Wa yasan gobe cmplt
Wa yasan gobe cmplt
Wa yasan gobe cmplt
Zaune take dirshan bisa carfet din dake mamaye da qaton dakin nata,ta tanqwashe
qafafunta yayin data tallafe kumatunta da dukka tafin hannunta,lokaciguda kuma ta
zubawa food flask din abincin dake gabanta ido,a zahiri idan ka dubeta zakayi
tsammanin flask din take kallo sai dai sam ba haka bane zuciyarta da ruhinta sun
lula wata duniya ne ta daban,da yunwa ta shigo gidan saidai sam ta kasa sa koda
loma guda ta abincin a bakinta,cikin kwanakin tana cikin wani yanayi wanda ta
kirashi da jarraba ko musifa dake tunkaro rayuwarta
Wannan ne karo na hudu a rayuwarta da idaniyarta tayi tozali dashi saidai ya zame
mata masifa,tun daga ranar da ta dora idonta akansa wani baqon lamari ya ziyarci
zuciyarta da gangar jikinta,zata iya kiran lamarin da zazzafan so wanda ya zamto
mata tamkar harara a duhu,dalikinta na fadar haka kuwa shine wanda zuciyarta ke
budurin a kansa baisan Allah yayi ruwan halittarta ba a doron duniyar subhana,tayi
kukan tayi takaicin yadda zuciyarta tayi mata rashin adalci ta hanyar kamuwa da
soyayyar wanda batasan koshi waye ba?,meye sunansa?,a ina yake?,taja doguwar ajiyar
zuciya sannan ta jawo flask din ta bude da niyyar taba wanu abu a ciki kota tsira
daga fadan umminta,ilai kuwa tana loma ta biyu taji sallamar ummin tana daga tsaye
ta dubeta tace"yanzu fadila tun shigowarki kika damemu da zancan jin yinwu amma
kusan aqalla awa guda banga wani abun kirki da kika ci ba?,tadan yamutsa fuska tace
wlh ummi da yunwar na shigo amma kinga na kasa ci"ummi tace ,haka dai kika iya
kullum kamar wata qanqanuwar yarinya sai anyi fama dake akan cin abinci ko?,yayi
miki kyau ai kinsan ulcer dai ba gidanku daya ba bare kice idan ta kamaki zata miki
sassauci,tayi dan murmushi tace kiyi haquri ummi insha Allahu yanzu zan kawo miki
flask din empty,ummin tadan harareta tace ai jikina kunne ne,fadila tadan qumshe
dariyar da keson subuce mata,har takai bakin qofa ta juyo tace"af na manta ki
shirya yanzun zaki kaini gidan alh salim kwana biyu su shiru muma shiru"tadan sosa
kanta dake a tsefe saidai ta tufke shi da band tace anya ummi zan gane ma
gidan?,ungo wannan ja'ira cewar ummi da ta watsa mata daquwa yace"nima in banda
abbanku yace in tafi dake zaki maku siyayyar kayan make up da da driver zanyi
tafiyata"tayi ko saurin miqewa tace yauwa ummi dama jiya nayi masa zancen
kayan,tace ato minti goma ki sameni ina falo ina jiranki,ta amsa tana qoqarin shiga
toilet dinta dake manne da bedroom din
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tsaf ta shirya cikin abaya baqa mai sulbi saqar qasar dubai wadda aka mata ado da
jajayen dutsina masu sheqi,ta nannade tulin gashinta tayi a cuci dashi sannan tayi
rolling da wani dan kyakkyawan jan mayafi,simple make up tayi amma kasancewarta
tana da wani sassanyan kyau sai ta fito gwanin sha'awa,ta daura agogo na fata ja
sai plate shoe da tasanyawa qafarta mai ja ne mai baqaqen igiyoyi,wayar hannunta
kawai ta dauka hade da key din motarta ta sake kallon kanta a madubi,cikin
zuciyarta ta qaryata masu cewa abu mai duhu baya giwa baqi kyau,duk da cewa ita din
ba baqa bace irin matan nan ne masu launin fata(chaculet colour)wasu kuma suce
black beauty,fatarta batayi haske can ba kuma kai tsaye ba zaka kirata baqa ba
tamkar irin black american haka yanayinta yake,fadila nada wani irin kyau mai sanyi
wanda tashin farko bazaka gama tantance kyawunta sai kuna tare wato qananun kyau ne
da ita,ba abu mafi daukan hankali a tare da ita irin qirar jikinta cocacola
shape,idanunta manya masu dauke da gazar gazar din gashi wanda hakan ke taka
muhimmiyar rawa gun tafiya da zuciya gami da ruhin mazaje da dama,goshinta kam irin
qananun Gashinnan ne kwance luf wanda ko tayi dauri basu boyuwa,muryarta a sanyaye
take cike da wani sirri wanda idan tayi magana take janye hankalin jama'a da
dama,fadila tako ina Allah ya bata zubi da tsari wanda yasanya take burge mutane ba
maza kawai ba hatta ga yan uwanta mata ma,sai dai gwanar miskilanci ce,sam magana
bata dameta ba,tafi ganewa tayi karance karance maimakon zaman tadi,fadila yanzu
haka daliba ce a jami'a bayero kano tana karantar mass com,duk da cewa abbanta yayi
mata sha'awar karantar medicine ganin cewa mass com bana mutum ne mara son magana
ba amma data nuna masa tafi sha'awar mass com din sai ya barta da zabinta
kasancewarsa mutum ne mai sauqin kai,sai ya maida zabin nasa kan 'yar uwarta
farida,alh abbas ahmad shine mahaifin fadila dan kasuwane mai rufin asiri,domin
Allah ya bashi wadata irin wanda ko wane dan adam ke fatan samu ba abunda aka nema
a gidansa a ka rasa,asalinsa bafulatanin bauchi ne,yana sana'ar sai da shaddodi da
yadiddika cikin kasuwar kwari,yakan tura babban dansa wasu lokutan china ko india
domin shigo da kayan su kuma zuzzuba a shagunansu dake cikin kasuwar,ya auri
mahaifiyarsu haj amina a maiduguri cikakkiyar shuwa ce wadda Allah ya qaddari
aurensu tun bayan da yayiwa manemanta dintinkau a zuciyarta,anan garin kano suka ci
gaba da zama tunda anan kasuwancin nasa yake,haihuwar farko suka sami da namiji
inda yaci sunan ahmad,baiyi wani tsawon rai ba Allah ya karbi abinsa,shekara daya
tsakani suka sake samun wani yaron aka mayar masa da sunan ahmad din,daganan
haihuwar tayi musu dif tamkar aun daina,wanda a tsakanin har amina ta soma
fuskantar qananun maganganu irin na dangin miji duk da cewar ba a kusa suke ba,sai
bayan shekaru goma Allah ya sake qaddara musu samun wata haihuwar,ta haifi 'yar
kyakkyawar budurwa taci sunan fadila,shekara biyu tsakani Allah ya sake kawo wani
rabon nan ma mace ta haifa aka sa mata farida,kasancewar fadila mara saurin girma
sai suka taso kai daya da farida idan ka gansu zakayi tsammanin twince ne don
kamarsu daya saidai farida tafi fadila garin jiki da kuma farar fata,tasowarsu tare
yasanya komai daya ake musu hatta makaranta tare aka sanya su,sai da suka shiga
jami'a ban bancin course ya raba su,shekara shidda da haihuwarsu umminsu ta sake
haihuwar da namiji inda aka sa masa muhammad tun daga lokacin kuma haihuwar ta musu
bankwana
Babban wansu ya ahmad yayi aure tuni da matarsa anty hafiza harsun samu albarkar
twince duka mata ,rayuwar gidan rayuwa ce mai ban sha'awa cike take da son junansu
suka taso girmama juna da qaunar juna,sai dai tsakanin fadila da farida akwai
tsokana fada da wasa na tsakanin sakuwa da sakuwa sai dai duk da haka farida na
respecting din fadila

S.A huguma
  
[10/16, 12:18 PM] Salma:
Wa yasan gobe?

2 2
▶2⃣
Sun fito kenan daga gidan farida ta shigo da motarta layin (da yake ya ahmad yayi
qoqari bayan kammala secondry sanda suka samu admission a jami'a ya sai masu yan
qananan motoci rio,yace tunda fadila baqace ta dauki fara farida kuma ta dauki
marun)farida ce ta soma jan burki ta tsaya don tasan halin mutuniyar zata iya
shigewarta tace"ummi ina zaku je?" "Gidan alh salim kwana biyu haduwa tayi wuya
shine zanje dubasu"cikin tsokana ta kalli fadila tace "wlh ummi gwara da kika
banbaro kifin rijiyar nan kika fito da ita inaga tafi shekara dubu bata je gidan
uncle abba ba"fadila ta watsa mata harara tace"ni sa'arki ce"ta qyal qyale da
dariya tace sorry yaya fadila"fadila tayi saurin yiwa motar key suka wuce,suna
tafiya a hanya suna hira jefi jefi da ummi abinsu gwanin sha'awa har suka isa
gidan,gidan na jerin gidajen kundila housing estate dake maiduguri road,gidane irin
na masu naira da suka ci suka tada kai,mai kula da qofa ya dage masu wakeken get
din gidan cikin fara'a suka shige kasancewar akwai sanayya mai yawa tsakaninsa da
ummin
Ummi ce a gaba fadila na binta a baya har suka isa tafkeken falon gidan ,haj
maimuna na zaune bisa luntsuma luntsuman kujerun dake kewaye da falon kallo suke
ita da yaranta sumayy da rabi'ah,sallamar su ita ta dauki hankalin su suka juyo
hade da amsa musu,haj maimuna ta miqe cikin girmamawa tana cewa lale marhabin haj
kune tafe da yammarnan ,ummi tayi murmushi tace ai kuwa dai kam"ta sake fadada
fara'arta tace sannunku da zuwa ai......,maganar haj ta katse ta kama baki
tace"a'ah yarannan yau yaushene?,ta fadi tana kallon fadila,dukkansu sun fahimci me
take nufi suka qyal qyale da dariya suka ce momi yau laraba,ta gyada kai tana cewa
lallai ba shakka ta bawa ranar samu,wlh haj bazan iya lissafa yaushe rabon fadila
da gidannan ba,"ummi tace"hmmmm to wlh yauma da qyar na banbarota don taji zamu
biya store ne zata kwaso kayan make up shine ma qarfin biyonin"momi ta sake gyada
kai cike da mamaki tace lallai yau mun tashi da bismillah haj ku zauna mun tsaya
zance na barku a tsaye,dukkansu suka zauna sannan suka fara gaisawa fadila ta gaida
momi a kunyace ,ta amsa mata tana cewa"kyaji kunya mana mara zumunci ,sam farida ta
fiki zumunci "sumayya dake kusan sa'a ga farida tace"wlh anty fadila faridammu ta
fiki zumunci"fadila ta dan harareta da taga idonsu ummi baya kansu tace"ta dai fini
qafar yawo yaufa sai da zamu fita ta dawo tun azahar wai ta tafi gidan qawarta
"sumayya tace "to ai zumunci taje"fadila ta dan tabe baki tace"ke ni qyaleni yawon
farida yafi qarfin qafata ko ina a kano kika kwatanta mata ta sani "sumayya da
rabi'ah sukai dariya suka ce "kai anty don dai ke bakison fitarne shi yasa kikace
sister ta fiya yawo"
Hira suke suka tsinci qanqanuwar muryar yarinyar na sallama ,ta saki hannun wanda
ya riqota da gudu ta fado falon,momi ta cewa wanda ya kawota din sannu isah,yace
yawwa haj ya juya ya fice,rabi'ah tace oyoyo ifti na,muga kitson,da gudu ta fada
cinyarta ta janye hular da ka rufe mata kanta da ita tana nuna mata,kalbace mai
kyau twisting wadda aka lafe jelar ta da beads masu kyau,kasancewar yarinyar nada
tsawon gashi sai ta kwanta lub tayi kyau har dokin wuyanta,tace anty sumy tayi
kyau"sumayya tace gsky qawata ba magana "ta bata hannu suka tafa,ta miqe tayi gun
momi ganin ummi yasata duqawa ta gaidata,ummi ta amsa fuskarta dauke da fara'a momi
tace"har yanzu fushi ake kenan da ni shi yasa ni baza'a nuna min kitson ba"cikin
magana irin tq shagwababbun yara tace "ba cewa kikayi ayimin mai zafi ba"sai kuma
ta juya ta koma gunsu sumayya tana bata lbr,ummi ta kalli momy tace"wai iftihal din
Aliyu ce wannan?"momi dake tsiyayawa ummi lemo a cup tace"itace mana kinga yadda ta
girma ko?"ummi ta jinjina kai tace"ba shakka gata nan kuwa masha Allah,ina zaton ai
ba zata wuce shekara bakwai ba ko?"momi tace "idan watan nan ya mutu sabon wata ya
kama yakai ashirin zata cika shida",sai bayan sunyi magariba suka fito,tuni iftihal
ta maqale wa fadila domin cikin qanqanin lokaci suka saba,don fadila ba daga baya
ba gun son yara,bare iftihal yarinya ce kyakkyawa ga wayon tsiya,har bakin mota
suka rakosu sumayya na yaba kyawun motocin nasu,fadila tace idan kina so ki amsa
mana,sumayya ta kama baki tace rufamin asiri kada kisa yaya aliyu ya babbalani kina
ganin abba zai sai mana ma ya hana wai har yanzu bamu da hankali sai randa muka
qara nutsuwa?fadila tayi dariya tace "sai kace yau aka haifeku""kema dai kya fada
sister cewar rabi'ah,dai dai nan ummi da momi suka qaraso momi ta miqawa fadila
baqar leda tace"to ga kayan kwalliyarnan aje ayi tayi ana samo mana sueukai"a
kunyace ta amsa tana mata Godiya,momin tace to sai wata shekarar kenan,fadila ta
sadda kai qasa tace"a'ah momi insha Allahu zaku dinga ganina"Allah yasa inji
momi,ummi tace"wai ni kuwa ina Aliyu ne,na kwana biyu rabon da na ganshi fa"fuskar
momi ta canza zuwa yanayin damuwa tace"hmmmm,mtsw,ke dai bari kawai haj kwanan nan
zaki jiyomu da shi,Aliyyu fir ya guji aure yaqi fidda mace yayi aure,yafi ganewa
kasuwancinsa kawai nayi har na gaji hakanan abbansa kullum zancen kenan amma yaron
nan sam yaqi mai dakansa"ummi tace"addu'a kawai zaku ci gaba da yi masa Allah ya
kawo ta gari kada a kuma komawa 'yar gidan jiya a bata goma daya bata gyaru ba"momi
ta gyada kai tace hakane,Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi"tace amin
Daqyar iftihal ta rabu da fadila harsai da ta laluba cikin motarta ta samo mata
chaculet sannan ta yarda ta barsu suka tafi,basu tsaya ako ina ba sai a shop rite
dake ado bayero mall,ta nufi parking space ta gyara tsayuwar motarta sannan ta
kashe,ummi ta zaro kudi cikin jakarta ta miqa mata,tace maza kiyi da jiki ki
fito"tasa hannu biyu ta amshi kudin tana qoqarin maida murdin motar ta rufe ne ummi
tace"saura ki kwaso kayan zaqi da sanyi ki koma gida ki guji maqiyin naki
abinci"tayi murmushi kawai tace baza'a siyo ba ummi ta rufe motar ta shige,cikin
nutsuwa take daukar musu abinda tasan suna da buqatarsa ita da farida har ta
kammala,har zata nufi kanta ta tuna bata dauki turarenta ba blue lady,cikin sauri
ta koma,hankalinta yatafi ga turarurrukan tamkar ance ta kalli gefanta,tsaye yake
shima yana zaban nasa kalan,yana sanye cikin shadda dinkin tazarce blue Black ce ta
haska farar fatarsa matuqa,ta gefan tana iya hango qaya taccen sajensa dake kwance
luf bisa tsararriyar fuskarsa,ga tsinin hancinsa nan yayi das qasan farin qal din
glass dake bisa fuskarsa,kyakkyawan idonsa wanda gashin idon suka yiwa rumfa suna
juyawa cikin farin glass din nasa yan karanta rubutun dake jikin kwalin
turaren,kansa ba hula sai sumarsa dake kwance an dan saisayeta,ya zari turaren
kwali uku cikin sassarfa ya juya yabar gun,samun kanta tayi da bin bayansa zuwa
inda zai biya kudinsa ,kusan tare suka biya sai dai sam shi bai lura da ita ba ya
juya ya fita ta sake bin bayansa,tafiyansa ma abar kallo ce tamkar wani saraki haka
yake takawa,daga nesa tadan tsaya a harabar adana motocin don batason ya
ganta,cikin aljihunsa yasa hannu ya zaro key ya bude wata baqa sidiq din mota qirar
range rover ya shiga yayi mata key ya jata da gudu ya bar gun,jan ajiyar zuciya
tayi gamida lumshe idonta hadi da dafe goshinta da tafin hannunta"inna lillahi wa
inna ilaihir raji'un allahumma ajirni fi musi bati wa akhlifni khairan minha"abunda
take ta nanatawa kenan,wannan wace iriyar musibace zuciyarta ke son jefata ba gaira
ba dalili?,ta bude idonta ahankali jikinta ba laka ta soma lalubar inda tayi
parking
Cikin motar tayi dif zugi da radadi take ji,ba abunda zuciyarta keyi sai zillo cike
da dimbin qaunarsa,shi wa?,ita kanta bata sanshi ba,ummi nata mata hira tana cijewa
tana amsa mata har suka isa gida,farida na falo ta baje kolin takardu da alama
assignment takeyi,batason ta dameta da hira don haka tadan daure fuska,itama
faridan data fuskanci hakan bata ce mata komai ba illa sannu da zuwa ya kuka
barosu?,ta amsa mata ta haura sama inda dakinsu ita da farida yake,ta watsa
siyayyar tasu kan gado zuciyarta cunkushe ta cire kayan jikinta ta fada toilet da
niyyar sakarwa kanta ruwa ko zataji sanyin zuciyarta
Muje zuwa
✍🏻
S.A.M huguma
[10/16, 12:19 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 
WA YASAN GOBE?
▶3

Lotion kawai ta shafa bayan ta fito ta feshe jikinta da body spray ta lalubi rigar
bacci doguwa har qaurinta ta zura don bacci take da muradin yi, ta daura zani a
sama ta sanya hijabin sallarta ta gabatar da sallar isha'i, ta dora da shafa'i da
wutiri, bayan ta shafa addu'o'inta tabi lafiyar gado, a maimakon bacci yazo mata
sai tunani ya mamaye gurbinsa, ba zato ta tsinci kanta da zubarwa kanta da kanta
hawaye na tsananin tausayin kanta, a cikin jikinta da zuciyarta take jin ta shiga
halin tsaka mai wuya, zuciyarta na bulayi da lalube cikin duhun son wanda bai ma
san tana yi ba, farida ta shigo dakin hade da sallama hakan ya sanyata saka hannu
tana goge hawayen cikin dabara don bata son faridan ta gani, faridan tadan kalleta
jikinta yaso ya bata tamkar yar uwarta na cikin damuwa, don haka jikinta sai ya
danyi sanyi ta shigo ne da niyyar tsokana don flask guda ummi ta ciko da abinci
tace kada ta sauko da shi sai ta cinye Farida ta ajjiye flask din a gefan gadon ta
janyo dressing chair ta zauna tana fuskantar fadilan tace"sister lafiya naga kamar
fuskarki ta nuna kamar kina cikin damuwa? ,ta qaqalo murmushi sannan tace"ba abunda
ke damuna just na gajine fitar nan da nayi"farida ta girgiza kai ba don ta yarda ba
tace"ok,to ga abincin ki nan ,ummi tace " kada ki sauko mata da shi sai kin cinye
tana daga kwancen ta zubawa flask din ido tace"har gabana ya fadi wlh, ina zan kai
wannan abincin? ,farida ta qyalqyale da dariya tace"ni dai yar aikece kuma na isar
da saqo,qafafunta tayi saman tiles din daya mamaye da qaton dakin nata
Ta daura zani a sama ta sanya hijabin sallarta ta zari flask din, farida ta kalleta
tace " a'ah ina zuwa? "Ba tare data kalleta ba ta juya tana shirin fita sannan
tace"jirani ina zuwa"farida ta bita da kallo tana dariya ciki ciki ,ta qofar baya
fadila ta fita ta bulla bakin get din gidan,kai tsaye ta nufi gun idi mai gadinsu,
mutuminta ne dama da hangota kuwa ya miqe yana cewa " uwar dakina"miqa masa flask
din tayi tace"yi sauri ka juye idi"cikin qanqanin lokaci kuwa ya juye abincin ya
bata flask din yana zuba godiya Ta tarar da fadila na waya da alama da saurayinta
take, ta koma gefan gadon ta zauna tana kallon faridan har ta kammala tsaki fadilan
tayi, farida tayi murmushi tana kallon flask din da fadila ta dawo dashi don tasan
kwanan zancan, bata son idan zatayi waya tayi mata a dakinta,fadila ta harareta
tace"bana gaya miki ki daina shigomin daki idan zaki shirmen wayarki ba? ,tace tana
gyara kwanciyarta akan sofa qwaya daya dake dakin " sorry anty na"tana dan murmushi
tace kiyi haquri
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tun bakwai na safe take a kitchen dama haka al'adarta take, idan bata da lecture to
Itace mai shirya musu breakfast haka da rana ko da daddare,girki yana daya daga
cikin hobby dinta hakan ya sanya ta zama gwana ta fannin abubuwan ci da na sha,
Awa daya da rabi ta kammala komai ta koma dakinta tayi wanka ta shirya kasancewar
tara da rabi tana da lacture,dakin ummi ta shiga bata nan sai muhammad ta tarar
yana kan gadonta yana bacci,dala masa duka tayi tace"tashi malalacin banza eight
thirty amma kana bacci ina school din?"cikin magagin bacci yake murza ido yace"wlh
nayi wanka bacci ne ya daukeni"tace"oya tashi ka shirya idan zan wuce na sauke ka
na baka eight minute"da sauri kuwa ya duro daga kan gadon ya shige toilet
Bangaren abbansu ta wuce tare da diba masa breakfast dinsa ta tafi masa da shi,yana
zaune kan kafet din falon hannunsa dauke da jaridar daily trust,haka yake a
al'adarsa bayan ya dawo a masallaci yakan yi azkar da tilawar qur'ani idan gari ya
dan sha kuma sai ya karanta jarida kafin ya fita aiki,fadila ta shigo da sallama,
ya masa yana dubanta fuskarsa dauke da murmushi,ta dire kayan abincin ta rusuna
tana gaidashi ya amsa yana fadada fara'ar shi yace"sannu fadila da qoqari hala
yauma anada da lacture din safen"kanta a sunkuye tana qoqarin hada masa kunun
shinkafa da yasha madara tace"eh Abba",ummi ce ta fito daga bedroom din Abban
hannunta dauke da doster da alama goge goge ta gama,fadila ta gaidata tana qoqarin
tashi tace"abba zan tafi"ya dubeta sannan yace"ai banga kin ci komai ba haka zaki
tafi?""abba zan karya a capteria idan na..........
Ummi tayi saurin katse ta da cewa"yi mana shiru wlh abbansu idan taje ma bacin take
ba farida ai ta gaya min wai ba zata iya cin abinci a waje ba,wannan yarinya na
rasa meke damunki anya lafiyarki qalau kuwa?",abban yayi murmushi yana dakatar da
ita"dakata umminsu,fadila lafiyar ta qalau,kin manta yawon asibitin da muka dinga
yi da ita tun tana qarama?,haka dai halittarta take"ya juya ga fadila yana tura
mata cup din da ta hada masa kunun yace"maza zauna kici wani abu kada ki qara bata
ran umminki kinji ko?"tamkar zata sa kuka😟 ta zauna tana cewa"to abba"yaci gaba da
cewa"gashinan fadila tafiki abin arziqi shi yasa ta rainaki tana ganin kanku
daya,ummin tace sai rawar kai da gwanintar yin girkin amma saidai wasu su ci
mata,abban yayi murmushi yana kallon yadda take tura abincin kamar magani😣
Kafin ta kammala muhammad ya shigo don haka abban ya sallamesu suka fita tare,suna
mota muhammad ya dameta da surutu,ta daga masa hannu ✋🏻hadi da cewa kaga malam bafa
aku na dauko baidan kuma kai aku ne ka gayan"ya qyalqyale da dariya😂 yace"anty
ke dai ba dama mutum yayi hira dake sai kice ya dameki shi yasa yaya farida ke
burgeni ke halin ya ahmad kikayo kun fiya kwafsawa wlh,ta harareshi sannan tace"ai
da itan da kai duk zamuce ta tadda mujemu idan mutum baiyi surutu ba baya
burgeku,kada Allah yasa mu burgekun muyita kwafsawar,idan ka qara magana kuma sai
na saukeka anan" take ya rufawa kansa asiri yayi shiru🤐
Taso makara saboda ajiye muhammad da tayi don ita ta saba da wuri take zuwa don ta
samu sit din gaba,bata da wata qawa bare ta tarar mata hakan ya jawo batayi parking
din motar ta daidai ba ta nufi ajin cikin sauri
Lacture din ta daukesu awa uku har da mintina,kanta ya dauki chargy sosai,don haka
da fitowarta ta samu wani guri dake nesa kadan da ajinsu bashi da yalwar jama'a
sosai yafi kusa da inda suke ajjiye motocinsu idan sunzo,gurine mai wadatar shuke
shuke ita kuwa ma'abociyar son tsirrai ce
[8/8, 3:24 PM] LOADING......
gun na burgeta saboda son tsirran da take dashi,tamkar a cikin iska ta ke jiyo
qamshinsa,gabanta ya tsananta faduwa,ta gefan ta ya wuce saidai bayansa kawai take
iya gani,ahigar suit ne a jikinsa masu dan karen kyau da sheqi,kayan baqaqene sai
tsintsiyar hannunsa da ta gani wadda yake daure da agogon fata baqi,gefansa wani ne
ke biye da shi riqe da takardu da brief case,sam sai ta kasa dauke idanunta daga
kanshi,hakanan gabanta yaci gaba da faduwa cikin zuciyarta take fadin inna lillahi
wa inna ilaihir raji'un"har ya danyi nesa da ita sai taga ya waiwayo,cikin wani
irin sauri ta dauke kanta tayi wani sashen da shi zuciyarta kamar ta tsinke ta
fado,ganin yayi gaba tayi hamdala da Allah yasa bai lura da ita ba,tana tsammanin
jikinsa ne ya bashi ana kallonsa,a sace taci gaba da kallonsa har ya bacewa
ganinta,taja ajiyar zuciya sannan ta dauke idonta daga kallon hanyar ta jawo
jakarta ta zuge ta fiddo da wayarta tana danne danne,ta doshi kusan minti aahirin a
gunbtana hutawa sai sannan ta tuna zata fa gidan ya ahmad,da sauri ta miqe tana
gyara yafen gyalenta,atamfa ce ajikinta dinkin riga da skirt ne,atamfar England ce
dark green mai ratsin yellow,sai mayafinta da takalminta agogo da jakar hannu duk
yellow,fadila ba qarya ta iya daukan wanka don duk munin atamfa takai aka mata
dinki ya saka komai kushe da hassadarka baka isa kace batayi kyauba haka Allah ya
bata wannan baiwar,tana tattare komatsanta tana sanyawa a jaka taji ana kwada mata
kira,a nutse ta dago tana neman daga ina wannan kiran mafarautan ke fitowa?,wata
class mate dinta ce binta auwal fadila taci gaba da binta da kallo har ta
qaraso,"fadila abbas yaufa kinyi tabargaza"abinda ta soma cewa kenan,fadila
tace"kamar ya fa?"tana dubanta tace kinyi wrong parking kin toshewa A.s mai tama
hanya"ta sake dubanta cikin rashin fahimta tace"waye haka kika bi kika rude?'binta
ta zaro ido😳 tace"kar dai kice min baki san a.s mai tama ba,hadadden guy din da
duk nigeria bama kano ba ansan da zamansa"fadila ta dakatar da ita ta hanyar
cewa"na gode"taci gaba da mayar da kayanta jaka
Iya dube dubenta ba wanda ta gani sai mutum daya,a tsammaninta idanunta ke mata
gizo,sai dai har ta qaraso gun shi din dai ta gani,yana tsaye hannayensa harde a
qirjinsa fuskarnan a murtuke,ta qaraso ne da niyyar bashi haquri sai dai lura da
irin kallon qasqancin da yake mata mata yasa tayi banza da shi kai tsaye ta nufi
motarta ta bude,ta zauna a seat din tana qoqarin jan murfin ta rufe taji an dafe
murfin motar,ta dago ta dubeshi,yana tsaye yana mata irin kallon dazun,cikin
qasaita taji yace"baki da ladabin bada haquri ga wanda kika aikatawa laifi?"duk da
yadda zuciyarta ke sake ninqaya a zuciyarta,muryarsa mai sanyi ta kwanta a
zuciyarta,amma ta dake gami da cewa cikin zuciyarta"duk da dumbin qaunar da nakeji
taka a zuciyata hakan bazai sa na bada girma da jan aji irin na 'ya'ya mata,ta
dauke kanta sannan tace"ai shi wanda akawa laifin baisan darajar bil'adama ba"ya
saki murfin motar hadi da watsa hannayensa yace"ok,ba laifi"ya saki murfin
motar,cikin wata iriyar gaggawa taga ya amshi key din tasa motar daga hannun wanda
suke tare ya bude motar sa ya shiga cikin gwaninta ya take motar ya kurda ya matse
motar fadilan ta yadda itama bata isa ta fita ba harsai da ya gogeta,ya kashe motar
ya zare maqullin ya rufe motar ya fito yana cilla maqullan yana cafe wa ya danyi
tsalle ya haye bayan motar ya zauna,da hannu ya kirashi yadan yi masa rada ya amshi
tak ardun hannayensa shi kuma ya juya da sauri ya bar gun
Sarai fadila ta fahimci abunda yake nufi saboda haka ta zaro wayarta ta nemi number
farida ta kirata"hello farida kin shigo school?"tace"eh ya akayi?""kizo ina parking
space ki daukeni mu wuce"farida tace"me ya sami motar ki?""kinga idan zaki zo kawai
kizo malama""ok sister gani nan"
Cikin 'yan mintina sai ga farida horn tayi mata ta miqe ta fito ta kulle motar ta
gabansa ta shige ta nufi farida,dai dai lokacin ta jiyo saukowarsa daga bayan
motar,wata yar qaramar mota ce tayi parking a gabansa kusan tare suka shige
motocin,ta madubin motar farida suka hada ido ta sakar masa tsaki hadi da murguda
baki,cikin zafin nama ya balle murfin motar ya fito da sauri tacewa farida"yi sauri
ki bar gurinnan,tamkar kuwa tasan meke faruwa ta figi motar ta bar gun
Muje zuwa
  
[10/16, 12:21 PM] Salma:
Wa yasan gobe?

4 4
▶4⃣
Sai da motar ta saitu akan titi sannan tace mata"gidan ya ahmad fa zamu"ok" inji
farida,"sister wai me ya faru naga kamar wadda aka biyo a guje?"taja tsaki
tace"wani dan rainin hankali ne yaso wulaqantani bai san bana daukan wulaqanci
ba"ta bata lbr yadda sukayi da shi akan toshe ma juna hanya da sukayi,me farida
kuwa zatayi idan ba dariya ba,"kefa 'yar wulaqanci ce shi yasa ban fiya saki cikin
lamarina ba,a yar madaidaiciyar harabar gidan sukayi parking,kai tsaye suka nufi
falon gidan,ba kowa cikin falon da alama matar gidan na ciki don haka suka dinga
kwada sallama,daga kitchen matar gidan ta fito anty hafiza kenan kyakkyawar
bafullatana,tana ganinsu ta saki fara'a😊 cikin barkwanci tace"lallai yau baquntar
tamu ce"suka saki dariya😀dukkaninsu suka gaidata cikin girmamawa ta amsa musu
cikin kulawa tana tana tambayarsu ummi,suka ce tana lpy tana gaidata,fadila ta zaro
packet na chaculet tace gashi injita a baiwa twince,wai ni ina suke nema
anty?""tace yau ai ranar school ne suna can amma suna hanya don bala ya tafi dauko
su,""na manta wlh"ta fada tana qoqarin kwanciya bisa doguwar kujera"anty hafiza
tace"ah ya haka ina murna kuku tazo kuma naga tana neman bin lafiyar kujer?"fadila
ta dan murmusa 😊tace " anty yau saidai amin afuwa yau kasala nake ji""na
miki"inji anty hafiza,farida dake canza tasha a t.v tace"qyaleta anty muje na
canjeta yau tsokano fada tayi sauran kadan taci na jaki badan Allah ya kawoni na
ceceta ba""tab wucenan wlh wa ya isa yayi gangancin taba mana ita?😳""fada mata
dai anty😏"cewar fadila,suka shige kitchen nan suka barta a falon
Gyara kwanciyarta tayi don taji dadin yin tunaninsa,shi wa?,idan bata manta ba A.S
mai tama binta tace da ita,A.S mai tama ta shiga maimaita sunan ita da
zuciyarta,"to me A.S mai tama take nufi?"A dai duk inda aka zaga farkon sunansa
ne,to ahmad ne ko ko abubakar ko abdul?,oho itama bata sani ba,wani murmushi ne ya
subuce mata😊 sai tunaninta ya dawo kan abinda ya faru tsakaninta dashi
dazun,sassanyan muryarsa ta dinga yi mata amsa kuwwa a kunnenta,kyawawan idanunsa
yanayin zubinsa da tsarinsa,sai ta tuna sanda ya fito a fusace lokacin data murguda
masa baki ta harareshi,nan ma dariya ce ta subuce mata,"lafiya kuwa?"ta tsinci
muryar farida na tambayarta,ta hade rai tace"lpy lau me kika gani?"farida ta dan
tabe baki tace"hmmm tun dazunfa kike murmushi har da dariya ke kadai kamar wadda ta
fara soyayya"da sauri fadila ta kalleta tace"lallai yarinyar ni kikewa wannan
titsiyen?to gyada na zama na soye qarewar soyayya"anty hafiza dake zaune saman
kujera bata sa baki ba sai yanzu tace"um um yaya fadila wannan fa sign ne na
falling in love😜"fadila ta miqe daga kwanciyar tana cewa"kai anty,please kada ki
biyewa shirmen farida,ita 'yar sa ido ce komai ta gani idonta na kai,kuma sai ta
sanya ma question mark😏",ta gyada kai sannan tace " alright idan tayi wari
maji,Allah yasa alkhairi ne""amin amma ba abinda zaiyi wari ma anty",nan gidan suka
wuni har 'yan biyu suka dawo suka yini tare da su,suna son yaran sosai ko dan su
kadaine jikokin gidan nasu,sai bayan magariba sukayi sallah sukaci abinci har yaya
ahmad ya dawo ya tarar da su,bayan sunyi shirin tafiya ne ya ahmad ya baiwa ko
wacce 4000 anty hafiza kuma ta basu turarurruka.
to daren ranar sam fadila bata samu bacci ba,kusan kwana tayi tunanin A.S
maitama,duk da ta danji dadi don aqalla tasan yanzun yasan da fuskarta a
duniya,koda bazai iya shaidata ba bare tana tunanin mawuyacine ace yayi saurin
manta ta ko dan irin karon da suka yi,har washegari da taje school bai janye motar
tasa ba,sun dauki aqalla sati guda a haka sannan taje ta tarar ya cire,a gida tace
ne kawai tana tana garage ana duba mata ita
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin wannan yanayin suka soma attachment,ranar laraba aka turasu domin tattaunawa
da wani fitaccen dan kasuwa,ita da abokiyar karatunta ne hafsat sai wani ma'aikacin
gidan radion khalid da zasu tafi tare qarfe hudu na ranar larabar.
cikin yellow din atamfa ta shirya mai zanan blue din qananun taurari,skert ne rafa
da riganshi wanda dinkin yayi mata cif a jikinta kamar don ita aka qera atamfar,ta
maqala qananun fashion na dutse masu kalan blue,ta daura dan siririn agogo na
fata ,qafanta blue din hill shoes ne mai madauri sai mayafi data yafashi a kafada
bayan ta soka daurinta wanda ya fito da dogon gashinta ta qasan daurin,jakarta ta
dauka 'yar madaidaiciya wadda ake maqaleta a gwiwar hannu ta feshe jikinta da
turaren shamsul imarat,shigar ta haska fatarta sosai ta fito dagwas da ita,farida
dake nade a tsakiyar gadon fadilan tana charting ta dago ta dubeta"gsky yaya fadila
kinyi masifar kyau,tsiyar abun daya da baki kula kowa,sai ance anasonnki kuma ki
kama mita bayan laifinki ne saiki yi shiga ta janye hankali kuma kice ba wanda ya
isa ya kalaki"banza tayi mata ta dauki wayarta dake kan dressing mirror ta
fice,farida ta dan daga murya yadda zata jiyota tace"a dawo lpy antyna Allah ya
hadaki da mannau ya biyoki har gida😜"bata dai ce mata ci kanki ba ta wuce dakin
ummi don tasan a wannan lkc tana daki tana azkar,daga bakin qofa ta tsaya don ta
kusa makara tace"ummi zan tafi""to Allah ya tsare hanya ki kula sosai kuma kuna
kammala abinda kukaje yi ki taho gida kada ki yadda kiyi dare a waje"tace insha
Allah ummi",acan gidan radion suka hadu,bata shiga ba ta yiwa su Hafsa waya su fito
su wuce don a motarta suka tsara za suyi tafiyar,Hafsa na zaune a baya yayin da
khalil ya shige gaba,tsaf fadila ta gama karantar manufarsa saidai tayi banza da
shi tamkar bata fuskance shi ba,tun zuwanta gidan yake rawar qafa a kanta saidai ya
kasa furta mata kamar sauran maza da yawa,tana da wani irin kwarjini ne a idanunsu
ita sam baya burgeta,ya fiya surutu shi yasa sam bata son ko aiki ne a hada ta da
shi,kamar yanzun ya takura mata sai zuba yake shi ala dole sai ya burgeta,Hafsa na
baya tana ta tuntsira dariya don tasan halin kayarta sarai,daqa qarshe c.d plate
ta dauka tasa sannan yayi shiru
A hankali suke binkwatancen har suka gano gurin,qaton get din gun aka bude musu gu
ne a tsare ahankali aka dinga nuna mata inda zata bi har taje inda aka tana da don
ajiyar motoci tayi parking suka fito,ta jingina jikin motar tata tana qarewa gun
kallo,tamkar ma'aikata gun yake saidai ya tsaru sosai komai neat,khalil ya qarso
gunsu bayan yaje yayi tambaya yace muje can sunce mu jirashi yana fitowa,wani dan
gune da ka qawatashi da flastic din kujeru da teburinsu kowanne yaja kujera guda ya
zauna
sun dan dauki mintina har fadila ta soma qosawa da zaman jiran
Tun daga nesa da ta hangoshi qirjinta ya hau luguden bugawa,ji tayi tamkar ta tashi
ta bar gurinsai kuma taga idan tayi hakan ta bada kanta,don haka sai ta basar ta
zarme da bude jakarta ta soma fiddo da kayan aikin da zasu buqata,qashin mayen
tutarensa da taji ya mamaye gurin shi ya tabbatar mata da qarasowarsa,sallamarsa ta
same tabbayr mata da hakan dukkansu suka amsa saidai ita ta kasa dago ido ta
dubeshi ta fake da laluben jaka,ya .iqawa khalil hannu sukayi musabaha hafsat ta
gaidashi,sai a sannan ta dago kanta caraf suka hada ido saidai ga mamakinta dauke
kansa yayi tamkar bai taba ganinta ba,a hankali ta radawa hafsa"da wa za muyi hirar
ne?""gashinan a gabanki a.s maitama "inji hafsat"take taji ta dan rude amma cikin
dabara ta gayyato dakiya da nutsuwa ta yafawa kanta,kasancewar Ita ce mai
tambayoyin jfsat da khalil na tayata da rubutu dolenta ta jawo kujerarta ta sake
matsowa daura da shi ta sanya 'yar qaramar recorder dinta a tsakiyarsu suka sake
zama verry close aunyi face to face sosai,wani yanayi ya dinga shiga zuciyarta da
gangar jikinta wanda hakan ya haifar mata da kasala,tanason tayi.masa tambaya ta
farko saidai ta kasa,har sai da hafsat ta dan dungure sanna tayi ta maza ta dago ta
fuskanceshi,saidai ga mamakinta hannauensa na harfe ne bisa qirjinsa yana mata
wannan salon jallon rainin nasa😏,da fari munason muji ainihin cikaken sunanka,ta
fada yayin da ta mayar da dubanta kan radio dinta taga tana nadar sautin yadda ya
kamata,shiru taji har yayi yawa ta dago ta sake dubansa a karo na biyu,saia taga ya
saki hannunsa ya dauke idonsa daga kanta ya kalli khalil yace"ko zakuyi musayar
aiki ita ta ta karbi rubutun kamar ba zata iya aikin ba"khalil ya dan rusuna yave
ranka ya dade zata iya haka tsarin aikin yazo"ya kalleta cikin gatsali yace"zaki
iya?"batayi qasaaqwiwa ba tave aisai an gwada aknsan na qwarai"ta mayat masa da
irin yanayim yadda ya yi mata tambayar,cikin ransa yake jinjina rashin kunyarta
tare da fafin nasan maganinki" a zuciyar sa ya fadi hakan
Ku biyoni muje......
  
[10/16, 12:21 PM] Salma:
Wa yasan gobe?
Safiyya Abdullahi musa huguma

✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
5 5
▶5⃣
Ya dan gyara zamansa cikin isa ya amsa mata"Aliyyu salim maitama shine cikakken
sunana""sunan ya dace da maishi"ta fadi a ranta,cikin nuna qwarewa da gwaninta ta
shiga jefa masa tambayoyi daya bayan daya,sai da suka kwashi kusan awa guda sannan
ta saurara masa,ta katse abun recording din nata ta jefa a jakarta,ta miqe tayi
gaba abinta,saidai can qasan zuciyarta farinciki ne fal ranta,yau ta zauna daf da
shi ta shaqi qamshinsa ta saurari muryarsa son ranta,shi kam bin ta yayi da kallo
cike da mamaki da takaicin raininta don a gurinsa wannan raini ne.
Zaman ta tayi cikin mota tana dakon zuwansu hafsat
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Dukkaninsu suna gidan alh salim,kasancewar yau ake birthday din
iftihal,rabi'ah sumayya farida da fadila anty hafiza sai anty hauwa'u(babbar yar
haj maimuna)duk suna bedroom din momi,fadila na kwance bisa gadon momin,dakin ya
kaure da hayaniya amma banda ita,sam gun ma baya mata dadi,tun jiya da Abba yayi
mata da ya ahmad suka yi masu magana ita da farida kada su kammala attachment dinau
ba tare da sun kawo mijin aure ba,farida kam ko ajikinta tunda dama irin wannan
damar take jira ita da masoyinta mubarak
Ta sake juya kwanciyarta hannun damanta kanta yayi mata gingirin zuciyarta a
cunkushe,anty hafiza ta juyo ta kalleta "fadila ki saki ranki don Allah kiyi addu'a
shine kawai mafita "fadila ta lumshe idonta hadi da sake qanqame pillow tana sake
jin nauyi cikin qirjinta,anty hauwa tace "me ya sameta ne tun dazun na lura bata
cikin sukuni",anty hafiza ta gaya mata hadi da cewa"na rasa irin farida kwata kwata
bata kula kowa,nan da kika ganta bata da wani gwani"farida tace " anty itama fa da
laifinta ya za'a ce duk mazan dake mutuwar sonta ace babu daya da ya mata"a fusace
fadila ta kalleta😡"anty kinganta ko ko da ita ake magana?😫"dama zuciya kusa a
kusa sai hawaye wani na bin wani😭"anty hauwa'u tace"duk ku tashi ku fita ku bamu
wuri"tsam suka fice dakin ya rage daga ita sai fadilan sai anty hafiza,anty hauwa'u
taja ajiyar zuciya tace"sai nake gano dacewa tsakanin fadila da Aliyyu Abban
iftihal ba don kada nayi muku shishshigi ba da na hada wannan alkhairin"gabanfadila
yayi matsananciyar faduwa jin an ambaci Aliyyu,inama ace shine aliyyun da anty
hauwa'u ke magana akai?,ina ma ace shine zai taho da neman soyayyarta?,ina ma ina
ma.........taci gaba da zancen zuci
Anty hauwa taci gaba da cewa"shima anyi anyi da shi ya fidda mata tayi aure ya
qi,sai jiya ya kawo wata yarinya mai zubin yare ba alamun tarbiyya a tattare da ita
wai ita yake son aura,hafiza yarinyar bata da maraba da matarsa ta farko,amma sai
ya kakkareta da cewar wai zaman cikin yare ne yasa aka ganta haka amma da
nutsuwarta.
Fadila tayi hanzarin tashi don batason zancan da anty hauwa'u ta dauko yayi ma wani
nisa,tayi qasa da idonta😪 tace"anty ba wai inason watsa miki qasa a ido bane
a'ah,bansan ya Aliyu ba sani na da shi tun ina qarama ne wanda a yanzu na manta shi
gaba daya,shima kuma nayi imanin ba sanina yayi ba,ba ta wannan ba anty a zamanin
nan auren soyayyar ma ya aka cika bare auren hadi,matar cushe anty ba ta
daraja,kawai ku tayani addu'a Allah yayi min zabi mafi alkhairi"suka amsa da amin
suka kuma bar maganar suka shiga wata badan maganar ta bar ran anty hauwan ba
Kwana biyu da yin maganar anty hauwa na juya maganar cikin ranta sai ta kasa hadiye
maganar har sai da ta niqo gari ta dawo gidan don tattatunawa da abba"tana zaune
gaban abban bayan sun gama taba hira tace"abba nazo maka ne ne da wata muhimmiyar
magana"abban ya bada dukkan hankalinsa kanta sannan yace"uhm ina jinki maijidda"ta
dora"abba kasan fadila 'yar abba abbas tafida?"yayi murmushi irin na manya
yace"banda abinki maijidda idan ban san su farida ba ai kuma bansan kuba,"tayi
dariya ita da momi tace hakane abba"tiryan tiryan take gaya masa halin da yanzu
fadila ke ciki game da zancen fiddo da miji,sannan ta dora"abba inason ne na haska
muku abinda tuna nina ya hasko min game da wannan lamarin""uhn"cewar abba,anty mai
jidda ta dora"abba Ali ya kawo muku yarinyar da azahirin gaskiya baku yadda da
halaye da nagartarta ba,ali abba ya riga ya fada soyayyar yarinyar wadda da zarar
kunce zaku hana shi auren ta dama ce tq zo masa ta yaci gaba da zama babu zancen
aure,zai kafa hujja da cewa ai tun tuni ya kawo ku kuka qi abun"abba ya gyada kai
cikin gamsuwa maijidda ta dora da fadin"to abba mai zai hana ku bashi damar ya
aureta amma abba ku hadashi da fadila?,abba kai ganau ne ba jiyau ba ka fini sani
kasan fadila kasan irin kyakkyawar tarbiyyar da suke da ita,mai zai hana muyi
kwadayin hada zuri'a da su abba?,abba kada mu bari ta subucewa family dimmu saboda
fadila macace ta gari wadda nake da yaqinin samun alkhairai masu tarin yawa da
zuriyya dayyiba tattare da ita?"
Shiru sukayi gaba dayansu bayananta na ratsa su tabbas duk abinda maijidda ta fada
gaskiya ne,sun gamsu matuqa da bayananta,abba yaji dadi matuqa sosai tare da sawa
maijidda albarka gameda zurfin tunanin da tayi akan makomar rayuwar dan uwanta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari alh salim da kansa ya taka ya nufi gidan amininsa alh abbas tafida,suna
babban falon sa bayan sun gam gaisawa alh salim yace"abbas nasan zakayi mamakin
ganina ko da daddarennan bayan jiya da azahar ma muna tare"alh abbas yayi murmushi
yace ai nasan akwai dalili,kuma ma mene a aciki don dan uwa ya ziyarci dan uwansa
aduk sa'adda da yaso?"alh salim ya gyada kai yace"hakane dalili ne kuwa babba ya
taso da ni"alh abbas ya vyara zama yace"ina jinka Allha yasa lpy"alh salim
yace"danka Aliyyu nazo nemawa auren'yata fadila"alh abbas yace"fadila?"ya gyada kai
qwarai fadila ko anyi mata miji ne?"alh abbas ya girgiza kai yana murmushi yace"ko
daya wlh,rigimar da nake ma da ita kenan a 'yan kwanakinnan kenan akan sai ta fito
da miji,maganarka alh ta yimin dadi sosai wlh,amma ina fatan da amincewar
alin?"a'ah ko daya wannan hasashe nayi na son hada zuriyya da aminina"alh abbas ya
saki dariya yace"yayi wlh wannan tunani naka yayi kyau qwarai da gaske,domin samun
nagartacce kamar Aliyuna a wannan zamanim abune mai matuqar wuya qwarai da
gaske,fadila'yar ka ce halak malak kuma ko wani kaso bata wlh zaka iya bashi bate
aliyu,na bawa aliyu ita har abada abokina"alh salim yace"a'ah abokina kada kayi
saurin yanke hukunci ba tare da kaji ta bakin ta ba ka bari su gana taga idan har
yayi mata"alh abbas yace"haba salim Haba salim yaya zaka ce haka bayan kasan
yarinya budurwa ubanta ne ke da ikon zaba mata mijin aure ballantana duk yaron da
zata zaba mawuyacine yakai nagarta da ingancin aliyyun,ai magana ma ta qare dama
dab suke da kammala attachment dinsu nafison ace da zarar sun kammala su tafi
dakunansu"
Alj salim yaji dadin maganar yace"amma fa wani hanzari ba gudu ba,akwai yarinyar da
aliyun zai hada su ya aura tare,to ya kamata a sanar da ita kasan yaran yanzu basa
son abokiyar zama kaga ya kamata ta sani kafin ayi"alh abbas yayi dariya
yace"shirmen banza ne iri na 'ya'yan yanzu zan sanar da ita kada ka damu,bamu
buqatar duk wasu kaya na bidi'o'i"alh salim yace"a'a kaima ka sani momimta haj
maimuna ba zata yarda ba yadda za'a yiwa dayar itama sai an mata"suka sa dariya
gaba dayansu cikin farinciki,cike da godiya bisa karamcin da amininsa yayi masa"alh
abbas yace ka daina godiya da Aliyu da fadila duk daya ne a gurina"alh salim
yace"na sani amma duk da haka godiya ta zama dole duk wanda yayi ma jininka kyautar
da sukutum da guda ai ba qaramin masoyi bane,cikin girmamawa da mutuntuna juna
sukayi sallama
Wa yasan gobe?
Safiyya Abdullahi musa huguma

6 6
▶6⃣
Cikin daran alh abbas ya sanar da mai dakinsa,tayi murna qwarai don tasan amincin
dake tsakanin mazajan nasu da irin tarbiyyar dake gidan alhj salim,sai dai tace
wani hanzari ba gudu ba alhj ba lallai yaran su so junansu ba fa?,abba yayi dariya
yace"duk soyayyar yqnzu shirme ce,ina soyayyar take zuwa?daga anyi auren ta mutu
sai ki rasa ranar da tayi musu,wani auren hadin ba yafi qarko da albarka ba,ga
auremmu ya isheki misali sai da aka kawo ki muka ga juna ko kin manta,gashinan
haryau shekara kusan talatin da biyar ba fada bare yaji"ya dan kalleta ta sigar
tsokana yace"nasan dai abu daya kikayimin kin shanye ni na kasa qaro miki abokiyar
zama"kunya ta kamata tadan rufe fuskarta da tafin hannunta🙈tana cewa"kai
alhaji"shina dariyar yayi yana bude mata fuska yace"ai gaskiya ne"
Misalin goma na safiyar washegarin ranar alh salim da kansa ya sanya aliyu a gaba
ya tuqoshi zuwa gidan aminin nasa alhj abbas don kawo sadakinsa,aliyun yayi kyau
abinsa cikin shadda gezna dinkin tazarce farace qal sai maiqo take,ya saye idanunsa
cikin farin glass wanda bai hanaka tozali da farar qwayar idanunsa,takalminsa baqi
ne na kamfanin batozi sai baqar hula duk da bai sanya ta ba tana riqe ne
ahannunsa,kana nazaratar fuskarsa zaka karanci damuwa a tattatare da shi,sam alh
salim bai bi ta kansa ba don yasan kwanan zancan,ya sani cewa gata ne yake son ya
yiwa aliyun wanda ko bayan ransa zaiji dadinsa.
A nutse yake murza sitiyarin motar har suka iso cikin gidan,alhj abbas da kansa ya
fito yayi ma abokin nasa iso zuwa cikin gidan bayan sun gaisa da Aliyu suka barshi
cikin motar,ya dan kwantar da kujerar motar yayi rigingine yana kallon yanayin
ginin gidan,
Alhj salim ya fiddo da daurin bandir na dari biuar biyar rafa daya ya ajjiye a
gaban alhj abbas yace "ga sadakin aliyu ga 'yata fadila"alhj abbas yace "amma ai a
yimin kara ko ni na biya ai"alhj salim yace"ni da kai ai duka dayane babu komai
wlh"alhj abbas yace"Allah to ya yiwa auren albarka yasa ya zamo farinciki a gurimmu
da gun yaran gaba daya""ameen"ya amsa masa"auren zai kama nan da sati shida dai dai
lokacin da zasu kammala attachment dinsu"alhj salim yace"anya ba'ayi gaggawa
ba?""wani irin gaggawa kuma me zasu zauna su yimin agidan ?"to shikenan abbas Allah
yasa ayi a sa'a""amin dama ban sanar da yarinyar ba niyyata dama yau ta sani amma
munyi zancan da mahaifiyarta,to tunda ga sadakinta ga kuma mijin sai a kirata tasan
komai""to ba laifi"inji alh salim
Tana ysaka da baccinta😴 taji ana dukan saman qafafunta,ta daga kanta idanunta
cime da bacci tana kallon muhammad da ya tashetan cikin jin haushin tashin nata da
yayi tace masa"meye?,ba nasha gaya maka idan ina bacci ka daina damuna ba"ya hade
hannayansa yace"am sorry anty,abba ne ke kiranki""abba kuma?😳"ta ta tambayeshi
cike da tsoro saboda ta tuna agender su,ya gyada mata kai cike da
tabbatarwa,tace jeka ina zuwa"tuni ragowar baccin da take ji ya gudu daga
idanunta,ta dirgo daga gadon ta shige toilet ta wanke fuskarta tayi brush sannan ta
dawo cikin dakin ta daura zani kan rigar baccin ta ta fesa turare sannan ta zira
zumbulelen hijabinta mai hannu,a falo taci karo da umminta tana saka turaren
wuta,ta gaidata sannan fuskarta kamar mai shirin rushewa da kuka😟 tace"ummi wai
abba ke kirana"ta kalleta tace"to kije mana na ganshi da alhj salim"gabanta ya qara
faduwa ta juya ta bar falon
A salube tayi sallama a sitting room din,dukkansu suka amsa mata,ta samu gefan
kujera ta gaida uncle abba(hka suke ce masa)kasancewar sun gaisa da abbanta tunda
asuba,uncle abba ya amsa yana mai qara nazaratar nutsuwa da ladabinta,abbanta ya
kalleta yace"fadila ina son ki bani aron nutsuwa da hankalinki "tace"to abba
😔""kin sani cewa shekarunki sun isa ace kina dakin mijinki tunda an aurar ma da
wadanda basu kaiku shekaru ba,sannan na baki dama ki fito da wanda kikeso kamar
yadda qanwarki ta fiti da shi amma har yanzu baki cemin komai ba,na qyaleki har
lokacin da nabaki ya qare ban tanka miki ba duk da cewa ina da iko in zaba muku
miji amma na baki damarki "ta gayada kai "hakane abba yace"fadila"ta amsa
"na'am""abbanki ya nemawa yayanki aurenki kuma na bashi"wata mummunar faduwar gaba
ce ta risketa tamakar an daddaure jijiyoyin jikinta taji,hakan yasa ta kasa dago
idanunta ta kalli kowa bare su fahimcin halin da ta shiga,ya dora da cewa "yanzu
haka ga sadakinki a hannuna"jin hakan yasa ta qarasa rikicewa sauran dauriyarta
tuni tayi qaura,addu'o'i ne barakatai suka dinga zuwa bakinta tanayinsu cikin
zuciyarta,shikenan na rasa aliyuna?shikenan zuciyata ta rasa muradinta?shikenan
mafarkina ya zama hasashe?,abinda take jujjuyawa kenan kawai a zuciyarta,duk
maganganun abba ba wanda ta ji ko ta fahimta sai maganarsa ta qarshe wadda sauran
qiris ta sa numfashinta ya dauke"kije kuga juna yana falon waje duk da shekarun
baya kun sanshi amma saboda tsawon shekarun zaki iya mantashi ya kwana biyu baya
qasar"uncle abba ne yayi saurin cewa"a'a saurara✋🏻ina da magana ke fadila gayamin
gaskiya idan bakiso kina da wanda kike so"tabbasa da zata iya da ta fayyace musu
sirrin dake zuciyarta ko zasu tausaya mata su bar zuciyarta taji ma da masifar da
take ciki,amma ko kusa batajin zata iya kunyata abbanta,bayan ya isa da ita yana da
iko da ita fiye da yadda take da iko da kanta yayi mata komai a rayuwa ya bata dama
masu yawa a rayuwa irin wadda kowane mutum ke son samu,duk ma a ture wannan gefe
baza iya daga iso ta budi bakinta tace da aminin mahaifinta wanda yake tamkar uba a
gareta cewa batason dansa jininsa ba,hakan yasa tayi saurin girgiza kai tace"ko
daya abba na gode da zabin da kukayimin,Allah ya saka muku da alkhairi"ita kanta ta
jinjinawa kanta kan namijin qoqarin da tayi na furta haka,uncle abba har zuciyarsa
yaji dafi matuqa tare da sake gode ma allah da zata zamo daya dqga cikin ahalin
gidansa,albarka suka sa mata sannan abbanta ya umarceta taje su gana
Takai kusan minti biyar a qofar sitting room din ta kasa shiga,gaba daya a rude
take zuciyarta a cunkushe take,daga qarshe taga tsayuwar batada wani amfani don
haka ta tattaro dukka nutsuwarta da dauriyarta ta kutsa kai hade da sallama kanta a
qasa😔 ta lalubi kujera daya ta zauna cikin fargabar wa zata daga kai ta
gani,muryar da taji ta masa mata ita ta razanata da sauri ta dago kai ta gani ahin
da gaske ne ko kunnuwanta da zuciyarta ke yaudararta yadda suka saba?idanunsu suka
hadu da juna wanda hakan ya tabbatar mata da tsammaninta,ba qaramar razana tayi ba
duk da bata nuna hakan ba,A.s mai tama Aliyyun uncle Abba?,take ta jera sunayan a
zuciyarta,komai tsaya mata cak yayi,tunaninta ya kasa gaba ya kasa baya,shiru daki
ya dauka ba wanda ya tankawa dan uwansa wanda hakan ya sanya fargabarta daduwa,bata
kuma sake kallonsa ba bare taga a wane irin yanayi yake ciki ba,sun jima a haka
sannan ta jiyo alamar miqewarsa,har ya kai bakin qofa yayi taku uku ya dawo da
baya,kallon nan nasa da ta fari gani a qwayar idonsa ta kuma tsaneshi shi yayi mata
sama da qasa sannan yace cikin izza da qasaita"ban iya qarya ba kuma bazan fara
taba saboda ke,bazan iya tafiya ban amayar da binda nake ji cikin zuciyata
ba,bakimin ba baki dace dani ba,baki ma dace da tsarin rayuwata ba,ke da kanki
shaidace ce idan dq zaki iyq yiwa kanki adalci bamu dace da juna ba,baki ma da zubi
da tsarin da nake so gun mace,idan banda tsaurin ido ma irin naki taya zaki hada
kanki da ni?kinga nayi kala da ke?gaskiya kin cuceni,god forbid ki zama matata,kada
kuma ki soma yaudarar kanki ta hanyar zato ko tsammanin nan gaba zan iya sonki
harki cuci kanki ki aure ni,wannan maganan daga cikin zuciyata direct take fitowa
Wani mugun takaici da baqinciki ne lokaci guda ya rufeta,tunda take babu wani da
namiji da ya taba mata munanan furuci makamanta wannan,ta tuna uawan samarin da ke
kara kaina a kanta,samari masu ji da kudi kyau nasaba isa da qasaita,ba wanda ta
bawa dama a cikin su,wasunsu dama suke so ta basu koda ta friendship ne amma basu
samu ba,samari da dama sun sha kuka a gabanta kan ta mallaka musu zuciyarta,amma
yau wani daya daga cikin jinsin maza ke gaya mata wadannan kalaman,ji take a rqntq
matuqar ta barshi ya tafi haka ba ta da ta mayar masa da martani ba wanda zai dade
yana cizon zuciyarsa ba to ba shakka tayi faduwar baqar tasa"hey🙋🏻"tace da shi
sanda ya sanya kai zai gice daga falon,ta miqe tsaye ta yi masa kallon sama da qasa
ta yatsina fuska😏 ta tofar yawu a gefanta sannan tace"see you wane mashahurin
maqaryacin ne ya gaya maka ina maraba da kai da zaka zo kanata soki burutsu,ni
dinma ba yimin kayi ba don baka wuce dan aiken gidana ba a tsarina,amma ni nasan
darajar dan adam banga a gidammu ana tozartashi ba kuma na iya darajatta zancan
magabata na shi yasa ban tozarta mutumin da mahaifina ya zabamin ba,idan banda
qaddar ina budurwa sabuwa dal a leda mai zanyi da bazawari ragowar wata..........
Wata iriyar wafta ya kawowa bakinta wanda ta tabbatr da ya sameta sai lebunanta sun
fashe,da gudu ta bude daya qofar falon da zata kaita cikin gida ta baya ta shige ta
bankowa aliyu qofar ta batshi tsaye zuciyarsa kamar zata fito saboda fushi,ya ga
alamar akwai rainin wayo tattare da yarinyar,yayi qwafa cike da zafin zuciya ya
fice,kai tsaye daķinta ta nufa ta kulle qofarta gam tayi zaman dirshan saman carpet
dinta,wani irin kuka ta saki😭tayi qasa da kanta😪,ta rasa me zayayi farinciki ne
ya kamaceta ko baqinciki?ta jima a zaune tana kukan tate da tambyat kanta da kanta
shin dama baqinciki da farinciki na haduwa lokaći guda cikin zuciyar bil'adama?yau
kam ta fahimci hakan na faruwa tunda gashi yau ta tsinci kanta a ciki
Aliyyunta mafarkinta na kullum?burin zuciyarta muradinta yau shine zai zama mijin
aurenta babban burinta kenan dama anan duniya,sai dai kash yazo mata ta wata iriyar
fuska da sigar da bata tsammatar mata ba,baya sonta baya qaunarta abin har ya kai
tsananin da bazai iya boye qinta a zuciyarsa ba harsai da ya tsaya a gabanta ya
fesar mata,baya ga haka ba ita kafaice zata zama mallàkinsa ba?zata yi sharing
aliyunta da wata?ga ahi har waya ma ta rigata samunshi(maman iftihal)
Da qyar ta iya janye jikinta ta gada saman gadonta,ba abinda ke mata amsa kuwwa
akunnenta irin kalaman aliyu,kafin azahar zazzafan zazzabi ya rufeta,sau biyu
farida na shigowa dubata tana ganinta a duqunqune tayi tsammanin bacci take,a
shigowarta ta uku ne tace"kai yaya fadila wani irin bacci ne haka tun ten o'clock
har one thirty?"tasa hannayenta ta janye bargon tana fafin"ba sanyi ake ba ba komai
ba kuma kin.......
maganar ta maqale mata sanda idonta yakai kan fadila ta zaro ido😳 tana cewa"kinga
idonki kuwa?"ta juyar da idonta daya side din sannan tace"kaina ke ciwo"
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7 7⃣▶ 7
8 8⃣▶ 8
Bata nemi kowa ba kai tsaye dakinta ta nufa ta shiga wanka ta hado da alwala ta
gabatar fa shafa'i da wutirinta tunda tun a gidan ya ahmad tayi isha,ta dauki
kimanin minti goma ta azakar dinta sannan ta ninke sallayar ta sauko qasa ta nufi
dakin ummi,ummin ta amsa sallamar bayan ta mata sannu da zuwa ta sanar da ita anty
hafiza na gaisheta ummi tace "kinje kenan?"ta gyada kai tace"bayan fitarku ne ummi
gidan shiru ba dadi😒shine nace bari kawai na leqa biyu"har ta bude baki zata mata
fadan fita ba tare da ta tambayeta ba sai kuma ta tuna fadilan ba gwanar yawo bace
banza bata kai zomo🐇kasuwa,ta tabbatar ba'a banza ta fita ba,dama farida ce to
tasan hali,sai kawai tace"ina amsawa"fadila tace "ummi bari na wuce na kwanta na
gaji"ta dubeta tace"au yau ba zaki jirayi dawowar abban naki ba?"ta gyada kai"um
ummi abincinsa na dining area na parlour dinsa ni dai sai da safe"ta miqe ummi
tace"Allah ya tashe mu lpy nima wanka zan shiga ki jamin qofar"tana qoqarin fita
taji ummi ta kirayeta ta dawo da baya tana amsawa"bayan fitata wa ya kawo kaya a
baqar leda suna nan a parlour?",sai a sannan ta tuna da kayan da aliyu ya aiko a
kawo mata,ta sunkuyar da kanta😔tace"ummi yaya aliyu ne ya kawo to sai na mantasu a
parlour"ummi ta gyada kai tace"yayi miki kyau,fadila ki maida hankalinki fa,gidan
kishiyafa zaki,ba ke kadai zaki zauna ba ballantana kice zaki dinga abinda ranki
keso......ta danyi jim,jin fadila bata ce komai ba ta Dora"sai kije ki debe tun
kafin abbanki ya zo ya gani ranki ya baci"ta qarasa maganar tana shigewa
bandaki ,jikinta a salube ta fita,ta isa inda ledar take ta dauke ta tayi sama da
ita
Hannu biyu ta tallafe habarta da su ranta a jagule,yaushe su ummi zasu fahimci
tsananin da take ciki?,har ga Allah tana son ali yana burgeta a rayuwarta komai
nasa yana bata sha'awa,yau da za'a ce aliyu yana sonta a sai ta fi kowa
farinciki,to su su ummi suna tsammanin ita ke son kawo cikas,ta share hawayenta ta
daga ledar tana zazzage kayan ciki
Bandir ne na 'yan dubu dubu sababbi fil a miqe💶 guda hudu sai chocolate packet hudu
manya🍫,sai turare guda hudu designers,sai awarwaraye banguls da zobensu na gold
guda biyu💍,sai agogon hannu na azurfa guda biyu shima,komai tsada ne da tsari,cikin
zuciyarta take fadin"yadda Aliyu na ke da kyau da tsari haka everything na shi
yake,yadda aliyu yake special haka komai daya dangaceshi yake,komai nashi special
one ne hakanan abun ban sha'awa ne,ina ma aliyu zai soni?,ina ma Aliyu zai rufeni
da da so da qaunarsa da na zamo daya daga cikin mata masu tsananin sa'a a
rayuwarsu"hawayen tausayin kanta suka ziraro mata,ta dauki daya daga cikin rapper
din kudin tana shinshinawa,ta lumshe idonta don qamshin turarensa kawai ke tashi a
jikinsu(haka aliyu yake saboda yadda turare ya zaunar masa a jikinsa duk abi da
yayi gogayya da shi sai yayi qamshin turarensa)
Farida ta shigo dakin da sallamarta,fadila ta amsa tana janye mata kayan dan
faridan ta samu gun zama,cikin tsokana faridanke tambayarta kayan,tace"duba ki gani
ya Aliyu ne ya kawo dazun ki zabi abinda kike so(haka ummi ta koyar da su tun suna
qanan idan daya ya samu abu to zai raba tare da dan'uwansa )ta yaba kayan sosai ta
dauki turare biyu tace sun isheta,fadila tayi tayi da ita ta qara taqi,ta turo mata
kudaden gabanta hadi da yage 'yar paper da taga anyi rubutu a jiki kamar haka"kiyi
hidimar biki idan basu isa ba zansa a adado miki"tadan tabe baki ☹cikin ranta
tace"nafi buqatarka da su da zaka gane hakan""farida ga kudin hidimar bikinan inji
aliyu idan basu kai ba a mishi magana"farida ta dauki kudin tana juyawa tace"har
dubu dari hudu😳"fadila tave"hmmm ni da ua ban su nasan mai zanyi ma da su"farida
tace"ni da anty hafiza munsan me zamuyi miki da su,ko iya wadannan ma sun isa ya
sallameki"ta miqe tana cewa"bari in nunawa ummi,sai da safe sister"ta fita taja
mata qofar tana ayyana abubuwan da zasu yiwa fadilan masu amfani
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Duk cikin satittikan da suka biyo baya cikin hidamar shirye shiryen biki suke,ita
kam fadila bata da wani zabi na kanta,da zasu yarda ma da sun qyaleta haka don bata
da sha'awar yin komai kama daga gyaran jiki zuwa kan duk wasu events da ake yi
yayin bikin aure,don duk abinda zatayi wanda za'ayi don shin abun bai dada shi da
qasa ba baya gabansa hakan yasa itama ta tsani komai,sai da anty hafiza ta zaunar
da ita ta nuna mata duk abinda tayi idanun👀 duniya na kanta,zata tona asirin kanta
da kanta ne sannan ta amince da tsare tsaren da suke zuwar mata da su,hatta
magunguna tanajin farida na sha da qyar tana mita ita kam nata ido👀karba kawai take
ta daddake tunda tana ganin babu wani amfani da zasu yi mata
To fa masu karatu ga fadila Abbas na shirin shiga gidan Aliyu salim maitama,gidan
da aka gargade ta da shigarsa tun kafin ta kai ga shigarsa,shin mene shawararku
gareta????
10:34 pm
07066139278
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻 ✍🏻 ✍🏻

  
[10/16, 12:25 PM] Salma:
Wa yasan gobe?

Written by safiyya Abdullahi musa huguma

9 9
▶9⃣
Ranar laraba 12 ga watan biyu aka soma da kamu👰🏻,ba dan qaramin kyau amare sukayi
ba,kai kaso kazo kaga yadda kamun ya qawatu matuqa da gaske,an zubar da dukiya
sosai kasancewar wannan ne bikin ummi na farko kuma na qarshe,tamakar tagwaye haka
suka zama komai iri daya suka sanya hatta da awarwaro da zobe
Kasancewar abban su babar bare umminsu bafulatana sai aka raba abun biyu shigar
farko sukayi shiga irin ta bare bari cikin wata lafiyayyar lafaya wadda kudinta ya
tasamma kimanin dubu ashirin kamu aka musu irin na bare bari sosai sannan daga
bisani kuma suka canza shiga irin ta fulani cikin kayan saqi nan ma aka musu kamun
fulani,shida na yamma aka tashi bayan sallar magariba kuma masu kidan qwarya suka
zauna zuwa goma na dare
Irin cikar da gidan yayi yasa su fadila haqura da zaman gidan su da qawayansu suka
koma gidan maman zainab maqociyarsu ce kuma babbar macace don idan batayi sa'ar
umminsu ba to zata girmemeta,zainab din yarinyarta ce kusan sa'ar farida ce
Fadila nabin kowa da ido don a yanzu kam jikinta ya qarasa mutuwa murus,bata da
kuzari ko qanqani komai cikin dakiya da qarfafa mata gwiwa da anty hafiza ke mata
take yinsa,ga wani ciwon kai da ya addabeta,ta riga ta saba ita ko da can bata saba
da shiga hayaniya ba ko bikin dangi ne bata kwana sai dai farida ta kwana ita kam
komai dare zata dawo gida ne,ko hayaniya tayi mai yawa to yanzu kanta zai fara ciwo
ko qirjinta ya dau zafi
Kwance take kan gadon zainab din ta juya ma tarin 'yammatan dake dakin sunata
hayaniyarsu baya ta fuskanci fuskar gadon,yawancinsu duk qawayen farida ne sai
'ya'yan 'yan uwa,farida tayi sallama ta shigo dakin ita da aminiyarta ruqayya
hannunsu dauke niqi niqi da ledoji na take away wanda aikin mubarak(angon faridan)
ne shi yace a tazo suje tayi musu take away,ta zube musu nan hayaniya ta qaru
kowacce tana daukar tata,ta iso kan gadon hannunta da ledoji biyu,ta dan taba
qafafun fadilan tace"sister tashi"fadila ta miqe daga kwanciyar ta zauna tsakiyar
gadon ta tanqwashe qafafunta tana kallon farida,qasa-qasa muryarta tace "yayaa ga
abinci ki daure ki ci sai ki sha maganin ciwon kan ko dan idon mutane ida yaso sai
ki kwanta ki huta,"tana maganar tana bude ledar da ta shigo da ita din ta tura mata
gabanta,ta sake bude dayar ledar tana cewa"ga dinkimmu na dinner din gobe ta can
muka biya da mubarak muka maso"ta soma fito da su
Wani dan ubansun material ne mai azabar kyau wanda ko makaho ya shafa yasan cewa ba
qananan kudade aka sa aka siyeshi ba,milk ne da ja(milk and red),ita kanta faridan
da tunda ma anty hafiza ta bawa ya ahmad da zashi india ya siyo musu bata ganshi ba
sai yau da aka karbo dinki faridan ce ke zuzutashi sai yau taganshi yayi bala'in
tafiya da ita ,ta jinjina kak tace"an gode miki sister farida"farida tayi dariya
tace"ai wannan aikin anty hadiza ne ragowan su earings ma da zamu sa suna
gunta"fadila tace"Alla ya saka mata da alkhairi"ta jawo ledar da faridan ta bude
mata,gasashshiyar kaza ce🍗 da hanta wadda aka mata gashi mai ruwa ruwa da
albasa,shawarma🌮 sai kuma ice cream roba biyu,tayi murmushi ta kalleta kafin tave
komai faridan ta rigata magana"ke dai yaya ki ci kawai,kina tsammanin bansan abinda
kime boyewa bane a dan qaramin fridge dun gefan gadonki ba wanda ke hanaki maida
hankali kici abinci?☺"sai dariya ta kama fadila,lokaci guda kuma tausayin rabuwa
da junansu da qaunar 'yar uwarta ya kamata,lallai ne dan uwa rabin jiki,naka nakane
qwalla ta ziraro mata ita ma faridan sai ga qwallar,dai dai nan rumasa'u(yar qanwar
umminsu ce(ta shigo dakin,ganin haka ta saki dariya"a'ah kaga twince sisters
wato ku daga fara biki har kun soma gunsheqen kukan rabuwa tun kafin aje ko
ina?"yawan hayaniyar da yammatan keyi ya hanasu jin abinda take cewa,farida na dan
murmushi ta goge hawayanta,ita kuwa fadila da yake sa'annin juna ne saita
harareta"to ina ruwanki 'yar sa ido?"cikin dariya tace"🤗a'ah Allah ya huci
xuciyarki bani na kar zomon ba ratayar ma ba'a bani ba ni ummi ce ta turoni tave
inzo inga kinci abinci don tasan hali"ta fada tana leqen ledar gaban fadila,fadila
ta muwa lanqwashe ledar,tana cewa"kuma duk kwadayin mutum bazaici ba ba?"cikin son
zolaya rumasa'u tace"haba aminis ni dake fa bata baci"fadila ta zaro kazar ta
nannde mata tace "ungo a banni na hadiyi yawu"tafice tana dariya,farida da tun
dazun take ta musu dariya tace"hoo yaya ruma akwai zolaya da abun dariya yanzu fa
idan kika bibiya itama bacin zatayi ba baiwa wani zatayi"fadila tayi murmushi
tace"ta ji dai
Shi dai gundura kawai"
Da taimakom farida fadila ta saki jikinta sosai don har ta samu ta shige cikin
'yammatan aka shiga hirar harda ita,hakan ya taimaka mata ta samu sauqin takurar da
zuciyarta tayi sosai kafin dare yayi kowa ya kwanta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari gidan kwalliya anty hafiza ta debesu suka tafi,cikin wasu awoyi aka
qalqale wa kowacce fuskarta da kwalliya ta garari dubu ashirin aka ajiyewa
matar,itakam anty hafiza tsayawa tayi tana kallon sarautar Allah kyansu ya qara
bayyana qarara,daga baya ta kasa ahiru sai da tace"ashe haka kuje da kyau yammatan
ummi musamman fadila ashe hasken fata kawai za'a nuna miki?"dariya dukansu sukayi
har da ita mai kwalliyar wadsa itama tinda tayi musu take kallo fuskarsu tace"dama
ai ba fari ne kyau ba don wani choculet din yafi fari kyau nesa ba kusa ba"
sai bayan idar da sallar magariba aka kammala kwashe yammatan zuwa royal
tropicana,amare sun gama shirinsu kayan kam sun amshi jikinsu don tamkar saboda su
aka halicci yadin da shi kansa dinkin,kiran mubarak ya shigo wayar farida yana
sanar mata isowarshi qofar gidan,ta kashe wayar fuskarta na bayyanar da damuwa ta
kalli anty hafiza da ta luea tun dazun ta kasa zama sai kaiwa da komowa taketana
kiraye kirayen waya ta fuskanci akwai abinda suke boye mata,farida tace"anty ya
za'ayi gashi har mubarak ya iso?"hafiza vikin damuwa ta kalli fadika tace"fadila
kibi motarsu farida kawai kije"ba abinda tace mata kawai tabi bayan farida suka
fice,ko ba'a gaya mta ba itafin ai ba yarinya bace qarama ta sani koda wasa aliyu
ba zuwa zaya yi ba,ko da yazo ma tana fargabar kada ya yi mata wani abun da zata
kunyata a idon duniya,shi yasa tun usuli ta so su shiryawa farida dinner din ita
kadai abunta,mubarak ke driving motar da kansa don haka suna fitowa da kansa ya
bude mata kujera mai zaman banza ta kusa da shi ta shiga ya rufe sannan ya koma ya
shiga nasa gun,ita kuwa tana baya ita kadai,tunani ya cika zuciyarta tana sha'awar
soyayyar farida da mubarak dinta,yana matuqar nuna mata qauna da kukawa ko da a
gaban waye,tunda aka fqra hidimar bikinannan kusan tare suke jigilar shi da ita,duk
da tana da moyar ta amma ba ruwansa da wannan,
da yake basu fito da wuri basun dan bata lokaci gun jira jiran da fadila ta samasa
jiran gawon shanu don tasan ba komai bane face jiran tsammanin zuwan Aliyu ya
dauketa ita damata ahekara da sanin ba zuwa zaiyi ba,a farfajiyar farko kafin ka
shiga tafkeken hall din mubarak yayi parking,saiga anty hauwa anty hafiza da tuni
ta iso sumayya rabi'ah da 'yan biyu,fuskar anty hawa da alamun bacin rai ta kalli
su mubarak"kama hannunta ku shiga su fadila zasu shigo daga baya"yace "to"ya kama
hannun farida su sumayya suka take musu baya su da wasu yammata cikin anko codelace
milk dake tsaye bakin qofar ahiga hall din,cikin son kauda ahitun da gun yayi antu
hauwa tace"gsky hafiza mun tsinci dami a kala fa,irin wannan tsaleliyar budurwa
haka?"duk sai da ta basu daroya,anty hauwa ta budewa fadila motarta gun kujera mai
zaman banza tace zauan fadila,wayarta ta zarota shiga kira"muna qofar hall inda ka
shanya mu muna jira"ta fada cikin fusata sannan ta kashe wayar,sundebi kusan minti
ashirin suna zaman jiran har fadila ta qosa sosai tayi kamar ta nemi alfarmarsu
akan su qyaleta ta koma gida tana ahirin yin hakan waau jerin gwanon baqaqen motoci
motoci suka danno kai cikin harabar gurin,anty hafiza ta sake feshe fadila da
turare sannan duk da qamshin da take zubawa fuskarta fes take kamar yanxu aka gama
kwalliyar sai alamun damuwa da suka bayyana a fuskar anty hafiza ta rada mata"be
free and comfortable you have to invite happiness in you face even its not true,
zaku shiga cikin mutane ke zaki bawa kanki confidences na zaki zaki zama amarya
kamar farida da mubarak right?"fadila ta gyada kai tana qoqarin daidaita yanayin
din fuskarta,ta maida turaren cikin hamarta tana cewa sai kun shigo "ta wuce
ciki,daganan tana hango anty gauwa yadda ta nufesu tana wurwurga hannu da alama
masifa take nasa shì kuwa ya yi kicin kicin ya hade ransa sanye yake cikin wata
dakakkiyar shàdda milk colour yar ubansu komai na aliyu classic ne yayi wani
shegyan kayu dinkin babbar riga da yar ciki ne da wando sai takaminsa half cover na
kamfanin mister,daga bisani tafa tana nuno masa ita da hannu itama ta juya tayi
shigewarta
Duk takunsa daya shike qaŕa bugun da zuciyarta keyi ta dauke idanunta ta ditasu
kacokam kan sitiyarin motar kunnanta na jiyo mata takun tahowarsa gun hancinta na
shaqo mata daddadan turarensa,sau biyu taji yayi knocking glass din motar bata da
zabi illa ta fuskanceshi sabida haka ta dago razanannun idamunta ta saukesu cukin
nasa idanunta da nashi suka hadu gu guda,zuciyarsa taďan kai ta jawo kadan duk da
yaga kyaunda tayi amma sau yaga batakai kyan da samira ta masa ba,cikin halun ko in
kula yace mata"les go"fuska a tsuke ya juya😠,ta bude murfin motar tana qoqarin
fitowa ta gurde ta tafi luu zata fadi saboda yadda jikinta ke rawa,yasa sangalalun
hannunsa na hagu ya tare ta sannan ya miqar da ita tsaye ya saki tsaki yayi gaba,ta
yi qoqarin daidaita natsuwarta sannan ta bishi suka jera
Shigarsu mawaqin ya sauya kidan zuwa wani take na musamman aka bisu kuma da abin
qyalli ana fesa musu🎊 ga gayyar yan rakiya a bayansu da suka sasu a tsakiya,suna
zama aka maida waqar da shahararren mawaqin nan yayi musu nura m inuwa(anyi aure
biki na'ya'yan girma 'ya'yan alhaji abbas bashir sunyi aure)aka dan cashe kadan
sannan m.c ya amshi abun magana🎙ya soma zugasu kamar yadda aka sani sunawa amare da
angwàye,lokacin mubarak da aliyu suka gaisa cikin mutunta juna,mc bai qyalesu haka
ba har sai da ya samo musu kyautar mota daga gun Aliyu mubarak ya bada dubu dari
hajiya shatu yayr alh salim maitama ta basu wata qaramar motaŕ dangin mubarak kuma
suka qara musu da dubu hamsin,tunda suka samu abinda suje si suka bude fa bakin
gangat zamar da bikin qayatacce a idon duniya,biki kam ya qawayat ta kuma
nishadantar musamman farida da angonta,don da aka kira amare da angwaye su shigatsu
sukayi filin rawa suka taka sosai itakam ita da aliýu sun tsaya ne kurum suna
facing juna ita kanta na qasa ma aka musu ana cikin yi aliyun yaja hannuta suka
koma sit din su umarni ma yabi da tafiyarsa zaiyi ya barta ita kàdai tsaye a filin
sai akan kujerunsu aka qarasa musu liqin,wayrsa ta dauki wani daddadan ringin,ya
daga yar kyakkyawar wayar a kunnensa sannan u
yace"oh baby I already told you sai na fara zuwa gun daya dinner din ko idan kuma
nabar nan din can zan taho tunda na da wuri zaku tashi ba......ok take care"ya
kashe wayar yaja dan siririn tsaki
Farida da mubarak ne suka soma yanka nasu cake din sannan dan gaa kadan nasu fadila
mai hawa shidda ne milk sannan red milk sannan red haka haka har step shida🎂,bayan
su farida sun koma aka kirasu gabanta na ta duka,suka tsaya gaban cake din maimakon
ua fara daukar wuqar saboda tsorata ita tà fàra daùka akasa tagi mc yace yau zamuga
sabon salon soyayya uwargida zata fara ci da mai gida wata wuta tayi tsiri saman
cake din lokacin da tasa yar qaramar wuqar tana yanko cake din hakan ya sake sa
jikinta rawa tadan tsorata
duk da ta saba gani ammada yake a rude take sai hakan ya sake duburburtata,tayi
qasa da idonta sanda ta kai cake din bakinsa ,ya kuwa basar ya sa bakinsa ya karba
cikin mugunta ya hada da hannayenta ya datse mata sutaji zafi sosai amma kasancewar
tasan da gayya yayi sai ta basar kamar baþa ji zafin ba,bai damu da qanqantar
bakinta ba ya yanko qaton cake da tasan yafi qarfin bakinta ya danna mata duk da
haka itama tayì namijin qoqarin lalubo yatsunsa ta ganyara masa cizo maimakon ya
cire hannun nasa sai kawai ya birkitota ya mannata da jikinsa ya maqure ta sosai
duk a zuwan rungumeta ya yi ya sanya bakinta cikin nasa yana tsotse butter din da
ta bata dan qaramin bakinta,duk gurin ya dau sowa da tafi masu hotuna📸 da video🎥
suka yo ca suna aikinsu saidai fafila ita tasan azabar da take ji domin tsotsar
mugunta ce su kuwa a tsammaninsu tsantsar soyayya ce,ta tabbatar lebunanta idan
basu tsage ba to daf suke da au tsage din,kunya da takaici suka dabibayeta cikìn
dinbin jama'a saboda rashin kunya irinta aliyu ya mata irin wannan abun?ya saketa
sannan ya jata zuwa gun zamanta ya zaunar da ita ya dan ranqwafa mata yace"matuqar
idan nayi miki abu kikace sai kin rama u wil b suffer"yana gama gaya mata ya juyà
yabi ta cikin mitanen ya bar halla din sai jiyowa tayi ta cikin macros phone mc na
sanarwa cewa ango yace a masa afuwa kayansa sun bavi zaije gida ya canza yana kuma
yiwa kowa fatan alkhairi godiya da kuma ban gajiya amarya kùma tadan daure taje
zasu tafi,kasa tashi tayi kuka kurum take na takaici da kunyasam Aliyu bashi da
kunya ya rasa tame zai rama saita irin wannan hanyar?idan su sunsan abinda ke
zuciyoyinsu ai ragowar jama'a basu sani ba ko?,harsai da text din anty hafiza ya
shigo mata kamar haka sannanta iya tashi"malama kukan ya isa haka ki taahi ki bishi
yana wahan hall din yana jiranji isan kùna so kike ki tona abnda muka binne to
bismillah"ta miqe tana kare fuskarta da purse👛ta fice
Wannan saurayin da ta saba ganinsu ko yaushe da aliyu shi ya fito ya bude mata
gidan baya ta shiga sai da ta zauna ta lura da aliyu ahima zaune gefanta bai ko
kaeta ba yavi gaba da abinda yake bako motsin mutum cikin motar sai qarar fitar ac
har suka qaraso ni'ima guest place,motocin sukayi parking na ciki suka firfito suka
tsaya jiran fitowar Aliyu tuni drivan ya fice aliyu ya zube wayoyinsa bayan ya
kashesu yà fice shima a motar ya kulleta tare da sa security
Wucewarsu cikin hayaniya ta tawagar ango yasanya gun komawa tsit kamar yadda
yake ,tun tanajin tsoro har ta dake tana ta addu'o'i,a hankali abinda ke wakana
agun ke isowa kunnuwanta ta hanyar lasifiqan da suke amfani da shi,sunan samira da
ta ji hade da na Aliyu shi ya tabbatà mata gun bikinsu ne,wani kishi mai zafi ya
shaqeta,ta jingina sosai da makarin kujerar tana ambatar sunan Allah tà lumshe
idanunta tana ci gaba da sauraren abinda ke wakana cikin gun dinner din,gajiya
tsoro kishi da takaici suka mata taron dagi, tun bata gaji ba har ta sare da zaman
gashi ba damar fita bare tayi tafiyarta yabi ya kulle matar,zaman jira na kìmanin
awa uku tayi a motar sannan ta fara hango tawagar aliyu
Tamakar ya manta akwai wata halitta da ke cikin motar ya shigo abinsa driver yaja
motar suka bar gun,ganin haka yasa tayi kamar ta tuna masa su sauketa a gida fa sai
taga ai ya ma raina wayonta duk inda zai kaita ya kaita,ganin sunyi hanyar gida
yasa ta sake tabbatarwa yana sane kenan
A daidai qofar gidansu driver yayi parking yana tsayawa tasa hannu ta bude motar
tayi ficewarta ba tare da tace masa kanzil ba haka shima baice komai din ba dama
kuma tasan ba cewar zaiyi ba bata kuma dada ta da qasa ba maganarsa,ahankali take
tafiya saboda kasala da bacci ga takaici da ya rufeta ya dan bita da kallo yana
mamakin haqurin da tayi bata ce masa komai ba ua juya ya bawa nasiru umarnin ya ja
motar su wuce
Kai tsaye gidansu zainab ta tafi don kwanciya kawai take buqatar yi a halin
yanzu,dakin da aka basu ta tura ta shiga wasunsu yammatan sunyi bacci wadanda suka
rage kuma kowacce na maqe da waya tana tadi kamar yadda farida tabi sahu itama
ganin shigowar fadilan ne ya sata katse wayar ta dubeta tace"ya naga kin jima sosai
haka"sai kuma ta danyi murmushi😊 tace"um mace da mijinta meye nawa?",tabe baki
fadilan tayi☹ta jawo jakar kayanta ta dauki towel ta kwabe mayan jikinta tadaura
ganin haka yasa farida ta gane tambayarta bata da amsa kenan,ta sake dariya bayan
taga shigewarta toilet tace"ya fadila tawa......miskili kafi mahaukaci ban haushi
Washegari ummi tayi mother's day,cikakkiyar shigar hausawa sukayi ranar don hatta
mayafi na atamfa sukayi,kwatsam sai ga momin Aliyyun a gun da mutanenta sunzo wai
za ta yi wa fadila nata kamun,gun yayi armashi sosai don kidan qwarya akayi zalla
bayan lecture ga amare wadda aka shafe fiye da awa ana musu inda daga baya kuma gun
ya karade da waqoqin da irin nasu mamman shata sani sabulu dan qwairo dan indo audu
wazirin dan duna da sauransu suma iyaye aka tuno musu da da tunda dama ranar ta
iyaye ce,
Washegarin ranar sukayi kuma wuni a gida,wata Washegarin kuma ta zamto ranar daurin
aure,daurin auren da ya tara jama'a na ban mamaki garin ranar unguwar ba masaka
tsinke,jama'a ne tako ina na nan qasar dama maqwaftan qasashe har da na qetare
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Misalin takwas na daren ranar daurin auren fadila da farida na durqushe gaban
umminsu sanye cikin atamfa super England lemon grean ce da pink sai adon fari
dinkin riga da zani an nannade masu jikinsu da wata danyar lafaya fara tas mai dige
digen pink a jiki,dan kunne da sarqa sai banguls duk na azurfa ne ,babu abinda ke
tashi jikinsu sai wani rantsatstsan qamshin turaren humra yar gasken ta bare barin
usuli
Da fari ummi kasa magana tayi saboda tausayi da qaunar yaran nata sai jimamin
rabuwa da zatayi da su,daga baya ta daurw ta musu yar tunatarwa saboda ita damacan
koda yaushe mai dora yayanta ce kan tarbiyyar zaman gidan aure ce,ta kammala
nasihar tata da addu'a da fatan alkhairi a garesu,umma A'i yayar ummi ta leqo tana
cewa su fito angwaye nata jira fa,wani kukan suka sake saki suka ruqunqume ummin
suna neman yafiyarta,tace ta yafemusu burinta kawai su zauna da mazajanasu lafiya
kada taji kada ta gani shine farincikinta,ana riqe dasu amma suna waiwayowa suna
kuka idanunsu a kanta kamar zasu qwace su dawo,itama sai ta kasa jurewa suka sata
qwalla duk sai suka karyar da zuciyar kowa sai muhammad shima ya dauki masa kukan
da ya bawa mutane tausayi kasa zama yayi yabi yan uwan nasa yana ta kuka kowa ya
tausaya mai saboda tunda ya taso suna tare da su ya saba su ya saba gani gashi yau
an dauke masa su duka biyun
Cikin wata arniyar mota qirar sail akace a shiga da fadila suna qoqarin sa farida a
dayar ta riqeta gam tace bata yarda ba saidai a hadasu a mota daya,ganin da gaske
take yasa suka sasu a mota gudan,lokaci guda motocin suka tashi suka kuma jeru
reras bisa titi tamkar motocin rakiyar shugaban qasa,duk da cewar darene amma duk
inda suka bi sai sunja hankalin mutane saboda kyawun motocin,kai tsaye yahaya gusau
suka fara nufa inda anan gidan farida yake,a nutse suke shiga gidan saboda ba yara
ko daya sai manya da yammata tun la'asar aka kai yara suka gama gani aka dawo da su
gida tsarin gidan farida gwanin sha'awa ya burge jama'a da dama atsare ginin yake
kana kallonsa kasan sai da aka sa nutsuwa aka fidda masa fasali
Sai da suka ajiyeta a bedroom dinta su umman abuja(itama qanwar abba ce)suka sata
tayi addu'o'i sannan sukayi haramar tafiya,fadila na nanuqe da farida har yanzu
kukan suke sunqi sakin juna harsai da umma a'i tq fusata dama akwai lafiyar fada ta
hau sababi tace"ku kunga bamason isknci,kanku aka fara aure ai kowa da haka ya
sabatun dazun ake fama da ku ki fito kin noqe to kada ki sake na qaraso dakinann
baki fito mun tafi ba"suka sake rushewa da kuka 😩ganin lallai dai rabuwar za
suyi,mama sadiya(abokiyar wasan abbansu ce)tazo ta kama fadilan tana rarrashinta
tafito da ita tana jiyo kukan faridan kamar yadda itama take jiyo nata
Cikin nasarawa G.R.A motocin suka kutsa qofar wani katafaren gida suka tsaya,kewaye
yake da dogayen kuma qawatattun katangu da fitulu masu tsananin kyau makeken get
wanda saboda tsananin girmansa sai kayi tsammanin qofar shiga garice suka tsaya,duk
yawan motocin sai da kyakkyawar harabar gidan ta lamushe su,sai ma suka tashi yan
tsurut harabar wadace ta take da haske tamkar rana sai ka rantse da Allah rana ce
ba dare ba
"Kai jama'a yanzu kamar ba za'a mutu ba?,wannan gidan dai.....inda ni kadai na
shigo wlh ihu zan sak na ce gidan yankan kai nazo,kamar ba mutuwa a
duniya?"kakarsu fadila hajja gana mahaifiyar abbansu ke wannan santin,su kam me za
suyi idan ba dariya ba,sai da suka nufi sashen fadilan masu yaba kyau da tsaruwar
gidan suka dadu,ginine wanda kaf garin kano baifi ka qirga masu irinsa da hannu
ba,ginin part hudu ne sai boys quarters makeken lambu swimming pool gun wasanni
kala kala,basketball table tennis,football boxing,tokwand da sauransu baya ga
haraba biyu da gidan ke dauke da shi harabar farko dakin mai gadi da parking space
take dauke da shi,sun dan tarad da jama'a a gidan acan part din samira suna jira a
kawota,ba abinda ke tashi sai kida da yan uwanta suka ware mai barazanar fasa
kunnuwa ganin haka hajja gana ta hana su koda guda suyi ta shiga gidanta da
addu'o'i bakinta
"🤔wai ni Allah wannan gida naki fadila idan baka da qarfin imani zai iya saka ka
manta Allah "gaba dayasai da hajja gana ta sake sa kowa dariya a gun duk da suma
sun lalace ne gun kallon tsaruwar gurin nata falone two in one wanda kan ka shigo
main falo akwai varender a farkon sashin sannan ka tadda falon,dukka falukan sun
qawatu da kayan qyale qyale na falo babba da qaramim falon kowanne ansa masa abinda
falo ke buqata ba abinda aka rage masa,acikin main falon anan daga hannun damanka
matattakala ce masu fadi guda hudu zaka taka ka haye gun dining wanda ke daume da
wasu hadaddun labulaye masu kacar kacar anan qofar kitchen s dinta take wanda duk
wayewarka sai quyancinka ya fito,gaban gun dainin kadan wata yar qoface mai kyau ta
glass wadda ke dauke da corridor shimfide da lallausan carfet da hadaddun labulaye
dakunan bacci ne guda uku daya furniture ne yan Saudi pink da purple daya dakin
kuma yan italia ne ash da pinch yayin da daya dakin kuma aka malaleshi da carfet da
manyan tuntuna aka zagayeshi da labulaye masu shegen kyau aka rarrataye mata kayan
kaba da kumbuna tamkar jeran qauye sai wani dan gado irin na qauye mai rumfa amma
wannan an zamanantar da shi kowanne daki da toilet dinsa sai public toilet dake
varender da kuma wani a falo,daga kitchen akwai qofa da zaka zagaua bayan part
dinka(ventilation)wanda akayi dan qaramin lambu da wata rumfar bunu sai yar qaramar
qorama da aka qirqira da doguwar kujera ta siminti qwaya daya,a falo aka
ajiyeta,ido kam ya raja'a da kallom kyawun gidan,sanyi a c da qamshin freshener ya
game ko ina ga qamshin sabunta,gidan ya kaure da hayaniyar yammata dake ta zuba
santi da yiwa kansu fatan samun koda makamancin wannan gidan ne,
Wata hayaniya da suka ji ta kunno kai gidan ya saka su yin shiru suna sauraron daga
ina take?,guda ce da aka cakudata da kirari iri iri hafe da habaice habaice"taka
lpy uwar gida sarautar mata,isaahshiyar mace a gidan aliyu maitama ,eh anqi Allah
yaso,qaryar mahassada ba zasu iya da ke ba wallahi sama ta yiwa yaro nisa saidai ya
tada kai yayi kallo,an buga da ke an barki wlh yarinya ko yar sankin santanbul ce
kinfi qarfin ta kara da ke saidai tayi iya nata salon ta haqura,"
hakane ya tabbatar musu masu rakiyar samira ne mama sadiya suka hana kowa fita har
suka qaraci ahewarau da shegantakarsu suka shige da ita,zuwa wani lokaci kuma
sautin sabon kida na kujerar tsakar gida ya karade gidan tamkar wani club,Allah ya
kayuta abinda suka ce kenan
Qarfe tara aka soma kwashe yammatan ana maida su kafin tara da rabi gidanta babu
kowa,kadaici ya kama fadila,tsoro ya cikata,bata jin sautin komai sai hayaniya da
kidan yan uwan samirah,zuciyarta tayi rauni sosai tunanin irin zaman da zatayi a
gidan take,Aliyunta bai sonta,kishiyarta kuwa salon da ka rakota da ahi ya tabbatqr
mata ba zaman lafiya tazo ayi da ita ba,hawaye ya balle mata😭 zuciyarta kaar tayi
tsalle ta fito saboda zullumi da radadin da take mata
Horn din motoci ya sake cika gidan,ta daga kanta ta kalli agogon bangon dake falon
sha daya na dare ya nuna mata🕚 ba shakka angone da abokansa suka shigo zuciyarta ke
gaya mata haka,sannu taji hayaniyar jama'ar na raguwa hakan ya tabbatar mata ana
debe su ne tafiya suke,ga tarin mamakinta sai ta jiyo muryar samira na cewa"ku
gaida gida na gode Allah ya huta gajiya,ina jiranku gobe da safe,kuma wlh kada ku
yarda sai sun vika muku kudin siyan bakin"fadila ta jinjina kai tana cewa cikin
zuciyarta lallai ba shakka kowane tsuntsu kukan gidansu yake
Cikin qanqanin lokaci gidan ya sake zama tsit,ba komai cikinsa sai hasken fitilu
daya gauraye da kukan tsintsaye da kuma gyare jefi jefi,haka ya sake assasa tsoron
dake zuciyar fadila ta runtse idanunta gam😣
tana ambaton sunayan Allah hadi da
addu'o'in tsari,sannu a hankali taji idanunta da jikinta sun fara nauyi ,gajiyar
kwana da kwanaki suka fara sauko mata,taji bata da buqatar komai illa kashingida,ta
zame ta dogara gwiwar hannunta a hannun kujerar,tsananin gajiya yasa bacci har ya
dauketa bata sani ba
Firgigit ta farka kamar an tasheta,ya zame mata jiki tun a gida assalatun farko
take tashi tayi yan nafilfilu kafin assalatu na biyu daga nan idan ta idar tayi
baccin mintuna idan tana da lacture ta shiga kitchen ta shirya
breakfast,yauma gajiyar bata hanata tashin ba saidai ta sabawa lkcn da ta saba
tashi sai kiran a kiran sallah na biyu ta tashi,cikin kasala ta miqe don har yanzu
tanajin nauyin jikinta tayi miqa hadi da salati idanunta suka kai kan wata farar
leda babba mai dan duhu guda biyu tsoro ya darsu a zuciyarta ta katse miqar a iya
saninta sanda zata kwanta babu ledar a gun to ya akai ta samu?cikin sanda ta isa
inda ledar take kamar wadda akace za'a kama,saidai tunkan ta bude ledar qamshin
turarensa ya ziyarci hancinta,hakanne ya bata amsar tambayarta lallai aliyu shi ya
shigo da ledar tayi mamakin yadda har ya shigo ya fita bata sani ba,
Ta bude ledar gasashshiyar kaza ce wadda akai wrapping dinta guda uku sai ice cream
da ya gama narkewa saboda an ciroshi daga ma'ajiyarsa sai fresh milk manyan roba
har uku,sai yoghurt shima roba uku tayi ajiuar zuciya ta mayar da kayan,kasala ta
sake kamata taja da baya ta koma bisa kujerar ta zauna tana aheqar daddadan
turarensa tamkar yanzu yake a gun,ta shiga hasashen fuskan aliyun a cikin wadannan
awoyin da yake angon mutum biyu,kishi ya taba zuciyarta,tafan bata waau lukuta a
zaune ta kasa tabuka komai sannan ta miqe ta lalubi corridor din nan ta zabi
bedroom daya ta shiga,tana alwala tana qarewa tsaruwar toilet din kallo,tabbas dole
hajja gana tace kamar ba za'a mutu ba,bayan ta idar sa sallar ma tana lazumi dakin
taci gaba da bi da kallo tana yaba irin namijin qoqari da iyayenta da yayansu Ahmad
suka yi,bata kammala ba wani daddan bacci ya rinjayi idanunta nan bisa dardumar
sallarta
Hasken rana da ya soma shigowa ta window yana taba fuskarta shi ya farkar da ita,da
addu'ar tashi daga bacci ta miqe a bakinta ta dubi agogon dake ajjiye kan bedside
ya nuna mata goma da minti sha biyar na safe batayi mamakin awanni data shafe ba
tana baccin ba,toilet ta shiga ta kunna water heater dake manne a kusurwar bandakin
cikin mintina qalilan ruwan ya tafasa ta kunna shower ta daidaita zafinsu ta shige
kwamin wankan🛀🏼,tsaf ta shirya cikin atamfa mai zanan manyan ganye mai kalolin pink
da ja sai light blue,dinkin da ita atamfar kanta tayi.masifar karabarta duk da ba
wani make up tayi ba hoda ce kawai sai man lebe da kwalli,dinkin ya lafe mata sai
kayi tsammanin fitted gown ce daurinta yayi das wanda ya awa gashinta damar
kwanciya bisa dokin wuyanta
Ta fito falo ta kwashe siyayyar jiya ta kaisu kitchen,tsayawa tayi kallon kitchen
din tana jinjina kai da dan guntun murmushi akan fuskarta😊ba shakka ummi tasan
tsarinta game da kitchen kuma ta san maitar kitchen irin tata don haka ta cika mata
ahi da dukkan wani nau'i na kayan amfanin kitchen babu ce kawai babu,abun nema ya
samu nan ta bata lokaci gun tsara da shirya kitchen dinta yadda take muradi,tana
tsaka da aikin ta jiyo ringing din wayarta wadda ita sam ma ta mance da ita ta fito
galin tana laluben inda take,tsakiyar filalluka ta hangota tasa hannu ta dahota
tana duba mai kiran garida ta gani tayi yar dariya sannan ya daga hadi da
sallama,muryar farida a qasa ta amsa fadila tace lafiyanki qalau kuwa?"ta masa mata
da "hmmmm,ai dole ki ce min lpy qalau tunda ke naji miryarki garau da ke "fadila da
bata fuskanceta ba tace"kamar yaya? Wani abu ya faru ne a gida?"farida ta sake
ajiyar zuciya tace"mubarak bashi da tausayi Allah sister fadila jiya kada kiso kiga
rashin imanin da ya gwadan,anty hafiza tasan haka amma ta dinga dirka mana
magani"fadila data dau haske a zancan nata tace"to Allah ya kyauta""wlh kin ga na
kasa tashi sister"ta fada cikim karyewar murya,wani yarrr fadila taji tausayinta da
tsoro suka kamata tace"ai ke likita ce saiki kula da kanki Allah ya bada
lpy"tace"amin na gode ina ya Aliyu"
"Baya nan"
Cikin sauri farida tace "kada dai ace samira kika miqawa uwargidan bayan ke aka
fara daurawa aure kuma ke aka fara kaiwa?"
Fadila cikin son abar zancan tace"ban sani ba 'yar jarida kije ki fara jinyar kanki
tukun idan kin warke sai kiji amsa"ta katse wayar,jikinta yayi sanyi sosai a salube
ta zauna agefan kujerar,ashe har faahin matsayinta ma sai da aka mata?ita idan
banda yanzun ma bata san itace gaba da samiran ba tasa hannayanta biyu ta dafe
kanta cikin wani irin yanayi da ta kasa tantance ame take?,ganin ba mafita yasa ta
koma kitchen taci gana da gyare gyarenta zuciyarta cike fak da tunani,
Da azahar baqi suka soma zuwa mata sallama din komawa gidajensu yan maiduguri ne da
yan gwambe,zuwa qarfe uku suka tafi sai su rumasa'u sa'adah minah rahama da hafsah
duk cousins dinta ne rumaisa tace'?"wai ke ya ne?"fadila ta kalleta da alamun
tambaya ,sa'adah ta karbi zancan "gidan farida muka fara zuwa tana can kwance
mubarak nata hidima amma ke gaki dungur gur a zaune"fadila ta juya idanunta🙄
tace"lallai yarannan"da yake ta basu tazarar yan kwanaki ta Dora"kuce kawai uawon
sa'ido yau kuka fito ko"dukkansu suka sheqe da dariya,suka ce"to ai gwara kafin
mu wuce muga lamira sun daidaita " tace"to Allah ya qara muku himmar sa'ido"ta fada
tana shirin shigewa toilet rahama tace"to ai sai ki kira mana angon mana mu gani ko
shi aka dorawa jinyar"ta jiyo ta harareta tace"baki isa ba kuma kwa qaraci zaman
gulmarku ku tattara yammatan qafafunku ku koma inda kuka fito"suka sake aheqe mata
da dariya,ita kuwa ta shige toilet din tana fadi a ranta"koni bancin arziqin samun
ganinshi ba rabonku da ganinsa tun a dinner to nima hakan take"
La'asar gidan ba kowa duk sun yoye sun mata yan gyare gyaren da suka ga ya dace na
game da jere da yan goge goge sukayi sallama cike da kewa tabi kowaccensu da dan
dasheshan turare,turaren wuta ta zuba a bin turare mai amfani da wutar lantarki ta
daidaita sanyin a.c falon yayi wani dadi qamshi da sanyi auka hafe guri guda,turare
na musamman da hajja gana ta musu da kanta kuma ya tsumu sosai don ya jima a ajjiye
ta musu tanadinsa,don haka qamshin har farfajiyar gidan,wajajen biyar ta sake gyara
fuskarta ta feshe jikinta da turarurruka don dama babdaga baya ba fadila gun qamshi
ta gabatar da la'asar da ta kufce mata,tana linke sallayarta tana ci gaba da jiyo
hayaniyar dangin samira don tun farkawarta da safe wajan goma da rabi ta fara jin
zuwansu,ta gama ta koma falo ta kama mbc bollywood dan ta samu ta debe mata
kewa,kafin takai ga zama kan kujerar taji ana knocking din qofarta,ta nufi qofar
tana cewa "waye?"saidai shiru ba'a amsa ba,don haka tasa hannu ta bude idanunta a
waje don ganin waye,a subhanallah,ta fadi a zuciyarta saida bugun zuciyarta 💓ya
dadu sosai fiye da qima,Aliyu ne tsaye a bakin qofar yana sanye cikin wani
lallausan farin yadi qal(tissue),yadin nada shara shara don hakka hatta farar vest
dinsa kana iya hangota,dinkin yarbawa aka masa(boda)iya gwiwa da dogon wando yana
sanye da baqin takalmi idanunsa saye da farin gilashinsa na qa'ida kansa ba hula
sai kwantacciyar sumarsa kamar mai sa mata relaxer saidai natural ce haka sumarsa
take,qamshin turarensa ke dukan fuskarta,tsintar muryarsa tayi yana cewa"su bar
maka a nan ka dinga daukowa kana ahigowa da su"hakan yasa ta tabbatar bashi kadai
bane,tayi niyyar yin sauri ta koma ciki don ba hijabi a jikinta saidai ta kasa
moysa qafafunta,sai jan jiki da tayi ta rakube a bayan qofa,nasiru n yake shigowa
da kayan abinci duk wani dangin abunci da nasha na har ya kammala shigewa da su
tsaf aliyi na tsaye tsakiyar falon hannayansa zube cikin aljihunsa yana facing
qofar store yayin da ya juyawa qofar shigowa baya,ta haka fadila ta morewa kallonsa
ba tare da ya sani ba,ingarman namiji ne wanda siffar qarfi ta bayyana atare da shi
bayansa kawai ka kalla zaka fassara hakan,nasiru ya fito yana kade hannayansa ya
dan russauna yace"yallabai na gama"yana qoqarin zaro kudi a aljihunsa yace"yauwa ya
miqa masa kudin yace"raguna zaka samo guda biyu ka biyaau su gyara komai su wanke
acan ka duba motar zuwa kasuwa ka tafi a ita""to yallabai"ya fada yana shirin
wucewa"nasir"aliyu ya kirashi a aladabce ya juyo yana amsawa"ka biya ta gidan gona
su gyara kaji ka taho da su""an gama sir"cewar nasiru ya fice da sauri
Ya juyo yayo tattaki har zuwa bakin qofa,fadila ta saci kallonsa sai taga
hankalinsa na waje,cikin sanyin jiki da sanyin mutya tace masa"ina wuni"yqdan kalli
sashin da take ya kauda kai,cikin wata dakakkiyar murya yace"kada ki qara zama haka
bayan kin san cewa ba ni kadai bane,in kunne yaji......"tace"to"har yasa qafarsa
awaje yadan dawo da baya ba tare da ya dubeta ba yave"qarfe takwas ki sameni a
gefena"to ta sake cewa,"shikenan babu abinda kike da buqata?"ya fada yana duba
agogon hannunsa,"babu"tace
"Ok ki duba saman kujerarki"kawai yace yasa kai ya qarasa barin sashin aransa yana
cewa"ta wani labe sai kace wadda ake kora"
Hannayansa harde bisa qirjinsa yake bin harabar gidan da kallo ,ko ta ina dangin
samirah ne kamar wani sabon bikin suke sakewa,ba bainda auke illa aikin dafa abinci
da kade kade,shiba wannan ne damuwarsa ba hayaniya ce baiso sam ko kadan,musamman
wannan lokavi da tun daren jiya zuciyarsa ke a cunkushe,lamarin na taba ransa sosai
yanayin da ya samu samira a daren jiya tun daren bacci ya qauracewa idanunsa,yaja
siririn tsaki a ransa yace"wai duk haka matan suke ne?"bashi da mai bashi amsar
tambayarsa don haka ya nufi sashensa
Damuwa ita ta haddasa masa gajiya da kasala ya zauna bisa kujera ya miqe duka
qafafunsa kan kujerar ya hardesu yasa hannunsa na dama yana shafar sumar shi,tunani
ya masa yawa ya rasa da wanne zai fara,yana a haka yaji knocking kafin ya nada
izini har ta shigo,tafiya take tana wani karairaya kamar mai ahirin tsinkewa ta
kafa masa ido tana murmushi,sam ko kusa bata burgeshi ba hasalima wani tsanarta da
baqinta yake gani,ta haue kujerar da yake kai kamar zata koma cikinsa"sweet aly ina
ka shiga tunda ka kawo kayan abinci ka fice"ya dauke kansa yana qoqarin janye
jikinsa yace"na koma kasuwa ne"
Ta dan bata fuska ganin yadda yake nuna kamar yana qanqyaminta tace"haba sweet wai
meke damunka tun daren jiya fa ma lura da sauyawarka,bayan wannan lokacimmu ne da
ya kamat ace mun moreshi,pls kada ka bari wani dan qanqanin abu ya tarwatsa mana
jin dadin wannan lokaci da muka dade muna tanadin zuwansakada ka lalata mana
suitable moments dimmu"kallon da ya watsa mata shi ya firgitata ya kira sunanta da
wata murya da ta qara razanata
"Kin dade da wargaza farincikin wannan lokaci tuntuni da hannunki"ta dan zaro ido
cikin duniyanci😳 tace "kamar ya wai me ya faru?"ganin tana shirin raina masa wayi
yasa ya.miqe gami da jan tsaki yace"ni zaki mawa silly question irin wannan?"ta
kama gefan rigarsa tana shirin kecewa da kukan kirsa tave"din Allah ka gayamin me
na maka?",ransa tafasa da suya kawai yake,ya dawo da baya yana huci ya ranqwafo
kanta tamkar maiahirin fadowa kan nata har tana jiyo hucin numfashinsa,ya ware sexy
eyes dinsa soaai a kanta wadanda bata san suna da girma ba haka miuyarsa a shaqe
yace"u mean bakisan kinyi loosing virginity dinki ba,u did not know u r not a
virgin!! A ina kika bada kanki samirah!!!"ya qaraahe cikin qaraji saboda wani kishi
dake sukarsa,
Wani kuka ta rushe masa da ahi harda dora hannu a ka🙆🏻 kasancewar tasan halinsa
baisan kuka ko da na yaro ne qarami yanzu zai dameshi,gunji take sosai hakan yasa
temper dinsa ta fara raguwa,ya koma da baya ya zauna sosai,ta qasqantar da kanta
tamkar wadda zata masa sujjada ta muzanta sosai,ta tsara masa qaryar fyade aka mata
tun tana qanqanuwa"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"ya dinga mabata ahankali har
yaji zuciyarsa ta fara sanyi duk da wani bangaren na zuciyarsa ya kasa gasgata
labarinta,ya amince haka qaddararsa take,shi kam ya sani bai taba koda kusantar
zina ba bare ya aikata ta amma Allah ya jarabceshi da samun mata har biyu da suka
zo masa babu budurci,harda matarshi ta fari
"Ya isa,is ok "yace da ita,"hakan baza ta sake faruwa ba"yaci alwashin hakan,ta
ruqunqumeshi tqna ta zuba godiya xikin zuciuarta tana godewa allah da asirinta
baitonu ba don bazata iya jure rashin aliyu ba,baiga alamun tayi wanka ba don haka
ya tambayeta,ai kuwa ta narke murya tave"na manta yadda ka koyan jiya da
daddare"cike da madaukakin mamaki yake kallonta mace yar kimanin 25yrs amma ace
bata iya wankan janaba ba ya koya mata ta kasa daukewa ?tun asubar jiya kuma tana
zaune da janaba ajikinta bata damu ba to ina ga ban sallah kuma?ya jin jina kai
yana hamgo girman aikin da ya sameshi,duk kuma yawan yanuwanta da sukazo a rasa
wanda zai kwatanta mata harkar gabansu kawai suke,ya fuskanceta sosai ya sake koya
mata ,nan toilet dinsa yasa ta shiga bai barta ta fita ba sai da yaga ta kammal ta
kuma rama dukkan sallolin dake kanta
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 12:30 PM] Salma:
Wa yasan gobe?

