samun nasara kan duk wani abu da suka sanya a gaba.

"To ku bani hankulanku nan,akwai muhimmiyar maganar data sanya na buqaci


ganinku,na kuma taraku a nan....." Sanun cewa duk sada malam din yayi haka magana
me muhimmanci zaiyi yasa kowa sake shiga nutsuwarsa,suka kuma zubawa malam din
idanu suna jiran abunda zai fita daga bakinsa.......

*afwa da qaramin page,nayi busy ne👏🏾👏🏾*[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara:


"Alhamdulillah.....Alhamdulillah,mungodewa
Allah da yadda rayuwa tayi da kowannenku,kuma
ubangiji gayi muku baiwa da kyauta wadda ba
kowane ya samu kwatankwacinta ba...….ya zuwa
yanzu kowanne ya samu duk wani rufin asiri na
rayuwa,ya kuma samu madogara da madafa
koda babu ranmu,abu guda daya ne ya rage
muku,ku dukka ukun kun isa kun kuma kai
munzalin daya kamata ace kowa nada aure a
cikinku......" Matsananciyar faduwar gaba ta
saukarwa iman,jin malam ya ambaci kalmar
aure,uwa uba kuma cikin jawabin nasa harda
ita, kenan ko meye zai fito daga bakin malam
din.……kowanne irin hukunci ne ya shafeta?,harda
ita a ciki kenan?,take taji gaba daya jikinta ya
saki.tafin hannaventa dana gafafunta sukayi wani Saki,tarn hanhayenta dana
q'dravunta sukayiWanl
irin sanyi,saita fara murxasu tana addu'a cikin
ranta, ko meye zai fito daga bakin malam
din,indai maganar aure ce Allah yasa a tsameta a
ciki,ta maida hankalinta tana son jin qarashen
bayaninsa
"Dukkaninku kowa yana da sukunin ajjiye
iyali,gurin zama da sana'ar yi,sannan hankali a
yanzu ya game kowa a cikinku……..kema kuma kin
qara hankali,a yanzuk kinsan dai dai,kinsan ba
dai dai ba, kinsan me ya kamata, kin kuma san
abinda bai kamata ba,saboda haka,inaso kowa a
cikinku ya gabatar min da wanda zuciyarsa ta
kwanta masa dashi,duk da dau na fara samun
labarai daga wajen innarku,amma inason naji ta
bakin kowa"
Shuru ne ya ratsa parlorn,aka rasa wanda zai
fara magana a cikinsu,iman dai kanta na
qasa,yayin da lamin iya nashi idanun ni a
qasa,yana caccaka yatsansa cikin carpet din qasa,yana caccaka yatsansa cikin carpet
din
dakin, fuskarsa babu yabo babu fallasa,sadiq
kuwa sai faman shafa sumar kansa yake yana
murmushi
'"Waye babba a cikinku ne?,ya fara magana"
malam ya fada ganin alamun jin nauyinsa sun
bayyana a fuskokinsu
"Nine" sadiqu yayi hanzarin fada,abunda yasa
lamin daga kai,ya jefeshi da harara kai
tsaye,murmushin fuskarsa kuma ya dara na dazu
"Mara kunyar banza, mayen aure kawai"
"Babu komai,ni ai tawa maitar ce ta fito fili,amma
dai na tabbata bankai wanda kusan duk asuba
kafin ya tafi sallah sai yayi wanka ba"harara, auk magandr dd sukdy Can gas
sukdyI,la
yadda babu mai iya jinsu,saika dauka wani abun
suke tattaunawa,lamin din baisan duk abinda ke
faruwa dashi sadiq din yana sane ba sai
yanzu,tabbas badon su malam na wajen ba sai
yakai masa mugun naushi
"To malam babba,muna saurarenka" malam ya
fada yana crossing qafafunsa waje guda,qas yayi
dakai yana sake shafa kan nasa
"Eh....ni sunanta fatima,gidansu yana unguwar
dorayi,sunan mahaifinta alhj usman"
"'Ma sha Allah,ka rubutan cikakkem address da
komai,zan sanya ayimun bincike akanta kafin ka
shaida mata ta gayawa iyayenta su saurari
zuwanmu.
"'In sha Allah" sadiq ya furta kansa a "To... kaifa malam aminullahi" malam ya
furta
yana murmushi,idanunsa akan lamin
din,hakanan zuciyarsa,wadda ke cike da fata da
buri,duk da jikinsa yana bashi abune mai wuya
gurguwa da auren nesa inji bahaushe,koda
burinsa da fatansa basu samu tabbatuwa ba
bayajin cewa hakan rashin kyautawa ne face
tsantsar adalci da zai gwada masa. Ba malam kawai ba,hatta da inna idanunta
akansa suke,duk da tana kallonsa ne afakaice,ta
yadda babu lallai ka gane kallon nasa take kai
tsaye,haka kawai ta tsinci zuciyarta na bugawa
fiye da yadda ta saba buga matan,itama nata
idanun cike suke da fata da kuma burin,burin da
itama rashin tabbas yafi rinjaye a cikinsa,iman
kuwa......gaba daya rinse idanunta tayi,tanajin
inama ace mallam bai gayyaceta wannan waje
ba,inama ace ita daya ya kebe?,saidai amsar data
fito daga bakinsa zuwa ga malam ta sanya taji
gaba daya jikinta ya dauki rawa, kamar wadda
aka yiwa wanka da ruwan qanqara "Sunanta samha,mahaifinta alhj mutallab
garba,a unguwar court road take,nan wajen
tudun murtala,duk wanda ya nemi gida
mahaifinta zaa kaishi har can" Nannauyar ajiyar zuciya inna ta sauke tana
saukar da idanunta qas, wani abu na son rige
zuciyarta amma tana yaqi dashi,cikin taimakon
Allah ta kawar dashi,saidai zuciyar gaba daya taqi
karbar yanayin da lamin din yazo dashi,saidai a
hakan tana gayawa zuciyar tata,dole ta rusuna,ta
kuma karbi dukkan abinda lamin din yazo dashi a
matsayin zabi hannu bibbiyu.
"Ma sha Allah,alhamdulillah" malam ya fada
wani nauyi yana cika muryarsa,yana kuma rage
armashi da karsashin maganarsa "Kai bani da matsala, unguwar tasu ina da aboki
acan,malam gambo,zan masa magana akai,idan
ya kammala zan shaida maka kaima ta shaidawa
iyayenta"
"Allah ya qara girma da lafiya" lamin din ya amsa
yana russunar da kansa ga malam
'"Amin amin" ya amsa yana waiwaya gefen iman
"To nazo kanki auta" yayi furucin yana
murmushi,saidai kiranta da malam din yayi wani
nauyi taji ya hau kanta,tanajin kamar gaba daya
mutanen duniya aka tara mata suke kallonta
suna kuma sauraren ta basu amsa game da wani
in baracu tanail a
suna kuma sauraren ta basu amsa game da wani
gagarumin al'amari daya tunkarosu,tanaji a
ranata da zuciyarta wanna shine titsiye mafi
wahala da kuma fargaba da zata fuskanta tsahon
rayuwarta
"Waye shi?,a ina kuma yake?" Malam ya jefa mata
tambayar da shi kansa yasan babu lallai a samu
cikakkiyar amsa daga bakinta,tunda dai bai taba
jin anyi zancan wani cikin gidan ba tun bayan
fitowarta daga gidan bassam,kuma shi shaidane
na yadda take barin samarin nata a waje,wani
lokaci sadiq yake sawa ya sallamesu. Yatsanta takeson ta motsa wai don ta tabbatar
qwaqwalwarta na aiki kuwa yadda ya
kamata? idan tana aiki wa zata kira sunanshi ta
gabatarwa da malam shi?,wa take saurare?, waye
ta bawa damar da suka fahimci juna da zai iya
tsayawa a mizani da ma'aunin mijinta?,idan duka
ya cika wadan nan yana da gurbi a
zuciyarta?,gurbin da zai bashi damar zama
mijinta?,ta zauna dashi cikin soyayya qauna da
kulawa?,sam!…...duka biyun babu ko daya da
wani da namiji zai samu daga gareta. Akwai dimbi tulin tarin masoya,saidai babu
wanda ya samu koda taku daya na fili a zuciyarta
da sunan tana so qauna ko jin shaugi a
kansa,mutum daya ne dai tak!,wannan wanda
yafi kowa sanin wacece ita duk duniya.......wanna
wanda yafi kowa sanin ciwonta!..
......wannan
wanda baya ga iyayenta shi daya zai iya tsaiwa ya
gayawa duniya wace ita ya kuma tabbata
hakanne!….
...Wanda koda yayanta da suka kwanta
ciki daya,tanajin bashi da wannan qwarin gwiwar
da kuma cancantar.
„.shine dai kuma mutumin
data butulcewa!…
„..butulci mafi munil,ta karya
zuciyarsa!,ta iya kallon tsabar qwayar idanunsa ta
shaida masa BANA SONKA! ,ALLAH YANKIYAYE NA
AUREKAI,DANA AUREKA GWARA NA KASHE
KAINA!,ta zame masa KUFAN WUTA!,ta tafi ta
barshi da tarin tabo da ciwo!,ta zabi waninsa,waninsa din da baisan ciwonta ba,ta
kasa waiwayarsa,zuciyarta ta dode,ta kasa tuna
komai,ta kasa tuna wayeshi a tare da ita,taji masa
mummunan ciwon da ba kasafai masoya ke
warkewa ko su mata ba.....shin a yanzu,a dalci ne
ta tsammaci samun juyowar soyayyarsa
gareta,ko kadan. Take kwanyarta ta fara mata
hasashe da laluben cikin masoyanya dake
karakaina,wadanda suketa turo da applications
nasu waye ya cancanta?,wa take gani ya kamaci
ta gabatar da sunansa?, waye zai hau mizani ko
nagartarsa zata iya maye mata koda kwatar
kwatar wannan babban gibi?
"Dr Ahmad" ta samu kanta da furtawa ba tare
data gama tantancewa ba,ita kanta sai da sunan
ya fita sannan ta tsaya tuhumar kanta,yaushe ta
bashi damar da yaketa nema akan zuwa ya
sameta su tattauna har suka gama fahimtar juna
Ladaamanchi7tamhavar data dashi?,da har zata bada sunanshi?,tambayar data
sake sauke duk wata gaba ta kuzari datayi saura a
jikinta
"Wayeshi?" Malam din ya tambayeta kanshi tsaye
idanunsa a kanta,zuciyarsa nata fadin inama
inama.…...saidai dole abar komai a yadda yazo,yafi
tunanin haka Allah ya tsara,bayason yiwa kowa
shishshigi cikin al'amarinsa
"Likitan da nake gani ne"
"Kin tabbatar?" Ya jefa nata tambayar dashi
kansa yasan bata gama cika ba,yana fatan ko
yaya ne hankalinta yakai kai
"Eh" ta amsa tana gyada kai,tare da bawa kanta
qwarin gwiwa.
"To ba laifi, ki bawa wani cikin yayunki address
dinsa da komai da komai,ubangiji ya zaba mana
abunda yafi alkhairi,Allah yasa kuma dukkaninku su zamto silar qarin arziqi da
shiga aljannarku"
"Amen" muryoyin mutum uku suka amsa,banda
iman da bata gama tantance wanne hukunci ta
yankewa kanta ba,me kyau ne ko mara
kyau,waye dr Ahmad a badininsa,meye
halayyarsa,duka bata sani ba,illa dai tasan kawai
ta bawa malam sunansa. addu'a malam din yasa
alameen ya rufe musu da ita,zuciyarta ta dinga
bugu kamar zata faso qirjinta sanda daddadan
muryarsa mai taushi ke fita cikin sautin addu'ar
da yake karanta ga da harshen larabci, murya ce
mai tarin daraja da muhimmanci a wajenta,iya ita
kadai idan taji yana saukar mata da wata
nutsuwa,saidai a yau jin muryar ya haddasa mata
tara qwalla mai yawa cikin idanunta,tana kuma Tuna mata da cewa tayi bankwana da
zama mammallakiyar me murya da dame ita sun kusa zama malamin wata A sanyaye inna
ta taso daga inda taje zaune bayan malam ya sallamesu,ta qaraso inda ta
ajjiye kwanukan abincin malam din ta fara
budesu a nutse,ta zuba komai yadda ya
kamata,sai ta koma ta zauna wajen,
Kallonta yayi,kamar zaiyi magana sai kuma ya
fasa,ya dauki kwanon abincin,ya saka hannu
kamar yadda ya saba yayi bismillah ya fara ci.
Kasa hadiye abunda ke ranta inna tayi,gani
take kamar ba yanzu malam din xai gama cin
abincin ba,kamar baya sauri,sannan uwa uba
yanayinsa bai nuna zaice komai ba
"Malam…..….kagayadda abun ya kasance ko?" Kai
ya gyada
"Eh,Allah ya sanya hakane yafi alkhairi" sosai
fuskarta ta nuna damuwa "Amma malam shikenan kuma?,me yasa ba zaka
ankarar dasu ba?,me yasa ba zaka qarasa aikinka
ba?" Tsame hannunsa yayi daga abincin,ya
ajjiyeshi a gabansa, murmushin dake cike da
kamala dattako da dattijankata ya subuce masa
"Ashe duk abubuwan da akewa hajar ana sonta
har yanzu?" Kai ta karkada,tasan malam din yana
sha'awar tsokanarta ne kawai, banda haka har
akwai wanda ya kaishi son iman din,da rashin
son ganin abunda zai zama illa ko aibu ga
rayuwarta,maida dubanta tayi gareshi ba tare
data iya bashi amsa ba,shima a sannan fuskarsa
ta koma serious
'"Duk yadda kikai ga son ganin iman da amin sun
zabi junansu baki kaini ba binta,kullum ko a dare
ko a rana idan na saka goshina a qasa,ad du'ata ko a rana idan na saka goshina a
qasa,addu'ata
itace,ya Allah idan da alkhairi a tarayyarsu,idan
har tarayyarsu zata zama wani sabon mataki
kuma tsani na dorewar zumunci da ganin
mutuncin juna muda 'ya uwan aminu Allah ya
qulla,idan kuma har tarayyar tasu zata haifar da
sharri,yankewar zumunci ko tabarbarewar
al'amura,Allah ya hada kowa da rabonsa na
alkhairi.
.…..ta iya yiwuwa ubangiji ya duba cewa
babu alkhairin,shi yasa ya aiko da abun a
haka,…...idan mukace zamu matsa ko mu takura
to tabbas zamu yiwa Allah shishshigi ne,sai ya
qyalemu da iyawarmu muyita shan wahala,kuma
bugu da qari shi kansa yaron bamuyi masa adalci
ba,a baya bamu iya tanqwara diyarmu ta aminta ba,a baya bamu iya tanqwara diyarmu
ta aminta
dashi ba....sannan kuma a yanzu shi zamu
dubeshi muce ya auri diyarmu?,bayan ina da
tabbacin ko ruwa mukace ya fada zai fada babu
musu?,ba dai dai bane wanna,saboda haka, mu
tattara muci gaba da gayawa Allah,da kuma
addu'ar zabi mafi alkhairi" .
Kai inna take jinjinawa,ta yarda ta kuma gamsu
da bayanan malam,babu son rai ko son zuciya a
cikinsu ko kadan,hakanan sun sake saukar mata
da nutsuwa,saboda haka ta dai data kanta,tare
da fadin "Ubangiji yayi zabi mafi alkhairi"
"Amen bintu" sunan da ya saka inna sakin
murmushi,shi kuma ya dauki plate dinsa yaci
gaba da cin abincin,yana kuma janta da hira.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 52

Empty take jin qwaqwalwarta sanda take takowa daga parlor din malam zuwa
dakinta,fayau take jinta kamar wadda ke tafiya saman iska,kwanyarta kamar an share
mata komai,ba zata iya tantance a wanne yanayi take ciki ba.

Tana saka qafa a dakin wayarta dake charge ta dauki ruri,ta ja qafafunta
zuwa inda wayar take,don dama tana da buqatarta,ta riga ta sani,malam din baya
daukar magana biyu,don haka tunda ta furta dole tasan yadda komai zai tafi.

Dr Ahmad shike kira,tamkar yasan dambarwar dake faruwa a kansa,taja da


baya a hankali kamar zata zube a qasa,sai kuma Allah ya taimaka ta samu gefan gadon
ta zauna,ta latsa wayar dai dai lokacin da take dab da katsewa.
Ajiyar zuciyarsa ce ta fara sauka a kunnuwanta,kafin daga bisani yace

"Ni kadai nasan damuwa da kuma dimuwar da nake shiga,duk sanda na kwadaitu da son
jin muryarki,na taki rashin sa'a baki daga kirana ba"

"Duka wannan ta qare, finally iman na gayyatarka zuwa gidansu a yau" sak yayi a
wajen kamar wanda jinin jikinsa ya qare,daga wayar yayi ya kalla,ya kuma tabbatar
iman din ya kira,amma duk da haka.....mamakin da ya shiga yasa ya kasa shuru

"Idan wasa kikemin,ki tamakeni ki gayamin,kada sai daga baya,saboda wallahi


zuciyata ba zata iya daukan wannan wasan ba"

"Mun taba irin wannan wasan dr?"

"Ko kusa"

"To kana iya daukarsa duk yadda kaso,either ka daukeshi da wasanne ko kuma ka
daukeshi a gaske" saita zarta yatsunta ta shafe wayar ta kashe,ta kuma zame a
hankali ta kwant a wajen.

Jinjinawa girman katobara da kuma aika aikar da take shirin yiwa rayuwarta
tayi,tasan cewa ba komai ta aikawa kanta da kanta ba illa wani dan qaramin
ta'addanci da zai iya zama silar wargajewar dukka wani farinciki a rayuwarta na din
din din,ko sau daya bata taba jin dr Ahmad a koda gefan zuciyarta ba.....kai bama
shiba,tana jin hakanne akan kowanne da namiji illa halitta daya,abu daya ta sani
shine,tana matuqar ganin girma da kimarsa,saboda kasancewarsa nagartaccen
mutum,hakanan kuma nutsatstse ne,bashi da makusa tako ina,saidai ita zuciyarta ba
wannan take hange ko kuma kalla ba,duk wani bugunta da fitar numfashinta qwalli
daya tak tana kiran al'ameen ne,saida shi din yayi mata nisan kiwo,nisan dake
alamta mata bazaiji kiranta ba.

Idan taqi zaben dr ahmad hakan bazaisa malam ya qyaleta da zancan aure
ba,idan bata zabi dr ahamd ba batasan kalar wanne zata zaba ba,qila a sannan babu
me quality dinsa ma sam a kusa.

Waiwayawa tayi tana duban tex din daya shigo wayarta dava dr Ahmad

"Godiya tayi kadan wajen bayyana miki farincikina da kuma yabawata da karramawar da
kika yimin a yau,ki zuba idanun ganina,ki kuma tanadi wanne kalar tukuici zan baki"
rufe wayar tayi haskenta ya bace daha screen din,ta lumshe idanunta kana ta
maidashi wani side din cikin rashin sanin madaafa.

Wata iriyar juriya da dakiya ta ara wadda bata taba tunanin samunta anan
kusa ba,to juriyarce ma ko kuma zuciyarta ce ta gama qeqashewa?,ta qone babu wani
qauri yanzu da yayi saura?,ta fita tayi aikace aikacenta tana qarfafawa kanta
gwiwar cewa,babu ita a zuciyar ameen ya kamata itama ta fiddashi daga tata
zuciyar,ya kamata ta jingineshi ta fuskanci reality dinta,a haka ta gama girkin
rana ta kuma dora dana dare.

Loma daya inna tayi a abincin ta sake kallonsa cikin mamaki,saboda a yau
girkin sam baiyi kama dana iman din ba,qwararriya a fannin girki,tarin kura kurai
fal cikin abincin,saita qyaleta bata yi mata magana ba,saidai ta leqo sanda take ta
hidimar hada sanwar dare ba tare da ita ta sanyawa cikinta koda qwayar shinkafa ba
tun tea din safe tace da ita

"Ki tattara hankalinki waje daya iman,yau din akwai yiwuwar malam zaiyi baqi,kiyi
abinci me kyau"
"To inna" ta amsa mata da salon son nuna she's okay

"Ko na turo miki mufida?"

"Qyaleta inna,damuna zatayi da surutu" kai ta jinjina kawai,uwa uwa ce,ta karanci
zallar damuwa kan fuskarta,duk da qoqarin boyewar da take,saita juya ta fita ranta
fal damuwa,cikin zuciyarta tana cewa

"Ya hayyu ya qayyumu,ya rahmar rahimin,bi rahmatika nastagisu ya Allah".

Karfe biyar da ashirin da bakwai ya shigo gidan,ta jiyo muryarsa a parlor


amma bata taba kawowa kanta zai qaraso kitchen din ba,wannan amannar data yi ya
sakata ta sakankance,taci gaba da yanka albasa saman chopping board,a hankali kamar
wadda ke yankae naman jikinta,saboda yadda zuciyarta da gangar jikinta ke neman
gazawa da yaqin da take tayi da kanta kan hana kanta tunane tunane.

A hankali yake takowa zuwa kitchen din,hannunsa dauke da cup din daya
cika da damammen fresh yoghurt na L&Z da fura,bai samu suger a parlor din ba,shi
yasa ya yanke qarasowa kitchen din,mufida yaso bawa ta zuba masa,saboda baison zaqi
da yawa yasa ya yanke zuwa da kansa.

Yana saka qafarsa ya hangeta,bai tsammaci tana cikin kitchen din ba,sai ya
dakata daga bakin qofar kitchen din saboda babu hijabi ko mayafi a jikinta,yayi
matuqar qoqarin ganin ya hana idanunsa qare mata kallo amma hakan yaci tura,kamar
wanda ake ingizawa ya bita da kallo,tun daga qafafunta dake sanye da slipper na
robber zuwa sama,skart dinta daya zauna sosai a jikinga ya fidda shape na
qugunta,hakan rigar jikinta duk da cewa gefenta daya yake iya hangowa,gashinta dake
daure cikin dankwali ya fito ta qasa yabi bayanta sosai ya kwanta,saboda gashin
buzaye gareta irin na inna.

"A'uzu billahi minash shaidanir rajim" ya furta a hankali cikin


zuciyarsa,jin wani abu ya fara yawo cikin jininsa,sai yaja da baya ya koma a
hankali,yana fatan kada ta ganshi gudun zubewar mutuncinsa a idanunta.

Mufida dake kallo a parlor ya miqawa

"Jeki ki kai mata ta zubamin,amma kada ya wuce cokali daya,sannan kice mata idan
babu mayafi a jikinta ta nema ta saka"

"Tom" yarinyar ta fada tana miqewa da sauri ta karba tayi kitchen din,ya zame a
hankali ya zauna saman kujerar yana sauke ajiyar zuciya yana ci gaba da kiran sunan
Allah tare da korar shaidan daga zuciyarsa,jiran fitowar mufida ya amsa furar ya
wuce ne kawai ya tsaidashi,amma banda haka da tuni ya tsufa a daki,don dama yunwa
ta dawo dashi ya shigo ya samu abunda zaici ya koma,to abincin da zaici ya tarar
yayi sanyi,shi kuma bai iya cin abincin daya huce har haka ba,inna tace yayi haquri
a gama na dare,don dama girkin ba kowa zainiya cinsa ba,wannan ta sanya ya nema
furar.

Idanu iman ta zubawa mufidan sanda take gaya mata saqon ameen din

"Na nemi mayafi na saka?,kenan ya shigo?,yaushe?" Duka ta maimaita tambayar wa


kanta da kanta,sai data karba cup din xata zuba masa sugern hancinta ya zuqo mata
qamshin turarensa wanda ya tabbatar mata da shigowar tasa,to amma batasan yaushe
ba,kuma har ya fita bata ganshi ba.

Tana gama afawa ta miqawa mufidan,sannan ta janyo hijab dinta wanda tun
dazun dashi ta shigo ta saka taci gaba da yankan albasarta.

Ta sake komawa duniyar data fito wato duniyar tunani,tayi nisa sosai,har
bata iyajin motsin abinda ke gefe ko kusa da ita,a hankali hancinta ya fara shaqo
mata wannan mayen qamshin,qamshin da aduk sanda ta shaqeshi saiya birkita mata duk
wani lissafinta,tadan tsaida yankan albasar,tanajin kamar akwai mutum a cikin
kitchen din,kuma a gefanta,kamar duminsa ma take ji,ta waiwaya a hankali take
fuskarta ta fada cikin tashi.

Kwayar idanunsa cikin tata yake kallonta,dab da ita yake tsaye,riqe da cup
din a hannunsa,take dukkanin jikinta ya amsa,saita dan matsa kadan kamar yadda
shima yaja baya,yabi albasar da take yankawa da kallo,koshi da yake namiji amma sam
baiga nutsuwa cikin aikinta ba,hasalima wata albasar bata gama baruwa gaba daya ba

"Ya akayi aka zuban gishiri instead of sugar?" Yayi maganar da lallausan muryarsa
wadda ta sake kashe mata jiki.

Cikin dakiya ta fiddo idanunta waje

"Gishiri?,sugar dai" ta fada adan daburce,batason yadda yaje kafeta da mayun


idanunsa,ita kadai tasan me yake bar mata,wanda a yanzun wannan yanayin da yake
barwa jiki da zuciyarta zai iya zama barazana ga dukkan wata jarumta data shirya
aiwatarwa.

Cup din ya miqa mata kawai batare da yace komai ba yana ci gaba da
kallonta,a hankali ta miqa nata hannun zata amsa,abunda ya kawo haduwar yatsansu
waje guda,kowanne kuma ya janye hannunsa, cup din yayi qas zai fadi ya
tarwatse,cikin wani zafin nama da kuma mazantaka ya sanya daya hannun nasa ya
taroshi,sannan ya dorashi saman drawer din kitchen din,ya taka a hankali ya
rabeta,ya dauki wani cup din da kuma sugarn ya fice a kitchen din a hankali,yanajin
yanayinsa kamar yana shirin canzawa zuwa wani irin feeling dake kashe gabban
jiki,wanda a yanzu baya nemansa ko fatan zuwanshi.

Hannayenta duka biyun ta saka ta kama kanta sosai,tana tambayar kanta


da kanta meye yake damunta ne haka?,me yasa ta gaza samun nutsuwa?,saita matsa inda
ya ajjiye cup din,ta saka yatsanta ta lakaci furar ta dandana.

Tabbas gishiri ne ta zuba maimakon sugar,ta sauke ajiyar zuciya mai


matuqar nauyi,kamar zata hado da zuciyarta,ta tura cup din cikin sink,ta matsa
wajen chopping board din ta dauki wuqar tana kiran

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" taci gaba da yankan.

*_BAYAN WASU AWANNI_*

Sosai ta tsurawa kanta idanu a gaban madubin,cike da wasi wasi da kuma


tunanin anya abunda take shirin aikatawa shine dai dai?,to idan ba dai dai bane
meye yafi dacewa ta aikata din?,me zatayi?,zata zauna ne har sai ruwa ya qarewa dan
kada ko kuwa?.

"Ya iman,baqonki yazo" muryar mufida ta katse mata tunaninta,ta waiwaya a


hankali ta dubeta

"Yana ina?"
"Yana qofar gida,amma naga ya ameen ya masa iso,ya bashi kujera ma ya zauna"

"Ya ameen?" Ta fada cikij dimbin mamaki

"Eh,sun gaisa ma sannan ya wuce" baya tayi a hankali ta zube saman gadonta,ya ilahi
me ameen yake buqata da ita ne?,ko sai ya manna mata ciwon zuciya zai qyaleta,sai
yaga ta haukace sannan zai daina nunawa duniya ya daina yi da ita?,kullum kwanan
duniya sai yayi abunda zai tabbatarwa da kowa baya qaunarta baya kuma kishinta,ta
gaji da gani hakanan,yana kasheta ne ba tare da kowanne makami ba,ya kamata yabarta
hakanan

"Me za'a ce masa?" Mufidan ta katseta

"Kikai masa ruwa da lemo,ina zuwa" ta fada ba tare da tana da tabbacin iya futar
tata ba.

Ta jima zaune a wajen tana dai daita kanta sannan ta miqe,ta fesa turare
sama sama,ta yafa mayafin daya dace da kayan jikinta sannan ta fito,takunta a
kasalance,zuciyarta babu dadi ko kadan,ta gayawa inna ta fita,innar ta bita da
kallo
"Saikin dawo" ta amsa mata a sanyaye.

Tunda ta fito idanunsa na akanta,murmushin dake nuna zallan farincikin da


yake ciki yaqi gushewa daga kan fuskarsa,miqewa yayi kafin ta iso ya kuma gyara
mata kujerarta

"Barka da fitowa sarauniyar mata"tale labbanta kawai tayi ta yadda tsokokin


fuskarta suka bada shadow na murmushi,don kwata kwata babu wani digo na farinciki
da zai haifar da murmushi na ainihi a saman fuskarta

"Barka kadai likita,ya na ganka kai kadai?,ina babyn?" Ta tambayeshi tana shirin
zama

"Milha?,tana wajen mamanta" shima ya amsa mata yana zama

"Halan batasan zaka fito zance ba?" Ta tambayeshi tana qoqarin bude masa robar
lemo,duk a qoqarinta na kauda dukka wani alamu da zai alamta samuwar matsala rashin
walwala ko takura a tattare da ita.

Dariyarsa taja hankalinta

"Da kin zaci diyata ce kenan?,eh diyata dince,amma bani na haifeta ba,'yar lil
sister dina ce......any way na godewa Allah,ko babu komai hakan yana nufin ana
kishi na" murmushi ta qirqira kadan tana aje masa cup din.

Baibi takan lemo ba sai gaisuwa da suke sabuwa,ya kuma gabatar mata da
kanshi,cikakken suna da tarihinsa,ya kuma sake jaddada mata soyayyarsa sannan ya
rufe da cewa

"Ina fatan za'a karbeni a yadda nazo,gani dai qaton tuzuru ne ni,wanda yasha gori
har ya godewa Allah" murmushi tadanyi kawai kanta a qasa tana murza yatsunta

"Idan har kin aminta dani,kin kuma amince zaki aureni,toki gabatar dani ga malam,ba
dogon lokaci nakeso a dauka ba,so nake ayi komai a gama ki zama mallakina"

"Amma bakajin ka tauyi kanka,kana saurayi zaka fara da bazawara?,ba kuma zaka samu
matsala daga gida ba?"

"Wace bazawarar?" Yayi tambaya yana dube dube,kamar me neman wani abu,lamarin da
yasa dole murmushi yafita daga fuskarta

"Ki ajjiye wannan batun please,bashi ake yayi yanzu ba,ana yayin samun
nagartaccuyar macene,wadda ta fito daga gidan tarbiyya" saita jinjina kawai bata
iya cewa komai ba.

Bai jima sosai ba yayi mata sallama,yana jaddada mata ta gabatar dashi,ga
komai nashi da ake buqata suna iya yin bincike a kansa,ya tafi ya barta da gift na
zobe mai kyau,wanda bai bar wajen ba sai daya tabbatar ta sanyashi a yatsanta,ya
zauna kuma yayi matuqar yi ma zara zaran fararen yatsunta kyau.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 53

Kwanakin da suka biyo baya gaba daya gidan cikin hidima da shiri suke na bikin
bude katafaren kamfanin ameen din,wanda suke samar da dukka wani nau'i na suttura
na qasashe daban daban,kama da dinkakku da wanda ba'a dinka ba,na maza da mata yara
da manya,abayas ne yadididdika laces harma da mayafai takalma da jakankuna,ga
bangaren qwararrun teloli da yanzu yanzu ka siya kaya za'a canza musu kamanni da
dinki na kece raini kowanne kala kakeso,wajene da zai kafa tarihi mai dimbin
yawa,kuma guri ne da duk wanda ya kalla sai ya juya ya sake kallonsa,shi kansa
ameen din ya qarar da duka abinda ya mallaka a wajen,saidai sam bai damu ba,sabida
yana da kyakkyawan zato da kuma fatan zai maida adadin abinda baisan yawansu ba.

********Yammaci ne lis,wanda yayi dai dai da washegari itace ta kasance ranar


juma'a,ranar da za'a gudanar da bikin bude companyn IB COUTURE,ya zabi ya sakawa
wajen sunan malam ne,saboda girmamawa a gareshi,da kuma nuna jin dadinsa da
godiyarsa bisa halaccin da yayi masa a rayuwa.

Zaune suke a 'yar qaramar harabar gidan ita da dr,wanda wannan shine
zuwansa na biyu bayan malam ya bata saqon ta shaida masa cewa ya turo da
magabatansa,ya gama bincike a kansa ya kuma tabbatar da ingancinsa.

Gaba daya ya sanyata a gaba da kallonshi,ya kasa boye mata abunda ke


ransa,farinciki zumudi da kuma fatan zuwan ranar da zaace ta zama tasa

"Allah yasa kada malam ya saka doguwar rana" dan dubansa tayi

"Ka shirya kenan?"


"Na dade ai a shirye Hajiya,ke kadai nake jira dama" murmusawa tayi kadan

"Inda zai tambayi shawarata,zance masa a bari sai na gama dukka sauran watannin da
suka ragemin a makaranta,saboda hankalina yafi tattaruwa waje daya"

"Mene?" Yafada da sauri yana fidda idanu,sai kuma ya hade tafukan hannayensa waje
daya

"Ki rufamin asiri,kar kimin haka,indai makarantace baki da matsala dani,practical


dinma sai kiyi a asibitina,koda bakiyi ba gaki ga likita matsalan me kike dashi?"
Dai dai sannan aka tura dan madaidaicin gate din gidan mota ta fara yunqurin
shigowa.

Dauke idanunta tayi sanda ta fahimci motar alameen ce ke shigowa ta maida


wani sashen daban kamar bata ganshi ba,batason su hada ido ko waga magana ta hadasu
bare zuciyarta ta karye,duk wani guntun qwarin gwiwa data tattaro ya zagwanye ya
barta da tarin rauni.

,don haka ta waiga da dan sauri.

Yaya baraka ce,miqewa tayi a nutse murmushi na subucewa daga fuskarta,matar


nada kima da daraja a idanunta,ko sau daya kuma ko a fuska bata taba nuna mata wani
canji ba kan abunda ya faru tsakaninta da alameen ba,yadda ta saba mata har a
lokacin da kuma yanzu babu wani abu daya canza

"Yaa baraka....." Ta kirayeta tana qarasawa bakin motar,fuskar iman qunshe da


murmushi,sai itana ta juyo tata fuskar kamar gonar auduga
"Hajaru hanjartu" sunan da take kiranta dashi tun zamanin quruciya,tun sanda suke
zuwa mata hutu jigawa

"Sannu da zuwa yaya,ashe kina hanya?" Ta fadi tana duban 'yar budurwar diyar yaya
barakan,wadda a hakan itace autarta

"Wallahi dai kin gani,sai da aminu yaje ya daukoni,wai lallai sai nazo bikin buda
kamfani,ni kuma naga me zanzo nayi ga inna ga malam,sai yace wai malam dinne yace
lallai lallai nazo din"

"Gaskiya ne,ai ya kamata" iman din ta fada har yanzu fuskarta da murmushi,tana kuma
dauke idanunta daga kewayen da ameen ke tsaye,ta fara qoqarin amsar jakar
hannunta,diyarya badi'a tana gaida iman din,ta amsa mata cikin kulawa tana sake
cika da mamakin girman badi'a,yarinyar da idan sunje qauyen take goyata a baya,ta
taya yaa baraka rainonta.

Ita tayi musu jagora zuwa cikin gidan suna taba hira abunsu da yaa
barakan a sake kamar yadda suka saba a baya,kusan daura da dr ahmad xasu wuce,don
haka tadan dakata sanda ya miqe tsaye yana gaida yaa baraka

"Bari na rakata ciki"


"A fito lafiya" ya bata amsa cikin nuna kulawa,ya bi iman din da kallo,abinda yasa
ya gaza ganin tahowar ameen,har sai daya kusa gotashi.

Cikin girmamawa ya bashi hannu sukayi musabaha,sannan ameen din yayi


gaba,saidai kafin yakai ga qarasawa ya dakata,ya bawa sayyadi jakar kayan nasu yace
ya qarasa musu da ita ciki,sai kawai ya koma cikin motarsa ya tasheta ya fita daga
gidan.

Sosai suka kaure da murnar ganin juna ita da inna,don an dan kwana
biyu ya barakan batazo garin ba,an saba da juna an zama tamkar 'yan uwa,har kowacce
tsakanin inna da yaa barakan takejin 'yar uwarta cikin jikinta sosai.

Bata baro ciki ba sai data tabbatar inda yaa barakan zata zauna ya
saitu,ta samu dr ahmad din ma yanata waya,fitowarta yasa ya sauke wayar,ya tarbeta
da murmushi

"Barka da fitowa gimbiya" murmushi ya kubce mata,taja kujera tana shirin zama qofar
gidan ta sake budewa,saita maida hankalinta ga can maimakon zaman.

Tun kan ta qaraso fa ganeta,bushira ce,suna hada idanu suka sakarwa juna
murmushi,ta miqe tana tunkararta

"Wata sabon gani,yaushe a gari inji maqi baqo?" Iman ta fada tana dariya,harara
bushira ta watsa mata

"Au haka ma zakice?"


"Tuba nake" iman ta fada tana fadada murmushinta,saboda tasan ta yiwa bushiran
laifi,sai suka gamu a hanya sannan suka sake takowa zuwa ciki

"Dr......ga childhood friend dita,sunanta bushira" iman ta fada sanda


suke qarasowa inda dr ahmad ke zaune.

Cikin fara'a suka gaisa da ita,kasnacewarta itama bushiran gwanar kirki


ce da fara'a,sai ya miqe

"Hajjaju zan wuce gaskiya hakanan,na fuskanci kina da baqi da yawa yau,bari na basu
aronki na yau kawai" murmushi tayi sannan ta taka masa har qofar gida inda motarsa
take fake sukayi sallama ya wuce,sannan ta dawo ciki.
A inda dr ya tashi ta samu bushiran zaune tana jiranta,hannunta riqe da
wayarta

"Waye wannan kuma?" Bushiran ta fara da tambayar iman sanda iman din ke saka jan
kujera daya ta zauna akai

"Ba zamu koma ciki ba kika zauna a nan?" Iman ta maida ma bushira tambayarta da
tayi

"Nan dinma ai yayi,mu gama gaisawa dake,saiki rakani ciki na gaida inna" kai iman
din ta gyada,shuru na kusan sakan uku ya ratsa sannan tace

"Ya kika ganshi yayi ne?" Tayi tambayar da dan guntun murmushi saman
fuskarta,murmushin da ya sanya bushira ta zuba mata idanu kafin ta amsa mata

"Yayi,bashi da wata makusa,yana kuma da kirki a idanu"

"Haka dabi'arsa ma ta badini da malam ya bincika" kai bushira ta jinjina

"Wayeshi din?"

"Dr Ahmad, shine wanda zan aura" tayi maganar babu wani armashi ko confidence a
tattare da ita,ido bushira ta zuba mata sosai,ta buda bakinta a hankali

"Ina kuma ya lamin din?" Lumshe idanu iman tayi,ta kuma bude lokaci guda tana
girgiza kanta,yanayin fuskarta ya canza a take

"Yafi qarfina zuwa yanzu,don kuwa ya fitar da wata matar,ya lamin ya kasa gane duk
wata kulawa da nake bashi soyayya ce,ya kasa gane duk wani motsina a kansa
zazzzafar qauna ce,ya kasa fahimtar furucina motsina da aiki na,kamar yadda yake
fahimta a baya" sosai bushira ta gyara zama ta kuma ajjiye wayarta,tana iya hangen
wani pain mai kaifi daga zuciyar iman din

"Indai har ya lamin ya cancanci a soshi,me yasa zaki jira sai ya gano wani motsi da
action naki?, just go straight forward.......ki sameshi ki furta masa kamar yadda
ya furta miki,meye a ciki?,dan uwanki ne kuma yayanki ne" kai iman ke kadawa a
hankali a hankali

"Bazan iya ba bushira.....bansan ta yaya zan tari namiji nace masa ina sonshi
ba,karfa ki manta,har abada ni din diya macace,ya ameen kuma namiji ne"

"Akan hakan kin gwammaci ki rasashi?,kin gwammaci wata ta sameshi?"

"Ina addu'a,kuma Allah yana sane idan har na cancanci na sameshi ta kowacce hanya
bazai hanani shi ba,idan kuma ahmad ya zabarmin na gode masa,bazan iya cusa kaina
zuwa ga wulaqancin namiji ba bushira,a wannan matsayin da nake kai,addu'a da
tattarawa ubangiji lamarina shine kawai abinda yafi dacewa dani"

Kai bushira ke jinjinawa,sosai iman tayi matuqar bata tausayi,maganganunta


akan hanya suke,tabbas kowacce mace tana buqatar kare martaba da kuma kimarta wajen
namiji kodon gaba,amma ita a nata hasashen,case dinta dana alamin daban yake da
sauran cases.

Miqewa iman tayi tana daukar jakar bushiran

"Mu shiga ciki bushira,mintuna kadan suka rage a kirayi magrib" miqewa tayi tabi
iman din,tana kallon yadda aketa kokawa tsakanin zuciyarta da kuna qwarin gwiwar da
take dashi.
******yadda gurin ya qawatu haka ya cika da jama'a wadanda suka halarci
taron bude kamfanin,sosai kamfanin ya qayatar,ya kuma bada mamaki fiye da zato,waje
ne mai girma da tsari,kowanne sashe daban.

Floor na farko anan masu dinki suke,dinki kowanne nau'in sutura,second


floor wanda xaka hau sama shi kuma anan suke ajjiye kowanne kaya da aka gama hadasu
dama wadanda ba'a dinka ba game son siyansu a haka,da sauran tarkacen su takalma da
kayan ado,third floor kuwa acan office na mai kamfanin wato lamin da sauran
ma'aikata yake.

Bayan bude kamfanin ta hanyar yanke wani dan zare,tarin 'yan press suka
cika ma'aikatar,aka kuma gama komai akan idanunsu,sannan akayi qwarya qwaryar
walima jama'a suka shiga suka ga yadda waje yake da ayyukan da za'a dinga
gudanarwa,daga nan wasu suka fara ma lamin sallama da fatan alkhairi,abunda ya fara
rage cinkoson kamfanin.

A hankali take takawa cikin kamfanin,bayan an ajjiyesu waje na musamman


ita da inna da mufida an gabatar musu kayan ciye ciye da shaye shaye da kowa yaci a
wajen,sosai kamfanin ya burgeta,tana kuma jinjinawa lamin na yadda ya zama
tsayayyen namiji,bai bar sana'arsa ta asali ba,hasalima ya qara qaimi ya kafa
kanshi ra hanyarta,ya kuma zamanantar ta zama abar sha'awa ga kowa.

Doguwar barandar ta dinga bi tana kallo qasan kamfanin har sai data kai
qarshenta,wanda a wannan kwanar office din din CEO yake wato lamin,ganin taka
qarshe sai ta fara qoqarin juyowa ta dawo

"Me yasa samha....i told you har yanzu akwai mutane da yawa,da kin zauna abunki iya
abunda kika yimin ma i appreciated it" muryar lamin ta ratsa kunnenta,yana rufe
baki kuma muryar samhan ta biyo bayanta

"Yanzu my man.....daga abun arziqi,a qa'idama fa dani ya kamata a gabatar da komai


ina ta damanka.... but ka bani excuse kuma na karba,na bari sai da aka ragu,don
nazo.naga kamfanin mijina laifi nayi?"

A hankali iman ta juya idanunta zuwa sashen da takejin muryoyinsu,lamin


na tsaye daga qofar office dinsa,sanye da suit da yayi amfani dasu a wannan rana
iri daya da ya sadiqu ash da da ratsin orange dan kadan,suit din da sukayi masifar
tafiya da imanin mutane,sai samhan tana tsaye itama tana fuskantarsa,sanye da Dubai
abaya zoom material,ta yane kanta da mayafin abayar,an qawata mata fuskarta da
makeup,da alama takanas taje akayi mata ita,qafafunta sanye da high shoes masu
tsinun dunduniya,qaramar jaka ce a hannunta dakuma wata leda wadda ke dauke da gift
data shirya musamman saboda lamin din.

Dauke numfashinta iman tayi,ta sake dage takunta da kyau,qirjinta na


bugawa saboda kusancin data gani tsakanin lamin da samhar,taku biyu idan ya qara
yana iya hade tazarar dake tsakaninsu,saidai bata kai ga cimma nasarar barin wajen
ba kamar ance masa ya juya suka idanunsa ya sauka a kanta,yasan tabbas ta gansu
shida samhan

"Zonan" ya fada a dake cikin salon bada umarni,maganar da taja hankalin samha
itama,saita iman din ta tsaya cak ba tare data waiwayo ba

"Rakata ta gaida inna" ya fadi yana sanya card dinsa jikin qofar office din zai
bude.

Idanun samha qur akan iman sanda take qarasowa inda iman din
take,wadda tunda ta tsaya bata juyo ba,daga sama har qasa take qarewa dressing
dinta kallo,wani abu taji ya caki zuciyarta me kama da kishi,me yasa tunanin yin
irin wannan shigar bai shiga kanta ba?,ta tambayi kanta,dressing me aji wanda kana
kalla zai gaya maka mamallakiyar shigar tasan me takeyi.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 54

Tare suka jero,saidai girman kai ya kama kowa,kowacce ta gaza yiwa 'yar
uwarta magana,kishi yana cin zuciyar kowaccensu,yayin da samha tata zuciyar ta cika
da qyashi irin na kyan da iman din tayi,zuciya nata raya mata yanzun qila tare suka
taho da ita a mota guda,wala'alla ma ita ta zauna a gaban motar,wannan kwalliyar
qila shi ya fara ganinta kafin kowa ya gani,yanzu da wannan kyan nata suke rayuwa
gida daya dashi?,gaskiya batajin zata juri barin iman din ta dinga zuwa mata gida
duk sanda sukayi aure da alameen din,duk da itama me kyau ce,amma batasan me yasa
kyan iman din ya tsole mata ido har haka ba,tana da azababben kishi,ita kanta tasan
da haka,tayi.mamaki ma da yazo mata da sauqi akan iman din,bata iya furtawa,saidai
yana cinta cikun zuciya qwarai da gaske,wala'alla ko don ta lura basa wani good
time da alameen dinne yasa bakinta ya iya har yayi controlling kansa ba.

Daga qarshe shawarar zuciyarta tabi,wadda ta kwabeta kan ta daure


zuciyarta ta tanka mata

"Dake da ameen bansan wanda yafi wani miskilanci ba,duk miskilancin da ake fadin
ina dashi sai nazo na tarar da wani kuma daban" ko kadan maganar tata bata burgeta
ba,saima haushinta daya ninku cikin zuciyar iman din,wannan wanne irin rashin ajine
da xaki biyo mutum cikin taro irin wannan,da familynsa a wajen da komai,bayan
gidansu da kika tattaka da qafafunki kikaje,wannan duka bai isheki ba

"Innar tana tacan" ta tsaya daga baya tana yiwa samha nuni da wajen da innar
take,saita qarasa jikin glass na ginin saman ta tsaya,tana ci gaba da kallo
farfajiyar kamfanin,inda tsirarin mutane da suka rage suke ta kai komo,wasu na fita
wasu na shigowa,saidai fiye da rabin hankalinta ba a na wajen yake ba,ya lula
duniyar tunani.

Zafi sosa zuciyarta take mata,tanata qoqarin controlling kanta ne,tana ta


hadiye abubuwa, bataso su taru suyi mata yawa,tana fata Allah ya cire mata amin
daga ranta kwata kwata,kwana take ta kuma wuni tana addu'a,batason ta nacewa kanta
da damuwa kan abunda ba zata samu ba,batason zuciyarta ta dinga wahala akan abunda
tasan yayi nisa daga gareta,bataso ta dinga damuwa da tarayyar samha da amin,tanaso
wadan nan abu uwan su fita daga ranta ko xata huta,saidai babu wani ci gaba da take
gani kan abunda take roqo din,ta dai sanyawa ran nata lokaci ne.

Ruri wayarta ta fara yi,a sanyaye ta daga tana kallon screen din
wayar,dr ahmad ne,ba zata iya share kiransa ba,saboda yana matuqar damuwa da
al'amuranta da kuma bata kulawa ta musamman.

Ita tafara masa sallama,ya amsa mata yana tambayarta yanayin taron,yaso
zuwa qwarai amma ranar yana da patient da zaiyiwa theatre har mutum uku,dole ya
haqura

"Alhamdulillah,taro ya tashi lafiya" ta bashi amsa a taqaice

"Ma sha Allah,Allah yasa albarka"

"Ameen,thanks" shuru ya ratsa wayan,cikin zuciyarsa yana ji muryarta batayi masa


yadda ya saba jinta ba,kamar tasan tunanin da yake kenan tace dashi

"Zamuyi waya anjima please"

"Alright, take your time and be safe"


"Thank you" ta sake amsa masa tana katse wayar,a yanzun bata jin zata iya wata
doguwar magana,shi yasa tayi masa sallama.

Numfashi ta fitar daga bakinga hade da iska,tana ci gaba da kallon


waje,cikin jikinta takeji kamar ana kallonta,idanun kuma ya wuce na mutum daya,sai
ta maida hankalinta ga wajen,tana tsammanin daga canne wasu suke hangota.

"Alameen" muryar yaa baraka ta bayyana daga bayansu,da sauri gaba dayansu
suka juya,babu wanda yasan da tsaiwar ya baraka a wajen,iman ta sauke kallonta ga
alameen dake tsaye a baya ta wanda a yanzu ya waiwaya ga yaa baraka,saidai akwai
tazara sosai a tsakaninsu,batasan tsahon yaushe ya dauka a tsayen ba,kamar yadda
gaba dayansu basusan tsayin lokacin da itama ya barakan ta dauka a tsayen ba.

Dukkaninsu suka taka zuwa inda take tsaye

"Me kuke a waje?,innar aka bari ita daya a ciki?" Shafa kwantacciyar sumarsa mai
kyau da qayatarwa yayi

"Ba ita kadai bace,tana tare da baquwa"

"Baquwa kuma muka samu?...." Bata tsaya jin amsarsa ba kuma sai ta shigo da wata
maganar

"Wannan matattakalar taku badai yawa ba,yanzu kullum haka zaku dinga dawafi daga
qasa zuwa sama?" Sai da sukayi murmushi gaba dayansu,dai dai sanda suka fara takawa
zuwa ciki,suka sanya yaya barakan a tsakiya

"Akwai na'uran dake ragewa mutum tsahon tafiya,daga sama ta kawoshi qasa,ko kuma
daga qasa ta kaishi sama"

"Ayho,koda naji" daga haka kuma sai hirar ta koma tsakaninta da iman din
kawai,kusan wasu abubuwane da batasaji game da iman din ba take tambayarta,kamar
karatunta da sauransu,a haka suka qarasa inda innar take.

Kanta ta dago daga hirar da sukeyi da samha tana amsa sallamar


tasu,shigowar tasu a haka sai wani abu ya mintsini zuciyar inna,ta bisu da kallo a
yadda suka shigo din,tana jin inama inama,inama ace.....

Tunaninta ya katse sanda yaa barakan take zama tare da mitar barin innar
ita daya,murmushi inna tayi

"Basu barni da kadaici ba ai,ga mufida muna tare,daga baya ma saiga diyata kuma ta
shigo" duba sashen da samhan take yaa baraka tayi,kasancewar batasan wacece ba
batace komai ba,dakin ya dauki shuru kamar qiftawar tsawa,inna ta san lamin din
nada kara,bazaya iya gayawa yaa barakan wace samha ba,amma tayi zaton iman zata
gabatar da ita sai taga wayarta ma take dannawa kamar bata cikin dakin,tilas
tadanyi gyaran murya

"Baraka,gafa surukar tamu,yarinyar da ameenu zai aura in sha Allahu" da hanzari ta


kalli gefanta inda samhan take,a sannan ta sadda kanta qasa tana kuma dan murmushi
dake nuna kunya

"Too ikon Allah"abunda ya barakan tace kenan,bayan ta gama amsa gaisuwar samhan
dakin shuru ya sake dauka,sai inna dake qoqarin jefowa samhan hira saboda kore
zaman shurun nasu,duk wanda ya kalli fuskar ya barakan yasan ta canza,ba haka
yanayinta yake a dazu ba,saidai bata ce komai ba,amma tana biye da hirarsu da inna.

