Amy Adams
Amy Adams | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Amy Lou Adams |
Haihuwa | Aviano (en) , 20 ga Augusta, 1974 (50 shekaru) |
ƙasa |
Tarayyar Amurka Italiya |
Mazauni | Beverly Hills (mul) |
Harshen uwa | Turanci |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Richard Kent Adams |
Abokiyar zama | Darren Le Gallo (en) (2015 - |
Karatu | |
Makaranta | Douglas County High School (en) |
Harsuna |
Turanci Italiyanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo, mawaƙi, mai rawa, dan wasan kwaikwayon talabijin, stage actor (en) , jarumi da dan wasan kwaykwayo mai magana amma ba a ganin shi a fim |
Tsayi | 1.63 m |
Kyaututtuka |
gani
|
Ayyanawa daga |
gani
|
Kayan kida | murya |
IMDb | nm0010736 |
Amy Lou Adams (an haife ta 20 ga watan Agustan shekarar 1974) 'yar wasan fim din Amurka ce. Ta shahara a fannin barkwanci da wasannin ban dariya, ta fito sau uku a cikin jerin manyan yan matan da suka fi karbar kudi a duniya. Kyaututtukan da ta samu sun hada da lambar yabo ta Golden Globe Awards guda biyu, bugu da kari ta samu wasu lambar yabon har sau shida da kyaututtukan fina-finai bakwai na kwalejin Burtaniya.
Kuruciya
[gyara sashe | gyara masomin]Amy Lou Adams an haife ta ne a ranar 20 ga Agustan shekarata 1974, iyayenta Richard da Kathryn Adams 'yan asalin ƙasar Amurka ne, kuma a lokacin da mahaifinta ya kasance jami'i ne inda yayi aiki tare da Sojojin Amurka a rukunin sojoji na Caserma Ederle da ke Vicenza, Italiya. Ita ce ta tsakiya cikin yara bakwai da iyayensu suka haifa, tare da 'yan'uwa maza hudu da mata biyu. Bayan sun tashi daga wani sansanin sojoji zuwa wani, dangin Adams sun zauna a Castle Rock, Colorado, lokacin da take 'yar shekara takwas. Bayan barin soja, mahaifinta ya rera waka cikin kwarewa a wuraren shakatawa na dare da gidajen abinci.
Hoton Media da salon wasan kwaikwayo
[gyara sashe | gyara masomin]Yayin da yake bayanin mutum na fuskar allo, Hadley Freeman na jaridar The Guardian ya rubuta a shekarar 2016 cewa "[tana] nuna matukar shagaltuwa, da gaske amma tana da alamar magana kai tsaye da zarar ta tafi".