Written by safiyya Abdullahi musa huguma

1⃣2⃣ 1⃣2⃣
▶1⃣2⃣
Har magariba fadila na bisa kujerar ta kasa tashi,kudin da ya jiye mata na gefanta
tafa ce ta dubu dubu guda biyu,tasa hannu ta sake juya kudin a karo na barkatai
"nafi buqatarka Aliyu fiye da kudinnan fiye da komai ma,me zaniyi da kudi"ta raya
haka a ranta,kiran sallar magariba da aka qwalo a masallacin qarshen layin shi ya
kawo qarshen zaman dirshan din da take,wanka ta soma dama ita gwanar sa ce don wani
lokacin farida kan tsokaneta da agwagwa sarkin wanka ta hado da alwala bayan ta
fito ta sa hijab ta gabatar da magrib sannan ta zauna tana azkar tana kuma jiran
kiran isha'i
Minti arba'in tsakani ta jiyo kiran isha'in saboda haka ta tashi ta bada ita ta
kammala da addu'oi ta shafa sannan ta isa madubinta dake cike da kayan
kwalliya,kwalliya ta yi mai qayatarwa bata hauka ba mai cika fuska da yake ba baya
bace gurin kyau sai kayi tsammanin bata lokaci tayi gurin yinta ta amsheta sosai ta
kuma dave da yanayinta,ta bude duk sif dinta ta zuba mata ido tana tunanin wanne
kaya zata saka?,hankali take shafa su har hannunta ya kai kan wani material
Pink ne mai adon dark blue da dark green din zare da golden sai wasu dutsuna da aka
caba ado da su masu sheqi suma golden colour,dinkin doguwar riga ne da mayafinsa
material din yake zuwa,yana da sulbi da taushi ba santsi ba yana shaking kadan a
jiki don haka da tasa sai yabi jikinta ya lafe ya kuma haska kyakkyawar chaculet
din fatarta fashion na dutse ta dan madaidaici ta maqala a kunnenta sai siririyar
sarqarsa data lafe a dogon wuyanta sai zobe blue shima qwaya daya da ta saka a
yatsan tsakiuar hannunta,ta shafe jikinta da tutaren asaal da ahlamul arab tame
suka gauraya suka bada wani daddadan qamshi mai sanyi ta zura plate shoe pink ta
dau mayafin kayan ta nade kanta da shi
Sannu ahankali tame ratsa gidan sai yanzu ta qarewa gidan kallo ita kam ya burgeta
tsarin sosai,tamkar kana turai,ta sauke ajiuar zuciya sanda zuciyarta ta raya mata
dama ita da Aliyunta ne kadai ke rayuwa cikin gidan rayuwa kuma irinta soyayya
cikin takun nutsuwa ta nufi qofar da zata sadata da bangaran nasa ido ta saki tana
kallon ko ina,tako ina bangaran nasa yafi naau kyau da tsaruwa sosai,tun daga
varender dinsa take jiyo sassanyan qamshinsa,ta shiga falon a nitse falone da ya
tafi da gaba daya tunaninta tamkar gadar shugaban qasa,haduwarsa da tsaruwarsa tafi
gaban kwatance
Idanunta suka sauka kanta tana hakimce kan kujera tana fuskantar t.v tana sanye ne
da riga body huge da wando na jeans wadanda suka mata dam dam,ta baza kitson
attachment din da aka jibga mata aka har gadon baya,fara ce sosai don har wani kore
da yalo gefe da gefan fuskarta yake tabbacin kaso saba'in cikin dari na farin nata
ya qara shi ne da man kanti,tana da jiki amma ba can ba da alama nan gaba kadan ta
samu hutu zata narja qiba ne,tabbas ba don farin da ta aro daga kanti ba kana mata
kallon farko zaka saka ta a sahun muna na amma sai farin ya boye kaso hamsim cikin
dari na munin nata
Fadila ta sake jadda da sallamarta a karo na biyu sai Aliyu ne dake zaune bisa step
kan dining ya amsa yayin da samira tayi saurin dago idanunta tana kallon mai
shigowar idanunta suka fada kan fadila wani faduwar gaba taji amma ta maze don bata
son fadilan ta fuskanci ta razana da ganin da ta mata,maimakon haka ma sai ta mata
wani kallon raini na sama da qasa sannan ta janye idanunta ba tare da tace kanzil
ba
Bata ma lura da kallon ba tana qarasowa cikin falon ta yiwa kanta matsugunni bisa
tattausan carfet din da ya malale dakinta jingina jikinta da kujerar dake
bayanta,wani abu ke tsunkular zuciyarta game da kishi duk da ta godewa Allah da ta
tarar samirah bata fita da komai ba sai farar fata don ta tsammaci aliyu zai so
matar da ta fi samira ne ba kamar samiran ba cikin ranta take cewa lallai so hana
ganin laifi,to ganin samiran ko sashen da take bata kalla bayasa itama ta dauke
mata kai sai ma ta zaro wayarta ta shiga latse latse
To shima Aliyun sai da ya kammala abinda yake ya shiga bedroom dinsa ya dan jima
sannan ya fito ya samu kujera daya ya zauna ai kuwa tsam samira ta bar gurinta ta
dawo jikinsa ta lafe kamar mai shirin komawa cikin sa ta gefan ido take satar
kallonsu wani abu mai daci na damunta,amma a haka idan ka kalleta sai ka rantse da
Allah batasan Allah yayi ruwansu ba don bata fasa danne danne a wayarta ba
Da bismillah ya fara yayi salati ga fiyayyen halitta yaja dogayan addu'oi wandabhar
samira ta fara nuna masa tafa gaji,fadila ita mamakin yadfa Aliyu ke zuba addu'a
take tamakar ba daga bakinsa suke ba(hmmm fadila kenan bakisan waye Aliyu bane
😜)ya kammala sannan ha shafa,ina godiya ga Allah bisa ni'imomi da ya yimin a
rayuwata tun daga haihuwata har kawo yau,ya kalli samira yace ga abokiyar zama nan
Allah ya qaddara tare zan aureku sai kj zauna lpy bana buqatar hayaniya ko tashin
hankali a gidana kowacce ta kama kanta ta tsaya inda Allah ya ajjiyeshi....
Ya dan sarara sannan yace idan da mai magana bismillah ya koma ya jingina da kujera
yana jiran cewarsu,samira ta saci kallon fadila tana jiran taga zata tanka sai taga
ma Sam idanunta bai kansu ta aza su ne bisa carfet,ta gayara zama cikin iyayi da
kisisina tana kuma yatsuna 😏 tace"to nidai bana son shishshigi kuma bana son
raini ehe.....kuma kowa ya kwana lpy shi yaso,sweet banji kayi rabon kwana ba?"ya
daga kafada yace"its un 2 u ai"tayi wani fari da ido🙄tace"zamu raba kwana dai dai ne
yayi aiko?"ta tambayeshi ya sake faga kafada yace taakaninku ai nikam ban iya yawon
bin bangare bangare ba,"hmmm shegen girman kan tsiya"fadila ta fada a zuciyarta,duk
da idan ka kalleta zakayi tsammanin bata tare da su,yauwa sweet ina kuma da buqatar
☝🏼
masu aiki do.....cikin dakiya ya tari numfashinta,ba'a gidannan ba ,inji aliyu,ta
narke murya,please sweet pls mana"bani buqatar roqo✋🏻ra'ayina ne"shiru tayi don
tasan Aliyu idan yace eh babu mai sashi yace a'a,bare ita da take lallabawa tasan
har yanzu lamarinta bai saki zuciyarsa ba
Dakin yayi shiru har ta gama kidanta tayi kuma rawarta ita kadai,ba wanda ya nemi
jin ta bakinta Aliyu ya rufe da addu'a,ita din ma bata zaton ko sun ce tace dinma
zata tsinka wani abu,suka shafa addu'ar ta miqe ta fice ba tare da ta cewa kowa
komai ba,samira ta bita da kallo ranta cike fal da kishi saboda komai hassadarta
bata gano abun kushewa tattare da fadilan ba
Shima kallon gun da ta tashin yayi yana dan mamakin sauyawarta yayi tsammanin za
susha artabu ne kamar yadda suka saba a gida sai kuma yaga b sabanin hakan
A bangaranta fadila dana sanin zuwanta tayi gun sosai don bai qareta da komai ba
sai hanata bacci da ya yi duk yayin da ta runtse ido da niyyar baccin sai hoton
fuskar Aliyu ya bayyana cikin duhuwar idanun nata,wata iriyar soyayyarshi ke mamaye
ruhunta cikim tsakiyar daren kewa ta kamata ga kadaici da ya hanata sakat,so ne da
bata yaba jin irinsa ba a rayuwarta qauna ce ta musamman,hakanne ya zama sanadiyyar
karyewar zuciyarta duj yadda takai ga bawa kanta qwarin gwiwa,kuka ne matsananci ya
sarqeta,daren tayi kuka mai yawa a kwancan tana tausayawa rayuwarta da
makomarta,tasan tabbasa son Aliyu na daya daga cikin jarabobin rayuwarta,tanajin sa
a jiki jini jijiya da ruhinta
Cikin taimakon Allah bata manta da ambatonsa ba hakan yasa bacci yayi nasarar
daukarta
👏🏻👏🏻👏🏻 ayimin afuwa a danyi haquri da wannan sai Allah ya kaimu gobe
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 
  
[10/16, 12:31 PM] Salma:
Wa yasan gobe?

Written by safiyya Abdullahi musa huguma

1▶1⃣3⃣
3 13
1⃣3⃣
Kwanakin da suka baya ta yisu ne cikin kadaici da kewa,ita kadai ke wuni a bangaren
nata,bata da aiki sai wanka da sallah da shi dama abinci ba gwaninta bane saidai
tayi ta jiyo muryar baqin samira da har yau suka qi qarewa,wani lokaci kuma ta kira
farida su sha hirarsu
Ranar da ta cika kwanaki bakwai a gidan ranar tana kwance a falo hannunta riqe da
littafin sahihu muslim mujalladi na daya tana karantawa da yake mayyar hadisi ce
ita ta jiyo ana knocking din qofarta ta dora littafim a saman kujerar taje ta bude
Anty hauwa ce da yaranta bilkisu kausar Ibrahim sai qaramin su muhammad sai kuma
madina qanwar momy da yaronta hamid sai iftihal,farinciki sosai fadila tayi don
tasan yau babu wunin kadaici,nan falin ya kaure da hayaniya su suna hirarsu yana na
nasu,ta shiga kitchen ta hado musu kayan motsa baki sannan daga bisani ta nufi
kitchen don dora girki iftihal da bilkisu suka bita zasu tayata don sune yan manya
madina ma binsu tayi aka bar anty hauwa da ragowan yaranta suna kallo fadila tayi
tayi madina ta bari amma taqi don haka tare suka kammala komai,tare suka ci a
babban plate guda yaran ma aka hada musu anti hauwa ce tace ayi haka kada a bata
mata kwanunka,bayan sun gama madina ta hada kan kwanunkan ita da su bilkisu suka
gyara mata komai,ganin ba kowa a gun anty hauwa ke tambayarta ina fatan dai baki da
matsala da Aliyu ko dan kishiya wannan kam ita ba'a rasa ta da matsala saidai
haquri ,dan murmushi fadilam tayi tace"ba wani matsala anty lpy lau muke"ta jinjina
kai tace to saidai a yita dai haquri don kinsan zaman aure ya gaji yau fari gobe
tsumma,tayi mata nasiha sosai tare da bata shawarwari masu gamsarwa fadila sosai
taji dadin maganganunta hakan ya sake qara mata qwarin gwiwa da nutsar mata da
zuciya
Bayan sun idar da sallah ne ta la'asar wajan biyar da rqbi suka soma haramar
tafiya,iftihal tace da naty hauwa mummyn kausar nidai anan za'a barni ko?,antu
hauwa ta girgiza kai tace a'ah ai ba haka kukayi da mummy ba,bazan iya da wannan
rigimarba tate zamu tafi da ke,ta soma diddira qafa tana maqale kafafa tana cewa
nidai anan zan zauna mummyn kausar gaskiya,fadila tace da anty hauwa"anty don Allah
ku barmin ita mana dama ni kadai zaman ba dadi wlh"anty hauwa ta zaro ido
😳 tace"wai rufamin asiri ai mummy bazata iya zama ba iftihal ba ko na barta da
kanta zatq zo ta dauki abarta baki ji yadda aka kafa mana sharadi ba kan a bamu mu
taho da ita kamar tasan za'ayi haka"jin haka yasa fadila ta haqura
Ta tako.musu har waje bakin part dinta yara nata tsalle kowa da packet na chaculet
dinsa a hannu ta bawa su anty hauwa turarurruka da qyar ta karba tace ita lpyrsu
kawai ta zo gani,ganin suna shirin yin gaba ba tare da sun shiga gun samira ba
tace"antu baku leqa gunta ba kun gaisa"anty hauwa tace o'o'o ni kam tun shigowarmu
muka gaisa da ita a harabar gida ta rako baqinta sai dai ko madina ita da
yara,madina ta tabe baki tace nima bani zuwa anty ina kallo fa sanda muka shigo
tana ganinmu tayi saurin sallamar baqin ta juya ciki kema sai da kika kirata kusan
sau uku sannan ta amsa miki,sai dai su kausar maza kuje ku gaidata ku fito mu tafi
ungoshi bilkisu ga hamida ma aje da shi ai ya wakilceni
Suna tsaye suna jiran yaran sai kuwa gasu jiki a salube sun dawo Ibrahim sarkin
zuciya hadda guntun hawaye madina na amsar hamid daga hannunsu tana tambayarsu me
ya samesu,bilkisu tace anty koromu tayi wai ba mun gaisa a waje ba meye kuma na
wani biyota,ibrahim da ya fisu shekara yana kusan 12yrs yace"har tsawa fa tayi mana
wai masu qwala qwalan ido sai kallonta muke wa ya sani ma ko turo mu kayi mu
cinyeta"iftihal kam fuskarnan a turbune tqma kasa cewa komai,anty hauwa tace ya
'isa haka is ok bata mata rai baqinta suka yi ku wuce muje,sukayi gaba fadila da
mamaki ya kamata tana biye da su mamakin samira take sai kace wata mahukaciya yara
zata tsaya tana gayawa irin wadannan magan ganun sai ka ce wasu manya,suna gab da
get suka ji ana kwararo horn mai gadin ya tashi da azama ya bude wawakeken get din
wata farar motace sol qirar range rover ta shigo ta samu gun parking ta tsaya da
gudu iftihal ta kwasa tayi bakin motar
Ya bude motar ya fito sanye yake da suit masu bala'in kyau baqaqe sunyi masifar yi
masa kyau da kwanciya lif a farar fatarsa tas da shi kamar yanzu ma yake ahirin
fita aikin ba wai ya dawo bane,iftihal na qarasawa ya cafeta ya daga ta sama ya
jujjuyata yayi kissing kumatunta sannan ya direta ta tsugunna da alama gaidashi
tayi,madina tayi dariya😀tace "oh uwar wayon tsiya wai har motocin Abbanta ta sansu
wannan yarinya "anty hauwa tace"ke ai iftihal da wayinta aka haifeta don.mummy tace
duk cikin jikokinta bata ga mai wayonta ba"da hirar iftihal da suke suka qarasa
gurinsu ,cikin motoci fadila ta dan rabe bayan wata mota tana ganinsu tana kuma
jina binda suke cewa,ya dago yana masa sallamarsu.lokacin da yake tambayar
iftihal"ashe tare kuke mummyn yara"anty hauwa ta mayar masa ta sigar da ya fada"😊
mummyn yara tun dazu tazo kuma yanzu zasu koma"ya juyo yana kallin madina yadan
hade rai yace"au da waccar kima zo"anty hauwa dake danne dariya tace"eh duk tare
muke"tasan yar tsamarsu da Aliyu don tun ranar da take fadin ita babarsa ce tunda
qanwar mummy ce bata san yana gun ba suke yar tsama ya daina sakar mata
Ya miqawa su ibrahim hannu suna musabaha haka halayyarsa take dama yana dan
tsokanar ibrahim din kasancewar sunan kakansu ne shi kuma ibrahim na murmushi ya
karbi hamid daga hannnun madina yana duban anty hauwa yace ba wanda ya rakoku
ne?,anty hauwa tana dube dube tace tare da fadika muke ina tayi ne?,fadila data
dora hannayenta saman motar tana game a wayarta har dankwalin kanta ya zame bata
sani ba ta dago jin an ambaci sunanta idanunta suka fara sauka kan aliyu cikin sa'a
suka hada ido harara taga ya balla mata wani abu taji ya caki zuciyarta ta lumahe
idanunta am ta kasa budesu wani sinsa taji na mamayar zuciyarta da gangar jikinta
kamar ana zira ra mata ruwan sanyi bugun zuciuarta ya sake qaruwa,bata san me tayi
masa ba yake harararta,sai tq sunkuyar da kanta😔 tana kallon yatsun qafarta dake
saye cikin slippers,sai da iska ta watso mata gaahin kanta gefen fuskarta sannan ta
gane ma'anar hara rar da aliyu ke mata don bata manta ba rabi'ah ta taba fada mata
ya aliyu baison yawo a waje ba dankwali idan ya ganki kuwa kin shiga uku,da sumauri
ta jawo mayafin data yafa ta lullune kanta sosai
Duk daga idon da zatqyi a rayuwarta ta kalli aliyu sai taji an qara manna mata
sonshi ji taje kallomsa ma kawai jaraba yake zamewa rayuwarta sai dai koda tayi
niyyar qin kallon nasa sai ta kasa jure haka domin zuciyarta bata lamunce mata
ba,ba abinda ke sata nishadi irin kallon kakkyawar qayatacciyyar fuskar tasa
To fadila za mu wuce sai an kwana biyu kuma,cewar anty hauwa tana dan murmushi
😊 ta taso daga jikin motar da niyyar sake yi musu tattaki suka sake hada ido da
shi sanda tayi niuyar satar kallonsa wata hararar mai zafi ya sake watso mata wadda
ta sata tsayawa daga nan cak,yaram suka taho suna kama hannunta suna cewa anty bye
bye,itama ta daga musu hannu✋🏻 tana dan murmushin yaqe😇 tana cewa"bye"sai kuma
iftihal ana su taho ta ja tunga ta tsaya ita allan katafar ba zata bisu ba aliyu
dake karbar takaddu daga hannun nasuru ya juyo yana tambayar meke faruwa anty hauwa
ta masa bayani,kallo daya tak yama iftihal din tabi bayansu jiki na rawa

1⃣4⃣ 1⃣4⃣
▶1⃣4⃣
Bata sake sha'awar kallon inda yake ba don ta gaji da ganin wanna hararar tasa da
kallon qiyayya da yake jifanta da su sai ta juya da sassarfa don barin gurin
"ke"taji dakakkiyar muryar Aliyu,batason irin wannan kiran sam don haka tayi banza
bata juyo ba bata kuma amsa ba kuma bata daina tafiyarta ba ya sake daga murya
yace"dake nake"sai ta tsaya cak saboda tsoron da ya bata muryarsa ta canza tayi
fakare tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,da tsawa yake mata magana bayan ya sha
gabanta"ki baki isa a kira ki ba kenan ki tsaya"tamkar tace wani abu sai kuma taga
bai kamata ba tunda a harabar gida suke wani zai iya zuwa giftawa ya jisu
Aliyu ya kafeta da ido yana huci a zuciyarsa yana fatan ta tanka masa ko zai samu
ya huce mata haushinsa amma ko kallon fuskarsa taqiyi hasalima sadda kanta tayi
qasa,ganin da ya yi bata da niyyar ko alamun tanka masa sai ya dora mata baqar leda
mai dan matsakaicin girma bisa qafarta yaja tsaki gami da hura mata hucinsa akan
fuskarta ya wuce,sai sannan ta dago tabi bayansa da kallo tana sheqar iskar wadda
ke bada qamshin lemon fresh na mouth fresh,ta kauda idonta sai kuma ta hango
samirah na tsaye bisa varender dinta ta zuba musu ido don haka sai ta saki murmushi
ta kuma yi saurin dauke ledar tayi bangarenta tana qara hasko fuskar aliyu qamshin
turarensa maganarsa komai nashi unique ne mai tsari ba baunda tafi buqata a yanzu
irin aliyum saidai tasan samun nasa ba baune mai sauqi ba wanda zata cimmawa cikin
qanqanin lokaci
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Kamar ko yaushe a irin wannan lokaci tana kwance kam dogowar kujera a main parlour
kunnenta maqale da earpiece tana sauraron suratu baqara cikin qira'ar sheikh
Abdurrahman assudais taji ana mata knocking kafin ta bada izini tuni an bude an
shigo,ga tarin mamakinta samirah ce ,ta tashi zaune tana qoqarin cire earpiece
samirah ta qaraso tana kallon yadda take qarewa parlour din kallo zuciyarta cike da
kishin yadda parlour din fadilan yafi nata tsaruwa da kyau,fadilan nata biye wa
wanna ba ta nunawa samirah gun zama tace bismilla ga guri zauna😒"ta wani tabe baki
tace"ba zama na zo yi ba don nima gidana akwai gun zaman "jin haka yasa fadila ta
gane ba mutuncine ya kawota badon haka sai ta koma tayi kwanciyarta kamar yadda
take da ta kuma maida earpiece dinta kunne ba tare da taci gaba da sauraron karatun
ba
Da samira taga haka sai ta yatsine fuska sannan ta fora da cewa"nazo ne don na
tuntubeki bakiyi shirya fara zuwa turakar miji bane?,sai tambayar ta bawa fadila
mamaki ta kuma ji wani bawai tana daga kwancan ta dubeta"kamar ya?,me kike nufi
ne?"samira ta juya ido👀 tace"a....to gani nayi har yau baki fara zuwa ba shi kadai
yake kwana nima ba zuwa nake ba tunda lissafe kwanakin amarcinki ne"mamaki ya sake
kama fafila don ko a lbr bata taba jin ko ganin raahin kunya irin wannan ba wato ma
idonta na kanta kenan
Tilas ta miqe ta zauna sosai don nuna wa samira ba ita ce kawai mara munya ba itama
ta iya barikancin nan,"da farko baiwar Allah ajiyata aka baki?,ko kuma da mai gidan
kukayi maganar bana zuwa gunsa?,to idan ajiyata aka baki ina mai baki shawarar kiyi
gaggawar maidawa wadda ya baki ajiyar don wannan aniyar tafi qarfin ki wlh ba zaki
iya ba idan kuma shi mai gidanne ya gaya miki bari na sake tambayomiki shi.....,ta
fada tana jawo wayarta tana shirin shiga contact cike da barazana don bata
tsammanin ko number dinsa akwai cikin wayarta😜
Ganin da samirah tayi da gske kiransa zatayi kuma ta san sarai halin Aliyu bare
tana cikin case har yanzu lallabawa kawai ake sai tace"dakata ni ba gangami nace
kiyo ba magana ce iya kacina da ke"ta juya tana shirin barin falon fadila ta dan
daga murya tace"ai da kin tsaya an sake jin ta bakinsa ko kinga maji dadin qarasa
maganar,mu amarci muke mai lasisi ba irin naki ba"bata ce uffan ba ta fice ta ja
mata qofa,wani takaici ya kama fadila taja wani dogon tsaki tana cewa"banza
ballagaza ko angaya miki ke daya kika iya bariki ne kina ganin kin girmeni ko,da
auren so mukai da aliyu wlh kallonki ma kace yayi sai yaji an hada shi da aiki"ta
koma tayi kwanciyarta yadda take taci gaba da bin karatunta
Kwanaki nata tafiya da fadila cikin gidan,ba wani qiba da zaka ce ta qara sai
fatarta da tayi lumi lumi ta sake fresh saboda zaman guri daya
Watanta biyu kenan da sati yakwas kwankin da take jinsu kamar waau shekaru saboda
zaman kadaici,Allah allah take sakamakonsu ya fito bata da sha'awar komai illa ta
fara fita aiki,ta jawo wayarta ta soma neman nafisah classmate dinta ce suna
gaisuwar mutunci da fadila don har bikinta tazo tave cikin zuciyarta bari ta kira
ta tambyaeta ko sakamakon ya fito saidai nata sameta ba number dinta a kashe don
haka ta maida akalar kiran layin anty hafiza sunsha hira aosai ta kuma yi mata
qorafin sunqi leqota ba ita ba yan biyu gsky tayi fushi tace tayi hqr insha Allah
zasu zo su yinin mata,bayan sun gama sai ta kira hafsah da aukayi attachment tare
sun gaisa sosai take tambayar hafsa ko result ya fito tace yana dai hanya da ya
fito insha Allah zata sanar mata tayi mata godiya suka kashe wayar
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Zaune take alambun dake bayan part dinta kan kujerar siminti under wear dinta take
wake wa su brassiere pant da skert gun tsit yake shima kamar yadda gidan nasu yake
saidai ahi akwai kadawar ganyayyaki da kuma kukan tsintsaye jifa jifa wadanda take
zubawa gero shi yasa suka dadu kuma suka fi yawa alambun nata fiye da ko ina a
cikin gidan tana son gun sosai saboda yawancin lokuta yakan zamo daya daga cikin
abinda ke debe mata kewa ko da yaushe gun luf yake dauke da inuwa mai sanyi
bata barin undies dinta wanna ma kwana biyu ne da bata jin dadin jikinta dama
cutarta ciwon kaine ko ciwon mara shi yasa suka taru haka ita dama can ko a guda da
wahala kaga kayanta cikin kayan wanki ko za'a mai saidai kaga na fatida tafi ganewa
tana cire maya ta sabesu ta shanya sannan ta shigà wanka,tana cikin shanya ne taji
takun taviya sai tayi sak don dai tasan ita kadaice a gun kuma ta kulle sashen nata
da idanunta take bin gun da kallo don gane daga ina takun yake,Aliyu ne ke taho wa
hannayensa harde a qirjinsasanye yake da jar t.shirtmai gajeran hannu sai dogon
wandon jeans mai kalar black blue sau ciki ya sanya balck blue idanunsa saye cikin
glass dinsa na qa'ida fari qal zuwa lokacin fadila ta soma tsammanin medical ne
bana gayu bane,tayi saurin dauke idonta dag kansa zuciyarta na wani das das das har
ya qaraso gabnta ta kasa moysawa tamkar ta nutse saboda irin kayan dake jikinta ta
tabbatar babu mai shigo mata ne don ta kulle qofarta shi yasa ta saka su rigane da
akery sosai sai dai maau roba ne iya qibarka iya yadda zasu fidda shape dinka gashi
gaba daya hannayen ta da skrt din anbi an tsaga ko ina babu inda ya tsira wuyan
rigar mai fafi ne son ana hango saman qirjinka sosai kanta kuwa ba dankwali sai
tafkeken ribbom da ta saka ta mate gashinta ya sauka mata a kafada duk da ya danyi
tauri sabida raahin zuwa saloon kwana biyu
A dabarance take duba jikinta tana sa hannu tana gyara inda hannunta fuk yakai
saidai ina duk In da ta sa taja ta rufe sai wani gurin kuma ya bayyana shikam
hannàyensa na harde ya jinggina jikin qarfen da ta ware tan shanya kayan idanunsa
duka ya zuba mata duk dabararta na tattare jikinta sai da ya ganota shi sai abin ma
yaso bashi da riya duk da a fuaka sai ka ranyse rufeta ma zaiyi da duka"bari nayi
maganin yarinyarnan'ya fadi haka cikin zuciyarsa"ni da waye a gun kiketa wani aikin
rurrufe jiki?,gabanta ya fadi kunya ta sake kamata sai taji ya ja tsaki wanda yasa
ta dago ta kallo shi ba tare da ta dubi qwayar idanunsa ba don tana kaucewa hakan
bataso au hada ido sam don tana tsammanin yana da wani asiri ne cikin qwayar
idanunsa aduk sanda qwayar idanunsa auka hafu da nata takan kwana ne ta wuni cikin
begensada kuma aAbar aonshi da take ta yaqin ganin ta bunneshi cikin babin
rayuwarta,wa ya gaya miki an damu da jikin naki da kiketa qoqarin killaceshi
ne?...... Ba wannan ba na duna store naga yadda aka Uba kayan abinci haka suke ba'a
taba ba kamar wadda ka bai wa rancansu sannan fridge ma haka yake abu qalilan ne
suka ragu mekike nufi? Salon kija min bala'i ko?wannan wankin kuma da kika hafo na
meme?duk masu wankin gidannan suma basu miki ba ko gulmar azo a tarar kina wanki
ace wuya kike sha?burinki dai kawai na zama mai lafi
Ya tsagaita da fadan ya kafeta d ido ko zata ce wani abu amma yaga ba alamu duk da
zuciyarta ta baci da yadda aliyu ke mata a cikin gidan ba dama inuwa daya ta haasu
sai fada tsakaninta da shi?cikin zuciyarta taja tsaki gami da cewa"shikenan kuma
sai akace mutum bàshi da aiki sai dirkar abinci kamar tsohon jaki?kuma ma wane aiki
nake don na dwbo yan kayana na wanke da hakan zai zama laifi agun wannan mutumin?
Bata tsammci a fìli tayi maganar ba sai da ta ji yace"duk basu zama laifi ba amma
ki shirya duk ranar da aka tuhumeni da wani laifi akanki kisan yadda zaki kanki don
daukar ki zanyi cancankat nakai musu ke"ya maida kansa gun agogon dake daure
atsintsiyar hannunsa 😠 yace"me dame kike da buqata?a gajarce tace masa"ba
komai"yayi tattaki ya sake qarasowa gabanta ya ajiiye mata kudi kamar yadda ya saba
ya rabe ta gefanta ya wucè tana sheqar daddadan qamshinsa wanda yaja mata kasalar
da ala dole ta tattara ragowar da bata wanke ba ta maida ciki
Mrs muhammad ce
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 12:33 PM] Salma:
Wa yasan gobe?

Written by safiyya Abdullahi musa huguma

1⃣5⃣ 1⃣5⃣
▶1⃣5⃣
Washegari misalun takwas na dare tana zaune a falo tana kallon wani film gabanta
plate ne ta yanka kankana apple da gwanda tana sha dama abincin bai wuce ire ire
wadannan qwaqwaso qofar taji anayi ta dauki hijabinta dake gefanta wanda ta idar da
sallar isha'i da shi ta zura sannan ta miqe tana tambayar wane?ki bude mana,taji
ance bata dau murya ba amma ta gane maca ce,ta bude ba yare da ta kauce daga hanya
ba,samirah ce tsaye cikin kwalliya rakacau a fuskarta tana sanye da doguwar rigar
atamfa tayi rolling dawani siririn mayafi sai uban turare data bulbule jiki da shi
tana taunar chewing gum qas qas qas, tana wani ya tsina fuska tace sweet yace ki
fito zamu siyayya,fadila tace😏 waye sweet kuma?,ta wani juya ido tace my aly,
Tabe baki fadila tayi tave kice bani buqatar komai,bata jira cewarta ba taja
qofarta ta rufe,wani kishi ne ya motsa mata ita kanta tasan tana da tsananin kishin
aliyunta amma ya ta iya?,ta jiyo muryar samirah na masifa"aikin banza wa ma ya damu
da ke
?kada Allah ubangiji yasa ki je din dama sho ya takura ayi kiranki waishi mai
adalci toga abinda ya jawo mana nan wulaqanci agun wadda bata isa ba"fadila dai
murmuahin uaqe tayi wanda akace yafi kuka ciwo,ta dauki plate dinta taci gaba da
cin fruit din ta ba tare da tana jin dadinsu ba kamar da
Knocking ta sake ji ana mata ta maida plate din kitchen sannan tazo ta bude yana
tsaye a bakin qofar hannayensa zube cikin aljihun jeans dinsa fuskarnan kamar
hadarin dake shirin zub da ruwa😠ba tare da ya dubeta ba ya kalli agogon hannunsa
kana yace"nan da minti biyar ki sameni a mota,abindabya fada kenan ya juya yayi
tafiyarsa,cikin qanqanin lokacin kuwa ta shirya kasancewar ita dama koda yaushe
bata taba yarda ta zauna babu wanke bare uwa uba qamshi da yariga ya kama jikinta
kida muwa bata sanya turare ba,shigar doguwar riga abaya tayi baqa wuluk mai sheqi
saqar qasar dubai an mata ado da dutsuna masu kalan sararin samaniya(sky blue)rigar
tayi bala'in amsarta musamman da tayi rollinga da wani dankwali madaidaici shima
sky blue ta nannde gashinta tayi acuci da shi,ta saka zobe qwaya biyu a yatsunta na
tsakiyar hannu plate din takalmi ta saka baqine mai light blue din igiyoyi,ba wani
make up tayi ba hodace kawai da weet lips amma kada kaso kaga kyawun da tayi kamar
wata baqar balarabiya kasancewarta mai zagayayyar fuska da cikakken gshin gira ga
yalwar sumar kai wadda ta bayyana har a gaban goshinta
Suna zaune shi da aamirah cikin motar tana ta faman mitan dole wai sai da gadilan
za'a tafi ne ya daga mata hannu✋🏻 fuska ba walwala kamar kullum yace"ya isa fa
mitarki tayi yawa,for god sake,zaki taimakeni ranar da na tashi barin jiki na
ashanye?,anje da ita kamar yadda kaje da ke ruwanta ne ta siyi abinda take ruwanta
ne ta barshi fine an fita haqqinta,cikin salon jan hankalinsa tace da tuni ni
kadaice taka sweet,an tashi an.manna maka wannan baqar yarinyar,wani kallo ya sakar
mata wanda ya tilasta mata tsuke bakinta don kuskuren da taso tafkawa,baya ga haka
ma aliyu shi tun usulinsa bai iya yi da mutum ba gaskiya daya ce zai fade ta ne
agaban mutumin koda zai mutu ko zai kasheshi
Sukayi tsai suna sauraron isowarta aliyu nebya faa hangota ya glass din gefansa,sai
ya samu kansa da qarewa shigarta kallo tabbas tana da kyau babban abun ma iya
dressing na nutsuwa bana hauka ba fuskarta babu tarin kwalliya irinta ta samira
hakanan babu qamshin turare har sai da ta ahigo motar gidan baya ta zauna sannan
yaji nata qamshin,shigar tadauki hankalin samirah tamkar ta fito itama ta canza
irinta haka ta ji tunda ita fara ce ai zata fi karbarta haka ta gani,amma a fili
sai ta wani tsaki,aliyu ya tashi motar ya yi ribas ya nufi get tun kafin yayi horn
salisu mai gadin ya dage grmet din gidan nasiru da suke zaune tare da slisun ya
taso ya iso saitin da aliyu yake ya fan ranqwafa yace yallabai kai kadai yau zaka
fita,ya girgiza kai ina tare da matan gidan ne,nasirun ya dan sake ranqwafawa yace
barkanku da dare hajiya an quni lpy,fadila ce kawai ta amsa samirah kam dauke kai
tayi kamar batasan yana yi ba takaici ke cin ranta da dab banzan kishi sai tayi
banza da shi
Aliyu ya qare maganar da suke yi da shi da"sai na dawo kaima zaka iya wucewa gida
sai gobe insha Allah"nasiru ya dan ja baya yana cewa to yallabai a dawo lpy Allah
ya tsare,har ya saoma jan motar ya tsaya ya dannawa nasiru horn ya dawo da sauri
yace masa"nasiru kayi qoqarifa gobe ka fita da wuri ka fara zuwa gunsu haruna ka b
tabbata a gobe an gama sa kayan duka cikin store qarfe sha biyu zan qaraso insha
Allah ,yace to da yarda Allah goben za'a kammala,aliyu yace sai ka wuce gida ka
kwanta da wuri don ka samu tashi da wuri Allah ya bamu alkhairi,ya ja motar suka
fice
Yanayin tuqinsa salon da fadila bataso ne sau tari sukanyi fada da frida akan haka
wato gudun tsiya ne da su,ya iya gudu da keta motoci,motar ta dauki shiru sai
sanyin raba dake ratsa kowanansu kowa kuma da abinda zuciyarsa ke saqa masa,a sace
fadila ke kallon aliyu ta mirror,fuskar nan ahade tan shaqar qamshin turarensa na
chastity sai ta kasa dauke idonta a kansa sonsa na mamayarta,ji take tamkar ta
kamoshi ta rungumeshi a qirjinta ko zaiji yadda zuciyarta ke bugawa saboda shi ya
tausaya mata,a yanzu ba abinda tane buqata illa soyayyarsa,tana ji ne kamar ta
furta masa abinda ke danqare a a zuciyarta ,don kanta ta dauke idonta tana sauke
boyayyar ajiyar zuciya
Tafiyar mintina qalilan suka isa katafaren kantinnan na shoprite,ya dauki wayarsa
iPhone 6 yayi yan danne danne sannan yayi kira da bai wuce na second goma ba ya
maida wayar gefensa ya kashe motar minti ashirin na bayar kada kuma a wuce
haka,samirah tace cikin murmushi"ok sweet"ya maida mata da cewa"ok dear"wani dadi
ya rufe samiran kamar ta taka rawa💃🏽 domin ta dade bata samu hakam daga gareshi ba
duk da tsan ba laifinsa bane ita ta barar da damarta,ta kama hannunsa ta masa kiss
sannan ta fice,abinda bata sani ba tuni fadilan ma ta rigata ficewa
Ta kwashi kusan minti goma bata dauki komai ba tana zaune duniyar tunani sai da
taga giftawar samiran a inda take sannan ta ankara ta miqe,wani abu ya darsu a
zuciyarta,nana da nan ta soma zabar vest ta maza cotton fala qal mai kyau da taushi
ta dauki gajerun wanduna dozen sai hand kerchief dozen agoguna na kamfanin gucci
uku azurfa biyu takalma hudu budaddu biyu rufaffu biyu sai turarurruka na kamfanin
rasasi sai rezar aski ta maza tare da shaving cream na nair,ta daukarwa kanta
turaren blue lady sai relaxer,sannan ta amshi mutuminta wato ice cream manya robobi
guda hudu,leda biyu aka mata kayan sai tata ledar ta tashi shafal babu wani abun
kirki da ta dauka,kayan basu da wani nauyi don haka da kanta ta dauka ta fito,tana
kusantar motar gabantana dada faduwa bata ga alamun samira ta dawo ba don haka ta
iso motar ta sanya hannu ta bude gidan baya ta zuba ledojin hannunta sam sai ta
kasa zama cikin mitar kasancewar aliyun na ciki don haka sai ta tsaya jikin motar
ta jingina da ita ta harde hannayanata bisa qirjita tana bin harabar gun da kallo
gamida qare masa nazari na yadda matasan yan birni maza da mata keta kara kainar
shigowa gun da motocinsu
Sai fadila ta soma qosawa da tsaiwar gun ganin yadda duk naminin da zai gifta sai
ya zuba mata idonsa,taja tsaki tana jin takaicin matsanancin kallo irin na waau
mazan,kamar daga sama ta jiyo dakakkiyar muryar Aliyu yana cewa"malama koma.mota ki
zauna tun ke bakisan me ya dace ba" a sanyaye ta juya ba tare da ta kalleshi ba ta
shige cikin motar zuciyarta na mata quna da jajen yadda aliyu ke mata mu'amala
tqmkar wata mara rai kunnuwanta basu taba jiyo mata kyakkyawar kalma daga bakin
aliyu ba akanta,zuciyarta ta fara tafasa saidai ta danne bacin ran nata da kiran
sunayen Allah,dama ta tsammaci fiye da haka ma daga gurinsa
A hankali ta soma jiyo maganganun aliyu dake tsaye jikin mota sai ta tsinci kanta
da kasa kunnuwanta cikin qaqanin lokaci ta fuskanci da mace yake hirar,kai tsaye ba
zata fassara hirar data soyayya ba amma zaka fuskanci cewa akwai alaqa
tsakaninsu ,mai da bayanta kawai tayi ta jingina da makarin kujerar ta lumshe ido
tana sauraron bugun da zuciyarta keyi ta dauki tsaqon mintina a haka ba tare da ta
tantance halin dabm take ciki ba sai da aka gama zubawa samirah siyayyarta a but
qarar rufe buut dinne ya dawo da ita duniyar data Lula
Muryar samira ta karade gun cikin tuhumar aliyu da wace yake waya cikin rashin
ladabi bai kulata ba sai da ya gama wayarsa tsab yayi sallama dabwadda yake wayar
ya kashe bai ko kalleta ba ya bide side dinsa ya shiga itama cikin sauri ta zagayo
tana huci ta shiga itama ta bame qofar yana yiwa motar key ta sake jaddada masa
tambayarta "na ce ma da wakake waya?"aliyu bai iya qarya ba don haka kansa tsaye ba
tare da shayin komai ba yace"da maman iftihal kin gane?"ba samira da tayi tambayar
ba hatta fadila da amsar ta daketa,samira ta hadiye abinda ya taso mata don bin
qwaqqwafi ta sake jeho masa wata tambayar daidai sanda motar ta saitu akan
kwalta"ro mw kake nufi da yin magana da ita gidanka take nufin dawowa koko ya aka
soma?""duk yadda ta kama haka za'ayi"ya mayar mata kansa na kallon kwalta,saiga
samirah ta dora hannu aka tana shirin zunduma ihu🙆🏻,da sauri aliyu ya sauka gefan
kwalta ya taka birki yace"bari na sauke ki idan kin gama ihun saiki tari mota ki
biyo ni tunda lasheki nayi ko kuma satoki nayi"ba tare da ta sauke hannun ba ta hau
maganganu bai kulata ba ya figi motar ya koma hanya,fadila kam na baya ji take
kamar babu jini a jikinta babu abinfa kunnanata da qwaqwalwarta ke ganewa har suka
iso gida ita dai taga ficewar samirah fit kamar walqiya bata ma jira motar ta gaa
parking ba don saura kadan ta fadi,ita kam bata da kuzarin yin hakan don haka ta
jawo ledar da ta yiwa kanta siyayya tabar wadda ta masa,ta fara tafiya ta jiyo
maganar sa abayanta yana tambayar ledar meye ta bari?ta sadda kai qasa😔cikim
sanyin murya tace kayanka ne,ya sake damqe rai😠 yacekayana?na sanar da ke ne ina
da buqatarsu?"dum dum taji atsakiyar kanta wadda tamkar an buga mata guduma a
tsakiyar kanta taji,batasan sanda ta isa sashenta ba ita dai ta tsinci kanta ne
kwance bisa carfet din falonta
Aliyu yabi inda ta wuce da kallo ganin bata tanka masa bailla ma ledar hannunta da
ta saka ta wuce tana raba hanya,sai yaji wani iri a cikin zuciyarsa yake jin kamar
bai yi abu mai kyau ba ya sunkuya ya dauki ledar da ta saki din ya bude mota ya
hada da tasan ya wuce sashensa don ko kusa baiyi sha'awar neman samira ba don yasan
bazai tainci komai ba illa qarin damuwa da koke kokenta na tsiya,kai tsaye ya wuce
bedroom dinsa ya dora ledojin bisa center table din dake gaban gadon ya cire
kayansa ya shiga wanka bayan ya fito ya ciro kayan bacci ya feshe su da turare su
haka nan jikin sa,ya shimfida sallayarsa yayi shafa'i da wutiri sannan yayi
addu'o'insa ya shafa,ya murzawa qofan dakin key yasa hannu zai kashe wutan dakin
din kwanciya idanunsa suka fada kan ledojin da ya shigo da su,bayan ya kashe ya
koma ya dauki ledojin ya koma saman gado ya kunna fitilar gefan gado ya zazzage
kayan dake ledar farko,daya bayan daya yake daga kayan sannu a hankali yake binsu
da kallo,sai yaji kayan aun nurgeshi kamar ta san zabinsa,kayan sun masa sosai ya
maida su cikin ledarsu,ya jawo tata ledar ya bude wani dan qaramun murmushi ya saki
😊hadi da wani abu mai kamar tausayi da ya kamashi,sam list din siyayyar da aka
turo masa nata bai kai daya bisa biyar din siyayyar samira ba,ya tashi ya bude dan
qaramin pridge din dake dakin ya debe ive cream din ya zuba aciki ya hade ragowar
kayan ya dora bisa bedside
Kwananta biyu kenan tana fama da matsanancin ciwon kai da yaqi saukar mata ta wani
rame tunani biyu ne ya addabeta,yiwuwar qara masu abokiyat zama wanda take
ganinhaka wabi babban qalube ne da zai qara nisanta ta da aliyu sai kuma raahin
sauki na qiyayyar ta da take gani qiri qiri atsakiyar idanun Aliyu
Mrs muhammad ce
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 12:34 PM] Salma:
Wa yasan gobe?.......


1⃣6⃣ 1⃣6⃣
▶1⃣6⃣
Yauma tana kwance saman carpet ta kanta bisa pillow kwanciyar rub ciki tayi saboda
yadda take jin kan nata kamar zai tarwatse doguwar rigar bacci ce a jikinta iya
gwiwa,gashin ta yayi dai dai kan pillow din,idanunta runtse suke ciki n haka ta
jiyo sallamarsa,ta kadu sosai wanda hakan ya sake haifar mata da wani ciwon ko
motsi ta kasa yi bare tayi yunqurin barin falon,tana jinsa har ya qaraso kanta yana
sake maimaita sallamarsa,sai dai dif ta kasa amsawa sai wani bari da jikinta yake
yi,yasa qafarsa ya dan bigi gefan pillow din da take kai ga zatonsa bacci take
saidai nan ma yaji shiru,hakanne ya danso taba tunaninsa,ya sunkuya a hankali yasa
hannayensa biyu ya birkitota gaba daya ta dawo rigingine fuskarta cikin tasa saidai
idanunta na runtse don wani tsoron ne ya sake mameyeta,hawaye ya gani sharkaf a
fuskarta ga wani dan banzan zafi da jikinta ya yi har haqoranta sun fara haduwa da
juna"subhanallah😳"aliyu ya fada,surarta gaba daya ta bayyana har baisan sanda ya
fadi hakan ba kyakkyawan gashinta ya sauko ya rufe fiye da rabin fuskarta,sai kuma
yadda jikinta yayi zafi da yawa da yadda idanunta suka tasa,ya sunkuceta kamar
wanda ya dauki tsinken sakace yana laluben bedroom dinta
Saman gadonta ya ajjiyeta ya zuba hannayensa cikin aljihun wadonsa yana kallonta ya
rasa mai ya kamata ya yi mata wane taimako ya kamata ya fara bata,don da gaske
tanajin jiki rashin lpyr na damunta,a hankali ya bude labbansa yace"relieve ur self
and stop d crying "sai da ya kwashi kusan minti biyar sannan yace"already dama baki
da lpy?"ta gyada kai ya sake tambaya"meke damunki?"ta nuna masa kanta,bai sake cewa
komai ba ya shiga toilet dinta ya hada mata ruwan wanka mai dumi a bathtub sannan
ya fito "kishiga ki shirya kanki likita zata zo"daga haka ya fice,ta daddafa bango
ta shiga toilet din ta sabe jikinta ta dawo ta saka doguwar riga ta atamfa mai
dogon hannu ta fesa body spray ta hade kanta da band qarami ba tare da ta taje shi
ba ta koma ta kwanta,bata dade da kwanciya ba taji ana knocking aliyu ne ya tura ya
shigo bai dubeta ba taji yana bada umarnin a shigo
Likitace sanye da kayan aiki,aliyu dama bai lamunci hurda da likita namiji ba akan
matsalar iyalinsa tun usuli tun maman iftihal doctor sa'adah itace family doctor
dinsa ta qware sosai akan aikinta tasan me take tamakar mayya haka take akan cuta
da maganinta,da sallama ta shigo farar macace dirarriya wadda aqalla shekarunta ba
zasu haura talatin da biyar zuwa arba'in ba doctor sa'adatu akwai ta da fara'a
don.mawuyacine kaga fuskarta babu murmushi yanzun ma da fara'ar a fuskarta suka
gaisa da fadila tana mata sannu yayin da Aliyu ya jawo dresaing chair dinta ya
zauna hadi da zaro wayarsa ya soma danne danne,doctor sa'adah ta ajjiye kayan
aikinta a gefan gadon ta fara fito da su tana tsokanar fadila"Allah dai yasa qaruwa
muka samu madam😃"kunya ta kama fadila don a haife doctor ta haifeta,ta dan saci
kallonsa sai ta ga ma sam hankalinsa bai kansu
Cikin qwarewa ta soma aikinta tana gwaje gwajen tana hada mata da
tambayoyi,tambayoyinta har suka so rikita fadila domin tamakar doctor na son
karanto zuciyarta ne ,fadila tayi ajiyar zuciya lkcn da doctor ta tsagaita da
tambayoyin ta zauna a gefan gado yadda zata iya fuskantar aliyun sosai tace"gsky
a.s maitama damuwa ce fal a zuciyar madam wadda itace musabbabin wannan ciwon nata
wanda Allah ya gani da ace tana fa qaramin ciki da tuni tayi miscarriage
dinsa,aliyu ya maida wayar sannan ya kalli😒sa'adatu ba tare da yace komai ba
tasan bazaiyi maganar ba don ba komai yake bada amsarsa ba saboda haka sai kawai ta
dora da bayaninta"ya kamata ka binciki abinda ya sanyata damuwa mai yawa haka,ya
dauke idanunsa daga kan likita yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa
yace"doctor iya sanina bata da wata matsala amma gaki gata ai u can ask her"ya dago
kyawawan idanunsa masu tafiya da zuciyoyin miliyoyin 'yammata ya zubesu fes bisa
fuskar fadila,tayi gaggawar yin qasa da kanta don kada tana fama da kanta ya baro
mata wani aikin,tasan cewar a yadda take jinta dinnan matuqar ta yadda suka hada
idanu to la shakka qaryarta ta qare domin daga shi har sa'adah ba zasu sja wahalar
gano mai ke dawainiya da zuciyarta ba"meye damuwarki?,ya furta cikin dakakkiyar
murya ba tare da ya dauke idonsa a kanta ba ,da zata iya ba shakka da tace masa
kaine!,kishinka da qaunarka aliyyu sune damuwata!!!,sai fainkash ko kusa bata jin
zata iya,abinda take jin zata iya kuma ahi yafi dacewar tayi din shine shiru kuma
shi tayi din
Shiru din kuwa ya ratsa dakin doctor sa'adah tace"mai tama ba haka ake ba,it can be
d screat ne she dnt wanna share it with another person so ka bari idan na tafi ta
gaya ma a nutse"ta qarasa maganar tana yago pepper daga memonta mai tambarin
asibitinta a jiki ta soma rubutu bayan ta kammala ta ajjiye takardar kusa da fadila
da har yau kanta ke sunkuye tace"to madam Allah ya qara sauqi but pls kiyi qoqarin
rage damuwa"kai ta daga ta mata godiya,sa'adah ta kalli aliyyu tace ga magungunan
da za'a siya mata a nemo.yanzu ta soma sha zata samu relief insha Allah amma ta dan
ci wani abu before ta sha din,ta miqe tana hada kayanta tqna musu salllama aliyu
yace"thanks sa'adah a gaida yara
Mrs muhammad ce
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻

Wa yasan gobe?
1⃣7⃣ 1⃣7⃣
▶1⃣7⃣
Fitarta da yan mintina aliyu ya dauki pepper din maganin ya fice ba tare daya ce
mata kanzil ba,shima ba dadewa da fitar tasa wayarta dake qarqashin pillow ta dau
tsuwwa alamun shigowar kira,a kasalance ta daga wayar tana duba mai kiran sister
farida ce ta daga hadi da yin sallama farida tayi dan jim sannan tace sister ya
naji muryarki ta canza ne?fadila cikin muryar marasa loy ta masa mata wlh bani da
lpy ne farida ya gida ya kuma mubarak?cikin yar qaramar dariya farida tace duk muna
lpy sister ko ta samu ne?,samuwa kamarbyaya? Ta tambayeta,farida tayi qasa da murya
tace ian nufin fa juna biyu,ta dan basar tace abinda kika bugo ki tambaya
kenan?,a'ah anty dama ina ceqa ne gibe ki duba haya ina nan zuwa harda result dinki
tun last week ya samu,duk da bata jin da lafiya hakan ya mata dadi sosai har ta
nuna zumudi,jin bata da lpy yasa farida qyaleta akan sai tazo goben,ta amsa don
dama kantabhar ya soma sarawa ta maida kanta saman pillow ta kwantar tana addu'ar
Allah yasa ta samu damar aiki
Ya shigo hannayensa biyu riqe da ledoji ya shigo ya zubesu kan bedside ya maida
hannayanaa aljihu kamar kullum,ji tayi kamar ya cika mata dakin wani kwarjininsa ya
cika mata gu jikinta yayi sanyi tanajin kamar ko hannuta ba zata iya dagawa ba ta
shiga satar kallinsa duk fa batayi niyyar yin hakan ba zuciyarta ce ta tursasata
kansa na qasa ne yana kallon carfet kamar mai nazari,sai ya mata kyau sosai
fuskarana fes kama ganinta kasan tasan hutu tabbas maza irin aliyu sai ka tara dari
zaka samu biyu cikinsu ga tsawo da qaqqarfan gangar jiki mai murdadden damtse mai
cike da qarfi faffadan qirji mai cike gargasa wadda ta bayyana har hannayensa yana
da jiki amma ba zaka kirashi mai qiba ba domin tsawonsa ya shanye ta,kusan ko
yaushe fuskarsa a haka take ba fara'a sam don ita a iya saninta da shi bata taba
ganin haqoransa ba,
Saura qiris ya kamata tana satar kallonsa tayi gaggawar janye idanunta daga kanshi
a hankali taji yace dazun na tambayeki meye damuwarmk yanzun ma na maimaita karo na
biyu"shiru ta sake yi.masa hakan yasa ya kausasa.murya yana sake tambayarta,cikin
cool voice dinta tace babu komai,ya dago kamar zai kalleta sai kuma ya lumshe ido
ya budesu kan.ledojin da ya shigo da su sannan yace idan tashin hankalinki da
damuwarki sun ta'allaqa ne kema kan dawowar maman iftihal to kiyi saurin taimakawa
kanki ki nemi sassuci a gun zuciyar ki don zata dawo ne amatsayin mata ta karo na
biyu ba wata baquwa bace......sannan ki bawa zuciyar dai taki again shawara da kada
ta cika kanta da damuwoyi masu yawa tun yanzun......ya danja fasali sanna ya miqa
hannunsa ga wayarta dake gefanta abinka da giant tuni hannun yakai ba tare da ya
hau gadon ba ya lallatsa sannan ya ajjiye mata yace"ga abinci nan da magunguna ki
sha,then ga number ta if there is any problem contact me"daga haka ya juya ya fita
ba tare da Saura ron komai ba
Sai abun ya zamewa fadila wani iri ta jima akwancen kafin ta samu damar miqewa
zuciyarta na qarfafa mata gwiwa ta tashi ta taimaki kan nata kamar yadda aliyu ya
shawarceta,tq shiga toilet tayi fitsari sannan ta daura alwala wai ko zata ji
sauqin zugin dq zuciyarta ke mata,ta dawo bakin gadon ta bude ledojin daya
magunguna ne a ciki daya kuma gasashshiya,ta dinga zare tsokar tana ci zuciyar ta
dauke da addu'o'in samun sauqin daga quncin zuciya(inda Allah ya taimaki fadila
kenan bata mantawa da add'a duk irin situation din da take ciki,muyi koyi da ita
yan uwa domin hatta qaddara babu abinda yake tareta sai add'u'a,mu dinga tuna Allah
a yayin da muke cikin jin dadi da walwala sai Allah ya tuna da mu lokacin da mu
kuma muke cikin qunci da neman taimakonsa wannan fadar annabi ce s.a.w,kai ta
addu'a da sannu Allah zai isar maka,take note pls!)jin naman take kamar magani mai
daci haka taci gabada dannashi har tqji kamar zata yi amai,ta balli.maganin adadin
yadda aka rubuta tasha sanna ta dan zauna na mintina don abincin ya fada mata sanna
ta ja pillow ta kwanta,cikin ikon Allah ta dinga jin sassuci a zuciyarta,ta jawo
wayarta sai taji tana qamshin aliyu ta soma duba contact dinta taga number din da
yace yasa mata ai kuwa a rukunin A taci karo da sunansa full name dinsa ya saka
mata ta bude numbers din tana qare musu kallo suma special ne don cikin taqaitattun
daqiqu zaka iya haddacesu,(mrs muhammad nace ko na sato muku numbers din A.s
maitama ne cikin wayar fadilan?to gasu 0803344.......😜😜 to naqi don naga wata har
tana saurin kwafa ba ruwana ku da fadila😜)ta zuba musu ido kamar tana son ganin
fuskar mamallakin numbobin da ta gaji da kanta ta rufe wayar ta maida ta qarqashin
filon ta lumshe idonta tana maida numfashi cikin zuciyarta ta soma tilawar suratu
yusuf tana yi tana bin labarin annabi yusuf din da Allah s.w.a ke bayarwa cikin
surar,zuciyarta ta mata sanyi damuwarta ta ragu sosai lallai Allah yayi gaskiya da
☝🏼
yace(ala bi zikrillahi tadma'innal qulub/ku saurara da ambaton Allah ne kadai
zukata ke samun nutsuwa)
To fa makaranta na labari yanzu muka soma shigarsa kuci gaba da jumurin bina insha
Allah zamu cimma gaci😊
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ........
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 12:35 PM] Salma:
Wa yasan gobe?

Written by safiyya Abdullahi musa huguma

1⃣8⃣ 1⃣8⃣
▶1⃣8⃣
Washegari misalin sha biyu na rana tana kitchen tana tafasa ruwan lipton so take ta
dan sha ko zai warware mata ciki don tun tashinta yau ba abinda ta iya ci,muryar
farida taji tana qwali mata kira da gudu ta fito suka rungume juna suna dariyar
farincikin ganin juna,farida ta dan janye fadila daga jikinta tana cewa sister
yi a hankali kada ki mana asarar baby,fadila ta ballamata harara tace"wai ke wa ya
baki wannan labarin qanzon kuregen?farida tace bayan mun gama waya jiya da ke da
daddare rabi'ah ta kira ni take gayan again,fadila na qoqarin komawa kitchen din
tace uhm sai ki zauna ai kiyi ta jiran cikin,farida tayi dariya ta bita,maimakon
daba lipton sai ruwan zafin ya koma na girki,suna yi suna casar hira,suka kammala
suka zuzzzuba su a warmers suka wanke kwanukan hadi da gyara kitchen din
Wash! Inji farida bayan ta zauna fadila ta kalleta tace kin canza sister fa sosai
kinga qibar da kika fara yi?farida tayi murmushi tace ke dai bari ya fadila ina
tsammanin ciki ne fa?,fuskarta cike da fara'a tace ke dan Allah,tace wlh da jibi
ko gobe mubarak ya matsa sai naje an min test wai kada na jawo masa asara cikin
rashin sani ni sai naga kamar ba shi ba,kasala kawai fa nake da yawan bacci,fadila
tace,a'ah nima fa ina bayan mubarak sister kije a dubakin meye amfanin zaman
haka,kina likita ai kinfi kowa sanin alfanun abin,tace insha Allahu gobe zamu je
Takwas da mu
mintina na dare nasiru ya turo hancin motar ogan nasa cikin gidan,ya samu parking
space ya daidaita tsayuwar motar sanna ya kasheta,a hanzarce ya fito ya budewa
aliyu shima ya fito sannan ya miqa masa keys din motar yana fadin gashi sir ya amsa
yana cewa debo min files din nan na sit din gaba,ya debosu ya bashi sukayi sallama
aliyu ya sallameshi,hankalinsa gaba daya ya yi gaba burinsa kawai ya isa sashen
nasa ya watsa ruwa a jikinsa ya samu ya kwanta ya huta,ya soma tafiya idanunsa suka
kai kan sashen nata babu wadatar haske kamar bangaren samira dake tarwai da haske
harda qarar abin kida ya dauke kai ya shige
Yana fitowa daga toilet ya zabi doguwar riga jallabiya fara sol.mai yankakken hannu
ya saka ya feshe jikinsa da turarukan baccinsa masu sassanyan qamshi kan sofa ya
fada ya miqe qafafunsa sannan ya hardesu ya kansa na kallon sama yasa daya hannun
nasa ya shafi cikin sa,yunwa yakeji amma ya rasa inda za shi ya samu abincin da zai
gamsar da shi,mutum ne shi.mai tsan tsami ba ko ina yake iya saki jiki ya ci
abinscinsu ba sai ya yarda da ingancin tsaftarka hakan ne yasa ya tsani masu aiki
hakan yasa tun yana gida ya yi ruwa yayi tsaki ya hana mominsa daukar masu aiki
yace meye amfani su sumayya duk da suma bai yarda ko kadan yaci girkinsu sai na
mominsa
Ya tashi ya qarasa fridge ya bude ya dauko yoghurt na l&z ya hado da fura ya samu
cup ya dama ya sha ,ya sake tashi ya maida cup din kitchen sannan ya qarasa window
dinsa yana bude glass din don ya bawa iska daman shigowa duk da iskar a.c da ta
mamaye dakin kasancewar mutum ne shi maison natural air,idonsa ya sake fadawa kan
bangaren nata duk da yaune ya shigo bashi da niyyar ganin kowa bacci yakeso ya samu
isashshe don haka har wayoyinshi ya kashe su gaba daya
Ya saki labulen yana ajiyar zuciya saboda tunawa da yayi haqqine a kansa ya kula da
lafiyarta don rabonsa da ita tun jiya da ya batta da magungunan da ya siyo mata ,ya
zari keys dinsa ya zura slippers dinsa ya fice

1⃣9⃣ 1⃣9⃣
▶1⃣9⃣
Tana kwance a miqe sambal bisa kujera three sitter don tunda tayi sallar isha'i
bata tashi ba agun falon tsit yake ba komai sai sanyin na'urar sanyaya daki wanda
ta gauraye da qamshin freshner mai dadi idanunta na lumshe ne tamkar mai bacci
saidai ba bacci take ba tayi nisa ne a wata duniya mai wuyar fassarawa duk da ciwon
da kan yake mata das das das amma hakan bai dameta baqarar bude qofan falon da
qamshim mayen turarensa dake rataye da zuciyarta shi ya dawo da ita,ta bude manayan
idanunta akansa yayin da shi kuma ke qoqarin tura qofar tayi namijin qoqarin tashi
ta zauna kanta na sunkuye a qasa don ba zata iya jurewa kallonsa ba,hannayensa ya
goye a bayansa ya qaraso falin yana kallonta da qayatattun idanunsa ya lura kamar
ta dan rame duk da ba sanin ainihin kamanninta ya yi ba"ina yini"tace still kanta
na qasa,cike da qasaitarsa da izzarsa ya dauke kai ya maida mata gaisuwarta da
tambayar jikinta,da sauqi ta fada cikin sassanyar muryarta data sanya yaji wani dan
yam ajikinsa
Bata zata ba bata kuma tsammata ba sai jinsa tayi zaune kan kunerar da take
kai.kuma dab da ita ya sanya bayan hannunsa a wuyanta da niyyar jin temperatures
din jikinta ba komai aransa,sai dai baisan illar da ya sake yiwa fadila ba a zuciya
da gangar jikinta ba,kasala mai tsanani tashi guda da kuma wani irin shauqi taji ya
saukar mata numfashinta ya tsaya cak na wucin gadi,sam bai kulaa ba yace"still
jikinki da ragowar dumi ya kamata ki warke kafin isowar abokiyar zamanku right?ya
qare maganar da sigar tambaya,ya.miqe yana cewa babu abinda kike buqata,tamkar ta
ce masa"kai nake buqata aliyyu ka qarashe awoyin wannan daren naka tare da
ni,maimakon haka sai ta sake gyada masa kai,yace " alright gudnyt"ta bishi da kallo
idanunta fal cike da qaunarsa da kewarsa har ya fice daga part din nata ya rufe
mata part din,ta koma da baya ta jingina jikinta da kujerar hadi da runtse idanunta
hawayen dake maqale a idonta suka gangaro mata wani radadi da zugi zuciyarta ke
mata lallai kishi masifa ne
Cikin daren bacci gagararta yayi juyi take kawai akan makeken gadonta cike da
sha'awar aliyu tunda take bata taba jin makamanciyar sha'awa arayuwarta irin wannan
ba
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Sannu a hankali ta miqa dukkan lamuranta ga Allah cikin ikon sa kuwa ta fara samun
sauqinsu saidai fa har yanzu babu sauqi ta bangaren soyayyar Aliyu dake maqare
cikin zuciya ,cikin lokacin sam ta daina bari idanunta suga aliyyu duk da tarin
zugi da zullo da zuciyar keyi na son ganin nasa amma ta danneta
Cikin lokacin aikinta ya samu freedom da express din duk suka buqaci yin aiki tare
da ita,ya ahmad dinne ya kawo.mata da kansa bayan ya sanar da aliyu da kansa ya
kuma amince mata da fara aikin nata,tayi murna tayi tsallae tun a gaban ya ahmad
din ya sha godiya sosai har da qwallar farinciki saboda yadda take masifar son
aikin jarida shikam dariya yayi yace Allah zata godewa,bayan tafiyarsa ta kira
farida dake fama da laulayi suka sha murnarsu tare,nan fa ta zauna ta soma tsarawa
kanta yadda zata tafi da rayuwar aikinta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin satin Aliyu ya shirya musu fita wadda ta farko ce agun fadila don bata taba
fita ba wani gu da sunan unguwa ba bayan shopping da suke zuwa duka qarshen wata za
suje ne gaida hajiyarsa
Tun rana fada ke zumudin fitar tana tunanin mai zata kaiwa momin,akwatunan lefenta
dake shaqare da kaya wadanda kamar ba'a taba amfani da komai a ciki ba ta bude ta
zabi turarurruka designers guda uku ta warewa abba,ta duba akwatinta da ta adana
gift da ta samu na biki ta cirarwa momin atamfofi super Holland da England guda
biyu,da kanta ta aiki yaron dake musu gyaran flowers ya samo mata kilishi mai kyau
da zuma
Tun magariba ta yi wanka ta shirya kanta cikin atamfa dinkin riga da zani kamar
light grean da milk sai ratsin baqi dinkin ya mata cas kamar a jikinta aka
qirqireshi yari da sarqa ta saka ma dutse masu kalan milk sai farin agogon hannu tq
zuba awarwaro mai 24 farare takalmi da jaka milk sai laffaya data nannade jikinta
da ita milk ce mai adon baqi ta debi tsarabarta ta dawo falo ta kunna arewa 24 tana
kallon shirin matasa at 360,tayi wani masifar kyau ta fito sosai a babarbariyar ta
Ya qarashe karin hular sa yana daidaita ta a kansa shaddace fara qal a jikinsa
dinkin tazarce sai walwali take ta sake fidda sirrin kyawunsa mutum ne shi
ma'abocin iya ado ta wannan fannin kam ko mace haka ta ganshi,komai nashi fari ya
sanya hatta da agogo,ya sanya glass dinsa sanna fesa turarensa ya rufe sashen
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2▶2⃣0⃣
0 20
2⃣0⃣
Bangaren samirah ya nufa wanda sai ta kama dole yake shigar sa,ga mamakinsa aai ya
taddata sirshan tana zaune abinta zaninta da rigarta daban daban kanta da ta tsefe
shi yana tsaitsaye kamar tabarya😜dama ita ba wani tsawon gashi gareta ba sai qarfi
da gashin yake da shi,ba abinda falon keyi saiqarnin kifi sardine ta tara
gwangwanayen a gabanta ua daurw yadda qarnin ke bugar hancinsa yana tayar masa da
zuciya cikin bacin rai yace mata zaman me kikeyi baki shirya ba tun dazun?ta dan
yatsina fuska tace qawatace wlh ta kiarani a waya ta kwasheni da jira ya gyara
tsaiwarsa cike da qosawa da azababben qarnin kifin yace mata is ok sai ki nemi
wanda zaku tafi tare kinsan bana jira yana kaiwa nan ya sanya kai zai fice yana jan
tsaki cike da takaici ,ta yi saurin shan gabansa tana cewa haba sweet kayi haquri
mana pls ka bani minti uku kaya kawai zan canza,ya kauce ya fice yana cewa wataqila
idan kinyi sauri kin tadda ni kafin in ciro mota is ok,ya barta nan baki a sake ta
bishi da kallo sai kuma ta zabura tayi cikin daki don ta shirya
Knocking taji anayi don haka ta zira hill shoes dinta fari ta rataya jakarta ta
dauki ledarta don jikinta ya bata aliyu ne shi dinne kam idonsa na bisa screen din
wayarsa yana danne danne bai dube ta ba ya juya taja part din nata ta kulle tabi
bayansa tana qare masa kallo"ya gaji da haduwa"ta zanta hakan a ranta,tana jingine
da rumfar ajiyar motoce har ya gyara parking qa'idarsa ne indai tare zasu fita baya
neman driver duk da dama nasiru ne kawai.ke driving dinsa,wanni dogon hirn ya ja da
sauri ta daidaita nutsuwarta ta nufo motar tun kafin ta qaraso taji an bangaji
kafadarta da mamaki ta dago don ganin waye samirah tana ta zuba sauri zani a hannu
tana gyara daurinsa,duk saurin da take gidan gaba aahe takewa,abun ma sai ya baiwa
fadila dariya ta saki murmushi😊
Cikin mintuna da basu gaza talatin ba suka qaraso gidan,harabar gidan tsaf kuma
fetal da haske ba kowa sai mai gadi shi da wasu mutum biyu zaune kan benci suna
sauraron duniya tumbin giwa suna cin gyada jefi jefi suna taba hira,cikin girmamawa
ya gaida aliyu sannan ya gaida su fadila ta amsa masa fuska a sake tunda dama da
yar sanayya tsakaninsu ya samirabko kallo bai isheta ba bare tasan yana yi,ya dage
masa get din ya wuce ya yafitoshi yayi masa ihsani kamar yadda ya saba shi da
wadanda ke zaune a gun suka hau zuba godiya abinsa shi kuma baiso
Samira da aliyu suka jera suka fara yin gaba zuwan falon gidan fadila bin bayansu
tayi ,sumayya da rabi'ah ne zaune a falin da hijabai ajikinsu da alamar sallar
isha'i suka idar,suka juyo suna amsa sallamar sannan suka miqe tsaye cikin farin
ciki suna gaida su hankalinsu na kan fadila itama su take kallo suna gaisawa
sabanin samirah da ta riqe qugu tana qarewa falon kallo tana yaba tsaruwa da dukiya
da ya lashe kamar wadda aka bawa kwangila sannan daga bisani ta zabi kujerar da
tayi.mata ta zauna akai,cikin dakiya irin ta babban wa yake tambayarsu ina momy
sumayya tace tana sama ya nufi benan taku biyu uku sukayi kacibus da iftihal na
saukowa kamar yadda ta saba ta tsugunna ta gaidashi sanna ta daneshi ya sabeta a
kafada yana tambayarta momi
Tare suka sauko shi da momin yana take mata baya iftihal na hannunshi ganin fadila
ya sata ta zille ta diro ta nufeta a guje cikin murmushi fadilan ta tareta ta dora
ta bisa vinyarya dukkaninsu suna dariya ta gaisheta,duskar momi washe da fara'a
take.musu barka da isowa samira dake zaune dare dare bisa kujera kamar tata tave
yauwa fadila dama.na qasa ne kan carpet ta duqar da kanta qasa tana murmushi cike
da kunyar momin,gaisuwa aukai da samirah kamar qawa da qawa yayin da fadila ma ta
kasa hada ido da ita a haka suka gaisa,ganin taqi sakin jiki ya sa momyn tace su
rabi'ah su kaisu dakinsu itama zata gun abbansu yanzu ya shigo gidan,hira suke
abinsu da fasika yayin da samirah ta zaro wayarta ta hau danne danne tana ganin duk
ta girmesu tafi qarfin zama cikinsu ai,ga takaicin yadda aujewa fadila haba haba
itq aunqi mata haka cikin ranta take cewa hmm dangin miji kenan tsinannu(kunji fa?)
A haka bacci ya dauki iftihal akan cinyar fadila aliyu ne ya leqo hukarsa a hannu
yace ke sumayya ku taho dining"samrah ce ta fara miqewa tana cewa dama yunwa nake
ji ta fice,qememe iftihal taqi kwanciya dole iftihal na nishi ta sabota a kafada
suka fito su sumayya nata dariyar yadda ta dauki ifrihal din da qyar,momy ce da
abba sai aliyu bisa dining din kusa da abban abba na dariya yaceyau ban dawo da
wuri ba bare a murqushen tsohon
qashi na shine aka rama akanki ko?
Duk sukayi dariya kowanne ya samu kujera daya ya ja ya zauna banda fadila dake
tsaye sabe dà iftihal wani baccin nason daukarta amma ta qi yarda tayi don kada a
sauketa
Mrs muhammad ce
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣1⃣ 2⃣1⃣
▶2⃣1⃣
Momy ta kalli aliyyu tace alii rabata da rigi mammiyar yarinyar nan don idan ba kai
ba ba wanda zata yarda ya sauketa,ya miqe ya nufesu yanayin yadda ya tsaya gab da
ita yana yunqurin karbar iftihal ya haifar mata da wani yanayi cikin jikinta,ya sa
hannu zai dauketa cikin rashin sani hannunsa ya shafi qirjinta wani abu taji ya
tsirga mata tun daga kanta har tafin qafafunta hakanan shima yaji tsigar jikinsa ta
tashi wani shocking yaji kamar an jashi da wutar lantarki,ya sabata a kafadarsa ta
miqe zata soma rigima suna hada ido da shi tayi gum da bakinta🤐 ta mayar da kanta
kafadarsa ta kwantar ya sauka da ita cikin falom ya kwantar da ita bisa doguwar
kujera ya karanta mata addu'o'in bacci na tsari ya tofa mata sannan ya koma
Ta tsugunna ta gaida uncle abba ya amsa mata cikin kulawa yana cewa lpy lau diya
ta,sannan ta ja kujera itama ta zauna,sumayya tayi serving din kowa🍽🍴 sannan akai
bismillah aka fara ci,kwata kwata kasa sakewa fadila tayi ta kasa kai koda loma
guda bakinta sai juya cokalin kawai take a cikin abincin ,amma ga tarin mamakimta
sai taga samira ta saki jiki tana ta kaiwa uwar hanjinta🍜 harda tsiyaya lemo 🍹🍾da
ruwa da kanta,tayi sakewar da ko ita da uncle abba yake kamar uba a gareta ba zata
iya irinta ba
Abinka da mata momi na ankare da yanayin nutsuwar kowaccensu tana kuma sake godiya
ga sarki Allah da ya qaddara fadila ta zamo daya daga cikin family dinsu,afakaice
rabi'ah ta qarewa samirah kallo uadda take lodar abincinta ko aliyyu da yake dan
gida baiyi haka ba,ki saki jiki mana fadilan ummi kici abincin ki mu fa iyayenki ne
ko babu aliyu baki ga yadda yar uwarki ya saki jikinta ba?,cewar ummi,samirah ta
amshe cikin tabe baki tace momi kinsan wani akwai qauyanci da rashin wayewa atare
da shi"sai kowa yayi dif rabi'ah da takaici ya cikata tace ba rashin wayewa bane
kowa dai da irin yanayinsa,ta sake tabe baki tace uhmm,ita kuwa fadila dariya ma ta
bata sai daga qarshe ne taga kada suji ba dadi ta kurbi lemon da rabi'ah ta zuba
mata
Bayan sun kammala momi tasa rabi'ah da sumayya suka gyare gurin suka kwashe
kwanukan,suna shirin wucewa don su basu guri momi tace su dau iftihal su wuce da
ita,falon yarage daga fadila aliyu samirah sai momi da uncle abba
Abba yayi gyaran murya yayi bismillah sannan ya kirawo sunan aliyu ya amsa
masa"naam abba"ya dora "aliyyu girma yanzun ya hau kanka duk da a baya kwatan
kwacin wannan girman ya taba hawa kanka kuma kayi namiji qoqari wajen riqeshi yadda
ya kamata amma bai kai wannan ba,a yanzu dole na sake jaddada maka saboda zama ne
da zaka yishi tsakanin iyalinka har su uku wanda ko ni mahaifinka banyi duk da
komai tsarin Allah ne
Daga samirah har fadila babu wadda gabanta bai fadi ba har sai da samiran yabdaga
kai ta kalli abban,uncle abba yaci gaba "lamarin mata ali sai da haquri kawaici da
kuma jajircewa halitta ce su maau wuyar sha'ani amma idan ka duba Allah sai komai
ya zo maka da sauqi ,aliyyu ina horarka da kaji tsoron Allah ka tsaida adalci
tsakanin matanka duk wadda ka cuta wlh wlh sai allah ya bi mata haqqinta sai kuma
ya tambayeka,kuma ko ni ban lamunci rashin adalci ba acikin gidanka ka riqe Allah
ka kuma ji tsoronsa
Ya juyo gunsu fadila da kansu ke qasa kowa da abinda ke cikin zuciyarta yace
"dukkaninku ina kallonku ne a matsayin 'ya 'yana na na cikina da na haifa nasihar
da zan muku itace kuma ku ji tsoron Allah kuyi zamqn aure a matsayin ibada kuyi
biyayya ga mijinku.ku kyautata zamantakewar ku domin kuwa shine muqullinku na shiga
aljanna ko wuta idan kuka saba masa Allah ya tsare mu,magana ta biyu kuma na
dakatar da shi ne daga gaya muku don inason na gaya muku ni da kaina ta hanyar da
ta dace,nasan kowacce mace haka Allah ya halicceta da kishi kuma ba zaku so
abokiyar zama ba a yanzu amma ba yanda muka iya da hukuncin ubangiji kuma aure rai
ne da shi matuqar bai qare ba komai dadewar zamani sai an dawo anci gaba da yinsa
to ina mai baku haquri a madadin aliyyu,mahaifiyar khadija(sunan iftihal na gsky
haka abba ke kiranta yawancin lokuta)zata dawo dakun aurenta ina fata zaku hada
kanku ku zauna lpy,samirah ta dago kanta a gigice tana fiddo da idanu waje😳
tace"abba mai kake fada ne?dama da gaske aliyu yake da yafara zancen?" aliyyu ya
juyo ya kalleta wani huci ya saki abba ya lura da yadda yanayinsa ya canza ya san
yadda fishin aliyyu yake don haka ya danne shi,cikin tausasawa ya kalli samira yace
ki kwantar da hankalinki yata insha Allahu ba zaku fuskanci rashin adalci ba daga
gun aliyu ni kaina bazan lamunci hakan ba shiru tayi tana muzurai idonta ya kada
yayi ja saboda ganin yadda aliyu ke gasa mata hara ra tamkar zai cinyeta
danya,itakam fadila gabq daya jikinta ya saki tunaninta daya ta ina zata samu
aliyyu bayan ga wasu na farautarshi ? Jin sunyi shiru dukkaninsu abba yace da
momi"kina da magana momin yara?" Ta danyi murmushi tace" aikace komai abban
yara,saidai nace aliyu kaji tsoron Allah kamar yadda abbanka yace sannan ku kuma
Allah yayi muku albarka kuyi haquri kuma kuyi biyayya sai.kuci riba"suka amsa da
amin banda samira da ta kasa furta komai sai tafasa da zuciyarta keyi,abban ya sake
basu dama akan idan da mai magana ya yi,ba wadaa tace komai sai aliyu da yace"abba
da momi na gode muku kuma insha Allah zaku sameni mai amfani da duk nasihar da kuka
yimin zan zamo mai adalci da yardar Allah"Allah ya amince suka ce,fadila ta fito da
kayan data taho musu da su ta dorawa abba nasa a gabansa sann ta dorawa momi nata
Duk da ranta babu dadi amma ta ji dadin yadda suka nuna jin dadinsu suka sa mata
albarka,aliyyu kansa can qasan zuciyarsa yaji dadin hakan don shi mutum ne mai dake
qaunar wanda ke kyatatawa iyayensa,haushi ya sake cika samira tayi dana sanin zuwan
ta gidan yafi sau cikin carbi bata son taga wani yana yabo ko son fadila kwata
kwata
Cikin mota ma kowa da irin zaren da yakr saqawa zuciyarsa shikam ya dake abinsa
kamar bashi ya sanar da mata har biyu zai qara musu abokiyar zama ba tuqinsa kawai
yake a nutse,fadila tata saqar na yadda zata juyo da hankalin aliyu take bata so
kuma bazata so ace kishiyoyi har biyu su fuskanci raahin qauna da jituwa dake
gudana tsakaninta da shi ba,samira kuwa wani mahaukacin kishi ne ke taso mata
zuciyarta namata saqa da baqin zare,tana shirya mata irin mummunan matakin da ya
kamata ta dauka abu guda ke taka mata burki idan ta tuno yadda aliyyu ya birkice
mata da yanayin da ya sameta a daren farkonsu tasan har yanzu dafin na sukar
zuciyarsa somin kuwa duk wani tanadin soyayya da sukayi wa juna tn daga ranar ya
rushe,duk kuma waa qauna tata dake zuciyarsa wadda ta rage tuni ta rushe
Cikin satin komai ya fara kankama abubuwa suka cedewa baiwar Allah fadila ga zirga
zirgar shirye shiryen fara zuwa aikinta ga kuma lamarin na dake mintsinin zuciyarta
duk da shiryr shiryenta ya tafi da kaso.mafi tsoka daga damuwar dake cin
xuciyarta,tuni tayi waya gidan an ma motocinta service daya tsohuwar tata ce tun ta
gida aka sake mata fenti da wasu abubuwa sai ta tashi ta dawo sabuwa dal don tana
qaunar motar bata son rabuwa da ita yanzu sai kuma wadda aliyyu ya sa musu a lefe
wadda ta sam ira tuni ta dade da cin uban tata ta mora qawaye su ara suma su mora
Kira ta dinga samu daga su anty hauwa anty hafiza har da farida kowannan su nasiha
ce da jan hankali ne nasa har farida ta so karayar mata da zuciya saidai tayi
qoqari matuqa wajen nuna dakiya da mai da komai ba komai ba
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
2⃣1⃣ 2⃣1⃣
▶2⃣1⃣
Samira kuwa abun nata sai ya zamto tamkar mai qaramin ciwon hauka kamar a kanta aka
fara kishiya kasancewar ta samu gudun mawar zuga daga qawaye da yan uwa kala daban
daban duk da wasu ba don Allah suke bata basuna baqinciki da rufin asirin kawai da
take ciki ne(qalubale a garemu mata sai azo ayita baki shawara akan za'a miki
kishiya ko wani harkar wani ahaka kamar mai sonki amma da zaki ga cikin zuciyarsa
game da ke tsoronsa ma zaki koma ji,sanin haqiqanin mutum sai Allah,sai ki auna da
hankali da Allah ya baki a matsayinki na mutum mai tunani)sai ta sake zama kamar
zararriya ita kadai ma abangarenta sai ka jiyota tana bala'i tana zunduma
ashariya(wa'iya zu billah)cikin satin baqi ta dinga yi kala daban daban kowanne da
tasa guzuri da salon hudubar waccan ta shiga waccar ta fita
Tun Aliyu na zuba mata ido idan tana salon rashin mutuncinta da haukanta har sai da
ya zamto idan tazo sai dai ta gajibda bugun sashen nasa ta juya da haukanta ta koma
inda ta fito,tuni fadila tabgama tsarawa kanta yadda zata tafiyar da rayuwar
aurenta ta gama tanadar komai,tana hango cewar itama fa maca ce tana da duk wani
abu da da duk wata ya mave maiji da kanta ke taqamar tana da shi,tana da duk wasu
qualities da ake buqatar mace da su kafin ta amsa sunan ta na mace,to me yayi saura
banda itama ta shiga fagen a dama da ita?? Me zata jira banda ta shiga ta karbo
aliyyunta? Ta gaji kuma lokaci yayi da take ganin ya kamata ace ta kasance da da
shi ta gaji da dako da rainon soyayyarsa ita kadai
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Biki ya zamto saura kwana uku wanda yayi dai dai da sauran kwanaki bakwai fadila ta
soma zuwa aikinta
A ranar ne bayan sallar magariba aka shigo mata da akwatina set shida masu matuqar
kyau maqarenda kaya nasiru yace mata inji maigida,ta jinjina kai ta rufe qofar
sashen nata ta koma kan kujera ta zauna daya bayan daya ta budesu ta zubawa kayan
ido duk budurin da ake sai yanzu zuciyarta ta tsinke hawaye suka soma zarya a
kuncinta a hankali take sa yatsunta tana sharesu tabbasa an jarrabci rayuwarta da
jarabta mai girma ta sani cewa son aliyu jarabta ce daga ubangiji acikin jininta
yake kuma bata fatan Allah ya dandanawa wata mace kwatankwacin yadda take ji a
zuciyarta,nan saman kujerar ta lafe tana hawaye a hankali take furta HASBUNALLAHU
WA NI'IMAL WAKIL har taji zuciyarya ta soma sanyi
Haya niya da hargowa take jiyo wa maau qarfi suna karade filin gidan hakan ya sanya
kukanta katsewa ta tashi kamar mai sanda ta isa window dinta da yake cikin balcony
dinta ta yaye labulen ta riqeshi a hannunta,daga nan tana iya hango dukkq sararin
gidan samira ce ke wannan hayaniyar cikin hargowa da babat tanajanyo akwatina irin
wanda nasiru ya kawo.mata dazu daga part dinta daya bayan daya tana cillarwa anan
tsakiyar filin gidan ko nauyinsu bata ji ,aliyyu na tsaye hannayensa harde a qirji
ya zuba mata ido bai ko motsa ba
Sai da ta gama lodesu sanna tayi cikin gidan nata a fusace sai gata da gallon da
ashana ta daga tana qoqarin bulbula musu fetur din da yake ciki sai a lokacin
aliyyu yasa hannu ya fincikota baya a fusace ya nunata da dan yatsa yana cewa kul
kada ki soma,ta dubeshi duk da ta tsorata da yanayinsa amma sai ta dake cikin
bala'i take cewa" sai na qona aliyu sai na qona wallahi kayan fadar kishiyan wata
tsiya ce,sai dai idan na qona idan ka so nima ka qona ni" ta sake zabura tayi kan
kayan da nufin idar da niyyarta cikin qaraji da tsawa ya ambaci sunanta wadda sai
da hantar cikinta ta kada amma sai ta waiwayo tace"ko kasheni zakayi ba zan fasa
ba" tadai sake nufar kayan cikin azama a karo na uku,cikin fusata yasa hannu ya
janyota baya harsai da ta zube warwas a gun tamkar ya bita ya tattaka haka yake
ji,don da namiji ne ya masa haka to yanajin ba shakka sai ya nuna masa qwarin
qwanjinsa
Ta sani cewa idan taci gaba da abunda take hukuncin da zai yanke mata ba mai sauqi
bane hakan yasa tana daga zaunan ta hau borin kunya cikin surutai da maganganu
marasa kan gado daga baya ma da taga ya qi kulata sai ta fashe da kuka
Ko kallo bata isheshi ba ya dinga siban akwatunan bibbiyu bibbiyu ya shigewa da au
bangarensa yana gamawa ya rufe qofarsa ya barta a nan,data waiga ta waiga taga ba
kowa ba wanda ya gansu sai ta goge idonta ta miqe tana kade zaninta tana wa allah
godiya da ba wanda yaga abinda ya faru tana yi tana tsinewa hannatu qanwarta
gashinan ta jawo mata asarar akwatinan ma dungurun gum dan ita ta bata shawarar
tayi haka
A falon sa ya zube ya dafe kansa hannu bibbiyu yana tsananin jimanta al'amarin to
haka mata suke ne basu da hangen nesa ya jima a haka sannan ya tuno bai ma shiga
bangaren dayar ba kamar yadda yake ce mata a ransa"itama idan ka shiga wataqila
haukan da zata yi maka kenan"wata zuciyar ke gaya masa,ba yadda ka iya tunda itama
aqarqashinka take kuma ka shigarwa 'yar uwarta indai adalcin kake son yin
Da sallama ya shiga ta amsa a sanyaye tana zaune ne kan kujera hijabin da tasa ta
budewa masu shigo da kaya har yanzu shine a jikinta saidai sabanin da yanzu
akwatinan a rufe suke,a fakaice yake dan nazarin falon komai tsaf yake cike da
tsafta da qamshi hakanan komai a killace yake a muhallinsa da kyawunsa kamar yau
aka jerashi sabanin falon samira da komai ya fita hayyacinsa saboda rashin kulawa
duk da dama tsadar kayan ma ba daya bane don iyayenta basu da qarfin iyayen
fadilan,kanta na qasa ta dam zamo daga kan kujerar tace ina wuni? Duk da bata sa
ran masawarsa ba don bai taba amsa gaisuwarta ba ga mamakinta wannan karon sai taji
yace "lpy ga kaya nan abinda babu ko baiyi ba sai ki yi maga ko ki rubuta ta
girgiza kai tana cewa😔 komai yayi mun gode Allah ya qara arziqi" ya lumshe
idanunsa don har zuciyarsa ya ji dadin addu'ar "madalla" yace ya zaro bandir na
dubu dubu guda uku ya dora saman akwatinan ya juya ya fice sai yaji wani sauqi na
radadin da zuciyarsa ke masa addu'ar ta faranta ransa don tunda yake bai taba samun
kwatan kwacin wannan ba daga bakin wani abu wai iyali ba
Muje zuwa yanzu aka soma
Mrs muhammad
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
12:45 pm 03/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣2⃣ 2⃣2⃣
▶2⃣2⃣
Ana ya gobe daurin aure su anty hafiza anty hauwa farida sumayya rabi'ah har da
rahama suka zo wa fadila,farida ta zube dinkunan da fadila ta bayar aka mata sunyi
matuqar kyau da gaske duk da tana da sababbin din kunan ma da bata taba sa su
ba,kala ashirin farida ta zabar mata aka dinko su lace biyar atamfa biyar shadda
biyar material ma biyar ne,anty hafiza ce ta taho mata da mai gyaran jiki gashi da
lalle takanas sai hade haden magunguna namu irin na mata imgantattun na 'ya'yan
itace,anty hauwa sai dariya take tana cewa o'o'o fadila 'yar gata to ai ko kece
amaryar sai haka,sai dai tayi dariya ta sunkuyar da kanta qasa cike da kunyarnan ta
ta,anty hauwa ta zuge jakarta ya fito da littattafai tace ga saqon momi nan,hannu
biyu tasa ta amsa tana godiya litttafai ne kusan goma na addu'o'ine da kuma gyara
zamantakewar aure,
Zuwansun ya sake debe mata kewa taji dadi nan suka fara tsara yadda za su gudanar
da yinin su na gobe wanda ko wacce mace da za'a qarawa abokiyar zama ke
gudanarwa,wuni akai ana qalqale mata jiki yayin da su rabi'ah sumayya da rahama
suka zage wajen qal canzawa gidan fasali,sune canza labulaye canza carfet goge goge
da ahare share duk da komai na fadila tsaf yake sai abinda ba'a rasa ba,cikin
qanqanin lokaci kuwa gidan nata ya canza kamar ba shi ba,hatta qamshinsa sai da aka
canza kalarsa ya zama na musamman abinka da diyar bare bari
Rahama ke tambayar fadila samirah fa?fadila tace wlh tun safe dai naji tashin
motarta amma ban sani ba ko qunshin itama ta tafi "Allah ya kyauta inji anty
hauwa ,bayan isha'i komai ya kammala anty hauwa tace zasu wuce sai gobe kuma idan
Allah ya kaimu anty hafiza da yake kwana za suyi ita da farida tace"dama kwanciyar
ku muka yi maman kausar wlh ,a'ah hafiza na bar yara su daya a gida daga su sai
Abbansu wunin yau fa duka?"anty hafiza tace to don Allah ga laila(mai qunshin da ta
dauko)ku sauke min ita a dorayi
Suna kan gado duk su ukun sunyi shirin yin bacci hafiza ta zubawa ido dake qoqarin
shafa addu'a tace wai yau wa kuka barwa mijin ne?samira fa bata dawo gidannan ba
haka kuke masa?"cikikin son rufe sirrinta da son gyara rayuwar aurenta ba tare da
taimakon kowa ba tace "girkin samira ne anty bana son neman rigima da tashin
hankali me zani in masa tunda ba girkina bane?salin inje mu raba dai abun
fada?"daga haka suka qyale zancan
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegarin aka zo akawa salima jeranta da yake aikin maza ne nan da nan yayi sauri
amma akwai wasu daga cikin yan uwanta mata da suka zo da su,girkinsu su fadila
sukayi sosai suka zuzzuba a manyan warmers suka aikawa yan uwan salima da wani wasu
kuma suka barshi nan cikin kitchen dinta saboda mutane yan uwa da maqota da keta
zuwa Allah ya sanya alkhairi har a lokacin sashin samira na kuelle ne alamar bata
dawo ba kenan hakan yasa kowa ya shigo gun fadila yake yowa idan suka tambayeta
samira sai tace ta tafi gidan qunshi
Ba qaramin kyau fadila ta zuba ba tamakar ita ce amaryar daga wayewar garin zuwa
yanzu ta sanya kaya kusan kala takwas kenan har harabar gidan jama'ace don babu
laifi yan taru duk da ba wanda suka gayyata
💔💔💔💔
Qarfe sha daya da rabi na rana aka daura auren Aliyyu salim maitama da salima tukur
Abubakar,kasancewar gidansu salima na na unguwar dake daura da g.r.a ne yasa
yanuwan fadila na jiki da suka halacci daurin auren suka dinga zuwa ana gaisawa
suna tafiya ciki kuwa harda abbanta da muhammad da ya ahmad taji dadin zuwan hakan
kuma ya faranta mata ranta don tun da aka daura aurenta rabonta da taga abban nata
kuma shima yaune zuwansa na farko gidan nata,ya mata nasiha sosai da ta qara mata
nutsuwa ta kuma sata kuka ta sake tabbatar da cewa ba qaramin zumunci bane tsakanin
abban nata da uncle abba mahaifin aliyyu tabbas babu abinda zata wa abban ta
aduniyar nan fiye da ta jure zaman aure da aliyyu,anan suka bar mata muhammad zuwa
yamma abban zai turo a daukeshi
Qarfe sha biyu da rabi ta sake wanka ta sanya wani Swiss lace pink ne mai dan
turuwa kadan sai kore aka masa da ratsin silver din zare sai manyan dutsina masu
walqiya sarqarta abun hannu da dankunne mayafi da takalmi duk silver ne dinkin riga
da skert aka mata skert din eight pieces ya bude daga qasa sosai ,yayi matuqar
karbarta ya haska chaculet din fatarta gashinta mai tsawo da santsi da baqi ya sha
parking da pink and green din ribbom sai ya kwanta a bayanta sai sheqi yake tayi
daurinta das wanda ya ta qasansa gashin nata ya fito,ta dauki turare tana fesawa
taji ana kiranta maqotanta sun shigo kuma wasu na nemanta a harabar gidan saurin da
take yasa ta manta bata dauki mayafi ba,suka gaisa da baqin tasa aka kawo.musu
abinci sannan ta qarasa harabar gidan, nasiru ne da wasu mutane suke neman gun
jibge abincin da ake ta shigowa da su,ta nuna musu store dinsu dake harabar gidan
ta farko kusa da parking space
Tana shirin shigewa ciki motocin suka soma danno kai suna parking daya bayan
daya,bata fuskanci su waye a ciki ba sai da suka cika harabar gun dukkaninsu cikin
fararen kaya suke,Aliyyu ta hango a tsakiyarsu fuskarsa nata fitar da wani annuri
cikin wata rantsatstsaiyar shadda babbar riga da yar ciki sai wando zata iua cewa
bata taba ganinsa da irin wanna shigar ba ya qara wani kyau da kwarjini sosai ta
shagala da kallonsa har suka hada ido
Haushi ne da takaici suka cika shi ganin yadda tayi kwalliya kuma ta fito har kusa
da get a haka na tare da tayi lullubi ba,yayi mata kallon nan nasa data tsana wanda
ya saba yi mata hakan yasa ta tuna a uadda ta fito fa tayi saurin shigewa cikin
jama'a ta bacewa ganinsa
Tana zaune cikin baqinta sumayya ta shigo tace anty kije inji yaya sai taji maganar
banbarakwai gabanta kuma ya fadi tace yana ina?yana cikin garden,dakinta ta shiga
ta sake fesa turare sannan ta lulluba mayafinta,tunda ta nufo lambun zuciyarta ke
dukan uku uku a haka har ta cimmasa,yana tsaye ya goya hannunsa a baya ya juyawa
qofar shigowar baya,batasan yadda akayi ya gane ta shigo ba don gurin gaba daya
grass carfet ne bare tace yaji takun tafiyarta ne sai ji tayi yayi gayaran murya
gayaran muryan sai ya zamo kamar ya mata luguden guduma a qirjinta🔨,me ya fito dake
harabar gida babu lullubi?shiru tayi muryarta na dan rawa tace ka.....kay......kayi
haquri"ya dan dauke wuta na dan lokaci kana ya juyo da azama kar mai shirin waftar
wani abu,hakan ya sa tayi tsammanin duka zai kawo mata tayi baya da sauri cikin
tsautsayi ta taka wani dutse sai kuwa ta tadeta tayi baya luuu zuciyarta na bugawa
da sauri don ta gama saddaqarwa sai ya sha qasa,sai kuma ta jita jikin mutum aliyu
ne ya sa singalalin hannunsa ya tallafeta ta bude idonta data lumshe tana jiran ta
jita ta sha qasa sai ga idonta cikin nasa,ya tsuke mata fuska 😠kana yace meye haka
tashi" tayi azamar zare jikintata tana cewa kayi haquri,sai ya harde hannunsa
aqirji ganin yadda duk tabi ta duburburce yabi gashinta wanda ya bi wuyanta ya dawo
kafadar ta ta dama da kallo lace din ya zauanar mata caras cas yabi lafiyayyar
fatarta chaculet,ya dan dauke kansa yabi gefansa da kallo yana jan tsaki a fili
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
2⃣3⃣ 2⃣3⃣
▶2⃣3⃣
Sai da ya gama shan qamshinsa sannan yace ina da baqi dame dame kuke da shi a
kitchen?cikin dai rawar muryar tace akwai sinasir masa funkaso da miya fried rice
sai white rice da miya,ya danyi shiru sanna yace cikin sweet a bamu sinasir da masa
sai a hado da white rice tace to har ta juya yace hey! Tadan waigo idonta na kallon
qasa yace idan min kawo kiyi knocking kawai ki barsu a bakin qofa ta gyada kai ta
wuce
Bayan isha'i gidan ua dade ba mowa sai anty hafiza da farida suma suna gama kintsa
mata ko ina suka turare shi sannan sukai haramar tafiya,godiya ta musu mai yawa su
kuma suka cikata da nasiha ta rakosu tana bawa naty saqo don allah ki kawo min yan
biyu tunda kika kaisu gida yaye anty minqi karbosu tace yayanku ma mita yake amma
shekaran jiya munyi waya da mama sun kusa dawowa insha allah da haka suka rabu ta
dawo ta koma bedroom dinta ta hada ruwan wanka wanda ya wadata da turarukan
wanka,bayan ta fito ta shirya kanta ckin wani lafiyayyen material kalar qwanduwar
qwai wanda aka masa ado da qyalli silver da ratsin fari kadan kadan ,shima yana
daya daga ckikim dinkunan da aka kawo mata jiya riga ne da skert amma wadannan sun
kamata sun muma fito da shep din ta sosai,tana gyara kayan kwalliyar dake kan
madubin nata ne taji gudar yan kawo amarya jikinta ya saki ta zauna bisa dressing
chair
Tana kwance bisa kujerar qaramin falonta agogon bango ya kada qararrwar qarfe goma
tayi ajiyar zuciya ta gayar kwanciyarta goma da ashirin da biyu qarar intercome ta
tada ita daga bangaren aliyu ne hakan yasa ta fahimci hadasu yake sonyi kamar yadda
al'ada ta tanadar gabanta ya tsanata faduwarsa💔,cikin nutsuwa ta sake feshe jikinta
da turare turare ta lulluba mayafi a lallausan gashin kanta wanda bata daura
dankwali ba
Da sallama ta tura qofar falin nasasu biyun ne suka amsa amaryar na tsaye gaban
fridge tana ciro ruwan roba da lemo yayin da gogan ke hakimce bisa kujera two
sitter shigar jikinsa ta yanzu ta babbanta da ta dazu duk da dai babbar riga ce
yanzu ma a jikinsa ta shadda milk colour ya ajiye babbar rigar a hannun kujerar da
yake kai,salima ta dan zubawa fadila ido na yan sakanni sannan ta dauke kai ta
dauki plate saman fridge din ta dora kayan fadila ta samu one sitter dake gefansu
ta zauna ,saluma ta janyi centre table dan madaidaici gaban aliyun ta dora masata
tsiyaya ya masa ta jiye ta koma kusa da shi kan kunerar da yake kai ta zauna,fadila
ta saukar da idanunta qasa tana cewa cikin ranta "ni kadaice bani da irin wanna
damar me yasa why Aliyu?,na kusa samota na kusa da qarfin zuciyata insha Allah"
muryarsa ta jiyo yana fadin kefa mume jira ko?,shiru na yan mintina sanna ya qara
cewa"yayi miki kyau" ya ajiye wayar ,saluma tace kawai ka qyale ta ni na gaji bacci
nake so nayi,fadila ta dago kai suka hada ido sai kuma kowacce ta dan saki fuskarta
fadila tace sannu amaryarmu"itama da dan murmushin a fuskarta tace sannu kuna lpy"a
taqaice fadila ta amsa mata da" lau"ta dan saci kallonsa shi lemonsa ma yake kurba
idonsa na kan qofa
Banko qofar akayi aka shigo samirah ce sanye da baqar doguwar riga babu ko alamar
hida bisa fuskarta sai dan kwalun atamfa da ta dauro a kanta wanda tayi masa daurin
ture kaga tsiya,ta kama qugu tana cuno baki gaba tace da aliyu "gani" wani banzan
kallo ya jefeta da shi sanna yace "ga gurin zama nan ko ina idan kuma bai miki
�
ba.....ya nuna mata qofa da hannu,sai da ta qarewa ko ina kallo sanna ta nufi
kujerar da aliyun ke kai kusa dashi a daya side din ta dora qafa daya kan daya tana
girgizata harara salima ta makawa samirah itama kuwa batayi jinkiri gun ramawa
ba,taja tsaki sanna taci gaba da jijjiga qafarta,hara rarta aliyu yayi ya kalli
qafar da take jijjigawa ta fuskanci abinda yame nufi kuma tasan ba magana zai.mata
ba don haka ta sake zumbura bakinta sannan ta sauke qafar tata
Godiya ya far yiwa Allah sanna ya dora dukkaninku a qarqashin iko na kume kuma
tsarin Allah ne shi ya tsara hakan kamar yadda yame da ikon tsara rayuwar ko wane
bawa nasa to ma gode masa akan duk yadda yayi da tawa rayuwar "daganan ya dora da
yi musu gargadi da jan kunne sannan ya tunasar dasu tsarinsa na zama a bangarensa
mai girki ta biyoshi"salima ta kanne masa ido tave" dear ani dama na nasan da wanna
tsarin naka tuntuni saidai kawai ya zamto kamar tunasarwa a gareni"murmushin shima
ya mayar mata yace "yes"
Zuciya ta kawowa samirah iya wuya sai da ta tanka" a banza ai wai talaka ya girmi
�
sarki dolen mutum yanzu shinr qarami ko yaqi ko ya so"cikin fusata salima tace "ke
nifa ba dake nake ba,ban gayyatar irinku a zancena don ni idan banda qaddara ba ma
baki kai matsayin ma ki zama kishiya ta ba wlh don ko yar wanke wanken gidammu ta
�
fiki kwarjini sai kuwa samira ta nuna ta da yatsa tace"don kutumar uban mutum ya
qara gaba mana don ni duwa wuce dole ne a zauna da ni zama daram wlh "sai suka so
su kacame
Cikin wata gigitacciyar tsawa aliyu ya dakatar da su sannan yace kowacce ta bace
masa agun ba zasu haddasa masa ciwon kai ba haka kawai"salima ta miqe ta shige
bedroom dinsa samira kuwa ta fice tana gungunin a qyaleta wlh taci uwar mata,ita
kuwa fadila abun nasu tsorata ta yayi don bata taba ganin fadan kishiyoyi ba
hasaluma ma ba'a taba yiwa umminta kishiya ba gidansu daga ita sai farida sai
muhammad ko a tsakaninsu ba fada suke ba don haka tun ma kafin ya kammala bada
umarni su fice din ita tuni ta riga su fita yana juya lamarina ranta
Ransa abace ya shiga dakin duk yadda taso lallashinsa yayi banza da ita ta san
halinsa tun ba yau ba kuma bata manta da shi din ba don haka da taga yayi banza da
ita yana shirin shiga wankà sai ta qyaleshi sai da ya fito yana shirin kwanciya
sanna ta langabe a jikinsa tana bashi haquri,ya dan kalleta ya basar sannan yace
matuqar kika ce haka zaki dinga biye mata kunayi a cikin gidana to na rantse babu
wadda zan saurarawa acikinku,idan banda raini ma a gabana? Ta sake marairaicewa
tana cewa "Allah na lura ita wannan kanta na hayaqi ne da kamar dayar ce da babu
ruwana da ita,su auremin mijin kuma suce bazanyi kishi ba" shi sai a lokacinne ma
ya tuna da fadila baima san sanda ta fice a dakin ba donsanda yake musu jawabin ka
ta na sunkuye ne sai ya tuna rana shigen irin wanna da ya hadasu ita da samirah ba
wanda ta kula a ranar ma ahi ko samiran harta wuce" ya kauda wannan yace mata" am
telling uh indai kina son zama da ni cikin kwanciyar hankali" "baza'a qara ba dear"
Ganin yadda yaqi sakin jiki da ita yasa ta dinga masa wasu abubuwa wanda suka sa
ala dole ya ajjiye fushinsa abinka da dama wanda yake cikin wani hali nan ya bada
kai bori ya hau aka tuno da tsohuwar zuma don salima dama idanunta a goge take ta
wannnan bangaren to haka shima aliyyun yake dalilin da yasa saliman ma ta kasa
auren kowa kenan tayita naci har sai data dawo masa
Mrs muhammad
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?.......
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣4⃣ 2⃣4⃣
▶2⃣4⃣
Cikin kwanakin amarci kawai ake ta ballewa a gidan ,salima wayayyar gaske ce ko da
wani lokaci tana manne da A.s maitama samira kuwa ta kasa tsaida hankalinta gu
guda,yiwa salima itada da aliyyu labe kuwa ya zamo.mata kamar ibada mintina kadan
sai ka hangota tana ta safa da marwa tsakanin sashenta da na Aliyu,fadila baiwar
Allah lissafinta yafi ga kwanakin da zata soma shiga office da kuma ranar da zata
zamo itace ranar girki a gareta
Kwana uku kenan da tarewar salima fadila ta soma zuwa aikinta ya kama ranar
laraba,shiga tayi ta hausawa atamfa ce dinkin riga da zani wadatattu yayin da tayi
lullubi har kanta cikin yalwataccen mayafi komai nata cikin kamala yake da nutsuwa
haka nan halittarta take kamar wata babbar mace duk da shekarun nata qana na ne,ta
bude sabuwar motarta fara qal wadda bata taba shigarta ba saiyau,ta zauna a sit din
zaman driver ta kunnata ta wana ta sosai sanna ta sauke hannunta daga kan key din
ta hada tafukanta ta soma addu'a🙏🏻,sai da ta gama tana shirin tasar motar ta tuna
da hand bag dinta data manto kan gadon ta da sauri ta bude motar ta koma ciki
A hanyar dawowa ne sukayi kacibus da shi kasancewar ta gefansa ne zata wuce din sai
tayi tsammanim bai ganta ba don haka ta dauke kanta cikin sauri ta wuce don ta kusa
makara ta ajjiye jakar a asit din baya tasa hannu zata kunna motar taji an janye
hannun gami da zare key din ta daga kai tq bishi da kallo bai ko kalleta ba ya
zagayo sit din mai zaman banza dake kusa da ita ya zauna sosai sannan ya maida
qofar ya rufe,ta dan sunkui da kanta😔 ya dan kalleta sannan ya basar don ya lura
kamar al'adarta ce hakan,ya tabe baki cikin muryar nan tasa ta isassun maza mai
cike da izza ya soma ce mata"ko banza a qarqashin mulki da ikona kike saboda haka u
must obeying my statute and order if kina son aikinki,ya dan qara tsuke fuska 😠duk
da yawancin lokuta haka fuskar take ya dage kafadunsa sannan yace" I don't know why
aka wani tsiri yin aikin bayan ban gaza komai a gidana ba......
Ya dan sha qamshi sannan ya dora firstly ya zama dole kanki shiga ta kamala idan
kin tashi fita,sannan ban lamunce da yawace yawace abu na gaba kada ki kuskura na
ganki da number din wani qato a waya ko receiving calls ba and d last one kuma mafi
girma wanda zai iya causing loosing din aikinki mu'amala da maza,kada ki dauki
damar da na baki na fita aiki lasisi ne da na baki da zaki dinga ganin kina da
right na yin duk abunda kika ga dama,take note👉,yana qoqarin ficewa tace insha
Allahu zan kiyaye"duk da ranta a abace yake da irun dokokim da yake kafa mata da
ita a karan kanta ai tasan ya kamata,baice komai ba ya cilla mata key din yaja
qofar ya fice ya tafi abunsa,ta miqa hannunta ta rufo qofar sannan tabi bayansa da
kallo yanayin yadda yake taku kamar zabar masa inda zai taka ake,ranta babu dadi ta
ja motar ta fice a gidan ,yanayin motar yana da dadin tuqi hakan ya taimaka mata
wajan dawo mata da walwalarta,a hankali temper dinta take sauka sai ta dora da
fadin la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalim cikim zuciyarta,da haka
har ta qarasa gidan radiyon freedom don can ta tafi sha'awa amma duk da haka akwai
wasu privet ayyuka da zata dinga yi da express radio din
Yanayin yadda ta samu karbuwa ya sake sa mata interest akan aikin sosai,su biyu ne
kawai a office din ita da wata fauziyya kusan za tayi sa'a da fadilan amma ita nada
yarinya daya iman,fauziyya shekararta uku da soma aiki da tashar,sosai fadila taji
dadin samun fauziyya da tayi wayayya mai faran faran da son jama'a duk da ita
miskila ce,wunin ranar tayi shine tare da managing director da wasu ma'aikatan tana
arranging din ayyukanta ciki harda tsara sabin shirin da suka qirqiro wanda za'a
fara gabatar da shi a asabuwar shekara wanda itace mai gabatar da shirin da
taimakon fauziyya ta sake fuskantar yadda abubuwa suke duk da dama tasan da wasu
lokacin attachment dinta
Kwana biyu tayi tana tsara komai ta mai da kanta busy sosai ta hana kanta sukuni
hakan yasa bata da wani lokaci na tunani ,da ta koma gida tayi wanka tayi sallah
sai ta samarwa kanta abunci simple ta ci sai kwanciya idan da wuri ta dawo kuma
takan yi tilawar alqur'ani tunda dama ta jima da kammala haddarsa tun lokacin da
tayi candy,idan ta gama taga tana da wani lokcin sai ta dauki wani aiki da zai
taimaketa a office ta yi ko tayi amfani da laptop dinta tayi research na wasu
abubuwan masu muhimmanci,a rana ta uku ne da taga komai ya kammala ta nemi hutu na
kwana biyu ba wani matsala suka bata tunda dama bata soma gabatar da ayyukan ba
cikin shirye shirye dai take,tayi hakanne don a lissafinta ya bata yau itace zata
karbi girki ,kuma dama tuni ta shiryawa zuwan ranar
Da wuri ta koma gida ruwa kawai ta watsa ta zura doguwar riga har qasa mai hannun
shimi ruwan hoda ta saka,ta taje dogon gashinta ta daureshi da ribbom shima ruwan
hodar ne,farin hijabi ta saka wanda iyakacin qirjinta kawai ya rufe,ta wuce locker
dinta ta lalubi inda ta adana muqullan da bata amfani da su ta debesu gaba daya ta
zira farin silifas na fata ta fito,a falonta ta soma tsayawa ta bude fridge ta
dauki lemon chi exotic nectar na pineapple da yayi sanyi sosai ta sha ta maida
sauran ta rufe sashen nata,
TO FADILA SAI INA?🤔
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣5⃣ 2⃣5⃣
▶2⃣5⃣
Kai tsaye sashen Aliyyu ta nufa gabanta na dan faduwa kadan kadan har ta isa
qofan,addu'a fal bakinta ta ke sanya muqullan daya bayan daya take gwadasu har ta
dace da na qofar,ta tura babbar qofar ta shiga sanyin a.c ne da daddadan turaren
aliyyu ne yayi mata maraba,ta dan lumshe ido kadan sannan ta waresu sosai kamar mai
neman wani abu,a hankali take bin kowane sashi na falon da kallo tabbas yana
buqatar gyara,bata shakka cewa har bedroom dinsa ma na buqatar a kintsashi,ba tare
da tsayawa wani dogon nazari ba ta dauko dust bin dake falon ta ajjiye a tsakiyar
falon ta zare dan hijabin nata ta jefashi kan kujera ta fara tattare ta fara
tattare leda takarda gwangwani da duk wani abu da ya zama datti ne tana jefashi
cikin kwandon sharan
Tana tsaka da aikin ne taji ana taba qofar alamar an shigo a tsorace ta dago tana
tsammanin aliyu ne sai dai kuma maimakon haka sai taga ashe salima ce tayi tsaye a
abayanta tana qare mata kallo ,fadila ta tsani yadda matar me mata naci nkallo
haka,dama ita tun da can ta tsani mutum mai azabar kallo,to haka saluma ke mata a
duk sanda hanya zata hada su ,abinda ita fadila bata sani ba shine kishine taf cike
a zuciyar saliman don so tayi ta samesu gaba daya babu mamora kamar yadda taga
samira bata da qira sam,saidai ance gwano baijin warin jikinsa ne ita dinma da tayi
dogon nazari da tsinkaye da ta fahimci yadda tata qirar take irin matan nan ne masu
azabar tsawo da sirantaka sai wani azababben fari da take da shi irin me gauu din
nan to duk da babu laifi tafi samirah amma ko kusa bata kamo qafar fadila
ba,tsawonta da azabar sirantaka su suka sata take a miqe kamar number 1 ba wani
shape sai tsabar iyayi da yauqi
Ta kau da kai.daga kallon fadilan ta tabe baki sannan tace"oh nayi tsammanin mai
gidan ne ya dawo da naga gun a bude" a taqaice fadila ta amsa mata da"A'a" taci
gaba da aikinta,sai kawai salima ta bude fridge ta dau maltina hadi da kunna t.v ta
nemi gu ta hakimce,sarai ta gano ba abinda yasa saluma zama a gun banda bin
qwaqawafin taga me take yi hakan yasa ta sa key ta bude bedroom dinsa ta shige tare
da rufe qofar da muqullin ta ciki,salima tabi qofar da kallo cikin takaici don ba
haka ta so ba,nan ta zauna tana ci gaba da shan maltinan tana dakon fitowar fadila
wadda batasan ma tana jiran ba
Ta qarewa shima bedroom din kallo sannan cikin nutsuwar nan tata ta fare tattare
shi shima tana kintsa komai a muhallinsa tanayi tana mamakin kamar babu wasu mata
dake kwana a dakin komai a yamutse?towel ne underwear ne comb ne mayuka ne turaruka
ne kai tarkace dai wanda da alama a safiyar yau kafin ya fita yayi amfani da su
warwatse bisa gadon bedsheet din kansa duk da babu datti amma ya yamutse,kowanne
abau ta maidashi inda ya kamata cikin qanqanin lokaci dakin yayi fes komai ya dawo
cikin hayyacinsa ta kunna kaskon turaren wuta electric ta zuba irin turaren wutan
da take amfani da shi a bangarenta sanna ta wuce toilet
Toilet ne qaton gaske wanda yakai girman ciki da falo na mata da yawa yana dauke da
duk wani kayan amfanin toilet na zamani,cikin lokaci qanqani shima ya dau haske
komai na cikin sa farine sai da ya dawo daidai tamkar ka zuba abinci a qasan ka
ci,sai da komai ya mata yadda take so ya wadatu da sanyayyan qamshi sannan ta bude
qofan ta koma falon don ta qarasa aikinsa
Salima ta bar falon saidai ga gwangwani nan da tasha malt cups da qarin ledojin
cake da na wasu tarkacen ciye ciyen nata watse a agun da ta tashin,baki ta tabe
cikin ranta tana cewa"Allah ya sawwaqe an san yadda za'a bata amma ba'asan yadda
za'a gyara ba sai kace ba mata ba,tana wanna zancan zucin tana kammale falin duk da
girmansa kuwa,har kitchen bata barshi a baya ba sai da ta gyareshi ,"haba duk kyan
abu ai yana buqatar gyara"inji fadila tana riqe da qugunta ta fada bayan ta gama
aikin tana qarewa bangaren kallo yadda ya koma tamkar ba shi ba
Aikin ya ja mata lokaci sosai kuma ya gajiyar da ita,tana kimawa bangarenta nan ma
dai ba zama din kitchen ta shiga ta kama habarta🤔 cikin tunanin me zata girkawa
aliyyu wanda zata iya kammalashi kafin kiran sallar magariba ganin gashi hudu tayi
har da rabi,abu mafi muhammancin ma bata san choice din aliyyu ba ,sai ta yanke a
ranta bari ta fara gwadashi da tuwo ta gani din ta fuskanci wasu mazan ba sonshi
suke ba in yaso idan yayi masa shikenan an wuce gurin
Tuwom shinkafa ta daura miyar danyar kubewa wadda ta dagargaza mata zallar tsokar
kaza sanna ta sa tantaqwashi ya wadatu a ciki,misalin qarfe shida komai ya kammala
ta soma mulmula tuwon da yayi fari sol cikim farar leda ya tuqu sosai ya hada
jikinsa,sababbin warmers masu kyawun tsari ta dauko ta jerashi a ciki,ta gama ta
gyara ko ina kamar bata yi aiki a kitchen din ba,ganin tana da ragowar lokaci
yasata ta dora farfesun danyan kifi ragon ruwa maimakon zaman jiran dahuwarsa sai
ta hada zobo wanda ta markada wadatacciyar abarba ta zuba a ciki ta hada da citta
da kanunfari ta dafa,shima ta zubasu a mazubi ta wanke tukwananta,cikin azama ta
shiga toilet ta silla wanka
😂😜 na gano su maman sa'ida fa na son jin qwaqwaf an baza👀👂🏻👄 anason aji ya aka
kaya ko
To🤔🤔🤔kada dai ku gaji ku biyo safiyya insha Allah don jin kanun labaran
Mrs muhammad dinku ce 07066139278
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 12:38 PM] Salma:
WA YASAN GOBE?