Lamin ne ya duba agogonsa bayan ya sauke wayarsa da aka kirashi

"Inna ko zaku wuce kada ku gaji da zaman,an kai malam yaron daya kaishin ya dawo"
"To babu laifi,hakan yayi" daga haka suka miqe suka fara shirin tafiyar.

Yaa barakan tana tason yin magana da lamin,saidai samhan tana maqale dashi
sanda suka fito gaba daya,tana masa magana qasa qasa,har suka qaraso bakin mota.

Inna lamin ya budewa gaban motar,sai taqi shiga tace samha ta shiga,tadan
doje kadan kan innar ce zata shiga,bata sake jan zancan da tsaho ba ta bude ta
shigan,ya baraka ta fara shiga baya,sai iman sannan samhan,yaa baraka ta leqa ta
window

"Yau komai dare idan ka dawo ka nemeni,inason yin magana da kai"

"To in sha Allah" ya amsa mata cikin girmamawa yana rufe murfin motar.

Cikin motar ma dif kowa yayi,samha aka fara saukewa sannan su aka qarasa
gida dasu.

Kamar jira ya barakan take,suna shiga parlor abinda ta soma shine


qorafi,a sannan iman tuni tayi daka,saboda gajiyar da takeji a jikinta.

"Yanzu inna,ta yaya kuna gani kuka bar aminu ya dauko wannan yarinyar?" Dubanta
inna tayi tana cire abun hannunta

"A iya abunda ido da kuma bincike ya nuna bata da wani aibu,tuni malam ya gama duk
wani bincike a kanta,abunda yasa ma yace kizo din lallai,ina kyautata zaton jibi
za'a kai kudaden aurensu shi da sadiqu.....dana 'yaruwarsu ma gaba daya" zama ya
baraka tayi,gaba daya wuta ta dauke mata,ashe ita abunda take lissafi tattare dashi
da kuma iman din ba haka bane,yaya amin din zai aikata wannan gangancin da kuma
katobarar?

"Amma binta,tsakanin da Alla ta yaya gida bata qoshi ba za'a bawa dawa?,har iman
din bada ita za'ayi?" Murmushi kadan inna tayi,inda ita ke da ikon sarrafa
al'amuran zuciyar kowannensu,da tuni ta gama da tabbatarwa ameen iman

"Dama ce aka bawa kowa ya zabi abokin rayuwar da yake ganin yafi dacewa dashi
baraka,baka isa sauya abunda Alla ya rubuta ba" kai ta girgixa,a karon farko da
takejin zata ja da wani hukunci akan lamin din tsahon shekaru sama da ashirin da
uku

"Zanyi magana da malam,wannan ba abunda zaa zuba idanu bane ace haka Allah ya tsara
bane,a fara jarrabawa,idan bai yiwu ba sai ace haka Allah ya tsara din,ni zanga
malam din da ameenun ma gaba dayansu"

"To Allah yayi jagora" abunda inna ta iya fada kenan saboda kara,uwa uba can qasan
zuciyarta sai ya cika da fata da kuma burin cika da tabbatuwar abinda baraka ke
hari.

*IMAN*

Tun bayan shigarta daki Allah ya taimaketa barci me nauyi ya dauketa,baccin


daya dauketa lokaci mai tsaho,koda ta farka taga lokacin data share tana baccin
bata damu ba,saboda tasan tana fashin sallah,sannan babu wani sauran aiki cikin
gidan,tun kafin su fita ta gama komai na gidan,saita dan yaye labulenta tana hangen
waje,sararin samaniya har tayi duhu wanda ya gauraya da ragowar hasken magariba da
bai gama dusashewa ba,ta saki labulen a hankali ta kuka zarce bandaki.

Ruwa mai dumi sosai ta saka tayi wanka,ta fito tana qamshin shower gel
dinta mai taushi,gaban madubi ta tsaya,ta tsane jikinta ta mulkeshi da mayukanta
masu kyau da tsada,wanda zuwa yanzu sun zame.mata jiki ta saba amfani dasu,sun
karbeta matuqa,qamshinsu kuma ya zauna sosai a fatarta,ta gyara gashinta shima ta
feshe shi da hair mist,sannan ta shirya cikin wasu ready made data siya a wani
kanti,riga budadden hannu da straight skeet,kayan basu da nauyi sam,shi yasa take
sonsu takejin dadin sakasu,cikin kayanta ta duba hijabi qarami da bai wani sauko da
yawa ba ta zura,zaman dakin ya isheta,don haka ta qarasa inda wayarta take ta dauko
tana dubawa,saqonni da kuma miscal masu yawa,wanda batasan dasu ba,sabida saka
wayar da tayi a silent tun sanda zata kwanta,saita zarce da fita waje kawai wayar
na riqe a hannunta.

Ba kowa cikin parlor din,amma ta dan jiyo murya daga sashen dakin
inna,tunawa da tayi yaa barakan tace tanason ganin ameen komai dare yasa ta yanke
fita can bayan gidan ta zauna abinta,don babu mamaki shi dinne suna tare,itako
batason duk wata harka da zata hadata dashi,a yanzun lallaba rayuwa da kuma
zuciyarta takeyi.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 55

Wani yanayi me haifar da walwala ne ya sauka a zuciyarta sanda ta fita


qaramar harabar tasu takuma zuqi fresh air dake kadawa,iska ce mai wani irin taushi
a cikinta,kamar ta farkon shigowar damina,idanunta suka sauka a hankali kan motarsa
dake fake adan filin gidan nasu,tabbacin ya dawo kenan,dole kam ta kama kanta
itama,saita kalli hagunta da damanta,tana shawarar daga wanne side zata
zauna,karkata zuciyarta tayi da bangaren hagunta,wanda yake daura da wajen ajiyar
motar sannan kuma ventilation ne da suka jere tukunen shuke shuke,ba kasafai aka
fiya zuwa wajen ba,saboda daga nan zai sadaka da qofar babban parlor dinsu ameen
din dake dauke da dakunan baccinsu,wajen yana da dan tsaho,hakan yasa idan kana
daga ciki ciki ko daga baki baki ba zakasan da wani a farko ko qarshe ba.

Tana takawa tana duba saqonnin dake wayarta,kusan fin rabinsu daga Dr
Ahmad ne,wanda yaketa mata bangajiya da kuma alhinin rashin samunta a waya,har ta
qaraso wajen,ta daga ido taga plastic chair guda daya a wajen,takai hannunta guda
daya da bai riqe da wayar ta niyyar jawota.......sai kuma ta tsaya cak,cikin
sakanni kuma zuciyarta ta balle da wani irin gudu,qarfin jinta ya qaru,kamar yadda
harbawar jinin dake jikinta ya birkice ya sauka daga kan tsari,fitar muryar alameen
din na dauke da wani saqo da bata taba ayyana jinsa daga ba daga gareshi

".............duka ba haka bane yaa baraka.....kuma nima nasan da wannan,amincewar


kowanne sashe shine jigon zamantakewa,sannan na roqeki kibar wannan maganar, let
bygone be bygone,abunda ya wuce ya riga daya wuce,tun a wancan lokacin na shafe
babinta daga raina da zuciyata gaba daya,na maidata matsayin wadda muka fito ciki
daya,koda bata taba auren wani ba a yanzu bani da sha'awar aurenta kwata kwata bare
ta taba auren wani, I can't.....bazan iya ba yaa baraka,infact ma a yanzu dai bana
son iman kwata kwata,soyayya dai irin ta aure,kiyi haquri,ki kuma yi qoqari ki
fahimceni,bazan iya ba" so take ta zauna din ko zata daina jin abunda takeji amma
kuma batason taci gaba da sautaren maganganun dake fita daga bakin ameen
din,kalaman da sukayiwa kunnuwa da zuciyarya matuqar munin da ba zata iya fasalta
kamarsa ba,cikin juriya da jajircewa ta fusgo numfashinta da yake qoqarin yi mata
wahala,ta cira qafafunta ta kuma tunkuda kanta da kanta zuwa gaba da sauri da
sauri.

Cikin taimakon Allah ta lalubi hanya tas ta maida kanta zuwa daki,ta
wurgar da wayarra ta bude bandakinta,ta kuma saki rufa afamfo ta dinga tara
tafukan.hannuwanta tana watsawa a fuskarta,bata damu da yadda jikinta yake jiqewa
ba,illa dai hucin da takeji.kamar yana fita daga saman fuskarta duk sanda ta watsa
ruwan,a hankali a hankali ta soma jin na'urorin jikinta suna dai daita,saita kashe
famfon,ta kuma ja da baya ta sulale a hankali zuwa qasa,a lokacinne kuka ya samu
hanyar fita.
Tayi kuka kwatankwacin kukan datayi sanda ta gane waye bassam,waisu dama
maza basu da alqibla?,waisu maza dama idan ka kamu da soyayyarsu baka tsintar komai
face wahala da tashin hankali?,dama haka soyayya take?,me yasa soyayya bata karbeta
ba kwata kwata,me yasa take wajigata?.

Me yasa zaki tsaya fana wahal dake tana wajigaki?,ki karbeta aduk yadda
tazo miki kawai,idan ta barki kema ki barta ki huta,ki maida hankali da tunaninki
ga barayin da ake da buqatarsu,a yanzu komai yazo qarshe tsakaninki da ya lamin,kin
samu cikakkiyar amsar da kika jima kina lalubenta,meye kuma yayi saura?,a nan wajen
cikin hali na zafi da quncin zuciya zuciyartata ta yankewa kanta da kanta
hukuncin,hukuncin da takejin koda bataso xata tilasta kanta,ta tanqwara kanta ta
karbeshi a haka,ta miqe ta zare kayan jikinta da suka jiqe,ta fito ta canza wasu
cikin wani irin yanayi na siyawa kai jarumta,da son danne qunci da halin tashin
hankali da zuciya ke fuskanta.

Saqon qarshe data fara dubawa taci karo da maganganun ameen ta koma ta
sake dubawa

_"Ki shaidawa malam,gobe idan Allah ya kaimu su kawu zasu zo,sai a basu lokacin da
yafi dacewa,kiyi mana addu'a,Allah yasa wannan shine matakin ingantacciyar rayuwa a
garemu gaba daya"_

Da qwarin gwiwarta ta maida masa amsa,tana jin wani confidence yana


shigarta sanda rauni yake qoqarin rinjayarta,ta ajjiye wayar gefanta itama ta zauna
cikin matuqar kasala da mutuwar jiki,lokaci yayi da zata ajjiye komai,ta haqura
itama,duk da tasha gayawa kanta wannan kalmar,amma tana saka ran wannan snine karo
na qarshe da zata gayawa kanta haka.

Turo qofa mufida tayi ta shigi,ta ganta ta mudubin dakin don haka bata
juyo ba

"Ya iman.....ya ameen yace akai masa abinci" ta mudubin ta zubawa yarinyar idanu

"Akai masa abinci,wato amfaninta kenan kai abinci?,me zaiyi da abincin da hannuwan
wadda baya so suka dafa?,daga yau ta yanke,ta kuma canza,ta tashi daga wannan iman
din zuwa wata daban" tayi dukka wannan tunanin da hukuncin cikin zuciyarta

"Kice musu a kwance nake,a kishirya food flask din a nutse kikai musu da daya da
daya,zaki iya"

"Tom" yarinyar ta fada tana dan kallonta,sabida yadda taga yanayinta,batace dai
komai ba ta juya ta fita sannan taja mata qofar.

Ba zata iya fita tayi magana da kowa ba,don haka taja wayarta ta turawa ya
sadiqu text kan saqonnda dr ahmad din ya bayar,bayan ta tabbatar ya tafi saita
kashe wayar gaba daya,ta hada da qwan dakin gaba daya ta kashe ta koma ta kwanta
lamo,kamar ba daxu dazu ta tashi daga kwanciyar ba,bawai barci takeji
ba,a'ah,tanason ta tattara duk wani courage nata da zata fuskanci rayuwarta da
mutanen da take rayuwa dasu daga gobe idan Allah ya kaimu.

*********Da sakakkiyar fuskar dake boye da damuwa fal bayanta ta fita ta kama dukka
wata sabgar data saba,kamar kunnuwanta basuji komai ba,kamar kuma babu wani ciwo
cikin zuciyarta,ta yadda ba shakka duk wani abu daga tilastawa kanka yinsa zaka
aikatashi,koda zuciya da gangar jiki bata gamsu da hakan ba.

Qarfe sha daya na rana tana dawowa falon xata ciri charger dinta datayi
charge da safe ta tadda yaa baraka na fitowa daga dakin data sauka,'yarta na tsaye
saqale da jakar kayansu
"Ke kuwa baraka,aiko azahar kya bari kikai idan su malam sun dawo daga kai kudaden
auren nan" baki ta tabe

"A'a...a'ah,ai gwara na tattara komatsaina,tunda na fuskanci gidan yanzu ya zama


gidan marasa son gaskiya,zamana kuwa bazai amfana komai ko ya rage komai ba" iman
dake takowa parlor tasan komai,saidai babu wanda yasan ga sani din,cikin dauriya ta
kalli badi'a

"Ke badi(haka take kiranta wasu lokutan)yanzu ko dan zaman nan ma na sati daya kiyi
mana baxaki iya ba,qafarki qafar yaaya?" Murmushi badi'an tayi

"Makaranta wallahi yaa iman,yanzu ma kinga don a weekends muke,amma dai in sha
Allah wataran zanzo" kai ta jinjina tana fidda dan murmushi

"Muna zuba ido....ya baraka da sauri haka?" Murmushi tayi

"Kada ki damu diyata kinji,zan dawo ko don saboda ke,bawai na tafi kenan ba" tayi
maganar duk da tasan bawai lallai iman da duk wanda ke wajen ya fahimci abinda take
nufi ba,hakan kuwa yake,saidai akace babba babbane,inna ta fahimci inda maganarta
ta sanya gaba.

Tsaf murmushin fuskarta ya dauke sanda ta hangi shigowarsa,sanye cikin


jallabiyya milk color mai gajeran hannu,duba daya zaka yiwa fuskarsa ka gane yana
tsaka da barci ya taso,saita janye jikinta daga wajen,ta zagaya wajen chargenta ta
cira,ta dawo daga bayan yaa barakan tace

"Yaa baraka zan shiga wanka,ina da makaranta yau,Allah ya tsare hanya,ya huta
gajiya,Allah ya qara zumunci"

"Ameen imani" ta amsa mata cikin kulawa da jin dadi,ta yiwa badi:a magana kan ta
biyota ta karbi saqo,batako waiwayi inda yake ba tayi gaba,tana jinsa shima yana
qorafin ta tsaya su malam su dawo,ya karbi motar daga hannun sadiq,koda bai kaita
jigawa ba ko wudil ne ya ajjiyesu,saidai fir taqi tace ko minti guda bata qarawa
cikin ikon Allah.

Wani abu yadan tarar mata a wuya,ya sadiq ne kenan ya tafi kaisu,saidai
da qarfi tayi qoqarin kawar da abun,ta duba wani seat na turaren jiki sabulu da
spray ta bawa badi'a,dadi sosai ya kama badi,tayita maga godiya ta fito da abunta.

Da idanu ya kalla kwalin bayan badi'a ta fito dashi tana nunawa yaa
barakan,yasan kudinsa sarai,don ya taba siyawa samha gift dinsa,saidai batayi
amfani dashi ba,sabida tace scent din bai mata ba,shi kuma ya siyo ne saboda irin
launin qamshin da yakeso kenan,sai yace ta barwa suby'a ya canza mata da choice
dinta.

Bata sake fitowa ba har sai data kammala shirinta na fita zuwa
makaranta,tayi kyau cikin fararen kayansu data dora baqar after dress akai,komai na
iman din mai kyau ne da sanyi kamar dai yadda take ada can,wannan yanayi nata yana
ja mata farinjini da masoya masu yawan gaske a cikin makarantar dama
wajenta,sauqinta daya,bata bada fuska,miskilancinta idan ya motsa ba zaka taba cewa
wannan iman din bace.

Komai take a ranar dauriya ce kawai take yinta,amma bata da wani kuzari ko
karsashi,a duk sanda ta tuna a yau za'a bada ita ga wani,a yau kuma za'a bada
alameen ga wata sai zuciyarta ta buga,saidai tanata gayawa kanta, she's ready to
face any challenge......zata kuma iya jurewa,zata iya dauka.

Daga makaranta bayan ta gama duk abinda takeyi kasa wucewa gida tayi,sai ta
wuce gidan kawu muntari wajen matarsa,mutuniyarta ce qwarai,ta tarbeta kamar koda
yaushe,suka gaisa ta tambayi kawu muntarin

"Kawunki har yanzu bai dawo ba,tun daxun dai daya shigo bayan sun dawo daga kai
kudaden auren yayanki,sai kuma ya sake fita,yace malam yayi masa waya ya dawo,yaron
dake nemanki yace wakilansa na hanya.....to tun lokacin dai bai dawo ba".

Idonta kawai ta lumshe,zuciyarta na gaya mata shikenan,ta faru ta


qare,alameen ya zama alqawarin wata,kamar yadda itama wala'alla kawo yanzu ta zama
alqawarin wani,sai kuka tayi maza ta kauda wannan tunanin da kuma duk wata fargaba
data taso mata,sanda zuciyarta ta tuna mata da kalamansa,kamar a sannan yake gayawa
yaa baraka su.

Tana idar da magriba tayi haramar tafiya,dai dai sanda kawu muntari yayi
sallama ya shigo gidan,saida gabanta ya fadi data tuna daga inda yake,suka
gaisa,yayi mata Allah ya sanya alkhairi sannan sukayi sallama ta wuce gida.

Daga baya baya tasa me napep ya ajjiyeta,ta qarasa takowa a qafa,idanunta


kan motar dake fake a qofar gidansu,data duba da kyau sai taga motar lamin
dince,kuma suna tsaye a jiki shida ya sadiqu suna maganganu,ta wucesu a hankali ba
tare data ji ko ta saurari abunda suke tattaunawar ba.

Da idanu yabi bayanta sanda take giftasu ta gefe,cikin takunta a


hankali,sai kuma ya lumshe idanunsa yana janyesu,ya sake maida hankalinsa ga sadiq
sukaci gaba da maganar da sukeyi yana jin wani baqon abu cikin zuciyarsa,wanda bai
iya tantance meye ba.[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 56

Tunda ta shiga cikin gidan taketa tattalin farincikinta,da wankanta da cin


abinci duka tanayi ne cikin son share kowanne tunani da dora sabuwar rayuwa bisa
tsakiyar zuciyarta.

Tana dakin malam ya aiko kiranta,kamar wancan lokacin batasan ba ita


kadai bace sai data shiga rumfar tasa,suna zaune sadiq din da ameen,a wannan karon
wayar ameen din tana a tsakaninsu,da alama wani abu suke kalla,shigowarta kuma bai
canza komai ba,sai ta rabesu ta isa ga malam ta yiwa kanta mazauni ta fara
gaisheshi,ya amsa mata cikin kulawa.

"Alhamdulillah,kowannenku akwai alqawarin aure akansa nan da watanni shida,mun


sanya hakane saboda kusan kowanne bangare a shirye yake,iman....kece zakiyi
haquri,don ba lallai yayi dai dai da sanda zaki gama jarrabawarki ba,saiki addu'a
Allah yasa haka ne yafi zama alkhairi"

"Ameen" ta amsa idanuwanta a qasa,sannan kuma ta miqe tabar dakin ba tare data bari
ta kalli koda sashen da yake ba bare yaga idanuwanta.

*********Yanayine mai matuqar wahala wajen jureshi,yana da matuqar daki tsanani da


kuma wahala me yawa a cikinsa,ba qaramin abu bane kaso mutum so mai yawa,baya ga
yawan kuma yake cike da zallar gaskiya da sahihiyar soyayya,kana sanya ran samun
koda kwatankwacin abinda kakeji ne a matsayin tukuici da sakamako......sai kuma ya
zamana abunda zai dawo maka shine dauke kai.....rashin nuna halin ko in kula da
yanayin da kake ciki.

A duk da hakan ta dinga dorawa hadi da lallaba rayuwarta,ta kuma rungumeta


a yadda tazo mata,tayita tasa al'amuranta a gaba tana watsa damuwarta baya,saidai
duk da hakan babu wata nasara me yawa data ci,domin kuwa a kwance damuwar take a
qasan zuciyarta,duk wata walala da fara'a dake saman mu'amalarta ta yau da gobe
fake ce,wato jabu.
A hankali ranakun suka dinga zuwa suna wucewa fewww kamar ana
jansu,watannnin da malam ya sanya na aure suka dinga qaratowa,a lokacinne iman din
ta dinga wata rama a tsaye tana qarewa,saidai hakan bai hanata duk wasu sabgogi
nata ba,musamman makaranta da karatunsu ya sake daukar dumi,dama bahaushe yana cewa
idan aski yazo gaban goshi yafi zafi,sau tari inna na binta da kallo fana qiyasta
ramar datayi,sau daya ta kwatanta yi mata magana tace mata

"Inna,makarantar nan babu sauqi,don dai kawai burina ce da tuni na barta,bakiga


karatun dake gabanmu ba inna da sai kin tausaya min" da wannan amsar ta fuskanci
inna,ta qyaleta akan hakanne amma badon ta gamsu ba.

A lokacinne sadiqu yayi mata zancan motarta wadda ta taho da ita daga gida
bassam,motar da tun a sannan take ajjiye,cewa tayi a tattara a saida komai daya
danganci gidan bassam din,saboda batason koda tuna cewa ta taba rayuwa dashi,aka
siyar din kuwa,saiga kudi tarin yawa,ya buqaci jin me take so ayi mata dasu,tace ya
tarkata kudin kawai ya bawa inna ta ajjiye mata,saboda a yanzun bata da nutsuwar
sanin me za'ayi mata dasu.

A nutse sannan kuma a hankali shirye shirye suka gudana cikin gidan na
auren cikin ruwan sanyi,bata data cewa kamar yadda bata da wani feeling akan
auren,dukkan wata kulawa da tattali tana samunta dari bisa dari wajen dr ahamd,ta
yadda gwanine ta fannin soyayya,ta kuma yadda da cewa likitoci ba baya ba wajen iya
soyayyar, they are very romantic,saidai kwata kwata babu wata gamsuwa ko burgewa
tattare dashi a ranta.

Hutun da suka samu juma'a asabar da lahadi taji tana sha'awa matsawa daga
bigiren da take izuwa wani,tayi gajeran tunani akai,nijer yayi mata nisa,hakama
maiduguri,sai ta yanke zuwa jigawa,gurin data jima bata je ba,duk da cewa garin na
daya daga cikin garuruwan da take qauna,sai faduwa tazo mata dai dai da zama,dama
kuma yaa baraka tana yawan qorafin yadda ta zubar da ita gaba daya.

Ta sanarwa inna batun tafiyar,inna ta gayawa malam,babu wanda ya


hanata,saboda gidan yaa barakan kamar gidane a wajensi gaba daya,a ranar tahau
shirinta,ta kuma kwana dashi,washegari qarfe goma na safe ta gama komai,ta fidda
qaramar jakar hannunta ta matafiya,mayafinta na rataye bisa kafadarta batakai ga
yafawa ba ta fita parlor.

Mutum na farko data fara gani alameen dinne,sanye da shadda wadda aka
yiwa dinkin zamani,yana zaune saman carpet,ya tanqwashe qafafunsa yana cin funkaso
da miyar da tayi da safen,hularsa na aje gefe,wayarsa kuma na saman hular a
ajjiye,sai muqullin motarsa daga qasa daban shima.

Kamar ko yaushe gabanta ya doka,wani sassanyan kyau me aji yake


fitarwa,sumarsa dako yaushe take qara kyau tayi kwance tana ta qyalli,tadan saci
kallon hannunsa,har yau bataga mutum mai tsananin gayu da tsafta dake cin abinci da
hannu ba irin ameen ba,yayi masifar iyawa kuma,abun sai ya zama wani ado,kamar irin
yana cin abincin ne in a stylish way kuma gangan.

"ina kwana" ta gaidashi ba tare data kalleshi kota tsaya ba tana takawa
zuwa gaba,shima hankalinsa na ga tv ya amsa mata yana ci gaba da cin abincinsa a
nutse.

Qaramar ajiyar zuciya inna ta sauke a fakaice tana fuskantar iman

"Har kin fito?"


"Eh inna,inaso na isa ne kafin rana tayi zafi,kinga ya baraka da zumudi harta
kirani wajen sau biyu fa wai na taho kuwa?" Tafada murmushi na subuce mata,kyawawan
farare kuma jerarrun haqoranta suna bayyana.
Sunan ya barakan data kira yadanja hankalinsa,da idanu yadan dubeta sanda
blue eyes dinga kega inna,amma yana iya hangen fuskarta tar,fuskar data qara haske
amma ta dan sirance kadan,a yadda yake kallon wajen ba zaka taba zaton ita yake
kalla ba,saboda tsabar qwarewa wajen iya basarwa,jigawa kenan zata je?,amma ko jiya
da daddare sunyi waya mai tsaho da ya barakan amma bata gaya masa ba,hakanan ita
dinma jiyan daya dawo ya taddasu parlor amma baiga alamun zata wani waje ba.

Zaren tunaninsa ya katse sanda inna ta miqe tana cewa

"Malam yasan kayarsa,shi yasa kafin yafita yabar miki saqo yace koda zaki tafi
kafin ya dawo din"

"Wallahi inna,banaso rana ta take din nan ban isa ba" tayi maganar tana kallon
agogonta dake daure a tsintsiyar hannunta,daga bisani kuma ta sauke,ta maida
dubanta ga mufida,wadda taqi magana tun daxun,cikin qaramar dariya tace

"Wai har yanxu fushin ake dani saboda nace bani zuwa dake?,yanzu banda abunki
mufida.....kwana uku fa kacal zanyi na dawo,ta yaya zamu yoye mubar inna ba
mataimaki?,ki bari na miki alqawari kuna hutu zan kaiki,indai ya baraka ce tana
maraba da kowa" sai a sannan ta saki ranta.

Inna ta dawo da saqon tana miqa mata ya miqe shima,ya dauki dukka
kayansa

"Zan wuce inna,sai na dawo"


"Har ka gama?"
"Eh ya isa haka"

"To Allah ya bada sa'a,a dawo lafiya,Allah ya tsare" ta rakashi da kyawawan


addu'o'inta kamar yadda ta saba gami da fatan alkhairi,sannan ta maida hankalinta
ga iman tana sake mata bayanin saqon malam da kuma kudin motar daya bayar a bata.

A hankali take takowa zuwa harabar gidan,tana tunanin tashan da zataje ta


samu mota mai kyau wadda kuma zata tashi da wuri,ta buda qofar gidan ta fita tare
da fatan samun abun hawa da wuri,saboda unguwar tasu wani lokaci wahalar abun hawa
akeyi.

Batayi nisa ba taji nishin mota daga bayanta,bata damu ta juya ba don
tasan adai dai take ba sama hanya take tafiya ba,motar na gotata kadan tayi
parking,sai a sannan ta dubi motar.

Ya ameen ne,kafin ta qaraso taga ya bude front seat,hakan yana nufin kenan
ta shiga. Tsaiwa tayi sanda ta qaraso wajen,saboda murfin motar ya rufe hanyar da
zata iya wucewar

"Shiga mu tafi" taji ya sake fada,ta kalleshi idanuwansa na kan hanya,fuskarsa kuma
sam babu alamun fara'a ko kuma wasa,lallai yau akwai damuwa,idan batayi wasa a yau
din ciwonta zaisha sabon fami,ita da ameen din a mota daya?,da kuma kusanci irin
wannan?,bata da sauran option face shigar,ta janyo murfin motar ta rufe,ya dage
dukka gilasan sama tada motar ya fara gangarawa a hankali,sannan ya saka hannunsa
ya kunna ac madaidaiciya yadda ba zaka takura ba.

Shuru ne ya ratsa cikin motar,sai wani slow music dake tashi can qasa cikin
qaramin sauti,tafiyarsu ta dauki kusan mintuna goma,sannan lallausar muryarsa mara
son hayaniya ta motsa

"Da gida yaa baraka zaki baki gayamin ba?" Yayi maganarne idanunsa nakan
kwalta,hannunsa daya kan sitiyarin motar,daya hannun kuma yana zagaya labbansa da
'yan yatsunsa.
Yadda yayi maganar koda bata kalleshi ba tasan 'yan sarautar ne suka motsa
masa,tafi kowa sanin halayyarsa ciki dabai,sau da dama tana iya gane mood dinsa
daga sound dinsa ba tare data kalleshi ba.

Bataga dalilin da yasa saboda zata wani waje sai ta gaya masa ba,kamar
hakan a yanzun bashi da alaqa da rayuwarta.

"Na zaci ka sani" itace amsar data iya bashi kawai,saiya waigo ya dubeta ya kuma
maida kansa ga titin duka cikin abunda baifi second uku ba,kafin yace komai wayarsa
ta dauki qara,yadan saci kallonta,sai ya sauke hannunsa guda daya ya latsa wayar ya
maqalata a kunne

"Wa'alaikumussalam....." Yafada da muryarsa mai nauyi a wasu lokutan,murmushi ya


danyi,abunda yasa iman juyar da kanta sosai ga taga tana tabe baki

"Alhamdulillah" ya sake shuru kafin ya kuma cewa

"Zan kiraki,ina tuqi ne..... okay,nima haka,byee" ya zame wayar a hankali ya


maidata inda take,bai kuma cewa komai ba,itama bata sake magana ba,don dama bata
son magana a tsakaninsu,taci gaba da kallon titi.

Kamar zatayi magana sanda taga yanata wuce tashoshin motar daya dace ace
ya sauketa,amma kuma daga bisani itama sai ta shareshi,tunda yafi kowa sanin ya
daukota,tun tana saka ran zai sauketa a wata tashar qila a gaba har ta debe
tsammani,saboda sun fara barin kano,sun wuce tamburawa ma,don haka saita zaro
wayarta kawai ta kunna data ta shiga WhatsApp.

Tayi chart mai yawan gaske da qawaye da kuma dangin da take mu'amala
dasu,tanata kasa kunne taji yace sauko amma shuru,sannu a hankali sai gasu a garin
wudil,ya gangara gefan titi,ya shiga wani layi,tabi layin da kallo tana mamakin
yadda aka samu layi me kyau da girma haka cikin qauye,saika dauka cikin unguwar
gadon qaya dake birnin kano kake,baiyi nisa a layin ba taga ya tsaya,ya dauki
wayarsa yayi kira

"Gani na qaraso..... okay.... okay" wayar ya ajjiye ya sake taka mota zuwa
gaba,sannu a hankali sai gasu a qofar wani babbar katanga,ya sake daukar waya yayi
magana,bai sauke wayarba mutum ya fito daga babbar qofar dake maqale da katangar

"Ku qaraso ciki mana" mutumin ya fada da murmushi,yana yiwa wani dake zaune a wajen
magana kan ya bude qofar,ya dage musu alameen din ya saka kan motar ciki,sai gasu a
wani katafaren waje dake da yalwar shuke shuke iya ganinka.

Baice komai da itaba ya fita,saidai ya zagayo side din da take yabuda


murfin motar,take iska me kyau da dadi ya fara shiga tana fita,ya juya cikin
takunsan nan mai cike da aji yabi mutumin sukayi ciki,ba jimawa suka bace cikin
wajen.

A hankali take nazartar wajen,data lura da kyau ya fahimci gidan gona


ne,saidai da alama wajen ya mutu ne,ma'ana ba'a aiwatar da komai a ciki,taci gaba
dabin wajen da kallo,saita sauke ajiyar zuciya ta sake jan wayarta tana duba
lokaci.

Batasan me yasa. Ya daukota nan yakeson bata mata lokaci ba,duk da cewa ta
sani inda motar hayane babu lallai ma ace yanzu sun kawo wudil din.

Tana tsakiyar tunanin taji ana sallama,ta waiwaya a hankali,su biyu ne a


tsaye riqe da manyan ledoji guda hudu,da alama mutanen karkara ne
"Hajiya yalallabai ne yace a kawo,a saka a cikin mota"

"To bismillah baba" ta fadi tana bude musu seat din baya,suka saka ledan suka
rufe,basukai ga bacewa daga wajen ba taga bullowarsa tare da mutumin,kusan minti
goma suka kashe a waje suna sake magana sannan sukayi sallama,ya sake shigowa
motar,yayi bismillah ya kunnata suka fice daga wajen.

Tun kafin su shiga wajen ta karanci tasha suka shigo,a nutse ya sanya
motarsa a ciki,bau saurari masu tararsa suna tambayarsa inda zashi ba,da alama
yasan wajen wanda zashi,baiko tsaya ba har sai daya qaraso.

"Bismillah muje" yafada yana bude motar,yadda yace haka ta biyoshi a


baya,tana tsaye sukayi magana da wani,kafin a bude qaramar golf,lamin din yace ta
shiga,aka debo wadancan ledojin aka saka a ciki,ya qaraso bakin window din motar

"Ki gaisheta,Allah ya kiyaye" yayi maganar idanunsa tar akanta

"Ameen" ta amsa ba tare data iya dubanshi ba,sabida tasan tayi qarya a yadda suke
very close ta iya kallon qwayar idanun nasa,janye dubansa yayi zuwa ga driver din

"Mutumina ayi tuqi a hankali"

"In sha Allahu yallabai,ni daka biyani harda riba,gaggawar me zanyi kuma?"

"To Allah ya tsare"

"Ameen ameen" daga haka yaja da baya,shi kuma ya tashi motar suka fara ficewa daga
tashar,zuciyarta natason ta waiwaya saboda ta tabbatar yana tsaye yana kallonsu
amma ta hana kanta aiwatar da hakan,ta saki ajiyar zuciya sanda suka hau titi tana
duban hanya,duk da ya biya kudin motar wa ita kadai babu takura babu matsi,amma
hakanan kawai taji tafiyar ta rage armashi,ba kamar dazun ba.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 57

Ina ka saka ina ka aje yaa baraka ta dinga yi da iman din,farincikinta ya


kasa boyuwa,kamar zata goyata,wanda dama ko a baya kusan hakace tsakaninsu da ita.

"Aah,shine ya kawoki?" Ya baraka ta tambayi iman din sanda ta isar mata da


saqonshi,farinciki na taso mata

"A'h,yadai ajjiyeni a wudil,yaje wani waje ne" farincikin data soma ji sai ya
koma,batajin zata iya qyale wannan abun yatafi a haka,ba zata barsu duka su biyun
suyi asarar kyakkyawan yabanya da iri ba,kara da alkunyar malam da inna tayi
yawa,ta tabbatar dukkaninsu suna da buqata da kuma interest akan tarayyar iman da
ameen,amma dukkaninsu suna duba wani abu daya faru a baya suna dauke kai da bawa
ameen din dama,bayan dukkaninsu asara ce ace kowanne bangare sun rasa wani tsakanin
iman da ameen din.

Sosai ya baraka ke ririta iman,cikin kwanakin data debo zatayi,sun sake


sabo sosai a tsakaninsu,suna zama suyi hira mai yawa,irin wadda a baya basu taba
yin irinta ba,a nan ta sake jij tarihin ameen din da kyau,tayi shuru tana tariyo
maganganun da yaa barakan ta gaya mata,lallai sun sha gwagwarmayar rayuwa,kuma dama
yawancin irinsu ameen din ariqi Allah yake musu na ban mamaki,gashinan kuwa,kome ya
saka kansa zaiyi sai Allah ya sanya masa albarka.

Kwanakin da iman din taso yi wajen yaa barakan ta koma gida bai samu
ba,saboda zazzabi da ya kama ya barakan,iman dince ta dinga kula da ita,tayi
treating nata sosai,cikin kwanaki biyar ta soma murmurewa,ta warware sarai abunta.

********Karfe takwas saura ne na dare,suna zaune a tsakar rumfar ya barakan wadda


ke wadace da haske saboda qaramar wutar solar da ameen din ya hada mata,tuwon dare
suke ci,iman ya baraka yaranta maza ukusai autarta,kana ganinsu xakasan cikin
walwala suke,har iman din.

Wayar yaa baraka ce tahau tsuwwa,iman dake zaune dab da wayar ta dauko tana
duba mai kiran,AMINULLAHI ne a jiki kamar yadda ya barakan tayi saving

"Waye?" Ta tambayeta kafin ta miqa mata,batace komai ba sai ta miqawa usama da yafi
kusa da ita ya miqa mata,yayin data ja kwanon tuwonta a hankali taci gaba da ci.

Har sukayi wayar suka qare batace komai ba,yaa barakan ta ajjiye wayar
tana sake jan kwanon abincinta

"Qarfe nawa zaki tafin gobe?" Ta tambayi iman,ta daga kanta tana dubanta

"Sai wajen yamma inajin,tafiyar ranar nan bata da dadi ga motar haya,duk sai ka
jigata kafin ta isa gida,sannan juma'a ce,zuwa yamma an sauko daga
masallaci....akwai wani abune?" Kai ta girgiza

"O'o'o'o imani,akwai saqo ne da nakeso na baki ki kaiwa inna"

"Okay" ta fada tana ci gaba da cin abincinta.

Gefanta ta duba itama inda tata wayar ta kada,da alamun kira kenan,dr
ahmad ne,dama kuma kusan lokacin kiransa kenan,sai ta tsame hannunta tana daukar
wayar ta miqe a hankali,ya baraka ta bita da kallo,itama tasan me kiran,haka kawai
take kishi dashi,bata sani ba....ko kishin da ya kamata qaninta yaji ne ita take
jiye masa?,tana kallon sanda iman ta wanke hannunta ta kuma shige daki,saita sauke
idanunta a hankali tana addu'a qasan ranta,zuciyarta tana motsuwa.

**********Washegari tunda suka tashi suka kammala abincin safe iman taga ya baraka
nata hidimar hada dambu

"Shi kike sha'awa kuma yau yaya?" Iman ta tambayeta tana murmushi sanda take tayata
tsinke zogale

"Wallahi,kuma baqi zanyi ma yau din" daga haka bata sake tambayarta komai ba,don ba
dabi'arta bace bin qwaqwafi ko yawan tambaye tambaye.

Sun dan dauki lokaci kafin su gama hada komai,ta dauraye hannunta ta tashi
tana bude tukunyar da badi'a ta saka musu ruwan zafi na wanka,ta diba ta sirka tana
cewa

"Naga alama kadan ya rage dambun nan ya gama turara,bari kiga na fara shiri"

"Don Allah ki qara kwana yaa iman" badi'a ta fada tana kwabe fuska,don sosai taji
dadin zuwan iman din,taji kuma dadin zama da ita,ta qaru da abubuwa masu yawa
sosai,hakanan ta qara mata sha'awa da kuma qaimin zama nurse itama

"Makaranta badi'a" ta fada tana dan fidda blue eyes dinta

"Kai" badi'ar ta fada tana dan kare fuskarta tana dariya

"Me?" Iman ta tambayeta

"Wadan nan idanun naki ya iman.....aisai su tsiratani,kinga sheqin da suke a hasken


rana?,na yarda da maganar kawu aminu kam"

"Me yace?" Ta tambayi badi'ar cikin mamaki


"Idanun imani na musamman ne,akwai wasu abubuwa masu yawa a cikinsu,amma ba kowa ne
yake ganewa ba,amma ni nafi kowa fahimta da karantar haka' haka yace,amma nima
yanzu na gani,idanunki na gayu ne" murmushi kawai iman din tayi,bata iya amsawa
badi'a ba,sai kawai ta tsugunna ta dauki botikinta ta shige bandaki tana cewa

"So kike dai ki tsaidani badia,idan na biye miki lokaci zan bata,azahar ta kusa".

Koda ta fito alwala ta daura ta shige dakin d aka sauketa,ta tsane jikinta
da kyau ta zube kayan shafarta ta fara gyara jikinta,komai na iman din mai
ajine,farawar karatunta yazo mata da sauyawarta zuwa 'yar gayu ta gasken gaske,duk
da cewa dama tunda ta taso ita mai son ado ce,Allah kuma ya hadata da lamin dake
fiddata cikin tsararrkinta da dinkuna masu ban sha'awa,wanda ko a sannan sai jikin
wance da wance,style kuwa duka yaran layinsu a wajenta suke karba.

Cikin wani lallausan lace mai zanen manyan flowers ta shirya,ba makeup
tayi ba,amma yadda hodar da ta saka tabi fatar fuskarta man leben ya haska jajayen
labbanta....daurin kanta ya zauna da kyau cikin wani style mai ban sha'awa ya sanya
zakayi zaton zama tayi tayi kwalliya,iman me kyau ce har yau har kwanan gobe,kyanta
yana da wani irin sanyi da kuma fusgar hankali,inda Allah ya rufa mata asiri,ta
tashi gidan tarbiyya,batasan shigar banza ko fidda tsiraici ba,da mazan da zasu
halaka ta sanadinta suna da yawa.

Tsakar gida ta fito zata shiga rumfar yaa baraka ta dauko jotter dinta
da tayi amfani da ita jiya ta barta,zata qarasa rubutawa badi'a sunan wasu
litattafai da zata dinga dubawa saboda turancinta ya zauna sosai,ya barakan dake
cikin daki tace ta duba mata dambu ya nuna,ta zame murfin tukunyar ta bude buhun ta
debo tana tabawa,dai dai lokacin da sallamarsa ta ratsa tsakar gidan,abunda batayi
zato ko kuma tsammani ba,don haka ta waiwaya gefanta inda qofar shigowa take.

Aminullahi ne,cikin shigar manyan kaya,komai nashi fari tas,kayan da


suka qara masa cika kwarjini da kuma kamala,fuskarsa tayi fes fresh da ita,ba
abunda take fitarwa sai annuri,gashin kansa dana fuskarsa yasha gyara,duk da cewa
matafiyi ne amma jikinsa bai nuna hakan ba,sassanyan qamshinsa ya busa da iskar
dake kadawa cikin tsakar gidan ta kwasoshi da gudu izuwa hancin iman,yanayin da ya
haifar mata da faduwar gaba,tsimammun idanunsa masu dauke da wani magnet suka so
kashe mata jiki da zuciya,cikin tata jarumtar ta janye idanun nata tana amsa
sallamarsa,tare da qoqarin saka dambun data debo da yatsun hannunta a baki ta fara
taunawa.

Idanunsa sauka kan labban nata da suke qyallin lip balm,tana motsasu a
hankali saboda taunar da takeyi,ya dauke kansa da sauri saboda wani abu daya zuba
cikin jikinsa,ya waiwayawa ga usama da musa da suke biye dashi

"Kun dauko komai?"


"Eh kawu" sai yaci gaba da takowa zuwa cikin gidan,wanda kafin ya qaraso iman ta
shige rumfar yaa barakan,a saurin da take na dauko jotter din tayi tabar masu
falon.

Saidai kuma sanda ta dauka take shirin juyowa tuni ya cire rufaffun
takalman qafarsa ya sanyo qafarsa zuwa parlon,dole cikin hikima ta koma da baya ta
zaune cikin kujerar da tafi kusa da ita tana buda shafukan jotter,batason a yau ta
bashi dama ko qofa ko guda daya da zata bada kanta ko aikata wani abu ba dai dai
ba,don haka tabi sahun 'yan sannu da zuwa ta marabceshi kamar kowa,dai dai sanda ya
baraka ta iso falon fuskarta cike fal da fara'a

"Wai dama da gaske kake?,kai dake da tarin ayyuka fal a gabansa?,da kayi zamanka ai
tunda na warke,itama iman din anjima kadan zata koma"
"Bazan nutsu bane idan banzo na ganki ba" ya qarashe furucin idanunsa na sauka akan
iman,tayi masa wani kyau daya jima bai gani ba,shigar ta karbeta abundanita bata
sani ba,abunda yadan ja hankalin ya baraka,ta gefan idanu take qoqarin gano me yake
kalla?,saita saki boyayyen murmushi kafin ta amsa masa

"To ai gani lafiya qalau alhmdlh,babu abinda ya gutsireni ko?" Maida dubansa yayi
gareta,cikin girmamawa ya fara gaisheta

"Barka da yamma,mun sameku lafiya?"

"Alhmadlh,ya inna da malam,ya ka barosu?"

"Lafiya qalau,sunce na gaidaki da kyau"

"Na gode sosai,na warware" waiwayawa tayi inda iman take

"Iman,muna da ruwa kuwa?" Sai a sannan ta daga kanta,cikin wani salo da bilhaqqi
batasan tayishi ba tayi maga a yangance

"Ba za'a rasa ba" saita ajjiye jotter din ta fara takawa a hankali zuwa tsakar
gidan,inda a rumfar da aka kafawa qofar dakunan yaa barakan dan madaidaicin fridge
dinta da lamin din ya siya mata yake,kamar wanda ake jansa haka yaji zuciyarsa na
mararin binta da kallo,amma ya nuna matuqar mazantaka ya danne kansa

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ya dinga maimaitawa,baisan


me ya faru dashi ba,wani tsohon abu......wani tsohon miki keson tasar masa,wani
tsohin feelings da kuma wani mataccen yanayi daya jima da zubdashi a wani waje mai
nisan gaske.

Da ruwan dama sauran lemon kunun aya datayi musu a jiya ta shigo saman
dan faranti,tana shigowa ya baraka ta miqe

"Zuba masa ina zuwa,bari na sauke dambun"

"Ki bari na sauke yaaya" iman ta fada tana sauri saurin dire masa ta fice

"A'ah,wanka zan shiga ai daga can,ni kaina zafi nakeji,wasu zannuwa na nakeso kiyi
musu iron inason sakasu anjima zan leqa suna hayi" bata saurareta ba ta nuna mata
dutsen gugar ta sanya kai ta fice.

Daga tsakar gida ta yiwa yaran magana kan kada wanda ya shiga parlor
din,ta sauke dambun,ta saka badi'a shiryawa ameen nasa a fulasai masu kyau sannan
ta wuce wankan.

Daga can parlor kuwa kamar an buge mata gwiwoyinta haka iman taji,bata
shirya zama dashi waje daya ba amma yaa baraka ta rushe mata dukan plan din
nata,hasalima inda socket din gugar yake yana daura da ameen dinne,saidai duk da
haka ba zata bari yaga lagonta ko karayarta ba,don haka ta qarasa gabansa ta
tsugunna,ta bude lemon ta fara tsiyaya masa a cup daidai misali,sannan ta dauko
zata miqa masa.

Batasan duk abinda take ya kafeta bane da ido sai data miqa masa
lemon,maimakon yakarba sai yaci gaba da sauke mata nauyin idanunsa

"Gashi" ta fada cikin jarumta,duk da yadda taji zuciyarta kamar ta fara narkewa

"Mantawa kikayi cikin gidan nan ba mata bane kadai akwaisu usama?" Da mamaki ta
dago ta kalleshi,saidai ta kasa jurar kallonshin,saboda idanunsa sun ninka nata a
nauyi da dafi mai tarin yawa
"Su usama kuma?"
"Eh,ko su ba aure a tsakaninku?.....duk da ban sani ba ko wancan likitanne ya baki
wannan damar......" Daga haka ya miqa hannu zai amshi cup din,ta fada nazari kan
ma'anar maganarsa,abunda yasa bataga tahowarsa ba,sai sukar dumin hannunsa saman
nata hannun,take ya ratsa dukka wasu sassan jikinta qashi da jini yakai ga
qwaqwalwarta cikin sakannin taqaitattu.

Kamar jan wayar wuta hakanan kowannensu yaji,suka janye hannunsu lokaci
guda,sanadin barewar lemon kenan saman skeet dinta,ta miqe da sauri sakamakon sanyi
daya ratsata,kallon kallon sukayi na second biyu,sai ta juya da hanzari ta fita a
parlor din.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 58

Ajiyar zuciya ya saki yana maida jikinsa zuwa bayan kujerar yayi relaxing
yana sauke ajiyar zuciya,wani yanayi na bin dukka sassan jikinsa,gajiya na sauka a
gabbansa kamar wanda aka yiwa duka,gajiyar da tuqin ma da yayi daga kano zuwa
jigawan bai jita ba,a haka yaci gaba da kasancewa,shi baisha ruwan ba bai kuma sha
lemon ba,hakanan bai buda idanunsa ba har saida ya baraka tayi sallama cikin parlor
din,idanunta kan fuskarsa sanda ya bude idon nasa tana karantar yanayinsa

"Ya bakasha komai ba?"

"Am ok,da ruwana a mota ma.....qarfe nawa masallacinku suke tayar da sallar juma'?"
Yayi tambayar yana duba agogon hannunsa don kaucewa tuhumar ya baraka

"Qarfe biyu ne"

"Ok,bari muje can muyi salla mu dawo,naga biyun saura" saiya miqe yana kashe
wayarsa ya barta nan saman kujerar,ya zare agogon hannunsa yana kiran usama

"Kuyi alwala mu wuce masallaci,kuna kusa da masallaci amma ku dinga zama a gida?,ba
zaku tafi da wuri ba har sai kunji an kira sallah?,kunsan falalar zuwa masallaci da
wuri kuwa?" Da wannan fadan suia fita tsakar gida,badi'a ta zuba masa ruwa a buta
yayi alwala,ya cire babbar rigarsa ya bata suka wuce masallaci shida 'yan mazan.

Tana daga daki tana jiyo badi'a dake shanshana rigar ameen

"Kai jama'a,kawu wanne irin turare yake sakawa?,waishi wanne irin dam gayune?,komai
nasa qanshin yake,yaaya,Allah rannan da yazo ya kwana yace na hada masa kayan datti
cewa nayi basuyi datti ba,don ni dai qamshi naji sunayi" bata ji dai amsar da ya
baraka ta bata ba,amma taji badi'ar tayi dariya sannan ta wuce zuwa cikin parlorn.

Shuru shuru basu dawo ba,harsai da ya barakan ta fara jajjabi da cigiyarsu


sannan taji shigowarsu,muryar usama taji yana lissafa mata gidajen 'yan uwa sa
sukaje,yaje gaida tsofaffi cikin danginsu da kuma yi musu alkhairi kamar yadda ya
saba,wannan al'adarsa ce kuma dabi'arsa ce duk sanda ya shigo jigawa zaiya zagayawa
dattijai da manya na gari dama na cikin familynsa,wannan ya sanya masa farinji da
kuma daukaka,sannan ya siya masa soyayya mai tarin yawa daga wajen mabanbantan
mutane,iyayensa da suka rasu kuma suka samu addu'o'i masu tarin yawa daga
makwancinsu.

Tanaji ya baraka na kirata,sai kawai ta miqe ta tayar da sallah abunta,data


idar ma zamanta tayi,sai data ji tana sake kiranta sannan ta tashi,ta sauya kayan
jikinta tun dazun zuwa wata bubu ta material ruwan makuba mai dan haske kadan,ta
yane kanta da mayafinta ta nufi dakin.

Shi ta fara gani,sabida ya zauna ne yana fuskantar qofar shigowar,cikin


babban faranti aka zuba musu dambun shi da usama da musa suke ci tare,yana da
wannan sauqin kan qwarai da kuma son mutane,a jininsa yake,ita shaida ce,kanta ta
kawar cikin basarwa da nuna halin ko in kula ta qarasa wajen ya baraka

"Ya zaki zauna daki kowa yana zaune yana cin abinci?" Murmushi tayi,murmushi da ya
qawata fuskarta qwarai

"Sallah nayi,yana raina,har Alla Allah nake na idar" agogo ya barakan ta kalla

"Ai gwara ki hanzarta,don kamar qarfe biyar naji yace zaku wuce" dan turus tayi,ita
sam bata wani kawo tare zasu tafi ba,kuma ko yanzun batajin zata bari su tafi
tare,bata marmarin hakan,gwara kowa yayi hanyarsa

"Ko?,tafiyar tamu zatayi dai dai?,ko na biyo shi a motan kasuws gudun bata
lokaci?" Tas ya gano inda ta dosa,ya kafeta da idanunsa daga nesa inda yake zaune
yana karantar fuskarta

"Aha saboda wahalar dakai?,ki gama a nutse,abunda baki hada bama na taho miki dashi
idan zan wuce maiduguri" a hakali ya dauke dubansa daga kan iman ya maida kan ya
baraka,me zataje yi a maiduguri kuma?,iyakar saninsa a danginsu basu da kowa a can
bare yace zumunci ko kuma wani abun zai kaita,bai tambaya ba,sai ya maida kansa
kawai ga abincin da suke ci.

