Jump to content

Damaturu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Damaturu


Wuri
Map
 11°45′N 11°58′E / 11.75°N 11.97°E / 11.75; 11.97
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Yobe
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 88,014 lissafi
• Yawan mutane 37.2 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 2,366 km²
Altitude (en) Fassara 371 m
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
jami'ar damaturu
Garijin federal Polytechnic Damaturu

Damaturu karamar hukuma ce kuma babban birnin jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.[1] Nan ne hedikwata inda fadar gwamnatin Jihar Yobe take wadda gwamna Mai Mala Buni ke mulkinta a halin yanzu, sannan kuma cibiyar gudanar da mulki na jahar. Masarautar Damaturu, ita ce masarautar gargajiya daya jal ta sarkin yanka mai daraja ta daya a gabadaya fadin birnin. Kebantacciyar lambar akwatin waya na birnin ita ce 620. Karamar hukumar tana da fadin kasa 2,366 2 da yawan jama'a 88,014 a kidayar shekara ta 2006. Garin Damaturu yana kan babbar hanyar A3. A alkaluman ilimin zanen kasa, birnin Damaturu ya gindayu ne akan alkaluman kwa'odineto 12°00′00″N 12°00′00″E / 12.00000°N 12.00000°E / 12.00000; 12.00000.

Fadar sarkin Damaturu mai tarihi

Damaturu ta kasance a matsayin mallaka a lokacin da turawan Ingila suka sassaka ta daga gundumar Alagarno . Hakan ya haifar da mamaye daular Bornu a shekara ta 1902 da sojojin mulkin mallaka karkashin jagorancin Kanar Thomas Morland suka yi.

Damaturu dai ya sha fuskantar hare-haren mayakan jihadi na Boko Haram a yakin da suke yi na kafa daular halifanci a yankin arewa maso gabas.

  • A watan Nuwamba 2011, sun kashe sama da mutane 100 a wasu hare-hare .
  • A watan Disambar 2011, sun kai hare-haren bama-bamai biyu .
  • A watan Yunin 2012, mahara 40 sun shiga gidan yari . Fursunoni 40 ne suka tsere sannan aka kashe mutane takwas.
  • A watan Yunin shekarar 2013 ne mahara suka kai hari wata makaranta inda suka kashe mutane goma sha uku da suka hada da dalibai da malamai.
  • A watan Oktoban shekarar 2013, mayakan sun yi artabu da jami’an tsaro tsawon lokaci tare da kai farmaki a wani asibiti.
  • A watan Disambar 2014, mayakan sun sake kai hare-hare. An ji karar harbe-harbe da fashe-fashe, an kuma ce an kona sansanin 'yan sandan kwantar da tarzoma. Jami'ar jihar Yobe ma an kai hari.
  • A watan Fabrairun 2015, wata matashiya 'yar kunar bakin wake ta kashe mutane 16 a wata tashar mota .
  • A watan Fabrairun 2020, an yi kisan kiyashi a Auno da ke kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri . Maharan sun kashe matafiya 30, sun kona motoci tare da yin garkuwa da mutane.

11°44′40″N 11°57′40″E / 11.74444°N 11.96111°E / 11.74444; 11.96111Page Module:Coordinates/styles.css has no content.11°44′40″N 11°57′40″E / 11.74444°N 11.96111°E / 11.74444; 11.96111Samfuri:Yobe State