Written by safiyya Abdullahi musa huguma

2⃣6⃣ 2⃣6⃣
▶2⃣6⃣
A bakin mudubi ta yada zango ta fara shafe loko da saqo na jikinta da turare dama
ta saba da yin hakan kwalliya irin ta zamani mai tsari ta shiryawa fuska fuskarta
bata cikata da jagwalgwalo ba ta taje gashinta mai tsaho da sulbi ta daureshi da
ribbon ja swiss lace ta saka orange mai adon ja riga da skirt dinkin rafa wanda
yayi masifar fito da sharp dinta,ta bata lokaci tana zana dauri a kanta ya zauna
gwanin sha'awa fashion ta saka na dutse na sarqa da dan kunne sannan ta cika
hannunta da awarwaro irin na india ja mai ashirin da hudu ya ahmad ne ya taho musu
da tsarabarsa sati biyu da suka wuce,plate shoe ta saka orange and red ta sake
feshe jikinta da turaruka sanna ta kalli kanta a mudubi,masha Allah ta fadi ba tare
da tasan ta fadi ba sai murmushi ya subuce mata ita kanta yau ta sake gasgata
kyawun da ake fadar tana da shi,kiran sallar magaribar da taji shi ya sata saurin
fitowa ta shiga kitchen ta shirya kayan abincin ta kulle sashen nata ta fito tana
tunanin qila ma aliyyu har ya dawo,ta cikin balcony din ta ta isa sashen ba alamun
ya dawo don haka ta sa key dinta ta bude tana shirin shiga tajiyo alamun tsayuwa
mota ta waiwaya sai taga samirah ce ke shirin fitowa daga motar tata wani irin
kallo samiran ta watso mata wanda fadila ta gaza gane mai take nufi,dauke kanta
tayi abinta ta shige don ba ita bace a gabanta tana mamakin masifaffen yawo irin na
samira
Cikin qwarewa ta shirya table din sannan ta sauko cikin falon ta kunna tafkekiyar
t.v plasma din dake manne a bango cikin sa'a kuwa malaminta ne ke karatu a saudi
qur'an ta dan qaro volume matsakaici ya game falon ta koma gefe ta tada sallarta
cikin nutsuwa bayan ta idar ta koma ta zauna tana kallon yadda mahajjata ke dawafi
Mintina biyar da zaman nata taji ana bude get jikinta ya bata Aliyyu ne jikin
window taje ya dage labulen tana kallonsa har ya fito daga motar dukkan alamun dake
nuna gajiya ga mutum sun bayyana a tare da shi,duk da ya gajin amma a nutsenshi
yake kyawunsa na nan saidai fara'a da tasake yiwa fuskarsa qaura hirar da fadila
keyi kenan ita da zuciyarta nasiru ne ya kulle motar bayan yafito sanna ya miqa
masa kayayyakinsa da muqullan cikin rusunawa kamar ko yaushe aliyu ya karba yana
cewakada kowa ya jirani gobe ka sallamesu don bazan fito da wuri ba idan ka
sallamesu sai kuci gaba da list din suna yan wadanda suka karbi kayan amma a cire
sunan alhaji hamza wannan mun gama da shi✋🏻,nasiru yace ok insha Allahu ya juya
yana shirin wucewa yace Allah ya tashe mu lafiya,ameen ya amsa masa
Burinsa ya isa gida yayi wanka ya samu abinda zaici ko da tea ne donshi kam har yau
cikin matan gidan babu wadda zai nuna�yace girkinta ya masa har gwara salima yakan
qoqarta yaci indomie dinta don kore yunwa,yayi mamakin ganin qofar tasa a bude amma
sai yayi zaton ko salima ce,ba wani dadi da yaji don ason ransa so yayi ya zauna
shi daya ya samu hutu
Saidai yana tura qofan wani daddadan qamshi ya daki hancinsa wanda ya tilasta shi
lumshe ido kasancewarsa ma'abocin son qamshi sai ya shiga tunanin inda ya taba jin
qamshin amma ya kasa cankowa idanunsa suka sauka a kanta bata anakara da ya shigo
bane ko tsorone ya hanata motsi?ya dan tabe bakinsa 😠yana tunanin mai ya kwao ta
kuma? Ya qarasa shiga falon yana sallama a nutse ta dago tana amsawa ya dan zubawa
fuskarta ido zuciyarsa na son yaba wani abu amma ya rasa meye shi?ita kuwa gabanta
ke faduwa cike da fargabar kada ya wulaqanta aniyarta yadda ya saba ganin yaddda ya
hade rai kamar ya ga kashi,sai kuma taga ya dauke kansa ya nemi kujera can gefe ya
watsar da kayan hannunsa sannan ya zauna har baisan sanda yace wash! ba ya sake
lumshe ido yana ci gabada sheqar qamshin da ya ji yayi masa har cikin zuciyarsa ya
rasa kuma ta Inda ya samu don dai shi har ya bar falon baiji qamshin ba sai yanzu
da ya dawo
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣7⃣ 2⃣7⃣
▶2⃣7⃣
Sannu da zuwa tace cikin cool voice dinta,ya bude idonsa tana durqushe gabansa riqe
da cup da jug na glass baice komai ba yabi hannun nata da kallo dake riqe da cup
din tana tsiyaya masa lemon zobon dake ta tsatstsafar sanyi da qamshin abarba ta
janyo center ta dora a kai sanna ta balle murfin gorar ruwa na c'bon ta cika masa
shima cup da shi ta ajjiye masa duk baice komai ba cikin dari darin kada ya
gwasaleta ta miqe ta dauki briefcase dinsa safa takalmi key dinsa da duk ya wurgar
din ta yi cikin daki da su
Tana shiga tayi maza ta maida qofar ta jingina jikinta ta dafe qirjinta tanajin
yadda yake bugawa da sauri da sauri idanunta a lumshe tana dan murmushi☺, cikin
zuciyarta tana cewa wai Allah na! Sai da ta dan nutsu sannan ta ajjiye kayan a inda
ta tsara musu kai tsaye ta wuce toilet ta kashe makunnin heater din don har jar
danja ta kama alamar ruwan ya tafasa ta hada masa ruwan wankan a bathtub ta
saisaita shi ya zamo mai dumi sosai yadda zaiyi saurin saukar da gajiya sannan ta
zuba masa turarukan wanka a ciki
A hankali yasa hannu ya dauki cup din zobon yana tunanin meye wannan? Ya kai
bakinsa da niyyar dandanawa sai gashi ya shanye har da qari sai da yasha cup uku
sannan ya saki ajiyar zuciya saboda yadda dadinsa da sanyinsa ya ratsa shi sai yaji
kaso goma na gajiya da qishirwarsa har ma yunwar sun fara sakinsa ya samu relief
har a qwaqwalwarsa ya jingina bayansa da makarin kujera
Sai a yanzu ne ya lura da canjin da falon ya samu ko ina tsaf tsaf kamar yadda yake
so,tunanin wa ye yayi aikin yake don shi kqm daga samira har salima yasan cewa
matane masu azabar ganda da ko ruwan sha sai ya tambaya ake iya tashi a dauko
masa,ga ruwan wanka can a toilet ko kana da buqatar yin wanka,ya dago da kansa tuni
har tayi hanyar kitchen fadila tayi hakanne don gujewa baqar maganarsa ko da ziyi
mata ta maqale a window din kitchen tana leqensa
Sai da ya bata lokaci sosai har fadila tayi zaton bazaiyi wankan bane ta soma dana
sanin shishshiginta sanna ta hangoshi yana kwance agogon hannunsa hadi da cire suit
dinsa ya riqesu a hannu ya shige dakin tabi bayansa da kallo,ta janye idanunta hadi
da lumshesu ta dafe goshinta da tafin hannunta tana cewa a can qasan maqoshinta"wo
hoho Aliyyu badai miskilanciba?.... sai kuma ta sake sakin murmushi tana cewa"Allah
ka mallakamin Aliyyu"tayi saurin dafe bakinta tama zare ido saboda ta fuskanci
maganar zuci ce ta fito fili
Sak yayi ya tsaya yana kallon dakin baccin nasa komai kamar yanzu aka jerashi ko
tsinke babu a farin tiles din dake mamaye da dakin ya jinjina kai ya ajjiyr kayan
hannunsa a gefan gado ya fara binciken inda ya ajjiye rigar wankansa sai ya bude
wardrobe donnya dubata a ciki,canji idanunsa suka masa karo da shi,wardrobe ce ta
jikin bango mai hangar komai ya canza bangaren shadda daban yadi daban suit dinsa
haka kai hatta socks dinsa da handkerchief an masu nasu tsarin bai san sanda ya
saki murmushi ba don tsarin ya burgeshi kasancewarsa dan gayu ya tabbatar babu
tsarin rigar wankansa a gun don haka ya haqura ya wuce toilet cikin ransa yace
wonderful cikin wani glass dake manne a kwanar bandaki ya hango rigunan a tsare
jikin hanger bai bata lokaci ba ya shige cikin ruwan wankan duminsa da qamshinsa
suka ratsashi sai yaji kamar kada ya fito,ya shafe kusan minti talatin sannan ya
sabe jikinsa ya dauraye ya fito bisa gefan gadon ya zauna ya tsane jikinsa ya nemi
farar jallabiya yasa don yafi son sata idan ya dawo daga aiki ya taje kansa ya
feshe jikinsa da turare sanna ya bude jakar computer dinsa ya cirota yayi waje da
niyuar shiga kitchen ya tafasa ko tea ne ya sha
Ganin ya zauna yana aikinsa ya sanyata debo kayan ta shimfida babbar ledar cin
abinci a gabansa baisan me takeyi ba sai da yaji qamshin abinci nata shiga hancinsa
sanna ya dago kansa ya dubi gabansa ta jera tuwon a farin kyakkyawan plate miyar na
wani dan kwano na tangaran shima fari ne tasha man shanu ta cika wani plate din da
farfesun ragon ruwan ta zuba ruwa na sha da na wanke hannu ta tsiyaya masa lemo
sanna ta janyo tissue box ta ajjiye masa tace bismillah ya kalleta 😠yace " ce miki
akayi da yunwa na zo? Ko an baki labari ina buqatar abincinki kinga malama kwashe
abincinki ki ban wuri,
Ba qaramin sosa mata zuciya maganganun suka yi ba bata san sanda hawayen da take
boyewa suka silalo mata ba😭karo na farko kenan tun sanda ya fara mata cin
kashi,batayi qoqarin maidasu ba ta barsu suka ci gaba da zuba
Cikin zuciyarsa addu'a yake allah yasa kada ta kwashe din don tunda yaji qamshin
sha'awar cinsa ta kamashi ai kuwa aadu'arsa bata karbu ba don a zuciye ta soma
maida abincin cikin warmers din
😜😜😜
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 12:39 PM] Salma:
WA YASAN GOBE?


Written by safiyya Abdullahi musa huguma

2⃣8⃣ 2⃣8⃣
▶2⃣8⃣
Sai da yaga da gaske take cikin daurarriyar fuska yace kinga malama zuba kada a
qarani gaba ace bani da adalci tunda kin kawo kanki" ya fadi kamar wanda da gasken
tilastashi akayin,kalmar tunda kun kawo kankin tayi matuqar bada gudun mawa wajan
qona mata rai don haka hawayen da suke zuba suka qara gudu😭
Malmala daya ta saka masa da miya ta miqe wata zuciyar na zugata kiyi tafiyarki
kawai wata kuma na lallashinta da hanata tafiya tana gaya mata saurin fushi ba nata
bane yanzu da sauran lokaci dai,kujerar da ta tashi a kai can ta koma ta zauna tana
qoqarin maida kukanta ta canza tasha zuwa mbc boollywood ta tarar suna film din
kuch kuch hotahie tsohon film ne amma bata gajiya da kallonsa
Ta kasa hankalinta kusan gida uku kason farko na kan aliyyu ne da taga ya ci gaba
da danne dannensa a computer ya shanya abincin,na biyu na kan matan gidan da ta ga
har yanzu ba wadda ta leqo da niyyar yi masa barka da dawowa ashe haka suke masa
har ita din?,na uku kuma ta dorashi kacokam ne bisa t.v dake gabanta sai ka rantse
da Allah ta bata hankalinta ne gaba daya
Ta gefan ido taci gaba da satar kallo da nazarinsa sanda taga ya rufe computer din
ya sauko qasa mamakinta zaman da taga yayi zamane irin wanda annabi yake yayin cin
abincinsa mamakinta ya sake qaruwa ne sanda taga yayi bismillah ya sa hannunsa ba
tare da ya nemi cokali ba
Hankalinsu dukkansu ya kai bakin qofar jina naturo ta,saluma ce ta shigo da yalwar
fara'a a fuskata amma sai taja tayi turus ganin fadila a falon,cikin iya tsabar
duniyanci da iya waskewa ta gayyato fara'a fuskarta ta dubi sashen aliyyu tace"
a'ah dear inacan ina zullumin yau ka jima baka dawo gida ba"ya miqamata hannu sanda
ya sa lomar tuwo a abakinsa yana mata nuni alamar ta taho ,ta taho din kuwa ta
zauna kusa da shi sai da ya hadiye sannan yace almost one hour da wani abun da
dawowata na gajine shi yasa ba wanda na nema"da ido ta nuna masa fadila tana masa
nuni da ita ya akai tasan da dawowarsa har ta rigata zuwa?,dauke kai yayi kamar bai
fuskanci abinda take nufi ba don ba'a haka shi da shi,itama tasan hali don haka ta
bar maganar
Murya a anarke tace dear dama zancan ankon lubabatu ne qawata da nayi maka,kudin
nakeso na karba don banason in zama a qarshe saboda baka fiya samun mai kyau ba"ya
gyada mata kai yana ci gaba da cin abincinsa,ta tsare shi da ido ganin baice komai
ba bayan gyada kan sai tace sake cewa naji kayi shiru baka"ya dago cikin qosawa
yace ba munyi maganar ba tuntuni ba kuma ana amsa miki kuma yanzu baki ga abinci
nake ci ba" tace cikin son wayancewa ok takai dubanta ga abincin gaban nasa sannan
tace" dear yaushe ka fara cin tuwo?"kai tsaye yace "yau"cikin mamaki ta maimaita
yau" ya gyada kai yace "yes"sai kuma tace ammafa nima abincin ya burgeni bari
muga"ta tsoma hannu a plate din nasa,aliyu ya tsaida cin abincin ya bata fuska ya
dago yana dubanta "repeatedly am telling you duk sanda kika soma cin abinci ba tare
da kinyi bismillah ba kina cine tare da shaidan ko?" Ta dan dafe kai tace oh sorry
na manta bismillah amma fa abincin nan dear yayi sosai a wane restaurant ka siyo"
na gida ne ya bata amsa ya dan dubi sashen fadila wadda idan ka kalleta a zahiri
zakayi tsammanin kallin film dinta takeyi haiqan sai dai duk tana jinsu tayi kunnan
uwar shegu da su,salima ta fuskanci abinda yake nufi don haka ta tsuke bakinta😷
tana da na sanin yabawar da tayi wa abincin din bata yi tsammanin fadilan ce tayi
ba
Salima na ta zubawa aliyyu surutu jefi jefi yakan tanka mata har suka kusan tashi
da abincin gaba daya har farfesun kifin,suka gama aliyyu ya koma kan computer dinsa
ya ci gaba da lissafe lissafensa na kayyayakin dake cikin store da wadanda za'a
zuba sababbi da kuma wadanda ya saba rabawa yan kasuwan
Har kusan tara na dare salima na zaune taqi tafiya,cikin haka saiga samira itama ta
shigo yanayin samira ne yasa sauran kadan farida ta tuntsure da dariya duk da
quncin da zuciyarta ke ciki,nikam safiyya kasa daurewa nayi sai da na dara har
sai da maman walid ta rufemin baki don kada su ganni
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
03:15 pm
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
2⃣9⃣ 2⃣9⃣
▶2⃣9⃣
Salam! Samirah tace cikin daga murya tana tafiya tana wani budewa babu wanda ta
kalla direct ta wuce gun maigidan hannunta dauke da zungureriyar farar takarda,ya
dan bar abinda yake kana ya dubeta yana masawa,ta qaraso inda yake ta zauna hannun
damansa yayin da salima ke hannun hagunsa takardar ta miqa masa ya amsa kafin ya
duba yace" kada ki sake min irin wannan sallamar da kikamun yanzu don ba sallama
bace take note,ok?"ta gyada kai tana buntsuro baki,ya bude takardar yana dubawa,ya
qare dubawar sannan ya dago kai yana kallon fuskar samiran idanunsa da alamun neman
qarin bayani,ta dan yatsine fuska sannan tace"eh abu uwan amfani ne da suka qare
nake da buqatarsu" ya dan gayara zamansa ya jingina da makarin kujerar ya sanya
idanunsa sosai cikin nata,sai ta kasa kallonsa ta dan soma rikicewa tana son janye
idonta ta kasa tasan shi tamkar maye yake wajen naqaltar mutum tasan yanzun nan ba
qaramin aikinsa bane ya harbo jirginta,da zarar aliyyu yayi ma irin wannan kallon
yake gamawa da kai,sai da yayi shiru na muntina sannan yace"ina zaton yau ko sati
biyu ba'ayi ba na karbi list na dukkan abunda baku da shi na kawo.....ya akqi naki
ya riga na kowa qarewa bayan ko sati biyun ma ba'a cika ba?"
Ganin tayi shiru ta kasa bashi amsa yasa ya maida kallinsa ga salima wadda tayi
kasaqe tana sauraronsu zuciyarya cike da farinciki tana mai addu'ar Allah yasa a ci
mata mutunci"nawa ne kudin naki ankon"tawani yi fari da ido sannan tace😊 atamfa
dubu arba'in ne lace dubu sittin aai gudun mawar da zan bata dubu dari"(kunji
tsabar rashin hankali irin na wasu matan mutumin da duk qarshen wata yake fita da
su suyi siyayyarsu idan akwai abinda sai anshiga kasuwa ake samu zai sa su su
rubuta ya bayar a akawo musu haka nan kayan abinci da na ciye ciye zaisa a sabunta
miki koda basu qare ba kuwa ruwanki ne kisan yadda zakiyi da su shi dai duk qarshen
wata zai miki haka,hakanan zai kawo kudi masu kauri ya baki bayan wanda kullum zai
baki koda ba ranar girkinki bace )baiji komai ba kasancewarsa mai hannun kyauta ne
koda ba ga iyalinsa ba,amma ya lura barnar ta soma yawa don haka ya sake waiwayawa
ga samira yace"uhm....am waiting for d answer
Ta yatsina fuska tace" kasan ni maca ce mai jama'a 'yar dangi kuma duka dangina
anan garin suke ba baquwar haure ka auro ba wannan ya shiga ne wannan ya
fita"salima tasan da ita take kasancewar iyayenta da danginta ba a garin suke ba a
hannun qanwar mamanta take anan kanon amma ba yan garin bane,cikin hasala tace "da
uban wa kike?"kamar dama jira samiran kuwa take tace da ubanki nake👉,kinji na kasa
da ke ne bare ki dauka banza kawai😙 mtswee!"ai kuwa salima tayo kukan kura tayi
kan samira da niyyar shaqota dama da qullin samiran a ranta
Wata gigitacciyar tsawa ali ya daka musu wadda hatta fadila dake gefe sai da ta
miqe tsaye saboda razana bare su salima da suka koma sukayi zamqn dirshan ba tare
da sun shirya ba,ran 'yan maza ya baci fa zuciyarsa ta tabu take idanunsa suka kada
Cikin tsananin bacin rai ya kallesu "wadanne irin mahaukata ne da baku da burin da
ya wuce kuyi kokawa?"salima da ta shaqa da yawa ta nuna kanta👆🏼 tana cewa aliyyu
nice mahaukaciya?" Ya dora da cewa "kun
wuce hakanne?bai sauraresu ba ya murza yatsunsa suka ce das das das ya nuna su�
sannan yace dis is d last worning kunyi na farko kuma kunyi na qarshe dambe a
☝🏼
agabana..... bazan dauka ba don ni ba shasha sha bane" salima da idonta ya ciko da
qwalla😢 tace"amma fa kana gani fa tana shigowa ta hau habaici daga qarshe ta hau
zagina.....samirah ta tari numfashinta da cewa"tambaya kimayi na baki amsa daidai
da tambayarki" shut up!" Ya sake dakawa samira tsawa ya nuna mata qofa😡� sannan
yace da ita get out of my room,jiki a salube ta juya zata fita ya ce hey🖐🏽ta juyo ya
nuna mata paper dinta�take your rubbish neman tashin hankalinki ya siya miki ya
bita da "stupid" wani takaici ya sake turnuqeta ai kuwa buguzum buguzum ta qarashe
ficewa
Ya dawo da idonsa kan salima yace"ni bani da kunne sanda tayi zagin ba zaki bari
kiga hukuncin da zan dauka ba sai ke sarkin iya hukunci?,sai kuma alokacin ta soma
shagwabe masa da sunan bashi haquri ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu"🖐🏽
dont disturb me please leave me alone"ta san bacin ran aliyu bashi da dadi do haka
ta ja qafafunta ta fice cikin takaicin asarar da sira ta jawo mata na kudaden da
take son karba a gunsa,yaja tsaki mai qarfi cikin ransa yace"silly girl" ya juya a
hanzarce ya shige bedroom dinsa
Ransa ya baci sosai mutum ne da baison hayaniya yanzu haka qirjinsa zafi yake haka
yake ko hira yayi mai tsaqo yanzu kansa zai fara ciwo shi yasa ko musu bai iya
ba,ba ruwanshi da shiga wata harqalla ko abokai bai fiya tarawa ba baifi ka qirge
abokansa ba da hannu,to da shi da fadilan bansan wanda yafi wani ba🤔

Writting by safiyya Abdullahi musa huguma

3⃣0⃣ 3⃣0⃣
▶3⃣0⃣
Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya canza kayansa zuwa na barci farare ne sol masu
taushi mutum ne shi ma'abocin son fararen kayan amfani ya fada bisa gadon yayi
rigingine qafafunsa na qasan gadon ranshi a cunkushe yake
Fadila da ke tsaye sai yanzu ta motsa ta saki ajiyar zuciya gami da fadin Allah ya
kyauta ya iya mana abinda ba zamu iya da shi ba,ta isa inda suka baje kolin
abincinsu suka ci suka tashi bar kwanukan ta tattare su ta gyara gun kamar ba'a yi
hada hadar abinci ba agun
Ta isa kitchen ta zubasu cikin sink ta kunna gas ta hada ruwan bununsa wanda ya
wadatu da citta kanunfari da lemon grace ta saka lipton daya sannan ta rufe
tukunyar,ta koma ta saki fanfo ta wanke duka kwanukan ta adanasu sannan ta juye
mishi tea din cikin wani dan qaramin flask mai kyau ta dauki cups guda biyu na
tangaran ta dora a saman plate ta hada masa da spoon,ta rufe qofan kitchen din ta
doshi bedroom din nasa
Ta tura qofar tana dar dar don tana tsoron kada ya maimaita mat abinda ya mata
dazun,ya canza kwanciyar tasa zuwa barin hannun damansa yayin da ya juyawa qofar
shigowa baya,qafarshi da yake dan kadawa kadan kadan shi yasa ta fahimci idanunsa
biyu a hankali ta ajjiye tire din a asaman bedside sannan ta koma saman kujerar
madubi ta zauna tana fuskantar bayan nasa,dakin ya yi tsit kamar ba wata halitta a
dakin sai qarar agogon bango dake maqale a abangom dakin yana ta aikinsa,ita batace
komai ba bareshi da tasan dama ba maganar zaiyi ba
Zuwan can ta dan ja numfashi sannan ta tattaro dukka dauriyar da ta rage mata bayan
ta gama wassafa da tsara maganar da zata fito a bakinsa,tayi yar gajeriyar gyaran
murya a dan tsorace sanann tace" nazo ne baka haquri game da bata maka rai da
mukayi dukkaninmu mu ukun,zan ari bakin yan uwana na ci musu albasa ince kayi
haquri da mu baki daya,idan ban manta ba haka Abba ya gaya maka a ranar da mukaje
masa _lamarin mata sai da haquri da kuma jajircewa halitta ce maau wuyar sha'ani
amma idan kasa Allah a gaba sai komai ya zo maka da sauqi_"kayi haquri da mu Allah
kuma ya huci zuciyarka😔,ga black tea nan ko kana da buqata sai da safe
Ta miqe tana barin dakin ya dan waiwayo yana dan kallon ta har ta fice,yana cike ne
da mamakinta dama tana da saurin sauka a fishi ne?,at least ya samu relief ainun
daga damuwarsa,hakan ne ya bashi dama har ya jawo flask din ya murda murfinsa ya
bude qamshinsa ya taso ya mamaye hancinsa ya dan lumshe idonsa take kwadayin tea
din ya kama shi,yasa kofi ya tsiyaya ya sanya zumarshi ya kurba qamshin cittan da
kanunfarin da lemin grace suka hadu a abakinsa suka masa dadi
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tana idar da sallar asuba bayan kammala al'adarta ta kullum wato azkar na sabahi
wal masa wanda annabi ya koyar ta koma ta jingina da gefan gadonta idanunta a
lumshe ta soma tilawa kamar yadda ta saba cikin sassanyar muryarta,sai da tai izifi
biyar sannan tayi addua ta shafa,ta linke sallayarta sannan ta soma gayara bangaran
nata duk da ba datti ko kadan sai 'yar qura da ba'a rasa ba wadda hadarin da ake
tayi kwana biyu idan ya hado sai kuma ya zama iska mai sanyi wadda ke tashi hade da
yar qura,tana kammalawa tayi wanka sannan ta shirya cikin doguwar rigar yan kanti
mai roba roba red ce ta sauko mata har qasa ,daga gaban rigar wajen qirji an kamata
an mata tattara yayin da ta bude sosai daga qasan aka jera wasu irin dutsuna manya
guda uku masu garai garai da qyalli hannun vest ne da ita saboda haka ta sanya long
sleeve shirt fara ,tayi rolling da farin mayafi wanda acucin da tayi da gashinta ta
mai doughnut ya taimaka wajan qarawa rolling din nata kyau iya kafadunta mayafin ya
tsaya,qananun fashion na barima farare ta saka sannan ta jawo takalminta slippers
na fata shima fari ne,wayarta ta dauka ta kulle bangaran nata
Yauma da keys dinta tayi amfani ta bude gurin,shiru yake ba motsin komai hakan yasa
tayi tsammanin bacci yake,hakanne kuwa ta gani sanda ta leqa bedroom din nasa cikin
sanda,yana kwance tsakiyar gadon duqunqune cikin farin lallausan bargo ,gefansa
daga qasa dardumarsa ce qur'ani da kuma carbi 📿akai,yayi mata kyau sosai aliyyi
gwanin kyau kome yakeyi kyansa fita yake,baccinsa yake verry calmness fuskarsa tayi
fresh,sai ta lumshe ido tana tuna da yadda daren jiya tayi nata baccin cike da kewa
da azaba,amma shi yanzu gashi yana nasa hankalinsa a kwance har da qarin wani na
bayan sallar asuba kenan,ta dauko wayarta ta kashe plasher dinta tayi snapshot din
fuskarsa,ai kuwa ta fito shar zara zaran gashin idanunsa sun kwanta luf,tayi
kissing din hoton sannan ta juya ta yi kitchen
*mrs muhammad ce*
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣1⃣ 3⃣1⃣
▶3⃣1⃣
Chips ta soya hade da wainar qwai sannan ta dama masa kunun gyada da ya sha madara
yayi fari qal sai zuba qamashi yake,sannan ta bare indomie ta yi masa awarar
indomie,nan fa qamshin abincin ya karade gaba daya falon har cikin gidan to wani ma
yayi rawa bare dan makadi,fadila gwanar girki ce mayyar kitchen ce tun tana gida
ma,tana saitin window inda kan famfo yake tana wanke kayan da ta bata ta ke jiyo
motsi kadan kadan,windon na cikin lambun bangarenshi da ke bayan part din kowa,tana
daga kai ta hangoshi qarfe yake dagawa🏋🏼ya hada gumi sosai,armless riga ce a
jikinsa da shortnekeer damtsensa cike da qwanji a murde,ya ajjiye qarfen ya dau dan
farin towel dake gefansa yana sharce gumin kana ya dauki bottle na ruwa ya daddaka
ya rufe ya koma kan keken training kuma🚵🏻
Ta saki murmushi ta kada kai,da azama ta hada komai ta koma bedroom ta gyara masa
ta wanke toilet ta hada masa ruwan wanka,ta budade ko ina da qamshin nan nata
sannan ta dawo parlour ta zare rolling din kanta ta fara gyare falon shima ,yana
daga can yake jiyo qamshi kala kala na shiga hancinsa da fari qamshin girki ya fara
jiyowa ya bude dogon hancinsa yana shaqar sa saboda ya masa dadi daga bisanai kuma
ya jiyo wani qamshin qamshin da ya kwana jiya yana sheqa,ya sauka daga kan keken
shima ya dauki wayarsa da towel dinsa ya bude qofar bayan ya shigo ta cikin kitchen
wanda yasa sauran kadan suyi karo,ta ja baya da sauri tana gaidashi kanta na duqe a
qasa kamar kullum bai amsa mata ba dama ta zaci hakan ya dai daga mata hannu🖐🏽ya
wuce
A bandaki ya tarar da ruwan wankan nasa,ya dan yi dam domin bai saba ganin hakan ba
a tarihin rayuwar aurensa ba ganin tunanin zai bata masa lokaci yasa kai tsaye ya
shige cikin ruwan🛀🏼yana sheqar qamshin da yake
Cikim suit ya fito baqaqe masu sheqi sunyi masifar fito da ainihin kyawunsa,takalmi
ne half cover dan hasken marun kamar yadda tie dinsa yake marun da jakarsa a hannu
fuskarsa saye da fari qal din medicated glass dinsa wanda bai hanawa mutum ganin
kyakkyawan qwayar idanunsa,sumarsa a kwance luf baqa sidik sai sheqi take ita ba
mai yawa ba kuma ba a aske ba qamshin nan nasa na musamman ke fita a jikinsa,ya dan
zauna a hannun kujera yana qarasa taje sumarsa da brush dake hannunsa
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
Afuwa afuwa
Nayi rubutu mai yawa zan turo muku na ajjiye wayar ina dan wani uziri kafin na dawo
ya goge,chargy kuma ya riga yayi halinsa,kuyi haquri da wannan ku bini bashi da
yardar Allah
Na gode
Mrs muhammad ce
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 12:40 PM] Salma:
*wa yasan gobe?.....*

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

3⃣2⃣ 3⃣2⃣
▶3⃣2⃣
Ganin wannan dama ya sanya fadila tayi saurin sauko da kayan breakfast din gabansa
duk da cike take da fargabar kada ya gwasaleta,tayi saurin hada masa tea☕ ta
daidaita masa zafinsa ta ajjiye masa sannan ta sa masa wainar qwai🍪 da farfesun
kayan ciki,taji dadi da baice komai ba ya sauko ya karya,bayan ya kammala ya dauki
jakar laptop dinsa ya ciro yan dubu dubu guda uku ya ajjiye mata kamar yadda yake
ajjiye wa sauran matan ranar nasu girkin duk da kuwa babu abinda zasu siya komai
diba za suyi yana ajjiye,ya yi gaba ta biyoshi a abaya gabanta na dukan uku uku
bangaren samira ta ga ya shiga don haka ta ja tunga ta tsaya baifi mintina biyar ba
ya fito ya shiga gun salima mintina takwas sai gasu sun fito yana gaba tana biye da
shi ganin fadila na tsaye da alamum jiran fitowarsa take sai yanayin fuskarta ya
sauya😠 take ta juya ta koma ciki
Har sai da ya shiga mota ya zauna sannan tace a dawo lafiya tayi saurin juyawa ba
tare da ta jira cewarsa ba don tasan bazai ce din ba ma idan ma ua fadan to ba mai
dadi zata ji ba,tana hango salima da ta yaye labulen falonta tana kallonsu don haka
sai fadila ta qorqiro murmushi ta dora bisa fuskarta
Ta rasa hali irin na salimar mutum ce mai tsananin qyashi da hassada ga azabar sa
'ido komai idanunta na kai kamar wadda aka bata aikin yin hakan ita dai samira
barta da kishi masifa da tsokalar rigima kuma kana tabata za kuyi uwar watsi agun
shikenan duk da haka kishin salima har yafi na samira ita kawai tanada duniyanci da
yasa take iya boyeshi ba kamar samira da ba ruwanta ko a gaban uwar waye ayita ta
watse ba munafunta
⚜⚜⚜⚜
Haka fadila taci gaba da tsara rayuwarta duk ranar da take da girki zata shiga
bangaren ta gyara ko ina da ina,tana kuwa fama da aikin domin tsakanin samira ko
salima babu mai iya yin cangal kowacce haka take fita daga girkin ta tabar sashen a
ahautsine
Tsakaninta da aliyyu sai girki ta shirya masa daddadan abinci ta zuba masa ya ci
idan ya kammala ta kwashe ta wanke kana ta ja qafarta ta bar sashen sai kuma
washegari idan ta shigo hada masa breakfast,da zarar kuwa kwanakinta ya qare bata
bi ta kan kowa da zarar ta taso a aiki ta shiga sashenta ta qulle qofa tofa sai
washegari zata sake fitowa
Wai inji hausawa sunce jiki da jini kuma mutum da zuciya cikin lokacin sai sai
qyamar girkin su samira ya fara kama aliyyun ransa ya soma sosuwa da ganin sam
gyara bai damesu ba,har gwara ma.salima tunda at least akwaita da son ado da
kwalliya zata yi wankanta tayi kwalliyarta hakanan zata qoqarta ta dafa masa koda
jallop ce albarkacin masifar son sa da take duk da bata taba girki a gidansu ,amma
samira kuwa babu daya qanwar biyu daga ciki
Cikin harshensa da zuciyarsa yana jin dadin girkinta sosai dandanon da bai taba
jinsa ba gun kowa ba baya ga mominsa,miskilanci irin nasa yasa ko a fuska bata taba
ganin alamun haka ba,takan tattare masa socks singlet handkerchief three quarters
da duk inner wears dinsa harda jallabiyoyinsa da yake sawa ta wanke su tas ta goge
su sannan ta feshe su ta turare ta jera masa su to ammafa insha Allahu bayan kwana
hudu ta karbi girki zata zo ta tarar da su kamar kamar ba su ba komai an hargitsa
shi sai ta soma fuskantar wani abu akwai gayya a ciki ta kuma san bazai wuce su
salima ba don adawarsu gane da aikin nata a fili yake qara ra wani lokacin takan
jiyosu suna yan qana nan maganganu takan sharesu taqi tankawa don basu tari gabanta
sun gaya mata ba bare ta kula da shashancinsu
Abu daya ke qona mata rai aishi aliyyun na gani suke batawar shin bazai tsawatar
musu ba idan su basu da tunani?
Ga misali a farkon fara aikin nata kafin su soma adawarsu takan tsince kayan aliyyu
ne kawai a dakin a watse takan gyara ba tare da ta damu ba tunda tasan aikin ta ne
dama,da tafiya ta soma nisa sai suka dinga barin brassiere panties sleeping dress
underwear 👙👗musamman salima wadda kullum sai ta tsince nata tunda samira ke fara
girki sai ita wanda a qa'ida fadila ce ya kamata ta zamo mai girki a farko amma
suka maida ita ta qarshe ta qyalesu duka ta zuba musu ido ,tasan da gayya take zub
da kayan,zuciyar fadil na matuqar baci da hakan,a duk lokacin da ta tsinci kayan
takan bata lokaci mai yawa tana qissima dalilin barin kayan daga jikin mai su wanda
hakan ke qara ta'azzara kishinta ga aliyyu
Wani sabon rainin hankalin kuma sai ta fuskanci ya shigo ta soma gyaran sai ta
shigo tace"☺sorry fa don Allah,jiya na mance kayana akan gado wallahi dear ne ya
rudani daren jiya shi yasa da safe na manta da su ban dauka ba,kinsan shi akawai
nacin abun,sai dai fa ba sauqi shima fa gwani ne😉"wannan ya bata ranta fiye da
abinda tayi mata,har ta soma hasashem anya basu da masaniyar babu abinda ya taba
gilmawa tsakaninsu?
Akwai lokacin da ta zube har da magungunan mata maau dauke da hotunan banza,wannan
fadila maganinta tayi ta dauko mata wasu wanda wata maqociyarsu a acan gida ta bata
ita basonsu take bame ma zatayi da su tunda ta bata ta jawo locker ta watsasu sai
yau ta tuna da su ta qara mata tace ga wasu sai ki qara naga naki basu kai wadanan
tsada ba ni kinsan bana amfani da su halitta ta bata buqatarsu komai nawa yaji ba
sai da kwaskwarima ba"jiki a salube ta karba duk da bata nuna mata hakan ba,ai kuwa
da ta karanta kwalin sai taga tabbas sun fi nata kyau to tun daga ranar bata sake
bari ba
samira nata rashin mutuncin yafi ysakanin falo da kitchen parlour zuwa kitchen,zata
dauko plates ne🍽 kofuna ne🍶 da su spoon tayi ta batawa wani abun plate din ma leda
ce ta chewing gum ko biscuit zata dora akai kuma ta barshi a nan tunda ta sani cewa
babu mai aikin gyara gun sai fadilan,duk da wannan neman masifa da suke ba wadda ta
isheta kallo a cikinsu
Mrs muhammad
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
01:18 pm 05/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
3⃣3⃣ 3⃣3⃣
▶3⃣3⃣
Lahadi daya daga cikin ranakun qarshen mako ne wanda yake zama ranar hutu ga
ma'aikata to haka ne ya zama ga fadila hutun ya zame mata double babu zuwa office
kuma bata da girki,la'asar sakaliya ta ranar ta shirya tsaf cikin doguwar riga
shigar da tafi so kenan ta material ce ruwan qwaiduwar qwai dinkin rigar ya bude
sosai dga qasa an mata dogon hannu tayi rolling dinta kamar yadda ta saba da jan
mayafi,takddunta ta diba 📄📉📈 na aikin office da takeson dubawa zata yi wani aiki a
kansu ta dauki yar madaidaiciyar dadduma da daya daga cikin matashin kujerarta ta
zira takalminta ta firo harabar gidan,sai ta tarar da saluma da samira zaune
kowacce a harabar sashenta bisa farar kujera plastic,novel a hannun salima📖 samira
kuma na riqe da wayarta📱 tana tana ta faman danne danne,tun kafin fadila ta kai ga
zama ta fuskanci zaman nasu ba na Allah da annabi bane don kuwa taba fitowa ta fara
cin karo da baqaqen maganganun da auke jifan juna da shi a fakaice ba tare da kowa
ya kalli dan uwansa ba
kamar ta koma ciki sai kuma ta duba agogon wayarta📱taga biyar harda rabi da minti
uku bata da wani lokaci na duba takadddun idan ba yanzu ba cikin gidan kuma zafi
yayi yawa sanadiyyar hadarin da keta hadowa ana yin yayyafi dan kadan wanda ke qara
tada zafin garin,ga injinsu yayi tsiya yaqi tashi tun wajen uku bakaniken ke kansa
yana fama da shi kasancewar ba dan qarami bane yana daukar dukka freezers dinsu
heater a.c da sauransu sun riga sun saba da wuta ko yaushe 24 hours,sai kuma ta
ahimfida dardumarta cikin ranta tana fadin _ina ruwan biri da gada?_,tayi bismillah
ta zauna ta soma aikinta,ashe duk suna ankare da ita,minti goma bai cika ba da
zaman nata samira ta soma receiving call "shegiya kina duniya?......heeeee wlh gamu
a cikinsa muna gogawa.......hahahahahaha aike kinsan fa hali tun ba yau ba"ta danyi
shiru sanna ta sake kecewa da dariya kamar wani gardi tace"a haba haba ke sai kace
ba nice samira ba?.....k kinsan saidai a gaji aqyale mana,kowacce qaramar shegiya
sai ta kama gabanta da qafafunta🏃🏽 ,salima ta bude shafin gaba na littafin dake
hannunta tamkar da gsken karatun take tace"qaramin dan iska ma yaci uwatar ai yasan
kansa,samira ta sake kecewa da dariya "wlh har mai share share da goge goge ita
wannan ai ba wahala zata bani ba.....yo hannatu yar anacen ma ba komai bace a guna
wallahi duk hasashen da take na ita wata ce a gunsa
Sarai fadila ta san da ita take amma sai taga ba mutuncinta bane tsayawa tana cece
kuce da wadda batasan ciwo mutunci da kuma darajar kanta ba ,kan ta qare wannan
tunani sai ji tayi tas!
Da sauri ta dago idanunta don ganewa kanta wanda ka zubawa wannan lafiyayyen
marin,aikin salima ne tana tsaye a gaban samiran bayan ta kwasheta da marin tana
huci,tuni samira ta katse wayar hannunta na kan kumatunta ta miqe tsaye salima ta
dora mata da bayani👉shiru shirun da kike ganin ina miki ba fa tsoronki nake ba ki
bar ganin kina min kina samun nasara wallahi kin kaini bango nifa ba sa'ar yinki
bace don uwarki"tasa yatsanta tan nuna qirjinta👆🏼 tana cewa"ni kika mara?"😁an
marekin kadan ma kika gani wata rana zaki ga abinda yafi marin ma,kina tsammaninke
kaďaice tantiriyar karuwa ko?💁🏽to 👆🏼nima karuwace nayi nayi kuma yaqon duniya fiye
da naki ke da kika local ma
😳😳mamaki da tsoro suka kama fadiladama har akwai abun tutiya gun mace don tayi
yawon karuwanci?wannan wane irin zama nine da Allah ya kwomù da har karuwanci ya
zama abun ado?ita takaici ma sai ya sata ta maida kanta kanrubuce rubucenta📝taqi
kola kowaccensu tana jinsu cacar baki mai zafi ta barke tsakaninsu tamkar zasu
cinye junansu 🎭
Duf taji gun yayi shiru kamar an sanya musu kwado a baki🔐,ta dago da hazari don
ganin mai ya sanya su yin shirun ba tare da kowa ya raba su ba?,aliyyu ne ashe ya
ahigo kuma baau ankara da shigowar tasa ba sai da ssuka soma daga hannu da niyyar
😢
kaiwa juna duka,kowaccensu tayi sak saluma ce ta fara cewa 😢 wallahi tallahi ban
kulata ba itace ta fara takalatakuma ka tambayi fadila"jin sun sanyo sunanta cikin
sha'aninsu ya sanyata azamar taahi ta soma linke sallayarta,daidai lokacin da ya
kai dubansa😒 gun da fadilan take da salimar ke nuna masa,ga mamakinsa tana gama
ninke sallayar a nutse ta duqa ta mwaahe takardunta ta juya ta shige sashen nata ba
tare da ta kalli ko da daya daga cikinsu ba cikinsu ba sai aliyyu ya bita da.kallo👀
karon farko wani abu daga garetà ya fara burgeshi nutsuwarta ,sai da ta shige ta
kulle qofarta sannan ya dawo da idonsa kansu tuni samira har ta gudu🏃🏽ta rufe itama
qocarta cike da fargaba da tsoron fushin Aliyyu😡 a akanta don ta tabbatar In dai
ya bincika ya tarar bata da gaskiya to la shakka fa kashinta ya bushe,ta ruwan
sanyi yake ma hukuncin da zaka raina kankà babu duka ba zàgi bà baqar magana,ya
juyo ya dubi saluma da jikinta ke rawa sai kawai shima ya gewayeta ya shige nasa
part din
⚜⚜⚜⚜⚜
Kwana uku tsakaniya kamaqarshen wata ne,kamar yadda ya zama al'adar gidan fita
aiyàyya a iřin lokacin don sabunta abu uwan buqata na amfanin yau da kullum
Yaune za auyi fitar farko tun bayan dawowar salima gidan gidan
Fadila ta shiryq cikin shigarta ta bare bari tana nannade cikin lafayarta ,ta
kammalà komai ta kira umminta don su gaisa,hira suke sosai ta jiýo tashin horn ta
tabbatar aliyyu ne don bai son jira kuma baya jira saboda haka shima bai bari a
jirashi tayi saurin maqale wayar a kafada tan ci gaba da hirarta da ummin tasa daya
hannunta dauki jakarta🎒ta sa mèy ta kulle sashin,ta qarasa jikin motar tana sallama
da ummin ta ciro wayar daga kafadarta tana kashewa sai ga salima da samira tamakar
an jehosu kowacce na qoqarin bude gidan gana ta shige don badon fadila tayi azamar
matsawa ba da daita zasu yi awon gaba,ta rufe bakinta da tafin hannunta🙊 dariya na
shirin subuce mata😂,cikin zuciyarta tana cewa sunan wani film *qauyawa* Allah kayi
mana magani wannan ai kishin jahiliyya ne
😂😂😂😂😂
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 12:41 PM] Salma:
*wa yasan gobe?*

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

3⃣4⃣ 3⃣4⃣
▶3⃣4⃣
Allah ya sawwaqe tace,ta bude gidan baya ta shiga tana kallon drama,aliyu ne ya
juyo don ganin meke faruwa haka ake shirin cire masa hannun mota?cikin tsawa musu
su matsa masa daga jikin mota,bai wata wata ba ya figi motarsa ya barsu a gun sake
da baki😦,gudu yake zubawa abinsa bisa dukkan alamu ransa ya baci,duk sai fadila
tayi tsuru-tsuru don da irin wannan gudu da yake zabgawa gwara ya sauketa salun
alun ,
Qiiiii...taji ya taka burki,ya gangara gefan titi ya faka motar cikin shaqaqqiyar
murya taji yace"fito ki dawo gaba don ni ba driver din gidanku bane😠"bata ce
kanzil ba ta dawo gaban
Yanayin zaman yayi wa fadila kusa sosai,mayen turarensa ya soma raba mata
hankali,lissafinta ya soma qwacewa take kasala ta saukar mata,wani shauqin aliyyun
ya mamayeta duk da azahiri idan ka kalleta zaka yi tsammanin ko inuwar sa bata
gabanta
Sun isa shoprite inda suka saba siyayyar duk qarshen watan,ta san tsarinsa bai
shiga yana tsayawa ne a waje yayi zamansa cikin mota,da sun gama siyayyar ayi masa
total a turo masa list da amount,da yake yana harka da su akwai kamfaninsa dake
india wanda akwai hurdar kasuwanci tsakaninsu,"u have twenty minutes idan kima gota
haka so sai ki nemi motar mai da ke gida"ta jinjina masa kai duk da idan da sabo
yaci ace ta saba don duk sanda ya kawosu mintina ashirin din yake basu basa kuwa
darawar domin dukkaninsu sun san halinsa yana iya tafiyarshi
A nutse ta shiga ta duba muhimman abubuwan da take buqata don tana lisaafin jibi
ita zata karbi girki duk da ba wani tsiya bane a ciki banda tsabar bauta ta gyare
gyare da dafa masa abinci wanda sau da yawa tare suke cinyewa da samira da
salima ,sukan daidaici lokacin cin abincinsa ne su shigo da nufin sun zo taya shi
hira sai kuma su taya shi lamushe abincin
A gurguje ta kammala zabar duk abinda tasan bata da shi ba wani kaya ne mai yawa ba
tunda bata iya gama amfani da siyayyar tsohon wata suke sake sabuwa saidai ma wani
abun ta bada shi,sai ta soma dibarwa salima da samira abinda ta lura sunfi siya
yawancin lokuta idan suka zo,Allah ya taimaketa minti goma sha takwas ta gama
komai,ta riqe leda daya ragowar aka biyo ta da su
Tana fitowa suka yi kacibus da shi yana tsaye a hanyar wucewar tata,shi da wata
matashiya ce wadda a qalla shekarunta ba zasu gaza ashirin da shida ba,abunda ya
bata mamaki shine ganin hawaye bibbiyu bisa fuskarta😭,ta maida dubanta garesu a
karo na biyu daidai lokacin da aliyyun ya nuna ta da yatsansa yana cewa " this is
d last warnings da zaki sake bina wani guri ki kama kanki tun kafin ya gudu ya
barki and respect ur self"
Daf da zasu qarasa cikin motar wadda tuni an kammala zuba kayan taji ya tureta daga
jikinsa ,ta tsaya a baya sai da ta bari yayi gaba sannan ta biyoshi,zaman kurame
suka sakeyi cikin motar har suka isa gida
Ta kammala shirin baccinta ya sanya night gown sannan ta dora dogon hijabinta mai
hannu da ya sauka har saman qafafunta ta sanya sannan ta kwashi ledojin da ta yima
su salima ta su siyayyar ta nufi sashensu,saidai ta tarar dukkaninsu basa nan don
haka zuciyarta ta bata amsar ba zasu wuce sashen aliyu ba
Mrs muhammad👑👑
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
5:44 pm 5/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣5⃣ 3⃣5⃣
▶3⃣5⃣
Da sallamarta ta shigo falon sam bata ma lura da shi ba bisa dining,ta dan dora
murmushi bisa fuskarta🙂,salima ce ta masa sallamar itama ciki ciki kamar wadda aka
cusawa tsumma a baki,ta qaraso gabansu ta direwa ko wacce ledarta🛍 a gabanta tana
cewa"sannunku,ga siyayyarku nan Allah yasa na haso muku da abubuwan da kuke buqata
" salima shiru tayi saboda tafasa da zuciyarta keyi,yayin da salima yar takife
tace" waye ya saki sarauniyar masu shishshigi ,kina murna kina rawar kai an koro mu
ke an tafi da ke,shine don digimi da neman gindin zama harda wani yi mana siyayyar
kaya ko?to ahir dinki wlh ni ba'a shiga gonata don kiji na gaya miki,har wata fada
ce dake a gunsa banda ta shara da zaki mana rawar kai?ko an gaya miki sonki yake?"
"Hmmmm matar cushe kenan"cewar saluma da bata tofa ba sai yanzun,cikin wani irin
mamaki da al'ajabi ta dago tana dubansu,meke faruwa?a ina suka san wannan ?haka
aliyyu ya gaya musu cewar ba aonta yake ba?,wannan wane irin kwance zani a akasuwa
ne?,wanne irin cin kashi ne haka yayi mata?"take idanunta suka sauya launi,wani
irin fushi da bata tsammaci tana da shi ba ua sauko mata😡😣,kamar hadin baki suka
miqe suna shirin barin dakim don dama haushin kaza ne huce kan dami,tunda sunsan ko
giyar wake suka sha basu isa su juye haushinsu ba kan wanda ya musu laifin sai suka
juyeshi kanta,suna shirin ficewa suka jiyoshi cikin lion voice dinsa yana kiransu
"😠ku kwashe kayan nan daga gun nan ku bace min da gani"kunnen uwar ahegu sukayi
�
niyyar yi a zafafe yace da su"billahil azim duk wadda tabar ledarta a nan tamu ce
ni da ita"tilas kowacce ta waiwayo ta dauki tata tabar sashen
Cikin matsanancin bacin rai ta dago kantasai suka hada ido,wani baqinsa ta gani
wanda bata taba ganin yayi makamancin haka a idanunta ba,kafin ya janye idanunsa ta
fara janye nata tayi azamar juyawa ta bar sashen
Kusan kwanan zaune tayi ,babu abinda ranta bai gaya mata ba,abunda take ta qoqari
da fadi tashin bunneshi ashe ya dade da yin tsiro har yqyi yabanya?tabbasa aliyyu
ya cutar da zuciyarta ya cutar da zuciya da ke cike da qauna gami da begensa cikin
kowanne fitar numfashi na dan adam,tabbas a ayu badon mutum bai da ikon cire son
wani daga zuciyarsa ba da itakam ta ciro har zuciyar ta wurgar ta huta ma gaba
daya,ranar idanunta basu ga bacci ba sai tunani data takurawa.kanta da shi wanda ya
haifar mata da da ciwon kai da zazzafan zazzabi,ba ita ta samu kanta ba sai
washegari da la'asar bayan ta takurawa kanta ta cire damuwar ta ajjiyeta gefe
⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin qyanqyami yake shiryawa,gaba daya dakin ya hargitse sun kuma barshi kamar
yadfa suka saba,sai dan yakanji relief idan ya tuna zaije ya dawo ya tarar da komai
ya zama neat,da hanzari ya kammala ya dauki jakarsa💼 ya fice ba tare da ya saurari
breakfast da salima ta hada ba ruwan tea ne fari sol babu citta bare kanunfari sai
soyayyen qwai wanda qarninsa ke hanashi hadiyarsa,shi kuma akwai qyanqyami yayin da
su kuma basu maida tsafta 💄👠👒💅🏽da gyara wani abu mai muhimmanci ba
Sanda ya dawo ya tarar da sashen nasa yadda ya barshi yayi matuqar mamakin
hakan,don bai saba ganin haka ba,yasan ranakun girkinta zai tadda komai a kintse
hakanan yaji ransa ya baci da ganin haka,ya zube anan saman kujera yana fitar da
iska mai zafi daga bakinsa,ya dubi agogon hannunsa qarfe shida da arba'in har da
hudu,mintina qalilan suka rage a shiga masallaci sallar magarib,a kasalance ya duqa
yana zare sau cikin qafarsa👞hadi da sabule safar,wata bahaguwar yunwa ke
rarakarsa,yinin yau gaba daya ba abinda yaci banda maltina mai sanyi da ruwa da
yake ta dirka,saoda yana da yaqinin zuwa ya tadda abinci mai kayau🍛,
Kai tsaye ya shige toilet ya dauro alwala ya dawo falon yana goge ruwan jikinsa da
handkerchief,gidan🏛 tsit sai hasken fitilu da ya gauraya da duhu suhun magariba da
ya soma kawo kai ,ya dan lumshe idanunsa kewar qanan yara na shigarsa👫,ya tabbata
da yana da su da zai dinga jin koda hayaniyarsu ce da gilmawarsu ,ya riga ya saba
da tsabar qwarewar.matan gidan wajen iya rashin kula da miji,ya katse tunaninsa
sanda ya jiyo kiran salla a masallacin dake can farkon layinsu ya sanya silifas ya
fice yana maìmaita abinda liman ke cewa kamar yadda annnabi ya horemu idan munji
kiran salla
A can ya zauna ya jira sallar isha'i sannan ya dawo gidan,still gidan dai na nan
kamar yadda ya barshi kowa na kulle a sashensa,ya dauki wayarsa ya kira nasiru ya
gaya masa inda zaije ya samo masa masa da miyar ganye,cikin lokaci kadan saiga
nasirun ya dawo ya amsa ya koma ciki yayi wanka ya sauya kayan bacci,ya zuba masar
ya ci sai da ya qoshi sannan ya jawo computer💻 dinsa ya soma shigar da lissafinsa
na yau,hankalinsa ya kasu kashi biyu,ko alama zaman gun ya gundireshi sabo da
tsaftar gun bata masa ba,shigowar saluma ce ta saka shi tsai da abinda yake ,ba
laifi salima indai ta bangaren qalqale jiki ne salima ta iya wannnan kam,yanzun ma
ashirye take cikin dinkin lace baqine mai adon ja,ya sauke biron dake hannunsa
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 12:42 PM] Salma:
*wa yasan gobe?*.......


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

3⃣6⃣ 3⃣6⃣
▶3⃣6⃣
Ya sauke biron dake hannunsa🖍yana dan binta da kallo,tayi masa kyau sosai,fuskar sa
ta dan sassauta daga dauretan da yayi ganin yadda take masa murmushi😃,gefansa ta
zauna cikin salon kissa take cewa"barkanka da warhaka ranka ya dade"yadan janyota
jikinsa yana cewa "barka kadai......sai yanzu aka ga damar zuwa yimin sannu da
zuwan?"ta san tabe baki tace"girki na ne da zan taho daga dawowarka?" "Ko ba girkin
ki bane ni ba mijinki bane?" "To ayi haquri ko" yace "ya wuce"ya maida kansa kan
aikinsa tana tayashi da hira jifa jifa yana amsa mata
Samira ce ta shigo wannan karan harda sallama,abun arziqin nata yau yana da
yawa🤔 don ba'ayi wari da.wari ba riga da zani ta saka na atamfa,kanta tsaye ta
zauna daf da shi tana mata sannu da zuwa ba tare da ta nuna ma ta san da zaman
salima ba agun,ya dan saki fuska bayan ya ja yatsun hannunta da nashi zara zaran
yatsun yace"bana amsawa tunda kema sai yanzu" "bana shishshigi ne sweet kuma bana
son maiyi shi yasa"ya dade da haddace wannnan kalma daga bakin samiran,don haka ya
mele baki gefe sannan yace"lallaikam,da kun bani babies ai da sai nace kusha
zamanku ni kuma insha hira da yara na ko?"
"Nikam ai na riga nabada tawa baby din"cewar salima"no she is belongs to momy,u
already know...sabuwa nake so"cikin shagwaba ta dan bata rai sannan tace"haihuwa is
not easy dear"samira sai ta tabe baki hadi da cewa"mukam ai ba yanzu ba,tunda
sauran quruciyata🤔"aliyyu ya jawo ragowar takardunsa yaci gab da rubuce
rubucensa ,kowacce yasan inda tasa gaba dama salima d tasu ai tun shekarun
baya,shikam idan da abunda ya rage masa yanzu shine tara family babba
Cikin kwanakin fadika ta watsar da duk wata harka data danganci aliyun ta koma
rayuwarta irin ta da,idan gari ya waye tayi ayyukanta na gida ta fice office sai ta
dawo tan dawowa ta shige to sai washegari idan ta gaji sai fa kira farida ummi ko
anty hafiza su sha hirarsu,ko muhammad yazo mata su wuni tare abinsu
Gaba dayan bangaren ya fita daga ran aliyyun saboda tsabar kacamewar da yayi,ko ina
ba kyawun gani a hargitse,ranar da salima ta fita daga girki yaga tana shirin kulle
sashen ta wuce nata sashen,cikin takaici ya kalleta ganin bata da niyyar kawar da
ko cup din da ta hada masa tea bare akai ga batun gyara "jimana!" Yace da ita a
zafafe ta dawo tace gani"bai ko kalleta ba ya daga intercom ya kira sashen
samira ,sai da ta qara wasu mintina kana ta iso hakan ya sake hassala shi,ya dubesu
cikin bacin rai yace
"Anya kuwa ky mata ne cikakku?ba ko wani jinsin bane ku?"a mamakance suka dago suna
kallonsa,"kamar ya?"inji samira,da hannunsa ya soma yi musu nuni da falon suna
binsa su kuma da kallo,"ku duba....dubi......haka ya kamata ace ya kasance?haka
sauran mata suke barin turakar mazajensu?....abun naku ba ya yi yawa na lira ba
hankali a ciki,ba tsafta ba iya kula da miji?kuma ni kuna son kyautatawa daga
gareni?....it cant abun yayi yawa na gaji da tolerating bad attitude dinku....as
from today ya zama dole a kanku kowacce kafin ta bar nan ta tabbatar ta gyara duk
inda ya kamata ba ruwana da qazantarku ruwanku ne ku gyara naku ko ku barshi haka
is not my own business.....
Ya suri briefcase dinsa ya fice,da kanshi yau zaiyi driving kasancewar nasiru baya
nan ya tafi ganin gida ,ya juya kan motar ya danne horn yana jira a bude masa,ta
kalli gilashin mudubin dake gefansa da niyyar gyara zamansa don ganin wanda kebin
bayansa sai yaga wata motan na jira ya fita itama ta fita,ya duba sosai sai ya
hangota zaune hannun ta saman sitiyarin fuskarta tayi fresh cikin safiyar,agogon
dake daure a tsintsiyar hannunta take kallo da alama ta kusa maka rane don sai
yatsina fuskarta take,material ne ajikintan yellow mai adon coffee,ba makeup ko
kadan a fuskarta banda powder data shafawa soft chocolate skin dinta,sai lips balm
data shafawa lips dinta sirara masu taushi,tayi lullubinta na mutunci har saman
ka,ya dan tabe baki ya dauke kai itakam bata san ma yana yi ba,duk da ta ganshin
Ayimin afuwa kasancewar yau ina da uziri irin wanda ke kama ko wanne irin dan adam
na turo muku shi late kuma ba yawa amma zamu hadu insha Allah,ina godiya a gareku👏
🏻👏🏻
Mrs muhammad ce
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 12:42 PM] Salma:
*wa yasan gobe?......*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

3⃣7⃣~3⃣8⃣
3⃣7⃣3⃣8⃣
Fisgar motar yayi ya ficee daga gidan sannu sannu take binsa a baya har suka bar
cikin layin suka hau babban titi,yana hangota ta qarawa motar gudu tayi over taking
nasa ta wuce shi ba tara da ta dubi koda sashen sa ba,ya daga idanunsa yabi motar
da kallo yana dan gyada kai cike da mamaki da jin izza shi zata nuna wa iyawa da
qwarewar sarrafa mota?,yaushe ma ta fara kama sitiyarin
Wani girman kai ne ya kamashi,ya qarawa motar shi speed cike da qwarewa da gwaninta
shima ya mata over taking,ta lura sarai da shi amma sai ka rantse da Allah batasan
da wanzuwarsa akan titin ba,ta dan cije lebenta sannan ta dan daki saman
sitiyarinta cikin zuciyarta tana dariyar mugunta,sai da ta barshi ya sakankance
sosai ta take motar ta qara maya gudu sai ji yayi fit ta wuceshi ,cikin zafin nama
da mazantaka ya qara wa tashi shima wutar don ya nuna mata bata isa ba saidai kafin
ya qaraso har ta qaraso kwanar freedom ta sanya signal ta shige,ta morrow din gaba
suka hada ido yana wucewa amma sai ya wuni mugun dauke kai kamar ma bata sanshi ba
Ya girgiza kai ya miqe kasancewar b.u.k zai shiga hanyar ta rabu cikin zuciyarsa
yana fadin"zan koya miki hankaline kin maida ni abokin wasanki kenan
Qarfe biyu ya baro b.u.k din bayan ya kammala abinda ya kaishi,kai tsaye ya tashi
motarsa ya bar makarantar,biyu da rabi ya iso freedom hakanan bai taba zuwanta ba
koda hira suke son yi da shi yana basu appointment ne,ahankali ya gangara layin ya
qaraso bakin gidan radio din ya yiwa mai tsaron bakin qofa horn ua taso don yaji me
ke tafe da shi,da ganinsa ya fara fara'a cikin mutunci suka gaisa ba tare da jiran
komai ba ya bude masa qofa yana jira ya shiga,da hannu aliyu yayi kiransa ya qaraso
saitin window ya ranqwafo yana saurarensa,"wata sabuwar ma'aikaciyar ku nake nema
ina fata bata fita ba"cikin tunani yake kalleshi,aliyu ya gyada masa kai da son
tabbatar masa,sai kuma yadan saki murmushi yace "oh ko haj fadila?"aliyu ya gayada
kai yace"yes itace"😃 tana nan ciki kuwa bata fita ba mutuniyar arziqi kuwa ranka
ya dade.....ko kira maka ita za'ayi"aliyu ya dakatar da shi"✋🏻a'ah barshi zan dan
jirata ba matsala"ya tada motar ya shiga security suka nuna masa gun parking"ya
daidaita motar qasan bishiyun dake gun ya kasheta,ya miqar da sit din nasa ya
kwantar da shi yadda zai masa dadin kwanciya,yayi sama gaba daya da glass din motar
kasan cewarsu akwai (tinting)jikinsu,yasa hannu ya qaro qarfin a.c dake jikin motar
ta gauraye masa ko ina ya kashe dukkanin wayoyinsa ya watsa su sit din gefansa,ya
maida bayansa ya kwantar jikin kujerar yana fuskantar ginn gidan idanunsa akan
reception,lokaci lokaci kuma yana bude mujalla yana dubawa
Zaman minti ashirin yayi ya ganta ta fito gefanta wata yar matashiyar ce sabe da
baby girl a kafadarta ,ita tayi hanyar waje ita kuma ta nufi inda tayi parking tasa
maqullinta ta bude motar tashiga,ya miqe ya gyara zaman kujerarsa ya jawo belt ya
daura,ya kunna motar ya biyo bayanta sanda take ficewa daga ginin gidan radiyon
Ko kusa fadila bata lura da shi ba don bata kawowa ranta ba,cikin kwanciyar hankali
take tuqinta,wani mahaukacin horn taji ana mata kafin ta ankara motar ta zo daf da
ita tana shirin gogarta a gigice tayi gefe da motar tana ci gaba da kallon motar da
ta kasa tantance waye a ciki?,kafin ta gama wannan tunanin har ya dawo daya side
din data koma ya sake matsowa daf da ita yana shirin gogarta,sai ta tsorata 😳
kasancewar titin da ta biyo ba mai yalwar jama'a bane bugu da qari kuma rana ce
babu gilmawar mutane sosai a gun
Cikin lokaci qanqani ya gama rudata gaba daya ta tsorata dama da hugunta ya dinga
komawa,tuni lissafinta ya qwacr tama manta sitiyarin na hannunta ne,sai ta taji
motar ta soma yawo da ita saman titi idanun aliyu na kan motar,ya zubawa motar ido
ganin ta soma yawo bisa kwalta a hankali yana nazari,ya saki ajiuat zuciya sanda
yaga ta daidaita ta daina tangal tangal din da takeyi,ya qaraso saitin window dinta
sai ya sauke glass ta juyo idanunta cike da taf da tsoro suka hada idanu,ya dauke
kansa ya qarawa motar speed yayi wucewarsa,wani abu ya daki zuciyarta sai ta kasa
tuqin,ta sauka a hankali ta gangara gefan kwalta ta kashe motar ta jingina da
makarin motar idanunta a runtse😣zuciyarta na ci gaba da bugawa,sai hawaye ya biyo
rufaffun idanunta ta saki kuka silently,sai da taji don kanta ta samu nutsuwa
sannan ta kunna moyar taci gaba da tafiya slowly a gefan titi don gaskiya ya dauki
haqqinta
Tana isa parking space taga motar tayi tsammani ya shge cikin gidan saidai tana
gama kulle motar ta ganshi tsaye jikin motar yana amsa waya,idanunsa suka shiga
cikin nata wadanda suka dan kafa alamar tayi kuka takaici yasa ta sakar masa
harara🙄 hadi da murguda masa baki😙ta shige jin alamun taku tayi ana bin
bayanta,tana juyawa taga kuwa shi din ne,tasan mai yasa ya biyota cikin azama ta
qarasa shigewa bangaren nata daidai lokacin da yakai hannunsa zai fincikota,tayi
saurin sanya maqulli ta qulle qofar hadi da jingina a jiki,tana kallonsa ya juya ya
koma" kawai"ta fada a hankali
Zaune take tana kallon wani Indian film hum dil de chuke sanam tana ganin son maso
wani tamkar nata da aliyu,ta bada hankalinta kacokam bisa t.v din sai tsintat
qamshinsa tayi yana yawo bisa hancinta,ta dago da sauri yana tsaye bisa kanta
hannunsa harde a qirjinsa shima idanunsa na kan t.v din sai a lokacin ta tuna da
abinda ta masa dazu da hanzari ta miqe ta jawo hijabinta ta zira tana neman guduwa
sai alokacin ya dawo da idonsa kanta fuskarsa a dinke tsaf,da baya da baya ta soma
tafiya yana binta har ta dangane fa qofar bedroom dinta ta fafa ciki tana shirin
danno qofar,yasa hannu ya kare ta,yaci gana da binta sai da ta dangane da sif dinta
,qwalla ta cika idanunta idonta tuni ya raina fata,girgiza kanta ta soma yi tana
cewa cikin tawar murya"donA....Allahh kay......yi...yih.....haquri...."yasa
yatsansa ya dalle mata baki,taji zafi sosai ta sanya hannunta ta dafe bakin🙊,ya zare
mata ido sosai yace"wa kika harara? Ni sa'anki ne?kin raina ni ko?,still tafin
hannunta na dafe da bakinta ta girgiza kai tuni hawaye ya balle mata😭,ya saka
hannunsa ya kama gashinta💆🏼 da ta tufke cikin hijabin har sai da tace "wayyo Allah
na!......,hadi da wani dan guntun hawaye da ya silmiyo mata,ya saketa yana sake
matsota har tana jin hucin numfashinsa,ta runtse idonta gam tana jiran jin hukunci
na gaba,ta yarda aliyyun mugu ne,tasan yau Allah ne kawai zai qwaceta
Shirun da taji yayi yawa ya sata bude idonta,ba kowa a dakin hasalima an ja mata
qofar dakin sai ita kadai dake tsaye jikinya na kakkarwa,ta sake sakin kukan ta
kifa kan gadonta
⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin kwanakin gaba daya ya gama tsanar bangaren nasa,bedroom sin da suke cikin
corridor din wadanda bai amfani da su duk sai da ya budesu yayi amfani da su ,duk
da alokacin su su samira suna ganin suna qure adaka gun gyaran amma shi sam bai
masa ba,don ba wani qwarewa sukayi ba kamar na fadilan,yakan daure ne kawai ya nuna
yabawarsa,ya tabbatar wa ransa nata yafi wannan kimtsuwa
Kowanne dan adam wani lokacin kakan tsinci kanka cikin rashin jin dadin rai hakanan
to haka yau aliyu ya tashi,alhamis ce wadda aka wuni garin lullube da hadari da
iska mai cike da qamshin qasa,mutane da yawa yanayin yayi musu amma banda shi,biyar
saura yama yi dawowarsa gida,yayi cilli da jakar tasa a falo,gidan dai na nan a
yanayinsa na kullum wato shiru,toilet ya shiga ya watsa ruwa ya fitar jallabiya mai
sulbi irin ta maza milk colour mai dogon hannu ya saka,ya feshe jikinsa da shamsul
imarat ya hada da turaren chastity ya dawo parlour ya fitar da computer dinsa ta
tafi da gidanka(laptop)ya jona mata chargy ya jawota har kan kujerar da zai zauna
ya dora ta a saman kujerar,ya daddanata ya bude bayan komai ya gama daidaituwa ya
soma aikin da ya dawo da shi
Munti biyar goma sha biyar sai aikinbya soma gagararshi saboda yunwa,ya dafe kansa
da hannu daya yasa dayan ya lallatsa comouter din ya kasheta,ya zubawa fridge dinsa
ido yana nazarin me zaici a ciki?komai dai na nau'in ciye ciye akwai aciki🍏🍎🍐🍊🍋🍌🍉🍇
🍓🍈🍒🍑🍍🍅🍆🌶🍠🍤🍟🍔🌭🍕🌮🌯🍕🍘🍦🍧🍨🍺🍷🍾
Saidai gaba daya sun gundireshi babu abinda yagi buqata sai abinci mai nauyi da
gishiri,gaba daya taste din girkinsu salima bai gamsar da shi bare yasa su dafa
masa wani abun,koda ranar gikinsu ne yana yin kawaici ne kawai yaci don kada suga
rashin kyautawarsa
A nutse ya isa gaban freezer din ya bude yana sake kallonta kamar baisan meye da
meye a ciki ba,hannunsa yakai kan madarar fresh yo da tayi sanyi sosai tanata fidda
tsatstsafar sanyi yasa daya hannun ya maida murfin freezer din ya rufe,ya maida
kallonsa kan robà dake riqe a hannunsa yana jujjuyata tamkar mai karanta rubutun
dake jikinta
Ya saki tsaki hadi da cillar da robar kana yayi tattakì ya isa bakin window dinsa
yajanye labulayen jiki gefe daya ya dora idonsa a harabar gidan,idanunsa suka sake
kaiwa kan bangaren nata a karo na barkatai,tarwai yake da haske alamun tana nan,ji
yayi yà gaji baAi iya jutewa ba sole ne yazo tayi masa aikin da tasabar masa idan
yaci gaba da jurewar yana jin qila yunwa da tsantsami na iya illatashi,ya juya ya
zira slipper dinsa ya fito....
3⃣9⃣~4⃣0⃣
3⃣9⃣4⃣0⃣
Ya juyabya zira slippers dinsa ya fito Gaba daya tana ma gida babu inda ta fita
saboda ba ba abinda zatayi a gidan radiyon shi yasa bata shiga ba,zamanta tayi ta
dinga bacci abunta sallar azahar kawai ta tashi tayi ta dan sha yoghurt ta koma
baccinta
Qarfe hudu da rabi ta farka tayi wanka,tq gabatar da sallar la'asar din da ake
binta,riga da skert ta saka hade da mayafinsu sannan tayi kitchen da azama saboda
wata hadaddiyar yunwa dake sakadarta
A tsaitsaye ta hada jallop din taliya da tasha kifi ta watsa mata carrot piece da
grean beans,da zaman jiran dahuwar abincin da zata yi sai taga gwara ta hada
lemo,cikin lokaci kadan ta hada lemon kwakwa da yasha madara ta bude freezer din
kitchen din ta sanya ta a ciki,bayan ta kammala ta juye a plate ta kalli plate din
tana murmushi hadi ya tsina fuska don ita kanta tasan ba iya cinyeta zata yi ba ta
mata yawa"let me try"ta fada tana gyada kai ta hado da lemonta dake cikin jug din
ta taho dashi parlour ta zabi kujerar da zata zauna akai don haka ta jawo centre
table ta dora su a samansa
Ta juya ta koma daki don daukar wayarta ta tashi ne ta tarar da missed call din
fauziyya colleague dinta ta barshi da niyyar idan ta gama abinda take ta kirata
Ya kama handle din ya murda hadi da tura qofar ta bude ya shiga,qamshin freshner
din parlour hadi da qamshin jallop din ya dunqule ya daki hancinsa wanda hakan ya
sake haddasa masa yunqurowar wata matsananciyar yunwa,idanunsa suka kai kan plate
din dake dauke da jallop din😋dake ta tururi da qamshi,
Fadila ta fito hannunta dauke da wayar tana duba missed calls din data tarar ciki
harda na rumasa'u da farida,,sam bata lura da shi ba agun sai da yayi gyaran
murya,adan furgice ta dago don bata zaceshi ba,a dinke fuskarsa take kamar kullum
ya cillo mata muqullai suka sauka a kusa da qafafunta,yayi gefe da kansa sannan
cike da ginshira yace"ki gyara min bangarena sannan ki sama min abinda zanci yanzun
nan tunda sai an koya muku abinda ya dace" ya nemi kujera ya zauna hadi da jawo
wani dan qaramin table din na glass ya miqe qafarsa akai
Kamar jira yake ta fita din ya jawo abincin gabansa,ya dauki cokali mai yatsu yana
jujjuyata yana qare mata kallo,a zahiri shi taliya bata dameshi ba don haka ya ture
plate din gefe sai kuma qamshin ya addabeshi don haka dole ya jawo yakai loma daya
bakinsa
Ya miqe a kan three sitter🛋saboda yanaji har cikin zuciyarsa yanayin qamshi da
tsaftar falon sunyi.masa,idanunsa a lumshe yana tunane tunane har aka fara kiraye
kirayen sallar magariba sannan ya miqe ya bar sashen,kafin ya qarasa nasa suka ci
karo da samirah na shigowa da motarta,ya tsaya qam yana dakon qarasowarta hannunsa
zube cikin aljihun wandonsa,tunda ta hangoshi tace da qawarta sa suka shigo tare
"na shiga uku kubra mai gidan nan ya dawo"kubra da hankalinta ke kan waya ta ja
tsaki tace"mtswee to sai me?ni wlh samira mamaki kike bani tunda.kika yi auren nan
duk kin canza komai adarare duba fa dazu da zamu fita fitted gown fa kawai nace ki
saka amma kika qi bayan kinsan gun manyan mutane zamu ji,tsoron mutumin nan kike ji
kamar wani Allahn ki ke yadda ma kike tsoronsa baki tsoron Allahn naki ma,nidai
gwara ma dai yau naga wanne dan mulkin nan ne wannan da.kike masa biyayya haka
kamar shi ya tsuguna ya haifoki
Cike da gadara da rashin kunya kubra ta fito yayin da samira keta.rabe rabe don
kuwa riga da skert ne a jikinta na shadda kana kallon shaddar kasan an kashe mata
naira mai tsada ce saidai anci mutuncinta ta wajen kacalcalata da yi mata
matsatstsen dinki,ga mayafin jiki ta sai kace wadda aka yiwa gorin lullubi
Kallo daya ya yiwa kubra da ta tsareshi da ido duk wata rashin.kunya da ta fito da
ita tayi nata gun,hakanan aliyu yake Allah ya bashi baiwar kwarjini masifa,ta sake
kallonsa karo na biyu"wow"ta fadi a hankali don gaba daya ya tafi da tunaninta,sai
ta mance mission din ta fito da shi,ta zuba masa ido gaba daya,sai a lokacin idonsa
ya kai kanta bayan ya dauke kansa daga samira,takaici ya kama Aliyu ganin irin
kallon qurillar da take masa ya sake dinke fuska tamau,sai lokacin ta kula da ta
bada kanta fa ashe,
Ta dauke kai cike da duniyanci da niyyar bin bayan samira dake ta zuba sauri jiki
na rawa,tsawa ya daka mata😠 hadi da nuna mata qofar get sannan yace"get out of my
house idiot kada na kuma ganin wadannan lalatattun qafa fun naki a
gidana"murmushi ma ta saki ta juya ta fice cikin karairaya wai ko zata janyo
hankalinsa, bata san wani takaicin ne ya sake qumeshi ba yaja wani dogon tsaki ya
juya ya nufi sashen samira
Mrs muhammad👑
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
3:37 pm 8/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣1⃣~4⃣2⃣
4⃣1⃣4⃣2⃣
Kubra ta tsaya a bakin get din tana jinjina kai ita daya take sumbatu"kut lallai
yarinyarnan dole ta matowa gayen nan shi yasa take ta faman rawar qafa?ai kuwa wlh
baza'ayi bani ba"tayi qwafa sannan ta ja qafa tayi gaba,
samira ta kasa zaune ta kasa tsaye tasan halinshi sarai yarjejeniya kuma suka qulla
tun kan aurensu kan shi baison wadannan kwashen qawayen nata gashi yau ta saba
yarjejeniyar,tana shirin guduwa dakin gadonta ya damqota ya maidata kan kujera,ya
kalleta sosai sannan ya jefo mata tambaya"ina kika samo waccar shedaniyar?"ta dake
duk da tsoro ne fal cikin idanunta tace"qawata ce fa"ya gane mai takeson yi
duniyancin nata data saba don haka ya shirya nuna mata nasa salon,don haka sai ya
saketa daga riqon da yayi mata,ya saki fuskarsa ya daga kafadarsa hadi da watsa
hannayensa na nuna alamun rashin damuwa da abu kana yace"good....verry good tunda
qawarki ce kinga abun zai zo min da sauqi kenan ko?,dama gani nayi tamun inason
aurenta aikinga zaman naku zai miki dadi tunda kun fuskanci juna, bata san sanda
tayi zumbur ta miqe ba tana zazzare idanu ba baki na rawa tace"iyi...mme...me
kace"ya daga mata gira sannan yace"abinda kunnen ki suka ji shi nace"ya juya yana
niyyar barin dakin,hankalinta a tashe ta riqoshi kasancewar tasan halinshi *fada da
cikawa*ya dubeta fuska a turbune yace"meye haka"don Allah ka rufamin asiri wlh
bazan qara ba kasan wace kubra kuwa?"ya sake dage kafada hadi da cewa"ni ina ruwana
da koma wace ce tunda kin kawo min ita har gida ni kuma na gani kuma ta yimin"ya
zare hannunsa yayi ficewarsa,yana jiyo kururuwarta sai ya tuna haukan da tayi masa
sanda zai dawo da salima,murmushi🙂 ya subuce masa ba tare da yayi niyya ba,yasan
cewa shikenan yayi abinda zai rabasu kenan har abada ba tare da ya wahal da bakinsa
ba,(samira irin mai rawar kan tara qawayace ko wa qawarta ce kare da doki ga son
birga da burgesu ita dole sai an san mijinta wani ne,kaya komai tsadarsa suka gani
a gunta tofa take zata basu ko nawa aka siya musu ko na aliyyun ne kuwa,indai zata
burge tofa magana ta qare,gata da saurin daukar maganarsu don yadda take jin
zancansu nata jin na mahifanta haka ne yayi silar lalacewarta,wannan ne yasa aliyu
ya rabata da kowacce qawa amma da yake akwaita da kafiya taurin kai da naci sai ta
sake wasu sababbi wadanda aliyyun bai sansu ba)
Kai tsaye ya wuce sashen sa tun daga falin ya ga canji komai fes ya koma
hayyacinsa,daddadan qamshin girki ya cika falon nasa,bedroom ya zarce ya daura
alwala ya nufi masallaci,kan ta kammala aikin ta gama gajiya tubus don kuwa aikine
ya gama taruwa ya cakude ita kanta wani gun cike da qyanqyami ta daure ta gyarashi
to ina kuma ga aliyyu
Take tasha alwashin zata yiwa tufkar hanci don badaqalar data tarar a bedroom din
tasa ta isa,tuni ta gane cewa fushinta bashi da amfani don yadda komai ya qazance
ta sani cewa da duniya zata gani ba iya su samira kawai za'a zaga ba harda ita,don
ba wanda yasan mekw gudana tsakaninsu,ta sake gayawa zuciyarta lallai ibada tazo yi
ibada kuma mai wahala wadda itace tafarkin shiga aljannarta kuma ta dade da sani
aljanna bata samuwa daga zaune ba tare da ka tashi kayi aiki tuquru ba kuma dole ka
ninka haqurinka(wannan sune daya daga cikin lafuzan umminsu garesu ko yaushe,uwa ta
gari kenan)
Aliyu bai shigo ba har sai da yayi sallar isha'i don haka tuni ta gama komai har ta
jere a dining taje tayi wankanta ta shirya tsaf cikin dark blue din shadda doguwar
riga wadda aka mata surfani mai kyau tun daga sama har qasanta ,hankalinta dai na
kan taliyarta don haka ta nufi table din saidai wayam don ko plate din babu,ta juya
ta shiga kitchen acan ma a bude ta tadda tukunyar wayam
Ta san babu wanda ya cinye abincin sai shi don ba wanda ya shigo din,wata dariya😂
ta subuce mata data tuno yadda ya shigo dazun rai a hade yayi wani kicin kicin da
shi😠 ashe harda yunwa itama ta taimaka wajen dinkewar fuskar tasa,ta hade
kwanunkan ta dauraye ta maida su muhallinsu cikin ranta tana cewa"babu rabona nasha
ice cream🍧
Tana bisa carfet ta bude babbar robar ice cream din tana diba a hankali tana kaiwa
bakinta lumshe ido take don babu abinda take jin dadin shansa kamarshi din,wayarta
ta duba jin qarar shigowar text _kizo ki bawa mutane abinci_"haka taga an saka,ta
duba sunan Aliyyu salim maitama kamar yadda yayi mata serving din ta ranar da bata
da lafiya"ta miqe hadi da dauke ragowar ice cream din ta maida cikin fridge ta koma
daki ta fesa turarenta na blue lady ta hada da asaal brush perform ta nade kanta da
da farin hijabi ta zari wayarta ta fito hadi da kulle gun ta,a hanya suka hadu da
salima ta rako baquwa suna tsaye da alama magana suke ganin fitowarta duk sai
sukayi shiru suka bita da kallo ganin haka yasa tace musu salamu alaikum sanda zata
giftasun,baquwarce kawai ta iya amsawa itama can xiki kamar wadda akayiwa dole,suka
ci gaba da kallon nata har ta shige bangaran aliyun
sai a sannan suka dauke idonsu baquwar ta saki ajiyar zuciya tace "tab gaskiya
salima tahir na janjanta miki don wannan kam banga ta inda zaki ci nasara akanta
ba,saidai ban sani ba ko ta bangaren farar fata"salila ta kai mata duka hadi da
cewa"banason iskanci sadiya kota farar fatar ai sai na yi yaqi da itan ,dadin abun
ma miskilancin mai gidan bai bari ki gane wa yafi so cikinku ai da tuni inaga na
dade da kamuwa da ciwo yanda nake bala'in a son my dear💘 "ta fadi tana dafe
qirjinta"(abunda bata sani ba aliyyun irin mazan nan ne wadanda ke nunawa mace
qauna wadda kan bawa mutane mamaki har adinga zaton kunya ce basu da ita ko
mallakesu akai sunyi sake da damar da ya basu tun farko har ta subuce musu)sadiya
ta dafa kafadarta tace"to Allah ya bada sa'a don ko nice a matsayinki gaskiya
bazanyi wasa da aliyyu ba"salima ta juya ido tace "ashe kin fara gano gaskiyata🙄 "
Mrs muhammad ce
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:42 PM] Salma:
*wa yasan gobe?....*