Karo na biyu kenan badi'a ta shigo dakin,ta dubi iman dake xaune sosai
abunta,kamar ba ita ya ameen din ke jira ba

"Yaa iman.....yace ki fito,ke kadai suke jira wallahi,har ya kunna motar" a nutse
ta dubeta hankali kwance

"Tare mukazo da xaki damu yana jirana?,ba nace miki yayi gaba zan taho a bayanshi
ba?" Dan buga qafarta kadan tayi sannan tace

"Wallahi na gaya masa....shine ya sake turoni"

"To kije ki maimaita masa,tunda saqon dai dana baki kenan" daga haka ta jawo
wayarta tana duba kiran dake shigowa,ba kowa bane dr ahmad ne,saita daga wayar ta
kara a kunnenta.

Kashe motar yayi yabar key din a jiki bayan badi'a ta gama bayaninta,ya
zuro qafafunsa a hankali ya taka zuwa cikin gidan,ransa yadan baci amma kuma ya
danne,zuciyarsa nata lissafa masa abubuwa iri iri kan ma'anar qin tafiyarta dashi.

Kai tsaye dakin da take ciki ya nufa,yasa hannu a nutse ya yaye kabulen
dakin,hasken da ya bayyana shi ya ankarar da ita wanzuwarsa a wajen.

Wayar dake kunnenta fa sauke,yabi wayar da kallo kafin ya maida dubansa


kan fuskarta

"Tashi ki wuce muje" ya bata umarni kai tsaye cikin dakakkiyar muryarsa yana
kallonta tsakiyar idanunta kanshi tsaye,irin kallon da a baya yake mata can
shekarun baya duk sanda tayi wani laifi yakeson kuma nuna mata tayi laifin ba tare
da ya magantu ba.

Bata da zabi illa miqewa da tayi,saidai fuskarta ba annuri,ta qarasa inda


ta ajjiye akwatinta ta kuma dora mayafinta akai sanda tayi shirin tafiyarta tun na
dazu,ta yafa mayafin ta fidda takalmanta ta sanya duka yana tsaye,saita tako a
hankali zuwa bakin qofar fita,sai kuma taja ta tsaya,saboda babu wani sauran space
daya rage mata da zata iya fita,idan kuma tace zata saka kai a hakan ta fita to ba
shakka saita fara mannuwa da jikinsa.
Kamar xata saki kuka yadda ya tsaya ya zuba mata idanunsa yana kuma
hukuntata dasu ba tare da ya dauke kallonsa ba,ya kuma sani cewa lallai saiya matsa
din xata samu hanya,duk da yadda ta dauke masa kai amma jikinta yana karbar horo
yadda ya kamata,idanun ameen din nada wani irin tasiri tattare da ita,don ko sanda
tasha giyar maqaryaciyar soyayyar bassam tayi tatil bata iya kallon qwayar idanunsa
ta gaya masa magana kanta tsaye

"Zan wuce" ta fada ganin bai da niyyar matsawa

"Wuce" yace da ita,ta daga kai tana duban hanyar daya bata,tazarar bata da wani
yawa,idan ba mugun kulawa tayi ba saita shafeshi,wannan wanne irin sabon abune kuma
ya amin din yazo dashi?.

A hankali kuma cikin takatsantsan ta soma ratsawa ta gabansa,sai dataje


tsakiya ya rufe hanyar,numfashinta gaba daya ya tsaya a maqogoronta,da tabbas ko
yaya ta motsa cikin faffadan qirjinsa zatayi masauki

"Duk randa na sake cewa ayi abu kika musamin zakiga yadda zanyi dake,idan kin manta
na tuna miki....lameen ne.....yayanki daya raineki da hannunsa tun kina majina a
hanci,wannan girman da kuma auren da kika tabayi bazai sauya komai ba" ya qarashe
maganar yana duqawa har tana jiyo saukar numfashinsa saman fuskarta,ya sabule
jakarta data ruqo

"Wuce ki jirani" ya fada tana dai daita tsaiwarsa,wuf tayi ta samu ya


fice,qafafunta na sarqewa saboda tsaratan da tayi,saboda ta tsammaci lamin din
rungumeta kawai zaiyi saboda tsabar kusancin da yayi yawa a tsakaninsu.

Luf tayi a gidan gaba,tana jin yadda kowanne sashe na jikinta yake
amsawa,ajiyar zuciya take saukewa a jejjere,idanuwanta a rufe har zuwa sanda badi'a
ta kawo mata jakarta ta sanya cikin motar,tazarar kusan minti biyar taji
muryarshi,ta karkata kanta zuwa gefe a hankali,ta hangeshi yana rabon kudi wa su
usama da abokanshi,fuskar nan a tsume,batasan me yasa idan ya hade rai irin haka
yake qara masa kyau ba,sai ta maida idanunta ta lumshe,don bata fatan ya juyo yaga
tana kallonshi ta kunyata,ko kuma ajinta ya zuba.

"Subhanallazi sakkara lana haza wama kunna lahu muqrinun,wa inna ila
rabbina la munqalibun" ya furta addu'ar da lallausar muryarsa bayan ya kunna
motar,har zuwa sannan bata yarda ta bude idanunta ba,a hankali ya fara motsata suka
fara barin layin.

Wata tafiya sukayi ba um ba um um,sai daga bisani ya dannan wani karatu


wanda ke magana kan bin iyaye da kuma haqoqinsu akan dansu,a hankali karatun ya
dinga shigarta,ya kuma kashe mata dukkan wata laka ta jikinta,sosai karatun malamin
ke shiga duk wani bargo na jikinta ya kuma bi ta magudanar jini,lallai da gaske a
baya ta tafka kuskure mai girma a rayuwarta,Allah ne yaji qanta ya kuma tsamota,da
kuma addu:ar da ta tabbatar su innan sunci gaba da yi mata ita,koda a zahiri sun
nuna basa tare da ita.

Ko wayar da dr ahmad keta faman yi mata kasa dagawa tayi,tayita rejecting


tana maida idanunta ta kulle,sunyi nisa sosai ya sake kira

"Koki kashe ko ki sata a silent,ko kuma ki daga,qararta yana damuna,idan kuma na


karba ta tafi kenan,ta window zan cillata" sosai kalamansa suka bata mamaki,wai
yaushe ya lamin din ya koyi zafi haka?,tadan saci kallonsa da hanzari ta kuma dauke
kanta,har yanzu fuskarshin a cakude take,sai kawai ta tura masa gajeran saqo tans
hanya,idan ta isa gida zata sanar masa,ta kashe wayar gaba dayanta ta jefata a
jakar hannunta,ta gyara zamanta da kyau ta lafe cikin kujerar motar.

Sun baro jigawa da wuri,to amma wajen shigowa kano anan matsalar bata
lokacin take,sun tadda tarin traffic a hanya daya dinga bata musu lokaci,wannan
yasa basu isa gida ba sai ana sallar isha'i,don suna shiga ma a toilet din
farfajiyar gidan ta daura alwalarta tayi ciki,Allah yasa ma ya tsaya a wani
masallacin hanya na matafiya sunyi magarib,ya kuma siya musu takeaway.

Da idanu inna ta bisu sanda suka shigo mata,wani abu na taba


zuciyarta,tana kuma rayawa cewa inama a matsayin miji da mata suka shigo
mata?,sunyi bala'in dacewa,irin dacewar data amsa sunanta,sannan fili da badini
kuma babu ta inda basuyi marching ba.

Mufida kam dadi ya isheta yaa iman ta dawo,sadiqu ya kalleta

"Idan tayi aure naga ya zakiyi,ba zaki iya zama gidan nan ba kenan" sadiq na gama
fadawa miqewa ameen yayi,hannayensa cikin aljihunsa yace

"Zan shiga na watsa ruwa,a gajiye nake,idan ka shigo xakaji yadda ake ciki da
mutanen nan,dazun inakan hanya sun kirani"

"Okay,karka damu,ka huta sosai,ko zuwa gobe ma tattauna"

*********** Da sauri da sauri kwanakin bikin da aka sanya suke qara rage
kansu,lokaci yaci gaba da wullawa yana kuma matsantowa,ya zuwa lokacin iman din sam
ko a jikinta bata wani jin cewa aure zatayi,kawai kallon kowa da komai takeyi,a
yanzun hankalinta gaba daya yafi tattara ga karatunta,saboda batason ta samu wani
kuskure ko tasgaro,tanason koda bata tsira da komai ba ta tsira dai da karatun
nata.

*********Ranar wata laraba da yammaci ta dawo daga makaranta sukaci kacibus da yaa
baraka a qofar gida,tana rataye da jakarta,sadiqu na biye da ita da wata babbar
leda a hannunsa

"Ashe da rabon dai zamu hadu,shi yasa ya gana ta zaunar dani" ta fada fuskarta fal
murmushi tana duban iman,murmushi itama iman din ta maida mata,a wannan karon ta
cika da mamakin yawan ganin ya baraka da take a gidansu,wanda a baya sam ba
al'adarta bace,takan jima bata shigo kano ba saida wani dalili,amma kuma data tuna
bikin dake cikin gidan nasu harda na dan uwanta qwaya daya tilo sai mamakinta ya
ragu,saidai kuma taji ta ambaci yaagana,badai bikin da ya rage sati kusan hudu ta
tahowa tun yanzu ba?.

"Don Allah ya baraka ki bari sai gobe,kinga fa yamma tayi sosai,kafin kije
dare yayi,kuma naga ya lamin din baya kusa bare ya kaiki koda tasha ne" ima din ta
fada cikin kulawa

"Ahaf.....rabu da dan nema,dama banaso yasan nazo din ai,saidai yaji labarin zuwan
nawa....kedai ki kwantar da hankalinki,tun ana saura sati tahowa kano ya sameni,sai
an gama komai 'yan jigawa zasu kuma ganina" murmushi kawai iman tayi wanda ya tsaya
mata iya wuya,ita kanta kenan tana farinciki da auren samha da dan uwanta,saidai
sam bataga laifinta ba,babu wanda bazaiso ace nashi yaci gaba ba,dole a nan sukayi
sallama ta bata sallahun gaida mata da badi'a ta sanya kai zuwa cikin gidan.

A hankali tayi sallama cikin parlor dinsu,saidai a maimakon ya gana dake


zaune a parlor din ita da inna ta amsa,saita rafka mata guda,gudar data sanyata
karaya,wasu tarin tawagar hawaye suka danno kai,saidai tayi qoqarin tsaidasu,sannan
uwa uba salatin da taji yaagana ta rabza wanda ya sanyata tsaiwa cak cikin tsoro
tana dubanta...
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 59

"Yau me zan gani ni aishatu?" Ta fada tana kame baki tare da qarewa iman
kallo,kallon da ya sanyata ta tsargu,ta kuma soma bin jikinta da kallo,mufida ce da
itama ta tsorata tayi qarfin halin tambaya

"Mene yaa gana"


"Amarya nake gani gayanta,babu wani canji,babu kuma wani abu da zai nuna maka cewa
amarya ce,wannan abun kunya har ina?,ke binta kina me?" Cikin kara da kuma alkunya
irin ta innar ta miqe tana murmushi,ba zata iya cewa yaagana komai ba a matsayinta
na yayar mijinta,sai kawai ta fada kitchen tabar su mufida da dramer.

Cikin sanyin jiki dana gwiwa iman ta fara takowa,a qalla tadan samu wani
qwarin gwiwar,tsoron da ya ganar tasa taji ya ragu

"Wallahi yaagana kin masifar ban tsoro,na dauka wani abun kika gani a jikina"

"Wani abunne mana,wannan abun kunya har ina?,kina can zaki qare a yawon
boko,auranki saura 'yan satittika amma baki canza daga yadda na sanki ba?,to Allah
ba za'ayi wannan abun kunyar damu ba,wannan auren dole ayi masa shiri na musamman
ehe...saboda wancan babu rawar da muka taka,so nake ki canza gaba daya,idan ba
kyakkyawan sani akayi miki ba banason a ganeki" baki kawai iman din ta saka tana
kallon yadda yagana ta haqiqance,wai ko don basusan yadda takeji bane a
zuciyarta?,jinta take kamar mutum mutumi,basusan ta fidda miji bane saboda ba zata
iya cewa malam bata da kowa ba?,ta fidda mijine saboda ta fuskanci sun shirya aurad
da ita?,batason tace bata da tsayayye kada hakan ga sake bata musu rai.

Duk lissafe lissafen da yaagana ta shiga yi kallonta taci gaba dayi,so


take ta sarara mata ta barta ta shiga dakinta ma ta raba kanta da kayan jikinta.

Kamar bushira tasan me akeyi saiga sallamarta,ajiyar zuciya iman ta saki

"Yauwa,don Allah bushira qaraso"

"Eh qaraso ciki,dama ke nake nema" yaagana ta fada,akwai kyakkyawan sani da kuma
alaqa mai kyau tsakaninta da bushira,tun zamanin rikicin aurenta da bassam

"To gani yaagana,Allah yasa ba laifi mukayi ba?" Ta fada tana dariya hadi da neman
wajen zama

"Qatoton laifi ma kuwa,zaman me kuke naga amarya gaya babu kayan hadi?" Kallon iman
bushira tayi,ta danne dariyarta sanda iman din ta rausayar dakai,duk ta zama kalar
tausayi,da alama kwata kwata lissafin yaagana baizo dai dai da kwanyarta ba a
wannan lokacin,babu abunda maganar ke qara mata sai sake jefata a rudu da takeyi

"Kiyi haquri ya gana,daga gobe in sha Allah xaki fada ganin canji"

"Yauwa,so nake kowa yatabbatar yanzu zatayi aure,kuma ita din jinin kanuri ce,nan
da kwanaki biyar ma idan zan tafi tasata zanyi a gaba mu wuce borno,idan hidimar ta
matso ma dawo tare,saina tsumata na jiqata da kyau" miqewa kawai iman din tayi,ta
kuma ja hannun bushira,saboda duk wata dauriya tata ta qare,kuka ke shirin kubce
mata.

Suna shiga dakin kuwa ta saki kuka sosai,bushira ta fidda idanu tana
jawota zuwa kafadarta,babu musu kuwa ta dora kanta akai

"Meye haka iman?,so kike ki tadawa mutane hankali?" Da qyar ta samu tayi
controlling kanta,cikin sautin dake dauke da kuka kanta ta fara magana

"Wai me yasa bani da sa'a kwata kwata bushira?,me yasa soyayyaa take zuwa a
hagunce?,cikin mummunar rashin sa'a" da sauri bushira ta dakatar da ita

"Ki gyara kalamanki iman,yanzu kuma me kikaga anyi?" Wani dunqulallen abu mai ciwo
ta hadiye kafin ta iya bata amsa

"Kinga fa,wannan auren nawa sukewa murna haka?,wannan auren nawa kowa yake ciwa
alwashi?,auren da har yanzu bani da tabbacin na shirya ko ban shirya ba?" Hannu
bushira tasa tana goge mata hawayen,ta kuma ja tsaki

"Wannan shine tashin hankalinki?,indai shine ki kwantar da hankalinki,indai har


kina yin addu'a kici gaba dayi,na tabbatar da cewa ubangiji yana tare dake,kuma
yana sauraronki,hakanan bazai kunyataki ba" cikin hikima da tatausan harshe da
qawar da tasan ciwon qawarta bushiran ta saukar da ita qwarai,har iman din ta shiga
wanka bayan ta sanya mufida ta kawo musu abinci.

"Na jiki kina gayawa yaagana wai daga gobe zan fara gyaran jiki,toni bazan
iya wannan aikin ba,hasalima bansan wajen wani gyaran jiki ba yanzu,iya mayukan da
nake amfani dasu sun isheni,idan baya sona a haka har sai an masa gyaran jiki ya
haqura" iman ta fada suna tsaka da cin abincin ita da bushira.

Murmushi ya kubcema bushiran


"Shikenan,saiki shirya bin yagana maiduguri ta kaiki ta killaceki" wani kallo tabi
bushira dashi

"Babu inda zani,don a satin nan din ma da take zance,muna da abu mai muhimmanci
cikin makaranta"

"Kinga to muyi magana,Alla yagana da gaske take,kuma matuqar taga bamu fara anan
ba,babu wanda ya isa ya hanata tafiya dake,idan kinason ta barki ki yarda kawai a
fara goben ta gani,idan ta tashi tafiya saiki bata uzuri,wala'alla ta yarda,idan
don wajen gyaran jikine,ga AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISES" ambatar sunan ya tuna
mata da wajen,ba shakka matar duniya ce wajen iya gyaran jiki,ita ganauce ba jiyau
ba,hakanan ya tuna mata da lokaci irin wannan,lokacin da batajin bari,lokacin da
suke kan digimi da rawar qafar aurenta da bassam,ya Allah!....kada ka kawo abunda
bazai wuce ba, tafada tana lumshe idanunta,har kwanan gobe tana jin haushi da kuma
zafin aurenta da bassam,inda ace tana da iko da zata dawo da rayuwarta ta baya ta
shafe bassam a ciki,tunda suka rabu basu hadu ba,batasan ma wacce rayuwa yake ciki
ba,bata kuma fatan haduwarsu ko jin labarin nasa,don hakan kamar famin ciwone zaiyi
mata.

"Bani number dinta nayi loosing tawa tunda na canza layi,don a karan kaina
ina buqatar zuwa wajen matar dama,har kema,bawai sai amare ko matan aure kawai
ba,ko babu komai zaka kwaso sirrin qamshi da sirrikan gyaran jiki"

"Ni kuwa nasan da haka,ga number don bana rabo da ita,kona rasata ma ina da ita a
rubuce saboda bacin rana irin haka" wayarta ta buda ta fara karanta mata number
kamar haka 08067558902.

Iman din tayi serving ne kawai ba tare da tana da tabbacin cewa zata je
wajen ba,duk da yadda tayi amanna da yaqinin iya gyara da kuma sirrikan qamshi masu
gigita hankalin abokan zama dama oga mai gida gaba daya,amma da yaagana ta tashi
tafiya ta tabbatar zata tafi da itanne kamar yadda tace,babu shiri ranar daga
makaranta ta wuce wajen,sukayi total ta biyata kudaden gyaran jikin na tsahon
satittikan da suka rage,tayi mata transfer take ta tura mata,rai da zuciyarta fal
haushi,don tana ganin kamar asarar kudinta tayi.

Kwata kwata ko a mafarki bata kawo zancan fidda anko ba a ranta,amma saiga
bushira da atamfa

"Bushira......wai meye hakan?,ko aurena na fari banyi anko ba sai yanzu?,wai da


wanne irin farinjini dr ahmad yaxo muku ne?"
"Aurenki na fari daban da wannan ai,shi kuma dr ahmad ai kowa da irin nasibinsa"
kai iman din ta kada ta jawo wayarta tana latsawa

"Banga amfanin yin anko ba,saboda ba taro zanyi ba ni"

"Eh ai dama iya na ran yini ne malamarsu sai walima kuma"

"Itama walimar bance ma dr zanyi ba"

"Ni na gaya masa da kaina" bushira ta bata amsa tana miqewa

"Already ma yaagana ta bada kudin an sarota,duk meso ki hadani dashi,karki damu


kanki sai kin shiga harkar bikin nan" daga haka bushiran tayi gaba abunta,sai iman
din ta bita da kallo,tana mamakin yadda suka daukaki lamarin gaba dayansu.

Dauke kanta tayi bayan fitar bushiran ta mayar kan wayarta tana neman number
dr ahmad din,karon farko da zatayi kiranshi tsahon tarayyarsu,tana son suyi magana
dashi,batason wani bidi'a ko wani abu daya danganci shagalin biki,saboda a yanzun
gaba daya ba wannan bane a gabanta.

Sau wajen uku tana kira amma number taqi shiga,sai ta ajjiye wayar tabar
kiran,ta miqe ta ta dauko wata qaramar hula mai santsi ta sanya a kanta,gashinta
dake fake cikin ribbon ya fito ta qasan hular,baqi sidik dashi mai santsi da daukan
idanu,saboda ita din ba baya bace wajen kula da gyaran kanta da jikinta gaba
daya,wata irin 'yar gayu ce iman wadda bata wasa da duk wani abu daya shafi gyaran
mace,kama daga turaruka mayukan da sabulai na wanka masu kyau da qamshi,don ko
lalle da wuya ka dubi yatsunta ka ganshi fari babu jan lalle,dama ba kasafai ta
fiya yin baqin lalle ba.

Bata tsammaci samun kowa a parlor din innar ba,saidai tana sanya qafarta
dashi idanuwanta suka fara cin karo,yana zaune qasan tiles saman dardumar daya
shimfida,sanye yake cikin wani lallausa yadi ruwan sararin samaniya wanda aka yiwa
dinki me kyau da aji irin na matasan zamani,hannunsa dake sanye da lafiyayyen agogo
na fata me tsada na kamfanin Prado yana riqe da paper da kuma biro yana ta rubutu
yana kansile wani,kaya ne masu yawan gaske a tsube a tsakiyar parlor din,kama daga
atamfofo laces mayafai da jakankuna.

A hankali ta janye idanunta daga kansa,ta rasa yadda zata hana kanta jin
faduwar gaba duk sanda haduwar waje daya ta gamasu,dai dai lokacin da ya sanya
yatsansa guda daya ya sake gyara zaman glass din fuskarsa,ya daga kansa a hankali
xaiwa anty hassana matar ya muntari magana,idanunsa suka sauka a kanta sanda take
takowa fuskarta na fidda murmushi,idanunta akan fuskar anty hassana

"Kai....anty yaushe kika shigo?" Iman ta fada da muryarta data zama mai wani irin
sanyi

"Shigowata kenan inna tace na zauna na duba kayan nan ko akwai abunda babu a
ciki,to bamu gama ba kuma sai gaki kin fito" qarasowa tayi ya zauna a hannun
kujerar dake dab da anty hassana ta fara gaidata sannan ta duqa tana daukar yaronta
dake saman cinyarta Tana dan masa wasa,kana cikin basarwa ta gaida ameen din ba
tare data dubi sashen da yake ba.

"Lallai amarcin nan da Alama zai karbeki da kyau,irin wannan kyau haka?,amma ko
wace tayi miki wannan gyaran jikin ta iya...." Kamar wanda aka fusga hankalinsa ya
daga idanunsa a hankali ya sauke a fuskar iman din sanda take duban jikin nata gami
da tabe baki

"Wallahi yaagana ce,haka kawai ina zaman zamana ta tattago min aiki,ko naje ayimin
ko ta wuce dani maiduguri,haka ta sakani ba shiri na fidda kudina naje na biya"
sauke idanunsa yayi daga kanta yana fidda wata ajiyar zuciya,ilahirin gangar
jikinsa tana amsawa,sai ya ajjiye abun rubutun ya miqe yana xuba hannayensa a
aljihun rigarsa

"Idan kun gama dubawa mom(haka yake kiran anty hassanan)kuyimin magana,sai aga
abunda ya kamata a qara din"

"To to shikenan,ba damuwa" ta amsa masa,saiya juya a hankali yana takawa har ya
fita a parlor din,abunda ya bawa iman damar sakewa ta zauna sosai sukaci gaba da
hirarsu da anty hassana,harma ta manta cin abinci ne ya fiddota,bata bar wajen ba
sai da antyn tayi maganar kayan lefen ameen dinnne ake hadawa,ta duba taga sunyi?.

Maida dubanta tayi ga agogo tana son hadiye da kuma basar da abinda ke taso
mata,sai ta miqe tsaye

"Ba lokaci anty hassana,kema ai kinsan kan kaya sosai,munyi da me gyaran jikin nan
kada nayi yamma sosai"

"To shikenan" daga haka ta samu ta wuce kitchen,ta zuba abincin ta tsaya a nan ta
cusa shi,don dama ba wani abincin kirki take iya ci ba,a haka take tilasta kanta
saboda gudun ulcer,don a jikinta ta fara ji kamar tana son kamata ne.

Ba lokacin tayi niyyar fita a gidan ba amma dole ta fidda kayanta don yin
wanka,sai ta tuna sunyi da bushira zata zo da yammar,don haka ta qarasa wajen
wayarta da niyyar kiranta kada tazo bata cimmata ba.

Envelope guda biyu dake nuna shigowar saqonni daga mabanbantan gurare cikij
wayarta ne suka nuna,ta zuba musu idanu kafin ta shafa fuskar wayar ta bude ta nufi
ma'adanar saqonnin nata.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 60

Daya saqon daga banking da take amfani dashi ne,suka turo mata alert na
shigowar kudi a wayarta naira dubu dari hudu da hamsin,mamaki sosai ya kamata,ta
duba sunan wanda ya turo babu suna,pos agent ne,da alama daga wani shagon pos din
kudin suka shigo,to waye zai turo mata wadan nan kudaden?,fita tayi ta buda daya
saqon

*_Assalamu alaikum warahmatullah,ga saqo nan na gyaran jikine,here is my new


number_*

Dr ahmad ne yazo kanta,layi ya sauya kenan,shi yasa koda ta kira kiran bai
shiga,ta sanshi da busy,wala'alla wata sabgar ce ta riqeshi,saita sauka gaba
daya,tayi copyiny number ta fara trying layin daya turo saqon,saidai kuma abun
mamaki a kashe ta sameta,gajeran saqo kamar haka ta tura masa

*_thanks_* ta sauka ta sake kiran bushira

"Ai saidai kiyimin haquri yau amarya,wallahi umma ta aikeni gidan basira,amma zamu
hadu gobe in sha Allah"

"Ba matsala,ki gaisheta" ta sauke wayar tana shiga bandakin.

Tsaf ta shirya cikin atamfa riga da skart,jikinta ba abinda yake fiddawa


sai qamshin hadaddiyar humrar da turarukan jiki dana kaya da aka samar a amaryar kb
global enterprises,ita kanta a karan kanta jin dadin qamshin turaruka take,abinda
ya sanyata ta fara amfani da abinta kenan,ta dauko hijabinta da yasha karin guga
kala da kayan jikinta ta sanya,sai tayi wani irin kyau me sanyi,kyakkyawar fuskarta
ta fita ta tsakanin colour din hijabin da yayi masifar fidda kyau da haskenta wanda
ya cakuda da lafiyayyen gyaran jikin da take samu daga amaryar kb global
enterprises.

Tayi sallama da inna da anty hassana ta wuce zuwa farfajiyar gidan,daga


can sashe daya na 'yar farfajiyar gidan nasu ta hangi malam da amin,malam din na
daga tsaye,amin din ya russuna kadan da alama magana sukeyi.

Cikin girmamawa ta yiwa mallam din barka da warhaka

"Ina zuwa da yammacin nan" dan murmushi ta saka tayi qas da kanta,tanajin nauyin yi
masa bayani,a jikinta takejin idanunsa na kanta

"Zanje waje me saida turare ne"

"To yayi kyau,kada kiyi dare"

"In sha Allah" ta fada tana takawa zuwa gaba a hankali ta tura qofar ta fice a
gidan.

Layin nasu babu mutane sai jefi jefi,hakan baya rasa nasaba da kasancewar
yammaci ce,duk da dama dai unguwar bata fiya cunkoson jama'a ba.

A hankali iska ke kada hijabin jikinta daga hagu zuwa dama,lokaci lokaci
tana saka hannu tana riqeshi saboda yadda yake damunta,kwanyarta na mata tariya na
da lissafin kwanakin da suka rage mata na zamantowa matar wani,sam bataji tahowar
motar ba,sai uban horn da ya kusa gigitata,saitinta ya tsaya,ya sauke glass na
motar,idanunsu suka hadu waje daya,ita ta fara janye idanunta kamar ko yaushe

"Tunanin me kike haka har kin fara hawa hanya baki sani ba" ya fada da muryarsa mai
nauyi da kwarjini,har yanzu idanunsa na bisa kanta,amsar da zata bashi ta laluba ta
rasa,ita sam banda ya fadi bata wani lura ta hau kan hanya ba,kafin ta gama qulla
amsar da zata bashi,har ya bude murfin motar dake daura da ita

"Shigo muje" seat din ta kalla sannan ta kalleshi,kamar zata musa masa,amma bataga
alamar wargi ko wasa saman fuskars ba,a dinke take tsaf,sai tayi taku uku ta qarasa
jikin motarta saka jikinta a hankali sannan ta janye qafafunta ta maida murfin ta
rufe,a hankali ya danna ya dage dukka gilasan sama,a boye ya sauke wata boyayyar
ajiyar zuciya tare da qoqarin danne kanshi da zuciyarsa,wani irin qamshi jikinta ke
fiddawa wanda bai taba jin qamshi me taushi irinsa ba,ya kunna ac motar ya daidaita
sanyinta,sannan ya tashi motar cikin wani kasalallen tuqi suka fara tafiya.

Kamar wadda aka hana ta gaza ce masa komai,tana so ta gani ne yasan wajen
da zata ko kuwa?.

Zaman kurame kawai sukeyi,zaman duka ya gundureta,gaba daya ya cikata da


kwarjininsa ya cika motar gaba daya,baya ga qamshinsa da ya cika mata hanci ya
haifar mata da wata irin kasala da kuma wani irin yanayi mai nauyi a zuciya.

Sannu a hankali sai gasu a amaryar kb global enterprises,mamaki ya


kamata,ta dan juya kanta kadan da nufin duban sashen da yake zaune,saidai yayi mata
kwarjini da yawa,ta gefan idanu dai tana iya ganin yadda ya maida hankalinsa ga
gabansa,baiko juyo sashen da take ba,abinda yasa itama ta dake kenan,ta sanya hannu
ta buda murfin motar ta kuma fice a hankali.

Ta mudubin gaban motar yake hangenta,tana takawa a hankali,wani irin cat


walking take,wanda idan ka nutsu tsaf zaka fahimta,haka yanayin tafiyarta yake,sai
ya janye idanunsa daga kanta yana gargadar kansa.

Taci sa'a ita daya take jira,don haka suna zuwa basu bata lokaci ba aka
fara yi mata,tasan makamar aikinta,ba bata lokaci suka kammala,ima din tayi tsaye a
gaban babban mudubin dake wajen tana kallon fuskar tata,yadda kullum take sake kyau
da sheqi kamae ta jariri,ita kanta tasan gyaran yana karbarta yadda ya
kamata,saidai gaba ta laluba zuciyarta kaf babu wani abu me suna farinciki ko
qanqani a cikinta.

Waiwaya tayi ta miqa hannunta sanda take miqa mata wani turare da kullum
take mulke jikinta dashi baya gama gyaran,ita kanta tana son turaren qwarai saboda
yadda yake da wani irin sassanyan qamshi,ta karba ta zuba ta shafe jikin nata,ta
maida zaman hijabinta a jikinta sukayi sallama ta fito.

Turus ta tsaya cikin madaukakin mamaki,alameen ne a booth din motar,ya harde


qafafunsa waje daya,wayarsa a hannunsa,sai earpiece da ya sanya kunne daya,da alama
waya yakeyi,kallo daya zaka masa ka karanci zaman bai wani dameshi ba,take
zuciyarta ta shiga taraddadin ba ita ya zauna jira ba,qila wajen wani yazo.

Ta fara takawa da zummar ta wuce sai suka hada ido dashi,ya katse wayar a
nutse ya zare earphones din dake kunnen nasa,sannan ya sauka daga saman motar a
hankali,ya taka yana bude murafun motar,dole ta dawo ta bude ta shiga itama ta rufe
murfin ya tada motar,saidai a wannan karon sauke gilasan motar yayi duka iska ta
dinga shiga tana fita ba kamar wancan karon ba,a hankali yaje furzar da iska daga
bakinsa,saiya qara gudun motar ba kamar daxu da suka tafi akan low speed ba.

Titi suka hau sosai,yayin da ta kama gefan mayafinta tana wasa dashi,tunani
iri daban daban fal zuciyarta,ta rasa da wanne zata fara,abu daya yafi damunta
zamansun tare waje daya,babu abinda ke haifar mata sai matsala daga zuciyarta zuwa
gangar jikinta

"Dame dame kuka tsara zakuyi na biki?" Tambayar tazo mata a bazata,har sai data
waiwaya ya dubeshi sanda yake kallon titi,ta dauke kanta tana son yiwa maganar tasa
muhalli,tanajin kamar ba ita ya kamata ya yiwa wannan tambayar ba,me ya kawo
tambayar gareta

"Babu abinda aka tsara" ta amsa masa kai tsaye,saboda tana ganin babu amsar data
wuce haka,baice komai da ita ba yaci gaba da tuqinsa har zuwa sanda suka tsaya a
qofar katafaren wani shago na saida furnitures.

Har ya gyara parking ya fito ya zagayo inda take zaune ya bude mata murfin
motar tana zaune

"Bismillah" yace da ita idanunsa nakan shagon,sai kuma ya fara takawa zuwa gaba a
hankali,bata da wani zabi illa fitowar,duk da batasan me ya kawosu wajen ba.

Bata fuskanta ba kuwa saida suka shiga cikin babban store din,ya sadiqu ta
samu a tsaye a ciki shida anty hassana

"Wayarki saura kadan ta zama mara amfani,ayita kira bakya dagawa" ya sadiqu ya fada
cikin mita,dai dai sanda alameen yayi zaune kan wata kujera dake wajen,ya kuma ci
gaba da amsa wayarsa,wayar data dinga ji cikin jikinta kamar da samha yake.

"Banji ba wallahi yaya" ta fada tana kiciniyar ciro wayar daga jaka

"Kinga yanzu ba wannan ba,ki zagaya ki zabi kalar furniture din da kikeso,dare yana
qara yi,anty na sauri zata koma gida"

Kamar wadda aka bugewa qafafu sai ta koma ta zauna kan daya daga cikin
kujerun dake wajen

"Ya ana magana kika koma kika zauna?" Kai ta girgiza,bata jin zata iya aiwatar da
komai a yadda takejin jikinta,ta lura ba iya bushira da yaagana suka daukaki abun
ba,kusan kowa ma hakane,kamar dama sun gaji da zamanta,har yanxu bata rufa shekaru
biyar a gabansu ba,hakanan duka duka har yanzu shekarun haihuwarta basu wuce
ashirin da uku cikin da hudu ba

"Ya sadiqu,ga anty sannan kuma ace da kaina zan zaba kaya?,don Allah kayi haquri
bazan iya ba wallahi" ta qarashe maganar tana jin wani weakness yana ratsata

"Kaga sadiqu muje,mu zaki tsaya yiwa fulako" cewar anty hassana tana jifanta da
harara wasa,qas tayi da kanta itadai,batasan yadda al'amarin ya kaya ba,illa dai
tasan bayan tsahon wasu mintuna anty ta qaraso wajen tana ta sumbatun kayan,da kuma
kudin daka kashe wajen siyansu,suna daga motar taga fitowar ameen daga shagon
hannunsa dauke da receipt,bata iya qara cewa komai ba har suka sauke anty hassana
su kuma suka dunguma gida.[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: "




Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ's
Privacy Policy
Terms of service
Logout

KUFAN WUTA
Chapter: Shafi na sittin da daya

Share:





Report

KUFAN WUTA
View: 15

Words: 1.6K


Shafi na sittin da daya

Chapter 62
Shafi na sittin da daya

61

*****"To yadda shirye shirye ke kankama hakanan gadan gadan cikin gidan kawai ya
isa gaya maka cewa gagarumin biki aka tarka,yadda suketa shirye shiryensu hakanan
iman ke sabgarta,ganin komai take kamar bazai faru ba,kamar lokacin bazaizo
ba,musamman da ya zaman yanzu ba waya suke da dr ahmad ba,saidai suyu exchanging
tex massage ta sabuwan number dinsa,sai takejin komai kamar ba wani me muhimmanci
ba.

Shaf tama manta saura kwanaki goma biki saida yaagana ta iso,a ranar ma tadawo
daga makaranta kenan ta samu yaagana a parlor har ta watstsake gajiyarta

"Ke kuma daga ina kike?" Ta watso mata tambayar tana mata wani duba na sama da
qasa,da mamaki a fuskarta ta kalli yaganan

"Makaranta mana yaagana"

"Hodijam" ta fada tana kama baki

"Ke a yawon boko zaki qare?,to daga yau koki sanar musu su baki hutu,koma kada ki
shaida musu keda fita makaranta sai bayan biki,gyaran jiki alhmdlh gashi yayi kyau
a ido amma kina maida ma mata aikinta baya?" Mamaki yacikata,ta koma ta zauna kawai
tana sauraren ikon Allah,wai duka meye haka ake mata wani titsiye ne?,jiya jiya
suka gama da bushira kan lefe,don tace ma dr a barsu sai ran daurin aure a kawo
bushiran kamar ta cinyeta danya,yanzu kuma ga yaagana da nata tarin damuwar,sam
itafa ba zata dauka ba.

Batasan da gaske yaganan take ba sai washegari data shirya zata fita
makaranta,da sallama ta ratso ta parlor din,kamar kowanne lokaci matuqar yana a
waje shi idanunta ke fara hasko mata,yana zaune qasan carpet ya tanqwashe dukka
qafafunsa a gaban yaagana,yana sanye da wata jallabiyya ta maza mai gajeran hannu
da wuta me dan fadi ba turtle neck da aka saba gani ba,kalarta ruwan hanta da yayi
masifar haskashi,duk da safiya ce amma qamshinsa ya cika wajen.

A nutse ta qaraso,ta dan rusuna daf da yaaganan tana gaidata,ta amsa tana qare
mata kallo,kallon da iman batason taga tanayi mata shi,saboda tasan indai taga irin
hakan akwai magana bakin yaaganan

"Barka da asuba" ta furta a hankali tana gyara zamanta,sai a sannan ya daga kansa
daga danne dannen da yake a waya,kallo daya yayi mata ya sauke kansa,kamar ma
baisan da wanzuwarta a wajen ba,ya amsa mata da wata irin shariya data sanya ta
sake kame kanta da kyau,gaba daya ta dauke kanta daga sashensa tana duban yaagana
dake mata magana

"Wannan safkon fa?"

"Makaranta" wani duba yaagana tayi mata


"Au ashe jiya baki riqe abinda na gaya miki ba kenan?.....to nabi makarantar da
gudu na tattaketa na kuma bubbugeta da sanda" a hankali ya maida wayarsa aljihu
yana miqewa

"Inason fita yaagana.....zuwa yammaci amma zan dawo" ya fadi mata da tattausan
muryarsa dake cike da nutsuwa da kuma kamun kai

"To ba laifi" daga haka ya taka a nutsensa ya fita a parlor din,abunda ya bawa
yaagana maida hankalinta kan iman,ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,tun
iman na daukan abun da wasa har sai da ta sakewa yaagana kuka,wai me yasa babu
wanda ya damu da damuwarta ne?,ko yaushe kawai sake jefata kawai suke cikin damuwa
da kuma nuna halin ko in kula a kanta.

A hankali inna ta koma da baya,ta saki labulen tana sakin murmushi ba tare da
wani cikin iman ko yaagana ya ganta ba,abinda take shirin yiwa iman din kenan yau
yaagana ta aiwatar,ta tabbatar rashin dangin uwa ko na uba a kusa ne yasa wasu
abubuwan da yawa suke faruwa,ita din tun asalinta me kara ce da alkunya,musamman
akan 'ya'ya,sau tari tanason musu magana ire iren wadan nan abubuwan amma sai taga
kamar rashin kunya ne,har yau har gobe akwai kunya tsakaninta da malam,shi yasa
wani lokaci shike karbe ragamar fadan.

Luf inna tayi cikin dakinta kamar bata gidan,mufida ko dama bata tashi ba tana
fa barcinta,sosai yaagana taci qaniyar iman,sannan ta sanyata ta dauko mata
jakarta,ta dinga fidda rabobi masu dauke da magunguna,tsumammu na asalin kanuri,ba
bata lokaci ta fara hada mata tana bata tana sha,duk da tasan cewa iman din babu
wani abu data rasa na game da budurci,amma hausawa na cewa idan kana da kyau sai
kuma ka qara da wanka,ita kadai tasan kudin data kashe wajen hado magungunan,saboda
bana wasa bane,ko a can ba kowacce mace ke iya siyanshi ba.

Tun iman na kuka da hawaye har ta koma na zuci,saboda iya ranar magungunan da
yaagana ta dirka mata kadai sun sanya ta saddaqar ta kuma tabbatar auren fa da
gaske ne yazo,zuwa washegari kuwa tuni suka fara bin jikinta sosai yadda yaganan
keso,ita kanta ta shaida haka,kawai saita saka kuka,lokacin bushira na dakin tana
duba dinkuna iman din da aka kawo.

Da farko tsoro bushiran taji

"Tsakani da Allah wannan fa daukan haqqine,pants nawa na canza iya yau,haka kawai
an maidaka kamar wata karuwa,wallahi ko ta sake bani zubdasu zanyi" dariya sosai
Bushra ta saki

"To wallahi kin tona kanki,zan gayawa yagana kada ta bari ki matsa daga inda take
saikin shanye koma menene,ina cewa gata akayi miki,shi dr ahmad din so kike ya
rainamu?" Harara me zafi ta watsawa bushira,tana ganin ma kamar bata bakine ta
tsaya ci gaba da magana da ita,kawai saita kewayeta ta fita a toilet din,yayin da
bushiran ta rakata da dariya tana cewa

"Kamar wata baqauya wallahi,idan aka cewa wani nurse kike shirin zama qaryatawa
zaiyi" itadai iman ta fice waje abinta,ranta fal qunci bacin rai da kuma jin
haushin kowa ma.

**********Tun saura kwanaki shida a fara bikin gidan ya fara karbar baqi,dangi
na kusa kusa da inna dana malam din gaba daya,abinda ya sake takura iman kenan tare
da sake sanyayar mata da jiki,ta kuma tabbatar lallai da gaske auren nata za'ayi.

Yau tun safe take ta shiri,akwai guraren da bushira ta matsa mata


zasuje,karbo dinkunanta da kuma siyayya da bushiran tace zatayi cikin
kasuwa,batasan dai me zata siyo ba,amma yawan kudaden da ta bata ajiya ya bata
mamaki,daga nan zasuje amaryar kb yau zata fara mata wani gyaran jiki na musamman
da ake cikin satin da za'a fara biki,duka ba wannan ne a gabanta ba,tana so ta
shiga makaranta tayi settling komai na kwanakin da bazata samu shiga ba.

Comb din da take taje dogon gashinta ta ajjiye sanda wayarta tayi ringing,tasa
hannu ta dauka tana duba me kiran nata,wata abokiyar karatunta ce da suke mutunci
sosai,duk da cewa ta girmeta,don matar aure ce yaranta biyu,saidai tasu tazo daya
sosai da iman din saboda nutsuwar matar.

Gaisawa suka farayi da ita sai ta fara yiwa iman din qorafi

"Yanzu duk yadda muke hajar sai da biki ya rage saura sati daya zamu sani?,kuma har
kizo ki dauki excuse ma ba wanda ya sani?" Mamaki ya kama iman sosai,tama rasa abun
cewa

"Amma mun baki uzuri ai,tunda a qurarren lokaci komai yazo,Allah ya sanya
alkhairi,ranar yaushe ne waliman?" Ajiyar zuciya ta sauke a boye tunda ta samu
mafita,batasan ranae yaushe zatace mata ba,saboda ita kanta batasan yadda komai ke
wakana ba,bushira ce uwa kuma makarbiya ta komai

"Ran juma'a,amma kiyi haquri maman sauda,zan sake kiranki,ayimin afuwa"

"Babu komai" daga haka sukayi sallama da ita ta sauke wayar,mamaki fal
zuciyarta,komai nata a sakwarkwace,banda tallafawar bushira ta tabbatar babu abinda
zai yiwu,idama ya yiwun to zaizo ne a mugun baude.
Amma kuma wa ya shiga makaranta ya daukar mata excuse?,waye ya sanar musu da
auren nata?,tunda dai ita tasan babu wanda ta gayawa,bushira itace amsar data zo
ranta,saita girgiza kai kawai,ta wani fannin bushira na sake samun kima da daraja a
ranta.

Har zata ajjiye wayar sai wani abu yaja hankalinta,ta sauke daukar wayar tana
lalubar number dr ahamd,ba zata iya tuna rabon da suyi waya dashi ba,saidai musayar
text lokaci lokaci.

Kamar ko yaushe yauma data kira dai qin shiga tayi,ita ba'a kashe ba kuma ita
bata shiga ba,mamaki ya kamata ta sauke wayar tana kallon number,dai dai sanda
bushira ta shigo dakin,abinda ya dauke hankalinta kenan bata kuma bi ta kan wayar
ba,har suka fice daga gidan.

Cikin damuwa iman ke kallon bushira

"Na rasa wanne irin zumudi akewa bikin nan,ina tunanin fa ki gyaramin wajen
kwanciya,don bazan iya ci gaba da zama cikin gidan nan ba"

"Bismillah,ina miki maraba,amma dai biki kam bakiga komai ba,bikin mutum uku fa
za'ayi" harara ta watsa mata

"Duk jirgi daya ya deboku daman,ke kika kaiwa 'yan class dinmu gayyata ko?,kika
kuma settling abubuwan da zan shiga yau nayi"

"Abun kuma harda sharri saboda an tsaneni?,nakai musu card tabbas,saboda akwai
qawata a cikinsu,so bazan bata ita kadai na tsallakesu ba tunda nasan kuna
mutunci,amma duka sauran abunda kika fada bansan anyi ba" tasan bushiran,qarya ba
halayyarta bace,tunda ta fada hakanne,to amma waye?,ko dr ahmad ne?,amma kuma
bushira kadai tasan zata shiga yau makaranta,ko inna bata gayawa ba saboda yaa
gana.

Kusan wuni sukayi a waje kafin su gama komai,abu daya ne ya tsaidasu neman
wani turare,ba inda basu duba ba babu,qarshe a wani store akace zasu samu,iman tayi
mitar tayi mitar kan a abarshi su wuce gida saboda gajiyar datayi,tace ta yafe
tunda dai ita zaa nemowa shi amma bushira ta kafe

"Kinsan Allah tunda har angonki nason qamshinsa saina nemoshi ko qarfe dayan dare
zamukai"
"Yaushe kukayi doguwar magana da dr da har zakisan haka?"

"Oho miki" ta fada tana shiga napep,dole itama ta bita tana ta mita amma bushiran
tayi banza da ita.

K'in shiga ciki iman din tayi,tace tana daga bakin qofa,ta shiga ta fito,ta
samu daya daga cikin kujerun dake wajen ta zauna,ta fidda wayarta tanata replying
saqonnin fatan alkhairi da abokan karatunta ke mata.

Bata jima ba sai gata ta fito,ta fidda turaren ta fesawa iman din tana cewa

"Don Allah jimin qamshinsa" Idanunta ta lumshe,sosai qamshin yayi mata,zata iya
cewa wannan shine qamshi na biyu data taba ji me dadi da kwantar da zuciya

"Hajaratul iman ibrahim khalil" sunan da aka kirata dashi kenan,wanda ya sanyata
bude idanunta dake lumshe da gaggawa tana duban sashen da sautin kiran sunan nata
ya fito.

End of book

Leave a comment

Post

Comments
No Comments posted yet

Contact Us
Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742

Email: [email protected]

Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram


Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io

"
https://arewabooks.com/chapter?id=62cecd8e0ba46f15b711502c#:~:text=Chapter
%2062,nata%20ya%20fito.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: "Chapter 63
Shafi na sittin da biyu

Afuwa dai,ayi haquri dani,anata samun mistake,al'amuranne sai a hankali,sabgogi


sunyi yawa

62

  Sauka idanuwanta sukayi aka muneera,itama nata idanun nakan iman din,tana kowa
inda take cikin fara'a da walwala,tsam iman din ta miqe,ta dauki jakarta tana
saqalata a kafadarta,har yanzu idanunta nakan muneera,a duk sanda taga muneeran sai
wasu abubuwa da suka shude marasa dadi sun dinga dawo mata,wannan na daya daga
cikin abubuwan da ya sanya bata qaunar ganin muneera ko kadan

"Anya duniya da amana kuwa?,kin bacemin bat iman?" Muneera ta fada tana qare mata
kallo sanda ta iso inda take tsaye,murmushi ta qaqalo wanda baije ko ina ba,tana
duban muneeran

"Dama rayuwa ai ta gaji haka muneera,wataran za'a hadu kamar yadda dole wataran
arabu" kai ta jinjina 

"Gaskiya ne" ta furta tana qarewa iman din kallo

"Kinga yadda kika canza iman?,kin zama wata big madam,meke faruwa ne?,wannan gayun
da kyan ya zarta wanda na sani a baya"

"Ke bakiga yadda kika koma ba?" Itama iman din ta fada tana dubanta da murmushin
yaqe,da gasken take muneera ta canza,shekaru ba wasa bane,sun jima ita da ita basu
hadu ba,ba zata iya tuna yaushe rabon data sanya muneeran a idonta

"Bansan me nayi miki kika tsaneni ba iman,bayan duk abinda nayi nayi ne da niyyar
alkhairi,naje gidanku na tarar kun tashi,ance an qera muku gida,saidai ba address
babu phone number" kai iman din ta girgiza tana jin qosawa sa tsaiwar
"Bakimin komai ba,kawai Alla ne ya kaw lokacin rabuwarmu,idan babu damuwa zan wuce
don Allah ana jirana"

"Ba damuwa,ki bani address ko number waya,inason na sameki a gida muyi


magana,aurena ya kusa,kuma ya kamata ace kedin kinje....amma idan bazaki damu ba,ga
invitation din,a jiki akwai number wayata,idan kin kirani nayi saving "a gaggauce
iman din ta karba katin,ba tare data tsaya dubawa ta cusa a jakarta,tayiwa muneeran
sallama suka wuce.

      A napep bushira ke tambayar iman din wace wannan,kai tsaye ta gaya mata
muneera ce,saboda basu taba haduwa ba,bata santa a fuska ba,tunda suka dauki hanya
iman din bata tanka komai ba,sai ta samu kanta da tuna rayuwarta ta baya,daki
daki,guraben da tayi kuskure da a lokacin take kallonsa ba'a matsayin kuskure ba
suna fito mata daya bayan daya,kafin su isa gida zuciyarya da qirjinta sun mata
wani irin nauyi,suka hade da gajiyar da suka kwaso,don haka suna sallama da bushira
dakinta ta kulle,ta watsa ruwa ta samu waje ta kwanta tana qoqarin calming down
kanta.

    *_Biki Bidiri_*

   A hankali ta lumshe idanunta tana jin yadda kanta yake sara mata gefe guda,wani
irin ciwon kai ne da tun a jiya take fama da shi,rashin isashen barci,hayaniyar
gidansu gami da fargaba ne duka suka taru suke hade mata.

    Hannunta ta saka ta shafi fuskarta dasu,rangadeden lallen da aka bata wasu


awanni ana zana shi ya bayyana tarwai saman farar fatarta data tsumu da gyara ta
kuma karbi gyaran yadda ya kamata,duba daya zaka yiwa lallen kasan lallai sunzo
qarshen inda akasan ma'anar qunshi da gasken gaske.

    "Bushira.....i have to go......na gaji" bushira da ake zanawa nata lallen tace

"Ba zaki iya tafiya ba ke kadai iman,ki qaran minti biyar yanzu za'a zo a daukeki
don Allah,ki daure kisha magani kafin jibi ki warware,amarya da jinya ai ba kanta"
ta qarashe maganar tana tsokanarta,murmushin da yafi kama da yaqe tayi mata kawai
ta kifa fuskarta saman cinyoyinta,ita kadai tasan abinda takeji,wani abune cure a
qijrinta,inda kuka zaizo mata data fi kowa jin dadi,amma babu shi babu alamarsa,sai
dunqulallen qunci da ya barwa jikinta.

     "Yauwa,muje iman na rakaki ki wuce gida,idan maryam ta dawo aka mata nata
lallen ma taho tare,tunda tace na jirata kinga babu dadi na tafi na barta" bushira
ta fada tana miqewa,sai ta daga kanta a hankali sannan ta miqe,ba tare data ce koma
ba ta janyo mayafinta dake samun kujerar dake wajen ta yafashi saman kanta dake
cike da sassalkan gashin da yasha gyara,babu abinda yake fitarwa sai wani irin
qamshi ke tafiyar da zuciya,cikin set na kayan gyaran amaryar kb global
enterprises.

      A hannu ta riqe dankwalinta hade da wayarta,me qunshin na mata sannu bushira
biye da ita suka fito.

      A hankali take takawa,sam hankalinta baikai wajen ba sai da suka tsaya gaban
motar,hannun bushira dake dauke da danyen lalle ta saka cikin dabara ta bude mata
seat din gaba,qamshi da ya bugi hancinta gauraye da sanyin acn ya ankarar da ita
motar waye,cikin mamaki idanunta fal tarin tambayoyi ta kalli bushira,tafinkowa
sanin yanayi da kuma halin da zuciyarta ke ciki,me yasa zatayi mata haka?,qasa qasa
tace da ita

"Karki zargeni,na rasa wanda zan kirane wallahi,kinsan saurayina baida mota bare na
kirashi,kona kira ma bai kamata nabar matar mutane ta shiga motar wani ba,sai akayi
dace ina kiran yaa ameen din yana kusa da nan" ta yarsa da bushira,kuma tana iya
bakin qoqarinta,bai kamata kuma ga gwale qoqarin nata ba,zamane na mintuna sun isa
gida ita dashi kowa ya kama gabansa,saita dauke idaunta ta shiga motar cikin
sanyi,bushira ta maida murfin ga rufe,sannan ta juya zuwa cikin wajen,daidai
lokacin da ya fara tada motar.

     Tana jin sanda motar ta fara hawa kwalta,idanunta a runtse tana sauraren bugun
zuciyarta da take dokawa da wani irin qarfi,so take tayi controlling kanta kafin ta
buda baki ta gaidashi,saidai sunata kokawa da zuciyarta,ita a karan kanta bata da
muradin kallonsa amma zuciyarta na qarfafa mata gwiwar aikata hakan,ba zata iya
tuna kwanakin data diba bata sashi a idanunta ba,daga qarshe tadan juya kadan ta
dubeshin,duban da bai wuce na Sakan biyar ba,amma ya bar mata miki me tarin yawa
cikin zuciyarta,wani kyau daya sanya zuciyarta bugawa taga yayi,askinsa na musamman
dake qara qawata masa fuska yayi,an rage sumar kansa,bata kai yadda ta saba ganinta
yawa ba,gashin dake fuskarsa kuwa,wani gyara akayi masa na musamman.

 "Ina yini" ta furta tana rufe idanunta

"Lafiya lau" ya amsa mata a taqaice ba tare daya juyo ba,yana jin yadda shima tashi
bugun zuciyar ke canzawa,turaren ta ke fushar hankalinsa,wani mayen qamshi da
baisan a inda ta sameshi ba,saita maida kanta saman qafafunta kawai,can qasan
zuciyarta tana ambatar sunan Allah.

     Idanunta na a rufen taji yana gangarawa gefan titi,sannan yayi parking

"One minute please" ya fada da muryarsa data qara wani irin taushi,tamkar wanda ke
jin barci,ya buda motar a tausashe ya fita,abinda ya bata damar bude idanunwan nata
a hankali,ta zuba masa idanu ta cikin gilashin motar,ta tabbatar bazai iya ganinta
ba,yana takawa da wani irin taku cikin ginshira da kamala,ta dade da sanin cewa an
canza ya ameen tun da dadewa,komai nasa ba irin wanda ta sani bane,bata janye
idanunta ba har sai daya shige katafaren ginin IB COUTURE da yake mallakarsa,wajen
da yayi wata irin shahara taban mamaki cikin lokaci qalilan,yake kuma samar masa da
kudaden dashi kansa bai aza samunsu anan kusa ba.

     Idanunta ta janye,tana sauke ajiyar zuciya,dukka gaba daya yau ya fama mata
wani tafkeken tabo da kuma miki da take qoqarin rage radadinsa zuwa matakin waraka
kar ta shiga gidan wani dashi,sanda take qoqarin janye idanun nata.....a daidai nan
suka sauka kan wasu katina dake kife kusa da gear na motar,ta zubawa bayan baqaqen
katinan da aka yiwa kwalliya da gold idanu,zuciyarta bugawa das das das haka nan ba
tare data san dalili ba,a hankali ta miqa hannuwanta ta daga daya daga cikin
katinan.......cikin sakanin da basu gaza hudu ba ta karanto abinda yabi ragowar
kuzari da kuma walwalarta yayi rugu rugu dashi a take,yasa taji kamar kujerar da
take kai ba zata iya daukarta ba,dukka wani qunci fargaba da damuwa data nannade ta
wurgasu bayan zuciyarta suka dawo fil,a hankali ta runtse idanunta tana qoqarin
maida katin cikin 'yan uwansa,nadama da dana sanin daga katin na saukar mata,sunan
SAMHA da MUHAMMAD AMEEN dake rubuce jikin katin na wulgawa ta cikin duhun idanunta.

     Sake bude idanunta tayi tana fatar daina ganin sunayen da suka kasa bace
mata,saidai tana budesu basu sauka ako ina ba sai akan fuskarsa,yana takowa zuwa
bakin motar,shi da wasu ma'aikata dake sanye da rigar dake dauke da suna da
tambarin kamfanin a gaba da bayanta,tsura masa idanu tayi tana tuhumar
zuciyarta,shin meye dashi ne haka da zuciyarta takasa masa a dalcin tsige duk wata
soyayyarsa datayi saura ta wurgar da ita ta huta?,me ya mallaka daya banbamta da
tarin masoyan dake karakaina a kanta?,kudi?,Kyau?,ko dukiya?,akwai wasu da dama
cikin masoyanta da suka zarta lamin din,amma me yasa lallai lallai saishi?,me
yasa?. Tajefawa kanta tambayar tana maida idanunta ta kulle sanda taga ya sallami
ma'aikatan yana tunkaro motar,kanta na sake tsananta ciwo.

    Tanajin sanda ya buda murfin motar ya shigo,yayi bismillah sanda yake zama,yana
shirin tada motar muryar wani ma'aikaci ta riskesu

"Yallabai,dukka kayanka fa sun kammala"

"Harda gugar?"

"Eh harda ita,amma guda talatin ne suka samu,sauran biyar din suna hannun
inusa,amma yace yau zai kammala su"

"Okay,ka bawa lawan kace idan kun tashi a company yakaimin gida"

"To yallabai,a sauka lafiya" ya fadi yana ja da baya,shi kuma ya tada motar suka
wuce.
     Wayoyinsa yaketa amsawa sanda suke tafiyar,wanda dukkansu kusan sun danganci
dauren auren da zaa gabatar jibi,tayi Allah wadai da ganin baiken kanta na shiga
motarsa yafi sau dubu,ta tabbata da ita din tana da fiffike da tuni ta jima da
sulalewa daga motar takai kanta gida,saidai ba wannan damar,haka ta haqura tana
Allah Allah sukai gida,sam gani take ma tuqin baya sauri,kamar wanda babu laka a
jikinsa.

     "Me yake damunki?" Taji ya jefa mata tambayar sanda suka gangarowa cikin
layinsu,cikin mamaki tayi shuru tana maimaita tambayar cikin kanta ba tare data
bude idanunta ba

"Babu komai" itace amsar data zabi ta bashi,bai sake cewa komai ba kamar yadda
itama bata sake koda motsi ba,har zuwa sanda suka qaraso qofar gidan,ya kashe motar
yana kallon qofar gidan nasu wanda ke a bude da dan tashin maganganun mutane daga
ciki.

      "Wait" ya fadi sanda ta sanya hannu tana yunqurin bude qofar ta fice,wayarsa
ya cire daga charge,ya laluba wata number ya kira

"Fito,ina qofar gida" yafada a taqaice yana cire wayar daga kunnensa,baa cika mintu
guda ba gate din ya bude,badi'a ta fito,ta qaraso bakin window dinsa cikin fara'a
tana masa sannu da zuwa

"Ki rakata daki,ki tabbatar tasha magani" ya bata umarni kai tsaye,sai a sannan ta
kula da iman,ta zagayo fuskarta cike fal da damuwa tana mata sannu,murmushi tayi
qoqarin sakar mata ganin yadda duk ta damu

"Karki damu,dan qaramin ciwon kaine,ina hutawa zai warware" ta fada tana fita a
motar cikin bawa kanta qwarin gwiwa.

     Ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi sanda suka shige gidan,baisan me yasa ya
tsaya kallonsu ba.....baisan me yasa yakejin damuwa ba,baisan me yasa yakejin farga
ba,duka ya rasa dalilin hakan,bashi da wani cikakken qwarin gwiwa,wayarsa data
dauki qara yasa ya maida kansa gareta,ya daga da sauri ya maqala a kunne yana fadin

"Am on my way sorry bello" ajjiye wayar yayi yadan qara mata speed,sam ya mance
yabar baqinsa suna jiransa zai daukosu.

     Koda suka shiga gidan gani tayi kamar baqin ma qara daduwa sukayi,bata da
walwala ko qwarin gwiwar fuskantarsu,hakan ya sanya ta kama hannun badi'a suka wuce
dakinta kai tsaye

"Kijamin qofa idan kin fita,zan sha magani na kwanta,duk wanda zai bugan qofa ko
kikaga yana nemana kice barci nake"

"To yaa iman,Allah ya sawwaqe,kisha maganin don Allah,don nasan idan kawu ya dawo
saiya tambayeni kinsha" kai ta gyada mata cikin dauriya tana sakin mata
murmushi,saidai cikin ranta tana fadin,ba kawunki nada da kika sani bane,a yanzun
bata iman yake ba,duk wata kulawa da zaki gani fake ce,yana yinta ne kawai saboda
inna da malam,yana musu kaara ne.

     Bayan badi'a tabi ta murzawa qofar key,sannan ta jingina da qofar,a hankali


sai abinda ya tsaya mata a wuya tun ganin katinan da tayi ya soma narkewa izuwa
wani kuka mai nauyi da cin zukata,dukka jikinta ya fara shaking hawayen suka cika
idanunta suka fara gudu saman fuskarta,sai tsaiwar ta gagareta,ta sulale a hankali
zuwa qasa tana qanqame jikinga waje daya kamar maijin sanyi,bata wani option a
yanzu banda tayi kukan,shi kadai ya rage mata,ta tabbatar ta gama rasa ameen rashi
na har abada,tayi kuskure guda daya tak daya ruguza mata dukka rayuwarta, maybe
rugujewar ta bibiyeta har zuwa qarshen rayuwarta,taqi shi a sanda gaba daya duniya
ke mata sha'awar kasancewa dashi,sai ta tuna wata magana da inna ta gaya mata sanda
take shirin barin gidan zuwa gidan kawu muntari inda acan ta zauna har zuwa sanda
aka miqata dakin bassam

  *_dama sau daya taj take zuwa maka a rayuwa,sai mai matuqar sa'a ne take
waiwayarsa a karo na biyu,kada kiyiwa kanki hukuncin da zai zame miki qarfen qafa a
rayuwarki_*

    A sannan gani take innar bata fahimci komai ba,gani take inna ta daina sonta
ameen akwai takeso data damu tabar wanda zuciyarta takeso ta auri ameen din,tabbas
maganar inna gaskiya ce,qila tana cikin mutane marasa sa'a a rayuwarsu,wadanda
damarsu bata saje waiwayarsu,ta tafi kenan har abada.

     Dama ta bawa kanta sosai tayi kuka ta qoshi,wanda ya rage mata nauyi me yawa a
zuciyarta,ta kusa awa biyu kafin ta tashu,ta laluba maganinta tasha,sannan ta
qarasa izuwa bandaki.

    Ruwa mai zafi ta hada tayi wanka,tanajin yadda ruwan bai zama saman fatarta
saboda yadda tayi sulbi da yawa da kuma laushi,ta nade jikinta da babban towel
dinta ta dawo daki.

    Sau daya ta kalli fuskarta a madubu bata qara ba,tayi jajur saboda kukan da
tasha,abunka da farar fata,undies ta saka ta zura dogywar riga kawai ba tare data
shafa komai ba banda turare ta haye gadonta a hankali,ta runtse idanunta dake mata
radadi a hankali tana fatan Allah ya aiko mata da barci,saidai amaimakon haka,wasu
hawayen ne masu dumi suka zuraro mata har cikin kunnenta,ta bude idanun nata a
hankali,ta jawo wayarta dake saman kanta,ta bude bayan wayar,ta ciro sabon layin
mtn data siyo tun wancan satin zatayi amfani dashi,ta dora kan wayar ta sake
kunnata,sannan ta tafi kai tsaye tana laluben number ameen din, number da bata taba
kiranta ba tsahon rayuwata,ta zubawa number idanu tana kallonta, number da tayi
saving da MA.

     Tanaso ko yaya kafin shudewar wannan dama da take da ita ta aje masa wani
saqo,koda basu da yawa,koda bazai fahimta ba, at least karin farko ta rage nauyin
dake saman zuciyarta,ta kuma fitar d wani abu daga cikinta komai qanqantarsa,saita
shiga ma'adanar saqonni wajen da zai bata damar aika saqo,ta saka number dinsa ta
fara rubuta masa saqo ta sabuwar number dinsa kamar haka......

"
https://arewabooks.com/chapter?id=62ced7ea0ba46f15b711fc31#:~:text=Chapter
%2063,dinsa%20kamar%20haka......
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 63

_Rasa abinda muke so na nuni ne da cewa rabonmu yana ta can wani wajen yana
nemanmu, dan mun fad'i a soyayyar wani ba wai mun rasa soyayya ta har abada bane,
Ba asara bane danka rasa wanda kake so, asar shine ka rasa kanka wajen kaunar wanda
kai a wajensa ba komai bane, sauk'i yana tare da tsanani, mai hak'uri yana cimma
dad'i, mai kyauta baya rasawa, kowa yaji tsoron Allah, Ubangiji zayyi masa mafita,
manta da damuwa ka fuskanci rayuwa, kowa ka gani a duniya akwai abinda ya dame
shi,fatan nasara sa kuma fatan dacewa ga sabuwar rayuwar da zata fuskanci kowanne
bawa_

Dai dai sanda saqon ya isa dai dai lokacin ga lumshe idanunta,hawaye suka
gangaro,sai ta danna wayar ta kasheta gaba daya,ta yadda bazai sameta ba,koda ace
zaiyi yunqurin kira don bin ba'asin wanda ya tura saqon,a hankali ta tunda da ita
din mahaddaciya ce,ta kama farkon suratul a'araf can qasan ranta tana karantata,a
hakali idanunta suka fara nauyi,baccin da bata zaci zuwansa ba ya rarrafo ya rufe
mata idanuwa ruf.

_sai muce a tashi lafiya amaryar dr_😊

Sanda saqon ya rikeshi yana zaune tsakiyar baqinsa suna duba kayan da zasu
sanya ranar daurin aure,wanda dukka abokan angon akayi musu dinki iri daya,ya
karanta saqon ya sake maimaitawa ya kusa sau biyar,baisan number din ba,sai yayi
yunqurin bi ya kira don yaji waye kamar yadda ta zata,saidai ya tadda layin a
kashe,ya sake gwadawa suka sake bashi amsa guda daya dai,dole ya maida wayar ya
ajiye yana tattara hankalinsa ga abinda sukeyi,saidai abun mamaki saqon ya tsaye
masa cak a zuciyarsa,ya kuma barshi da tunane tunane,hakanan ya samu kansa da
yawaita duba wayar lokaci zuwa lokaci,kamar me neman wani abu.

Sanda samha ta kirashi ya duba wayar da wani zato daban a ransa,bai daga ba
yasa wayar ne a silent,saboda yasan maganar da zatayi masa

"Anata kiranka fa" daya daga cikin abokansa me suna abdus sabur ya fada,sai ya
dauki wayar yadan matsa daga dakin zuwa farfajiyar hotel din yana kara wayar a
kunnensa.

Lumshe idanunsa yayi bayan yayi sauraro na wasu mintuna kana ya budesu

"Samha......na gaya miki am not interested....


Albarkan aure nake nema,kuma albarkan yafi dukka wani abu da za'ayi,am ready to pay
ko nawa ne indai walima ne,so karki sake sako maganar wani dinner ko something else
please" daga haka ya datse wayarsa,ya furzar da iska daga bakinsa,baisan me yasa
samhan ke matuqar son bidi'a a biki ba harda wadda ta wuce gona da iri ba,ya shirya
musu walima a waje mai tsada ya kuma kashe kudi sosai,hakanan shima ya shirya
reception na musamman shi da abokansa immediately ana gama daurin aure,shi wannan
yafi burgeshi tun asali dama,ma'adanar saqonninsa ya bude yana sake karanta saqon
dazu,sai ya samu kansa da sake trying kiran wayar,amma dai amsar iri daya ce switch
off,haka ya juya zuwa ciki,zuciyarsa cike fal da tunani iri daban daban,yana jin
samha na kira amma ya shareta ya sanya wayar don't disturb yaci gaba da sabgarsa.

**********Sosai gidan ya sake hautsine da jama'a da kuma baqi iri daban


daban,lallai bikin mutum uku ba wasa bane,tuni iman ta aro dukka wata juriya da
dauriya ta azama kanta,tunda kowa ya sani bikin dake hade dana maza da kuma
mace,macen kusan itace take zama madadin sauram angwayen,kowa yazo ita yake
nema,irin tarin kayan da taga inna da malam sunyi mata yayi matuqar bata mamaki
qwarai da gaske,kaya ne na gani na fada,kaya na 'yar gata wanda ba kowacce mace ke
samun irinsu,ko ba'a gaya mata ba ta tabbatar da cewa sun kashe iyayen kudi masu
yawan gaske,hakanan ta fannin cimar abincin biki babu abinda ba'a tanada ba cikin
gidan,tun daga ranar yau din da take gobe daurin aure gidan ya kaure da hada
hada,tuni su yaagana aka shiga hidima,yaa baraka ce bata qaraso ba sai a
gobe,saboda daga can wajen ma a jigawan tana da baqi,kuma zatayi nata bikin.

Sanye take da wata doguwar rigar atamfa exclusive,dinkin free gown wanda
yayi matuqar zauna mata a jikinta,tun daga nesa idan ka hangeta zakaga yadda take
zuba qyalli tako ina,irin qyallin nan da ake kira na amarci,nata na musamman ne
tafe da wani irin kyau da kwarjini data yi,a hankali take ratsa mutane,fuskarta a
sake tana magana da wasunsu idan sukaci karo,innarta take nema tun dazun,saidai
innar tayi mata baton dabo cikin gidan,daga qarshe mufida ta gano mata innar cikin
kitchen,saboda haka ta nufi can din kai tsaye.

A tsaye ta hangi innar ita da wasu 'yan uwanta guda biyu,sai wani a tsaye
wanda ya baiwa qofa baya,kuma tun kafin ta qarasa zuciyarta da gangar jikinta suka
bata lamin ne,sabida tsaiwarsa ba baquwa bace a wajenta,yana tsayen hannayensa zube
a aljihun rigarsa.

A hankali ya waiwaya sanda tayi sallama,sai kuma ya dauke kansa ya maida


ga inna sautin matan na amsa sallamar tata yana karade kitchen din

"Yauwa to shikenan,jeka ma ga iman nan sai ta kawo maka,ka kira sadiqun ku zauna da
Allah kuci abincin,itama ka turke min ita,gaba daya ku ukun kun sauya kun zama wasu
iri,kullum da abincina kuke barina,sai tafiya kuke da yunwa a cikinku,kada ma kai
kaji labari,mutumin da baya wasa da cikinsa amma yau ya zama haka?" Daya daga cikin
matan dake aikin abinci a wajen ta saki dariya tana cewa

"Aure kenan,ai aure ba wasa bane" dan qaramin murmushin gefan baki ya saki,shi bama
abinci ba,komai jinsa yake wani iri,wai a goben ne zai zama magidanci kamar
kowa?,hatta da gangar jikinsa bayajinta yadda ya saba ji,yana matuqar jin dadin
nuna kulawa da damuwa da al'amarinsa da inna keyi,ya rasa dame zaya saka mata a
rayuwa?,kome zuciyarsa tace ya yiwa innar sai yaga yayi kadan a tsaya dai dai da
matsayin abinda tayi masa a rayuwa

"To na gode,a fito lafiya" ya fada cikin girmamawa yana juyawa,sannan yabar kitchen
din.

Ko tsayawa jin abinda ya kawota innar batayi ba yasa lami wata cikin matan
ta hada abincin tace ta dauka taje can suci,sai tafi sakewa saboda can sashen nasu
ne babu mutane sosai,kamar ta aza hannu aka haka ta dauki kayan abincin,saidai duk
wanda ya kalli fuskarta yasan akwai abinda ya sosa zuciyarta.

Zaune yake saman kujerar falon,ya jingina bayansa da kujerar yayin da yayi
crossing qafafunsa,hannunsa riqe da wayarsa yana taba a hankali,yana fuskantar qofa
ne,ta yadda duk wanda ya shigo shi xai fara gani.

A nutse ya daga kanshi yana amsa sallamarta,sallamar data yita ciki ciki,ya
zube idanunsa fes saman fuskarta yana nazartarta,fuskarta ta sake zama cute and
adorable,komai nata ya canza,saidai sauyin mode dinta ya tsaya masa a rai,ba haka
fuskarta take ba sanda ta shigo kitchen din ba,ya kafeta da idanunsa da taji sun
mata nauyi suna shirin kayar da ita harta iso ta ajjiye abincin,ta kuma tashi da
niyyar tafiya

"Zo nan....dawo ki zauna" ya bata umarni kai tsaye,yadda umarnin ya fita da sautin
muryarsa datai kauri da kuma nauyi yasa ta kasa bijirewa abinda yace din,saita dawo
ta kuma zauna nesa dashi.

"Ba cewa inna tayi kici ba?....oya,maza zuba" ya fada nuna abincin da hannu,batason
maganar tayi tsaho,don haka ta fara zubawa a plate.

Ci gaba yayi da duban fuskarta,a hankali yace

"Me ya bata ranki?" Tambayar data sanyata tadan daburce kadan,batayi tunani zaiyi
noticing hakan har ya tambaya ba,sai ta miqe da kwanon tana cewa

"Babu komai,zan wuce da abincin ciki zanci a can,ana jirana" kamar ba zaya amsa
ba,sai kuma ya gyada kansa,baiga muhallin takura mata ko matsa mata ba,ya bita da
rakiyar idanu sanda take takawa,duk da cewa cikin mayafi take,amma yana iya hangen
yadda sassan jikinta suke juya kansu da kansu

"Ya Allah" ya fada yana lumshe idanunsa,yafi kowa sanin akwai wannan tattare da
iman,shi yasa ya zama telanta yake kuma tattalin duk wata sutura ko dinki da zata
sanya a wancan lokacin,kafin ta wargaza komai da hannunta.

Number badi'a ya laluba ya kirata,ya kuma gaya mata ta tabbatar iman din
taci abincin data fita dashi saboda ya idar da saqon da inna ta danqa a
hannunsa,babu jimawa badi:an tayi masa text kan taci,sai ya jawo abinci ya buda ya
fara zuba nashi yana kiran sadiqu yaji a ina suke shima.

*_RANA BATA K'ARYA saidai uwar diya taji kunya inji 'yan magana_*

Yau take juma'a,kuma dai dai da ranar da dukka bangarori waliyyai da kuma
wakilan angwaye da amarensu suka tsayar a matsayin ranar daurin auren yaran nasu,ta
kowanne sashe idan ka kalli gidan cike yake da al'umma,kowa cikin ado da
mabanbantan shiga da zata nuna zallar farincikin da mutanen ke ciki,hayaniya ke
tashi tako ina,ga abinci nan da aketa hada hadarsa tun daga tashinsu har zuwa yanzu
da zugar maza mai yawa tayi gaba zuwa gidajen amaren don dauro auren angwayen guda
biyu,kafin a dawo a daura na iman wanda shine na qarshe dama a yadda aka tsara.

Daga can ciki quryar dakin iman,iman dince tare da qawayenta,wanda kusan
a cikinsu zata iya cewa babu wanda ta bawa card din gayyata da hannunta,kusan dukka
bushira ce tayi wannan aikin.
Tayi kyau iya kyau,kai kace diyar sarkin aljanu ce cikin shigar fari da
gold,tun daga suturar ciki zuwa ta waje,komai nata fari da gold ne,shigar da tayi
masifar hawa da fatarta,bawai kwalliya tayi ba,aah,hasalima banda hoda babu komai
saman fuskarta,saidai wani glowing da take zaka dauka canza iman din akayi ko kuma
wankan inji akayi mata,jikinta wani irin mayataccen qamshi yake fitarwa,wanda duk
wanda ta gifta sai yace

"Kai masha Allah,lallai amarya da gaske kinsha qamshi" tuntuni kafatanin ilahirin
kayanta bushira ta zauna tasa kabbasa ta turare mata su,qamshin ya cakuda dana
jikinta ya bada wani ni'imtaccen qamshi,sahihin hadin turare daga AMARYAR KB GLOBAL
ENTERPRISES da kuma hadi na musamman daga wajen yagana tun daga maiduguri.

Dukka maganganu hira da kuma tsiyar da suke mata bin kowa da idanu kawai
take,wayarta na hannunta tana jujjuya wayar,shigowar wani saqo mintuna talatin da
suka shude shi ya sake jefata duniyar tunani,saqone daga dr Ahmad,dr din data manta
rabon da taji muryarsa direct ta waya,saidai musayar saqonni kawai,ta gaza gane ko
fahimtar dukka kalmomin da saqonsa ke dauke dashi,kanta ya daure tam,don haka taci
gaba da juya wayar kawai,tana tunanin dimuwa da yadda zuciyarta ayau din ke wani
irin bugu da sauri ya haifar mata da dodewar tunani ta kasa kowanne irin tunani
akan saqon.

A hankali a hankali hayaniya ta sake qara qarfi cikin gidan,har iman din
taji kamar wani abu yana hawa kanta

"Mun dawo,ai an daura,saura na iman.....eh suna waje" muryar halifa wani jikan
yaagana ta iso har inda iman din ke zaune.

Yadda zuciyarta ta buga ya sanyata furta

"La haula wala quwwata illa billah" hadi da rintse idanunta,shikenan.....shikenan


ta faru ta qare fa furta can qasan ranta,ta maida bayanta sosai jilin kujerar da
take kai ta runtse idanunta,kunnuwata nata debo mata hayaniyar jama'a mabanbanta a
cakude da surutai iri daban daban.

"Lafiya dai ko?" Taji muryar bushira daga gefanta,ta bude blue eyes dinta
da suke wani sheqi ta zubesu fuskar bushira

"Kun cika surutu wallahi"


"To a gidan makoki muke da za'a hanamu magana?" Bushira ta fada tana
harararta,tadan zubawa bushiran idanu cikin mamakin yadda take ta sabgarta
itama,kamar batasan komai kan sha'aninta ba.

Wayarta ta miqawa bushiran bayan ta bude saqon

"Karanta" tace da ita a taqaice,saita sanya hannu ta amshi wayar,ta kuma duba saqon
kamar yadda ta umarta,tabe baki tayi ta miqa mata wayar

"Ungo,ni ban fahimci komai ba" idanu tadan zuba mata,sai kuma ta amsa wayar kawai
ta maida idanun nata ta rufesu ba tare data sake cewa komai ba.

Daga inda take tana iyajin yadda aketa bada umarnin shirya abinci,saboda
yanzu yanzu za'a gama daurin aurenta,ana gamawa kuma ance a fiddashi sanoda mutane
suci su samu tafiya da wuri,tsam ta miqe qafafunta na rawa,wani irin fargaba da
tashin hankali ma cika qirjinta,saita kawai fa nufi toilet ta tura qofar ta
shige,bushira wadda ita daya ke ankare da ita ta bita da kallo har zuwa sanda ta
shige din,sai taci gaba da sabgarta ba tare data ce mata komai ba.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 64

Sosai ta dafe sink tana duba fuskarta a madubi tana son bawa kanta qwarin
gwiwa,tana son gayawa kanta da kanta kalmomin da zau qarfafeta,saidai duk yadda
takai ga wannan dakiyar abun ya faskara,wasu irin hawaye masu zafi ne suka kubce
mata,saita sadda kanta tana kallon yadda suke diga dis dis dis,duk da haka bata
sare ba tana qarfafawa kanta gwiwa.

A qalla ta shafe mituna kusan ashirin cikin bayin,saita yagi tissue ta


gyara fuskarta,ta kalli kanta kana ta fara takawa zuwa bakin bandakin,ta sanya
hannu ta bude qofar,kalmar farko data shiga kunneta cakude da guda ta haifar da
wata irin tsawa tsakiyar kanta,tsawar da ta sanya kanta a take ya sara,ciwon kai
kuma ya saukar mata,ilahirin jikinta ya dauki rawa,ta zubawa ya baraka dake dakin
tana sakin guda idanu

"Allah na gode maka,ko yau na mutu burina ya cika,iman ta zama ta lameen lameen ya
zama na iman,alqawarin Alla ya cika" bakin yaa baraka takebi kawai da kallo,ta
tabbatar da cewa yaa barakan ba zata taba yin wasa makamancin wannan ba,saboda baby
wasa a tsakaninsu,tamkar wata doluwa ta tsaya kawai tana kallon ya baraka,bushira
data fara hangota ta qaraso bakinta kamar zai bare

"Kizo ki bani tukuicina na wahalar banza dana dinga yi na rarrashi kan dr ahmad din
bogi......harda tafiya toilet za'ayi kukan gulma,anaso ana kaiwa kasuwa" ta qarashe
fada qasa qasa tana dariya.

Lokaci daya taji zuciyarta na gaya mata cikin duniyar mafarki take,ta
runtse idanunta da qarfin gaske tanason tabbatarwa kanta mafarki ne ko kuwa
gaske?,gudar da wata cikin qawarsu ta sakar mata a tsakiyar ka ya sanya kanta ya
sake sarawa,sai gwiwoyinta sukayi sanyi,maimakon hawaye a wannan karon gabbanta ne
suka gaza daukarta,numfashinta ya fara kakkatsewa,batasan me yake faruwa ba,ta
daiji qafafunta sun kasa daukar gangar jikinta,a hankali taji tana sulalewa,takai
qasa bata kai qasa ba dukka bata da wannan amsar.

Sama sama kamar kuma cikin duniyar mafarki take jin hayaniya cikin kanta

"Bata farka ba likita" wata murya data kasa tantance ta wace tayi maganar cikin
sanyi

"Kada ku damu,zata farka,ba wani abu bane babba ya sameta ba,razana ce ko kuma taga
wani abu da yayi matuqar bata tsoro ko firgitata,zata farka nan da kowanne
lokaci,anyi mata allurorin bacci ne don qwaqwalwarta ta huta" muryoyi iri daban
daban suka hau masa godiya.

Wadan nan maganganun suka tabbatar mata a duniya take,kana kuma ba mafarki
takeyi ba,don haka ta fara qoqarin buda idanunta da takejin kamar an watsa mata
tsakuwa,sun bude din saidai hasken daya cika dakin taji ya yiwa idanun nata
yawa,wala'alla hakan yana nufin idanun nata sun jima arufe

"Hasbiyallahu la'ilaha illa anta" tayi qoqarin furtawa,abinda yaja hankalin dukka
wanda yake kusa dasu

"Ta farka likita.....ta tashi" muryar yaagana cikin zumudi ta fada,abinda yasa
likitan tsayawa sannan ya juyo zuwa inda iman din ke kwance,zuwa sannan idanun nata
sun samu damar budewa,dukka jama'ar dake dakin ta bisu da kallo tana amsa sannun da
suke mata daya bayan daya,yaa baraka,badi'a,bushira yaa gana da anty lami qanwar
inna.

"Sannu ya jikin?" Likitan ya tambaya yana buda file dinta dake nuni da
sabone

"Da sauqi" ta amsa masa da dasashiyar muryarta


"Ma sha Allah,me yake damunki yanzu?" Ya sake tambayarta yana gyara gilashin
fuskarsa

"Babu komai,sai kaina da nakejin yamin nauyi kadan"

"Babu komai zai daina" ya sake fada yana duba zubar qarin ruwan,magunguna ya rubuta
ya bada file din

"Zuwa anjima kadan zan sake round na dubata,da yiwuwar basai ta kwana a asibiti ba"
"To likita,sannu da qoqari" cewar yaa baraka,juyawa yayi ya fice,abinda ya basu
damar sake matsowa suna dubata,kowa na nuna kulawarsa a kanta,binsu take da kallo
kawai,zuciyarta na mata tariyar abubuwan da suka shude a baya

"Ya kamata tasa wani abu a cikinta kafij tasha magungunan nan" anty lami dake saman
kujerar dake dakin ta fadi sanda usama dan yaa baraka ya shigo da magungunan

"Gaskiya dai,don na tabbatar babu komai a cikinta,don ko da safe bushira tace


bataci komai ba" sai a sannan ta daga kanta tana duban window din dakin,duhu ya
ratso sosai,da alama an jima da yin sallar magariba,to duka tsahon awannin suma
tayi ko barci take?,yaagana tacewa zata shiga bandaki,bushira ta qaraso zata kamata

"Barshi zan iya zuwa da kaina" duk da hakan bushira bata barta ba,saita taka mata
har qofar bandaki sannan ta jirata ta fito,alwala ta daura ta nema abun sallah
bayan ta tambayi qarfe nawa?,badi'a tace mata qarfe tara na dare,ta jinjina abun
cikin ranta,a yau ta rasa dukka sallolinta na ranar,a zaune tandinga ramasu gaba
daya guda hudun saboda rashin cikakken qwarin jiki,bayan ta idar ta miqe a hankali
tahau saman gadon sosai ta zauna,yaagana ta saka mata pillow daga bayanta yadda
zataji dadin zaman,daidai lokacin da usman qanin usama ya shigo dauke da manyan
ledoji

"Ina ka shiga tun dazun?,anata neman dan aike da zaije gida ya karbo mata wani abun
tasa a cikinta?"

"Kawu ne ya kirani,gashi yace na kawo" yamatso kusa dasu ya ajjiye,badi'a ce ta


tsugunna tana fidda kayan abincin,kana gani basai an gaya maka ba takeaway ne,amma
bisa tsari da tsafta,faten dankalin turawa ne me kayan lambu da wadatacciyar hanta
da qoda mai yawa,zazzafan ruwan zafi da yaji kayan qamshi,sai kuma wasu plates dake
nannade wanda aka shirya fried rice da coleslaw sai gasashiyar kaza.

"Matso bushira ki zuba mata wanda zata iya ci" yaa gana ta fada,saita matso
ta zuba komai a plate,da kanta taja kujera ta zauna gaban iman din,ta kalleta
fuskarta dauke da murmushi,kamar ma qunshe dariya take,ta ajjiye plate saman cinyar
iman din

"Oya mrs lameen,ga abinci"dubanta iman kawai tayi ba tare data ce komai ba,don har
yanzu qwaqwalwarta da zuciyarta sun kasa yarda da abinda ya farun,garin yaya?,waye
ya qulla ko ya shirya?,tallanta aka yiwa lamin?,ko.haquri aka bashi?,ya akayi dr
ahmad ya barta katsam ba tare da sanin ko yardarta ba?,wanne laifi ta yi masa data
cancani ya barta haka kamar wani abu ne mai sauqi aikata hakan?,wadan nan
tambayoyin ta dinga yiwa kanta sanda take kai cokalin abincin bakinta,kaiwa kawai
take ba tare data lura da abinda take diba ba

"Kici abinci da kyau mana iman,wanne irin ci kike masa ne?,sai diban ruwan kike kin
bar abubuwan amfanin" duban tsanaki tayi ma plate din,sai ta fara hadawa da
dankalin tana ci a hankali,cusashi kawai takeyi,amma bakinta sam babu dando.

Tana tsaka da tsakura aka turo qofar dakin,sallamarsa ta karade cikin


husky voice dinsa ta ratsa dakin tun kafin takai ga daga idanunta taga wanda ke
shigowar,idanunshi bisa saman fuskarta,itace ta farko a dukka dakin da idanunsa
suka fara sauka akanta,yayin da ita kuma ta gaza daga qwayar idanunta ta
kalleshi,kamar yadda ta gaza ci gaba da cin dankalin da bushira keta mitar ba wani
ci take ba,ta fara motsa cokalin cikin plate din.

Dukka dakin suka fara masa maraba da shigowa,ya janye idanunsa a hankali
daga kanta ya maida ga jama'ar dakin,ya fito shar cikin shadda gezner mai asalin
kyau da tsadar army green me haske,dinkin babban riga da 'yar ciki da dogon
wando,takalmin qafarsa rufaffe ne baqi,duk da darene hasken fitilun da suka wadaci
dakin sun fidda kyau da walwali da shigarsa takeyi,tun daga hularsa takalmi zuwa
shaddar dake jikinsa,kai da gani basai an gaya maka ba zakasan cewa ango ne.

Yadda takun takalminsa ke bada sauti haka bugun zuciyarta ke


daduwa,qamshinsa ya mamaye ilahirin dakin,kamar shi daya ne ke amfani da turare a
duniya,qamshi mai sanyi da tafi da tunani,ba me qarfi da saka damuwa ba.

Miqewa bushira tayi daga inda take zaune itama tana masa sannu da zuwa

"Yauwa sannunku" ya amsa mata yana isa gaban kujerar bayan sun gama gaisawa da
mutanen dakin,dafe makarin kujerar yayi kawai da hannuwansa ba tare da ya zauna ba

"Sannu,ya jikin naki?" Ya tambayeta idanunsa na bin hannayenta daya tsaru da lallen
amarci tana wasa da spoon cikin abincin

" Da sauqi" ta amsa masa tana jin kaifin idanunsa a kanta,wani irin kwarjininsa ne
na musamman ya saukar mata,gefe daya kuma wani tsoro da cika ido nasa suka mamayeta

"Tunda Allah ya kawoka kai ka gwada ko zataci abincin,mu munyi iya yinmu taqi cin
abin arziqi,ga magunguna agabanta suna jiranta" yaagana ta fada tana saba jakarta
tare da miqewa tsaye tayi qofar waje,da daya da daya sai gasu suna ficewa daga
dakin,kafin kace wani abu dakin ya koma wayan,daga ita sai shi.

Shuru ne ya ratsa dakin,kamar babu sauran wata halitta a cikinsa,kurrrr


yaja kujerar baya kadan,sannan yayi taku biyu,ya isa gaban kujerar ya zauna,qiris
ya rage gwiwoyinsu su hade waje daya saboda irin kusancin dake tsakaninsu,qirjinta
ya tsananta faduwa lokacin da taji hannunsa saman nata hannun,ba musu ta sakar masa
plate din da yake niyyar karba din,ya daukeshi daga saman cinyarta zuwa tasa
cinyar.

Sosai ya nannade babbar rigarsa,yayi bismillah ya debo abincin yakai


bakinsa,sai kuma taji yace

"Oya,take it" tare da kafeta da idanu,yana tauna dankalin a hankali cikin bakinsa.

"Open your mouth mana,ko sai na tashi?" Ya fada a dan kausashe wannan
karon,jin ya motsa ya sanyata daga idanunta da sauri tare da bude dan qaramin
bakinta hadi da daga idanunta zuwa fuskarshi,ta tsammaci zai taso inda take ne.

Shigarsa ta fara keta tunaninta,kyansa ya bayyana baro baro saboda kusancin


da ke a tsakaninsu,saita runtse idanunta sanda yakai cokalin bakinta,yayin da shi
kuma yabi qaramin bakin nata da kallo wanda yadan sake yin jaa,tsigar jikinsa ta
zuba,karon farko daya sake yiwa fuskarta kallon qurilla daya wuce kima,saboda yana
da tabbacin a yanzun bai wuce kimar ba,bai kuma taja sharia ba.

Saman cinyarta ya maida abincin,yaja kujerarsa gaba sosai ya cike sauran


gap din da yayi saira a tsakaninsu,a hankali ya kama qafafunta dake lillo ya dora
saman cinyarsa,qanqame jikinta tayi waje daya tana jin tsigar jikinta na
zubawa,mamaki sosai ya cikata,bayajin komai ne?,baya gudun ta bata masa wannan
shaddar tasa me dan karen tsada?,dama ya bata kan taci da kanta,gaba daga a takure
take,wani kunya da nauyinsa ya cikata,ga kuma dumin tafin hannunsa dake saman
qafafunta yana ratsa kowacce gaba da sashe na jikinta.

Tanayin spoon daya taga ya dauke cokalin shima ya sake diba yakai
bakinsa,ya sake miqa mata taci ya kuma karba,da alama karba karba yakeso suyi da
cokali daya,abinda ya sake daure mata kai,ya kuma jefata a tunani,har ta kasa
daurewa ta daga idanunta ta saci kallonsa,sai gashi karaf ya kamata.

Girarsa ya dage mata kana ya langabar da kansa

"Karki damu,bazan cinye miki ba,banci abinci bane tun safe....." Qas tayi da kanta
saboda yadda lumsassun idanunsa ke saukar mata da gajiya,haka sukaci gaba da karba
karba,idan tayi spoon daya shima shima zai karba yayi,wani lokaci kuma har spoon
biyu yakeyi,da haka ta tabbatar da gaske lallai yunwar yakeji sosai kuwa.

Wasa wasa sai gashi sun tashi da dukka dankalin dake wajen,ya miqe da
kansa ya dauke plate din,ya ajjiyeshi,ya dauko tissue da kuma magungunan nata ya
dawo ya zauna kamar yadda yake daxu,ya miqa mata tissue da ruwan,magungunan kuma ya
balla da kansa,ya buda tafin hannunsa ta miqa mata yana kafeta da idanu,yana tuna
yadda take gudun magani.

Sauke idanunta tayi kan lallausan jan tafin hannunsa me dauke da zara
zaran yatsun hannu,ta kalli magungunan,ta miqa hannu da daya da daya tana dauka
tana kuma runtse idanunta tana korasu da ruwa,guda dayan data rage ta miqa hannu
zata dauka,sai ya maida hannun ya rufe harda yatsunta da suka shiga ciki,tsigar
jikinta ya zuba,tayi nufin janyewa amma yayi mata riqo irin na maza,duk da cewa
babu zafi a riqon amma tana jinsa har cikin qashinta

"You better stop it iman......me yasa koda yaushe kike kai kanki asibiti?,rayuwarki
nada tsada.....kuma yi miki auren dole bashi yake nufin rayuwarki tazo qarshe
ba,kada ki damu, there is a way.......akwai chance da zan baki,ni bazan takuraki
tauyeki ba" mamaki daurewar kai da rudani suka kamata lokaci daya,dole ta sake
dubansa don tabbatar da abinda ke saman fuskarsa,ya tsareta da sexy eyes dinsa da
suka sake lumshewa kamar mejin barci,dai dai lokacin aka tura qofar tare da yin
sallama.

Fauzan ne daya daga cikin abokansa na kusa kusa,tunda dama shi bashi da
wani amini sama da sadiqu,tare suka taso tare suke sharing matsalolinsu,kunya ta
cika iman,ta soma qoqarin zame hannunta amma yaqi bata wanna damar

"Sir lokaci yana tafiya fa" ya fada cikin salo na tsokana,ameen din bai damu ba sai
ya duba agogon hannunsa yana cewa

"Ta nan dinma wani aiki nakeyi.....da Allah taimaka ka duban likitan nan yazo ya
sallamemu....inajin zata iya kwana a gida ai" ya qarashe maganar yana aza mata
idanunsa daa kasa jurewa daukarsu,yanata dora mata nauyinsa ga kuma nauyin fauzan

"Ba matsala,madam ya jiki?"


"Da sauqi" ta fada cikin wani irin sanyi
"To Allah ya bada lafiya" yayi maganar yana juyawa ya fice abinsa ba tare daya
tsaya jin amsarta ba,saboda ya lura nauyinsa takeji,uwa uba lamin din harara yake
maka masa a fakaice,don dankwali ne kawai saman kan iman din.

A hankali ya sakar mata hannu,ya tura kujerar baya ya miqe,ya fara tattara
magungunan yana maidasu leda,ya gama yayi musu waje,ya dawo gabanta ya zuba
hannayensa cikin aljihun wandonsa yana ci gaba da kallonta,kamar zata nutse haka
takeji,kamae gadon bazai dauketa ba,gefe guda kuma kalamansa na mata yawo aka,tana
son fahimtar abinda yake cewa.

Turo qofar da akayi ya maida hankalinsa ga qofar,likitanne ya shigi,ya bawa


lamin hannu sukayi musabaha sannan ya dudduba abinda ya kamata ya duba din,ya maida
hankalinsa ga lamin ya masa dukkan bayanin daya dace yayi,kai yake gyadawa cike da
gamsuwa har ya gama sannan ya bashi amsa

"Inajin kamar wannan file din daga yau ya gama aiki,indai wannan damuwar ce ba zata
sake kawota asibitin nan ba,saidai wani ciwon kuma daban idan Allah ya kawoshi,in
sha Allah" murmushi likitan ya saki,kalamansa sun burgeshi,ya miqa masa hannu
sukayi musabaha yana cewa

"Well-done,Allah yasa" ya bashi file din yace zaiji balance na abinda zasu cika a
reception,duk da cewa baya tunanin zasu cika din saboda kudin da suka ajjiye kafin
ayi admitting nata,qilan ma ciko za'ayi musu.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: "




Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ's
Privacy Policy
Terms of service
Logout

KUFAN WUTA
Chapter: Shafi na sittin da biyar

Share:





Report

KUFAN WUTA
View: 852

Words: 1.8K


Shafi na sittin da biyar

Chapter 66
Shafi na sittin da biyar

65

Waya yayi daha waje ta 'yan sakanni zaiga usama ya shigo,ya miqa masa file din

"Kaje kuyi settling komai,idan ka gama ka samemu a waje"


Qarasowa inda take bushira tayi,murya qasa qasa take tsokanarta

"Irin wannan luf da kukayi a daki?,ahhh.....sai naga kuma kwanin abincin babu
komai,a ina kuka zubashi?" Bashi da nisan gazara tsakaninsa dasu,yana tsaye tana
magana da yaa baraka,don haka ta watsawa bushira harara da sauri,dariya bushira ta
bushe da ita,koda bata buda bakinta tace komai ba,kana kallon fuskarta zaka
tabbatar akwai salaama mai yawa daga zuciya da ruhinta,wanda ya bayyana har saman
fuskarta.

Dukka gaba sukayi suna kwashe kayansu,ya tako a hankali gabanta ya miqa mata
hannunsa,ta sanya nata a ciki a hankali,saiya hade tafukan hannayensu waje
daya,yana sarqafe yatsunsu cikin na juna,ta zamo daga saman gadon a hankali ta
sauko,bai saketa ba yana cu gaba da riqon hannunta,suka fara takawa suna fita daga
dakin,tanason zame hannunta saboda idanun mutane amma ta kasa,abinda ta lura dashi
shine....shi sam bai damu ba,ita kadai tasan wannan connection din me yake haifar
mata ga gangar jiki da kuma zuciyarta,haka taci gaba da binsa sannu a hankali har
suka iso farfajiyar asibitin,sai a sannan ta lura motocine kusan guda huduna fake a
wajen,bisa dukkan alamu suna kan hanyar yi masa rakiya ne kenan zuwa gidansa,sai a
sannan ta tuna da samha,zuciyarta ta buga,ranta yana neman jagulewa,amma data
ambaci sunan Allah sai taji kamar cirar qaya abun cikin ranta.

Da kansa ya bude mata gaban motar ta shiga ya mayar ya rufe,ganin komai takek
kamar almara,kaffa kaffan da yake da ita wNi sabon al'amarine a wajenta da bata
saba gani ba,musamman idan ta aunashi da rayuwarta da bassam,kudi kawai sune a gaba
da komai a wajensu.

Qamshinsa ya sake cika motar sanda ya shigo ya maida murfin ya rufe ya gauraya
da ac ya bada wani yanayi na musamman da zai iya narka da dukka wanda zuciyarsa ke
cikin ganiyar soyayya,ya juya ya kalleta kadan ya janye idanunsa,su kadai ne a
cikin motar saboda akwai wadatar abun hawa,yana shirin tada motar fauzan ya qaraso

"Yaaa?"

"Ku jirani mu dawo saimu wuce"

"Muje tare din kawai,ya za'ayi sarki guda yabi kwalta shi kadai?" Ya fada yana
dariya da alama wani yaren ne nasu,murmushi kawai yayi,zai tada motar yaagana ta
qaraso itama

"Ameenu.....me xai hana kayi tafiyarka kawai ku wuce gida,mu idan yaso ma fita titi
mu samu abun hawa?" Zuciyar iman ta buga,kamar tayi magana amma ta hana kanta,Allah
ya sani sam bata shirya ba itakam,da wanne zataji?ba zatar sata kwantar da ita,ko
kuma tafiya gidan miji shima babu shiri?,abun ai sai yayi mata yawa wai shege da
hauka.
Duban iman din yayi na tsahon minti daya sannan ya maida kallonsa ga yaagana

"Babu matsala yaagana,ku shiga mota fauzan zamu kaiku gida,har yanzu da sauran
lokaci ai daren bai gama yi ba"

"To ai shikenan" ta fada tana qarawa gaba,dai dai nan iman ta saki ajiyar zuciya a
boye gana godewa Allah da bai aminta da shawararta ba,tana buqatar lokaci da kuma
nutsuwar da zata tattara dukkan wasu tunanuka da suka cika kwanyarta,ta zubda na
zubdawa ta dauki na dauka,idanun taci gaba da bari a lumshe,tana jin sanda motar ke
fita a asibitin har suka hau titi.

Shurune ya wanzu a motar,daga bisani ya maye gurbinsa da sautin karatun


qur'ani da muryar sheik shuraim da qaramin volume,abinda ya sake haifar mata da
tarin nutsuwa qwarai har suka shigo layinsu.

Tun daga nesa zaka fahinci akwai sauran jama'a baqi a gidan,a hankali yaci gaba
da jan motar har suka qaraso qofar gidan,ya kashe motar kawai ba tare daya fito
ba,tana kallon sh yaagana da aka sauke suna shigewa ciki abinsu,sai ya sauke glass
dinsa ya kira badi'a,ta qaraso cikin girmamawa,ya bata umari ta karbo key wajen
inna,sannan ta buda motar ya fita,ya zagaya inda take itama ya bude mata.

A gaba ya sanyata kamar wani bodyguard,suna shiga ciki jamaar dake wajen suna
mata sannu,batasan ya akayi ba sai taga ya saita mata hanya zuwa sashen da
dakunansu shida ya sadiqu suke a maimakon cikin gida,gab da zasu qarasa badi'a ta
qaraso miqa masa keys din ya karba ita kuma ta juya.

Daga bayanta ya taka a hankali ya tsaya,har tana jin hucin saukar


numfashinsa,inda zatayi wani kyakyawan motsin ba shakka zata tsinci kanta a jikinsa
ne,ta gefen qugunta ya miqa hannunsa ya zura key din ya bude qofar ya kuna turata.