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

4⃣3⃣~4⃣4⃣
4⃣3⃣4⃣4⃣
😳
''
| |
/ \
 
Ku tayani duba jama'a na taho da sauri na ina neman littafina na *wa yasan gobe*zan
muku typing na nemeshi na rasa
😜😜😜😜😜😜😂
Just for fun ga wadanda suka ji haushina
*PART 2*
🌺
1⃣2⃣ 1⃣~2⃣
Sadiya ta dafa kadar salima tace to Allah ya bada sa'a don ko nice a matsayinki
gaskiya bazanyi wasa da aliyyu ba"salima ta juya ido tace ashe dai kin fara gano
gaskiya ta🙄"
Sanda ta shiga yana zaune gaban na'urar tafi da gidanka yana qarasa aikin sa da
dazun yunwa ta hana shi yi,sallama tayi ya amsa kansa na kan allon computer
din,kujerar dake gefansa ta samu ta zauna,kusan mintina sama da ashirin bai ce mata
kanzil ba don haka itama ta bude wayarta ta soma register din watsapp saboda yanzu
as journalists tana buqatar wadannan kafofin sadarwar,
duk da basu dameta ba don ba yadda farida batayi da ita tun a gida ta bude koda
watsapp ne kawai ba amma taqi tafi ganewa karance karancen magazines da wasu rubuce
rubucen
Cikin yan mintoci qalilan ta kammala da account dinta na watsapp ta soma qoqarin
hada na facebook,falon yayi tsit kowa ya sanya na'ura a gaba,lokaci lokaci takan
daga ido ta saci kallonsa,qayatacciyyar fuskarsa da hasken screen ya sake hasketa
tayi fresh,ta zubawa hannayensa ido yadda yake sarrafa computer din cikin qwarewa
da da gwanancewa typing yake cikin sauri tamkar shi ya qera computer din yasan
madannin kowanne abu abun sai ya burgeta sosai
Wayarsa ta soma ringing ya dauke kai daga kallon fuskar computer din ya maidaa
idonsa kan wayar ba tare da ya daga ba,baquwar numbace kuma bai dagawa,kira aka ci
gabaa da yi akai akai har ya gaji ya danna ok ya dora ta bisa computer ya sanya ta
a hands free
Muryar mace ce "hello ranka ya dade" "salamu alaikum wake magana?"ya fada
hannayensa na saman laptop dinsa yana aikinsa,"daga daya bangaren aka sake
maqe.murya"suna na nadiya ina kiranka ne daga unguwar rijiyar zaki kano"bai maida
hankalinsa ba kan wannan yace"me kike nema?"aka danyi jim har yana shirin kashewa
sannan akace "don Allah ka rufawa zuciyata asiri kada ka kashemin waya domin kashe
wayar tamkar kashe ni ne"ya tsayar da abinda yake sannan yace "uhm go on" aka saki
ajiyar zuciya sanna tace "maitama Allah ya jarabceni da tsananin qaunarka wadda
tasa na kasa jure hakan cikin zuciyata har sai bakina ya furta maka,ina roqonka don
Allah ka taimakeni ka so........" "hey!"ya daka.mata tsawa "stop that,rubbish!"tsit
tayi,ya ware idonsa kamar tana gabansa yace"ke baki da ajine irin na mata?" Shiru
ba amsa don haka ya dora "let me tell you baki da shi,and inason gargadinki wannan
ya zama na qarshe da zaki kira numberta,I hope kin fahimta ko"ya katse kiran hadi
da jan tsaki,fadila tayi saurin dauke kanta lokacin da ya dago kansa taga tamkar
ita zai kalla zuciyarta na wani irin bugu,kishi ya tokare mata qirji,ta lumshe ido
bugun zuciyarta na qara sauri.......
*PART 2*
3⃣4⃣ 3⃣~4⃣
Kusan kimanin minti biyar idanun nata na lumshe ta kasa budesu saboda wani abu da
takeji a jikinta wanda tasan baya rasa nasaba da tsan tsar kishi,ta sauke boyayyar
ajiyar zuciya sannan ta bude idonta ta dora su bisa screen din wayarta tana ci gaba
da qoqarin kammala bude account nata na Facebook duk da wani bari na zuciyarta na
ci gaba da mintsininta,cikin zuciya lallai ta godema Allah da bai qaddara ta zubda
ajinta ta bayyana abinda ke zuciyarta ba har ta kai aliyyu ya fuskanta bare ta samu
nata kason cin zarafin kwatankwacin wannan wanda it may break her heart
Tabbas ta sake yarda cewa so masifa ne musamman son da hausawa kema laqabi da son
maso wani,babu irin baiwar da tabbas bata da ita iya kyau Allah ya mallaka mata shi
ilimi hankali da nutsuwa,tasha jin mata yan uwanta da yawa na yaba ta bare tarin
maza dake kara kaina a kanta
Ta sake satar kallon nasa wannan karon maimakon ta tadda shi yana aiki kamar dazun
yanzun takardun na watse ne a gabansa ya jingina kansa harda bayansa a jikin kujera
dukkanin tafin hannunsa ya tallafe bayan kansa da su idanunsa na rufe,gashin idonsa
yayi ma idon rumfa tamkar an jera su
"Bani abinci"ya fada idonsa na a rufen,ta miqe ta shirya masa komai still dai
idanunsa na arufen har ta gama ta koma ta zauna,a hankali ya bude idonsa ya kalli
warmers din"u mean ni zan zuba kenan da kaina?"😒 ta girgiza kai sannan ta taso ta
zuba masa white rice ce da miyan kaza sai hadin coleslaw tana kammalawa ta miqe da
niyyar fita "ina zaki je?"ya tambayeta cikin izza,ta kawar da kanta sannan tace
"sashina zan koma" yaci gaba da cin abincinsa sai da ya mula don kansa sannan yace
"ban baki izini ba"cike da haushi da takaicin irin mulkin da yake mata ta koma da
baya ta zauna kanta a qas
Kamar zata fashe da kuka☹ ta shiga kitchen cikin mintina biyar ta hada masa ta juye
cikin cikin wani set din butar shayi irin na larabawa na silver da cups dinsu yake
hade da tray
Hade da sallama ta shiga dakin yana cikin lallausan bargonsa cikin shirin bacci ba
haske a dakin sai na fitilar gefan gado,yana receiving call har ta shigo ta isa bed
side ta dora plate din daidai lokacin da ya kammala amsa wayar ya kasheta gaba daya
ya cillata bayansa tana tsaye har ya kammala addu'o'in bacci sannan ya juya mata
baya yana gyara kwanciyarsa hadi da jan bargonsa "kina iya tafiya" dama a gundire
take Allah Allah take ta bar masa dakin ta juya ta fice abinta
Tana shiga bedroom dinta nightgown kawai ta sanya ta fada gadonta tana addu'o'in
kadan kadan har ta gama,a hankali ta lumshe idonta tana da muradin yin bacci amma
ina sai tunanin da akullum yake zame mata na qarshe a rayuwarta shi ya lullube
qwaqwalwarta,duk yadda taso bacci yayi awon gaba da ita abun ya faskara har sai da
ta dade tana ninqaya a duniyar qaunar aliyyu haidar sanan baccin yayi awon gaba da
ita bacci ne mai cike da mafarke mafarken aliyyun
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin hukuncin ubangiji rayuwar ke tafiya da bawa wani lokaci ta zo maka uadda kake
so kake tsammaninta wani lokacin kuma ka samu akasin haka yau fari kenan gobe
tsumma jibi nasara gata asara duk cikin hukuncin ubangiji ne da yadda yaso rayuwar
bayinsa ta kasance,to bawa mai cike da tauhidi da imani sai ya godewa masa don
kamar yadda haka yake ga fadila,shekararta guda kenan cikin igiyar auren
aliyyu,shekarar da ta ga abubuwa daban daban ta fuskar qalubale da nasara
Zamu iya cewa babu wani abu da ya sauya dangane da salon mu'amala da alaqa dake
gudana tsakaninta da shi baya ga wadda muka riga muka sani,nasara daya ce zata iya
daga hannu🙋🏻 ta fadeta cike da alfahari shine duk cikin samira ko salima babu wadda
take iya sarrafawa aliyyu girki da tsaftar muhallinsa kamar ita
Abunda suka fi qwarewa ciki sune kowacce ta fito tana tunqaho da hura hancin Aliyyu
yafi sonta akan sauran 'yan uwanta,takan kau da kai cike da yakanah tayi kamar bata
san abinda suke yi ba,wani lokacin kuma sukan bata dariya har ma ta murmusa takan
daukesu ne a matsayin wadanda basu san mai ya kamacesu ba duk da kuwa duk sun bata
wasu shekaru sun kuma girmemata sosai tana ganin tutiya bata kamacesu ba a irin
wannan rayuwa da suke,ta sanu da gayya suke mata wani abun ganin cewa bata taba
daga ido ta kallesu ba bare suyi 'yar tankiya
So suke ta zamo daya daga cikinsu domin kuwa fada tsakaninsu sun koma tamkar
'ya'yam tumaki har bangarenta tana jiyo hayaniyarsu,sukan ji kasiririt ne idan
aliyu yana gida don ko giyar wake suka sha a yanzun basu fada gabansa tun tuni
yayima tufkar hanci ya kuma tauna tsakuwa don aya taji tsoro ta kuma ji din saidai
su yita 'yan habaice habaice wadanda shi da yake namiji me bai ma fuskantar me suke
Ta riga tuntuni ta saddaqar da cewa soyayayyar aliyyu wani gine ne daga Allah cikin
zuciyarta,tayi imani koda bai sonta ba koma zai sota din ba kamar yadda yayi mata
tunqaho Allah bazai taba wofintar da ita darajar biyayyar aure da take hidima a
gareshi da kayutata gami da girmama buqatunsa,duk da babu wani sauqi da take ganowa
a tattare da aliyyun amma har kulluma tana bawa kanta confidence kan hidimar da
take masa especially a duk sanda haduwa ta hadasu da uncle abba momi abbanta ko
umminta taga yadda suke nuna jin dadinsu har yau da wannan aure nata sai taga zata
iya ci gaba da faranta ransu indai hakane
Saidai abinda bata sani ba shi kansa yakan samu kansa cikin nutsuwa a duk ranakun
da suka zamo nata ne ko banza ya san yana sakewa yaci abincinsa cikin nutsuwa da
kwanciyar hankali kuma cike da gamsashshen dan dano irin wanda yake so duk da babu
ruwanshi da ita,some times ma kafin ya dawo ta hada duka abinda yake so ta bar masa
bangaren,mutum ne aliyyu maciyin abinci bao wasa da cikinsa ko kadan hakanan
halittarsa take,duk qwaqwar mutum bai isa yayi indication wasu sign da zai nuna
yana jin dadin hidimarta ba
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
[8/25, 3:45 PM] +234 812 673 9684: 5:08 pm 20/08/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 2*
5⃣6⃣ 5⃣~6⃣
Cikin watannin da basu gaza biyar zuwa shida ba fadila ta samu gagarumar nasara
ta bangaren aikinta,nasarar da bata taba tsammanin zata sameta in a few months
ba,ta soma aikine cikin sa'a,farin jini sosai take da shi,sunanta ya fara fantsama
cikin al'umma shirye shiryenta sun samu karbuwa matuqa da gaske,ki ina ka zaga
zancan matashiyar 'yar jarida fadila Abbas wakili ake,ita kanta tana mamaki with
her few age ta samu daukaka haka,saidai da yake mai hankali ce takan godewa Allah
domin tasan babu wanda ya isa yayi mata haka sai Allah,hakan yasa ta sake daura
damarar riqo da aikinta cikin qwazo amana da kuma gaskiya da kuma manufa kyakkyawa
da zata kawo gyara da ci gaban al'ummarta,bata mantawa da ya ahmad da abbanta
wadanda su suka jagoranci samuwar ci gaban nata
Bayan ta kammala duk wasu ayyukanta kamar yadda ta saba,ta shirya masa komai
hatta da tissue bata barta ba,sauri take ta yi ta fice daga gun kafin dawowar
tasa,saidai kash bata ci nasarar hakan ba don kuwa a bakin qofa suka yi kacibus
kadan ne ya rage basu bige juna ba,da sauri taja da baya tana shaqar numfashin ta
dake gudu sakamakon tsoratar da tayi,qasa tayi da kanta tana murza tafin hannunta
gami da cewa "sannu da zuwa"
Kusan minti biyu taji shiru shi bai wuce ba ba kuma alamun juyawa yayi,ita kuma ya
bashi dama ne ya fara wucewa duk da sauri da take ta koma bagarenta ta cire pad din
jikinta ta sauya wata,ta dago kanta don taga me yakeyi ne haka yana tsaye
hankalinsa kwance kamar bai tsarawa kowa hanya ba don bashi da wani alamu na
matsawa hasalima tie dinsa da coart yake cirewa a nutse
Ganin haka yasa ta raba gefansa don ta shige ashe bata sani ba ya sanya mata
qafarsa dake saye cikin sau ciki👞sam bata lura ba don hankalinta yayi gaba,luuu
tayi baya ya goce sai kuwa ta bugu da qofan falon ,cikin azabar radadi ta dafe gun
ta dago a hankali ta kalleshi sai taga tamkar ma baisan mai yayi ba agogon hannunsa
na gucci yake cirewa,malolon takaici ya kama mata maqogaro tuni kuka ya kufce mata
tasa kai tanashirin bar masa gun tana dafe da goshinta
Ji tayi ya jawota baya ta dawo tayi kamar zata sake faduwa Allah ya taimaketa ta
tsaya da qafafunta bayan taga tagar da tayi "sama fa qasa ya kalleta sannan yace
"😠baki da kunya ko?,ni zaki buge ki wuce kenan?"tafin hannunta tasa ta kate
fuskarta tana ci gaba fa kukanta shi kuwa ya zuba mata ido ba tare da ya sake cewa
komai ba, sai da ya gama ikon nasa don kansa ya kauce tare da wucewa ya bar gurin
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Su biyar ne zaune cikin office din fadilan sai fauziyya fa'iza aisha da halima
dukkaninsu abokan aikinta ne matasa ne son saidai duk sun girmemata aqalla zasu
bata shekaru uku zuwa hudu,amma nutsuwa da kaifin hankalin fadila yasa ta saje
cikinsu suna jin dadin zama da ita sosai duk da miskilace saidai akwai karamci da
mutunta mutum
Hira suke gaman da zamantakewar aure irin hirarmi dai mata da aka sani wadda
matuqar mayan aure suka wuce biyu aka hadu sai an yita,hira ce ta qaruwa ba banzar
hira ba wadda bata kamata ba,duk da haka fadila na gefe don bata da abun fadan
saidai jifa jifa takan ce wani abu
Hira tayi nisa fa'iza ke basu labarin wata maqociyar yayarta 'yaf nijar dake saida
magungunan mata masu kyau na gargajiya wadanda basu cutarwa,dukkansu suka ce ayi
kiran matar suna so fadila kawai ta rage,fa'iza ta kalleta"ke ba ki siya fadila wlh
maau kyau ne"murmushi tayi tana neman qaryar da zata gilla musu,don ko ta siya me
zata yi da su,ta kalli fa'iza "to a hado da ni ga nawa kudin"ta nude zif din
jakarta ta fito da kudin,fa'izan ta kuma cewa idan ma bakiso akwai wani hadin
tutare mai tada sha'awar mai gida sai a kawo miki shi"cikin basarwa fadila tace"a
hadomin duka kawai"(kaji fa mai karatu kamar gasken tana da buqatarsun 😜😜)
Take fa'iza ta kirata ta sanar mata,ta kaahe wayar tana dubansu tace kun taki sa'a
don gata nan ma anan kusa don tana ja'en,cikin minti talatin sai gata kowacce ta
karbi nata ta sanya ajaka
Qarfe biyar ta soma hada kayayyakinta tana sallama da su zata wuce gida don ta
kammala aikinta ,wayarta dake aljihun bayan jakarta ta dauki qara alamun ana
nemanta *sister ta* ta gani bisa screen din hakan na nufin farida ke kiranta,da
sauri ta daga hadi da yin sallama,"sister ki taho kiga baby girl mai kama da ke
kamar copy naki akayi na haihu yanzu haka ina gida"wani tsalle fadila tayi hadi da
qaramin ihun farinciki sam ta mance a office take ba a gida ba sai da taga su
fauziyya sun taso suna tambayarta mai ya faru sannan ta tuna ta maida wayar tana
dariya cikin doki tace junior sister na ce ta haihu wlh"suka mata barka hade da
dariya suna cewa saura ke kenan,murmushi 😊kawai ta musu ta saba jakarta tana
cewa"Allah ya bamu alkhairi"ta kama kumatun yarinyar fauziyya tana mata wasa har ta
fice yarinyar nata kuwa bangala mata dariya don fadila akwai son yara yarinyar ta
soma sabo da ita yauma sa'a akaci bata sa kuka ba da zata tafin
Da dokinta ta shiga motarta da niyyar wucewa gidan farida kai tsaye,har ta kunna
motar ta tuna cewa sai fa ta sanar da aliyyu,take
murnarta ta ragu tamkar an zare mata laka ta kashe motar,ta jawo hand bag dinya
dake kusa da ita ta ciro wayarta ta bude sannan soma searching number'n sa cikin
contact dinta wadda yayi mata serving da kansa ranar da bata da lafiya,tayi
attempting din kiransa yafi sau goma ta kasa,sai ta fara dialing sai ta katse da
kanta,bata san answer da kuma result da zata samu ba
Daga qarshe taga hakan bazaiyi mata amfani ba sai kawai tayi shahada ta kira
din,yadda wayar ke qara yin din din haka zuciyarta ke bugu,idanunta a rufe gam tana
jiran wayar....
Mrs muhammad dinku ce👑👑👑
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*PART 2*
7⃣~~8⃣
7⃣8⃣
Tana daf da tsinkewa ya daga wannan karon ita ta fara yin sallamar ,yayi dan dum
sannan ya masa a daqile sanan ya dora da "who's on d line?"cikin in ina ta soma
magana don gaba daya dakiyarsa ta rudata "nice" "kewa"ya maida mata da
tambaya,"fad...fadila"ya sake shiru na yan sakanni har tana tsammanin ko baya kan
layi ta duba wayar sai ta ga yana nan
"What's going on?"ya sake tambaya,wani abu ya dan taba ranta da gaske bai ganeta ba
har sai da yayi analysing a qwaqwalwarsa,"sister farida ce ta haihu" "uhm labari
kike ban kenan?"ya fadi cikin watsar da muhimmancin batun a gunta,tambayar ta
quleta hakan yasa tayi shiru,"me kike buqata ne ina fa da aikin yi"ta daure tace
"baby nake son inje na gani" "ban amince ba"ya fadi kansa tsaye,din din ya katse
wayar,wani hawayen takaici ne ya sulmiyo mata,tayi wurgi da wayar kujerar
gefenta,cikin takaici ta figi motar sai gida
Danja na tsaida su tana ganin wani wani saurayi dake gefan tata motar yadda ya zuba
mata ido da alama yana mamakin me ya sanyata kuka ne,ta kawar da kanta gefe cikin
zuciyarta tana ayyana in banda babu kyau fita babu izini tabbas da sai tayi
wucewarta gidan farida saidai aliyyu yayi tsirenta,ta share hawayen sanda danja ta
sake su ta sake figar motar,tana kallon yadda saurayin ke sa mata signa yana son
tsaidata tayi banza da shi ta qarawa motarta speed,ita kanta bata san tayi gudu
haka ba sai da ta iso gida agogon wayarta ya harba taga yan taqitattun mintocin da
suka kawo ta gida,tana qoqarin shiga gidanne bayan mai jire bakin qaton get din
gidan ya dage mata qofa ta soma shiga taji wani horn din,ta glass ta hangota motar
samira ce wadda take cin ubanta da hawa ta tabbatar da motar mutum ce da tuni ta
dade da guduwa,ba samiran ba hatta qawayenta sai suzo su ari motar su wuni sur suna
cin ubanta ko a daddoke mata ita su kuma dawo su yasar mata ita ce mai kudin banza
ta gyaro ta zuba musu mai gobe su dawo su sake ara ita kuma ba lissafi ta basu
saboda tsabar neman suna irin na samira,shi uasa tayi nacin aliyyu ya canza mata
mota qememe yayi buris da ita don yana sane da abinda takewa tatan
Mrs muhammad ce
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
12:36 pm 22/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 2*
9⃣1⃣0⃣ 9⃣~~1⃣0⃣
Ta ajjiye motar a parking space ta kashe ta tana mai dauke idanunta daga kansu
samira zuciyarta na tur da irin halayen mutanen da samiran ke mu'amala da
su,hakanan ko yaushe zaka gansu cikin shiga ta banza da rashin da'a,yanzun ma
qawayenta ne su uki ta dauko cikin motar kowacce kuma cikin shigar tasu dai ta
dabi'ar da suka dorama kansu ,tana jin shewarsu sanda take rufe motarta kasancewar
suna bayanta ne tsaye jikin motar samiran su basu shige ba hakanan basu komacikin
cikin motar ba,sun saba yi mata haka tun ba yau ba kula su ne sam bata taba yi ba
don bata kallonsu ma a matsayin cikakkun masu hankali,tana ganin idan ya kula su ma
tamakar ta basu wata martaba da daraja ne,kallon tsiya ma basu isheta ba bare su sa
ran wataran zasu samu na arziqi bare fadilan dama miskilar kanta ce sai ka gama cin
kashinka a gabanta idan bata ga dama ba quda bazata kore maka ba
Kamar ko yaushe yauma har ta bawa banza ajiyarsu tayi gaba abinta maganar da ta
jiyo suna fada ita ta sanyata dawowa da baya ta tabbatar ya zama dole yau ta yiwa
tufkar hanci bare yadda take cikin takaicin hanata zuwa gidan farida da aliyyu yayi
shewa suka yi sanda take yin gaban sannan daya daga cikinsu tace"badi'a (sunan daya
daga cikinsu ta kama)saiki dinga fakewa da fita aiki ana yawo a kwararo
Da baya ta dawo sannan ta fuskancesu,dubansu tayi daya bayan daya up to down ta
saki wata 'yar siririyar dariya tace "😏 ai karuwanci iyawa ne kuma karba karba
ce,💁🏽wata hajar sai ta qaraci zamanta a kasuwa tasha qura tayi futu futu kullum
kuma sai an fito da ita an kasa amma sai kiga ko kallonta al'umma basuyi bare su
baqaci siya,kinga kenan inda wani yayi rawa aka bashi kudi wani idan yaje yayi dan
banzan duka zaici
Ta sake watsa musu kallon raini sannan ta dora"ku ba abokan yina bane don ban hada
sabga da ku ba wannan.....ta nuna samira da key din mota dake hannunta "itace
abokiyar yina,ita din ma zata gaya muku inuwarta bata isheni kallo ba bare
zahirinta,but.... well zan baku shawara guda daya hade da gargadi mai kama da jan
kunne,shawara ta farko itace ku rufawa kanku asiri ku samu ku raba jikinku a dakin
aure kafin a rasa mai kwasar ragowarku......😂 au am sorry na manta yanzun ma fa
hakance ta faru da ku fa shi yasa kuke gararamba da yawon kwadayi da maula agidajen
matan wasu
And gargadina shine kada wadda👉 ta sake bude rubabban bakinta da niyyar shiga
gonata don nikam duk cikinku babu wadda tayi isar da zan shiga gonarta,saboda haka
nima akiyaye shiga tawa gonar👉"ta kama kunnenta daya da hannunta tace"idan kunne
yaji......gangar jiki ta tsira"ta saki hannunta ta juya da niyyar shigewa dukkansu
sunyi mutuwar tsaye don nasu taba tsammanin ta iya magana haka ba a yadda samira ke
basu labarinta,samiran ce tayi yunqurin nuna jarumtarsu tasha gabanta ta kama qugu
tana cewa"ke qaramar 'yar iska mu kike nufin zakiyi wa rashin mutumci?"
Murmushi fadila tayi tace"🤗 a'ah sanin kanki ne fa ni ban iya hayagaga ba ke zaki
fara baiwa wanda bai sani ba labari ,to kuwa akan wadancan👈🏼 shashashan bazan fara
ba"ta gewayeta tayi wucewarta,tana jiyosu suna ci gaba da kuri da cika baki kala
kala akanta har suka wuce sashen samira,cikin ranta take fadi Allah ya bawa daya
daga cikinsu sa'a tace zata biyota taga yadda ake rashin albarka
Wanka tayi don taji sanyin zuciyarta tuni ta watsar da batun su samira don basu
gabanta hasalima bata daukesu wani abu ba don tasan baya ga tsabar jahilci dake
damunsu rashin tarbiyya na bibiyar rayuwarsu,tana mamakin tsarin rayiwa irin tasu
sam basu damuwa da yanayin da rayuwarsu ke gudana,falo ta dawo ta hada yoghurt mai
sanyi da fura ta dama ta koma saman kujera tana diba da cokali a hankali tana sha
zuciyarta sam bata gidan,kira ne na anty hafiza ya soma shigowa wayarta tana neman
farida ne tayi ta kiran wayarta busy shine ta kira ko suna tare ta bawa faridan,nan
da nan ta tabo mata miki basu gama sallama ba ta kashe wayar don bata son taji
kukan da ya qwace mata,kamar kuwa hadin baki yan uwa ke kiranta suna cewa ita zasu
yiwa barka itace uwar 'ya,hakan ya raunana zuciyarta sosai tasha kuka,sister
faridanta guda amma wai a hanata ganin 'yarsu?
Har magariba jikinta amace yake,sai sannan ta tuna bata kira umminta ta mata barka
ba,jin muryar ummin bayan ta daga sai ya karyar mata da zuciya kuka ta saki,a
tsorace ummin tace "meye haka lafiyarki kuwa?"cikin kukan tace "ummi ya hanani zuwa
ya hana ni inje inga baby ummi"ummin ta saki ajiyar zuciya sannan ta ja tsaki"wlh
harkin tayarmin da hankali na zaci wani abune ya faru ko ya sameki?" Ta sake
marairaicewa cikin muryar kuka tace "ummi wani abune mana sister farida fa ummi"
"to sai me idan baki je din ba?,idan kinje ma me zakiyi mata iyakaci kije kuyi ta
surutu,tunda Allah yasa an sauka lpy bashi kenan ba abunda dama ake buqata kenan"ta
sake sakin kuka tace "ummi ki masa magana don Allah idan ba haka ba baza ni ba"kama
haba ummin tayi kamar fadilan na gabanta tace"🤔lallai bansan haryau quruciya na
damunki ba fadila,to ba da ni ba wannan shiriritar,bana som sakarci ki maida
hankalinki fadila kada na soma jin wani abu kuna jina ko?" A sanyaye ta gyada kai
ta sani ummin bazata so ace bata je ba amma bazata taba bata goyon baya ba,halin
ummimsu ne a gidan aure maca ce mai tsananin biyayya ga abbansu ko layi uaja yace
kada ta tsallake to insha Allahu ba zata tsallake din ba hakanan kaf yaran babu
wanda zata bari ya tsallaka hakan ne yasa har yau har gobe har ma jibi inji shi
abban nasu yake alfahari da kuma ji da ita
Ta saki ajiyar zuciya bayan ta kashe wayar tana jan majina hadi da son maida kukan
ta,alwala ta daura tayi sallar magariba ta zauna kan sallayar tana jiran a kira
isha,hakanan fadila take tana da kwadayin wannan garabasa da ake samu ga duk wanda
ya idar da salla bai kuma tashi daga gurin ba,jira ne baifi na awa daya da rabi ba
aka tada isha'i ta gabatar da ita duka harda shafa'i da wutiri sanann ta sake zama
ta karanta subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azim,don kanta ta gaji da zaman
ta ninke abun sallar ta maida shi muhallinsa ta baro dakin sa hijabinta a jiki don
dumin cikin hijabin ya mata dadi
Cartoon ta maida tana kallo kan tashar m.b.c 3,lokaci lokaci tana sakin ajiyar
zuciya saboda kukan da tayi,sannu a ahankali ta soma jiyo qamshinsa ,ta daga
fararen idanunta ta maida su bakin qofar shigowa falon,cikin nutsuwa da sallama ya
shigo yana sanye da jacket black blue sun haska farar fatarsa,sunyi amsarsa matuqa
da gaske adorable structure dinsa ta fito sosai,sassanyan kyawunsa din nan ya
bayyana cikin kamilalliyar tafiyarsa ya qaraso falon hannayensa sarqe a
qirjinsa,can qasan maqoshinta ta amsa sallamar carelessness ya samu hannun daya
daga cikin kujerun ya zauna ba tare da ya dubeta ba
With bounded face yace"ki fito na miqaki kiga baby"tamkar tayi banza da shi ko tace
ta fasa sai taga idan ma tayi hakan ai kanta ta yimawa ba wani ba don shi kam bashi
da asara,ta miqe kamar marar laka ta shige bedroom dinta tana qunquni qasa qasa"sai
an ma gama qonawa mutum rai sannan za'a wani tasa shi a gaba akaishi kamar wani dan
qanqanin yaro" "idan baki zuwa ba saiki zauna ba ke ya shafa"ya fada a tsawace,baki
ta rufe da sauri ta qarasa shigewa bedroom din don batayi tsammanin ya ji ba,lallai
shi kuwa wane irin kaifin ji gareshi take mamaki cikin zuciyarta
Na biyu kuma masu ganin abunda aliyyu yake yayi yawa kada kusa gaggawa a lamarinku
kuma kada ku manta shi haquri shine jagoran kafatanin lamuran mu na duniya bare
haquri ga 'ya mace kuma acikin gidan aurenta hanyar shiga aljannarta riba ce ba
kadan ba,ina so ne yan uwana mata muyi koyi da halinta koda cewa ba irin auren ta
kikayi ba amma nasan baza'a rasa matsala daya ko biyu da kike iya fuskanta ba daga
mai gida wadda shigen halin da aliyyu ya taba nunawa fadila ne to ga yadda ta
shanyeta ga kuma ribar da ta samu,na godewa masoyana gana daya ,Allah yayi mana
sakamako agidan aljanna ya hadamu dukkanmu a cikinta in kuma ci gaba da zama
marubuciyarku ta gidan aljanna 😜😜😀😀
4:50 pm 23/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 2*
1⃣1⃣1⃣2⃣ 1⃣1⃣&1⃣2⃣
Yana tsaye a wajen motar yana amsar calling yayin da salima ke tsaye kusa da shi
hannunta harde a qirjinta tayi kicin kicin da fusaka,sallama fadila tayi mata sai
taga ta dauke kai don haka sai ta ja tunga itama tayi banza da ita,ya gama amsar
kiran ya kashe wayar hannunsa na kan mabudin motar salima ta kalleshi tace"please
dear"kai ya gyada yana cewa"dont mind" ya bude gidan gaba kusa da kujerar mai tuqi
ya zauna ta bude baya itama ta shige,nasiru ya gaida ta cikin girmamawa a mutunce
ta amsa sannan ya tada motar suka fice
Tafiya ce kamar ta kurame sai ka rantse bata cikin motar sai shi da nasirunne ke
hira jefi jefi galibi ma bai wuce zancan kasuwa,idanunta na kan titi yayin da
zuciyarta ta lula duniyar tunani
A bakin get suka dakata bayan mai gadin ya dage masu get aliyyu yasa nasiru yayi
masa magana ya rufe ba shigowa za suyi ba,fadila ta tabe baki cikin ranta tana
gulmar aliyyun,nasiru ya gyara parking din sannan ya fice daga cikin motar,fadila
ta sa hannunta a kan mabudi zata fice "twenty minutes"haka ya fada cikin
carelessness,ba abunda tace da shi tayi ficewarta "ko baka gaya min ba ai na sani
uban masu tsari da qa'ida na duniya😙"tayi zancan cikin zuciyarta
Da yake takwas na dare ma ta dan gota gidan ya samu sararawa daga cincirundon 'yan
barka mutum hudu ta tarar Amina da mariya qannan mubarak ne sai maqociyarta guda
daya sai kuma wata dattijuwa inna jummai wadda mahaifiyar mubarak ta kawo mata ita
saboda kula da mai jegon da kuma jaririyar,alokacin da ta shiga ma tana kitchen
tana kwashe tuwon da ta yiwa faridan,fadila nata qyalqyala dariya ganin inna jummai
nata loda tuwon a flask tana ce mata"inna zanso naga dambarwar ku kam da farida don
ba abincin da taqi jini irin tuwo,dama dai ni kika baiwa"innan da yake macace mai
kirki da saurin sabo da jama'a tace"ai duk qinta kuwa da tuwo yanzu ya zama
abokinta dole ta cishi tunda jego ya zo"
Tayi sallama ta shiga falon faridan dukkaninsu suka amsa mata cikin fara'a suna
dariyar hirar fadilan da inna jummai,farida kam ture kayan jarirai dake gefanta
take tana cewa sister taho nan daya hannun nata kuma cup ne cike da tea tana sha
sai hada gumi take inna kuma taqi ma a kunna fanka bare a.c saboda wai jego faridan
zatayi irin na da,fadilan ta qaraso tana cewa "🤔sister farida mai tsokana da yawon
gidan qawaye yau gata dq baby" dariya ta basu dukkaninsu harda faridan,idanu fadila
ta baza tana neman baby tace nifa baku nazo gani ba wlh ina 'yata ku bani ita naji
duminta"yarinyar na hannun maqociyar ta ta nannade cikin farin shawul mai taushi ta
miqe tana miqawa fadila ita hadi da yi misu sallama ta ajjiyewa faridan 1000 kudin
barka ta mata godiya ita kuma ta fice
Ta kammala shanye tea din tas ta dire cup din tana kallon fadila tace "sister da fa
har nayi fushi kece ta farko da kika fara sanin haihuwarnan baya ga abbanta amma
sai yanzu zaki zo mana tun dazu baby ke son ganin mummynta bata zoba sai da aka
rigata gane mata ita" "hmmm lallai yarinyarnan kukan dadi fa kike da yaya yanzun ma
ya barni tare ma fa muke"cikin zolaya wadda attitude din farida ne tun usulinta
tace "wow kice har an fara boyonki lallai soyayya ruwan zuma"fadila ta harareta
tace "wlh badan kin mun abun kaiba kin bani baby mai kama da ni ba da sai na
bubbuge bakinki"su amina suka qyalqyale da dariya sannan suka miqe suka ce bari dai
mu baku guri kada a buge mana anti a gabammu"dariyar suka bawa fadila su kuma suka
fice kitchen gun inna jummai
Fadila ta sake zubawa yarinyar ido tubarkallah masha Allah qatotuwa da ita lallai
kam wannan photo copy dinsu ce ta kalli farida tace sister sannu"farida ta ya da
kai gefe tana tuno wuyar da ta sha"hmmm ke dai bari sister ansha gwagwarmaya ni kam
dan ba qara"fadila ta sake rungume yarinyar a qirjinta tana sake jin qaunarta na
shigarta bata qi ace tata bace,ta saki dariya tace "yanzun fa aka fara farida me
akai da maza daga ihu daya sai kuma murya ta dashe?😜"ta qarashe ta sigar tsokana
yau dai ta maida raddin tarin tsokana irin na farida da take mata ko yaushe,ko da
can dama fadila Allah ya zuba mata son yara,sanda suka tashi muhammad ne kawai yaro
a gidansu to har gidan maqofta take shiga dauko yara duk da yanayin unguwarsu irin
unguwan nin nan ne da ba ruwa na da kai kowa na qulle shi da ahalinsa cikin gida
amma haka fadila ke shiga ta taho da su,miskila ce ako ina magana bata dada ta da
qasa ba amma banda kan yara hakanan zaka ga ta sasu a gaba suna ta wasansu,farida
kam dama idan taga dama idan suka zo neman anty fadila sai ta korasu tace bata nan
zasu zo su dameta ne
Farida ta girgiza kai da sauri tana juya ido tace "kai sister is hardly in sake ko
zan qara sai after five to ten years,nikam na barmiki ki taba kiji"dariya ma ta
bata ganin duk yadda tayi laushi duk rashin tsoro da dakiya irin na farida,murmushi
fadila tayi tana ci gaba da kallon yarinyar tayi kissing dinta agoshi,"ina aliyyu
ne sister?"🙄af yana waje " farida ta miqe daga kashingidar da tayi tace "kada dai
kice mun kuna tare yaushe ya aliyyu boss ya fara kai matarsa unguwa"fadila
tace"saboda ya bata min ya fara ta kaina yau kina gani fa kamar gidqn nan yace min
wai twenty minutes?"farida tace "wlh am serious ya aliyyu ko salima matarsa ta
farko bai taba kaita wata unguwa ba idan ba monthly shopping naku ba(farida ta fi
fadila sanin halinsa ne kasancewar tq fita shiga jama'a hakanan ta fita zuwa gidan
uncle abba)kuma shine kika barshi a waje ga sitting room nan"fadila ta tabe baki
tace "oho masa har get malam salisu ya bude masa yace a maida arufe ba shigowa za
su yi ba" "gashi mubarak yanzu ya fita maida hajiyarshi gida da ya shigo da
shi"farida ta fada tana lallatsa wayarta,"zancan kike so ki bar mubarak kada ki
taso shi idan da rabon zasu hadu zasu hadun don ko mubarak ya zo idan bai ra'ayi ba
bazai shigo din ba"
Minti goma sha biyar ta shude suna ta hirarsu farida na cin tuwonta a sake
kasancewar su mariya sun bar masu dakin,dahiru yaron dake wa farida aike aike ne ya
shigo karbar abincinsa bayan ya miqawa inna jummai kwanon ya tsaya bakim falon
faridan yace"anty wai baquwa ta fito za su tafi"fadila ta bata rai don tasan aliyyu
ne yayi aiken kuma aqa'ida tana da sauran minti biyar
Ranta a bace bayan ta bude camera din wayarta ta yiwa baby pic ta sake sumbatarta
ta ajjiyeta gefan faridan ta dubeta tace sister zan dawo insha Allah me kikeson na
kawo miki"murmushi tayi tace"sister fadila nayi missing din wainar shinkafarkin nan
da kike mawa dady,idan zan sameta inaso"dariya fadilan tayi saboda ta tuna mata
lokacin da suna gidan idan tayi insha Allahu kan ta gama shiryawa Abban a warmer
taci na ci kuma ta bi ta har falon abban suci tare da shi tana hara rarta tana
komai amma sai tayi biris,"insha Allah kamar kinci waina ta kin gama"sukayi sallama
tamkar kada su rabu
Tana fita taga motar mubarak fake kusa da tasu shi dinne kuwa da alam yanzun ya iso
don lokacin suke gaisawa da aliyyun ta qaraso suka gaisa ya juya yayi cikin gida
yana cewa bari ya dauko ma aliyyun babyn ,hannu biyu yasa ya dauki babin mubarak na
gyara masa riqon don da gani bai iya ba,ya riqe ta sosai yana kallinta hadi da
fadin"masha Allahu la quwwata illa billah"(yan uwa gaka annabi ya horemu da fada a
duk lokacin da muka ga wani abu da ya qayatar da mu to ko kana da kambun baka bazai
kama abun ba domin wasu ma auna da shi amma basu san suna da shi din ba,sai kaga
abu kayita kodashi ba tare da ka fadi hakan ba daga qarshe sai wani ibtila'i ya
saukarwa abun ya lalace don Allah mu kula da wannan)
Fadila na satar kallonsa kadan kadan tana kallon yadda ya zubawa yarinyar ido ya
lumshe idanunsa daga baya ya budesu ya sumbaci goshin yarinyar sannan ya miqawa
mubarak ita yana sake cewa Allah yayi mata albarka,ya amsheta sukai sallama ya
shige gida da babyn
Aliyyu ya yafito qasimu dake fitowa fitowa daga gidan hannunsa da robar abinci
qasimu ya qaraso hadi da rusunawa aliyyu ya amshi bandir din kudin dake hannun
nasiru ya miqawa qasimu yace ka kaiwa maman baby ya zaro 1000 daga aljuhun trouser
dinsa ya bashi ya shige motar yabar qasimu nata zuba godiya yare da komawa cikin
gidan don sada saqon aliyyu ya bawa nasiru umarni ya tada motar suka bar layin
fadila nata satar kallonsa don kiwa dubu dari ce ya bayar a kaiwa babyn
Mrs muhammad ce 👑
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
*Part 2*
1⃣3⃣1⃣4⃣ 1⃣3⃣&1⃣4⃣
Fadila tacigaba da sake2 azuciyarta bata ankaraba taji ana bude get tana dago
kaitaga harsun iso gida ashe,parking space ya nufa ya kashe motar,fadila
dakekokarin bude motar setaji ya kulle motan ta waiwayo tadubesa suka hada ido tayi
saurin dauke kanta zuwa gefe,shiko gogon sebinta ya ke da kallo can yace wai meye
kiketa wani bata rai tamasa banza yacigaba damagana ,inatambayarki,kaikidanayine
nayi lefi koso kike danabarki kikwana? nan ma shiru yaharzuka cikin tsawa yace wai
badakenake maganaba salan wulakanci,
Se asannan fadila tadago kai da fuska cike da hawaye tace wulakanci? wulakanci
yawuce wulakantani dakakeyi Wanda haka har matanka suka sami damar gorantamun,Aliyu
nayi nadamar aurenka auren bakinciki Inatabbatarma dabadan mahaifinaba dana dade
dabarin gidan nan,cikin kuka takemaganar yayin da Aliyun yatsinci kansa da
tausayinta Yakuma kasa cewa kome illa binta da kallo.
Can Aliyu kuma kasa futa yayi daga motar jikinsa duk yamutu zuciyarsa ta cunkushe
abinda yafi damunsa shine kalmanta datayi kansu samira da salima domin yakaratunawa
da yanda yasamu samira adarensu nafarko,sannan Salima bayan rabuwarsu itama ba
agida tayi rayuwaba,yadafe kansa karo na farko da naga A S metama na kwalla daya
nazurarowa daya bayadaya😰 yace inna lillahi wa inna ilaihirraji un.tabbas jidakai
bekama ceniba domin ina tare da wadanda basu cancanci suzama iyayan yayanaba,gashi
inakallo se haihuwa ake Wanda akai bikinmu tare duk sun haihu,su naji kowacce tace
batashiryaba itakuma wanan yarinyar banashiga harkanta,gashi du k ta gane
kome,Aliyu yacigaba da hawaye yana maibakkincikin abubuwa kala kala yadaure ya fita
daga mortar jiki akasalance yanufi bangaransa yanashiga ya kulle kofar yabar
makullin ajiki sabida bayasan ganin kowa domin koda sunzo sunyi amfani da
makullinsu bazebuduba.yashige bedroom yafada gado yacigaba da tunani aranar dai
Aliyu beruntsaba Dan maganganun fadila kemasa yawo akwalkwaluwarsa,
Itako fadila cikin nishadi tayi barci domin tafidda wani tabo da kedamun zuciyarta.
*amun afuwa Mrs Muhammad nayi muki shishshigi amma haka mukeson buk yadawo
munakara mikamiki godiya dayabawa Allah yakara basira kidora saga inda natsaya
domin zansamu goyon bays amma kitambayi friends sunyarda kidora😀*bye nabarki Lfy
Wanda sukaji haushi suyafemin kar azagen nima wlh soyayyar buk din yasa nayi👍🏻
  
[10/16, 1:46 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?..*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*part 2*
1⃣5⃣&1⃣6⃣
1⃣5⃣1⃣6⃣
Qarfe tara fadila tayi wa iftihal wanka itama ta shirya cikin riga da skert na
atamfa a cikin qana nun kayanta ta cirowa iftihal wasu riga da skert dama sun mata
kadan jajayene in and top ta raba mata gashinta gida biyu ta tufke mata da ribbon
sosai iftihal tayi kyau suka yi break sannan ta soma gyara part dinta kafin ta isa
ga na aliyyu don duty dinta ne duk inda ta shiga yarinyar na biye da ita ita ala
dole sai ta taya ta aiki sai da fadila ta bata mopping din kayan kallo sanna ta
rabu da ita
Fadila ta fito tana goge hannunta da duster bayan ta gama aikin ta iftihal dake ta
fama da chocolate tace "anty ina daddy na?"murmushi fadila tayi ta kama kumatunta
tace"kwantar da hankalinki 'yar daddy yanzu zaki ga daddy shiga daki bakin gado ki
dauko min hijabina"da gudu kuwa ta shiga sai gata da shi a hannu ruwan madara ne
iya qugu wanda ya shiga da atamfar jikinta sosai,ta kama hannun iftihal din bayan
sun rufe qofan
Tana sa kai falon taji hayaniyar sama sama muryar salima ke a sama,tana tsaye
hannayenta harde saman qirji kan aliyyu shi kuma na zaune kan kujera yana sanye da
kayan bacci na maza ruwan madara shima hannun nasa harde a qirjinsa😠,shigowar su
yasa salima yin dif daga maganar da take yi din gami da sakin fuskarta daga
tsukewar da tayi tana dan binsu da kallo(salima akwai duniyanci)sam bata lura da
iftihal ba da suka shigo tare sai da yarinyar ta zame hannunta daga na fadila wadda
ta shige kitchen ta ruga a guje tayi gun daddynta tana cewa"daddyyyy
daddyyyy...."kamar yadda ta saba ta durqusa a agabansa kafin ta haye cinyarsa tana
cewa"morning daddy sabahul khair",murmushi ne sosai dauke a fuskarsa wanda bai
bayyanar da haqora😊yasa hannu ya dagota yana kallonta yace"sabahun nurrrr my
lovely khadija"tayi tsalle ta dane cinyarsa abinta tana wasa da maballan gaban
rigar baccinsa tana cewa"daddy tunnjiya nazo da daddare kaqi zuwa na ganka"
"wonderful,anan kika kwana ke da wa?""ni da anty fadila tare ma yanzu muka taho"ya
daga kansa yana nemanta da idanunsa sai dai tuni ta jima a kitchen bata a gun sai
salima dake tsaye ta zubawa 'yar tata ido
Kallonta take tana jin wani alfahari na shigarta tana godewa Allah da bai bata
damar rasata ba,wani dadi ne ke cikata ganin gudan jininta ita da halitta mafi
soyuwa a gareta wato Aliyyu salim Abdallah maitama,tabbas iftihal abar alfaharinta
ce yarinyar bata debo kammaninta ba ko kusa babu wani abu nata data dauko illa
farar fata wadda aliyun ma na da ita,kowa ya ganta ya san jinin su ce family din
alhaji salim Abdallah maitama ce jininsu ce
Ta dawo daga duniyar tunaninta hadi da miqawa iftihal din hannu alamar ta taho
sanda suka hada ido fuskar salima dauke da murmushi,da taga kamar yarinyar bata
fahimta ba sai tace"come on baby na come on my dear " yarinyar ta noqe kafada tayi
luf jikin mahaifinta kamar mai tsoron ta babu sabo ko kusa tsakaninsu,wani kishi ya
kama salima don taga yadda suka shigo da fadila yarinyar a sake take kana ganinsu
kasan akwai sabo mai yawa tsakaninsu
Ta sake gwada sa'arta ta miqa mata hannunkaro na biyu tana sake cewa"come on mana
mai dear kin manta mominki ne iftihal? Me yasa baki zo guna kin kwana ba ina da
chocolate da biscuit da yawa da zan baki"ta sake noqe kafada tace "um um nafison na
kwana gun anty fadila she's nice like daddy"sai salima ta maida hannunta ta rungume
cikin jin haushi
Aliyyu na ankare amma yayi kamar baiga abinda ke faruwa ba,sai da yaji tana jan
qwafa sannan ya tanka mata"duk uwar da bata yi showing mercy akan yaronta ba tayi
abandoning duk wasu duty nata akansa no need to deceive her self akan shi zai iya
jin qanta ya kuma ji tausayinta"idanunta sun kada sunyi ja kadan take jira ta fara
malalar da hawaye tace"aliyyu abinda ya wuce ya riga ya wuce please"ta juya cikin
zafin nama ta bar part din nasa kamar zata rushe da kuka

*TUNA BAYA*👈🏼
🔱🔱🔱🔱🔱
Aliyyu da salima sunyi aure ne irin auren da zaka iya kiransa na soyayya,karatu shi
ya fara fitar da aliyyu india cikin garin mumbai dake qasar india,ya karanci fannin
kasuwanci da masana'antu ne tun usulinsa,kusan binda ma ya zaunar da shi kenan a
qasar bayan kammala karatunsa kafin daga bisani ya soma kai kawo tsakanin nijeria
da indian
Tun kafin aliyyu ya kammala degree dinsa na farko yake siyan kaya yana turawa uncle
Abba yace a siyar masa tun uncle abban na dariya yana dauka wasa ne abun nasa
yakance"alii rigima idan banda abinsa mai ya nema ya rasa da zai takurawa kansa sai
ya fara kasuwanci tun kafin ya kammala karatunsa?"shi kama aliyyu ya dage aiko kaya
yake tun daga lokacin da uncle abba ya fuskanci son kasuwancin a jininsa yake sai
ya qyaleshi ,sai gashi tun kan ya kai ga kammala degree dinsa na biyu ya mallaki
kudade masu tarin yawa na qashin kansa tsantsar guminsa,sam yaqi amsar tallafin
sisin kwabo dag dukiyar da Allah ya horewa mahaifinsa,kwata kwata aliyyu ba cima
zaune bane akwai zuciyar neman na kai tun yana qaraminsa,bai damu da arziqin da
mahaifinsa ke da shi ba
Wadannan kudade yaci gaba da juyawa har kawo yanzu matsayin da yake kai na
mamallakin companies da share shares a gida nijeria da wadansu maqwaftan
qasashen,aliyu ya zamo daya daga cikin matasa masu tarin dukiya mutumne shi da
Allah bai bashi dagawar son a san wayeshi ba,yasha gayawa abban nasa tun kafin
zuwan wannan lokacin shi yafison yasan ya san zafin neman na kai,sai gashi burinsa
ya cika don ya tara dukiyar da shi kansa bai sa ran samun kamarta ba,darajar
addu'ar mahaifa riqon gaskiya da amana tausayi da taimakon na qasa su suka kaishi
ga wannan matsayin da yake kai
Cikinsu harda salima su hudu ne ita sai wata qawarta 'yar nijeria sa'adiyya abikan
karatunta biyu 'yan qasar data nemi rakiyarsu don qasarsu ce sun fita sanin kan
farashin kayayyakin shruti da arohi,sun ahiga shagon a sanda aliyyu ke ciki yana
zaune kan daya daga cikin kujerun dake ajjiye a shagon suna lissafi ne shi da mai
mai shagon kan wasu kaya da aliyyun ya sara a gunsu alokacin tun kafin ya bude
kamfaninsa
Abu na farko da ya fara kama jan hankalinta game da aliyyun shine baiwar tsantsar
kyau da Allah ya bashi da daddadan sauti ,abu na biyu ya bata mamaki jin yadda yake
hira tar tar da indiyanci tamkar haifaffen can,tunda suka shigo shagon daga kallon
farko na amsa sallama bai sake duban sashin da suke ba ya mai da kai yaci gaba da
abinda ya kawoshi shagon
Ita din ma azahiri idan ka kalleta sai kayi tsammanin hankalinta bai kansa saidai
duk siyayyar da take yi kusan qani abun ma bata san me zatayi da shi ba data dauke
shi don hankalinta na kan alin
Tuni ya kammala abinda yake yayi sallama da raja ya wuce,sanda yake fita ashagon
garin karkatawa ya wuce taga silmiyowar wani abu daga aljihun trouser dinsa ma baya
amma bata zaci wani abu mai muhimmanci bane sai da ta sake matsowa ta sa idonta
sosai sannan taga ashe wata 'yar kyakkyawar wallet ce ,da sauri tasa hannunta ta
bude ciki,rupees(kudin india) ne masu yawa aciki a miqe,sai dan qaramin hotonsa
wato passport,sai kuma wasu kati guda uku biyu na wasu shaguna dayan an rubuta
*adishwar garment* shagon na cikin *janta cloth market hawkers plaza*ta maida shi
ta duba dayan shi kuma na shagon *ajmeri fashion* shagon shi kuma na *hazarat abbas
road Samuel street*,duk cikinsu babu shagon da ta taba zuwa tunaninta na kan yadda
Atayi masa da wallet da kuma yadda zata sake samun damar hanawa da shi,tana duba
kati na uku uku na dauke da sunan hotel din da ya sauka haka jikinta ya bata tunda
su muta nene da komai ka siya ko kayi mu'amalar ciniki da shi sai sun baka rasit ko
card nasu,tasan hotel din tunda takan ziyarci cikinsa lokaci bayan lokaci nan kusa
da makarantarsu yake
Ta maida duka kayan ciki tana sauke ajiyar zuciya,bayan sun kammala siyayyar suka
koma cikin makaranta,da daddare ta canza shiga irin tamu ta hausawa atamfa ce
saidai dinkin riga da skert ne tayi kwalliya sosai a fuskarta,ba wata tafiya ce mai
nisa sosai ba tsakaninsu don haka irin keken nan nasu ta hau ya qarasa da ita,bata
sha wahalar samunsa ba saidai da yake hotel ne na manyan mutane akwai tsaro sosai
da kuma tsari duk magiyarta basu yarda sun bata number din room din ba sai da sika
kirashi suka sanar masa,duk da yayi mamakin mai neman nasa kuma sunce mace yace a
bata number din baisan me ya kawota ba ko da taimakon da zai iya bata
Ku biyo
Mrs muhammad😘
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:47 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*part 2*
1⃣7⃣&1⃣8⃣
1⃣7⃣1⃣8⃣
Sai da tayi knocking sama da sau biyar sannan aka bude mata,fuskarta ta wadatu da
murmushi😃 yayin da tasa take a tsuke😠 kamar hadari,"sannu ko?"tace da shi cikin
fara'a"yauwa sannu" ya fadi adan dake yayi bake bake abakin qofar babu wata hanya
bare ta sa ran shiga ciki don ko kalan labulen bakin qofan ba zata tantancewa
ba,cikin qosawa ya gyara tsaiwarsa ganin tayi shiru yace "I hope lafiya dai ko?"ta
sake yin murmushi a karo na biyu ya zaro wallet din daga cikin yar purse👛 dinta
dake damqe a tafin hannunta sannan ta dubeshi tace"wannan ka yar dazun a mall din
paras mahal collection"ta miqa masa tana dan murmushi,ya sa hannu ya amsa yana
cewa"thank you verry much"ya juya yana qoqarin mai da qofarsa ya rufe
Girgiza kai yayi hadi"it can't ki zabi wani abun dai daban banda wadannan"ta kanne
ido daya😉 tace"ni su din dai nake so"kafewa yayi kai da fata bazai bata ba"i told
you ba zaki samu ba"itama kafewa tayi akan shi take so indai alherin da tayi masa
yake son rama mata,daya lura tana da yawan taurin kai sai ya bude wallet din ya
zaro rupee dubu daya kwatan kwacin kudin nijeria a yanzu naira dubu hamsin ya
ajjiye mata saman qafarta ya juya karo na biyu yana shirin sake rufe qofarsa
Ta tabbatar idan ya subuce mata a yanzu mawuya cine ta sake samun dama kwatan
kwacin wannan don haka cikin zadin nama ta tattara kalmomin"idan kamin haka baka
min adalci ba zaka kashe min gwiwa ne na aikata aikin alkhairi,ni bana buqatar
kudinka
Da haka ta kashe masa gwiwa don bazaiso ta zama mara kirki ba ta sanadinsa ya sani
idan har hakan ta faru yana da tagomashi a agun Allah,dole ba dan yaso ba ya bude
wallet din ya bata passport din hadi da karanto mata numbobinsa ta kwafe tsaf bisa
wayarta tayi serving,tun daga lokacin hotonsa shi ya zama abokinta da zarar ta
kadaice shi take sawa a gaba tayi ta kallo,kyan Aliyyu na qayatar da salima ya tafi
da imaninta 100%
Takan bata lokaci tana gurin kiransa amma ba zai daga ba,ta jure hakan ba tayi
zuciya ba tana ci gana da kiransa,yau da gobe tafi qarfin wasa har takai da idan ta
kirashi sau goma zaoyi qoqari ya daga mata ko sau daya ne shima daga gaisuwa bai
bari a wuce haka,an halicci zuciya abisa son mai kyautata mata to hakan yake don
kuwa kulawa sosai salima ke nunawa aliyyun mutum ne dama da bai taba budurwa ba
samun hakan yasa ta shiga cusa masa ra'a yinta sannu a hankali har ya minta da ita
ya bada amannar zata zama abokiyar rayuwarsa
Cikin lokaci qanqani salima ta dage a tada maganar aure don kuwa tsoron take kada
ta rasa aliyyun saboda tana ganin yadda mata jinsin qabilu kala kala dake indian
mazauna can yan asalin indian da kuma baqin haure ke kara kaina akansa abunda ya
sauqaqa abun ma babu fara'a ma bisa fuskarsa ko yaushe tana daure ne tamau balle
kice zaki kawo masa wargi
Bai damu ba suka koma gida nijeria aka gama komai sannn ya dauko ta suka dawo
indian saboda business dinsa ita kuma ta samu ta kammala karatunta,dole salima ta
yakice duk wani abokin shashancinta saboda matsananciyar qauna da take ma aliyyun
Cikakkiyar kulawa aliyyu ya dinga samu sosai daga farkon aurensu duk da ya fuskanci
qalubale da dama na wasu ayyuka na cikin gida wanda ya zama dole kowacce
*cikakkiyar mace* ta iya su,kama da girki zuwa tsaftace gida amma sai yayi haquri
da hakan yake koya mata wasu abubuwan da niyyar idan sundawo gida nijeria zai
turata makarantar koyon irin wadannan abubuwan
Abu na farko da ya fara kawo babbar baraka a zamantakewarsu wanda shi ya zama sila
kuma sanadiyyar barkewar alaqar dake tsakaninsu shine,wata uku da yin aurensu ta
soma rashin lpy,tuni suka yiwa mumbai general hospital tsinke sabodancita take
sosai ,ba bata lokaci likita ya fara aikinsa cikin dan taqaitaccen lokaci sakamako
ya bayyana sun samu qaruwa Allah ya albarkaceta da samun juna biyu
Ba qaramin tashi hankali da razana aliyyu ya tsinkaya ba kan fuskar salima shi da
ya tsammaci ganin farinciki,tun acikin asibitin take kuka wi wi har suka iso
gida,duk da ya kawo abubuwa da dama cikin ranta game da kukan da take sai dai ya
hani zuciyarsa da yanke hukunci bisa zato da zargi,don ya tabbatar ya matsa mata da
tambayar mekw faruwa? Bata yi qasa agwiwa ba kuwa budar bakinta tashin farko ta ce
masa"gaskiya darling ban shirya haihuwa ba yanzu babu abinda ke cikinta banda
wahala da tsofar da mutum,just shekarata ma nawa da zan fara shiga rayuwar raino da
wahalar 'ya'ya?,am just 25 fa"ta qaraahe maganar idanunta na malalo da hawaye
Da fari ua dauka rashin fahimta ne saboda boko da ya dabai baye rayuwarsu don haka
sai ta ma bashi dariya ya murmusa idanunsa akanta yace"that's my salima,wannan
tunanin naki fake ne it's not real,haihuwa ai ni'imace daga Allah wanda kudi ko
mulki ko wata isa basu isa su baka ita ba,tsufa kuma ai lokacine,idan yazo babu
abinda ke tareshi,bama haka ba idan kika ga haihuwa tasa mace tsufa ya danganta ko
daga gareta ne rashin gyara ko kuma daga yanayin kulawar da take samu daga
mijinta,ke kam baki da wannan matsalar ko daya,come on baby dont bother your self
kinji,I promise I wil be with you cikin ko wanne irin yanayi"
Wannan duk baiwa salima ba tun aliyyu na rarrashinta har ya gaji ya sanya mata
idanu,daga qarahe ma ganin ya zuba mata idanu sai tayi tsammanin ko ya haqura ne
gaba daya?,sai kuwa ta fito masa da aniyarta na son zub da cikin wai ko don ta samu
taci gaba da yin karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tunda tana final year
dinta watanni kadan suka rage mata zata fuskanci exams
A ranar taga bacin ran aliyyu irin wanda bata taba ganin irinsa ba,yayi mata kaca
kaca ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba ya mata jan kunne mai zafi akan kada
ma ta yarda koda mistake wani abu ya samu cikinsa bazai lamunta ba bare kuma
intentionally,ta tsorata ainun amma duk da haka ta kafe ta turje akan bata ga
abunda zai sata zam da cikin ba tunda bata so ai ba'a dole shi kuma yace zai mata
dolen kuma zata gani,kamar ta haqura amma zugar qawaye na sake
tunzurata,cikin rikici ta dinga rainon cikin ji take kamar tasa hannu ta fisgo
abinda ke cikin ta jefar ta huta,wani takunkumi ya kafa mata ya hanata fita ko ina
hakanan ya hanaduk wani mai zuwa zuwa gurinta,makaranta ma shike daukarta ya kaita
ya kuma tsaya a bakin inda da zata dau lecture din har sai ta kammala ya daukota ya
maidota gida ya kuma kulleta sannan ya fice sabgoginsa
Da wannan rikici ta kammla karatunta yayi clearing din komai nasa ya dawo Nigeria
shi da ita gaba daya sai dai idan wani abu ya kamashi na yaje indian sai ya tasata
agaba suje tare su dawo tare don kada ma ya barta tsautsayi ya gifta tayi abinda
ranta ke raua mata,don baijin idan ta aikata hakan zai iya qyaleta ko ya daga mata
qafa,
Ita kuwa ta samu sake rigima harda mara dalili yinta salima take dom dai taga duk
ya dora burinsa kan cikin,ya zuba mata ido ne saboda albarkacin yaronshi da take
dauke da shi gashi mai tausayi ne qwarai da gaske kan mace mai ciki,hakanan
tsakiyar dare sai ta tashi ta zauna ta kuma taahi aliyyun suyi kwanan zaune ta kuma
kwana tana rusa masa kuka da ihu ita wai cikin ya dameta ya hanata sakewa
Cikin haka ne ranar wata juma'a aliyyubya fito a masallaci aka masa waya asibitin
doctor sa'adah yazo salima ta haihu,yayi matiqar mamaki don kuwa cikin watansa
takwas da sati biyu kuma lafiyar Allah ya fita ya barta a gidan babu wasu alamun
naquda tare da ita don baccinta ma take shirga,baiyi qasa agwiwa ba ya isa asibitin
cike da murna doki da koma mamaki,yana zuwa ya samu qarin bayanin zuwa tayi aka
turo naqudar ta qarfin tsiya wai ta gaji da zaman cikin ajikinta don lafiyarta lau
ta iso asibitin,yayi fada sosai don sunga doctor sa'adah bata nan ne da ko bakin
salima zai cire don roqo bazata yi mata ba har sai da yarda da kuma izinin aliyyun
Ransa yayi mummunan baci saidai yana yin tozali da santaleliyar baby girl din da
Allah yayi masa kyautarsa sai farin ciki ya mamaye gurbin bacin ransa tuni yama
mance da abunda ya faru,sak kamammin family dinsu tayo ya rungume yarinyar tsam
tsam a qirjinsa qaunarta na mamaye jinin jikinsa,ya dinga kissing din yarinyar da
tofeta da addu'o'in tsari kala kala,tuni gidansu ya cika da yan uwa mominsa farin
ciki tamkar akan yarinyar ta fara jika,duk wani uatsina da salima keyi da daga kai
ita da yam uwanta hakan bai dami yan uwan aliyyu ba domin su gadon arziqi ne ba
taka shi sukayi suka haye ba rana tsaka,harkar girma kawai sukeyi
Suna akayi na tserewa sa'a,yarinya tayi albarka sosai don daga salima jar aliyyin
babu wanda bai ga hakan ba,khadijatu shine sunan da ya mominsa ta zaba mata don
abba ya bawa zabi shi kuma yace ya bawa momin ta zabawa kishiyarta sunan da kanta
tayi murmushi tace ta bata khadijatu tana fatan Allah yasa ta yi gadon hali irin na
mai asalin sunan,salima dama wannan bai dameta ba ita dama ta rabu da cikin shine
agabanta alaqaqai kamar yadda ta laqaba masa
Aka gama wannann ta wuce salima ta sake qirqirar matsala ta biyu wadda ta
tunzurashi ta koma jawo igiyar aurensu ta guntule
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:48 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*Part 2*
1⃣9⃣&2⃣0⃣
1⃣9⃣2⃣0⃣
Yadda abun ya faru shine salima sam taqi shayar da iftihal,anty hauwa ita ta gani
ta yiwa salima magana cikin nasiha da kuma fadakar da ita illolin dake tattere da
qin shayar da yaro nonon uwa indai ba lalura ba mai qarfi wadda zata jawo hakan
koda hakan ta faru wasu basu yarda da madarar suna kai dansu ne ga wata wadda suka
amincewa halayenta ta shayar musu da yaro balle ita da lafiya lau ne babu wata
lalura,qememe salima tayi da ranta taci gaba da dirkawa iftihal baiwar Allah madara
ba tare da masaniyar aliyyu ba
Ranar da lamarin ya faru sati biyu ne da yin haihuwar cikin yan suna wata ta sanar
da ummi halin da ake ciki don haka ta aiko anty hauwan takanas da roqo da kuma
lallashin salima tayi haquri ta shayar da iftihal don abun ya daga hankalin momin
tace ko lafiya ce bata da ita tayi magana sai a a samo mata magani cikin tsiwa da
rashin kunya salima tace"ita momin ce ta aiko ki?to ki gaya mata babu dan iskan da
ya isa ya jawomin abinda zaisa jikina ya lalace lafiyatq qalau saidai tun farko na
gayawa ubanta ban shirya haifarta bane,don da na samu dama da tuni tabi rariya ba
zata ma zo duniyar ba bare azo ana min iyayin banza da wofi akan...........
Bata qarasa ba taji saukar lafiyayyun mari hagu da dama na kumatunta,da sauri ya
daga kai din taga wanda yayi mata irin wannan aika aikar,aliyyu ne tsaye bisa kansa
cikin matsanancin fushi fuskarsa tayi jajur😡 abunka da fari huci kawai yake
fitarwa kamar wani zaki ya dora da cewa"bansan baki da mutunci ba sai yau ashe ke
'yar iska ce ban sani ba? Mahaifiyata kike fadawa wadannan mugayen
kalaman?.....to bari kiji salima.....har yau ba'a haifi yarinyar da zata ci
mutuncin iyayena ba wallahi duk son da nake mata,yarinyata kuma daga kin bar bata
madara indai ni ke aurenki"
Cikin hasala ta miqe tana nuna kanta tace 👆🏼ni ka mara aliyyu?....ni ka mara?,to an
fada din yarinya kuma wallahi ko sama da qasa zasu hadu ba zata sha min nono ba,ai
kana da yan uwa mata kana iya basu ita su shayar maka ko ka samar mata wata uwar ko
kuma ka maidata cikinka ka sake haifeta"ya harzuqa matuqa ya daga girarsa yana
kallonta "oh haka kika ce! Indai kuwa haka ne baki da wani amfani" "to ba sai ka
yiwa tufkar hanci ba"a zafafe ya gyada kai yace "ok,well kije na sake ki saki daya"
Ta fito dauke da akwati tana shirin fita,sai lokacin anty hauwa ta samu bakin
magana "kiyi haquri don Allah ki dauki yarinyar nan"ta juyo a fusace sannan tayi
murmushin takaici ta dubi anty hauwa"ai burinku ya cika ko?kuma ina tsammanin kema
macace akwai nono a qirjinki kamar nawa to kina iya bata naki"a fusace aliyyu ya
sake tasowa da niyyar kai mata wani marin anty hauwa ta tare gabansa
"a'ah aliyyu kada ka sake dole taji haushi its our fault dont beat her again mu
lallabata ta dauki yarinyar dai"cikin harzuqa da tsawa wadda baisan yayi ba yace da
anty hauwan"ni👆🏼 ni zan lallabata don ta dauki iftihal god forbid anty"ya fada yana
kada kai"ko zata nemi hakan ba zata samu ba"bai san ya sake tura ma salima wani
baqincikin ba da sauri ta ja akwatinta ta fice,a sanyaye anty hauwa ta juya ta
dauki baiwar Allah iftihal dake nannade cikin showel tana ta tsanyara kuka kamar
tasan abunda mamanta ke yi ,sanyata tayi a kafada tana jijjigata tana kallon aliyyu
dake zaune saman kujera dafe da kansa idanunsa alumshe jijiyoyin kansa sun fito
sunyi rada rada tasan alamun tsananin fushin aliyyu kenan tun yana yaro ,a hankali
tana shafa bayanta har yarinyar ayi shiru da yake mai haquri ce bata da rigimako
kadan matuqar ta qoshi
Zaman sukayi tamkar na makoki na kusan minti talatin sanann tace"aliyyu tashi mu
wuce gida dole su abba suji irin aika aikar da kayi,ya kada ki bayan ya bude
idanunsa da suka koma ja ya kalleta"ban yi laifi ba wannan shine hukunci da yafi
dacewa da ita,ni nasan me dame salima ta yimin bayan wannn tun alokacin ta cancan
ci narabu da ita amma na daure"ya maida kasa kujera yana maida numfashi ya daga
mata hannu alamun ta tafi kawai
Ta girgiza ki tace "a'ah bazaiyi na qyaleka ki kadai ba kana cikin irin wannan mood
din"ita tayi driving shi kuma ta bashi iftihal din ya riqe,ido sosai ya zuba yana
kallon yarinyar tausayinta matuqa ke shigarsa yana tausaya mata na rashin dacen uwa
da bata yiba ya rungumeta tsam tsam a qirjinsa cike da qaunarta
Fa babu irin wanda momi bata yi ba tamkar ta ari bakin wasu,kamin abbansa ya dawo
ya dora da nashi,ce masa auke ai haquri shine mafita ba saki ba,shi dai uffan bai
ce ba don baijin koda salima ta dawo tofa ta rasa shi shi da 'yarsa har abada
To kuma sai aka taki saa ko rashin saa zance ne?uncle abba me ya nuna dattako da
kansa ya taka gidansu salima don yin bikonta,qara ra a gabansa abban ta ya nuna
masa shifa ba ruwansa bazai tursasawa 'ya 'yansa ba don suna da 'yancin yin duk
abinda suka ga ya dace da rayuwarsu,amma zai kira salima atambayeta idan zata koma
to,da yake a cikin zafin kanta take a lokacin bata ji kunyar budar ido tace da
uncle abba ba itafa ba zata koma ba"abban nat ya kalleshi yace"to kaji mai zaman
tac3 bazata iya ba"abba bai sake tofa kanzil ba ya bashi hannu sukayi musabaha ya
dawo gida
Lamarin rayuwar gidan nasu yayi matuqar bawa uncle abba mamaki,rayuwar'yancin kai
suke irin ta mai jan kunne?ba rayuwa ba irin ta addininmu wadda fiyayyen halitta ya
koyar da mu ba?,wanna wane irin masifane da a yanzu muka qaqabawa kanmi?,bayan ya
dawo ya sanar da momin yadda sukayi,ita kanta da ake mace abun ya daure mata kai
amma kasancewarsu iyaye masu dattako da basu so dansu yayi saki sai ta nemi izini
gun uncle abban akan ita ma zata je ko za'a dace"uncle abba bai hanata ba yadda mai
akai da mahaifin salima exactly haka akayi da mahaifiyarta don aqidar duka iri guda
ce
Saidai ita an samu dan bambanci kasancewar salima tafara saukowa har ta fara kewar
aliyun sai mamarta tace wa momi saidai aliyyun yazo da kansa,nan momi ta saka shi
gaba akan lallai lallai ya shirya yaje,shi dai kullum yana binta ne da to don kuwa
ya riga ya gama yankewa ransa cewq ko itace autar mata yq haqure mata don gaa daya
ta qarasa ficewa fit daga ransa,bata da wani abu a yanzu da zata burgeshi da shi
Ganin momi ta soma tsanantawa a al'amarin sai ya soma shirin komawa indiyarshi ba
tare da sanin kowa ba bai so ba ba kuma a son ranshi ba don baiso yayi nisa da
yarinyarshi sai da ya kammala ne suka sani,momin taso ta hana abba yayi mata magana
aka ta tsagaita hakanan da Maganar dole sai salima ta dawo idan da rabo zaman bai
qare ba zata dawo ne,aliyyu mai tsananin biyayya ne bashi da tarin kunne akan duk
wani umarni da iyaensa suka bashi,yana dai da zurfin ciki ne da nauyin baki,tun
yana yaro idan suk ce yayi abu ya kafe baiyi ba to yanada dalilinsa ne mai qwari
wanda sai daga qarshe idan suka bincika sai suga lallai yana da gaskiya
Momi ta gamsu da bayanin abban ta kuma yiwa aliyyun fatan alkhairi da samun
dacewa,aliyyu ya bar nijeria 🛫cike da kewa da qaunar 'yar diyar tashi tsoka daya a
miya khadijatul iftihal,ya tanadar mata duk wani abu da zata buqata daki guda ya
ware mata yajibge mata komai hatta da ruwa da zata sha ya tanadar mata bai bari ya
dorawa kowa wahalarta ba harda kayan banza ma da wofi wanda bata buqatarsa,hakanan
ya bude mata account duk wata yana saka kudi a ciki yace da momin aje a cira ayi
mata abinda tale da buqata,to kawai take cewa kamar yadda uncle abba ya umarceta
don shi tuni ya karbe ragamar komai din kudin da aliyyun keta aikin turowa uncle
abba yace abarshi cikin account din ta amfanesu idan ta mallaki hankalin kanta
Wata shida kacal salima taji ajikinta qaunar aliyyu da yarinyarta tamkar zata
zautata cikin begensu take kwana take tashi,yayin d iftihal ke cikin walwala da
samun gamsashshiyar kulawa gata da soyayya ta qannen uba kakanni na gun uba da kuma
dangainsa,tayi bulbul abinta madarar dai ita taci gaba da karba don itama taqi
nonon kowa zakaran da Allah ya nufa da cara sai gashi cuta mai taba yaro bata taba
samun yarinyar ba don ko haqori tashi sukayi suka ganta da shi ya soma fitowa,ga
wayo a gunta gane mutane da kaifin basira
Acan din ma bata sameshi da wuri ba don ya canza gari ma gaba daya sun zauna a
mumbai ne shi kuma ya koma new Delhi taci wuya ka su hadun saidai haduwar tasun
mabata haifar mata da d'a mai ido ba,kaca kaca yayi mat irin wanda bata tsammani ba
ya kuma jamata kunne da idan har ta sake suka kuma hada hanya sai ya wulaqantata,ta
samshi qwarai idan ya fusata baida dadi iya kuma qurewa ta sani ta qureshin don
haka bashiri ta tattara ta dawo nijeria ba tare da ta cimma nasara ba
Aliyyu bai waiwayi nijeria ba sai bayn shekaru uku cike da nasarori da budi masu
tarin yawa wadanda bai taba tsammatar samunsu ba,company nasa ya bude babba acan
hadi da qulla harkokin kasuwanci kala daban daban da wasu manyan kamfanonin,yazoya
taras salima naci gaba da bibiyar rayuwarsu shida yarsa taqi aure sam duk wadata
tsaya da shi sai taga ba namiji bane ganinsa take kamar mace yar uwarta taqi
sauraron kowa da komai,itace kira saqonni na email sms duk wata kafa da ta samu ya
rabu da duk wasu layukansa saboda ita amma ya rasa yadda take samun sababbi,sunzo
don a basu iftihal yafi sau hamsin tun yana india suke da muradin haka ya gaya masu
su da iftihal saidai su ganota daga nesa don bata buqatarsu
 🔱🔱🔱🔱🔱
*samira*
🔱🔱🔱🔱🔱🔱
Itama tazo akan gaba don lokacinne tsananin ya sake aure ya masa yawa a gida ahi
kuma a zahitin gaskiya a wannan lokacin bai da time na duba mace,ganin ya samu
maison iftihal dinsa yasa ya amince daga qarahe ne ma momi ke masa albishir din
itafa ba zata bashi iftihal ba donnta riga tazo kenan,ba yadda ya iya duk da son da
yake wa yarinyar tasa
Sai da salima ta gasu sosai fiye da tsammaninta wanda tadinga jelen kamun qafa da
momi da abban da a baya ta watsawa qasa a ido kullum tana cikin gidantana magiya
sannan ta samu dawowa gidanta,gidan da ta tarar ya kubce mata har wasu biyun sun
samu mazauni cikinsa,ya ta iya da ranta son da take masa yasa bata ji wani abu ba
tayi zamanta duk da a baya tana daga cikin matan dake iqirarin basu ba kishiya don
ba zasu iya zama tare da ita ba
🔱🔱🔱🔱🔱🔱
*_dawowa labari_*
🔱🔱🔱🔱🔱🔱
Washegari tun qarfe tara fadila ke shirin fita suna,tayi wanka ta shirya tsaf cikin
shadda dinkin doguwar riga ne yasha aiki daga sama har qasa butter colour ta debi
wadanda zata sauya a can kala biyu ne da tayi musu anko ita da faridan zasu sa tare
ta shirya iftihal cikin itama doguwar rigar yan kanti wadda ajiya ta bada aka siyo
mata hade take da takalminta da ribbons dinta red ce in and top ta tsaya mata iya
qauri takalmin boot ne na yara fari qal tayi ma gashin yarinyar ado da fararen
ribbon tayi kayu matuqa kasancewar yarinuar mai yalwar gashi mai tsawo da santsi
Hat ta tada motarta iftihal ta hango abban nata ta balle murfin motar ta fice
aguje,bayan ta duqa ta gaidashi ya dauketa yana wulla ta a sama shiko nauyi bata yi
masa"cewar fadila cikin ranta tana satar kallonsu,tana ganin iftihal na nuno mishi
ita,ya juyo ya kalleta suka hada ido tayi maza ta sunkui da kai don kada qwayar
idanunsu ta hadu ya saka mata dafin da ya saba jefa maya cikin zuciyarta na qarin
qaunarsa,"verry neat ya fada sannan ya dauke kai"iftihal ta leqa fuskarsa "daddy
munyi kyau kuwa"yayi kissing kumatunta yace kinyi kyau sosai my dear"tadan bata
fuska tace "anty na fa?"yayi yar qaramar murmushi yace "both of you""thank you
daddy"ya sauketa bayan ya sake kissing dinta tana daga masa hannu ta zura aguje ta
dawo cikin motar tana dariya
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:50 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?..*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*part 2*
2⃣1⃣&2⃣2⃣
2⃣1⃣2⃣2⃣
Fadila tayi murmushi sannan ta tada mota iftihal tace "anty Abba yace munyi kyau
wai na zama 'yar gatan anty ni 'yar gatanki ce wai anty?"ta shafa kanta da daya
hannun nata tana murmushi tace"iftihal ke 'yar gata na ce mana"
Minti arba'in suka qarasa gidan da yake safiya ce babu yawaitar mutane sai 'yan uwa
na jiki sosai,su hajja gana(kakarsu ta gun uba) umma a'i anty hafiza rumaisa da
sauran 'yan uwa na nesa da na kusa,Fadila ta fada jikin hajja gana tana cewa bari
na more cinyar 'yar tsohuwa" hajja gana ta sa dariya da yake sunfi shiri da Fadila
fiye da farida"more abinki kafin kema Allah ya kawo miki masu more taki"murmushi
fadilan tayi sannan suka soma gaisawa da yan uwan hajjar na tambayarta mai gidan
tace lpy lau yana ma gaisheki
Kafin azahar gidan ya tumbatsa da jama'a,ko ta ina,bayan azahar kuma da kadan sai
ga family din aliyyu momi ce kawai banda ita,cikin bedroom din farida sukayi
zamansu anata karbar baqi
Rabi'ah ta kalli fadila lokacin da take canza kaya su anty hauwa na sallah tace "ni
dai anty idan kuka tafi chinan nan qana nan kaya kawai nike son tsarabata"fadila ta
dago ta dubeta bayan ta gama zuge zif din rigarta tace"wace china kuma
rabi'ah"dariya rabi'an tayi"kai anty ko baki son asan zaki ne?"cikin rashin fahimta
take dubanta tana qoqarin daura dankwalinta"wai wa yace miki zani china rabi'ah?"ta
sake qyalqyalewa da dariya tace"tun last week fa yaya aliyyu ya gaya ma momi an
gama ginin sabon company dinsa da zai bude zai wuce china cikin satin nan ke da
shi,shekaran jiya kuma sai ga shi ma da visa dinku a hannu ta fito jibi zaku tashi
da daddare amma anty kice baki sani ba?😀"
A badini zancen yayi matuqar kidima fadila ya daketa sosai amma sai ta dake don
kada ta bada satar amsa ta qago murmushin yaqe"kinsan halin yayanku akwai lafiyar
miskilanci dazun dai yake cemin idan na dawo zai min wani albishir to ina tsammanin
shine"sumayya da a lokacin ta sallame sallarta tace "har Allah Allah nake na idar
kinga haukan da salima ta dinga yi wai da ita za'a tafi?"su sumayya suka kwashe da
dariya rabi'ah tace"qara fa ta kawo gun momi sai gata tayi tsuru tsuru da ya aliyyu
yake fadin babu abinda suka iya ba inda zai je da su su zamar masa nauyi"sumayya ta
dora "qarshe ma momi da yake zayyano mata matsalarsu kunya ce ta isheta ta bar
falon ba shiri tace suje gida su shirya kansu mu dai bamusan ya aka qare ba bata
sake tada zancen ba ma"anty hauwa tace"ku kuma gaku sarakan gulma ba,kwaci
qaniyarku da ya kamaku kuna labe ai"
Duka wunin ranar bunda ke cin zuciyar fadila kenan zancan tafiyar yayi masifar daga
mata hankali,sai ta rasa nutsuwarta gaba daya,lokaci lokaci qwalla kan taru a
idonta ta faki idon mutane ta matse ta,gaba daya sai kuzarinta ya ragu,Allah Allah
take su kebe da farida,bata tsammani alkhairi aliyyu ke nufi da tafiyarsa da
ita,nufinsa ma fa kenan gaba daya tabar aikinta da take masifar so ta kuma fara jin
dadinsa yake kuma debe mata kewa?sam ba zata iya wannan tsari nasa ba
Sai bayan sallar isha'i ta samu nasarar tadda farida cikin bedroom dinta zaune
gefan gado tana canzawa baby da taci sunan maman mubarak wato(aisha
humaira)pampers ta zauna itama a gefan gadon tana duban pampers din da faridan me
sawa humairar ,da fara'a farida ta juyo a fuskarta tana duban fadila zata dan
tsokaneta sai fara'ar ta janye sakamakon qwalla da ta gani tana bin kumatun fadila
tayi hanzarin sauke humaira da ta aza akafadarta tana cewa"lafiya sister?"tamkar ma
ta tunzurata sai hawayen suka dadu
Tafin hannunta take sawa tana share su da nufin tsaidasu saidai turereniyar fitowa
ma suke abinsu,sai da farida tasa hannayenta ta kamo hannayen fadilan ta sa cikin
nata sannan ta sake tambayarta,da qyar kuma cikin muryar kuka fadila ta bude
bakinta tace"yanzu tsakani da Allah abinda aliyyu kemin yana kyautawa?"tayi
tambayar wasu hawayen sabbi na shirin sake zubowa,farida ta sake fuskantarta a dan
kidime tace"meke faruwa sister me ya miki?"ta girgiza kanta cike da damuwa"wai
china zai dauke ni mu tafi har kuma na tsawon wata hudu
Sai farida ta sake ta hadi da sakin dariya tana tafa hannu"🤔yanzu sister fadila
wannan abun farincikin kikewa kuka kamar wata teddy?"fadila ta katseta"ba zaki
fahimta ba farida kwata kwata wata na nawa da soma aikina?"farida ta sake
dubanta"😏aikin banza sister fadila,ga inda zaki samu aljannarki kike zancan wani
aiki"sake girgiza kai fadila tayi"still farida baki fahimceni ba,zan gaya miki
abunda babu wanda yasan yana faruwa sai ke,har yau sister aliyyu bai sona,aliyyu
bai qauna ta kalma mai dadi bata taba hada ni da shi ba kallon arziqi bai taba
shiga tsakanin mu ba amfani na daya agunsa shara da girke girke tamakar wata 'yar
aikinsa tun muna kusa da iyaye kenan tun muna qasarmu kena ina ga nabishi can wata
uwa duniya mai kuma kike zaton zai faru a ni?"
Ga mamakin fadila sai taga farida tayi murmushi mai kaa da dariya sai fadila ta
saki baki tana binta da kallo tan tsammanin farida bata damu da halin da zata
tsinci kanta ba kenan ko yaya?,sai da ta gama dariyarta sannan tace"☺👏🏻bravo! bravo!
bravo!,wallahi aliyyu yayi miki gata ba da qarami ba"zaro ido fadilan tayi har ya
mamakin bai sake ta ba😳,ganin haka yasa farida ta kama kafadar fadila ta sake
juyowa da ita ta fuskanceta sosai,ganin yadda fadilan ta tsure sai ya sake bawa
farida dariya daga baya kuma sai ta dawo serious dinta ganin kallon sakarcin da
fadila ke mata,ta kuma kama hannunta sannan tace"ni na gano abinda qila ke baki
gano ba,kuma ba zaki gano shi ba yanzu,sister duk abin ya aliyyu koya nuna ko kada
ya nuna ko ya yarda ko kada ya yarda kina da muhammanci da wani tasiri a rayuwarsa
komai qanqantarsa koda kuwa ya qaryata hakan da bakinsa,sister a iya hangena da
tunani na na fuskanci cewa don kada ya aliyyu yayi missing girkinki ne baya so yayi
nesa da abincinki wanda yasan zaiyi wuya ya samu kamarsa nima shaida ce"ta qarashe
maganar cikin sigar tsokana wadda ta zame mata jiki
Ta nuna fadila da yatsa �sannan ta dora ke zaki canza wannan manufar ke zaki
sauyata da kanki,ke zaki canza wa aliyyu wannan lafazin nasa na bazai soki ba har
abada ki qaryata lafazin nasa ta hanyar nuna masa ba wanda *_yasan gobe_* sai
Allah,sosai ta gamsu da maganar farida dari bisa dari kaso sittin cikin dari na
damuwarta ya tafi,ta jinjina kai hadi da sakin ajiyar zuciya sannan tace"batun
aikina fa sister?" "So easy"inji farida ta gada tana murmushi😊"k8na iya daukar
excuse a gurinsu ki musu bayani tafiyar gaggawa ce ta sameki zuwa china zaki ajiye
aiki amma da manufar zaki je course ne na wata hudu,idan hakan bai samu ba su barki
a matsayin wakiliuarsu ta qasar china ta tsawon wata hudu" "great sister!"fadila ta
fada cike da farinciki,tabbas dan uwa na gari dadi ne da ahi gashi xikin 'yan
mintina qalilan ta warware mata damuwarta,ta rungume faridan tana cewa"thank you
sister ya barmu tare ya raya mana humaira"tace "amin Allah yasa kema ki samo mana
tsarabar dan china nan da wata tara ko goma mu dauki sabon baby " dariya sosai ta
bawa fadila tana jinta ne kawai
Sanda ta dawo gida yana zaune cikin balcony dinsa,tayi maza ta dauke kai gami da
qara sauri don ta shige shi
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari qarfe 6:40 pm ta dawo daga aiki sun gama settling komai da managing
director na express da freedom sai damuwarta ta sake raguwa qwarai da gaske,tana
toilet din falo tana wanka taji moysi kadan kadan a falonta,da sauri ta kammala
tana son taga waye don a bude tabar bangaren nata,kacibus sukayi da shi tsaye yake
tsakiyar falon yana sanye da kufta dark coffee wadda tasha aikin sarauta sai
hukarsa baqa abinka da fari sai yayi matuqar kyau kyansa da jaskensa ya sake fitowa
shigar ta amshe shi sosai fadila ta lumshe idonta tana jin wani abu na zagaya
jikinta"ki shirya na kaiki gida ki masu sallama,gobe zamu bi jirgin yamma insha
allah zamu wuce china"duk maganar nan da yake idonsa na kan wayarsa dake hannun
hagunsa damansa kuma cup ne cike da maltina mai sanyi🍺,ta dan langabe kai kamar
bata ji mai yace din ba"ina zamu je?""kaiki zanyi na siyar"ya fada yana ci gaba da
danne dannensa ta faki idonsa ta manna masa harar ta zagayeshi ta wuce zuwa bedroom
A sanyaye ta kammala shirinta cikin atamfa dinkin riga da zan8 simple style hakanan
fadila take bata fiya son abimda ya cika ado da yawa ko daukan hankalin jama'a ba
yadda take bata da hayaniua haka dabi'unta suke saidai idan ta so,ta lullube kanta
da wadataccen mayafi kalar kayan,ta jawo locker dintabta debo kudaden da suke ciki
ire iren kudaden da aliyyun ke basu ne duk qarashen wata da kuma na cefane acewarsa
tunda komai suna da shi a ajjiye hatta magi ba zasu buqata ba ta watsa su cikin
jakar sannan ta rataya ta ta fito,yana zaune a mazaunin driver tasan bata isa ta
shiga baya ba ko ya shiga zai maidoto ne gaba don haka ta bude gaban ta zauna,yadan
kalleta hadi da dauke kai ya daga glassan motar gaba daya samà ya rufe su ruf hadi
da kunna a.c,wani irin tuqi yake slowly tamkar baza'aje ba tayi tsammani zaiyi irin
tuqin nan nasa mai gudun tsiya,a hankali suke ratsa titi nan har suka qaraso cikin
anguwarsu fadila
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:50 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*part 2*
2⃣3⃣&2⃣4⃣
2⃣3⃣2⃣4⃣
A qofar gidansu yayi parking,bata ce masa komai ba kamar yadda bai tsinka mata
ba,ta bude murfin motar ta nufi bakin get din gidan cikin doki ta dan tsaya suka
gaisa da malam mai bude masu qofa idan zasu shige da motarsu
Parlour din babu kowa sai qamshin fresher da ya gauraye da na girki ,murmushi
fadilan tayi kai tsaye ta nufi kitchen cikin zuciyarta tana cewa"ummi na bakya
tsufa kullum gida kamar na budurwa" (haka haj amina take ma'abociyar tsafta ce da
gayu,don bata yarda wai don tana da manyan yara harda jikoki ta zauna haka ba,baka
raba qafarta da hannunta da jan lalle mai ado irin na yanzun wanda akeyi,hakanan
kullum kalolin girkinta daban ne masu dannkaren dadi hakan ne yasa yaranta sukayi
gadonta suma,tun aurensu ita da alhj abbas koda wasa bai taba tunanin qaro aure ba
donba cewarsa ta isheshi duk dashi qarin aure qaddara ce rubutacciya idan Allah ya
qaddaro maka sai kayi
Muhammad ta tarar ciki riqe da babban spoon na qarfe yana ta faman juya fried
rice,dariyar da fadila ta tuntsure da ita ita ta saka shi juyowa don bai ankara da
shigowarta ba sai lokacin,ya saki murmushi yace"anty fadila yaushe kika zo?" Ta
kama baki"🤔ina zaka san na shigo ka taqarqare kana ta jagwal gwalawa ummi abinci,wai
yaushe ma ka fara shiga kitchen?"ya saki spoon dinnyana share zufa a
goshinsa"😊 ni wallahi ma gwara da Allah ya kawomin dauki ,please anty karbi
girkin nan,haka yanzu ummi kemin ko ta daina sona ne ma oho?,amma don Allah anty
fadila ina ni ina wani kitchen?,wai gwara na iya tunda ku kun tafi saura ni da ita
kawai a gidan"dariya fadila ta sake saki ,ta qaraso kan girkin tana gyara wasu
abubuwa sai da ta hada komai ta rufe ta rage mata wuta don ta turara sannan ta
tambayeshi ya haye saman freezer yayi zamansa"ina ummi" "tana gun Abba yanzu ya
dawo daga kasuwa ne amma tunda an fara kiran sallah yanzu zaki gansu"
Yana rufe baki kuwa saiga dariyarsu cikin falo,da hannu Muhammad yayi mata nuni da
falon cikin salin gulma,dariya ma ya bata ta miqe da sauri ta isa falon,ita da
abban ne kuwa yana tsaye riqe da abun sallah ummin kuma na dauke da hularsa,da
murmushi suke kallonta ta durqusa ta gaida su abban na tambayarta yanzu take
tafe?,ta gyada kai yace masha Allah ya mai gidan?,tace abba tare muke yana
waje,"ashshsha banda abin fadila shima ai gidansu ne amma don sakarci kika barshi a
waje "ummi tayi saurin qwalawa Muhammad kira tace ya zo ya shiga da shi,abba yace
barshi naje na sameshi in yaso idan mun idar da salla sai mi shigo tare,a shirya
mana abinci kafin mu shigo din
Ummin ta dan rusuna tana miqa masa hularsa tace"insha Allah abban Muhammad a dawo
lafiya"ya karba yana dora ta a kansa yace "Allah yasa Allah yayi miki albarka"
cikin dariya yaran suka taya ta amsawa da amin
Sai da fadila ta taya ummin suka shirya komai kan dining sannan suka tafi yin
sallah ummi ta ahige dakinta fadila ma tsohon nata dakin ta bude ta shiga,bin dakin
tayi da kallo komai yana nan kamar yadda yake,dan fridge dinta na boye ice cream
'yar kwanar da take ibadunta,inda take boye kanta idan zatayi kukan Aliyyu,sai
komai yake dawo mata"Allah sarki" ta fada a fili tana shafa filonta da take cusa
kanta a qasansa ,qwalla ta dan taran mata a ido ta sa yatsanta ta dauketa,toilet ta
tura ta shiga ta daura alwala ta dawo inda ta saba yin sallarta tayi,bayan ta idar
ta duba kan mirror dinta powder ce kawai akai ita ta dauka ta sake gyara fuskarta
sannn ta mutstsika turare ya sauka qasan
Muhammad ne kawai zaune kan table din yana buga game a wayarsa ta zauna kusa da shi
hadi sa dan dukan kafadarsa,ya dago ya dubeta yana murmushi, "ka shiga aji nawa ne
har ummi ta yarda aka baka waya,cikin dariya yace "haba anty nafa zama senior ina
s.s one fa,kuma ma yanzu nine babba a gidan nan"dariya ya bata sosai tana cikin
darawar ne ummi ta fito,tuni har ta yi wanka ta canza shiga tayi kyau duk da ba
make up take yi ba,fadila na shirin tsokanarta tace tayi kyau sallamar abba da ta
aliyyu ta karade falon wadda ta yake hirar da suka so farawa
Abban ne a gaba aliyyu na biye da shi har suka qaraso dining space din abba ya fara
cewa da aliyyu bismillah kai tsaye taga yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna sai
tayi duru duru har rudewarta taso ta fito,ji tayi ya take mata qafa ta danji zafi
ta dago kai suka hada ido yayi mata alama da ido na ta nutsu,sannan ya duqar da
kansa ya gaida ummi cikin girmamawa,ita kuma ta amsa masa cikin kulawa tana
tambayarsa mutanen gidan
Fadila ita tayi serving kowa banda ummi don tasan ba zata ci ba,tazo kan aliyyu sai
ya rasa mai zata zuba masa idonta na kan warmer tace "mai zaka ci?" "Zuba min duk
abinda zaki ci" ya fada abunsa tamkar ba shi yayi maganarba,da sauri ta dago kai ta
kalleshi saboda wata kunya da ya bata amma sai taga shi ko ajikinsa,ta saci
kallonsu ummi sai taga hirar su ma suke da abba kamar basu san da su agun ba,sai
kawai ya zuba masa fried rice da farfesun naman kaza mai yawa tana son qureshi taga
zai cin?
Sai kuwa ya shayar da ita mamaki don abincinsa yake ci hankli kwance duk da baici
da wani yawa ba yafi shan lemo,bayan sun kammala ita ta kwashe kayan ta kaisu
kitchen ta hada ta wankesu kamar yadda ta saba tanayiwa ummin tun kafin tayi
aure,tana aikin cikin ranta tana gulmar aliyyu bai da kunya
Mrs Muhammad ce 
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
1:41 pm 29/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
2⃣5⃣&2⃣6⃣
2⃣5⃣2⃣6⃣
Abban ya jinjina kai yana cewa "kasan qasa ce mai tsari da doka ba irin namu
qasaahen ba da sai dai muce inna lillahi wa 'inna ilaihi raji'un,Allahbya taimaka
ali ya kuma yi jagora yasa a budeshi a sa'a,Allah yayi ma jagora a dukkanin
lamuranka"ummi na amsawa da amin yayin da shima yayi qasa da kansa yana cewa "ameen
ameen abba na gode Allah ya qara girma" yana shirin miqewa yasa hannu cikin aljihun
kuftanshi na riga ya zaro turare yan ubansu designers ya ajjiue wa abban,albarka
yasa masa tare suka qarasa miqewa abban zai masa tattaki kasancewar alhj abbas
mutum mai sauqin kai ba ruwansa da wai shi mai shekarune babba ne kowa nasa ne
Sai lokacin fadila ta janye idanunta daga kan aliyyu kallonsa tayi sosai don bata
taba ganin sa yayi doguwar magana irin haka ba,yanayin yadda yake maganar cike da
girmamawa sai ya sake burgeta ta sake lafewa jikin ummin tana saukar da ajiyar
zuciya,ummin ta kalleta sanda suka gama ficewa "au sake ma wani rabewa kike ajikina
ke da ake jiranki?" Dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki sai kuwa ta
saki kuka,ummin ta saki baki tana kallonta "wai wannan wane irin sakarci ne ko wata
matsala kike da ita?" Kai fadilan ta girgiza,ance tsakanin d'a da uwa sai Allah
hakanan sai tausayin gadilan ya kama ummin don yasan duk mace kimai jin dadinki
baki rasa matsala ta zamantakewar aure,a da rance take mata nasiha hadi da lallashi
Ganin hankalin ummin ya tashi sai tace cikin son kawar da hankalin ummi daga
tunanin ko tana da wata matsala tunda tasan halin iyaye yanzu sai ta fita shiga
damuwa"ummi bana son na barku ne har wata hudu" ta saku ajiyar zuciya tana godewa
Allah "idan banda quruciya irin taki fadila ko kina nan din ma basai ki kusa wata
biyu ma baki gan mu ba ummm.....kiyi addu'a kinji Allah ya kaiku lpy ya dawo da ku
lafiya kawai" tace amin tana share hawayen cikin dakiya
Ta zuge zif din jakarta ta fito da kudaden nan ta dorasu cinyar ummin,ummin ta
kalli kudin sannan ta dubeta "wannan fa na meye?" "Naki ne ke da abba" "ina kika
samo su fadila?yaushe kwata kwat kika soma aikin? Ina fatan ba roqonsa kike ba dai
ko?", ta girgiza kai "a'ah ummi shi yake bamu kullum idan zai fita" ta dauke kudin
ta ajjiye a gefe tana cewa "za'a dai juya miki zan bawa abbanki ko yayanki zasu san
inda zasu sa miki su" ta langabar da kai tace "don allah ummi to ko dan wani abu 👌🏼
ne ki cira aciki ke da abban ku samin albarka" ta bita da "to naji"
Idonta fal da hawaye zuciyarta a raunane ta fito ,suna tsaye jikin motar aliyun ta
qaraso ta tsugunna har qasa idanunta rau rau muryarta na rawa tana yiwa abban
sallama "to fadila Allah yayi muku albarka ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya,ki
zauna lafiya agidanki bana son fitina kada na ji kada na gani" tuni kukan ya qwace
mata "insha Allahu abba"kasa tashi tayi har sai da abban ya daga ta da
kansa,aliyyun ya zuba musu ido wani abu yaji ya taba ransa shi ya bude mata motar
Abban ya sata ciki da kansa,aliyun ya rufe qofar sukayi sallama da abba ya zagaya
ya shiga gun zamansa ya tada motar
Shiru cikin motar sai sautin kukanta danke tashi kadan kadan hadi da
sheshsheqa,burki taji yaja bayan ya gangara gefan tati ya kashe motar sannan ya dan
kwantar da kujerar da yake kai din ya kwanta rigingine idanunsa alumshe yana
sauraran sautin kukan,sai da suka kusan kwashe awa guda ahaka lokacin tuni har
kukan nata ya tsagaita,ya miqe a kasalance ya gyara zaman kujerar baice uffan ba ya
tada motar suka wuce
Cikin daren bata kwanta ba sai da ta hada duk abinda take da buqata cikin babbar
trolly dinta sannan ta kwanta zuciyarta fal da saqe saqe kala kala
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cike da kasala take janye da akwatin nata har ta iso bakin motar qirar sienna dake
fake a harabar gidan,yadine a jikinta mai sulbi blue 🔷 tayi rolling da red din
mayafi🔴🔵,sosai rigar ta bude daga qasa takalminta red ne hill sosai 👠,motar na bude
duk suna ciki nasiru na mazaunin driver aliyu na kusa da shi sai salima dake sit
din can baya bisa dukkan alamu ga fuskarta nan ta sha kuka,fuskar samira ba yabo ba
fallasa tana sit din tsakiya,yayin da fadila ta zauna a sit din farko nasiru ya
karbi troly din nata ya sanya a baya
Cikin hanzari nasiru ke ruqin aliyyu ya sake duba gaogonsa yace "nasiru qara sauri
zamu iya missing flight" ya sake qarawa motar gudu don bin umarnin ogansa
Ba dadewa suka isa aminu kano international airport nasiru ya ajjiye motar inda aka
tanada don ajiyar motoci,dukkaninsu suka fito daidai lokacin da airport din ta
karade da sanarwa neman masu tashi a jirgin ethopian airline,hakan ya tabbatar ma
da aliyu sun kusa makarar kam,tuni nasiru ya ciro musu jakankunansu,ya dubi samira
da salima da fuska take adinke musamman salima da takejin kamar ta dora hannu aka
ta zunduma ihu,"sai na dawo" yace kamar mai jira salima ta fashe da kuka ta taho a
guje ta fada jikinsa,ya saki dan qaramin murmushi hadi da sa tafin hannunsa yana
dan bubbuga bayanta alamar rarrashi,ya miqawa samira daya hannun alamar ta
taho,dauke kai tayi tana turo baki zuciyarta babu wani takaici sosai Idan ta tuna
da maqudan kudaden daya barwa kowaccensu tasan zasu sha bushasha don ma yayi misu
gqrgadi da jan kunnen akan fita"sai ka dawo"tace kawai,ya dan janye salima daga
jikinsa sukayi sallama da nasiru,ya wuve fadila ta rufa masa baya saluma ta bita da
harara kamar ta fincikota,batasan itama fama take da fargabar bin aliyyun ba
Reception suka wuce suka qarasa departure ta farko suka shiga layin screening,aka
kammala da su aka basu boarding pass suka qara gaba,immigration suka sake duba visa
dinsu suka buga musu stamp suka shiga dan dakin jiran jirgi,mintina qalilan jirgi
yayi ready suka bi layin shiga jirgi tana gabansa yana tsaye a bayanta
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:51 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*part 2*
2⃣7⃣&2⃣8⃣
2⃣7⃣2⃣8⃣
25 and 26 ne number din sit din nasu don haka sune maqotan junansu,aliyyu ya daga
yar trolly din da aka barsu suka shigo da ita saboda kilo din ba wani mai yawa bane
ya sanyata a inda mayafiyan ke ajjiye jakankunan nasu,yan kallo fadila nata
kiciniyar sanya tata saboda ta dan yi mata nauyi,sai da ta soma gajiya sannan ya sa
hannu ya janyeta ya fada kan kujerarta ya daga trolly din tata ya sanya mata ya
koma sit dinsa ya zauna yana gyara zaman suit din jikinsa
Kowa ya zauna a mazauninsu,fadila na bakin window ta zubawa filin airport din ido
tana fargabar yadda jirgin zai Lula da su sararin subhana duk da yawansu kasancewar
wannan shine shigarta jirgi na farko a arayuwarta
A hankali aka zare matattakalar aka maida qofar jirgin aka rufe bayan sun gama duk
wasu yan tsarabe tsarabensu suka bada sanarwar daura belt,fadila ta jawo belt din
saidai bata san yadda zata sata ba,tana satar kallon aliyyu ta gefan ido yana daura
tasa,ya kammala ya fito sa laptop dinsa ya dora bisa cinyarsa
A hanakali jirgin ya soma qugi hadi da shawagi a doron qasa na kimanin minti goma
sha biyar sannan ya yunqura don rabuwa daa doron qasa,fadila ta runtse idonta
saboda wani tsoro da ya kamata,ta qanqame belt din dake hannunta wadda ta kasa
daurawa jin jirgin na niyyar dawowa qasa ya tarwatse da su😂😂😜😜 lol har naga
idon masu karatu aliyyu salim mai tama da fadila zasu mutu
Ta qanqame belt din dake hannunta jin tana niyyar subucewa daga kan sit din
ta,cikin zafin nama aliyyu ya kareta da hannunsa sannan ya amshe belt din ya
zagayeta da hannayensa ya daura mata hadi da cewa "silly girl" ya gama ya koma kan
danne dannen da yake kan laptop abinsa ba tare da ya sake dubanta ba,a dan sace ta
harareshi gami da jan dan siririn tsaki ,ya juyo da sauri don tsakin kunnuwansa
sukaji kamar tayin da azama ta dauke kanta ta maida window Allah ya taimaketa basu
hada ido ba sai ta waske
Tafiya ce ta awa hudu ta saukesu a *ethopia* don musayar jirgi cikin babban birnin
na *ethopia* wato *addis ababa*,ba kwana zasuyi ba amma saida aliyyu ya kama one
room apartment cikin hotel din dake kusa da airport din,tamakar kazar da qwai ya
fashewa a ciki ta nemi gefan kujera qwaya daya dake cikin dakin ta zauna a
takure,sallar magariba da isha'in da bata yi bane ke damunta amma duk a takure take
bare tayi azamar tashi
Tana kallo ya dora jakarsa kan gado ya tube takalminsa 👞 da socks dinsa ya shige
toilet,motsin ruwan da ta ji yasa ta raya alwala yakeyi
Kusan minti arba'in ya fito sanye da rigar towel mai budadden qirji👘,kallo daya ta
masa ta dauke kai tsigar jikinta na tashi 😣,gashine kwance luf a qirjinsa baqi
sidik tamakar wanda ake sawa relaxer kamar yadda na hannayensa da qafafunsa suka
kwanta saboda ruwan da suka sha,ta sake runtse ido gabanta na dan faduwa💔 da alamu
ma shi ko ajikinsa don goge sumar kansa yake da dan qaramin towel dake riqe a
hannunsa
Ganin ya soma kunce dan zaren da ya taimaka wa rigar ta rufe jikinsa ya sata yin
azamar afkawa toilet,ta dade numfashinta na kaiwa da kawowa wani abu na mata yawo a
jiki sannan ta iya daura alwalar ta fito,ta cimmasa tuni ya har ya tayar da tasa ta
koma gefe ta kalli inda taga ya kalla ta tayar da alama nan ne alqibla har ta
kammala tata ta zauna tana lazumi lokaci lokaci tana satar kallonsa har ya sallame
Shirye yake a yanzun cikin jacket masu kalar green da black sabanin dazu da yake
sanye da suit baqaqe kullum aliyyu cikin sa kaya yake sabanin wadanda ta sanshi da
su,kusan ma zata ce bata taba ganinsa yayi maimaice ba,yana zaune saman qafafunsa
ya kammala addu'arsa ya shafa ya miqe tayi saurin yin qasa da kanta don kada su
hada ido tana yiwa Allah tasbihi saboda kyawun da taga yayi mata har ya juya ya
fice
Fitarsa ba dadewa daya daga cikin ma'aikatan hotel din yayi knocking ya shigo mata
da abinci fried spaghetti ce da roosted chicken sai drink da ruwan gora mai sanyi
duk da cewa akwai su cikin fridge dake dakin,babu abijda ta iya ci sai lemon da ta
sha
Saman kujera ta nade ta janyo wayarta ta kunnata wadda tun shigarsu jirgi ta
kashe,babu service da ya hau saboda ya fita daga inda yake da amfani ,ta danna
power off ta kashe don bata da wani amfani ta maida kanta ta kwantar a hannun
kujerar
A hanzarce ya shigo ya dauki jakarsa 💼 ya juya yana cewa "let's go"ta miqe ita ma
ta dauki tata👜 ta bi bayansa
🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*_CHINA (SIN)_*
*_guangzhou airport_*
Qarfe hudu ⏰ na yamma da minti ashirin a agogon qasar china qarfe sha daya da minti
ashirin agogon Nigeria suka sauka a qasar,iyakar gajiya fadila ta yita,tafiya ce ba
kadan ba tamkar ta yada shege zama ne na awanni kimanin goma sha biyar a jirgin
wadda bata taba tafiya makamanciyar ta ba
Da qyar take daga qafarta da tayi mata taruwar jini saboda tsabar zama,suka sake
bin layin screening immigration suka karbi passport suka kuma duba visa dinsu don
tabbatar da cewa sun samu izinin shigowa qasar tasu,bayan sun tabbatar da
ingancinta suka buga musu stamp suka wuce
Sauran kadan aliyyun ya bace mata saboda ta lura cike yake da kuzarinsa tafiyarsa
yake kamar baiyi wata doguwar tafiya ba bisa dukkan alamu ya saba da irin wannan
tafiyar,motar ce mai azqbar kyau da daukan hankali tayi parking gabansu mutum uku
ne suka fito dukkaninsu sanye da coart baqaqe baqin space da baqin sau ciki😎,cikin
girmamawa suka iso inda aliyyu yake biyu daga ciki suka miqa masa hannu sukayi
musabaha,cikin harshen nasara suka fara gaisawa dayan dake gefe ya dauki
akwatinansu ya sanya a bayan motar
Bayan ya ruge boot suka dunguna gun motar fadila ta bisu a baya,ita da shi na sit
din tsakiya biyun kuma na sit din can bayan driver din kuma ya shiga mazauninsa ya
tada motar,hira suke abinsu da aliyyu yayin da hankalin fadila ya kasu biyu,daya ta
dora shi ne bisa ga aliyyu yadda yake turanci kai sai ka ranyse
  
[10/16, 1:52 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?..*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*part 2*
2⃣9⃣&3⃣0⃣
2⃣9⃣3⃣0⃣
A hankali motar taci gaba da kutsawa cikin cikin kyakkyawan shimfidedan titin har
suka shigo cikin wata kyakkyawar unguwa mai tsafta da tsari wanda tafiyar fadila
tsakanin airport da inda suke yanzun ta fuskanci haka unguwanninsu suke,basu yi
wani nisa a layukan da suke wucewa ba suka sa signal suka gangara wani layi,sun
kusa kaiwa qarshen layin driver ya faka qofar wani dan kyakkyawan gida dake yanyame
da shukoki daga gaban gidan kuma grass carfet ne to kusan ko wanne gida dake layin
haka yake left to right
Driver din ne ya fito ya bude musu qofa sannan ya bude boot din ya fitar da
kayansu,Aliyyu ya ciro keys daga aljihun cikin rigar suit dinsa ya miqa masa ya sa
hannu ya karba ya nufi gidan ya bude,ya shigar da kayan sannan daga bisani shima ya
shiga
Tun fadila na tsaye har ta gaza jure tsaiwar ta maida bayanta ta jingina jikin wata
'yar bishiya dake dashe a gun,shi kam tsaye suke qyam jikin motar shida lukas da
andi suna ci gaba da hirar kasuwancinsu cikin harshen nasara,jifa jifa tana tsintar
wani abu wani abun kuma ya kuce mata idan tunani ya rinjayeta,tsayuwar awa guda cif
sannan ya fito ya qarasa shigar da ragowar kayan da bai dauka ba ya kaisu ciki,ya
dawo cikin girmamawa ya ya miqawa aliyyu maqullan ya karba yana tambayarsa "have
you finished?" Ya gyada kai gami da cewa "yes sir everything is ready"ya girgiza
kai yana cewa "well done"ya juya gunsu andi da lukas ya basu hannu sukayi musabaha
gami da sallama ya juya ya nufi cikin gidan su kuma suka shige motar driver ya jasu
suka bar gun a kasalance ta rufa masa baya zuwa cikin gidan
Falone wanda ba za'a kirashi qato can ba hakanan ba zaka kirashi da qarami
ba,saidai yadda ya tsaru dole ya qayatar da kai ta yadda zaka iya fin sha'awarsa ma
fiye da wani qaton,kujeru ne set guda yan madaidaita masu azabar kyau sai labulaye
na alfarma da suka kewaye falon ta yadda baka iya bambance ina qofa take center
carfet center table da wasu yan qanana dake maqale tsakanin kujera da kujera
tafkekiyar plasma TV da home theater dining area mai dauke da dining table mai
kujeru hudu komai na falon fari ne tas sai wasu abubuwan masu sirkin baqi
kadan,qofofine hudu cikim falon daya kitchen ne sai store sai public toilet sai
bedroom,komai tsaf yake kuma qal qal ta tsammaci hakan dama idan tayi la'akari da
dan karen son tsafta irin na aliyyu
Fadila ta zabi daya faga cikin kujerun tayi saurin zama saboda yadda take jin
gajiya na nuqurqusarta har cikin qashi ji take tamkar ba zata iya daga koda
yatsanta ba,tana nan takure kan kujerar tana satar kallonsa,gaba daya sanyin garin
ya soma takura ta tun yanzun,ga bashin sallah dake damunta tunaninta daya ta ina
zata soma iya taba ruwa da wannan azababben sanyin?
Key yasa ya bude dukkanin qofofin ya tura daya wadda a samanta aka rubuta da wani
dan siririn katako mai kyau *bedroom* ya shige,ta miqe itama a gajiye ta shiga
public toilet cikin sa'a ta tadda a kwai heater kunna ta tayi ruwan ya dan yi zafi
sannan ta kunna famfo na zafin da na sanyin ta saisaita su yadda zai mata dadin
alwala,falon ta dawo saidai bata san ina ne gabas ba don haka ta kintaci inda taji
hankalinta ya fi karkata ta tada salla
Cikin sabon shiri yq fito yana sanye da jibgegiyat rigar sanyi mai gashin dabba
daga ciki trouser ne da long sleeve shirt duka baqaqe kansa hular sanyi ce ta gashi
mai azabar kyau qafafunsa boot ne mai dan tsawo ya sanyawa hannayensa safofin
hannu ya saye idanunsa cikin gilashin nan nasa na ko yaushe👓 cikin hanzari ya fito
da niyyar fita don sama musu abinda zasu ci idanunsa ya sauka kanta tsakiyar centre
carfet din dake tsakiyar falon ta cure guri guda
Ya san sanyin garin ne ya soma addabarta shi kansa da ya saba zuwa abroad cikin
irin wannan yanayin wannan karon sanyin ya dameshi balle ita da bai tsammanin ta
yaba zuwa,ya dawo da baya a hankali ya isa ga makunnin na'urar dumama daki ya kunna
ta ya sake juyawa ya zuge gami da rufe duk wasu qofofi windows da labulaye dake
abude na gidan sannan yasa kansa ya fice hadi da sa key ya kulle gidan
Wanka a qa'ida take da buqatar yi da ruwa mai zafi don ta samu ragowar gajiyar ko
zata sake ta amma rashin ganinsa afalo yasa take tsammatar yana bedroom din,kasa
kunnenta tayi sosai bata jo motsin kowa ba don haka ta miqe akasalance,cikin sanda
ta tura qofar bedroom din ,babu kowa ciki daki ne babba yalwatacce ba wani tarkace
cikinsa cupboard ce sai dressing mirror hadi da dressing chair sai sofa qwaya daya
madaidaicin gado ne mai rumfa wanda aka kafashi daga jikin window sai center carfet
da center table daga gaban gadon kenan,komai na dakin shima farine kamar dai falon
hatta da kalan furniture din zuwa ga bedsheet
Ta sako kanta ciki bayan ta tabbatar babu kowa akwatunansu na saman gadon a ajjiye
nashi akwatin ne ta gani a bude kayan sun dan hargitse kadan da alama ya bude ne ya
debi wasu abubuwa,gefe ta zauna ta fiddo da duka kayan nasu ta shirya su cikin
cupboard,nashi ne auka cinye fiye da rabinta ta tsaya tana kallon yadfa kayan suka
tsaru ita kanta sun burgeta ta karkade hannayenta ta rufe qofofin sannan ta shige
toilet din bayan ta ciro kaya kala daya da zata sanya
Ta fito daure da towel wanda ya sauko mata qasan gwiwarta yayin da ta yafa qaramin
saman kanta tana goge ruwan da ya dan taba mata shi da wanda ya shigar mata
kunne,sam bata yi tsammanin ya shigo dakin ba shi din ma haka yana zaune ne kan
bedside hannunsa riqe da lemon kwali yana dan zuqa kadan kadan ,gabanta ya fadi
sosai don ta tsorata da ganin nasa,da azama ta juya don komawa toilet din garin
haka towel din kata ya zame ya fadi qasa kanta zuwa kafafunta suka fito
sarari,gashinta ya kwanta luf bisa dan dogon wuyanta zuwa gadon bayanta wanda ruwan
da ya tabashi ya sake sashi kwanciya,da sauri ya dauke qwayar idanunsa ita kam ko
ta kan towel din bata bi ba ta koma hadi da tura qofar
Ta hudar dan maqulli take leqensa tana gani ya daga lemon maimakon shan ganin dama
irin na dazu dai taga ya daga kwalin bai sauke ba saida ya daddake shi tas sannan
yayi cilli da kwalin yayi qas da kanshi yafi Minti guda ahaka sannan ya miqe da
sauri ya five a dakin,sai da tabbatar ya fita sannan ta fito da sauri ta sawa qofar
key sannan ta shirya cikin doguwar riga mai dogon hannu cotton ce sosai ta yane
kanta da mayafi ta duba jakarta don dauko turarenta na shamsul imarat da blue lady
Kuyi haquri da aliyyu kudai kuci gaba da bina komai daki daki yake a rayuwa
Na gode🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Mrs muhammad ce 👑
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:53 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*part 2*
3⃣1⃣&3⃣2⃣
3⃣1⃣3⃣2⃣
Ta dade a tsaye tana takaicin rashin sako turaren nata da batayi ba don gaba daya
tayi tsammanin ta sako su,taja tsaki yafi a qirga ita ba sanin gari tayi ba
hasalima yau ta soma shigowa qasar ko da ta sani din ma ai dole sai dai ta yiwa
aliyyu magana wadda ita kuma hakanne bata so,to idan kuwa haka ne bata da zabi illa
saka wannan turaren tunda sam bata son zama a rayuwarta ba tare da taji jikinta na
tashin qamshi ba haka take qamshi a jininta ya ke,ai shima wannan din turarene,sam
fadila ta mance aikinsa tama manta a inda ta sayeshi tunda abun bai gabanta tunda
ta wulla shi a jaka ta manta da babinsa
Ta kammala shafawa tana lumshe ido gami da cewa "hmmmm" saboda yadda qamshin nasa
ya yi mata dadi sosai,qanshi ne mai sanyi ya karade jikinta da ma dakin gaba
daya,ta maida shi cikin jakarta ta rataye jakar a abun rataye jakankuna ta jawo
qofar dakin ta dawo falo,yana zaune a gaban laptop dinshi (agogo sarkin aiki
😏)cewar fadila cikin zuciyarta,aliyyu hardworking person ne komai yasa a gabansa
yakan zama serious akai har sai ya kai ga cimma burinsa,yana jin fitowar tata amma
bai daga kai daga abinda yake ba bare ya dubi sashenta
Sannu a hankali qamshin ya soma karade falon ya soma kuma fisgar hankalinsa,ya rasa
daga inda qamshin ke fitowa,sannu sannu kasala ta soma rufeshi idanunsa suka soma
lumshewa,ya daga kansa ahankali ya dubi sashen da take waya ce a hannunta tana
danne dannenta saqonni take dubawa da suka shigo mata,ya maida ido runtse sosai
yana qaryata kanshi game da feelings din da yake ji,ya sani tun usul haka
halittarsa take yana daga cikin mabuqata,gaba daya ya mance da wannan matter din
sanda zai taho aiki ne kawai a gabansa da kuma tsaftar inda zai zauna da abincin da
zaici
Cikin lokaci kadan mood dinsa ya canza sosai he needs something really, idanunshi
sun jima a rufe aikun da yake ya gagareshi saidai still mood din da yake ciki bai
canza ba,ya sake kallonta karo na biyu bata san ma me ake ba har yanzu wayarta na
hannunta tana latse latsenta,"take dis bags ki samin nawa a plate ki dauki naki
Juyowa tayi don jin muryar tamkar ba tasa ba,amma sai taga latse latse yake bisa
laptop idanunsa na bisa screen din,bata ce komai ba ta ajjiye wayar a gefanta ta
debi kayan ta shiga kitchen,shawarma ce da Chinese spaghetti sai roasted chicken ta
saka kowanne a aplate din ta hada masa da ruwa da lemo ta jawo dan side table
gabansa ta dora masa akai,zuwanta gabansa ya sake sa qamshin ya cika masa hanci,ya
sake runtse idonsa hadi da qanqame hannayensa gu guda cikin wani irin lust
moode,sam bata lura ba ita dai ta kammala hada masa ta dauki tata ledar ta koma
mazauninta,duk yadda ya kai ga son cin abincin haka ya dinga tsakurarsa a kasalance
girman kai kuma ya hanashi ya sake koda duban sashen da take
🔅🔅🔅🔅🔅
Ta sake duban agogo karo na uku kenan sha daya da rabi na dare🕦,tuni bacci ya sake
cika mata idanu kamar ma batayi shi dazun ba duk da dama ba wani jimawa tayi ba ta
farka,tunaninta daya ko ina makwancinta? Tasan dai ko giyar wake ta sha bata tafiya
kai tsaye su hada dakin kwana da aliyyu ba bare ya yarfata
kasa daurewa baccin da take ji tayi saboda haka ta ware mayafinta ta lullube
kafadarta zuwa qafafunta ta ja filin kujera qwaya daya ta tada kanta da shi tunda
shi kam lura aikinsa yake tuquru hadi da amsa kiran dake ta shigo masa wanda dukka
da harshen turanci yake maganar hakan ya tabbatar mata yan qasar ne masu
kiran,batasan yayi hakanne bane ko zai samu feeling da yake ji ya sake shi shi uasa
ya takura kansa da aiki,ba abunda yake sai faman dirkawa cikinsa coffee flask guda
ta hada masa amma ya kusa tafiya abun har yaso bata tsoro
Tsaye yayi a kanta baccinta take sosai,bai taba qarewa fuskarta kallo ba irin
yau,gashin gaban goshinta ya sake kwanciya kamar relaxer ta shafa masa komai nata
medium mai kyau tamkar ma ba baccin take ba,a hankali abun nan da yake son ya danne
ya ci gaba da taso masa,ya tabbatar idan yaci gaba da kallin nata a yanayin da yake
ciki din nan zai iya aikata abinda yame ganin ita din ta masa kadan ta iya
daukarshi gane yake zai iya nakastata,ya janye ida nunsa daga kan fuskarta yana
maida numfashi,yasa hannunsa ya zare filon da take kai kanta ya sauka saman kujerar
Firgigit tayi ta farka don ta dan tsorata ya kalli idanunta wadanda bacci da ta
soma da tsoratar da tayi yasa su sukai wani kyau ya dauke kansa gefe guda zuciyarsa
na dan bugawa da sauri, ganinsa tsaye bisa kanta yasa ta dan sukuyar da kanta "idan
kinga dama ki koma bedroom ki kwanta"ya fada yai gaba hannunsa dauke da cup da
flask din tea
Ta dauki a qalla minti talatin a zaune tana doubting din aliyyu ne kuwa ma ya
tasheta?idan shi din ne ma ya zata iya kwana daki guda da aliyyu? Aliyyun da yaqi
jininta? Bai sonta bai qaunarta?,wani benefit nata kawai yake so tayi masa girki da
shara ba wai ainihin ita fadilan ba,ganin babu mafita ga wani sanyi da yake
sirarowa falin saboda kashe na'urar falon da yayi ya sanyata miqewa jiki a salube
ta njfi bedroom din
Kamar wata munafuka ta tura ta shiga,ga mamakinta yana kwance ne aqasa saman dan
qaramun carfet din nan na gaba gado mai dauke da center table ya sauke center din
shi kuma ya maye gurbinsa,trouser ne kawai ajikinsa da singlet,yayi ruf da
ciki,hannun hagunsa da damansa duka pillow ne ya jajjerasu ya kuma matsesu
ajikinsa,faffadan bayansa mai cike da siffar qarfi ya bayyana,ta dauke kanta cikin
sanda ta zagayeshi gami da hayewa kan gadon tana mamaki cikin ranta shi kam wannn
baijin sanyin garin nan ne?
Ga kuma sofa a dakin doguwa amma bazai hau kai ba?bata da courage din da zata
magana don haka ta maida gulmarta ciki ta tattara tafukan hannayenta tayi addu'ar
bacci ta shafe ilahirin jikinta da ita ta jawk bargon ta rufa tayi matashin kai da
hannunta kasancewar duka filon dake kan gadon aliyu ya kwashesu zasu taya shi
kwana😜😜
Idanunta fes a kansa tana gain yadda yake ta mutsu mutsu cikin ranta take
munafuncin haka yake wai baccinsa ne shi,tun tana kallonsa har bacci ya rufe idanun
nata,taso tayi daddan bacci mai tsawo a a lokacin saidai saidai hakan ya gaza
samuwa don ta tashi yakai sau nawa saboda rashin sabo duk kuma tashin da zata yin
idanunta na kan aliyyu sau uku tana ganinsa yana canza gurin kwanciya ana hudu ne
ta ruskeshi yana qiyamul laili tuni ta miqe don ita din ma lokacin tashi yin tata
sallar yayi
Aliyyu na bisa darduma yaga tashinta a zatonsa fitsari zata yi sai yaga bayan ta
fito ta tayar da sallah shi da zuciyarsa yaje gulmar isha'i ne bata yi ba kota
tsammaci asuba ce tayi?,shi kadai ke kida da rawarsa ita kam ta kafu gaban
ubangiji,har ta idar idanunsa na kan fejin qur'anin dake hannunsa yana karantawa
yana shafin qarshe ne cikin suratu anbiya'i,kusan yare suka sake miqewa suka tada
sallar asuba kowa yayi tasa,yana so ya samu falalar jam'i sai dai girman kansa
bazai barshi yayi mata tayi ba,bata jima da soma azkar dinta ba bacci ya sureta ko
gamawa bata yi ba
🔅🔅🔅🔅🔅
Sanda ta farka ta duba agogon dake ajjiye kan side drawer tayi mamakin yawan baccin
da tayi,ta yunqura da niyyar tashi sai ta ganshi shima kwance kan abun sallarsa
yana baccinsa cikin nutsuwa da alama shima surarsa yayi bai shirya ba kamar yadda
yayi mata,ta dan zubawa kyakkyawar fuskarsa ido wanda da idonsa biyu bata isa ba
🙊,fuskatsa tayi mata kyau tayi wani fresh,ta dan girgiza kai ta miqe tsaye ta soma
gyara gadona a nutse cikin taka tsantsan don kada ta sheshi sai da ta kammala tayi
mopping ta wanke bandaki duk da baiyi komai ba ta sake kintsa falo,ta koma ta buda
jakarta ta fiddo da turaren wuta ta jona abun turaren wuta mai amfani da wutar
lantarki ta zuba cikin qanqanin lokaci gidan ya dumame da qamshi har ya leqa moqata
ma,cikin sanda ta koma dakin gadon tayi saurin shiga wanka tun kafin aliyyu ya
farka ta kasa sakewa
Shigar shadda tayi pink dinkin riga da skert ne sun mata cif sun zuna das ajikinta
babu inda yayi kwarara kai ka rantse a jikinta aka dinka su,hida lip glosses sai
kwalli kawai ta saka ta taje dogo kuma baqin gashinta ta kameshi da ribbon pink,ta
ware dankwalinta tayi daurinta na zamani wanda ake sokeshi(ture kaga tsiya)hakan ya
bawa jelar gashin nata damar zubowa ta qasan daurin,rigar sanyi ce wadda ko ciki
bata rufe ba mai gashi dogon hannu ne da ita ita ta sanya light blue,ita kanta sai
da ta juya ta sake kallin kanta duk da ba wani make up tayi ba amma ta zuba kyau
ta dauko turarenta ta shafe lungu da saqo na jikinta,har ga Allah tana jin dadin
qamshin turaren yayi mata ta maida shi sannan ta koma kitchen din shirya break
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:56 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?..*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*part 2*
3⃣3⃣&3⃣4⃣
3⃣3⃣3⃣4⃣
Tun acikin baccin ya soma jin qamshin na ratsa qofofin hancinsa,duk zuqar numfashi
daya da zaiyi yana zuqarsa ne tare da qamshin,qamshin yayi masa,tun yana tsammanin
ko amafarki ne har ya soma gasgata cewa a zahiri ne ido biyu ne,sannu a ahankali
idanun suka ci gaba da buduwa ya soma zagaye dakin da idanun nasa ,ko ina fes sai
qamshin turaren wuta ke tashi da na wannan turaren nata da har yanzu ragowar
qamshin bai bar dakin ba
Komai na dakin a kintse neat " I like it" ya fada can qasa,hakan yakeso ko da wani
lokaci area din da yake rayuwa ta kasance,ya dan miqa hannunsa ya jawo wayoyinsa da
ya dora kan center ya duba agogo,lokaci ya gani ya ja sosai din kuwa qarfe goma sha
daya agogon china qarfe shida agogon gida nijeria,ya duba call logs nan ya tadda
missed call na mr lin,babban dan kasuwa ne dan qasar china saidai sananne ne a
qasashen duniya hakanan yana da companies anan gida nijeria sai missed call din
andi biyu sai na salima guda biyar da ya biyo baya,duka baiji ba don a silent wayar
take mantawa ma yayi bai kasheta ba don baya kwana da waya a bude saida babban
dalili
A hanzarce ya miqe ya watsar da fulallukan da yake kai ya nufi toilet,as usual tun
a gida a nan ma haka ya tadda ruwan wanka ready cikin bathtub shigewa yayi kawai
abinsa,mintina talatin ya kammala wankan a gurguje ya fito ya shirya kansa cikin
baqaqen suit harda baqar safar hannu saboda sanyi sunyi matuqar haska farar fatarsa
yayi kyau kamar wani bature tabbas aliyyu badai kyau ba
Da hanzarinsa ya wuce kitchen kai tsaye kamar yadda ya zame masa aladarsa shan ruwa
cup guda da safe kafin yaci komai,tun daga falon qamshin girki ya
😋
marabceshi,hancinsa ya bude sosai yana sheqar qamshin son ransa,cikin kuzari ya
qarasa kitchen din tana tsaye gabn gas tana kwashe chips don shi kadai ya rage mata
dama ta kammala,bayanta yake bi da kallo tayi kyau kamar wata 'yartsana don kayan
sun mata cif cif ajiki ya bi gashinta da kallo wanda ke reto a bayanta sai ya
tsinci kansa cikin birgeshi da hakan yayi don shi kam ma'abocin son gashi ne tun
yana qarami,ya dauke idonsa ya maida kan freezer bayan ya budeta yana jawa kansa
kunne
Sam bata san da shigowarsa ba qarar rufe freezer din ita ta ankarar da ita,ta dago
ta dubeshi yana shirin ficewa ya dan lumshe idanunsa sanda yake qoqarin barin
kitchen din saboda feeling da yake ji sosai irin na jiya da ya hanashi sukuni da
bacci mai dadi,bata ce komai ba ta biyo bayansa,har ya samu hannun kujera ya zauna
numfashinsa na fita da sauri da sauri,cikin hanzari ya balle hancin gorar ruwan ya
kai bakinsa ya soma daddaka
Bai ajjiye ba har sai da ya shanye tas ya wurga robar cikin dust bin dake kusa da
shi yana maida numfashi bayan ya rufe idanunsa
"Your breakfast is ready"yaji muryarta kusa da shi tana fada,a hankali ya bude
idonsa bai ganta ba don tuni ta wuce sai ragowar bayanta da ya gani sanda take
qarasa shigewa kitchen,bai sake komai ba illa wucewa dining da yayi don gwada cin
abincin
Ta zuba masa komai hatta tea ta hada masa a cup ya sanya cokali yana motsa
shi,mamakin kanshi yake yana kuma tambayar kanshi *meke faruwa?* da shi,ta fito
daga kitchen hannunta dauke da dan qaramin cup data hada black tea☕ta zauna cikin
falon tana kurba a hankali qamshin ne yaci gana da buwayarsa ta hanyar iska dake
kado mishi shi
Ya maida hankalinshi kan tea dinsa yana kurba kadan kadan,comfortably yake jin
zamansa kan dining din shi daya,ya debi chips da pork ya kai bakinsa yana ci gaba
da monitoring movement dinta da idanunsa,"hey" taji yace ta dago da kanta ya dan
dago hannunsa ba tare da ya dubeta ba"come here"ya kirata sai taji ban barakwai,ta
ajjiye cup din hannun nata a hankali ta qarasa dining din,ya sake kurbar tea din
idanunsa na kan ruwan tea din da yake sha "sit" yace da ita,ta ja kujerar gami da
kasa kunne tana sauraran mai zaya ce mata
Har ya ja kujerarsa baya yana niyyar tashi don ya tabbata ya sake qara wasu mintina
a gaba bai bar gun ba tabbas bazai iya mallakar kansa ba,abunda yake ji a cikin
gangar jikinsa is very strong feeling,yana so yace ta daina amfani da perfume nata
amma girman kai ya hana, yana ganin idan ya fadi mata zatayi tsammani ya damu ne da
wani abu nata,he feel he can sustain whatever zaici gaba da ji,wayarsa da ta soma
kadawa cikin tattausan ringing ita ta dakatar da shi daga tashin da yayi niyya
Mrs muhammad ce 
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:57 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?..*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*part 2*
3⃣5⃣&3⃣6⃣
3⃣5⃣3⃣6⃣
Ya ciro wayar ya duba mai kiran ya dan saki ajiyar zuciya kadan sannan yayi
pressing ok,sunan da taji ya ambata ya sata gane da wadda ya ke wayar,salima
ce,hira take yi masa sosai yana dan biye mata,hirar da tasa fadila kasa jure zaman
gurin ,satar kallonsa take ta qasan ido gaba daya launin idanunsa sun canza
muryarsa ta sake zama so cool
Idanunsa na kan fadila lokacin da ta miqe don basu guri don zuciyarta ta samu
salama daga mugun kishin dake taso mata,ya dan daki table din da hannunsa wanda
yasa fadila daje shirin sauka juyowa suka hada ido da shi,fararen idanun nan nasa
da sukayi returning zuwa ja ya lumshe su sannan yayi mata alama ta koma ta
zauna,kamar ta zura da gudu tabar gurin haka taji saidai ba yadda ta iya ta koma
din
Minti biyu tsakani yayi sallama hadi da kissing wayar sau uku,lumshe nata idanun
tayi tanajin wata dalmar kishi na digar mata cikin zuciyarta,bata bari shaidan ya
kitsa mata komai ba ta soma karanta *hasbunallahu wani'imal wakil*,wani gumi ta
gani yana tsatstsafo masa ya maida jikinsa ya jingina sosai da makarin kujerar
idanunsa a rufe wani weakness yake ji sosai cikin jikinsa
ya dauki aqalla minti goma sha biyar a haka kafin mood dinsa ya dan saisaita ya
dinga sakin 'yar qaramar ajiyar zuciya a jajjere,har a lokacin fadila na satar
kallonsa tana mamakin meke damunsa haka mood dinshi yayi bala'in canzawa within few
minutes,ya sauke doguwar ajiyar zuciya lokacin da yake bude idanun sa,caraf ya
kamata tana kallonsa sai yayi wani kicin kicin da rai yana ganin kamar tasan meke
damun sa,sunkuyar da kai tayi shi kuma ya zark handkerchief ya share ragowar zufar
fuskarsa
Sauka yayi a ahankali daga dining area din ya shige bedroom,tana zaune a gun ya
sake fitowa wannan karon yellow and coffe din suit ne ajikinsa da alama kaya ya
canza koma wanka yayi ne oho wa yasan masa😜😜😜,hannunsa riqe da brief case
yana amsa wayar mr lien a hanzarce yake tafiya ya sanya hannu ya bude pocket din sa
ya zaro yuan dari ya ajjiye mata(five thousand kudin naija) kana ya dago suka sake
hada ido dukkaninsu sunji jiki ita ta sunkui da kai shi kuma ya fice a hanzarce,ta
kalli kudin ta tabe baki "ne me zanyu da kudin qasarsu?tabdijan" ta fada a fili
amma qasa qasa kamar mai gunguni
Yana fita lukas da andi na qofar gida cikin motar kamfaninsa da yake shirye shiryen
budeshin *maitama group of companies* haka yake kowa yasan da su,da fitowarsa suka
sara masa kamar wani soja sukayi handshake kamar yadda yake a al'adar sa don
dabbaqa value ba addininsa a ko ina yake,lukas ya bude masa qofar zungureriyar
motar ya shiga suka rufa masa baya
Driver din ya bawa umarnin yabi ta lujing road huangtian street zasu fara shiga
yueyang hotel yana son ganin ramzan dan india ne wanda yana daya daga cikin wadanda
ya bawa contract na ginin factory din nasa,factory ne babba na qashin kan aliyyu
wanda ya narkar da maqudan kudade gurin samar da shi,factory ne da zai dinga
manufacturing kayan babies blouses na maza da mata
Wunin ranar cikin zirga zirga mai yawa yayi ta ahiga can fita nan,hakan ya taimaka
masa sosai gurin rage masa abinda yake ji cikin jikinsa,yayin da a daya bangaren
fadila ta wuni kwanciya sai bayan ta idar da sallar la'asar sannan ta shiga
kitchen,pepe chicken couse couse da miyar qwai sai mutuminta lemon kwakwa da ya
wadatu da madara da flavour wannan shine jadawalin abincinta na dare
Nan da nan ta gama kasancewar gas din nata mai hudu ne,ta turare gidan nata da
turaren wutanta bayan ta zuge duk wani glass da window dake gidan,sai gidan yayi
wani dumi mai dadi daya gauraye da qamshi,cikin ruwa mai zafi sosai tayi wanka
saboda sanyin dake damunta na garin,riga da wando tayi shirya kanta ciki wandon
dogone har qas pencil rigar kuma da kadan ta rufe cikinta jacket ta saka mai kauri
ta mata wanda ta sauko har qasan gwiwarta tana da dogon hannu sai manyan maballai
guda shida masu fadi da aka jera daga gaban rigar kusan sune kadai adonta,rigace da
yawanci a turai matansu ke amfani da ita musamman lokacin sanyi
Gashinta ta gyara sosai ta kamashi da band ta saya socks qafa da hannu ko zata samu
sauqin sanyin,da turarenta ta shafe jikinta ko ina ciki da waje,ta maida ta tattare
abinda ya dan yamutse a dakin ta gyara shi sannan ta ciro jakar laptop dinta da sam
ta manta da ita ta cirota tasan saqonnin email na nan na jiranta jingim ta dauki
wayarta ta dawo falo
Sai da ta zauna sannan ta duba agogo don ganin ko lakacin sallah yayi don bata
tsammanin akwai masallaci anan inda suke tun da tazo bata ji kira ba da agogo kawai
take amfani ko dazun ma sauran kadan sallar azahar ta qwace mata,lokaci kadan ya
rage lokacin sallar ya shiga don haka sai ta jona chargy na laptop din nata sannan
ta zira hijabi ta shimfida dadduma ta tada salla
Bayan ta kammala ne ta ninke hijabin hadi da daddumar ta maida daki sannan ta dawo
kan computer din tata,aikam ta tarar da saqonni masu yawa anty hafiza sumayya
rabi'ah na sister farida ne akan gaba harda pictures din baby humaira masu yawa har
da na ya ahmad ragowar kuma duka na masoya ne na gari dake qaunarta ,na 'yan uwanta
ta soma dubawa kowanne na tambayarta ne sun iso lafiya? Da makamantansu,dai sai
taji kewarsu ta cikata take ta shiga maida masu amsa lallai duk wanda yabar gida
gida ya barshi,sai data gama da su sannan ta soma duba na sauran jama'a wanda ke da
muhimmanci ta maida masa amsa mara amfani ta goge shi
A hankali ta daga kai karo na farko ta duba agogo,tara da mintina goma sha
biyar,duk da cewa unguwar da haske ta dan soma duhu alamun dare ya soma kenan wasu
sun kashe qwayayensu "me ya tsaida shi tun safe har yanzu?" Fadika kewa kanta
wannan tambayar da ita kanta bata san amsarta ba,fargaba ta dan soma shigarta da
tsoro lokacin da idanunta ke ganin kamar ana gilmawa ta cikin balcony dinsu,ta miqe
a dan tsorace ta maida hijabinta bayan ta zare computer din daga jikin socket ta
maida daki ta dawo falon ta tayar da isha'i
Har ta idar babu aliyyu ba alamunsa,zama tayi kan daddumar jiki a takure,kewa ce
sosai ta kamata,ita ba layin qasar cikin wayarta bare tayi kira,a gogon ta sake
kalla ya nuna mata qarfe goma da minti biyu,tsoro ya sake shigarta musamman da taji
unguwar ya sake yin shiru ba komai ke tashi sai haushin karnuka🐕da keta kai kawo
Dif wutar gidan ta dauke gaba daya,gabanta yayi wani matsanancin bugu yadda duhu ya
mamaye gidan ko tafin hannunta bata iya gani,tuni jikinta ya soma rawa ta dunqule
guri guda tsoro ya mamayeta haushin karnukan sai take jinsa kamar a qofar gidan
Bata san sanda ta wuntsila tayi bayan kujera ba jin haushin karen a bakin qofar
falon hadi da tsaiwar mota wadda aka yiwa full light aka dallare gidan gaba daya
daga baya aka kashe,ai bata san sanda ta saki kukan tsoro ba dumin hawayen kawai
itama taji,cewa take shikenan na banu,kusan minti biyar sannan ta daina jin motsin
karen,zama tayi dabas a qasa hadi da dafe goshinta da tafin hannunta,kuka sosai ta
saka,tana bala'in tsoron kare arayuwarta,don duk gidan da zata matuqar suna da kare
to komai mutuncin da kuke tafa bar zuwarmuku kenan daman yaya lafiyar kura,yana
daya daga cikin abinda yasa bata saba da gidansu aliyyu ba bata zuwa kenan da can
suna da karnuka har biyu kafin daga bisani uncle abba yasa aka fita da su
Sam bataji shigowa ba sai takun sawaye ta ji,a guje ta miqe tana neman mafaka a
rude ,ji tayi an cafkota cikin duhun,ihu ta bude bakinta da niyyar yi ko da wanda
Allah zai sa ya kawo mata dauki sai taji ansa hannu an toshe mata baki dai dai
lokacin wutar ta dawo,fuskarsa cikin tata yake kallonta ya zuba mata qwayoyin
idanunsa,fuskarta tuni tayi jage jage da hawaye jikinta sai bari yake don sai da
wutar ta dawo ta gane ashe tuni har hular kanta ma ta cire saboda tsabar rudewa
Ita ta fara janye idanunta hadi da kawar da kanya gefe ganin shi bashi da niyyar
janye nasa sexy eyes din da ya zuba mata,qoqarin zame hannunta take har a lokacin
kanta na gefe tana kuka mara sauti don iya tsorata ta tsorata,jikinsa a mace yake
murus ga gajiyar zirga zirga da ya wuni yana yi tuni rigarshi ma ta saman ya cireta
a hannu ya shigo da ita,yaqi sakin hannun nata yayin da yake qara zuba mata wani
dafin mai illa ga ruhinta har cikin qwaqwalwarta don baisan me riqe mata hannun ya
jawo mata ba,ta kuma rasa me yake yi a tsayen har lokacin don qeya ta juya masa
idanunta bai kansa ta kuma qi kallonsa
Gashinta yake kallo dake ta sheqi shigar ta karbeta sosai kamar yasa hannunsa ya
shafa gashin saboda sha'awar da ya bashi sai kuma wata zuciyar ta gargadeshi "zaka
jawowa kanka raini" a hankali qamshin turarenta ya ci gaba da sakar masa da gabobi
da qyar ya Iya dauke idanunsa yana jan tsaki cikin ransa yana jin haushin kansa
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:58 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?..*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 2*
3⃣7⃣&3⃣8⃣
3⃣7⃣3⃣8⃣
Ji tayi an janyota baya an zaunar da ita saman kujera ta dago kai suka hada ido
fuskarnan tasa kamar dai koda yaushe,ta sunkui da kai hawaye naci gaba da zuba,tana
jin tausayin kanta ne cikin zuciyarta soyayyar aliyu ta gama yi mata illa,yana
tsayen dai yayin da ya sauke dukka qwayoyin idanun nasa a kanta yana kallonta ita
kuma kukanta take haiqan mara sauti lokaci lokaci tana sa tafin hannunta tan rage
ruwan hawayen ta hanyar sharesu hadi da jan majina
Kusan minti biyar sannan taga ya dora mata handkerchief saman cinyarta qamshin
turarensa da yake jikin handkerchief din ya daki hancinta,briefcase dinsa ya dauka
ya wuce daki,saman gadon ya fada yayi rigingine yayin da qafafunsa ke qasa hadi da
cewa *"ya Allah"*
Lokaci sosai ya bata yana maida numfashi tukun kafin ya miqe ya cire kayan jikinsa
ya sanya rigar wanka ya wuce bandaki,ko cikin toilet din ma haka ya dade cikin
bathtub kafin ya cude jijinsa ya fito,jallabiyya ya gani saka da short nikker gefan
gadon a ajjiye bai kawo komai cikin ransa ba bayan ya tsane jikinsa ya shafa lotion
dinsa sannan ta taje soft sumarshi ya feshe jikinsa da designers turarukansa ya
jawo kayan ya sanya
Har yanzun tana bisa kujerar saidai yanzu har jingina tayi lokaci lokaci ta na dan
saki ajiyar zuciya irin na wanda ya sha kuka,kallo daya yayi mata ya dauke idanunsa
ita kam dama ko sashin da yake bata kalla ba don haushinsa take ji,sai da ya fara
zuwa gun makunnin t.v ya kunna ya dauki remote ya qaro volume gidan talabijin dun
qasar ne ke labarai ya maida remote din ya wuce dining,da kansa wannan karon yayi
serving din kanshi sannan ya soma cin abincin,yaci abincin sosai ba tare d shi
kanshi ya san yaci haka ba
Tuni bacci ya dauke ya dauketa kafin ya kammala,ta takure kan kujerar kamar
kwanciyar jariri cikin mamansa,ajiyar zuciya take saki kadan kadan cikin baccin,a
hankali ya qaraso gabanta ya tsaya bayan ya kammala duk abunda zaiyi,ya zuba
hannayensa cikin aljihun short nikker dinsa ya zuba mata ido "sleeping beauty" yaji
zuciyarsa na fada,wata sha'awa matsananciya ta taso masa har wani yarrr yaje ji
cikin jikinsa,ya tabbata da da salima yazo kai ko samira ce da tuni an wuce gun
Itama ita gani yake kamar bada kaine ya tunkareta tunda dukkansu sun fita
shekaru,ta sake jan wata doguwar ajiyar zuciya cikin baccin nata harda juyawa,ya
kalli hannunta handkerchief din da ya bata ne duqunqune tsakiyar dogayen
yatsunta,karo na farko wani abu mai kama da tausayinta ya ratsa zuciyarsa,ya tuna
yadda ta tsorata dazun ya tabbata rashin dawowarsa ne da baiyi da wuri ba da kuma
dauke wuta da akayi wanda qarewar kudin wutar su ne daga can company din ya jawo
haka,yasa hannunsa ya danyi mata baya da gashinta da keson shigar mata ido
Da sauri ya janye hannunsa kamar wanda wuta ta ja,ya daga kai ya kalli lokaci sha
biyu na dare saura minti shida,yasa hannu a ahankali kamar jiya ya zare filon
nata,a tsorace kuwa ta tashi don har sai da yasa hannayensa ya tareta don kada ta
fado,sai bayan ta nutsune suka hada ido ya janye hannunsa tayi qasa da kanta,tana
jin takunsa sanda ya shige bedroom,sai da ta tsaya ta tattare kwanukan ta mada
kitchen dare ya riga yayi ga dan Karen tsoro wanda ya hanata gyare gun kamar yadda
ta saba
Tamkar jiya yauma kwance yake saman center saidai yau lullube yake da wani qaton
lallausan farin bargo ba irin na kan gadon ba,saidai ya debe gaba daya filallukan
kamar jiyan blanket din kawai ya bar mata
Again yauma dai sallar ta tarar da shi yana yi saidai ita bayan sallar asuba bata
koma bacci ba breakfast ta hada masa don taji da yana waya kamar yana cewa zai fito
da wuri zasu Beijing
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari maqociyar ta ta hannun hagu mr lin ta shigo mata 'yar asalin qasar china
dince tana da yara uku,sosai fadila taji dadin kulawar da ta nuna mata sun dan jima
suna taba hira har daya mqociyar tata ta shigo,sunanta nadiyya 'yar asalin alqahira
ce sai fadila tafi farinciki da nadiyya fiye da mr lin saboda addini da suka hada
duk da cewar itama mai kirki ce,saidai ita nadiya yaronta daya mashkur sai mai
gidanta abdul-basid karatu ne ya rabosu da qasarsu,sunyi hirarsu da ita sosai cikin
harshen larabci don ta nan bangaren ma ba'abar fadilan a baya ba
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Rayuwa aqasar da baka da kowa ba wanda ka sani bata fiya dadi ba ba kamar idan kana
qasarka ta gado ba,to hakanne ya kasance ga fadila da zarar aliyyu ya fita ta
kammala aikace aikacenta sai ta koma kan waya ko computer ta duba saqonni,idan ta
gaji sai ta sanya hijabinta ta dawo balcony ta zauna tana kallon masu shige da
fice,duk da cewa unguwa ce da bata da yalwar jama'a amma ba'a rasa masu wucewa
jefi-jefi har wasunsu kan tsaya suyi mata magana ganinta baqar fata mutanen qasar
mutane ne masu so da girmama baqo hadi da mutunta shi
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
A irin wannan ne ranar bayan ta kammla aikinta da wuri ta hau social media dinta ta
gaji ta dawo balcony kamar yadda ta saba,saidai yau da gobe sai Allah sai zaman nan
din ma ya gundireta,wasu 'yammata su uku ta gani sunzo wucewa dukkaninsu akan
kekuna suna tafe ajere suna hirarsu abinsu🚴,sai taji tana da sha'awar zaga koda
layin sune zuwa qarshensa
Cikin zumudin tunanin da tayi ta zqro wayarta ta dan yima aliyyu text, _*please zan
dan fita qarshen layi*_
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
*PART 2*
3⃣9⃣&4⃣0⃣
3⃣9⃣4⃣0⃣
Ta kalmashe wayar a hannunta bayan ta tabbatar saqon ya je,ta miqe ta saya qofar
don bata damu da sai ta kulle ba ta san qasa ce mai cike da tsaro
A hankali take ratsa layukan duk da dan banzan sanyin dake bugarta amma yanayin
yayi mata dadi sosai,tana tafiya tana cilla hannayenta gaba da baya fuskarta qunshe
da murmushi ,unguwar ta burgeta matuqa babu yawan jama'a tunda dama can ita bata
son hayaniya,sai yara jefi jefi dake wasa wasu cikin balcony dinsu wasu kuma a
qogar gida duk wasannin nasu baya wuce tseran keke da buga qwallo(football)
Abinda ta lura da shi shine su kamar ma sanyin bai damesu ba ba mamki ko don
qasarau ce sun saba,har ta fita daga layin da shiga second street bata sani ba,yara
ta gani su hudu babbar ciki ba zata wuce shekaru tara ba ma bi mata ba zata wuce
takwas ba ta ukun kuma ba ta gaza uku qaramar ce mai alamun biyu amma da yake
yanayin qasarsu ya bam banta da namu buka buka da su masha Allah,ball suke bugawa
suka bugo mata saidai a qafarta ta sauka basu sameta ba
Babbar cikinsun ce ta fara lura da wadda suka bugawan ta tabo mai bi matan tana
mata rada akunne tana kallon fadila duk sai suka juyo suna kallonta,fadika ta
sunkuya ta dauki ball din ta nufi inda suke fuskarta dauke da murmushi suma
murmushin suke saboda ganin baquwa,ta ajjiye ball din agabanta tabuga ta ta tafi
gabansu ai kuwa suka hau ysalle da murna suka dawo mata da ita,duk da bata jin
yarensu amma ta gane dadin hakan sukeji
A nan gurin yaran ta bata lokaci sosai ba tare da ta sani ba,yaran sun sake sosai
da ita nan ta hada su dukkaninsu ta shige tsakiyar su tayi musu hotuna,suka shige
gidajensu suna daga mata hannu,sai alokacin ta duba gari taga ya soma duhu
hankalinta a taahe ta juya ta soma laluben hanya garin haka sukayi kacibus da
mutumin nata (kare)shaf ta manta kare baya son gudu don a rude take tuni ta takure
ta sheqa a guje shi kuwa ganin haka ya rufa mata baya
Motar kamfanin ta ajjiye aliyun a qofar gida yayi sallama da su yana jaddadawa
wanda ke gaban motar su tabbatar gobe early in d morning sun kawo engines din nan
an qarasa kafasu agurarensu,ya amsa masa cikin girmamawa,suka ja moyar shi kuma ya
juya ya shige gidan
Qwan lantarkin na kashe yasa hannu ya kunna haske ya gauraye falon,neat yake kamar
ko yauahe cike da qamshi ya jefa rigar samansa da ya cire hade da jakarsa kan
kujera shima ya zauna,a gajiye yake tubus ya soma zare takalminsa da safarsa sannan
ya kalli inda ta saba ajjiye masa ruwa da lemo wandayake fara sha da zarar ya
dawo,wayam babu sai abincinsa dake jere saman dining,yanmiqe ya bude freezer wanda
basu kunnata sosai yanzu saboda yanayin sanyin garin ya ciro ruwan roba,ko cup bai
nema ba ya balle murfin ya kafa kai sai da yasha kusan fiye da rabi sannn ya maida
ya rufe
Bedroom ya nufa don yin wanka hadi da alwala cikin zuciyarsa yana mamakin rashin
jin motsi ko yaya cikin gidan,mamakinsa ya dadu ganin babu ita a dakin ya bude
toilet babu ruwan wankansa wanda ya riga ya saba ya tadda shi yana
jiransa,tunaninsa sai ya tafi ga ko tana kitchen,ya nannade hannun rigarsa ya daura
alwala idan yayi sallar daga baya yayi wankan tunda yau bai samu ruwan ba,har ya
shimfida abun sallah zai tayar sai kuma ya fasa zuciyars ta kasa samun nutsuwa,sai
yakejin wani irin rashin ganinta amma sai ya alaqanta hakan da sabawa da yayi da
ganin nataidan ya dawo
Kitchen din ya nufa kai tsaye bata nan,wani dim yaji zuciyarsa ta harba💓,ya riga ya
sani tunda auke da ita bata taba fita koda qofar gida ne ba tate da izininsa ba,a
hanzarce ya koma bedroom inda ya ajjiye wayarsa saman madubi call logs ya shiga da
sauri da sauri yana dubawa dinta ko Allah zaisa yaci karo da number dinta,tsaf ya
gama bincikensa bai ganta ba,ya saki ajiyar zuciya hankalimsa amatuqar tashe,sai
sannan ne ma idonsa ya kai kan 'yar qaramar envelope dake maqale saman wayarsa
wanda ke nuni akwai sabon saqo a wayarsa,
Har zai maida wauar aljihu sai ya fasa ya jawo saman wayar ya shiga gun sms,numbers
ne guda biyu daya ba suna daya kuma ta mr jake ne,yana gama karanta tex din ya
tabbatar ita ta turo masa shi baisan sanda ya juya ba ya zira silifas ya fita a
sukwane ,da sauri yake daddanna numbobin jumong daya daga cikin direbobin
kamfaninsa wadanda suka fi kusa da unguwar da auke ciki yave ya kawo masa mota
yanzu yanzu,bai iya ysayawa jiran mitar ba ya fita da qafafunsa yana ji ajikinsa
cewa hanyar dawowa ta rasa
A hanzarce yake tafiya,kasancewarsa giant ma'abicin kuzari sai gashi yayi tafiya
mai dama kafin isowar jumong din
Ta waiwayo cikin gudun dai bata fasa ba taqin dake tsakaninta da karen dan kadan
ne,ta saddaqar cewa ta gama yawo,tuni tayi surrender ta tsaya cak lokacin da taga
ya daka tsalle tana jiran taji ya yago ta,qyam tayi jinin jikinta
adaskare,rungumeta taji anyi yayin da qamshin turarensa ya mamaye mata
hancinta,tsawq taji ya daka wa karen ta bude idanunta ahankali yayin da dumin
jikinsa ke ratsata,sum sum taga karen ya juya cikin sassarfa ya bar gun,sai da ya
bace alayin sannan ya juyo ya kalli qwayar idanunta,idanunsa fal da fushi sai huci
yake,hannunta ya fincika ya bude bayan motar ya sanyata sannan shima ya shiga
jumong ya tada motar
Bai ce mata uffan ba kamar yadda bai sake kallonta ba idanunsa na bisa titi har
yanzu kana ganin fuskarsa kasan cikin fushi yake,kuka take kanta na qasa ita kanta
ta rasa kukan kuma na mene tunda Allah ya taimaketa,sai da suka qaraso gidan sannan
ta tabbatar aahe tafiya tayi mai yawa bata sani ba irin haka?
Ya bude side dinsa ya fito sannan ya bude nata ya damqo hannunta ya fito da
ita,jumong nata cewa"gudnyt sir" amma baibi ta kansa ba,saman kujerar ya cillat
yana huci,shi kansa bai san me yasa yake jin wani fushi ba don ta bata hakanan yake
jin wani tashin hankali da bai ganta ba,cikin jikinsa yake ji kamar *ZATA IYA
GUDUWA* wataran tace zata barashi,
Saman kujerar ya dora qafarsa yayin da ya sauke dayar a qasa yana tsayw
gabanta,kukanta har yanzu take ci gaba da yi harda dan sautin sheshsheqa,hankalinsa
gaba daya ya rabu biyu ,hukunci sosai yake son yayi mata saboda kada ta sake fita
har ta bace agaba,yayin da qamshin turarenta keta rarŕaba masa hankali,ya kasa
komai kukanta na ci gaba da shiga kunnuwansa,hannu ya dunquke ya daki kujerar da
suke kai "keep quiet"ya fadu cikin tsawa,hannu tasa ta rufe bakin nata hawaye naci
gaba da silalowa🙊,ya dage girarsà yana fadin"kiwa mutane laifi kuma ki sasu a gaba
kina masu kuka?ko don kinga bakinki yafi nawa iya kuka?"ya qarashe maganar da sigar
tambaya
Ita dai babu abinda tace,kusan minti biyar shiru ya ratsa falon hawayenta naci gaba
da silalowa shi kuma yan ci gaba da kallonta yana jin 2ani abu kamar ya zaqe da
yawa why?,a hankali ya juya yana barin gurin hadi da cewa "silly girl"
Abincin da bai iya ciba kenan a ranar ita da kanta kuma sai taji bubu dadi,koma
mene tasan batan ta ne ya bata masa rai shi kuma ya jawo mishi,da bacci ya dauketa
ma kan kujera da asuba anan ta farka ta ganta bai tashe ta ba kenan
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻

  
[10/16, 1:59 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?..*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 2*
4⃣1⃣&4⃣2⃣
4⃣1⃣4⃣2⃣
Kwana uku tsakani tana zaune ya kawo mata foam🗞,gefan ta ya ajjiye bata san na mene
ba sai da ta bude sannan ta duba sosai ta gani ashe na wata instute ce, sabon corse
ne kan aikin jarida zasu fara wata uku ne kacal za'a kammala,daga qarfe goma na
safe zuwa daya na rana,zaka iya attending classes dinsu kokuma ka dauki lecture din
online kana daga gida
Tsalle ta dinga yi cikin murna bata san aliyyu na tsaye ba qofar kitchen ashe ita
ya zubama ido,a hankali suka hada ido tayi saurin komawa ta zauna kunya ta kamata
shi kuma ya ya dauke kai ya shige kitchen din,a nutse ta dinga cike foam din har ta
kammala da maida cikin envelop
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Sosai fadila ta soma jin dadin karatunta duk da online take daukan lecture ko
yaushe tana gaban computer din ta,koda ta kammala daukan lecture sai tayi zamanta
tayi ta research,tun daga lokacin da abin ya faru itama bata sake gigin fita
ba,iyakacinta gidan nadiyya ita din ma ba sosai don gidan mr lin ma sau daya ta
taba leqa mata,sai dai su turo mata yaransu suyita taya ta hira don ma bata gane
yaren nasu tafi hira da mashkur don ya iya yarensu na larabci sosai
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Zaman garin yanzun bai fiya takurata ba sosai tun lokacin da ta fara daukan lecture
dinta,sosai computer din ta sake zama abokiyarta shi kansa uban tafiyar ya lura da
yadda gaba daya walwalarta ta koma kan laptop dinta,haka nan sai ya soma jin
haushin computer din gani yake kamar ta tsare masa wani abu da ya rasa mene shi
gaba daya bata da wani sukuni sai ta zauna a gabanta
Shi yasa wani lokacin da zarar yaga ta dauko da niyyar yin karatu sai ya tsiro wani
aikin na babu gaira babu dalili,cikin zuciyarsa yake gulmar "reading like
machine"karatu kamar ranta,(hmmm kaji fa gwano baijin warin jikinsa shi da yake
wuni zirga zirga da kai kawon bude company dinsa)
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Kamar kullum yauma tara daidai ta kammala dukkanin ayyukanta sabida goma zata zauna
lacture,tana sanye cikin kayan sanyi na turawa ta yane kanta da dan qaramin hijabi
fari tas iya kafada,shigar orange and white ⚪
tayi sai ta haska chocolate colour
skin dinta,tana tsaye a dining area tana zuba masa farfesun kan rago cikin plate ta
hada masa tea cikin cup☕ don ya dan sarara kafin ya fito
Taa cikin rufe flask dinne taji takun tahowarsa ,a dabarance ta saci kallonsa ta
gefan ido cikin rashin sa'a ya kamata,da sauri ta dauke idonta ya qaraso dining din
ya jawo kujera daya ya zauna hadi da dora briefcase dinsa a dayar ya ajjiye wayarsa
☕
kusa da cup din tea,itama kujerar ta ja ta zauna kamar yadda yakeso kenan idan
zaici abinci(🙄🙄🙄 hmmmm)
Ta sake satar kallonsa a karo na biyu suka sake hada ido "hold on ur sight"ya fada
yana kai cup din bakinshi,sai ta danji kunya ta kamata duk da shi din ma tasan
satar kallon nata yayi har suka hada idon,tsakanin jiya da shekaran jiya zuwa yau
gani take mood dinshi ya canza,duk da dama bawai mai fara'a ne ba amma taga sauyi
cikin walwalarsa da kuzarinsa,hakanan ayyukan da yake tahowa da su yayi ta lodawa
cikin laptop dinsa ya ragu sosai
Haka nan cin abincinsa ya ragu daga kusan kaso saba'in cikin dari,cikin ranta take
ganin bata da wani matsayi gurinsa bare tayi gigin binciken meke damunsa,kamar
yadda ta zata kuwa tea din kawai ya shanye ya miqe yana rataye jakarsa ya kuma
ajjiye mata yuan 100 kamar yadda ya saba,a hankali yake saukowa daga daga step din
dining area din kamar mara laka
Tuni qamshinta yayi masa rugu rugu da gangar jiki da kuma zuciyarsa,babu abinda
yake buqata a yanzun idan ba mace ba koda samira ya samu ayanzun zai iya maleji da
ita,har sai da ya fice sannan ya kauda kanta daga kallonsa ta maida idonta kan
table din inda ta hada kayan break,tea kawai itama ta iya hadawa ta sha ta kwashe
kayan ta gyara gun takai kitchen ta wanke ta dawo kan computer dinta don yin
karatun
Qarfe daya da mintina goma sha biyar ta kammala ta rufe laptop din,ta danyi miqa
irin ta gajiya tana yar hamma,ta jawo wayarta ta dan duba saqonninta na watsapp na
tsawon minti arba'in sannan ta sauka,sallah ta soma yi don biyu tayi sannan ta
kwaba alkubus don shi ta shirya yi yau
Tana tsaka da aikin nadiya ta shigo nan ta zuba ido tana mamakin me fadilan ke
hadawa haka?,dariya fadila tayi tace irin abincimmu ne
Sai qarfe uku nadiyan ta tafi fadilan ta rakota bakin qofa tana gaya mata idan ta
gama zata ta turo mashkur ya karba mata taci taji,ta saye qofar falon ta koma
kitchen din fara aikinta,ta kammala komai da wuri ta gyara gurin ta koma bedroom
don daura alwalar sallar la'asar don har tana qoqarin subuce mata
Turus ta ja ta tsaya ta kuma saki baki,jakarsa da rigar suit dinsa na watse saman
sofa shi kuma na kwance saman gado ko takalmin qafarsa bai tube ba,cikin mamaki
take satar kallonsa tana mamakin yaushe ya shigo gidan don ko alamunsa bata ji
ba,kuma ma mainya dawo da shi gida a wannan lokacin
Rabawa tayi ta shige toilet ta dauro alwalar ta fito ta dauki abun sallarta ta koma
falo,bayan ta idar ta koma saman kujera ta zauna sai dai hankalinta ya kasu rabi na
kan t.v rabi na bakin qofar bedroom din don har yanzu bata ji motsinsa ba
Hankalinta ne ya gaza kwanciya cikin sanda ta miqe ta tura qofar tana leqen saman
gadon,har yanzu a kwance yake kamar yadda ta barshi,ta qarasa bude qofar gaba daya
a hankali cikin sanda ta qarasa bakin gadon ta duqa ta kama qafarsa a hankali ta
zame masa takalman bai motsa ba har ta gama cire masa sai tayi tsammanin bacci yake
ta sabule masa socks din ta cusa cikin takalmin ta kwashe su ta maida su muhallinsu
Ta juya zata fice ta sake waiwayowa kalleshi idanunsa na lumshe kan hancinsa yayi
wani ja irin na farin mutum kamar an murza gun,ta kauda kai ta fice daga dakin,duk
abinda take yana kallonta idanunsa biyu,matsanancin zazzabi da yake ji da ciwon
ciki mai azaba wanda ya jima rabonsa da shi shi ya hanashi koda yin motsi,yasan
yadda ciwon cikinsa yake idan ya kamashi baya masa ta dadi,sai yaji dadin yadda ta
sake dawowa ta dubashin ganin bai fito ba,ya tabbata kasa nutsuwa tayi da rashin
ganin bai fito din ba
Sai da ta shigo daura alwalar sallar magariba sannan ta ganshi zaune kan abun
sallah a side din gado duk da bata ga fuskarsa ba kansa na aduqe,ta sake wucewa
tayi alwalar
Qarfe tara na dare zaman falon ya gundireta ita daya kamar mayya,sabo mugun abune
zaman da sukeyi tare duk dare shi ya sanyata kewa ganin yau babu shi duk da ba wani
zaman da za'a fadeshi bane kowa harkar gabansa yake duk da da zarar daya yayi wani
motsi mai qarfi zaka ga hankalin dayan yayo kansa
Sai da ta hada masa coffee ta hada harda abincin cikin babban tray guda daya don
har lokacin bai ko leqo koda falon ba bare yaci abincin nasa,ta dauka bayan ta gama
shirin kwanciyar ta cikin night gown riga da wando ne wandon har qasa rigar iya
gwiwa cotton ne very soft sai hijabi saboda sanyi
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
3:54 pm 5/09/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
*PART 2*
4⃣3⃣&4⃣4⃣
4⃣3⃣4⃣4⃣
Ta ajjiye tray din kan bed side tana tunanin ina ne makwancinta yau kuma?,saboda
aliyyu na kwancene a kai crossing gadon,bata jin kuma zata iya kwanciyar qasa yadda
shi yakeyi domin matsanancin sanyin garin ya girmi qashinta,ta kuma kallinsa karo
na biyu yana duqun qune cikin bargo gaba dayan jikinsa kansa ne kawai a waje
Sai ta rasa ta yadda zata tada shi tafi qarfin minti goma ahaka kafin dabara ta zo
mata,gyaran murya ta taqarqare ta ja har aai da maqogwaronta yayi mata zafi,a
hankali ya bude idonsa ya zubesu fes kan fuskarta tsakiyar qwayar idonta,fadila ce
ta soma janye nata qwayar idon tana jin wani magnet na fusgarta,tabbas ba don
aliyyu mutum bane zata iya cewa wani mayen qarfene cikin idonunsa da duk sanda ta
kalla yake fusgarta,cikin ranta taje mamakin yadda fareren qwayar idanun sa kar
suka rine zuwa ja
Cikin jikinta ta soma jin anya lafiyar aliyyun qalau?,ta kawar da wanna tunanin
tana ji a jikinta har yanzu ita aliyyu yake kallo, "na zuba maka ne abincin?" Can
qasa ta jiyo shi yace " I don't need",ya maida idanunsa ya lumshe,ta kuma kallon
nasa tace "but...." "leave me "ya fada can qasan maqoshinsa cikin katseta,ta ga
alamun bai da lafiya ne don haka bata yi zuciya ba tace masa "please ko coffee ne
kasha mana" shiru yayi kusan minti uku baice komai ba,hakanne yasa ta gane ya yarda
Ta jawo flask din ta tsiyaya masa rabin cup din sannan ta sake matsowa kadan yadda
zataji dadin miqa masa "take it pleas",da qyar ya iya miqewa ya jingina da makarin
gadon,ta sake miqa masa yasa hannunsa zai amsa ya hade da hannun nata,kamar bashi
ya riqe mata hannu ba bai saka ba bai kuma ce komai ba
Wani shocking take ji ga kuma dumin zazzabin jikinsa da yake ratsa ta itama,sai
lokacin ta sake tabbatar da ashe bai da lafiyar,a hankali ya zame mata hannun
sannan ya riqe cuo din sosai ya sale maida idonsa yaumshe kamar ba zai sha ba,illar
da turaren ke masa nada yawa haka yake rayawa cikin zuciyarsa,ya sashi cikin wani
yanayi nason kasacewa tare da ita fiye da tsammaninsa,
Bai damu da dan banzan zafin coffee din ba ya daga kai ya kwankwade tayi saurin
amshe cup din ta hada kayan ta maida kitchen ta dawo dauke da cup da gorar ruwa ta
dora kan bedside,sai ta tsinci kanta cikin damuwa da cutar yasa duk da bai buda
baki yace mata komai game da lalurar tasa ba tasan yana jin jiki,tuni ya kwanta a
daya side na gadon ya juya wa ragowat sararin dake bayansa baya
A hankali ta haye gadin gami da debe qafafunta ta maida su saman gadon ta rungume
gwiwoyinta da hannayenta tana kallon bayansa,tana iya ganin yadda numfashinsa ke
sauka a hankali,jikinta ya soma saki bacci ya kamata batasan sadda ta zame ta
kwanta ba
_*2:30 pm*_
Can cikin tsakiyar baccinta taji ayi mata wani irin mugun riqo,nishi take ji cikin
kunnuwanta sama sama dumin numfashin na dukan wuyanta,a firgice ta farka amma ta
kasa tashi sabida namijin riqon da yayi mata gaba daya ya cukuikuyeta,da qyar ta
samu ta juya tana fuskantarsa,murqususu sosai yake yana hada gumi numfashinsa ke
fita da sauri da sauri,tuni ta gigice ganin yadda yana yinsa ya sauya gaba daya,ta
tashi ta zauna dirshan hannunsa na riqe da cikinsa idanunsa adamqe daya hannun kuma
ita ya zagaye da shi,sosai ta rikice babu abinda yake fadi sai *"ya Allah"*
Kimanin minti goma ta shude a haka ta rasa ya zatayi,tunaninta suna da first aid
kit a gidan?to koda ma akwai din bazai qyaleta ta tashi ta dauko ba don gaba daya a
kanainaye yake ajikinta,dabara ta zo mata da sauri ta miqa hannu ta dauko robar
ruwanan da cuo din da dazu ta shigo da su,ta tsiyaya ruwan sannan ta sa bakinta ta
tofa masa ayatush shifa ta hada masa da _*allahumma rabbin nas,azhibul ba'asi,wash
fi antash shafi,la shifa'u illa shifa'uk,shifa'an la yugadiru saqama*_
Ta dan kalli fuskarsa da tayi ja har yanzu idon ke rufe yana hada gumi "pls can you
take it?" Ya dan motsa kadan tasa masa cup din abaki yasha kuwa fiye da rabi
Cikin ikon Allah da taimakon ayoyin al qur'ani sai mutsu mutsun da yake ya soma
raguwa,riqon tsaurin da yayi mata ya fara sassauta,sai ajiyar zuciya da yakej saki
kadan kadan,bata samu sukuni ba sai da taji numfashinsa ya soma daidaita,a hankali
jikinsa yayi weak bacci sosai ya daukeshi
Ta saki ajiyar zuciya tana kallin irin yanda ya zagayeta da hannunsa,ta tabbatar da
a hayyacinsa yake bazai yi hakan ba,gumin fuskarsa har yanzu da saura,tasa
lallausan tafin hannunta tana share masa kadan kadan gami da bin fuskarsa da kallo
ganin yadda tayi ja alamun wahala,tayi tayi ta janyeshi daga jikinta cikin dabara
saidai abun ya faskara yayi mata nauyi ahaka itama baccin yayi awon gaba da ita
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
  
[10/16, 1:59 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 2*
4⃣5⃣&4⃣6⃣
4⃣5⃣4⃣6⃣
Yau kam sun makara sosai suka makara don ko sallar daren babu wanda yayi a cikinsu
sakamakon bacci da basu samu ba jiya,shi ya fara farkawa ganinta cikin jikinsa ya
bashi mamaki,kamar ta san me yake faruwa ta farka itama fuskarsu cikin ta
juna,kamar hadin baki da sauri kowa ya janye jikinsa suka miqe a tare,shi ya fara
shigewa toilet ita kuma ta shiga na parlour
Ta rigashi idarwa tana zaune tana azkar har ya idar,tana zaune har ya kammala nasa
addu'o'insa, tadan waiga kadan tana duben gefansa tace "ina kwana" kamar yadda ta
saba ba tare da neman amsa ba tunda ta sani ba masawar zaiyi ba don bai taba amsawa
din ba,saidai idan yaga dama ya daga mata hannu kawai,saidai yau ga tarin mamakinta
karo na farko sai taji ya amsa da "lafiya",ta sake cewa "ya jiki?" Kai ya daga
mata,ta tabe baki ta miqe cikin zuciyarta tana cewa"hmm an ma yi yau abun arziqi"
tana kallonsa ya sake komawa gado ya duqunqune
Bai dade da kwanciya ba wayoyinsa dake gefan gadon suka hau ruri,hannu yasa ya debo
su bai daga kiran ba hakanan ba tare da ya duba mai kiran ba ya kashesu duka sannan
ya maida su kan side drower hadi da jan bargonsa ya sake rufa
🔅🔅🔅🔅🔅
Tana kitchen tana hada breakfast tajiyo muryarshi cikin parlour yana amsa
waya,saidai muryan tayi qasa sosai alamun bai cikin jin dadinsa don bata iya jin
abinda yake cewa,cikin rarraba hankalinta da takeyi ne ta yanke hannunta da
wuqar🔪 da take rarraba kazar da take so tayi masa pepper chicken ba tare da ta sani
ba,wuqar ta shigeta sosai don yankan ba qarami bane,zafin ya ratsa ta har cikin
qwaqwalwarta batasan sanda ta saki razananniyar qara ba,jini ne sosai ke zuba ta
runtse idonta tana jin azabar yankan
Ta bude idonta a hankali suka sauka kansa lokacin da yake shigowa kitchen din cikin
sauri,hannun nata da yake digar jini yake bi da kallo,da sauri taga ya ajjiye wayar
saman freezer,hannun nata dake digar jini ya riqe yana kalla,wani yarrr fadila ke
ji har cikin jininta,shi din ma haka,lallausan tafin hannunta yaso haddasa masa
wata sabuwar fitinar cikin jikinsa,yayi saurin sakin tafin hannun nata ya kama
tsintsiyar hannun
Janta yayi zuwa gaban sink ya kunna famfo ya tara hannun sannan ya barta gaban
famfon ya fice da sauri,cikin 'yan sakanni sai gashi dauke da first aid kit,abunda
tayi ta tunanin ina yake jiya,spirit ya fito da shi ya janye hannunta daga famfon
ya dangwala a auduga ya soma wanke mata kan yankar,zafi sosai take ji yana ci gaba
da ratsata ta runtse ido 😣tana dan yin baya da hannun,cak ya tsaya da wanke matan
da yake don spirit din baya samun inda yake so,fuskarta da idanunta ke rufe ya
zubama ido har wani abu yaso shagaltar da shi
Jin shiru ya daina sawa ya sanyata bude ido,idonta ya shiga cikin nasa suka
hadu,wani magnet ya hadu da qamshin turarenta yaso rikita aliyyu ya manta da abinda
yake,amma sai yaso nuna mazantaka ya dake har da qarfin halin kaurara muryarsa
"stop it,idan baki buqata zan hada kayana,kau da kai tayi don bazata iya jurar
kallon qwayar idanunsa ba,ya duqar da kai yaci gaba da wanke mata daga bisani ya
rufe mata da bandage don kada datti ya dinga shiga
Yana maida kayan cikin akwati ta dan motsa labbanta tace "thanks" "for what" ya
fadi ba tare da ya dago kai ba bai kuma tsaya da rufe akwatin ba,she became
speechless don haka ta zabi yi masa shiru kawai,haka shima bai sake cewa komai ba
har ya kammala rufe akwatin ya dauki wayarsa ya fice
Da hannu daya ta qarasa aikin don haka kafin ta kammala duk ta jagwalgwale hannun
jinin da ya tsayar mata tuni wani ya soma tsatsatsafowa ta bandejin da ya sa
mata,sai da ta gama serving dinsa sannan ya ankara da girkinta ashe ta ci gaba da
yi,ya dago ya dubeta tana ta faman hurawa yatsan iskar bakinta,baice mata komai ba
ya tashi ya sauka a dining din sai gashi dauke da first aid kit,ta zaro ido cikin
tsorata😳 tana tunanin mai kuma zai mata yanzu
Sosai ya riqe hannunta gam tana qoqarin zamewa saboda azabar yadda yake daye
bandage din da ya sa mata dazun zai canza mata sabo,sai da ya cire tas ya sake
wanke mata ya saka mata sabo sannan ya maida kayansa ya kwashe mai jinin ya sauka
da su
Ya dawo ya soma cin abincinsa yana kallonta time to time yadda take ta qwalla "ko
da yaushe kina acting kamar baby" hakanan taji ya fada can qasan maqoshinsa,sai da
ya kammala cin nasa taga ya ja plate ya zuba mata komai ya tura mata gabanta, "oya"
yace hadi da yi mata nuni da plate din da ido fuskarsa a hade,ta dan langabar da
kai gefe don bata marmarin cin komai yanzu sai ta tashi a lecture "am ok,na qoshi"
kallon nan nasa ya tsareta da shi cikin tsare gida,ta fuskanci hukuntata yake
sonyin da ido,tayi saurin janye idanun ta hadi da sake jan plate da cup din gabanta
ta soma ci tana yamutsa fuska cikin zuciyarta tana mitar "ya wani tsare mutane sai
sunci abinci sai kace wani abbana lokacin da ina gida"
"Good haka abban ke miki saboda baki jin magana kan cin abinci ko?"ya fadi yana
fuska a hade yana daga girarsa,da sauri ta dago ta kalleshi batasan sanda tea din
da ta kurba a bakinta ya dawo ba,batasan ya akayi yaji abinda take fada ba,anya
wannan mutumin ba maye bane?, "am talking to you kin qwalalomin idanunkin nan masu
girman tsiya"(lol aliyyu 😜😜😜😜😜) ya fada cikin dan daga murya,kai kawai take
girgizawa don babu bakin cewa wani abu,minti biyu tsakani yace "shi yasa kullum
store da freezer dinki ke acike kenan basuyin qasa ko?good.....to ni a gidana dole
adinga cin abinci.....oya....bismillah ina son naga plate empty"
Daga haka ya maida kansa gun wayarsa dake ruri ya fara amsa wayar mr lien,ci take
amma sam bata so,da zarar kuma ta tsaya suke hada ido dole take ci gaba da ci,sai
gashi taci abinci mai yawa wanda ita kanta ta jima rabon data ci,ta ture plate din
tana dan taba cikinta da taji yayi fam tana yatsina fuska yayi mata wani irin qabe
qabe babu dadi, "I think u filled your stomach,let me see" ya fadi yana qarashe
kashe wayar"qwalalo 😳 ido tayi tana tunanin anya kan aliyyu daya?ciwon cikinsa na
jiya kodai ya taba shi?,she dont know why he behaving like dis?,cikin nata zaya ce
ta ta yaye rigarta ta nuna masa?,ta dawo cikin hayyacinta lokacin da ya zare mata
ido yace "aha show me" ba shiri cikin sanyin jiki ta dage rigar sanyin hadi da
shirt din dake ciki,cikinta ya bayyana, ashafe yake tamkar zai hade da bayanta,ya
zuba mishi ido,soft skin tata ta bayyana kanta ko ba'a fada maka,wani irin magnet
ke fusgarsa,ya dubeta ta tsira mata ido duk a rude take,muryarsa can qasan
maqoshinta yace "up" yana ci gaba da kallon cikin,a zaton ta bai gani bane sosai ta
dan sake janye masa rigar "up again" ya sake fada,sai ta tsorata don dukka cikin
nata ya fito waje da zarar ta sake janye rigar qirjinta(breast) ne zai bayyana
Ganin bata sake dagewarba yasa ya dauje idanunsa daga kallon cikin ya maida qwayar
idanun nasa cikin nata,ya karanci ta tsargu don haka sai ya waske ya bata rai hadi
da janyo warmer yana budewa gami da cewa "no ni banga yayi full ba,don banga ya
daga ba" ta marairaice tuni qwalla har ta cika mata idanu "I swear idan ka qaramin
zanyi amai wlh Allah haka cikina yake" da mamaki can qasan ransa ya tsaya da abinda
yake din,dama akwai mata masu irin wadannan halittar cikin?,ya riga da ya saba da
matansa masu tumbi
Ya koma ya jingina da kujerar da yake kai yana cewa "ok remove dis items,but be
careful with your wound,dama neman mafita taje don haka da rawar jiki ta tashi ta
soma gyara gun ,cikin kitchen kitchen tafi minti biyar tana dafe da qirjinta
idanunta a lumshe kafin yanayinta ya daidaita "me ya sauya shi haka" can qasar
zuciyarta take tambayar kanta
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:00 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*part 2*
4⃣7⃣&4⃣8⃣
4⃣7⃣4⃣8⃣
Ta dade kafin ta baro kitchen din har yanzu yana dining area bisa kujera yana danne
dannensa a waya,a falon ta tsaya ta jawl computer din ta ta tafi da
gidanka(laptop) ta bude tana shirin kunnawa "hey stop" taji ya fadi cikin wata
iriyar murya mai kama da ta mai jin kasala,kasaqe tayi tana jira taji mai zaice
"shutdown ur system yau ba daukan lecture,kin mance wound dake fingers dinki ne?"
Sai ta rasa mai zata ce tana ganin ai hannunta bazai hanata lecture ba koda guda
daya zata iya yi,amma da yake mutum ce ba mai son jayayya ba don haka ta kashe din
ta koma ta zauna hadi da zubawa sarautar Allah ido
Tana zaune ya shiga ciki yayi wanka ya shiryo cikin kayan sanyi,kan kujerar dining
din dai ya koma ya zauna,babu dadewa kuma door bell ta kada,ya dubeta sannan yace
"put your hijab" mayafine yafe a jikinta bayan kayan sanyi masu kauri da tasa,nan
ma dai bata tanka komai ba ta koma daki ta dauko hijabin,ko da ta dawo su biyu ta
tarar shi da doctor yungpho,ta samj kuje daya ta zauna doctor yungpo mutumin china
na gaidata cikin harshen turanci
Suna gefanta doctor ya gama duk hwaje gwaje da tambayoyinsa,ya dago yana duban
aliyyu "sir,sanyin garin mu na son taba ka gashi kana kwanciya a inda zai iya
affecting health dinka,ya kamata ka kula saboda kada yayi maka yawa ya zamarmaka
illa" "ok" aliyyun yace, "sannan ciwon cikinka ciwon marasa aurene me yasa ya taso
maka a yanzu bayan kana da aure?...." da sauri aliyyun ya katseshi yana satar
kallonta duk da kanta baya fuskantar gun amma hankalinta na gurin haka nan kuma ta
dago wani abu duk da ya katse doctor din
Magunguna doctor yungpo ya bashi yana shirin hade kayansa aliyyu yace ya bashi pain
killers" ya hada masa duk cikin magungunan,fitarsa babu dadewa aliyyu yasa ta bashi
ruwa yasha magungunansa,tamiqa masa ita kuma ta wuce kitchen da zummar dora abincin
rana tunda taga alamun da qyar idan yau zaya fita
Sai tsintar aliyyun kawai tayi cikin kitchen din ya damqota yayo waje da ita,saman
kujera ya zaunar da ita yana ware mata sexy eyes dinsa kamar wata qaramar yarinya
"idan kika sake jangwale ciwonki I will wash it again budewa zanyi in sake wankewa
no pity ok?" Tayi qasa da kanta tana kallon yatsan nata mai ciwon,muryarta so cool
tace "lunch zan hada mana ne" "we don't need" ya fadi yana juyawa "wo hoho
Aliyyu.......Aliyyu...." fadila ke fada cikin zuciyarta,ya sata hutun dole
kenan?....... Babu karatu babu girki?.....fine" ta fadi tare da yin kwanciyarta
saman three sitter
Wunin ranar tana zaune ita dai sai gani tayi an kada qararrawa da rana an kawo musu
lunch hakanan da daddare,coffee kawai ta faki idonsa ta hada,shima tana dire masa
ta bar bedroom din don kada yace zai mata fada,sai da ta kintaci kamar yayi bacci
sannan ta koma,cikin sanda ta salallaba ta hau daya side din tana jan bargon zata
rufa taji ance "good" ta zaro ido tana shirin sake jin mai fada,jin yayi shiru bai
sake cewa komai ya sanyata jan bargo ta lulluba tana addu'o'inta cikin zuciyarta
tana yiwa kanta dariya,wato ita mai wayo taqi shigowa ta gudu sai yayi barci ashe
idanunsa biyu,ta saki ajiyar zuciya wadda ba don kwanciyar kai da qafa sukayi ba da
zai iya jiyota
Yafi awa biyu yana yaqi da zuciyarsa,qamshin turarenta ke ban banta masa tunani,ya
rasa wace iriyar masifa ce,sosai ya san yana cikin wani hali amma baisan me yasa ta
sanadiyyarta yake samun kansa cikin wannan halin ba,sunsha zama haka shi da salima
idan ta masa laifi don ya hukuntata,suna daukan tsawon lokaci a haka ba tare da
kuma ya damu ba,saidai ita ta gaji ta hanyar gyara laifin da kuma bashi haquri,ya
runtse ido,da qarfi yake son tilastawa kansa sai yayi bacci,da qyar wani wahalallen
bacci mai cike da mafarkai yayi awon gaba da shi
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Kwana uku tayi babu cas babu as,duk abinda ta dauka zata yi sai yace "stop it,hatta
da shara kuwa kawai akan dan yatsanta guda daya,saidai ta faki idonsa ta kimtsa
inda taga bai dace ace ana barshi haka ba,da zarar kuwa yazo yaga alamun hakan zai
zuba mata ido wanda ta fassara shi da *eyes punishment*,sai ta sunkui da kanta
kawai ta wuce sum-sum-sum ta bar gun,kwana biyu yana gida yana jinya babu inda ya
fita,sai a rana ta ukun ya koma kan ayyukansa
Sosai itama ta rungumi karatunta tana jin dadinshi matuqa ta bashi mahimmanci mai
matuqar tasiri don ta sani zai sake jawo mata qwarewa da kuma daukaka ta fannin
aikinta,hakanan tana sake samun goyon baya da qwarin gwiwa daga gidajen rediyoyin
da take mu'amala da su,su kansu ko yaushe suna fadi mata yadda sukayi missing
aikace aikacenta masu cike da inganci da juriya

_*SANADI*_
🔱🔱🔱🔱🔱🔱🔱🔱
Cikin nasarori masu tarin yawa dukkan wani shirye shiryen bikin bude kamfanin suka
kammala,cikin watansu na uku da sati na uku a qasar ta sin,wanda cikin lissafin da
fadika keyi kwanaki goma daka iya zuwa a gaba koma sati guda wato next week zasu
iya komowa gida,tun sati uku da suka gabata ta kammala naga coarse din ta kuma fita
da sakamako mafi kyau duk cikin daliban
Tuni ya sayi injina masu kyau ya aiko da su gida ta container din max air wanda na
wasu kamfanoni ne da yakeson budewa idan ya dawo gida a kano cikin rukunin
kamfanoni dake sharada industrial area
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Tsaye take a kitchen sauri sauri take ta kammala girkinta saboda yau tayi late
sosai,sanye taje cikin trouser na mata sai rigar sanyi in and top ta saqa ce irin
saqar turawa,yar cikin har gwiwa take mai gajeran hannu ta saman ce iya qugu mai
dogon hannu,wuyan rigar yankan *V* shape ne,ta taje baqi sidik din gashinta mai
sheqi ta sake shi ya sauka gadon bayanta,kanta na saye da hular sanyi na mata mai
wadda a jikinta yaje saqale da teddy's qananu,shigar dark pink tayi tayi masifar
yin kyau kamar wata black American
Hankalinta sosai yayi gaba,ta bada duk wani attention nata kan girkinta don hatta
dan siririn mayafinta da tadan yafa da hular kansu sun zame don haka ko shigowarsa
bata ji ba,fresh milk shi din ma ya shigo dauka hade da ruwa don busy din da tayi
yau ya sanya ta mance bata ajjiye masa ba yadda ta saba,wani strong abu yaja
hankalinsa sosai game da ita,sai ya koma jikin freezer din ya jingina ya harde
hannayensa saman qirjinsa kamar yadda ya harde qafafunsa yana bin duk wani moments
nata da kallo
Sosai ta tsorata lokacin da ta juyo zata dauki ragowar markadaddun kayan miyan da
ta sanya a fridge saboda ganin mutum a tsaye unexpected,tsananin tsoro ya kamata
tayi baya zata qwalla qara don rudewa ma bata barta ta kalli fuskarsa ba sai kuma
ta taka bawon doya ta zame tana shirin shan qasa saboda santsin tiles da doyar ga
kuma ruwa
Gaba daya taji ya rungumeta tsam cikin jikinsa yayi hada bakinsa da nata don hanata
yin ihun,zaro ido tayi,cikin yan sakanni ya soma kashe mata jiki saboda yadda yake
sarrafa bakinsa cikin nata tamkar ya samu sweet qamshin turarenta na dada
ingizashi,cikin lokaci qanqani ya soma burkice mata har ya fara bata tsoro duk da
ita din ma tana cikin shauqin abinda yake matan,wannan shine karo na farko da ta
soma hada jikinta da wani da namiji a rayuwarta
Caraf tayi qarfin halin riqe hannunsa jin yana qoqarin shiga wani fage,sai lokacin
da ta hada hannuntabda nasan sannan ya soma dawowa saitinsa,cak ya tsaya da abinda
yake yi din,cikin sauri ta 6ashi daga jikinsa tana maida botiran rigarta hadi da
maida gashinta baya wanda tuni ya hautsine,kunyan da tsoro suka hanata tsaiwa ina
zata boye?,bedroom nasu ne su biyu duka,kitchen gashi a ciki,gudu gudu sauri sauri
ta nufi qofar ventilation da niyyar ficewa
"Hey you" taji aliyyu wanda ke jingine jikin kantar kitchen yana maida numfashi
yace "cak ta tsaya ita bata qarasa ficewa ba hakanan bata juyo ba "duba girkinki it
burns",sai a lokacin ta tuna doyarta data dora
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:02 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*part 2*
4⃣9⃣&5⃣0⃣
4⃣9⃣5⃣0⃣
Verry slowly ta juyo kanta a qasa ta kashe gas din ta sulale ta fice ya bita da
ido,sirrintacciyar ajiyar zuciya ya saki jikinsa a mace ya juya ya dauki abinda ya
kawoshi
Tamkar sirikinta haka ya koma mata gaba daya taqi koda kallonsa a haka ta zuba masa
abinci ta miqa masa taja kujera ta zauna tana wasa da nata abincin sai
jagwalgwalashi take da spoon baice da ita komai ba har kammala nasa,sai da ta miqe
tana shirin hade kwanukan ta maida kitchen taji yace "baki isa ba sit and eat" ya
tabo mata abinda taqi jini wato ace taci abinci,ta langabar da kai cike da fargabar
ya za'a yi ta iya cin abinci yanzu?,ita hasalima tun abin nan da ya mata dazu taji
cikinta ya cike amma taga ma shi ko ajikinsa tamkar bashi yayi ba,tamkar ba aliyyun
nan ba kamar kullum canza shi akeyi
Da qyar tayi spoon biyar ta fara yunqurin amai "stop don't vomit,go" hakan dama
takeson ji saboda haka da sauri ta kwashe kayan ta maida su,sai ta kasa zama afalon
tayi komawarta daki tayi shirin kwanciyarta ta nade abinta a gado duk da a lokacin
bata jin wani bacci,a hankali ta dinga tuna yanayin da suka kasance dazu da aliyun
moments din yaqi bacewa daga kwanyarta,unforgettable ta fadi hakan a hankali can
qasa,sai kuma wani murmushi ya subuce mata ta cusa kanta tsakiyar filo tana jin
kunyar kanta da kanta,qaunar aliyun take ji na sake linkuwa cikin ranta,wannan
shine karo na farko da suka taba body contact yana cikin saninsa,ta dinga tuna
yanayin qamshi da laushin jikinsa,kamar yadda shi dinma yana zaune a falon ya kasa
hasala komai ga ayyukansa nan a gabansa amma ya kasa koda sa password ya bude
computer din bare akai ga batun yin aiki,tun barci ma fisgarta a hankali har mai
nauyin ya saceta
A hankali ta soma ware idanunta saboda jinta da tayi tamkar tana rungume jikin
mutum,qamshinsa ne ya bata amsar,a hankali zuciyarta ta tsananta bugu sosai ta
gwada yunqurin miqewa saidai ina ya zagayeta ne da hannayensa,ta tsammaci bacci
yake ko magagin bacci ne ya sashi yin hakan saidai sanda ta sake yunqurin zare
jikinta karo na biyu sai taji shi cikin soft voice can qasan maqoshinsa yace
"relax,relax,am not going to do anything with you....just am feeling like am going
to froze,I need to warmth my body ar you clear?" Bata ce komai ba ta maida kanta ta
kwantar idanunta kan ribbon da hular sanyinta dake watse a gefe da alama shi ya
zare mata su don kanshi ya tura cikin gashin yana saukar mata da dumin numfashinsa
tsakiyar kanta
Ta lumshe idanunta sanda ya sake janta jikinsa sosai ya nutsa zara zaran yatsunsa
tsakiyar gashin nata yana sake sheqar daddadan qamshin turaren gashi data ke fesawa
kanta wanda ya cakude da na jikinta yana rarraba masa hankali,turarenda bai taba
jinsa kan matansa ba,hucin numfashinsa da ta ji ya dawo sauka bisa dokin wuyanta
shi ya sake rikita ta,cikin rawar murya tace "a....a....am" tsayawa yayi cak "is
there any trouble?" "N....noo" bata san sanda bakinta ya fadi hakan ba,sake matseta
yayi cikin faffadan qirjinsa a hankali dumin jikkunansu ya soma ratsasu,sanyin nan
mai ratsa qashi ya ragu matuqa,a hankali takejin wani calmness da bata jin irinsa
ba na shigarta,hakanan 2ani daddadan barci mai cike da nutsuwa ya saceta
Ya saki ajiyar xuciya jin saukar numafshinta alamun bacci ya dauketa,ya ciro daya
hannunsa yana sake shafa gashin,sam ya kasa daurewa gashinta na burgeshi matuqa
kasancewarsa mai son gashi,yaci gaba da shafa shi yana jin dadin santsinsa cikin
tafin hannunsa har shima nasa daddadan baccin yayi gaba da shi cike da mafarkai
kala kala
🔅🔅🔅🔅🔅
A hankali ta bude idanunta tadan juya bayanta ba kowa sai qarar saukar ruwa da taji
cikin toilet,qarfe biyar na asuba,ta zubawa qofar toilet din ido lokacin da taji an
bude ta,aliyyu ne ya fito sanye da rigar towel nan tasa mai budadden qirji,gashin
qirjin san nan ya kwanta luf baqi sidik da shi,suka hada ido da shi kansa akwai
moisture da alamu wanka yayi na ibada,ta lumshe ido hadi da cusa kanta cikin filo
ganin yadda ya kamata dumu dumu tana qare masa kallo,shi kam kau da kansa yayi
baiso ta kamashi da yin wanka ba ya dauki jallabiyarsa cumb da perfume nashi ya
fice falo,sai da taji ya fice sannan ta zuro qafafunta ta sauko ta shiga toilet din
don dauro alwala ta bada nata faralin
🔅🔅🔅🔅🔅
Kamar kowacce safiya tana kitchen tana hada masa break,tayi wankanta ta shirya
kamar yadfa ta saba saidai yau ta gaji da sa kayan nasara din haka atamfa ta saka
dinkin riga da skert da suka mata cif suka bi shape din jikinta,tana jin shigowarsa
lokacin da take juya chips cikin frying pan,addu'a ta dinga yi Allah yasa wani abu
yazo dauka yayi ya fice a kitchen din
Saidai addu'arta bata samu karbuwa ba don kai tsaye ya nufi ma'adanin plates ya
dauki qwaya daya hadi da jawo plastic chair guda daya daga cikin biyun dake ajjiye
a kitchen din ya dawo opposite dinta ya zauna,
Plate din hannun nasa ya hau miqa mata yana yamutsa fuska cikin shirin fita yake
"pls help me kada yunwa ta yimin illa" sai yaso bata dariya yadda yake ta faman
turo mata plate din idanunaa kamar zasu fada cikin frying pan din,tuni ta gama
karantarsa akwai shi da ci ta amshi plate din ta cika masa shi da chips din sannna
ta dora masa waina,dayar kujerar ta jawo gabansa tayi masa table da ita ta hada
masa tea ta dauko masa ruwa da drink ta dora mishi gaba daya,ta gama hada tea din
ta ajjiye masa ta miqe zata gudu don duk a atakure take jin ta don ta kasa hada ido
da shi gaba daya ,rashin kunyarsa ma ita take gani kamar baiyi komai ba harkarsa ma
yake free
"Thanks" taji ya ambata,cike da shakku da dimbin mamaki ta tsaya cak tana doubting
anya su biyu ne kuwa cikin kitchen din nan,don bata gasgata cewa aliyyun ne ya fadi
haka ba,don kawai ta hada masa break?,wace irin hidima ce mai tsauri wadda tafi
wannan batayi masa ba bai taba yabawa ba ko a ido sai wannan?,sai ta yanke shawarar
juyawa don ta tabbatar suka hada ido kuwa lokacin da yake kai chips bakinshi,sai ya
tsaya ya fasa kaiwa bakin nasa tare da daga mata gira "yes thank you" da sauri ta
juya zata fice don tana tsammanin aliyyu na karantar zuciyar mutum ne "come
back,zaki broking rules dina,sai na gama kya fita"kanta a sunkuye ta dawo ta
jingina jikin kantar kitchen din tana jira ya kammala
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Yadda wasu lamuran na aliyyi ke sauya salo ke bata mamaki idan yayi wani abun sai
ta dinga tambayar kanta anya aliyyu ne?,shi kansa baisan ya canza ba ,sau tari sai
ya tsinci kansa cikin sa'ido akan duk wani abu da ya shafeta duk wani movements
nata,shi da kansa sai yayi wani abun sai ya koma yana tambayar kansa how comes?,sai
kuma ya koma nazarin halaye da dabi'u nata shi kadai idan yana zaune perfect
attitude nata,yakan daga kafada yace "perhaps she concern about me I think shine
dalili na nima,true?"hakan zaita tambaya da baiwa kansa amsa
Sosai aliyyun yayi wani fresh yayi wata 'yar cika data qara masa kyau da
kwarjini,ya gama zirga zirgarsa ya dawo gida ya tarar da lafiyayyen abinci da
tsaftataccen muhalli kamar yadda yake so,ita din ma yanayin garin ya amsheta sosai
don fatarta ta sake yin kyau da santsi ainihin chocolate clour mai kyau,
Tun daga ranar sai kwanciyarsu ta koma haka,koda tana wani aikin bata shiryawa
kwanciya ba dole sai ta taho don yace mata umarnin likita ne ya dinga samun dumi
sosai a jikinsa(lol aliyyu 😜😜),ita din ma bata damu sosai ba duk da yana sata a
wani yanayi saboda tana samun dumi sosai wanda ke sata tayi bacci nutsatstse kuma
mai tsawo ba kamar da da sanyin ke hanata wani baccin arziqi ba
*to be continued*.......
  