Kyakkyawan parlor din nan nasu daya tsumu da qamshinsa ya bayyana,yana nan a
killace komai neat,kamar ba cikin gidan sashen yake ba,don ko alama bai nuna yasan
ana biki ba saboda yadda yake fes,ci gaba yayi da directing nata har zuwa bedroom
dinsa,komai na ciki yana nan,babbar katifarsa da tasha zanin gado fes kamar wani
zai kwana a ciki,harda ragowar kayan amfaninsa wasu duka bai kwashe ba,zuba
hannayensa yayi a aljihunsa yana tsareta da ido,kallon qurillar da yau ya
koyoshi,ita kuma yayi mata zafi da nauyi da yawa,tanajin kamar ba zata iya jurar ci
gaba da daukarsa ba

"Akwai abinda kike buqata kuma?" Ya tambayeta da lallausar muryarsa,saita zame ta


zauna gefan katifar kanta a qasa tana girgiza masa kai alamun

"A'ah" hannunsa ya fiddo daga aljihun nasa tare sa wayarsa dake ringing yana
murmushi

"Meye ne ya kashe bakin iman yau din?" Ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya furta
mata ba,ya daga wayar ya kara a kunnensa

"Suna iya tafiya ai,basai sun jiramu munzo ba.....ai yafi dai,gani nan" iya abinda
ya fada kenan,ya fara takawa zuwa qofa

"Bacci yana da kyau a lafiya da qwaqwalwa,akan dauki jibgin kayan tunani a ajesu
gefe duk yayin da kazo kwanciya,saboda bawa qwaqwalwa da ruhi hutu,da kuma samun
lafiyayyen barci,ki kwanta kiyi barci sosai,asuba ta gari" kalamansa na qarshe
kenan sanda yake fita a bedroom din,tabi hanyar daya wuce da idanu kafin ta janye
idanun nata tana dawo dasu cikin dakin,qaqarfar ajiyar zuciya ta saki,wani abu
nason tsaya mata a wuya,wajen wata yanzun zai tafi ko?,shine tambayar data tsaya
mata,amma data zuqi numfashi da kyau....kwanyarta ta dawo mata da dimbin kulawar
data samu daga wajensa na taqaitattun awanni sai taji komai yana wankewa daga ranta
data kirayi sunan Allah,kafin ta bude idanun nata ma taji an turo qofar an
shigo,bushira ce,ta bita da kallo

"Ina zaman zamana ya tasoni,nida ya qyaleni,keda zakiyi kwanan dakin love" abun
bushira zuwa yanzu dariya yake bata,ita din qawace ta musamman kuma ta gari,wadda
samun irinta a wannan zamanin sai an tona,ta qaraso tsakiyar dakin tana dire
kayayyakin data riqo,duk abubuwan amfanine da zata iya buqata,harda kayan sawarta

"Gashinan inji inna,tace tana gaisheki" rau rau tayi da idanunta,tun a sannan kewar
inna da kuma qaunarta suka sake dirar mata,a yau da burin inna ya cika ko yaya
zuciyarta?,ko yaya matakin farincikin dake shimfide saman fuskarta?

"Ba zatazo ta dubani ba?"

"A'ah wallahi tace bada ita ba shiga dakin suruki,nima nan da kika ganni dakin nan
yafi qarfina,a parlor zan kwanta na rage zafi a waya nida sahibina,Allah muma ya
aurar damu ya bamu me tattalinmu irin haka" dariya bushira taso bawa iman,ba yadda
batayi da ita su kwana kan tafifar tare ba amma taqi,tace to ko qasan carpet dinne
ta kwanta nan ma taqi,ta dire mata komai ta juya zuwa parlor din tana cewa

"Nidai Allah barci xanyi,a gajiye nake tubus,Allah ya bamu alkhairi" bin bushira
tayi da kallo harta fice taja mota qofar sannan ta dawo da dubanta still dai cikin
dakin.
Komai nashi a killace a kuma tsare,hatta da saman madubinsa da bai kwashe kayan
shafawarsa ba sunanan a jere,ta dauke idanunta ta mayar kan katifar dake dame da
farin zanin gado gefe kuma ga lallauan bargonsa ruwan madara,sai tarin fulalluka
manya da qanana cikin wankakkun pillow cases,ko meye yakeyi da fulalluka haka da
yawa oho.

Ita kanta sai a yanzu takejin gajiya na sauko mata,amma ba zata iya kwanciya ba
sai ta watsa ruwa,ta miqe tana duba ledar,kayanta ne a ciki na sawa da undies,sai
su cake da qananun lemo da kuma qunshin kaza a ciki,wanda wannan ta tabbatar ya
lameen ne ya hadosu,saboda duka favourite dinta ne a ciki.

Saman madubi daga gefe ta hangi farin towel a ninke,ta fidda kayan jikinta ta
daura towel din daya saukar mata har cinyoyinta,ta lumshe ido tana shaqar iska
sosai,qamshin daya tsumu a jikin towel din na cika hancinta,qamshin turarukansa
daya hade da na sabulun wankansa,ta waiga kadan tana jin kamar yana labe a wani
wajen yana kallonta,baby kowa itama ta sani,kawai zuciyarta na raya mata ne,ta
qarasa gaban bandakin ta zura slipper dinsa,saiga qafarta ta tashi qarama a
cikinsu,sabida tazarar size na takalmi dake tsakaninsu,ta tura bandakin ta shiga.

Karamin bandaki ne,amma kuma komai nashi fes yake,sai ragowar dan damshi da
yake ciki,da alama ba'a jima can can da yin amfani dashi ba,komai nashi dashi tayi
amfani,sai gashi ta dosani kadan daga cikin qamshinsa,yasan sirrin turare da kuma
ya zabarsa,tayi wanka sosai da ruwa me dumi a qaramar heater dake bandakin,sannan
ta fito ta tsaya gaban mudubi.

Mayukansa ta tatsa ta shafa,nan qamshinsa ya sake qaruwa,saita dinga ji kamar


suna tare dashi,ta gama tsaf ta shirya cikin wata lallausar rigar barci pink mai
gajeran hannu,iya tsahon rigar cinya ne,wandon kuma iya saman idon sawunta ya
tsaya,ta gyara kanta ta matseshi waje daya,batayi amfani da sauran turarensa ba
saboda gudun wani abu,saita dauki nata ta fesa,zuwa sannan gajiya ta sauka a
gabbanta sosai,burinta kawai ta kwanta,ta isa karifar ta haye,ta ware duvet dinsa
ta lulluba tana sauke numfashi me qarfi,gaba daya qamshinsa ne tako ina,yama kashe
nata turaren,take taji yana haifar mata da wani yanayi cikin zuciyarta.

Idanunta ta rufe a hankali,fuskarsa ta ta daxun ta dawo mata tarwai,kyansa ya


fita ainun,yadda yake mata magana da dukka wani body contact da suka samu adan
qaramin lokacin,wani qaqqarfan so da batasan da zamansa a zuciyarta ba ya taso ya
mamayeta,take kewarsa ta saukar mata,wata irin soyayyarsa ta motsa mata,saita
qanqame daya daga cikin filallukan dake saman gadon cikin jikinta da kyau,take ta
fahimci amfanin tarin fulallukan dake kan katifar.

Sake jawo guda daya tayi ta kifa fuskarta a kansa,qamshinsa daya ratsa filon
yaci gaba da shiga hancinta,ya dinga haifar mata da wani yanayi,shauqi qauna da
bege zuwa ga masoyin da ya yiwa zuciya wawan kamu,sai take jin inama ace yana kusa
da ita?.
Kara ta fara ji qasa qasa kamar alarm tsakanin filallukan,ta miqa hannunta a
kasalance ta laluba sai ga qaramar waya,kira akeyi,kuma sunan LAMIN ne a rubuce
baro baro,mamaki ya cikata,daita daga wayar don jin waye.

Sassayar muryarsa dake dauke da wani abu me nauyi ce tayi mata sallama,muryar
data sauke wasu abubuwa masu nayi a zuciyarta,da qyar ta motsa labbanta ta furta
kalaman amsa sallama

"Kin kwanta ne?"

"Eh" ta amsa masa a taqaice,shuru ya ratsa na wasu sakanni,sannan ya sake cewa

"Good night, sleep tight,karki makara sallan asuba" lafuzzan suka fita a bakinsa
can qasa kamar bayason yin magana,abinda ya qaraaa saukar mata da gajiya kenan

"Okay"ta iya cewa,ta zame wayar daga kunnenta a hakali idanunta a lumshe ta maidata
inda ta dauko.

A haka tabar idanun nata suna ci gaba da hasko matashi,wasa wasa wani irin
bacci ya rarrafo ya lullubeta,dukka jikinta ya saki,wata nutsuwa ta fara zuwar
mata,ta lula duniyar bacci me dadi

_sai nace asuba ta gari amaryar muhammad al'ameen_

SAI KUMA MONDAY IDAN ALLAH YA KAIMU,BISSALAM.

End of book

Leave a comment

Post

Comments

nasrahsadiq
Masha Allah,naji Dadi sosai a wa'yannan shafukan ,Allah ya kara basira da
hazaka.Amin

13 hours ago

112201018644657456668
Da saura mudai dan Allah iman ta riqe ajinnan yadda ya kamata tunda ya riga yashigo
hannu

14 hours ago


rukeebuwangal
Monday yayi Nisa please sister love 😘💕
🥺💕

14 hours ago


jidderh4212
Nima dai har Monday Ina laifin gobe ki bamu Sai weekend aje hutun pls ataimaka
Monday. Yayi nisa😭😭😭😭😭

14 hours ago

Load More

Contact Us
Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742

Email: [email protected]

Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram


Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io

Shafi na sittin da biyar"


https://arewabooks.com/chapter?id=62d0173df9d9563d0156afa0#:~:text=Report-,KUFAN
%20WUTA,SAI%20KUMA%20MONDAY%20IDAN%20ALLAH%20YA%20KAIMU%2CBISSALAM.,-End%20of
%20book[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 66

Daga can nashi bangaren wayar shima ya sauke,ajiyar zuciya mai nauyi ta kufce
masa harda sheshsheqa,tamkar yaron da yasha kuka ya gaji,kowacce gaba ta jikinsa a
mace take,cikin ransa yake addu'a da fatan ubangiji ya jarabci iman koda da rabin
soyayyarta dake cike a qirjinsa,ya fara takawa a kasalance yana tunkarar ainihin
ginin gidan nasa hannunsa riqe da ledoji guda biyu.

"Alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimmus salihat" ya furta a bayyane


sanda ya shiga riski parlorn nashi,shuru yake kamar yadda gidan yake,saika zaci
babu kowa cikin gidan,ya juya a hankali da direction dinsa zuwa inda dakunan samhan
suke.
Da sallama a bakinsa ya tura qofar bedroom din ya shiga,bata amsa ba
kamar yadda bata motsa ba hakanan bata amsa ba,sai ya saki qofar ya tako zuwa cikin
dakin.

Saman bedside table ya ajiiye ledojin hannunsa yana sake maimaita


sallamarsa,still dai bata amsa ba,kanta na lullube da tsadajjen mayafi kalar lace
din jikinta.

Baya kadan yaja,yana zuba hannayensa cikin aljihu,ya kuma sake maimaita
sallamar,burinsa shine kawai ta amsa,saboda tarin lada alfanu da kuma albarka dake
cikin hakan,kodon kasancewar wannan rana da kuma lokaci na farko na tarayyarsu a
rayuwa

"Samha" ya kirayeta a tausashe,kamar jira dama takeyi ta yaye lullubin dake


kanta,ta dubeshi da idanunta da suka kumbura sukayi kuma jajur dasu

"Me kakeso kacemin ne ameen?,akwai abinda ya rage da baka fada ba"

"Ya salam" ya fada yana fidda hannayensa daga aljihun,sannan ya tako zuwa gabanta
ya sake tsaiwa

"Yanzu dukka bayanan da na miki da wanda akayi miki daga gida baki gamsu ba?"

"Wanne bayanai?,na yaudara da cin amana?", Maganar tata ta masa zafi,amma a yanzun
dole shine a qasa,kuma hankali da tunaninsu ba daya bane,sai ya sake matsawa
gabanta ya tsugunna,ya kama hannayenta ya riqe

"Samha,kada ki bari hankalinki ya gushe daga jikinki,ki tsaya ki nutsu ki fahinci


ki kuma kalli komai ta fuskar daya dace...." Zame hannuwan nata tayi ta kuma ja da
baya a razane

"Bazan fahimci komai ba,bazan kuma gane ba,abu daya na gane shine ka yaudareni ka
kuma ci amanata,a rasa yarinyar da za'a baka sai iman?,yarinyar da nakewa kallon
qanwa?,kuma ban san da hakan ba sai bayan an daura auren?,wannan wanne irin
munafurci ne?"

"Ya Allah" ya fadi saboda yadda yaji kalmar tayi nauyi da yawa

"Ka fita ka barmin dakina koni na fita" ta fada cikin daga murya hawaye na sauka
daga idanunta.

Cikin zuciyarsa yaji tana buqatar space,idan yaci gaba da pushing dinta
kan lallai su samu sulhu zata iya fadin maganganun da dukkaninsu ba zasuji da dadi
ba,don haka ya miqe tsam,ya cire leda daya daga cikin ledojin ya taka zai fice,yana
jinta tana cewa yazo ya dauke ledojinsa tana turosu cikin daga murya,saidai ko
juyowa baiyi ba bare ya kulata,ya fita yaja mata qofar ya haura sama zuwa dakinsa.

A nutse ya buda dakinsa zuciyarsa qunshe da tunani da kuma saqe saqe iri
iri,baisan wanne irin kishi haka samhan ke dashi ba,koma dai meye shi bazai dauki
irin wadan nan sabbin dabi'un da tun daren farko ta fara tsiro masa dasu ba,baiga
wani cin amana ko haramci da ya aikata ba,wala'alla tun asali don batasan wace iman
a wajensa bane,da batayi abinda tayi a yanzun ba,bayason kuma fayyace mata
komai,don ya tabbatar idan hakan ta faru sai taji ita din ba komai bace a wajensa.

Kayan jikinsa ya cire gaba daya,ya shiga toilet yayi wanka,yazo ya shirya
kansa cikin wasu pyjamas ruwan sararin samaniya,sunyi matuqar amsarsa,gargasar
qirjinsa gaba daya a waje take,ya sanya takalmin dake hade dasu ya dauki wayarsa ya
sake fitowa.
Yadda ya barta haka ya sameta,kai tsaye ya nufeta bakinsa dauke da
sallama,sai ta miqe tana kallonsa,yana isa gareta baiyi wata wata ba ya dagata cak
ya rabata da qasa,take ta fara wutsil wutsil gami da tattata dukka qarfinta tana
son qwacewa daga hannunsa,saidai ina,ya nuna mata banbamcin,bai tsaya ba ya jefata
saman gado,ya kuma matseta yadda ba zata iya tashi ba.

Kokarin qwace hannayenta daya riqe gam takeyi tana fadi cikin kuka

"Ka sakarmin hannuna,ni ka qyaleni"

"To dama waye yace miki wani abu zanyi miki?" Ya fada a nutse tsaf,idanunsa cikin
nata,kunya ta kamata saita ci gaba da borin kunyarta

"Indai kinason na fitar miki a daki to saikin tsaya kin saurareni" ta tabbatar idan
bata tsaya din ba qaramin aikine wajen ameen din suyita zama a haka,dole ta rage
turje turjenta,ya fara mata magana a nutse

"Zan gaya miki gaskiya ne samha,ni mutum ne da tun asali bame boyon gaskiya
ba,komai dacinta ina fadinta,zata yiwa mutum dadi ko bazatayi masa ba.......ima
itace mace ta farko dana fara so a rayuwata,kuma wasu dalilai a baya da kuma
qaddara Allah ya nufi ba zamuyi aure ba,saidai dai dai da rana daya ban taba cire
sonta daga zuciyata ba......a yanzu qaddarar aurenmu ta tabbata,wanda bazan iya
wofantar da hakan ba,uwa uba inna da malam....mutane ne masu kima da daraja a
idanuna,baya ga iyaye na sune mutane nafarko masu daraja ta farko a rayuwata da
zuciyata,sunmin komai,sune suka maidani wannan lameen din da kike kalla a
yanzu,jininsu yafi warfin wulaqanci,dake da iman duka matana ne,kuma na aureku
saboda kowacce akwai soyayyar da nake mata,kada ki tashi hankalinki akan lamarin
iman,kema matata ce kuma abar sona kamar ita...." Kalamai masu dadi gami da kwantar
da hankali yayi mata,irin kalaman da suka sauke zuciyarta sosai,saidai kuma tana
buqatar tayi shawara kan yadda zata bullowa abun,akwai babbar matsala ace ya auri
wadda ya fara so suka rayu gida daya ya hadata da ita,soyayyar farko ba wasa
bace,da yawa yawan mutane basa iya daina son wanda suka fara so a rayuwarsu,saidai
wani dalili ya dusasheta

"Naji,ka tafi zan kwanta"


"Naji nima zan tafi,amma tashi kije ki wanka ki cire wadan nan kayan na jikinki ki
sauya wasu" ya fada yana tsareta da idanunsa dake mata kwarjini da yawa,abu na
farko da ya fara jan hankalinta kenan tun farkon haduwarsu.

Ganun da gaske yake bazai tashin ba yasa ta shiga bandaki tayi yadda yace
din,ta fito a shirye cikin kayan bacci masu kauri tana dubansa,sai a sannan ya
sauko daga saman gadon cikin kasala da mutuwar jiki,ya Sanya slipper dinsa,har yayi
taku biyu ya tsaya ya waiwayo

"Da gaske na tafin?" Ya furta yana dubanta,hade rai tayi

"Eh mana" don har cikin zuciyarta bataji ta huce ba,batajin zata iya bashi komai a
yanzu,sai abinda ta tattara ta kuma yanke shawara a kai,bata hangi kawo iman yanzu
ba,saboda ance mata bata da lafiya,sannan auren ba zata ne,so saboda haka saita jaa
zarenta da kyau ta kuma wajigashi sannan,ta yarda da maganganun nan na wasu mata
dake alfahari da mutuntakarsu wajen jan ran miji,bata yarda ta sakar masa jikinta
ba bare ya moreta da yawa har raini ya shigo tsakani.

Murmushi ya saki yana ci gaba da takawa tare da fadin


"Allah ya bamu alkhairi" abinda take qiyastawa sam shi ba shine a ransa ba,bashi da
wani shauqi kwata kwata a yanxun haka,gaba daya ruhi da gangar jikinsa nat wani
gun,ya tabbatar da a bigire ko muhallin da zuciyarsa tafi karkata ne,zaiyi wuya ya
iya sanya qafarsa ya fita,ya sake tambayarta ne wai koda tana da tsoron kwana a
sabon waje.

*****WASHEGARI da cikakkiyar nutsuwa ta farka tayi sallar asuba,wani irin kwanciyar


hankali da nutsuwa data jima bataji kamarta ba yana saukar mata,har yanxu dakin dai
qamshinsa yake,wanda shi ya tayata kwana yake kuma debe mata kewa.

Ko addu'o'inta bata gama ba ta leqa bushira a falo,sai ta sameta ta gama


tata sallar tana a tsaye,ta qarasa suka gaisa bushiran nadan tsokanarta

"Ya kwanan dakin soyayya?" Harararta tayi

"Ke kika sanshi,don Allah muje ki rakani naga innata"

"Daga nan nima gida zan wuce naga tawa innar ba" fuska iman tadan bata

"Haba bushira,ya zaki tafi ki barni don Allah a wannan situation din?" Idanu ta
fiddo tana dariya

"Kijimin mata,ki kama mijinki a hannu abun sonki,ga innarki ga malam dinki,ga ya
sadiqu amma kicemin haka?,ciwo dai kin warke wallahi me kuma yayi saura?,duk sanda
aka tashi kaiki zan dawo qafarki qafata" shuru tayi,ita kanta tasan bushiran tayi
namijin qoqari,don a yanzu ta zarta qawa ko aminiya,saidai a bata matsayin 'yar
uwa,sannan tabbas ya kamata taje ta huta.

Tare suka jero zuwa cikin gidan,sun tadda baqi sun buga sammako sun
kammala shirin tafiya,cikin mutunta juna suka dinga gaisawa,ragowar dangin lamin da
suka rage sunata yi mata fatan alkhairi,sai da suka kebe da yaa baraka sukayi
magana ita da ita

"Don Allah hajar ki kula da lameen,bashi da kamarki,kuma duk duniya babu matar da
zai aura sama dake,mun godewa Allah da wannan damar bata kubce masa ba damu gaba
daya,ba ruwanki da lamarin kishiyarki mijinki shine a gabanki,in sha Allah zan dawo
nan kusa na hadaku keda lamin din muyi magana sosai,kiyi haquri da kutsen da mukayi
miki aka kasa dr naki.....ni dama nasan bazaikai labari ba tunda yace zai kara da
dan qanina....ba yabon kai ba" ta qarashe tana dariya,maganar data sanya iman
murmusawa,ta sadda kanta qasa tana jin kunyar yaa baraka.

Sai da suka fice duka su da 'yan maiduguri,yaa gana ce kawai ta rage,sai


dangin inna daga nijer su biyar,suma sun gama shirinsu,driver dinsu suke jira ya
iso.

Cikin bedroom ta cimma inna tana kintsashi mufida na tayata,waiwayowa tayi


tana amsa sallamarta,duba daya zaka yiwa fuskar inna kasan cikin farinciki
take,wata kyakkyawar fara'a ta sakarwa iman din,hakan yahaifar da farinciki a
zuciyarta mai yawa,ta tako cikin dakin tana duban mahaifiyartata,me yafi bin xabin
iyaye dadi matuqar babu son rai ko kaucewa addini a ciki?,ina zata kwatanta kallon
da take mata a yanzu da kallon data samu sanda ta zabi bin son ranta.

Gaida innar tayi,ta amsa mata cike da kulawa tana tambayarta jikinta

"Da sauqi sosai inna" mufida ta matso tana gaidata,saita saki murmushi

"Yammatan inna kinyi wuyar gani,ni ban ganki ba sam tunda aka fara hidindimun nan"

"Ina zaki ganta tana maqale dani,mutan nijer dai sunce lallai kam mufida ta zama
tawa,wai ta juye yanayinmu yanzu" murmushi Iman tayi
"Gaskiya ne mana inna" tana duban mufidan,tanajin dadin xaman yarinyar wajensu,ko
babu komai inna tana dame debe mata kewa,hira suka dan taba da inna,ta tambayi
malam tace tunda yayi sallah ya fita,maybe shima yana sallamar baqinsa ne,sai iman
din ta shiga ciki neman yaagana don su gaisa,saboda bata ganta ba.

A dakin da aka saukesu ta sameta,ita da bushira data gama shirinta tsaf,ta


zauna daga gefanta tana gaidata,ta amsa mata cikin kulawa tare da tambayarta
jikinta,ta amsa mata da sauqi,itama dai hirar suka dan taba,sakayau take jinta a
yau din,bushira ta yowa inna sallama,innar ta cikata da abubuwan alkhairi masu
yawa,tayi kamar ba zata karba ba amma inna ta dage saita amsa

"Bari na dauko wayata na rakaki" iman ta fadi tana miqewa,dakinta dake rufe ta buda
tashiga,ta laluba wayartata inda ta ajjiyeta sannan ta fito

"Idan kin rakata ki koma can sashen kiyi wanka ki kimtsa tukunna,amarya kike,bai
kamaci ki dinga yawo a haka ba" yaagana ta fada tana duban iman din,dole ta amsa da
to,amma bataga aibun nan din ba da baza'a barta tayi wankanta a nan ba.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 67

Duk da cewa ba datti dakin yayi ba,amma saita samu kanta da tsaiwa ta sake
kintsa dakin da kyau,ta kunna wayarta saidai ta nuna low battery,ta duba inda taga
charger a dakin ta jona ta sannan ta miqe tana duba agogo,har tara saura tayi,sai
ta fidda kayan jikinta ta daura towel din jiya a jikinta ta shige bandakin.

Ruwa zafi me yawa ta tara,ta jima cikin bandakin tana wanke jikinta,ita
da kanta ma take mamakin dadewar data yin,daga qarshe ta daura towel din ta soma
nemam brush dinta,babu cikin kayan,dole wanda ta gani a toilet din ta dauka tayi
amfani dashi,ta hada da alwala sanna ta maida komai a muhallinsa ta nufi qofa.

Wani yanayi me dadi ne yake sake ratsata,iskar dake kadawa cikin dakin
tana fifita jikinta dake dauke da damshin ruwa,ba shakka babu abunda yafi nutsuwar
ruhi dadi,haqiqa babu Abinda yafi kwanciyar hankali dadi,ta taka a hankali xuwa
gaban madubin,tana sake qarewa mayuka da turarukan dake saman madubin kallo wanda a
daren jiya bata yi ba,da daya da daya take dauka tana dubasu,dukkansu designers ne
masu matuqar tsada,ta ajjiye tana sakin murmushi sannan ta zabi mai daya da niyyar
shafawa,saidai turo qofar da akayi ya dakatar da ita.

Ta cikin madubi ta hangeshi,yayi tsaye daga bakin qofar,idanunsa suka sauka


saman farar fatar bayanta wadda keta qyalli,ta kuma bayyanar da kyawun surar
mamallakin jikin.

Tsorota tayi,sosai zuciyarta ta buga,saidai kafin tayi kowanne motsi yaja


qofar ya rufe mata,hakan ya sanya ta fasa shafa man,ta isa inda ta ajjiye kayanta
ta dauka ta fara zurawa,lallausar atamfar england light green mai adon dark green
da fari,dinkin half bubu da yayi matuqar yi mata kyau da fidda shape dinta,sai data
gama saka kayan sannan ta koma fa shafa manta,tabi jikinta da turare,tana tsaka da
fesawar aka sake turo qofar,shi dinne dai,sanye da wata danyar shadda dark ash da
aka yiwa aiki da baqin zare,rigar iyakarta gwiwarsa,sai gajeran hannu daya fidda
farin yalwataccen hannunsa dake da albarka gargasa,takalminsa half cover ne baqi
mai asalin tsada,sai sheqi yakeyi kamar ba'a taka qasa dashi,hannunsa dauke da wani
madaukin kayan abinci dake dauke da tambarin wani mai tsada kuma shahararren gidan
abinci,qamshinsa ya fara gauraye dakin,wani irin qamshi data saba ji daga gareshi
kadai.

Da tattausar muryarsa da ta sake zama so cool yayi sallama,fitar sautin


furucinsa ya shiga har cikin qashi da bargonta,uwa uba adonsa daya tafi da dukka
hankali da tunaninta.

A nutse ya tako,ya jawo wani table ya dora abincin a kai,daidai lokacin data
furta
"Sannu da zuwa....."
"Yauwa sannu" ya amsa mata yana sanya hannunsa tsakanin madubinsa,ya fiddo wata
lallausar darduma mai kyau ya shimfida,zare takalman qafarsa yayi ya hau kai ya
zauna

"Qaraso da kayan abincin can" ya fadi yana duban fuskarta da tayi wani
fayau,dankwalin atamfar data masa Vshape ta yafashi saman kanta yanaga
zamewa,lallausan gashinta daya fara daga gaban goshinta yanata fitowa tana sake
gyara dankwalin.

A nutse ta fidda komai ta budeshi

"Ina kwana"ta gaidashi tana niyyar miqewa,fuskarta na kallon wani waje daban

"Zauna kici abinci" ya bata umarni kai tsaye,sai ta koma ta zauna din sosai kamar
yadda ya buqata.

Plate daya ya zara ya zuba abincin,sai ya qara cokali daya,ya kuma sakashi a
tsakiyarsu

"Bismillah" ya fada yana fara cin abincin a nutse abinsa,sai ta basar dashi kamar
ba da ita yake ba,,bata ko motsa ba,illa wasa da take da yatsun hannunta,tabtasa
sukuni da sakewa gaba daya,yadda yake jefa mata kallonsa da yanayin kusancin zaman
nasu gaba daya ya takurata yanayinta,mamakin abinda ya fiddoshi daga gidansa da
wurwuri haka takeyi,a matsayinsa na sabon angon da jiya jiya ya shiga dakinsa,uwa
uba kuma yazo ya buge da cin abincin safe a waje,yaa sadiq kam ko motsinsa babu,don
ko dazun data shiga cikin gida tanajin ana kiran wayarsa ya fadi inda ya aje key
din setting room din malam amma wayar tasa a kashe.

Sai da yayi loma kusan biyar sannan ya sake motsa bakinsa a nutse

"Bismillah,me mike jira?" Ya fadi yana kafeta da idanunsa dake dauke da wani magnet
mai matuqar qarfi da kuma tasiri,saita motsa a hankali ta dauki spoon din ta fafa
juya abincin.

Duk bayan wasu sakanni sai ya jefa idanunsa a kanta,wani abu na motsa
zuciyarsa yana kuma tabata ta kowanne sashe,ita ta fara janyewa,ya bita da kallo
sannan ya tsiyaya mata tea mai zafi ya miqa gabanta,ya dauki cokalinsa yana ci gaba
da cin abincin.

Bai wani jima ba shima ya kammala,ya miqe ya dauki tissue yana goge gefe
da gefan bakinta,takawa yayi a hankali zuwa inda ta ajjiye magungunanta,hannayensa
ya zuba cikin aljihunsa yana qare musu kallo,ta motsa kadan itama tana kai kallonta
ga inda yake,nauyi da kunya suka kamata,tayi ajiyar pants nata a wajen wanda ta
cire,ya riga yaga koma meye bata da abinyi illa qas da kanta da tayi

"Idan kin tashi ki daukeshi ki wanke" taji ya fada sanda yasa hannunsa yana matsar
dashi gefe a nutse,kamar qasa zafa tsage ta shige haka taji,duka yaagana ce ta jawo
mata wannan aika aikar.

Takowa ya sakeyi zuwa inda take bayan ya balli dukka magungunan,yadda yayi
mata jiya a asibiti yanzunma hakan yayi mata,ya shinfide mata tafin hannunsa,ta
dinga daukan magungunan da daya da daya tana sha,har zuwa sanda ta dauki na
qarshe,dai dai lokacin da akayi knocking.

Kamar dazu yanzun ma baiyi magana ba,ya bude qofar ya karba abinda zai
karba,maida qofar yayi a hankali ya rufeta,wannan karon harda murza key,abinda yaja
hankalin iman kenan,ta daga idanunta tana duban qofar,sannan ta sake maida duban
nata ga lamin din sanda yake dawowa ciki.

Da mamaki tabi hannunsa dake dauke da wuqa da kallo,table din daya dora
abinci a dazu ya janyo zuwa gabanta,ya dora wuqar daketa qyalli akai,yayi taku biyu
zuwa baya,yasa hannayensa ya fara balle maballan rigarsa,sannan ya zareta ya
jefar,farar singlet dinsa ta bayyana,a hankali itama ya zareta ya jefar da ita daya
bangaren,take faffadan qirjinsa mayalwaci mai cike da albarkar gargasa ya
bayyana,gami da damtsensa dake nuni da alamun qarfi da yadda motsa jiki ya zaunar
masa.

Tsoro fargaba da kuma daurewar kai suka kama iman din sanda yake takowa
gabanta,idanun nan nasa akanta,wani abu mai nauyi da qarfi yana gilmawa ta cikinsu
Gwiwoyinsa ya sanya a qasa kamar wanda zaiyi kneel down,ya dauki wuqar ya buda
tafin hannunta dake cikin hannunsa ya sanyata still idanunsa nakan iman wadda
tsoronta da fargabarta suka ninka na baya,saita kalli wuqar kana ta kalleshi

"A wancan karon,kin furta cewa zaki kasheni muddin aka aura miki ni,sai
gashi a wannan karon ma bata sauya zani ba.....irin wancan auren akayi
miki....bansan wanne alwashi ne a ranki ba wannan karon,idan irin na baya ne,gani
nazo da kaina ki cika burinki!,saboda na sani qiyayya bata gushewa daga zuciyar
wanda ya furta qiyayya haka ta sauri.....,ki aikata abunda yake ranki iman!!!" Ya
fada da wata kakkausar murya mai madaukakin sauti,idanunsa na sauya kala,da alamu
tun daga zuciyarsa abun yake motsa masa.

Sosai ta rude ta kuma diririce, take idanunta suka hada qwalla wadda bata
iya tsaiwa ga iya ramin idanunta ba sai da suka gangaro saman fuskarta,wacce magana
ce haka me muni lamin din yakeyi?,shi baisani ba?,baisan shine farincikinta
ba?,baisan shine burinta dama mafarkinta gaba daya ba?,baisan shine duk wani motsi
tashinta da kwanciyarta ba?,waye xai tayata tayi masa wannan bayanin?,waye zai
tayata fahimtar dashi?,baya ganin komai rubuce saman fuskarta ne?.

"Na baki dama ki aiwatar da nufinki!!,ki cika burinki!!" Ya fada a tsawace yana
matsa hannayenta,furucin daya ida rudata,ta fusge hannunta da sari takuma yi
wurginda wuqar,
"Bazan iya ba" Ta fadi itama da madaukakin sauti gami da runtse idanunta gaba daya
kamar wadda taga wani abun tsoro,kuka mai matuqar qarfi yana qwace mata

"Saidai idan har ni din na maka kutse cikin rayuwarka.....na datse maka dukkan wani
tanadi da kuka yiwa kanku samakon tallata da aka yi maka aka maqala maka ni,kana
kallona kuma a matsayin matsala.....a yau na baka dama ka kawar dani
nima....hannuwana ba zasu taba iya dauke numfashin wani dan adam ba,dan adam dinma
dake da girma da kima da kuma soyayya daga zuciyata" ta fada da qarfi tana sauke
kanta qasa,sabbin qwalla masu zafi suna keta idanunta suka fara gudu suna sauka
saman cinyarta,ba shakka furuci masifa ne,shine abu guda dayan da yake da qarfin
gina ko ruguza komai.....komai girmansa,idan ya fita ya riga daya fita,ta tabbatar
kalmace mafi ciwo data furtawa lamin,kalmar da da alama ta tsaye masa a rai
matuqa,kuma kalma mafi girma da zaka nunawa maqiyinka girman qiyayyar da kake
masa,kalmar kisa.....idan ta tuna tana jin kanta kamar ba ita bace a wancan
lokacin.

Kamar me sauraren bugun zuciyarsa haka ya runtse idanunda yayi


shuru....kalmominta na qarshe sun dagargaza gami da narkar da wani abu daya tsaye
masa a wuya tsahon shekaru,yana jin yadda abun ke narkewa yana wucewa,yana da
yaqini yana kuma da kokwanto dukka akan iman din,saidai a yanzu ya samu zallar
yaqinin da babu shakka,soyayya yake buqata daga gareta,kalaman da zasu sake
tabbatar da kuma jaddada matsayinsa kai tsaye....bawai nuni ko ishara ba.

A tausashe taji an kama dukka kafadunta guda biyun an miqar da ita tsaye,sai
a sannan ta bude idanunta da suka jiqe da hawaye suka rage kaifi da tsahon zara
zaran eye lashes dinta,haduwar idanuwansu waje guda ya haifarwa da kowannensu wani
babban al'amari cikin zuciyarsa,saqon da kowanne ya sakarwa dan uwansa ba tare daya
sani ba ta hanyar idanunsa ya isa ga qirji yakuma zarce cikin zuciyoyinsu kai
tsaye,tsaiwarsu a hakan ya mata wani irin kwarjini mai yawan gaske,ya lameen tsaye
a gabanta,dukka surarsa a bude,abinda bata taba gani ba kenan daga gareshi tunda ta
mallaki hankalin kanta

"Ita zumar asali har abada tana nan a matsayin zumarta,har kullum binta ake a
nemota....bata buqatar a tallatata,ba maɗi bace da sai yasha talla kafin ya samu
masu so da kuma masu buqatan saye,abace mai darajar da har kwanan gobe saidai abita
anemota,koka tashi neman nata....wuyar samu take,duk duniya nafi kowa sanin
darajarki hajar....cikakken namijin da ya amsa sunansa,yana amfani da qwanjinsa da
kuma fikirarsa wajen samawa kansa abindan yakeso,abinda kuma ya dace da muradinsa
da mafarkinsa,baya jira azo ace masa gashi,koda yaushe farauta yake yaga ya
samu,muddin wannan abun nada kima da daraja a wajensa" wasu irin kalamai masu cike
da tarin hikima,gefe daya kuma suna fidda zallar kima da darajar da take dashi a
zuciyarsa,ta wani fannin kuma yanason bayyana mata shine ya nema aurenta kenan da
kanshi?.

Bata gama wannan tunanin ba taji ya sauko da hannuwansa daga kafadarta


zuwa nata hannayen,ya kamasu ya riqesu a tausashe cikin nasa hannun yana murxawa a
hankali,idanunsa cikin nata yana saukar mata da wasu abubuwa masu nauyi da
girma,wanda take taji qafafunta sun soma laushi,kamar ya fahimci hakan,sai ya hade
gap din dake tsakaninsu,ya jawota zuwa cikin jikinsa,yayi mata kyakkyawan masauki a
qarjinsa,kana ya sanya hannayensa yayi mata qawanta,al'amarin da yaso wucewa da
numfashinta,dumin jikinsa ya fara ratsa fatar fuskarta tare da wani qamshi na
musamman da bata ta jinsa daga jikinsa ba,da alama gashin dake qirjinsa turare na
daban yake masa amfani dashi ba wanda yake sanyawa a jikinsa gaba daya bane, tsigar
jikinta ta zuba,ta lumshe idanunta,tanajin wata nutsuwa da rahama daga
zuciyarta,yayin da a nashi bangaren tudun jikinta ya sanyashi dauke wuta na wasu
sakanni,saidai dole su qarasa maganar da suka dauko,saitin kunnenta ya fara magana
qasa qasa

"Da qyar na rayu iman....da qyar na kawo yau,saboda maganganunki sun zubamin dafin
da ya dinga cin jiki da zuciyata kullum,nabar qasar nan amma na tafi da tafkeken
tabo da kuma memory na dukka abinda ya faru,naci wuya a makaranta.....na gaza
fahimtar karatun da najeyi,har sai dana fara fuskantar barazanar na rasa damata
sannan na farga,ko sau daya ban taba warkewa daga ciwon da yake zuciyata ba,ban
warke ba iman sai ayau din nan,duk da haka na tabbatar an barmin tabon da bazan
manta dashi ba,nayita tuhumar kaina.....me yasa bazan cireki daga raina ba bayan a
yanzu kedain matar wani ce?,na gaza gano amsa,darare da yawa sunxo sun wuce ta
gaban idanuna sanda nake zaune ina tuna tashinmu zuwa rabuwarmu dake,barci ya
qauracewa idanuna,nayi kuka nayi kuka har bansan adadi ba,na zana na binciki kaina
laifina da kika gaza karbata amma na rasa,sai wasu uzururruka da zuciyata keta
baki,ta kasa gano laifinki ko daya,ina can labarin mutuwar aurenki ya ruskeni,nayi
matuqar baqinciki bazan boye miki ba....saboda inda ace nike da ikon rubuta
qaddararki.....zaki tsallake kalmar zama bazawara har qarshen rayuwarki,bai kyautu
nayi murna ba,saboda mutuwar aure ba wasa bane,sannan uwa uba a sannan gaba daya
duk wani burina dake kanki ya mutu murus,zuciyata taci gaba da kallonki a matsayin
qanwata,kamar dai matsayinki na daa can can,wani sashe na zuciyata na qaryatani,ni
kuma ina sake gasgatawa kaina hakan,komawarki makaranta ni na tsaya akai,na tursasa
sadiq wanda ke fadin shi har yanzu bai sauko ba,ko.meye ya faru dake ke kika jawa
kanki,nayi masa gori sosai na kuma fada masa ganganu,har yaso yaji haushina,daga
qarshe dole yatsaya akai kamar yadda na buqata.

Sanda na dawo na tadda komai na tafiya yadda ya kamata naji dadi sosai,na
karanci kunya da nauyin haduwa kikeji dani,abinda yasa a wancan lokacin nakiraki
nayi magana dake kenan,nayita karantarki a fakaice ba tare da kin sani ba,zuciyata
na gaya min akwai soyayyata a zuciyarki,Allah ya sani naso na fara jin daga gareki
koa jirwaye ne kiyimin amman banga wannan ba,katsam kuma saina fahimci akwai dr
ahmad cikin rayuwarki,kina kima bashi girma da kima qwarai da gaske,na shiga damuwa
da dimuwa sosai amma nayi qoqarin cinye abata,saboda wani sashen na zuciyata ya
sake shiga shakkun har yanzu da gasken baki sona,wannan yasa nayi shawarar jayewa
na sake baki damarki.

Ban qara shiga rudani ba sai randa malam ya taramu,a ranar nazo da qwarin
gwiwata na gabatar masa dake saboda sauyin yanayi dana fuskanta daga saman
fuskarki,ga mamakina sanda tambayar tazo kanki sai kika gabatar da dr ahmad a
matsayin zabinki,wannan ya qarasa kashe dukka wani buri nawa da fatana....ko ranar
da muke magana da yaa baraka a bayan gida naga tahowarki,daga ke har ita ba wanda
yasan na ganki,amsar dana bata sanda take nunamin asararki da zanyi.....ina sane na
bada ita,na zaci daga bisani zan sake ji daga gareki,ga mamakina sai naga kin sake
janyemin gaba daya......iman" ya kirata qasan maqoshinsa,yatsunsa na tsakiyar nata
yatsun,muryarta na rawa ta amsa masa

"Ba girman kai ko wani abu yasa nayita baki wannan damar ba,dalilina.....na yiwa
kaina alqawarin bazan taba tilasta wata mace ko a tilasta mata zama dani ba,saboda
zaman aure anyishi ne saboda farinciki da jin dadi mai dorewa,dakuma samar da
tsaftatacciyar zuri'a....nayi qoqarin mantawa dake amma yaa barakata fitittike,tayi
tattaki har maiduguri takai qarata wajen yaagana,yaagana ta nemoni,takuma ce zata
yi magana da malam,koda iman bata sona a wannan karon bata isa tsallakewa aurena
ba.......ban yarda na zauna anema min soyayya ba iman....idan nayi haka na zama
lusari,ban kuma yarda da kaina ba,don haka na nemi su barmin komai na daidaita
al'amuran bisa tsari,kaina tsaye na nema dr ahamd,yaso ya qi,amma daga bisani daya
fahimci lallai zai auri gangar jikinki ne kawai.....zarrarata tafi tashi,....kuma
ninafi cancanta dole ya sallamamin.

Ko yaushe rana da zata fito ya fadi dani kike musayar text da sabuwar
number da a wajenki dr ahmad ne" a sannan daga kanta tayi tana dubansa,kamar dama
ya shiryawa hakan,idanunsa na cikin nata ya dage girarsa

"Yes,na samu nutsuwa sosai,saboda na samu kalaman masu tsada daga gareki,duk da ke
a wajenki ahmad ne" kunya ta kamata,ta maida kanta tana son tunano dame dame ta
taba rubuta masa?,tabbas a lokacin ta shiga mamaki matuqa na yadda ta dinga ji da
ganin sauyin kalamai daga wajensa,wasu irin kalamai dake nuna zallar qauna zuwa ga
abokin soyayyarka,kalamai masu tsada da bata taba jinsu a wani waje ba,ashe yaa
lamin ne?,amma fa tafka abun kunya

"Karki damu,a yanzu ina da buqatar ninki wadan nan,abinda yasa nace aboye komai a
je a zuwan ahmad ne,saboda zuciyata na ganin kamar zan sake rasaki,a wannan karon
kuma inajin idan na sake rasakin bazan iya daukar hakan ba,me yiwuwa duka
makusantana nima su rasani" dagata yayi daga jikinsa,ya soma durqusawa a
gabanta,saita kasa ci gaba da tsaiwa itama ta sulale ta bishi,fuskarta ya kama ya
sanya a tsakiyar tafukan hannayensa

"Koda baki sona iman.....nayi alqawarin dasa miki soyayyarki a zuciyata,soyayyar da


zata hanaki sukuni...."
"......barema ina maka son da ban taba jin koda labarin irinsa ba" bai shirya ba
yaji saukar kalaman,idanunsa ya lumshe yaja numfashi kamar zai shide,kunyar barin
zancen da tayi yasa ta kama tafin hannunsa ta boye fuskarta a cikin murmushi yana
qwace mata,a hankali ya cusa daya hannun nasa saman sassalkan gashinta da yake
tsone masa idanu shekara da shekaru ya fara motsashi,yanajin laushin daya jima yana
hasashen yana dashi a idanunsa yau a hannunsa.......
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: "




Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ's
Privacy Policy
Terms of service
Logout

KUFAN WUTA
Chapter: Shafi na sittin da takwas

Share:





Report

KUFAN WUTA
View: 466

Words: 2.2K


Shafi na sittin da takwas

Chapter 69
Shafi na sittin da takwas

68

Har cikin qashi da bargonta takejin yawon da hannun nasa yakeyi saman
kanta,abunda ya sake iza wutar dake zuciyar kowannensu

"Kin shirya tafiya gidana,gidanki gidanmu?,na gayawa yaagana?" Qanqameshi tayi tana
girgiza kanta alamun a'ah

"Pleaseeeeeee" yaja kalmar data sauka kai tsaye a qwalqwalwarta ta baza wani yanayi
a sassan jikinta daya sanya ta sake qanqameshi,so yake ya rikita mata lissafinta
gaba daya da alama,zatafi kowa son hakan a yanzu,amma dole ta kame kanta,uwa uba
koda taje gidansa a yanzu sai tayi jira kwanakin samha sun qare sannan ya iso
gareta

"Ina buqatar tozali dake kowacce rana cikin qarqashin inuwar gidana..... please
queen,ki gaya musu kin warke" yayi maganar yana matseta sosai a jikinsa,bawai
sha'awa kawai ba.....wata qaqqarfar qaunarta daya dade da sakayata a wani lungu me
zurfi na zuciyarsa saboda tunanin zamantowarsa looser akan soyayyar iman din a
yanzun take fidda kanta
"Bazan iya gaya musu ba"

"Ni kin bani dama na gaya musu?" Murmushi ta sake,gani take kamar bazai iya ba,don
haka kanta tsaye tace masa eh,sai ya zame jikinsa a hankali daga gareta,ya fara
takawa zuwa qofa.

Idanu ta zaro sosai ganin fita zaiyi da gaske,uwa uba kuma babu riga a jikinsa
ya zubdasu a wajen

"Yaa lameen" waiwayowa yayi yana dubanta da idanunsa da suka sauka kala

"Riga fa" duban jikinsa yayi,har ga Allah ya manta ba riga a jikinsa,dumin jikinta
ya ratsashi sosai har bayajin sanyin iskar dake kadawa,iska mai zafi ya furzar kana
ya saki murmushi,da hannu yayi mata nuni kan ta kawo masa,saita maida masa martanin
murmushin ta juya zuwa inda ya yasar da rigar,yabi qugunta da kallo yadda suke
juyawa kamar tana yine da gangan,yafi kowa sanin bada gangan bane,haka halittarta
take,ta qaraso inda yake ta miqa masa,sai ya hada da hannyenta ya riqe,ya sanya
daya hannun a hankali ya kama qugun nata ya riqe yana dubanta

"Ranar dana fara ido hudu da wannan abun ban iya barci ba,nayi mafarki har babu
adadi,inda na godewa Allah ranar sadiq ya tafi borno,ni kadai na karbi punishment
dina,da lallai an tafka abun kunya,tun daga ranar na canza miki yanayin dinkinki
zuwa dogayen riguna,amma duk da haka ban tsira ba,saida wani ya qyallomin ke,bazan
taba yafe masa ba".

K'as tayi da kanta,karon farko tausayinsa ya kamata,ko meye ita ta jawo


masa,saidai ta godewa Allah daya tsare mata abunda yafi komai tsada a rayuwar
kowacce diya mace,ya barshi ga lamin din

"Kayi haquri ya lameen,ka yafemin don girman Allah"

"Shshshsh.....qaddararmu kenan,ba wanda kuma ya isa ya tsallakewa qaddararsa.....ya


wuce,ni dae mu manta gaba daya kin taba kasancewa halalin wani,tunda dai na samu
gundarin hajar dita shikenan.....Taimakamin na saka rigar please,kin tafi da duk
wani kuzarina.....zan iya ci gaba da fita aiki kuwa nan gaba?" Ya fada yana langabe
mata,qaramin kurmushi ta saki,ta qara matsowa dab dashi,sai ya riqeta sosai ya
shimfida mata qafafunsanya jata ta takasu,abinda yadan qara mata tsaho kenan,ya
saka hannayensa ya zagaye bayanta dasu,qamshinta na bugunsa duk sanda ta daga
hannunta da niyyar gyara masa rigar,a haka ta taimaka masa ya gama sawa sannan taja
da baya,sai a sannan ta maida masa amsar maganarsa ta dazu

"Kai dake da mata biyu kaga fita ya kamaka dole" agogon hannunsa ya kalla,sai a
sannan ya tuna da samha har ga Allah,duk da cewa sanda zai fito basiyi rabuwar dadi
ba amma dole ya dubata,a matsayinta na baquwa cikin gidan dama unguwar gaba daya,ya
laluba aljihunsa ya ciro wayarsa,ya taras da miscals na mutane,har ya dinga mamaki
ya akayi baiji shigowar kiraye kirayen nasu ba,da gaske iman ta musamman ce kamar
yadda zuciyarsa tasha gaya masa.

Baibi takan kiraye kirayen ba ya fara neman number samha,sau uku yana kira bata
daga ba,saiya maida wayar aljihunsa,iman bata ankara ba taji yayi sama da ita

"Bacci nakeji,muje ki tayani na rageshi,nafi samun qwarin gwiwar yiwa yaaganan


bayani" facin din juna suke,ya zubawa fuskarta ido kamar yadda itama take
kallonsa,kusanci da wani yanayi na musamman ya wanzu a tsakaninsu,kowa na sake
kallon kyau da kyautar da Allah ya yiwa dan uwansa,wani shauqi na fusgar
kowannensu,wata magana yake gayawa iman din can qasa,da alama wani sirri mai nauyi
yake furta mata,wanda har yasa ta gaza ci gaba da kallonsa,ta sadda kanta
qasa,fuskarta na fitar da qawataccen murmushi,baiyi qasa a gwiwa ba ya tattaro
cikin jikinsa gaba daya kamar xai maidata cikinsa,ajiya zuciya da kuma hamdala na
kubce masa lokaci daya.

A hankali bacci yayi awon gaba dasu gaba dayansu,wani irin bacci mai matuqar
dadi da nutsuwa.....

Ya rigata farkawa,hakan ya bashi damar kallonta yadda ransa yakeso,indai zai


yiwu da an bashi matarsa ya wuce da ita,motsawar da yayi da niyyar sauka ita ta
sanyata farkawa,saidai ta kasa motsawa saboda kunyar yadda ta jita a jikinsa kane
kane,waiwayawa yayi ya sake kallonta,yadda yaga fatar idanunta suna rawa ya
tabbatar masa ta tashi,sai ya saki murmushi,ya duqa a hankali yayi kissing goshinta

"Time for salat,kada mu makara" ya qarasa fada yana sauka din,kana ya wuce toilet.

A hankali ta bude idanunta ta saukesu a gurbin daya tashi,ba iya wajen ba,hatta
da jikinta yabar mata qamshinsa mai yawa,miqewa tayi taja dankwalinta ta rufe
kanta,dai dai sanda ya fito fuska da hannuwansa suka akwai lemar alwalar da
yayi,yana sauke hannun rigarsa da ya nannade saboda kada ya jiqe.

Da idanu ya bita tamkar wani tsohon maye,ta wuce ta gabansa ta qarasa toilet
tana jin mugun nauyinsa,ya saki qaramin murmushi cikin zuciyarsa yana fadin

"Daga dan wannan abun?"bugun zuciyarsa gaba daya ya sauya daga sanda suka kwanta
shida ita a shimfida daya,yadda dumin jikinsu yake ratsasu na junansu haka wata
sabuwar soyayya ta dinga huda kowannensu,tsohuwar shaquwar dake tsakaninsu ta motsa
kanta da kanta.
Gefan hannun damansa ta tsaya ya tayar musu da salla jam'i shi da ita,bai
tsawaitata sosai ba kamar yadda bai gajartata ba,suka sallame,kowa yayi addu'o'insa
na bayan sallah sannan ya miqe yana dubanta bayan ya saka takalminsa

"Muje ki rakani mu gaisa dasu,bamu gama gaisawa ba na shigo ta nan" kunya da nauyi
suka kamata,batasan da wanne ido xata kallesu ba,amma dole ta laluba dan kunnenta
data gani gefan pillow dinta wanda batasan ya akayi suka cire ba,tadai san dasu ta
kwanta,ta fara sanyasu,saidai gaba daya a diririce take saboda yadda yake ritsata
da kallonsa,ita dai tasan ba dabi'arsa bace kallon,amma ya zuwa yanzu ya canza.