[10/16, 2:00 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 2*
5⃣1⃣&5⃣2⃣
5⃣1⃣5⃣2⃣
Qarfe bakwai na dare ya shigo gidan bayan kammala sallar magariba da kadan tuni ta
kammala komai zaune take kawai tana duba saqonninta na email,kamar kowanne lokaci
da sallama ya shigo hannunsa daya riqe da rigar saman kayanshi da briefcase dinsa
daya hannun nasa kuma leda ce mai dauke da tambarin wani shago da suke sayar da
kayan sawa na mata,ta dago idanunta don amsa sallamar qwayar idanunsu suka hadu,ita
ta fara janye idanun nata don tasan idan bata janye din ba bazai fasa kallon nata
ba, "wani kallo ya koya" haka fadilan ke fada ko yaushe cikin zuciyarta duk lokacin
da yayi mata hakan,har wata rana bata sani ba zancan zuciyarta ya fito fili "see
you tell me what you think,me zan kalla a jikinki?" Hakan ya fada still kuma yana
ci gaba da kallon nata
Cikin falon ya qaraso ya zube kayan hannayen nasa saman kujera ya zauna hadi da
fadin "ya Allah" sannu da zuwa tace hadi da miqewa don zuba masa ruwan sha kamar
yadda ta sabar masa,baisan yadda akayi idanunsa suka bita da kallo ba,material ne
ajikinta dinkin riga da skirt,sosai dinkin ya fiddo duk wani sharp na jikinta,yau
babu rigar sanyin saboda yanayin sanyin da ya fara ja baya a qasar sai kawai ta
kunna na'urar dumama gida ta yafa dan qaramin dankwalin a kanta,tana tsugunne
gabansa ta cika cup din da lemo ta miqa masa 
Maimakon ya amshi cup din sai ya hade hannayenta duka biyun da nashi hannayen,dumin
tafin hannun nasa ya ratsa har ta qwaqwalwar ta,sosai yasa taji wani na yawo cikin
dukkan sassan jikinta,ta miqe da alamun tafiya zatayi ko zai sakar maya hannun
maimakon haka sai taji ya finciko hannunta ta fado jikinsa gaba daya tayi dirshan
kan cinyarsa,suka saki cup din duka su biyun ya tarwatse saman tiles din yayi
pieces
Sosai ya matseta tsakiyar faffadan qirjinsa yana cusa hancinsa lungu da saqo na
jikinta yana sheqar ni'imtaccen qamshin dake fita ta jikin nata,yamutsa ta yake son
ranshi sosai qamshin ke rikita shi,ya dora hancinsa bisa wuyanta hucin numfashin sa
ya daketa tsigar jikinta ta tashi,a hankali numfashin nasa ke kaiwa da komowa,tuni
ya soma birkita mata lissafi itama kamar yadda shi ya dade da fita daga nasa
hayyacin,qirjinta ke bugawa kamar tayi tseren gudu,tuni jikinta ya mutu murus ta
kasa wani motsi
Qarar wayarsa ce ta katse masa hanzarinsa,duk da haka bai bata damar tashi ba ba
tana jikinsa,yayi qoqarin daidaita nutsuwarsa sannan ya daga wayar "I will call you
back" kawai yace ya katse kiran tare da jefata kujerar gefansa,yakalli fadilan da
idanuwansa da suka canza launi kanta na sunjuye sai maqyarqyata take,sake matseta
yayi a jikinsa yana ci gaba da cusa kansa jikinta kamar zai maidata cikin
hancinsa,cikin kasalalliyar murya yace" da wanne perfume kike using?"karo na farko
da tambayar ta silmiyo daga bakinsa ba tare da ya shirya ba,
"am.....amw.....wan"jin gaba daya a gigice take yasa ya saketa, "shiryomin abinci
zanyi wanka" a hankali ta zame daga cinyarsa cikin gudu gudu sauri sauri ta fada
kitchen ya bita da kallo
Gaba daya jikinta rawa yake yana zaune shima a gun har ta soma debo kayan abincin
yana lure da ita,ruwanshi yake sha yana bin ta da kallo,sai da ya kusa tashi da
roba biyu,har barin miya tayi ta kuma taka ta santsin ya kusa dibarta kadan ya rage
tasha qasa sai da ya dan riqeta hadi da cewa "take it easy"sai da ta gama jera
abincin sannan ya miqe ya shiga wankan
Saman kujerar ta fada tana haki kamar wadda tayi tseren gudu,mirgina kanta kurum
take,ta rasa wanne tunani zatayi daga cikin tuna nukan da suka cushe a
qwaqwalwarta,me yake son canza aliyyun?ko kuma me ya canza shi din ma? Aliyyun da
yace bai sonta?aliyyun da yace bazai taba qaunarta ba koda wani lokacine a anan
gaba?me yasa yake son jikinta koda yaushe?bata da amsar kuma babu mai amsa matan
Sai da ya ritsata taci abincinta kamar yadda yake mata ko yaushe,ya jawo ledar da
ya shigo da ita ya tura mata" I think jibi ne bikin bude company,ga kayan da zakiyi
amfani da su nan" "thank you ta fada cikin sassanyar murya kanta a qasa don kallon
da yake mata yana takurata matuqa
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Da qyar yake iya jan numfashinsa saboda azabar da yakeji yana ciki,ji yake idan bai
kasance da ita ba kamar zai iya mutuwa,shi kansa yaga matuqar qoqarinsa a yadda
yana yin halittarsa yake,wata hudu babu wani abu yana cikin matsananciyar
sha'awa?,yana cikin matsanciyar buqata mai tarin yawa,baisan sanda ya sanya
hannunsa ba ya janyota a gigice ya matseta gam wanda hakan shi yayi sanadiyyar
farkawarta,tayi tsam tana jin yadda yake nishi numfashinsa na kaiwa da kawowa da
sauri da sauri tamkar yana shirin kufce masa,bata kawo komai ba cikin ranta illa
tunanin ko ciwon cikin sa ne ya tashi?
Tamkar a mafarki take gani,sosai taga lamarin na aliyyu da gaske yake gaba daya
kamar baya duniyar ya gama fita daga ainihin aliyyun ya burkice mata baya ji
hakanan baya gani,tabbas yana so ya mata abinda ta dade tana tsoro da
fargabarsa,ganin dan qarfinta bazai amfana mata komai ba sai ta koma magiya da
roqonsa yayi haquri,tamakar da dutse take magana ko wani kurman bebe,tuni ya gama
rabata da komai na jikinta sai 'yar mitsitsiyar vest da ta rage ajikinta wanda ita
kadai dama ta sanya don bata kwanciya da brassiere sai tasa vest mai dame jiki,
"pleeeeaaaaseeee aliyyu zaka jimin ciwo,pleeaasee kayi haquri don Allah" hannu tasa
tana rufe qirjinta saboda babu wani abu da vest din ta kare na surar
qirjinta,dukiyar fulaninta ta cicciko cikin vest din sunyo
Da hannunsa daya yasa ta riqe hannayen nata biyu yasa daya hannun ya tsarge vest
din gida biyu ya zareta ya wurgar,tuni dukiyar fulanin ta bayyana,wani iriyar
gigicewa yayi laushi da santsin fatarta ya kusa zautar da shi,bai taba karo da
qirar da ta taba tafiya da imaninsa ba irin ta fadilan tuni ya sake haukacewa kamar
mayunwacin zaki,kamar akuyar da ta shiga garken tumaki,magiya da roqon taga sunqi
tasiri gaba daya akan aliyyu sai ga barke da kuka,a hankali ya dinga lashe duk wani
hawaye da ya biyo kuncinta bai bari ko guda ya diga a aqasa ba,sannu a hankali ya
dinga kashe mata duk wata gaba ta jikinta da wani irin salon soyayya da bai taba
gwadashi kan wata diya mace ba,komai nata ya saki ya zare mata duk wata ragowar
qarfi da kuzari da ya rage mata
Sai da ya soma aiki tuquru sanan ta soma gane kurenta,ihun kuka ta soma saki a
maimakon hawaye zallah,kuka take mai hade da ihun,hawaye da majina kuwa tuni suka
hada kogo bisa fuskarta,cizo da yakushi kuwa har sai da ta gaji don kanta,tuni yayi
nisa cikin duniyar da bai taba koda giftawa ta kusa da ita ba,ya shiga wata duniya
mai wuyar fassarawa a gareshi,tuni sukayi hannun riga da wani abu da ake kira
hankali,tun fadila na fahimtar halin da take ciki har ta soma gane komai a hankali
idanunta suka rufe duhu ya mamaye mata idanu,dif komai ya dauke mata ba tare da
aliyyu ya sani ba
Gefe ya koma ya yashe tare da matseta gam cikin jikinsa ji yake kamar ya tsaga
qirjinsa ya maidata ciki,sosai ya rushe da wani irin kuka tamakar qaramin yaro,karo
na farko sa hawaye ya zuba a idanun Aliyyu haidar ta silar fadila tun bayan da ya
mallaki hankalin kansa,tuni hawaye sukayi male male bisa fuskarsa fadi yake a
zuciyarsa har ma a fili "alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus saalihat
(godiya ta tabbata ga ubangiji wanda da ni'imarsa ne abubuwa masu kyau suke
cika)ashe har yanzu akwai mata masu kai budurcinsu gidan mazajensu?ashe zai samu
wannan abun mai daraja?ashe dama babbar kyauta Allah yayi masa?ashe baiwa ce babba
a cikin gidansa bai sani ba?ashe gata abbansa yayi masa?ashe soyayya abban nasa ke
masa ta gaskiya?....ashe din ta aliyyu a lokacin mai dama ce,nadamarsa mai tarin
yawa ce,kuka yake sosai da hawaye masu tarin yawa kwance bisa fuskarsa
Wani abu mai girma yaji yana ratsa shi game da ita wanda tunda yake bai taba jin
makamancin hakan ba,ya dago da fuskarta yana kallonta,wani tausayi so da qauna
girmamawa da kunyarta suka rufeshi masu tsananin tasiri,ga shatin hawaye nan bisa
fuskarta da suka bushe sukayi alama,sai a lokacin yaji baijin sukar
numfashinta,yatsunsa ya sanya saman hancinta yaji dif babu alamun fitar numfashi,a
gigice ya zareta daga jikinsa ya wuntsulo daga kan gadon da gudu yayi
parlour,freezer ya bude ya dauko ruwa,jikinsa na rawa ya balle murfin ruwan ya
kwarara mata kan fuskarta,wani dogon numfashi ta ja hadi da saukar da ajiyar zuciya
mai nauyin gaske,muryarta can qasa qasa yadda bi jiyota sai da ya zauna tsakiyar
gadon ya dagota ya mannata da jikinsa yaji tana fadin "please kayi haquri kada ka
qara" qwaqumeta yayi ya dora habarsa tsakiyar kanta "relax am not going to repeat
it" jikinsa shi kansa rawa yake har yanzu,ajiyar zuciyar yake saki shima a kai a
kai tamkar marayam da ya ci kuka ya qoshi,kana kallonsu a lokacin dukkansu sai sun
baka tausayi dukkansu sun koma kalar tausayi
Azabar da fadilan keji ya sanyata sakin wani sabon kukan mai ban tausayi,radadi
sosai take ji kamar ana yankarta a gun,sake rufe ta yayi ruf da qijinsa yana cewa
cikin rawar murya da ta jiki "am sorry fadila am sorry please"
Duk da tana jin jiki kalaman sun bata mamaki,aliyyu?,aliyyu ne?"a hankali yake
dauke hawayen nata da harshensa yana shanayesu gami da shafa kanta zuwa bayanta
alamun lallashi yana fadin "am sorry...am sorry"abunda bakinsa kawai ke iya
nanatawa kenan kamar karatun sallah,sunfi minti arba'in a haka dukkansu suna sakin
ajiyar zuciya,ita bacci ya fara dauka don shi kam ko alamaunsa bai ji,a hankali ya
zamar da ita ,ido ya zaro ganin yadda jini yayi face face kan farin bedsheet
din,tausayinta ya sake kamashi,shi kansa yasan bai mata kadan ba,ya riga ne ya fita
daga hayyacinsa,hannu yasa ya yaye shi gefe ya kwantar da ita a ahankali don kada
ya tasheta yaja mata bargo ya lullubeta,yasa hannunsa ya kama mata gashinta da ya
yamutse gaba daya ya daure mata shi guri guda,fuskarta da tayi fayau ta bayyana a
dan hasken fitilar gefan gadon
Zaman dirshan yayi yana gadinta duk wani motsi nata na kan idonsa,ranar duk
qwarewar bacci kan iya sata haka ya haqura yabar aliyyu,har asuba yana zaune
dirshan idanunsa na kanta tana wani wahalallen bacci
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:03 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?....*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 2*
5⃣3⃣&5⃣4⃣
5⃣3⃣5⃣4⃣
Jinta kawai ruwan zafi na ratsata,a gigice ta farka saboda azabar zafi,a rude ta
qwalla wata gigitacciyar qara duk da muryarta a da she take,ta riqe hannunshi sosai
tana sheshsheqar kuka "calm down please,u wil get fine,pain din da kike ji zai
ragu" ya fadi cikin taushin murya da kwantar da kai,ba yadda ta iya haka ta maida
jikinta tayi laqwas tana jin yadda zafin ruwan ke ratsata har gun ciwonta,a hankali
ta dinga jin zafin na dan raguwa sai a lokacinne kuma ta fara lura ashe haka
aliyyun ya sunkutota babu komai a jikinta,hannu tasa tana kakkare qirjinta
Shi din ma tun dazun yake qarewa halittarta kallo tana ci gaba da attract nashi ji
yake kamar ya maidata ruwa amma raunin da yayi mata shi kansa ya san yayi
barna,hankalinsa ya bar jikinsa ne however ma baiyi zaton zai sameta da virginity
dinta ba,sai da yayi matuqar kai zuciyarsa nesa kan fadilan saboda yadda surarta ke
fusgar hankalinsa,ba halitta ce da zaka iya kalla sau daya ka kau da kanka ba,wanka
yayi mata ya nadota a towel kamar wata baby ya maidota daki,kunya babu kalar da
fadila bata jita ba yau,shi yasa mata pant har da brassiere tana ta ture hannunsa
kan ya qyaleta zata sa saidai yace "am sorry ki barni kawai,ba zaki iya komai ba"
ta rasa wacce iriyar rashin kunya ce da aliyyun,doguwar riga ya zira mata harda
hijabi ya shimfida mata dadduma sai da yaga ta hau sallayar sannan ya shiga nasa
wankan
A kwance ya dawo ya taddata kwance saman abun sallar,komawa taga yayi ya ciro wasu
capsule ya zaunar da ita ta sha sannan ya tayar da sallah,tuni bacci ya sake
dibarta kafin ya idar nan kan abun sallar ko azkar din ma bata samu tayi ba,cak ya
dauketa a hankali don kada ya yada ta kan gadon ya maidata ya zare mata hijabin
sannan ya ja lallausan bargon ya rufeta zuwa wuyanta,zaman dirshan yayi kusa da ita
yana kallonta tamkar an bashi assignment a kanta,wani abu ke ci gaba da ratsa
zuciyarsa,sosai baya ga qauna yake jin qimarta da darajarta na sake linkuwa cikin
zuciyarsa,tunaninsa mai zaya mata a duniya tukuici zuwa ga tarin kyautatawarsa
gareta?,me zaya mata wanda zai saka mata kan wannan baiwa tata yau da ta masa
kyautarta dungurun gum,kyautar da bai taba katari da makamanciyarta ba?,dame zai
faranta ranta da shi a fadin duniya?,she deserve anything
Qarfe takwas na safiya a gogon garin har lokacin baccinta take gashi fitar dole ta
kamashi saboda yau baqinsa zasu soma isowa,dole shi zai kama masu hotel da zasu
zauna andi kuma aikin da ya basu yayi yawa bare ya hada masu da wannan,ga mukhtar
(abokinsa ne na kusa)bai qaraso qasar ba bare ya hada shi da aikin,don haka fiya ta
kamashi dole,idan banda wannan dalilin kam baijin akwai abinda zai fidda shi daga
gidan yau,ya gama shiryawa tsaf cikin suit kamar yadda ya saba sai da ya shiga
kitchen ya hada mata tea ya zuba cikin flask ya soya mata chips da qwai ya hada da
cups yayi dakin don kada ta tashi babu abinda taci,ya qaraso bakin gadon bayan ya
ajjiye tray din kan 'yar locker din nan ta bedside yana sake kallonta,baccin take
kawai ko motsawa batayi,shi kansa yasan dole ne kam tayi bacci,ya zira hannunsa a
hankali ya sake maida mata gashinta gefe,karon farko cikin nutsuwarsa ya sanya
tattausan lebensa ya sumbaci goshinta sannan ya maida leben nasa saman nata leben
masu taushi da siranta,ya dan jima yana sheqar hucin numfashinta dake shiga
hancinsa yana masa dadi yana jin kamar tana qara masa wata ruyuwar ne ta musamman
Hot kiss ya bata wanda sai da yasa tadan motsa kadan ya miqe yana sake kallonta
tare da hade tafin hannunshi da nata,baya son fitar ko kadan,ya sani tana da
buqatar kulawa,sai da ya qoshi da kallon nata sannan can qasan maqoshinsa yace"i
will back soon" tamkar yana magana da wadda ke idanunta biyu,ya fice a dakin yana
waiwayenta hadi da ja mata qofofin gidan
Cikin ayyuka yake da mutane saidai duk wani motsi da zaiyi qwaya daya tana manne
cikin zuciyarsa,kaf hankalinsa na gida gangar jikinsa ce kawai a nan,har wasu
abubuwan mancewa yake maimakon ya fadi sunansu sai yace "fadilah",sai kuma yace
musu "am sorry I mean kaza.....",Allah Allah yake ya kammala abinda zaiyi ya koma
gida saidai yana murna ya kammala sai kuma wannan ya bullo dole haka yake sake zama
yayi settling
Da kanta taji ta qoshi da baccin ta farka bakinta dauke da addu'ar tashi daga bacci
*"Alhamdulillahil lazi aa faani fi jasady waradda alaiyya ruhi wa'a zina li
bizikrihi"*,tayi niyyar miqewa kamar yadda ta saba saidai jin yanayin jikinta da ya
canza shi ya tuno mata abinda ya faru da ita jiya tsakaninta da aliyyu
Daki daki komai ke dawo mata,tana tuno moment din tar cikin kwayarta *"wanne turare
kike amfani da shi?"* tambaya daya da ya maimaita mata ita sau biyu kenan a
jiya,sannu a hankali tunaninta game da turaren ya soma dawo mata *"hasbunallahu wa
ni'imal wakeel"* ta fadi cikin zaro ido da matsananciyar faduwar gaba,da sauri ta
diro a gadon tuni ta mance wani ciwo da take,kai tsaye gun jakarta ta nufa inda
taje rataye,tasa hannu ta cirota cikin rawar jiki ta soma laluben turaren ta
ciroshi hadi da zuba masa ido tamkar yau ta saba ganinsa
Da sauri ta daga jakar ta zazzage ta kafataninta,dukkayan ciki suka zubo,tarkacen
magunguna da suka siya ne gun fa'iza,wannan turaren da nake shafawa shine?shine
wannan turaren mahadin magungunan?" Jakar ta saki qasa hadi da komawa baya ta zauna
kata ta dafe hadi da sakin wani irin kuka mai cin rai, _*"saboda sha'awa aliyyu ya
tara da ita ba don so ba?turare shi ya ja hankalinsa kanta ba qauna ba?me yasa nayi
gaggawar baiwa aliyyu kaina ne?me yasa na amince na yaudari kaina? Tabbas aliyyu
bai sona kuma ta yarda bazai taba sonta din ba"*_,jikinta ne ya burgeshi ko me? Ta
ci gaba da fada cikin zuciyarta,tuni ta gama sarewa,ta gama yankewa kanta qauna da
zama tare da shi,babu irin abunda bata gwada ba amma babu nasara to sai yaushe?sai
yaushe nasarar zata zo mata ne? Da gaske kenan hasashen anty hafiza na zai soki
fadila wataran son da bai taba tsammani anawa wata diya mace irinshi ba,ai babu
*wanda yasan gobe sai Allah* ya zama mafarki........?,tana jin wannan karon ya zama
dole ta zare aliyyu daga cikin tsarin rayuwarta,ya zama dole ta rabu da shi haka
nan ya zama dole ta nisanceshi,ta gama yin duk abinda ya kamata tayi.....ta gama
duk abinda zata iya....ta gama bashi kuma duk wani abu da take da
shi,kulawa.....tattali....tausayi da soyayya......kai harma da jikinta da zuciyarta
gaba daya amma aliyyun ya gaza samuwa,to me yayi saura?,bata da wani ragowar abun
bashi banda ta bar masa sararin rayuwarsa itama ko ta samu salama?
Cikin azama tamkar ba mai ciwo a jiki ba ta hada kan kudaden(yuan) da ya jima yana
bata su har take ganin basu da wani amfani a gurinta,ta bude locker da ta ajjiye
passport dinta ta dauka,har ta juya tana shirin fita sai ta dawo da baya a
hankali,ta yagi paper cikin takaddunshi ta dauki biro ta ja dressing chair ta
zauna,tafi minti biyar da dora alqalamin kan takaddar saidai hawayen da ya cika
mata ido ya soma diga kan takaddar ya hanata ganin komai,ta miqa hannunta ta yago
tissue ta tsane hawayen sannan ta samu damar ganin ta,cikin kasala kamar mai ciwon
'yan yatsu hannayenta suka soma rubuta abinda ke qunshe qasan zuciyarta
*duk da na sani cewa saqona ba wani abu bane da zai dameka ba,domin kuwa ina
tsammani irin saqon da ka dade kana tsammani daga gareni*
*aliyyu na soka irin son da ban taba yiwa wani halittar da namiji ba a duniya ba,na
soka tun kafin na gama sanin wane ne kai,na soka son da ban yiwa kaina shi ba,na
soka a fili na soka a boye*
*saidai kash! Aliyyu ka qini qin da ban taba ganin ka yuwa wata halitta shi ba,ka
tsaneni tsanar da na gaza canko mai na maka da zafi haka a rayuwa?,ka qinin ne
kamar yadda ka fadamin gaskiyarka tun farko kace baka sona kuma ba zaka taba sona
ba hakanan kada nayi tsammanin kuma cewa wata rana ko anan gaba zaka soni*
*A lokacin na dauki zancan tamkar tatsuniya,na dauki zancen tamkar wani labari da
wata rana zai iya shafewa ya gushe,ashe na tafka kuskure,nayi kuskure ba dan qarami
ba,nayi abinda ni zan gushe ba zancanka ba,ashe ba zaka sonin ba har abada kamar
yadda kace din,naji...na gani na kuma gamsu aliyyu...dama hausawa sunce jiki
magayi,haka din ne ni ganau ce ba jiyau ba*
*a yau na rabu da kai aliyyu kamar yadda kake bege....na fita a rayuwarka kamar
yadda kake muradi.....,wata qila lokacin da kake karanta wannan saqo na dade da
fita daga rayuwarka,kuma na yima alqawarin fita fita ta har abada.....koda sonka
zai samo sanadiyyar daina numfashina a duniya,I promise I leave yiu
forever.........😔*
*na sani ko ban roqeka ba abu ne mai sauqi in samu sakina daga gareka,to ina fata
zata zamo rubuce jikin takarda don samun shaida ta kuma samu isuwa zuwa ga magabata
na,na gode da jurar zama da kayi da halittar da baka so cikin inuwa guda.......na
gode da da ci...sha.....suttura da ka dinga bani ba tare da zulunci ko gajiyawa ba
thanks for everything,na gode na gode....🙏🏻*
Ta ninke wasiqar cikin wani irin kuka mara sauti mai azabar cin zuciya da azabtar
da rai,gefan pillow din da ta tashi ta ajjiye ta,cikin azama ta rataya jakarta ta
fito hadi da jan qofar gidan,tana son koda sallama ne tayi da maqotan arziqi nadiya
da mr lin amma bata son su fahimci wani abu har suyi yunqurin tsaidata,zuciyarta ta
riga ta qeqashe duk radadin da ciwonta ke mata hakan bai dameta ba burinta kawai ta
baf qasar,burinta ta fice a qasar ta china da take kallonta baqiqqirin
Tana bayan taxi din ta ciro katin tana dubawa ta fada masa address din inda zai
kaita branch ne na kamfanin ethopian airline taje ta fara rage bucking tunda tim
din fitarta a qasar bai cika ba,cikin lokaci qanqani suka qaraso tace masa ya
jirata yanzu zata fito
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:04 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 2*
5⃣5⃣&5⃣6⃣
5⃣5⃣5⃣6⃣
Da sauri ta koma gun mai taxi ta shige gidan gidan baya tana bashi umarnin su wuce
airport,koda suka je kasa zaune tayi babu abinda take banda duba agogo hadi da
sharar qwalla
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Da qyar aliyyu ya samu ya yage aiki da kuma jama'ar dake dakonsa,ya bawa jumong
umarnin ya maidashi gida,cikin motar ya zaro wayoyinsa ya kira lukas yace kada a
nemeshi ko menene ya taso shi ko mukhtar yayi handling dinsa,ya wuce gida ne madam
ba lafiya,cikin girmamawa ya amsa masa,ya cire wayar daga kunnensa ya hada da wadda
ke ajjiye kan cinyarsa ya kashe su gaba daya,ya zuba su cikin 'yar jakar laptop
dinsa
Jumong ya tsaida motar aliyyun ya fice,jumong din nata yi masa sallama amma hannu
kawai ya iya daga masa ya shige gidan,fuskarta kawai yake da muradin kallo,ita
kadai yake son gani,ta bashi wani abu mai tsada muhimmanci da daraja agun 'ya
mace,ta bashi abunda ya kasa samu shekaru masu dama,abinda ya debe tsammanin ana
samunsa gun matan yanzu,yana jinta sosai cikin jikinsa zuciyarsa ruhinsa...yana
kuma jin wani matsayi da daraja mai girma nata cikin idanunsa
Wullar da jakar tasa yayi kai tsaye ya nufi bedroom don yafi tsammanin samunta a
can,yanayin yadda dakin ya dan yamutse ya danji mamakin ganin hakan,saboda bai saba
gani ba ko tsinke bai taba katarin tsinta cikin kitchen dinta ba ballantana
bedroom,to amma bai kawo komai cikin ransa ba sai ya dan ganta hakan da yanayin
raahin jin dadin jikinta,saboda haka ya juya ya koma ya duba kitchen,shi yana nan
kamar yadda ya barshi da safen babu wani abu da ya canza,sai ya sake komawa bedroom
din yana bawa ransa tana toilet to
Gefan gadon ya zauna yana zaman jiranta wanda daidai yake da a kirashi da zaman
jiran gawon shanu,har sai da ya dan soma qosawa ya miqe bayansa sama gadon fuskarsa
na kallon ceiling,sai yaji qayau qayau kamar ya kwanta kan wani abu,yasa hannun
nasa qasan bayansa ya zaro ta yadan jujjuyata sai ya wullata daya gefan gadon,ya
mirgina kansa da niyyar duban qofar toilet din sai idanunsa suka sake kaiwa kan
takaddar,sai ya tsinci kansa da son budeta yaga mene a ciki don bata barin komai
saman gadonsu
Yana daga kwancen ya jawota ya warwareta yakai idanunsa ciki ganinta cike taf da
rubutu ya bashi mamaki,paragraph din farko kawai ya karanta sai gashi zaune dirshan
tsakiyar gadon ba tare da ya san yaushe ya tashi ba,kafin aliyyu ya kammala karanta
saqon tuni ya jiqe da gumi duk da ragowar sanyin dake qasar ta sin,ya kammala
karanta layin qarshe na takardar gami da cukuikuyeta cikin tafin hannunsa da
qarfi,rawa kawai jikinsa yake tamkar sojan da aka bugawa kugen yaqi,launin idanunsa
tuni sun canza daga ainihin fararen nan qal masu haske zuwa jajaye,babu launin na
alamun tashin hankali a lokacin da bai bayyana bisa fuskarsa ba,tsananin tashin
hankalin da yake ji a lokacin bazai misaltu ba "why?why fadilah?me yasa kika yimin
gurguwar fahimta?,me yasa kika fahimceni a abaibai?,ina zaki tafi?ina zaki tafi ki
barni?,ba haka bane fadilah....ba haka bane abinda kike zato"shi kadai keta
wadannan sumbatun ya dunqule hannayensa cikin junansu takardar na tsakiya
Safa da marwa take cikin departure din,hankalinta a tashe yake gani take tamkar
aliyyu zai biyota ne ya hanata tafiya,wani bangare na zuciyarta ke tunatar mata
babu yadda za'ayi aliyyun ya biyota,abunda kake qauna shi kake nunawa kulawa da
damuwa da halin da kake ciki,koda sace ta akayi bata tsammanin aliyyun zai biyo
sawunta bare tafiya tayi da qafafunta,duk da haka hankalinta bai kwanta din ba sai
da suka hau layin shiga jirgi,ko anan din ma bata fasa sharar hawaye ba,sam bata
damu da yadda jama'ar keta kallonta ba har wasu kan gaza shiru suce mata "sorry"
kallon da suke mata bai dadata da qasa ba don ji take tamkar ansa mata wani hijabi
ne cikin zuciyarta,tuni kowa ya kama sit din sa ya zauna tana sit 34 A,sanarwar
daura belt ta biyo baya bayan an rufe qofar jirgin,a lokacin ta tuna tahowarsu da
aliyyu qasar ranar da ta kasa daura belt dinta,kuka ne sabo ya sake qwace mata
*kukan baqincikin rabuwa da shi ne ko kuma na farincikin rabuwa da shi ne?kukan
shaquwa ne ko kuwa na kewa ne?* oho ita kanta bata sani ba,ita dai kawai ta tsincin
kanta tana yinsa,a hankali jirgin ya soma qugi yana motsawa sannu sannu har ya ware
sosai ya fara shawagi kan kwaltar dake doron qasa
Tafi yafi har suka zo list din qarashe wanda suka sanar masa jirgin yana daf da
cillawa sama,daga qarshe sunan fadila Abbas Bashir ya bayyana,cikin azama ya
dakatar da su yana fadin"mai wannan sunan nake nema" "ai tana cikin wadanda jirgi
zai daga da su nan da yan sakonni" cikin sauri ya tashi yana fadin yana son a
dakatar da tashin jirgin,cikin girmamawa yace "sorry sir bazai yiwu ba mun riga mun
gama handling din komai,duk ma'aikatan mu sun san da tashin nasa,haka na qasar da
zai sauka" da qarfi ya doki sama table din cikin zafi yace " I said stop the flight
now!!!" Ya sake rusunar da kansa yace "sorry sir it can't,but idan kana buqatan
tafiya zuwa nijerian ne sai amaka printing ticket"
Ya harde hannayensa a qirji ya lumshe ido yana maida numfashi,shi kadai yasan yadda
zuciyarsa ke masa zafi da quna,shiru yayi tamkar baza ya furta komai ba
"hasbunallahu wa ni'imal wakeel" yake karantawa cikin zuciyarsa,a hankali ya soma
jin temper din na nasa na raguwa,still idanun nasa na alumshen yace"ok ina son
jirgin da zai kuma tashi anjima" "sorry sir yau babu jirgin da zai kuma zuwa
nijeria" "gobe da safe " "sai da yamma sir" "noooo!!!" Ya fadi sa qarfi hadi da
bude idaunsa wadanda suka kuma zama manya ya ware su sosai kan ma'aikacin,ya sake
dan rusunar da kansa gami da cewa"sir sai da yamma kayi haquri"shirun ya sake yi
yana ci gaba da kallonsa,cikin ransa yake dana sanin rashin mallakar jirgi na kansa
da yaqi yi a baya bayan yana da damar hakan,sai da ya gaji don kansa sanan ya sanya
hannu cikin aljihunsa ya fito da kudi wanda baisan nawa bane ya ajjiye masa,ya miqa
masa ticket sannan cikin sauri ya irgi kudin su ya muqawa aliyyun sauran saboda
gudun kada ya karya dokar qasarsa,wani irin wawan kallo aliyyun ya watsa masa wanda
ya sashi janye hannunsa shi kuma ya fice abinsa
Tafiya ce mai tsawo tamkar a zuwan ta kawosu airport din addis ababa,hamdala tayi
da taji cewar nan da awanni biyu jirgi zai sake kwasarsu ya miqa su nijeria kanon
dabo babu batun kwana kenan a ethopia,hakan yayi mata dadi sosai don burinta kawai
shine ta bude idanunta ta ganta cikin nijeria zuwa lokacin idanunta sun sake yin
luhu luhu saboda kuka wanda ta kasa tsaida shi
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Qarfe takwas na dare agogon nijeria jirginsu fadila ya landing cikin aminu kano
international airport,sannu a hankali passengers suka soma saukowa,tun sanda suke
kusa da sauka ta soma tunanin ina zata nufa?gata dai a nijeria?,ba zata nufi
gidansu ba ko giyar wake ta sha,ta sani idan dai har taje din babu shakka babu
ruwan abbanta ko umminta zasu maidata ne gidan aliyyu hankali kwance,ta tabbata ko
ta bakinta ba zasu buqaci ji ba,bayan ta riga ta yiwa aliyyu da ita kanta alqawarin
yanke zamansu,ta masa alqawarin yin nesa da rayuwarshi,a yanzun bata da muradi ko
digo kan ci gaba da zama da shi
*"ta inda aka hau ta nan ake sauka"* haka zuciyarta ta gaya mata,take ta amince da
batun zuciyar tata,ta yiwa daya daga cikin direbobin airport din magana kan inda
zaya kaita,take ya amince tare da tsula mata kudi,bata damu ba ko a duska din ita
ba wannan ne a gabanta ba,ba ta wannan take ba ta kanta kurum take yi
Har a lokacin hawaye bai daina bin fuskarta ba kamar yadda bata fasa gogeshi ba,har
ta soma jin babu dadi saboda kukan da take,har qofar get din gidan mai taxi din ya
ajjiyeta,ta fidda kudinshi ta bashi,unguwar ba kowa shiru kasancewar haka yanayinta
yake koda da rana ma balle dare,ta qarasa ta qwanqwasa get din,mai gadin ya yaso
yana tambayar wane? dare ya soma a lokacin don tara ma ta gota,"nice" ta amsa masa
bai dai gane wace din ba har sai da ya leqo ta 'yar qaramar qofar dake maqale jikin
get din,cikin rawar jiki ya soma ture wagegen get din yana fadin sannu da zuwa
hajiya,ga tsammaninsa a mota take,shigewa kurum tayi ta ajjiye masa dari biyar
canjin da mai mota ya bata bisa bencinsa tana cewa "rufe get dinka bada mota nazo
ba"yawan kyauta da fadila ke dashi yasa yake daukin zuwanta din bata taba ahiga ta
fita bata yi musu ihsani ba
Tana shiga anty hauwa na fitowa daga kitchen da yake qofar shigowa falon opposite
qofar kitchen din ta ne na qasan,hannunta dauke da food flask guda biyu,baki ta
saki galala bayan ta tsaya cak tana kallon fadila,har ta bude baki zata yi magana
sai ta lura da yanayinta a hargitse taje ba kamar yadda ta santa ba ba lamaun
nutsuwa tare da ita,mamakinta yaushe suka dawo daga china babu labari?,kan tace
komai din fadilan ta share wani qwallar "subhanallahi" anty hauwa tace ta qaraso da
sauri ta dire flask din saman kujera ta kama hannayen fadilan tana fadin "lafiya
fadilah?"a rude,"daga ina haka?" "Daga airport nake anty" ta bata amsa murya a
dashe
Bata kuma cewa komai ba don tasan ba lafiya ba ta ja hannunta suka bi ta wani dan
madaidaicin corridor dake hannun hagun falon,dakunan bacci ne ciki guda uku,daya na
baqi wadanda baza'a kaisu boys quarters ba daya na yaranta wanda du sun kwanta
bacci kasancewar da wuri take sasu suna yi saboda makaranta,daya kuma nata ne duk
da ba kwana take ciki ba sosai ko yaushe suna sama a tare da mi gidan ta saidai
idan yayi tafiya ne,ta tura qofar dakin suka shiga tare,daki ne mai kyau kamar
sauran dakunan bakin gado ta zaunar da fadilan hadi da cewa"kiyi wanka kiyi
sallolinki,nasan cewa ba lafiya ba lo baki gayamin ba"ta miqe ta fita jim kadan ta
dawo dauke da wani cooler madaidaita guda biyu na baincin daya hannun nata kuma
sabuwar abaya ce ta ajjiye mata,"ga abinci kici,ga kaya ki sauya don kifi jin dadin
jikinki,zani na sallami abbansu kausar right?"ta qarashe da tambayar fadilan,kai
kawai ta gyada mata kamar qadangaruwa a sanyaye anty hauwan ta juya ta fice
Cikin abinda anty hauwan tace tayi abu uku ta iya wanka canza kaya sai sallah,tana
zaune akan darduma tana share hawayen dai nata,ta yanke hukuncin da taga shine
daidai saidai ta rasa me yasa zuciyarta ke son bijere ma umarninta?,anty hauwa ta
turo qofar ta shigo ,a sanyaye fadilan ta dago kanta tana masa mata sallamar sai
kuma wani dan kukan mai dan qaramin sauti ya kubce mata ta sunkui da kai,dirshan
anty hauwan ta zauna gabanta ta riqo hannayenta "cool down fadila mana,ki nutsu ko
gayamin me yake faruwa?,ni kuma na miki alqawari tunda kika zabeni kika kawomin
matsalarki zanyi qoqarin warware miki ita"cikin sigar lallashi har anty hauwa ta
ciyo kanta ta tsagaita kukan duk da hawayen dai basu bar zuba ba
Ta danja majina irin ta mai kuka tace "anty so nake na rabu da aliyyu"zaro ido
antyn tayi har da sakin hannun fadilan,daga bisani ta tattro kalaman tambayarta
"saboda me fadila?,me ya shiga tsakaninku haka bayan kowa na ma ali murnar morewa
aure yanzu?kowa sha'awar zamanku yake?,"murmushin takaici ne ya kama fadila ta
girgiza kai "anty zaman mu abun sha'awa ne ga wanda baisan halin da nake ciki ba,ni
da nasan me nake ciki banga abun sha'awar ba,banga sha'awa ga tilastawa wanda bai
sonka ya zauna tare da kai ba,kin taba ganin inda anty wuta da ruwa suka hadu suka
cakuda suka zauna kuma suka rayu suka wanzu gu daya?,banga abin shaawa ga
zamantakewar auren da babu soyayya cikinta ba sai zallar qiyayya,anty aliyyu na
cutar da ni ta hanyar rashin samun soyayya da kulawarsa,hakana ina matuqar cutar da
shi ta hanyar tilasta masa zama da ni baya baya so,baya sona,ina cutatsa ta hanyar
sashi kallona a matsayin matarsa,bayan ya gayamin baya sona bakuma zai taba sona
ba,don me zan zauna anty allah ya kamani da haqqin cutar da shi?" Ido ta kuma
zarowa tace"kamar yaya fadila,kimin gwari gwari ki daina min zancen kurma da bebe"
Ta dago tsaf tana kallkn antin don mafita yanzu take nema,so take ta canza
rayuwarta yanzu,so take ta bude sabon babin rayuwa ta manta komai,rayuwartatake so
ta maida ta ta mafarki ta fara ta gaske,tana so ne ta manta da aliyyu ta manta ta
taba sonsa,baya sonta(a zatonta) itama ya kamata ta qishi(nikam nace hmmm zaiyiwu
kuwa????)hmmmmm muje dai zuwa ga *part 3*
🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*alhamdulillahi rabbil alamin,wassalatu wassalamu ala man talaqqal qur'nu mi ladun
hakimul khabir*
🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*godiya ga mahaifana*
*sannan godiya ga dukka members din group dina huguma novels readers da dukkan wani
masoyi na wa yasan gobe,Allahbya bar qauna ameen summa ameen*
🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*kuci gaba da bina da jin yadda wannan rikita rikita zata kasance,meye ra'ayinku
game da jaruman wannan littafi?ina saurarenku ta number wayata*
*na gode*
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:08 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 3*1⃣
0⃣
A hankali ta bude bakinta tace "anty *ta inda aka hau ta nan ake sauka* ,kece silar
qulluwar igiyar aure na da aliyyu,ranar wanka kuma ba'a boye cibi"............A
nutse cikin hikima ta soma labarta mata tun ranarhaduwarsu da aliyyu,ta fara sonshi
tun kafin tasan waye ne shi,hakanan tun kafin shima ya san tana yi,ta rufe da cewa
"sai ajiya na sake tabbatarwa aliyu ba sona anty yake ba bisa wani qwaqqwaran
dalili nawa"(ta rufe ba tare da ta gaya mata ba),tayi shiru hawaye na diga a
fuskartaShuru anty hauwa tayi don ta kasa cewa komai,ta jima cikin jimami,ta jima
tana gyada kai kafin daga bisani ta saki nanauyan ajiyan zuciya "fadila sannunki da
qoqari,ba shakka ke din jarumar mace ce mai son farincikin iyayenta,kin cika 'ya ta
gari kuma 'yar halak,dama wannan zaman kike amma bamu taba gani ko a fuska kin nuna
alamu ba?,tabbas aliyyu zaici qaniyarsa duk hukuncin da kika daukar masa ya dace da
shi,wanne taimako kike da buqata a guna fadila fadeshi,kowanneiri ne zan iya miki
shi,nayi da na sanin zamowa silar hada aurenku,na zamo silar xamanki cikin qunci
bayan ni ima zaune cikin walwala"anty hauwan ta fadi cikin takaiciGirgiza mata kai
fadilan tayi "kada ki soma dana sani anty,domin kuwa qaddarar Allah ce,ya hukunta
hakan dole sai ya faru koda babu ke anty......alfarma daya nake so anty....bana son
kowa ya san ina gidan nan koda kuwa 'yan gidan mu ne,bana son in sake tozali da
aliyyu har sai ya ban sakina,rabuwa nake son nayi da shi saboda na barshi ya sake
yayi rayuwarsa ba takura,in barshi ya rayu da masoyansa don rayuwa tare da miqiyi
cikin inuwa guda ciwo ne da ita"ta fadi maganar tana jin wani daci har kan
harshentaSosai anty hauwa taji wani tausayi nata har cikin ranta ta girgiza kai
gami da kama kafadarta"indaiwannan alfarmar kawai kike nema fadila baki da
matsala,kin samu dari bisa dari,amma in one condition.....sai kin min alqawarim
cire wannan damuwar daga zuciyarki,kin bar wannan dan banzan kukan da kike,ba
lokacin ki bane na kuka yanzu lokacin aliyyu ne har taya shi ya kamata ayi saboda
asarar mace irinki da yake shirin yi,asarar da bazai taba maye gurbinta ba,dubi
fuskarki yadda ta canza saboda tsananin kukaMurmushin yaqe tayi"insha Allahu na bar
kukan anty daga yau,bazan sake zub da hawayena ba akan aliyyu,yadda bay sona ni din
ma na bar sonsa kenan har abada" "good" anty hauwa tace tana dariya hadi da girgiza
hannayen fadilan,sai kuma kunya ta dan kamata yadda ta taqarqare tana gaya mata
bata son dan uwanta ita kuma ta kuma tana bata goyon baya ba tare da son kai ko
zuciya ba ta sunkui da kai,Murmushi anty hauwan tayi "kada ki ji kunyata fadila
gaskiyarki kike fadi,kowanne hukuncikuma da kikayi yayi daidai,don wallahi kinji na
rantse miki mace dai dai ce zata iya irin zaman da kikayi ba"🔅🔅🔅🔅🔅Ya sallami mai
taxi din da kudin da shi kansa baisanyawansu ba sannan ya shige gidan,bisa kujerar
falo ya zube yana maida numfashi,wani azabar ganinta yake son yi ,a hankali ya kai
idonsa inda ta saba ajjiye masa ruwa da drinks wayam gun yau ba komai,ba qamshin
girkinta babu na freshner dinta,sai yaji gidan tamakar kango garin ya koma masa
tamkar maqabarta,burinsa kawai gobe tayi yafice ya bar qasar,wayarsa ta soma karadi
ya cirota don takaici bai san sanda ya bugata da qasa ba ta bude komai ya tarwatse
a saman centerA sanyaye ya zauna gefan gadon hadi da zubawa farin bedsheet din nasu
ido yadda ya baci da jini haryanzu yana bisa gadon,bai son tayar da ita ne a jiya
shi yasa ya tureshi gefe ya kwantar da ita,idanunsa suka sake kaiwa kan tray na
breakfast da ya hada mata tun safen kafin ya fita,yana nan yadda ya shigo da shi
dai dai da cup ba'a juya shi yadda ya saka shi ba da alamun babu abinda taci kenan?
Ya daga zanin gadon yana qarewa jinin jiki kallo,shi kansa bedsheet din wata
qimarsa yake gani,daga qarshe ya duqunquneshi a qirjinsa da dukka hannayensa biyu
idanunsa na a lumshe,wata mahaukaciyar soyayyarta ke ratsa shi,baisan lokacin da ya
kwanta saman gadon ba,fuksarta ce kawai ke masa yawo cikin idanunsa,zanen fuskar
yake gani sanda suka kasace a lokaci mafi tsada dadaraja a rayuwarsa,lokacin da
bazaya taba barin tunaninsa saidai mutuwa ta cire masa shi,lokacin da bazai taba
daina ganin darajarsa ba saidi mutuwa ta hana shi,qamshinta ya dinga ji sosai kan
pillow din da ta kwata tamkar tana gurin,da sauri ya bude idonsa,vest din ta ce ta
jiyan daya yaga saitin hancinsa,da sauri yasa hannunsa ya dauko ta yana sake
mannata cikin hancin nasa,tamkar zai shide tamkar zai zuqo fadilan daga jikin vest
dinJuyi yake sosai cikin wai irin shauqin qauna da soyayya da bai taba zaton akwai
makamanciyarta ba a duniyarmu "why u leave me?why?,I cannot sustain missing you,I
can't,me yasa sai da kika mun kyautar abu mai tsada da daraja baki tsaya kin
karbikema abu mafi tsada da daraja aguna ba kika barni?,me yasa ba zaki tsaya na
saka miki dimbin kyautatawarki gareni ba?,why baki sanar da ni sirrin zuciyarki ba
sai lokacin da kika barni why?....." shi kadai qwal cikin gidan harma a dakin yake
ta wadannan sumbatuSam ya kasa hassalawa kansa komai,koda suit dinsaya gaza cirewa
bare akai ga yin wanka ballantana kuma batun abinci,koda yana da buqatarsa bazai
iya ci din ba don harshensa bai gamsuwa da girkin kowa idan ba natan baSai yanzu ya
soma tantance son da yame mata ashe yafi wanda yake ma girkin ta?,sai yanzu ya fara
ankara da dalilin da yasa yake hasala da yawa idan bata gyara masa part ko bata
masa girki ba fiye da yadda yake jin zafi yake hasala fiye da su samira?,sai yanzu
ya gane dalilin da yasa yake jin haushi idan ta kammala girki ta bar masa
bangarensa kafin ya dawo?,sai yanzu ya fuskanci dalilun da yasa yake qin cin abinci
har sai ya tilasta ta ta zauna by his side har sai ya kammala?,ashe sone
hakan?,wani irin salon sone wanda bai farga da wane lokaci da kuma yaushe ya shiga
zuciyarsa ba sai yanzu?,ba abun mamaki bane don bai taba kamuwa a akaran kansa da
*SO* din ba sai a kanta,tamkar ya taso ne ya saba da cusa masa shi ake ta qarfin
tuwoKamar ya jawo goben haka yake ji,daren gaba daya ji yayi yayi wani mugun tsawo
a gunsa kamar jansa aka dada yi,gani yake kamar gari bazai waye ba,kayanta dake
cikin cupboard gana daya ya watsosu ya barbazasu kan gadon ya kwanta akai yana
shaqarsu ko zai samu sa'idar zugi da zillo da zuciyarsa ke masa game da ita,saidai
inaa....kama da wane bata wane,tamkar wani zautacce haka ya koma idanunsa jazur
bashin baccin jiya da yau gabadaya kuma bacci bai ziyarceshi ba sai gab da
suba🔅🔅🔅🔅🔅🔅Kiran wayarsa su mr lun ke tayi amma gaa daya layukan switched off,suna
baqatarsa sosai don awanni uku kacal ya rage a soma gudanar da bikin,baqi masu zuwa
nata tambayarsa,hakan yasa andi da kansa ya taho gidan takanas ba shiriCikin bacci
yaji anataba qararrawa da alamun neman izinin shigowa ake,tsaki yaja ya maida
kansasaman filon hadi da maida fuskarsa hannun hagu maimakon dama a yadda take dazu
bashi da ko niyyar tashi,saidai mai danna qararrawar yaci gaba da matsata kamar
babu gobe har sai da mijin nadiya ya fito abdul basid,hakanne ya sashi miqewaa
fusace ya zare rigar saman ya cire tie din ya wurgar ya bar 'yar ciki ya fito cikin
haushin kaza huce kan damiSuna hada ido da andin yasan cewa babu lafiya fa,don
kalli daya zaka yima aliyyun kasan ya koma wani hargitsatstsen aliyyu,cikin tsawa
yace "what doyou want?!" Cikin girmamawa yace "sir d time is passing,u have to
prepare........." "leave me alone!" Aliyyun ya dakatar dashi ta hanyar daga masa
hannu cikin wata tsawar,ya ja qofarsa garam ya kulleta ya koma cikiSaman kujera ya
koma ya zauna yana nishi,sai a alokacin idanunsa suka sauka kan wayarsa da ya
tarwatsa jiya,yasa hannunsa ya tsince ya maida layukan ya sanya batirin ya
kunnata,servicena gama hawa massage suka yita shigowa sun kusa hamsin,ko guda baiyi
sha'awar budewa ba bare ya karanta,hasalima hankalinsa bai kanta nashi tunanin
daban,cikin haka kira ya shigo,bai ko kalli wayar ba bare akai ga batun dagawa,sai
da tayi ta katse har sau biyu,cikin jan tsaki ya sanya hannu ya janyo wayar da
niyyar kasheta,number din uncle abba ya gani,bau damar kashewa kenan,luguden bugu
kawai zuciyarsa ke masa,ya danna ok,ya gama bada amannar cewa fadila taje musu
ne,ba qaramin rudewa yayi ba saboda sanin halin abban nasa sarai bashi da sauqi kan
wasu lamuranYa kara a kunne jiki a sanyaye,tambayar da abban nasa ya masa ta sake
sashi cikin wani halin ha'ula'in"me kake yi haka ne aliyyu?,lafiyarka kuwa qalau?"
Cikin rawar murya yace "abba...wallahikuskure ne....kuskure aka samu kuma....."ya
dakatar da shi"ya isa bana son jin komai maza ka tashi ka shirya,mr lin ne ya
kirani ya gaya min komai har mutum ya aiko maka ka koreshi,damar da ka ka jima kana
jira yanzu don ka sameta shine kakeso kayi wasa da ita?,maza ka ahirya kafin
lokacin yayi kamar yadda aka tsara"wata boyayyar ajiyar zuciya ya saki ya maida
bayansa jikin kujera "to abba inshaAllahu" suka qare wayar yana masa addu'ar samun
nasara tare da sanya masa albarkaYa kashe wayar sannan ya zuba mata ido,yana ji a
jikinsa da zuciyarsa bai kyautawa abban nasa ba ma,bai san da qanne ido zai
kalleshi ba,cikin kasalartasa ya miqe ya shiga toilet ya hada ruqan wankanshi da
kanshi don cika umarnin abban nasa,awanni biyu ya dauka ya kammala shiryawa,komai
da yakeyi babu walwala a fuskarsa,dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka? Hakanan
babu kuzari ko qanqani tattare da shi,shigarsa ta suit yayi saidia wannan ta
musamman ce 'yar ubansu,wadda dama an tanadeta ne domin wannan rana,maqudan kudade
aka kashe gun siyan nata,kai da kanka idan ka kalleta ba sai angaya maka ta lashi
kudi ba zaka baiwa kanka amsa ash ce mai cakude da yarfin baqi rigar ciki kuma da
tie dinsa kuma light pink ne,agogo da ya daura da takalmi na qafarsa ma kawai abun
kallo ne,sumarsa tayi kyau sosai kamar yasa mata relaxer,sosai aliyyun yayi kyau
tamkar balarabe,yaya dama mai kyau yasa abu mai kya?,saidai cikin zuciyarsa sam
babu nutsuwa ko farinciki ko dayaSuna waje suna jiransa cikin dalleliyar
sabuwar baqar mota,sabuwar qira ce don a shekarar aka farahawanta,yana daya daga
cikin kutane na farko da suka mallaketa ko a qasar chinan,mutum uku ne suka miqe ya
watsa musu harara don yana ganin susuka takurashi zuwa gurin tamkar su suka yi
laifin,dayan ya bude masa inda zai zauna yayin da ragowar biyun suka bishi da
gaisuwa,baiko kallesu ba sun san ba lafiya son haka basu sake cewa komai ba suka
shiga mai tuqi ya tafa motarTafkeken dakin taro ne dake cikin ginin
kamfanin*maitama factory*,hall ne da yaci sunan hajiya*maimunatu ibrahim muhammad*
mahaifiya gareshikenan,cike yake da al'umma mahalarta taron,sosai aka qawata
gun,decoration aka masa mai azabar kyau da tsari,kowanne table kujeru hudu ne suka
zagayeshi,kusandukka mahalarta taron sunyi shiga ne ta baqaqen coat kamar masu
ashobi,maza ne damata jinsin yarw da qabila daban daban,kowanne zaune gurinsa a
nutse cikin tsari suna sauraran bayanai daga bakin mai gabatarwa duk cikin dakon
isowar aliyyu,babu wata hayaniya kai sai ka rantse babu mai numfashi cikin hall
dinShigowar tasa ya sanya duk wani dake dakin taron miqewa tsaye cikin
girmamawa,tafi ya cika hall din raf raf raf,tamkar ya zura da gudu ya bar hall din
haka yake ji don tafin nasu wani kuda yake masa akunne,sai da ya hau step din da ka
tanadar musu don zama gefan hannun hagunsa mr lin kusa da shi miss sisineo ce
hannun damansa kuma ramzan ne kusa da ramzan kuma mukhtar ne,sai da auka kmmla zama
sanna kowa ya koma.mazauninsaya zaunaDakin taron ya sake yin shiru,mai gabatarwa ya
yi wa aliyyi barka da isowa,sannu a hankali aka ci gaba da gabatar da taron yadda
aka tsara daki daki,duk anun nan da kae maganar minti biyu aka ritsa aliyyi da
bindiga aka ce ya maimaita saidai a harbeshin don baya gurin *gangar jikinsa* ce
kawai zaune,hankalinsa na kan fadila da agogo,duk bayanminti guda sai ya duba
lokaci,jawabai masu muhimmanci da ka tsara shi zai gabatar babu ko daya da ya iya
yi,sai ya bada uzirin baijin dadi sosai,drinks da kayan ciye ciye da ka cika gaban
kowa da shi babu qanda ya iya kalla balle ya tantance yana sha'awarsu ko baya yi
bare akai ga batun zai ci ko zai shaAwanni biyu aka dauka sannan aka zo gangara,su
mukhtar suka tilastashi kan dole ya karba yayi jawabin godiya ga dimbin al'ummar da
suka.tako gari ya gari suka zo masa,yana ture lasifiqar yana komai haka mukhtar ya
manna masa ,idanu da sukamasa ca yasa ya sa hannu cikin kasala da rashin sanin a
halin da yake ciki ya amsa"Fadeelah!" Abinda ya soma mabata kenan cikin bututun
maganar,tsit suka yi fiye da wanda sukai dazun tamkar wanda yayi calling attention
nasu,ido kowa kr binsa da shi don dai sun san suna.ya ambata "fadeelah ta soni
matuqa cikin rayuwarta.....na zauna da ita cikin boyayyen nuni gairin tawa kalar
soyayyar gareta",ya danyi jim sannn ya shaqi numfashi ya dora "fadeelah ta barni a
lokacin da ya bayyana gareni na dade nima ina sonta ba tare da nawa sanin ba....ta
barni a lokacin da nake da buqatar yi mata mafificiyar soyayyar da ba'a taba
gwadawa wata 'ya mace irinta ba......ta barni da wani nauyi mai azabar nauyi cikim
zuciyata ba tare da na samu na sauke mun raba tare ba......fadeelah ta zama ruhina
da gangar jikina"dora hannun sa yayi saman qirjinsa saitin zuciyarsa "fadeelah ta
mallaki nan ba tare da saninta ba,ya dade da zama mallakinta ba tare da sanin ku mu
duka biyun ba""Na tsinkayi fushi fusata da rashin fahimta masu tarin yawa qunahe
cikin kalamanta,qunshe cikin takardar da ta zamo baqa aguna,cikin saqon dake
bayyana bankwana da abinda zuciya ke so,cikin shafin takarda qwaya daya tal saidai
sun yimin nauyi fiye da littattafai dari masu shafuka dari dari"ya hade tafukan
hannayensa guri guda yana yinsa ya sauya soaai da alamun abinda yake fadi din na
taba zciyarsa sosai,da alama zancan daga ainihin zuciyarsa yake fita ba daga
harshensaa yakeba "ku yimin alfarmar sani a addu'o'inku....ku yimin alfarmar roqa
min Allah ya huci zuciyarta,na gode muku baki daya...."ya fadi yana qoqarin komawa
ya zauna,gaba daya suka.miqe suna tafi,yanayin salin ne ya burgesu,fuskarsu da
zuciyarsu cike da tausayinsa,abunka da mai jajayen kunnuwa akwai girmama soyayya
komai tsufanta,miss sisineo ce tabude 'yar jakarta ta fiddo da bangles na gwal guda
biyu danqara danqara ta ajjiye gaban aliyyu tace ga kyautar ta a isar da ita ga
fadilaSosai abun burgeshi ta yima fadilansa kyauta duk da yana da arziqin da zai
siya mata ninkin wanann amma ayi kyauta wa masoyinka ma abun faranta ranka ne,yasa
hannu ya dauke yayi masu kyakkyawar ajiya..........*mrs muhammad ce*✍🏻 ✍🏻 ✍🏻 ✍
✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻
✍?
👉🏼 *PART 3*👈🏼
3⃣&4⃣
3⃣4⃣
Bayan ciye ciye da akayi a gun suka soka fita gun ainihin ginin kamfanin wanda aka
zagaye shi da wani yadi mai kyau aka daure bakin qofar shigar da shi,aliyyun ne a
gaba a tsaye andi ya miqo masa qaramin almakashi ya amsa ya dora saman yadin ya
datse,tafi aka saki sannan suka dunguma gaba daya sukayi ciki,guri guri suka dinga
shiga daya bayan daya cikin kamfanin,sosai ginin ya tsaru yayi kyau matuqa da
gaske,komai cikin fasali gwanin sha'awa
Ba qaramin qaguwa yayi ba,duk bayan minti daya idanunsa na kan agogo,gani yake
kamar yanga lokacin yake masa,binsu kawai yake ba tare da fahimtar abinda suke yi
ba,sam hankalinsa bai tare da su,cikin dabara ya zame jikinsa ya koma office dinsa
wanda aka tanadar masa ko da zai zo wani lokacin,yasa key ya bude ya shiga sannan
ya koma ya kulle ya koma saman kujera ya zube,awoyi uku ya rage jirgin nasu ya
tashi,baya tsammanin zai iya zaman jira,ya zaro wayarsa cikin hanzari ya kira
jumong da mukhtar
Tare sukayi knocking ya tashi ya bude musu,kan kujera mukhtar ya qarasa ya zauna
yayin da jumong ya rusuna yana jiran jin umarni,"ka shirya mota zan fito yanzu zaka
kaini airport" "ok sir" ya fadi hadi da juyawa cikin hanzari ya fice,yayin da
mukhtar ke kallonsa yana son tambayarsa me zaya yi a airport?,bai bashi wannan
damar ba ya soma masa bayani da kansa ba tare da ya tambayeshi ba "nijeria zan wuce
mukhtar nan da awa uku,ina son na bar komai a hannunka kayi handling dinsa,bazan yi
sallama da kowa ba its urgent,ka wakilceni please"cikin rashin fahimta yake dubansa
"like how aliyyu baqin naka zaka bari ka wuce nijeria?" "Pls mukhtar if u cannot
help just tell me directly" yasan halin kayan sa sarai saboda haka ya gyada kai "is
ok,is ok I will" ya miqe tsaye ya sake duba passport nashi da ticket dake cikin
jakan sa,yaga komai na nan yadda zai buqace shi,ya dauka gami da zaro master card
platinum ya ajjiyewa mukhtar din sukayi hand shake "thanks" aliyyun ya fada a
gaggauce sannan ya bude qofar ya fice,mukhtar da mamaki ya cika shi yabi aliyyun da
kallo galala,gaba daya aliyyun ya fita daga hayyacinsa sam ya fice daga nutsuwarsa
Ta get din baya ya fice don baison kowa ya tsaidashi,don kuwa baiga abinda zai
tsaida shi daga tafiya nijeria ayau din nan ba saidai ikon Allah,ko cikin motar ma
gani yake jumong baya sauri laqaqai laqaqai kawai yake,gaza haquri yayi har sai da
ya soma masa maaifa kan ya qara gudu "sorry sir ida mukayi gudu ya wuce qa'ida
camera na kallon mu za'a iya kama mu" sai a lokacin ya tuna ba'a nijeria yake ba
dole ya haqura a haka har suka isa airport din,ko jirgin ma gani yake ba sauri yake
ba shirme yake(hhhhhh),da suka sauka ko a ethopia aka basu dakunan kwana kan sai
gobe zasu qarasa nijeria jinsa yayi kamar a saka shi a kurkuku,masifa kawai yake
yana fadin dole ya sayi private jet nashi,dole yana ji yana gani ya haqura har sai
washegarin
🔅🔅🔅🔅🔅
Qarfe goma na safe a garin kano tayi masa,tuni nasiru yazo da mota don
daukarshi,gidansu yace ya wuce da shi kundila maiduguri road,yana shirin fitowadaga
cikin motar saiga sumayya ta fito cikin shirin tafiya school,da sauri ta sauya
akalar tafiyar tata ta nufo gurin motar fuskarta qunshe da fara'a"sannu da zuwa ya
aliyyu" ta fadi tana leqa cikin motar cikin neman fadila,"yauwa" yace yana sanyo
qafarsa waje,ya dubeta cikin dakiyar nan tasa "ke,me kika bani ajiya kikemin leqe
leqe cikin mota" sai ta dawo ta tsaya dai dai cikin fara'a "anty fadila nake leqe
ko zan gani yaya,surprising din mu kuka so yi shi yasa ko a waya bata gaya mana
ba,kwananta biyu ma bata kira mu ba ashe kuna hanya"da sauri ta juya tana shirin
komawa ciki tace "bari na fara yi mawa momi albishir"sosai jikinsa ya mutu basu da
labarin ma ta dawo to me yake faruwa ne?"maida qafar tasa yayi cikin motar ya rufe
ya bawa nasiru umarnin ya kunnata su wuce sani mai nagge(unguwar su fadila)
Har cikin gidan malam ya bude musu suka shiga,ya fito ya ningina jikin motar
bakinshi fal addu'a,yana tunanin yadda zai shiga gidan ne,sai ga muhammad ya fito
daga inda suke ajiyar motocinsu hannunsa dauke da qaton almakashi irin na yankan
shuka,nasiru ne ya qwala masa kira,da sauri ya juya ganinsu yasa shi nufo gurin
yana fara'ar ganin aliyyun,"sannu da zuwa yaya"muhammad ya gaida shi ya amsa masa
"kai da anty ne yaushe kuka dawo amma bata gayama ummi zaku dawo ba"ya fadi yana
washe baki da son jin amsar inda yayarsa take,innalillahi wa inna ilaihi
raji'un"aliyu ke fada cikin wani irin hali,muhammad ya juya yana fadin "bari nakira
abba bai fita ba"aliyu na shirin hana shi saiga abban ya fito ummi na riqe da
jakarsa
Sosai abban ya nuna jin dadin ganin aliyun,yasa muhammad ya bude sitting room suka
shiga,maganar da abban ya qara fadi ita ta sake tabbatarwa da aliyyu fadilan bata
zo gidan ba"ina mai kukan tafiya yanzu dai ai kuka ya qare ko tunda gashinan anje
lafiya an dawo lpy"aliyun ya sunkuyar da kai wata fargaba na shigarsa "tana lafiya
abba" abinda ya iya fada kenan,to shima abban bai takura masa da wata doguwar hira
ba ya sallameshi shima ya fice kasuwa
Gidansa kawai yasa nasirun ya kai shi don bai san kuma me ya rage masa ba,tunaninsa
ya tsaya cak,a harabar gidan ma'aikata ne kowa na masa barka da dawowa,baijin ma me
suke fada hannu kawai yake daga musu,ya sallami nasiru ya fito daga cikin motar
yana shirin shigewa ciki aka sake dage gate din gidan,tsayawa yayi hadi da juyowa
don hajin wanda aka bude mawar,motar samirah ce wadda ta sake cin ubanta,su hudu ne
cikin motar,wata dabance ke driving din samirah na gefanta sai wasu su biyun a
baya,dariya suke ta sheqawa sam basu ma kula da wani aliyyu ba har suka yo
parking,har ta fito tana sheqa dariyarta kamar wadda aka yiwa albishir din ba zata
mutu ba,cak ta tsaya tana kallonsa kamar yadda shima ya zuba mata ido,suma qawayen
dariyarce ta tsaya cak,sun san halinsa sarai baya da kyau,sum sum daya bayan daya
suka fice daga gidan,kai kawai ya gayada ba tare da yace mata komai ko ya sake
kallonta ba ya shiga bangaransa
Yafi mintin talatin a zaune kafin ya miqe yaje yayi wanka,kafin ya kammala shiryawa
anyi kiran sallar azahar,duk wani motsi da zaiyi tana manne cikin ransa,duk wani
tunaninsa na ina zai sameta?ina zai ganta?ina kuma yanzu zaije nemanta?,cikin yadin
tissue fari tas ya shirya,yayi kyau sosai duk da kana kallonsa zaka karanci bai
cikin walwala duk da kusan hakan yanayin fuskarsa yake amma wannan karon ya ninka
yadda yake da,ficewa yayi kansa tsaye ba tare da ya nemi kowa ba da kansa ya ja
motar ya bar gidan
Sai da ya fara tsayawa a masallacin bakin layinsu ya bada faralin sallar azahar
dinsa sannan ya wuce,kai tsaye yahaya gusau ya wuce gidan farida,ya dan jima a
tsaye a qofar gidan baiga gilmawar kowa ba har yana shirin komawa sai ga dahiru
almajirin faridan,da sauri dahirun ya qara so inda aliyyun ke tsaye don ya
ganeshi,cikin girmamawa ya gaida aliyyun,ya amsa masa yana tambayarsa matar gidan
na ciki?,ya amsa masa da "eh alhaji ko a kira maka ita za'ayi?" "A'ah tambayarka
dai nake so nayi"aliyu ya fda yana gyara tsaiwarsa "to..Allah yasa na sani" "tayi
wata baquwa tsakanin jiya da shekaran jiya da yau?" "Kai gaskiya a'ah,don suma jiya
suka dawo daga lagos ita da mai gidan"ya fada masa cikin bashi tabbaci
Idanunsa ya rufe yana jin wani abu sannan ya bude,ya saki qaramar ajiyr zuciya
sannan ya ciro kudi ya bama dahirun ,cikin murna ya amshe yana zuba godiya,bai bi
ta kan godiyarsa ba ya shige motar ya tasheta ya bar layin
Har la'asar aliyyu salim na bulayi bisa titunan kano,shiga wancan fita wancan,ko
manshi da yake qonawa bai damu ba,ya rasa inda zai zauna bare yayi tunanin
mafita,gaba daya feeling kansa yake a matsayin guilty,cikin rudanin inda ta tafi
yake,ina ta boye kanta haka?,duk da yana ji daga can cikin wani sashe na zuciyarsa
na gaya masa she is safe and she is in safety place
Sai da ya soma ganin gurare daban daban na ta alwalar sallar la'asar sannan ya samu
ya kashe motar a bakin wani masallaci ,ya daura alwalar ya bi jam'i,sai bayan da ua
idar ne yaji cikinsa na qugi sannan ya tuna rabonsa da abinci har ya mance,ya miqe
ya koma cikin motar tasa ba tare da yabi ta kan yunwar dake sakadarshi ba,sai da
akayi sallar magariba yana bilayin yawon titina sannan ya gano cewa wannan fa ba
mafita bace,tunanin matsalar itace zata samar masa mafita da gano masa inda fadilan
ta boye,ya juya akalar motarsa ya nufi gidansu dake kundila. .......
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻

  
[10/16, 2:09 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

👉🏼 *PART 3* 👈🏼
5⃣&6⃣
5⃣6⃣
Yana shiga ya tadda rabi'ah kan dining area ita da iftihal momy na kitchen,da alamu
su din ma zaman na cin abinci ne,da gudu iftihal ta gangaro tana ihu "yeyyyyyy
daddyyyy"kamar yadda ta saba ta duqa ta gaidashi,ya amsa mata maimakon ya dauketa
ya shilla sama yadda suka saba wannan karon sai taga kawai ya shafa saman kanta
yayi hanyar kitchen din,ta tabe baki kamar zata saki kuka
Tana kiciniyar rufe warmer taji an rufe freezer,ta dago kai da sauri aliyyun na
tsaye yana daddakar ruwan mai azabar sanyi,sai da ya shanye robar guda momin na
kallonsa ta zuba mai ido,ganinsa take a wani birkice duk da jikinsa fes yake kuma
ya yi kyau da 'yar cika(sakamakon kulawar da ya dinga samu a china)amma abunka da
mahaifiya kallo daya tayi masa t gano akwai damuwa a ransa
Yana qare shanyewar suka hada ido da momin,sai ya kautar da kai ya sanya robar
cikin dust bin yana cewa "momi barka da dare ina wuni"bata dai daina kallon nasa ba
tace "lafiya lau Ali kun dawo lafiya?" "Lafiya qalau ha fada yana jan kujerar
plastic dake kitchen din zai zauna "mun sameku lafiya?" Ya sake tambayar momin yana
dauke kai don baya son irin kallon nan na momi,nan da nan take naqaltar mutum,itama
sai ta dauke kan tana ci gaba da rufe warmer din tace"lafiya lau,tun safe sumayya
tace min gaka,shiru shiru baka shigo ba ko da aka leqo kuma ba kai a gun"ta qarashe
maganar idanunta a kansa kamar tana son jin amsa kenan
"Zani gida ne momi za muyi magana da mukhtar,na baroshi ne da mutane a can wadanda
ban sallamesu ba na taho" to da yake ma qaryar bata karbeshi ba sai ya jada harda
subul da baka ba tare da ya ankara ba "ya zaka dawo bayan baka sallami baqi ba
ali?,wai meke damunka ne haka?,a kunnena fa abbanka ya tursasaka zuwa bikin bude
kamfani,yanzu kuma ka taho ka bar jama'a acan,baqonka annabinka fa ali"yayi saurin
dosar qofar fita yana cewa"momi ai ba matsala mukhtar zaiyi komai kamar ina nan,sai
da safe momi idan abban ya sauko ki gaida shi ina hanya goben"baki sake ta bishi da
kallo tana ayyanawa tabbas akwai abinda ke damun yaron nan,gashi da shegen zurfin
ciki kamar mace,idan kaji cikinsa to ya ciyoshi ne,ta dan daga murya tana cewa"ka
gaida mutan gidan" "zasu ji momi" ya fadi yana barin falon cikin sauri don kada
suci karo da iftihal ta tsaida shi
Har ya koma ya bude sashensa ya shiga yayi wanka ba wadda ya gani,shi yama fi son
haka din ma,yasa koda sunzo babu abinda.zai samu sai qarin tension,shi kuma yanzu
abinda ke damunsa yasha kansa fiye da komai,sai da dibi kusan awa daya da wani abu
sai ga salima,fuskarsa ta zubawa ido tana murmushi saboda sosai aliyyu ya canza,ya
qara ja sumarsa ta sake baqi sidik,gargasar jikinsa kamar an dada mata baqi laushi
da yawa,ya sake kyau,badon fadila da ta hargitsa masa lissafinsa ba da abun yafi
haka,hakanan shima ya sakar muta fuska don ya zama dole haqqinsu ne don bazaya yiwu
haqqin wani ya danne na wani ba,kuma matsalarsa yasan ba tasu bace indai ta wannan
bangaren ne
Da sauri ta qaraso ta zube ajikinsa tana fadin "oyoyo welcome my dear"yadan karata
ajikinsa yace "thank you ya muka sameku?" "We are fine but I miss you" yadan saki
fara'a "ok,to ai yanzu gani mai zan samu?" Ta tabe baki sannan tace "ba komai tunda
ai ba yau kace zaka dawo ba ganinka kawai mukayi tsakar rana,ni ta window ma na
hageka ka fice" "ni din ma haka dawowar ta zo min" cikin son bin qwaqwafi tace "ko
fadilan ce ta takura sai andawo?" "Eh"kawai yace mata cikin som kashe maganar don
tamkar allura ce akan qurji idan aka tada masa da zancan fadila, "but ban gata ba
kuma ma bangaren ta akle yake" "eh"ya kuma cewa dai bai buqatar taci gaba da yin
maganar
Shiru ya dan ratsa dakin kanta na jingine a kafadarsa,kishin fadilan duk ya cikata
gani take kamar wani gun ya kuma kaita don ta huta,samira ta danno kai harda
sallamarta kamar gaske kai a sunkuye,duk da haka saboda tsabar neman bala'i sai da
ta gasawa salima hara ra,ai kuwa itama bata yi qasa agwiwa ba ta rama don ba
qaramin adashen tsiya suka dinga shukawa ba sanda baya nan,kullum sai an raba gari
a gidan saidai idan garin Allah bai waye ba,amma kwana suke su wuni suna abu guda
kamar karnuka,suna hada ido da aliyyu ya bata tasa hararar tayi saurin sadda kai
qasa,gefansa ta zauna cikin tausasa murya tace masa "sannu da zuwa an dawo lafiya?"
"Lafiya"yace mata a taqaice,duk sai taji ta muzanta,tafi kowa sanin
laifinta,gargadi mai zafi babu irin wanda bai musu ba kafin ya tafi kan fice
fice,duk da yau ma tsautsayine amma ta kwan biyu bata saci fita din ba,wannan ne
satar fitarta ta hudu salima tayi biyu tana tsammanin tayi na qarshe tunda ya kusa
dawowa qasar bata san yau ya dawo ba
Shiru ya gauraye falon kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,aliyyu yafi kowa
nisan kiwo cikin duniyar tunani,"dear ya kamata muje ku kwanta ko?"salima ta fada
tana kashe masa idanu,da sauri samira ta dago "kamar yaya?"cikin daga murya samira
ta tambayeta,itama ta dubeta ta mayar mata "kamar yadda kika kunnuwanki suka ji
nace"da sauri ta nunata da yatsa "baki isa ba wallahi kinyi kadan don yadda kike
buqatarsa nima hakan take.....ke bari ma nayi miki dalla dalla...yadda kike a matse
ni nama fiki matsuwa"ta fada tana wani gayara zama,sai kuwa cece kuce ya barke dama
kadan kowacce take jira 'yar uwarta ta tabo ta,sak yayi yana kallonsu,sai ya zama
kamar wani mutum mutumi,babu wadda tayi masa wani abu na azo a gani a matsayinsa na
matafiyin da yayi wata judu bai cikin iyalinsa yanzu ya dawo musu,shegiya shinkafa
fara sol da yaji babu wadda ta turo masa tace gashi,amma aqalla ai ko tsakar dare
ya dawo idan da tunani sa tashi su sama masa wani abu ko drink ne,to amma ga drink
din ma jibge a freezer dinsa su dauko ma su hada masa da cup suce masa gashi babu
wadda ta iya yin hakan,babu wani welcoming na arziqi,amma ko wacce burinta ya
kwanta da ita ya biya mata buqata kamar wani inji
Ganin abun nasu ma shirin wuce makadi da rawa don har an fara 'yar lakace lakacen
hanci yasa ya dakatar da su ta hanyar daka musu tsawa don idan ba tsawar ya musu ba
yadda suka kacame babu wadda zata iya jiyo shi"bana buqatar kowa cikinku,duk ku
tashi ku bani waje,tunda ku baku iya kwantarwa da mutum hankali ba saidai ku tayar
masa,ko kwana daya banyi ba cikin gidana amma kun fara samin bacin rai?" Tuni
samira ta miqe,salima ta rausayar da kai tana cewa "amma aliyu ......." "amma me?
Please stay away" ya fada yana nuna mata hanya,samira ta sheqe da dariya tana cewa
"ato saiki taso ai mu daye,ki daina naci haka kowa sai ya riqe kwadayinsa tunda
yace bai yi" wani banzan kallo alin ya watsawa samiran yana cewa "kin sanni,kada ki
bari muyi arangama dake bani da kyau!"tasan hakan kuwa tuni tayi gaba salima ta
bita a baya,yan jiyo kici kicin kokawarsu a bakim part din nasa,yayi banza da su
_*12 PM*_
Sha biyu na dare ya dinga gwada maqullan hannunsa a qofar har ya samu na qofar
tata,ya tura ya shiga ya haska makunnin fitila ya danna dukka qwayayen suka kama
bangaren ya cika da haske,qamshi falon yake tamkar tana nan,kamar bata yi tafiya ba
na tsawon watanni hudu ba,hakanan komai akillacensa,kai tsaye ya shige bedroom
dinta,shima dai kamar falon cikin qamshi yake da tsafta,gadonta a dame yake komai
ajere,pant da brassier dinta ne kawai a gefan pillow,ya qarasa ahankali ya haye
gadon hadi da kwanciya pillow din ya janyo hadi da rungumeahi tsam tsam a
qirjinsa,qamshi pillow din yake kamar a shafa masa turare ne,ya sake miqa hannu ya
dago pant and brassier din farare qal ya zuba musu ido,a hankali ya mannaau a
hancinsa yana sheqar qamahin turarenta na shamsul imaraat
Juyi kawai yake samar gadon,jinsa yake tamkar wani maraya,wani irin kewa yakeji mai
zafi da radadi tana kamashi,ya riga da ya saba da kwana jikinsu na gogayya da na
juna,ya saba da sheqar qamshinta,sosai ya sake rungume pillow yana sakin numfaahi
sama sama,yafi awa biyu kafin wani wahalallen bacci awon gaba da shi ,ko cikin
baccin ma bata qyaleshi ya huta ba sai da ta jawo masa yin wanka,ya dawo bakin
gadon yq zauna yana tsane jikinsa da towel dinta,idanunsa ya sauka kan wani dan
kyakkyawan madaidaicin frame da yake zaune dirshan bisa side bed,yasa hannu a
hankali ya dauki hoton ya zuba masa ido yana kallonta,murmushi take yi
sosai,fararen haqoranta jerarru reras sun bayyan,yar lobawar dake tsakiyar habarta
ta fito sosai,ya sanya bakinshi saitin lips nata yayi kissing,murya qasa qasa yace
"I love you"ya dan manna hoton a qirjinshi
Sai da yayi sallar asuba sannanya baro bangaren har ya fito ya manta bai dauko
hoton ba ya koma ya dauko abinsa,kan side drower dinshi ya kafa sa,yana shiryawa
yana kallon hoton har ya kammala shirinsa tsaf cikin shadda fara tas mai asalin
tsadar sai maiqo take da daukan idanu,yayi masifar kyau saidai fuskarnan na
kirtibe,qarfe bakwai ga fito ya soma da sashen samira don itace a damansa,yana tura
qofar ta bude alamuna bude ta kwana,kai tsaye ya zarce bedroom din ta don yasan
tana ciki,yana tafiya yana bin falon da kallo tamkar dakin ajiyar shirgi haka ta
maidashi
Dai dai ya sameta saman gado hannu can qafa can,gajeran gashinta maras tsawo wanda
bai hadu da mace mai gyara ba duk ya hautsine ya tashi yayi cako cako kamar
bishiyar qaya(don ko baki da tsawon gashi matuqar ke mai gyara ce to zai bada
sha'awa,amma komai tsawonsa indai ba gyara abin qyamata zai zama),sosai iyyu ya
tsani irin wannan kwanciyar tata,don kuwa insha Allahu kuka hada gado daya da
samira to ranar fa ka shieya zaka daku da hannu da qafa,haka kullum yake fama da
ita,shi yasa ya gwammace ya matseta a jikinsa ayi baccin haka
Ya dan taba qafarta yana kiran sunanta,saidai kamar gawa ko motsi bata yi ba bare
yasa ran zata tashi jan minsharinta kawai take,yasan hali dama bata motsa din ba
kuwa har sai da ya dage ya daki daki qafar da hannu sannan ta miqe a zabure tana
cono baki gami da mutsitstsika ido,sai da ta gama mutstsike idanun sannan ta
dubeshi,ganin aliyyu a tsaye ya sata shiga taitayinta,addu'a take cikin ranta Allah
yasa maganar laifinta yazo yayi mata,don tasan halinshi shirunsa ba abu mai dadi
yake haifarwa ba,fuska a murtuke yace "hala ko sallar asuba bakiyi ba?" Nan ta hau
kame kame "zan....zanyi....yanzu ne na tashi ai..." "good" yace da ita cikin
takaici yana gayada kai,ya juya zai fita "zan fita sai na dawo" "to" tace kaar
wadda aka tilasta ta sai ta fadi hakan,Allah Allah take ya fitan taja bargo ta koma
barcinta,bata sani ba shi din ma Allah Allah yake ya bar dakin,don zarnin
bandakinta dake cikin bedroom din shi ke busowa har cikin dakin gadon,sai taga kuma
ya juyo hadi da cewa "bani key din motarki da wayarki" cikin marairaita tace "don
Allah kayi haquri bazan sake ba" a zafafe ya kalleta "will you keep quiet or not?
Da baki iya bada haqurin ba kenan sai yanzu?common bani key da phone nace"nuni tayi
masa kan hargitsatstsen dressing mirror dinta,ya juya ya kalli kan madubin saboda
hargitsewarsa ma shi bai hango wata waya ba ballantana maqulli "ok...ni zanje ma na
dauko miki ko?" Dolenta ta sauka daga kan gadon ta dauko ta miqa masa tamakar zata
yi ihu,ya amsa ya fice da sauri ba tare da yace mata qala ba don zarnin sake busowa
yake,kuma ko yace ta gyara ba zata yi din ba don sau nawa yana fama da ita kan
hakan sai tave masa yau fa sati daya kacal da wanke shi ba wani dadewa yayi ba
Salima ma na bisa gadon a nade bacci na dibarta sama sama,ita din ma sai lokacin
bakwai da wani abu ta yi tata sallar,saidai yana sallamar ta amsa gami da miqewa
zaune kan gadon,murmushi take masa wanda hakan ya sanyashi rage daurin fuskarsa"kar
daiace har ka fito" ta soma cewa,ya kalleta yace "eh"yana mamakin yadda basu iya
gaisuwa wa mijinsu ba,babu wadda ta fado masa sai fadilan,duk safiya sai ya
gaidashi kamar yadda ya zame mata qajibi sannu da zuwa da adawo lafiya duk da sai
yaso yake amsawa amma hakan bai dameta ba haqqinta take saukewa, "amma yaci ace yau
a gida zaka wuni ko" ta sake shigowa da wani qorafin "a hakan kuna batan ran babu
wani caring bare a faranta maka"yayi zancqn cikin zuciyarsa,a fili sai yace
"maiduguri zani zuwa anjima zan dawo insha Allah"cikin tuhuma tace "maiduguri?gurin
wa?...." "stop your suspicion,sai na dawo" ya katseta, "madalla"tave tana binsa da
cike da kishi har ya fice
Cikin motarsa qirar 4matics fara ya zabi yin tafiyar shi kadai,bayan yin addu'o'in
matafiyi ya kunna motar ya fice daga gidan cikin tsammani mai yawa da fata na gari
akan kanshi
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:10 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

👉🏼 *PART 3* 👈🏼
7⃣&8⃣
7⃣8⃣
Cikin kwankin kullum cikin kuka take kwana take wuni,a haka ma an samu sauqi saboda
takan kaucewa idon anty hauwa don kada ta dinga jin ba dadi,damuwa sosai ta yiwa
zuciyarta yawa,tana jimantawa kanta yadda soyayyar aliyu ta gama illata ta,saidai
bata barin damuwar ta tsawaita mata da yawa ba ta tsananta yin addu'o'i,da taimakon
hakan ta soma samun kyakkyawar nutsuwa cikin ranta,koda yaushe cikin kula da ita
anty hauwa take bata barinta ta zauna ita daya bare ta damu sosai,sau da yawa anty
hauwan idan tana bata haquri kunya fadilan keji "nifa babu wanda yayimin laifi don
Allah anty ki daina bani haquri,kunya hakan yake bani wallahi"
Yara kam murna suke anty fadila ta dawo gidansu sunata tsalle,idan akace babu
makaranta to suna liqe da ita wani lokacin har sai anty hauwan ta kore mata su tace
su barta ta huta,ita kam dadi take ji idan tana tare da yaran saboda dama can mai
son yarance ita,sosai mamansu taja kunnensu da kada su sake su gayawa kowa cewa
anty fadilan tana nan gidan saboda yadda taga suna rawar qafa zasu iya subul da
baka
Ita kanta tayi mamaki qwarai yadda ta soma ragewa kanta damuwa kan aliyun duk da
yake ba abun mamaki bane addu'a ai tafi qarfin wasa,sosai tayi yaqi da
zuciyarta,bata bari bacin rai ya rusata ba,da zarar ta soma tunane tunane zata
datseshi ta hanyar daukan qur'ani ta karanta,idan ta gama kuma ta shiga shafukanta
na sada zumunta,komai anty hauwa ta hanata yi,duk da hakan fadilan taqi yarda don
kullum tare suke shiga kitchen yin lunch ko dinner,wani lokaci kuma ta shirya mata
yaran da safe
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Gudu sosai ya dinga yi shi daya cikin motar,cikin ikon Allah ya sauka lafiya,saidai
tun daga yadda su ya gana ke faman tambayar fadilan ya sare da al'amarin ya
tabbatar bata garin ma baki daya bare gidan,sallah kawai yayi ya baro garin,bai
damu da yawan tafiyar da yasha ba bare ya nemi hutawa har yaci abinci,juyin duniya
ya gana tayi ya tsaya yaci abinci amma qeme me yaqi,ya bata haquri bayan ya ajjiye
musu kudade masu dama yace yana da abubuwan yi masu yawa a kano,haka ya kamo hanya
ya taho,gudu na ban mamaki ya dinga shararawa ba qaqqautawa,sai da yaji tuqin na
neman gagararsa sannan ya samu wani shago kam hanya ya siyi yoghurt yasha,bai fasa
gudun nasa ba wanda ikon Allah ne kawai ya kawoshi garin kano lafiya
🔅🔅🔅🔅🔅🔅
Kwana hudu bai cikin daidanshi,matansa mata ne marasa kulawa,tabbas sunga canji
sosai tattare da shi amma babu wadda ta damu da tambayarsa mene damuwarshi,momi kam
ganin baice komai ba yasa ta tsuke bakinta ta qyaleshi don ta sani ida dai ya soma
zurfin cikin nan nasa bai gayawa kowa komai sai lokacin da yaga dama
*G*idan anty hauwa shine gida na qarshe da hankalinsa ya kai kai,anan ya tattara
dukkanin fata da tsammaninsa,duk da wata zuciyar na tantamar mai zaya kaita can
bayan ko gidansu bata je ba?,qarfe biyar da shirin na yamma ya gama shirinsa cikin
qananun kaya da sukayi matuqar yi masa kyau
Suna kitchen ita da fadilan suna hada abincin dare sunayi suna hirarsu,yara suka
jiyo wadanda suka bari a falo suna kallo da yake alhamis ce suna cewa "ina wuni
uncle....ina wuni uncle" gaban fadila yayi mummunar faduwa ta saki mirfin hannunta
da take shirin rufe miya da shi,"shikenan yau zan amshi takardar rabuwa da shi"
abunda zuciyarta ke gaya mata kenan "anty aliyu ne"ta fada tana kallon anty hauwa
dake tace shinkafa "aliyu?" Ta fada tana kallon fadilan cikin kasa kunne,"ina zuwa"
anty hauwa fada bayan ta ajjiye tukunyar hannunta ta fice da sauri,komawa fadila
tayi jikin drawer ta jingina bayan ta hatde hannayenta a qirjinta tana jiyo sweet
voice din sa,batasan me yasa take jin qunci a qirjinta dalilin gaya mata da
zuciyarta ke yi takardar sakinta aliyun ya biyota da ita
Ruwa aliyun yace ma anty hauwa ta bashi,duk ruwan dake freezer din falonsu ya qare
sai lemo,da hanzari anty hauwa ta miqe ta hau sama ta dauko masa a parlour din
abban kausar don bata son ya shiga kitchen din,ji yayi bazai iya jiranta ba don
haka ya miqe ya shige kitchen din,a hankali fadila ta bude idanunta da a da ke a
lumshe,cikin jikinta take jin tahowar tasa,nan da nan tayi wuri wuri da ido tana
neman maboya,a asukwane ta shige bayan qofar wadda a kusa da ita freezer din take
Kai tsaye ya qaraso ya dage freezer din ya sunkuya yasa hannunsa ciki,cak ya tsaya
da qoqarin ciro ruwan da yake yi,sai yake jin qamshinta cikin hancinsa,irin qamshin
da ya ji cikin bargo pillow da undies dinta,sakun murfin yayi ya soma kallen kallen
kitchen din yana neman ta inda qamshin ke fitowa,ko ina ya kai idanunsa sai yaga
babu kowa,tuni fadila tayi surrender bayan qofa numfashinta kamar zai dauke
musamman da taji ua jingina a bayan qofar ya kuma qin barin gurin,yafi minti uku
cikim kitchen din yaqi fita din qamshin turarenta na ahlamul arab kawai yake ji,hat
sai da anty hauwa ta shigo hankalinta a tashe tana tsammanin ya ga fadilan,sai ta
tadda shi a tsaye kawai jingine jikin qofar hannayensa harde a qirjinsa,"ina ka
shiga ga euwan can na kaimaka" "ok" kawai yace ya gewayeta ta fice daga kitchen din
itama ta rufa masa baya
Ta maida yara dakinsu daga ita sai shi a falon,zuba masa ido tayi sosai tana
kallonsa canji qara ta hango tattare da alin,fara'arsa ta sake qaranci
sosai,tsiyayar lemon kawai yake yi yana dirkawa cikinsa,yadda bai tanka ba itama
bata ce kamzil ba har sai da ya tashi da roba biyu ta ruwa da lemo,ya dago kai ya
kalli antin hadi da sakin ajiyar zuciya "ni wai uncle meke damunka?tunda kazo naga
kamar a hargitse kake?"wata ajiyar zuciyar ya kuma saki "fadeelah nake nema mummyn
kausar" kamar gaske ta nuna alamun rashin fahimta sosai "kamar yaya?fadilan da kuke
tare,yaushe dududu sumayya ta ke gayamin kun dawo daga china zaka ce ita kake nema
kamar wadda ta bata" "bata tayi....bacemin tayi"ya fadi yana jingina jikinsa da
kujera,yayin da fadila dake labe cikin kitchen ta zaro ido jin cewa wai nemanta
yake "yayimin me? Me zayayimin ne?"ta tambayi kanta ba tare da tasan amsar tambayar
ba
Ya dora cikin wata iriyar murya "tayi tsammanin bana sonta ne bayan nima na dade
ina sonta,tayi zatin maqiyinta ne ni alhali duk duniya babu mai sonta kamar ni...ta
dauka ina zaune da ita ne bisa dole bayan kan son raina nake zaune da ita.....anty
ta yimin gurguwar fahimta,ta gujeni a lokacin da na qara zurfi cikin qaunarta....ta
gujeni a lokacin da dukkanmu ni da ita muka fi buqatar kasancewa da juna"ita kanta
anty hauwa baki ta saki tana tsammanin ba aliyu bane,aliyyun da tunda take tare da
shi zata iya cewa bata taba ji ko ganin yana kwatanta qaunar da yakewa wata diya
mace ba aduniya koda uwar 'yarsa,fadila kam dake cikin kitchen duburburcewa
tayi,sai jikinta ya fara rawa qafafunta suka gaza daukarta ta lallaba ta ja jikinta
ta zauna kan kujerar roba bakinta rufe da tafin hannunta yayin da hawayen da sukayi
kwana da kwanaki tana qumshe su yau suka samu qofa.
Lallai ma yaudararta aliyu keson yi?,dama shi din shahararren mayaudari ne,shine a
yanzu zai furta cewa yana sonta?wanne irin zama ne basu yi ba baice yana son nata
ba sai ayanzu?sai yanzu da ya kwanta da ita?,ya tabbata kenan jikin nata yake so
kamar yadda tayi zato tun farko? (Illar zato),sha'awarta yake kenan ba qauna yake
mata ta cikin zuciya ba?,kuka ne sosai mara sauti ya kufce mata yayin da shi din ma
ke can zaune dirshan gaban anty hauwa yana fayyace mata irin zaman da sukayi da
fadilan,kunne sosai ta saka tana jinsa duk da yake tamkar tishi yake mata,duk yadda
fadilan ta fada hakanne harda wasu abubuwan da fadilan ta boye ta qi fada
Kafin ya kammala tuni har qwalla ta cika idanunsa duk da bata gai ga zubowa ba amma
qiris take jira,soyayyar 'yan uwan taka sai Allah tuni tausayinsa ya kamata don
zata iya dafa qur'ani kan aliyyu bai taba shiga makamancin wannan halin ba akan
wata mace,ta karanto gaskiyarsa qarara,don dama ko ada bai iya qarya ba tun yana
qaraminsa,zai gaya ma gaskiya ne ko za'a tsireshi don haushi,to saidai bata jin
kuma zata shiga haqqin fadilan ta karya alqwari da ta daukar mata don aliyyu nata
ne,bata jin zata sarayar mata da haqqinta tunda nata din ne,ita ke da iko da
abunta,ita kadai tasha haqurinta ita kadai tasan me ta hadiya
Cikin sanyin jiki da qunar rai yace"wai anty roqona take na saketa,tana tsammanin
sakin nata abu ne mai sauqi har irin haka a gurina?" Ya kada kai yana cewa"bazan
iya ba,bazan iya furta wadan nan kalmomi gareta ba koda duka duniya zata taru a
kaina" dole ka sake ni aliyyu dole mu rabu ,bani kake so ba jikina kake sha'awa" ta
fadi haka qasa qasa cikin kuka mara sauti,ya miqe "zan tafi tafi tunda kema bata
gunki zan ci gaba da nemanta",tuni ya juya ya fice daga gidan,tausayin dan uwan
nata ya kamata don tasan wahla kawai qanin nata zaici gaba da sha tunda fadila na
tare da ita
Kifa kanta tayi kan cinyarta ta sake sakin wani sabon kukan mai dan qaramin
sauti,wani qunci zugi da radadi data rasa na meye take ji cikin ranta,anty hauwa ta
kama hannayen fadila tana kallin qwayar idonta "fadila.....fadila,naga abubuwa da
dama cikin qwayar idanun aliyu,naga soyayya naga qauna cikin cikin idonsa irin
wadda ban taba gani ya yiwa wata 'ya mace ba,kinji komai da kunnuwanki no need na
maimaita miki"
Kada kai fadilam keyi,"anty na yarda aliyu na sona a yanzu bazan qaryata ki ba,anty
amma ba ni fadilan yake so ba wani abu dake gareni yake so,tun yaushe anty....tun
yaushe nake tare da shi nake kyautata masa bai taba cewa yana sona ba sai yanzu?sai
yanzu da wani dalili ne ya jawo hakan?...Thank god aliyu na sona yanzu
anty,saidai ......is too late anty I already displaced him from my heart,na goge
cikin kundin rayuwata zan rayu da shi" kalmar ta fito daga bakinta hade da hawaye
Sai dariya taso kama anty hauwa amma ta gimtse,with confidence fadila ke fadin
maganar saidai qwayar idanunta kadai ta ta qaryata ta,bata sani ba ita kanta qaunar
aliyyu tayi mata illar wadda take huduwa tun daga zuciyarta har zuwa idanunta da
bakinta,bata da abunyi anty hauwa ta sani wani daci ne da fadilan ta dade tana
guntsa taje fesarwa idan ta hanata kuma bata yi mata adalci ba,tasan cewa kokwanto
ne yasa fadila fadin wadannan maganganun amma ba har cikin zuciyarta bane,ta kuma
gama gasgatawa wani irin salon rikicin soyayya ne ya kunno kai kawai tsakaninta da
aliyyun,sanoda haka sai kawai tave mata "shikenan fadila kici gaba da addu'o'inki
ki yi ta istihara,Allah ya zaba abinda yafi alkhairi"
Har anty hauwan ta kai bakin qofa fadila ta dakatar da ita ta hanyar cewa"am sorry
anty idan maganganuna sun bata miki rai" murmushi ta saki "don't mind,banji komai
ba araina fadila" murmuahi itama tayi mata tace "na gode" haka Allah yayi fadila
bata aon bacin rai ko yashin hakai ko kadan kamar yadda bata son taa ta batawa wani
rai ko ta shiga haqqinsa
Kwana biyu yama cikin wannan hali,duk wasu harkokinsa na gida dana waje yaqi maida
hankali kan kowanne,daga qarshe dai kasa jurewa yayi gani yake kamar su suka boye
masa fadila,yana ganin da wani yashin hankalin gwara wani,da ya rasata gwara a
yanke masa duk wani hukunci da za'a yanke masa idan yaso su bashi ita,ya gaza jure
kewarta komai nasa ya yi missing dinta,
🔅🔅🔅🔅🔅
Tsakiyat uncle abba da momi ya zauna ya warware masu abinda ke faruwa kamar yadda
halayyarsa take fadin gaskiya,momin ce ta saki salati mai nauyi yayin da uncle abba
yayi shiru gami da yin tsai da ransa,sai a lokacin ne kuma hankalinsa ya soma tashi
momi tayi shiru ne tana jiran jin umarni ko me mijin natazaya fada?,yayin da uncle
abba ya rasa me ma zaya ce din?,sama da minti biyar kafin ya dago yace "tashi kaje
aliyyu" cikin firgici ya dago kai yana kallon uncle abban,ya sake maimaita masa"ka
tashi kaje nace mu zamu nemota" alhaji yaje fa kace?" Momi ta fada cikin fushi,a
nutse uncle abba ya kalleta "to maimunatu mai zai zauna yayi min?,yaje kawai tunda
ya gama nasa aikin ko,mu kuma ba sai muyi namu ba?"
Tasan sarai halin mijin nata saboda haka ta gamsu da abinda yace "gaskiyane"shi kam
aliyyu yadda bai tanka ba sabida rudani haka ya kasa tashi kansa na sunkuye jinsa
yake kamar wani mutum mutumi,har sai da uncle abban ya gaji da ce masa ya tashi shi
da momin suka taahi suka bar masa falon
Da azahar momi ta dauki wayarta ta kira anty hauwa kamar yadda uncle abba ya ce ta
ce mata yana son ganinta ko zuwa najima ne,sai kuwa aka taki sa'a suna cikin
gaisawa kausar ta soma qwala kiran "anty fadilah!anty fadila!!na kasa daukowa"nama
ne tace ta ciro mata cikin fridge sunce suna son dambun nama to naman ya riga yayi
qanqara,tuni momin ta tsaya da amsa gaisuwar "maijidda wace fadilance a gidanki?"
Cikin son boye boye tace "am ....fadila ce ta zo mu gaisa,dazun aliyun ya sauketa"
"mu kuma dazu aliyyun ya bar nan yana cigiyar ta ba"momi ta katseta "aljanu ke miki
wasa da hankali ko gida biyu su aliyun suka rabu?" "A'ah momi ai" "kinga dakata shi
aliyun ya riga da ya sanar da babaku komai da kansa,dama maganar da na kira ki
kenan akai,saboda haka idan anyi magariba ki dauko ta kuzo"
Hawaye bibbiyu fadilan keyi"anty me yasa kika sanar musu anty,munyi alqwari dake
anty,me yasa suka sani?" "Fadila aliyyu da kansa yakai kansa gun abba,momi kuma ta
san kina gidan nan dazun da kausar ke qwala miki kira" "me yasa aliyyu zai min
haka?,don me yasa zaije ga uncle abba?,me yasa baiyi sakin cikin rufin asiri ba?,so
yake kowa sai ya ga laifinshi kenan?"sai lokacin tayi dana sani,tayi data sanin da
ta fito tun ranar da yazo gida anty hauwan ya bata takardarta ba tare da kowa yaji
ko ya gani ba,suna sake doso unguwar bugun zuciyarta na daduwa,tabbas da kafin su
yi nisa naty hauwan ta gaya mata inda zasu babu shakka ba zata ba sauka zatayi,gaba
daya jikinta rawa yaje ta kasa nutsuwa sai da anty hauwan ta riqeta sannan ta iya
shiga falon.........
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:11 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?....*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

👉🏼 *PART 3* 👈🏼
9⃣&1⃣0⃣
9⃣1⃣0⃣
Umminta ta gani da mominta zaune kujera daya,uncle abba da abban nata kuma na
kujera daya,sai iftihal dake zaune dare dare kan cinyar abban nata,duk kansu suka
amsa sallamar,sosai taji dadi cikin ranta don rabon da tasa iyayen nata a ido har
ta manta,sai dai hararar da ummin nata ta watsa mata ita ta sagar mata da
gwiwa,anty hauwa ce ta fara gaida su sannan itama ta gaidasun,sama sama ummin ta
amsa mata don har gwara abbanta,cikin salubewar jiki ta koma gefan kujera ta rakabe
Aliyyu ne ya shigo cikin sallama yana sanye da shadda dinkin tazarce kansa babu
hula,da gudu iftihal tayo gurinsa,hannunta kawai ya iya riqewa bayan da ta
gaidashi,gaida su yake saidai abba da umminta ne kawai suka amsa masa,yana shirin
samun guri ya zauna uncle abba ya dakatar da shi ta hanyar cewa "kai....dakata ba
zama na kiraka kayi ba...ungo nan" ya miqa masa farar takarda da abun rubutu
"rubutawa yarinya sakinta tunda Allah yasa mun ganta" da sauri ya daga kai ya soma
rarraba ido cikin filin falon yana neman inda fadilan take,can ya hangota a takure
a gefan kujera kanta a qas
Gaba daya idanunsa suka rufe,tuni ya manta da cewa akwai wasu wai iyayensa a falon
ya durfafeta,idanunsa qir bisa kansa,wani shauqi mai cakude da matsananciyar
qaunarta yake fisgarshi,sai da yaje daf da ita uncle abba ya daka masa tsawa wadda
ta sashi dawowa cikin hayyacinsa "qaniyarka nace dawo nan" inji uncle abba yana
masa nuni da gabansa inda zai zauna din bayan daquwar da ya watsa masa,a salube ya
nufi gun yana tafiya yana waiwayen fadilan da kanta ke qasa idonta na digar
hawaye,takardar ya sake miqa masa "ungo nan rubuta" sai a lokacin abban fadila yayi
magana "haba alhaji bai kamata ba,ya za'ayi yaro da matarsa kuma yana son abarsa a
tilasta masa saki,abinda ya faru ai ya riga ya faru,kuskurene kuma babu wanda baya
yi,kuma ni idan banda shirmen quruciya irin na fadilan ma banga abun da yayi zafi
haka ba,tunda kuma alhamdulillah ya gane sai muyi addu'ar Allah yaci gaba da hada
kansu"
"Wa?wannan?"uncle abban ya fada yana nuna aliyu da yatsa, "ai bai isa ba tunda
tafiso ya saketa sai ya saketa,ai zaluncin ma alhaji yayi yawa,mun zaba mata miji
ba tare da jin ta bakinta ba ko musa mana bata yi ba ta karba harda godiya tayiana
biyayya,taje ta zauna da shi zuciya daya amma ya dinga azabtar da ita,babu kuma
wanda ya taba sani ko sau daya sama da shekara guda har da kusan rabi,kuma yanzu
don bamu da adalci tace bata da buqatar zama sai mu tilasta?don me?,mu zamu yi mata
zaman auren?," sai lokacin itama ummi ta tanka "to alhaji tunda ya gane kuskurensa
don Allah sai abar maganar,ke fadila wallahi tallahi na kuma jin kin furta mijinki
ya sake ki ko mai ya hada ku kuwa sai....." "a'ah hajiya,ya kuke neman daure ma
yaro qarqashi ne?" Inji momi" "barsu indai baso suke su nanamin su suka haifi
fadila ba"inji uncle abba
Cikin sauri hajiya amina(ummi) tace cikin girgiza kai "Allah ya kiyaye alhaji Allah
ya sawwaqe,haba haba da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne"ya dauke kansa ya
maida kan aliyyu "saketa nace ko?"ya nuna shi da yatsa "kuma don ubanka" (aliyyu
bai yaba jin yayi zagi ba ko da wasa sai ranar "a gidan nan zata ci gaba da zama ni
ne dai ubanta "qasa yayi da kansa yaqi furta uffan,babban abunda yasa jikinsu yayi
sayi ganin hawaye nabin fuskar aly,mutumin da komai tsanani ba zaka ga koda qwalla
bane bisa fuskarsa yau shi ke kuka saboda mace?,anty hauwa kamar ta tayi haka take
ji don dai kawai zancan manya ne kuma basj bata damar shiga ba,sauqinta daya ma
iftihal tayi bacci kan cinyar ummi
"Abba wallahi ko wuqa zaku sa ku dinga yankan naman jiki na bazan iya sakin ta
ba,kuyi min afuwa abba" abban fadila ya dubi uncle abban "don Allah salim a naci
albarkacin amintaka ina mai baka haquri kan ka sassauta fushinka kan yarona"falon
ya dauki shiru na wasu lokuta kamin abban ya saki ajiyar zuciya "naji...naji,abu na
farko da zan fara fada shine alhj abbas kai da hajiya amina ku yimin alqawarin babu
wanda acikinku zai tursasawa fadila koda ta bayan fage ne kan sai ta koma gidanta
ba tare da ita ta yanke hakan ba?" Ba yadda alh salim ya iya don yana tausayama
aliyun yace "nayi" ummi ce tayi shiru har sai da hajiya maimuna tace "baki ce komai
ba" "nima nayi"itama ta fadi cike da tausayin aliyu
"Abu na biyu,anan gidan fadila zata zauna har sai taji ta amince don radin kanta
zata koma,idan yaso naga mara kunyar da zai koreta don ba gidansa bane haka nan ba
da qwandalarsa na hada na gina gidana ba"ya fadi yana muzurai,sarai aliyun ya sani
da shi abban yake amma sai ya sunkuyar da kansa,saboda shi kam a yanzu kome zasu
fadi yaji ya gani kuma ya yarda suyita fadin,ko bulala dukkansu zasu dauka suyita
zabgarsa yaji ya amince zai kuma shanye tunda dak an janye batun saki cikin
lamarin,uncle abba ya nuna shi da yatsa "saura kuma naga qafarka inda take bare
kace zakayi yunqurin takurawa ko tursasa mata sai na saba maka fiye da
tsammaninka,tashi ka bawa mutane guri mutumin banza kawai",bashi da zabi illa barin
falom kamar yadda abban ya umarcesu ya miqe ya fita bayan ya duqa yace "na gode
Allah ya saka da alkhairi ya qara girma,Allah kumabya huci zuciyoyinku"yana tafiya
yana satar kallonta har yanzu kanta na duqe taqi ma ta dago ya kalli koda fuskarta
ne
Sosai uncle abba bayanin dalilin yin wannan hukuncin bayan ya sallami fadilan da
anty hauwan,yana sone koda aliyun yayi nadama ya sake sanin darajarta da amfaninta
a gunsa kafin ta koma masa,cikin dariya abban ke cewa"haba alhaji ai ba sai kace
komai ba,amma dai don Allah a sassautawa yarona haka"dariya duk sukayi,daki aka
bawa fadilan kusa da nasu sumayya,amma tace tafiso ta zauna cikin su sumayya,a
daren aka kawo mata madaidaicin gado da cupboard irin nasu rabi'ah aka sa mata duka
adakin kasancewar dakin qato ne sosai,su suka taya ta shirya kayan suna ta rawar
jiki zasu zauna tare,batasan lokacin da su ummunta suka tafi ba sai da anty hauwa
ta hauro saman take sanar mata
Cikin daren babu dan qaramin haukan da baiyi ba,kuka ma kasa zuwa masa yayi sai
zafi da radadi da zuciyarsa keyi,daurewa kawai yakeyi yana sakar musu jiki don kada
ya shiga haqqinsu,wani lokaci idan kewar ta isheshi dakinta yake tafiya yayi bacci
cikin bargonta ya kalli hotunanta sannan yake samun relief
(Qalubale a agareku iyayemmu mata har ma da mazan,da kuna ji kuna gani 'ya'ya yenku
zasu dinga auri saki,babu kwaba balle hantara,wani lalacewar ma idan anyi sakin wai
sai ya kwaso yaran ya kawowa uwar ita ce mai riqe masa kuma tana ziga shi har kina
furta gwara da ya saketa,,to ahir din mu domin kuwa kada mu manta mun haifa ko bamu
haifa ba an haifa mana,za'a yiwa taki 'yar ko 'yar 'yan uwanki kiji idan da dadi?
Ai ko.matar ba ta gari bace akwai matakai da Allah s.w.a yace abi kafin akai ga
rabuwar bawai rana tsaka daga an dan saba masa laifin da bai kai ya kawo ba ya
karkace ya danqaro saki ba,to wallahi muji tsoron Allah,shi mai sakin dake
mahaifiyar me goyon bayansa ina zato a cikin 'ya'yansa ko jikokinki ba za'a rasa
mace ba,ya zakuji yayin da aka koro muku ita?,saki yayi yawa musamman acikin
al'ummar mu ta hausawa,don Allah mu daure mu gyara ko ma samu gyaruwar al'ummar mu
wadda wata tabar barewar tarbiyya daga an saki uwa ne shikenan sai gida ya tarwatse
kowane yaro yayi nasa alqibla,babu mao saita siu kan hanya wato uwa ta gari,Allah
kasa ku dace mufi qarfin zuciyarmu,ameen)
🔅🔅🔅🔅🔅
Sosai ta koma bakin aikinta don uncle abba yace babu mai hanata,babu yadda aliyyu
ya iya haka ya zubawa sarautar Allah ido,ina ma yaga bakin magana koda yana da ta
cewar?,don ko yazo gidan iyakacinsa parlour ko kallon upstairs inda dakunan
baccinsu yake momi ta shiga balla masa harara kenan,haka zatayi kicin kicin da
fuska har sai ya gaji da muzurai ya qara gaba
Ita kuwa uwar tafiyar tun daga lokacin da akayi hukuncin bao sake sanyata cikin
idonsa ba,har addu'a yake Allah ya hadasu amma daidai da gilmawarta Allah baisa ya
gani ba,tana sane ta sani,matuqar taji muryarsa to babu ita babu fitowa tana qule
cikin daki ko kitchen idan a qasa take har sai ya bar cikin gidan
🔅🔅🔅🔅🔅
Da yammacine suna zaune cikin parlour ita da sumayya da rabi'ah,momi bata nan ta
tafi dubiyar yayanta da baya jin dadi alh datti ita da iftihal suka wuce,gidan sai
su ukun,lokaci lokaci rabi'ah naeqa kitchen ta duba abincin dare da ta daura
sumayya kuma na tsefewa fadila calabar din da take kanta,saboda tsawo da santsin
gashi da hannu suke tsifar,yayin da fadila ta jawo wasu fuskarta tana tayata,wani
film da suke masifar ao suke kallo a m.b.c bollywood,na soyayya ne sosai,jarumin
film din na musu kama da aliyyu sosai hatta da halayya,don haka wani lokacin ma ya
aliyu suke kiransa duk sanda aka sako film din,suna son film din don haka idan ana
kallonsa ko hira ba'ayi,saidai idan anzo wani gun daya burgesu,
A hankali aliyyun ya turo qofar falon with confidence don tun a gate ya tambaya aka
sanar masaomin bata nan,basu ga shigowarsa ba sai sumayya kawai don rabi'ah na
kitchen duba girkinta,fadila kuwa gashin da ya rufe mata fuska da yadda film din ya
yafi da hankalinta sosai yasa sam bata lura ba
Sumayya ta bude baki zata yi masa sannu da zuwa ya dora yatsansa kan labbansa,gum
kuwa tayi shiru,ya bata umarni na gaba da ido alamun ta tashi a hankali ta haye
samansu,ba musu kuwa cikin sada ta haura saman,gurbin da sumayyan ta tashi nan ya
maye,harda dan jawota ya jinginar jikin gwiwoyinsa,fadila uwar 'yan son jiki kuwa
ya jingina abunta harda cewa"yauwa sumayya dama baya na ya gaji,calabar ko ashirin
bata kai ba amma taqi tsefuwa ta dadin rai?"baice uffan ba ya kama jelar kitson ya
soma tsefe mata kamar yadda yaga sumayyan nayi,ita kuma bata damu da rashin amsawar
sumayyan ba ta bayar duk film din ne ya dauki hankalinta,rabi'ah ce ta fito da
sauri daga kitchen din don kada tayi missing wani gurin,turus tayi ganin aliyyun a
gun da sumayya tasan ta bari,itama yatsan ya dora mata kan lips nashi,yayi mata
nuni da ido kan ta koma kitchen,nan ne ma fadilan taga giftawar komawan rabi'an
kitchen din "rabi'ah za'a wuce gun da kike son kalla fa" "ina zuwa anty ban qarasa
hada miyar bane"
Gaba daya ya shagala,wani irin farinciki ke ratsa shi,santsi kyau da qyallin gashin
ya hanashi ganin wahalar tsifar,sai gashi sun kusa gamawa saura guda daya,yana
ankare da yadda take bawa film din muhimmanci,murmushi kawai take zubawa hadi da
sakw gyara zama,sai da aka zo wani gu da yayi masifar qayatar da ita ta saki
murmushi tana cewa "hmmmm......soyayya" ta dan waigo tana cewa"don Allah sumayya
basu burgeki ba yadda....."kasaqarasa maganar tayi ganin aliyyu zaune dare dare
saman kujerar yaa mata tsifa,to sumayya ce ta rikide ta zama shi ko idanunta ke
mata gizo?.......
👉🏼 *PART 3* 👈🏼
1⃣1⃣&1⃣2⃣
1⃣1⃣1⃣2⃣
Sai da yasa bakinsa ya hure mata idon sannan ta dawo hayyacinta,da hanzari ta miqe
sannan kuma a guje tayi sama tamkar wadda taga dodo,binta shima yayi a hanzarce
yana kiran ta tsaya,ganin da gaske take ba tsayawa zata yi din ba ya sanya shi
cafkota a matattakalar qarshe,cak ya dagata yayi dakinsu rabi'an da take son
shigewa,cikin sauri sumayya dake zaune saman dressing chair ta fito ta bar musu
dakin
Tsakiyar gado ya direta sai haki suke dukkansu saboda gudun da suka kwasa a step
din benan bugu da qari yadda zuciyar kowannensu ke bugawa,sun zubawa junansu ido
cirko cirko da su kamar zakaru,a hankali yake hawowa gadon yayin da ta soma ja da
baya har ya qureta,suka sake zubawa juna ido,shi nashi na tsantsar so da qaunace da
suke sake huruwa cikin zuciyarsa take kuma aika saqonni zuwa sassan jikinsa,yayin
da nata kuma na jin haushi tsoro da fargaba ne don bata manta wannan dare ba,kasa
jurewa yayi sai da ya miqa hannunsa ya janyota ta fado jikinsa ya matseta gam a
qirjinsa
Cikin fusata haushi da mamakin aliyyun ta soma tureshi,saidai ko motsi baiyi ba don
qarfin ba daya bane,a hankali ya soma sinsinar wuyanta cikin kunnuwanta zuwa gashin
kanta,ya dago fuskarta a hankali ya tura harshensa cikin bakinta,tsotsa yake sosai
tamkar wanda ya samu sweet yayin da ita kuma take turje turje hadi da yunqurin
tureshi daga jikinta saidai sam ma shi baisan tana yi ba,ganin duk iya qoqarinta ta
kasa barin jikinsa sai ta fashe da kuka,hawayen da ya gangaro fuskarta ya taba
nashi fuskar shi ya ankarar da shi,ya zare bakinsa daga nashi ba tare daya bari ta
bar jikin nasa ba,kukanta take sosai yayin da ya zuba mata ido,gaba daya ya
marairaice ya koma kalar tausayi " *fadeelahhhhh*"ya kira sunanta cikin wani irin
yanayi tamkar mai rada,da sauri ta dago kanta ta kalleshi don wannan shine karo na
farko da ta taba jin sunanta a abakinsa, "fadeelah" ya sake kiran nata ta sake
itama kallon nasa "please fadeelah forgive me,I know I hurt you I break your
heart,babu wanda ya wuce kuskure,fadeelah I love you more than words can say,I
can't do without you,na kamu da soyayyarki,pls kada,pls kada kice zaki hukuntani da
tarin laifuffuka na,if bazaki iya yafemin ba ma na amince kiyimin kowanne irin
hukunci zan dauka,amma bazan iya jure rashin ki ba"
*_1:30 am_*
Qarfe daya da rabi na talatainin dare fadila na kwance rub da ciki tsakiyar gadon
ta,gaba daya ta rasa bacci cikin idanun nata,duk juyin da zatayi qamshin turaren
aliyyu take ji daga bakinta har kayan jikinta,har kaya ta sauya amma a banza man
kare don bata daina ji din ba,tana kallon yadda su sumayya ke baccinsu hankali
kwance sai take jin dama ita dince su,basu da wata damuwa,wayarta dake gefan pillow
dinta ta soma haske wanda ke nuna alamun kira ne ke shigowa,cikin mamakinta daga
wayra tana duban kiran baquwar numbace,ta zubawa kiran ido har ya katse,ba'a fasa
kiran nata ba har sai da ta tashi da missed call bakwai ana takwas dinne ta yanke
shawarar dagawa ko wani abunne ya faru,ta danna ok ta kara a kunannta tayi shiru ba
tare da tace komai ba
"Bakiyi bacci ba fadeelah?" Ya tambaya cikin wata iriyan sassanyar murya wadda har
sai data sanya fadila runtse idanun ta,tana jin qaunarsa na yawo cikin jinin
jikinta,shiru tayi masa har ya qara cewa "me ya hanaki yun bacci a irin wannan
lokacin fadeelah?" Nan ma shirun ta sake yi masa,saidai ita kadai tasan yadda take
ni'imtuwa da jin muryarsa mai tsada "nasan kika jina fadeelah,kuma bana tantama
abunda ya hanani bacci shi ya hanaki....,sau da qauna ne ke dawainiya damu baki
daya,tunaninki shi ya hanani sakat kamar yadda na san cewa tunani na shi ya hana
miki yin bacci,da zaki ganni a yanayin da nake ciki zaki tausayamin,da zan iya ciro
zuciyata kiga dumbin qaunar ki da ta cikata fadeelah da nayi,na tabbata da sai kin
min addu'ar Allah ya rage min,jin shirun yayi yawa yasa yace "hello,are you there?"
Ya duba phone dinshi tana nan bata yi hanging up ba,ya sake maida wayar kunnensa
yana cewa "please fadeelah say something ko zan samu relief,am sorry fadeelah and I
said it really" tsananin mamaki ne ya mamaye fadila,shin da gaske ne ba mafarki
take ba aliyyun ne kuwa?aliyyu salim maitama? Aliyyunta?,mafarkinta na kullum,burin
zuciyarta,shike gaya mata wadan nan tsadaddun kalamai?....kalaman da ta dauki
tsawon shekaru tana dakon jinsu?irin qaunar da ta jima tana lalubenta daga gun
aliyyun,shin da gaske ne a yanzu ta samesu?,eh...yes ta samesu but he didn't
deserve ya samu amsarta a arha har irin haka,now its her turned,its her field to
play her game.....
Muryarsa ta tsinto cikin sanyi yana cewa"fadeelah I know you gave me happiness and
I gave you a reason to cray,u gave me your care and I stabbed you from behind,am
sorry for having given you nothing in return for you having given me everything am
sorry kiyi haquri....." kasa jure ci gaba da jin kalamansa tayi,tasani ko iya
wannan ya isheta,ta samu qauna daga gun aliyyun,ta samu soyayyarshi,ya kawo mata
kansa yana begging dinta ta bashi soyayyarta.....,tuni ta katse wayar wani dadi na
nuqurqusarta,ta sani tabbas zai kuma gwada kiranta saboda haka ta kashe wayar gaba
daya,cikin zaqi da gardin kalaman da aliyu ya kasheta da su bacci yayi awon gaba da
ita tamkar dama au take jiran ji,bacci ne mai cike da mafarkan aliyyun a yanayi
daban daban,shi kam tsai yayi da wayar a hannunsa cike da al'ajabin yaushi mace ke
kashe wa waya?,tabbas ya sake yarda fadilan tana da wani matsayi da babu wata 'ya
mace da ta kama koda gefanta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tunda ta kashe wayar bata kunnata ba sai washegari sha daya na safe tana shirin
tafiya office sha daya na safe,cikin shadda take pinch sai maiqo take dinkin
doguwar riga aka mata,cif cif rigar tayi mata kamar a jikinta aka dinkota,ta bude
sosai daga qasa rigar,tana cikin yafa orange mayafinta sumayya na koda kyawun da
tayi"wallahi anty kyawunki na daban ne Allah kuwa ba don wai nayi ziga ba,ko bakiyi
kwalliya ba kyanki fitowa yake,zanso yaya yaga wannan kwalliyar"
Harararta fadilan tayi"ke dai kin shiga tara,tuni rabi'ah ta dade a school ke kin
zauna kanzagi kinqi fita,to bazai ga kwalliyar ba,sumayyan ta qyalqyale da dariya
hadda kwanciya saman gadon"wallahi anty kiyi a hankali kada amiki qwace don har yau
yayin ya aliyyu ake ba'a dena ba,kullum Allah ne da kullum wallahj dai ya fatattaki
'yammata,kada ki dauka qananu,a'a wlh anty hadaddu masu ji da kansu 'ya'yan manya
kuma",fadila ta tabe baki kishi na cin ranta duk datasa haka dinne amma sai tace
"dawar wani karkarar wani abincin wani kuma gubar wani"ta dauki wayarta dake gefan
sumayyan zata fice sumayyan nata sheqa dariya,text ne taji ya shigo hakan ya
sanyata dakatawa daga yunqurin fitar da takeyi,number din da aliyyu ya kirata ne
jiya
Tun shidan safe saqon ya shigo "if u can't see the tears in my eyes,I beg you feel
the pain in my heart....fadeelah na rantse I will do anything and everything just
to take away all d hurt that you feel,please na roqeki give me and let me set thing
straight,am sorry once again fadeela and I love you I really love you...."gaba daya
ya zare mata dukkan kuzarinta,jikinta ya saki,maimakon fita sai ta koma bakin gado
ta zauna,sumayya daketa leqen wayar tana qumshe dariya tace "anty lafiya dai ko?"
Ta saki ajiyar zuciya gami da dauke idonta daga kan screen din wayar "lafiya lau me
kika gani?"sumayya ta kada kai tana cewa "gani nayi kin shirya zaki fita kin dawo
kin zauna,jiya kuma fa anty naga cikin dare baki yi bacci ba ko" hararar fadila ta
sake aika mata tana kada kai cikin zuciyarta tana cewa "lallai na yarda ba qaramin
illa soyayyar aliyyu ta yimin ba,a fili sai kuma tace "naji to sai kuma akayi
yaya?" Ta fada tana ci gaba da jifanta da hararar wasa,miqewa summayan tayi tana ci
gaba da qunshe dariyarta tace "k'n,uhmmmm,a'ah anty ni bance komai ba daga
wannan,amma dai anty kiyi a hankali saboda yayammu gwarzo ne kuma gwani ne,he is
hero,zai iya saaaaaace zuciyarki ba tare da kin sani ba"
Pillow dake kan gadon ta jawo ta jefi sumayyan da shi tana cewa "ban guri mara
kunya" gocewa tayi ta fice da gudu tana dariya,sake mai da kanta fadila tayi kan
saqon taa sake karantawa,ba shakka aliyyu shu'umi ne,so yake ta qarfi da yaji ya
wargaza mata duk wasu makaman yaqinta,ya shirya tunkararta da duk wasu makamansa
wanda tana tsammanin indai haka ne mawuyacine ta iya kubuta daga kaifinsu,duk ya
kashe mata jiki kamar yadda ya saba ta qarfin tuwo ta gayyato dauriya sannan ta
samu ta fita,ta tadda momi da sumayyan a falo,ta yiwa momin sallama,sumayya tace "a
dawo lafiya anty.....momi dama inason baki labarin abinda na gani dazu,wata soyayya
ake mai fada fada aciki"ya fada tana satar kallon fadila dake qoqarin ficewa daga
falon fuskarta dauke da murmushi,a sace fadilan ta watsa mata harara mai nufin
gargadi a fakaice ta qarasa ficewa,sumayyan nata qyatunta tace "na fasa anty kada
ki hanani kudin ankon"..........
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻

  
[10/16, 2:13 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?....*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

👉🏼 *PART 3* 👈🏼
1⃣3⃣&1⃣4⃣
1⃣3⃣1⃣4⃣
Qarfe hudu dai dai ta kammala sallar la'asar dinta a masallacin mata da nan cikin
gidan radiyon,ta goge kyakkyawar fuskarta da hoda,ta murza dan qaramin turarenta na
(asaal brush perfume)wanda bata rabo da shi cikin jakarta saboda dadin qamshinsa
gashi kuma qaramine baya da cika guri,ta saba jakarta bisa kafada sannan ta dauki
wayarta ta nufi office dinsu don ci gaba da aikin takaddun programme dinta na gobe
da ta baro ta taho yin salla
Ta tura qofar ta shiga kasancewar babu kowa ciki fauziyya ta tafi yiwo wani aiki a
a ministry of education shi yasa bata damu da yin wani sallama ba,
Taja takardun gabanta bayan ta zauna ta dora daga inda ta tsaya,sosai yanayin
tsarin programme din na gobe ke burgeta muhawarar da za'a tafka cikin shirin,lokaci
lokaci takan saki murmushi gami da gyada kai,hakanan cikin jikinta ta dinga jin
tamkar ana kallonta,cak ta tsaida rubutun,kan ta kai ga yin komai an zuro hannu an
zare takaddun,tabi hannun da kallo har zuwa fuskar wanda ya gabatar da aikin,aliyyu
ne tsaye qyam a agaban teburin nata,sanye yake da shadda ruwan madara(milk colour)
dinkin yarbawa,rigar iyakacinta gwiwa hakanan hannun rigar shima gajere ne iya
gwiwar hannu,sai manyan aljihu gefe da gefe,wandon dogo ne,kanshi babu hula sai
kyakkyawar sumarshi dake cike da gayu da tsafta,idanunsa na saye da gilashin nan
nasa fari qal wanda tana iya hango fararen qwayoyin idanunsa dake zube fes a kanta
Kallonta yake sosai ba tare da yace komai ba,da azama ta miqe hadi da ture kujerar
da take kai baya,tasa hannu zata dauki jakarta gami da qoqarin ficewa daga tsakanin
table din,taku uku yayi ya tsare mata hanyar ficewar,baya tayi da sauri saboda
ganin yadda yayi gab da ita kamar mai shirin fadowa jikinta,ganin ta sake yin baya
ya sanya shi sake shigowa cikin shima,da haka har ya danganeta da bango,sosai take
jin fitan numfashinsa wanda ke cakude da qamshin turarensa
Ya dage sai ya sanya qwayar idanunsa cikin nata,saidai sam taqi yarda hakan ya
faru,lumshe idanunsa yayi gami da nufar bakinta kai tsaye yana mai kwadayin tsotsar
tattausan lips dinta,tuni ta gano manufarsa ta sunkuya ta qasan table din ta
zille,bai san hakan ya faru ba sai da ya jishi ya dangane da bango,da sauri ya bude
idanunshi,can ya hangota har ta dora hannunta kan handle,cikin zafin nama irin na
cikakken da namiji ya haura ta saman table din don sai yafi masa sauri,taku hudu ya
isa gareta,lokacin tuni har ta sanya qafarta waje
Jawota yayi har sai da ta fado jikinsa uasa hannayensa ya rungumeta,da qarfin tuwo
take son qwatar kanta saidai hakan ya gagara,batasan wani yazo gilmawa ya gansun a
hakan saboda qimar da take da ita agun dukka ma'aikatan gidan ba zata so hakan ya
faru ba,ta kuma kasa bude baki balle tace ya saketa sai kawai hawaye ya balle
mata,Allah ya taimaketa sai ua dauketa cak ya dawo da ita cikin office din hadi da
murza masa maqulli ya kullesu
Ko daga kai ta kalleshi bata yi ba balle yasa ran zata ce wani abun,hakan take masa
ko wani lokaci,ya tsani shirun nan nata,yana ci masa tuwo a qwarya,ya fuskanci babu
ta yadda za'ayi su fuskanci juna babu ta yadda za'ayi ya samu abinda yake buqata
matuqar ya barta taci gaba da yin shirun bayan kullum bai cikin nutsuwarshi duk ta
sanadiyyarta....duk ta sanadiyyar qaunar da yake mata,bayan kk yaushe bashi da wani
muradi sai nata,ta riga da ta gama kashe masa jiki da qwayoyin sonta da bai taba
tsammanin akwai kalarsu a duniyarmu ba,banda time to time yana ganinta da yana
tsammanin tuni ya dade da zaucewa,yana tare da ragowar matansa amma ita yake
gani,zaici abinci amma sai ua bude hotonta cikin wayarsaa fakaice yana kalla ko da
su salima na gun sanna zai samu ya iya ci
A yau dai yaci alwashin ba zaya qyaleta ba sai yaji ta bakinta,bazai barta ba sai
anyita ta qare,ya jawo daya kujerar ya zauna a gabanta gwiwarsa na manne da
tata,yayi mata kane kane ya hanata ta ko motsa duk lokacin da tayi yunquri sai ya
maidata ya zaunar,idanunsa sun kada jajur "I promised ko da yau zamu kwana anan
indai bakice komai ba na shiryawa hakan,ni ko ke babu inda wani zaya motsa,u stole
my happiness any moment in my life am feeling am lonely,ina jin na rasa komai na
rayuwata,why me yasa ba zaki yafemin ba?"
"Na sani I let you down,I made you frown,na sani I dont deserve forgiveness,but I
want you to see the depth in my apology just listen to mu heart,it has been torn
apart broken,but it still beats for you,ina sonki fadeelah ina sonki!!!.....
"Baka sona! stop saying it aliyyu,already ka riga ka gayamin *baka sona baza ka
soni ba ko anan gaba kada nayi tsammanin zaka soni*,ka manta aliyu?..ka manta?,duk
wanda yace baya sonka da safe ya dawo da yamma yace yana sonka he does not mean
what he said,yana nufin wani abu ne na daban ba son ka ba
Sak yayi yana kallonta,bai taba tsammanin tana da baki har haka ba,but....at least
yaji dadi...yaji dadi da yau ta bakinta ya gaya masa wani abu da ta qunshe cikin
zuciyarta game da shi,don haka yana ganin dama ce ta samu gareshi,hannayenta ya
kamo tana qoqarin zamewa,hakan bai dameshi ba ya riqe hannayen qam qam, "duk abinda
kike tuhumata da shi na amince na aikata din,annabimmu ya umarcemu muyi soyayya
saisa saisa don zata iya juyewa qiyayya,hakanan ya umarcemu da kada mu zafafa
qiyayya don wata rana zata iya zama soyayya,na mance da hakan,na tozarta kyautar da
iyayena suka min shi yasa yanzu Allah ke mani hukunci,na manta da cewa *babu wanda
yasan gobe sai Allah*,but now fadeelah I identified my mistake,I made so many
mistaken,sai dai ki zama mai afuwa yafiya rangwami da sassauci" ta sake zame
hannayen nata da sauri ya kama su "I love you.....I love you" "nooooo!" Ta fadi
hawaye na zirya a kumatunta, "baka sona aliyyu....bani kake so ba jikina kake
soo.....don me yasa da can baka kusance ni ba sai da nayi amfani da wani abun?,don
me yasa baka soni ba sai da ka kusanceni?,ina buqatar amsoshin wadan nan tambayoyin
aliyu!"ta qarasa fada a dan tsawace wadda kanta bata san ta iya ta ba balle aliyyu
da ya zuba mata ido hadi da sakin hannayen ta ba tare da ya sani ba
Kafin yace komai akayi knocking qofar ana fadin "yau kuma me muka samu a office din
namu anty fadila ta rufe mana qofa?"cewar fauziyya da yarinyarta dake tayata
knocking qofar,kasa motsi fadilan tayi koda na yunqurin goge hawayen ta ne,cikin
rashin kuzari ya isa ga qofar ya bude,fauziyya ta kalli fadila da aliyyun tana son
tuna inda tasan fuskar,sai ta saki murmushi tana komawa baya "oh...sorry na katse
ku ko?,ku gafarceni"ta juya zata wuce tana murmushi"anty fadeelah iman tace a rage
kukan nan,duk da ta sani na soyayya ne"aliyu baisan sanda yace "baiwar Allah....don
Allah sai ya zama laifi don mutum na tsananin aon matarsa?,don kawai.........
Zumbur tayi tace"ni din ma bance laifi bane"fadilan ta katse shi da sauri,dariya
fauziyya ta sake yi ta gyada kai bayan ta gama qare musu kallo"wow,salonsoyayyarku
abun sha'awa ne,ya burgeni hakan,well.....koma dai mene ne naga zallar son junanku
cikin qwayar idanunku,Allah ya bar soyayya"tayi gaba ta kama hannun iman da tuni
tayi gabanta tana ta tsalle tsallenta,ta nufi ofishin da zata kai aikin da taje yi
A sanyaye ya koma gabanta ya tsaya ya zubawa qasan office din ido wanda ke shimfide
da terrazzo,a hankali ya saki hannayen nasa,ya tsugunna a gabanta tamkar mai kama
ruwa ta yadda zai iya gano fuskarta sosai don kuwa kanta na duqe tana sharar
qwalla,"fadeelah" shiru tayi ya sake cewa "fadeelah kin daina sona?" Nan ma shiru
"fadeelah kin daina qaunata ko?!" Ya fada cikin dan fusata,a zafafe itama ta mayar
masa "amsa kake so kaji?"daga girarsa yayi idanunsa na kanta"yes!" "Na daina sonka
bana sonka,kai ada din ma ba sonka nake ba,ban fahimta bane sai yanzu!" Ta fada
kanta tsaye ba tare da kawaici ba,lumshe idanunsa yayi yana jin radadin saukar
kalaman cikin kunnuwansa kamar ana soka masa mashi,kusan wannan itace kalma mafi
muni da yaji wadda ya jima baiji irinta ba,mace ta farko da zuciyarsa ta soma so
don radin kanta ta kuma yi mata wani irin kyakkyawar masauki can cikinta tunda
Allah ya ginata,irin masaukim da bai taba budewa wata mace koda bakin qofarsa...yau
ita ke furata bata sonsa,kalmar da tunda yaje babu wata 'ya mace da ta taba furta
masa ita sai ita din,wani daci na kalmar qiyayya da aka gaya masa ke ratsa
zuciyarsa
Sai yaga bashi da wani mataki da zai dauka saboda haka itama ta dandani makamancin
wannan dacin koma wanda ya fishi,saidai yana son tabbatatwa da kansa da gaskene
bata sonsa?,ya bude idanunsa ya zubesu fes a kanta har yanzu kanta na qasa tana
share qwalla,"fadeelah!" Ya kirata cikin wata iriyar murya,bata amsa ba hakanan
bata kalleshi ba,ta sani babu abunda bai so irin shirun nata "fadeeelahhhh!"ya fada
cikim qaraji,bata sanda ta dago kai suka hada ido ba,da sauri tayk qoqarin maida
kan nata amma sai ya fita hanzari,da sauri ya riqe habarta ya dago kan nata........
*note*:don Allah masu caccanza numbers na novel dina na roqeku ku daina🙏🏻,sai nayi
typing sai acanza tsarin number a dinga rikitarmin da makaranta na to gaskiya bana
so,idan kuma aka ci gaba to ba shakka zanyi Allah ya isa,sannan na samu wata kuma
tana samin number din wayarta cikin typing dina,to itama na roqeta ta bari,idan
bata ji ba zan kai qararta gurin Allah,don kuwa yana gaggawar amsa addu'ar wanda
aka zalunta,ku barmin novel dina yadda na tsara,kuma kuyi naku ba wanda ya
hanaku,Allah yasa mu dace🙏🏻
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:13 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?....*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

👉🏼 *PART 3* 👈🏼
1⃣5⃣&1⃣6⃣
1⃣5⃣1⃣6⃣
Da sauri ya riqe habarta ya dago kanta,"ki kalli qwayar idona ki gaya min baki
sona,I promised zan bace daga rayuwarki kamar yadda kikamin alqawari kema!" Ta sani
qwarai aliyyun kaifi daya ne,yana aikata duk abinda ya furta komai
tsananinsa,tashin hankali da tsantsar rigima da take hangowa yanzun a qwayar idanun
aliyyun ba kadan bane,ko bama haka din ba tana jin ko kanta za'a sanya gabas a dora
mata wuqa ba zata iya kallon qwayar idanunsa tace bata sonshi ba,ita kanta ma tasan
ta yima kanta qarya koda ta fadi hakan,wannan ma wasa ne
Ko motsi kasawa tayi don tasan abinda yake buqata din ba qaramin girma ke da shi ba
a gunta, "uhummm.....am waiting,tell me fadeelah.....tell me baki sona kamar yadda
kika fada dazun"shirun dai ta kuma yi din bata da abun cewa,yasa yatsunsa ya sake
dago fuskarta ta sosai still dai taqi yarda su hada idanun"fadeelah ni na sani kina
sona,kina qaunata,amma me yasa ba zaki yafe min ba?me yasa ba zaki manta komai
ba?,if u are nt willing to forgive someone,then you don't truly love them,fadeelah
silence the mind and hear the heart,ina sonki fadeelah ina sonki har bansan adadi
ba"cikin murya dake nuna alamun karaya ta dago kan nata ba tare da ta dubeshi ba ta
dawo da tambayarta ta dazu "na gaya ma baka sona aliyu jikina kake so!" Cikin rudu
ya sake kamo hannayen nata da ta sabule ya riqe gam "wa ya gaya miki hakane
fadeelah?,who told you?" "Ni na gani da idona,baka soni ba aliyyu sai da kwanta da
ni?" Bai son wanna kalmar da taje furtawa
bai san sanda ya zauna dirshan ba qasan office din,"wallahi Allah fadeelah idan ba
tare muka fara son juja ba to da kadan kika rigani,wani kurman so nake miki
fadeelah ki yarda da ni ba tare da ni kaina na sani ba,zuciyata na sonki ba tare da
nasan hakan ba,na sani......kuma na zaci haka dama zaki zaci cewa jikinki nake
so,saboda ban tashi sanar dake ina sonki ba sai a wannan gabar,bani da kalmar da
zan kare kaina da ita,amm abu daya ne zai tabbatar miki da gaskiya ta,abun kuwa
shine....ki amince ki dawo gidana fadeelah wannan shi zaisa ki tantance wanne irin
so nake miki,zaki gane za kuma ki fahimci ba wani abu daya nake kwadayi tare da ke
ba....a'a....kedin gaba dayanki nake qauna nake so fadeelah,na miki alqawarin baza
sake taba koda yatsanki ba har sai kin nutsu kin amince da soyayyar da nake miki
"Fadeelah na sani ni da bakina nace miki bana sonki amma wallahi Allah shine shaida
ba haqiqanin abinda ke zuciyata ba kenan,ban taba jin qinki a zuciyata ba dai dai
da qwayar zarra,wallahi fadeelah da bana sonki bazan aurenki har na iya zama da ke
ba,bana iya zama da abunda zuciyata ke qinsa,mata nawa ke sona?mata nawa aka kawo
min a take na qisu?,amma fadeelah na amince na aureki na zauna qarqashin inuwa guda
dake.....nake ci daga abincin da hannayenki suka sarrafa shi....nake buri da
muradin sha daga abunda hannunki ya hada,nake kuma kwanciya bigire daya dake
qarqashin rufin kwanon daki guda"
"Fadeelah.....kalli qwayar idanuna na tabbata sun isa amsa a gareki,ban iya qarya
ba fadeelah,amma karo na farko da na fara yinta a rayuwata,na bugi qirji nace bana
sonki bayan nasan ba haka bane,nace bazan soki ba koda wata rana ne bayan *bansan
gobe ba,ba wanda yasan gobe sai Allah*,gashi yau wata ranar tazo ta riskeni ta
qaryatani......kuma nima na qaryata kaina da kaina"yayi shiru idanunsa na kanta
yana maida numfashi
Gaba daya ya gama da ita,ya lalata mata dukkanin tunaninta,ya tarwatsa duk wani
mummunan tunani zato da tsammani da a da take da shi a kansa,maimakon haka ma sai
wata sabuwar qauna da soyayya tasa dake ratsata har jinin jikinta,ahankali take
fasa qashi tana malala har zuwa bargonta,jinta take kamar ba'a duniyarmu take
ba,abinda ta jima ta jima tana bege da yaqin samu gashi yau a gabanta,yau ga aliyyu
zaune dirshan a gabanta,yauga aliyyu zaune ya zamo kalar tausayin a qasan
qafafunta,bayan babu abinda ya rasa a rayuwarsa soyayyarta kawai yake nema,aliyyun
nan dake bata tsoro,aliyun nan dake da girman kai aji da kuma kwarjini yaushi yake
roqon soyayyarta?,to itakam idan bata sallama ba tayi haqurin ai ta yiwa Allah
butulci,me take nema dama idan ba wannan din ba?,tasan wasu daga halayensa sarai
kamar yadda kowa ya shaideshi bai iya qarya ba....shi din kaifi daya ne da ko
gaskiyarsa ba zata faranta maka ba hakan bai dameshi ba
Cikin cool voice da wani irin kunya da nauyi kanta a qas tace "na yafe maka,komai
ya wuce "lumshe idanunsa yayi wani sanyi na kwara cikin ransa,ji yake kamar an masa
gafara da bushara da aljanna,me yafi so dadi?,me yafi qauna faranta rai?,amma duk
da haka yana neman qarin bayani,ya bude idanunsa ya sake matsowa jikin
gwiwoyinta,"fadeelah kalmomin da zan miki godiya da su na tabbata sunyi kadan,bani
da su saidai na kwatanta yin hakan don bani da abunda zan iya saka miki da shi,na
gode na gode Allah ya miki sakamako da aljanna,but I need more fadeelah I need
more,please tell me kina sona kina qaunata kuma zaki koma gida na"kafin tace komai
aka sake knocking,da sauri ta daga kai ta kalleshi "please ka tashi daga qasa ka
koma kan kujera,za'a iya shigowa a ganka a haka fa" ya noqe kafada ko matsawa baiyi
ba yana ci gaba da kallonta "no,I don't care ko waye ma zai ganni a haka,a gaban
fadeelah ta nake kuma ta cancanci komai har ma fiye da hakan,idan tana sone ma na
kwanta ta dinga taka gadon baya na tana tafiya am ready if I can make her
happy"dariya ce ta subuce mata tasa tafin hannunta tana qunshe bakin,ya kalli
qwayar idanunta da suka sake yin kyau da 'yar ragowar qwalla aciki wadda tasa shi
ya koma kamar oily eyes ya dage girarsa "oh,kina tantama ne?,let me show you"tuni
ya soma qoqarin ruf da ciki a qasan,batasan lokacin da ta kama hannunshu ba tana
qoqarin hanashi ba"no haidar,I trusted you"yabi hannayen nasu da kallo yadda ta
riqe masa hannu da tattausan hannunta,ganin yana kallon yadda ta riqe shin sai
kunya ta kamata tayj saurin janye hannun hadi da yin qasa da kanta tana
murmushi,shima murmushin yake sannan ya nufi bakin qofar ya bude,fauziyya ce har ya
dawo tace cikin fara'a "ina fatan kun kammala ban sake katse ku ba karo na biyu duk
da takaddu kawai na shigo diba zan wuce gida"yasa hannu ya dauki baby iman dake ta
miqa masa hannu taba masa dariya tamkar dama can ta sanshi ya soma mata wasa,baice
mata komai ba sai hanya da ya bata yace"bismillah"
Yana ji tana tsokanar fadila haddi da yi mata sallama "yau dai ban sani ba ko anan
office din zaku kwana ke da ogan" cikin murmushi ta mayar mata "a haba
fauziyya,gida za muyi yanzu muma"ya sauke mata iman hadi da zurawa yarinyar five
thousand cikin awarwarayenta dake hannunta,yaro ba wayo sai kallon kudin take gami
da qoqarin zarosu tana ganinsu kamar abun wasa ne,yana ta murmushi son yara na dada
kamashi,fauziyya ta masa godiya,shi ba ma'abocin son ayi masa godiya bane don yayi
kyauta don haka baice komai ba ya dauke kansa ya maida kan fadeelah dake qoqarin
miqewa don hada kan komatsanta da niyyar tafiya gida,wani jiri ya debeta duhu ya
gilma idanunta tayi baya luuuu zata fadi,cikin zafin nama ya qaraso gareta ya mata
kyakkyawan masauki cikin faffadan qirjinsa yace "subhanallah",fauziyya dake
yunqurin jan qofar ta dakata gami da juyowa "sannu fadila jirin ne dai?" Da mamaki
a fuskarsa ya kalli fauziyyan "dama jiri take yi?"
"Wallahi tunda ta dawo aiki take fama da shi,kullum haka take yi,matuqar tayi dogon
zama ko zirga zirga,nayi zaton ma ta gaya maka,don nayi nayi da ita taje taga
likita sam taqi,don ko jiya sai da na dan riqeta na wasu mintina sannan ta zama
normal"
"Thank you" yace ya maida idanunsa kan fadilan wadda ta sake cusa kanta cikin
qirjinsa tana shaqar daddadan qamshin da jikinsa keyi,dadi qamshin ke mata sosau
kamar su dawwama ahaka haka take ji,maidata yayi ya zaunar saman kujerar ya hada
mata dukkan takardun da take buqata din cikin hand bag dinta ya dauka sannan ya zo
ya miqar da ita ya rungumeta ta kafadarsa yadda zasu iya tafiya a hakan
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:14 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?....*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

👉🏼 *PART 3*👈🏼
1⃣7⃣&1⃣8⃣
1⃣7⃣1⃣8⃣
Ganin ya nufi qofa alamun ficewa za suyi ya sanya fadila zaro ido "a haka zamu
fita?"
Ya dubeta "yes ko yayi miki kadan na daukeki ne?"
Ta kuma zaro ido cikin marairaicewa tace "no,please ka cika ni ka ban jakar,ai na
daina jin jirin zan iya tafiya da qafata"
Girgiza kai shima yayi"no,bazan iya barinki ba,bazan bari kisha wahala ba indai ina
tare da ke,ko ki bari mu tafi a haka ko na daukeki gana daya na kaiki har cikin
motar"
Ta san halin aliyun kadan ne daga aikinsa,zai iya aikatawa ba tare da yaji ko dar
ba,tilas tayi shiru suka fita tana sunne kai
Motarsa taga ya nufa da ita,ta dago da kanta tana ce masa "amma da ka bari tunda a
motata na zo sai na koma aciki ko?kada momi ko uncle abba su gammu tare"
Ya tabe baki sannan ya saki dan qaramin murmushi dake qayata fuskarsa "kada su
gammu tare?,so what?,ai ni dama haka nake so,kinga daga nan sai su tarkata min mata
ta mu koma inda muka fi wayo"murmushi ta saki ta maida kanta don dariya aliyun ya
bata,ya bude mata gidan gaba kusa da shi sai da ta shiga ya dan kwantar mata da
kujerar ya sumbaci goshinta duk tana kallonshi "ki zauna a haka don bani so a
ganemin ke a hanya"murmushi kawai tayi cikin jin kunya,cikin zuciyarta tana
cewa"idan banda abun sa wa zaya ganni mota duk baqin glass"ya zagaya nasa bangaren
ya bude yana shirin shiga
Wasu 'yammata su uku suka fito daga reception,daya daga cikinsu ta finciko hannun
dayar tana nuna mata aliyyu,damar da ta jima tana neman kena taga aliyun don haka
ta jawo hannunta ta rakota har bakin qofar motar,yana shirin sanya qafarsa yaji
ance "ranka ya dade ya kai kyakkyawa" kusan ha saba jin irin wadannan babatun
abakin 'yammata saboda haka bai juyo ba sai da ya shiga motar ya rufe qofar sannan
yayi qasa da glass din,fuskarsa a yamutse kamar ya ga kashi yake kallonta,yayin da
ita kuma ta harde hannaye ta zuba masa ido tamkar mayya tana zabga murmushin neman
shiga "kina da matsala da ni ne?",cikin murmushin tace "yes,babba ma kuwa"aliyu ya
fasa kunna motar da yake qoqarin yi da dayan hannun nasa ya dogara hannun jikin
murfin motar yana shafa sumarshi hadi da tsareta da ido,ya sani sarai qarya take
don yaci karo da mata irinta sunfi dari
Sai yayi mata kwarjini domin shi din ba kalar wasa bane,ba tare da ya sake tambayar
tata ba ita da kata cikin diriricewa tace "zuciyata ka sace min ne,kuma na jima ina
jiran rana irim wannan da zan sanar da kai"fadila dake kashingide cikin motar
kalaman suka shiga kunnuwanta,amma sai taga meye nata tunda ba'asa da ita ba,bari
taga ya drama din zata kaya,sake kallonta aliyu yqyi cikin raini "ke! Ki shiga
hankalinki,ni ba sa'an wasanki bane,bana son shashancin banza" yaja tsaki yana
shirin tada motar ya kunnata ya fara dan janta yana duna inda zaiyi ribas,"ko baka
sona ni ina sonka wallahi kuma suna na mansurah"ya leqa kansa ta window "sai ki
bada himma ko,stupid" "Iove you idan baka soni ba bazaka hanani in soka ba aliyyu
salim kuma sai na aureka na shigo gidanka"zuciyar 'yan maza ta motsa ya tsani mata
masu naci irinta haka,niyyarsa ya fice yayi maganinta ta kama hannunsa dariya na
shirin subuce mata "haba sonka fa tace tana yi ba qinka ba,masoyi ai yafi maqiyi
meye laifinta?" Tana gama fada dariyar ta kubce mata
Tuqi yake amma gaba daya kaf hankalinsa na kanta,duk second biyar zuwa goma sai ya
juyo ya kalleta,sai daga baya ta lura da hakan "please ka maida kanka gun
driving,kaga muna kan titi ne"ta fada idonta na kallon kan titi,gani tayi yayi
gefan titi a hankali ya gangara gefan kwalta yayi parking din motar sannan ya kashe
ta,ta juyo ta dan dubeshi don bin ba'asin abunda suka tsaya yi din,amma sai ta kasa
furta komai saboda wani mayen kallo da yaje binta da shi wanda ya haddasa mata jin
wata matsananciyar kunya mai kashe jiki,ya sake raunata mata zuciya da gangar
jikinta da wani kurman saqon soyayya mai zafi,bata san sanda ta maidq bayanta jikin
kujerar ba ta lafe hadi da langabar da kanta gefen kafadarta hagunta
A hankali yasa hannunsa ya juyo da fuskarta zuwa gareshi, "no,kada kimin rowar
fuskarki baby na,barni in more abuna" bata ce komai ba sai dan qaramin murmushi da
ta saki wanda ya sake shagaltar da aliyyu,sannu a ahankali ta dora qwayar idanunta
cikin nasa tana morewa kallon aliyyun,rana ta farko da hakan ta soma kasancewa
tsakaninsu,dukkaninsu kallon so qauna aminci da yarda suke wa junansu
A hankali ya soma motsa labbansa da yakejin suna mishi nauyi still idanun nasa na
cikin nata yace "please,tell me kina sina baby nah"ta dan lumshe idanun nata tana
jin wani shauqi cikin zuciya da gangar jikinta sannan ta sake budesu ta watsa su
cikin idon aliyun "bau wasu kalmomi da zasu iya bayyana abinda nake ji cikin
zuciyata, I love you more than I did yesterday,and I will love you more tomorrow
than I do today,kai na fara so kuma kai zanci gaba da so har qarshen rayuwata,inaji
a jikina an halicceni ne kawai saboda kai" jinsa yake tamkar yana yawo a sararin
samaniya,yana jin tamakar su dawwama a gun tana ci gaba da bayyana masa irin qaunar
da take masa da sweet voice dinta
Karo na farko da fadeelah taga dariya mai cakude da murmushi cike da nishadi kwance
bisa fuskar aliyyun,har yanzu idanun nasu na manne dana juna "is what I see in your
eyes true or the mirror?"gyada kai tayi tana mai bashi tabbaci "its true,da gaskene
miji na" "really?" Ya sake tambayarta "yes its real"ta amsa masa tana sake bashi
tabbaci,hannayenta ya kamo ya matse cikin nasa tafin hannun,"please ina neman
alfarma guda daya" gyada kai tayi alamun tana saurarensa,ya sake matsowa kusa da
itan har suna shaqar numfashin juna yana murza tattausan tafin hannunta "ina
roqonki fadeelah if u reprimand me hug me and give me bliss and let it to be a
loving touch,please na roqeki kada ki sake yin nisa da ni,kada ki kuma barina,kada
ki kuma raba ruhina da naki,kimin alqawari fadeelah na,are you promised to do
it?"ta gyada kai tana murmushi "yes I promise you" "good and I promise you too....I
will never do it again,all I want is to see you smile forever not just for a
while...." ya rungumeta tsam yana fadin"am sorry I will never hurt you again" "ya
wuce wallahi ya wuce,Allah ma muna masa laifi ya yafe mana"
Tsawon mintina yana rungume da ita yaqi sakinta,ita din ma dadin hakan take ji
sosai,don ba zata yaudari kanta ba sosai tayi missing soft skin nashi,tayi missing
scent nashi masu dadi,kai komai nashi ma tayi missing dinsa,sai gashi lokaci guda
Allah ya maido mata da shi da kuma abunda bata taba tsammanin ba ma,duk da ta sani
addu'a bata faduwa qasa banza dama,kuma lallai wani jinkirin alkhairi ne,sai da
taga lokaci na qoqarin qwace musu gashi bai da niyyar sakinta bare ya tada motar su
tafi "lokaci na tafiya fa,kada momy taga ban dawo on time ba"ya dagota yana
kallonta"sai kice mata kin sha'afa ne kina tare da lovely husband dinki"ta rufe
fuskarta da tafin hannunta "momin zan cema haka?"ya dage girarsa "yes kinga sai
tace tattara kayanki kibi mijinki,kinga fine komai yayi kyau ko?",sai ta maida
jikinta kan kujerarta tana murmushi qasa qasa,qamshin turarensa da ya manne a
mayafinta yana sake yi mata dadi tamkar yau ta sanshi
Kusan sai da suka tsaya sau kusan uku kafin sukai gida,kallonta yake ne yaqi maida
kanshi yayi tuqin,idan tayi masa qorafin hakan sai ya yace "gaskiya gaskiya bazai
iya tuqi baya kallonta ba,saidai a haqura da tuqin idan ya gama kallon nata sa
tafi,lokacin da suka isa gida tuni anata tada iqama,tana qoqarin ficewa daga motar
ya kamo hannayenta,ta dan fiddo da idanunta tana kallonsa,ta shagwabe fuska kamar
zata yi masa kuka " please ka sakemin hannu muna cikim gida ne fa yanzun,it can be
possible wani ya fito ya gan mu a....." kanta qarasa tuni ya janyota jikinsa daidai
lokacin uncle abba ya fito daga cikin gidan hannunsa dauke da carbi da alamu
masallaci zashi
Sarai ya gansu amma sai ya dauke kai tamkar bai kula da su agun ba,farinciki yaji
sosai cikin zuciyarsa "alhamdulillah"kawai yaje fadi cikin ransa,bisa dukkan alamu
sun sasanta kansu kenan,yanzu yake ji a zuciyarsa zai iya maida fadilan gidan
aliyyu,don duka alamu sun nuna na qauna da soyayyar da suke ma juna,fadila ce ta
soma ganin abban lokacin har ya basu baya,ta zare jikinta da sauri tana gyara yafen
mayafinta zuciyarta na bugawa tace "innalillahi" aliyu ya kalleta"lafiya baby?"
Uncle abba ta nuna masa da yatsa tuni idanunta suka cicciko da qwalla "ya ganmu
wallahi,sai da nace ka bari ka bari fa"
Dariya ya saki cikin nishadi "to mene ne?,kinga addu'ata ta karbu kenan,kuma ma
baby naga da mijinki ya ganki fa mene na rudewa har irin haka?" Ya jawo hannunta
yana goge mata qwallar da ta soma gangaro mata "calm down my unique,don't cry
again,kin gama kuka a duniya ai matuqar ina tare da ke,I will never let your tears
to fall down again.....muje ma raka ki ciki"sai taga tunda abba ma ya riga ya gansu
a dazun don rakata ma cikin gida ba komai bane,abun kunyar dai an riga an gama
tafka shi,tayi tayi da shi ya bata jakarta ta riqe yaqi yace sai ya kaita har
ciki,sai da yace idan ma ta fiya matsawa zai goyata ne ya kaita har cikin
gidan,tasan kadan ne daga aikinsa,tilas ta bar masa tayi gaba yana take mata
baya......
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:15 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?....*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

👉🏼 *PART 3* 👈🏼
1⃣9⃣&2⃣0⃣
1⃣9⃣2⃣0⃣
Ai kuwa sukayi kyakkyawan gani cikin parlour,momi ce da iftihal dukkansu suna zaune
kan kujera sanye da hijabi da alama sallah suka idar,karatun qur'ani iftihal keyi
da ka momi na gyara mata kura kurenta,kallo momin ta bisu da shi daga bisani sai
kuma ta dauke kanta tamkar bata gansu ba,ya miqawa fadila jakarta da take ta Allah
Allah ta bar falon kunya gaba daya ta rufeta,gogan harda hadawa da hannunta lokacin
da zai miqa matan,ta zame hannun nata da sauri ta haye sama inda dakinsu yake,ya
wani bita da kallo ko kunya baiji ba,sai da ta qare hawa sannan ya janye idonsa ya
juya da niyyar gaida momi
Ashe idanunta na kansa take suka hada ido,sai yaji wata kunya ta kamashi,yasa
tsinin key din motarsa yana sosa tsakiyar kansa irin najin kunya,yakoma gefe ya
tsugunna yana gaidata yayin da tuni iftihal tayo qaura gurinsa,maimakon momin ta
amsa sai tace "rasa kunya beran tanka,tashi ka bani guri,kada na kuma ganin kana
takura mata daga yau,na gaya maka ka qyaleta tayi hukunci da qashin kanta,idan ba
haka ba tamu ce ni da kai"ya miqe yana murmushi lokacin da yake maida iftihal kan
kujerar kusa da momin,abinka da wanda bai iya qarya ba sai yace "momi ba takura
mata nake ba,ai tama gama yanke hukuncin,mun gama magana da ita momi"baki sake ta
bishi da kallo lokacin da ga fara tattaki zai bar falon "iye?,me kace?"
"A'ah momi bari inje nayi sallah"shima ya fada yana waiwayo wa gami da sakin dariya
wa momin har ta fice
"Ja'iri ka maida ni kakar ka ko?"
"Momi ai dama kakarsa ce ke"inji iftihal dake faman wasa da bezar hijabinta,duk sai
suka bata dariya 'yar da uban,cikin zuciyarta tqna addu'ar Allah ya daidaita ya
sake tsakaninsu
Kowa ya hallara a dining har aliyyu da yaqi tafiya amma qememe fadila taqi
saukowa,ita kam ba zata iya ba,bala'in kunyarsu abban take ji don aliyyu ya gama
kunya tata,kuma ta sani ko da ta sauko din tunda aliyun na gun ta tabbata sai ya
sake kunyatata kafin a tashi,haka abban yace a qyaleta don yasan me take yiwa
kunyar,sam sai yaji abincin bai masa dadi don mafi rinjayen zaman cin abincin nasa
saboda ita ne,suna tsaka da cin abincin ya soma tari kamar ya qware,sai yaqi daukan
ruwan dake kan table din yayi hanyar kitchen su abba na masu sannu,ganin idon kowa
bai kanshi sai kawai ya haye matattakalar sadaf sadaf yayi sama,momin ce ta soma
ganoshi ta dan tabo uncle abba yadda su sumayya ba zasu gani ba ta nuna masa
aliyyun,dariya uncle abban ya saki shida momin duka,
Tana zaune dirshan tsakiyar gadon,gabanta system ce a bude tana faman aiki
cikinta,doguwar rigar yellow din material mai santsi ce a jikinta,mai tankakken
hannu ne dinkin ,babu abinda ta shafa illa man lebe da ya qarawa lips dinta
taushi,sai jikinta dake tashin qamshin turaren asaal,kyakkaywan gashinta baqi sidik
mai tsawo da qyalli yasha gayara ta tajeshi ta daure shi da qaramin ribbon yellow
ya sauka gadon bayanta yana reto,hundred percent hankalinta na kan system
din,alewar mints ce a bakinta tana tsotsa a hankali,sai da ya gama qare mata kallo
iya son ranshi "unique lady"ya fada cikin ransa,komai nata mai aji ne,yanayin zaman
nata bisa gadon sai ya zamewa aliyyu abun sha'awa,lallabawa yayi ya haye gadon ta
bayanta,sai jinta kawai tayi rungume jikin mutum,a dan firgice ta waiwayo ya manna
mata kiss a goshinta tare da sakin murmushi"me yasa kika qi saukowa kici abinci
bayan kin sani bazan iya tafiya ba tare da na kalli wannan kyakkyawar fuskar taki
ba"ya qarashe maganar yana shafa gashinta da ya qayatar da shi
Zumburo baki tayi kamar na shagwababbun yara tana dan kici kicin qwace kanta "haba
mana dear dakinsu sumayya ne fa,suna iya shigowa su ganmu"daga hannunwansa yayi
yana murmushi🤗"is ok,indai so kike na qyaleki sai idan kin yarda zaki bani hot
kisses a matsayin sallamarmu ta yau"sak tayi ta kuma yo kicin kicin da
fuska,murmushinsa ya dadu yace "uhm,am waiting dear"nan ma shiru,ya dora kansa
saman kafadarta yana leqen fuskarta,saura kadan ya fashe da dariya yadda yaga tana
zare idanu,ta gintse dariyar yaba cewa "don't mind dear,if you are not ready kinga
sai muyi zaman mu a haka ko?"da sauri ta noqe kafada "no am ready,but.....Please ja
rufe idanunka" "ok....ok" ya fadi yana cikata gamida rufe idanun
Shiru yaji hadi da qarar qofa,da sauri ya bude Idanun nasa,ta qarasa sa key din
qofar toilet tana qyakqyala masa dariya,sai ya harde hannayensa ya zubawa qofar ido
fuskar sa qunshe da murmushi"no baby,kin karya agreement,kisses sun qara nukuwa,sun
zama double yanzu,ko ki fito ki bani ko in kunce gidan key din yanzun nan in shigo
toilet din"dariyarnan tata mai saurin shagaltar da shi taci gaba da yi
Sai da taji sukur sukur dinshi jikin qofar sannan ya sata nude qofar da sauri,wayo
dama ya mata ba wani gidan muqulli da zai kwance,ya cafkota ta fado jikinsa suna
dariya,dariyar tasu ta tsaya lokacin da wayarsa ta soma ruri,ya cirota daga
aljihunsa yana dubawa,salima ke kira don itace da girki dama yau zata fita,ya kara
a kunnensa,da qorafi ta fara masa kafin sallama, "ok gani nan"kawai yace mata ya
maida wayar aljihun,fadila tayi lamo jikinsa kishi na sukarta,ya dago fuskarta yana
kallo sai yaga alamun ta dan canza,yasan dalilin hakan saboda haka dadi ne ya
kamashi don yasan abunda ake so ake kishi, "oya babe,give me"ya fadi yana sake dago
fuskarta gareshi,wani hot kisses ta soma bashi wanda ita kanta bata san ta iyasu ba
sai yau,sosai ta rudashi har suka gagara tsaiwa suka zube saman
carpet,shigowar rabi'ah da komawarta da baya da sauri shi yasa fadila saurin zare
jikinta,a kasalance ya maida idanunsa kanta,kanta a qasa tana tattare gashinta da
ya yamutse tana maida shi cikin ribbon,ya sake maida idonsa bakin qofa inda rabi'ah
ke tsaye a bayan labulan ta yadda yanzun bata iya hangosu "yaya,momi ce ke kiranka"
"bace min a gun stupid kawai,baki iya sallama ba zaki shigowa mutane daki kai
tsaye?"
Sum sum ta juya tana tabe baki cikin ranta tana cewa "sallamar miliyan nawa kakeso
nayi muku ,ka shiga wannan yanayin koda ganga nake sallama taya za'ayi kaji,su yaya
aliyyu ashe haka aka iya soyayya?" Sai ta qyalqyale da dariya ita kadai,yasa
yatsunsa ya dago da fuskarta yana son kallon qwayar idonta amma taqi yarda "I need
more please..."ya fadi muryarshi qasa qasa tamkar mai rada,tuni ta shagwabe fuska
tana cewa "please.....Please,na yima fa,kuma momi ke jiranka fa ma"ya yunqura ya
miqe yana gyara botiran rigarshi da suka balle yana cewa "ok"sai da ya gama ya miqa
mata hannunsa har lokacin tana zaune kanta a qasa "oya get up"a hankali ta dora
hannunta saman nashi ya dagata,sai jirin nata ya kwasheta tuni ya riqeta don kada
ta sha qasa "fadeela I think you are not well"
"am well"
"A'ah,ki shirya gobe zan daukeki ta office in kaiki kiga likita"
"Amma....ai zan...."ya tsansa ya dora kan lips dinsa "shshshsh...kada kice
komai"shirun tayi ya leqa fuskarta "zaki rakani gun momi muyi sallama?"girgiza
kanta tayi "um um"yayi murmushi "shikenan to kwanta abinki"ya zaunar da ita gefan
gadon,system din ya fara kashe mata ya maida mata ita saman madubi,ya dawo inda
take yana kallonta ya kama hannunta ya sumbaci sama yana cewa "good night my dear
baby na,sweet dreams,I love you"a hankali ya bude bakinta tace "I love you too my
dear *haidar*"farinciki ya cikashi kamar ya taka rawa,tuni saboda kunya ta cusa
kanta qasan pillow tana murmushi har ya fice
Momin kawai ya tadda a parlour din yanzun ma ita da iftihal dake shimfide kan
cinyarta tana baccinta abunta,a yatsine momin ta kalleshi "sannunka kaji?" Murmushi
kawai yayi idanunsa na kan 'yar diyarshi,ya shafa kan iftihal din "ayi haquri momi
zan tafi sai da safe" "kada naga qafarka da safe a gidan nan" da sauri ya dawo da
baya ya taugunna gaban momin "yauwa momi na,Allah indai kika bani fadeelah ta ba
zaki kuma gani na da sassafe a gidan nan ba,saima kin aika a nemo miki ni" dariya
taso qwace mata amma sai ta kaba habarta yana cewa "o'o'o,sannu mara kunya,to anqi
din har sai ta yarda da kanta" ya kama qafar momin yace "wallahi momi fadeelah ta
haqura" ta dake dariyar dake cinta "kaga,mu bata gaya mana ba yallabai sai ka jira
har sai ta gaya mana da kanta"ya marairaice "momi kunya fa kinsan take ji,ba zata
iya gaya muku ba"momin ta tabe baki "ok,sai kai wato rasa kunga shine kazo kayi
rashe rashe a gabana kake gaya min ko,don Allah tashi ka tafi gidanka ni na gaji da
ganinka anan"
Kai yake gyadawa kamar qadangare "shikenan momi,shikenan sai da safe"ya miqe ya
fice cikin zuciyarsa yana fadin "zan shuka tsiya kawai,komai ta fanjama fanjan,su
momi basu yanda nake ji bane"uncle abba dake can tsaye yana kallonsu yqna shan
dariyarsa ba tare da sun sani ba ya qaraso "haba maimunatu,ayi haquri haka nan a
bashi matarsa,tunda sun sasanta kansu,ni kam na fara tausaya masa,kinsan ciwon da
namiji ma na da namiji ne"ya qarashe fada cikin zolaya,dariya uncle abban ya bata
sosai"shikenan tunda abun wariyar launin fata ce nima ai ciwon 'ya mace na 'ya mace
ne,sai na gyara diyata nima,idan yana so jibi ko gata sai a bashi ba don halinsa
ba"
Ya sunkuya yana qoqarin dauke mata iftihal daga kan cinyarta "mudai tunda za'a
bamun ai shikenan godiya muke,bari in dauke miki amaryar taki,kije ki huta kema"ta
saki murmushi tana cewa "godiya nake abba"ta miqe tabi bayansa tana barwa sumayya
da rabi'ah dake kitchen auna wanke kwanukan da aka bata don basa barin wanke wanke
ya kwana sallahun idan sun gama su kashe duk qwaya qwayai da kayan electronic na
parlour da kitchen din
Tunda ya zaunar da ita a gun ta bingire ta kwanta saboda kasala,juyi kawai take
tana tariyar abinda ya farun a wunin gau gana daya tsakaninsu,babuabunda take saki
sai murmushi,shi din ma koda ya fito daga wanka kasa hasala komai yayi,sai da ya
zauna gefan gado ya dauki wayarsa ya kirata,tana tsaka da juyin nata ne kiran ya
shigo mata,ta gyara kwanciyarta hadi da rungume pillow sannan ta amsa,sallama ta
masa da muryarta mai sanyi wadda ke saka susuta shi "fadeelah bazan iya bacci ba
sai naji muryarki"
"But...."sai kuma tayi shiru
"But what?,pls gaya min abu daya wanda zai sani samun nutsuwa idan nazo baccina"
numfashi ta ja sosai sannan tace"i love you for all that you are,all that you have
been,and all you're to be my haidar"kalaman sun tsaru sosai cikin kunne da
zuciyarsa,ta kashe masa jiki da zaqin kalamansa,idanunsa na a lumshe yace "are you
sure babe?" "Yes am sure,duk abinda na fada I mean it"dogon sumba ta bashi a wayar
sanna ta kashe tana murmushi qasa qasa,shi kuwa mutuwar zaune yayi gaba daya tsigar
jikinsa ta zuba..........
✍🏻 ✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻
  
[10/16, 2:16 PM] Salma:
*WA YASAN GOBE?....*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