Bataji tahowarsa sai saukar hannunaa data ji saman nata hannun,jikinsa yana
gogarta kadan kadan,zame hanunta tayi ba shiri har dan kunnen nafaduwa,ya duqa a
nutse ya debosu,ya kama kunnen nata yana saka mata,ya sanya ya bamesu,saiya tura
bakinsa gefen kunnen yana ce mata

"Dama can tun asali nike saka miki dan kunne,lokacin kina mitsitsiyarki kin
tuna?,eheennn,daga yanzu aikina ya dawo gareni" sai yaja da baya yana gyara zaman
hular kansa,yayin da tayi mutuwar tsaye a wajen saboda yadda numfashinsa ya hade da
kalaman ya shige mata kunne gaba daya,cikin jarunta dason nuna dakiyarta ta bude
idanun nata saidai juya masa baya tayi da sauri ta kuma nufi qofa.

Bai dakatar da ita ba,a haka suka tafi,saidai tayi nadama,ta gwammace jerawa
sukayi,saboda yadda takeji a jikinta yana qare mata kallo ne har zuwa sanda suka
isa sashen.

A kofar kitchen ya samu inna,cikin matuqar girmamawa ya gaidata

"Ya lameen.....naga shigowarka fa,inata nemanka,naje sashenku inata bugawa baka


buden ba" cewar mufida cike da quruciya,kunya ta kamasu su duka,har innar,da sauri
iman tayi gaba zuwa dakin yaagana,yayin da lamin ya shafa kanshi yana son basar da
zancan,itama innar gaba tayi,wani mayalwacin farinciki yana ratsata,irin farincikin
da kowacce uwa keji sanda ta kalli diyarta a tare da ita da managarcin miji,tasan
da shigowarsa,sabida baqin da tayi sun gaya mata,amma jin sashensu ya nufa kuma
tatabbatar iman nacan yasa bata nemi kowana cikinsu ba,yaagana ce keta qorafin
saita qwanqwashi kawunan ja'irai,daa anata fama da kowa a cikinsu ashe gulmace,data
sani tabar 'yan banxa kowa yaji a jikinsa,taga inda kowa zaikai soyayyar
tashi,itadai inna murmushi kawai takeyi,don bata da amsar data wuce
murmushin,farincikin dake ranta Allah ne kadai yasan yawansa.

Batasan malam yana dakin suna magana da yaagana ba sai data shiga,cikin jin
kunya ta zube tana gaidashi tun bata qarasa shiga ciki ba,tana addu'ar Allah yasa
lamin ya wuce kada ya biyo bayanta,malam ya amsa yana tambayarta jikinta
" Da sauqi malam" ta amsa masa tana duban qasa

"To alhamdlh,dama abinda nake jira kenan,qaraso ciki hajar,dama inason magana dake"
sum sum ta miqe zuwa cikin,yaagaba da farinciki itama ke ratsata ta bita da kallo

"Ja'ira,kamar wata ta Allah" ta fada tana jefa mata harara,gabanta ya fadi,Allah


yasa kada ta titsiyeta gaban malam din,don ta fuskanci 'yar ba ruwana ce itama
yaaganar,Allah ya taimaketa daga haka bata qara ba.

Tana zama lamin din ya shigo,kunya ta kamashi,shima ya samu waje ya zauna


kamar yadda malam yasa iman din,maganganu yayi musu masu yawan gaske,wanda kusan
sunfi karkata ga iman din

"Kada ki bamu kunya iman,ubangiji shine yasan manufarsa da ya juya al'amarin yazo
ahaka" abinda tafuskanta shine har malam su yagana suka ninke,shi da ita ne basusan
abinda ke faruwa ba sai data fashe.

Godiya sukayi masa gaba dayansu,musamman lamin wanda kamar zai shige
qasa,malam din ya miqe yana duban yaagana

"Yaaya,inaga tunda ta warware ai zasu iya wucewa gida koda zuwa anjima ne" wani
dadi ne ya kama lameen,kamar ya tashi yayita shiwa malam albarka saidai babu dama

"Ba matsala,idan ma tafiyar bata samu yau ba gobe ko jibi idan ta sake warwarewa
saisu tafi,kafin nan an sake qarasa sauran kintse kintsen da ba'ayi ba"

"Yau din dai yafi dacewa.....ni xan fita,sai na dawo" dukkansu suka hada baki wajen
yi masa a dawo lafiya,ya fice ha barsu,zuciyar lamin a dagule,me yasa yaagana zata
hanashi iman dinsa alokacin da yafi dacewa ta kasance dashi,a yanzun da ya tabbatar
sa samun iman din gundarinta,sai yakejin kamar bazai iya nisa da ita na awa guda
bama.

Ficewar malam din yasa yaagana ta dawo da hankalinta kanshi

"Bana nufin hanaka iman....saboda gaba dayanmu a yanzu burinmu shine ta kasance
cikin dakinta,akwai dalilin da yasa nakai abun zuwa jibi,kayi haquri Muhammad"
murmushi ya sakewa yaagana din,bashi da yadda zaiyi bashi da kuma da zarrar yin
jayayya da ita,yafi kowa sani baya ga yaa barka itace mutum ta farko datafi kowa
son tarayyarsa da iman din.

Miqewa yayi yana cewa

"Zan wuce yaagana,sadiqu har yanzu bai shigo ba"

"Uhmmm,wannan,kada ma ka sanya ran ganinsa a yau,jiya sai daya gamamin iskanci


sannan yatafi,bai tadda kakannin ba ni sai ya maidani kakar tasa" murmushi yayi
mata ya sanya hannunsa a aljihu ya ciro rafas na 200 sababbi,ya jima yana ayyana
irin alkhairin da zaiwa yaagana amma ya kasa ganin me yafi dacewa da ita,ya ajiye
kudin a gabanta yana mata sallama

"Dawo nan ameenu ka dauki kudinka,meye haka?"

"Ayi mana addu'a yaagana" abinda ya fada kenan ya sanya kansa ya fice.

Ajiyar zuciya yaagana ta saki

"Tashi ki rakashi,idan kin dawo ki shigo inason ganinki" tsam ta miqe tabishi kamar
yadda yaaganan ta umarceta,cikin zuciyarta take jin batason yin nesa dashi.

Kamar yasan da fitowarta kuwa ta sameshi zaune cikin motar,yadan kunnata tana
warming kanta,duka qofofin gaban a bude suke,saita shiga seat din mai zaman banza a
hankali,tana shiga yasa hannu da hanzari ya maida murfin motar ya rufe.

Ya kwanto jikinta sosai sanda zai rufe murfin,koda bayan ya rufe din bai
dagata b,ya danne kusan rabin jikinta,idanunsa ya zuba cikin nata yana aika mata da
kallo mai nauyi da ajjiye saqo a qwaqwalwa da zuciya wanda zaiyi mutum ya manta
irin wannan yanayin.

Bai iya cewa komai ba sai morewa kallonta da yayi na kusan mintuna goma,sai da
yaji ya gamsu don kansa sannan ya kama tafin hannunta yayi kissing dinsa,ya hada da
goshinta,sannan ya nutsa hannunsa a hankali zuwa qugunta ya riqeta sosai

"Kiyi matuqar kularmin da kanki iman,kwanakin da yaagana ta dibamin sunyi yawa,amma


tafi qarfin haka a wajena"kanta ta jijjiga tana murza tafin hannunta saitin inda
yayiwa kiss din
"Ko bai isa ba na qara miki?" Dan zabura tayi,shi wai bayajin komai ne?,baisan
nauyinsa takeji ba,ya lameen din da takewa kallon yaya a wajenta yau shine yaketa
mata wadan nan abubuwan?,kamar ya karanci abinda ke ranta ya sakar mata wani
tattausan murmushi,ya fidda hular kanshi ya ajjiye

"Ki tsammaci abubuwa masu yawa da suka fi wadan nan zafi.....na yadda bakisan komai
a soyayya ba iman,banga abinda kika iya ba,dole na bata lokacina na baki horo na
musamman" saiya buda murfin motar,ya zagayo side dinta ya bude mata ya matsa gefe
ya bata daman fitowa.

Tamkar makaho da dan jagoransa haka ya sanya hannunsa cikin nata,bai saketa ba
sai daya kaita qofar parlor sannan ya koma,kasa wucewa tayi,ta labe ta bayan labule
tana hangensa,cikakken gentle man din da a yanzun ya zama mallakinta,bata bar wajen
ba sai daya shiga motar ya tayar.

Tana juyowa wa zata gani?,inna ce a zaune,amma saita dauke kai kamar bataga
komai ba,kamar zata fadi saboda sauri ta wuce dakin yaagana don taji kiran datake
mata.

Kala kalan magungunanta ta ritsata dasu,dama wancan gutsuro wannan,inda tasan


neman da yaaganar ke mata kenan ba zata dawo ba,hakanan tana bata rai ta karba ta
shanye kowanne,yaa ganar kuma ta sanar mata zaman kwana biyun da zatayi a gida
dalilin wannan ne,sai final gyaran jikin da takeso azo goben ko jibi ayi mata,daga
nan ta zarce da bata wasu shawarwari da hikimomi gami da dabarun zaman aure wadanda
zasu amfaneta.

*_LAMIN_*

Tunda ya dauki hanyar gidansa tunanin iman dinne fal zuciyarsa,duk wani moment
da sukayi spending tare ya dinga dawo masa,shi kadai cikin motar ya dinga sakin
murmushi,hannunsa yana tuqi,daya hannun kuma na dafe a qirjinsa,daidai sanda ya
tsaida motar qofar baqin gate din gidansa ya sauke ajiyar zuciya,yabar samha cikin
yanayi na rashin fahimtada daidaito a tsakaninsu,a yanzu kuma baisan me zai shiga
gidan ya iske ba......

End of book

Leave a comment

Post

Comments

109346365637918680979
Allah ya biya ki da aljjana huguma kinyi duk yadda akeyi luv u so much

2 minutes ago


103039842410465448425
Muna godiya

2 hours ago


112699676368185333462
Nice one

3 hours ago


116654277997892434205
Wai wannan buk har banason ya qare godiya me tarin yawa

3 hours ago

Contact Us
Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742

Email: [email protected]

Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram


Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io

"
https://arewabooks.com/chapter?id=62d57954241eaa1ff3ba79b0#:~:text=Chapter
%2069-,Shafi%20na%20sittin%20da%20takwas,yanzu%20kuma%20baisan%20me%20zai%20shiga
%20gidan%20ya%20iske%20ba......,-End%20of%20book
[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: "




Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ's
Privacy Policy
Terms of service
Logout

KUFAN WUTA
Chapter: Shafi na sittin da tara

Share:





Report

KUFAN WUTA
View: 334

Words: 2.7K


Shafi na sittin da tara

Chapter 70
Shafi na sittin da tara

69

Tun daga dogon corridor da zai sadaka da babban parlor din gidan zaka fahimci
akwai wadanda sukazo,saboda tarin robobi da gwangwanaye na lemo har zuwa cikin
ainihin falon,baiyi mamaki ba,saboda sanin yadda samhan keda jama'a da tarin
qawaye....yasan hakan zata faru,shi yasa tun safe yabar musu gidan,saidai abinda ya
bashi mamaki yadda aka gaza tsaftace wajen,duk da falon a yanzun babu kowa,shaidar
sun tafi.

Sallama ya sakeyi karo na uku,shuru babu amsa,saiya nufi hanyar sashenta da


dan hanzarinsa,saboda so yake ya qarasa dakinsa yayi wanka ya sake kwanciya,don sam
jikinsa babu wani kuzari,kamar ya baroshi ga iman ne.

Mamakinsa ya ninku sanda ya shiga parlor dinta,kamar sautin kuka ya dinga ji


daga bedroom dinta,abinda ya daga hankalinsa qwarai,ya qaran saurin da yake zuwa
bedroom din.

Zaune take saman gadon,ta bawa qofa baya,bai tsaya rufe qofan ba ya qarasa
gareta da sauri
"Dakata" ta fada da sauri sanda yake niyyar riqoni,sai ta daga kanta tana
dubansa,mamakin dai still bai barshi ba,meye haka yake damun samhar daya sanyata
irim wannan kukan?,har idanunta sukayi luhu luhu haka,ta fita hayyacinta?,uwa uba
ma kayan dake jikinta sune dai bata sauya su tun safe daya fita ya barta,sai yayi
calming kansa ya jawo kujeran madubi ya aza a gabanta,yahau kai ya zauna,cikin
kulawa ya fara tambayarta abunda ke faruwa

"dama iman ta taba aure?" Ta jefa masa tambayar kai tsaye tana duban idanunsa

Ga mamakinta murmushi ya saki

"Eh....me ya faru?" Yadda ya dauki maganar ba da wani muhimmanci ba ya tunzurata


matuqa,cikin tsananin fushi da fusata ta fara magana

"Oh.....kana sane kenan zaka auri matar da ciwon qanjamau yayi sanadin mutuwar
mijinta?,ka kwaso mana masifa,mu taru mu mutu gaba daya ayiwa iyayena asarata?" Ko
darr baiji ba game da abinda samhan ke fada,wanda ita awajenta maganar dai dai take
da tashin duniya,yayin da a wajensa maganar bata kama koda matsayin tudu na
slippers dinsa ba,ya riga daya samu dukkan wani bayani daya dace game da iman

"Ke waye ya gaya miki?"

"Masoyana wadanda basason halakata"

"Duk wanda ya kawo miki labarin to ba shakka cikin biyu daya ne,kodai ya kawo miki
shine saboda ya tarwatsa farincikinki da zaman lafiyarki,ko kuma ya samu labarin ne
daga muhallin da qarya da sharri da yarfe ta gurbatashi ko kuma shi ya zauna ya
yiwa maganar ado.....tabbas iman ta taba aure kuma sun rabu da mijin,wannan kuma ba
hurumin da lallai saina gaya miki bane,abune daya shafeni ni kadai,amma maganar
tana da HIV wannan bata taso ba,so please ki kwantar da hankalinki mu shimfida
kyakkyawan zama a tsakaninmu"

Cikin kukan dake cakude da masifa da tashin hankali tace

"Wallahi bazata sabu ba,ta yaya inaji ina gani za'a cuceni,mutuwa ta shigo jikina
nasa hannu na tarbeta?,dama ku maza idan idanunku suka rufe kunason mace ko wanne
aibu ke gareta bakwa gani,to ni bazan yarda ba,muddin kana sona kana son zama
dani....dole ka haqura da auren iman,domin kuwa ni ban shirya mutuwa ba" idanu
kawai ya zuba mata yana kallonta,saboda yadda ta juye masa daga samhar daya sani
zuwa wata ta daban,a nutse yake karantarta,yadda wutar kishi ke huruwa cikin rai da
zuciyarta,tun ba yau ba yasan wace samha wajen kishi,irin matan nan da suke daukan
kishi kamar ibada,basa ji nasa gani akan wanda sukeso,ya dauka duka zata
hankalta,kuma komai zai ragu,sai gashi a yau yatabbatar da cewa babu wani abu da ya
sauya.

Tsam ya miqe saboda yadda ta fara fadin maganganu kan iman din,bayaso ya
shigarwa iman din konya rama mata,saidai yana tsoron kada samhar ta shiga
mutuncinsu malam.....tabbas a nan yasan bazai iyayi mata kaara ba

"Dukkaninku ina sonku,keda iman baby wadda ta isa ta sanyani na rabu da 'yar uwarta
bisa bin son rai da zuciyar 'yar uwarta,ni nasan me na aura....hakanan nasan nasan
wace iman,na kuma bibiye waye bassam" daga haka ya juya yana barin dakin,tayi kukan
kura ta tare masa hanya

"Wallahi wallahi bazai yiwu ba" abinda ta dinga fada kenan,ganin da gaske ba zata
bashi hanya ba sai ya dauketa cak ya.maidata dakin gadonta yaja mata qofa,cikin
hanzari ya wuce nasa dakin ya murza key yana fesar da iska me zafi daga
bakinsa,wannan wacce irin masifa ce haka?,wannan shine auren dama ko kuwa ya
yake?,har yanzu ko hutun awa daya bai samu ba cikin gidanshi,banda ya fita kenan
haka zai wuni suna irin wannan abun?.

Baiko gama sauke wannan tunanin ba bugun samha da muryarta ya riskeshi har
dakin,bugu take da gaske kan ya bude mata qofa,lallai ba shakka ya tabbatar ta
haukace tuburan samhar,wai anya ma kuwa bamai motsuwar kwanya ko lalurar aljanu ya
dauko ba kuwa?.

Barinta yayi taci gaba da bugun iya qarfinta,ya shiga bandaki ya hada ruwa
yayi wanka,sanda ya fito shuru babu bugun,da alama tayi wanda zata iya ta
gaji,saiya haye saman gadonsa,idanunsa a lumshe ya fada nazari,wacce irin mace ya
daukowa kansa?,anya bai tafka kuskure ba?,kodai wannan shine abinda yaa baraka ta
hango masa tun yanzu ya fara riskarsa?,da ya rasa iman da wanne suna ya kamata a
kirashi?.

Bai sake jin motsin samha ba,bai kuma tashi a wajen ba sai da aka kirayi
magriba,ya daura alwala ya sanya slipper dinsa da carbinsa counter ya fito.

Shuru falon yake dai,hakanan yana nan da shararsa,yaji motsi daga sashen
samhan,don haka ya sanya kansa ya wuce masallaci,bayan yiwa daya daga cikin yara
guda biyun daya aje a gidan saboda aike da bude masa qofa kan ya shiga ya gyara iya
hanya da babban falon kadai.

Ya jima zaune a masallacin,tunani iri daban daban na sauko masa,bai taba


tunanin riskar matsala irin wannan ba kwata kwata da samha,ya zaci koda.mata uku ya
qara bayan ita ba zatayi haukar datakai wanan ba,sai gashi ta bashi mamaki,ta kuma
kwance masa kai gaba daya.
Bai bar masallacin ba sai da akayi sallar isha'i dashi,yaga maqotansa sosai
suka gaisa,yaji dadin ganin karamci da mutunci daga garesu,daga nan bayan ya fito
ya yanke shawarar samar musu abinda zasuci,daji da gani ma basai ya batawa kansa
lokaci ba,babu wani abinci da zaici a gidan,bayason batawa kansa lokaci wajen
komawa gida dauko mota,don haka ya tari napep drop zuwa da dawowa ya wuce dashi.

Da tafiyarsa da dawowarsa gaba daya bai wuce awa guda ba,mai napep din ya
direshi qofar gida,ya biyashi kudinsa harda qari,ya dinga zabga godiya kuwa cikin
jin dadi,hannunsa dauke da leda ya juya zuwa gate din gidan nasa,saidai mamaki
sosai ya kamashi,ganin sabbin baqin motoci har guda hudu.

Layin nasu yabi da kallo,yana son tantance qofar gidan ne kawai keda sararun
yin parking?,sai yaha ba haka bane,ko inama kawai space,jikinsa da zuciyarsa suka
bashi wani abu,sai yaci gaba da takawa zuwa cikin gidan yana nazarinsa,har zuwa
sanda yake gab da falo,inda ya fara jin tashin muryoyi.

Bai gaza ba bai kuma sareba yaci gaba da kutsawa,bai tsaya ba sai daya dangana
da falon bakinsa dauke da sallama,dukka hankulan mutanen dake cikin falon suka dawo
kansa,alamu masu qarfi na nuna cewa zancansa akeyi.

Mamaki sosai ya cikashi sanda sukayi idanu biyu da mahaifin samha,qanin


mahaifinta dana mahaifiyarta,sai ita kanta mahaifiyar tata,amma duka sai ya shanye
wanna,ya ajjiye ledojin saman daya daga cikin kujerun,ya qarasa falon yana gaidasu
cikin matuqar girmamawa,suka amsa dukkaninsu,saidai da qyar mahaifiyar samha daketa
shafa bayan samhan cikin salon lallashi ta amsa masa,bai damu da wannan ba,koma
meye macace yayi mata uzuri,saiya maida kanshi zuwa ga mazan.

"Malam ameen,nasan zakayi matuqar mamakin ganinmu cikin gidanka ko?" Kai ya
gyada,so yake kawai yaji qarshen zancan,duk da zuciyarsa tagama ayyana masa komai

"To ba abun mamaki bane duba da yadda diyarmu wadda ke da kwana guda tal cikin
gidanka ta kiramu tana gursheqen kuka gami da neman agajinmu,sanda muka iso kuma
mun iske mummunan labari mara dadi,wanda mu bashi ka bamu ba,meye abinda yake
faruwa" mamaki ya kama ameen din,wannan wacce irin haukace samha ta aikata?,tana
nufin dukka abinda ya gaya matan bata yarda da gaskiyarsa ba?.

A nutse yayi musu bayani kamar yadda yayi mata,saidai yana direwa ummanta ta
cafe

"Dukka wadan nan bayanan baki ne ai babu wata gamsashiya hujja....ni banga laifin
samha ba data nemi ka sake yarinyar nan ba,don ko nice abinda xan aikata
kenan,bazan yarda ina zaman zamana a laqamin cutar da bata da magani ba" a nutse
lamin ya daga kai ya kalleta kana ya sauke,yanzu ya gano daga inda kowanne hali ya
fito daga samha,maida dubansa yayi ga qanin mahaifinta

"Yanzu kai banda abinka ameenu,da jininka a jika,da rufin asirinka,me zakayi da
wata bazawara,bayan Allah ya maka baiwa da yarinya budurwa kamae samha?" Wani abune
yazo ya tsaye masa cak a wuya,ya hadiye yawu da qyar yana jin yadda zuciyarsa ke
masa zafi kan yadda ya aibata iman din,aibu mai muni kuwa,yadda ransa ya motsu da
bacin rai yasa ya kasa bashi amsa,har sanda qanin mahaifinta shima ya tofa tashi

"Kuma ni nakega akwai qamshin gaskiya cikin al'amarin,tunda gashi ta bayyana har
mijin nata ya rasu,kuma mun tambaya an tabbatar mana lallai HIV dince fa kasheshi
tun kafin muzo wannan zaman,saboda haka nima dai gaskiya ina goyon bayan samha"

Gaba daya kansa ga qarasa daurewa da mamakinsu,daga mazan har macen duka babu
mai hankali ashe?,zuwa sukayi su tursasashi zama da 'yarsu kenan ita
kadai?.......da idanu shima ya kalleshi har zuwa sanda samha wadda ke gursheqen
kuka jikin mamarta tayi magana

"Wallahi kawu dama ba sharri bane,kowa fa ya sani,shine kawai idanunsa suka rufe"

"Ni inaga aje kawai ayi gwaji" mamanta ta fada kanta tsaye tana dubansu

"Shikenan,magana ta qare" baban samhan ya fada yana kallon lamin.

Wani kallo lamin din yayi musu,wanne irin cin fuska ne wannan sukazo
dash?,iman din tasa za'a dauka saboda cin fuska a tafi da ita gwajin cutar
qanjamau?,kawai saboda kishiyarta daya tabbatar da gangan take wannan haukar ta
buqaci tozartata?.

"Duk duniya banajin akwai wanda ya isa ya fiddamin matata zuwa layin gwajin cutar
qanjamau,bayan ina da dukka yaqini da kuma hujjar lafiya lau take,tunda ta dawo
mana gida bata taba wata nummunar cuta ba.....idan dai kuma shakka kan gaskiya da
amanata kuma kuka dauki auren diyarku kuka bani to kun tafka kuskure,kuje ku sake
bincike akan waye lameen yaron malam khalilu" tsam ga miqe yana jin wani irin zafi
tun daga fuskarsa zuciyarsa zuwa gangar jikinsa,bai sauraresu ko waiwayesu ba ya
soma haurawa zuwa dakunansa,yana jin yadda cecekuce ya barke a tsakaninsu,yana iya
jin muryar maman samha na sake kafa hujja da cewa bashi da gaskiya shi yasa ya
bijire,kuma babu makawa zancan samha gaskiya ne,ba wanda ya waiwaya a cikinsu har
zuwa sanda ya kammala hayewa,kaifin muryarsu ya ragu,ya tura dakinsa ya shige.
Ya jima zaune yatsunsa cikin sumar kansa,kanshi yayi matuqar daukar zafi,wata
qauna ta samha datayi saura a zuciyarsa ta fice fit,bashi da sauran wani buri a
kanta,irin wannan tozarci datayi masa gangami har cikin gidansa,yayi mamakin yadda
akayi ya debo 'yar gidan qananun mutane,ya dauka 'yar dattijai ce,ya jima zaune a
haka ransa a matuqar bace,har zuwa sanda wayarsa tayi ringing,ya waiwaya yana duban
fuskar wayar dake aje gefansa.

Sunan malam da ya gani ya sanyashi tashi ya zauna sosai kana ya janyo


wayar,cikin girmamawa ya daga ya kara a kunnensa,a nutse malam yayi masa sallama,ya
amsa sannan ya fara gaidashi kamar basu hadu ba dazun

"Me yake faruwa ne cikin gidanka lameen?" Kansa ya daure,ya akayi malam yasan da
wani abu?

"Yanzu matarka da iyayenta suka bar nan wajena,karka boyen komai ka gayamin" kamar
yadda ya buqata hakanan ya zayyane masa komai din,bai kuma boye masa ba,malam ya
jinjina kai,yana boye razani da damuwa tare da sosuwar da ransa yayi

"To ai duka wannan ba abun bacin rai bane ko damuwa,qaramin abune da maganinsa
bashi da matsala,yanzu abinda za'ayi shine,gobe da safe ka shirya ka dauki ita
hajar da samhan,ku wucw asibitin a yiwa hajar din gwajin data buqata din a gabanta"

"Amma malam......." Karon farko a kafatanin rayuwasa daya kwatanta musu wa malam
din

"A'ah lamin,kada kace komai,ni dakai da sauran makusantanta ne kadai mukasan lafiya
lau take,amma su da basu sani ba akwai buqatar kankare musu shakku,kayi yadda nace
din saboda a samu kwanciyar hankali da kuma nutsuwa"

"To malam,in sha Allah" daga haka suka katse wayar,yana jinjina halin girma da
dattako irin na dattijon,saidai kuma abinda ya sake qona masa rai yadda suka dauki
samha har tasa qafa tabar gidan ba tare da sani ko neman yardarsa ba,baya koda son
ganinta a yanzu,don haka baima nufaci zuwa yaja mata kunne ba,saiya koma da baya ya
kwanta idanunsa a rufe,zuciyarsa na masa suya,yana son kiran iman,don yana da
tabbacin muryarta kadai zata shafe bacin ran dake ransa,ta kuma wanzar da farinciki
cikin zuciyarsa,saidai kuma bayason ya qara mata damuwa da tasa damuwar,ya tabbatar
duk wadda taji wannan batun a kanta dole hankalinta ya tashi.

Hasashensa kuwa haka yake,kuka sosai iman din ta dinga yi sanda taji case
din,duka wannan sakamakon bijirewa iyaye ne,tana fatan kuma wannan shine sakamako
na qarshe da zata amsa cikin punishment na laifinta,tausayin iman din ya cika inna
qwarai,wannan karon da kanta ta zauna sukayi magana da iman din,irin magana ta 'yar
da uwa

"Ki daina kuka iman,ina mai yaqini da tabbatar miki ba zaki tozarta ba in sha
Allah,babu wata rana data fito ta fadi ba tare da nayi addu'a a gareki ta samun
dacewa da kariya ba,kamar yadda babu wata rana guda daya dana yarda na wuce minti
biyu ina fushi dake.....komai munin laifin da kika aikatamin kuwa,ciki harda auren
bassam" idanunta dake cike taf da hawaye ta daga ta kalli inna,saita sakar mata
murmushi gamida jinjina mata kai tana bata tabbaci

"Duka abubuwan da suka farun ba shakka naji babu dadi,saidai tashin hankali yafi
fushi yawa a ciki,saboda na riga dana sani kin tafka babbar asarar rasa miji na
gari,wanda nayi imanin bassam bai kama koda yatsar lamin ba wajen nagarta,wannan
shine tashin hankalina,bawai fushi da zaben bassam ba,ko a lokacin kina ganin fushi
saman fuskata ne kawai saboda ina fatan hakan zai canza ra'ayinki,to amma da yake
rubutacciyar qaddararki ne babu abinda ya canza,tunda kika tafi ban zauna da
fushinki ba ko qanqani,na maida kaina ga yimiki addu'a kan kubuta daga dukkan wani
sharri da wahalar gidan aure.....ko sau daya jikina da bakina basu huta ba,inajin
zafi.....ina kuma kasa barci duk sanda kikazo gidan nan kika tafi,saboda na karanci
akwai matsala tare dake,nayita zuba idanu ki furta min amma baki fada ba,na zabi na
barki ki gayan da kanki ne,saboda kada irin soyayyar da kike ma bassam tasa kiyi
tunanin ina tambayarki ne don na na samu hanyar rabaki dashi kiyimin kallo na
zalunci,saidai da yake Allah Allah ne,kuma baya bacci,yana tare da dukkan bawansa
daya roqeshi da kyakkyawar zuciya da kyakkyawan nufi sai gashi ya kawo komai cikin
sauqi,dukkan wata matsala ta warware.....ubangijin da yayi miki dukka wadan nan
baiwarwarkin?.....kina tunanin zai saki hannunki akan wannan qaramar matsalar?,kuma
matsala ta qarshe da yardar Allah?" Kai iman ta girgiza,tana jin nutsuwa na saukar
mata,imani da kuma gamsuwa da hukuncin ubangiji na bijirar mata,qaunar inna tana
sake ratsata,sai kawai ta rungume innan tana sake sakin kuka

"Na gode.....na gode inna,ba shakka uwa wata halittace ta musamman,kuma baiwa ce ga
dan adam,kyauta daga Allah wadda babu kamarta" murmushi inna tayi tana sake kwantar
mata da hankali.

**********Washegari malam ya fiddo sadiqu daga gidansa,ya kuma wakiltashi ya dauki


iman ya kaiwa ameen ita,sannan yayi musu rakiya zuwa asibitin da zasuje.

Tsaf ya shirya cikin kyakkyawar shaddar wa gambari mai asalin kyau da tsadar
ruwan sararin samaniya,sanda yake saukowa daga bene yayi tsammanin ganin
samha,saidai waya babu ita,kai tsaye ya zarce zuwa harabar gidan,inda acan yaga
abun mamaki,tuni iyayen samha da kawun nanta na jiya sun halasto wajen,suna ma
cikin motocinsu,hatta da samhan tana gaban motar babanta,kansa a daure amma ya
qarasa ya basu girmansu ta hanyar gaidasu,suka amsa masa ba yabo ba fallasa

"Saimu wuce ko?" Agogonsa ya kalla


"Iman din bata qaraso ba tukunna,so xamu jirata ne" ya amsa musu yana yin gaba,ya
bude tashi motar yayi zamansa,duk duniya banda malam babu wanda ya isa ya sashi
aikata wannan abun me kama da tozarci da wulaqanci,koda yaa baraka bayajin zataiys
tan qwarashi.

Sau biyu qanin mahaifiyar samha na masa magana kan jiran da sukeyi

"Ina cewa dole jininta ake buqata ko?,idan kun qosa kuna iya yin gaba,na biyoku
daga baya" amsar da ya bashi kenan ya maida idanunsa ya rufesu yadda suke. Jin jina
kai yayi ya juya yabar wajen bai sake cewa komai ba shima,saboda ya fuskanci lallai
lameen din ba kanwar lasa bane shima,da alama ma maganar da sukayi da malam din ta
tilastashi aikata abunda suka buqata din.

End of book

Leave a comment

Post

Comments

112201018644657456668
Me ake jira da ita tunda tafice a zuciyarsa. Waje road please taje gatan datake
gani tanada shi ya aureta

9 minutes ago


deejerh27
Allah yasa takara wani chapter din dai

37 minutes ago


deejerh27
Ai wallahi ko bai saketa ba bazai taba son sontaba kuma, abun haushi 🙄

38 minutes ago


ummueamn01
Kai wannan samha anyi daqiqiya🤦 Allah yada daga can ya baki red card.well done
huguma, amma aqara muna more pages plsssss

an hour ago

Load More

Contact Us
Arewa Books Publishers
WhatsApp: 09031774742

Email: [email protected]

Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram


Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io

"
https://arewabooks.com/chapter?id=62d667a17fc1109aa61070e1#:~:text=Chapter
%2070-,Shafi%20na%20sittin%20da%20tara,da%20malam%20din%20ta%20tilastashi%20aikata
%20abunda%20suka%20buqata%20din.,-End%20of%20book
[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: 70

Ba'a qara minti biyar ba suka shigo gidan,take kallo ya koma kanta,cikin
shiga take ta alfarma wadda tayi matuqar dacewa da farar fatarta da kuma kwarjini
da ajin da Allah ya bata,samha dake cikin mota ta tsurata da idanu,take ta raina
kanta,wani kishin iman din na sake turnuqeta,alwashinta da burinta suka qaru,ta
yaya ma zata yarda ta hada miji da iman din?,itakam ta godewa bassa daya bar mata
makamin da zata yaqi iman din cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya zargeta ba.

Ta cikin madubi ya hangesu,saiya tada motar a hankali ya nufi bakin


qofa,saitinsu ya tsaya ya bude motar ya fito,dukka idanunsa naga iman din,akwai
damuwa mabayyaniya sama fuskarta,duk da yadda tayita qoqarin dannewa,ya tako a
hankali zuwa gabanta,kwalliyarta na fusgarshi,daso samune ya sanyata cikin qirjinta
ya shaqi ni'imtaccen qamshin da take fitarwa,ya kuma rabauta da dumin jikintan nan
na musamman wanda yake gasgata cewa qalilan cikin mata keda shi.

Dab da ita ya tsaya,taqin dake tsakaninsu kadanne,kowa idanunsa cikin na


dan uwansa,wani abu na ratsa jikinansu game da kowannensu,sai ya janye idanunsa a
hankali ya maida kan sadiqu dake tsaye a gefe yana waya da matarsa

"Dalla malami dama a motar haya ka daukomin mata?,wannan cin amana ne wlh,ka siya
mota ka tsaya kana batawa kanka lokaci" da alama akwai wani zafi qasan ransa,duk da
yasan da wasa ya fadi maganar amma tabbas tana bayyana jin zafinsa cikin
maganar,yayi masa uzuri mai tarin yawa sabida yafi kowa sanin waye lamin,jin
zafinsa yana da alaqa da situation din da ake ciki a yanzu,don haka ya maida.masa
da sassauqar amsa cikin rama wasan

"Idan mutum yaji zafi ya saka kaina gabas ya yanka mana.....zuwa dai a nepep an
riga anyi,mota kuma bazan siya ba,a siyamin" sai ya kanga wayarsa a kunne yaci gaba
da soyewarsa

"Allah ya sakamin" lamin din ya amsa masa yana janye idanunsa daga kan sadiqun zuwa
ga iman,sake matsawa yayi daf da ita,wannan karon har suna musayar numfashin
juna,ya sanya lallausan tafin hannunsa ya sanya nata a ciki yana dan murzawa kadan

"Kuka kikayi ko jiya saboda wannan wasan kwaijwayon?" Tambayarsa taso karya dukka
wani qwarin gwiwa nata,sai qwalla ta nemi taruwa cikin idanun nata,kansa ga girgiza
da sauri

"Noooo,wannan kwalliyar amarci ce zuwa ga sabon angon da babu irinsa.....don Allah


na roqeki kada ki batamin abata,i like it queen,kuma nayi alqawarin bada tukuici me
yawa,ki zaba,goyaki kikeso nayi mu tafi tun daga nan har asibitin a qafa a gadon
bayana,ko kuma so kike na daga murya na shelantawa jama'ar unguwar nan ina
sonki,ina kuma maraba da shigowar hasken gidan nan zuwa cikin gida?" Wani abu mai
sanyi ya ratsa zuciyarta,kamar yadda kalamansa masu dauke da sanyayyar soyayya suka
yi mata ba zata,bata shirya ba saiga murmushi ya kubce mata,abinda ya sakashi shima
sakin murmushin kenan

"Babu ko daya a ciki"


"Saifa kin zaba"
"Jiranmu suke yaa lamin,kanaji sun fara hon" girarsa dukka biyun ya dage mata
idanunsa tsakiyar nata qwayar idon

"Really?,ni ai banji bama,kinsan kurma ne ni kuma makaho ne a duk sanda nake tare
dake,komai baya tasiri a wajen komai girma da qarfinsa,so ki manta mu qarasa
uzurinmu.....zabi daya sarauniyata"

"Kayi haquri.... next time zan gaya maka"

"Promise?" Ya tambayeta yana murmushi gami da dage girarsa,martanin murmushin ta


maida masa tana jinjina kai

"Ok,muje to" ya fada yana tasata a gaba,ta gabansu suka wuce,wanda kusan kowa yayi
suman zaun acikinsu,kadama samha taji labari,wadda dayqar mamanta ta riqeta

"Mama ki barni na koma motarsu" ta fada sanda taga ya bude mata gidan gaba da
kansa ta shiga ya maida murfin ya rufe

"Kiyi haquri ki zauna a inda kika fara zama,komai ya kusa zuwa qarshe fa,gaggawar
me kikeyi?" Da qyar ta tausheta,tuni ameen tashi motar ta fara yin gaba,suka tashi
tasu suka biyo bayansa.

Ya sadiqu da tunda yaga tsiyar da suke tsulawa sun manta ma dashi ya zare
jikinsa ya yiwa kansa mazauni a bayan motar ya fidda wayarsa yaci gaba dayi,a
hankali taji ya lalubo hannunta ya hade tafukan hannayensu waje daya,daya hanun
kuma nakan sitiyarin motar,ya matse hannun gam cikin nasa,kana ya fara magana da
tattausar muryarsa

"Kina tunani ko tsammanin akwai abinda yake da qarfi ko tasirin da zai iya rabani
dake?,duk duniya babu shi,ban ganshi ba,idan ma kina ganin akwai kiyi gaggawar
shafe wannan tunanin daga ranki" lumshe idanunta tayi ranta na sake yin
sanyi,lallai taso tafka babbar hasara,yadda lameen yake na daban haka soyayyarsa
take ta daban,tana tafe da wani irin sanyi da nutsuwa,bai sake mata magana ba amma
yadda yake sarrafa hannunta cikin nashi dukka wani saqo da baki bai furta ba yana
isa kai tsaye zuwa zuciyarta.

Wayarsa tayi ringing ,ya kalli wayar ya bawa iman din umarnin dagawa,don
bayason cire hannunsa daga nata,ta daga ta saka handsfree

"Malam lamin,ka sauka daga hanya fa,akwai asibitin da zamuje wanda suka qware sosai
wajen yin wannan test din...." Da ido yayi mata alamar ta kashe,saiya gangara gefan
titi ya faka motar,ya kuma kasheta gaba daya.

Kashe wayar da sadiqu yakeyi yayi yana zare earpiece din kunnensa
"lafiya?,me ya samu motar?" Dukan sitiyarin motar lamin din yayi,fushinsa ya
bayyana sosai,wanda hatta sadiqu ba iman ba basu taba ganin irinsa a fuskarsa ba

"Wai ni yaron mutanen nan ne?,kawai don na auri 'yarsu zasu dinga yin dukka yadda
sukaga dama dani?,asibitin ma sai wanda suka zabarmana zamuje?"

"To sai me?, please kada ka bata ranka,minti nawane anyi an gama
shikenan.....kaga,abinda za'ayi ku koma back seat ka bani driving din" haka kuwa
akayi,suka koma bayan shida iman,abinda ya sake bashi damar sake kusanta kansa da
ita kenan,cikin qirjinta ya kifa fuskarsa,kunya ta kamata,tanason ta tayashi sauke
masa temper din daya dauka kamar yadda yaagaa ta koya mata amma kuma tana kunyar
idanun ya sadiqun,duk da hankalinsa sam ba'a kansu yake ba.

Tsaiwar da sukayi ya sanya su samha suka rigasu isa asibitin,suna zuwa


aka buqaci daukar jinin iman din,lamin ne ya rakata aka dauka a gabansa sannan suka
dawo zaman jiran sakamako.

Ko sau daya lamin di n bai zauna ba,yanata kai kawo a area din da iman din
take kamar mai bata tsaro,yayin da samha da tawagarta ke zaune daga gefe,baisan me
suke tattaunawa ba amma hankalin samha a tashe yake,hakanan dukka hankalinta naga
iman din,wadda suke zaune benci daya ita da ya sadiqu,yanata sako mata hirarki duka
don ya dauke hankalinta daga tunane tunane.

Jira na wasu mintuna masu yawa kafin likitan da ya tafi gwajin ya dawo,dan
gajere baqi,yaci farar labcoat,hannunsa sanye da safa irin ta likitoci

"Ku sameni a office" ya fada yana yin gaba cikin hanzari,dakatawa sukayi saida
iyalan samha sukayi gaba sannan sukabi bayansu,kowa a zaune amma lamin na a
tsaye,ya zubawa mutumin da aka kira da likita idanu yana nazarinsa,banda ma rainin
hankali da wayo irin nasu duka manyan asibitocin gwamnati su rasa wanne asibiti
zasu kawosu sai private?.

"Bayan sakamakon gwajin da mukayi ya bayyana cewa....." Sai ya danyi jim yana
rarraba idanu ta cikin gilashin da lameen ya fahimci kamar ma yayi masa yawa,yanata
saukowa yana turashi da hannu ne tun farkon ganinsa dashi sanda yake tsaye wata
nurse na daukan jinin iman din,gyaran murya yayi sannan yaci gaba

"Jinin wadda muka dauka yana dauke da cutar cuta mai karya garkuwar jiki,wato HIV a
taqaice" wani mugun samha da mamanta suka ja,wanda ya cika dakin,yayin da wani
tashun hankali ya saukarwa iman,salatin dasu samha ke maimaitawa tare da maganganun
dama sunsan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya ya sake ruda iman din.

Duk wannan rudun lamin din a nutsensa yake,shi ya kama iman ya zaunar da
ita dai dai sanda samha ke fadin

"Daina tabata,saboda a yanzu aure ya haramta a tsakaninku" tsawar daya dakawa


samhan ta haifar da wanzuwar shuru cikin dakin,ta kuma tafi da kowanne hayaniya
data soma tashi,ya maida dubansa ga likitan da yayi dafafa saman kujerarsa yana
qoqarin maida gilashinsa daya zamo sanadiyyar tsawar lamin din,sai ya miqa hannu ya
dauki takardar dake gabansa wadda yake karantowa ta result din,ya cukuikuyeta ya
cusa a aljihu,sannan ya waiwaya ga samha data miqe tsaye tana kallonsa.

"Yadda iman keda qanjamau nima itace dani,na boye miki ne saboda inason kema ki
samu rabonki,amma tunda gaskiya ta bayyana,kije na sakeki saki biyu" salati suka
dauka gaba dayansu,wannan karon harda mazan,tashin hankali wanda ba'a saka masa
rana,tuni.mamar samha ta miqe kamar zata kife tana ambatar sunan lamin din,tama
rasa me zata ce masa,bata taba tunani ko kawo abin zai juye haka ba,saidai bai
saurari kiranta ba ya juya ga likitan
"Kai kuma,ka saurari kira daga kotu kan abinda ka aikata,ko dukka kudina zasu qare
saina tabbatar an rufe asibitin nan" yana qarasa fadi ya damqi hannun iman,bai
saurari dangin samha daketa kakkabi da fadin maganganu,ko ita samha data zube jikin
mamanta tana rusa kuka ba,ko kuma sadiqu dake qoqarin dakatar dashi da nuna masa
aikata babban laifi na rashin dacewar sakin samha,idanunsa jazur ya dubi sadiq

"Ta yaya masu cutar qanjamau zasu zauna da lafiyayya su shafa mata?na godewa Allah
da banyi tarayya da ita ba bare na shafa mata kona zalunceta ba" daga haka yaja
hannun iman suka fara fita daga office din,saidai tun kan yakai ga ida ficewa saiga
likita a gabansa,yayi zaman 'yan bori,babu glass babu labcoat,duka sunyi nasu
waje,ainihin kayan dake jikinsa suka bayyan,wanda wani wajenma a kode yake,ya fashe
da kuka wurjajan

"Kayimin rai kayimin afuwa,wallahi wallahi indai abundanka fada zaka aikata dr
dawood saiya daureni dauri na har abada,ka taimakeni kamar yadda Allah ya
taimakeka,wannan aikin dashi nake ci nakesha nake kuma kula da mahaifiyata da bata
da lafiya,nidin ba kowa bane face masinja,aikina aike aike da sharewa dr dawood
wannan office din da kake gani,ina zaman zamana suka na nayi musu wannan
aikin,wallahi ba halina bane" maganar dafa sandarar da duk wanda baisan shiryayyar
da aka shirya ba,saidai lamin ya dake ya dubeshi

"Ai gwara aje kotun,kaga nan dawood din zai gane baragurbi irinku dake bata sunan
asibitinsa" daga haka ya tsallakeshi yanata faman magiya da ban baki,suna zuwa ya
budewa iman mota ta shiga,shima ya shiga,ya tayar da ita a zafafe ko sadiq bai
tsaya jira ba ya fice abinsa da wani irin gudu dake nuna tafasar da zuciyarsa keyi.
[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: 71

Wani irin gudu yake,yayin da ita kuma ke kuka,gaba daya zuciyarta ta karye,duk
da kuka take amma ta fuskanci ba hanya gida ya nufa da ita ba,hakanan ba hanyar
gidansa ya nufa da ita ba.

Tana jinsa yana wayar cewa a rufe gidan,yaran kuma dake nan su
tafi,tafiyar gaggawace ta sameshi,idan ya dawo zai nemesu,ya ajjiye wayar dai dai
sanda sukakaraso qofar wani katafaren hotel,yana horn aka wangale masa babba gate
din hotel din,ya gangara a hankali xuwa parking lot ya daidaita tsaiwar motar tasa
sannan ya kasheta,maimakon ya fita a motar sai ya juyo gaba daya yana fuskantar
iman wadda ke cure waje daya tana shesheqa,idanu ya zuba mata sosai yana dubanta
duk da baya iya ganin fuskarta,qoqarin yake ya rage kaifin fushinsa kafin yayi
magana da ita,tsahon mintuna sannan ya sauke qaqqarfar ajiyar zuciya,a tausashe ya
kamo hannun iman din yakaishi saman qirjinsa saitin zuciyarsa,kana ya kwantar da
kansa jikin kujerar,sosai take jin yadda zuciyarsa ke bugawa a tsakiyar tafin
hannunta,koda baice komai ba tasan fushine sosai cikin ransa

"Iman......so kike zuciyata ta buga gaba daya?" Yayi maganar muryarsa can qasa yana
dubanta

"Tun ba yau ba kinsan fushinki tarwatsa min nutsuwa yakeyi,bana qaunar sautin
kukanki ko kadan......ya kamata zuwa yanzu kiyi shuru hakanan" a hankali ta daga
kanta,idanunta a kansa,cikin muryar kuka ta fara magana

"Me yasa zaka aikata haka?,saki ya ameen a kwanakin da ko bakwai basu kai ba?,ya
kake tsammanin ni zan dauka kenan?,wanne kallo kakeso duniya tayi mana musamman
ni?" Ajiyar zuciya ya sauke,ya lunshe idanunsa yana budesu duka lokaci guda ya
zubesu a kanta

"Iman.....ta zagi malam da inna....ta kirasu mayaudara maha'inta macuta.....ta fadi


munanan kalmomi a kansu ba tare da tasan kunnuwana duka sun jiyemin ba lokacin da
nake zirga zirga kuna zaune ke da sadiq,zuciyata ba zata iya jurar zama da duk
wadda ta tabasu ko ta zagesu ba,bata taba zaton naji ba,Duk wanda ya zagi inna ko
malam......kamar ya zagi wadanda suka kawoni duniya ne,su suka raineni har na zama
mutum data kalla tace tana so,tana kuma muradin aurensa,koda iyayena sun kawoni
duniya ne.....amma inna da malam sune sukayi raising dina up har na kawo matakin da
nake kai a yanzu,bazan iya yiwa duk wanda ya nema wulaqantasu uzuri ba....koda haka
bata kasance ba dama babu lallai na iya zama da samha,ba yabon kaina nake
ba.....amma ni mutum ne da baya qaunar qarya ha'inci da kuma yaudara,dukka samha ta
hada wadan nan,tunda ta iya shirya wannan ita da mahaifiyarta.....me kike tunanin
zai faru nan gaba?kina zaton za samu nutsuwa da kwanciyar hankali a rayuwata da
ita?,meye abun sha'awa ko jan hankalin bata dama ta zama uwar 'ya'yan da zasu fito
ta tsatsona,na musu adalci ida na bari ta zama uwa a garesu?" Ya qarashe maganar
yana zuba mata idanu,tabbas maganganunsa akan hanya suke,saidai ga tabbatar basu da
wata mafita ko excuse da zasu bawa malam,dukkansu zasu tashi a matsayin masu laifi
ne

"Nasan abinda kike gudu ko kuma tunani,kada ki damu da mutanen duniya,ba zaki taba
gamsar dasu akan kowanne abu da zaka aikata ba,kaidai ka damu da aikata dai dai da
kuma abinda mutanen qwarai zasu yaba dashi,komai zaizo ya wuce kamar bai faru
ba,malam kuma nasan yadda zanyi da batunsa,kin gamsu?" Kai ta gyada masa a
hankali,sai ya sakar mata murmushi yana saje matsowa kusa da ita

"Komai ya wuce?" Kai ta sake gyada masa

"Oya.... give me a kiss" daga kanta tayi da sauri cikin yanayi na kunya ta
dubeshi,saiya dage mata girarsa yana sakar mata murmushi

"Eh,ko kiyimin koni nayi miki,amma nawa zai zama deeper than yours......don haka ki
zaba" ta tabbatar da gaske yake,kuma daga yanayin kallon da yake mata ta tabbatar
idan ya fara zataji a jikinta,saita kauda kanta

"Ya lameen...."
"Noooo.....wannan ba yayanki bane,mijinki ne"
"Kunya fa....."
"Ban santa ba.....bafa takura,the choice is yours.....ki bani dama kiga yadda zata
kasance" sai ya fara qoqarin sake matsowa,abinda ya sata ta waiwayo da sauri da
nufin yi masa abinda ga buqata din,saidai ya goce bata sameshi ba,sannan ya fara
nuna mata bakinsa

"Right here nakesonshi" idanu ta fidda,saita runtse idanunta

"Let me help you" kafin ta gama tantance abinda zai fada din tuni ya riqe fuskarta
tsakanin tafin hannunta,kamar yadda ta fada mata dinne kuwa, kisses ya bata masu
dogon zango da kuma tsananin zafi,wanda da qyar ta samu ya saketa,kowa ya koma da
baya yana maida numfashi,sai daya daidaita nutsuwarsa sannan ya miqa mata hannunsa

"Wayarki please"batayi musu ba ta miqa masa wayar,tana kallonshi ya bude wayar,ya


cire layinta ya karya gida biyu ya watsa ta window,ya daga sexy eyes dinsa ya
kalleta

"Am sorry......bana buqatar kowa ya nememu ne a yanzun haka,zan musanya miki da


wani layin,xan kuma saka miki number duk wanda kike da buqata" kai ta gyada masa
kawai,don a yanzu bata da wani abu da yayi saura face bin umarninsa da kuma yin duk
yadda yakeso,hannunsa yasa ya zaro tashi wayar,ya laluba wata number yakira.

Batasan wa ya kira ba,amma taji yana maganar flight from kano to Lagos,ya
buqaci a yanka masa ticket guda biyu.

Yana gama wayar ya kasheta gaba daya shima,sannan ya fita ya zagaya ya bude
mata seat dinta kamar yadda ya saba ta fito,ya kulle motar suka taka zuwa ciki.
Batasan lokacin da ya karba musu daki ba,tunda suna zuwa key kawai ya karba
na dakin,tana gaba yana take mata baya,kamar sarauniya da yaran gidanta,yadda yake
matan kawai yana sanyawa taji kanta ya kumbura da yawa,wata kulawace da bata saba
ganin irinta ba,kulawa ta musamman mai tsayawa a rai,wadda ke ratsa jiki da bargon
masoyi.

Suna shiga abinci ya iskosu da wata leda ta daban da batasan meye a ciki
ba,sallah suka fara yi saboda quracewar lokacin azahar din,sanna suka zauna zaman
cin abincin,wanda cikin plate daya ya zuba musu,suka kuma yi sharing one spoon
kamar yadda ya fara koya mata tun daga sanda suka zama ma'aurata.

"Uku ta kusa,jirgin qarfe hudu kuma zamu bi zuwa lagos,kiyi wanka ki


shirya,akwai kaya cikin ledar can ki zaba ki saka kafin na dawo" bayanin nasa yazo
mata a bazata,idanunsa yana kanta har ya ja qofar,abunda ya zama shamaki tsakaninsa
da ita kenan.

Yana fita din ta shiga toilet ta soma shiryawa kamar yadda ya umarceta,duk
motsinta ba abinda ke yawo a ranta sai abunda ya auku yau,komai tana ganinsa kamar
a mafarki,addu'a ba wasa bace,hakanan duk wanda ya riqe Allah....yakuma yi abu ko
ya bar abu saboda girman zatin Allah to ba shakka Allah bazai wofantar dashi
ba,kalaman inna suka dawo mata,ta fadi gaskiya,duk da itama bata taba kawo lameen
din zai aikata danyen aiki irin wannan ba,shiri tayi sosai,ta tadda komai cikin
ledar,kana ta fidda wani dinkakken lace na alfarma,wanda koda idanu ka kalleshi
kasan yaci kudinsa,akwai takarda a maqale a jiki wadda ke dauke da tambarin
kamfanin IB COUTURE,kenan dinkakke ne daga masarrafar suttura ta lameen din.

Ta tabbatarwa kanta shi ya zabar mata kayan,saboda yadda yayi mata cif a
jikinta,dinkin kuma ya zauna mata matuqa,kamar don saboda ita aka qirqiri
kayan,turare ta fesa baya ta daura dankwalinta daya zauna mata das da salon dauri
zamani na gaban goshi,wanda haka ya qarawa kwalliyar tata armashi.

Tana gamawa yana shigowa janye da qaramar jakar matafiya mai azabar
kyau,idanunsa a kanta,tayi masa kyau fiye da yadda ya zata,ya kasa dauke idanunsa
daga kanta har ya qaraso dakin bakinsa dauke da sallama can qasan maqoshinsa.

Bata ankara ba har ya cimmata,saiji tayi ya dagata sama cak ya dire saman
madubin,ya kuma zagaye qugunta da hannayensa yana kallon cikin idanunta da wani
narkakken kallo mai cike da soyayya,cikin wani low tune yace

"Fatabarakallahu ahasanul khaliqin,ma sha Allah,ma sha Allah,tsarki ya tabbata ga


sarkin da ya tsaga wanna halittar..... queen,kinyi kyau kinyi kyau fiye da yadda
zan fada miki.....inason wanna kwalliyar queen.....inason kici gaba da kasancewa a
haka" a kunyace ta amsa masa

"Consider it done sir" da sassanyar muryarta,murmushi ya kubce musu duka su


biyu,yaja da baya yana cewa

"Tsaf zamu iya rasa jirgi idan naci gaba da kallonki" sai ya taka da baya da baya a
hankali

"Banason nayi missing kallon fuskarki kona second ne....ki jirani" ya fadi yana
juyawa da sauri ya fada toilet din,yabar iman daskare a wajen cike da
shauqi,qirjinta cike da soyayyar lameen din,zuciyarta ta cika da hamadala ga
ubangiji da bai haramta mata ni'imar samunsa a matsayin miji ba.

Duk da yadda take tajin kunya tana doddojewa tun daga fitowarsa daga wanka
shiryawarsa zuwa ficewarsu filin jirgi bai damu da wannan ba,yana maqale da ita
yana karanta mata wani karatu na musamman,karatun da shi daya ya sanshi,ya kuma
gama tsarashi a kwanyarsa da zummar zai dora rayuwar auratayyarsa akai,yanason ya
morewa rayuwarsa qwarai da matarsa ta sunna,irin rayuwar da zata kasance abar
sha'awa da kwatance ga dukka ma'auratan da suka sansu.
"Wannan sissinqewar da kikeyi baby ba inda zata kaiki.....inda xamuje sabon shafin
rayuwa zamu bude,inda bau takura ko matsi,zamu tafi inda babu wanda ya sanmu bare
mu samu naqasu" ajiyar zuciya ta sauke,da gaske dai lamin yake,ta gaji da yadda
yake sanyata jin kunya,idanun mutane nata kaiwa kansu,don tun a daki kafin su fito
sanda ya rungumeta ta baya a gaban madubi bayan ya gama shiryawa ya musu hoto ita
kanta ta tabbatar duk wanda ya kallesu sai ya sake dubansu,sabida wani iri match da
bata taba kula dashi ba taga sunyi,uwa uba dressing dinsu,tun kafin ma subar hotel
din receptionist din dake wajen ta soma fada musu,yare ce,hakanan tana da barkwanci
da haba haba da jama'a.

Kafin su tashi taga ya kunna wayarsa ya turawa sadiqu texs,tasan kuma


bazai wuce shaida masa ya gayawa su malam sun wuce ba tare da neman afuwa da
addu'ar su malam ba,itama hakan ya qara kwantar mata da hankali,tasan at least
hankalinsu zai kwanta tunda a qalla sunsan suna lafiya kuma ga garin da suke.

_sai muce a sauka lafiya LAMIM_


[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: "




Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ's
Privacy Policy
Terms of service
Logout

KUFAN WUTA
Chapter: Shafi na saba'in da biyu

Share:





Report

KUFAN WUTA
View: 534

Words: 2.6K


Shafi na saba'in da biyu

Chapter 73
Shafi na saba'in da biyu

72
. Awa daya da wasu 'yan tsirarin mintuna suka sauka a garin lagos din,sun sauka
cikin yanayi na lullumi harda ma tsarabar yayyafi,tunda suka sauka har zuwa cikin
motar hannayensu na sarqafe da juna,tana cikin jikin lamin din wanda hakan yake
sake kunnashi,a hakan ya dinga nuna mata wurare,sun wurwuce unguwanni da dama,duk
inda suka wuce din kuma sai yayi mata bayanin wajen,ta bude idanu kuwa tana kallon
bigiren da bata sanshi ba,xuciyarta cike da mamakin yadda lamin din yasan Lagos har
haka.

A hankali suka fada wata unguwa,unguwace mai kyau dai dai gwargwado da kuma
tsari,babu cinkoso babu kuma yawaitar jama'a,gidajenta moderate ne masu ban
sha'awa,hakanan birji ne a tsakiyar layin,har suka qarasa qofar wani dan
madaidaicin plate house mai dauke da qaramin gate.

Lamin dinne ya fara fita ya bude qofar gidan da maqullin da drivern ya


bashi,sannan ya dawo ya bude mata murfin motar ta fito,yana riqe da hannun nata dai
ya tura qofar gidan suka shige.

'yar madaidaiciyar haraba zaka fara tararwa wadda bata wuce shan iska ba,don ta
yiwa mota kadan,saidai qawace take da shuke shuke da kuma marble tiles masu kyau da
daukan idanu,da gani kasan baa jima da kammala ginin gidan ba,qaramin balcony ke
kallonka,wanda a ciki qofar parlor ne,kana buda qofar falon zaka samu madaidaicin
falo da akayi masifar qawatashi kamar ba gobe,a cikinsa akwai qofar kitchen,dining
area mai dauke da dining mai kujeru hudu,sai bedrooms guda biyu.

"Zauna ina zuwa" ya fada yana juyawa zuwa waje,a nutse iman ta zauna saman
kujerun falon masu azabar kyau,tana sake kallon gidan,ya burgeta qwarai da
gaske,komai nashi bai cika yawa ba kamar yadda baiyi qaranci ba.

Tana nan zaune ya shigo da jakarsu,sannan ya duba agogo

"Akwai sauran lokaci,me ya kamata yanzu muyi?,gidan babu komai a cikinsa,zanje na


samar mana kayan amfani" rau rau tayi da idanunta,sabida jin cewa zai fita ya barta
a baqon wajen dako minti goma cikakke batayi a cikinsa ba,takowa yayi gabanta

"Karki damu, you are safe,zan rufeki ta waje,idan na dawo zan bude da kaina,ga
bedrooms nan ki zaba wanda nayi miki" ya sunkuya a tausashe yayi kissing forehead
dinta,ya danyi waving mata hannyensa sannan ya fita,ta rakashi da addu'a yana amsa
mata.

Duk da atsorace take amma sai dafa dudduba kitchen da dakunan,komai lafiya lau
kamar dama can ansan da zuwansu,sai kawai ta janyo jakankuna biyun daya shigo dasu
ta bude,ta fara fidda musu kayansu tana jerawa a daya daga cikin bedroom din data
zaba,bayan ta gama jera nata a dayan shima ta fara shirya masa nashi a daya
dakin,duk kayansa da zata daga sai wani qamshi ya ziyarci hancinta,kamar dama ca
kayan da turare aka qirqiresu.

Awa daya da rabi aikin ya dauketa,tana fitowa daga bedroom din yana buda qofar
falon,idanunshi a kanta,sai yayi mata nuni data koma ciki,shi da wani yaro ne,tana
jinsu suna shiga da kayan store har suka gama ya sallameshi sannan ya cimmata a
daki,tana tsaye bakin window tana kallon kyakkyawar harabar gidan.

Ta baya ya rungumota yana axa fuskarsa saman kafadarta,sannan ya zagayo da


hannayensa saman shafaffen cikinta yayi mata qawanya

"Ina fata gidan yayi miki?" Kai ta gyada a kunyace

"Anan nake fata zamu axa harsashin tubalin ginin kyakkyawar rayuwar auratayya mai
inganci....kin shirya?" Kan ta sake gyada masa murmushi yana kubce mata

"Good" ya fada cikin jin dadi da kuma wani irin shauqi

"Muje ki duba kayan kiga abinda babu a ciki" tana duba kayan tana mamakin yadda
yasan kayan amfanin gida haka,kusan shi ya dinga jera kayan a duk inda suka
dace,ita din 'yar tayi kawai ta zama,a hakan ma dai a takure take,yana sane sai ya
taba wani wajen ko wani sashen daga gareta,amma sai ya narke ya hade hannayensa
waje daya yace

"Am sorry" wani abun ta rasa me zatayi,wani kuma kunya ta daureta gaba daya,har
suka gama,zuwa sannan lokacin sallar magariba ya shiga,ya buqaci taje tayi wanka
tazo suyi sallah.

Ruwa me zafi ta hada saboda yadda takejin dan sanyi sanyi a garin saboda
yayyafin da aketa yi tun zuwansu,taji dadin dumin ruwan hakan yasa ta jima a
bandakin ba tare da ta ankara ba,ta hade da alwala sannan ta fito.

ta dauki minti kusan hudu tana goge lemar jikinta,sannan ta daga kanta da
nufin qarasawa bakin madubi ta samu mai ta shafawa jikinta,saidai wanda ta gani
zaune saman madubin harde da hannayensa ya zuba mata idanu yayi matuqar razanata.

Lameen ne,yayi bala'in kyau cikin wani lallausan yadi gray color kamar ba dare
ba,baqar hula ce a kansa,kamar yadda qafarsa ke sanye da baqaqen takalma mai
budadden sama,fadin irin kyan da yayi ma bata bakine,sexy eyes dinsa a bude tarwai
a kanta,da hanzari ta soma komawa da baya da nufin komawa toilet,saidai ina,yana
saukowa daga saman madubin,taku uku ya cimmata,batasan ta kaucewa qofar toilet din
ba sai data ji ta dunguri bango,cak ta tsaya,ya riga ya cimmata,duk da cewa akwai
yar tazara a tsakaninsu amma bata da shaawar motsawa,saboda yadda idanunsa ke yawo
a jikinta tun daga sama zuwa qasa,ta tabbatar ko yaya ta motsa akwai matsala,ta
gwammaci ci gaba da tsaiwa a haka.

Ci gaba yayi da sauke idanunsa kowanne sashe na jikinsa da idanunsa zasu iya
kaiwa,karo na farko tsahon rayuwarsu daya taba ganinta cikin yanayi makamancin
haka,kasala ta soma saukar masa tare da wani irin shauqi dake fusgarsa,shuqin da
bai taba jin makamancinsa ba,gefe guda kuma yana karantar irin rudewar da tayi,abun
sai ya bashi wani nau'i na nishadi sa dariya,baisan me yasa taji tsoron ganinsa
ba,yanason sake ganin tsoronta irin haka muraran,ko zamanin quruciya idan iman din
ta rude fuskarta kan masa kyau qwarai,don haka ya qara kusancin dake tsakaninsu,har
sai daya zamana babu wani sauran space ko na taku daya daya rage a tsakaninsu.

A hankali ya sanya hannunsa saman towel din dake tattare a qirjinta,


intentionally yayi hakan da niyyar tunzura tsoronta,amma sai yaji ashe abun ya
girmimi tunaninsa,cikin rashin sani ya shafi qirjinta,abinda yasa ta sake razana,ta
kama towel din ta riqe tam,tanason ta kalleshi ta roqeshi ya bari amma ta
kasa,akwai girma a faruwar lamari irin wannan,ya lameen da take matuqar girmamawa
da yi masa kallon yaya a wajenta,koda bassam ba zata iya tuna rana daya data taba
bayyana tsiraicinta a gabansa ba,yo inama ta ganshi?.

Sulalewa ta samu tayi,tana kaiwa qasa saita cure waje daya,a boye ya saki
murmushi,ya taka da baya ya dauko.kayan da yaga ta ajjiye saman gadon,da alama su
zata saka ya ajjiye mata a gabanta,dai dai lokacin da akayi knocking qofar falo,sai
ya juya zuwa bakin qofar yana cewa

"Ki saka kayanki" ya buda qofar ya fita,abinda ya bata damar miqewa da hanzari ta
koma toilet zuciyarta na bugawa,komai zai fara tsakaninta da ya lameen daga
tsammanin mafarki zuwa gaskiya,tana ji a jikinta tabbas zuwa yanzu komai gaske
ne,ya kuma gama tabbata.

Da takeaway ya dawo a hannunsa na abinci idonsa na dubanta kamar zata bace masa

"You look so cute my queen" ya fada ta hanyar motsa labbansa kawai,hakan ya sanya
furucin ya fita a hankali. Bandaki ya shiga ya sabunta alwalarsa ya dawo sukayi
sallah,sannan ya gabatar musu da abincin sukaci a mazubi daya kamar yadda ya sabar
musu.

"Ayimin afuwa,fitace ta kamani,akwai saqo da zan karba,banajin zan fita har nan da
one week,shi yasa dole a daren nan na fita na karba saqon,sako hijabinki ki
rakani,i promise you ba zamu dade ba" itakam dadin hakan taji,sai ta koma ciki,ta
laluba kayanta ta samu hijab,ta zura hade da plate takalmi ta fito.

Tunda ta fara takowa ya zuba mata idanu,hannunsa zube a aljihunsa yana qare
mata kallo,komai ta saka kyau yake mata,komai ta raba da jikinta sai ya haska ta,ya
Allah......" Ya fadi yana lumshe idanunsa,kana ya bude mata qirjinsa ta hanyar wara
hannayensa yayi welcoming nata kafin su wuce tana rabe da kafadarsa.

A qofar gidan suka samu mota yana jiransu suka shiga seat din baya ita dashi
manne da juna,ko yanzun ma bayani tare da nunnuna mata gurare yaketayi,lallai lagos
babban garine da aka ci gaba,har suka je suka dawo,duk da a mota ya barta ya karba
saqon amma taji dadin fitar.

Koda suka dawo din shirin barci kawai sukayi,dakin ya dauki wani duhu mai
cakude da dim light mai kyau,yadda gidan da garin ya dauki shuru haka dakin,tana a
cikin jikinsa idanunsa a lumshe,yanata qoqarin danne zuciyarsa saboda ya bata damar
hutawa a daren yau,yana jin dumin numfashinta cikin jikinsa ya gyara mata kwanciya
sosai,da qyar ya samu bacci ya daukeshi.

************Washegari garin a lullube da hadari suka tashi,weather din da ya haifar


da wani yanayi me dadi a jiki da zuciya,yanayin kuma ya dace da sabbin masoya
irinsu.

Tun daga safiyar ya fara bude mata aiki,muraran ya fara bayyana mata waye
lameen da irin rayuwar da yake sha'awar yi da iyalinsa,tare suka hada
breakfast,suka gyara wajen,wajen wanka ta shige toilet kafin ta gama rufewa ya
mamayeta,zatayi magana sai tsintar kanta tayi male male cikin bathtub,bata gama
wannan alhinin ba yasa hannu guda ya zare towel din da yayi saura a jikinta,ta
qanqame waje daya,sai yayi relax cikin ruwan yana qarewa fuskarta kallo,jikinsa ya
saki gaba daya,zuciyarsa na gaya masa ya aikata kawai,daren da yake tunani bazai
iya kaiwa ba,saidai akwai sauran abubuwa da yakeso ta fuskanta daga wajensa kafin
sannan,idanunsa suka sauka ga duk wata siffa da baiwa ta jikinta da Allah yayi mata
ta cikin ruwan da yake garai garai,tsigar jikinsa ta zuba,yaji kamar numfashinsa
zai wuce,cikin ransa gana dayanta Allah da idanuwansa basu taba kaiwa ga jikin wata
'ya mace kamar haka ba,sai a yau daya samu halalinsa

"Imaaaannnn" ya ambaci sunanta da wata murya me nauyi,a shagwabe tana shirin sakin
kuka ta amsa masa,abunda ya sake tunzurashi kenan,ya zame kadan cikin ruwan,ya
kamota zuwa cikin jikinsa sosai ya dorata saman ruwan cikinsa,abinda yaso ta wuce
da numfashinsu gaba daya shi da ita,saboda yadda kowanne sashe na jikinsu ya hadu
dana dan uwansa,wata ajiyar zuciya me hade da sheshsheqa ya saki kamar wanda
numfashinsa ke shirin kufce masa,wani shock mai bala'in qarfi ya ziyarci kowanne
sashe na jikin iman din,dukka wata juriya da yakejin yana da ita ta fara
kwaranyewa,jikinsa ya fara daukan zafi da chargy,sai ya kamo fuskarta cikin tafuka
hannayensa,kiran sunanta yakeson ya sakeyi amma ya kasa,sai kawai ya hade bakunansu
waje guda ya kai tsaye ya laluba harshenta ya sanya cikin bakinsa.
Wani zazzafan kiss da ya sake iza wutar da suke ciki ya fara aika mata,cikin
salon na ar qwarewa da sanin sirrikan rura wutar soyyaya cikin zuciyar masoyi,salo
mai tsafta da kuma tafi da hankali,tuni iman din ta narke masa itama,hakan ya bashi
damar sakin fuskarta ya maida hannayensa zuwa wani muhallin na daban cikin sassan
jikinta,lokaci guda gaba dayansu suka rude suka kuma fita a hayyacinsu shi da
ita,gaba daya ji yake bathtub din yayi masa kadan,sannan he's not comfortable,don
haka ya lallaba cikin mutuwar jiki ya dauki iman din cak suka baro toilet din.

Kasa qarasawa gadon sukayi dukansu,suka zube bakin gadon yana ci gaba da
charger mata kwanya gaba daya,komai yayi zafi ya kuma kai geji,yakai iya limit din
da baya buqatar komai sai kasancewa da ita,duk wani guri dake tsole masa idanu sai
da hannunsa yakai,ya gusar da ishirwarsa ya kuma morema wajen son ransa,duk da
cikin fitar hayyaci yake amma ya lura da wasu abubuwa tattare da uman din,wadanda
suke alamta masa kamar batasan kowa ba cikin rayuwarta,kamar komai bai canza ba
daga jikinta,amma bashi da tabbaci saboda yana ganin mawuyacin abune hakan ta
kasance,sake hobbasan mai data saman gadon sosai yayi kana yayi mata rumfa,yana ci
gaba da aike mata zafafan saqonni masu gusar da hankali tare da neman hanyar da zai
maidata mallakinsa ta har abada,sai a sanna iman ta farga.....sai a sannan ta gane
cewa lallai game din ya canza salo......sa a sannan tasan komai yana shirin canzawa
ne,hankalinta yaso dawowa jikinta,tasa hannu da niyyar dakatar dashi,saidai shima
nasa hannun yasa yakauda nata,gami da matseshi sosai cikin nasa tafukan hannayen
yana girgiza mata kai alamun a'a,gaba daya kamanninsa sun sauya,farar fuskarsa tayi
jazur kamar yadda tata tayi

"Bismillah,Allahumma jannib nash shaidan,w jannibash shaidana ma razaqtana" addu'ar


da fiyayyen halitta ya koyarwa ma'aurata kenan yayin da zasu kasance da
iyalinsu,saboda koda ubangiji ya qaddara samun qaruwa shaidan bazai iya cutar da
wannan abunda aka samun ba,addu'ar data sanya iman fashewa da kuka,kukan kuma daya
fita lokaci guda da azabar data fara ratsata.

Daga ita har lameen babu wanda yake tantance halin da dan uwansa ke
ciki,azabar daga dinga ratsata da kukan da.takeyi da kuma kalaman neman afuwa da
suke fita a bakinta kawai take iya tantancewa,yayin da lameen din kuma ya rasa
cikin wacce duniya yake,sama sama kunnuwansa suke jiye masa kukan iman din,amma ya
gaza controlling kansa,burinsa kawai ya cimma gaci,gacin da ya daukeshi wasu
mintuna kafin yakai inda yakeson kaiwan,ya saki wani sauti mai qarfi yana matse
iman gammm a jikinsa kamar zai tsagata gida biyu,kana yayi wani irin laushi gumi na
jiqa ilahirin jikinsa kamar wanda aka yiwa wanka da ruwa.

Zare jikinsa yayi yakoma gefan iman din,yanajin yadda bugun zuciyarsa har
yanzu bai daidaita ba,a tausashe yaja iman din cikin jikinsa sosai

"Subhana man khalaqal khalqa wa'ahsahum adad,subhana man laisa lahu sharikun fil
mulk,subhanal lahil azim...subhana man laisa ka mislihi shai'un" kalama daya dinga
fada kenan murya can qasa,wasu hawaye na sauka ta gefan idanunsa,ya tadda abinda
bai taba tunanin zai sameshi ba tattare da iman din,lallai wannan hikima da baiwa
ce daga ubangiji yayi masa ita,yasa bakinsa a tausashe ya ajjiye mata kiss dake
dauke da nannauyan saqo a saman goshinta,sannan yasa hannunsa yana tattare mata
gashin fuskarta,fuskarta ta fito sosai,gaba daya tayi jazur,idanuwanta dukka sun
tasa alamun kukan datayi masa ba dan kadan bane,take tausayinta ya kamashi,ya soma
tuna yadda take neman agajin inna da malam,yasa yatsansa guda daya yana goge
damshin hawayen dake kan fuskarta

"Iman" ya kira sunanta a hankali cikin rada,maimakon ta bude idanun nata,sai yaga
ta sake runtsesu gam.

Dumin da yaji daga gefen cinyoyinsa yasa yadan ja da baya kadan yana
dubawa,jini ne ta wajen daya bata inda suke kwancen,abinda yadan tsoratashi kenan

"Subhanallah" ya fada yana kwantar da iman din tare da janyewa yana duban wajen,sai
ya suturta jikinsa sannan ya dawo wajen iman din

"Iman" ya sake kiranta,saidai bata amsa masa ba kamar wancan karon,hakan yasa ya
sauko daga saman gadon,lallai dole yasan yayi aikin lallashi,don gaba daya taja
bargon daya rufe mata jikinta dashi ta lulluba har saman kanta,zagayowa yayi daga
side din data maida fuskarta,ya durqusa gaban gadon

"Iman.....am sorry kiyi haquri don Allah" duk da yanayin azabar da take ciki,da
kuma boyayyen kukan da takeyi ta cikin bargon sai dataji kalmar tayi mata girma,yaa
lameen da bata haquri?

"Don Allah iman..... please talk to me mana" nan ma kasa bashi amsa tayi

"Ba zaki ce komai ba?" Kai kawai ta girgiza,duk da ciwon da take ji a jikinta,amma
babban abinda yafi damunta ayanzu baisan ba zataya iya sake hada ido dashi bane har
abada,ta yaya zata iya sake kallon yaa lameen din?,su hada ido dashi har kuma ma
suyi magana ko suci gaba da mu'amala.

"Me kakeso?" Tafada da wata dasashiyar muryar dako ba'a gaya maka ba kasan tasha
kuka yadda ya kamata

"Ki tashi please na duba barnar da nayi hankalina sai yafi kwanciya,kema kuma ki
tashi ki gyara jikinki" tanajin ko sama da qasa zasu hadu ba zata miqe a gabansa ba

"Kaje zan tashi" ta amsa masa tana sake cukuikuye kanta,sam maganar bata kwanta
masa ba,ya tabbatar mawuyacine ta iya tashin da kanta

"Zaki iya?" Ya fada damuwa na bayyanuwa saman kanta

"Eh" ta amsa masa,dan jim yayi kafin yace

"Is ok" sannan ya miqe daga tsugunnon da yayi,saidai maimakon ya fita saiya nufi
qofar toilet da suka barta a wangale dazun,yadan turota kadan ya labe daga bayanta.

Minti kusan hudu ta bayar,sai data daina jin motsinsa sannan ta yaye bargon,a
hankali ta miqe ta zauna tana ciza lebe,a matsayinta name karatun jinya tasan
ciwuka taji a gurin ba shakka,saita matso da jikinta gaba a hankali da niyyar
tashi.

Wata qara ta saki ta koma ta zauna sanda tayi yunqurin tashin,ya saki murmushi
yana fitowa daga maboyarsa,duka saita rude,tana shirin komawa ta kwanta ya
qaraso,daukar cak yayi mata tana boye kanta cikin jikinsa,bai damu ko kula da
wannan ba ya wuce toilet da ita.

Next Chapter

Leave a comment

Post

Comments

112201018644657456668
Yaa rabb kabawa du wata diya mace musulma damar kai mutuncinta dakin auranta

2 hours ago


dadaummi1
❤️❤️❤️

3 hours ago

Contact Us
Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742
Email: [email protected]

Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram


Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io

"
https://arewabooks.com/chapter?id=62d6a0a47fc1109aa6133b68#:~:text=Chapter
%2073-,Shafi%20na%20saba%27in%20da%20biyu,ko%20kula%20da%20wannan%20ba%20ya%20wuce
%20toilet%20da%20ita.,-Next%20Chapter
[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: 73

Wata nutsuwa ce ke sauka a zukatan kowannensu sanda suka kammala sallar


azahar,ameen din yaja musu dogayen addu'o'i wanda suke dauke da kalaman yabo da
jinjina ga ubangiji da kuma nema tabarrakinsa kan zamantakewarsu,a nutse ya shafa
addu'ar sannan ya juyo inda iman ke zaune,kanta a qasa,tana jin nauyi ko yaya ta
motsa,idan ta tuna abubuwan da suka faru tun daga zamantowarsu abu daya da lameen
da kuma yadda ya tusata a bandaki ya gasata sai taji inama qasa zata tsage ta shige
ciki.

Dab da ita ya sake matsowa,ya kama goshinta yayi mata addu'ar nan da annabi
ya umarci kowanne ango ya kama goshin amaryarsa yayi mata

"Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi,wa'azubika min


sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi" ya zare hannunsa daga kan nata,maimakon ya
sauke hannun qasa sai ya kamo nata hannayen duka,ya riqesu a tausashe yana kallon
tsakiyar qwayar idanunta bayan ya matso sosai dab da ita,har gwiwoyinsu yana gogar
juna,cikin wata murya dake cike da taushi zallar shauqi da qauna ya soma magana

"Kin bani komai,kin kuma gama min komai hajar.....ban mallaki abinda zan iya saka
miki dashi ba,saidai ina fatan na zamo mafi alkhairin miji,kuma miji na gari da
babu tamkarsa,babu sauran abinda ya rage da zan sakawa inna da malam illa addu'ar
samun aljanna madaukakiya....sun ingantamin rayuwata,sun maidani cikakken
mutum,basu barni a haka ba sai da suka haifamin mata gangariya,wadda zata zamo waje
hutu da sanyin idaniya a gareni,duk kalmar da zan fada miki kan irin qaunar dake
cikin raina....inajin kamar na ragewa soyayyarki marta bane,fatana ki rayu dani
kamar yadda na alqawartawa kaina duk wuya duk dadi zan rayu dake,ki rufemin sirrina
iman......banso ko sau daya tak ki kai qarana wajen inna ko malam.....banaso suji
shakka ko susa a kaina,ko meye nayi miki ki zaunar dani ki gayan,idan nine keda
laifi in sha Allah zan dauki laifina zan kuma nema afuwarki na gyara.....idan kece
kuma zan nusar dake cikin salon daya dace wanda zai gamsar dake da kuma zuciyarki
da izinin Allah... and lastly......iman" Sai ya sauke numfashi yana sake matsa
hannuwanta

"Na'am" ta amsa masa tana sake gujewa kallonsa

"Kalli qwayar idanuna" sosai taji saukar maganar tasa da nauyi a kanta,wannan
umarin nasa yayi mata nauyi da yawa,wai me yasa yake acting like babu ma wani abu
da yafaru?.
"I said look into my eyes" a hankali kamar mai ciwon wuya ta daga kanta zuwa idanun
nasa kamar yadda ya buqata,take kuwa magnet din dake ciki ya jata sosai

"Ni mutum ne dake qaunar caring,inason matata ta soni sosai,kada ta raba kulawa ko
soyayyar da takemin da kowa....koda yaran da zamu haifa ne,ki bani soyayyarki ni
kuma nayi zan basu tawa soyayyar,nasan zata wadatar dasu in sha Allah.....kinyi
alqawari?" Duk da yadda ya aza mata nauyin idanu dana maganarsa,amma haka ta bashi
tabbacin da yakeson ji

"Ina fata ubangiji ya qadarta samun rabu a wannan haduwa tamu" ya fada hannayensa
asama,maganar data sanyata qarasa dunqulewa waje daya cike da kunya,ya miqe yana
dariya ya dagata ya rungumeta cikin dariyarsa yana ci gaba da murmushi,yau dai iman
baki ya mutu murus.

Wunin ranar wani wuni ne daya ajjiye dimbin tarihi cikin rayuwar aurensu,ya
koma sake kafa wata sassanyar soyayya a zukatansu,ta wani bangaren kuma soyayya me
zafi,ta sake sanin abubuwa masu yawa game da ameen din,tarihin rayuwarsa na zahiri
tun yana qaraminsa almajirtarsa da fadowarsa hannun malam,hakanan itama ya bata
dama a sanda kanta yake kwance saman cinyarsa ta bashi labarin abubuwa da dama da
bai sani ba,ciki harda zaman aurenta da bassam.

Shuru yayi abun yana tabashi,hannunsa saman lallausan gashinta yana wasa
dashi,komai Allah ke tsarashi ya kuma kawoshi a sanda ya dace,yana can cikin ciwo
da zafin soyayya.....ubangijinsa kuma ya dubeshi yana ta yi masa tanadi irin wanda
ya dace dashi

"I suffered a lot iman......ban zaci soyayyarki zata barni na rayu ba,amma
alhamdulillah,na godewa Allah" shuru tayi tana jinsa,murmushi kwance kan
fuskarta,taji tarin kalamai daga bakin lameen wadanda bata tabajin masu zaqi da
gardinsu ba,taji irin girman matsayin da take dashi a wajen lameen din,wanda ko
kusa bata taba kawoshi kusa cikin ranta kan tana dashi ba,tabbas inda ace ana buda
zuciyad mutum aga meke ciki,da bata gujewa lameen din ba,saidai kuma bawa baya taba
tsallakewa rubutacciyar qaddararsa.

Washegari tadanji dama dama a jikinta,saboda tabs din data rubuta lameen
din ya samo mata su,hakanan shi ya dinha dawainiyar gasata da kanshi,duk da yadda
kunya ke dawainiya da ita amma ya murje idanunsa fes,tana kukan shagwaba yana
tayata,haka suka dinga yi akai akai,har sai data narke masa da gasken ta gaji.

A hankali take takowa zuwa falon din a daren washegari,tayi masifar kyau
cikin wata straight gown data fidda shape dinta sosai,idanunsa na akanta sanda take
iskoshi,wani abu daketa motsa masa ya sake motsawa cikin jikinsa,sai ya miqa mata
hannu ya mata nuni data taho,bata taba lokacin ba kuwa ta taho ya kuma yi mata
kyakkyawan mazauni saman cinyarsa,ya kuma bude qirjinsa ya lullubeta a ciki.

Cikin wuyanta ya cusa fuskarsa yana shinshinarta,launin idanunsa da kuma


yanayin saukar numfashinsa yana sauyawa,tun daga wuyanta ya gangaro kunnenta,ya
kuma juyo da ita sosai ya cusa kansa tsakanin qirjinta numfashinsa na qara gudu
wajen fita da dawowa,a hankali ya soma yawo da hannayensa cikin jikinta,ya fara
aike mata sa saqonni,abunda ya rudata ta riqe hannayensa,cikin rudu take girgiza
masa kai

"Yaa lameenn...."
"Anty imann......." Ya tari numfashinta shima da sauri kafin ta qarasa fadin abinda
zata fada din,yadda taga ya birkice yasa ta kwantar da kanta sama kafadarsa kawai
cike da fargaba,tasan laifi da zunubin yiwa miji musu ba tun yau ba,bugun zuciyarta
na qaruwa,tana saddaqarwa cewa lallai tata ta qare,har yanzu akwai sauran jinya
tattare da ita,hakanan bata manta wuyar da tasha a hannunsa ba.
Sosai yake ya mutsata kamar wani mayunwacin zaki,sai wani numfashi da
yake fitarwa kamar gurnani,ita kanta sai daya rudata sosai,zuwa wasu mintuna ya
qanqameta kamar zai tsaga cinyarsa ya sakata,sai kuma ya zameta daga saman cinyar
tasa ya zaunar da ita yana cewa

"Ina zuwa" a hankali ya taka ya shige daya daga cikin dakunan,da kallo ta bishi har
ya bacewa ganinta,saita maida idanunta ta lumshe,ita kanta dukka jikinta ya
amsa,duk da cewa a tsorace take da wahalar da tasha a jiya.

Kusan mintuna ashiri sannan ya dawo,da alamu wanka yayi,idanuwanshi a


kanta,bai tsaya ko ina ba sai dab da ita,yasa hannu ya shafi saman kanta ya zarce
qirjinta,sannan ya maida kansa saman kafadarta ya kwantar,kamar sabon marayan daya
rasa mahaifansa

"Queen,inajin sai kinyi haquri da yaa lameen dinki.....bazan boye miki ba,tun ba
yau ba nasan ina cikin nau'in mutane mabuqata,abinda ya dinga wahalar dani,saidai
na godewa Allah daya dinga bani kariya,har kawo yanzu da ya rabautani da
halaliyata" sarqafe hannayensu yayi waje guda

"Kinyi alqawari zaki kula dani....wannan ma zai shiga ciki?" Cike da qwarin gwiwa
ga gyada kai
"I will do my best in sha Allah" cikin jikinsa ya sanyata tana mata godiya har taji
nauyin hakan.

A daren ya sake koyar da ita wasu sabbain darussa,qaramae akwati guda na


wasu irin sexy dresses ya ajjiye,yana daga kwance saman gadon tana saka masa yana
gani yana zabar wadanda yake so,wasu idan ta sakasu kamar tayi yaya don kunya,sau
tari idan ta gwada wasu duqewa take a wajen ta kasa miqewa,wasu baya ne a
kwashe,wasu tsakiyar ciki zuwa cinyoyi,komai a bayyane,bata taba sanin ya lameen
din cikakken dan duniya bane sai sannan,ashe kallon kitse akewa rogo,fitina ce fal
cikinsa a yanzu yake sauke mata ita.....ni kuwa nace banga laifinsa ba,illar dama
kaje baga halalinka na,amma idan halili ne to falillahil hamdu.

Daga qarshe kuwa kasa ci gaba da gwajin tayi,gaba daya kunya ta durqusar da
ita,da mabayyanin murmushinsa yataso ya dagata cak dama ya raina daukanta tuntuni

"Idan ina da hali zance kiyimin yawo cikin gidana daga ke sai fatar jikinki,ke
kadai Allah ya halastamin iman,kuma dake daya nakeso na rayu" dole dai duk yadda
taso masa rowa haka ta bada kai bori ya hau,duk da yayi mata fami qwarai,amma da
sauqi akan na jiyan,sannan a yau din tadan dauki haske,ta kuma fahimci wasu
abubuwan.

Washegari wajen sha daya na safe tana cikin jikinsa,suna zaune saman
kujera yayi relaxing bayansa da makarin kujerar,santala santalan qafafunsa a miqe
saman dan table,iman din sanye da wata 'yar fingilar shirt short sleeve,fara ce qal
kuma robber,hakan ya sanya ta dameta dai dai size na jikinta,ta kuma fidda kowanne
shape nata,wandon jikinta shima haka yake,iyakae tsahonsa gwiwa,ta gyara gashinta
cikin farin band jelar ta sauka kafadarta ta hagu,tuntuni ta sani white is favorite
color na ameen,don ko a sannan din shima kayan jikinsa farare ne

"Matso ki gani"yayi maganar yana rage sautin tv din dake aiki,kana ya jawo tab
dinsa wadda a yanzu da ita yake amfani,tunda ya kashe wayoyinsa,ta maqale sosai
kuwa cikin jikinsa tana kallon fuskar tab din daya dauko.

Fasa bude tab din yayi,ya waiwayo ya dubeta,dai dai sanda itama ta daga
kanta suka hada idanu

"Fisabilillahi haka akeyi,yanzun kuma nace zan dana asamin kuka?,bayan tun daxu
fuska kawai nakeyi?" Da sauri ta dagashi tana turo baki

"To ba kaine kace nazo na gani ba" ta fada a shagwabe tana karya wuya,abinda ya
tuna masa da iman din zamm dinta,murmushi ya qwace masa,ya kuma tarota sanda take
qoqarin sauka a jikinsa

"Zo mana,zo kiji 'yar qanwata,zo mu sasanta" saiya miqe ya zauna sosai bayan ya
ajjiye tab din daga gefansa

"Muyi ban gishiri na baka manda mana,kidan sanmin ko babu yawa kinji" yayi maganar
idanunsa cikin nata,launin idanun nasa suna canzawa,da alama da gaske kenan
yake,abinda ya tsorata iman ta fiddo idanu

"Yaa....."
"Shshshsh" yayi maganar yana dora yatsansa saman lebansa

"Babu wani yaya....na soke wannan sunan,kiji dani imani ta" kuka ta sakar masa,at
least dai yau ai ta huta,ta kuma sanya ran zata huta din,saidai yau dinma tana ji
tana gani ya mata wayo ya karba abunsa,tana jikinsa tana masa kuka wanda ke cakude
da shagwaba,shi kuwa yana aikin lallashi,hannunsa saman kanta

"Kiyi haquri....kullum sake ninka min qaunarki da sha'awarki ake,babu abinda ke


raguwa,keta dabance iman,wallahi da na zauna da wata tabbas dana fada cikin mazan
da Allah zai tuhuma,banajin zan iya hadaki da wata mace na kuma yi muku
adalci,sonki a jina na yake,bazai taba gushewa ba...." Duk wata tabararta haka ya
dauketa sai toilet,tare sukayi wanka sannan suka dawo ya dauko tab din ya fara nuna
mata abinda zai nuna mata daxun.

Wasu selective places ne best for honeymoon cikin garin lagos,da pictures
dinsu da bayanansu,ya bata daman zaban guri har guda hudu da zasuje,biyu a ciki
zasuyi sati daddaya a can,sauran kuma kwana uku uku ne.

Sanda taketa murna binta kawai yake da kallo,farincikinta kadai ya


wadatar dashi,inda yana da wani abun da zai sata farinciki sama da haka daya
bata,yana jin iman din takai masa ko ina cikin rayuwarsa,hatta fitar numfashinsa ya
tabbatar yana fita ne da so da qaunar iman din.

Cikin kwanaki da kuma wuraren da suka zaba din zasuje sun gudanar da
gagarumun honeymoon wanda dukkaninsu basa jin zai gushe cikin tarihin
rayuwarsu,wata wutar soyayya ce sosai ta kunnu cikin zukatansu da kuma ruhinsu,sun
sake dinkewa sun zama abu daya,ta sake sanin waye lamin.....shima ya sake sanin
wace iman a badininta,tayi kuka aboye a bayan idanunsa da nadamar gudunsa data
tabayi a cikin rayuwarta,tabbas inda tana da qarfin ikon maida lokaci baya ta shafe
wancan abun data aikata,ashe wata tarin qoramar zumar soyayya ce take jiranta ta
debi kashi ta watsa mata cikin rashin sani da wauta,dukka wani caring da soyayya da
take mafarkin samu cikin rayuwarta ta samu sama da haka daga wajen ameen din,ashe
ba kudi bane jin dadi?,ashe ba kyau bane soyayya?,ashe ba kudi bane qauna zaman
lafiya da kwanciyar hankali?,da gaske duk sanda bawa ya bijirewa zabin Allah,sai
Allahn ya barshi da zabinsa yaje yayita wahala,ta godewa Allah daya zabar mata
tsayayyun iyaye kuma nagartattu.

Fadin yadda iman ta sake mamaye rayuwarsa ma wannan bata bakine,a kullum
ya saka goshinsa a qasa zai roqa musu dawwamammen zaman lafiya da zuria
dayyiba,burinsa a yanzu a rayuwa shine ya rayu da iman din har abada,ta kuma tara
masa iyali masu yawa,mutum ne shi maison yara qwarai da gaske,kuma ita kanta iman
din ta sani.

Suna tsaka da honeymoon din issue na bude kamfanin saida spare parts na
motocin da yake shirin yi ya taso, issue din ya taso gadan gadan,dole suka dawo
gida,dama kwanaki biyu ne suka rage masa.

A lokacinne suka sake gasgatawa kansu daya bazai iya rayuwa ba saida
dayan,fitar da yake da safe ya dawo da yammaci liqis dukkansu shi da ita galabaita
suke da kewar juna,dole ba don ya shirya ba ya siya mata layin waya,idan ya fita
suna maqale da juna ta waya,duk da haka wataran bai gamsar dashi sai ya yanke
abinda yakeyi yazo ya ganta sannan zai koma,aikin me wahala da cin rai,saboda su
sona son kafin ya samu license yabar kamfanin a nan Lagos,shi kuma ba wanna ya
tsara ba,yanaso kamfanin ya zama a arewa cikin garin kano,bazai bar wannan damar da
kuma alfanun da dubba matasa zasu samu na samun aiki ya qare a can ba,bayan ga
jama'arsa suna da buqata,ya kashe gida ya raya jeji,yasha wahala dasu sosai kafin
ya samu komai ya dai daita,aka kuma sahale masan yayi a gida kanon dabo,cikin
qanqanin lokaci komai ya kammala cike da nasara,ya kuma siya dukka wasu kaya da
za'a buqata ya aikosu kano,a sannan ya shirya musu qarashen honeymoon dinsu,suka
raqashe da kyau,sannan suka fara shirin dawowa gida kuma,iman murna kamar tayi
me,kwanaki kadan suka rage su cika watanni uku a lagos din,tayi kewar inna,dole ta
haqura kiran gida duk da akwai waya a hannunta,saboda lamin yace yanaso su huce
sosai kafin su tunkaresu.

Wani irin kyau iman din tayi,ta sake fari ta cika tayi fresh da ita,duba
daya zakayi mata kasan ta samu dukkan wani jin dadi da kulawa da ya kamata diya
mace ta samu daga wajen miji,tabbas a yanzu a duniya babu abinda ta nema ta rasa,ko
yaushe tattalinta ameen din yake kamar yadda itama ta zage damtse tana tattalin
mijinta da dukan wani nau'in kulawa da tasan yanaso,zaiji dadi hakanan ransa zaiyi
fari.

Wata mahaukaciyar siyayya lameen din ya dinga mata kamar baisan ciwon
kudinsa ba,ta dade da sanin mutum ne shi mai kyauta da abun hannunsa,amma kuma sam
bashi da almubazzaranci ko barnatar da kudin a inda bashi da alfanu,anan ya hada
mata kayan lefe jimilla na kece raini,ya kuma qara mata da wasu kayayyakin da ita
kanta wani abun batasan yadda zatayi dashi ba,soyayyar gaskiya tayi.....babu abinda
ke raya soyayya irin kulawa nuna damuwa da masoyi a cikin kowanne irin hali.[7/19,
10:04 PM] Mummyn Yara: 74

Ana ya gobe zasu tafi ya fidda ita wani eatery mai tsada,yace ta zabi
dukka nau'in abinda takeso,bayan ya yiwa wani waiter na wajen magana kan su kawo
menu.

Tunda daya daga cikin ma'aikatan wajen mata ta doso wajen idanun lameen a
kanta

"Ya fa'alul lima yurid"ya furta can qasan zuciyarsa,idan idanunsa ba qarya sukayi
masa ba,ko kuma mantata yayi ba munira yake gani sanye da uniform din ma'aikatan
wajen,ta sauke abinci a wani table tana dosu nasu table din dauke da menu din a
hannunta,idanunsa ya dauke ya maida ga iman,sam bata lura da tahowarta ba,sai yaja
da baya ya miqe

"Ina zuwa queen" sai ya duqa yayi kissing nata forehead sannan ya taka zuwa wani
sashe nesa kadan dasu

"Good day madam" muryar munira ta fita cike da girmamawa tana dora menu din kan
table.

Da hanzari iman ta daga kai saboda jin muryar da ko a barci ta tashi zata
canki ta wacece,munira ce tsaye a gabanta,ta saje da ma'aikatan eatery din,idanu
dukkaninsu suka fitar,kowa yana mamakin ganin dan uwansa a wajen,kusan lokaci daya
suka ambaci sunan juna,sa munira ta fashe da kuka,abinda yasa iman tayi saurin
miqewa kenan ta rungumeta
"Muneera.....kece muneera?zauna" iman ta fada tana gyara mata kujera daya da
sauri,zare jikinta tayi da sauri

"Aah,zamana a nan wajen zai jawomin matsala idan har aka ganni....muje tacan
baya,akwai labarai iman" miqewa iman din tayi tabi muniran,tana qarewa muniran
kallo,gaba daya ta canza ta lalace,idan har kasan asali munira kanka tsaye zaka
fadi haka,a haka ma da sauran gayunta tunda babban gidan abinci ne,dole sai da
tsafta da kuma gayu,idan ba haka ba korarka ma zasuyi.

Hankalin lameen dake zaune can nesa dasu ya dauko sanda yaga tana jan iman
din zuwa can bayan wajen cin abincin,a nutse yake binsu a baya ba tare da sun sani
ba,sai dayaga waje suka canza,sannan ya koma can baya yana monitoring nasu ta inda
bazaiji sirrinsu ko abinda suke tattaunawa ba,bai matsa daga wajen ba saboda bawa
iman din tasa kariya.

"Ba'a yiwa Allah wayo iman,kuma duk sanda bawa ya matsa kan samun zabinsa ba zabin
Allah ba,Alla zai barshi da wayonsa ne yayita wahala,kwanaki da muka hadu dake nace
miki bikina za'ayi iman,akwai abinda ban gaya miki ba kafin zuwan bikin,nayi
saurayi mai dan datawar shekaru,yana bala'in sona,yana kuma da kudi yadda
nakeso,saidai matsalar bai cika sharadi biyu cikin sharadaina ba,na farko yana da
mata da yara,na biyu kuma yayimin shekaru da yawa,na dinga wulaqantashi qarshema
naci masa mutunci muka rabu,ba'a jima ba fallelen yaro ya fito min,ya hada komai
irin yadda nakeso,muka shiga soyayya gadan gadan,ya kuma shiga kashemin kudi babu
qaqqautawa,kullum mune yawon shopping,gidan cin abinci iri iri,cinema kullum muna a
hanya,duk abinda na buqata zan samu saidai idan ban buqata ba,hausawa sukace
kwadayi mabudin wahala da kuma wulaqanci,a irin wannan fice ficen da mukeyi dashi a
mota,kwatsam ranar mun dawo daga shipping,ya siyomin iphone 13promax,ina cike da
murna yace na rakashi gidansu zai karbo saqo wajen mummy dinsa saimu wuce zai siya
min wasu set na gold dana gani ana yayi,yace basai na shiga ba,nayi xamana a
mota,da murnata na amsa masa da to,muna zuwa ya bude ya shiga gidan,minti wajen
goma saiga wayarsa

"Na samu mummy bata jin dadi muneera,tana kwance zazzabi ya kada ita,daure ki shigo
kiyi mata sannu saimu wuce" ya fake da qaryar da ko baimin hidima irin haka ba
zanji nauyin cewa bazan shiga ga,da kwadayi da qaramar qwaqwalwa irin tawa na saka
kai cikin gidan,ashe tarko RUFA'I ya dana min,a ranar ya samu yayimin fyade na
rashin imani,yana gamawa saiga alhaji mando ya shigo mutumin da na wulaqanta

"Ba'a tabani a zauna lafiya,wannan shine sakamakon wulaqantani da kikayi,maga waye


zai dauki saura,idan kin rasa mai dauka ki dawo zan taimakeki na dauka a haka na
qarasa quruciyarki,nine naturo rufa'i,donshi ba kowa bane face yaron dakemin aikace
aikace,na bashi dukka kudin da xai isa yayimin wannan aikin,idan kin gama zaman
jinyar ki rufe gidan" haka suka tafi suka barni,bayan ya kwashe duk siyayyar da
yayimin dama a mota na barta tunda naga shiga kawai zamuyi mu fito.

Na shiga matuqar tashin hankali iman,saidai daga bisani sabbin qawayena da


nake tare dasu suka kwantarmin da hankali,suka kuma gayan kada na wani damu,akwai
dabaru da ake da magungunan da zaki koma gam kamar yarinya qarama,abinda ya kwantar
min da hankalina kenan,na bude sabon shafin rayuwata,naci gaba da zabe da kuma
laluben wanda zan aura,lokaci yanata quremin,damarmaki nata zuwa gabana amma
idanuna ya rufe,sai daga bisani irin taste dina yazo wato FAISAL.

Faisal yazomin da dukka wasu burika da sharudda nawa da nakeso ya cika,ya


cikasu fiye da kima,yaxomin da fuskar babansa wani shahararren attajiri ne da gaba
daya ba'a qasata Nigeria suke zaune ba,ya nunan gurare da kamfanoni masu tarin yawa
da sunan nasu ne,a gabana yazo da takardun wasu kamfanoni guda biyu ya sauke
sunansu ya maida sunana saboda son da yakemin,a ranar naji duk duniya nafi kowacce
mace sa'a a rayuwarta,tunda faisal ke zuwa bai taba zuwa da mamaicin mota kaya ko
waya ba,hakanan ya sanyani na zabi tsala tsalan motoci har biyu ya shaidan su xan
fara hawa daga randa na amsa sunan matarsa,fadi miki irin abubuwan da rufa'i
yazomin dasu iman kanki zai daure,don lefe ma cewa yayi ana daura aure zamu dage
dubai daga can mu zarce china,acan zan hada duk kayan lefen da nakeso,kayan daki da
za'a yimin cewa yayi na karba kudina nayi sabgar gabana dasu,don shi ya saka wani
kamfani daga turkey suna mana designs din da ko shugaban qasar nigeria bai taba
kwana a kai ba,na jarabtu da wata muguwar soyayya tashi,har bana gane dai dai da ba
dai dai ba,hakana bana sauraren duk wanda zaizo min da magana akansa musamman ta
suka ko zagi.