👉🏼 *PART 3* 👈🏼
2⃣1⃣&2⃣1⃣
2⃣1⃣2⃣1⃣
Shi kuwa mutuwar zaune yayi gaba daya tsigar jikinsa ta zuba
⚜⚜⚜⚜⚜
Zaune take a nutse cikin office din,sanye take da shadda dinkin riga da zani rapper
marun,sosai shigar ta yi mata kyau matuqa ta kuma dace da fatarta,hakanan take
kullum ba dai tayi kwalliya a kushe ba,ta iya dressing sosai,hannunta dan
madaidaicin cup ne cike da coffee tana dan kurba kadan kadan don babu abinda ta iya
ci tunda gari ya waye,gaba daya hankalinta na gun aliyu tunaninsa take,amma idan ka
kalleta a zahiri qata news paper dake gefan hannunta ta zubawa ido tamkar mai
nazarin wani abu a cikinta
Yafi minti goma a atsaye bakin qofa,sam baya gajiya da kallonta,baiqi su dawwama a
haka ba,tsarin shigar tata yayi masifar tafiya da shi tayi wani das tamkar fure,sai
kuma aka taki sa'a shi din ma marun din shaddar ce a jikinsa
Har ya iso bata ankara ba,a hankali yasa hannu ya zare cup din coffeen dake
tsakiyar tafukan hannayenta "irin wannan zurfi a tunani bai dace da kyakkyawa ba"
ya fadi yana maida cup din gefe,yaja kujerar dake opposite dinta ya zauna yana cewa
"nasan dai ji kike tunani ko....to gani na iso ai sai abar hasashe a koma
zahiri"murmushi ta saki a kunyace tayi qasa da kanta,ya sake binta da mayun idanun
nan nasa,gani yake tamkar kullum wayewar garin Allah kyau ake dada mata,ya jawo
tattusan hannunta dake zube saman table din yana matsawa,ji tayi kamar wani
sinadari yake zubamata cikin jikinta,ta soma qoqarin zame hannunta tun kafin yayi
mata illa cikin kunya "no baby,your hand fits in mine like its made just for
me,kada ki cire"
Ta dan zame dag kan kujerar ta gaidashi,noqe kafada yayi "naqi,ni ban irin wannn
gaisuwar nake so ba,let me show you irin wadda nake so"kafin tace komai ya zagayoda
ita zuwa inda yake zaune yayi mata mazauni kan cinyarsa,qam ya matseta,sai da ya
yamutsata son ransa sannan yace "irin wannn gaisuwar nake so ko a ina muke
right?"gyada ka tayi cikin jin nauyinsa,ta bishi ne da haka amma itakam rashin
kunyar aliyyun tafi qarfinta "a'ah dear,ki daina min rowar sweet voice dinki,ki
dinga bude baki kina magana sannan ki dinga bude idanunki sosai kina
kallona,zuciyarmu ta riga ta zama daya....dubi"ya fadi yana juna mata dressing din
da suka yi "baki san me zansa ba nima bansan me zaki sa ba amma saboda zuciyarmu na
manne da juna mukayi shiga iri guda"
Murmushi ta saki tana kwantar da kanta a kafadarsa,"ok,I hope kin shirya,don daga
nan sai asibiti,gwara muje kiga doctor sa'adah"ya fadi yana sunkutarta kamar wata
bebin roba,wutsil wutsil ta soma yi da qafafunta "please my haidar,zan iya tafiya
kada ka fita da ni a haka"dariya taga ya saka,ta dan saci kallonsa don bata taba
ganin dariyar tasa haka ba,ya maimaita abinda tace cikin kwaikwayar muryarta sannan
ya direta "matsoraciya,dama tsokanarki nake"duk da haka bai qyaleta ba sai da ya
kamo hannuwanta,a haka suka isa bakin motar,ya bude mata ta shiga sannan shima ya
shiga
Ko a office sai da doctor sa'adah tayi masa wayo koreshi waje da qyar don ya hana
fadila sakat ,kunyar doctor din fadilan keji shikam ko a jikinshi,da zarar fadilan
ta bude baki zatayi magana sai yayi sauri ya rigata cewa "doctor rabu da ita,awo na
kawo miki ita,na jefa qwallo a raga" mamaki da kunya suka kama fadila haka aliyyun
yake?,tamkar ba wannan aliyyun nata ba,ita kanta doctor sa'adah din tayi mamakin
yadda ya sake yana ta raha har irin haka kamar ba aliyu salim maitama ba,mintina
talatin doctor sa'adah ta gama duk wani bincike da gwaje gwajenta,madaukakiyar
fara'a da farinciki da ta gani kan fuskar doctor din shi ya bata mamaki
"congratulations fadila,naji dadi da ya zamo nice ta farko da zan taya ki
murna,Allah ya albarkaceki da samun juna biyu"ta fadi tana sanya tafin hannunta
cikin na fadilan
Sak fadilan tayi tanajin kunnuwanta kamar basu ji mata dai dai ba,ciki gareta da
gaske?,cikin aliyyu a jikinta?,aliyyu masoyinta?, *alhamdulilahil lazi bini'imatihi
tatimus salihaat*,wannan baiwa da ni'ima ta Allah da me tayi kama?,Allah kenan mai
kyauta da qari,buwayi gagara misali,mai azurta bawa a duk sanda ya so,mai amsa
addu'ar bayinsa,yau ga aliyyun Allah ya bata kuma ya bata dan aliyyun cikin
cikinta,ya zabeta cikin matansa yace ita zata haifa,batasan lokacin da hawayen
farinciki suka balle mata ba,a hankali bakinta ya soma salati ga fiyayyen
halitta,sannan ta dora da godiya ga ubangiji, "na godewa Allah gwanin iyawa,doctor
pls bana son ki sanar da aliyu batun cikin nan yanzu,nasan bazai iya shiru ba sai
kowa ma ya ji,kuma....."
Dai dai nan aliyyu ya turo qofa ya shigo,da sauri ya qaraso a rude ganin hawaye kan
fuskar fadilan,dagota yayi ya rungume yana goge mat fuskan"me ya faru ?,doctor me
kika yiwa mata ta?"ya fadi cikin hade rai,dariya sa'adah tayi "farinciki ne yayiwa
matarka yawa,don ance lafiyarta qalau shine don shagwaba take kuka"ta miqa masa
takardar magunguna "wadan nan zata dinga sha,but gaba buqatar hutu da kulawa
sosai,idan an gama lallashin ku rufe min qofar office din sir,zani inyi round na
marasa lafiya,ta sanya lab coat ta fice tana musu dariya"
Ko cikin motar kanta na langabe ne jikin sit,gaba daya jikinta yayi sanyi,sai ta
ruda aliyyun gaba daya ya kasa driving din dole yayi parking din motar yana
tambayarta,murmushi ta saki"am fine my haidar" duk da haka sai da ya sanyata cikin
jikinsa sannan ya samu ya iya ci gaba da tuqin,ga zatonta zai maidata ne gurin aiki
amma sai taga yayi nassarawa da ita,cikin rashin fahimta take dubansa "nayi zaton
zaka maida ni ne office ko tunda ban tashi ba"ya girgiza kai "no fadeelah,yau
gidammu zamu koma"
da sauri ta dubeshi "gida haidar?,bada izinin su uncle abba ba?"
"Shshshshsh!" Yace "nafi kowa iko da ke fadeelah,na gaji da rashinki,na qosa kiyi
haquri kawai idan naje gidan ni zan sanar musu,zan fahimtar da su ba laifinki
bane,bare ma ba zasu ce komai ba I know"
Ta zumburo zata sake magana "tuni ya sanya bakinsa cikin nata ya hanata cewa
komai,saura kadan sitiyarin ya kubce masa Allah ya taqaita ya kamo shi
Da kanshi ya bude mata part din nata don babu key din a a lokacin a hannunta,sai
zumbure zumbure take ita a dole fushi takeyi da shi,shi kam dariyarsa ma yake
lokaci lokaci,bai damu ba tunda burinsa ya cika,fridge ya nufa ya ciro ruwa duk da
babu sanyi kasancewar wutar bangaren a kashe take,ya jawo gabanta ya durqusa,ya
jawo ledar magungunan ya ballo mata,ya bude gorar ruwan sannan ya kalleta "haa"
yace da ita,shiru ta masa sai da ya sake cewa "bude bakinki"nan ma tayi shiru,sai
ya dire ruwa da maganin kan center ya miqe yana shirin core rigarsa yana cewa
"tunda kin zama kurma inada muqullin bude bakinki" a razane ta dubeshi,bata san
lokacin da tace "me zaka yimin?"yadda ta razanar da kuma yanayin yadda tayi maganar
shi ya bashi dariya,ya tuntsure da dariyarsa yana maida rigarsa da ya soma cirewa
har fara qal din vest dinsa ta soma bayyana,ya koma gabanta ya tsugunna yana cewa
"ashe dai matsoraciya ce,baki shirya fadan ba amma kika takaloshi,oya bude
bakin"bata ko sake musawa ba ta bude ya sanya mata magun gunan sannan yasa maya
ruwan a baki har sai da ta hadiye
Ya miqe ya cire mata mayafin da dankwalinta,ya zare mat sarqa da dan kunneta duk
tana kallonsa,ya debe qafafunta ya maida saman kujera ya dora mata pillow sanann ya
harde hannayensa a qirjinsa yana duba agogon dake manne a bango "oya,maza kwanta
kiyi bacci ko na one hour ne don maganin yafi saurin bin jikinki,after one hour sai
ki tashi kiyi sallah ok?" Cikin shagwaba wadd ta ruda aliyun tace"amma dai kasan
ban kyauta ba ace daga zuwa gun aiki ace na dawo gida na ko?"sauje hannun nasa yayi
ya dawo gaban kujer ya tsugunna har yana jingina gwiwoyinsa jikin kujerar,ya koma
serious sosai,yasanya tafin hannunta cikin nasa,sosai ya sa qwayar idonsa atata
"fadeelah" kallon cikin idonsa tayi,yadda taga ya zama serious hakan yasa ta bawa
maganar tasa muhimmanci "duk duniya babu mai haqqi a kanki daya kaini,bana so ki
dinga sawa ranki damuwa kan binda yake mai sauqi ne,su momi sun ajjiyeki ne don ku
sasanta kanmu da kanmu ba tare da kowa ya shiga ciki ba,sannan ni na sake gane
kuskure na,to yadda suke so din duk ya faru,me kuma ya rage?uumm?,sai mu dawo gidan
mu fadeelah mu shimfida sabuwar rayuwar auratayya wadda zata kuma farantawa
iyayemmu rai,ina kuma fatan zan samu goyon baya daga gareki?"
Sosai take gyada kai "insha Allah mijina,na yi maka wannan alqawarin" ta dam zamo
daga saman kujerar ta durqusa itama a gabansa "ka yimin afuwa ranka ya baci,ya saki
qayataccen murmushi "ba komai baby na,bakya taba yin laifi a guna"ya sumbaceta
sanna ya maidata ya kwantar saman kujerar,"kiyi bacci sosai,banda cewa zaki tashi
kiyi aiki,gidanki babu dattin komai,don kullum sai na share miki shi"tana daga
kwancen ta qwalalo ido "shara?kuma da kanka?"murmushi ya kuma saki"kina mamaki
ne?,kinfi gaban haka,mene ke baki bani ba a rayuwarki fadeelah?"itama murmushin
tayi "haqqina ne ai In maka har fiye da hakan" "jiniina kai yayi cikin zuciyarsa
yana godewa Allah,babu shakka yayi gamo da katar da mace ta gari,wanda samuntabke
matuqar wuya a wagga zamani "ina sonki my baby fadeelah har bansan adadi ba,ina
alfahari dake,ina alfahari da kasancewarki cikin rayuwata"ta rufe fuskarta da tafin
hannunta "ina sonka haidar dear,nima kuma ina alfahari da kasancewar ka miji a
gareni har abada"wani dadi yaji ya kama shi,ya sake sumbatar bayan hannun nata yave
"na gidewa Allah fadeelah,sai na dawo,zansa nasiru ya kawo miki motarki ,sannan zan
daukar miki excuse gurin aiki su baki hutu na sati"bata ce komai ba don bata son ta
kasance mai yawan musu da shi,bare itama zata so hakan,don tana buqatqr lokaci da
zatayi wasu 'yan gyare gyare,sabida haka kai kawai ta gyada masa tana satar
kallonsa ta tsakanin yatsunta har ya fice,wani annushuwa da farinciki da kwanciyar
hankali mara misali taji yana ratsata
Ta janyo wayarta ta nemo number din farida,bugu daya ta dauka tamkar dama tana
jiranta ne,cikin ihu take cewa "yeyyyyyy sister yaushe kuka dawo haka babu
labari?"cikin murmushi fadeelah ke cewa "wayyo Allah zaki kashemin dodon kunne
mana,cikin satin nan ne,kiraki nayi dama nace miki ki turo min mai gyaran jikin nan
don Allah"wani ihu faridan ta sake saki cikin dariya "kai mutuniyata,wallahi da
labari,tafiya tayi kyau mune winners ko?" "Kai....faridaaaa....sai yaushe zaki
girma ne don Allah?" Tayi qasa da murya "kai sister,rowar story zaki mun kenan don
Allah?"dariya ta bawa fadilan don tasan farida akwai son jin tsurku "hab abokin
kuka ai ba'a boye masa mutuwa,zaki sha labari har sai kin gaji kin toshe
kunnuwanki" "a'ah nasan halinki fa sister,zaki dai bani wanda kika ga dama,yanzu
zan mata waya na gaya mata"tayi dariya "yauwa ko da yamma ne sai tazo,sau nake ta
fara yimin yau don gaskiya nag ta iya" "kai sister sosai ma,ko sau daya fa ta miki
sai kinga kin canza gaba daya,akinta da kyau sai tsada,bayan gyaran jiki har kitso
da qunshi ma ta iya sosai"
"to yayi,ina humairata,Allah sarki aishana,nayi missing dinta a lot"
"Yanzu babanta ya fita da ita sitting room yayi baqi"hamma ta kubcewa fadilan har
sai da faridan taji "idan sun shigo kice ina gaidasu ita da abban nata,ni zan
kwanta"
Dariya farida ta saka "tabdi lallai sister,kai saidai na zo kawai"
Katse wayar fadila tayi taba murmushi don tasan halin farida bata qi su kwana suna
abu guda ba.........
*PART 3*
2⃣1⃣ 2⃣1⃣
Doctor sa'adah ta kammala rubuce rubucenta,ta dago ta kalli aliyyu "masu qaramin
ciki kamar hakan suna buqatar daga qafa adinga sassauta mata gaskiya"
Zaro ido yayi kamar yaro"what?!,su waye Duke da ciki?"cikin mamaki ta sake dubanshi
"oh,baka sani ba.....anyway kaji a bakinta,ga magunguna nan ,ba za'a yi birede a
gaba na ba,idan kun tafi nurse zata zo ta kulle qofa"tayi haka ne don tasan za'ayi
budurin yadda tasan alin da son yara na masifa
A hankali ya duqa gabanta "da gaskene Fadeelah kina da ciki?"cikin jin kunya ta
gyada kai,sai ya hade fuska tsam,ciki tsawa tace"don me yasa zaki boyemin kyautar
da Allah yayi min?shin ban can can ci in sani bane?"
A Dan tsorace ta kalleshi,sai Kuma taga ya rungumeta "am sorry dear,banji dadi bane
da kika boyemin,kunya Daren jita na cutar da ke,da wa ni Abu ya faru daku keda baby
na bazan yafewa kaina ba Fadeelah,bazan gaji da roqamiki rahamar Allah ba,bazan
gaji da roqarmiki albarkar ubangiji ba,ke din wa ni alkhairi ce a tartare da
ni ,bani d halin da zan miki godiya don tayi kadan,bansan da me zan saka miki da
shi ba fadeelah,Abu day dai da na sani kin zama mahadin rayuwata Fadeelah,na
tabbatar idan babu ke rayuwata bata da amfani"
Ga mamakinta sai taji ya fashe da kuka sosai,tabbas rabo ajali,rabo ne mai zafi
ashe tsakaninsa da fadilan,hawayene sosai ke sauka bisa fuskarsa,hakan ya sake
nunawa fadila yadda Aliyyu ke tsananin son yara,ita din ke share masa hawaye tana
lallashinsa
"Allah shi ya cancanci ka godewa bani ba,ni da kai duka bayinsa ne yadda yaso haka
zamu gani"
Baiyi qasa agwiwa ba Kuwa ya kama"alhamdulillah"ba qaqqautawa
"Allah ka yimin dukkan wata ni'ima a rayuwata,Allah ka bani ikon saka maka ta
hanyar yi maka da'a da biyayya da bin dukkan wani umarni naka"
Addu'ar d aliyyun y dinga yi kenan gwiwoyinsa kafe a qasa hannayensa a sama,ba fita
daga asibitin ba sai da ya yiwa doctor sa'adah albishir din Kujerar umrah,fadilan
ma hañata tafiya yayi ya kafe sai dai ya dauketa,sai da tasa masa kukan shagwaba
sannan ya bari,roqarsa ta dinga yi cikin mota don Allah kada ya fadawa kowa
Girgiza kai yayi"mummunan labari ake boyewa,ban miki alqawari ba ruhina,na dai
yarda bazan fada ba amma Duk wanda ya tambayeni zan fada masa"ba yadda ta ita haka
ta qyaleshi,motsi kadan yace"sannu,yaya?"
Tun tana amsawa har ya soma bata dariya,
Marairaice masa tayi kan sai ya kaita gida taga umminta,dole ya kaita ganin tanason
sa masa kukan nan nata da ba yaso,tayi Sa'a kuwa ta tadda Farida tazo,wayyo dadi
gun Fadila ba'a magana,humaira nata rarrafe abunta,yarinyar ta sake kyau kamanninta
da fadilan ya sake fitowa,sai ta sake shiga zuciyarta,Fadila na shirin daukarta
ummi tace"Allah yasa ta yarda da ke 'yar nema,wai nan qiwa fa take"sai kuwa ta ba
su mamaki don luf tayi abunta jikin Fadilan
Can jimawa saiga 'yan biyun Anty hafiza,tunda cikinta ya tsufa ya Ahmad ke
tarkatosu gun ummin lokaci bayan lokàci musamman weekend dob mamansu ta huta, ummi
ce ta kalleshi"gayamin kwana nawa za suyi,don bazasu zo tafiya amira rigima ba"yayi
murmushi"anjima ma zan dau ke su,idan natashi daga kasuwa,naji tana gobe can
gidansu za'a kaisu za suyi taro"
Sai kuwa hussaina tace"abba da hassana kawai zaka tafi ko?ni a gun ummi sanya
kwana"ta fadi taba fadawa saman cinyar ummin"kiji mai ka irin wayo wato don kin
fita baki ko"inji Muhammad daya dungure mata kai din shi hasana ce mutuniyarsa
Ummice ta bige masa hannu"ina ruwanka ,baban kawai"ya qyalqyale d dariya ya dauke
hassanar sukayi ficewarsu yana yiwa hussainar gwalo,bata damu ba don ta saba da
hakan ta fada cinyar ummin tayi kwanciyarta
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 3*
2⃣2⃣ 2⃣2⃣
Sosai Fadila taji dadin yadda ummin nata keta nan nan d ita cikin kulawa,saidai
yadda ummin nata ke binta da ido Duk Indi tayi ke sata jin kunya da rashin
sakewa,kiranta ummin tayi lokacin da su ke kitchen su na hada abincin rana ita da
farida,gefenta ta nuna mata "zauna a nan bar faridan ta qarasa aikin tunda ita
lafiyayyiya ce"kunyar ta sake kamata ,zaman tayi don dama aliyyu ya ja mata kunne
da kanta yake tace zataita aiki
Faridan ta fito daga kitchen din tana kallonsu "ya haka sister ina can ina jira?"
"Eh ni nace ta zauna ,jeki qarasa tunda kin fita lafiya"tsalle faridan ta daka
kamar yarinya"wallahi ummi sai da nace sister kamar mai ciki ta wani harareni ,ashe
na canko gaskiyar lamari"
"Tashi dalla Mara kunya ki bawa mutane guri fitsararriya"inji fadilah dake hararar
farida,bata damu ba taci gaba da murnarta
Gab da magariba aliyyu ya iso,ya shigo suka Gaisa da ummi wani kunyarta yakeji
sosai,yanata satar Kallon Fadila yana mata alama ta taso su tafi amma tayi
qirmisisi kamar bata gane me yake nufi ba,har sai da ya miqe yana yiwa ummin
sallama ya fice,ummin ta kalleta "zaman me kikeyi haka,ki tashi mana Ku tafi"
"Haba ummi banga abba ba fa,Kuma ga farida nan ita da ta fini zuwa ma bata tafi ba
sai ni"ta fada kamar zata saka kuka
"Nima Motata na gun gyara ne da tuni na wuce,Mubarak ne Zai biyo must tafi"tana
qunci tana komai ta fita
Aliyyu sarkin yara,yana jingine jikin motarshi shi da 'yan biyu sunata hirarsu
abinsu,shikam dama idan ka ganshi tare da yarda zakayi mamaki,sosai yake sakarmusu
hadi da biyewa shirmensu,tahowarta ce ta dauke masa hankali cake daya kan 'yana
biyun,tunda ta taho tunda ya lura ranta kamar a bace
"Allah ya taimakeki,wa ya tabamin ke?"y fada yana leqa fuskarta
"Bayan Kaine,ka barni kawai na kwana amma don Allah, yaushe rabona da gida,kunsan
five months fa"
Ya harde hannunsa a Qirji ya gyara tsaiwarsa"ba Matsala mana don dai kwana,amma ina
fatan kin tanadar mana dakin da zamu kwana diñ ko?"
Murnar da take ta koma ciki,ta zare ido"wai ni da kai Zamu kwana a Daki gudan,a
gaban ummin da abba?"
Baice komai ba ya bude mata gaban Motar sannan tace"kinga to ashe babu batun kwana
my queen, wlh bazàñ biya ba Fadeelah, daga yau fa sai nayi kwana hudu kafin
kwananki ya zagayo,pls ki tausayamin mana Fadeelah baby"
Sai ya kashe mata baki,tabbas aliyyu na qaunarta,bai kamata ta zalunceshi ba,saboda
haka babu musu ta shige,cikin jin dadin rashin musu irin nata ya rufe mata qofa,two
thousand ya ba wa su hassaña,da guduvsuka shige parlour suna tsalle su na ce
wa"uncle ne ya bamu naira biyarr"don basu San kan kudi ba
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin lkc qalilan Fadila ta fuskanci waye ainihin aliyu,very intelligent simple
peace and humble man,mutum ne mai kyakkyawar zuciya mai cike da alkhairi,maye ne
Kuma gwanin Soyayya,dau tafi idan ya rudata da salon soyayyarshi sai ta rasa a
wacce duniya take?,shin duk duniya ma akwai macen da ta ka ita sa'ar miji?
Soyayya yake gwada mata ba ta wasa ba,wadd ita da kañta wani lkc take roqonsa ya
rage nuna mata haka
Abinda ke tunzura Zuciya Salima da salima Kenan,sau tari yakanyi wasu abubuwan da
gayya wai ko zasu dauki darasi su gyara tsarin ràyuwàrsu,amma a'a maimakon suyi
Koyi da ita sai su sake fandarewa,maganganu kala kala marasa kan gado
"Matsafan chaina dai aka bi,idan baka ga haka ai kafin ku tafi ba haka yake miki
ba"dariyarta taci sosai,bata kulasu ba kamar yadda ta saba don aji tàyi musu gudà
sakasu,Aliyyu ne da yake jinsu yace"Duk wadda zàtayi bin màlamai irin nata yaso ni
zañ dinga biyañ kudin,indai irin nata ne"
Iya bakin qoqarinsa yanayi don ya saitasu a hanya amma inaaàa......kamar sake
rubuta su akeyi,ya gama haqaqewa ransa tabas babu Wanda ya isa ya shiryar da
batacce sai Allah
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 3*
2⃣3⃣ 2⃣3⃣
Daga hutun sati sai aliyyu ya birkice Fadila bata komawa aiki,bata iya sa'insa da
shi ba sai kunya da ta zauna tana rusa masa babu qaqqautawa,shu kuwa Abu guda dake
daga masa hankali kenan,zama yayi dirshan yana clarifying mata dalilansa
"Baby bana so ,duk sanda zaki fita baby na akwai mai kalle min ke,duk sanda na tuna
hakan sai naji zuciyata na quna,pls my unique ko don babymmu da kike dau ke da shi
ki haqura,ki gayamin nawa kike dauka a Wata nayi alqawarin zan miki multiplying
nasa"
Ta share qwallar dake shatata Duk da ba daina zubar tayi ba,"banaso ni aikina nake
so,ka ganshi fita ko ina sai tare da kai,matanka su da yake kana sonsu fiye da ni
ai gashinan babu inda baka barinsu suje,sai ni da nake fita aiki "ta fadi cikin
fushi tana zumburo baki,Dariya ta bashi sosai,don ya lura gaba daya cikin nata yasa
mata saurin fishi hasala da saurin kuka,kan cinyarsa ya dorata yana gorge mata
Hawaye
"Gaba maman biyu,kin manta ke din ta musammance?kin manta aliiyunki bashi da kamar
yake?ko kuwa kin manta cewa kace mace ta farko da aliyyun ya mallaka mata komai
nasa kamàr yadda kika kasançe mace ta farko da ta mallaka wa haidar din komai
nata?,hakanan ta farko da ya fara so da kangin kansa?"
"Kiyimin rai ki raini yarona ba tare da yasha wuya ba,dama tun farko aikinki din
nan ba Sonshi nake ba,idan ba zaki manta ba ranàr farko da zaki fara zuwa irin
sharudan da na dinga gindaya miki,wlh a lokàciñ zuciyata tàfasa kawai take,bans an
sink I da na boye ne yasa ni jin haka ba,banda Ahmad ne ya same ni kai tsaye da
maganar da ba zakiyi shi ba,na roqeki kiyimin wan an alfarmar ki haqura"ya Jade
hannunsa da nata yana Kallon qwayar idanunta,sai taji bazata ita wofantar da
alfarmar da aliyyun ya roqeta ba,saboda haka a take ta rubuta letter din barin
aikin ta damqa mishi,
Aliyyu ya cancanci komai a gunta,tsananin kulawa da qaunar d yake nuna mata kadai
ta isheta,abinda kullum ke dawwamar da ruhinta cikin farinciki da begensa,godiya ya
dinga mata har sai da ta rufe masa baki
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Duk cikinsu babu wadda ta ankara da cikin d fadilan ke duke da shi,ba wa ni shiga
sabgarsu take ba bare su ganta,don tuni aliyyu yayi mata maganinsu,iskancinsu na da
suka so su dawo da shi,su shigo musu ranar girkinta a cinye abiñci da su,sannan
kuma suqi tafiya suyi zamansu,bayan ita ranar nasu girkin da ta shigo ta masa barka
d dawowa minti goma ta bar gurin ta koma bangarenta,duk nacinsa bata zama don
bazata yi abinda idan ita akaiwa ba zata so ba
To su kam basu sàn hakanba,don haka da zarar sun wuce minti goman zai janyota
jikinsa ya fara yamutsata,to yanzun nan zaka ga kowàcce ta ja qafafunta ta
wuce,dariya yakeyi abinsa yace tunda ke kin kasa maganinsu abun ni gashi nayi miki
ko?"ita din ma wani lkc dariyar ke ka ma ta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Wata hudu cikin amma idan ka ganshi sai Kayi tsammani yayi wata shida,sosai abun
ke basu mamaki su duka,amma babu abinda fadilan ta fasa,mita da qorafi kam tana
shansa,don wa su lokutan ma idan ranar girkinta ne idan zai fita gidan anty hauwa
yake kaita tace"ga gajiya nan ya kawo kada a barta tayi koma,idan ya dawo sai ya
biyo ya dauketa,da ya ajjiyetan sai fa ta faki idonsa ta masa girki ko da mai
sauqine don tace ita kam ladan bai isheta ba
Aliyyu tace"shi kam indai lada ne ya isa haka,don kuwa ko iya cikin jikinta ya
isheshi,aljanna kuwa indai shi zai dage mata qafa ta shigà to tuntuni tasa a rage
take"dariya taci ranar cikin alfahari da jin dadin kalaman yabonsa a gareta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Ya kaita gidàn Anty hauwa yadda ya saba ita Kuma tace kausar tazo ta rakata gidansu
nuratu ayi mata Jan lalle,anty hauwa tace"sannu Fadila da qoqari,ko wuya zaman
lallen baya miki?"
Tayi 'yar dariya "wlh Anty bana jin dadin batun hannuna ne haka,Kuma ma ya aliyyu
naso"
"A'h tunda ya aliyyu na so sai a bada himma,don na fuskanci kin gama shagwabashi
gaba daya,mu nan duka yanzun ganin must yake bamu iya zaman aure ba"ta qarashe
maganar cikin tsokana,dariya ta kama Fadila lkcn da take sanya hijabinta "wlh Anty
ba haka bane"
"Allah kin gama shagwabashi,idan yaso gidan nan ya dinga min fi'ili kenan"ta sake
tuntsirewà da dariya lkcn bilkisu ta shigo tace"Anty kamalu driver yace ya fito da
Motar mu fito,tare suka tafi akabar antin a gida
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
2⃣4⃣ 2⃣4⃣
Har aliyyu yazo daukarta basu dawo ba,nan ya dinga saukewa Anty hauwa kwandon mita
ya dinga yi kamar zai ari baki,safe baki kawai Antin tayi tana kallonsa
"To ni meye nawa aliyyu,kwalliya take son yiwa mijinta sai na hana?"
Dariya taso ka nata ganin yadda yaketa safa da marwa kamar Wanda kace an saceta,ga
wayarta Kuma na kan Kujerar falo ta manta ta
Minti ashirin Motar su ta shigo,da suri ya qrasa ya bude mata qofar Gaisa miqa
mata hannunsa ta Dora nata a kai,Jan lallen kam yayi dau ya haska idanunsa,Zara
zaran yatsunta suka sake yin kyau,diba yasa ido ya sakar mata hararar wasa,ta saki
murmushi idanunta cikin nashi tana langabar da kai cike da kissa
"Zaki sani tunda kika ke kikayi zaman lalle kika wahalrmin da baby,punishment dinki
na yau babu ke ba tafiya da qafafunki"kafin tace komai har ya sunkuceta ita da
cikin jikin nata ba tare da jin nauyinsu ba,yasa kunya ce da ita bata son ya dinga
daukarta haka cikin mutañe
Yana tsaida motar ta farka idanunta fes bisa fuskarshi,sukayiwa Kuma murmushi yadda
suka saba a duk yayin da suka kalli juna,ya fice ya zagayo ya bude qofar hadi da
daukota cak
"Wayyo my haidar ,don Allah ka saukeni"ta fadi tana wutsil wutsil da qafafunta gami
da dan dukan qirjinsa kadan kadan
"Kun manta punishment dinki kenan?"
baiko kulata ba ya barta nan a tsayen ya nufi bangarensa don baisan me takeso ya
gaya mata ba,qasa qasa Fadila ke cewa"bai kamata ba dear fa,ko nice ba zanji dadi
ba"
Baisan lkcn da ya tuntsure da dariya ba"mene bai kamata ba?,cikin naji?,ai bani na
baki ba Allah ne ya baki,idan da sun so wataqil da tuni Allah yasa sun Samu tun
kafin ke,ko Kuma sahun nata zaki ni?"ya qarashe cikin sigar tsokana
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Dirshan take zaune saman cinyarsa,ayabarta wadda ita ce abincin yake bare mata,sai
zuba shagwabarta wadda take burgeshi take,qaramin wandone a jikinta sai Riga ta
vest wadda ta fito d turtsetsen cikinta,Kanta ya sha gyara Wanda Aliyyu ne ya zauna
ya gyare abunshi tsaf ya mata parking sonsa
Tuni ta saki handle din ta juya ta five ba tare da tace koma ba,kuka sosai ta rushe
da shi,matsananciyar qiyayyar cikin da uwarsa suka lullubeta,wani tsàutsayi ne
tuntuni ya hanata sakin jiki ta cika gidan aliyyu da 'ya'ya fiye da kowcce mace da
da zaya ajjiye?,take ta ciwa kanta alwashin ko ta halin qaqa ba zata taba lamincewa
cikin nan ya taka doron qasa ba,domin tana ganin ita tàfi kowacce mace cancanta ta
sake haifawa aliyyu yara ba Wata càn ba,nan shaidan da Zuciya suka ci gaba da
tunzurata gamida shirya màta sharri kala kala
*part 3*
2⃣5⃣ 2⃣5⃣
Doguwar Riga ce jikinta kamar yadda suka zamo sune shigarta na yau da kullum,sabida
cikinta bai bari ta sake cikin ko wani irin kaya idan ba su ba,ita kanta girman
cikin na bata mamaki,wayarta ce a hannunta tana tsarawq aliyyu tex na an wuni lpy
kamar yadda yake al'adatarta kullum idan ya fita babu fashi koda sunyi Waya koda
Kuma ba ranar girkinta bane
Cike da mamaki ta dagi tana masa sallamar Salima wadda ta shi go hannunta dauke da
wa ni madaidaicin food flask fuskarta qunshe da murmushi,Fadila ta boye mmakin nata
ta Hawa Salima tayi gurin zàma,ta sauna din kuwa idonta na akan fadilan
"Sannu uwar hudu"ta fadi cikin salon son nuna tsokana ,sai itama tayi qoqarin dora
murmushin kan fuskarta
"Yauwa sannu an wuni lpy?"
"Lpy qalau"ta fada tana tunda flask din gaba fadilah
"Wannan dama na kawo miki,nasa masu ciki akwaiku da kwadayi,Duk da ba'a gaya mana
qaruwr da aka samu ba,ai dan aliyyu namu ne mu duka"ta fada kai ka rantse har
zuciyarta,murmushin itama ta sake yi,t janyo flask din tana budewa
Fasten dankali ne Wanda ya sha danyen kifi irin marar qayarnan,a zahiri abincin
yayi don qamshin curry kawai yake zubawa,kana Kallon abincin kai kasan ba Salima ce
tayishi ba don ba zata iya din ba
Amma maimakon ya burge ta sai ma tashin Zuciya da haifar mata,don ita yanzu a
duniya babu abinda yake burgeta take biya ci irin ayaba ,komai dadi ko haduwar
abinci,saidai ko lemon zobo,koda ta kwata cin ma amai ne ke biyo baka
Ta rufe da sauri tana mata godiya,maimakon taga salimar ta tafi sai taga tana gyara
zama harda qoqarin zuba mata
"Gara kici tun da duminsa,nasan hàlin masu ciki yanzu yana kaiwa anjima zai iya
fita daga ranki",da sauri fadilan ta dakatar da ita"kada ki zubamin yanzu don
banajin yunwa"
Sororo saliman tayi cikin rashin jin dadi har hakan ya bayyana akan fuskarta,tilas
ta haqura ta rufe ba don ta so hakan ba,saidai don bata so ta fiya matsantawa har
fadilan ta dago wani abu,
Haka ta fice tana jaddadawa mata taci fa,sanda wai sai tana ci tana qoshi,hakanan
fadila taji ko bayarwa bata so tayi,saboda haka ta samu baqar leda ta kwafe a ciki
ta cilla cikin dustbin
kwana daya biyu salima taji shiru,ba qaramin tashi hankalinta yayi ba,Duk wani
shishshigewa da kulawa tayi wa Fadila shi,duk cikin qoqarinta na ganin ta samu
yarda gurinta,babu abinda bata dafa ba na kwadayi ta kai mata ba,sai dai
kash....abinda bata sani ba babu abinda cikin fadilan ya sani banda ayaba
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Dukkansu sun shirya don zuwa gidañ Momi karbar lefen sumayya da rabi'ah Wanda za'a
kawo ranar,mai gidan ne da kanshi zaya kaisu cikin motarshi sabuwa dal da duka
dauka shekaran jiya ta iso,yayi haka ne a fakaice don fadila wadda ke sanye cikin
doguwar riga ta atamfa exclusive mai adon orange da army green, Duk da turtsetsen
cikinta hakan bai hanata yin adonta ba,Kuma tayi kyau abinta,ta fita daban a
cikinsu tamkar zahra cikin taurari,hakan ne ya sanya aliyyu ya kasa yiwa idonsa
shamaki daga kanta,Duk inda ta motsa idanunsa na biye da ita
Baisan me yake sàurin daya fushi ba,kwanakin gaba daya a fusace take,Abu dan
qanqani sai ta hau masifa ko tasa kuka,har doctor ya tambaya tace masa kada ya Samu
wa su matañ idan su na da ciki hakan na faruwa da su,musamman idan yaw soma tsufa
suka fara gajiya da shi,to ko a yanzuñ ma ya lura kamar 'yan rigimàr na kusa,don ko
su Samira da bata kulawa a irin wannan mood din tana jin dai dai take da duk wadda
ta tabata a cikinsu
hannunta harde saman cikinta,tayi kicin kicin da fuska,hada ido sukayi ,ta same
qwayar idonta ta wani dauke kanta tamkar bata ganshi ba,dan qaramin murmushin nan
nasa ya saki,wani lkçn salon shan qamshinta da miskilancin nan nata na burgeshi,ta
iya shariya da dake kai da gangan
Ya dubi salima wadda ita ke dà girki,ba yadda ya iya a zahiri zaifi son ace Fadilar
ce kuwa da shi,ya danna madanni ya bude gidan gaban da a dazu yake a rufe yace da
Saliman"shigo nan"
sai ta tsinci kanta da jiñ wani bacin rai,suka Kuma hada ido,batasan sanda ta danna
masa harara ba gami dà Jan dan qaramin tsaki a ciki,ta shige sit din can baya na
qarshe tana kumburi
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 3*
2⃣6⃣ 2⃣6⃣
Jinta take kamar ta fashe,ita kanta tana mamakin yadda yake saurin fusata a
yanzu,Duk da ta sani akwai tsananin kishin aliyyu dake dawainiya da ita,tabbas ba
kuwa ce maca ce ce zata San Wayne ainihin aliyyun ba ta kada kishinsa,musamman ma
ita da kunsan tafi kuwa saninsa zahiri da badininsa
Salima nata rawar kai ta shige gaban,Aliyyu ya tada Motar yana qoqarin gyara
madubin motar ta yadda zai samu sukunin gano fuskarta sai dai sam taqi yarda da
hakan don tuni ta kautar da fuskarta,dole ya haqura ya soma tuqin hankalinda na
rabe gida biyu
Duk yadda salima yaso ta janye hankalinsa suyi hira mai tsawo da dadi ko don ta
cusa musu haushi abun ya faskara,dole daga qarshe itama ta haqura ta ja bakinta
tayi shiru
Ko da suka shi go harabar gidan tamkar dama Allah Allah take su iso tuni ta rigasu
ficewa tamkar bata jin nauyin jikinta,ya biya da ido don ba haka yaso ba
Yaso ne ya datseta a cikin Motar ya mannata da jikinsa ya dan rage mata temper,don
a matakin da take ciki tana buqàtar wannan,salima dake lure da shi takaici ya
cikata,ta sake qullatar Fadila,ta Kuma sake lasar takobin hana abun dake cikinta
tayuwa kota halin qaqa
Ya dauke idanunsa lokacin da ta bace wa gàninsa,bai bai ta kan yadda suke kàllonsa
kamar zasu cinyeshi danye ba ya jaw wayarsa dake gefensa ya latsa number din Anty
hauwa ya kira,bugu uku ta daga
"Hello mummyn kausar,ga ajiyata nan as usual, pls abata kulawa ta musamman Anty
na"dariya ta saka
"Ho,aliyyyuuuu.......to naji,mene tukuicina?"
"IPhone 7 da kike son siya ki bar kudinki ni Zan Waya miki"ta sake dariya"lallai
Ashe abun na yine,to ba Matsala,kada ka damu dan qanina"
"Thanks Anty",ya fadi yana kashe wayar
"Amma fisabilillahi tuni yaushe bace maka ina son iPhone 7 din nañ ,kowa cikin
qawayena ita suke riqewa ammavkaqi siya mini,sai ganshi rana tsaka kace zata siyawa
Waya",Kallon da yayi mata ya sanyata yin dañasañin yin furucin,tuni kafin yace wani
Abu ta balle murfin Motar ta fice tana qunquni cikin ranta Wanda ta bata isa ta
yishi a fili ba,don ba qaramin wuya ta ci ba lokaciñ da ya amshe mata key din mota
da wayarta bakamin ya dawo matà da su
Ya maida idonsa kan salima,tayi qoqarin hadiye bacin ranta don son cimma qudirinta
kan fadila cikin ruwan sanyi ba tare da an gano komai ba,ta bude motar itama ta
fice ranta na mata wata iriyar suya,tanajin zata iya koda kawar da fadilah ne don
ta shigar mata hanci da qudundune da yawa,tasa ta rasa fili da gurbin da ada take
jin tana da shi a zuçiyàrsa
Cikin falon ma kowa sannu yake mata,ciki wata bakwai amma sai ka dauka da ka bar
gun za'a bika ace ta haihu,haushi,takaici,kishi,qyashi da hassada ta cika
zuciyoyinsu,Samira da bata iya shiru ba tace"mu sai a tsine mana albarka ai tunda
bamu iya daukan ciki ba"ciki ciki tayi maganar amma wani abun ya dan fito,madina
tayi yunqurin magana Momi tayi mata inkiya da tayi shiru kada tabi ta kanta,sama
dakinsu sumayya ta haye abinta tayi kwanciyarta Anty hauwa ta cika mata plate da
ayaba ta bawa bilkisu ta miqa mata,Momi kuwa tayi ruwa tayi tsaki hawa,hana kuwa
hawa,fada ma ta dinga don me yasa bà'a barta ta zauna a gida ba tana fama da kanta
haka,batasan ita ta rage lallai sai ta so ba
Baccin kuwa take sonyi,don matuqar ba ranar girkinta bace bata ita wani baccin
arziqi,ta riga ta saba bacci jikinsa,yana làllabata kamar qwai harda tausa yake
Gara mata,baya runtsawa har sai ta rigashi yin baccin
Kira ya shi go wayàrta tana kwance lamp da tsammanin zuwan bacci,ta duba sai taga
sunan *darling blood* sunan da ta sama number dinsa kenan,sosai take da muradin jin
muryarsa sai dai tana sane tayi banza da wayarta,sau biyu tana rurinta tana katsewa
sai a Kira na uku ta sdaga,ta kara a kunnenta ba tare da tace koma ba,ajiyar zuçiya
ya soma saki wadda ta ratsa Fadila har ta tayar mata da tsigar jiki
"Babyyyy..."ya kirata Murya qasa qasa cikin Jan sunan,itama ajiyar zuciyar ta soma
saki"I missed you badly"abinda ta iya fadi kenan cikin narkakkiyar murya,ya sani
sarai akwai kewarsa dake damunta,kwana hudu ba tare da juñañsu ba abune ba mai
sàuqi qwarai da gàske,sai tausayintà da sonta ya sake kamashi,iya kawaici tana da
shi,gashi nan da kwana biyu zasu wuce umara shi da salima da Samira harda doctor
sa'adah wadda ya mata alqawari
"I know baby na,saidai hankalina na tashi idan na ganki cikin rashin walwala,please
smile my dearest wife,ko da bana kuwa nasan zànji a jikina"
Bata San lkcn da murmushin ya subuce mata din ba,musayar kalaman soyayya suka dinga
yi masu tsuma zukatan ma'aurata,aliyyu yaqi barinta har sai da yaji shiru alamun
baccin ya dauketa
*Mrs Muhammad ce 👑*
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
2⃣7⃣ 2⃣7⃣
Kai kawo take a bangaren nata don tuni aliyyu ya sawwaqe mata zuwa nasa bangaren
anan bangaren nata yake yada zango har ya kammala yi mata kwanakinta,yayi hakan ne
don hanata yin aiki Wanda ta saba da shi Duk ran girkinta sai ta qalqale bangaren
nasa da su suke barinshi babu kintsi
Amma Duk da hakan bata fasa Duk wa ni shirye shirye na karbar mai gidan nata duk
ranar girkinta,yayi mitar yayi fushin har ya gaji,ta Riga da ta saba bazata iya
zaman ba,bata jin nauyin da tayi,uban cikinta bai damunta Kuma bai hanata duk wani
abu d ya kamata ba,sosai aliyyu ke yabawa jàrumta da juriyarta
kamar yanzun ma ta kammala komai,sanye take cikin wata gown mai azabar
kyau,budaddiya ce sosai daga qugu zuwa qasa,hakan yasa bata takurawa turtsetsen
cikinta ba sai damar fitowa ma da ta bashi,yayi das a jikinta,qaramin hannu ne da
rigar,ta tattara gashinta a tsakiyar kanta ta daureshi da ribbon Kalmar
rigar,fuskarta tayi fayau tayi kyau cikin simple makeup, sai qamshin nan nata take
zubawa,
Ta jita da niyyar shiga kitchen don dauko banana taji sàllamarshi yavshigo parlour
din nata hancinsa na sheqar daddadan qamshinta,da sauri suka nufi Kuma kuwa na
qoqarin tar bar dan uwansa,shi ya soma nasarar cimmata ya rungumeta ta bata yana
sansanar wuyanta cike da farinciki
Fuskarta qunshe da murmushi tace"Baka da dawowa gida mijina"
"Yauwa matata abar alfaharina"ya mayor mata cikin salon qauna da kulawa,sunfi kusan
mint I biyar a haka sannan ta juyo da niyyar amsar jakarsa su qarasa daki,zullewa
yayi yana noqe kafada"naqi wayo nan naki,a waysnce fa kike Karya min doka daya
bayan daya,bayan na hanaki dawainiya da ni"
Murmushi ta saki,ya Dora lebensa a goshinta ya sumbaceta
Qoqarin ta rage masa kayan jikinsa take don ya samu yashiga wanka Sam ya hanata ta
gajiyar kama hannuwanta ya zaunar da ita gefen gado,tana kallonsa har ya gama ya
daura towel ya shige wankañ,tuni ya tadda ta ta fiddo masa da kayan da zai sa ta
feshe masa su da turare,ya gama shiryawa tsaf sannañ ta taka masa ya fice sallah
masàllaçi ita Kuma ta koma ta tayar da tata
Sai da ta cika masa ciki da abun ci shi Kuma ya ci ka mata nata da ayaba yana
tsokanarta ta zama qanwar monkey, bata kulashi ba sai da ta qarasa cinyewa abarta
sannan ta taqarqare ta tureshi ta haye kansa
"Wayo jama'a wayo mummy 'yar lukuta maman baby zàta karyani a kawo agàji"ya fada
yana qyalqyala dariyar tsokana,ta turo baki"kyau sai ka gayawa aya zaqinta"
"Wayo 'yar matata ki taimakeni ki dagani kada nayi amai
"To zan daya ka ammà kan sharadi dayà"
"Naji fadi indai zaki dagàni nidai"yana riqe da cikinsa yana qoqarin boye dariyarsa
hade da yi mata gwàlo a fakaice
"Ni ka yima gwalo?"ta na nuñà kanta da danyatsanta gami da shagwabe fuska,dariyar
da yake boyewar ta subuce ta fito
"A'ah,ni da baby na da yake ciki fa muke wasa"ta kalli cikin nata sai aliyyun ya
bata dàriya,sai ta sauka tana ce wa"sharadina kamin doki"tuni kafin ta qarasa ya
juyo mata bayàn nasa"maza hau,kada ki sauka har sai kin gaji da kañki"ta tattare
rigarta tana shirin hawa salima tàyi knocking,hakan yasa fadila sakin rigàrtata ta
koma saman kujera ta zauna,da qyar sàlima ta samu ta hadiye wa ni dunqulallen Abu
mai zafi da ya tokare mata maqoshi,a duniya ta tsani ta bude ido taga fadila dauke
da cikin nan a jikinta,ji takeyi da ta dunga ganin Fadila da shi ta gwammace ta
bude idoñta taga baqin kumurcin maciji
Babban Abu na gaba dàke tayar mata da hankali,so qauna kulawa màsu nauyi da take
gaji guñ aliyyu akan Fadila da cikinta,ta sani tayi sake Kuma ta barar da
damarta,ta kuma bar kari tuni ran tubani
dumbin kulawa da tarairàya babu wadda bata Samu ba guriñ Aliyyu,tuni yà bana mata
hanya qwaya daya da zata sake samun damar mallakeshi shine ta hanyar cika masa gida
da yara amma sai ta gaza yin hakan,ta watsa masa qasa a ido,a yanzun tana jin
shiryawa yin hakan,ta shirya kawàr da duk wani Abu da zai zama mata shamaki
tsakaninta da Aliyyu,Samira ba matsalarta bace lamarintà mai sauqi ne bata dameta
ba kamar yadda Fadila ta tsole mata ido.......
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed💞: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
2⃣8⃣ 2⃣8⃣
"To na gode"kawai fadilan tace, ta Daki remote ta qaro sautin t.v tare da maida
hankalinta kai,saboda jin wani kishi na taso mata yadda aliyyu ke hira da salima
cikin sakin jiki ta soma ka ranta "hasbunallahu wa ni'imal wakeel",Samira ce ta
shigo gamida ce wa"sllama" kanta tsaye ta nufi kusa da Fadila ta sauna don Neman
magana,ta kalli aliyyun yayi da shi din ma ita yake kallo ,cikin ransa yana
fadin"can za mutum sai Allah"baar doguwar Riga ce a jikinta kanta babu ko kallabi,d
slipper sonta ta shigo har tsakar faloñ,hannunta Kuma ga ragowar miya da maiqo
nan,ya sake fadin "yanzun haka qila ta taho har nan kenan"
"Gani,ina zaune zan fara cin abinci ka kirani,har na fara ci naga waccar ta taho
bace Gwara na haqura da abincin inzo inji kake faruwa kada ayi bàbu ni,ko a yimin
munafurci a cuceni ganin bani gun"sai Kuma ta maida kanta gun Fadila dake
gefanta"ummm,anata mana Kallon banza ko"ta sani sarai da ita yake don ta saba gaya
mata haka,wai tana mata Kallon banza tana ganin zata haihu
sau tari dariya Samira ke bata idan ta fadi haka,don ita dai bata ga wa ni Kallon
banza da take musu ba,sai bata fiya damuwa da shirmen ta ba,bata da qullaci kanta
tsaye take magana,haka idan zata ai kanta kanta tsaye take fadi ba boye boye
Salima ma murnar take yayin da Fadila tayi kamar Batasan me ake ba,don ta tsammaci
zai miqo mata nata passport din tunda yana guriñsa,a hankali ya maida idanunsa
kanta bayan fitarsu,ko motsi bata yi ba tana zaune a inda take kamar yadda taqi
furta komai
"Babyyyy"ya kira ta ta juyo ta kalleshi,sai Kuma qwalla ta ciko idanunta,ya miqe
tsam ya iska Kujerar da take kai
"Baby.......kuka?"kamar jira dama take sai kawai ta rushe da kunya
"Subhanallahi"yace ya kwantar da ita kan cinyarsa,a hankali ya dinga shafa gashin
kanta da yasha gyara yana jin sautin kukanta na sauka a kunnensa,bai hanata ba don
yasan ba yin kanta bane
sai da ta gama ta qoshi har tana sakin ajiyar zuciya sannan yace mata"baby me ya
faru erhmmm?"
"Shine zakayi tafiyarka umra kai da kayan ka wato ni a barni a gida ko?"
Murmushi ya saki mai dan sauti,ai kuwa sai ta sake qufula
"Dariya ma kake mini?ai dole Kayi dariya saboda yanzu bani da mamora kenan"sai ta
kuma sakin kuka,masifa ta hau zazzaga masa da bala'i,shi kam ma sakin baki yayi
yana kallon dan qaramin bakinta daketa zazzaga masifar yarda qoqarin qwacewa daga
jikinsa,sai ya hanata ya matseta a jikin nasa har sai dà ta gaji don kanta tayi
shiru,sai Kuma ta dinga sakin ajiyar zuciya alamun ta fara sauka
Yana dagota yaga tuni Ashe bacci ya dauketa,murmushi ya saki ya dagata cak ita da
uban cikinta ya kaita bedroom cikin dabara ya suya mata kayan bacci ya gyara mata
kwanciyarta sannan ya dawo parlour ya gyara gun dà suka ci abun ci ya hada kwanukan
ya wanke mata su tas,don yasan matuqar suka kai safiya saita wanke kafin ta hada
breakfast
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/28, 7:56 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
2⃣9⃣ 2⃣9⃣
Lokacin da ya dawo tuni ta Dade da yin nisa cikin barcinta,ya jima zaune yana
kallonta,ba qaramin tausayinta yake ji ba haka nan d wannan uban cikin nata da yafi
watanninsa girma
"Har yau Baki gama sanin irin matsayin d kike d shi cikin zuciyata ba
Fadeelah,sadai na sani lokaci zai ci gaba da nuna miki"ya fada a filing,bayanta ya
koma ya kanta bayan ya janyota jikinsa ya sake tofesu da addu'o'in tsari na
kwanciya barci,hannunsa daya na saman cikinta yana shafawa a hankali yana jin
qaunar abinda ke cikin nata yana sake ratsashi
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Qarfe goma su na falon zaune abinsu,Garin na lullube ne da hadari kadan don haka
babu batun rana,sanyin a.c da qamshi mai taushi ne ke ganshi a falon,tun dazun ya
tsura mata ido yana dariya qasa qasa,tun safe yake dawainiya da
ita,wqnka,shiryata,bata ayabarta amma taqi yarda ko daya su hada ido,kunyar abinda
tayi masa jiya ke cin ranta,tana ganin ta zaqe da yawa ta gaya masa maganganu da ya
cancanci yayi fushi d a ita amma yaqi maimakon haka ma sai ya buge da yi mata
hidima da dawainiya d ita
Zuwa can ya sake tsunkularta ta sa hannunta ta dan bugeshi ba tare da ta kalleshi
ba,tasan dai abinda yake so,da dai yaga taqi kallonsa sai ya sure ta gaba daya ya
azata bisa cinyarsa yana leqen fuskarta
"Haba baby nah,so kike ne yau na susuce ?,gaba daya yau kin hanamin Kallon sexy
eyes dinki"
Sai ta fada qirjinsa tana Hawaye
"Ka yafemin miki na,na maka rashin kyau tsawa jiya,na mance lokacin da ni ka dauke
ni mukà tafi Wata qasar tsawon watanni my biyu kacal,kishinka ne yamin yawa har na
ai kanta hakan,amma......"
Da sauri ya tura harshansa cikin bakinta ya hanata qarasa maganar tun dazun dama
lebunan nata ke bashi sha'awa,daga bisani ya cire yaba share mata qwalla"kada ki
sake yamin asàrar hawayena masu tsada,bayan already na gayamiki ba zaki sake kuka
ba har abada,ni baki yimin komai ba"aliyyu miki ne daya da daya Wanda sàmunshi a
irin wannan zàmanin sai an tona,wuni sukayi tarairayar juna,ita tana qoqarin
faranta masa shi yana qoqarin kyautata mata,ganin bashi da niyyar fita yasa ta
tambayeshi
"Kyau babu inda Zani sai la'asar,ina tare da masoyiyata"dariya ma ya bata,aliyyu
mayen Soyayya ne wani lokacin idan ya cikata da ita sai ta rasa inda zata tsoma
ranta
Duk d cikinta hakan bai hanata sakarwa aliyyu kanta yayi yadda yake so ba Duk da
qoqarin boye zalamarsa da yake hakan bai hanata dagoshi ba,shi Kansas mazewa kawai
yake amma yasa zaiyi kewarta ita da babynsa ba kewa ba na wasa ba,ya yaba sosai da
juriyarta d jarumtarta,sau tari taken danne farincikinta don shi ya samu nasa,hakan
yake qara masa qaimi gun kula da duk wani abu da zai kawo naqasu ga walwalarta
Sai da yayi la'asar din sannan yàce zaije shi da nasiru yayi masu handling din
koma,ana magariba zai dawo suje ta siyi abubuwan da take da buqata
Ta kashe hand drayer din da take busar da gashinta da ita"my haidar,ni bana guitar
koma,kada ka wani kashe kudinka"ya dau ribbon sonta yana tayata faire gashinta "ban
son in tafi in bar ruhina tana buqatar wa ni Abu"
Ta saki murmushi "bana tsammanin ko shekara hudu zakayi zan rasa wani abu cikin
gidanñañ"ya sani Fadila akwai tattali ,ko kadan bata da almubazzaranci"nasan wace
mata ta,amma Duk da haka a taimakeni a yimiñ alfarma aje Siyayyar nan"
"Kafi qarfin haka a wajena mijina ,nayi makà"
Yana fità ta shiga kitchen ta Debi fulawa ta kwaba cin cin d cake a mixer,ta Debi
zallar tsokar nama ta gyara ta dora kan wuta,abun ka da harkar na'ura nan d nan ta
kammala koma da wuri har dambun naman ta nade cikin papers masu kyau,sosai ta gaji
don ta jima batayi aiki irin haka ba,don haka ko da ta fito wanka zaune tayi German
gado tana daure da towel a haka ya shigo ya taddata
"Kinyi aiki bayan fitàta"tana dariya qasa qasa tace "waye ya gaya maka?"ya qaraso
inda take"kin manta zuciyarmu a hade take?,Kuma ina shigowa naji wani qamshi kuma
na tabbatar ke kadaice mai irin wannan girkin"cikin son bàsar da zancen tace"yanzun
dai ka hañzarta Kayi wanka ruwanka na bayi,ya gano wayanta.....
N.b:pls Ku yimin afuwa kwana biyu nayi busy ne wlh,na gode muku da haqurin da kuke
da ni,Allah yabar qauna
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/28, 7:58 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
3⃣0⃣ 3⃣0⃣
Ga zatonta zai zauna ne cikin Motar kamar yadda ya saba,sai dai wannan karon biyota
yayi yana tayata zabar duk abinda take so,ya iya Zabe kamar wa ni mace,su na tafe
suna hirarsu,yana cikin yi mata Dariya ne taga ya tsaya cake fyskarsa a murtike
yana kàllon wa ni guru,salima ce tsaye da wani suna hira hardà dariya,sakin kayan
hannunsa yayi cikin fusata yana wani irin huci da fishi ya nufesu
Kyakkyawan mari ya saka ma matashin,dago kai yayi cikin fushi "malam me nayi
maka!"bai tanka masa ba illa wani naushi da ya kai masa,take bakinsa ya fashe,dafe
halin yayi sannan ya duba tafi Hannun"kan bala'i"ya fadi gami da Hawa kan aliyyun
da niyyar ramuwa,saidai da hannu daya aliyyun ya kama hannunsa sai ji kake bas!,ya
saki wata qara nan ya zube,Kansa aliyyun ya sake yowa da saurin gaske Fadila ta
tokàreshi da hannunta ganin kamar bai cikin hayyacinsa,sauran kadan ita din ma
Takai qasa qasa,tayi taga taga ta dafa Wata kanta ta tsaya
Wayarsa ya zaro sai ji tayi yana magana da d.p.o na areansu yana a turo masa 'yana
sanda,da sauri ta sake yunqurawa ta amshe wayar,idanunsa jazur ya dauka wa fadilan
tsawa gami da miqa mata hannunsa,salima dake gefe tuni cikinta ya soma jiyaa
wa,Dana sani mai tsanani ta rufeta,Fadila ta girgiza masa kai taqi bashi tare da
juyawa don tafiya,don Tasan abun ba zaiyi kyau ba,cikin fusata ya fincikota sai
gata a qasa,ya amshe wayar yana qarasa wayarsa,wa ni zugi ya ratsa mararta,tada
Hannu ta dafe cikin tana runtse da ido
Cikin 'yan mintina sai ga police har biyar ,suka cafkeshi kuwa su Kayi wàje d shi
aliyyu na fada musu kada su soma Sakinsa ko Waye yazo su ya nasa umarni,wa ni
matsiyacin kallo ya juya ya wa tsawa Salima Wanda yasa hantar cikinta kadawa,bala'i
ya dinga zubawa Allah yasa area din da su ke ba kowà,idanunsa sun rude ya manta a
shoprite suke,tuni tsoro ya cika kowaccensu,sukayi tsuru tsuru gami da sake shirya
taitayinsu,ya juye ya koma aliyyunsa sak,kallonsa duka suke,sai da yayi ya gaji don
Kansa sannan yayi shiru
Dai dai suke ficewa Fadila na zaune tun dazun da ta fadi tashi ya gagareta,sai ta
yunqura sai zugi ya daya ta koma ta zauna, a hankali idonsa ya sauka kanta,wani
tausayinta ya lullube shi,ya qarasa a ahankali ya miqa mata hannunsada niyyar bata
taimako,tasa hannunta cikin bashi don Tasan dole tana buqatar taimako,ya miqar da
ita tsaye ta saki wata 'yar qara,
"Ayyah sorry baby na,Kiyi haquri"ya fadi muryarsa a raunane,shiru tayi masa ta
sabule hànñunta kawai tayi gaba ya bita a baya
Tamkar kurame haka suka zauna cikin Motar sai uban gudu da ya dinga tsalawa,yana
tsàida Motar yà finciki Hannu salima Zuwa bangarenta,Samira ta dafe ka"oh ni Samira
an shiga uku ta jama kanta"ta fita ta debe kayanta ta tafi,ita kam Fadila nata
kayan sunfi qarfinta sanda haka sai ta kashe masa Motar da bai kashe ba,ta kukkulle
Motar tayi nata bangaren
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/28, 7:59 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*Part 3*
3⃣2⃣ 3⃣2⃣
Qarfe tara jirgin su zai sauka sanda haka tuni take as nasiru ya debe su sumayya
yarda iftihal wadda itama tasha kit so da qunshinta Zuwa airport din,Fadila ce wa
tayi Duke kawai,fitarsu ta shiga wa ka,cikin lokaci qanqani ta shirya kanta tsaf
cikin dinkin Shadda buba orange colour mai combination da blue black sai zuba maiqo
take da qyalli, ta maqala fashion na sarqa da dan kunne mai duwatsu da abun hannu
suka blue black,sani azababben kyau tayi tamkar ka saceta,sai kace ba mai tsohoñ
ciki ba,ko ina a jikinta qanshi yake zubawa
Zamanta na 'Yan mintina ta jiyo shigowar motar,ta saki ajiyar zuciya tana
fadin"alhamdulillah",tsananin farinciki ya hanata miqewa Duk da irin dokin da take
nayin tozali da masoyinta,shi kansa tunda suka dauka yaketa taba ido yaga ta inda
fadilan tasa zata bullo
Sannu a hankali take takowa har ta iso inda suke tsaye ana fiddo music da kayan
su,sallamarta ce ta maido hankalinsu kanta,aliyyu ji yake kamar ya rungumeta sai
dai ya dake kawai,qaunart ce ke sake narkewa cikin zuciyarsa,ganin cikin nata yayi
ya sake girma fiye da lokacin da suka tafi,Kallon juna suke cike da murmushi ta
miqa hannu don amsar qaramar jakarsa bude da fadin"Barka da dawowa"ya noe kamar
alamun ba zai bata ba"barks ka dai maman baby"
"Ba magana ne qanwarmu?"cewr Salima da ta zuba mata ido cike da boyàyyen kishi,da
fara'arta ta waigo ta dubesu
"a'ah.....ina shirin gana wa da oga ne sannan mu gaisa,ya gajiya,kun dawo
lafiya?"kusan tare suka amsa sai dai kuwa ce da yanayin da ta masa dan,hankalinsa
gaba daya ya raja'a a kanta,Duk motsinta idànunsa na kai,hakan ya sake qulla mugun
qulli cikin Zuciyar salima da alwashi kala kala
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Da qyar take iya saga qafafunta,don idan tana tafiya tallafe cikin take,kinsan take
kamar zai sauko qasa,gaba daya ta can za kamanninta sun sauya,babu yadda aliyyu
baiyi da ita suje Dubai ko India ta haihu a can ba amma ta qiya,tace tafiso ta
haihu cikin qasarta da danginta
Fada babu irin Wanda momy batayi ba akan ya dawo mata da fadilan gurinta amma
Yaqi,sai dai kullum ya kalallameta da fadin halin zai kawota,batasan shi Baisan
Fadila tayi nisa da shi bane,tun bikinsu sumayya da rabi'ah Momi ta so riqeta amma
sai ya lallaba ya kai qararta gun uncle abba shi Kuma yace ta bashi matarshi,ta
barsu idan sun shirya a nutse ya kawota,tunda ya samu ya dauketa yaqi maidota
Sai su su Samira sukà tada tsiyar suma sai an nemo musu mai aiki,aliyyu ne ya musu
Jan idan nan nasa yace da su shiru dinsu,baaba talatu tamkar kaka take agunsa,kada
wadda ta soma kawo masa 'yar aiki gida
Taku hudu biya ta sake juyawa,da qyar ta samu tàyi hakan sau biyar don bin umarnin
doctor sa'adah,tuni ta hada gumi sharkaf,cikin Dauriya irin tata ta juya ta shiga
dakin baba talatu da ta kwanta yin qailula bayan sun gama hira tà tadata ganin
lokacin sallar azahar na qoqarin ficewa,ta farka ta dubi Fadila tana Mata sannu,ta
amsa a kunya ce sañnañ ta daura tata alwalar,a falcon Tatars da baban nayin
tata,itama ta zube sannan ta tayar
Baba talatu na saman kujera tana jañ carbi Fadila ta miqe tana fadin"yunwa nake ji
baba sosai,kamar ba dazun nan na gama can ayabarba"
Baban ta kalli inda ta Ajjiye ragowar da ta gama ci"ai kuwa dai ga ragowar da Kuma
rage can nama manta ban dauketa ba,maza ki cinye a barki ba dadi zama da yunwa,idan
baki qoshi ba sai a dado miki"tayi murmushi tana dada qaunar baban,maca ce wayayya
Duk d ba tayi karatun boko ba
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/28, 7:59 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
3⃣4⃣ 3⃣4⃣
Kimanin awa guda yana tsayen don ko sha'awar zaman baiyi har ruwan ya qare da suri
nurse din da ai bari a dakin ta taso ta cire mata ta sanya mata dayan,cikin karaya
aliyyu yabi saban ruwan da ta sa mata da kallo zuciyarsa cike da fargaba,sai dai
kafin ya dauje idonsa yaji an damqe hannunsa dake cikin nata tsam tsam tmkar zata
ballashi,da sauri ya kalleta still idanunta na rufe,a hankali numfashinta ya sima
fita da sauri da sauri,wa ni bashi ta soma mai cike da wahala
Tuni nurses din suka danna wa ni Abu,cikin qiftawa da bismillah sai ga doctor
sa'adah ta shigo,kanta sukayi suka soma bata taimako,aliyyu na tsaye cike da
rudani,tausayinta da qaunarta suka sake Hawa a zuciyarsa,idanunsa ya sake kadawa
babu hawaye sai azabar quna da zuciyarsa keyi ganin irin gwagwarmayar d take
share,idanunta na rufe amma gunji take da nishi mai ban tausayi,hannunsa dake cikiñ
nata har yanzu kamar zai balle
"Doctor idan babu dama wuyarnan ta isa haka,Gwara a yimata c.s a cire mata babyn ta
hira mana"ta girgiza kai"Daga take da haihuwa,don zata ita haihuwa da kanta"tana
rife baki Fadila tayi wani gauron nishi mai qaraji da yasa aliyyu ya sake rudewa
sai ga baby ya fado,kukansa ya cike Daki,daya Daga cikin nurse din ta
daukeshi,doctor ta taba cikin ganiñ fadilan na sakeyin wani nishiñ,sai ga kukan
wani yaron shima ya taya dan uwañshi callara kuka
"Alhamdulillah"doctor sa'adah ke fada tana sake dubà fadila
"Mtsweeu,inajin da wa ni yàron a cikin nan"ta soma taya Fadila qoqarin fidda sauran
abinda ya rage a cikinta kasancewar qarfinta ya qare,jikinta ya soma saki,da qyar
aka zaqulo dayan Maca ce,sai dai ita din wani irin kuka take baya ma fita sosai
bisa dukkàn alamu taci wahala don har ta fara kashi a ciki,kam wa ni gado doctor ta
dorata aqalla mintina girma sannan ta dagota
"Sa'adiyya karbi zaitun ko lotion a goge musu jiki,baza'a yi musu wa ka ba har sai
gone"tace da aliyyu Wanda baima San meke gudana a dakin ba ,kacokam hankalinsa na
kan matarsa
Ya kalleta"ki nadeshi kawai doctor, bamu zo da komai ba"ya maida hankalinsa kan
màtarsa dake ta sakiñ ajiyar Zuciya,doctor ta Daga wayarta tayi kira tana bada
umarni aje shop din cikin asibitin da yake nata ne a dauko riga unisex mai bude da
showel guda uku,cikin qanqanin lokaci aka gogesu fed,doctor ta qaraso kañsu,cikin
damuwa ya kalleta
"Doctor taqi motsawa fa har yanzu"murmushi tayi "kada ka damu,mun riga mun kashe
Duk wani tasiri na gubar ai zata dawo hañkalinta insha Allah nan da wa ni dan
lokaci,yanzu za'a gyara mata jikinta ne don tafi jin fadi,zatayi bacci na minti
talatin da zarar ta farka zata koma normal,congratulations *Mr Aliyyu Salim mai
tama*,ka Samu yara har uku,biyu maza daya mace"
Jinsa Kayi kamar cikin mafarki ake gayamasa hakan,wa ni sanyi ne mai dadi ke ratsa
zuciyarsa,ya zaro idànu"pls doctor bama irin wannan wasan,are you serious?"
"Am serious aliyyu,lokacin da suke isowa Baka ji ba?,gasu can ai"tai masa nuni da
su banda macen da aka ware a wani dan gado daban,ya zuba musu ido yanajin kamar ba
haka bane
"Kada a fiya daukan baby girl din,don ta bugu sanda mamanta ta fadi,ta fisu shan
wuya,zamu riqeku na three days don zamu na bata treatment"
Mai karatu fasalta irin farinciki da wannan family gida biyu suka Shiga wato
familyn *Alh Abbas Abdallah* da *Alh salim mai tama* bata baki ne,godewa Allah
kawai suke suka qarawa da 'yarsu ta tsallake rijiya da bakya ga kyautar kyawawan
yara har uku tare da sake addu'ar samun lafiya ga Fadila dà baby girl dinta,Daki ne
qato guda daya mai kyau aka ware musu aka zuba gàdajen yaran,aliyyun na zaune
dirshañ gaban gadon yana jiran farkawarta ,tuni ya miqa musu yaran bayan ya tofesu
da addu'a,ai kuwa dan qaramin biki aka bude a dakin,shikam yana jinsu don ta
matarsa yake tukun
Cikin ikon Allah ta farka da qwari a jikinta,da fuskar mijinta ta soma tozali,ya
sakar mata murmushi yana fadin "sannu 'yar albarka"ta dan lumshe idonta cike da
kunya,shi da Kansa ya taimaka mata ta wanke bakinta ya hadà mata tea mai kauri ta
sha,kowa sañnuñsa yake miqa mata
Dukka yaran ya Jere mata a gabanta yana dubanta"Fadeelah na kinga irin kyautar dà
Allah yayi mana ko?"kasa magana tayi,cikin zuciyarta godewa Allah take mai hukunta
abinda yaso,kunyar su momi take wa sanda ba su San ma suna abinsu ba,da yaga taqi
dauka sai ya debesu gaba daya ya dora mata saman cinyarta ya hadasu ya rungumesu
gaba daya yana jin duminsu,tuni kowa ya fice a dakin sai juyowa sukayi suka ga
Wayam
Fuskarta ta dago Daga kan yarañ tana Kallon aliyyu,gira ya Daga mata yana cewa"kin
yarda ni din jarumi ne ko?,Dukkaninsu da ni suke kama,baby girl ce kawai tayo kamar
fatarki"sai tayi kicin kicin da fuska"ai zasu dawo kamata ne"ya tuntsire da
dariya"inaaa......ai sai dai ki tara a gaba"
Gwalalo ido tayi"haba my haidar,ni kam na gama Daga wannan,wlh sun isheni"ta
qarashe maganar kamar zatayi kunya
"No baby,ni Kuma wlh inason kamar haka sau shida,"fashe masa da kuka tayi,Dariya na
ciñsa yana lallashinta a haka Momi ta shigo ta tadda su
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
3⃣3⃣ 3⃣3⃣
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"ta soma fadi tana riqe tamau d cikinta,cikin
azama baba talatu tayi kanta tana tambayarta"lafiya?,me ya faru?"
Sai dai ina!,tuni kafin ta qarasa kanta ta rikito daya kan Kujerar da take zaune ta
kifa qasa warwas kan turtsetsen cikinta cikin fitar hayyaci,da gudu baba ta qarasa
gami da dagota,jirin ne ke fita ta qasanta da bakinta gami da ragowar ayabar d
abata qarasa hadiyewa ba,ko kuwa babu alamun numfashi tare d ita,hakan ne y gigita
baba talatu ta saki salati mai Mutuwar qarfi da nuna razana Wanda yasa salima
juyàwa cikin sauri don barin gurin
Sai dai kafin Takai ga ficewa su Kayi kacibus d samira,tabi Salima da kallo ganin
irin saurin da take zubawà tuni har ta wuceta,ita kuwa salatin babarne ya janyo
hsnkalinta don wucewa tazo yi,da sauri ta taka tq shige bangaren Fadila don ganin
meke faruwa,dai dai lokacin baba jita kokawa da wayarta don Neman mutum daya cikin
biyun aliyyu ko momi,abinda Samiran ta gani yaso bata tsoro,da Sauri ta juya ta
koma da baya,batayi wata wata ba ta soma qwalawa isyaku kira,sun San halin rashin
Kirki irin natà don haka jiki na tmrawa ya iso
"Yi maza ka dauko Mota"
Bai tambayi ba'asi ba ya juya don cika umarninta,sanda ta shigo har baba ta gama
Sanar da Momi,Samira tace"rashin maza baba mu kamata ku wuce asibiti kada ta zamar
mana gawa my shiga uku gun Ali"(gaboncin magana kenan irin na samira),da ita aka
sanya fadilar a Motar sai dai bata bisu ba,ta dawo tana tunanin me ya sameta
haka?,dage kafada tayi don bata sani ba ta koma barandarta ta zauna tana nazarta
yadda salima ta killed bangarenta tayi lakur a ciki,duk da tana jiyo tarin salatin
da ma'aikatan gidan ke ta zubawa
Daga qarshe ta dauke kanta tana tsammanin shegen kishinta ne da yafi nasu ya
motsa,Duk da lokaci lokaci tana tambayàr kanta me tayi a bakin window din?
Bana talatu tace"ni kaina abuñ ya dauremin kai,muna cikin hira fa sai salatinta
naji"
"Baba ko wani ya shigo,ko Kuma kun bar qofa a bude?"aliyyun ya tambayeta
"Eh,tabbas ta dn fiya barañda ta tattaka yadda likita yace da ita,to kafin ta dawo
lokacin ni na shiga ciki na kanta,to ina tsammani ta manta ta bar" qofar a bude,kai
tsaye ya nufi dakin da aka shigar da ita din gadan gadan Momi na ta kiransa amma ko
daya kunnensa baima ji kiranba har ga Allah
Kafin yakai ga qofar ta bude ,likitoci uku ne suka fito ciki yarda doctor
sa'adah,tareta Aliyyu yayi da tambayoyi barkàtài har ta rasa wacce zata amsa masa
"Cool down Mr aliyyu,my qarasa guñsu Momi",ganin tahowarsu yasa duk suka miqe suna
tambayar me ake ciki?,doctor sa'adah tace"da farko dai mun gàno ayabarnan da taci
tana dauke da gaba mai màtuqar qarfi"
"Gaba!"suka hada baki gurin fada banda aliyyu DA yace"what?!"cikin qaraji"waye ya
aikata min haka?,tabbbas ko waye bazan qyaleshi ba"
Tuni kafin ta qarashe bayanintà aliyyu ya shige dakin,tana kwance sambal bisa gadon
sai uban ciki a sama tamkar an sake turoshi,idanunta a rufe suke ruf hancinta sanye
d oxygen, kayan d asibitin ke sanyawa mai naquda ne sanye a jikinta,fuskarta luf
luf tamkar zata yi magana,Zara zaran gashiñ idonta sun fito reras,sai dai babu wani
Abu dake motsi a jikintà,nurse biyu ne cikin dakin dayar na Gyara zanin da aka
rufeta da shi Zuwa saman cikinta,dayar Kuma na tattare kayayyakiñ da sukayi magani
da su
Zuciyar aliyyu ta karye gumi ya sàke yanko masa,hankalinsa ya sake tashi,ya qaraso
bàkin gadon ya sanya hannunshi cikin nata yà zuba mata ido"Fadeelah waye ya yamin
wannan aikin?me kuka yi masa ?,wanne zuñubi kuka aikata masa ke DA halittar da
bataji ba bata gani ba,pls Fadeelah kada ki tafi ki barñi,Kiyi qoqarin ci gaba da
rayuwa da ni don Allah matata,wlh idan babu ke nima babu ni"shi kadai ke zuba
sumbatun nurses na kallonshi,sai da ya gaji don Kansa yàyi shiru don wadda yàkeyi
don ita ma batasan yana yi ba....
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
3⃣5⃣ 3⃣5⃣
a haka Momi ta shigo ta tadda su"a'ah,Ali mai Kayi mata ne?"cikin dariya yace",sai
Momi don bace ina son kamar yaran nan sai shida"kunya ta lullube Fadila, daquwa
momin ta wata masa "ja'iri kawai,amma dai Baka da tausayi ko?,to yanzu zan kora ka
kuwa ka tafi gida"ya Daga kafadunshi duka biyun
"Momi na ba sai kun Kore ni ba ma tafiyar zanyi"sai Kuma yanayin fuskarsa ya can
za"zanje na binciki yadda akayi poison ya shiga cikin ayabar nan,dolene Duk Wanda
ya aikata hakan ya karbi sakamakon sa a hannu"
A hankali ta dago da kanta dake duqen"don Allah yaya kabar maganar nan,ni na riga
na yafe tunda Allah ya bani ka fiya da kariyarsa,Wanda ba wayo ko dabararmu bace
haka din"
"Shshshsh!,shut up, ni ban yafe ba,kada Kuma na sake jin bakinki a maganar don
yanzu hurumina ce"
"Gaskiya Fadila ta fada,idan ka dage da bincike kamar ka yiwa Allah butulcin
kubutar amma da iyalinka ne da yayi maka,sai dai Nima ban lamunci a qyale maganar
ba saboda gaba,ya zama lallai ka qara matakan tsaro"
Koma wa yayi da baya ya zàuña yana jijjiga kai,ba yadda ya ita tunda Momi ta shigo
ciki,wayarsa ya zaro yayi kira,ya soma magana inda yà Daga qarshe suka ji yana bada
umarnin a kawo masa c.c.t.v camera guda hudu Daga yau Zuwa gobe(hmmmmm,a juri Zuwa
rafi da tulu debo ruwa,wata rana.......)
Kwana uku Fadila tayi ragal da ita har yaran,tamkar babu wani Abu da ya faru da
su,tuni haihuwar Fadila ta karade ko ina,dangi da ba dangi ba,'Yan asibiti kam
sunsha kallo yawan 'yan barka dake tuttudowa a kullum yasa ta qagu a sallamesu wasu
ma fadila bata sansu ba
ga aliyyu dà kulli yaumin yake bata kunya, Duk yawan mutane idan yazo baijin
kunyar rungumeta ko riqeta,sai dai su bude ido suya kuwa ya fashe ya bar musu dakin
Cikin kwana na hudu ne doctor sa'adah ta sallamesu,da yake safiyya ce Daga rabi'ah
sai farida dake fama itama da qaramin ciki Duk sauran ba su qaraso ba,cikin
motarshi pilot suka shige shi d yaranshi,yayi da rabi'ah d farida kuwacce ta shige
tata don su rabi'ah ma sunyi mota suka bisu a baya
Sai da suka kuwa Zuwa titin gidansu taga ya dauke hanya ya sauya titi,ta
kalleshi"kai da zaka shiga lamido crescent ya ka canza hanya?"
"Eh ina sani"ya fada mata yana murmushi,sannu a hankali ba tare da wata tafiya mai
nisa ba suka qaraso
Baki ta saki cike da al'ajabin abinda take gani,wa ni irin mansion house ne da bata
taba tsammanin d irinsa a qasarnan tamu ba,tun daga makekiyar get da zata maka
hanya Zuwa ciki ta fara tsinkewa da lamarin gidan,har bakinta ya Gaza yin shiru
"Habiby wai gurin wa maka zo ne?"
"Gidanki ne fadilata"ya fadi yana kashe Motar
Har ya fito ya zagaya baya Inda yaran suke ya dauki babban d mai bai màsà ya
rungume a kadarsa tana zaune dirshan cikin Motar sai da ya leqa yace mata
"Mummy 'yan uku fito mana ki dauko baby girl"
Binsa kurum take a baya tana kalle kalle kamar dan qauyen da ya shigo birni,gida ne
amma gari guda,duk iya yadda kàke tsmmanin kyau haduwa da tsaruwar gida to ya kai
nan,fenti tiles furanni da hadi da roping da Kayi wa gidan duka fari ne,qyalli dà
qamshiñ sàbuñtà kawai yake yi
Kai tsaye suka nufi daya Daga cikiñ part din dàke kewaye dà harabar gidan,qofa ce
mài kyawuñ gaske suna zuwa ya Danna wàni maida ni cikin second biyu ta bude suka
shige,makekeñ parlour ne Wanda ya lanqwame kujeru har set uku,mai karatu sài na
kammalà rubutà littàfin nan ban gama fasalta muku shi ba,don haka na bàr mai kàratu
ya fàsàlta abinsa,
Ya juyo guntà a bayan ya kwàntar da yaran ya karbi macen itama ya kwantàr sannan ya
kama hannuntà ganin yadda qwayar idànuñtà sukayi raurau,baice mata komaiba ya ja
hannunta tana biye d shi,ciki da bai na part din nata yake nuna mata,sama suka fara
Hawa,parlour ne shima mai girma gaske sai dakunan bacci gida hudu,daya nasa ne daya
nata,daya na yaran,daya Kuma safaya ne kawai,ita dai ido ta zuba,don Duk wa ni Abu
na alatu da qawata gida da jin dadi babu Wanda ba'a zuba ba,dakin yaran kawai kansa
abun kallo ne,dauke yake da wa su irin hadaddun gadaje na yara musu rumfuna
kowanne da drower dinsa mai zubin cupboard wadda ta kere rabin bango,cike dakin
yake da Duk wa ni nau'i na kayan wasan yaran,sai many an frames masu dauke da
addu'o'in tsarist maqale saman gadon kowa,idan ka dauke tulin kayan wasan babu
surar photo ko daya a dakin,sai wata 'yar qaramar t.v plasma dàke manner a bangon
dakin tana fidda sautin karatun alqur'ani,sai c.c.t.v dake manner quryar dakin
wadda hatta fadilan bàtasan da ita ba,luf luf dakin yake dai dai da buqatar jariri
sake riqota yayi suka sauko suka ratsa ta wani corridor baya ga faluka biyu da suka
wuce,dakunan bacci ne guda uku baya ga kitchen store a parlour na biyu,sai kitçhen
store public toilet a parlour na farko,daki na uku da suka shiga nan ma dakin yaran
ne,gira ya Daga mata bayan ta kalleshi
"Nan dakin 'yan uku zasu dawo da zata kin kuma ajjiyen wasu ukun"
Cikin shagwaba ta soma dukan qirjinsa"Baka tausayi na ko?,ba momy tà hana fàdà ba"
"Sorry sañyin idaniyata"ya fàdà yana maida hàññuñsa ya rungumetà a qirjinsa
Zaunar da ita yàyi gefàñ gadon,dà Kansa ya dingà dauko dà wadansu irin akwatuna da
batà taba ganin irinsu ba,saida ya sauke 12 tana binsa d ido ba tare dà tace komai
bà
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
3⃣6⃣ 3⃣6⃣
"Kayanki ne ke da yarana"ya fadi yana bubbude mata akwatunan gami da yi mata bayani
nata uku yaran ma kowa uku uku
Shaqe suke da kayan na alfarma,musamman yasa ma'aikatan company dinsa na india suka
fidda taswirar design din kayan ,design ne da sai nan da shejara mai Zuwa ma zasu
fidda shi,ita kam ta rasa mai zata ce,da ta bude baki zata yi masa godiya sai yayi
kicin kicin,hakanan taja bakinta ta tsuke jiki a sanyaye ta tayashi rufe akwatunan
Yasa hannu ya dauko wa ni qarami dake rude daban ya budeshi,wasu takardu ya fito da
su ya dorasu saman cinyàrta
"Estate ne guda uku da dake ginawa cikin garin abuja,ga takardunsu nan na mallaka
wa 'yan uku,sannan akwai wasu tàkardun na company na ne da kikaje rakani budeshi na
China,Daga qarshe kika gudo kikà barni"ya qarshe da sigar tsokana da ta bata
kunya"na mallaka miki shi fadeelà ke kadai kikà fi cancanta ki mallakeshi,don
kinsan sanadiyyar budeshi ce ta jawo kika haifamin wadannan taurarin"
Takardu guda hudu Kuma daya na shaidar mallakar motoci ne guda biyu,daya taki daya
ta yaran na,ragowar Kuma ki cike min idan kin samu lokaci na central bank ne kada
Kuma ki tambayeni me zanyi da su"
"Wannan kyautar dear tayi yawa,kasa na zama abar zargi ,kada ina cikin zama na ka
jawomin wata fitinar ta daban,mun gode da kyautarka amma pls ka barsu"
"Idan mà Momi kike ji ta Dade da samun zamansu,gani ma take sunyi kadan"
Ta girgizà kai"Sam nasan momi sosai,ba ita nàke wa ba,abokan zamana fà?"
"Ina ruwanki da su?,su Haifa mana suga suma idan ban musu ba,wannan kyautatawa ce
kina yimin dole Nima nayi miki,sama na yi musu dai dai tasu,na canza musu komai na
part dinsu kamar yadda na yi miki,na basu kudade,na canzà musu mota,to me kike
buqata?"
Ta karyar da kanta"Duk da haka ina tsoron fitinà"sai ransa ya baci ,ya miqe ya
kwashe takaddun Daga cinyarta,bai ce uffan ba ya maida cikin akwatin ya fita da
su,duk sai taji ba dadi ta bishi da kallo
Kasa tashi tayi har sai da ta jiyo magana sama sama kamar a parlor din farko ta
miqe ta fito,umminta ce da Anty hafiza da yaronta khalifa Wanda yaci sunàn abba su
wato abbas sai farida da rabi'ah da suka Bari a baya,da sauri ta rungume ummin nata
tana jin wata qaunar ta na shigarta,tunda tq haihu bata zo ba sai ya,wani hawayen
dadi suka soma zuba,ita kanta ummin rungume fadilan tayi,Tasman 'yarta mai alkunya
ce da zurfin ciki,tunda har ta ita rungumeta tabbas ba qaramin jin dadin ganinta
tayi ba
Qarfe uku Muhammad ya shigo da akwati yana fadin ummi taje inji abba zasu wuce,ai
kuwa Fadila taçe ina ai sai ya shigo da kanta ta shigo da shi din,ya dauko yaran ya
musu addu'a cike da alfahari da jikokin nasa sannan ya Ajjiye musu check na dubu
Dari da hamsin kowa dubu hamsin hamsin,sai akwatin da ummin ta ciko guda biyu na
kayan Barka na fadilan da na yaran,kuka kawai fadilan ta saka tana jin qaunar
iyayen nata na sake daduwa a ranta,ita da farida suka yi musu rakiya har bakin
Motar su
Haka Mubarak shima akwati gud ya musu,farida Kuma dinkakkun shaddodi ne da atamfofi
na fitar suna ta yiw 'yaruwarta,haka Anty hafiza da ya ahmad kowa da nashi
barkar,yara dai sunzo da wani irin alkhairi mai tarin yawa
Tana shirin komawa ciki ya tsaidata"zan fita ki sañar da samira an jima na shiru
zai zo ya maida sabon gida,ba sa8 kun dauki komai ba sai dai ko kayan sawà"ko
amsawa bata iya yi bà,shim a bai lura ba don ya rigata barin gun
Tana shiga daki ta Dora Hannu aka ta zunduma ihun baqinciki da takaici
"Wayo Allah na na shiga uku Fadila kin fice ni,kin gama da ni,yara har uku bama
daya ba?,wlh bazan qyaleki ba"haka ta dinga Kuka shabe shabe kamar wata qanqanuwar
yarinya tare da sake cin alwashi
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/28, 8:03 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
3⃣7⃣ 3⃣7⃣
Ana saukesu a harabar gidan Samira ta fito ta qarewa gidan kallo,gida ta saki
"Allah na gode maka,kyau nice a wannan aljannar?"ta kama habarta,sai Kuma ta dubi
sashen Fadila da 'yan Baka suke ta kara kaina
"Wai Matar can ta haihu ne?"tayi tambayar ba tare da ta nemi mai bata amsa ba
Ko kula ta salima bata yi ba,don ji take kamar ta shaqeta,a son samunta tana gamawa
da fadila Samira ce next target dinta,sai nasiru ne dake rufe Motar yace"ta haihu
gajiya 'yan uku Allah ya bayar
"Iyeeee"ta fadi tana kama baki" gaba Samira tayi abinta ta soma gwada muqullanta
har ta dace era bangarenta ta bude ta shige
Sai da ta gama zàgaye bañgaren nata sannan tace bari the bangaren fàdilà taga
jàriran da dai ake fada,haka nan taji t Kasa kushesu yaran sun mata sosai,turare
qal da su tamkar diyoyin turawa,qaramar tasu ce kawai mai dan duhu,sai gashi ta
dauki kusan minti tàlàtiñ kafin ta baro bangaren
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tun ranar da aliyyu ya Baro bangaren nata bata Kuma ganinshi ba,Tun tana dan guntà
hakan da yawan jama'ar dake wuni zirga zirgar barka a shashen nata hàr ta qaryata
hakan,don ko kiranshi tayi baya Dagawa,a ranar ne Momi ta kira ta tana mata nasiha
me yasa zata maida hannun kyauta baya,ta bata haquri ka ba zata sake bà
Qarfe takwas na dare baba talatu ta gama Gyara yaran tsaf cikin wasu irin hadaddun
kayan bacci na jarirai turare qal duk iri daya sai qamshin turaren yaran su
ke,itama shirye take cikin kwalliyarta wadda tafi zubi da amarya ba mai jego bà,ta
goye qaramar a bayanta,sai ta rasa yadda zata sanar da baban
Sannu a hankali ta qarasa cikin Sa'a kuwa shi kadai ta taras cikin falon yana nutse
cikin lausasan kujerunsa,falon lufluf yake sai qmshin freshner yake,sanye yake da
jallabiyya blue black da tayi matuqar haska farar fatarsa,idanunsa saye da farin
medicated glass dinsa
Ya dàgo fararen idanunsa yana amsa sallamar tata,sai ya Kasa zama ya miqe ya karbi
biyun hannunta ,ta sauna tana niyyar kunto masa ta bayan,tuni itama Yan karbe
abarsa ya jerasu reras
Ya cakuli wannan ya taba wancan tamkar mai wasa da màñyan mutane,ido kawai ta zuba
musu tana Kallon tsantsar kamar da sukeyi,sai da ta gaji da shariyar tasa don tun
gàisheshin da tayi ya amsa yayi mata dif
"ranka ya dade ina màgana"
"uhm......me kike fada?"ya tambaya ba tare da yà dubeta ba
"hankali ka nake so pls"
"Ai kunne ke ji ko?"ya sake fada bai dubetan ba,sai zuçiyàrtà ta raunaña,da sauri
ta rungumeshi ta baya tasa masa kukan kissa
Sai ya tsaya cak yana ajiyar zuciya,bata sani bane amma yà fita shiga kewa,bai ita
daurewa ba sai da ya rungumeta tsam a jikinsa yana lashe hawayen
"I missed you to much "yake fada cikin rudewa,tuni ta lura ya soma fita daga
hayyacinsa,tsoro ya kamata tayi qoqarin zame jikinta,sai a lokacin suka ji kukan
yarinyar,tare suka kai hannu don daukarta,aliyyu ne yayi nasarar daukartà ya soma
lallashinta har tayi shiru
Cikin lokaci qanqani suka shirya Kansu dama ance *fadan masoya hutu*,dama aliyyu
màzewa kawai yake
"Baby hassan din nayi nayi masa huduba d Muhammad, usainin Kuma Ahmad, qaramar tasu
Kuma khadjà"tayi dariya tace"masu manyan suna ne ya kamata a basu nickname"
"As you wish my queen"
"To Muhammad Muslim, Ahmad aslam,khadijah Islam"tafi yasa mata
"Very good, that's my unique, komai naki mai kyau ne kin iya zabe,Muslim aslam
Islam,Allah ya raya mana su"
Tayi fari d ido tace"ameen"
Kudi masu yawa ya bata yace ta riqe a hannuñta ,kada Kuma ta wahalar da kowa duk
wani Abu naci ko na sha ko na rabo suna nan a shirye za'a kawoshi nasu yin amfàni
da shi kawai,bata dà ikon cewa koma sai addu'a cikin zuçiya don godiyar ma ya hana
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/28, 10:50 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
3⃣8⃣ 3⃣8⃣
Mai karatu fadar irin shagalin sunan da aka sha bata baki ne,sai dai an ci ansha
masu guzuri sun diba har suka suka bari,abunci indai na qasar Hausa ne babu Wanda
ba saka samu ba,an rabar gidan kurkuku d na nakasassu d masu rangwamen gata,masu
kinsan qwarya a ranar da yawa sun samu rabauta,don aliyyu bai yadda maza sun shiga
musu cikin hidima ba,hatta da masu hoto video coverage mata ne
Cikin ikon Allah taro ya water lafiya,salima na bangàranta zazzabi mai zai na bakin
Ciki ya rufeta *huguma novels readers* sun so ganinta nace kada kuje Ku qarasa ta
Ku zo mu tafi,
Jaridun washegari kuwa shafin farko hotunan yaran ne an rubuta da manyan baqi *'YAN
UKU KYAUTAR ALLAH,DIYOYIN HAMSHAQIN DAN KASUWA ALIYYU SALIM MAI TAMA*
Misalin takwas ne na dare bayan ta gama shirin kwanciya,haka ta shirya yaran yadda
ta saba cikin kayan baccinsu,kuwa ne t bashi nono ya qoshi,cikin lokaci anqani
bacci yayi a won gaba da su,ta saka kuwa ne cikin gadonshi ta ka musu net din dake
saman gadon
Kasancewar ranar ba ita ke da aliyyu ba yasa suka su na samun har baba talatu,ganin
sunyi bacçi yasa ta jà musu qofar dakin ta shiga dakin baba talatu don suyi hira
kafin lokacin baccinsu yayi
Sadaf Sadaf ta dinga takawa har ta nisa ga jerin dakunan baccin su,ta Kasa kunnenta
sosai ba motsin kowa hakane ya tabbatar mata su na sama,cikin dakiya qarfin hàli da
son cimma buri ta kama step din ta haye,kai tsaye ta nufi dakin yaran,ta tura qofar
a hankali farinciki ya cikata ganin ta taki sa'a babu kowa cikin dakiñ
Jikinta na rawa ta qarasa bakin gadon ta Ciro muslim ,hannu tasa a wuyanshi ta
kwatanta shaqeshi,sai kuma ta tuna zai iya tsala Kuma fa,ta jawo blanket din da aka
lullubeshi ta wurgashi bayanta ta Goya shi,ta kifi daya gadon ta zari aslam ta
sabashi a kafadar hagu,ta sake gaba ta dauki Islam cikin sassarfa ta fice daga
dakin tana waige qirjinta na dukan uku uku har ta samu nasarar zagayawa can bayañ
gidan inda tafkeken swimming pool dinsu yake
Dai dai lokacin fadilan ta fito zata komàwa dakin yaran ta dauko wayarta da ta
mance kan gadon aslam,tayi mamakin gañin qofar dakin a bude,bata kawo komai a ranta
ba sai tayi zaton aliyyu ne ya shiga,don wani lkcn idan ba ràñar girkinta bane
kafin ya kwanta sai ya zo ya gansu ya daukesu daya bayan daya ya rungume Yadi da
kissing nasu
Ba Aliyyu cikin dakin wayam Kuma babu aslam bisa gadoñshi,cikin sauri ta soma dune
dube,wasa-gaske sai ta rasa Islam da Muslim,a gigice ta fito tana qwalawa baban
kira,ta fito tana tambayarta lafiya,a rude take gaya mata
"Jeki gun babansu ko shi ya daukesu"
Duk d bata jin hakan don aliyyu baiso a dinga fitowa da su cikin sassarfa qirjinta
na wani irin bugawa ta sauko qasan ta nufi sashen aliyu
Samira taga giftawar mace da goyo Zuwa bayan gidan nasu,tayi mamakin wace haka
cikin dare,sannu a hankali take binta sai taga Muslim ne Ashe a goye a bayanta,da
sauri ta tàko don ta cimmata,saidai kafin ta qaraso din ta daga aslam ta cillashi
cikin swimming pool din,yaron ya canyara qara iya qarfinsa yayi qasa,abunda ya
razana Samira Batasan lokacin da ta saki razananniyar qara ba cikin firgici
aliyyu dake zaune cikin balcony dinsa yana jiran samiran ta kawo masa file din da
ya aiketa tà dauko masa file cikin mota qarar ta ratsa kunnuwansa,da sauri ya miqe
ya nufi inda yake jiyo sautin,fadila da taza gurinsa taga wucewarsa ta rufa masa
baya gabanta na ci gaba da biyu
Yana qarasowa idoñsa ya kai Kansu,wata iriyar mummunan faduwar gaba ce ta ziyarci
Fadila ganin Muslim goye a gun salima,Islam a Hannu samira
"Yauwa don Allah kayi sauri ka shiga cikin ruwañnan ta jefa aslam ci........"
Kafin ta qarasa fadi tuni ya tsunduma ciki cikin wani irin nau'in tashin
hankali,minti biyu kacal ya ciro yaron,
Suna tsaye cirko cirko Fadila na rungume da Muslim Hawaye ne kwance male male bisa
kuncinta ,yayin da Islam ke a Hannu Samira,salima kuwa na tsaye tana bari kamar
wadda aka sheqawa ruwan qanqara a tsakiyar hunturu,tuni fitsàri ya gama bata
ta,Kallon da aliyyu yayi mata yasa a take wata gudawa mai dumi ta balle
mata,zuciyarta ta nemi tarwatsewa saboda tsananin tsoro da razani
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 9:51 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
3⃣9⃣ 3⃣9⃣
Wani lafiyayyen mari ya sakar mata wanda yasa jinta da ganinta ya dauke na wucin
gadi sai gata ta zube a qara warwas
Aliyyu kam bai ma tantance a wanne halin yake ba,mintina talatin doctor ya fito,d
sauri suka tunkareshi Tun kafin ya kai ga qarasowa
"Doctor ya ake ciki?"
Ya danyi Jim sannan yace"saidai Kuyi haquri,munyi iyà bakin qoqarimmu,amma Allah
bai qaddara........"
"Doctor! Doctor!, numfashinsa ya dawo"cewar daya Daga cikin nurse din,da azama
likitan ya juya ya koma cikin dakin,Kasa jurewa aliyyun yàyi ya riga masa baya
*Zakaran da Allah ya nufa da cara* cikin ikon Allah suka samu ya far fado
numfashinsa ya daidaita,nan suka bashi gado dakin mutum daya,kafin lokàciñ tuni
salima ta jima cikin cell
Duk Wanda ya zo dubiya sai yayi mamakin rashin imani irin na salimar,domin ana
zaton wuta ne a maqera sai aka sameta a masaqa,tuni jikin samira yayi sanyi
matuqa,Duk iskancinta abunda salimar tayi yayi Mutuwar dau4e mata kai,don a zahirin
gaskiya ba zata iya koda kwatanta hakan ba
Lokacin da salima ke musanta abinda ta aikata aliyyu baice komai ba,na'urar c.c.t.v
din ya dauko,inda take Adana bayanan ta ya shiga,tiryan tiryan har shigowarta cikin
dakin ta bayyana har yunqurin shaqe muslim,wannan ya zama hujja mai qarfi a
gurinsa,mataki mai tsauri ya dauka a kanta,inda yasa aka sakaye ta babu Wanda ya
isa ma yàje ganinta,babu yanda iyayenta ba suyi da shi ba yasa a fito da ita ko
kotu ne suje akan ajiyar da yasa aka yi mata amma yace ina bai da lokacinta,koda
zaiyi shari a da ita a yanzu ma to sai yaronshi ya warke,don Tun ba yauba take yin
yunqurin kisan kai tun Daga kan 'yarta iftihal
ya tabbatar ita tayi poisoning din fadilar a baya,ya sake gasgata hakan fada masa
da Samira tayi ganin da ta yi mata a bakin window din fadilà,ya sake hada hujjarsa
da irin firgicewar d yaga tayi lokacin da yake Sanar da haihuwar fadilan
Tun suna bashi umarni cikin gadara har suka dawo lallashi amma fir yaqi sauraronsu
sai suka dinga biyowa ta gun Momi da suka fuskanci abun na yi ne,
"Babu ruwa na don bani na Haifa musu dan ba,haqqinsu ne ba na wa ba"haka ta sanar
da su,suka yita Neman uncle abba da suka ga babu nasara ta bangaren Momi to shi
bàya qasar ma ya tafi turkey duba company dinsa na yin carfet dake can
Duk wuni gu Wanda suka San za'asa aliyyu ya fidda salima sunje amma abun yaci tura
*sawun giwa ya take na raqumi*,ba su da dukiyar da zasu kara da shi,bai bari an
saketa ba sai da yasa tayi attachment na wata uku cikin gidan yari😂,zama ne na
azaba da aiki mai tsanani,ta Fige ta palace kai Baka ce Salimar nan bace,nan ma
cewa yayi shari'a zasu fara uncle abba yace ya barta hakan ma ko don 'yarsu
iftihal,Kuma Allah ai ba azzalumin bawansa bane,zai musu sakàyyà walau a duniya ko
a lahira
Cikin station din da aka dawo da ita ya barsu,yana shirin bude motarsa ta
tareshi,yaja da bàya saboda wani shegen tsami da take bugawa,ta zube a gabansa tana
ya yafe mata sharrin shaidañ ne"
"Ta riga ta wuce,idan ba hakan ba ai da baki isa ma ki tsaya haka a gabana ba,Kuma
shaidan din dake zugaki kinga ai Abu yayi kyau kenan ko?,abinda zan baki shawara
kada ki kuskura ki sake yin gaba da gaba da ni,idan takàdarki ce kuma already na
danqawa d.p.o babu Kare bin damo"
Kafin ta sake ce wa wani Abu tuni ya shige motarsa ya bule mata idanu da qasa ya
wuce abinsa,a take a nan ta sulàle ta fadi sumammiya ,bata tashi farkawa ba sai a
gadonn asibiti,ta farka tana surutài da buge buge
"Ni aliyu zaiwa haka akan Fadila da tsinannun yaranta?,to wlh sai na dau fañsà"sai
da aka zurkuda mata allurar bacci aka samu sa'ida
Rayuwar gidan ta soma sauyawa,wata nutsuwa ce ta zowa samiran, son yaran take
sosai,Tun Fadila na Dari Dari har ta sàkar mata jiki,cikin lokaci qanqàni tad
fuskanci babu abinda ya cuci samirar illa tsantsar jahicin ilimiñ addini da
shàidanun lqawaye dake zugata,amma baya ga haka bata da wata illa
Aliyyu kam ya daukewa Samira wuta matuqa da gaske,don yace itàma bai yarda dà ita
ba,Mara baki ma ya aikata ina ga mai baki,kuka ta dinga yi masa tana rantsuwar wlh
ko kaza ba zata iya kàshewa ba,har tausayi ta bawa fadila,ta dinga masa mita kan ya
dainà yi mata haka,ita ta sashi ya siyowa samirar littattàfan addini ta samu lokaci
tana karanta mata,tun daga kan su ahlari,qawa'idi,iziyya,arba'una hadith,umdatul
ahkam,usulus-salasa dadi makamantañsu qananu wadanda za suyi mata sauqin fahimta
*_SHIN MENE MAKOMAR RAYUWAR SALIMA ANAN GABA?_*
*_amsar sai 'yan mutan huguma,kuci gaba da haqurin bibiyarta mun kusa da yardar
Allah_*
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 9:52 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
4⃣0⃣ 4⃣0⃣
Cikin ikon Allah ta soma fahimtar rayuwar da take abaya rayuwa ce mai cike da
jagwalgwalo da qazanta,tabbas rashin ilimin addini ciwo ne da bashi da
magani,makanta ce da ka iya yima mutum jagora Zuwa ga halaka,haka nan duk ilimin
zamanin da ba'a hada nemansa da na adidni ba sunansa kwado ko Kuma ince
jahilci,sannu sannu kuma zai iya kaika ga ramin da zaka gaza fitowa,ilimin dadi ni
gaske ne da kullum yake zamowa dan jagora ga rayuwar bani adam
⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜
Da aliyyu ya ga Fadila na Matsa masa kan Samira sai ya shirya musu tafiya su d
yaran,da tayi magana sai yace honeymoon zasu da ya alqawarta mata kafin ta
haihu,qasashe biya suka je,suka fara da saudiyya,Turkey, Egypt, Spain suka qarqare
da u.k
Honeymoon kam an shashi babu qarya,jiki da Zuciya duka sun huta,watansu hudu a can
alokacin su aslam na da wata biyar suka dawo,ba 'ya'yan ba hatta da iyayen sunyi
bul bul fatarsu ganin sha'awa,aliyyu aslam da Muslim da suke farare sun sake haske
tamkar ka taba su jini ya fito,Fadila kuwa da Islam fatarsu wuni lumi lumi ta sake
yi,da wuni dan haske na hutu da jin dadi
Sosai yaran sukayi wayo,sun San ummin su sunsan abbansu,idan ka ga su sai ka rantse
sun ninka watanninsu,bula bula da su,ga wuni she gen kyau da kwarjini da su ke
dashi,hakan ya sanya su ke da farinjini,duk inda suka shiga kaga ana sha'awarsu da
son daukarsu,maman ni su daya saka su ukun,babu ta inda suka baro aliyyu photo copy
dinsa ne illa Islam da ta biyo fatar babarta,sun samu uwa gwanar iya tsàfta son
qamshi da kwalliya,zanso mai karatu ka ga wannan family mai ban sha'awa
⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜
Ranar da suka dawo da daddare bayan ta yiwa yaranta wanka itama tayi sun shirya su
Kayi kwanciyarsu nan cikin dakinta kan gadonta,baba talatu Tun randa suka tafi tace
itama zata gida,babu yadda Aliyyu baiyi ta zauna ba tace LA,LA,LA,
Ya turo qofa dakin ya shigo da sallama yana hararar fadila,ta ams masa tana Daga
gira alamar mene ne?
"Kinbi kin kwashe min yara,kun barni ni kadai kamar wani màraya,ko tausayi na baki
ji"
Ta danyi dariya cikin lanqwasa murya
"banda abunka gun matarka fa zaka,Meye na Neman yara,me za suyi maka,abinda tun
dazun sukàyi baçci"
Harara ya manna Mata mai dauke da salon so,ya soma qoqarin haurowa kan gadon yana
ce wa"bari ni na kawo kaina tunda ni baqin jini ne d ni ba'a nemana,bayan nima in
buqatar a rungume nin,ba su Islam kadai ke so ba"
Zuba masa ido tayi bayan tayi kicin kicin da ranta,sarai ya lura da ita amma ya
share ta don yasan tatsuñiyar tazo bata wuce ta qoqi,ya janye Islam dake kwance
saman qirjinta ya ajjiyeta kusa da 'yan uwanta shi Kuma ya maye gurbinta
"Abbu(wani lokaci haka take kiransa,saboda haka tashi yaran sun fara gwarancin
kiransa),me yasa kake son yana ka zama haka bayan da ba haka kake ba,yaushe rabon
samira d kai,nifa tsawon wata hudu muna tare,me yasa kake son janyomin zargi da
zagi n........."
Ya katseta ta hañyàr fadiñ
"Masu zagin naki suje su yita yi,tunda ba su isa suyi a gabanki ba kinga Kansu suke
batawa lokaci"Daga haka ya hana ta furta komai
⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜
Da safe shi da yaran na zaune a living room Duk sun karade gun kai kace wasu masu
shekaru ne,dukkansu tsaf suke sai qamshi suke kamar yadda gidan nata ma baki daya
yake kasancewarta wadda bata wasa da tsafta,cikin kitchen take tana hada musu
breakfast don sun saba basu karyawa da wuri
Kallo su take cike da sha'awarsu,ta karbe Hannu aslam Daga gunsa ganin ya rasa
yadda zai da shi yaron akwai hanzari,gashi yana ta qwalawa Fadila kira tayi banza
da su ya sani fushi take tun jiya,gyara masa jiki tayi tas,ta dawo tayi zaune
cikinsu tana masa wasa yana bangala mata dariya
Ta dire kwanukan abincin bayan ta fito Daga kitchen din tana Kallon yadda suka
bararraje su na biyewa yaran,sai taji ma kunyar samirañ ta kamata
"Lallai kam,sannunku kun samu aiki fa"
"Ina ruwa wuni,tunda mudai bamu ce ya zo ya taya mu ba"Tasan tsokana yake sonyi sai
taqi Kallon Duk da nacin son ganin qwayar idonta d yake,ta maida kanta gun Samira
su na Gaisawa,har ga Allah taji dadin ganin canji sosai gun samiran,don kafin
tafiyarsu bata bari karatunta ya yanke ba,da kanta taje *Darul hadith* ta yanko
mata foam bangaren kayan aure weekend kawai Tun Daga aji daya
A nan ta sauko musu da break din sukayi tare,samiran ta tayata suka gyara gurin har
kitchen ta bita ta tayata suka wanke kayan suka dawo parlour din,tana lura da yadda
aliyyu ke ta jifan fadilar da kalloñ qauna tana share shi,addu'a take cikin ranta
Allah ya bata haihuwà ko ta samu kwatar son da aliyyu ke wa fadila(hmmmm,batasan
abun Daga Allah bane)
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 9:52 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
4⃣1⃣ 4⃣1⃣
Ya miqe bayan ya kwantar da Islam da tayi bacci aslam da Muslim nata wasan su gun
Samira
"Madam tazo a shirya ni ko, zan fita"ya fada Kansa tsaye yana wuce wa cikin bedroom
sonta,share shi tayi taci gaba da hirarta da Samira don ta fuskanci so yake ya bata
kunya,bata Ankara ba sai ji tayi anti sama da ita sai bedroom, zillo ta yi ta dira
daga hannunsa
Cikin harara take ce wa"mene haka abban islam?"cikin gintse dariya yace
"Lallai yarinyarnan,ni zan kira ki ki wani jamin aji?,zaki San da Ali haidar
kike"yayi guntà gaba daya,ba zata ita hana mishi farincikinsa ba don haka ta
qyaleshi ya share budirinsa,bayan sun fito wanka Kuma ya tsareta yace babu inda
zata sai ya gama shirya wa sa fito tare
"Amma fa mun bar su Muslim da mummynsu a falo ko?"
"Basa nan"kawai yace da ita yana ci gaba da shirinsa tayi zaune kuwa taqi taya shi
sai kumbura take
Tana kallonshi yana kici kicin saka socks da takalmi,dariya ta so qwace mata amma
ta maze, ta gama shagwabashi koma ita ke masà a yanzun bai iya koma ba,ya lura da
ita d9n haka ya lakuto cream mai yawa ya yaba mata a kumatu,ta juyo tana sake hade
rai kamar gaske
"Kin bata ni da yauwa,shirya ka ina ma yanzu gagara ta yake,ke Kuma kin zauna kina
min dariya ko?"bata San lokacin da ta fas he kuwa da Dariya ba ganin yadda ya wani
màrairaice mata,sai ta hau shirya shi kamar yadda ta saba
Da suka fito falon babu kowa,aliyyu ya leqa dakin yaran sai Islam kawai da ke ci
gaba da baccinta nisa gadonta,da a lama su na gun samirar,har Mota ta raka shi
kamar yadda ta saba,yace su shirya anjima idan ya dawo zaya kàisu su Gaida momi,ta
ams masa na siru ya ja Motar suka fice,sai da ta leqa sashen samira ta tabbatar
suna can tace"yauwa mommyn su aslam,tunda su na nan bari nake na fidda kayan
tsarabar can"
Murmushi tayi "ba Matsala idan kin gama sai Kiyi kirana ,dama ina son
ganinki,sirrin tsafta kwalliya da kula da miji nake so a bani"
Murmushin itama tayi mata"to shikenan ba Matsala"ta juya ta fice tausayin Samira na
damunta tare da jin rashin dadin yadda aliyyun Yaqui sakewa da ita
Momi ta rasa inda zata sai jikokin da surukan nata,iftihal 'yammata Duk ta rude
anga qanne sai ta dau wan can ta Ajjiye ta dau wannan,Daga momin har uncle abba
sunyi mamakin sauyawar Samira,suka sake addu'ar Allah ya kade fitina yaci gaba da
hada kansu,tsaraba sosai ta yiwa Momi da iftihal har da uncle abba,sai goma na dare
suka tafi
ya ajjiye mata yaran ya fiya da niyyar bada umarnin a kulle gida,tuni kafin ya dawo
ta kulle sashenta,Tun yana danna bell har ya dawo bugu tayi masa biris,wayarta dama
a kashe take tilas ya haqura ya koma,da safe tana Kallon yarda yake aiko mata da
saqon harara,ta share shi kawai tana dariya,don idan bata yi masa haka ba sai a
shiga haqin samira,Daga qarshe sai da yasa yadda yayi ya biyota kitchen taci
zalinta"gobe ma ki kuma"yace da ita
Wannan karon ziyarce ziyarce sukai har Maiduguri gurbin hajja gaña,farida ta so
Zuwa saidài babu dama sanda tsohoñ cikin da take dau ke da shi,sai humairà ta bada
aka tafi da ita,tayi Sa'a kuwa ya zo a daidai bikin diyar qanin abba,aka sha biki
da ita,kuwa sha'awar Fadilan yàke,Duk inda ta gifta sai ta fita daban cikin
mutane,wanda ma ya Dade bai ga Fadila ba yau ya gañta har da 'yan uku,don idan Baku
manta ba farida dama na mata tsiyàr kafin rijiyà ce,ba Zuwa take sosai ba faridan
ta fita zuwà
*Mrs Muhammad ce*👑
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 9:54 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣1⃣
*_CONTINUATION_* 4⃣1⃣
Da qyar ta cinye kwana biyar aliyyun ya azalzaleta ta dawo shikam ya gaji haka
nan,gidan ya zama masa kango,haka suka dawo cike da farinciki don ta faranta wa
danginta sosai su Kuma suka cikata da tsaraba
Rayuwa mai kyau da inganci mai cike da tsaftatacciyar Soyayya ce ta kewaye aliyyu d
iyalinsa,tana ita bakin qoqarinta na ganin ya saki jiki sosai da samirar sai dai
har yau bata kai ga cimma ga ci ba,Duk da ya rage wasu abubuwan
⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜
Cikar Muslim aslam da Islam shekaru biyu samira ta hada musu gagarumin birthday
party,ita kam fadilah nata kallo don tuni suka maida ta 'har Kallon,wannan Abu na
daya Daga cikin abinda ya s aliyyun ya sake dan saukowa d samirar,don su Kansu
yaran sunyi Matuqar sabo da ita
⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜
Suna gadon baccin su bayan sun gama komai na shirin kwanciya,duka yaran na gun
samira don yawancin lokuta idan ranar Fadila ce to ita ke kwashesu tace zasu tayata
kwana
Envelope aliyyu ya miqa mata bayan ya hade girar sama da ta qasa,ga bata ya fadi
tabi envelope din da kallo,cikin sarqewar Murya tace"n......na
meye.....wannan?"cikin tsawa yace "bude mana ki gani"cikin rawar jiki ta sure ta ta
farke,dan qaramin ihu ta saki,ta Daki tsalle ta daneshi,Duk ta rude,shikam dariya
yake ta mata har da qwalla wait da har idan guntà sun fito waje sunyi hudun na su
Muslim,Sam bata bai ta kan tsiyar da yake mata ba,foam ne na jami'ar Bayero
university degree na biyu zata yi kan mass comm
Ya dubeta bayan ta natsu"ki dai na yimin godiya my life,har yau inajin ban saka
miki irin tarin alkhairi da haqurinki gareni ba"haka an aliyyu yake mutum ne mai
rama alkhairi komai qanqantarsa,cikin nasara karsashi qarfin gwiwa da nishadi ta
soma karatunta
,bata da matsalar koma,yaran samira ke kula mata da su,idan lecture ta fado a
weekend itama samira na da Darul hadith sai su taba ita ta dau biyu ta bata
daya,ganin haka ma sai Aliyyu ya niqi gari da kansa ya tafi gombe ta tattago baba
talatu da taqi dawowa,d year ta amince ta biyoshi,don tace bata son zama tsakiyar
rayuwar auren yara
Ganin haka yasa cikin gidan Daga can baya aka zuba fasalin irin ganin gidajammu na
ga gajiya mai tsakar gida da dakuna aka yi mata nata gidan Duk da ce wa akwai part
din da salima ta bari da Kuma wani spare daban amma tace bata sonsu sun mata zamani
da yawa,dariya Fadila da samira suka dinga mata tace eh ta ji
⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜
Tubure masa tayi har ganin samiran,murmushi tayi babu damuwa a tartare da ita"Kuyi
tafiyarku abba Islam rabu da ita,ranar da zaki tafin ma Samu fara jarrabawa,kinsan
Samu shiga s.s one mun zama seniors ba raini"
Sai ta bawa fadilan dariya,har yanzu fadar magana kai tsaye da calikancin samira na
nan tare da ita,sai dai wannan karon yana tafe ne da burbushin ilimi
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 9:56 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
4⃣2⃣ 4⃣2⃣
*ina salima?*
Qunci da baqinciki babu Kalar Wanda bata ji ba shi cikin zuciyarta,na farko rabuwa
da abinda tafi so Duk duniya wato aliyyu,na biyu Kuma rashin cimma burinta na raba
fadila da 'ya'yanta daga sheqar iskar duniya,gash a yanzu babu wata kafa da zata
sadata da cikar muradin nata
Ba tare da ta gama idda ba aka daura mata aure,tun daren da aka kaita ta soma gane
kurent,kwana auwal yayi yana Abu daya,Duk bakin tsiwa da rashin kunya ya mutu
murus,haka nan tana ji tana gaji ya gama budurinsa,dama auwal ya dade yana
sha'awarta,taqi bashi hadin kai ne Tun farko saboda tana ganin ta zarta ajinsa,sai
kyau ya samu cimma muradinsa
Wata daya na cika ta same shi da zumudinta ta tunasar da shi lokacin rabuwarsu fa
ya cika,wata mahaukaciyar dariya ya bushes da ita sannan yace
"Amma bansan ke daqiqiya bace sai yau,in banda ke mahaukaciya ce kina tunanin zan
sake ki ne?,to ki sani Kinyi kuskure,auremmu kuwa mutu ka taba takalmin kaza"
Miqewa tayi a fusace tace"tabdi,lallai auwal ka ga dama ta,to wlh bari kaji,ko Baka
qaunar Allah sai na bar gidanka,ai Kaine babban mahaukaci,banda haka ai ko makaho
ya Shafa ni ya shafaka yasan nafi qarfinka wlh,ni ba'a halicceni don nayi zàman
aure da kowa ba sai aliyyu jar......."
Gif!,tashi a bakinta,kafin ta qarasa tuni auwal ya dunqule Hannu ya Daki bakin,tuni
gurin ya haye ya suntume jini yace salami alaikum,bata gama tantance barnar da yayi
mata ya bita ya turmushe ta da duka tamkar wanda ya samu qato dan uwansa
Tun tana qoqarin ramawa har ta dawo sai zagi,qarshe bakin ma ya mutu,sai da ya gaji
don kansa sannan ya qyaleta,ya dago yana haki
"Shegiya qaramar 'yar iska,ke har kin isa ki bude kice na sakeki ki koma gidan
wancan dan iskan da na sha wuya a hannunsa saboda ke,to gobe ma idan kin cika 'yar
iska ki Kuma yimin makamanciyar wannan maganar,ke da fita daga gidan nan sai dai a
fidda gawarki"ya tsallaketa ya fice abinsa
Sai da taci kukanta ta qoshi sannan ta ja jikinta sannan ta hada kayanta a trolley
tayo waje,sai da tazo har soro saidai abun mamaki tayi tayi ta fita ta Kasa kamar
wadda aka daure da Sarqa,a ranar dai tayi yunqurin fita ya kai sau ashirin amma da
zata ta zo soro sai tashi kamar an riqeta,qarshe ta fas he da kukan baqinciki ta
zube a soron tana hango wajen amma ta kasa fita,
Cikin wata biyu ba izayar da salima bata gani ba,gashi ko Karen gidan su Yaqi
Zuwa,bata sani ba auwal ne yasa aka kadar da hankalinsu,ko tunaninta basu yi
A hankali cimar gidan ta canza sai qarma qarma kawai,auwal a qarqashin wini alhaji
sabo Alfa dake cikin kasuwàr kantin kwari yake,ya dade yana cutarsa ta hanyar sace
masa manyan kudade yasa an rufe masa ido bai gane ba,auwal bin malaman tsubbu gunsa
ko mace ta shafa masa lafiya,da kudadeñ yake burga cikin Garin tamkar ubansa wani
ne,daga baya da Allah ya yake alh sabo ya gane ya koreshi kudin Kuma da ya sata din
da yake ba ta hanyar halal aka samesu ba maimakon ya tattala sai yaci gaba da
harkar banza da holewarsa da su har suka soma qarewa
Allah qadiran Ala may yasha'u,cikin hikima ta Allah sai ga cikin auwal jikin
salliman,sai Allah ya dora mata son cikin,tana son ganin gudan jiñiñta a yanzu
tunda ta fuskanci rayuwar na dab da juya mata baya,sai dai inaaa.....ba'a yiwa
Allah wayo,domin a baya taqi cikin a lokacin da uban dan keson abinsa,to a wannan
karoñ Kuma sai ta so cikin a lokacin da uban cikin bai buqatarsa
Har gida auwal ya dauko wani inyamuriñ likita har da kayan aikinsa,ya danne masa
salima yayi mata allurar kashe baki,tana ji tana gani aka zurmuqa mata qarfe aka
zuqe cikin,kai qarshe ma yasa aka gutsire mata mahaifar ma dungurun gun,a cewarsa
bai da buqatar wata haihuwa,ta rasa lokacin da zata fara haihuwa sai lokacin da ya
fara fama da kansa.......
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 9:56 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣2⃣
*_continuation_* 4⃣2⃣
Saura qiris salima ta bar duniya amma da yake akwai sauran shan ruwanta a gaba sai
ta warke,tayi kuka tayi nadama da Dana sani maras iyaka,taso kashe Fadila da
'ya'yanta sai gashi ita tana eaten amma tayi Mutuwar tsaye,taqi ta Kuma wulaqanta
kyautar da Allah yayi mata lokacin da ya bata cikin iftihal,aliyyu ya biya da
lallashi sai ganshi yanzu da uwarta da ubanta aka bai aka zage sannan aka qwaqule
cikin ,maimakon ma ya dauki iya ajiyarsa sai da ya hada da ajiyar Allah yasa aka
guntile mata mahaifa
"Ashe dama haka rayuwa take?,Ashe Wanda yaqi zaman gidan aurensa ya rains matsayin
da yake kai ya butulcewa ni'imar Allah yaqi daukar ixina ta ruwan sanyi duniya zata
biyar da shi?
A yanzu take sake qaunar gudan jinin nata qwaya daya tilo iftihal,Ashe ita ka dai
ce qwanta a duniya?,ta yima aliyyu addu'a sosai da ya tsaya tsayin dauka ya hanata
yasar da cikin iftihal din,da tuni ta tashi a tutar babu kenan?,qaunar 'yar take
sosai sai dai ta sani babu qaunarta ko daya a Zuciyar yarinyar Wanda ita ce sula
ita ta haifar da hakan,wannan shi dake kira da Dana sani qeya ce
⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜
Wannan ce rana ta qarshe Kuma company na qarshe da aliyyun zai qarasa bude
wa ,dukkanin yaran nata uku sanye suke cikin sutura iri daya sai dai su maxan na
maza ne Islam Kuma na mata ne haka aliyyu ke sawa ana musu,tuni Muslim da aslam
suka saje cikin fararen fata su da abbunsu,Fadila kuwa shigar babarbariyar usuli
tayi (kanuri)cikin lafiyayyar laffaya maroon tayi mata kyau matuqa,sosai ta burge
mutanen sin har wata Daga cikinsu mr.shengping ta Kasa shiru har sai da ta yaba
family din na su
An tashi taro lafiya baya ga kyaututtuka da suka samu masu tarin yawa Daga abokan
kasuwancin aliyyu,direct gidan mukhtar (abokinsa)suka wuce,a can suka ci gaboncin
dare,Fadila na tare da matarsa Aisha suna hirarsu abinsu,Islam tayi bacci ita da
Muslim,aslam Kuma na gun abbansa a parlour su na lissafe lissafe kan company din
Fadila da irin ribar da aka samu
riba ce mai tarin yawa,da Kansas mukhtar ya shiga ya kirasu fadilan,sun soma mata
baya nin irin ribar da aka samu,Tun tana dauka har kanta ya gaza dauka,sai ta sai
kuka irin kudaden da dake ambato mata sunfi qarfin kanta,ace kamarta ba 'yar wani
ba ta mallaki irin wadannan kudaden a matsayin riba.......
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 9:56 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?.......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
4⃣4⃣ 4⃣4⃣
Ya duba littattafansu na makaranta dayake wuni lkc shike dubawar,ya taimaka musu
sukayi assignment, da suka bude na Arabic don son ya tsokaneta sai yace"kai kai
'yan uku wannan yafi qarfina,wannan ai sai balarabiyar mamarku,Ku kai mata maza"
Suka kwashi littattafan sai aslam ya noqe jikin abba nasa don tsoron zuwan yake ji,
To Ashe bata sani ba ta tada masa tsohon miki,don haka ransa ya dugunzuma,ya
ranqwafo wait in fuskarta"oho......alright, to wa ya sani ma ko ke kika hana kanji
sake dauka ciki tsowon wadannan shekarun don wadannan ma baki sonsu ko?"
Wani wal tayi da idanunta ,batasan lokacin da bowl din fruit salad din ya subuce
Daga hànnunta ba,mai aliyyu ke nufi?,zarginta yake yi ko me?,a guje tayi bedroom
dinta saboda wani kuka da ya qwace mata
Yana tsaye a gun ya bita da kallo,jikinsa yayi sanyi,sai yace jin baiyi furucin da
ya dace ba,sautin kukanta da ya soma ji sama sama ya sashi zabura ya nufi
dakin,saidai kafin ya kai gareta amai yabqwace mata,ta kuwa dinga kwarashi,Duk sai
da tayi aaman fruit salad din da taci,gaba daya ya rude fadi yake"am sorry my
queen, sannu kinji"shi ya gyàra gun ya sai Mata ka6an bacci,Duk fuskàrshi ta canza
kamar zai sai mata kuka,haka shim a ya gama nasa shirin baccin ya jawota ya manna
ta da jikinsa,
Kalaman ban haquri yake ta jeranta mata,sai dai taqi ce wa kanzil,kai Daga qarshe
ma sai ya juyata yaga ashe tayi bacci,ya sauke gajiyar Zuciya ya sake rungumeta
yana jin rashin kyautawarsa har cikin zuciyarsa
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 9:57 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?.....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣4⃣
*CONTINUATION* 4⃣4⃣
washe gari asabar ce bai tashi da wuri,hakanan bai fita da wuri sai kusa da wajen
azahar,don haka ta lallaba ta gama aikace aikacenta ta fice gun baba talatu wadda
ta dawo a Daren jiya,nan suka shiga hirarsu tana bata labarin tafiyar da tayi
Ko da ya farka bai ganta ba yasan tana can,sukuku ya shirya don ya saba ita ke masa
komai,wuraren daya ya daga Waya ya kira nasiru yace yaje ya dauko masa su Islam
daga gidan momi wadanda da sassafe suka addabeshi sai da aka kaisu,Fadila na jinsu
bata ce musu komai ba a lokacin
Hannunta riqe da kwanon zogalen da da baba ta kwadanta tana ci suna hirarsu cikin
nishadi har da dariya, ganin shigowarsu kawai tayi suna rigen rigen fada wa
cinyarta banda aslam da ya rakabe,batayi tsammanin dawowarsu haka da wurwuri ba,sai
yaron ya bata tausayi amma sai ta dauke kai,don kaxa na take ranta ne ba don bata
sonshi ba don ta koya masa darasi ne, duka yaran suka gaidata suka Kuma gaida babar
kamar yadda ta saba musu Gaisa babba,shima aliyyu suka Gaisa yayi mata sannu da
hanya tare da tambayarta mutan garin
Sai ya kalli baban yace"baba Zuwa mukayi ki taya mu roqo,'yarki muka yiwa laifi
Kuma taqi yi mana afuwa"
Baban ta kalli Fadila"a'ah,ni kam na San 'yata bata da riqo,ba shakka laifinku mai
girma ne,me kuka yiwa diyata?"
Da sauri Fadila ke girma aliyyu inkiya da ido na yayi shiru don Allah amma Sam sai
yaqi kulawa
,"baba,aslam ta daka har jikinsa yayi shatin bulala,Kuma suka shige ciki suka
barshi a waje,to nayi fada ne har ya wuce kima,na gane kuskure na na bada haquri
amma anqi yafe mana,sai ake mana horo da halin ko in kula"
"Sannan da ance za'a hukuntashi baban ya hana,to don kawai fa rannan na hukuntashi
suka dau fushi ya kwashe kayanshi ya maida gun mominsu,qarshe ma harda cemin wai wa
ya sani ko......"sai ta kasa qarasawa hawaye ya subuce mata,ai bai san lokacin da
ya isa gareta ba,hannayensa ya sanya yana dauke hawayen,sai baba ta yunqura ta miqe
ta fice tsakar gida,don ta lura abun nasu salon maganar nan ce da ake cewa *fadan
masoya hutu ne ko sunyi zasu dawo su shirya*
Yayi Kane Kane ya hana hawayen zuba"kada ki yimin haka mana Fadeelah ta,na riga na
yima ka ina alqawarin fa ba zaki sake zub da hawayenki ba,kinsa alqawari na ya
karye?,jiya Kiyi daya kyau kinyi,ina jin zuciyata cikin qunci duk sa'ilin da naga
hawaye a fuskarki,pls ki yafe mana,ni da 'ya'yana bamu saba ganinki haka ba kina
hukuntamu"
Sai ya juya gun yaran ya kira su da hannu"Ku zo mu bawa mamee haquri"ai kuwa suka
yaso da saurinsu duk suka durqushe a gabanta yadda suka ga abbun na su yayi
Aliyyu dake kallo su cike da sha'awa ya Matso yana turo mata kansa"Nina mamee a
samun albarkar"cikin hararar Soyayya take kallonshi
Sai ya kwabe fuska shims kamar tarin"kunga maminku taqi shafa min kaina ko?"
Nan suka rude da ce wa mamin mu a shafawa Abbu shima,dariya tayi shima ta shafa
masan
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 9:57 AM] My Mom: * 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
4⃣5⃣ 4⃣5⃣
Sai lokacin baba ta dawo,taji dadin ganin sun sasanta kansu ,nan taja hankalinsu su
duka har yaran,cikin gamsuwa sukayi mata godiya
Ya kalli fadilar cikin marairaicewa"to ataimaka azo a yimin Garin pepper chicken
din nan mana mai dadi, ni da abokaina duka zamu tayaki aikin"
Ta noqe hancinta tace"a dauri kashi ko a bata igiya,babu abinda kika biya sai qara
wa mutum aiki"da sauri Islam ta kalli mamin nata tana nuna kanta da yatsa"banda ni
ai ko mamee?"
"Har ke mana"jin haka yasa su Muslim suka qyalqyale mata da dariya,sai ta kwabe
fuska ta soma diddira qafafu kan Dariya da su Kayi mata,aliyyu ne ya taba fadan ta
hanyar daukarta ya sabata a kafada aka tafi yin paper chicken din baba talatu ta
musu a dawo lafiya bayan sun mata tayi Zuwa tace lazumi zata yi sai sun dawo,islam
tace zata kawo mata qashi,Duk suka sa dariya
Haka suka cikata da surutu cikin kitchen din,ba ga yaran ba ba ga babansu ba,aiki
dai na surutu kawai suka tayata ta,har ta samu ta gama ta tura musu,ya tasa
yaranshi a gaba bayan kowannnensu ya wa ke hannu suka soma ci cikin plate guda
Sai da suka ci kusan Rabi sannan ya dubeta tana zaune gefensu tana lura da yanayin
can abincin yaran nata,Duk Wanda ya gutsuro kafin ya ci sai ya miqawa abbunsa,
yaran na da matuqar son iyayensu
"Ke baki ci ne mamee?"
Ta zumburo baki "sai da ya rage saura qasusuwa wannan za'a yimin tàyi?"
Sai suka soma rige rigen bata a baki,kuwa yana ce wa nashi zata ci
Murmushi ta saki tace musu duka ta gode,Allah ya yi musu albarka ita ta qoshi,taci
zogale gun baba,aliyyu yayi qasa qasa da Maurya bayan ya dubeta"anya baby na lafiya
qalau kike?,ina lura dake rashin son cin abincinki ya qaru akan na ainihi,fruit
salad kawài kike bawa muhimmañçi,anya ba wani cikin gareki ba?"
Kai tsaye ta Daga masa gira tana murmushi,cikin zumudi har baisan sanda ya daga
murya ba yace"are you serious baby?"
"Yes"tace da shi cikin wata iriyar murya mai taushi
Ya lumshe ido a fili yace"alhamdulillah,alhamdulillah"
Sai ya tara yaran yana fada musu sun kusa yin qani,ihun murna da tsalle suka dinga
yi abbun na su na biye musu,ta saki murmushi bayan ta dau ke idoñtà daga Kansu
Gaba daya aliyyu ya maida yaran abokanshi"
⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜
Rayuwa mai cike da jin dadi amunci da qauna suke yi cikin gidan,tuni ganin gidan
rediyon Fadila yayi nisa,Wanda bai da nisa da qatuwar islamiyya da dake gana wa
samira wadda totally yanzu ta can a idan ka gantà zakayi mamakin yadda ta
sauya,ilimin addini sosai ya ratsatà
A nurse aliyyu ya zauñàr da Fadila yayi mata ba yamin abinda yasa yake ma Samira
haka duk da a yanzu ya soma daidàità lamuran,yana son ya gane turban muzuru tayi ko
na gaske,saboda canza mutum haka lkc guda sai Allah,zata iya zama da shi cikin
kowañne irin halin kamar yadda ita fadilan tayi a baya?,ta Kuma shirya can a tsarin
rawarta ta xamo ta dace da ra'ayinshi da tsarinshi?,
"Hakan ya tabbata ai tunda ga zahiri kana gani ko"
Tace da shi
Cikin ikon Allah Fadila ta dauka lafiya,ta samu qatotoñ lafiyayyen yaronta Wsuna
yaci su na *ABUBAKAR ASSADDIQ*,don su abba ba masu damu wa da wani takwara ne ba
Ganin dai da gaske su aliyyu na shirin basu kashi yasa ba shiri fadila ta radawa
iftihal yake tavtaho da mommy(samira) don itama gwanar table tennis ce,sai kuwa
gata tsaf a shirye cikin kayan sport din,su aslam suka sa dariya,aliyyu yace"Duk Ku
gama taron danginku,kun sani mune winners ba yau aka fara ba"
"Wlh kuwa abbu"inji aslam
Cikin ikon Allah sai su Fadila suka cinyesu,gufa ya rude iftihal tace"shikenan
daddy,mume da ikon zabar qasar da za'aje hutun qarshen shekara"tavfadi tana yiwa su
Muslim dariya don ra'ayinsu ya ban bata,haka suka haqura da akaxo dinner suka
zaba,wannan karon a Africa za suyi don haka iftihal ta zabi South africa,samira ta
zabi Ethiopia tana son taje taga garin da sarki najjashi ya mulka,suka tsara
tafiyar kuwa da tafiyarsu saudiyya sauke farali
A Daren aliyyu yasa Fadila ta kira farida tace"gobe driver ya kawo humaira ta tayi
da passport dinta za'a buga mata visa din qasashen da zasu,tunda tuni abbanta ya
buga mata ta saudiyya,jinin aliyyu ya hadu da na yarinyar sanda kama da takeyi da
fadilansa,shi yasa duk hutun da su ke fita da ita ake tafiya,ko unguwa fadilan zata
wani lkc ta fita da humairar da Islam sai ayita dauka humairar ta Haifa ba Islam
ba,don ita Islam da abbanta tayi kama
Duka family ukun da su aka saukre faralin bana,yarda Anty hauwa da iyalinta,scan ne
Fadila ta so lura kamar amai wani Abu tsakanin iftihal da Muhammad(qaninta)sai dai
bata tanka ba,ta barwa ranta ne idan lokaci yayi zasu nuna kansu
Daga saudiyya suka wuce hutunsu na qasashe biyun Hutu Kayi mai dadi sosai,Hutu ne
da Iyalan suka dinga ji dama kada ya qare,ciki yarda samira domin tuni aka 'yantà
ta,sai dai ta riga ta sani ta Kuma saddaqar Fadila ta riga ta yi mata fintikau,tayi
mata zarrar da ba zata iya kamota ba ta kuwa ne ganin,saidai ita kanta tana jin
dadin yadda tayi wata ta canza,Allah ya nufe ta da gane gaskiya tun lokaci bai qure
mata ba irin yadda ya qurewa salima,tana Kuma sake yin addu'a ga Fadila don kaso
casa'in na gyaruwar rawarta ita ta bada gudunmawa
To Tun a can Fadila ta soma jin canje canje a jikintq,sai dai tayi shiru da
bakinta,suna dawowa gida duka sai suka kwanta ciwo ita da samiran,til as doctor
sa'adah ta ziyarci gidan,bayan gwaje gwaje ta shaida musu *duka su biyun suna dauke
da ciki*,kuka Samira ta dinga yi haiqan tana gode wa Allah cike da yabo na yadda
bai dubi halàyenta ba na baya da kurakurenta ba ya azurtata da samun qaruwa
Kasa zama Fadila tayi Duk da jirin dake dibanta sai da ta taho bangaren samiran,ta
rungumeta cike da farinciki,jin sumbatun da samirar keta yi ya sanya ta hanata
magana tace
"Shi Allah babu ruwansa,Mutuwar Kayi tuba tuba mai kyau to zai gafarta maka
zunubinka komai yawansa ko da shirk a ce indai Baka mutu kana aikatawa ba"
Tsananin farinciki ne ya rufe aliyyu,Duk da yaran dake gabansa amma ninkinsu yake
buqata,taga kulawa Daga kuwa wadda bata taba katarin gamo da irinta ba
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 10:01 AM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
4⃣6⃣ 4⃣6⃣
Haka suka dinga rainon cikinsu,sai dai Samira lamarin sai a hankali,yau da lfy gobe
babu,wata bakwai daidai cikin nasu samira ta soma wani irin ciwo Wanda ya tilasta
yi mata c.s aka cire mata yarinya mace aka sanyata a kwalba,saboda yarinyar tayi
nauyin da mahaifarta ba zata iya ci gaba da daukan yarinyar ba saboda laushin da
tayi
hakan ne ma yasa bayan cire yarinyar aka juya mata mahaifar don doctor tace Duk
lokacin da ta sake dauka ciki tayi wata na cikin hadari,za'a ita rasata gaba
daya,mahaifarta tayi rauni sakamakon maganin hana daukar ciki da zubar dashi data
dinga dirka a baya ba bisa qa'ida ba
Cikin ikon Allah ta warke sumul taci gaba da shayar da diyarta Fatima(zuhra),ba
dadewa aliyyu yasa aka soma gina mata super market qato ne sosai,bayan kammalà
ganin aka zuba komai ciki ya soma aiki yàna dauke da sunàn *zuhra maitama shopping
mall*
Wata goma sha daya wannan karon fadila ta santalo 'yan matanta kyawawa guda
biyu,wannan karo sai dayar tayi ta sak tamkar humairar farida,dariya aliyyu ya
dinga yi mata"babe kinga da daya fa kika tsira cikin yara takwas,to ban sani ba ko
a gaba qila ki sake tsira da gudà ko?"
Ta bata fuska"gaba dear,gaskiya ni na gama haihuwa kam daga wannan ai nayi
qoqari,idan na ci gàba da yi ai sai na lalàce kaga kaji dadin auro mana wata ko"
Lakuce mata hanci yayi yana qasaitaccen murmushin nan nasa da har ysu bai barin
fuskarsa Mutuqar yana tare da fadilan tasa"ban taba ganin Mace iriñki ba baby na,ko
yàushe qara miki kyau ake tamkar ba ke kika haifi wadannan zaratañ ba har takwas"
Kallo mai cike da qauna tayi masa "har na kaika?,ni fa har tsoro ma nake kada wata
ta qyalla ido ta qwace mana kai"
Dariya ma ta bashi"indai wannan tsoroñ kike to ki kwanta kiyi bacci harda
minshari,ni aliyyu ba kowacce Mace a gabana zuciyata da ruhina sai ke,Duk kallo su
nake tamkar maza 'yan uwana"
Sosai maganar tasa ta fasa mata kai
Take ya yiwa yaran huduba da sunan umminta amina,dayar Kuma yama faridanta takwara
kamar yadda mubarak ya yiwa fadilàrsa takwara,hakan ya faranta ran fadilan,Islam ta
musu laqàbi da *afrah da amrah*
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 5:32 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 3*
4⃣7⃣ 4⃣7⃣
*my lord,have mercy on them both as they did care for me when I was little,
ameen*👏🏻👏🏻
Bayan ya shigo ta nemi gafararsa,Fadila ta hanata gaya mishi komai,shi dai yace ya
yace,godiya ta dinga masa tana zub da ruwan hawaye
Da suka tashi tafiya tamkar ta busy haka ta dinga ji sai dai ina ba hali,ta dinga
rings su da kallo cike da sha'aea yadda 'Yan Mayan keta karakainar duba gyaran
gashin su jikin mirror
Fadila tace ta sameta a gida bayan kwana uku don gobe da jibi basa nan,ta danqa
mata rafa ta 'yan Dari biyar biyar guda daya,godiya ta dinga mata tamkar ta kife
⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜
Ranar juma'a ce,Duk a parlour din Fadila ake haduwa aci abincin rana bayan sakkowa
sallar juma'a matuqar ogan na gari,tana kitchen ita da 'yan matan ta tana ba su
warmers plates da cups su na kaiwa kan dining suna shiryawa,ta cake cikin kwalliya
tamkar ba Daga jikinta wadannan 'yan mata da samarin suka fito ba
Cikin barkwanci hira mai dadi irin ta familyn da suka fahimçi junà suke cin
abincin,kowa tsaf yake cikin kwalliyarshi,sai dai kam aliyyu babu adon Wanda ya
burgeshi irin na tauraruwar tasa fadila,sallamar da aka kwada sau biyu cikin falon
taja hañkalinsu,tuni aliyyu ya Ajjiye lomar abincin da ya Kai bakinsa,samira kuwa
zumbur tayi ta miqe dafe da qirji ido a waje,Fadila ce kadai ta kalleta da
sakakkiyar fuska ta kuma sauko daga dining area din tana mata marabà
"Me kika zo yi gida na?"aliyyu ya fada cikin Daga murya take jikin Salima ya hau
bari,don har kyau ba5a manta Waye aliyyu salim maitàma ba
"Ko kin biyo su ne a yañzun ma ki dauka ki kashe?,ina mai baki shawarar ki fice Tun
muna shaida juna,don baki da alaqà da kowa a cikin gidannan"
"Wlh kuwa kada ta cuce mu ba,ta cutar mana da yara"inji samira da ta Kasa zama
Fadila ta dan bata fuska tana kallon su"gaba Abby pls mana"
Shima ya sake hade rai"cewa fa nayi ta tashi ta fice,tunda dai ai ba gidan su bane"
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 5:32 PM] My Mom: *WA YASAN GOBE?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*CONTINUATION 4⃣7⃣*
4⃣7⃣
*_I DEDICATE THIS CONTINUATION TO MY SISTERS AND BROTHERS, SONS AND DAUGHTERS OF
ALH ABDULLAHI MUSA HUGUMA*😍😘
*AS'ALUL LAHA TA'ALA AY YUWAH HID SUFUFANA*👏🏻
Ta dakatar da samira dake qoqarin rufa musu baya,ido dai a waje ta kalleta tana
nuna kanta
"Ni?,ai Nima din ai ba tsayuwar zanyi ba wannan ai tauraruwa mai wutsiya ce,banda
mana da saura shan ruwa a gaba ai da tuni muna kushewa,zan dai tsaya a waje idan
naji kina buqatar taimako na kawomiki"tasa kai ta fice
⚜⚜ ⚜⚜ ⚜⚜
Bata sake ce masa komai ba kan abinda ya danganci salimar ba sai ranar dabgirki ya
sake zagayowa kanta,sai da suka zo kwanciya sannan ta Sanar masa qudirinta,tana so
a kayan da akeyi a company dinta ake kawowa nijeria tana rabawa samira da farida ta
saka Salima a ciki,sannan tana so ta Gyara mu'amala da alaqar dake tsakanin salimar
da 'yarta iftihal,don mahaifiya ba wasa bace
Bai tanka mata ba sai da ya ware shigar da bayanan harkokin kasuwancinsa cikin
computer laptop dinsa ,ya kasheta sannan ya rufe,ya zare farin gilashin nan nasa ya
dora a samanta,ya soke yatsunshi cikin na juna yana kallonta
"Fadeelah"yayi kiranta cikin dakakkiyar muryarsa,ta amsa masa a nutse
"Dukiya taki ce,company ma naki ne Kiyi Duk abinda like so da su mallakinki ne ba
mallaki na ba,but........akeai Abu daya da nake umartarki ki zare hannunki
ciki........za can Gara alaqa tsakanin salima da iftihal,babu ruwanki,na riga nayi
magana da yarinyar tace bata buqatarta,Ku kun isheta,so......don Allah kada ki dawo
mana da Hannun agogo baya,I hope kin fahimta?"
Ya shige bargo yayi kwanciyarsa abinsa
Duk da maganan bata yi mata dadi ba amma ta shanye,tayi alqawarin sai ta qarshe
jihadin nan
Container din kayanta da tazo a satin ta taba kayan harda saliman,kika ta dingabyi
tana sake roqarta ta yafe mata,sannan ta rows mata iftihal da aliyyu gafara,tace
tuni ita ta yafe mata,suka insha Allahu zata yi qoqari su yafe matan
Ganin Daga aliyyu har iftihal din sunqi su fahimceta,aliyyu ke fiya wa diyarshi
bakya sai ta gwada dauka matakin fiya harkarsu gaba daya,ai kuwa ranar dabiftihal
tazo gidan yin weekend dinta kamar yadda ta sabà,tana jirin"Mamee,Mamee na"fadila
tace ni ba maminki bace,kike ki nemi maminki,tunda ni ban isa na gayamiki ki ji ba
baqaramin gigicewa iftihal din tayi ba,ta dinga kuka bana bawa Mamee haquri,tace
indai tana so ta haqura to ta shirya maza yanzu driver ya kaita gun momin ta,ta
Kuma gaya mata da bakinta ta yafe mata
Haka kuwa akayi,ranar ma salima sai da ta koka din,ta Gode ma fadilan ba iyaka,ba
laid I iftihal din ta saki jiki da ita,don har zancan sure ta da Muhammad din
fadilan sukayi,sosai Salima taji dadi
Saidai bayan dawowar Aliyyu Daga office ya tambayi ina iftihal tunda yasa anan take
weekends,ya samu labari ta tafi ganin ummanta salima,fada ya dinga zabgawa,ta inda
yake shiga bata nan yake fita ba,ya bata mata rai sosai,amma tunda Allah yaga
niyyarta Kuma har muràdintà ya cika shikenan,samira ce ta dinga bashi haquri domin
itama ta fuskanci fadilan Daga baya,lokacin sunavtare fadilan na biya mata
*minhajil Muslim* da Samira ke koyarwa a makàantarta,bai ko kula su ba sai da ya
gama zazzagarshi ya wuce sashensa
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻
[1/29, 5:33 PM] My Mom: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?........*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 3*
4⃣8⃣ 4⃣8⃣
🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊
Kwana daya biyu yaso dauke mata wata kamar yadda tayi masa dif,don irin salon
horonta da ba iso kenan Kayi masa a dauke masa wutà
Sai dai inaaaa ya Kasa,ya yarda ya Kuma amince shi sadauki ne Kuma jarumi ta
kowanne Fanni na rayuwa,saidai tuni ya dade da sanin cewa shi mugun rago ne indai
bangaren abinda ya shafi Fadila ne
🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉
Tana cikin kitchen yau ita daya ce,ita dai Tun safe take jiñ kaya kayar yaran suna
ta shiri,abbun su na bada direction na inda za'a kai kowa,aslam da Muslim dama na
Egypt su na shiru shiryen shiga *jami'atu al azhar* bayan sun kammala secondary
dinsu kenan
Zuhra Islam da iftihal yasa aka kaisu gidan ummi,faruq da saddiq Kuma aka kaisu
gidan uncle abba,afrah da amrah Kuma sukayi gidan farida,sai gidan yayi tsit,baba
talatu na sashenta,samira kuwa tayi gidan su itàmà bikin qanwarta,can zata kwana
Ita kam batasan tafiyar tasu duka ta kwana bace don haka har da su take
girkin,tanayi tana mita cikin zuciyarta an kwashe mata 'yan aikin,don idan su na
gida bata yin komai banda Gyara bedroom dinta da part din abbunsu,nata bada umarni
ne da yin gyara inda aka kuskure
*part 3*
4⃣9⃣ 4⃣9⃣
👬👫👭👫👬👫👭👭👫
🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊🎊
*wannan page din naku ne HUGUMA NOVELS READERS tare da iyalanku gaba daya*
*Allah ya bar qauna ina godiya*
👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻
Ta juya don dauka abarba cikin freezer zata niqa ta hada zobo,sai riga mutum tsaye
a bakin qofa,sqnye yake da long sleeve t.shirt maroon colour wadda tayi masa dai
dai jikinsa,sai trouser baqi,idanunshi tsaye da gilashinsa nan,hannayensa duka
harde a qirjinsa,gaba daya ya zuba Mata mayatattun idanunshin nan masu shegen
maganadisu,
Tayi masa kyau matuqa da gaske,ba zai iya tuna lokacin da yazo ya sameta ba cikin
ado da kwalliya ba,haka itamq din a dan Kallon sakqnnin da tayi masa,aliyyu bai
tsufa,ko yaushe kamar ana sabuntashi,idan ka ganshi tare da su aslam sai Kayi
tsammanin yayansu ne ba wai mahaifi ba,Duk wani kyau kwarjini da farin jini nashi
sunyo shi,ginshira gaji da shan qamshi tamkar shi da su din tagwayene,shine
gamboñsu
Sai ta kawar da kanta tamkar ba yanzun suke qarewa juna kallo ba,ta duqa don ciro
abinda tazo daukan,ya saki lafiyayyen murmushin nan nasa,wato har yanzu fadilan nan
tashi ce dai,miskilar nan,mai shan qamshi jan aji da dauke kai,yana jin shima ya
kamata ya tuna Mata aliyyun nan nata, *Aliyyu Salim maitàma* mai qarfin hàlin nan
da yawan qaunarta
Kafin ta kai ga ciro abarbar taji caraf an riqo hannunta,da sauri ta dago gami da
juyowa,sai dai tuni yayi mata masauki cikin qirjinsa,yasa hannayensa ya
rufeta,kafin ta kai ga furta koma ya hade bakinsa cikin nata
Sai da ya zare mata laka baki daya,tuni tsaiwa ta gagaresu suka zube saman tiles
din kitchen,ganin yana qoqarin wuce makàdi da rawa yasa tayi qarfin halin tureshi
"Abbu so kake muyi abun kunya?,yara fa zasu iya dawowa kowañne lokaci"
"Eh shi yasa ai na korasu don kada su hanamin cin amarci da matata,ke da ki gañsu
sai after three days"
Harararsa take saidai da ka kalli tsabar qwayar idontà zaka gane cike hararar take
da qauna da bege
"Wanne amarci kuma?,mutumin dake shirye shiryen aurar da first born dinshi"
"Haka kika ce,to zamu gani?"yace da ita gami da sungumeta da hannayenshi,bai
sauketa a ko ina ba sai a fadarshi,Kallon juna suke suna murmushi cike da
shauqi,sake rungume ta yayi cikin faffadan qirjinsa yana rada mata
"Fushinki kashni yakeyi *HASKEN IDÀNIYATA*,zuciyata ràguwa ce a kanki,zan iya jure
koma amma banda lamuran da suka shàfeki,na tuba *RAYUWA TÀ*,kace *GATA NA*
itama cikin salon radar take ce masa"idan na dau ke ma wata tamkar ina hukunta
kaina ne bisa ga Kasa bin ra'ayinka da nayi,mijina Kaine *DUNIYA TA*gaba daya,na
gode wa Allah da ka zamo *uban 'ya'yana*"
Da sauri ya tari numfashinta "ni yafi cancanta na godiya ga Allah da ya rufamin
asiri ya hana inyi asararki,da haka ta faru Fadeelah na,........da tuni na dade a
kushewa ta"
Sai jin qauri suka cikin kitchen,da sauri suka rige rigen isa kitchen din
*PART 3*
5⃣0⃣ 5⃣0⃣
💘💝💘💝💘💝💘💝💘
*_I DEDICATE THIS PAGE TO MY LOVELY HUSBAND,MAY ALLAH HELP AND GUIDE YOU,I LOVE
YOU_*😍😍😘😘
Shi yayi nasarar kashe gas din,suka kalli tukunyar miyar da tuni ta qone sannan
suka kalli juna,dariya sukayi a tare,ya kama hannunta yasa cikin nashi tafin
hannun bayan ya dage girarsa
"Kwanaki ukun nan na amarci ne
Babu girki.......
Babu aiki.......
Babu hayaniya.......
Babu yara.........
Ba surutu........
*just Fadeelah and aliyyu* kawai zasu more duniyarsu"
Itama girar ta daga "wow....I like it, *duniyar Fadeelah da aliyyunta kenan ko?*"ya
gyada kai
"Yes!,yes my own"
Riqo hannunta yayi suka jero Tun Daga kitchen din,tafiya Duke very slowly kamar ba
zasu isa bedroom din ba,kowanne jikinsa da zuciyarsa ta mutu da qwayar son dan
uwanshi
*"na maka alqawarin zamowa kusa da kai duk rintsi duk wuya"*
*"na miki alqawarin dawwamar dake cikin farinciki har qarshen numfashin mu*"
*na miki alqawarin........*
*na miki alqawarin*.........
Haka aliyyu ya dinga hero mata har ta Gaza fadin koma,kukan dadi ya kufce mata,ta
samu aliyyu fiye da yadda take zato hasashe ko tsammani,tabbas
*BABU WANDA YASAN GOBE SAI ALLAH*
Tana tsaye tana Hawaye ya zube a gabanta kan gwiwoyinsa,ya lalubo qwayar idonta ya
sanya nashi ciki,ya soma girgiza kai
"Um.....um baby, *No more tears* kin manta?, *na miki alqawarin ba zaki sake kuka
ba fa har abada*"
Dai dai lokaçin da hawayen idonta suka silmiyo su na qoqàrin dinga a tiles,yayi
maza yasa tafin hanñuñshi ya tareshi,tas ya lashe hawayen kan fuskàrta
" *NURY* kukan farinciki samun ka a matsayin miki nake,irin mijin da ke wa mata
tsada da wuyar samu a wannan lokaçin"
*tammat alhamdulillah*
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
*tsira da aminci su sake tabbata ga dan gatan Allah shugaban dukkan wata halitta
baki daya annabi Muhammad s.a.w*
*ina Neman afuwa da yafiya ga duk Wanda na bata wa ko littafina ya batawa rai,duk
dan Adam ajizi ne,ba lallai Kuma mu sake saduwa bà*
*fatan alkhairi ga mahaifana*
*Alhamdulillah* *Alhamdulillah*
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
✍🏻 ✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