Naso na taba kama faisal,na ganshi a hanya yana tafiyar qafa,gaba daya
jikinsa ba irin suturar dana saba ganinsa da ita bane,na kira sunansa sai naga bai
juyo ba,nasha gabansa ina nuna masa kaina amma sai ya nuna bai taba ganina
ba,harshe ha juya ma ya fara yimin yarbanci,ya balbaleni da fada cikin harshen
yarbanci har yaso taramin jama'a,abinda yasa jikina yayi sanyi kenan naja baya ya
wuce abinsa,har sanda ya wuce din yanata masifa yana nunani da hannu.

Washegari sai gashi yazo a faisal din dana sanshi,maganar dana fara yi masa
kenan,amma sai ya nuna zallar mammaki

"Kece mutum ta uku data taba cewa taga wannan bawan Allan,ni kaina da ban taba
ganinsa ba mamaki nakeyi sosai,ance sak ni,saidai shi yaren yarbanci yakeyi"

"Exactly" na fada da sauri,zuciyata na gasgata faisal,saboda yadda naga zallar


shima mamaki kan fuskarsa

"Ba matsala,zan saka escort dina su lalubomin shi,nima dai naga mekama dani" dariya
nayi,na kuma ce

"Ai ikon Allah yafi gaban haka" daga wannan muka shiga wata hirar ta daban.

Bai gane dukka wasu magangu da ayyukan faisal qarya bane,ban gane duk wani
magana nashi plan bane,ban gane rami ya shirya min ba sai randa aka kaini gidan
faisal,madadin a shiga dani kai tsaye zuwa ainihin ginin tanqamemen gidan,sai akayi
boys quarters dani,kowa mamaki da al'ajabi ya cikashi na wannan juyin juya
halin,matar gida a boys quarter?,tarin cincirindon qawayena irina 'yan qarya,harda
ma wadanda hayarsu nayo su qawar qawa saboda su fidda bikina a duniya,duk haka suka
tafi suka barni cikin tashin hankali da mamaki,amma mayaudariyar zuciyata gayamin
takeyi wataqila don kada a bata masa gida yasa yayi wannan dabarar,saboda yasha
gayan shi mutum ne mai tsafta,amma bai cika son jama'a ba,da wannan na share nayi
zamana,ina kallon boys quarter din da yake kamar kango,babu komai sai katifa da
labule.

Sanda ango ya iso shi daya kamar maye,da shaddarsa tun ta wajen daurin
aure,zan tarbeshi ya matsa

"Dakata.....dakata,opay ce,tanayin squeezing kin jawomin jangwangwama,saina qara


dubu biyu akan yadda na karbo aronta,shi yasa tun daxu na kasa sakewa na zauna na
sake,sai yawo nake a tsaye kamar wanda ya hadiyi tabarya" uban mamakin daya cika ni
yasa na sandare a tsaye,ya zare rigar ya zauna ya bata lokaci ya ninketa tsaf,harda
zama akai wai don tafi komawa dai dai,sai daya gama duka sannan ya fuskanceni.yana
yaqen baki,zuwa sannan duk wani noti a jikina ya kwance,na gama sallamawa

"Faisal,ka gayamin waye kai"


"Yanzu kuwa,cikakken sunana shine haladu murtala,kuma haifaffen qauyen namuduka ne
can iyaka da garin kano,ci rani ya kawoni na hadu da wayyayun abokai wanda suka
taba jana zuwa wata dinner,a nan na ganki.na nuna inasonki kika yarfani harda
guzurin mari" yana fadar haka fuskarsa ta dawomin tar da kuma abinda ya faru a
lokacin,wanda har ga Allah a inda akayi abun s nan na bar batun,na mance da
fuskarsa bare abinda ya faru

"Wannan yasa naci alwashin saina rama,kuma saina mallakeki kota halin yaya,nayi
bincike a kanki na samo komai,na shigeki.ta yadda kikeso,yanzu gashi na sameki,duk
da naji jiki na kashe kudadena sosai,amma babu komai tunda burina ya cika kuma zan
fanshe" ina kuka ina komai haladu na sha'aninsa,a daren ya kwanta dani abunsa,babu
kazar amarci ko lemon fata na naira 30 ban gani ba,yana gama abinda xaiyi dani ya
haureni da qafarsa na fado qasa

"Shegiya tsinanna,girman kan banza ne,ashe fanko ce?,duk wannan wahalar da


nasha?,to billhillazi saikin maido min duka abinda na kashe,kuma aure yanxu aka
fara bazan sakeki ba" duk da cikin azaba nake amma mamaki ya cikani,saboda nasan
anyimin duk wani gyara da zai maidani mace,ko a jikina inajin na matse gam,to amma
komai na Allah daban yake,idan ya tafi ya tafi kenan,babu wanda ya isa yayi halitta
irin ta ubangiji koshi waye.

Kwananmu uku cikin wannan gida dana fuskanci na uban gidansa ne dake rayuwa
a lagos,a kwana na ukun da sassafe naga yana hada kayanmu waje daya,dama nawa kayan
da nazo dasu ne daga gida,don ba lefe ba batunsa

"Lagos zamu tafi ci rani,na samo miki aiki a gidan cin abinci,zakiyi aiki harki
hadan kudadena dana kashe,na saida gonakina da gidajena na gado duka a qauyenmu
saboda ke,to wa billahi bani haqura saikin dawomin dasu" inaji inagani ya kawoni
nan,ya kuma danqani a hannunsu yace a sanyamin idanu sosai idan aka ganni da
wasu,saboda ni din bin maza ne dani" kuka muneera ta sake sosai,bama ita kadai ba
harda iman din

"Inasu mamee,me yasa bazaki sanar musu ba"

"Ya karbe wayata tuntuni,amma na taba satar wayarsa na kirasu,abun mamaki wallahi
iman na kasa gaya musu komai,yazo ya sameni a haka yayita dariya,dama nasan zaa
rina,shi yasa nayi maganinki,duk wani naki da nasan zaki gaya masa.matsalarki nasa
an rufe bakinki,tashi ki ban waje,hakkin mazan da kika zalunta kika ciwa kudi baki
auresu bane.....wannan ne abinda ya gayan"

Kukan daya hangi iman din tanayi yasa hankalinsa ya tashi,ya gaza daurewa
ya tako a hankali zuwa inda suke,babu wanda yaji zuwansa,sai hannunsa da iman ta
gani qasan habarta yana tare digar hawayenta dake shirin sauka qasa

"Meye haka queen?" Maganar data ja hankalinsu,muneera ta bishi da kallo,iman kuwa


ta rungume hannunsa tana sake sakin kuka,a hankali ya dagata ya sanyata a jikinsa,a
kunne ya gaya mata

"Da nasan kuka zata saki bazan bata damar ganinki ba,muje" da sauri iman ta balle
jakarta,ta fiddo dukka kudin ciki ta ajjiyewa munera

"Zan nemeki munira,kiyi haquri" binsu da kallo tayi,har xuwa sanda taga sun bude
motarsu sun shige,kanta ya daure matuqa,lamin ne dai haka?,lamin din data rabasu da
iman din?.

Cikin mota tana kuka sosai tana baiwa lameen din dukka labarin da iman din
ta bata

"Mu taimaketa don Allah honey bee"

"Zan duba" amsar daya bata kenan a taqaice,kafin ya sake waiwayawa yana dubanta

"Amma indai kikaci gaba da wannan kukan,babu abinda zanyi a kai" da sauri tahau
goge hawayen,duk da zuciyarta a karye take,munira na cikin masifa qwarai.
************

Jirgin safiya suka bi zuwa gida kanon dabo,cuie da tarin nasarori cikin
rayuwarsu ta kowanne fuska ta kuma kowanne fanni,tun a cikin mota iman fake kwance
laqwas cikin jikinsa,a hankali ya dora hannunsa saman fuskarta

"Are you okay Baby queen......?" Kai ta gyada masa kawai,saboda cike take da
fargabar abinda zai faru tsakaninsu da malam

"Amma duk da hakan kamar jikinki akwai dumi,tun jiya nayi noticing hakan"

"Kaman yanayin weather ne daya juya" dan bata rai yayi cikin wasa yana dubanta

"Kada kicemin haka mana please,ba wani weather,baby ne,ajiyata ce" dariya ce ta
qwace mata,ta rasa wanne irin son yara lamin din ke dashi,abinda duka duka satinta
uku kenan da ganin period dinta har yake zancan baby?,....gabanta ne yadan fadi
data tuna cewa ranar ovulation day dinta sun samu intercourse dashi,kuma lallai
komai zai iya faruwa ba,sai tayi shuru tana irgen kwanakin,tare da laluban canje
canjen da takeji ajikinta,saidai ta rasa ko guda daya a ciki,bata jin canjin
komai,kawai dai daga shekaran jiya jiya zuwa yau dukin jikinta ya qaru ba kamar
yadda yake normal ba.

Suna isa gida lameen ya shirya su wuce wajensu malam kai tsaye,itama da
wannan zumudin ta iso,saidai tana fitowa a wanka barci yayi awon gaba da ita,ba ita
ta tashi ba sai gefin azahar.

A gefanta ta sameshi zaune yanata calculation da lissafe lissafe na wasu


kudi,suna hada idanu ya sakar mata murmushi wanda ta kasa fahimtar me yake nufi

"Sannu baby"
"Don Allah ya lameenn.....bafa haka mukayi dakai ba" lumsassun idanunsa ya zaro
mata yana dubanta

"Me kuma nayi?"


"Gida fa kace zamuje wajen malam" tana kaiwa nan sai kuka ya qwace mata,ba lameen
kadai ba,ita kanta abun sai ya bata mamaki.

A mamakance ya taso ya riqeta sosai ya sanyata cikin jikinsa yana shafa


bayanta

"Akan wannan kike kuka?,to ya isa,tashi kisa kayanki mutafi" sai daya dan jima yana
lallashinta sannan tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya,shi ya taimaka mata ta
shirya duk don ya saukar da ita,koma bayan daa da ota ke gaimala masan ya shirya
idan zai fita,suyita rigima tana jan gashinsa kan cewa har yau baby ne bai gama
iya shirin office da kansa ba,duk gyara daya punishment nasa zai bata hot kisses
both kumatunta guda biyun,batasan wayo yake mata ba,shi hakan yafi masa komai dadi
a rayuwarsa,shi yasa idan ta gyara masa abu gobe idan yazo bashi zaiyi ba,yana sane
zai canza ko kuma yayi ba dai dai ba,moments da suke spending kafin ya fita aiki
yana daya daga cikin memorable and sweet moments a rayuwarsa da bazai taba mancewa
dasu ba,ya fuskanci zuciyarta a kusa take,ajiyar zuciya taketa saukarwa,don haka ya
dinga lallabata har ta gama nata shirin sannan yayi nasa,cikin wani yadin kufta da
aka zubawa aiki irin na matasan zamani dake ji da kudi da ilimi,kalar yadin kalar
kayan dake jikin iman dinne,sai gasu sun fito fess dasu,best couple ever.

A harabar gidan taga yana yunqurin bude wata sabuwar mota,mamaki ya


cikata,saboda batasan da ita ba,hakanan sanda suka shigo gidan bata lura da ita
ba,sai da suka shiga sannan ya dubeta bayan ya furta "alhamdulillahil lazi
bini'imatihi tatimmus salihat"
"Ma sha Allah,tayi kyau honey"

"Taki ce dama" ya fada yana murmushi,idanu ta zaro cikin mamaki

"Da gaske?"
"Da gasken gaske,na taba yi miki qarya?"

"Ko sau daya yaya na...." Farinciki na wanzuwa saman fuskarta


"ta yaya zan nuna godiyata ma a gareka?"

"Ki haifamin babies masu kama dake da zasu cikamin gidana,sannan ki bani dama naci
gaba da kasancewa dake har abada" murmushi ya kubce mata

"Allah ya cika maka dukkanin burikanka,yasa ka gama lafiya,Allah ya kiyayemin kai"


"Ameen uwae yayana,mace ta gari"sunan yayi mata dadi sosai,har sai datayi fari da
idanunta

"Amma yaya ka barmin waccan ka dauki wannan kai" motar ya kunna ya fara qoqarin
fiddata daga cikin gidan kafin ya amsa

"A sabuwa dal na sameki.....saboda haka baci cancanci kyautar tsohon abu ba,kawai
dai idan ina da sha'awar hawa zan ara,kafin komai ya qarasa warwarewa nima na sauya
tawa,amma yanzun kam wannan takice,banason ki koma zirga zirgar makaranta rana tana
dukarmin lallausan fatarna me tsada" dadi ya sake cikata,kalamai da gaske sune
mutum,kulawa itace gishirin zaman aure,kwanciyar hankali da nutsuwa kuma sune
jigo,bawai tarin dukiya ko qyale qyale ba.

Duk yadda iman din takai ga zumudin xuwa gidan sai gata tana rabewa a bayan
ameen din sanda suke shiga cikin gidan,dariya ya saki ya jawota zuwa gabansa

"Matsoraciya,babu abinda zai faru fa,fada kawai malam zaiyi ni na sani,kuma koda
yayi fadan ni zai yiwa bake ba" saita san saki jikinta tana qanqame da hannunsa.

Mufida suka samu a falo tana gurxa danyar citta ginger,da alama lemo zata
hada,gefanta wata kyakkyawar black beauty matashiya ce zaune suna hira da mufidan
tana tayata kankare bayan ginger din.

Dukka abun hannunta ta watsar ta taso tayo kan iman din tana qwalla qarar
murna abinda yaja hankalin inna da Sadiq dake falon malam duka suka leqo da sauri.

Sak inna ta tsaya,wani sanyi yana ratsa zuciyarta,tabi sanyin idaniyar tata
wato lameen da iman da kallo,zallar nutsuwa wadata da kwanciyar hankali na bayyana
kansu da kansu daga jikkunansu,ba wanda bai qara haske da qiba ba a cikinsu,sai
tayi hanzari kau da kai sanda duke gab da hada idanu da ita,saidai kuma murna da
farincikin dake saman fuskarta bai canza ba.

Gaba dayansu yau har iman din zubewa sukayi suna gaidata,ta amsa musu
cikin kulawa da nuna farinciki,kai tsaye kuma suka wuce wajen malam,kwarjinin nan
nan nasa dai yayi musu,saidai shi dinma farincikinsa ya kasa boyuwa,sadiq na gefan
lameen din yanata kwasarsa yadda suka saba qasa qasa yadda ba wanda zai fahimta
saisu yasu

"Zaku hade da yaagana,tace kun maidata mutuniyar banza,tana zaune zaman jiran gawon
shanu ka sace matarka kuka barta gaho" dariya taso qwacewa lamin,ya jima yana
tunanin dama yadda zata kaya a tsakaninsu da yaagana din.

Hirarrakin yaushe gamo ne suka barke sosai a rumfar malam,dukka aka tattaru
aka dawo nan,harda matar ya sadiq wadda a ranar suka fara ganin juna face to face
ita da iman,kuma wani haduwar jini ya qullu a tsakaninsu,saida aka gama hira lamin
ya gabatar da bude kamfanin sarrafa motoci malam yasa rana kamar yadda ya
saba,sannan ya buqaci ganinsu,hakan yasa matar ya sadiq me yawan kunya da hankali
ta janye mufida cikin hikima suka bar dakin.

Fada sosai malam ya dinga yima lameen din irin wanda bai taba yi masa ba
kan sakin samha da yayi,ya kuma hada harda iman din kan cewa ita ya kamata ta dinga
controlling nasa,shine zata amsa sunan mace ta gari,ya kuma umarceshi da lallai
lallai ya tashi a yanzu basai anjima ba,sadiqu ya rakashi biko.

Sosai hankalinsa ya tashi,ya cire hularsa ya aje yana satar kallon iman
wadda kanta ke qasa batace komai ba bata kuma motsa ba,duka sun karanci inda
hankalinsa ya karkata,sai malam din ya umarci iman din ta tashi tabar wajen

"Ka maida hankalinka ameenu,ka zama tsayayyen namiji bame bin umarnin matarsa ba"

"Kayi haquri malam,kada ka zargi iman ko kawota cikin batun nan,wlh bata da ruwa ko
tsaki a ciki"

"Naji,ku tashi ku wuce nace" dolen dole lamin din ya miqe,sadiq ya rufa masa baya

"Ya kamata malam ya haqura haka,shi da kansa fa yaje gidansu yarinyar amma bakaga
abinda sukayi masa ba,wai saidai kazo da kanka" kashe motar da yake shirin kunnawa
yayi

"Malam din?" Ya tambaya cikin jin xafi

"Eh mana"

"To babu inda zani wallahi,bata kai wannan darajar ba" yayi maganar yana shirin
bude motar sadiq ya danqo shi

"Kana qin zuwa laifi zai dawo kaina,ban gaya maka bane saboda kaqi zuwa,na gaya
maka ne saboda koda kaje kaga wata fuska ta daban kayi haquri da hakan" da qyar ya
shawo kan lameen din,wanda a qarshe yace saidai shi ya tuqasu,shikam baxai kaisu
ba,lallabawa akeyi,haka sadiqun ya karba tuqin.

Sun jima sosai suna zaman jiran samhan,daga bisani sai gata ta fito,ta
canza gaba daya tadan rame,ta kumayi duhu sai tsaho data qara,kamar wadda aka yiwa
dole haka tazo ta zauna hannun kujera tana busa hanci,ita a lallai ba zata nuna
masa ta damu dashi ba,ganin haka sai lamin din ya miqe tsaye,ya maida hularsa
kanshi

"Malam ne ya aikoni nazo nayi bikonki......" Kafin ya qarasa ta juyo a fusace

"Indai sai ta hannun wanna munafukan tsaffin zan koma wallahi na haqura da aurenka
har abada......" Gigitacciyar tsawa daya tabbatar ta isa har cikin gidansu ya daka
mata

"Kika kuskura wannan qazamin bakin naki ya sake aibata mutane mafi daraja a
rayuwata na rantse da sarin dake busamin numfashi saina zubda miki
haqora.........tun daga sanda na sakeki kika fita daga sahun matata saboda dama ban
dora miki idda ba,inda akwai sauran iddata a kanki da a yanzu zan cikashe miki
sakinki daya da yayi ragowa shashasha,amma na godewa Allah daya sanya ban hada
jikina da naki ba........wawiya kawai wanda iliminta bai amfana mata komai ba" daga
haka yayi waje da mugun fushi,dole sadiq ya miqe ya bishi,zuciyarsa cike fal da
mamakin hali da dabi'a irin na samha,lallai babu abinda zamuce da iyayenmu da suka
tsaya tsayin daka suka bamu tarbiyya ganin daraja da kimar mutum sai godiya da
fatan alkhairi.
Da kallo ta bishi,tana jin kamar ta dora hannu aka ta zunduna ihu,last
chance da hope da take dashi shikenan ya qare?,me yasa batayi controlling fushinta
ba?,me yasa bata iya yiwa harshenta waigi ba?,idan yaso in ta koma ayi duk wacce
za'ayi ma

_Ni kuwa nace harshe dama mafarin dukkan wata nadama,indai baka iya controlling
dinsa ba,Allah ya rabamu da sharrin harasunanmu_
[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: 75

Koda iman ta koma falon innan sai tayi qoqarin sakewa tare da mai da komai ba
komai ba,duk da cewa taji fitarsu zuwa bikon samha,ta sani cewa duk yadda takai ga
so da qaunar lameen bata isa ta hanashi abunda Allah ya halasta masa ba,shi majin
mace hudu ne,ko yau ko gobe,da dadi babu dadi,ba dawowar samha ce damuwarta
ba,damuwarta ta samu adalci daga wajen ameen tsakaninta da samha,wanda bata haufi
ko kadan a kan hakan.

Hirarsu sosai suke da matar ya sadiq wadda ta fahimci ciki gareta dan
qarami,duk da hankalinta rabi da rabi ne,har zuwa sanda matar sadiq din ta tashi
yin alwala,iman din kuma ta shiga daki wajen inna.

Hira ce ta barke tsakaninta da innar,tanata bata labarin abubuwan da suka


faru da bata nan,idan innar ta manta wani abun mufida ta tuna mata,a nan taji zacan
auren bushira da dr ahmad

"Aikin yaagana ne wannan,nima bansan yadda akai ta hadasu ba,jiya iyanzu ma


bushiran tana nan muna ta hirarku,tana ga qorafin kuyi hijira kun bace bat a qasar
nan" inna ta fada har cikin zuciyarta na haduwar auren dr da bushiran.

Dadi ya kama iman naji yadda innarta ke kewarta,a yanzu dukka wata soyyaya
ta dawo tsakaninsu,gefe daya kuwa albarka kawai iman ta shiga sawa yaagana,saboda
tayi abinda ya dace,an kuma aza qwarya a gurbinta,daga dr har bushira nagartattun
mutane ne da suka dace da juna qwarai.

Aiken mufida inna tayi kitchen,sannan ta ajjiye abinda takeyi,ta zauna tana
kallon iman bayan ta kirayi sunanta. Nasiha tayi mata sosai kan xaman aure,irin
nasiha ta tsakanin uwa da 'ya,ta bude mata abu uwa sosai masu tarin yawa irin wanda
basu taba maganarsa ba tsakaninta da innar

"duk yadda maeenu ke sanki akwai sanda zaku bata kiyi rashin dadi,ban yarda ki
gayawa kowa ba koda jice,a matsayinki na mace kiyi amfani da hikina da baiwar da
Allah ya bawa kowacce 'ya mace ki gyara natsalar,idan kika fuskanci tafi qarfinki
ko akwai barna me yawa a ciki a sannan ne zaki nema shawarata,daga kaina kuma ban
yarje miki ki gayawa kowa matsalarki ba,koda ya kuke da mutum.......Kada kice zaki
dinga amfani da soyayyar da mijinki yakeyi miki ki sake jiki,ki barshi yana aikata
ba dai dai ba,ko dorashi akan hanyar da zai tsira ranar gobe,na sani na kuma gani
kan fuskarsa,soyayyar da yake miki tana da tarin yawan data wuce ma yadda muke
hasashe,kiyi qoqarin amfani da wannan damar ki dinga dorashi kan hanyar data dace"
sosai maganganun inna suka shigeta,suka kuma sanyata fidda qwalla,ta kama hannun
inna tana mata godiya tare da sake neman gafararta,daga bisani tare suka fito daga
dakin sukaci gaba da sabgarsu.

Shuru har yamma lis babu 'yan biko babu dalilinsu😂,abinda basu sani ba
tuni mahaifiyar samha ta kira malam da kanta,tace ya jawa lamin kunne,aure babu
dole,bashi ba 'yarta,malam baice komai ba har ta gama ta kashe wayar,abinda ya sake
sanyayar masa da jiki kenan.

'yar halak bushira sai gata kuwa,iman tasha tsiya tasha tsiya,tun tana
ramawa har bakinta yayi shuru,uwa uba kuma ga mayen zazzabin yammar nan da yake
yawan rufeta ya fara sako kai,saidai hirar da suka dinga yi tadan rage mata jin
zazzabin,ta kuma dauke mata kewar lameen din da take tayi tun dazu,sai takejinta
yau duk wani iri,wuni guda bata jita a jikinsa ba rungume cikin faffadan qirjin nan
nasa na alfarma dake cire mata duk wani damuwa da fargaba,daga qarshe dai daki dole
ta koma saboda zazzabin,tabar bushira da matar sadiq suna ci gaba da hirarsu.

Kwance tayi saman gado,zuciyarta tayi nisa a kewa da tunanin


mijinta,cikin hancinta ta fara shaqo qamshinsa,tana bude idanu kuwa shidinne a
tsaye,sai ya bude mata hannayensa gaba daya,batayi sanya ba kuwa ta garzayo ta
fada,ya maida.hannunsa ya rungumeta tsam yana sansanarta

"How was your day?"


"So boring " ta amsa masa tana yatsina fuska,idanunsa ya fiddo waje

"Beside inna da malam din?" Kunya saita kamata ta boye fuskarta a qirjinsa,abinda
ke zuciyarta ne kawai tayi subutar baki ya fito,dariya ya qyalqyale mata dashi
kafin ya dagata sama ya juyata,ya kuma ajjiyeta kan madubi yana kalln fuskarta

"Don't be shy.......gaskiyar cikin zuciyarki kenan,nima kuma banajin akwai wani


sauran waje a duniya da zanje naji dadin kasancewa a wajen ba tare dake
ba.....oya.... pack your stuff mu wuce gidanmu" shi ya tayata suka tattare
kayanta,sai gasu a falo da shirin tafiya.

Inna dai dauke kai tayi tayi kitchen tana cewa su tsaya a zuba musu tuwo su
wuce dashi

"Kinaso baby?" Ya tambayeta,ta gyada kai,mufida ce ta biyosu dashi,bushira tayo


musu rakiya har bakin mota tana yiwa iman tsiya qasa qasa yadda ameen bazaiji
ba,don tanajin nauyinsa da girmamashi,ba zataso yaji ba,bushira da bata qyaleta ba
saida iman din takai mata duka sannan taja baya tana daga mata hannu.

Yana driving amma yana riqe da hannunta,bai boye mata komai ba kan abinda
ya faru gidansu samha

"Allah ya gani dukkanmu munyi iya yinmu,mun kuma fita haqqinsu" ya fadi,saita
lumshe idanu kawai,bazatace taji dadi ba,saboda kimar aure,amma ranta bau baci
ba,duba da cin kashin data yiwa mutanen datafiso inna da malam

"Allah ya zaba abinda yafi alkhairi"

"Ai yama zaba din in sha Allahu tunda akayi haka"

"Baby,asibiti zamu wuce fa,jikinki yayi zafi da yawa" maqale kafada tayi

"Ka siyon paracetamol kawai ya isa" kansa ya jijiiga

"Ban yarda ba,nifa nafi yarda da cewa cikine Allah" yadda ya dage yasa ta yarda a
siyo paracetamol din,sanna ya hado mata da pt strip ta gwada fitsarinta da kanta a
gida.

Shuru sukayi dukkaninsu kowa ya zubawa strip din idanu sanda suka fiddoshi
daga cikin fitsarin bayan sun idar da sallar asuba,dubanta iman din yayi

"Ki tabbatar fa saikin bani alqawarina indai nine nayi winning cikine" idanunta ta
fara saukewa kan strip din kafin takai ga bashi amsa,tar layukan jajaye guda biyu
suka bayyana radau,gabanta yadan fadi,ta dauke idanunta ta maida ga lamin,ashe
shima ita yake kallo,sai ya dage mata girarsa guda biyun,fararen haqoransa dukka a
waje saboda yadda murmushinsa da murna suka gaza boyuwa,ya zuba mata idanu,sai taji
wani weakness na yakamata,zuciyarta ta karye,wai itama tahau turbar zama uwa
kenan?,nan da wasu watanni zata zama uwa itama?,zata riqe danta ko 'yarta a
hannunta?,qwalla ta taru ta cika Blue eyes dinta,saiya bude mata tafukan hannayensa
ta shige ciki ya rufe yana sakin qaramar dariya cike da nishadi,hannunsa akan gadon
bayanta yana shafawa a hankali yana jero kirari da godiya ga ubangiji,zamewa yayi
ya durqusa a gabanta,ya kama dukka tafukan hannayenta yayi kissing tsakiyarsu

"Kin gama min komai hajaru,na yafe duk wani abu da kikace zaki bani,abu daya ne ya
rage.....ki haifamin baby girl me kama dake"kai kawai take gyadawa

"Alhmadulillah" bakinta ya furta a sarari,sai suka sake rungume juna,qauna da


soyayya abinda ke cikin yana hudasu tun basusan meye ba.

*******Tubali me kyau hadi da kyakkyawan dashe na harsashin kyakkywar mu'amalar


auratayya ne a tsakanin lamin da iman,wani irin zama daya zama madubi abun kallo ga
kowa,abun sha'awa kuma abun kwaikwayo,duk inda namiji jarumi kuma jajirtacce yake
lameen yakai can,banbanci mabayanni iman ke gani,tsayayyen namiji da ya daukewa
iyalinsa komai,ya hanasu kuka ko damuwa,ya hana zukatansu jin ciwo kewa ko kuma
rashi na wani abu komai qanqantarsa,zallar zama na amana,zama na sanin daraja da
kimar dan adam,iman ta sake gani ta kuma sake gasgata kudi da soyayya ba koma suke
iya siyawa dan adam ba,daraja kima da dattako gami da sanin kima da darajarka yafi
komai tsada da wahalar samu,tayi godiya ga Allah tayi sadaka me tarin yawa kan
yadda ubangijinta ya fiddata daga mummunan ramin data afka,tana yima lameen kallon
duniyarta koma muce rayuwata gaba daya,qauna ta haqiqa mara misali,wanda ashe a
gida rabin rabinta ya fiddo ya nuna mata,a yanzune ya fiddata gaba
daya,tsaftatacciyar qauna me cike da tsari da salo na daban.

Ya zame mata aljannar duniya,wannan yasa itama ta zame masa jin dadin
rayuwarsa gaba daya,cikinta daya fara fitowa baisa ta gaza wajen yi masa komai
ba,ta zame masa cikakkiyar mace ta gari,wadda duk inda hake duk yanayin da yake
ciki kallon fuskarta ne kadai ke sauke masa nutsuwa da kwanciyar hankali,duk yadda
takeson abu idan lameen bayaso ta barshi kenan,hakanan ko yaya ya nuna yanason abu
to ta riqeshi kenan sai inda qarfinta ya qare.

Cikin wata kulawa ta musamman yake tattalinta da kuma rainon cikinta,gefe


guda ta koma kan karatunta,ta bada hankalinta akai matuqa,ya bata dukka wani
support don ganin ta samu kyakkyawan sakamako ganin suna kan gangara,watannu
qalilan suka rage mata,sai Alla ya bata ciki mai sauqi,bata wuce zazzabi ko ciwon
kai shine cutarta,sai kuma abincinta wanda kullum tuwone,wannan kuma sai ya zama
dutyn inna,kullum sai tayi mata sabon tuwo,yaran dake mata aike a gidan suke
jigilar karbowa,duk tuwon daa buqata shi inna zata mata,zaya yiwa lameen girki kala
kala na burgewa,amma saidai ta tayashi zaman ci,haka zaici wataran yana
tsokanarta,wataran yana tausaya mata sosai,yakam bata lokaci yana lissafo mata
nau'in abinciccika ko zataji wanda take sha'awar ci yaje ya nemo mata duk inda za'a
samu,saidai kawai ta tabe baki ko tasa dariya,wani lokaci tace....abu kaza ma ni
sai naji kamar zanyi amai,wani lokaci yakai mata bugun wasa yace ta rainashi,ya
zauna ya zayyano mata abincin yaruka kala kala amma tace masa amai ma taji,saidai
tayita dariya ko tayi masa gwalo....haka rayuwarsu take,cike da barkwanci farinciki
da girmama juna.

Sannu a hankali wani irin budi yaketa shigowa lameen harda sadiq
dinma,kamfaninsu guda biyu kowanne wani irin kudi yake kawo musu naban mamaki,ba
komai bane sirrin nasararsu face malam,wanda koda yaushe yake basu shawarwari na
yadda zasu kaucewa duk wata hanya da zasu gamutsa halal da haram,duk wanda yayi
hulda dasu sai ya dawo ya sake nemansu,saboda komai nasu cikin aminci inganci da
amana suka dorashi.

Ameen mutum ne mai hannun kyauta da bayarwa,hakan ya sanya hatta danginsa


dake jigawa sukasan lallai fa budi yazo,don kuwa bayan kowanne watanni baya wuce
daya zuwa biyu sai yayi rabon kayan abinci kudi da sauran kayan buqatu,iman ta
qarfafa masa gwiwa sosai,ta kuma sake dorashi ka wannan hayar,tunda babu abinda
suka nema suka rasa a rayuwarsu,kafin kace meye saiga yaa baraka ta zama
hajiya,gidanta baya abo da mabuqata da masu zuwa mata fadanci,dama kuma ita din
mutum ce mai yawan alkhairi,tun bata dashi abun hannunta bai rufe nata idanu ba,sai
kowa ya zama nata,daga dangi har maqota,sosai iman ta samu farinji da karbuwa dari
bisa dari wajen dangin lamin,kamar xasu cinyeta saboda qauna da suke gwada
mata,hakan kuma ya samo asali ne daga yadda bata qyamar su,tamaishesu kamar nata.

Hankali bai kwanta ba saida iman ta kammaka jarrabawarta gaba daya,ta


gama school of nursing,komai ya tafi maya successful saboda taimako gwarzon miji na
gari data samu,wanda a lokacin daya fuskanci cikin ya fara mata nauyi sai ya dauko
mata usama,shike tuqata ya kaita,ya kuma dawo da ita,sai data kammala sanna usaman
ya koma,bai jima a can ba ya sake dawowa nan shima,saboda BUK da lameen din ya
samar masa,amma fir yaqi zaman gidan lameen din,ya dawo waje inna yayi
zamansa,hakan sosai ya faranta ran inna,ko babu komai ta sake samun mutum a kusa da
ita,ga usama ga mufida,gidan sai ya sake mata dadi.

Wata daya da gama makaranta bikin bushira ya tashi da dr ahmad,sosai dr


din yayi mata bajinta ta nunawa,tabbas Alla ne yake qulla soyayya,todai ya qullata
tsakanin bushira da dr ahmad din,tamkar dama tun da farko sun jima da fara son
juna,ko kuma babu wanda suka fara so sai junansu.

Duk yadda iman taso ta gwangwaje a bikin malam al'ameen ya hana,wasi


events dinma bai barta taje ba,tayi nacin tayi kukan amma fir yaqi,ya wuni a gida
ya sanyata a gaba yana kallon abarsa,taka qararsa wajen amarya bushira amma saita
gwaleta

"Kin fara nauyi iman,me zakizo kiyi,kun gama mana komai,sadaki ma ya lameen ne ya
biya,ida kika lura ya ameen yana da kulle,yakamata ki saba da hakan ki daina
damuwa" haka maganarta take,indai fita bata kama ta zama dole ba lameen din baya
qaunarta,ya gwammace idan ya hanata yaga rata ya baci,sai ya zauna ranar ya tayata
wuni,yakance

"Shikenan.....munyi one one ko?" Maganar bushira haka take,don haka sai ta saki
ranta kawai ta shiga shirya masa dan abun sha da yafiso kafin ta gama girki.

Sanda ta kawo masa drinks din jawota yayi jikinsa ya azata saman cinyarsa

"Zo nan madam.....ki rufan asiri ki rage fushi da saurin kuka,kada ki haifan
raguwar baby.....me idon mage" idon magen daya fada a shagwabe ya bata dariya a
dole,saboda ya tuna mata zamanin quruciya,ya dinga tsokanarta sai data sake,sai
datazo tashi qafa ta riqe

"Bari na baki albishir,ladan fushin da nasa akayi dani...." A kunne ya rada


mata,saita zare ido ta kima hangame baki,fuskarta dauke da dariya

"Da gaske ya lamin....kace nayi shirin zama dr"

"In sha Allah" ya fada yana murmushi,gam ta qanqameshi tana masa godiya,sai kuma
kukan farinciki ya qwace mata,yasan duk wani burinta wanda ta taba furtawa dama
wanda bata taba furtawan ba, he's genius lameen din musamman akan duk wani abu daya
shafeta

"Banda kuka queen...... stop it please" ya dinga fada yana shafar bayanta.
[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: 76

Randa ta dawo daga raka bushira dakin mijinta,suna hanya ya daukota da kanshi a
motarta kamar yadda shi ya kaita da kansa ya kuma jira ta gama duk uzurinta,yake
gaya mata ya gama da issue din muneera,yanzu haka auren ya rabu,muneeran tana gida
gaban iyayenta

"Zaku iya ci gaba da zumuncinku ta waya,ban hanaki ba,amma ban yarda ko sau daya
tasan hanyar gidana bama bare gidana"

"As you wish sir" ta fada tana jin dadin taimakon muneera har qasan ranta,saboda ko
babu komai muneeran ta sota da gaske,kawai wata qaddara ce tasa ra ingizata suka
yita tafka kuskure,ko bai fada ba dama bata da sha'awar ci gaba da
qawancensu,qawance na kusa da kusa,gwara daga nesa nesa,ita a yanzun a duniya
qawayenta kuma aminanta guda biyu ne,ta farko innarta,ta biyu kuma busheera.

Lameen da kansa yaje ya dauko mata badi'a daga jigawa saboda ta dinga
hutawa,tabbas ta samu hutu,shima kuma ya huta sosai,don sai data ce

"Ni ban gane wayon kawo badi:a ba,kanka ka yiwa aikin nan Allah honey" idanu ya
lumshe yana murmushi,iman din ba zata gane yadda ta sake zama cikakkiyar mace ba.

"To nidai abun arziqi da alama bai karbeni ba,fisabilillahi,idan ma na huta to


mene" ta motsa ya sake kanannadeta

"Tabbas Allah ya dubi zuciyata,ya kuma soni da rahama da ya hanani hadaki da


kowacce mace,dako tantama banayi,zaiyi wuya na tsallake sahun mazan da zasu tashi
da shanyayyen barin jiki......wallahi har yanzu iman baki gama sanin yadda nake
jinkina a raina ba,abinda zai iya bayyana kawai kika gani,sauran saini
da.mahaliccina da kuma zuciyata" duk sanda lameen din yayi mata magana irin wannan
jin kanta take a sama,ta yarda da duk maganarsa,saboda tana gani a zahiri,wannan
yasa take sakar masa ranta rayuwarta dama gangar jikinta yayi duk yadda yaso da
ita.....to sai muce Allah ya raba lafiya hajara aya.

*_BAYAN SHEKARU_*

Tsaye motar tayi a qofar mayalwacin gate din gidan da yake mallakar
malam ibrahim khalilu tana danna horn,maroon color ce mai matuqar kyau,yadda kuma
take daukan idanu kawai ya isa ya gaya maka cewa sabuwa ce dal.

A hankali gate din ya fara motsawa gaba kafin ya yaye gaba daya,dan
matashin yaron da ya doshi shekara goma sha biyu ya bayyana,sak PHOTOCOPY na
MUHAMMAD AL'AMEEN mamallakin katafaren kamfanin IB COUTURE daya zagaye qasashen
africa kaf sai dai daiku,kyakkyawar harabar gidan ta bayyana,mai tuqa motan ta
motsata zuwa ciki,idanunta nakan gilashin mudubin motar tana hangen yaron sanda
yake biyo bayan motar bayan ya maida gate din ya rufe.

Shi ya bude mata mota yana fadin

"Sannu da zuwa ummee" takalleshi da kyau,shi yasa koda yaushe yake sake kama
ranta,ya debe halayen malam ya cakuda dana babansa,dabi'unsa na dattawa ne,yana
matuqar qaunarta da kuma tausayinta,wannan shine first born dinsu

"Yauwa me sunan malam.....ya na ganka a nan?,kun gama musaffar ne?"

"Mun gama ummee,har malam din ma yadan kwanta ya huta" ya amsa mata yana zagayowa
daya seat din yana debe mata takardunta da jakar data fita dasu,sannan ya zagayo
inda take zaune tana qoqarin daga qafarta data maqale saboda tuqin datayi

"Ko na matso ki dafa ni ummee" ya fada a tausashe,ta kalleshi ta saki mirmushi,ya


sani,aikin mahaifinsa ne wannan,wato yau da baya kusa shine zai karba masa

"A'ah,zan iya me sunan malam" sai tayi bismillah ta yunqura ta fito.


Dr iman ibrahim khalilu kenan,cikakkiyar likitar mata,kuma mamallakiyar
asibitin nan dake aiki da tsarin addini wato AL_EMAN CHILDREN AND WOMEN HOSPITAL
wanda yake duba mata da yara zalla,hakanan tun daga kan nurses da likitocin dake
aiki qarqashin asibitin mata ne,tsiraru ne maza suma aikinsu bai shafi duba marasa
lafiya ba,kamar masu share haraban asibiti da masu gadi da sauran wasu ayyukan.

Kallo daya zakayi mata kasan ta zama babbar mace,wadda ta gogu da ilimi da
kuma wayewa,duk da tulelen cikin jikinta hakan bai hana kyanta da tsarin adonta me
burgewa fitowa ba,komai nata classy ne,daga duba daya zaka karanci hakan.

Abinda ya fiddata yau din tana daga cikin ranakun da take zama cikin
asibitinta,tana da office nata mai zaman kansa,tana kuma da selective ranaku guda
biyu a sati da take zuwa asibitin,duka sauran kwanakin tana zaune a gida,badi'a da
bushira na cikin masu kula mata da asibitin,suma kuma suna wasu ayyukan acan,uwa
uba usama wanda gudanarwar asibitin ke hannunsa,lameen ne ya gina mata asibitin ya
kuma danqa mata shi kyauta halas malak,lokacin data haifa masa yaronsa na uku wanda
a yanzu cikin na biyar ne da ita,yara maza hudu reras gareta,cikin da akaci masa
burin haifar diya mace kamar su sayo a kasuwa,kada ma lameen din yaji labari,tadan
qara lokacin dawowarta akan yadda ta saba,saboda tsayawa da tayi duba muneera wadda
itama haihuwa ko yau ko gobe,don sai ta haihu da wajen wata daya ma kafin ita ta
haihu,to cikin nata ana tunanin yi mata cs ne saboda yadda babyn yake
breech,muneeran ta samu tayi aure bayan shekara kusan uku da mutuwar wancan auren
nata,daga qarshe dai tailor da take rainawa ta aura,cikin ma'aikatan dake aiki a IB
COUTURE mallakin lameen din,saidai yana cikin ma'aikatan dake daukan albashi mai
tsoka,shi kansa bai sani ba sai da auren ya tashi,ya gayyaci lameen din a
matsayinsa na ogansa,kuma babban baqo a wajen,ya mata murna sosai saboda mudassir
mutumin kirki ne,ya kuma gayawa iman a sanna,har ya barta taje mata yinin biki,daga
qarshe bayan sun tare suka matsa ita da mudassir din dai sai da sukeje sukaga
gidansu,komai dai dai wadaida,cikin rufin asiri,abun gwanin sha'awa game wadatar
zuci.

"Su isma'eel fa?,sun dawo kuwa?" Ta tambayi mai sunan malam wanda ke take
mata baya yadda dai lameen keyi mata har kullum,tana kutsa kai zuwa cikin gida
wajen innarta

"A'ah basu dawo ba,naji abee ma yayi waya,idan anyi sallar magarib zaizo ya daukemu
gaba daya" kai ta gyada don ya kirata ta gaya mata.

Ta samu inna rungume da falle fallen qur'ani tana dubawa,ta daga kanta
tana amsa sallamar imanin tata,cike da kulawa

"Sannu" inna ta fada cikin nuna kulawa tana tattare alquraninta,dai dai sanda mai
sunan malam ya dawo daga kitchen dauke da ruwa ya miqawa iman din,sai da yaga tasha
sannan ya fice abinsu barsu da innar.

Inna da kanta ta hada mata ruwa mai dumi tace tayi wanka,sanna ta tayar da
mufida dake bacci wadda zuwa yanzu ta zama budurwa,don zancan karbar kudin aurenta
akeyi da usma dan yaa baraka,duk sun tsaya qumbiya qumbiya suna ta yiwa innar boye
boye bayan kowa ya gama ganosu,ta shiryawa iman din abincin sannan ta zauna ta
tayata ci,don wannan cikin acicine,komai ta samu ci take.

Suna tsaka da hirarsu hayaniya ta fara tashi daga harabar gidan

"To bismillah,da alama su isma'il sun dawo,kuma mawuyacine idan ba dasu maama
fatima ta hadomin su ba(yaran sadiq,wanda su kuma su hudu ne,mai sunan inna itace
maama kuma babbar,sai lailah....sai hanif,sai aslam shine qarami)" kafin inna ta
rufe bakinta kuwa basawan nata suka bayyana cikin falon,isma'il ne mai kado kansu
wanda shike bin mai sunan malam,sai Abdallah sajid,sai muhammad da suke cewa
mamman,sai kuma yaran sadiq din,fatima matar sadiq tana biye dasu a baya dauke da
aslam.

Falon kuwa ya kacame gaba daya,Allah ya taimakesu mai sunan malam ya leqo
yace dukka suzo inji malam,basusan malam din yana gida ba,sai kuwa aka fara rige
rigen fita zuwa wajen mlam din har ana karo da juna,sunsan kilishi ne ko zuma ko
kudi zasu samo,alaqa me mai kyau da matuqar shaquwa tsakaninsu da malam din,yana
matuqar ji da jikokin nasa kamar yadda suma sukeji dashi

"Alhmadlh,haba,maji kunnuwanmu,da alama basusan yana gidan ba dama" iman dake zare
hannunta daga abinci ta fada.

Indai suka hadu tsakanin fatiman da ima basa jin kunne dama,da inna tayi
iya tata hirar saita miqe ta barsu,suka kuwa dasa har sai da aka kira sallar
magariba sannan suka wuce sallah.

Basu jima da idarwa ba aka kira cin abincin dare,saboda yau family din ya
hadu,can babban falon malam.

Tunda suka shiga idanunta shi suka fara gani,shima nashi idanun ita suka
fara gani,anacin abinci ana kuma taba hira cike da raha,harda malam din da
inna,family ne mai ban sha'awa da qayatarwa,basuyi boko ba iyayen,amma suna bin
tsarin koyarwar musulunci,wanda yafi na boko ban sha'awa tsari da kuma
qayatarwa,shi yasa abubuwansu ke burge mutane da yawa.

Wata kulawa ta cikin ido ake bawa juna tsakanin iman da lameen din,amma a
haka zaka zaci ita dashi kowa harkar gabansa yake idan ba kana da kula da bin
qwaqwafi ba,basar dashi take,tasan sarai me yakeso,abubu biyu ne kuma duk sai taja
masa rai a kai.

Shi ya fara janyewa daga cin abincin,ya koma gefe ya tsume yana gayawa
yaran su hanzarta zasu wuce gida

"Nayi zaton dana gansu duka nan zasu kwana?sannan shi kansa takwara izifin qarshe
na suratul baqaransa bai zauna masa sosai ba,so nake cikin watan nan ayi bikin
haddarsa,sai amaisa hakali sosai ga isma'il" Malam ya fada yana dan duban
lameen,sai lameen din ya shafa kansa,shi dama hakan yafiso,bayaso ne kawai yabar
inna da bari bari shi yasa

"Ba wani abu malam,saisu kwana din,duk yadda kayi da ai ne" nan fa suka hau murna
da tsalle dukkansu,don dama haka sukeso,ya zamana ya sadiq zai dauki matarsa da
aslam,shima ya dauki iman din su wuce,su babu dan rakiya ma,tunda gaba dayansu babu
me shan mama a cikinsu.

Tana hanya zafa wajen inna kiran bushia ya shigo mata,ta daga suka gaisa
gaisuwa irin ta aminan juna,suka taba hira suka kuma tsokani juna sannan bushiran
ta shaida mata birthday din hamdan danta,next week,ta godewa Allah da yaran basa
kusa,da sai sun haukatata,saboda dama birthday din suketa jira,kasancewar lameen
bai taba bari an yiwa kowa cikin yaransa ba,ta tayata murna tace kuma za'a kawosu
in sha Allah ko su taho ma gaba daya,sukayi sallama tana tsokanarta daa

"A gaida yallabai baban soyayya" dariya tasake

"Zaiji kuwa"
"Ba daga bakina ba pls bama 'yar haka dashi,kada mutuncina ya zube"
"Saiko na fada" ta katse wayar tana dariya.
Kira ya dinga jera mata a waya bayan gama wayarsu da bushira,yana mota
yana jiranta,da qyar ta baro cikin gidan ta fito,tana shigowa kuwa ya cukuikuyeta
amma a tausashe,ta saki qaramar qara a shagwabe

"Saboda kinsan ke daya nakeson kasancewa dake shine kike jamin rai ko?" Fari ta
sakar masa murmushi na kubce mata

"Idan bakai wasa ba wankan gida zan taho wannan karon ma"

"Saiki shirya dakin xaman mutum biyu"dariya ta qwace mata a boye,tasan tun
haihuwarta ta hudu yace an daina wannan,ya gaji da zaman tuzunrantakar da yakeyi,ta
tsokaneshi kan yayi aure,yace mata saidai tayo masa auren dole idan ta isa

"Ya ake ciki?,kuma ki gayan gaskiya me aka gani?,banda baqin da mukayi yau dama so
nayi ayi agabana kada amin rufa rufa" ya tambayeta sanda motar ke fita daga
gidan,kanta ta kawar gefe

"Abinda dai aka saba"


"Uhmmm....me kenan?"
"Namiji ne" hannunta dake cikin nashi ya matsa,wanda dama ya saba al'adarsa ce,duk
sanda yake tuqi tana gefansa to hannunta cikin nashi yake,qara tadan saki a
tausashe

"Macace in sha Allah" lafiyayyen murmushine ya kubce masa

"Yes!....alhamdulillahi rabbil Aalamin,nima na kusa samun photography din me idon


mage" ya fada yana dariya cikin nishadi,harara mai cike da qauna ta jefa masa

"Idanun nan na qaramin shauqi a kanki iman,saika tara mutum million da wuya zaka
samu daya mai irinsa,yadda kike special haka komai naki yake.....Allah ka san irin
son da nakewa wannan halitta,Allah ka bani tsahon rayuwa tare da ita" murmushi ya
kubce mata,a kullum kalaman da takeji daga bakin lameen,tana tunanin ko daga yanzu
zai daina gaya mata su sun isheta rayuwa.

"Ya Allah.....kaga yadda wannan bawa nake yake kula da baiwarka iman,yake kuma
qoqarin cika burikanta da faranta mata ita da iyalinta,ya Allah kada ka barshi
haka,kayi riqo hannayensa,ka zama ji da ganinsa,ka zama gatansa,ka yalwata kabarin
iyayensa kasa kuma dukka alkhairansa ga jama'ar gari da iyalansa ya zamana
sadaqatul jariya ga iyayensa batare daka rage lada ko daya daga cikin ladan da zaka
bashi ba"

"Ameen" ya amsa yana lumshe idanu,duk da tuqi yake amma sai daya janyota jikinsa
yana buga kafadarta,zai iya cewa babu mace kamar iman duk fadin duniya,addu'ar
datake masa ko mahaifiyarsa iyakarta zatayi masa

"Me dame ya faru wunin yau...." Ya tambayeta yana jifarta da murmushin dako yaushe
yake saukar mata da nutsuwa.

Wannan kusan al'adarsu ce,duk lokacin da suka wuni da daddare kowa yana
baiwa dan uwansa labarin abubuwa masu muhimmanci da suka faru ko ya aiwatar a
wunin,sake rage kaifin muyarta tayi,muruar da take wa lameen hira ko bashi labari
ta banbanta da muryoyin datake magana da kowa,saita tabbatar ta qwatata yadda zata
saukar masa da shauqinta da kuma cikakkiyar nutsuwa,cikin wani irin sanyi ta fara
zayyano masa,yana saurarenta yana lumshe idanu,saboda dadin muryar tata tafi
labarin dadi,cikin zuciyarsa yana tasbihi ga Allah da kyautar iman da yayi masa
halak malak

*ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMEEEEN*👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽


*_Anan na kawo qarshen labarina mai suna BUTULU KUFAN WUTA,,ina fatan kurakuren
dake ciki Allah ya yafe mana_*

*_fatan alkhairi a gareku zafafa customers,muna fatan qananun laifuffuka da kura


kurai da aka samu a ciki zakuyi mana afuwa,Allah ya qara danqon qauna da
zumunci,team zafafa biyar na godiya da jinjina muku qwarai_*

*Inda aka manta ba'ayi conclusion ba ajizanci ne irin na dan adam,Allah ya sadamu
da alkhairi,ya kuma hada fuskokinmu da alkhairi a rubutu na gaba*

*Subhanakallahumma wabi hamdika,ash hadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'a


tubu ilaika*👏🏽👏🏽👏🏽

You might also like